TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 87-88

 87-88



Yau ranar ta kasance ranar Alhamis, ina zaune a falo ina karanta wani novel mai suna "Behind our love".



Knocking d’in da naji ne yasa na tashi na bud’e k’ofar.



Halima na gani a tsaye a bakin k'ofa.



Rungume ta nayi cikin murnar ganin ta.



Ita ma murnar take yi saboda mun kwana biyu ba mu had’u da ita ba.



Hannu ta na rik’o muka dawo falo muka zauna.



Hira muka fara yi kafin na tuna ban kawo mata abin motsa baki ba.



Tashi nayi naje na kawo mata drinks da snacks a gaban ta kana muka ci gaba da hirar da muke yi.



A cikin hirar da muke yi ne Halima ta kalle ni cikin kulawa ta ce "Wai Fatima kin yi rashin lafiya ne nag a kin canza, ko ciki kike dashi yasa kika canza".



Murmushi nayi na ce "Ba ko d’aya a ciki".



K’ara kallo na tayi kana ta ce " Serious speaking Fatima kin canza, yanayin ki ya nuna kamar akwai abin da yake damun ki".



Tun da Halima ta tambaye ni abin da yake damu na naji ta ta’bo min abin da ya ke min k’aik’ayi a raina, a yanzu ba na jin zan ci gaba da adana abin da yake damu na saboda nasan fad’ar zai rage min halin damuwar da nake ciki.



"Halima ba zan ‘boye miki abin da yake damu na ba tsakanina da Dr" na fad’a cikin sanyin murya.



Halima bi na kawai take yi da kallo tana jiran jin abin da zan fad’a mata.



"Halima tun da muka yi aure da Dr nake fuskantar problem ni da Dr in one way on the other, wanda yafi damu na a yanzu shine mu’amalar shi da Meema, duk yadda na nuna ‘bacin raina hakan bai sa komai ya canza ba, na rasa yadda zan yi Halima" na fad'a.



"Wacece Meema kuma" Halima ta tambaye ni.



Nan na bata labarin Meema har kawo yanzu da muke ci gaba da takun sak’a da Dr.



Cikin tausayawa Halima ta ce "Gaskiya Dr bai kyauta ba, ban zaci hakan daga gare shi ba saboda yadda na ga kuna nuna ma junan ku soyayya kafin ku yi aure, sai dai shi namiji dama ya kan iya canza wa a ko wane lokaci, A b’angaren Meeman tun da kin nuna ba k’ya son tarayyar shi da ita Meeman ya kamata ya ja baya da ita, kinsan maza baka gane in da suka fuskanta, amma abin da nake so dake Fatima shine ki ci gaba da hak’uri, ki daina sa damuwa a ranki sannan ki daina yawan mishi magana akan ita Meeaman, tun da ya tabbatar miki da ba komai a tsakanin su ki yarda a hakan, insha Allah komai zai dawo normal, may be ma kishin ki ne yasa ki ka ga kamar akwai wata alak’a a tsakanin su da Meeman" Halima ta k’arasa maganar cikin tsokana.



Ni ce na ce "Na gode da shawarwarin ki Halima".



Tabbas na ji dad’i shawarar da Halima ta bani, ko ba komai na samu sauk’in damuwar da nake ciki.



Haka Halima ta ci gaba da ba ni shawarwari wanda za su amfane ni kana muka ci gaba da hirar mu.



Sai bayan la’asar sannan Halima ta tafi.




B’angaren Meema kuwa tun da ta ga Dr na sakar nata fuska yasa ta fara zargin ko yanzu Dr ya fara son ta ne kamar yadda take son shi.



Yanda take damun iyayen ta da maganar Dr yasa Mominta ta fara mata fad’a akan irin son da take ma Dr sannan ba ta ganin za ta bar Meeman ta auri mai Mata tun da bai aure ta a ta farko ba, da farko Momin ta fad’a ta fara mata akan ta hak’ura da Dr tun da ba shi ba ne autan maza sannan mai zai tayi da Dr tun da ya riga yayi aure, Dadin ta kuwa lallashin ta yake yi akan ta hak’ura da Dr ta za’bi d’aya daga cikin samarin ta masu son ta amma duk maganar da iyayen ta ke mata ta bayan kunnen ta take bi saboda tana gaanin Dr shi yafi dacewa akan ya zama Sanyin idaniyan ta sannan kuma mijin ta.



Ba in da take samun goyon baya akan son da take ma Dr da ya wuce Hanan da Momin Dr.



Kullum Meema ba ta da wani buri da ya wuce a ce Dr ya amshi tayin soyayyar da take mishi amma har yanzu ba ta kai ga cin nasara ba.



Meema ce da Hanan zaune a Gurin shak’atawa dake harabar gidan su Dr.




Zaune suke akan wasu kujeru da aka ke’bance na musamman dan hutawa, ko waccen su na rik’e da favourite drinks d’in su suna sha.



Motar Dr ce ta danno kai cikin gidan.



Parking yayi a parking space kana ya nufi cikin gidan ba tare da lura da su Hanan da ke zaune a gurin shak’atawar.



Meema ce ta mik’e da niyyar barin gurin.



Hanan ce ta kalle ta kan ta ce "Ina za ki Meema".



"Yanzu zan je in dawo, ina son mu yi magana da yaya Sadik ne" Meema ta fad’a.



Ta’be baki Hanan tayi kana ta ce "Ok sai kin dawo".



Bayan tafiyar Meema ne Hanan ta ja d’an k’aramin tsaki saboda tun tana tausaya mta a irin son da take ma Dr yana share ta duk da d’inbin masoyan da Meema take dasu amma a yanzu Meema ta fara ba ta haushi akan yadda ta nace ma Dr alhalin shi ba ya son ta hasalima shi yayi aure, k’arin abin haushin shine har yanzu Dr bai nuna tausayawar shi ga Meema ba duk da irin son da take mishi, ba laifi yanzu su na shiri da Dr saboda ta rage wasu behaviours d’in ta da ba ya so, ita a ganin ta bai kamata Meema na wahalar da kanta ba akan Dr a yadda take, ita kanta za taso Dr ya auri Meema ko dan son da take mishi.



San da Meema ta shiga falon ba kowa a ciki, hakan yasa ta nemi guri ta zauna tana jiran fitowar Dr.



Ya d’an jima a ciki kafin ya fito daga side d’in Momi.



Ganin Meema da yayi a zaune a falon yasa ya sakar mata murmushi.



"Ina wuni Yaya Sadik" Meema ta fad’a cikin kwantar da murya.



"Lafiya lau Meema, ya su Momi" cewar Dr.



"Suna nan lafiya lau" Meema ta amsa mishi.





"Yanzu kika zo ne?" Dr ya tambaye ta.



Meema ce ta amsa da cewa "Na d’an jima da zuwa, muna wajen shak’atawa ne ni da Hanan".



"Ok san da na shigo ban lura da ku ba, bari in tafi Meema, ki gaida su Dad".



Har ya fara tafiya Meema ta kira sunan shi cikin marairaicewa.



Juyowa yayi ya kalle ta kan ya ce " Ya aka yi ne Meema".



"Dr ina so muyi wata magana dakai ne" cewar Meema.



Murmushi yayi kana ya ce "Ina jin ki Meema".



Meema ce ta ce "Dr me yasa ba ka so na?’".



D’aure fuska yayi kamar ba shi ba ne ya gama sakar mata fuska ya ce " Look Meema, in dai akan wannan maganar ce ina ganin ba ki da buk’atar amsar ta, na riga na fad’a miki cewa ki yi hak’uri da ni, already yanzu ina da mata, na fad’a miki tun a baya na d’auke ki ne as a sister not a lover, zan iya miki duk abin da zan ma su Hanan, sannan za ki iya tambaya na duk abin da kike so zan miki shi, but ina so ki ajiiye maganar soyayya a tsakanin mu dan ki ga akan shi ne nake b'atawa dake".



Hawaye ne ya fara zubowa a idanun ta kana ta ce "Yaya Sadik dan ka ga ina son ka shine kake min haka, ni kaina ban san tsawon lokacn da na d’auka ina jiran ka amshi tayin soyayya ta but you refuse, why yaya Sadik?, ka taimaka ka so ni sannan ka aure ni a matsayin matar ka, hakan ne zai sa in samu peace of mind na samu abin da nake so, yaya Sadik I don’t care about your wife in dai za ka aure ni zan zauna da ita".



Tausayin ta ne ya kama shi da har yake jin kamar ya amince da buk’atar ta, sai dai yasan hakan ba zai yiwu a gare shi ba dan bai ra’ayin mata biyu sannan har yanzu bai jin son Meema a ranshi.



Cikin sweet voice d’in shi ya ce " Sorry to say Meema, ki hak’ura da ni don ba na so in yi deceiving d’in ki, infact in da zan aure ki da tuntuni zan aure ki tun kafin in auri Zarah, a tsari na ba na ra’ayin mata biyu" yana gama fad’ar haka ya bar gurin.



Kan kujera Meema ta fad’a ta fara kukan k’in amincewar Dr da bai yarda zai aure ta ba.



Momi ke sakkowa daga upstairs ta hango Meema na kuka, hakan yasa ta k’arasa sakkowa da sauri ta k’araso gurin da Meema take.



Kwantar da ita tayi a jikinta tana tambayar ta abin da ya same ta.



Meema cikin kuka ta ce "Momi yaya Sadik ne".



Da sauri Momi ta ce "Me ya miki".



Nan Meema ta fad’a ma Momi yadda suka yi da Dr kana ta d’aura da cewa "Momi ki taimake ni in sami Dr a matsayin miji na, shi nake so, na kasa ba ma kowa wannan damar da na ba ma yaya Sadik amma duk da haka ya k’i so na, akan haka yasa Momi take ganin laifi na saboda yadda na dage sai yaya Sadik, Momi ki mishi magana ya aure ni, ni zan zauna da Zarah, plss Momi ki fad’a min ko ina yin wani abu ne da Dr ba ya so in daina" ta k’arasa maganar cikin shashshek’ar kuka.



A yadda Momi take jin tausayin Meema tana ganin za ta iya mata ko wane taimako dan taga ta samu Dr a matsayin miji, ita ba ta ga wani aibun Meema ba da Dr yake fad’a tana dashi, dan kawai tana yin social life shine zai zama tana da aibu.



Ba ta son takura ma yaranta, tafi son basu duk abin da suke so, amma wannan karan tana ganin za tayi ma Dr magana akan ya auri Meema ko dan zaman jiran shi da tayi tak’i auran kowa akan shi.



Kukan da Meema shi ya dawo da Momi daga tunanin da ta fara yi.



Cikin lallashi Momi ta ce "Is ok Meema, ki daina kukan hakan, zan san yadda zan yi ki samu Dr, ni kaina ina so ki auri Sadik".



Cike da jin dad’i Meeme ta rungume Momi tana godiya.



Hanan ce ta shigo falon ta nemi guri ta zauna tana kallon fuskar Meema da ta canza kala saboda kukan da tayi.



Cikin tuhuma Hanan ta ce "Meema me yasa ki kuka?".



Shiru tayi ba ta ba ta amsa ba, hakan yasa ta fahimci dalilin kukan ta.



"Yaya Sadik ne ko?" Hanan ta tambaye ta.



D’aga mata kai tayi alamar haka ne.



Tsaki Husna tayi kana ta watsa mata harara ta ce "Wai ke Meema ba za ki hak’ura da yaya Sadik ba ne, sai ka ce shi kad’ai ne namiji, ga maza nan da suke son ki kala-kala amma ke kin nace sai shi, yanda kike da class ya kamata a ce kin hak’ura dashi tun da ya nuna ba yi da interest akan ki".



Momi ce ta harari Hanan kana ta ce "Instead of ki lallashe ta Meema amma kin tsaya kina kara ‘bata mata rai, laifi ne dan Allah ya jarrabi mutum da soyayya".



Hanan ce ta mik’e cikin shagwa’ba ta ce "Shi kenan Momi ai ga ta ga yaya Sadik d’in nan" tana gama fad’ar haka ta nufi d’akin ta.





Yau Momi ce ta kira Dr akan ta na neman shi in ya taso daga aiki.



Bayan tashi daga aiki ne ya wuce gidan Momi.



Side d’in ta ya wuce direct ganin ba kowa a falon.



A zaune ya same ta tana danna laptop sanye da medicated glass a fuskar ta.



Guri ya nema ya zauna kana ya gaishe da Momi.



Da murmushi a fuskar ta ta amsa mishi kana ta ajiye laptop d’in ta a gefen ta.



"Ya aikin Sadik" Momi ta tambaye shi.



Amsa mata yayi da cewa "Aiki alhamdulillah".



"That’s good, Alla ya taimaka" Momi ta fad’a.


"Amin Momi" cewar Sadik.



Momi ce ta kalle shi cikin kulawa ta ce "Sadik magana nake so mu yi dake mai mahimmanci".



Sadik ya fad’a "Ina jin ki Momi".



Momi ce taci gaba da cewa "Akan Meema nake so muyi maganar".



"Meema kuma Momi" Sadik ya tambaye ta.



Gyad’a mishi kai tayi alamar Eh haka take nufi kana taci gaba da cewa "Gaskiya Sadik ba na jin dad’in yadda kake ma Meema, yarinyar nan tana son ka, tun kafin ka auri Zarah take son ka kana share ta till now ba ta daina son ka ba duk da tana da masu son ta, a lokacin da na maka maganar auren ta ka kawon wasu weak excuse which i was not satisfied dasu, na k’yaleka ka auri choice d’in ka saboda ba na son matsa maka, amma a yanzu ina so ka auri Meema ko dan darajar son da take maka, in ka min haka zan ji dad’i".



"Amma Momi ni ba na ra’ayin mata biyu, beside Zarah ba za taji dad'in wannan labarin ba in har taji zan k’ara aure, sannan ni har yanzu Momi ina d’aukan Meema kamar su Hanan ne, sannan Momi kin san Meema akwai wasu behaviours na ta da ba na so, kar mu zo muyi aure da ita ana samun matsala a tsakanin mu da ita".



Cikin fad’a Momi ta ce "Oh because of Zarah shi yasa ba za ka aure ta ba saboda ba ka so ranta ya ‘baci, I am tired of your complain about Meema, this time around sai ka auri Meema, I din’t care about her behaviours kamar yadda kake fad’a, in an yi auren you can change her the way you like, I am absolutely sure she will change since she love love you, ina so ka fara zuwa zance gurin ta dan ina so ayi bikin da wuri, this time around command nake baka ba request d’in ka nake yi ba".



Rasa me yake masa dad’i Dr yayi jin cewa Momi ta ce command take bashi, a yadda Momi tayi maganar yasa da gaske take yi, zai yi wuya ta canza daga maganar da tayi.



"Zan yi yadda kike so Momi, in dai auren Meema will make you happy zan aure ta" cewar Dr.



Murmushi ne ya bayyana a fuskar Momi jin cewa Dr ya amince da buk’atar ta.



Momi ce ta ce "Yawwa Sadik, nasan ba za ka ban kunya ba, nasan za ka amince da buk’ata ta, Meema na son ka Sadik, shi yasa nake son ka aure ta, in kuka yi aure sai ka ga a hankali son ta ya shiga zuciyar ka".



A yadda yake jin zuciyar shi bay abo ba fallasa game da auren Meema da Momi take so yayi, ya sa ma ranshi zai auri Meema dan farin cikin Momi ba wai dan yana jin nan gaba zai iya son Meeman ba, yanzu abin da yafi damun shi shine in naji maganar auren yasa ba k’aramar matsala za mu samu dashi ba, dole ya bi komai a sannu dan guje ma faruwar wata matsala da ka iya zuwa a tsakanin mu.



Kallon Momi yayi ya ce "Momi plss ina buk’atar ki d’an k’ara min time akan maganar".



Momi ce ta ce "Kar ka damu Sadik, tun da har ka amince shi kenan, daman hakan na fi buk’ata daga gurin ka, sai dai ina so ka fara zuwa gurin Meema zance dan tasan ka amince za ka aure ta".



"Zan yi k’ok’ari in je Momi" Dr ya fad’a.



"Yawwa Sadik, Allah ya maka albarka" cewar Momi.



"Amin Momi" Dr ya fad'a.



Nan Dr ya canza maganar zuwa wata hirar dan ba yaso Momi ta ci gaba da mishi maganar Meema.



Ya d’an jima a gurin Momi kafin ya mata sallama ya tafi.



Bayan tafiyar shi ne Momi ta kira Meema ta sanar da ita yanda suka yi da Sadik akan amincewar auran ta da zai yi.



Farin cikin da Meema ta shiga ba zai fasaltu ba jin cewa Dr zai aure ta, tsalle ta dinga yi kamar k’aramar yarinya taje ta rungume Mominta tana cewa "Momi Dr ya yarda zai aure ni".



Ita kanta Mominta taji dad’in wannan labarin saboda yadda take son kwaciyar hankalin yarinyar ta.



Tun da Meema taji Dr ya amince da auranta ta fara matsa mishi da waya akan yaushe zai fara zuwa zance gurin ta amma sai Dr ya basar da zance ko ya ce mata sai ya samu lokaci.



Hakan ya fara d’aga mata hankali saboda tasan Dr na mata kora da hali ne saboda tayi fushi ta ce ta hak’ura da auran shi, tasa a ranta cewa za ta jure duk abin da zai mata in har zai aure ta, in yaso in aka yi auren sa yi wacce za suyi dashi dan ba za ta juri rainin hankali daga gurin shi ba dan ya ga tana son shi.



Yau ma kiran shi tayi amma bai d’auka ba sai da ta kusan tsinkewa kan ya d’auka.



"Ya aka yi ne Meema" Dr ya fad’a.



Cikin kwantar da murya Meema ta ce "yaya Sadik na ji ka shiru, har yanzu ba ka zo ba".



"Me zan miki in na zo" cewar Dr.



Marairaicewa Meema tayi kamar za tayi kuka ta ce "Haba yaya Sadik, wannan wace irin tambaya ce za ka ce me za ka min in ka zo, aure fa za muyi, ya kamata a ce kana nuna caring d’in ka a kaina, amma ko kira na ba ka cika yi ba sai in ni na kira ka".



" In na samu time zan zo" yana gama fad’ar haka ya katse wayar.



Wani irin takaici ne ya kama Meema ganin irin wulak’ancin da Dr yake mata, in ban da so yaushe za ta jure wulak’ancin namiji ko waye shi kuwa, maza nawa take juyawa yadda take so.





Yau ranar ta kasance ranar lahadi.



Muna zaune a side d’in Dr muna kallo yain da nake kwance a jikin Dr shi kuma yana shafa min gashi na.



Wayar shi ce tayi k’ara alamar kira ya shigo.



D’aga wa yayi ya ga mai kiran kana ya ajiye wayar a gefen shi ba tare da ya d’auka ba.



Ci gaba da k’ara wayar tayi amma hakan bai sa Dr ya d’auki wayar ba.



Hakan yasa na kalle shi na ce "‘Dr kana ji sai kiran wayar ka ake yi…".



Ban k’arasa maganar ba wani kiran ya sake shigowa.



Picking d’in call d’in yayi kana yayi shiru.



Ni dai ban ji me aka ce mai ba amma na ji dai ya amsa da cewa " Why are you disturbing me Meema, what do you want from me".



Jin ya ambaci Meema na tabbatar da ita yake wayar.



Kau da kaina nayi duk da raina da ya soma b’aci akan kiran da Meema ke ma Dr, ba na son yi mishi magana akan haka saboda kar ya d’auki hakan a matsayin kishi kamar yadda yake cewa in na mishi magana, sannan ina so in yi amfani da shawarar Halima akan kar in sa ma kaina komai ga me da alak’ar Dr da Meema.



Tsawar da Dr yayi ma Meema ita ta dawo dani duniyar tunanin da na fad’a.



"Will you keep that your mouth shut, kin bud’e min baki kina kuka, what have i done to you da kike min kuka".



Ban ji mai ta ce mai ba, na dai jiyo shashshek’ar kukan ta.



"Wannan matsalar ki ce Meema" Dr yana gama fad’ar haka ya katse wayar.



Ni ko tun da na ji Dr na ma Meema fad’a na fara tunanin me ya had’a shi da ita, ganin ba abin da ya shafe ni ba ne yasa na ja baki na nayi shiru, ni hakan ma dad’i ya min dan yadda na ke jin haushin Meema akan yadda take ma Dr shishshigi ji nake yi kamar in kama ta da duka.



Ko minti biyar ba ayi ba da wayar da Dr ya gama yi da Meema sai ga wani kiran ya shigo.



Cikin ladabi ya d’auka ya ce "Momi good afternoon".



"Afternoon Sadik" Momi ta amsa mishi a tak’aice.



"Sadik ya muka yi da kai akan zuwa gurin Meema?" Momi ta tambaye shi.



Shiru yayi ba tare da ya ba ta amsar tambayar da ta mishi ba.



"Sadik ba ka ji tambayar da nayi maka ba" Momi ta sake watso mishi tambaya.



"Zan je Momi, ban samu time ba ne" Sadik ya amsa mata.



"To sannu agogo sarkin aiki, duk rashin time d’in ka ina so kayi squeezing d’in time ka je gurin ta, in ba haka ba you will see my bad side of me Sadik".



"Sorry Mom" Dr ya fad’a.



Momi ce ta ce "My last warning shine Meema ta fad’a min ba ka kiran ta sai ka gadama, sannan in ta kira ka sai ka fara mata fad’a, ba nason irin haka, kasan Meema ba ta son fad’a da tsawa, in ma wani abu ta maka ka mata magana in a polite way not rude, ina fatan ka fahimce ni".



"Na fahimta Momi, zan kiyaye" Sadik ya fad’a.



"Amma ita Meema ita tace ina mata fad’a in ta kira ni" Sadik ya tambayi Momi.



"Ta fara gajiya ne da yadda kake mata, shi yasa ta kawo min k’arar ka, beside magana ta riga ta wuce’ Momi ta fad’a.



Dr ne ya ce "Shi kenan Momi".



"Ka gaishe da Zarah" cewar Momi.



"Za taji" Dr ya amsa mata.



Da haka suka yi sallama da Momi kana ya juyo da kallon shi gare ni ya sakar min murmushi.



Tun da Dr ya fara waya da Momi na fahimci akan wata magana mai mahimmanci suke magana saboda amsar da Dr da na ji yana ba ta, sai dai hak’urin da Dr na ji yana ba ma Momi ne ya tabbatar min da wani laifi ya mata, a hasashe na a maganar da suke yi yana da alak’a da inda Momi take so Dr ya je bai je ba, gurin wacce Momi take so ya je ne ban sani ba, shi yasa yake ba ta hak’uri, sannan a maganar su na fahimci kamar har da maganar Meema take mishi, tambayar da na dinga juyawa a raina shine ina Momi take so Dr ya je?.



Zuciya ta ce ta fara ayyana min wani tunani da yasa na fara sa wa a raina ko dai gun Meema Momi take so Dr yaje, to in akan Meema ne mai zai je ya Meema?.



Saurin kau da wannan tunanin nayi dan nasan zuciya ta c eke son sa min wani tunani na daban, sannan maganar da Momi tayi da Dr a waya ba ta shafe ni ba tun da har Dr bai fad’a min akan abin da suka yi magana da Momi ba, hakan na nuna cewa maganar ba ta shafe ni ba.



Dr ne ya katse ni da cewa "Zarah ya aka yi ne".



Murmushi na mishi kana na ce " Ba komai Dr".



"Momi na gaishe dake" Dr ya fad’a.



Da fara’a a fuska ta na amsa da cewa "Ina amsawa".



"Su Farida kwana biyu ba su zo ba ita da Hanan" na fad’a.



Dr ne ya ce "School yayi zafi, nima sometimes in naje ba na samun su".



Ni ce na ce "Allah ya taimaka".



Lallausan murmushi ya min kana ya ce "Amin my Zarah".



Kwantawa nayi a jikin shi muka yi fara gudanar da wata zazzafar soyayya mai wuyar fasalta wa.



Da daddare Dr ne na ga ya canza wanka ya yayi shiga cikin wani lallausan yadi kalar madara.



Ina zaune a falo na naga Dr ya fito yana ta baza k’amshi.



Kusa da ni ya zo ya zauna yana sakar min murmushi.


Kallon shi nayi na ce "Ina zaka Dr na ganka da key a hannun ka".



"Zan je wata unguwa in dawo ne" cewar Dr.



Kallon tuhuma na mishi kana na d’aure fuska na ce "Unguwa fa ka ce Dr, ka ga kuwa kyan da kayi shine za ka fita da shigar nan, salon ka fita mata su dinga kalle min kai".



Dariya yayi yace " Kai Zarah, dad’i na dake kishi, kar ki damu ni naki ne, ba dad’e wa zanyi ba, yanzu zan je in dawo".



Cikin shagwa’ba na ce "Gaskiya ni ban yarda ba Dr, sai dai ka je ka canza shigar da kayi ko ka hak’ura da fitar gaba d’aya".



Da lallashi Dr ya ce "Kin ga Zarah na riga na shirya, ki yi hak’uri in je in dawo".



"Na hak’ura, amma kar ka dad’e" na fad’a cikin shagwa’ba.



Kiss ya kai min a goshi kana ya ce "Ba zan dad’e ba tun da my princess ta ce kar in dad’e".



Murmushi na sakar mai had’e da jefa mishi wani kallo da Dr yake so in mishi irin shi.



"Me zan tawo miki dashi" Dr ya tambaye ni.



Amsa mishi nayi da cewa "Duk abin da ka ga ya maka".



"Ni nasan abin da zan tawo miki dashi" cewar Dr.



"Sai ka dawo" na fad’a.



Dr ne ya amsa min da cewa "Ok sai na dawo".



Tafiya ya fara yi yana waving d’in hannun shi, nima ina waving d’in hannun na.



Kamar yadda Dr ya ce ba zai dad’e ba, ya cika alk’awari dan ya dawo da wuri, haka ya tawo min da kayan ciye-ciye da drinks had’e da snacks.





A ‘bangare na kuwa ban san me ake ciki ba ga me da auran Meema da ya amince zai yi saboda bai min maganar Meeman ba.




Ina iyaka k’ok’arina na ganin na toshe duk wace b’araka da za ta had’a ni da Dr.




Wasa-wasa sai Dr ya tsiri fita da daddare, in na tambaye shi ina zai je sai ya ce min unguwa zai je.



Yadda yake cin kwalliya in zai fita shi yasa na fara zargin ko dai gurin budurwa yake zuwa, sai dai ba ni da wata hujja da na ke da ita da zan yarda da cewa gurin budurwa yake zuwa.



Kamar yau muna zaune na ga wayar shi na vibrating amma bai d'auka ba.



Kallon shi nayi alamar tuhuma amma ban ce komai ba.




K'aramin tsaki yayi kana ya mik'e da niyyar fita.



"Ina zaka Dr?" Na tambaye shi.



Zarah kin cika rigima, duk inda zan sai na fad'a miki kenan' ya fad'a da alamar wasa.



D'aure fuska nayi na ce "Joke aside Dr, gaskiya fitar nan da ka fara yi da daddare ya fara damu na, wace unguwa ce ka ke zuwa da ba ta da suna, in na tambaye ka sai ka ce unguwa za ka, ai da baka yawan fitar nan, wai ina kake zuwa ne Dr?" Na k'arasa maganar da tambayar shi.



Cikin kwantar da murya ya ce "Relax Zarah".



" In ka fita tsoro nake ji, ni kad'ai a gida, sannan wace fita ce sai da daddare ake yin ta" na fad'a cikin marairaicewa kamar zan yi kuka.



Dawowa yayi ya zauna kana ya fara lallashi na.



Ranar sai da nasan yadda nayi na hana Dr fita.



Tun lokacin da nuna b'acin raina akan fitar shi na samu ya daina fita.



Kiran da Meema ta ke ma Dr ya wuce limit, a fahimtar da nayi shine yanzu bai cika son amsa kiran ta ba a gaba na, wani lokacin kuma zan ji yana k'asa-k'asa da murya in rasa me suke cewa.



Hakan ba k'aramin b'ata min rai yake yi ba, bana so muyi ta samun sab'ani da Dr akan Meema.



Yau Ni kad'ai ce a gidan Dr ya tafi gurin aiki.



Knocking naji na tashi na bud'e k'ofar.



Meema ce tsaye cikin wani tsadadden material da aka mata wani irin shegen d'inki.



Fuskar ta sanye take da wani space da ya rufe rabin fuskar ta.



Hanya na bata ta shigo ba tare da ta min magana ba.



Nima guri na nema na zauna ba tare da na ce mata komai ba saboda yadda ba ta min sallama ba san da za ta shigo.



"Hi Zarah ykk" cewar Meema.



Wani banzan kallo na watsa mata kana na ce "normal".



" Dr na nan ne?" Meema ta tambaye ni.



"Gidan ai ba bak'on ki bane, za ki iya zuwa ki duba ki gani" na ba ta amsa.



Wani tak'aitaccen murmushi tayi kana ta ce "Kar ki damu, in lokaci yayi da kaina zan je in duba ba sai kin fad'a min ba".



Kallon ba ki san abin da kike fad'a ba na watsa mata kana na kau da kaina daga kallon ta.



"Na zo ne in miki tuni akan maganar da muka yi dake na cewa sai na auri Dr, kar ki ga kamar tsoro ne yasa har yanzu ba ayi bikin mu dashi ba, lokaci ne zai nuna hakan a lokacin da kika ganni a matsayin amaryar ki, ina so ki kasance cikin shiri saboda a ko yaushe hakan na iya kasancewa".



Raina ne ya fara b'aci da irin maganganun da Meema take fad'a min, sai dai ba na son in biye mata dan nasan nema rigima take yi dani, na d'auki maganganun ta kamar tatsuniya wanda ba za su faru ba, dan haka nayi saurin danne fushi na kana na sakar mata murmushin yak'e na ce "Allah ya kaimu lokacin".



" Amin Zarah" ta fad'a tana pressing d'in wayar ta dake hannun ta.



Mik'ewa tayi da niyyar tafiya kana ta kalle ni tace "Zarah na tafi, sai gani na biyu".



"A sauka lafiya" na fad'a.



Tun tafiyar Meema na fara nazari akan maganar ta, karo na biyu kenan tana min magana akan auren ta da Dr, ban san me ta shirya akan haka ba da take da tabbacin Dr zai aure ta, koma dai mai ta taka ba na jin zan iya zama da Meema a matsayin kishiya ta dan tun kan ta shigo take nema na da rigima, ina ga in anyi auren, ban san me za ta k'ullo min ba cewa Meeman ba ta fad'a mishi zuwan ta ba.




Post a Comment

0 Comments