TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 58

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 5️⃣8️⃣

________

Tun around goma na safe Safeerah ta isa squadron cikin farinciki tana jiran saukar jirgin su Abideen, har kusan sha ɗaya saura amma shiru bata ji ɗuriyarsu ba, wani kujera ta samu ta zauna tana ta juya wayarta a hannunta tana jiran isowarsu. Kamar da wasa ta fara jin ƙaran propellern jirgi nan da nan ƙura ya buɗe koina, da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta kafin ƙasa ya shige mata ido, sae bayan da jirgin yyi landing ta buɗe fuskarta ta miƙe nan da nan sojoji suka cika filin suka yi forming layi a jere a jera, ƙofar na buɗewa ita dae gawawwaki taga an fara fitowa dasu, take taji zuciyarta na tsinkewa ga faɗuwar gaba da takeji, gaba ta ɗan ƙarayi tana kallon fuskokinsu tana fatan bbu mijinta a ciki duk da zae zamo abun alfahari agareta koda ace mijinta ya rasa rayuwarsa a yayinda yake neman cetowa dubunnan rayuka ƴan cinsu amma ba a yanzu ba gaskiya saboda tafi kowa buƙatarshi a yanzu, tana a tsaye amma har hawaye sun fara cika mata idanu. Tsaye Major General Sani Tanimu yyi yana kallon wata kyakkyawar halitta dake a tsaye cikin black abaya da tayi matuƙar yi mata kyau ga yanda ta sake fitar da hasken fatarta, gashi ba dae diri ba dan basu ɓoyu ba, haka kawai MG ya fara fatan ace mijinta yana cikin matattu koda waye kuwa idan har zae iya mallakar ta koda kuwa na kwana ɗaya ne, har wani lashe leɓe ya fara yana cin wani excitement tun daga cikin ƙashin jikinsa har zuwa ɓargonsa. 


Daga cikin jirgin kuwa Beta ne riƙe da Abideen dake sanye da drip a hannunsa, wani kallon banza Abideen ya watsa wa Beta da yyi mugun tsoratar dashi tunda 15hours ya kusa ya cika kuma har ya fara affecting ɗinsa, ga idanunsa sunyi wani mugun ja kamar an kunna garwashi, tsaye Abideen ya miƙe tareda fincike cannula dake hannunsa nan jini ya tsinke ya fara zuba tun daga cikin jirgin, shi ta window ya hangi Safeerah dan ko a ina ya ganta sae ya shaida hakan yasa burinshi ɗaya kawai ya nuna mata cewa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar mata ya dawo da ransa, ji yyi kamar ana cikwikwiye masa zuciya amma hannu kawai yakai ya ɗan taɓa ƙirjinsa kafin ya sauke ya fita daga jirgin. Lokaci ɗaya duk sojojin dake gurin suka sara mishi, MG ne kawai bae sara masa ba tunda shi ogan sane har yanzu, ko kallon martabawar da ake yi masa bae gani ba bare yasan ana yi ma, wani murmushi ne ɗauke a fuskarsa da kuma kwalla cike da idanunsa yana farincikin ganin matarsa bayan lokaci mae tsayi da ya ɗauka ba tareda ya saka ta a ido ba, takowa yyi cikin wahala yana ƙarasawa gurinta kusan ma jan ƙafarsa yake saboda jin yadda ƙarfinsa ke narkewa, da sarfa ta fara takawa tana ƙarasawa inda yake, sosai tayi farincikin ganinsa dan har ta fara tunanin bazae cika alƙawarinta ba sae dae a kawo mata gawarsa, farinciki sam bae bari ta ga jinin dake zuba daga hannunsa ba, jin baze iya ƙara taku ko da ɗaya bane yasa ya tsaya kawai ya buɗe hannayensa, tana ƙarasawa ta wani rungumeshi cikin tsabar kewa da ƙauna, sosai sojojin abun ya birgesu kowa murmushi ta fara bayyana a fuskarsa amma badda mutum ɗaya. Sosai Beta yyi farincikin ganin two lovers ɗin a tare amma yasan ya kamata Abideen ya samu taimakon gaggawa, sosai hawayen idanunta suka fara zuba cikin farinciki nan takai hannayenta ta zagaye su a bayansa, sakinta yyi ya kalleta yace, "Na cika alƙawarin, I love you too!" Yana gama faɗin hakan jini ya fara fita daga bakinsa tana kallon yanda idanunsa suka juye suka rufe sae ya zube a gurin. 


Cikin horror tayi tsaye tana kallonshi a ƙasa ga jini daya fara zuba a gurin gaba ɗaya dan har ta hancinsa jinin yake zuba, ƙasa tayi tana kuka mae ƙara sosai tana taɓa shi tana faɗin, "Yaa Abideen ka tashi! You promised you'll come back safe!!!" Ai sojojin nan basu yi wata wata ba aka ɗaukeshi sae asibiti, harda ita ake tura stretcher ɗin zuwa ICU a waje aka takatar dasu nan nurses suka shige dashi ciki likitoci kuma suka fara aikinsu. Kafin kace mae sae ga Sadique ya ƙaraso da Ya Jamilah, Safeerah ce ta kira Ya Jamilah amma bata iya ce mata komai ba sae dae sunan asibitin da ta faɗa mata ta kashe wayar da kuka ne ya nemi kwace mata, zaune tayi hannunta a dafe da goshinta tana adduoi, a gefenta Ya Jamilah ta zauna tana lallashinta kuma duk abunnan da akeyi rundunar sojojin nan yada zango suka yi a asibitin nan dan yanzu kam an tabbatar da cewar Abideen yana da rank ɗin BG a ƙasa kuma dole su kasance a tareda da shi ko yaushe saboda security. 


Doctors ɗin sun ɗauki kusan 3 hours kafin suka fito ɗauke da murmushi a fuskarsu, Safeerah take jiransu suka ƙarasa gurinta suka ce, "Congratulations, he pulled through! He's one strong man!" Murmushi tayi sannan ta fara jerawa Allah godiya, ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "Can I see him?" Girgiza kai Dr yyi yace, "No! Ya kamata ya huta yanzu ki bari sae ya tashi sae ki ganshi!" Kai ta ɗaga kafin ta koma ta zauna tana sake godewa Allah, zama gefenta Ya Jamilah tayi tace, "Kije gida ki shirya kiyi girki sae ki dawo nasan zae tashi zuwa time ɗin!" Farincikin sake haɗuwa dashi kawai yasa ta miƙe bbu ko musu, nan sojoji biyu suka kaita gida, tana isa ɗakinta ta wuce ta ajiye kayanta kafin ta koma kitchen ta ɗaura kunun gyaɗa, tana gamawa ta saka a flask da sauran delicious ɗin da ta dafa masa na taransa ɗazu. Wanka tayi ta chanza kaya zuwa wata sky blue material da tayi mata kyau sosai, tsab ta sake gyara gidan kafin ta haɗa kayan da zasu yi amfani dashi overnight a can. Tana gamawa ta fice waje aka mayar da ita asibitin, can ta tarar da Ya Jamilah kan darduma da alama sae lokaci take yin sallar Azahar dan kusan biyu da rabi ne yanzun. Abinci suka ci kafin suka zauna zaman jiransa ya farka, Ya Jamilah na can kwaryar ɗaki har ta ɗan fara gyangyaɗi ita kuma Safeerah ta samu guri a gefensa tana kallon handsome face ɗinsa. Hannunsa ta ɗauka cikin nata tana murzawa a hankali ga wasu hawaye sirara dake zuba daga idanunta, saurin goge su tayi kafin ta cigaba da zaman jiransa har zuwa lokacin da zae farka. 


Sae can around taran dare ya farka kuma ko daya farka wani matsanancin ciwon kai yaji yana damunsa gashi yanda yake jin kamar anyi masa duka dan jin baya da karsashi yyi ko kaɗan ga kuma zuciyarsa da yake jin kamar ana sukanta, wanko fuska Safeerah tayi sannan ta kalle fuskarta jikin mirrorn bayin kafin ta buɗe ƙofar ta fice, tana mayar da ƙofar ta rufe tayi tsaye tana kallon wanda yake a zaune akan gadon asibitin, sakin mayafinta tayi tana ƙara taku gaba, murmushi yyi mata tareda buɗe hannayensa, da sauri ta ƙarasa gurin ta rungumeshi kyam a jikinta tana murmushi, wani sautin, "Ouch!" Ya sake jin yadda ta ɗan bugi ciwonsa da ɗan ƙarfi cikin rashin sani, tana sakinshi ya jawota kan jikinshi yana kallon fuskarta yana jin kewar taste ɗin lips ɗinta, lashe lips ɗinsa yyi kuwa kafin ya manne lips ɗinshi da nata ya fara tsotse su cikin kewa, jin cannula dake hannunsa na neman kawo masa cikas yasa ya fincike shi nan ma jini ya fara zuba amma shi ko a jikinsa dan ji yake kamar idan baeyi kissing ɗinta ba mutuwa zaeyi. Suna cikin haka ƙofar ɗakin ta buɗe sae ga Ya Jamilah da Dr sun shigo ciki, ita Ya Jamilah yanzu harkar Abideen da Safeerah ya dena bata mamaki sae dae tsoro amma mae zata ce musu kawar da kai gefe tayi tana jin kunya tunda su sun dena jin kunyar sae dae a ji masu. Dariya likitan yyi yace, "Easy there, idan kana yin haka ai bazaka warke ba, stitches ɗin ciwonka zasu iya buɗewa. You have to be careful!" Cikin kunya Safeerah tayi zumbur ta miƙe ta matsa can baya ta bar likitan yyi aiki amma idanun Abideen na biye da ita kamar an ɗinke idanun da jikinta, likitan dae bae ce komai ba ita kuwa Ya Jamilah jakarta ta ɗauka tayi masu sallama ta fice abunta ta basu guri kafin suyi wata katoɓarar a gabanta su barta da jin kunya, sae da doctorn ya gama yi masa komai ya gyara masa drip ya fice abunsa ya barsu su ci kansu.


* Hehe! Ana buƙatar privacy kuwa!🤭😁🥂

* Don't forget to drop your votes!^‿^♡


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments