TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 91-92

   _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey 🖋_ 


    *(Yar mutan kankia👸🏻)*  


   





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍``` 



91&92



"Mama wai ya maganar auren na da Abbu yace, zaiyi man har yanzun ango bai zo ba kuma bikin saura sati haka za'a kaini gidan miji bai ɗoukin gani na."? 



"Hikimatu ina sane da haka, karki damu Hikimatu dole Hakim ya soki ko ta wace hanyane, kedai ba gurinki ya cika ba, ko kin manta bakoye nawa muka bi kafin mu samu asiri ya hau Abbunki ya yarda da zaije ya nema maki auren Hakim."? 


"Mama wallahi ina san Hakim kan Hakim ina iya kashe mutu, wallahi sai na raba Hakim da Hakima ai boka yace man Hakima ita ta ɗauke man hankali shiyasa baiyi ma ko wace mace kallon arziki, to wallahi Mama ina shiga gidan Hakim zani rabashi da matarshi ba ma matarshi ba harta uwarshi sai na rabasu, dan Hakim nawa ne ni ɗaya, dan haka ni *GIMBIYA HIKIMATU* na dauki alkwarin raba Hakim da kowa nashi nayi wannan alkwarin Mama."



"Tabbas Hikimatu kinsha Nonona, naji dadin maganarki ina san naga mutun mai zuciya dan haka karki kuskura ki ɗaga ma kowa, duk Wanda ya nuna mako yatsa kema Ki nuna mashi ban yarda Ki zauna lafiya da Gimbiya Hakima ba, Ki fidda ta a gidan wannan shawarace na baki ni *GIMBIYA BINTA*, karki manta Hikimatu ni nan baiwace a gidan nan, Amman bala'i na sai da na shiga na fita na zama matar Sarki Abubakar gashi har na haifeki, kuma na rabashi da kowa nashi dan haka inasan kema idan kika shiga masarautar zaria Ki raba Hakim da kowa nashi sannan ki haifamai magaji haka nike bukata daga gareki."



"Shiyasa nike sanki Mama, Ina alfahari da kika zamo mahaifiya a gareki, Mamana kwantar da hankali koda na taida Hakima tana ɗauke da cikin Hakim ni Gimbiya Hikimatu sai na zubda shi har lahira dan ni yafi dacewa da na haifama Hakim ɗ'a wanda nan gaba zai gaji masarautar zaria, nayi wannan alkwarin Mamana."



(Wata sabuwa 😳 ita kuma Gimbiya Hikimatu da da salon da zata shiga gidan Hakim kenan😰😭) 


______________ 



"Maryam wallahi nagaji da magangunan da Fulani take bani, baki ji yanda nike jin kaina ba, wallahi jiya kasa bacci nayi wani magani da Fulani ta bani dan wallahi har sai da nasha kuka na kafin na samu bacci ya kwasheni."



Hahhahhha! "Hakima wallahi ki bada kai bori ya hau, dan wallahi idan baki ba Yaya Hakim hanya ba akayi komai aka wuce wajen amaryashi na shigowa za ta bashi abunda ke kika hanashi tunda ke baki so ai ita naso."



"Maryam kin san bani boye maki komai nawa, keɗin ƙawatace kin san nasa gaya maki a da bani son Hakim na tsaneshi ko."?... "Eh hakane Hakima bani ɗaya had ta su Maryama sun san baki san Yaya Hakim baki kaunarshi."



"Hakane ko gaskiya Maryam.".. Hakima tace tashi tayi tana zagaya bedroom ɗin ta ruwa ta ɗauka tasha sannan ta numfasa tace, "Maryam yanzun ina son Hakim ina kaunarshi, amman bansan ya zanyi ba duk da ina iyakar kokarina na ganin na shawo da hankalinshi a kaina."



"Alhmdulillah, Allah nagode maka Hakima da gaske kina son Yaya Hakim."? 


"Wallahi Maryam inasan Hakim sosai maiye mafita Maryam."? 



"Mafita ɗaya ce Hakima ai yanzun gobe ne za'a kawo Amarya ko."? 


"Eh gobe ne ɗaurin aure Hakim, Maryam wallahi ji nike kamar nayi hauka."... "To shikenan idan kin yarda yau za'ayi komai a wuce wajen amman idan kin bani haɗin kai daman dare yayi."




"Eh na yarda Maryam.".... Magana ta raɗama koni bansan mai tace ma Hakima ba naga kawai suna dariya sannan suka tashi su duga biyun suka shiga kitchen suka fara girki Hakima ita ke sauwa ita kuma Maryam tana haɗa juices, haka suka gama sannna suka fito, tare suka ci da Maryam sannan ta tafi gida ita kuma Hakima ta shiga wanka ta shirya cikin ƙananan kaya masu kyau doguwar rigace tasa iyakarta cinya sannan ta baza gashinta baya, ɗakin Hakim ta shiga ta haɗa mashi ruwan ka sannan ta fito, tana fitowa yana dawowa bata kyaleshi ba tadai ce mashi sannu da zuwa sannan ta shiga kitchen ta cigaba da fiddo abinci shi kuma Hakim ya shiga room ɗin shi wanka yayi ya shirya sannan ya fito cin abinci zuba mashi tayi sannan itama ta zuba suka fara ci bayan sun gama ta wuce room ɗin ta ta sake wanka dan wanka tayi na mutuncin ta fito ta fara shiryawa tana cikin shiryawa taga Hakim ya shigo room ɗinta direct wajenta ya nufo fisgota yayi yana manna mata kiss ta ko ina, cewa take "Hakim maiye haka baka laf.... Taji ya haɗa bakin su waje guda yana yi mata wani irin kiss wanda take ya mantar da Hakima duniyar da take ciki daman abunka da tana hannu sai ta fara biyema Hakim, murzata yake san ranshi itama baye mashi tayi suna ta murzar juna wani kallar numfashi suna fitar da sauti, tun suna tsaye har Hakim ya ɗauke ta ya sauketa bisa gado rumfa yayi mata da faɗanɗan girjinshi nan ya cigaba da murzata tun  Hakima najin dadin abun har ta fara yi ma Hakim nisa dan Hakim yayi nisa bayajin kira ni Jameey da naga abun ya girmi tunani na kulle masu kofar na  haɗo yan tarkacena na kama gabana nace masu asuba ta gari🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️. 




Washe gari Hakim da kanshi ya taimaka ma Hakima tayi wanka ta gasa jikinta sosai yanda ya kamata dan bata sa san jiki ba ta gasa jikinta sosai sannan ta fito tayi sallah tana bisa abun sallah tana azkar Hakim ya shigo ji tayi anyi sama da ita cewa tayi, "wai maiye haka haba mana duk cin zalin ɗina da kayi bai isheka ba har sai ka dawo kasake cucata."



Tunda take maganar  yake kallonta, dariya yake yi mata sai da ya gama dariyar shi sannan yace, "haba Jewel yanzun ni zaki cema naci zalin ɗinki bayan haƙina nazo na ansa."


"Ya isa haka."... Hakima ta faɗa cikin kukan wasa dan ita kaɗai tasan yanda take jin jikinta gashi kuma yazo yana niyar ɓatama rai, dariya ya cigaba da yi sannan yace, "wallahi Hakima ina sonki, ina kaunarki please i beg you Hakima ki soni ko da kadan ne, ki taimaki dan almajiri."... Yace yana langwabar mata dakai alamun ban tausayi, wani dadi ne ya ziyarci Hakima wai Hakim ne yake gaya mata kalmar so, Hakim ɗin da tasan baisan ta bai kaunarta amman yau ita yake roƙar ta soshi, Allah kenan tana cikin wannan tunanin taji yace, "Hakima gani gaban na duge ina neman soyayyarki Hakima please Hakima duk abunda ya faruna tsakani na dake a baya muyi fecing abunda zai faru gaba amman karki manta Hakima ina sonki kuma ba sai wannan abun ya faru a tsakaninmu ba a jiya naji ina sonki Aa na fara sonki tun randa idanuna sukayi gamo dake, amman na kasa gane hakan sai daga baya, baki ce komai ba." 



Kallonshi ta kama yi sai da tayi kusan 6min tana kallonshi sannan ta kwanciyar ta, ta kyaleshi ba ta ce mashi komai ba, cewa yayi, "please Jewel ibeg uh karki hukanta da laifin da nayi maki a baya na roƙeki zan jure ko wani hukunci daga gareki amman karki juya man baya karki kujeni domin kece rayuwata Jewel."



Sai da ta numfasa sanann tace, "naji Hakim ka tashi ka tafi please ina bukatar na huta, kuma ko ka manta yau ake kawo maka sabuwar amarya kaga ba abunda zanyi maka tunda yau za'a kawo maka sabuwar amarya dan haka dan Allah nima na roƙeka ka tashi ka fita ina bukatar hutu."



"Naji zan barki ki huta nima ai ina bukatar na huta dan haka tare zamu kwanta dake kuma kisani ina sonki ina kaunarki ba zan daina sonki ba har abada.".... Bude baki tayi zatayi magana yayi saurin haɗe bakinsu waje  ɗaya yana aika mata da wasu hotskiss, nidai Jameey da naga lamarin yana neman ya wuce kiss na kulle masu kofa na nace dai Prof Hakim karda ka manta yau ake kawo maka sabuwar amarya 🤪. 





______________



Yau aka ɗaura auren *HAKIM ABDULMALAK DA AMARYARSHI HIKIMATU ABUBAKAR*, akan sadaki naira dubu ɗari da hamsin, ango Hakim shi dai bai san wani yanayi zaice yake ciki ba, dan shi ba farin ciki ba kuma ba baƙin ciki ba, bayan angama ɗaura auren suka ɗauko amaryarsu sai gidan mijin ta, bayan angama komai kowa ya watsi ya kama gabanshi, kamar yanda al'adarsu take haka ta kasance sai da Hakim ya ɗauki Hikimatu suka je gaida kowa  shashen sannan suka dawo gida. 



Tunda Hakim ya fita Hakima take kwance bata lafiya dan bata fita ko da aka kawo Amarya kwance suka iske ta hakanan ta tashi ta anshi Amarya ita dasu Maryama, waya Maryama ta kirashi ta gaya mashi Hakima bata lafiya shiyasa hankalin shi yana kan Hakima kawai dai ganinshi suke, bayan sun dawo shashen su sakin hannun Hikimatu yayi ya wuce room ɗin Hakima bai ce mata komai ba, tsaye tayi tana kallonshi tsaki tayi sannan itama ta shige room ɗin ta itama. 







 _By Jameelah Jameey ✍🏻_




Post a Comment

0 Comments