TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 4

 


D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA HUƊU.*


        A raina na ci alwashin daina bi ta kan Haidar ma balle Mukhtar. Duk da ina ji a kamar ba zan iya haƙura da bincikar lafiyar yarona ba. Domin Mukhtar ko kansa cuta yake yi, balle ya sauke haƙƙin wani da ke rataye wuyansa.

      Sai da na shiga natsuwata sannan na shiga gidan Kawu Sale da murmushin yaƙe. Saboda tsoron faɗan Umma, da jar hararar da take wurgo mini mai saka ni tsurewa.  Su Ummu Salma suka tarbe ni cikin fara'a suna ta murnar gani na. Hannunsu na riƙe na yi wa Inna Kulu ya gida sannan na shige ɗakin Umma. Inda na hango ta tana ta lissafin kuɗi kashi-kashi. Sai da na yi murmushi mai sauti sannan na ce,

      

     "Yau kam shar! Da mu, da alama za mu ci kaza!"


     Ba ta ce da ni komai ba illa cigaba da lissafin da take yi. Zama na yi a bakin gadonta ina faɗin,


 "Wash! Allah"  


Tare da cire mayafina na miƙe da nufin yin salla, ina ƙoƙarin ficewa ɗakin na ji ƙarar wayata da ke cikin jaka. Da sauri na juyo na fiddo ta cikin zafin nama na danna kore, don ganin sabuwar lamba bai hana ni ɗauka ba.


     "Aunty ni ce Sajida! Kwana biyu? Ya su Ummu Salma?"


     Komawa na yi na zauna a gefen gadon fuskata a washe na ce,

       "Allah Sarki Sajida kowa lafiya. Ya jikin naku?"

       "Jiki Alhmdulillah! Aunty na ji sauƙi, shi ne dai da saura har yanzu!"


     Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce, "To Ubangiji ya bi da lafiya. Shi ma Allah ya tashi kafaɗunsa cikin aminci."

        "Amin-amin Aunty! Daman kira na yi mu gaisa. Sai batun da na ji wanda ko kaɗan bai mini daɗi ba."

       "Sai haƙuri kawai, haka Allah ya tsara. Fatan mu kawai ya sa shi ya fi alheri."

      Abin da na faɗa kenan zuciyata tana harbawa bakina yana rawa, saboda kallon da na ga Umma tana yi mini, bayan ta gama harhaɗa kan kuɗinta ta soke lalita.

      "To Ubangiji ya tabbatar mana da alherin da ke ciki." 

        Zancen Sajida kenan cikin sanyin murya, wacce a lokaci ɗaya na gano sauyin da ta shiga  tun a kan muryarta. Sai da na shiga natsuwata sosai sannan na ce da ita,


       "Ina Taufiƙ? Fatan yana lafiya shi ma?" 


      "Lafiyarsa lau Aunty, sai dai yaron ya shiga damuwa sosai a kan abin da ya faru. Saboda kullum kuka yake yi musamman ya ga ciwukan da ke jikin Baban shi. Ba ki ga yadda ya rame ba, duk da rarrashin da Baban yake yi masa koyaushe. Ni tausayinsu ma nake ji daga shi har Baban na shi. Don ya kasa daina zancen rashin imanin da Matarsa ta aikata mana. Dalilin da ya hana wa danginta tafiya da Taufiƙ kenan. A cewarsa ko lahira ba ya fatar Allah ya haɗa fuskarsa da tata."


      "Subhanallah! Abin bai yi daɗi ba! Ai da ya yi haƙuri har ya samu sauƙi kafin a san abin yi. Saboda yanzu ita kanta ba a san ina take ba balle halin da take ciki. Don Allah ki dinga nuna masa komai na duniya fararre ne kuma yana da ƙarshe. An san abin da ta yi ba ta kyauta ba, amma ya yi mata uzuri don shi ne silar faruwar komai."


      Cikin sarƙaƙƙiyar murya ta ce, "Ni ma dai haka na ce masa. Kuma ai son shi ne ya sa ta yi abin da ta aikata. Amma ya kafe a kan babu shi babu ita, asali ma bai bari danginta suka bar garin nan ba; har sai da ya rattaba mata saki biyu ya bayar a ajiye mata."


     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" 

    

    Umma da Inna Kulu suka iso inda nake da sauri suna tambayar lafiya. Jiki babu kuzari na katse wayar ina ta maimaita kalmar,

       "Hasbunallah wani'imal wakil." 


     Saboda ban ji daɗin sakin ba, na so ya bar ta ta ji da abin da ke bisa kanta har ta dawo hayyacinta. Domin mugun kishin da take yi masa babban ciwo ne a wurinta, wanda warkewar shi ba nan kusa ba, balle ta manta cin amanar da take hangen ya yi mata. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce da su Umma,


       "Mijin Maman Taufiƙ ne ya sake ta, kuma sakin ma har biyu duk da jinyar da yake yi."


      "Ai ta yi ganganci! Don wannan shi ake kira baɗi babu rai! Ta yi haukar kishinta saboda shi, ya raka ta da takardar sakinta har gida ta ci wautar ta. Ai shi ɗa namiji ba a yi masa gwaninta, yanzu wa gari ya waya? Ita ko amaryar da ya auro?"


     "Ita!"


Amsar da muka bai wa Umma kenan har muna haɗa baki ni da Inna Kulu. Fuskokinmu ɗauke da alhinin abin, musamman ma ni da gabaɗaya jikina ya mutu. Saboda sanin ɗaukar da Maman Taufiƙ ta yi wa Aminin mijinta, amma ga yadda ƙarshen so da kulawar da ta nuna masa ya ƙarge. 

   

     'Ni da ita ƙaddararmu kusan ɗaya'


    Zancen da na yi kenan a zuciyata ina ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, yayin da na bar Umma da Inna Kulu suna zanta abin a tsakaninsu.


****

Tsawon kwana biyu ina jimamin sakin da aka yi wa Maman Taufiƙ, wanda na ji zafinsa fiye da wanda aka yi mini. Haka ma ɓangaren Haidar na yi iya bakin ƙoƙarina wurin yakice ƙulafucinsa a raina. Domin na zille wa buƙatar Najib, da yake so mu je sabuwar makarantar da aka sauya masa, Domin na gan shi. Cikin dabara na bar masa wuƙa da nama, sannan na nuna masa ba na so na je ya ce sai ya bi ni. 

     Amma kuma duk na tuna shi a raina sai na ji kuka ya taso mini. A gefe ɗaya kuma matsalar MD da ta so kassara ɗan kuzarin da ya rage mini. Saboda ƙoƙarin kauce wa duk abin da zai haɗa ni da shi nake yi. Kuma ban fasa zuwa aikin ba duk da gargaɗin da ya yi mini. Aikin ma ina yi tuƙuru babu kama hannun yaro, Amina ma da ke ɗauke mini hankali ko ta zo; ba na bari mu yi doguwar magana. Da mun gaisa muka taɓa hira sama-sama nake kama bakina na tsuke. 

       Sai dai kuma ga dukkan alamu matakin da na ɗauka bai yi masa daɗi ba. Saboda na fahimci damuwa ƙarara a kan fuskarsa, ina hankalce da shi wani lokaci sai ya so ya yi mini magana, sai kuma ya tsuke fuska kamar ba shi ba ya waske. 

      Ban san na kai shi bango ba sai da aka tashi aiki, ina ƙoƙarin miƙa wa Baba Masinja takardun da ke hannuna, da nufin ya kai masa. Babu zato na tsinkayo muryarsa a sama cikin tsawa ya ce,


      "Baba bar mata kayan! Idan ba za ta iya kawo wa ba ta bar su a hannunta!" 


     Duk da na ji tsoron ganin shi a yanayin da na gan shi, amma har ga Allah ya so ba ni dariya. Saboda ganin shi da kansa ya ce kada na sake zuwa ofishinsa. Tare da faɗar na dinga bai wa Baban saƙo ya kai masa ko ya karɓo mini. To sauya zance na mene ne bayan umurninsa nake bi.

     Baba Masinja yana sosa kansa ya ce,


     "Ranki ya daɗe ki yi haƙuri ki kai masa kawai. Tun da ba ya so kina ba ni, yana da kyau ke ma ki daina."


     Ɗan jim na yi riƙe da takardun ina nazarin abin yi, sai da Baban ya sake maimaita maganarsa tare da ba ni umurnin na je, sannan na nufi hanyar ofinshinsa. Zuciyata cike da tunanin abin da ya sauya masa ra'ayi cikin kwanaki ƙalilan.

     Tura ƙofar na yi da guntuwar sallama ba tare da na nemi izinin shiga ba. Kai-tsaye bakin tebutinsa na nufa babu jinkiri na dire masa takardun zan juya.


    "Wai me kike nufi ne?"


Babu shiri na yi hanzarin juyawa fuskata ɗauke da zallar mamaki. Idona a kan fuskarsa na ce,

 

    "Me ya faru kuma?"


"Au! Tambaya ma kike yi ko?"


    Ya ƙare maganar tare da wurgo mini wani kallo cike da tsare gida.


      "E, saboda ban san me na yi ba!"


     Bayan ƙeyarsa ya fara shafawa kansa a duƙe, sannan ya ɗago fuskarsa a zafafe yana faɗin,


     "Saƙon da kike bai wa Baba ya kawo ke me ya ci ƙafafuwanki da hannunki?"


    Mamakinsa ya so kashe ni, idona a kansa na ce, 

       "Yanzu har ka manta kashedin da ka yi mini a kan zuwa ofishin nan?"


    "Ban manta ba! Amma ba na so kina bai wa kowa saƙon, musamman mai muhimmancin da ya dace mu tattauna shi da ke."

      "Sir! Akwai bayanin komai da nake yi a jikin takarda, wanda nake zaton idan ka gani za ka gamsu, kuma zai wadatar da duk wani bayanin da zan yi a baki..."

        "Ba zai wadatar ba! Saboda zuwa da kai ya fi aike!"

         "Ok tom! Zan kiyaye! Iya matsalar kenan na tafi?"

 

      Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan ya zagaya cikin kujerarsa, yana tattara takardun da na kawo da wasu wuri ɗaya. Sai da ya tura su drower ya rufe da key, sannan ya ja wasu takardun a hannunsa ya raɓa ta gefena zai fice. 

      Bayan shi na bi da kallo kamar na yi magana kuma na fasa, ni ma na take masa baya na fito, ban tsaya komai ba na nufi harabar ma'aikatar. Amina na hango ta nufo ni na dakata har ta iso, a daidai lokacin da zai bi ta gefena ya wuce fuuu! Ya bar ni ƙamshin turaren jikinsa. Kaina na duƙar kamar ban lura da shi ba, ina duba agogon hannuna har Amina ta iso tare da wasu abokan aikinmu maza da mata. 

      Duk da gaisawar da muke yi, hakan bai hana ni kallon motar MD ta gefen idona ba. Wacce ke ƙoƙarin ficewa daga cikin gate ɗin ma'aikatar zuwa bakin titi.  

       Tare muka jera da su muna ta hirar zafin ranar da ake yi a lokacin, har muka fita gate kowa ya kama gabansa. Zuciyata cike da tunanin MD da kalar da ya koma, mai wuyar fahimtar inda ya dosa.






     Ni ma dai ina so na gane me yake nufi da wannan sabon halin🧐






manage plss!




Post a Comment

0 Comments