TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 12

 D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Yabo da jinjina gare ki Daughter Hanne Magaji. Har kullum idan na tuna alherinki gare ni ina jin daɗi har cikin raina. Ubangiji ya saka miki da mafificin alherinsa👏🏻*



*LAMBA SHA BIYU.*


       _Nan take raina ya ɓaci, saboda haushin yaudarar da yake yi mini. Daren ranar ba mu yi bacci mai daɗi ba daga ni har shi. Saboda ɗan banzan rikicin da muka tafka da shi, a kan cin amanar da yake ƙoƙarin yi mini ya raba ni da ƙawata. Bayan kwana biyu da wannan zancen Hafsa ta zo gidan. Babu kunya na sanar da ita abin da na ji kuma na fahimta, wanda ke tsakaninta da Mukhtar. Yanayin da ta nuna mini tare da rantsuwa a kan, ba za ta iya auren mijina ba; hakan ya sa na yarda da ita. Kuma na goge tsanar da na fara yi mata a raina, wacce ta sa na ci alwashin daina kula ta har ƙarshen numfashi. Haƙuri ta dinga ba ni tare da kalaman kwantar da kai a kan ko mutuwa na y; ba za ta iya auren mijina ba, balle ina da rayuwa._

      _Ba na mantawa akwai watarana da ta zo gidan tana taya ni aiki; Mukhtar ya shigo tare da abokinsa. Baki har kunne yake kallon mu yana 'yar dariya ya ce,_


    "Ina ma a ce ku matan mutum ɗaya ne? Wallahi kun dace sosai a kira ku da matan mutum ɗaya."


     "Ai kuwa gani nan bari nan dukiyar Alawa. Domin har abada ba zan yi kishi da ƙawata ba. Don haka ku gama tsegumin da ya kawo ku ku fice. Mukhtar nawa ne ni kaɗai, babu macen da ta isa raba ni da shi balle kuma ƙawata!"


     _Sumi-Sumi suka fice bayan sun gama borin kunyarsu, domin ita kanta sai da ta ce, su raba ta da wannan zancen. Domin ta san yadda nake kishin Mukhtar; ko kashe ta zan iya yi idan ta aure shi. Dariya suka saka sannan Abokin nasa ya ce, 'Ai Allah bai haramta ba' cikin ƙololuwar ɓacin rai na ce da shi; to ni na haramta masa auren wata ma balle ƙawata. Yanayin da suka ga na shiga ina ta zuba musu baƙaƙen maganganu ya sa suka fice bayan sun gama borin kunyarsu._

       _Domin ƙarfin zumuncin da nake da ita, har turmin atamfa na sa ya saya mata a wata sallah. Ashe ni suke yi wa kallon biri boko sun san abin da ke tsakaninsu. A lokacin wani sabon wulaƙancinsa ya tashi, ya yi ta mini abubuwan da ke ɓata mini rai, kuma ya san abubuwan da na tsana a rayuwata kenan. Ya tsiri wayar dare sai na yi bacci na farka na ji shi yana waya, haushi ya turnuƙe mini zuciya. Musamman kashe muryar da yake yi kamar na shaƙe shi ya mutu. Sai da muka yi gumurzun bala'i da shi sannan ya daina mini wayar tsakiyar dare cikin ɗaki._

       _Ina da tsohon cikin Iman, ya samu aiki a Community Bank. A lokacin likkafarsa ta fara cigaba, domin kuwa komai ya yalwatu Allah ya buɗe masa ƙofar samu. Hakan ya ba shi damar fantsama cikin neman matansa har da na aure. A ranar da na je gidansu Hafsa ina sanar da ita Mukhtar ya samu aiki; tsalle ta dinga yi tana murnar shi kenan sai ya aure ta. Mamaki ya sa na dinga kallon ta baki a sake tamkar wata wawuya, saboda tsabar mamakin maganar da na ji ta faɗa da bakinta._

   _Ban ji nauyin Mahaifiyarta da ke zaune tana sauraron mu ba, na ce; na rantse da Allah ba zai taɓa auren ki ba! Wata mata daga ke zaune ta ce saboda mi na ce haka, idona a rufe na ce da ita; ni da ita duka ɗaya ne a wurinsa. Don haka muddin ina tare da shi sai dai ita ta haƙura, idan kuma auren shi take son yi; to ni zan fita gidan na bar mata Ummu Salma da abin da zan haifa, sai ta ci gaba da rainonsu a matsayi uwa kamar yadda nake yi yanzu. Mahaifiyarta ta yi saurin faɗin; Allah ma ya kiyaye Zaituna! Ai da ki fita ki bar mata 'ya'ya, gara ta haƙura ki ci gaba da rainon yaranki._

       _Haka na fito gidan cike da mamakin zancen Hafsa, duk da daga baya ta ce da ni wasa ce take yi, domin ta ji abin da zan ce. Amma na ji zafin ta sosai, sai dai dole na haƙura saboda ba na son ƙawancenmu ya lalace sanadin hakan. Muka ci gaba da zama ba tare da na canza mata fuska ba, saboda iya fahimtar da na yi musu duka; na gano shi yake son ta ba ita take son shi ba._ 

        _Sai dai kuma har abada ba zan manta wani abu da ya yi mini ba. A lokacin da cikina ya shiga watan haihuwa, ya dinga yi mini abubuwan baƙƙan ciki iri-iri, wanda ban kawo dalilin faruwar su, balle laifin da na yi masa yake yi mini haka. Damuwa ta yi mini yawa ga haihuwa yau ko gobe, a gabansa zan ci kukana na ƙoshi; amma ƙanzil ba zai ce da ni ba balle na samu arziƙin ya ba ni haƙuri. Amma idan ta zo ya yi ta yage mata baki yana jan ta da surutu tana fuskewa._

       _Ranar da naƙuda ta kama ni gadan-gadan, ya kira mini wata malamar asibiti har gida ta duba ni. Ta ce ina da sauran awanni kafin na haihu, don a yadda ta ce zan ɗauki awa bakwai kafin kan Bbyn ya sauko ƙasa. Ta ba ni lokaci da nufin ta je ta dawo, tun misalin ƙarfe goma na safe nake ta shan wuya har zuwa yamma. Ganin ina ta fama da kaina ya kira Hafsa ta zo ta taya ni aiki, don ko shara ban yi ba ranar._

        _Jikinta yana ɓari ta fara aiki tana jera mini sannu, shi kuma sai tsokanarta yake yi da hira, ba tare da ya nuna damuwar halin da nake ciki ba. Asali ma yadda take nuna mini fuskar tausayi, shi ko rabin hakan ban samu a wurinsa ba. Bayan ta gama gyara gidan ta yi wa Ummu Salma wanka ta shiryata; ta dawo inda nake ta zauna, tana ta jera mini sannu a duk lokacin da marata ta murɗa. Ina ɗaukar lokaci cije da baki gumi yana tsattsafo mini kafin ta lafa na dawo sauke numfashin wahala. Amma a haka ya je ya siyo abinci a ƙatuwar kula. Ya zuba wa kansa ya zuba mata, ni kuma tun da ya ce zan iya ci na ce a'a, bai sake bi ta kaina ba.  Amma ita sai faman rarrashinta yake yi a kan ta ci abinci kada ta zauna da yunwa. Ni ko furar da na ce ina so na sha ma, tun da na kurɓa na ajiye bai damu da cewa dole sai na ƙara ba. Kuma a gabansa nake ta nishin wahala idan marar ta murɗa mini tamkar na shiɗe. Amma babu wata damuwa kan fuskarsa dangane da halin da nake ciki, saboda hankalinsa kacokam yana kanta sai faman kallon ta yake yi. Ita kuma tana haɗe masa fuska tana jera mini sannu cikin kulawa kamar ta yi kuka. Hakan ya sa na ƙara tabbatar da  shi yake haukarsa a kanta, amma ita ba ta damu da shi ba._


  




Na muku typing da yawa ya goge. Ku yi manage🧐




Post a Comment

0 Comments