TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zazzafan so page 16

 

📄 *16*



Sallama ya musu, Yusuf ya amsa.

Sannan ya matsa kusa da su ya mik'awa Yusuf hannu suka gaisa..

Sai lokacin Hafsah ta sami damar matsawa daga kusa da Yusuf, ta d'an wayance ta gaida Auncle Abdallah.

Ya amsa cikin sakin fuska, sannan ya kalli Yusuf yace.

"Kuyi hak'uri fa, na shigo muku babu shiri"

Kafin yayi magana Hafsah tayi saurin cewa..

"Auncle dama, mun gama raka shi zanyi ya gaida Hajiyah"

"OK shikenan to"

Ya fad'a yana binta da wani kallo da bata san na meye ba..

Ta kalli "Yusuf mu tafi koh?

Ya bita da wani kallon shima, sannan ya bi bayanta.

Auncle Abdallah ya k'ara binsu da kallo.

Yarinyar na da hankali bai jin zata saka rayuwarta cikin irin wannan soyyayar ta zamani.

Sannan me ma ya kaishi zarginta shida kawai shigowa yayi ya ganta tsaye??

Yai A,uzubillah" azuci. Amma kuma yana da yak'inin bata zance Yarinyar ko dai yau suka had'u ne?..

Ya san dai ba zata taba gangancin kula wani bada sanin abbanta ba.

To ko Yaya Habeeb d`in ya sakko da raayinsa ne"?

Ya kasa gano amsar, kawai sai ya bar wannan tunanin, ko ma dai menene ai yarinyar ta girma..


♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥


Da sallama suka shiga falon Hajiya, bayan Hafsah ta shiga ta fad'a mata zai shigo.

Yusuf ya zauna akan kujera Hafsah kuma na kusa da Hajiyah..

"Granny, ina yini"

Yusuf ya gaisheta.

"Lpia lau" ta amsa cikin fara,a.. Sannan tace 

"Ya mutanen gidan duk suna Lpia?

"They are all fine wllhi"

(sabon-salo🤔)

Hajiya ta fad'a a zuciyarta.

Suka d'anyi shiru sannan Yusuf yace

"Ajiya (Hajiya) you remembered me my grandma,.. Kakana Dada, she was old enough like you before she died.."

Hajiya dai cewa tayi 

"Allah sarki.

Ya kallo Hafsah da tayi shiru ya mata kallon da ya saba.

"Baby, let me go home"

Ya mik'e sannan ya kalli Hajiyah ya had'e hannayenshi biyu alamar girmamawa (kamar yadda indiyawa suke) sannan yace.

"Stay strong and blessed grandma."

(wai fa shi nan addu,a yai mata)😅

"A sauka lafiya."

Hajiyar tace masa.

"Bye bye"

Ya d'aga mata Hannu.

Hafsah ta mik'e ta bishi..

Suna fita taga ya wani had'e rai.

Tuni tana d'an sha jinin jikinta.Ta rakashi har waje, inda ya ajye motarshi.

Har yanzu ko k'ala baice mata ba.

Suka tsaya a bakin motar, ta d'anyi murmushi sannan tace,

"Baby me ya faru ne?

Ya d'an kalleta ya watsar. Sannan yace.

"OK, ke biki san abinda kika min ba koh?.. Is good, ai nine nazo gidanku ai,..This gave you opportunity to disgrace me!".. Ok let's see if you will see me here again!"

Take tsoro ya kamata. Ta tausasa murya.

"Haba Baby, me kake fad'amin ne ? Me aka maka kuma koh Hajiyah c..

Bata k'arasa ba ya shige motar shi ya figa da gudu ya bar ta da k'ura.

Ta d'aura Hannu aka tare da cewa "Oh my God, me ke shirin faruwa da ni ne?

Tana tsayen uncle Abdallah ya fito daga gida, dole ta bar wajen.

Ta shiga gida zuciyarta a jagule.. Wannan wacce irin al,mara ce?

Yanzun idan Yusuf ya rabu da ita ai ta kad'e.. Take kwallah ta ciko mata ido.

Har yanzu bata gano me yasa ya chanja mata ba, a cikin abinda baifi mintuna biyu ba.

To koh don ta kaishi wajen Hajiyah ne.? Ko kuma yanayin da Hajiyar ta karb'e shi ne bai mishi ba?? 

Yace wai tayi 'Disgracing' d'insa?

Bata lura ba ashe har ta shigo falon Hajiyah, tayi saurin goge fuskarta, kawai sai ta nufi hanyar d'akin kwananta.

Muryar Hajiyah taji tana ce mata,

"Ke Hafsah zo nan"

Dam.. Gabanta ya fad'i, yanayin yadda Hajiyar ta kira ta ya nuna mata akwai wata a k'asa.

Ta tako ahankali ta zauna a k'asa gefen Hajiyah.

"Gani.

Hajiya ta fara magana fad'a-fad'a.

"A ina kika samo wannan Yaron?.. bata jira cewarta ba ta d'ora.

"Yaro kamar ba d'an bahaushe ba, sai wani turancin k'arya yake yana wani b'ab'bata hausa?..

"Kuma don rashin d'a,a ya wani gaisheni yana kan kujera koh..? 

Wai ku 'yan boko har yana cemin wani 'Bebai' (bye bye) saboda raini😠

" wato don ina kakarki ba zai girmama ni ba. Ko ance mishi wasa nake da ku?..

"Kiyi ha'kuri Hajiyah"

Hafsah ta fad'a tana share kwallah.

"Ke hak'uri ya kama." 

Hajiya ta fad'a tana kauda kai gefe..

"Yo ni Allah na tuba meye abin yabawa a wannan yaro abu kamar 'Karan-bawul'🤣

"Yaro sam babu hankali a tattare da shi.?

"Shi habibun har yana ina kike kula wannan d'an?"

Gaban Hafsah ya fad'i. Ya zatayi idan Abba yasan da wannan magana?

Sai yanzu ta gane kasada tayi fa ta kawo Yusuf gidan hajiya, sam ta manta zancen zai iya zuwa kunnen Abba, idonta ya rufe buqatar ta kawai ganin Yusuf, nan fargaba da tsoro suka cika ranta.

"Don Allah kiyi hak'uri Hajiyah."

"Hmm Ni me akayi min ki tashi kije ki kwanta.

Zumbur ta mik'e dama Zaman ya isheta, to da wanne zataji?

Ta fad'a kan katifa ta kife kanta, tana tuno maganganun Hajiyah..

"Wai Yusuf bai da d'a,a?? 

To me yayi wa Hajiyan?

Ita bata ga me yai mata ba? Meye abin kushewa a Yusuf?

Ahankali taji haushin Hajiyah na shigarta. Yanzu idan taja Abba ya rabasu ai an cuceta..

Sai yanzu take danasanin kawowa Hajiyar shi.

wallahi ba don dare yayi ba babu abinda zai hanata tafiya gida.. Haka kawai don jininsu bai had'u ba sai ta hau aibata shi?

(A tak'aice dai idanun Hafsah sun rufe, so ya hanata ganin aibin Yusuf.

Ta manta abinda babba ya gani yaro baya iya hangoshi.

Zatonta k'iyayyar Hajiyah da 'Boko' ne yasa ta aibata Yusuf, wanda azahiri Hajiyah bata k'in boko sai dai tana kyamatar dab'iun turawa da yaran yanzu ke ara yawanci, wanda ita sam 'ya'yanta da jikokinta Allah ya tsare su.

Kana ganinsu kaga wayayyu wad'anda Bokon ya ratsa sai dai kuma wayewa irinta addini da sanin rayuwa da kuma addu,ar iyaye ya hanasu su kaucewa hanya.

Sab'anin irin Basma ko Yusuf wad'anda basu sami wannan gatan ba. Amma Hafsah sam ZAZZAFAN Son data ke yiwa Yusuf ya hanata ganin hakan.)

Tunaninta ya tsaya data tuna yadda suka rabu da shi Yusuf d'in..

Tayi saurin mik'ewa ta dauki wayarshi ta danna kiranshi.

wajen sau biyar bai d'aga ba.. Sai a na shidan ya d'auka

"Mene ya faru?

Da haka ya amsa wayar..

Cikin kuka tace:

"Haba Yusuf yanzu na chanchanci haka a wajenka?..Please me na maka? Baka ganin irin son da nake maka Koh?

"To me zan miki ne while kink'i ki min abinda nakeso, mene amfanin relations enmu, kina wulak'anta ni, So I think kawai mu rabu, am tired with this meaningless relation. Wanda babu wani abu da kike min and u always claiming kina so na!?.. A ina son yake?


*Nikam nace azuci yake Yusuf*😇🏃🏼‍♀


Ya cigaba u can't even allow me to kiss you?.. Wanne irin Soyaya ne kina min?..

Sai yanzu Hafsah ta gano zancen.. Tab' al,amra sun Chakud'e.

'Anan ya dace ta fahimtar dashi wani abu, amma kalmar 'su rabun' daya fad'a shine ya rudata ga kuma tasirin soyayyarshi a zuciyarta bata son ta kuma bata mishi, don haka ta kwantar da murya ta shiga rarrashinshi.'

please kayi hak'uri ni ba ina nufin komai ba ne,..

please ka daina fad'amin cewa mu rabu, numfashi na ba zai d'auka ba." please am sorry.

"I know I hurt u but

trust..

"Noo ya katseta, I need to rest, ki kyaleni kawai.

Ya katse wayar.

Tafi minti biyar bata motsa ba, bare ta cire wayar daga kunnenta..

Ya akayi Yusuf ya iya fushi haka shi baya lura da cewa hakan bai dace ba?

Baya tausaya mata da irin son da take mishi har yake ik'irarin su rabu??

Wai Ita meye mafitarta a wannan al,amari, zata kwa iya yin abinda yakeso?.. Wata zuciyar tace

"Idan har shi kad'aine mafita ba!!

To ldan tayi haka kuwa laifi nawa tayiwa iyayenta, musammaman ma abbanta?

Ta mallaki waya bada saninshi ba.

(Duk da tana da yak'inin lokaci yake jira ya mallaka mata ko da iPhone ce idan tana so)

Tana tare da Yusuf bada saninshi ba.

Sannan ta zo taci amanar tarbiyyar daya mata??

Wata zuciyar tace,

"Hafsah idan fa kika rabu da yusuf kin rasashi fa har abada... Ki tuna gogewarshi da wayewarshi ga kud'i kuma, duk matan garinnan ke kad'ai ya zab'o kina da yaki'nin ('Assurance') baya kula kowa sai ke.

Secondary level kike , amma haka ya zab'o ki..

Yusuf ya fiki sanin rayuwa amma ahaka yake sonki. Shin ma ya zaki iya jurar rashinshi bayan shine daidai da burinki?

"Hafsah idan fa kika yi asarar Yusuf ba zaki sami wanda ya fishi ba..

*Ku biyo ni don jin ko Hafsah zata bi layin da jamila tabi ne??*




Post a Comment

0 Comments