TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina Na book 2 page 6

 D. Auta ce✍🏼

*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



 *LAMBA TA SHIDA.*


       Gabaɗayanmu ta ba mu dariya, saboda kalar muryar da ta yi waƙar kaɗai ta isa saka mutum dariya. Sai dai ni kam ban iya ko murmushi ba balle na yi dariyar. Saboda kaina ya gama ƙullewa tamau, da tunanin MD da yanayin yadda yake ba ni kulawa kafin yanzu. Wanda idan ba mantuwa na yi ba, daidai da rana ɗaya bai taɓa nuna mini wata alamar da zan gano rashin ɗa'a a wurinsa ba. Amma tabbas na san kulawa tana daga cikin So da ƙauna. Ya'la'alla mai ƙarfi ne, ko kuma  sassauƙan da ba ya luguiguitar da zuciyar ma'abocinsa, balle har a ramfo shi da inda ya dosa. 

       'Idan har kulawar da MD yake ba ni shi ma so na yake yi; to ni kuma babu abin da zai hana ni karɓar shi ɗari bisa ɗari. Duk da kuma ina jin fargabar haɗuwa ta wuri ɗaya da matarsa...'


     "Tunanin me kike yi?"


Firdausi ta katse mini  tunanin da na lula, ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce,

       "Zancen Inna Kulu ne nake juyawa a cikin raina. Wanda ni kaina na daɗe da haddace shi tun kafin yanzu!"


      "To ki yi ƙoƙarin ƙarfafa zuciyarki ko don abin da zai taso a gaba. Domin ko ba ki auri MD ba dole dai wani aure za ki yi. Kuma ba lalle ne ki samu wanda bai da mata ba. Don haka yanzu ya dace ki fara shirin fuskantar kowane irin ƙalubalen da zai fuskanto ki."


Maganar da Inna Kulu ta faɗa kenan tana ƙoƙarin miƙewa tsaye.


     "In Sha Allah!"


Abin da na iya furtawa kenan saboda gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau.

       "Hmmmm! Waton ko bayan dara akwai wata caca!"

        Maganar da na yi kenan bayan Inna Kulu ta fice daga ɗakin, Firdausi ta yi mini kallon tsanaki sannan ta miƙe tsaye tare da jan hannuna tana faɗin,

        "Zo mu je ki raka ni wurin wata dubiya kafin Abban su Khadija ya zo ɗauka ta!"

       Mayafina kawai na ja muka fita, Umma na yi wa bayanin inda za mu je sannan muka fice. Bayan fitar mu gidan, Firdausi ta kira sunana da wata murya mai cike da natsuwa. Sannan ta karkace kanta tana kallo na ta ce, 

      "Kada ki yi wasa da wannan damar matuƙar Allah ya kawo miki ita gabanki." 


        "Wace dama kenan?"


"Zuwan MD a cikin jerin masu neman auren ki. Saboda babbar sa'a ce gare ki da rayuwarki. Ko babu komai shi ne ya san sirrin zaman auren da kika yi da Mukhtar. Kuma ina kyautata zaton ba zai miki riƙon sakainar kashi kamar yadda Mukhtar ya yi miki ba. Domin wannan mutumin tun a duba ɗaya za ki gano natsuwa da kamalar da ke tattare da shi. Sannan ya tausaya miki kina gidan wani ina ga kin zama matarsa?"


      "Hmmmmm! Ba ki ma sani ba, a lokacin auren Mukhtar dubu talatin ya turo mini na yi hidimar bikin. Kuma har ga Allah na ji daɗin kuɗin, kuma sun rufa mini asirin da ake ƙoƙarin bankaɗe mini a lokacin."


       "To bari ki ji! Wannan shi ne mijin rufin asiri wanda zai fi kowa sanin darajar ki! Ba kuma wai don yana miki alheri ba ko don ya ba ki kuɗi, a'a! Ita Jumu'a mai kyau tun daga Laraba ake gane ta. Domin akwai tazara sosai tsakaninsa da Mukhtar. Idan aka yi dace Allah ya haɗa kanku shi kenan kin huce haushin aure! Don samun irin wannan mutumin abu ne mai wahala a wannan lokacin da muke ciki. Saboda maza da yawa sun zama ba ni gishiri na ba ki manda. Ba za su bayar da abin su ba; sai sun san za a dawo musu da tukuici. Ke kuma bai taɓa nuna miki wani baƙin hali a ƙwayar idonsa ba. Ko iya haka ya dace ki gano gaba ma da gabanta."

         Zancen Firdausi kenan bayan mun shiga adaidaitasahu mun zauna. 

         Hawayen da ke ta ambaliya a kan fuskata na goge, sannan na ce da ita,

      "Ni matsalata da shi a 'yan kwanan nan bai wuce laifin da yake ta ɗora mini ba. Bayan ban san lokacin da nake masa laifin ba ma balle na kauce wa wani idan ya zo"

      "Kamar zama da Mukhtar ya sa kin manta tantagaryar So da hidimarsa. Abin da ba ki sani ba; So mai zafi shi yake sa duk abin da mutum ya yi ki ga bai yi miki daidai ba. Domin abu kaɗan idan ya yi za ka ji ranki ya ɓaci nan take. MD yana miki So mai zafi, ta yadda yanzu abin ya so ya fi ƙarfin tunaninsa balle ya yi controlling kansa. Ki masa uzuri a kan duk abin da kika gani ko za ki gani, saboda akwai bambanci tsakanin So da ƙauna na gaskiya, da irin tafiyar da kika yi a baya ke da Mukhtar. Domin yanzu ne za ki san mene ne so da abin da ya ƙumsa a cikin duniyar aure. Don haka yana da kyau ki zama cikin shirin tarbar sa kamar yadda ya zo miki. Ko babu komai yana da mata, kuma ba don ba ya son ta yake ƙaunar ki ba. Ya zama dole ki koyi dabarun yayyafa wa lambunsa ruwan sanyi, ko don tsiron da ke ƙoƙarin fita ya yi kyau ya yi ƙarko."


      Baki a sake na dinga kallon Firdausi, saboda a baya na fi ta dubarun magana, kuma na fi ta sanin makamar So da komatsansa. Amma yanzu ita ce ke karantar da ni saboda Mukhtar ya daɗe da goge mini hadda.

       "Rayuwa kenan! Daman abin da kake so ba lalle ne ka same a lokacin da kake buƙata ba. A baya ni ce malamarki a ɓangaren So, amma yanzu ga shi reshe ya juye da mujiya."


     Dariya muka yi gabaɗayanmu, saboda tuno abin da ya wanzu a can baya. 

     Firdausi ƙawata ce tun ta ƙurciya, a lokacin da ina zuwa islamiyar da ke cikin unguwar Sama Road, a duk lokacin da na zo garin. A can muka haɗu, kuma a nan na san ta, har gidansu da ke kusa da makarantar ina zuwa.

      Akwai zumunci mai ƙarfi tsakaninmu wanda har ya shafi Iyayenmu. Saboda su Umma suna zuwar musu abu idan ya samu na murna ko na jaje. Haka ma Mamarta tana zo wa su Ummu ko da ba na garin. Sannan ko da Iyayenta suka bar Sama Road suna zumunci da su Umma sosai. Yanzun ma a can Sama Road zan raka Firdausi, don ba ta yada zumuncin suka yi da mutanen 'yan unguwar ba.


       Idan ban manta ba, a baya ni ce nake rubuta wa Firdausi wasiƙa ga samarinta. Saboda na fi ta iya kalaman soyayya da yadda ake tsara zance daki-daki, ta yadda zai sace zuciyar wanda aka yi da zummar a burge shi. Kuma Alhmdulillah kwalliya tana biyan kuɗin sabulu. Domin duk muka yi sai an yaba kuma an jinjina mata, daga baya idan ina son yi mata rashin kirki sai na ce sai ta yi da kanta, dole ta koya saboda jan ran da nake yi mata. Da tafiya ta miƙa sai ga Firdausi tana tsara wasiƙar soyayya tiryan-tiryan, wacce ta ƙunshi kalamai zafafa musamman da ta haɗu da miji ɗan Aljannah.

     Ni kuma rayuwa ta juya mini baya na dawo wata doluwa, komai ya tsere. Aka bar ni da azancin magana, wanda shi kaɗai na tsira da shi a gidan Mukhtar, wanda ya rage bai salwantar mini ba. Shi ɗin ma don bai da iko a kan hakan da tuni ya saka ƙafa ya murje.


     Har muka isa gidan da za mu je, ba mu daina tuna baya da shirmen da muka yi ba. Tare aka tarbe mu a gidan saboda ni ma sun waye ni ba su manta fuskata ba. Kasancewar dubiyar rashin lafiya ce muka je, addu'a muka yi wa mai jinyar sannan muka fito, masu gidan suna ta saka mana albarka, tare da sallahun mu gaishe da gida.

      Mun fito titin kenan muna neman abin hawa, sai ga wata mota ta karyo kwana aguje har tana ƙoƙarin ture mu. Cikin sauri muka ja baya Firdausi ta fara masifa, har motar ta yi gaba ta dawo a hankali ta tsaya daidai inda muke tsaye.

     Kasancewar gilashin motar tintac ne, hakan ya sa ba mu hango wanda ke ciki ba sai da ya zuge gilashin. Baki buɗe muka dinga yi wa juna kallon-kallo, saboda tsohon sanin da muka yi wa juna da mai motar. Shi ma cikin sauri ya buɗe ya fito fuskarsa ɗauke da murmushi da mamakin ganin mu.


      "Firdausi daman kuna duniya ke da Zaituna?" 


    Harara ta maka masa tana 'yar dariya ta ce,

      "Daga lahira muke, shi ya sa kake ƙoƙarin aika mu mu koma saboda ka yi sabuwar mota!"

       "Ashe har yanzu wannan bakin naki bai daina tsiwa ba?"


     "Idan da ire-irenku a gari ai dole mu tayar da tuba ko da mun daina!"


     "Allah ya yafe miki Firdausi! An girma ma ba a canza hali ba! Ke kam Zaituna kina nan da sanyin halinki har yanzu! Shi ya sa ake cewa idan ka daɗe ba ka ga mutum ba; ka tambaye shi bayan rabuwa kawai, kada ka tambaye shi halinsa. Saboda hali zanen dutse ne ba ya canzawa sai dai a rage."

      "Kai ma ai halinka yana nan na zuba! Na zaci yanzu da girma ya zo ka daina surutu magananne kawai!."


     Dariya muka yi dukanmu, saboda zancen Firdausi, inda da sabo na saba da ganin rikicinsu tun muna yara. Musamman a lokaci da ya nuna yana so na, tsiwa da tsokana babu kalar wanda Firdausi ba ta yi masa.

     Yana dariya ya ce, 

         "E, na ji dai, komai za ki ce ki ce kawai, tun da kin fi ni baki. Ni iya surutun kawai gare ni amma kin dame ni kin shanye da zaro zance!"

     Gaisawa muka fara yi a tsanake tare da tambayar bayan rabuwa. Daga nan ya sanar da mu dawowarsa kenan a ƙasar, ko sati bai yi ba ya je karatu Sudan ya kammala.

     Fatan alheri muka yi masa sannan ya ce mu zo ya kai mu gida. Na nuna masa ya tafi kawai kada mu takura shi, Firdausi ta yi tsalle ta dire, a kan bai isa ba sai ya kai mu har ƙofar gida ya ajiye mu.

      Ba don na so ba na shiga motar muna tafe yana satar kallo na ta madubi. Hira suke yi da Firdausi tana tambayar shi matarsa da 'ya'ya. Ya ce da ita har yanzu bai ga matar auren ba balle zuwan 'ya'yan. 

      Firdausi ta dinga yi masa sharrin tuzuru za su kiɗa masa gangar Gwauro, tun da ya tsufa  da gemu babu aure. Har ya ajiye mu suna ta tsokanar juna ya juya, tare da saƙon mu gaishe da Umma kafin ya zo gaishe ta.

      Ina dariya na ce da Firdausi, 

 "Arma ya yi ƙiba kamar ba shi ba."

     Mere ta yi sannan ta ce, 

 "Tun da sun ci kuɗin Gwamnati ai dole su yi ƙaton tumbi."

    

     Tuno wane ne Arma da gidansu da ma Baban shi, ya sa na ja bakina na tsuke. 

     Saboda Mahaifinsa tsohon ɗan siyasa ne da ya yi zamani tun muna yara. Yanzun ma da shi ake damawa a cikin siyasar Jahar Sokoto duk da shekaru sun gangara. Ya taɓa riƙa muƙamin mai bai wa Gwamna Shawara, bayan muƙaman da ya sha riƙewa masu daraja a cikin Jahar har zuwa Tarayya.


     Wunin ranar zir ina tare da Firdausi, sai dare maigidanta ya zo ya ɗauke ta. Bayan ya yi wa su Umma alheri ni ma ya yi mini jajen abin da ya faru.

      Kwanan farinciki na yi da dare. Saboda duk lokacin da na tuna MD so na yake yi sai na ji wani farinciki ya lulluɓe mini zuciya.

      Don daman can mikin son shi yana nan bai bar ni ba, kawai dai ina basarwa ne tun lokacin da ya hana ni barin gari. Wanda na ƙarfafa haushin shi da nake ji fiye da son da nake yi masa. 


     'Ohhh Allah! Yanzu ni ce bazawarar da Umma take ta gudun kada na zamo?'


     Zancen zucin da na yi kenan a zuciyata, a lokacin da na juya kwanciyata. Saboda baccin da ya ƙaurace wa idona. Na shiga saƙa da warwara ni kaɗai daga ni sai raina da zuciyata.





Hmmm! Wani kafcen zai fara.🤭 Allah ya sa kun hango🧐




Post a Comment

0 Comments