TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 93-94

 *Wa�nan shafin tukwici ne gare ku*


WMasoqa wannan littafin ban$san(kuna da iawa heka ba,`ban daabi� da zan ce muku sAi dai in muku fatan alohairi, yanda kuke yabawa wannan littafin da d’aukan darasi da kuke yi a cIkin littafin yasa nake jin dad’i, fata ~a a kullum labariL da nace rubutaw! ya dinga fad���akarwahad’e da oishad’antarw!_.


_Unisue wife da Khadija AndijA na ga comment d’in ku, ina godiya_





93-94



Yaya Faruk d‹akin Naja ya w�ce ya same ta a gaban mirrow tana make-up.



Jikin kafad’ar ta yahe ya kwanta�yana �akar mata murmushi.



Ita ma Murmus`in`take"mayar mi shi&


Daidai sa�tin kunnen �a yaya Faruk ya ce "Kin yi k9aU Kladijah".



"Na gode yaya Faruk" Nana"ta fad∙a cikin�s�ririyar murya.



Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah bari in je masallaci na ga lokaci ya kusa, daga nan zan biya gidan su Dad da Abbu".



"Ka gaishe su yaya Faruk" cewar Nana.



"Za su ji" yaya Faruk ya fad’a yana fita daga d’akin.



Bayan yaya Faruk yayi sallar magrib ne ya wuce gidan Abbu.



San da yaje gidan, Abbu da Ummu ya samu a falo suna zaune.



Sallama ya musu kana ya shigo ya zauna akan rug kusa da Abbu.



Da murmushi Abbu da Ummu suka amsa mishi sallamar.



Bayan sun gaisa ne Ummu ta ce "Faruk ya wajen su Khadijah, tun da kuka zo Kaduna wannan karan sau d’aya ka kawo min ita, yaushe za ka k’ara kawo min d’iya ta".



Murmushi yaya Faruk yayi ya ce "Gobe zan kawo miki ita Ummu dan ina jin nan da kwana biyu ko uku za mu koma Abuja".



"Allah ya kaimu Faruk" Ummu ta fad’a ta amsa mishi.



Dadi ne ya ce "yanzu nan 2 days kenan za ku koma Abujan".



"Eh Abbu" yaya Faruk ya amsa.



"Allah ya kaimu ya kuma ba da sa’a" cewar Abbu.



Yaya Faruk ne ya amsa da cewa "Amin Abbu".



Sun d’an tab’a hira kana yaya Faruk ya kalli Abbu ya ce "Abbu wata magana ce ke tafe dani akan Fatima".



Abbu ne ya maida hankalin shi gurin yaya Faruk ya ce "Ina jin ka, Allah yasa ba wata matsala ba ce".



Yau kwana na hud’u da zuwa gidan Aminu, a hanyata ta dawowa sai na ga Fatima a bakin titi tana tsaye, so shine sai na tsaya dan na rage mata hanya, bayan ta shiga motar ne nake tambayar ta inda zan kai ta sai take fad’a min sun sami matsala da mijin ta ne, sai yau da na sake tambayar ta take fad’a min cewa sakin ta yayi, yanzu haka ta na gida na".



Ummu da tun da yaya Faruk ya fara magana ta tsura mishi ido, jin Kalmar sakin da ta ji yaya Faruk ya ambata ne yasa ta sunkuyar da kanta.



Abbu shiru yayi kafin ya ja gauron numfashi ya kalli yaya Faruk ya ce " Ka ce yau kwana hud’u kenan".


"Eh Abbu" yaya Faruk ya amsa.



Yaya Faruk ne ya ci gaba da cewa "Abbu ina neman alfarma a gurin ka akan sharad'in da ka yanke mata kayi hak’uri ka janye….".



Da sauri Abbu ya dakatar dashi cikin b’acin rai ya ce "Faruk kar ka ce za ka nemi wannan alfarmar a guri na dan ba zan iya maka ita ba, sharad’i ne na gindaya mata a matsayina na uban ta kuma ta yarda dashi, sai yanzu da aka samu matsala shi ne za ka ce in yi hak’uri, ai ko a lokacin da ta amince da sharad'in nasan har da k’uruciya ke damun ta da kuma Makauniyar soyayya da take ma wannan Dr d’in, nasan dole wata rana sai tayi nadamar amince wa sharad’ina da tayi dan iyaye ba abin wasa ba ne, kai kan ka Faruk ban san ba ka da hankali ba sai yau, yarinyar da ta k’i ka ta k’i bin shawarar iyayen ta, miye ba ka fuskanta ba a dalilin ta, shine za ka d’auke ta ka kai ta gidan ka, daman ai na fad’a mata in dai ta samu matsala da mijn ta kar ta doshi wani d’an uwa na da matsalar ta ko ta zo guri na, saboda haka kaima ina ba ka umarni ka je ka sallame ta, in ma za ta koma ma shi Dr da ta zab’a akan kowa wannan matsalar ta ce amma kar ta kuskura in ji ta je gurin family d’ina in ba haka ba kuwa za ta fuskanci mummunan hukunci daga gare ni".



Yaya Faruk cikin ladabi ya ce "Abbu dan Allah ka janye wannan hukunci daka sa ma Fatima, ita kan ta tayi nadamar….".



Abbu ne ya k’ara katse shi da cewa "Faruk kar ka bari raina ya b’aci akan maganar Fatima, ka dai ji abin da na fad’a maka, ka je ka sallame ta kafin ka koma Abuja dan ba kunya ne da ita ba za ta iya cewa za ta bi ka Abuja".



Abbu na gama fad’ar haka ya tashi ya bar falon.



Shiru ne ya ratsa falon, tsakanin Ummu da yaya Faruk ba wanda ya samu k’arfin yin magana.



In ka kalli Ummu a lokacin ba za ka iya fad’ar halin da take ciki ba, sai dai kasan ta shiga damuwa a lokacin.



Ummu ce ta ja wata nannauyar ajiyar zuciya ta ce "Faruk ka je ka sallame ta tun da ita ta yarda da sharad’in da Abbun ta ya fad’a mata, ita ta ja ma kanta duk abin da ya same ta, gashi nan tana k’aramar yarinya da ita ya mai da ta k’aramar bazawara, nasan in da kai ta aura da ba za ta fuskanci wannan k’alubalen ba duk da k’addara kowa ba ya kauce mata, ba irin nusar da Fatima da ban yi ba amma ta k’i jin magana ta saboda Makauniyar soyayya da ta d’aura ma kan ta, yanzu wani riba ta samu akan abin da ta yi, yau shekaru ba na nawa ban tab'a yaji ba amma sai gashi y'ar da na haifa an sake ta a cikin k'uruciyar ta ".



Hawayen da ya zubo ma Ummu ne yasa tayi saurin goge hawayen da hannun ta.



Jikin yaya Faruk ne yayi wani irin sanyi ganin yadda Ummu ta zubar da hawaye akan jin zafin sakin da Dr ya min da kuma rashin bin maganar su da ban yi ba.



Yaya Faruk ne ya ce "Yanzu Ummu ina Fatima za ta in na ce ta fitar min daga gida? Laifi ne tayi kuma ta gano kuskuren ta ya kamata a tausaya mata, ko a lokacin har da k’uruciya da ke damun ta, na tabbata a yanzu ba za ta k’ara kwatatanta kuskuren da tayi ba, Ummu ki min alfarma in tafi da ita Abuja kafin komai ya daidaita".



Cikin sanyin jiki Ummu ta ce "Faruk, Alhaji yayi fushi sosai da Fatima, idan har yaji ka tafi da Fatima Abuja kai ma laifin zai iya shafar ka, ka je kayi abin da ya ce, wannan sai ya zamar mata izina".



"Toh Ummu" yaya Faruk ya fad’a.


Sallama yayi ma Ummu ya fita daga gidan.



Ko da yaya Faruk ya fito gidan su Dadi ya wuce.



Sai da ya tsaya yayi sallar isha’i a masallacin da ke layin kana ya shiga cikin gidan.



San da ya shiga falon ba kowa, hakan yasa ya wuce side d’in Dadi dan yasan suna can.



Bayan sun gaisa ne yaya Faruk ya sanar da Dadi halin da ake ciki ga me da ni.



Dadi bai ji dad’in hukuncin da Abbu ya yanke min ba dan haka ya kalli yaya Faruk ya ce "Gaskiya abin da mijin Fatima yayi bai kyauta ba duk da ban san me ya had’a su ba, shi ma Ibrahim d’in bai kyauta ba, tun lokacin da ya fad’a mata sharad’i nasan ran shi a b’ace yake zai iya janyewa daga baya, ashe shi da gaske ya ke yi, in ban da abin shi ai ba a biye ma yaro in ya b’ata maka, yanzu da ya ce kar ta je gurin family d’in shi ina yake so ta je? yanzu kai Faruk ya ka ke ganin za ayi, yanzu in na ce ka kawo ta nan a yadda ran Ibrahim ya b’aci zai iya turo Aminu ko Khalil su mata hukuncin da bai dace ba in ba na nan, ina so ka tafi da ita Abujan ta d’an yi kwana biyu a can, ita ma nasan Fatima yanzu hankalin ta ba a kwance yake ba, in yaso in Ibrahim d’in ya huce daga fushin da yake yi zan maka magana sai ka dawo da ita, nima zan ma Ibrahim d’in magana".



Momi ce tayi saurin kallon Dadi ta ce "Haba Alhaji ya za ka ce Faruk ya tafi da Fatima Abujan, ka manta abin da ta mishi ne, dan ita ma Fatiman ba ta da kunya har ta iya zuwa gidan shi ta zauna sannan yanzu kuma Alhaji ka ce ya tafi da ita Abujan, ai ko ita matar tashi ba za ta ji dad’in wannan hukuncin ba, gwara ta zo nan ta zauna a gurin mu".



Dadi ne ya ce " Hajiya ba laifi ba ne dan Faruk ya tafi da Fatima Abuja ta zauna a gurin shi, ai ba wani dad’ewa za tayi a can ba, ko me Fatima ta mishi matsayin y’ar uwar shi ta ke, ba zai dubi abin da ta mishi ya ce ba zai kyautata mata ba dan ta mishi laifi, zai kyautata mata ne dan girman zumunci, ita kan ta Fatiman nasan duk in da za ta zauna ba za ta sake ba saboda abin da ya faru da ita, amma in ta bar garin za ta samu relief d’in halin da take ciki dan rabuwa da miji ba k’aramin ciwo ba ne bare wanda ka ke so".



"Shi kenan Alhaji, ni daman abin da nake ji kar ta bi su Abujan ne ita matar shi ta ga kamar an takura mata, ita ma Fatiman Allah ya daidaita tsakanin su da mijinta ta koma, ni kaina ban ji dad’in abin da Dr yayi ma Fatima ba, yarinya k’arama ya sake ta, Allah dai ya zab’a abin da yafi alkhairi".



"Amin dai" Dadi ya amsa.



Yaya Faruk ya d’an jima a gidan kana ya musu sallama ya tafi.



Lokacin da yaya Faruk ya dawo gidan ba kowa a falon, hakan yasa ya wuce d’akin Nana in da ya same ta akan gado ta kwanta.



Sallama yayi kana ya k’arasa gadon da take ya zauna a gefen ta.



Nana wacce barci ya fara d’aukan ta ba ta san da zuwan shi ba.



Kan ta ya fara shafa mata gashin kan ta da tayi parking d’in shi da ribbon.



A hankali ya kira sunan ta a saitin kunnen ta had’e da hura mata iska.



Jin sunan ta da yaya Faruk yake yi yasa ta bud’e idon ta da yake cike da bacci ta sakar mi shi murmushi.



Fuskar ta ya shafa kana ya ce "Sleeping baby".



"Sannu da zuwa yaya Faruk, ashe ka dawo, ban ji shigowar ka ba, ya su Momin da Ummu" Nana ta fad’a.



"Suna nan lafiya lau, suna gaishe da ke, Yanzu na shigo na ga har kin fara bacci" cewar yaya Faruk.



Nana ce ta ce "Tun da nayi sallah na fara jin baccin, shi yasa ina idar wa na kwanta".



"Sorry na tashe ki, bari in je in watsa ruwa, ki koma baccin ki kin ji my Khadijah" yaya Faruk ya fad’a.



Murmushi ta mishi kana ta ce "Abincin fa yaya Faruk".



"kar ki damu na ci a gurin Momi" cewar yaya Faruk.



"Sai da safe yaya Faruk, dan za ka iya dawowa ka tarar da nayi bacci" Nana ta fad’a.



"Gud night dear" yana gama fad’ar haka ya manna mata peck a cheeks d’in ta kana ya fita daga d’akin.





Su yaya Aminu da yaya Khalil kuwa ba su san abin da yake faruwa ba.



Sai san da yaya Aminu da yaya Khalil suka je gidan Ummu take fad’a musu sakin da Dr ya min ba k’aramin girgiza su maganar tayi ba.



Fad’a musu tayi yanda yaya Faruk suka yi da Abbu a kaina.



Yaya Aminu bai wani jin haushin hukuncin da Abbu ya yanke min ba dan yana ganin duk abin da ya sameni ni na ja ma kaina duk da yasan har da k’addara.



Yaya Khlalil kuwa tausayi na ne ya kama shi jin matakin da Abbu ya d’auka a kaina.



A ganin shi ya kamata a tausaya min da abin da ya same ni.



Da yana da hali da ya d’akko ni gidan shi na zauna kan Abbu ya sauka, sai dai yasan bai da halin yin haka saboda yadda Abbu yake fushi dani, hakan zai iya shafar shi in Abbu ya ji labarin shi ya d’auke ni.



Dad’in da yaji shine yadda yaya Faruk bai yi fushi dani ba akan abin da na mishi, hakan ya k’ara tabbatar mishi da yaya Faruk daban ne a cikin mutane saboda halayen shi nagari, ba kowa ba ne zai iya yin abin da yaya Faruk d’in yayi.




Washegari yaya Faruk ya d’auki Nana ya kai ta gidan Momi, Momi rasa in da za ta sa Nana tayi, haka ta cika da kayan k’walama irin na ma su ciki, bini-bini ta tambaye ta me take so a dafa mata.



Ita Nana har kunyar Momi take yi, ba za ta iya fasalta farim cikin ta yadda Momi ke ba ta kulawa a matsayin ta na surukar ta, sun d’an jima a gidan kafin su ka musu sallama suka tafi.



Next day ma haka yaya Faruk ya k’ara d’aukan Nana suka je gidan Anisa ganin yadda take mishi k’orafin wannan zuwan da suka yi bai kai ta ba.



Ranar ma haka na zauna ni kad’ai a gidan, kad’aici ya same ni ga gidan shiru ba ka jin motsin komai.



Haka na wuni a d’aki ni kad’ai, in ban da tunanin yadda rayuwa ta canza min ba abin da nake yi.



Nasan a yanzu yaya Faruk ya riga ya fad’a ma Abbu abin da ya same ni, hankali na ba a kwance yake ba dan ban san wani hukunci ya tanadar min, gashi ban da damar tambayar yaya Faruk saboda yadda nake shakkar yi mishi magana ganin yadda bai sakar min fuska.



Haka suka je Anisa ta musu tarba mai kyau, ba su sami yaya Khalid ba saboda yana wajen aiki.



Ba su wani jima ba suka musu sallama suka tafi.



Daga nan gidan su Ummu suka wuce, haka Ummu tayi ta nan-nan da ita, ita kanta Nana tana jin dad’in yaddda Ummu ke janyo ta jikin ta in ta zo gidan.



Ko da Abbu ya dawo bayan sun gaisa ne ya kira yaya Faruk side d’in shi.



Bayan yaya Faruk ya je kiran da Abbu ya mi shi ne ya ce "Faruk kayi abin da na sa ka?".



Sunkuyar da kanshi yaya Faruk yayi cikin ladabi ya ce "Abbu kayi hak’uri, ba zan iya cewa Fatima ta bar gida na ba".



Abbu cikin d’aurewar fuska yace "Ok ba za ka iya ba ko, that’s good, tun da kai ba za ka iya ba zan aiki Aminu ya je, dan in har na ta ka k’afa ta na je gidan kai da ita abin ba zai muku kyau ba tun da kaima ba za ka bi abin da na ce ba, ka fad’a mata na ce ta manta da sharad’in da muka yi da ita ne lokacin da ta zab’i shi Sadik d’in".



"A yi hak’uri Abbu" yaya Faruk ya fad’a.



"Zan hak’ura amma sai kayi abin da na ce" cewar yaya Faruk.



Yaya Faruk ne ya ce "Abbu gobe insha Allah gobe za mu koma Abuja".



Wannan karan Abbu cikin sakewar fuska ya ce "To Faruk Allah ya ba da sa’a ya taimake ku, amma Faruk ka tabbatar da kayi abin da na ce, akwai dalilina nayin haka, nasan ko ka ce ta bar maka gida Fatima ba za ta je gurin da bai dace ba, ina so ta k’ara fahimtar yanda rayuwa take da kuma kiyaye kwatatanta kuskuren da tayi a baya ta kuma gane mahimmancin bin maganar na gaba da ita da iyayen ta".



"Toh Abbu" yaya Faruk ya amsa mishi amma ba wai dan zai iya kora ni daga gidan shi ba kamar yadda Abbu ya ce.



Kud’i masu yawa Abbu ya ba ma yaya Faruk ya ba ma Nana, godiya yaya Faruk ya ma Abbu kana ya koma side d’in Ummu.



Fad’a ma Ummu yayi kyautar da Abbu ya ma Nana ta nuna jin dad’in ta.



Turaruwa masu tsada na jiki ta ba ma Nana da za su tafi.



Haka Nana tayi ta godiya irin karamcin da su Ummu da Abbu suke mata.



Ummu ce ta ce su gaishe mata da ni lokacin da za su tafi.



Yaya Faruk yasan Ummu na daurewa ne amma tana cikin damuwa a kaina.

San da suka dawo ne Nana ta shigo d’aki na ta sanar da ni dawowar su, sannan ta sanar da ni Ummu na gaishe da ni.



Hakan ba k’aramin dad’i ya min ba jin Ummu ta ce a gaishe dani, nasan hakan na nuna ba ta fushi da abin da ya same ni duk da nasan ita ma sai taji haushin sakin da Dr ya min, Abbu ne fargaba ta dan ban san fushin da yake yi da ni ba.



Da daddare yaya Faruk suna zaune da Nana a bedroom tana kwance akan cinyar shi.



Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah gobe za mu tafi Abuja da Fatima, a can za ta zauna kan komai ya dawo normal".



Da sauri Nana ta tashi ta zauna ta kalli yaya Faruk.



Cikin sanyin murya ta ce "yaya Faruk ba misunderstanding ka ce sun samu da mijin ta ba".



Yaya Faruk ne ya ce "Haka ta fad’a min da farko, ashe divorcing d’in ta yayi, akwai dalilin da yasa ba zan kai ta gidan Abbu ba ne, nafi son komai sai ya dawo normal".


Hawaye ne ya fara zubowa a idanun Nana.



Mamaki ne ya kama yaya Faruk ganin yadda Nana ke zubar da hawaye saboda yace zai tafi dani Abuja, yasan hakan ba zai rasa nasaba da kishi ba, kallon ta kawai yake yi.



"Me ya faru Khadijah kike hawaye, ko ba kya so in tafi da Fatima ne" yaya Faruk ya fad’a.



Kuka ta fashe dashi ta fad’a jikin shi ta ce "yaya Faruk dole in yi kuka jin za ka tafi da Fatima, ka fad’a min sun rabu da mijin ta, nasan ita kake ma so tun a farko, yaya Faruk ka nuna ma Fatima so saboda ni kaina shaida ce akan haka, nasan in har kuna tare a ko wane lokaci son ta da ka danne zai iya taso maka at any time, hakan zai sa ka dawo da son ta sabo fil a zuciyar ka, ka ga kuwa hankali na ba zai kwanta ba, yaya Faruk ina son ka kuma ina kishin ka".



D’ago da fuskar ta yayi yana goge mata hawayen fuskar ta.



Cikin lallashi yaya Faruk ya ce "Pls Khadijah stop that crying, ki daina sa ma kanki wannan tunanin har ranki ya b’aci, kin ga you a pregnant, kar hakan ya shafi lafiyar babyn mu, tabbas nasan na so Fatima amma hakan ba zai sa dan ta rabu da mijin ta yasa in dawo da soyayyar da nake mata ba, tun san da Fatima ta nuna ba ni take so ba na sa ma kaina cewa na hak’ura da ita, ita kanta na fad’a mata cewa na hak’ura da ita tun a lokacin da ta fad’a min Dr take so, ba yanda za ayi in dawo da Fatima cikin rayuwa ta bayan na samu tabon da ta min a zuciya ta ya warke, ko ba haka ba ma ina dake yanzu ban da burin k’ara yin soyayya da wata y’a mace, ke kad’ai kin ishe ni, ina son ki Khadijah" ya k’arasa maganar da murmushi a fuskar shi.



Jikin shi ta fad’a ya rungume ta tana cewa "Na gode yaya Faruk".



Dariya yayi cikin tsokana ya ce "Ashe Khadijan tawa kishi ne da ita haka, ki ce sai nayi da gaske kar a bar ni na k’ara wata amarya".



Rufe fuskar ta tayi tana dariya.



Haka suka canza hirar ta su zuwa nuna ma junan su zallar so da kulawa had’e da tarairaiya.




Post a Comment

0 Comments