TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 38

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 3️⃣8️⃣


_______

Shiri yyi cikin riga fari da ta kama jikinsa sosai tana exposing hard chiseled muscles ɗin chest ɗinsa da black wando, car keys ɗinsa ya ɗauka ya fice daga gidan ko sallama bae yi mata ba, Garrison ya wuce abunsa cikin kayan gida, a can ya tarar da LTC suka sake yin magana inda yake sanar da cewar baze sake zuwa Garrison ba har zuwa lokacin tafiyarsa tunda dama week ne kawai ya rage masa kafin tafiyar, ba yadda LTC zai yi hakan yasa ya yarda inda Abideen yasa kai ya fice daga Garrison ɗin.


Gidansu Sadique Abideen ya wuce yana neman magana yana yiwa Sadique faɗar cewa ya kamata yyi aure, shiru Sadique yyi yana kallon Abideen kafin yace, "Wai kai yaushe kayi auren da har kk neman cemun turzuru?" Dariya Abideen yyi yace, "Toh ba tuzurun bane? Ji ba duk ka bushe ya kamata kayi aure ko za'a fara kula da kai mae kyau.." dariya Abideen ya sake kwashewa dashi, sae a lokacin Sadique ya kalli Abideen yaga da gaske yyi haske gashi har saje ya fara ajiyewa duk da gidan soja ba'a yarda amma da yake jan wuya ne ya raina ƴan Garrison ɗin shine ya fara bari amma dole zai aske nan da zuwa ranar tafiyarsa mission. "Tashi muje kaga Amarya treatment!" Dariya Sadique yyi yace, "Ji maganar banza! Watan ku nawa zaka wani ce amarya! Ai ta tsofe.." dariya Abideen ya bushe da ita yace, "Toh wallahi ni a gurina sabowa take fil a leda, malam ka biyo ni muje ta ci girkin amarya naga kamar an gaji da ciyar da tuzuru a gida duk jibi takeaway, ɗakin ma ko gyara.." dariya Sadique yyi yace, "Eh naji dae amma ai a haka kk zuwa ɗakin da bbu gyaran ai" taɓe baki Abideen yyi yace, "Idan kayi aure zaka samu mai yi maka aikin ai amma ya zanyi tunda ina son ganin Abokina! Muje na gaishe da Mama na jima ban duba ta ba.." miƙewa suka yi suka fita daga part ɗin Sadique dake a waje kafin a shiga cikin gidan, gidan mae kyau ne sosai tunda baban Sadique ɗan kasuwa inda Sadique kuma yake business ɗin siye da siyarwa na manyan motoci a Kaduna amma da yake ɗan duniya ne bai cika zuwa ba sae lokacin daya ga daman zuwa. 


Cikin gidan suka ƙarasa nan suka ga Mama da Ansar suna zaune a parlour suna hira, gaisawa sukayi da Abideen inda ya gaishe cike da girmamawa itama ta amsa cike da fara'a tana sha'awar abotansu dan tun daga Primary school kuma har yanzu basu watsar da ita ba, kallo ɗaya Sadique ya watsawa Ansar yyi saurin cewa, "Ina wuni Yaya Sadique, Ina wuni Yaya Abideen.." amsawa Abideen yyi da fara'a sosai kamar bae taɓa hade fuska ba, kallon Mama Sadique yyi yace, "Wai yaron nan bae koma ba har yau?" Dariya Mama tayi tace, "Sadique wai meye naka da yaron nan ne? Yaushe yazo ma har kk so ya tafi? Ummansa aiki yyi mata yawa shys ta barshi a nan!" Taɓe baki Sadique yyi yace, "Ke dae Mama son yara ne dake amma ke daya kamata ki huta.." dariya Mama tayi tace, "Sadique yaron da ya girma sosai har shekara 10 wani sa magana zaiyi, kaima dae idan ka haihu zan riƙe naka ai.." dariya Abideen da Mama sukayi inda Sadique ya haɗe fuska jin kamar za'a sake yi masa maganar aure, jayo Abideen yyi suka fice daga parlourn inda a tsaitsaye Abideen yyi mata sallama suka fice daga gidan. Motar Abideen suka shige wai Abideen a dole zai kai Sadique gidansa cin girkin amarya. (Nace ƴan kishin basu nan yau kenan!😂🤭)


Abideen na tafe ga Sadique na biye masa baya har suka shiga cikin parlourn, wani ƙamshi ne ya daki hancinsu su biyun, gida ya sha gyara sae ƙamshi yake dan Safeerah bata wasa da gyaran jiki da na gida, tana daga kitchen tana haɗa fruit salad taji ƙarar ƙofa kuma tasan Abideen ne, sanye take da wata doguwar riga na atampa mae blue, fari, ash da black a jikinsa, ɗauri ne ta buga a kan nan gashi ta sake gashi. Parlourn ta nufo kanta a ƙasa tana tattare rigar da tayi tsayi da ɗan yawa tana faɗin, "Ya Abideen! Shine ka fita ko sallama bbu.." cikin shigar shagwaɓata faɗa hakan har ta ƙarasa parlourn, tana isa taga idanun mutum biyu akanta da Abideen da Ya Sadique, tsuru tayi da idanu tace, "Ya Abideen sannu da zuwa, Ya Sadique ina wuni!" Shiru Abideen yyi jin kasala tana neman saukan masa bayan yanda yaji tana neman yi masa shagwaɓa wato bata gama da safen ba shine zata ƙarasa yanzu.. 😝😅


Sadique ne kaɗai ya amsa mata nan ta miƙe ta koma kitchen, Allah Ya sa ta ɗauko mayafi amma sae ta ajiyeshi a kitchen ɗin dan tasan halin Abideen da kishi, ɗan sakaya veil ɗin tayi ta kai masu ruwa sae kuma ko koma ta jera masu abinci a dinning table, ƙarasawa suka yi nan tayi serving ɗinsu sannan ya wuce ɗakinta a upstairs kunya kamar zai kashe ta dan tun ɗazu ta lura da idanun Abideen a kan ta kamar yana jiran tayi abu, ɗakinta ta koma tayi zamanta tana danna wayarta tana hira sa Safna a chat.


💬Safna: Wai kin karanta littafin nan kuwa?

💬Safeerah: Aah, amma zan karantashi yau InshaAllah! 

💬Safna: Toh Allah Ya baki iko😏

💬Safeerah: Ameen😅! Ya jikin Umma?

💬Safna: Ta warware sosai 

💬Safeerah: Allah Ya ƙara mata lafiya, bara na tafi. Ya Abideen yazo da friend ɗinsa...

💬Safna: Ai ko dae, tashi maza...


Tana ganin reply ɗin Safna tayi murmushi ta miƙe zata fita dan ta daɗe sosai kuma yaci sun gama, har ta kusa kai ƙofar taga Abideen ya shigo da sallama a bakinsa, mutuwar tsaye tayi dan ya kashe mata jiki ganin yanda rigar jikinsa ke nuna muscular physique ɗinsa, kasa motsi tayi har ya ƙaraso gurinta, fusgarta yyi ya manna ta da jikin bango ɗakin, dangerously close ya matsar da fuskarsa har tana jin numfashinsa na sauka akan fuskarta, lips ɗinta da ta manne da juna yake ta kallo tun ɗazu yace, "Manne bakin me kike yi tun ɗazu?" A hankali ya faɗi hakan amma bashi ya hana zuciyarta fara bugu da sauri ba, kamar jira take yyi magana aikuwa ta sake bakin, sae ga kumburarrun lips ɗin nata da suka zama very succulent and luscious akan da da suke ƙananu, tana sake baki kuwa ya chafke su da nashi ya shiga kissing ɗinta tareda kamo kanta yana moving ɗinta yanda yake so, mayar masa tayi da kiss ɗin tayi kuwa wanda ya sake zautar dashi, jin numfashinta na barazanan ɗaukewa saboda sun daɗe yasa ta fusge kanta tana mayar da numfashi, wani kallan kallo Abideen yake yi mata kamar wani mayunwacin zaki.


Kallo ɗaya ya ƙara yi mata ya juya ya fice daga ɗakin, a hankali taji ranta yana ɓaci, yanzu ba tada privacy kenan tunda ya balle mata lock ɗin kofar gashi ya kawo abokinsa kuma ko faɗi mata bae yi ba, yanzu inda wata shigar ce a jikinsa har Abokinsa ya gani sae yace zai ɓata rai kuma fah, ai ya cancan ta ya riƙa faɗa mata abubuwa ko dan ta kwana, tsuka ta ɗan sannan ta fice daga ɗakin, sallama Sadique yyi mata inda itama tayi sallama nana yake cewa, "Amarya girki yyi daɗi, Allah Ya karo zaƙin hannu.." murmushi tayi wanda ya sauka a daidai idon Abideen, ɗauke kai yyi sannan ya fice daga gidan tareda Sadique ɗin da alama shi zai maida sa gida, suna shiga mota Sadique yace, "Kai Alaji ai dole nayi aure wannan kulawa haka???" Dariya Abideen yyi yace, "Aah, da kar kayi ka zauna a tuzuru.." dariya Sadique yyi yace, "Habaa! No going back wallahi.." a haka suka cigaba da hira a hanya dae Abideen ya tsaya ya siya carton ɗin Yoghurt biyu da basket ɗin fruits biyu aka saka masa a boot suka wuce gidansu Sadique, suna isa Sadique yyi masa sallama inda Abideen yace, "Saƙon Mama yana boot, ka shigar mata!" Kallon banza Sadique yyi yace, "Wa kace ya shigar, kai ka shigar mana kaga tafiyata. Thanks for the ride!" Yanda Abideen yyi da fuskarsa kafin yace, "Dan Allah Sadique kaga sauri nake yi, ana jira na a gida.." yasa Sadique bushewa da dariya sannan ya buɗe ya ɗauki carton ɗaya da basket ɗaya ya riƙe, gaban Abideen ta tsaya kafin yace, "Kayi mata a hankali kar ka ragargaje yarinyar mutane Abideen!!" Wata dariya Sadique ya bushe da ita har yana duƙawa wanda yasa few mutanen dake gurin suka fara juyowa suna kallonsu, taɓe baki Abideen yyi yace, "Ni bana magana sa mahaukaci.." dariyar abunda ya faɗa yyi ganin Sadique ya haɗe fuska sannan ya taka motarsa ya bar gurin yana yiwa Sadique sign ɗin zasu yi waya, sae da Abideen ya bar gurin Sadique ya sake kwashewa da dariya sannan ya shige cikin gidan riƙe da kayan da Abideen ya haɗa sa da su, ko daya wuce mae gidan gidan shima dariya yake yi yana kaɗa kai dan bbu abunda bae ji ba, haka indae mutum yana tare dasu zaiyi ta shan dariya...


Gidansu ya wuce daga nan ya faɗa part ɗin Hajiya kusan cikin sanɗa dan baya so ya ga kowa shi gurin Hajiya ya zo, gaisawa suka yi cikin farin cikin ganin juna nan Hajiya ke sanar dashi, "Dazu wannan yaro Sammani ya kawo mani Carton ɗin Yoghurt da basket ɗin fruits kuma nasan aikin kane! Allah yyi maka albarka ɗan nan Ya albarkaci zuri'arka.." murmushi yyi tayi tun daga lokacin da Hajiya ta fara yi masa addua. Bae jima ba yasa ƙafa ya fice daga gidan, a hanya yyi sallar Ishaa saboda nisan dayake tsakanin gidansu zuwa gidansu hakan yasa yyi a wani Masjid dake hanya kafin ya kama hanyar gidansa, guards ɗin sane suka shigo da kayan boot ɗinsa suka ajiye a parlour inda da kansa kai mata kitchen ya bar su anan. Ganin bae ji motsin ta ba yasa ya nufi ɗakinta, ba ƙaramin jin daɗin rashin lock ɗin ɗakinta yake yi ba saboda shi yake da upper hand akan haka kuma yana samun advantage. 😁🤭


Drop your votes lovely people! 😘✨️

Don't forget to drop your comments about what you think!🥂


^_^


*_khanoum_ on Wattpad for more amazing and cool stories!😉🥂💕


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments