TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 71

 7⃣1⃣






*Dedicated to maman nour, soupnass, ikra rukayyat, maman 4H,hauwa lawal,kucigaba da comments*💓






Jiki a mace ya shigo dakin tabishi da ido tanata kallonshi mamaki kawai yake bata yasha jibgarta amma bai taba yi mata wannan jina jinan ba, kenan itama watarana yakan iya yi mata haka, 


Bakin gadon amira yaje yayi tsaye yanata kallon fuskarta da yadda take nishi zuciyarshi takara cunkushewa yanajin tsanar kanshi ,ya dade tsaye yana kallon amira Aisha batace mishi komi ba yajuya yafita daga dakin tabishi da ido, 


Office din doctor ya shiga yaja kujera ya zauna yana yamutsa fuska yace "me ke damun amira? "


Doctor dake duba wani buk ya dago face yace "she's very scared and shocked abun ya girmi brain dinta ,that force her to fainted ,amma she'll be okay, "


Fahad yace "what about my wife? "


Doctor okato yakara gyara zama yace " sakamakon dukan da akamata sosai tayi miscarriage sannan taji ciwuka sosai tana bukatar kulawa da lokaci kafin tasamu lpy "


Fahad ya daga kai ya hadiyi miyon bakin ciki, 


Doctor yace "as ur family doctor I want to advise you, dukan mata baya taba kawo gyara sede yabata, mata wani lokaci they're crazy se ana kai zuciya nesa ana kaucemusu amma duka bedace dasu ba saboda they're weak , ina maka jajen rashi da kukayi Allah ya bata lpy"

(wani lokaci sekaga Christian da soft heart kuji yadda yake bawa fahad shawara) 


Fahad yace "thanks you"


yatashi yafita yanajin duk duniyar tamishi zafi, 



omer yakira abba yafada mashi suna asibity kuma ana bukatar jini ba bata lokaci segashi asibityn aka dibi nashi dana abul, aka cigaba da sawa faseelat dake kwance tana nishi, 


Duk kansu hankalinsu tashe abba yakasa yadda da abun da yake gani, 


ummi dataci kuka tagaji tacewa abba "wlh seya saketa yata bazata zauna da meduka ba, wannan shine karshen zamansu"


abba yace "kiyi hakuri asiya amma kidena rantsuwa cikin bacin rai, amma ni kaina bazanso takoma gidan shi ba"



ummi tace"hmmmmm"!



fahad dakin da akai admitting faseelat ya nufa ,akunyace ya tura kofar ya shiga wayam ba faseelat basu ummi yabi gadon da kallo zuwa jinin dake sargafe ,ya karasa ya tura kofar toilet nanma wayam hankalinshi tashe yakaiwa abunda ake dannawa for emergency bugu ya dauki kara, duk yaburkice ko 1mnt baaiba doctor yashigo da nurses biyu, sukaga gadon wayam se fahad dake tsaye kamar mahaukaci, 


fahad jijiyoyi amike yace "where's my wife? Ina matata where do you take her? "


Doctor da mamaki yagama cika shi yace "this is unbelievable, how will this happened in my hospital? "


Ya kalli fahad yace "I'm sorry sir bansan komai ke faruwa ba amma we have CCTV cameras all around the hospital zamu gano mike faruwa"


Fahad ya dafe goshi kanshi na mugun bugawa ,su ummi suka dauketa kokuwa? Yana ta tambayar kanshi, 


Doctor yadafa shi yace "meet me in my office "


Yajuya yafita tareda nurses ,hawaye suka zubowa fahad yace "meyasa zaku dauketa? Ni yadace na kula daita"


Ya fita ya nufi office na likita,likita yanata duba computer abunda yafaru akofar dakin faseelat ya juya wa fahad computer yace "take a look at them do you know them or seen them before? "


fahad ya kalli computer omer ya fito dauke da faseelat ranshi yakara baci yace "he's her brother, but saboda me zaabari sufitar min da mata a asibity su suka kawota ?yama akai suka san we are here? bazan kara kawo patient a asibitin nan ba tunda it's not safety "


doctor yajawo computer gabanshi yayi rewinding lokacin da bello yakawosu kofar dakin ranshi ya baci yaja telephone ya kira number office dinsu bello ba dadewa sega shi ya shigo yanata hada zufa, 


fuska tamke okato yanunawa bello computer yace "meyasa ka kira wadannan mutanen waya aike ka? meyasa ?"


bello yace "I'm sorry nasan yayanta ne banyi tunanin fadamishi ze zama matsala ba kuma nayi iya kokarina na tsayardasu basu tsaya ba "


fahad jiyake kamar yakaiwa bello naushi don haka ya tashi yafita ,


okato yace "meyasa baka fadawa securities ba?  U r suspended kaje sena nemeka "



Bello ya fara begging "I'm sorry sir it's a mistake wlh danasan haka zata faru da bazan kira shi ba dan Allah kayi hakuri "


okato ya nunashi da yatsa cikin nuna gargadi yace "next time idan haka tasake faruwa zaka bar nan harabada,now leave "


Bello yajuya yafita yana yamutsa fuska cikin ranshi yanata regretting kiran omer, 



Fahad nafita yashiga mota ya nufi gidan umma don besan ya zaiyi ba, a mota hawaye yake tayi duk lokacin da ya tuno ihunta da jinin da ya zuba seyaji hawayen tausayinta Sun zubomishi, 


ya samu yaisa gidan umma suna zaune suna kallon film din su bosho munafikin mata sunata dariyar yadda yake fadawa hafsa idris cewa jamila nagudu wari take seya toshe hanci yake bacci saboda tusa, kwasar dariyarsu kawai suke hankali kwance ,ya shigo main falon wuji wuji dashi riga duk jini, dukkansu faraar dake kan fuskarsu ta gushe yaje wurin umma ya zauna kasa tana kan kujera yadora fuska akan cinyar ta yasaki kuka, 


Umma tadora hannu ta tallabo fuskarshi zuciyarta na harbawa dasauri tace "meyafaru fahad jinin minene ajikin ka haka? "


yana kuka yace "umma I cheated myself na doki faseelat har tayi miscarriage "


umma dasu lady suka dau salati "innalillahi wainna ilaihi rajiun!"


Umma kamar zatai kuka tace "me tamaka da zaka  dauki wannan hukuncin? Faseelat ce fa ur love meyasa zakai haka? "



Muryarshi na rarrabuwa yace "naga pic dinta da wani awayarta I tried my best nakasa controlling kaina shine na doketa"


umma tai shiru hawaye suka zubomata na tausayin baiwar Allah, 


ya cigaba da cewa "na kaita asibity ,wani doctor yakira yayanta yafadamishi ina komawa nasamu Sun dauketa Sun tafi daita, ya zanyi ne umma? "ya cigaba da kuka, 


Su lady suna hawaye suka tashi sukabar main falon, 


Umma tasamu ta goge hawayen fuskarta tace "sunyi dede kuma Sun kyauta konice abinda zanyi kenan, banji dadi ba da dana yakasance mahaukaci me dukan mata ba don duk namiji me hankali bazaya iya daukar hannu ya daki matarshi ba ,bare faseelat yarinya me ladabi da biyayya me sonka me addini amma har kaiya cutar daita  kayiwa kanka ai don bazaka taba samun kamar ta ba "


yana hawaye yace "umma Dan Allah ki temakamin kije ki basu hakuri wlh inasonta kishinta ne yasa nai haka"



umma tace "yo kishi haukane ko kai kadai ne me kishi aduniya? Saad daya daga cikin  mubashshirina bil janna yace dazan kama wani akan shimfidar iyali na dazan sare shi da adda kuma ta wurin kaifin zansa se sahabbai sukaita mamakin kishinsa manzon Allah (S. A. W) yace shin kuna mamakin kishin saad ne? yace wlh ni nafishi kishi kuma Allah yafimu kishi gabadaya,bakai kadaine me kishi ba fahad amma ai kishi bekamata ya rabaka da hankalinka da imaninka ba har kayi kisan kai ko agadon ta kasameshi? kasan yaya suke daita ne? Shin kai baka daukar pic dasu lady dasu ramlat? , wai duka ne har ze zubar da ciki wlh fahad bakayi ba ni banda temakon da zan maka sede zan baka shawara ka koma wurin malamai kakara neman ilimi saboda da kanada ilimi wadatacce da baka aikata haka ba "


ta dauke kanshi tatashi zata haye sama ya waiwaya fuskarsa gwanin tausayi yace" umma tafiya zakiyi? "


Batare da ta jiyo ba tace"eh tafiya zanyi ko zaunawa zanyi na tayaka kukan katashi kabarmin gida "ta haye sama ranta bace, 


wasu zafafan hawaye suka zubowa fahad dama anan kadai yake tunanin samun sauki kuma itama ta hau ya dade zaune sannan ya tashi ya fita ya nufi gida, 



Yana zuwa ya danne horn bako dagawa baba tsoho na toilet yaji odar tayi yawa ko tsarki besamu yayi ba yafito da gudu yaja gate din dayake sliding ne, 


fahad da kanshi ke jikin sitiyari ya dago yaja motar cikin gida, 



Yakai kusan 15mnt zaune sannan yafito yashiga cikin gidan, dakin faseelat ya nufa zuciyarshi na harbawa tuno jinin dake kwance adakin, 


dakin a bude yake yana zuwa yayi tsaye ya dafe kofa yasa sabon kuka dakin duk jini bakyan gani, ya karasa ciki yanata kukan yayi zaman dirshan gaban gudan tsokokin dake a wurin yana ta kallonsu yana kuka, yake tuno maganar faseelat "amma kasani cikinnan shine farincikina shi nake burin gani ayanzu nabaka amanarshi karka bari wani abu yasameshi"



da kuma inda take cewa "zan haifarma baby boy kasamu freind"


Kamar dan maye yafara magana "meyasa zaka zube?inason naganka araye banyi don na cutar da kai ba, katafi kabarta she love you ur her happiness and joy why zaka gujeta? it's just an accident meyasa bazaka hakura ba..." maganganun duk gasunan yadade yana sambatu, har yakai yayi kwance agun, 


can zuwa yatashi yasamo leda ya sa hannu ya fara kwashe abinda zeiya kwasuwa yagama ya kulle ya ajiye gefe, ya cire shirt din jikinshi ya gogge abinda yasamu yafita ya dauko mofa yazo ya goge wurin sosai ya kuma sa fresheners duk da haka seda dakin yadauki kanni, 


yafita yaje can garden yayi rami ya rufe ledan da rigar yadawo ya shiga toilet yasakarwa kanshi ruwa yanata meda numfashi, yana cikin cuda jikinshi ya tuno yadda yaja faseelat daga toilet din tana cikin cuda jikinta yakai wa bango naushi yanajin haushin kanshi, wayar faseelat ta fado mai arai yayi sauri yafito ya dauketa duk ta tarwatse baxata kara amfanuwa ba, ya budeta ya cire sim dinta wanda take chart ya dauko one of his phone yasa sim din, ya sake download wats app yayi restoring duk messages suka dawo ciki, yakoma cikin chart din ta da baffa beko bude pic dinba yawuce gaba don kar zuciyarshi ta tarwatse , faseelat da taga pic din tace "baffa kayi hakuri plss bansan yaakai nai missing contact dinka ba, ya gida yasu hjya da alhaji? ashe haryanzu kanada wannan pic din yayi kyau sosai "


Baffa yace "lpy lau suke ,badole kiyi missing no dina ba tunda kinyi aure 😬 thank God ansamin rana jiya nima zan angwance "


faseelat ta tura laugh emoji 😁tace "wai dagaske ?yaakai bansaniba "


Yayi dariya yace "young girl ,ai ummi dazakiji gunta batanan nasan kuma wannan miskilin baze kiraki yafada miki ba "



faseelat ta turamashi smiling face tace "namaka murna wacece ita takaini kyau ? 🤣"


yace "kedin me kyakkyawa ce ajin karshe"



faseelat tace "muganta in dagaske ne "



yayi dariya yace"banda sheri fa "


tace "Allah aa kawai inason ganinta "



seya turomata pic din wata black beauty jibgegiya kamata😂 me dogon hanci da wawakeken baki tana da ido she's cute de 😂🙈,


Faseelat ta tura mishi "haba baffa wannan doshumar ina zaka ajiyeta 😂"


baffa yace "kambuuuu matar tawa ce doshuma?"


faseelat tatura mai "sorry sorry 🤭"


yace "ke ni banason fararen mata ni fari ita fara abun will waste, nafison baka  me kiba shiyasa seda na darje amma ai tanada kyau duba sosai inkuma Sheri ne sekitayi "


Faseelat takara kallon pic din itade awurinta batada kyau abun mamaki ma yabata yadda yake kyakkyawa amma wagga yakeso lalle so makaho ne, 


Tace " Allah yasa alheri, gaskiya tana da kyau ka gaidata kafin musan juna" 


Yace "wannan is not a villager wayayyace degree gareta  akan microbiology awani hospital ma take aiki kibari gobe innaje wurinta zan kiraki vedio call amma ta wats app seku gaisa daita ki kara ganinta sosai Allah tahadu kuma tanada hankali"


faseelat tace "ihmmmmm Allah yakaimu naganta "



Daganan se chart da yaturo mata yau wanda bata ganiba, 



"aljanah ya kk tashi? gani wurin waseela "


"zan kiraki yanzu"


Se kiran, 


fahad yasa hannu yaita bugun kanshi yana hawayen danasani "why ban tsaya ida karanta messages dinba? "


"meyasa zata dauki pic dashi? don yana cousin dinta ai zeiya aurenta donme zata sakarmishi jikina "


Yanajin wani malolon bakin ciki a makoshi yace "ya Allah ka ragemin kishinnan na zauna lpy kasamin hakuri akan dangin ta, don ban kaunar naga tana muamala da kowane namiji"niko nace insun barmaka ita ko? 


yatashi zuciyarshi na ciwo yasaka kaya ya tada salla har anyi laasar yayisu ahade, be taba adduar Allah yarage masa kishi ba segashi yau shine ke kuka yana rokon Allah yarage masa kishinsa, 


yana gamawa ya tashi yafita direct gidan su faseelat ya nufa amma gidan akulle don duk suna asibity, 


yadade yana kallon kofar sannan yajuya ya nufi asibity, 


A asibity amira ta farko a firgice, Aisha ta riketa tana rarrashi amira tana kuka take cewa "ina anty? Ni kikai ni wurin anty "suna haka fahad ya shigo ya karasa bakin gadon dasauri yana fadin "sannu princess "


amira naganinshi ta rumtse ido tai gum zuciyarta na harbawa don matsanancin tsoronshi takeji, 


Aisha dake hawaye ta kalleshi, 


Ya riko hannun amira yace "princess open ur eyes it's me ur dad "


gaf-gaf hannun amira ya dauki rawa, takara rumtse idonta yanzu in akwai abinda batasan gani befi daddinta ba, 


Aisha ta zare hannunshi tana hawaye tace "katashi kafita bata son ganinka tsoron ka takeji karka karasa rikitamin ita"


Yayi kasake yana kallonta yace "u r lying "


Ya meda hannu ya riko amira yace "amira it's me ur beloved dad"


amira tafasa kara idanunta a kulle wadda tasa seda fahad yasaki hannunta, amira na kuka tace "I don't want to see you  stay away from me"


ya fiddo ido waje "amira nine fa dad dinki bakison gani na inyi nesa dake? "


amira tace "mommy please take me to big mom house I'm scared here,"


Aisha tace "Dan Allah kafita kabarmu, badole taji tsoronka ba yadda kake dukan mu tana gani tanaji dan Allah kafita "


Fahad ya tashi yafita yanata tariyo maganganun umma da amira, wai his daughter da kullum take cewa she love him itace ke cewa yayi nesa daita ,ya shiga motar shi yayi zaune yakasa ma hawaye se zuciyarshi dake kuna, 



yadade zaune sannan ya nufi gidan mommy dan yafada mata amira ba lpy,kokadan beda niyyar fadamata abunda yafaru amma yasan she must heard it, 



har lokacin faseelat bata farfado ba daga baccin da take, dukkansu tun safe har yanzu bayan laasar ba wanda yakara sawa cikinshi komi, 




itako jamila gidan siyama tawuce tana ta kuka tafadawa siyama abinda tayi tace dan Allah taje tabata hakuri,bataso su mama suji siyama shiru tayi kawai jin abinda hjy keyi da tsiyar da jamila tayi, 


seda mijinta yayan mamar jamila yadawo cin abinci sannan siyama tafadamishi abinda jamila tayi tace anjima ze kaisu su bata hakuri, 


Ranshi ya baci yakira jamila ya rufeta da fada "ke dan uwarki saboda yana kai dare be dawo ba shine zakije kiwa hjy wulakanci, ke wlh a aljanna kike in kikaji matsalolin uwayen mazan wasu sakarai shasha hakanan zaki rusa mana zumunci, kika ma kanki wlh in kuma so kike ki zama karamar jawara to tashi kiban wuri "jamila ta tashi tana kuka tafita, 


Cikin kwantar da hankali siyama tace "kayi hakuri yarinya ce nangaba ko ance tayi bazata yi ba,Allah  yasa hjyar ta hakura "


Tai shiru tana tunani don tasan hjyar ma bata kyauta ba kuma zatai mata magana koba yau ba ,



Motarsu khalil tayi nisa da tafiya sunkusa kai batsari tunda yashiga counter dinshi kawai yake latsawa yana lazimi dede gadar wani kauye kurmiyal wata mota ta kwacewa wani driver tazo tabanki motar su khalil karfen da yakare gadar ya balle duka motocin suka afka cikin gadar akife , suna fadawa suka kama da wuta gabadayansu, 


Kafin mutane su taru mutanen ciki tuni sun kone koda mutane sukazo bakajin sautin komi se fasss! Dasss!! Tatasss!!! Jikin mutane na fashewa, mutane sunata zuba kasa da ruwa kafin motar kashe gobara tazo , daga katsina zuwa kurmiyal akwai yar tafiya don sunfi kusa da batsari,shiyasa abun yadauki  mintoci


wutar bata mutu ba har yan kwana kwana sukazo aka kashe wutar ,


ranar yan kauyen kurmiyal sunga tashin hankali tsoron Allah yakara shigarsu wadanda suka manta da Allah ranar Sun tunadashi sun koma agunshi, ga warwakin sunyi baki kirin wasu Sun fashe wasu Sun kwarkwarje wasu hanji awaje, yara, jarirai, maza, mata, samari da yanmatasa, 


kusan rai 15 don waccan motar j5 ce, 


ba jimawa police suka zo aka daukesu zuwa matuary kafin asamu danginsu dukkansu sun mutu kurmusss, 



dandanan gidajen radio suka fara baza labarin, 


Hjya aminiyar radio tana zaune tana sauraren radion taji hadarin gabanta yayi mummunar faduwa, tai sauri takashe radion, 


Ba arziki tana rawar duwawu ta shiga daki tana haki ta dauki waya takira mamar jamila, 


Mamar jamila dabatasan abinda ke faruwa ba ta dauka da sallama hjy batako amsa ba tace "khalil yaiso nan? "


mamar jamila tace "a, a khalil bezo ba da yataho.... "bata ida magana ba wayar ta sullube daga hannun hjy, 


Ta zame kasa zaune saboda kafafunta daketa rawa, ta dora hannu akai tafasa kara "nashiga ukku nabani na lalace wayyo Allah khalil dina ya mutu ya tafi yabarni"hawaye kamar famfo suke zubarmata ihun da take ta rafkawa yasa seda makwabtan ta suka shigo gidan suka rirriketa suna tambayar baasi, 





Allah sarki rayuwa in Allah yaso cikin kiftawar ido se kaga duniyar ta zama empty , mutum ba abakin komi ba amma munsamu duniya mun shan take ko tunanin mutuwar ma bamayi kamar anan zamu dawwama,mun manta kiyama munata tsiya,ya Allah ka kyautata rayuwarmu kasa mucika da imani kasa muyi kyakkyawan karshe amin, 







*ya ubangiji ina rokon ka kajikan dukkan musulmai maza da mata ka musu rahma kajikansu domin kai mai rahma ne me jinkai*😭😭😭   




Post a Comment

0 Comments