TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

HAUWA KULU BOOK 3

   ‘YAR CIKIN BADALA

   (HAUWA-KULU)

                                  3


              

      PAID BOOK

 SUMAYYAH ABDULKADIR

           babbangoro2015@yahoo.com

                        07030137870

                        (whtsp only)


            SADAUKARWA

SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTATAFAINA ‘YAN CIKIN BADALAR KANON DABO.












      HAUWA-KULU -3

        BAKO DAGA KUMASI (GHANA)

Y

ammacin ranar wata Alhamis, da misalin karfe hudu na yamma, iskar damuna na kadawa mai dadin gaske a tsakar gidan su Hauwa, hadari ya gangamo, gab ake da fara ruwan sama. Innar Hauwa na zaune akan kujera ‘yar tsugunne a madafinta tana kullin alalar leda wadda za suci da daddare. 

Idan ta kulla ta saka a tukunya. Tana yi tana sauraron radiyo abunta cikin shirin jakar magori A daidai wannan lokacin ita kuma Hauwa tana daga cikin dakinta a kwance kamar wadda ruwa yayiwa duka sabida yadda ta kudundune a cikin bargo bisa dindimemiyar sabuwar katifarta (vitafoam), amma kuma zuciyarta babu dadi, a kwanakinnan ta rasa me ya sa ta ke jin babu dadi sosai a cikin ranta, amma data yi tsam da ranta ta yanzun kusan ta gano dalilin hakan; LIKITA SARHAM! Shine dalili ba komai ba.

Yau kusan kwanaki bakwai kenan da take fama da wannan damuwar a kasan ranta, don ganewa da ta yi Dr. Sarham ya daina kulata, ga shi dai yana zuwa gidan ba wai ya daina zuwa ba, amma yanzu sai dai kawai ta jiyo muryarsa daga waje shi da Inna in suna babatunsu, ko nemanta ya daina yi a cikin gidan in ya zo. Balle ya zo kofar dakinta ya takaleta da Magana yadda ya saba. 

Hauwa ta yi duk iyaka tunaninta don gano laifin da tayi masa da har yasa Likita Sarham ya daina shiga sabgarta ta rasa. Kamar ma gaba yake da ita yanzu.

Hauwa ta muskuta ta gyara kwanciyar ta. Wata zuciyar ta ce da ita. "To ke Hauwa? Me ye abun damuwa don Sarham ya daina kula ki? Tunda dama ba don ke yake zuwa gidan nan ba, yau ina ganin ikon Allah don Innarsa ne yake zuwa fa shine har albarkacin ta yaga dama ya kula ki. Name zaki dorawa kanki damuwa a kansa don ya ga damar daina kula ki kuma??? Tayi wani tsaki irin na jin haushin kai. Ta ce wa ranta, daga yau ita ma za ta koyi fita sabgarsa, kome yake ji dashi ya tara ya samu, me yake takama da shi da ya wuce likitancin da bai iya ba? Ina dalili da za ta damu kanta akan fushinsa da ita, fushin ma na babu gaira babu dalili? Da dai ace ta san ta yi masa wani laifi ne sai ta damu, amma tunda ta san bata yi ba ina dalili?

 Don ko ta jiyo muryarsa a falon Inna, ta jawo mayafi ta fito daga daki, ta tsaya daga bakin kofarta ta gaishe shi, ta lura tana kuma jin sai ya ga dama yake amsawa, yana wani basarwa kuma a shalake kamar an yi masa dole sai ya amsa. Daga amsawar kuma baya kara ce mata komai saidai ta gaji da tsayuwarta anan ta koma dakinta.

Ta yi kwafa data tuna jiya haka haka yayi mata, ta girgiza Kai tana fadin. "yayi da ‘yar halak. Ni na damu kaina da shi, mutumin nan fa babu wata alaka ta jini tsakaninmu, banda ta zumuncin Allah da taimakon da ya saka kansa yi mana. In haka ne me zai sa canzawarsa gareni ta dame ni? Tunda ita Inna ai bai canza mata din ba kaamr ma yafi zuwa akai-akia yanzu har fiye da da, koda ba zai jima ba. 

Amma abin mamaki, duk yadda ta so ta daina damuwa din da sharetan da Dr. Sarham yake yi, ta kasa daina damuwar, abin ya dameta, saboda ko ta ki ko ta so, ta san cewa Sarham wani mutum ne mai matsayi a rayuwar su, wanda ya taka muhimmiyar rawar data fi ta dan uwan jini a rayuwar ta data Innarta, wanda ya fi gaban ta dauki gaba da shi, wai don kawai ya daina kula ta bisa ra'ayin kansa.

 Muhimmancinsa a gare ta ya zarta haka. Aka ce ka yiwa dana dam uzuri sau saba’in kafin ka kama shi da yi maka laifi.

Ta saka a ranta me zai hana in yazo ta tambaye shi ko tayi masa laifi ne? 

Tunanin da Hauwa ke ta yi kenan wuni guda yau ta kasa moruwa, ta jibge a katifa, ta kasa fitowa ta taya Inna aikin alale, tunda kullin alala ne zata iya don ta saba tayata, ta kasa jin dadin ranta ko kadan.

Ga yawan mafarkin Babanta Malam Bilyaminu data ke yi a kwanakinnan wai ta ganshi ya dawo amma bashida lafiya. Wannan ma ya kara dugunzuma damuwar Hauwa kuma ta kasa gayawa Inna don kada ta daga mata hankali in tace tana yawan ganin Malam ya dawo cikin halin rashin lafiya na shanyewar barin jiki.

Cikin wannan halin damuwar da Hauwa ke ciki, harda hawaye na diga ta gefen idon ta, daga bakin kofar shigowa tsakar gidansu aka rafka wata irin sallama cikin muryar girma da koshin lafiya.


Gaban Innar Hauwa ya yi mugun yankewa ya fadi ras, jin muryar da ko cikin barci ta ke ba za ta kasa gane mai muryar ba. Muryar da ko mutuwa tayi ta dawo bazata manta sautin amonta ba, muryar data yi amanna da cewa mutum daya ne mai ita a duniya, muryar data yi kewa sama da shekaru bakwai.

Mai sallamar ya sake cewa, "Ikon Allah, Allah dai ya sa ban yi batan kai ba, anya?".

Sai idanunsu suka sarke shi da matarsa ta lalle (Safiya) Innar Hauwa, ya saki hamdala duk da ta kara girma da nauyin shekaru tana nan yadda ya barta da kyan jikinta, ya soma takowa zuwa gareta da hanzari, yana sakin hamdala ba kakkautawa.

Fatar bakin Inna na rawa da karkarwa har ya iso ya tsaya gabanta, ta ta mike tsaye ta kai hannu shima yana rawa ta taba gemun shi ta ce, 

"MALAM!" 

Ya rike hannun ta shikuma y ace “na’am Safiyatu. Na godewa Allah da ya hada fuskokinmu lafiya”.

Da dai ta tabbatar Malam Bilyaminu ne a gabanta ba mafarkai take yi ba. Sai ta tafi baya luu! Za ta fadi jikin bango, ya yi maza ya taro ta jikinsa yana fadin, 

"Safiyatu, kada ki yi min haka, in ki ka fadi ki ka ji ciwo kafin mu gana fa? Ai godiya ya kamata ki yiwa Allah da ya hada mu a raye cikin koshin lafiya".

Ina! Inna Safiyya idanu sun bace, ta sume a jikin Malam Bilyaminu.

Shimfideta yayi a wurin wato ya kwantar da ita a dandanyar kicin din ya tafi ga famfo ya tari ruwa a buta da sauri ya dawo ya shiga shafa mata a fuska zuwa wuyanta. Ba jimawa Inna ta soma sauke ajiyar zuciya amma bata bude idanun ta ba. 

Daga can daki Hauwa ta ke jin motsin su, ka san makaho da ji! Sai faman tambaya take, 

"Waye a nan? Nace waye ne ya shigo? Inna kina ina, mene ne?"

Da taji ba'a amsa mata ba don a lokacin Inna ta samu bude ido suna kallon kallo itada Malam Bilyaminu, sai ta taso ta tako ta fito a hankali tana dafa bango, ta iso tsakar gidan tana faman juya idanunta harrr! Masu haske da girma.

“Wato an ga Inna ta fita shine aka shigo ayi mata sata ko?”

Malam Bilyaminu ya dago ido, yana duban diyarsa HAUWA-KULU da wani irin bege fal idanunsa, tana takowa tana ta tambaya alhalin idanunta a bude tangararas, "Wane ne ya zo wai? Nace waye anan?" Alhalin kuma ga idonsa ga nata tana kallonsa saidai ba cikin Ido ba.

Sanyin ruwan da ya shafa mata ya sa Inna farfadowa daga suman wucin gadin da ta samu ta saki ido kawai tana kallonsa, daga bisani data tabbatar bazata farka daga wannan gizagon da idanunta ke mata ba sai ta mike zaune, ta ja gefe ta zauna ta fashe da kuka tana rufe idanunta, ta ce.

 "Hauwa Babanki ne yake yi min gizo, yau har a jikina na ji shi, naji hannunsa jiki na na kuma ji kamshinsa kusa da ni".

Malam Bilyaminu ya ce cikin wani irin yanayi na shauki, da cikowar hawaye fal a idanunsa.

 "To tunda gizo nake yi bari kawai in koma kada in tsorata ku".

Ya mike zuwa kan tabarmar da ke shimfide a tsakar gidan ya z auna yana cewa, "Ku yarda ni ne ba gizo ba, ba kuma fatalwata ba, ba kuma gizo nake yi muku ba. Yau ne Ubangiji ya kaddari ganawar tamu. Babu tsimi babu dabara sai ga Sarki Allah. Alhamdu lillah da na same ku a raye, shine babban farin ciki na".

Hauwa ta kwalalo manyan idon waje, domin tabbas ta shaida muryar mahaifinta. 

Ta taho inda ta ke jin sautin muryar tasa gadan-gadan gaba-gadi.

Malam Bilyaminu ya tare ta, ganin zata taka shi ta wuce ta kansa, kuma nan da nan ya fahimci cewa Hauwa-Kulu ba ta gani, wato (ta rasa idanunta).

Ji ya yi zuciyarsa ta wani irin tsinke, mummunan tsinkewa. Da ya haifar masa da faduwar gaba. Ya kama hannunta ya zaunar da ita a gefen jikinsa, ya ce, "Nana Hauwa'u! haka Allah ya yi da ke???"

Duk dauriyarsa da farin cikinsa na sake saduwa da iyalinsa Malam Bilyaminu sai ga shi yaja gefe shima kamar yadda Inna tayi, ya sa habar babbar rigarsa yana shatatar hawaye yana kuka harda sharbe. Ba abinda zai ce banda Allah yayi masa sakayya.

Sai mu ce farin ciki mai yawa ne cakude da alhinin halin nakasar da ya samu Hauwa a ciki ya gudana a wannan ranar a gidan Malam Bilyaminu. 

Kuka-kuka, farin ciki- farin ciki, haka suka kasance a yammacin ranar. Har aka kira mangariba. Kafin Inna ta share ido, tace da Baban Hauwa ya dau kaddara kamar yadda suka dade da dauka suma, ya karfafe su a cikin halin raunin da ya same su. Sun riga sun yi amanna da kaddarar Hauwa-Kulu.

Sun yi sallar magriba da isha tare kenan cikin jam'I, Malam din ya limance su kamar yadda suka saba acan baya, bayan sun idar, Malam Bilyaminu sai bin gidan yake da kallo na mamaki da tu'ajjibi. Entirely modern! Babu bishiyun su na baya kuma. Ya ce, "Safiya, ki fidda ni duhu, kaina ya daure, a kan yadda aka yi gidan nan ya koma haka, da inda Hauwa’u na ta samo lalurar makanta??? Ya Subhanallah".

Inna tasa habar zaninta ta share Ido, taji wani irin karfi da kuruciya sun sake shigarta yau, kai har ma da koshin lafiya, tace,

 "wallahi daga annobar 'Apolo'. 

Daga nan ta shiga fedewa Baban Hauwa abubuwan da suka faru a bayansa, daga biri har bindi. 

Har abin da Zakari ya yi musu, na rushe gidan, da yadda rayuwarsu ta kasance cikin walagigi bayan nan. Baban Hauwa kuka kawai yake yi kamar ba namiji ba da sharbe yana sharewa da habar babbar rigarsa. Yana fadin “tsakanina da ZAKARI sai hisabin Allah”.

Ya ce, "Yanzu shi LIKITA SARHAMU din ina yake?" zan so kwarai na ga wannan jarumin, kuma BARDE! Ga rayuwar iyalina”

Inna ta ce, "Za ka ganshi ba da jimawa ba, duk da dai ya gaya min nan da sati biyu shi da iyalinsa za su koma garin Jeddah inda yake aikinsa na likita".

Malam Bilyaminu ya ce, "don Allah bani lambar wayarsa in kira shi. Ya zama lallai in yi masa godiya, in iyayensa na raye su ma in yi tattaki har inda suke in yi musu godiya kafin mu bar Kano".

Inna ta kai shi sabon dakin da yake a kulle, wanda shine nasa tuntuni, dama a gyare dakin yake har da gado da katifa Sarham ya saka a dakin, sai ta dauko wankakken zanin gado ta shimfida, ta hada masa ruwan wanka a bandakinsa, wanda ke like da dakin.

Sai da ya shiga wanka ta je ta zubo masa alalen wanda ta karasa a gurguje, tana aikin tana tazbihi na mamakin kyakkyawar kamar da ta ga maigidanta Malam Bilyaminu a ciki, babu alamun wahala ko kadan a tare da shi, maimakon ta ga ya kara tsufa furfura ta baibaye shi sai ta ga ya kara gyagijewa wato ya kara kuruciyama a idanunta fiyeda kafin tafiyarsa, ya yi 'yar kiba kib-kib irin ta hutu kuma cikin kyakkyawar suttura ta farar shaddar yayi ta lokacin (mirror), yar ciki da babbar riga wadanda suka sha aiki.

Malam yana fitowa wanka, Inna ta gabatar masa da abinci, bayan alalen kafin yayi wanka har tayi maza ta tuka masa tuwon masara da miyar kuka, ta zauna gefensa tana firfita masa sai cewa ta ke, "da dai a ce na san yau Malam zai dawo, da na yi masa girkin tarba na musamman". Shi kuma ya murmusa cike da kewarta da kewar kulawarta irin wannan, yana kara hada Zakari da Allah cikin zuciyarsa, a fili kuwa cewa yake, 

"Ai kema kinsan na yi kewar tuwonki Safiyya, kin san tukin tuwonki da dandanon miyarki daban yake da na kowa. 

Kwarai na yi kewar abincinki, kulawar ki, tattalinki da addu'ar ki gareni kullum zan fita, addu’ar nan taki ta Allah ya sa in kawo muku halal, in ciyar daku daga halal.

 Umh, ya nisa, “kada Allah ya maimaita mana rabuwa da juna kona kwana daya ne Safiyya, ina addu'ar daga nan mu wuce har gidan aljannah tare. Duk kuma abinda zai sake samunmu, ina rokon Allah ya same mu muna tare da juna.

Yadda na same ki ba ki yi aure ba har zuwa wannan lokacin ya kara min yarda  da kaunarki gare ni Safiyya, zan kuma saka miki da abishir din cewa har abada ni naki ne ke kadai. Allah ya yi miki albarka”.

Haka sukayi kwanan matsanancin farin ciki a yau. Malam Bilyaminu da matarsa Inna Safiyya. Hauwa kuwa ko na minti daya ba ta runtsa ba a nata dakin don farin ciki da godiyar Ubangiji, kwana ta yi sallah tana godewa Ubangiji da ya dawo da Babanta, a lokacin da duk suka fidda rai da rayuwarsa. Ta rasa inda zata tsoma ranta don farin cikin yafi gaban kuka ko dariya, tuni ta manta da damuwar wani Sarham da take ciki.

Washegari Inna ta fito madafi don dora abin kari sai ta tadda Hauwa a kicin ta hada kai da gwiwa a kan kujera 'yar tsugunno. Ta saka kai a tsakanin kafafunta kamar wata marainiya, ita ba kukan fili ba, ita ba kukan zuci ba. 

Inna ta karasa gabanta a hakali tace, "o'oh! Kayyasa Kulun Majadun, Kulu mai tuwon ‘yan birni! Lafiya da sassafen nan ki ka zo madafi kikayi wannan irin zama na kaka-nikayi haka?”

Ta dafa kanta tana tambaya cike da kulawa irin ta Uwa. Uwar ma irin Inna, da ba duk UWA ba! Uwar Hauwa wadda babu irinta.

Hauwa kamar jira take Inna ta tankata sai ta fashe da kuka mai tsuma rai, cikin kukan ta ce,

  "Inna.... !".

  Kukan ya kara kwace mata da karfinsa na gaske.

Inna ta kyaleta har tayi mai isarta, don ta san in Hauwa na kuka bataso ma a rarrasheta sai ta kai intaha, kafin da kanta ta gaji da kukan, ta share ido, tace, "Inna shikenan ni yanzu banida amfani? Ba zan iya amfanawa kaina da ku iyayena komai ba? sai dai in zame muku liability?

 Inna na tashi da dokin na yi wa Babana girkin barka da zuwa, girkin da bait aba cin mai dadinsa ba, tun ban kai haka ba ina yi masa girki yana shi min albarka, idan baki manta ba. 

Sai da na shigo madafin yau na tuna ashe fa ba zan iya aikin wuta ba, kada in tsumbula hannnuna a mai ko garwashi, tunda ba ni da ido, komai ma bazan iya ba Inna na taimakon ki, na zama banida amfani?".

Zuciyar Inna ta karye, wani irin karyewa, cike da 'maternal love' wanda ya motsa mata, ta ce, 

"Idan Allah ya nufa, da albarkacin tsarkin Al’qur’ani, da tsarkin mulkin Allah sai ganinki ya dawo kamar na kowa tun a duniya HAUWA-KULU, sai kin ga idon ‘ya’yan ki, sai kun hada ido a lokacin da kike shayar dasu, ina ji a jikina ba za ki dauwama cikin wannan halin na lalurar makanta har abada ba. ubangiji yayi alkawarin kowacce cuta tana da magani, amma waraka lokaci ce. Ina ji a jiki na takaitacciyar jarrabawar ki ce Hauwa mai zuwa ta wuce, da yardar Allah sai kinga fuskar 'ya'yanki a lokacin da kike shayar dasu.

Kada ki kara cewa kin zama bakida amfani, duk mai nakasa indai ba zuciyarsa ce ta mutu ba kuma ya tsaya ga neman ilmi ga kowa ina tabbatar miki zai iya komai da mai lafiya ke yi. 

Allah da kansa ya ce, "Ad'uni Astajib lakum! Wato (Ku roke ni, Zan amsa muku)". 

Ta daga hannu biyu sama tana fadin "Ya Allah Ubangijin sammai da kassai, ina Mai tawassuli da sunayenka tsarkaka guda 99, a yau ni Safiya uwar Hauwa ina rokonka; Ka budewa HAUWA-KULU idanunta ko kadan ne tun a gidan duniya darajar kaunar da ta ke yi wa iyayenta”.

Hauwa Kulu cikin tsananin hawaye da jin dadi ta ce, "Amin-Amin ya Allah Innata".

"Yanzu gaya min me ki ke so ki dafa masa sai mu yi tare?” Inji Inna.

Ta kara da cewa “duk uban aikin da kikeyi a Tashar kuka da kanoline kin manta, ai ke dinnan ba sakaltacciyar mai lalura bace". Hauwa ta ce cikin jin karsashi ya dawo mata, 

"Inna funkason fulawa da miyar taushe nake so in yi masa, ko kuwa alkubus da miyar ganye. Na tabbata ya jima bai ci su ba, in kuma ya ci din, to ba irin na gidannan ba".

Inna ta yi murmushi tace, "an yi an gama Kuluwar Babanta. To mu yi duka biyun mana? Malam dan gatan Kulu ya ci kala biyun. Bari in tattaro miki kayan hadin sai ki kwaba alkubus din da funkason da hannunki, nikuma in dafa alkubus din, in kuma soya funkason".

Hauwa ta yi murmushin jin dadi, Inna ta gama ganeta fiyeda kowa a duniya, bataso nakasar nan tata ko kadan ta maida ita useless (mara amfani), suka soma aikinsu tare suna yi suna hira kamar kawaye.

A haka Malam ya tadda su a kitchen din wajejen karfe takwas na safe.

"Hauwa da Innarta girki ake yi mana haka?"

Hauwa na kwabin funkaso ta yi dariya ta ce, "Ni nake maka girki na musamman Baba, na sannu da zuwa na tabbata zaka ji dadinsa".

Ya ce,"Allah yayi miki albarka. To ku gama in ba ki tsarabobinki daga Ubangidana, har da na'ura mai kwakwalwa sabuwa dal a kwalinta ya aiko miki".

Hauwa ta ce. "Ai kuwa an koya mana amfani da ita kadan a makaranta, lokacin da muna aji biyar, an gaya mana zamu iya amfani da ita muma ta duk hanyar da mutane ke amfani da ta a matsayin 'assistive technology' ga masu lalurar idanu". 

Can kuma ta dubeshi ta ce, "Baba baka gaya mana ina ka je ba, da abin da ya faru cikin batan naka, rana daya muka rasaka, haka rana daya katsahan muka ganka cikin koshin lafiya ka dawo. Ba tareda tsumi da dabarar mu ba.

  Ni dai na san addu’ata ce Allah bai wofintar da ita ba, don bana yin sallah na tashi daga inda nayi ta ban roki Allah ya bayyana min kai ba, ni nasan addua ta bata fadi ba, lokacin amsarta ne Allah ya jinkirta min".

Malam Bilyaminu ya ce, “Tabbas Hauwa’u, addu’a ba ta taba faduwa kasa banza, don nima na san tasirinta da alfanunta ne yau ya dawo da ni cikin iyalina lafiya da nisan kwana….".

        “Assalamu alaikum. Inna me kike dafawa ne haka duk lokon nan ya dauki kamshi?” 

Sai jin sallamar Dr. Sarham da korafinsa suka yi a gidan da safiyar Allah, wand aba lokacin zuwansa bane yafi zuwa da daddare, misalin karfe tara na safe yau yayiwa gidan tsinke.

Kallo daya za ka yi wa Dr. Sarham ka san ya fito daga gida ne ba tare da shiri ba, don Malam Isah ne ya kira shi da sassafe ya tabbatar masa Baban Hauwa ya dawo, har sun gaisa dashi yau a masallaci wajen sallar asubahi.

Dr. sarham ya zo gidan ba shiri ba don ya yard aba sai don tabbatar da labarin Malam Isah. Duk da dai ya san da kyar in zai fadi abinda bai gani ba. Ilai kuwa da Baban Hauwa ya soma tozali tsaye a kofar kicin, suna hira shi da iyalinsa. Sarham ya lumshe ido yana murmushi lokacin da ya karaso yayi musabiha da Malam Bilyaminu, yana kallon fuskokin wadannan family da suka cika da annashuwa yau. "What a family!" Sarham ya gaya wa zuciyar sa cikin jin dadin walwalar da suke ciki. 

Inna ta amsa masa fuska fal annuri. Malam ya yi masa barka da zuwa tare da cewa su karasa falo, suna shiga yana cewa, "ko ba a yi min gabatarwa ba, jikina da zuciyata sun gama bani likita Sarhamu ne wannan".

Sarham yayi kasa da kai cikin girmamawa, ya ji wani irin farin cikin ganinsu haka complete family kamar nasa iyalin, bakinsa da murmushinsa ‘from ear to ear’, wato daga jiyan zuwa yau kadai har Malam Bilyaminu ya san da zamansa, wanda ke nufin yana da matsayi mai girma a wajen Inna, (don ba zai ce a wajen Hauwa ba), ya san bazata iya bawa Babanta labarin sa ba don ba damuwa tayi da shi ba sai ko Inna. Amma tabbas ya san ta bashi labarin saurayinta dan polo.

Inna ta saka mishi funkason da alkubus din a nashi farantin ta zuba miya a karamin kwanon Samira ta aje masa gabansa, bai yi fulako ba don kuwa bai karya kumallo ba ya fito, kai ko wanka bai iya tsayawa yayi ba saboda wannan albishir din da Malam Isa yayi masa, Inna da Hauwa suka kammala aikin su suka dawo falon suka karya kumallon tare. Sai da suka kammala tsaf, kowa ya wanke hannu ya sha ruwa, suka sa Malam Bilyaminu agaba kamar sa hadiye shi, har Sarham din ya kagu yaji inda ya shiga, malam Bilyaminu ya fara basu labarin abin da ya fidda shi ranar daga gida, da rayuwarsa ta tsayin shekaru bakwai da yayi a ‘Kumasi’ ta kasar GHANA.

"Asali muna da gona ta gado ni da dan uwana Zakari, wadda takardunta suke hannunsa, kullum na yi niyyar karbar hakkina sai in ji kamar an mantar da ni. Rannan dai da karfin addu’a Allah ya ba ni sa'a na taka same shi har wajen sana'arsa ta wankin hula, da zancen ya kamata mu sayar da gonar nan tamu haka, mu ja jari mai tsoka, mu kama manyan shaguna ya fiye masa sana'ar wankin hula.

Ni ma in samu in zama babban dealer na gwanjo, in dinga zuwa sarowa da kaina, maimakon da da sai dai in sara hannun ubangidana. Wato ya zama cewa na samu jarin da zan dinga fita kasashen ketare kawo gwanjo da kaina.

Zakari ya gama saurare na tas, sai cewa ya yi, shi babu wata gona a hannunsa, bai kuma san da zancenta ba”. Na ce, to idan ya hana ni, wannan karon zan kauda ‘yan uwantaka, zan sa hukuma ta kwatar min hakkina, zuwa shari’a a kan gado ba yau muka fara ni da shi ba. sai dai wannan karon kotu zani ba gun mai unguwa ba.

Amma ko sati biyu ba muyi da yin wannan takaddamar ba rannan ba kya gidaina shirin fita kasuwa sai ga Zakari ya zo har zaurena ya same ni, tunda na yi tozali da shi gabana ya fadi, mummunar faduwa, mukayi tozali da juna sai kaina ya soma sarawa, duniya ta soma juyamin, sai ya miko min hannu ya ce, in ba shi takardun gidana da na saya a hannunsa, wallahi kamar sihiri, babu musu babu jayayya ko bakinsa bai gama rufewa ba na shiga gida na fiddo su na kawo masa. 

Sai da ya karba ya saka a aljihunsa, sannan ya ce min cikin daga sauti na bada umarni.

 "Tashi ka shiga duniya, kada ka tsaya cikin kasar nan, ka tafi ko can tsakiyar kasashen Africa ta yamma ka rayu a can, ko bangon duniya kai duk inda mai ya kare maka".

Malam Bilyaminu yace, "Iya abin da zan iya tunawa kenan, sai ganina na yi a mota mai zuwa kasar Ghana, kuma da yake ba ka raba dan kasuwa da kudi a jikinsa, sai ban rasa kudin biyan kudin mota ba. Musamman da yake a jiyan ranar, na bude dealer din gwanjo na sayar.

Saukata a Kumasi ke da wuya kuma wallahi cikin hankalina nake komai, muna tunanin inda za mu raba mu dan huta zuwa wayewar gari mu san inda zamu nufa na ji daga bayana an kira sunana cikin matukar mamaki.

 Ina juyawa na ga Alhaji Munkaila, wato Ubangidana wanda a wurinsa nake sarar gwanjo a Kano, cike da mamaki yace me ya kawo ni kasar su? Anya lafiya kalau nake? Wa na sani a Ghana me na zo yi kuma? Na samu bakina kai tsaye da cewa, "Neman na kai na fito!".

Alhaji Munkaila ya ce, “amma a sanina, daidai gwargwado Bilyaminu ai sana'arka na garawa a Kano, na ga in ka kwance dealer ba ka kwana uku ta kare ka zo neman sabuwa ba.

Na ce masa ra’ayina ne barin Kano in dawo Ghana don in yi sana'ata a nan, ya fimin kwanciyar hankali.

Alhaji Munkaila ya ce, Ina da wajen sauka ne? Na ce "ni fa Alhaji na dai zo Ghana ne. Amma ban san kowa a cikinta ba, ban kuma san meyasa na zabeta ba”. Alhaji Munkaila yace min tun a lokacin, ya fahimci ba cikin hayyacina nake ba shiyasa ma bai yarda ya barni na shiga gari neman masauki ba yaji tsoron kada in fada hannun bata gari. 

Sai ya ce, tunda na ce nema na fito, to in bishi ya bani masauki mu ci gaba da sana'armu a nan Kumasi yadda muka saba a Kano, don can din ma Ghana Gwanjo na garawa kuma ya bar Kano ya dawo gida.

Ya gaya min yanzu ya dawo Ghana gaba daya saboda mahaifin sa ya kwanta dama, zai kula da mahaifiyarsa da kannensa, dama kasuwanci kadai ke kaishi Kano, amma shi dan nan Kumasi ne. 

To kun ji yadda aka yi na samu Ubangida cikon taimakon Ubangiji ba tareda na tagayyara bat un daga ranar dana sauka a Ghana, muka ci gaba da sana'armu ta shigo da gwanjo.

Alhaji Munkaila na da karfi sosai a sana'ar mu ta Gwanjo don kai tsaye yake zuwa kasar Italy ya saro Gwanjo. Daga baya ma da ya koya mana ni da babban dansa Salisu yake turawa mu saro, shi kuma ya rarraba.

 Ba jimawa na iya manyan yaren Ghana tun daga yaren Akan, Ewe, Ga, har zuwa Dagbani da Turanci tsilli-tsilli na 'yan koyo a bakin Salisu da abokan cinikayyarmu.

Lokaci-lokaci da yaga kamar na dawo hayyaci na na koma cikin nutsuwata Alhaji Munkaila na yawan cewa ya kamata in je gida in ga iyalina haka, ko ya ce in daukoku, Sai in ce masa ba yanzu ba, har ya gaji ya rabu da ni. 

Mun samu alkhairi mai yawa a wannan sana'a tamu ta shigo da Gwanjo, har wani lokacin da zamana haka ya dame shi ya yi min tayin auren kanwarsa Yahanasu wadda mijinta ya rasu ya barta. Ni kuma na gaya masa cewa, har abada ba zan iya aure a Ghana ba, don na san uwargidana ko mutuwa na yi ba za ta iya auren wani ba ni ba. Ya ce, to lallai in koma gida in zo da ku.

 A wannan karon na gaya masa hakikanin gaskiyar dake zuciyata cewa ko sunan garin Kano bana son ji!

Alhaji Munkaila yace min shi da kansa ya fahimci al'amari na akwai saka hannu a ciki, da shekaru suka yi gaba banida niyyyar komawa gida shi da kansa yasa wani shaihun malaminsa ya dinga yi min addua a boye, ba tare da na sani bama. Idan ma wani makaru ne a jikina ya roke shi ya kwance in koma ga iyalina ko in dauko su inda nake, in Kano ce bana so kwata-kwata. Don a lokacin har gidan kaina da motar hawa na mallaka a kasar Ghana.

Rana daya na samu duk dabaibayin da ke zuciyata yana yayewa. Na ji hankalina bakidaya ya dawo Kano.

Na zama ba abin da nake so irin in bude ido in gan ni cikin iyalina. Ga mafarke-mafarke da nake tayi a kan Hauwa'u, wai ba ta da lafiya. Wani mummunan abu ya faru da ita. Rana daya ni da kaina na samu Alhaji Munkaila na gayamasa ina da mata da 'ya dana baro, ina so in je in taho da su Ghana, don ba zan iya kara zaman Kano ba, na fi jin dadin sabuwar rayuwa ta a Ghana, wani bare sau dubu ya fiye maka dan uwa na jini.

Alhaji Munkaila kusan ya fi ni farin ciki da dawowar hayyaci na, don da kanshi ya saya min tikitin jirgin zuwa Kano daga Ghana. Ya kawo tsarabobin sittiru na gwanjo masu karshen tsada na turawa da na na'ura mai kwakwalwa ya ce a kawo wa Hauwa'u, kuma yana yi wa dansa Salisu dana baro yana karatu a Italy kamun auren ta, don ya san zuwa yanzu ta girma.

Na iso Kano lafiya, na hawo drop din taxi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano na zo har kofar gidana. 

Na sha mamaki ganin sabon gida a muhallin gidana, sai da na tambayi mutane kusan uku ko a nan kofar gidan ko inda Innar Hauwa da 'yarta Hauwa suke zaune ne? Ana ta tabbatar min “eh a nan suke”, wani ya ce min amma ba su jima da dawowa ba, sannan na iya na shigo".

****                 ****              ****

Anan Malam Bilyaminu ya nisa, ya ce, "To kun ji wannan shi ne labarina. Da abunda ya faru dani bayan barina gida. Zakari shi ya yi min makarun da ya kore ni don ya cinye gonar gadonmu shi kadai. Na zo kuma na ji abin da ya yi wa gidana, don haka wannan karon nisa da Zakari shi ya fi min alheri, ba zan iya shari’ah da shi akan abun duniya ba amma bazan kara zama gari daya da shi ba, kuma ba zan yi shari'a da shi ba a matsayinsa na dan uwana na jini. Na bar wa Allah ya saka mini, domin hakika ba ya yafe hakkin wanda aka zalinta.

Don haka ku yi shiri Hauwa da Innarta za mu tattara mu koma Ghana ne, ina nufin zamu bar BADALA nan da kwana uku, son son samu ma gobe insha Allahu. Amma don in baku dama kuyi sallama da abokan arziki irin likita, zamu tafi kwanaki uku masu zuwa in sha Allahu.

Ya juya ga Sarham ya ce, "Likita Sarhamu, Da nagari, dan albarka na ji duk halaccinka a kan iyalina, ba ni da bakin gode maka ina rokon Ubangiji Ya fi ni godewa. 

Allah ya yi maka albarka duniya da lahira, ya tallafi haularka a bayan idonka kuma Ya jikan iyayenka, Ya kara yalwata musu kamar yadda ka zama yalwa kuma farin ciki ga iyalina.

Ina so kafin mu koma Ghana ka raka ni gun mahaifinka in yi masa godiya, don ni ban taba jin mutum mai kyakkyawar zuciya karimi kamarka ba, wanda ba komai ba ne kyawun tarbiyyar da ka samu daga garesu ne na taimakon mara gata da wanda yake cikin yanayi na bukatar tallafi da lalura irin wannan……

Kafin kowa ya yi magana, aka ji Hauwa ta saka gunjin kuka har da sheshsheka, hankalinsu ya koma gareta, Inna ta san Hauwa bata kuka na banza haka kawai mara dalili sai mai dalili, shiyasa ta san tabbas kukan nan baka da zuci take yin sa, tana fadin, “ni ba zan koma Ghana ba, ba zan iya barin Kano ba, b azan ma iya barin ko gidannan ba, ni Baba bazan iya barin BADALAr da aka haifeni a ciki sabida zaluncin Baba Zakari ba”.

Ta kare zancenta da cewa "ba inda zamu je, muna da gida na tarihi, ina son zaman cikin Badala, Baba da Inna ku barni in yi karatun da zan zama lawyer wallahi sai nayi muku maganinsa".

"Yau nake ganin sakarcin wofi. Lauyo!" In ji Inna,

 "wato kin fi so mu ci gaba da zaman Kanon dai yana binmu da kulli yana illata mu, ko saboda soyayyar da kike da dansa Jamilu ko? Ya ci gaba da yi miki naci yana zuwa azure yana kalallame ki da shirme, ke kuma kina biye masa, tun farko ma ai ni so na yi mu bar Kanon gaba daya tun ranar da ya rusa mana gida.

 Saboda Zakari abun gudu ne, kika dage kika hana ni sabida son Badalar ki, da kafiya da naci kamar kuturwa, ni na san a Kano cibiyarki ta ke, mu duka ruhinmu ana yake, amma Manzo (S.A.W) ma da kansa lokacin da Makkah mahaifarsa ta yi masa kunci saboda kiyayyar abokan gaba da kafirai yayi hijira ya koma Madinah inda ya samu sababbin masoya, suka karbeshi karbar da ahalinsa basu yi masa ba, sannan ne ya zauna lafiya. Ki duba tarihin Hijirar manzon Alah SAW zuwa Madinah.

Banda wauta irin taki wai har bayan jin abin da Zakari ya aikata wa mahaifinki kina marmarin ci gaba da zaman Kanon inda yake zaune taki kadan zuwa dan agundi, yo ni ai ko don in raba ki da dan Zakari haihata-haihata na tafi Ghana, kurwata kur da iyalin Zakari da shi kansa. Zakari abin neman tsari ne.

Malam Bilyaminu kam ya sha mamakin Jamilu a kan Hauwa, wai yana son auren Hauwa, koda yake tuntuni ya san halin Jamilu na kirki duk cikin ‘ya’yan Zakari shine kadai in ya hadu da shi a hanya yake gaida shi, sai ya rage mamakinsa ya ce, 

"ki mata a hankali, lallashinta za kiyi, sabo ne, amma Ghana dole mu tafi ba makawa muddin muka kai kwana uku a raye, komai na rayuwata ya koma can, sannan ba zan kara rayuwa a inda Zakari yake ba, na barshi da Allah, na bar shi da fitowar rana da faduwarta. 

Amma tafiyarmu zuwa Kumassi (Ghana) ita ce mafi alkhairi a garemu, ko yaya ka gani Likita Sarhamu?"

Dr. Sarham wanda tunda ya dukar da kai yana sauraron su bai ce komai ba, amma bai taba jin tashin hankali irin wanda yake ji a zuciyarsa yanzu ba, musamman da Hauwa take wani irin kuka kamar na fitar rai tana fadin bazata bar BADALA zuwa GHANA ba, tace gara abarta ita kadai ta zauna zata iya rayuwa a gidan su ko babu dan jagora.

Malam Bilyaminu wanda shi ma kukan Hauwa ya rikita shi, kalamanta kuma sun hautsina shi, amma bukatarta na ya cigaba da zaman Kano ba mai yuwuwa bace, ya ce, 

"Haba Hauwa-Kulun-Majadun, ‘ya daya tamkar da dubu!

 Shin ke ba kya fatan yin aure ne kamar kowacce mace, sai fatan dauwama a cikin Badala ko a gaban Innarta? 

Ai ke yar gidan wasu ce Hauwa'u, don haka barinki Kano zuwa Ghana ba komai bane, don idan ban da lalurar nan da na same ki a ciki, tuni na bada auren ki ga Salisu dan wajen Alhaji Munkaila, to a yanzu na san ba lallai ya yarda da zabin mahaifinsa ba, in ya kasance sun ji kin daina gani, ba kowa zai yarda ya auri marar ido ba sai mai soyayyar gaskiya, don haka na bar wa Allah ya zaba miki abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar ki, amma hakika nafi so kiyi aure".

Inna ta yi sauri tace, "Mafi alkhairi ya fi a ce yaro mai nakasar ido yana tare da uwa da ubansa a gefensa? Suna zama garkuwarsa da karfinsa a lokacin duk da yake bukatar su a tare? Ka taimaki kanka Mallam, ka kuma bai wa kanka zaman lafiya ta hanyar cire wa ranka batun son aurar da ita ga dan uwangidanka da kowa ma.

 Yau da a ce Hauwa da idanunta biyu, sai na fi kowa son ta yi aure a wannan matakin na girma data shiga a rayuwarta. Amma da ya kasance haka Allah ya zaba mata rayuwa barin maganar yi mata aure da kowa shi ya fi alkhairi Baban Hauwa".

“Kina wasa ne kema, lalura ce zata hana aure sunnar Annabi SAW?”

Kamar daga sama kawai sai suka ji Sarham ya ce (cikin rawar murya ta tangardar harshe), rudani da rawar murya,

 "Har da ni Inna? Ina nufin ko nine na nemi auren nata? Har ni ma idan na bukaci hannun Maijiddah zuwa aure ba za ki bani ba?"

Ya kuma tsareta da ido yaki dauke idanunsa da suka rine da damuwa da tausayin kukan HAUWA daga kan Inna, sosai yake casa zuciyar Inna da kaifin kwayar idanunsa, masu haske da wata nasaba ta musamman da ba duk Maza keda ita cikin idanunsa ba.

 Yanayin kallon da yake mata, irin kallon nan ne na hana ta kawo kowanne irin uzuri ko togaciya ko rashin yarda ne, a kan bukatarsa.

Dakin ya bada wani irin shiru. Daga Inna har Hauwa duk sun firgice da jin abinda likita Sarham ke cewa, Inna ta diririce ta rikice hau kame-kame ta rasa inda za ta sa kanta. Hauwa kuwa idanu ta firfitar waje kamar zasu fado kasa a soya su a cikin mai. 

Malam Bilyaminu kuwa murmushin manya ya yi, ya ce. "Da shi ke nan ka raba gardama, ka raba rigima tsakanina da Hauwa, da tsakanina da Innarta mai shirin ajiyeta a kwibinta har karshen duniya. ka Kuma yi Tuwona - Maina, wato dai ta kwana gidan sauqi idan yau aka ce LIKITA YAYAN HAUWA ya dauke abarsa, ya kai ta gidansa na aure ya killace ta sun tara zurri’a mai albarka, in yaso, ki yi ta karata da son Kanon naki, tunda kowa ya shaida ke 'yar Badala ce ba ‘yar Inna ba da ba’a dinga jin kanku ba, babu kuma wanda ya kai ki son zaman cikin ta.

 In yaso ni da Inna mu koma Ghana ki yi zaman aure kamar kowa. 

Yo kai mai abu maganin a kwabe ka, ai ba sai ka tsaya tambayar Innarta ba, sadaki kawai za ka kawo in har da gaske ka ke, kuma iyayenka sun amince ka auri Hauwa da zuciya daya duk da lalurarta, to nikuma in hakan ta faru, tuwon girma miyarsa nama! Na baka auren Hauwa duniya da lahira.

Ka sani ko aurenta na baka ba tare da na karbi komai naka ba bayan sadaki da Ubangiji yace na karba, tofa ban biyaka ko rabin-rabin abin da ka yi min ba na kulawa da rayuwarsu, da abinda kayi mata ita Hauwa din, tsayin lokacin da na dauka bana nan tare dasu baka bar su sun wulakanta ba sun tozarta ba.

Inna duk ta rude, rudewar ta ta kasa boyuwa fadi ta ke, "A’ah Malam, kada ka biyewa da na Sarhamu, kada yi gaggawa, bi maganar nan a hankali don Allah, na tabbata likita Sarhamu zolayarka yake, kukanta ne ya daga masa hankali, amma babu makamanciyar wannan maganar a tsakaninsa da Hauwa. Na rantse da Allah babu soyayya.

Ai ba yau muke tare ba, ko Sarhamu? Ba ka taba ce min kana rikon auren Hauwa ba koda da subutar baki ne. 

Idan muka baka ita alhalin bata da ido, hakika mun kware ka. Kada ka bari tausayi ya rinjayi zuciyarka ka aikata abinda zaka zo kana dana-sani.

Hakika ni uwarka ce da ba zan so ka yi auren wahala ba, kuma ba sai ka auri Hauwa bane zan san kana kaunata, ni shaida ce Allah kuma shaida ne".

Ta soma share hawaye tana cewa,

 "Malam ba ka san wasa ba ne? Ya daga wasa zaka Maida allura garma? Daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi Zaki mallam???"

Rudewarta da rikicewar ta ya kai intaha. Sarham sai ya mike tsaye yana dan murmushi yana shafar kansa, rikicewar Inna ce ta sa shi dariya, ya san dama za'ayi haka, ta sha fada ta maimaita a gabansa bazata taba yiwa Hauwa aure ba, koda kuwa da dan shugan kasa ne, don ma dai shine, wato don shine ya furta ba wani daban ba, tabbas da an ga dan karamin yakin sunkuru! Idonsa a kan Hauwan da ke ta ta kokarin kai kanta daki tana cuno baki tana zumbure-zumbure wai Inna wulakantata, ta kuma yi mata gorin ido tunda ta ce (ba ta da ido aurenta wahala ne). Cewa ta ke cikin turo baki gaba irinna shagwababbu.

 "Ni dai Inna a yi min gorin komai zan jure, amma ban da gorin idanu. In ma makantar ce ai shi ya bani lasisinta don haka don ta kare a kansa ba laifi bace. 

Allah ma ya sauwake in auri likitanki Inna, wushe nan inji dan fillo, ya yimin tsufa, bayan yanada matarsa har da goyo. Yo Allah na tuba ba gara min Yaya Jamilun ba yaro danye shar kama na?"

Ai ba ta kai ga rufe baki ba Inna ta mike ta sauke hannunta a bakinta, jikake bumm! Da sauri Sarham ya kauda kai, ganin har ta fasa mata baki, ya hau saka takalmin sa absent-mindedly.

Malam ya ce, "Haba Safiyya, in rai ya baci hankali ke nemo shi, ki rasa abin duka da fiddawa jini sai Hauwa abin Allah sarki wadda ko ganinki ba ta yi da idanunta?"

Da kuka da wiwi Hauwa ta ta karasa dakinta tana tafiya tana dafa bango har ta shige daki. Ta rufo kofa ta kifa kai a jikin kofar tana kuka.

Ba kukan dukan da Inna tayi mata a gaban Sarham take yi ba, kukan Malam yace “ita abun Allah sarki ce tunda bata da ido”. Bazata taba karbar kaskanci akan nakasarta ba amma zata karbi kwarin guiwa. 

Sarham ya yi musu sallama cikin sanyin jiki zai tafi, bayan ya roki Malam Bilyaminu ya daga komawarsa zuwa Ghana sai sun gana da mahaifinsa tukunna.

Yace zai dawo da daddare ya kai shi gun Abban nasa kamar yadda ya bukata.

Da haka Sarham ya juya ya bar gidansu Hauwa yana jin kansa kamar duk abin da ke faruwa din nan a cikin mafarkiyake gudana. Baban Hauwa ya dawo, har ga shi ya bashi aurenta da kansa. Duk abin da ya tsara wa ransa a kan matakan da zai bi ya auri Hauwa, da yardar Allah za su tafi cikin sauki fiyeda yadda ya zace su tunda mai kankat (Baban Hauwa) yayi amanna nan take, Innar Hauwa dama yake ji kuma ga mai tausa matai ta ya dawo. Sai ya gane har da daukin Ubangiji a cikin al'amarin nasu.

Daga nan gidan su Hauwa, ofishin Abbansa ya wuce cikin makaranta, don ya san a daidai wannan lokacin a can ne kadai zai same shi.

Abba Prof. na shan shayi a kujerar ofishinsa dake cikin tsohuwar jami’ar Bayero, babban dan sa, shalelen Abba (Dr. Sarham) ya yi sallama cikin rashin nutsuwa. 

Abba ya bashi izinin shiga idonsa a kansa. Kallo daya ya yi masa ya lura da cewa Sarham duk kwalisar shi wadda bata barinsa ya fito koda falon gidansu ne ba tareda ya dauki wanka na musamman ba ga dukkan alamu yau ko wankan safe bai yi ba ya fito har ofishinsa. 

A nitse yake kallonsa har ya zauna a kujerar gabansa, ya ce, "Lelen Abba, what's wrong with you haka? Daga kwanaki bakwai a baya zuwa yau, you are upset? Duk ka canza daga yadda na sanka anya kana auna bp dinka?".

Kai tsaye Sarham ya ce, "BP na lafiya lau Abba. Amma Abba aure nake so ka karba min, nan da kwanaki uku kafin su bar kasar nan. 

Abba alfarma nake so ka yi min, irin wadda ba ka taba yi min ba!

Abba ban taba rokon ka wani abu ka hanani ba, amma na san wannan zaka iya hana ni, nikuma bazan iya fasawa ba, sabida dalilai na masu yawa ne Abba. shiyasa ka ganni a haka, ba kuma zan kara nutsuwa ba sai ka yi min auren, Abba na zo neman amincewar ka da taimakon ka da albarkar ka don Allah Abba na, ni na san a komai kana fahimtata Abba”.

"Aure Sarham? Duka-duka yaushe ka yi auren fari?” Abba Prof. ya tambaya cikin tsoro da mamaki. “Wannan karon kuma ina ka debo auren? Namamajo sarkin mata, yau shekarata talatin da biyar da mahaifiyarka ita kadai. Kaji na taba sha’awar karawa?

 Ba zan taba hana ka yin aure ba, don ba'a hana namiji aure, don in an hana shi aure baza’a hana shi zin aba, ban san yanayin halittarka ba, amma ka sani ka dauko hanyar saya wa kanka rashin kwanciyar hankali muddin ka hada wa kanka mata biyu da kuruciyar ka to 35 baka kai ba, alhalin kana zamanka lafiya da matarka har ga albarkar haihuwa Allah ya fara ba ku. 

To karin auren na mene ne kuma? Ni dai nasan ba sha'awa bace, don nasan kaina kuma nasan ni ka gada, ba kuma rashin gamsuwa da iyalinka bane ya saka wannan rigimar".

Sarham ya yi maza ya ce da Abbansa, "Auren da zan yi yanzu na kwakkwaran dalili ne, wanda idan ka ji shi kuma kanada zuciya a kirjinka Abba zaka mara min baya, bana son zuciya ba ne, bana soyayya bane. Sannan ba sha’awace ta saka ni yin sa ba Abba.

 Auren jihadi zan yi Abba wanda dalilai masu yawa suka yi sanadinsa".

Duk ya saka Abba cikin rudu, ganin haka ya gyara zama ya shiga kwancewa Abbansa labarinsa da HAUWA, wato tun daga ranar da ya yi wa Hauwa aikin ido, abubuwan da suka faru bayannan, har zuwa dawowar Malam Bilyaminu jiya.

 Matakin da Inna ta dauka a kan Hauwa, da yadda ya ce shi a ba shi aurenta zai iya zama da ita da lalurar tata. Kai hatta rayuwar dasu Hauwa sukayi a baya ta sayarda abinci a Tasha Bai boyewa Abbansa komai ba.

Abba Prof, sai ya dan zakuda kadan a cikin kujerarsa, sau tari kana haifar Da har ya girma ya fika halin kwarai, in baka yi wasa bama sai ya riga ka shiga aljannah. 

Yana alfahari da Sarham akan halin kwarai da nagartarsa wajen darajja al'ummar Annabi, amma rayuwar Tashar nan da su Hauwa sukayi in ya tuna sai yaji ransa baya so, ace dansa ya auri ‘yar mai abinci a tasha, sai hya kada baki ya ce,

 "Lelen Abba na dade ina jiran ranar da za ka zo min da wannan bayanin akan Hauwa dinnan ai, na kuma san dama da wuya in ba karshen alewa kasa ba.

Ni ban yarda wai ba son Hauwan nan ka ke yi ba, ka cire maganar wani JIHADI da ka ke fakewa da shi, don jihadi kala-kala ne in shine akwai wanda yafi wannan lada ma, amma ka sani ni ba yaro ba ne kamar ka. Da zan tsaya yaudarar kaina da kaina.

 Ka saka sa a ranka kawai tuntuni, ko recently, ka fara son yarinyar nan ka fara developing interest a kan ta yanzu, ko ba yanzu ba.

 Well, ba ni da hujjar hana ka, amma ka shirya daukar dala babu gammo daga matarka, wai makauniya da auren nesa.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yarda wadannan mutanen suna cikin kaddararka, don haka ba ni da ja cikin abin da Allah ya hukunta. Kawai dai bana so ka gurbata zaman lafiyan gidanka da auren rainon tasha. Ka san rayuwar sayarda abinci a Tashar mota kuwa? Da kallon da akewa mai yin ta? Hummm. 

Amma tunda ka ga za ka iya ka kuma yarda da tarbiyyarta ni shawara ce kawai tsakaninmu.

Zan tura insha Allahu a karba maka auren kafin iyayen nata su koma Ghanan. 

Ko babu komai ni ma ban san yaya karshen rayuwar nawa 'ya'ya matan zai kasance watarana ba, ba wanda aka gama yiwa halitta sai ranar da ya koma ga mahaliccinsa".

Wani irin relief ya sauka a zuciyar Dr. Sarham. Tunda har ya samu hadin kan Abba ya san na Mama Maishari’ah ma ba zai zamo mai wahala ba. Mai wahalar da ma Innar Hauwa ce, ita kuma ya gane ba ra'ayinta daya da maigidanta akan Hauwa ba don haka nata ra’ayin ba zai yi tasiri ba, yana da tabbacin malam Bilyaminu din zai iya janyo masa ra'ayinta. Kenan matsalar in ma zai sameta to zata fi karfi daga matarsa uwar 'yar sa Dr. Madinah ne. Madinah zata fahimci komai amma banda lamarin kishiya ya sani. Inda shine babban weakness dinta.

Kamar Sarham ya sani kuwa, don kuwa Malam Bilyaminu yau wuni ya yi yana ganar da Inna, yana fadakar da ita don Hauwa ta rasa ido ba yana nufin bata da feeling ba, don Hauwa bata da ido baya nufin bazata so daukar yaran data haifa ba, ya kuma ce Allah ya halatta mata yin aure wanda sunnar kowanne musulmi ne don kare kansa daga dattin zina. 

Bata da hujja har a wurin Allah na cewa bazatayi aure ba, tunda yarinyar nan duk da lalurar ba ta rasa ma su son aurenta jajirtattun mazaje irin haka ba.

Yace idan ma ta hana Sarham to shi zai baiwa Salisu.

Bata yadda zaayi ya aje Hauwa a gabansa ba aure in ta kai shekaru 20 wai don kawai bata gani. In ita bata gani su sun ganta sun ce tayi musu. Duk yadda Inna ta so ta ganar da shi abin da ta ke hangowa wato wulakanci da tozarci take gujewa Hauwa Malam Bilyaminu ya ko ki sauraronta, cewa yake.

 “Ba ki isa ki katange ta daga duk wata rubutacciyar kaddararta ba. Mai lafiya ma yana shan wahala a gidan aure yana fuskantar kalubale kala-kala ba sai mai nakasa kadai ba.

 Aure ibadah ne dama ai, ba gidan jin dadi da kashe ahu bane.

Ni dai fatana da addu’ata Allah ya ba Hauwa dacewa a cikinsa, dama kowacce irin rayuwar aure ta samu kanta. Na yi amanna ibadah ce. Zan roki Allah yayi mata jagora a duk inda ta shiga ba tareda Dan Adam yayi mata jagora ba. 

Na yarda da wannan yaron SARHAMU dari bisa dari, daya ne tamkar da dubu, shi din mutum ne har da rabi, ban da dan Adam butulu ne a halittarsa, ai ko wani daban Sarhamu ya kawo miki koda kuturu ne, ya ce ki ba shi auren Hauwa-Kulu ba shi da kansa ba, tofa bai kamata ki daga ido a kan al'amarin kina jayayya dashi ba, balle shi da kansa yace zai aureta ba wani ne ya tursasa shi ba.

Duk abin da ki ke hango mata Allah Ubangiji da ya halicce ta ya riga ki hangowa, kuma yana tare da ita fiye da ke".

Inna ta rasa yadda za ta yi Malam ya fahimce ta, ita kam in ba tare da ita Hauwa za ta je gidan miji ba, hankalinta ba zai taba kwanciya ba. 

Hauwan da ko Saka always pad sai da ta tsaya tsayin daka ta koya mata. Ita har gobe Hauwa kamar 'yar goge take a wurinta, musamman da ta lura hankalin HAUWA yafi karkata ga Jamilu ta kara tabbatarwa kanta Hauwa bata gama sanin ciwon kanta ba har gobe.

Ta kasa boye wannan tunanin nata har sai da ta furta shi ga maigidan nata. Na cewa saidai su tafi tare gidan mijin ita da Hauwa. Wannan karon dariya Inna ta bai wa Malam Bilyaminu ya ce, 

"yanzu idan na kyaleki sai ki bar ni nikadai a Ghana, nida nake sabon angonki ki nima, tafi taya Hauwa zaman daki a gidan miji? Kai jama’a? yaushe kika barar da kunyar malam bahaushe har haka akan abinda kika haifa Safiyya? Bayan ni ma shekaru aru-aru ba na tare da ke inata dokin kasancewa dake?"

Inna ta ji kunya sosai harda sunkuyar da kai, ta ce, "Malam! To ai abin ne… ni kwatakwata ya ki zama daidai a kwakwalwata ko kankani. 

Hauwa ta je gidan Sarhamu alhalin ba ido, alhalin yana da mata har da 'ya. Da dai a ce ma babu kishiyar ko Hauwa lafiyarta kalau ko daga shi sai ita, sai na fi kowa farin ciki da wannan al'amarin. Don jinin Sarhamu abin so ne da kauna agareni".

Malam Bilyaminu ya ce, "Ki manta da komai kike hange ki bar Hauwa a hannun Ubangijinta, ki daina tunanin ke ce mai kare ta ko ke kadai ce garkuwarta.

 Allah shi ne mai kiyaye bayinSa, kuma Shi kadai ne garkuwar bayinSa a ko'ina suke, kada wannan ya shafi imanin ki da kaddara".

****            *****                ***

A daidai wannan lokacin, shikuma Sarham, yana durkushe gaban Mama shi kuma, wato mai shari’a Haj. Maimunatu yana fada mata bukatar da yake da ita a safiyar yau, don Daddy ya ce ya je ya nemo yarda da amincewar mahaifiyarsa da albarkar ta, kafin ya yarda ya je gun Baban Hauwa sai mahaifiyarsa ta amince ta kuma sanya albarka.

Mama shiru ta yi tana sauraron Sarham har ya kai aya a kan bukatarsa na auren HAUWA KULU nan da kwana uku kafin iyayenta su koma Ghana da ita.

Mama ta dade tana kallonsa kansa a sunkuye, kafin ta gyara zama tace, Sarham ni abin da ka zo da shi yanzu bai zamo bako a gare ni ba, ko da ma na san watarana makamanciyar wannan na nan tafe tsakanin ka da ‘yar mutanen Badala. Na kyale ka ne in ga iya gudun ruwanka a kan mutanenka na Badala.

Sarham ka daina fakewa da cewa za ka auri Hauwa don kada a koma Ghana da ita, wannan hujja ce wadda hankali ma ba zai taba kamawa ba. Ka fito kai tsaye ka ce min za ka auri yarinyar da ka dade kana so, ba tare da kai kanka ka san son nata ka ke yi ba….".

Dagowa ya yi cikin mamaki yana kallon bakin Mamansa wato Mai Shari'a da ke wannan furucin da shi bai taba sani ba, wadda a dabi'arta yasan ita bata daukar abubuwan da bata da hujja, sannan kuma ita mama bata kallon abubuwa sakaka yadda kowa yake kallon su, komai da muhimmancin da take bashi, yana son tabbatar da sahihancin maganarta a tsakiyar kwakwalwarsa; Anya yana da digon soyayyar HAUWA komai kankantar ta cikin ransa kamar yadda iyayensa duka biyu suke ikirari? Kamar yadda Mama ke jaddadawa bayan na Abba Prof.? A saninsa duk wata soyayya dake zuciyar dan adam ya gama mallakata ga matarsa first love dinsa MADINAH. 

Ba wata mace da zai so a bayanta. Ba ayi ba, kuma baza’ayi ba. Mama ta yi murmushi ta ce, "Sarham, Allah ya bada sa'a, Allah ya sanya albarka a ciki, amma hakika ina jiye maka wahalar dake cikin auren nan, musamman dai ido, da ake kira mutuwar tsaye, saidai na san ladan da ke ciki ya fi wahalar dake ciki yawa. Sannan ka tsayar da adalci a tsakanin matanka ba zancen mai lafiya da marar lafiya, duk sunansu matanka.

Madina ba za ta karbi al'amarin nan da sauki ba na sani, don haka sai ka aro hakuri ka kara akan wanda kake dashi. Na dade da sanyawa a raina duk ranar da ka zo min da batun auren Hauwa ‘yar mutanen Badala zan mara maka baya a bisa dalilaina na kashin kaina masu yawa”.

Mama bazata daina shayar dashi mamaki ba sai sauraron ta yake da sukunin zuciya, a yadda take magana kamar dama tana jiran zuwan wannan ranar ne. Tace.

 "Na farko son da ka ke yi wa Madina ya yi min yawa Sarham, ban sani ba ko saboda baku da wani tsiran shekaru masu yawa ne tsakanin ku, kuma matakin ilmin ku daya kaida ita, yasa nake kallon auren naku wani abnormal, zan so kwarai ka auri macen da ka girma nesa ba kusa ba, sannan wadda kafi ilmi da wayewa sosai, kuma wadda ka ke yi wa matsakaicin so. 

Sannan ne zaka san dadin aure Sarham da jin cewa ka isa a gidan ka. Amma yanzu kam! Ban san sunanka ba banda mijin Madinah.

Wannan din ra'ayina ne kawai na fada ba lallai sauran mutane su yarda da abin da na fada ba. wasuma cewa zasu yi na yi son kai. Amma iyaye irina zasu yarda dani.  

Sannan in har ba auren yarinyar nan ka yi ba 'yar mutanen Badala ni na san ba za ka taba samun kwanciyar hankalin da kake bukata ba a ko’ina kake. 

Ko don yadda ka damu da su, zamanta tare da kai matsayin iyalinka shi zai ba ka kwanciyar hankalin da kake nema shekara da shekaru, da albarkata nake cewa Allah Ubangiji ya sanya alkhairi a auren ka da Hauwa”.

Sarham, ya ma rasa inda zai sa kansa don farin ciki, kamar ya goya Mama, ya rasa ko wadanne irin kariman iyaye Allah ya albarkace shi da samu. Wadanda kullum bukatarsa da kwanciyar hankalinsa sune farkon abun dubawar su bata kowa ba. Har sai da ya yi kwallah saboda farin cikin amincewar su farad daya, abin da bai taba tsammani ba. Musamman Abba Prof.

Ita kuwa Mama dalilinta na amincewa farad daya shine har gobe ta kasa yafe abinda Baban Madinah yayiwa Sarham na rainin arziki, wato bai bashi ita cikin mutunci da darajjawa ba sai bayan ya wulakanta shi ya kuma maida ita bazawara, da kuma gorin arzikin da yayi musu kafin ya basu auren 'yar sa. 

Sai yau ta samu abunda ya tsaya mata tuntuni a kokon rai, akan auren Madinah taji sukuf! Ya fada cikin cikinta.

 Ta kasa yafe wannan sai yau dinnan da a wurinta Sarham zaiyi aure daidai shi. Kuma inda ake ganin darajarsa da tasu. Inda za’a mutunta soyayyarsa.

Da daddare suka shirya tafiya Kofar Na'isa shi da Abba Prof. don haka tun bayan isha Abba Prof. ke shiryawa. Sarham ya kira Madinah a waya ya gaya mata yau da dare ba zai samu shigowa Sorondinki ba, yana da uzuri wanda ba da jimawa ba zai sanar da ita ko mene insha Allahu.

Ya kare zancensa da cewa, "Ina fatan Munawwarahta, Giwar Sarham, za ta kasance mai fahimtata a wannan karon ma, kamar koyaushe".

Madinah taji jikinta yayi sanyi haka kawai, don bata ga dalilin wannan jirwayen ba, amma dai ta daure ta ce, "Insha Allah. Take care of yourself for us, good night Sweetheart".

Ya ce, "Night!".

Karfe takwas na daren ranar a kofar gidan Malam Bilyaminu ta yi musu shida mahaifin sa Abba Prof, Abbas Shanono. Abba ya zauna a mota har Sarham ya shiga ya yi wa Inna da Malam bayanin tare suke da mahaifinsa.

Malam ya kara yarda da cewa Sarham da gaske yake, “wannan kai ne sha yanzu magani yanzu”, ya saka hularsa yana cewa, "Ikon Allah, ni da nake shirin ka zo ka kai ni in kwashi gaisuwa in kuma yi godiyar zumunci da kyautatawa, sai ka dauko shi da kansa tun kafin ni in fara zuwa? Baka kyauta ba".

Da rawar jiki Malam ya yi wa Abba Prof. shimfidar darduma a nan tsakar gidansu ya je da kansa ya shigo da Abban.

Abba ya ga mutunci da karrama dan Adam da sanin halacci wajen iyayen Hauwa, duk yadda yake tunanin talaucin nasu sai ya ga ba haka ba, kuma ba su da wata makusa da za'a kushe har aki auren jinin su akanta. Da gaske sunansu talakawa a bakin malam bahaushe. Amma fa ba irin talaucin da ya zama illa ba, tun daga soron gidan ka san ka zo gidan mutane masu tsaftar muhalli da tsaftar zuciya. 

Ko'ina ka duba tsaf tsaf yana tashin kamshin turaren wuta. Suka gaisa cikin karrama juna, Malam ya yi masa godiya a kan Sarham, ya kuma yaba masa a kan irin tarbiyyar da suka ba shi. Sannan ya tabbatar musu alkhairi zai yi ta bibiyar su har zuri’ar su. Shi kuma Abba ya ce, "ai babu komai don ya gine gidan kakannin jikokinsa, tunda gashi yanzu ya zo neman auren Hauwan ma dungurugum. 

Shi kuma Malam Bilyaminu da dukkan zuciyarsa ya jaddadawa Abba cewa ya baiwa Sarham auren Hauwa, ya sake jaddadawa, “ba Sarham ba ko wani daban Sarham ya kawo zai ba shi aurenta. Fatansa kawai a tausaya mata, ayi mata adalci a kuma dauke mata wahalhalun aure da hidimar da aka san bazata iya ba saboda lalurarta.

Abba Prof. ya ce, Kada su ji komai, Sarham likitan ido ne, ya san komai a kan lalurar makanta, kuma tunda shi ya ce ya ji ya gani to ya ga zai iya ne.

 Ta fanninsu su iyayensa za su taya su kula da Hauwa kamar tana gabansu.

Abba Prof bai bar gidan ba sai da suka tsayar da cewa, lallai kafin komawarsu kasar Ghana za a daura auren Dr. SARHAM da HAUWA.

Malam Bilyaminu ya yi rantsuwa a kan bayan sadaki ba zai karbi komai ba, kuma ba za'a yi taron komai ba, aure kawai za a daura Hauwa ta tare a gidanta.

Da Abba zai tafi ya ce a kira masa uwar sa wato Hauwa, yana so ya ganta. Inna ta shiga har dakinta ta same ta tana barci sadidan bata san wainar da ake soyawa ba sai da Inna ta tashe ta, "Ke Kulu, Kuluwa, Hauwa, taso ki sa hijabinki ki biyo ni".

Hauwa ta mike cikin nauyin barci tana lalubar hijabin nata, ba tare da ta san ina za su je ba. Hannunta Inna ta kama har gaban Abba Prof. ta zaunar da ita tana gaya mata "Baban Likitana ne, ki gaishe shi".

Hauwa ta gaida Abba, ba wata kunya a idonta a kansa don bata san ma me ya kawo shi gidan su ba, shi kuwa ya amsa fuska a sake, a ransa ya ce, Ban da rashin idon ai wannan ta ko ina matar aure ce. Tsari da zubin halittar jikinta shigen na mutanen Senegal.

Ya koma gida a ranar ya gama magana da ‘yan uwansa waliyyan Sarham a kan ranar asabar su zo su je a daura auren.

 Wani ikon Allah tunda aka tsaida maganar auren Sarham da Hauwa ranar asabar Sarham bai iya ya kara zuwa gidan su Hauwa ba, kunyar Inna ya koma ji sosai. Sumayyah dai sai ji ta yi Mama ta ce mata asabar za a daura auren Bhaiya da yar mutanensa na Badala.

Sumayyah a zaune take amma wani dan karamin ihu data saki hadi da juyi nan take, ya baiwa Mama mamaki, ta yi ta taka rawa daga tsaye, sannan ta zauna ta rangada guda wadda ta tashi Aunty Surayyah daga barcin la’asar din ta wanda ya zame mata farillah duk da kullum Mama na hana ta.

Surayyah, data farka tagine me suke cewa, kamar kusan ace a sama ta tsinci zancen, bagatatan, wai Bhaiya zai kara aure, ta kuma tabbatar Madinah ba ta sani ba, don ko dazu sun yi waya da ita lafiya-lafiya ko kadan ba ta yi mata zancen nan ba.

Surayyah gabadaya rudewa tayi, tana son ta kira Madinah ta labarta mata tana tsoron Yayan nasu da abida hakan zai haifar, kada ta yi masa riga-malam masallaci. Ta sani shi kuma baya so ka shiga sabgarsa musamman in bai s aka ciki ba. Shi ya sa ta yi shiru tana ta kawa zucin maganar. Haka ta wuni bugun cikin Sumayyah tana ta tambayar ta ko wace ce zai aura din? Sumayyah da ya ke ta san Surayya sarai, kuma ta san tsakaninta da Madina sai ta ce mata, “in zan baki shawara ki dauka, duk da nake kasa dake, ki fita daga abinda babu ruwanki. Nima ban san ko wace ce ba, amma ina backing maganar dari bisa dari sai me za’ayi?”

Surayyah dai bata hakura ba, kuma bata dauki shawarar Sumayyah ba, ta sake bugun cikin Mama kan wace ce Bhaiya zai aura da Sumayyah ke ta murna haka??? Ta nuna kamar bata da issue da abin. Abinka da Uwa, sai Mama ta zauna ta bata labarin su kaf! Da irin kusancin da suke dashi da Sarham shekaru masu yawa a baya. 

Sai lokacin Surayyah ta tuna su, ta kuma gane yarinyar da yace yayiwa aiki ta makance ne wadada ya likewa tun daga lokacin, ta kuma gane sune wadanda yake turowa kudi tana cinyewa wadanda sabida su dan uwanta ya kusa daina gaisawa da ita. 

Surayyah cikin tsananin bacin rai ta ce, “kuma Mama shine kuka amince masa? Saboda Allah duka-duka yaushe Yaya Doctor yayi auren fari, wannan ai zalama ce da hadama, kuma me Madina ta rasa ko ta ragemu dashi da za’a yi mata kishiya ko arba'in ba ta yi da haihuwa masa ba?"

Numfashin Surayya har sarkewa yakeyi don tsananin bacin rai. Mama na observing dinta a hankali don bata ga dalilin daukar zafinta akan maganar haka ba, na farko ba itace Madinah ba, na biyu ta san dai bata isa ta sa Sarham abu ko ta hana shi ba, ta ce. Mama ta nuna ta da yatsa tace "Surayyah bana son ki da shiga harkarsa, ke me guntun kashi a katara a idonsa, amma yace ya ayfe miki duk da nasan har abada bazai daina kallon ki da abin ba, ki rufawa kanki asiri ki fita daga harkar aurensa da duk matan da zai aura anan gaba ma. 

Ni na amince masa don auren soyayya Sarham zai yi wannan karon ma, kamar yadda ya auri Madinah don yana sonta, ba kuma don Madina ta gaza dashi ba ko mu tayi mana wani laifi, a’a kaddararsa ce auren mace fiye da daya, wadda shikadai yasan karfin dalilinsa".

Tun magana na kankanuwa, wato abinda Hausawa suka ce abu kamar wasa karamar Magana ta zama babba cikin kwana daya, don har ga shi gobe ne daurin auren Dr. Sarham da Hauwa, kuma ya zo gidan ya fi sau a kirga sunyi hira da tsare tsare akan tarewar ta shi da Malam da Innarsa, inda Malam ya gaya masa baya bayan kowanne irin biki, a daura aure ya zo ya dauki matarsa ya tafi da ita duk inda yake so, amma har ya gama ya tafi abinsa bazaka ji ya nemi ganin Hauwa officially ba, ko ya nuna yana son yin magana kebewa da ita, kai gara da in ta gaida shi yana amsawa a shalake yanzu itama ko ta ji shi ta daina fitowa, ta daina ko kwakkwaran motsi idan ta ji shi a gidan, har sai ya tafi, ta maida kanta daddawar daka kawai.

Inna ta rasa me ya sa ko ya zo yanzu ba ya wuce minti goma, zai gaishe ta suyi maganar da zasuyi da ita da Malam, sai yace ya wuce Sorondinki gun su Waheedah. Ita kuma ta kasa ce masa ko sau daya ne kafin daurin aure, ya kamata ya zaunar da Hauwa ya zanta da ita ya nemi soyayyarta duk da dais hi din ba bako bane amma Magana ta aure ai daban ce, ya kamata da bakin sa ya fada mata abin da ake ciki kan maganar aurensu, don ita kam Inna ta kasa gaya mata gobe ne daurin aurenta da Dr. Sarham, don ta san bata so, ko kadan duk son tada aure hankalin ta ba’a kan Sarham yake ba. Har tafi son ace da Jamilu ne.

Wannan kuma shi ake kira ‘power of persuation’. Jamilu ya iya zama ya kalallame Hauwa da alkawarurruka da kalaman soyayya masu nauyi shiyasa kullum hankalin ta da kyakkyawan zatonta na kansa, tsinkayenta na gaya mata da shi ne kawai bazata samu matsalar zaman aure ba saboda tsakani da Allah yake sonta so kuma na soyayya mai zafi, in ka dauke matsalar Babansa. 

Yanzu Sarham a wajen su Waheedah yake kashe lokacinsa gaba daya, guiltness ya sakalo wuyansa ya hana shi nisa da Madinah, amma ya rasa ta inda zai fito mata da maganar wai zai kara aure a washegarin gobe, ko yayi kokarin yin jarumta ya fada mata in yaga yadda taketa haba-haba dashi, da kulawa da abincin data san yanaso, duk da take jego a gidansu ma bata fasa yi masa girkinsa shi kadai ba kuma na musamman, duk sai yaji ya kasa furtamata me yake ciki, Annabi SAW yace zuciya na son mai kyautata mata, inda Allah ya taimake shi gobe ne za ta cika arbain da haihuwa, don har sun gama yi mata shirin komawa Jeddah. Ya soma tunanin yabkyaleta ta koma in yaso ya gaya mata ta waya. Kai! Hakan kuma ba dabara bace gara duk halin da zata shiga ta shiga a gabansa

Fargaba mai cakude da shakka-shakka ba wai tsoro ba, irin wadda ko da ace a can baya babu ita a tare da namiji, komai yawan jarumtakar sa, irin wannan shakkar sau tari namiji na gamuwa da ita ne a yayin fadawa uwargida zai kara aure, irin tace ta bi ta addabi Dr. Sarham. Yaji yana matukar shakkar Madinah da gudun bacin ranta.

Madina ta fito daga dakin Haj. Laila (kakarta) ta tadda shi a babban falon gidan. Ta ce, "Dr na, Baban Waheedah yaya dai? Jikin ko garin? Irin wannan daure fuska haka? Ni fa har na sa Yaya Usman ya yi min booking zan koma Jeddah gobe, don na ga kamar kai kam baka da alamar barin garin Kano nan kusa, ka shantake abinka. You are enjoying Kano all the way. Ni kuma kaga inada sabgogina da zan koma inyi. Akwai wani ‘marriage coach program’ da zan gabatar dana koma.

 Kodayake ban san tsayin hutun naka ba, amma yaso yayi yawa".

Sarham da yake namijin duniya ne kuma dukinda namiji yake dan rainin hankali ne sai ya ce, "wai ni Madindin, saurin me ki ke da ba za ki bari mu koma tare ba?"

Ta ce, "na gaya maka inada muhimmin program, kuma Daddy zai yi birthday dinsa @70 ina son a yi tare da ni da Waheedah. 

Inyaso in ka gama sai ka taho dagabaya, babu komai, I will manage to miss you for a while”.

Duk yadda Sarham ya so ya gaya mata gobe za a daura masa aure da watanta kasawa yayi, musamman data hade bakinsu wuri guda tana manna masa wata soft-kiss mai fidda sauti da kashe jikinsa, sumbar bankwana indeed! Tunda har zuwa lokacin jego take yi, mai nuna yadda zatayi kewarsa har cikin idonta zaka ga hakan. Don haka har suka gama soyayyarsu ya baro gidan, ya shiga mota ya kunna, ya kashe ya sake komawa gidan, amma bai shiga ciki ba, ya sa maigadi ya kira masa ita.

A babban soron gidan Alkalin Alkalai Justice Habibu Sorondinki Madina ta cimma Sarham again, a dan kidime take da kiran da yayi mata din yaki shigowa kamar wani bako. Ta same shi ya harde hannuwa a baya kamar saurayin da ya zo zance wajen sabuwar budurwarsa, amma damuwar da ke kan kyakkyawar fuskarsa wannan karon ta fadar da gaban Madinah.

"Wai ni don Allah Baban Waheedah lafiya ka ke kuwa yau? Tunda ka zo na kasa gane kanka, kai ba damuwa ba kai ba farin ciki ba, mun yi sallama ka tafi, kuma ka sake aikawa a kira ni, kada ka sa in kasa tafiya, wallahi kasa gabana faduwa yake yi, musamman in na kalli yanayin damuwar da ka ke ciki". Ta kama hannunsa ta dora a saman kirjinta, "ji yadda kasa gabana ke faduwa, kirjina ke bugawa".

Sarham ya daga kai idanu sun yi ja, ya dubi Madinah cikin kwantar da ‘eye-lashes’ dinsa, sai ya ji kamar an kara masa sonta, ya hau tambayar kansa shi kuwa me yake nema a mace bayan tarin baiwarwakin da Allah ya yi wa Madinarsa? 

Me ya gani a Hauwa-Kulu wanda ya kamo na Madinah? Banda yana so ya tallafi rayuwarta yayi matsalolonta dana iyayenta? Ya kuma kawo maslaha akan soyayyarta datake yiwa Jamilu???

Bari kawai ya daure ya gayawa Madina gaskiya tunda ba zai iya komawa ya ce da Malam Bilyaminu ya fasa auren Hauwa ba, don a zahiri matarsa kadai zuciyarsa ke yi wa so na soyayya. Tsakaninsa da Hauwa har gobe bai gama tantance matsayinta ba. Ya san dai, da so ko babu so ya zama tilas zai auri Hauwa-Kulu, tunda dalilai da hujjoji kwarara duka sun sallada masa hujjar aurenta.

Madina gani ta yi Sarham ya tafi tunani kuma, ya manta ma tana tareda shi, ta kara tsurewa, sai ta matsa ta rungumeshi tsam-tsam da hannu bibbiyu ta ce, 

“Baban Waheedah, baka da lafiya ne?"

Sarham ya samu kansa da rike Madina gam-gam cikin jikinsa shima, ya ce, "Madinah lafiyata kalu, I am sorry, aure zan kara".

Madina ta ce, "Auren namu wani abu ya yi da za a sake daura shi?"

Gaba daya ta rude kamar yadda shi ma ya rikice, azancin harshe na shirya zance ko lallashi ya kwace masa, ya ce,

 "Madina ki fahimce ni da kunnen basira, wata matar zan kara aure. Gobe insha Allahu daurin auren".

Madinah ta san a lokuta da dama idan ta yi ‘losing control’ na ‘temper’ dinta tana iya aikata komai, ciki harda jiwa kanta ciwo wadanda ta kan buga su a jikin bango, don haka ta janye hannayenta daga cikin jikin Sarham a hankali, ta soma ja da baya tmkar jikin yana shocking dinta. Ganin haka shikuma ya soma takowa yana biyo ta, yana cewa, 

“Saurare ni Madinah, ban so zan fada miki ba, amma wallahi auren jihadi zan yi ba auren so ba....". 

Madinah ta ce cikin rufe ido da girgiza kai, hadi da toshe kunnuwanta hagu da dama da dan alinta "sannu MUJAHID!".

 Daga haka sai kawai ta juya ta runtuma da wani irin gudu zuwa cikin gidan Kakanta.

Sarham ya dade cikin wani hali na rashin sanin abinda ya kamata ya yi, ya bita cikin gidan ne ya ganar da ita babu wata mace mai irin nata matsayin a zuciyar sa? Ya ga ko me zai ce yanzu bazata saurare shi ba, kuma bazata yi masa uzuri da shi ba, idan ma ta fahimta din kenan, kafin ya ga babu sarki sai Allah ya ja motarsa ya wuce gida, don maigadin ya ce masa, Madina ta ce don Allah kada ya sake ya aika shi kiranta. Shi kuma yau ya samu kansa da maida kansa bako, ya kasa shiga gidan su Madinah kai tsaye ba tareda ya aika din ba. Ji yake laifin duniya ya gama yi musu.

Bai so suka yi irin wannan sallamar da Madinah ba, ko da ya koma gida ya gwada kiran wayarta ya fi sau shurin masaki tana kallonta tana ringing ba ta daga ba. 

A lokacin tana hada kayanta ne babu ko kyallin hawaye a tare da ita, illa kawai ta saka wa ranta idan har Sarham da gaske yake aure zai kara, to karshen zamanta da shi kenan daga nan gidan kakanninta gidan iyayenta za ta nufa a Birnin Jeddah.

 Idan kuma wasa yake yi, to sai ya gwammace bai kara yi mata irin wannan mahaukacin wasan ba wanda zai iya buga mata zuciya farat daya.

Asubahin fari direban Hajiya Lailah ya dauki Madinah da Waheedah da aka nannade cikin fararen kayan sanyi sai filin jirgi, da yake jirgin karfe bakwai na safe za ta bi da ma. Ba wanda ta yi wa zancen da Sarham ya yi mata, suna sauka a Jeddah ta kira Usman wato Yayanta da take bi, kan ya zo ya dauke ta a Matar (airport) din na Jeddah.

  *****           ******            ****

              MR&MRS SHANONO

                 (KARO NA BIYU)

Karfe goma na safiyar ranar asabar din da Madinah ta tashi zuwa Saudiyyah, iyaye da waliyyai da makwabtan malam Bilyaminu da mai unguwar Kofar Na'isa na lokacin, suka daura auren Hauwa'u Bilyaminu da Dr. Sarham Abbas Shanono, akan sadaki mai albarka wato mafi kankanta, daurin auren bai ja mutane da yawa ba, don ba su sanar ba sai a daren ranar.

A daren ranar, wato jajibiren daurin auren, bayan tafiyar Babansu Sarham. Malam Bilyaminu ya isa gidan makwabcinsa Malam Isah ya gaya masa komai, shi kuma Malam Isa cikin matsanancin farin ciki ya karasa ya fada wa sauran makwabtansu da Mai unguwa. Aka daura auren mai ban mamaki da karfe goma na safiyar ranar. Auren da ya janyo magana sosai a cikin Badalarsu Hauwa bayan daurin auren, kowa so yake ya san waye ya auri Hauwa-Kulu alhalin ta samu laluran da ake kira "mutuwar tsaye". Shi kuma Sarham a lokacin yana gida yana fama da tsokanar Sumayyah data saka shi gaba, ko na minti daya ba ta bar shi ya huta ba da shagube. "Yau dai Allah ya rubuta mai abu ya dauki abunsa kowa ya huta!".

 Ta kara da cewa cikin rufe baki da boye dariya “shikenan daga yanzu babu sauran korafi a kan Hauwa-Kulu na zance a soro da saurayinta Jamilu, ni ka me zance da wanan Jamilun banda godiya? Tunda shi yasaka yin hobbasa ka ceci kanka?” Sarham ya yi fuska sosai yace “Sumayyah zan sabar miki, ni sa’an wasan ki ne wai?”

 A lokacin ya gama shiryawa cikin wata (grey excellency) shaddah mai karkar kamar ansa mata starch, ya karya ruwan tokar hula zanna a kansa, shiri yayi zai tafi kofar Na'isa din, don an tabbatar masa daga Sorondinki cewa Madina ta tashi tun safe zuwa Jeddah.

Ya ce da Sumayyah “in ta gama yimasa shaguben ta wuce su je su gaida su Inna”. Duk dai don ya hana ta surutun da ta ke faman masa kamar an bude famfo.

Da murna Sumayyah ta je daki ta dauko abayarta ta rufa masa baya suka dauki hanyar Badala.

A hanya Sumayyah ta yi wa Bhaiyanta congratulations, da felicitations ya fi a kirga, amma a aurensa da Madina ai bai manta tsiyatakun da ta yi masa ba, alhalin Madina ba ta yi mata laifin komai ba. Sumayyah kenan.

Nan ya saka wa ransa sai ya tashi tsaye a kan mu'amalar matansa biyu da kannensa biyu, don ba ya son bangaranci irin wanda tun ba a je ko'ina ba Sumayyah ta soma nunawa. Surayyah ma ta soma irin nata na taya kawarta Madina kishi don ya lura ta daina kula shi. Abin mamaki ga idonta ga nasa sai tayi kamar bata gannshi ba. Ya kuma fahimci hakan ne zai kasance ta bangaren Sumayyah ma in bai yi da gaske ba. Wato itama ta taya Hauwa kishi da Madina. Mamakinsa daya ne, yaushe har Sumayyah ta yi wa Hauwa farin sanin da ta ke sonta har haka? Duka-duka ya san sau daya ya taba hada su suka gaisa a gidan su Hauwan.

Sumayyah ta tuno wani abu sai ta hau hadiye dariya. Da gefen ido Sarham ya kalle ta yana ci gaba da tukinsa cikin wata irin nutsuwa da bai taba ji a tare dashi ba.

 Yau ji yake ya fi kowa nutsuwa, ya fi kowa kwanciyar hankali da ya auri Hauwa-Kulu, da ba zai ce don soyayyarta ya samu wannan kwanciyar hankalin ba sai don Hauwa ta zame masa wani 'mission' mai muhimmancin da dole ya cika shi a rayuwa in yana son kwanciyar hankalinsa ya dore dari bisa dari.

Sumayyah ta ce, "Bhaiya!" 

Sai ya juyo kadan suka hada Ido taga ya kara mata kyau da kwarjini, har da kyallin angonci akan goshinsa da suka hada ido sai ta hango wani boyayyen ‘contentment’ a kwance kan kyakkyawar fuskarsa, ai kuwa Sumayyah ta fashe da dariya ta ce,

 "Yanzu Bhaiya, duk inda ka ga kare yana sunsunar takalmi ka yarda dauka zai yi ko?"

Shikam ya gaji da shegantakar Sumayyah Harararta ya yi, ya ci gaba da tukinsa, amma da da ne tabbas da ta sha Mari yatsu goma. Sumayyah bata daddara ba ta sake cewa, "Wato Bhaiya, soyayyarka da Hauwa na lura wata irin special soyayya ce boyayya a zukata, wadda Allah kadai ya san ta yadda ya tsara ta. tunda Hauwa dai bata taba ganinka ba. 

Amma ni dama, ko ka yarda ko kada ka yarda, na dade da sanin a haka za ta kare. Bhaiya Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka I am so happy Bhaiya na, nafi kowa murna da faruwar al’amarinnan nikam!". 

Sarham ya yi mamaki da ya samu bakinsa da amsa addu’ar Sumayyah da "Ameen" duk da ya san shi ba wata special soyayya tsakaninsa da Hauwa, sannan ba dole aka yi masa ya aure ta ba. A wurinsa aurensa da Hauwa kaddara ne, kuma DALILI MAI GIRMA ne ya yi sanadinsa.

Sai shigo da huhun goro da alewa ake yi ana ajiyewa a falon Inna, bayan ‘yan daurin auren sun watse kenan da waliyyan Sarham da suka zo daga Shanono. Malam Isah shi Baban Hauwa ya bai wa waliccin auren Hauwa-Kulu.

Hauwa ta fito wanka a daidai lokacin ta gefen sallarta a dakinta, ta zuba hijabin sallarta ta tada sallar walha kenan ta jiyo muryar Malam Isah na gayawa Inna daurin aure ya kammala, HAUWA-KULU ta zamo matar SARHAMU, Allah ya kade fitina ya bada zaman lafiya.

Kawai sai ta tada kabbarar sallarta cikin gigicewa da tare sautin kuka da tafin hannunta. 

Cikin sujjadarta ta farko taji muryar Sarham ya yi sallama a tsakar gidansu, sai ta ji gabanta ya tsinko daga kirjinta ya fadi kasa ras! Ras!! Ras!!! Har sau uku. Daga nan sai muryar data shaida ta kanwarsa Sumayyah ce ita ma ta karade gidan da sallama, da alama tare suke.

Ta ci gaba da sallahrta amma ta kasa karanta komai daidai har ta idar, lokacin Inna ta rako Sumayya dakin nata, ta ce, “Hauwa, kin idar ne? Sumayya ce suka zo tare da likita".

Sumayyah ta shigo ta zauna a kusa da ita, ta mika mata hannu ta rike nata wato (shake hands), sannan Inna ta ce, in sun gama gaisawa Sumayyah ta zo dakinta su yi magana.

Sarham na falo a lokacin da Inna ta ce ya shiga dakin Hauwa su gaisa, Hauwa ta idar da sallah. Cikin jin nauyi Sarham ya ce, “Inna ashe tun jiya baki yi mata bayani ba? Wannan zuwan ba nawa ba ne ai na Sumayyah ne, ni ai Yayanta ne ba zance nazo ba, na kawo Sumy ne ta gaishe ku ne".

Inna ta yi dariya ta ce, "na san da haka mana, nafi kowa sanin kai Yayanta ne. Amma wanda aure ya dan karawa Yayan matsayi yanzu ya daga darajarsa zuwa ta abokin rayuwa. Na kuma gode da zuwan Sumayya. Amma likita a yi haka? Yaushe rabon ku gaisa da mutuniyar taka idan ka zo? 

Daure ka je ka lallashe ta don Allah, don ni dai tun jiya da uban ya zaunar da ita ya gaya mata gobe daurin aurenta da kai ta daina kula ni, ta kuma kwana tana kuka.

Hauwa ta ina za ta gane cewa ba yinmu ba ne mu duka, wannan auren yin Allah ne, alkawarinsa ne tun fil azal ba na kowannenmu ba? Na fi kowa son kada a yi mata aure ka sani".

Idanun Inna suka ciko da kwallah, ta yi shiru don har ta fara jin kewar Hauwa a cikin jikinta, tun ma kafin a yi batun kai ta gidan miji.

Sarham ya sunkuyar da kai kasa yana jin wani iri a ransa da ganin hawayen Inna. Ya san irin shakuwar da ke tsakaninta da Hauwa. He can feel for her, na irin kewar Hauwa da za ta yi, amma hakan ne kadai abin da zai yi ya zama maslaha akan rayuwar HAUWA-KULU da ta iyayenta, hakanne kuma kadai abinda zai dorar da dangantakar su, musamman da aka yi sa'a ya lura Sumayyah na son Hauwa, ya tabbatar za ta taya shi kula da ita, kai dai bar Sumayyah da ra'ayin ta na rikau akan abin da ranta yake so da wanda ba ya so.

Ya ce, Insha Allah Inna ki sa a ranki ko kin koma Ghana Hauwa na hannunku ne, bana jin Mamana, bana kuma jinsu Sumayyah, za ta taya mu kula da Maijidda. Adduarki za ta bi Maijidda duk inda ta ke.

 Don Allah don Annabi ki cire damuwar wai Hauwa wulakanta za ta yi a hannun mijinta, wannan shi ne babban dalilina na auren Hauwa, don in tsare mata mutuncinta da martabarta in kuma kula da ita, rayuwar ta bakidaya da ilminta. 

Ba ni da haufi a kan kowa nawa. Babu Mai cutar da HAUWA cikinsu, Inna za mu rike Hauwa ne da amana da amincewar Ubangiji kamar tana gaban ku".

Sumayyah ta shigo tana cewa, "Bhaiya, wannan lallashin fa sai kai, Hauwa ta ki yin shiru duk irin lallashin dana yi mata".

Ta zauna a kusa da Inna.

Inna ta ce, "Je ka ka ji Sarhamu, lallashe ta, mace tafi son lallashin mijinta sama da na kowa, ta ci albarkacina ba don halinta ba".

'Yar dariya Dr. Sarham ya yi, kamar Inna ta san tun ranar da ya ganta suna tadin soyayya ita da Jamilu yake jin haushinta, ya kuma fita sabgarta bakidaya, babu gaira babu dalili ya tsani ganin da yayi mata da Jamilu. Ko ta gaisheshi sai ya ga dama yake amsawa. 

Amma yau ji yake duk haushin nata da yake ji akan Jamilu ya kau. Sosai yake jin tausayinta don ya san rabuwa da Inna ga Hauwa ba wasa ba. 

Sallamar Sarham a dakinta ya sa ta wani irin saurin dagowa, kamar a firgice. Ta watsa masa manyan idanunta harrrr! Kamar tana ganinsa da suke jike jagab da hawaye.

Dr. Sarham ya tsaya 'standstill' daga bakin kofa hannayensa duka biyu zube cikin aljihunshi, as ango as he is, ko makiyinsa ya san ya yi kyau har ya gaji kamar ranar farkon aurensa, ya koma kamar yaro matashi dan 27 kai ba za ka taba cewa ya ajiye hamshakiyar mace kamar Dr. Madinah Sorondinki a gida, har da albarkar 'ya ba. Hauwa tana iya jin idanun Sarham na bin jinin jikinta, don haka ta kasa jure kallon hararar da ta sa gululun idanunta yi masa, ta sunkuyar da su kasa. Ta kuma lumshe su duk a lokaci guda.

Sarham ya tako cikin dakin ya zauna a kujera kwalli daya da ke dakin, karonsa na farko da shigowa dakin Hauwa, tun dawowarsu sabon gidan. Saidai ya dan leko daga kofar daki I zai wuce gida.

Cikin rishin kuka Hauwa ta ga ya dace ta gaida Dr. Sarham, ko da kasancewar mugun haushinsa ta ke ji yanzu, nayi mata katsalandan cikin rayuwa, amma Dr. Sarham na da muhallin gaisuwa daga gare ta (no matter what), wato cikin kowanne yanayi. Hauwa ta sa habar hijabinta ta share fuskarta, ta kuma bar fuskar a cikin tafukanta da hijabin nata ta ce (kamar wadda aka yiwa dole sai ta gaishe shin), “Masa'ul Noor”.

Sarham bai yi gaggawar amsawa ba, don ya raina ‘yar gaisuwar tata mai kama data rowa, ganin irin kukan da ta ke yi kuma, bayan furta gaisuwar ya san takura kanta tayi ta furta ta tamkar kuma ta kwace abarta ta mayar cikinta, ya yi kwafa cikin jin wani maqaqi a ransa na rashin son da ya lura Hauwa na yi masa, ya ce,

 "Shin wannan kukan na mene ne Maijidda? Tsakani da Allah auren da ni ne ba ki so ko? Na tabbata da wancan yaron dan polo ne yau Inna ta aura miki, da yanzu kin takarkare kina shafa hoda don tarar zuwansa matsayinsa na angonki. 

Amma da yake nine dube ki don Allah, a haka wai amarya ce mai shirin tafiya dakin miji, da wani zurmemen hijabi kamar mai zuwa fadar limamin jihar Kano".

Hauwa ta tale baki ba ta ce komai ba, ya ce, "To ya ishe ni kukan nan haka Malama, ki tashi ki yi sallah raka'a biyu ki roka mana duk wasu alkhairai na duniya da lahira da zaman lafiya, har da jikoki masu yawa da albarka ga Inna da Malam".

Ai Hauwa ba ta san sanda ta sake barkewa da sabon kuka ba. Ya dai tabbata ta zama matar likitan nata yau, ba mafarki ta ke yi ba, ba kuma dan uwanta Jamilu data ke so aka aura mata ba. Dr. Sarham ne.

Hauwa ta yi kukanta mai isarta ta goge ido, Sarham da ya lura ta gaji da kukan sai ya mika mata farin hankicinsa cikin tafin hannunta yana fadin.

 “Ki yi kuka ba zan hana ki ba, don dole ne a wurin mai uwa irin Inna yayi kuka, in aka ce ga ranar rabuwarsu ta zo. Amma ki sa a ranki ba hannun makiyanta ta kai ki ba, ko inda ake son ta da tozarta da wulakanta kamar yadda ke ki ka fi so (hannun su Zakari). 

Na san duk wannan kukan don ba shi ne mijin ba, ni da ba ki so din ni Allah ya baiwa HAUWA, sai inga mai kwace mini, don haka ga hankici na baki, ki yi kukan da zai jika shi jagab, ki gama ki fara shirya goya 'ya'ya na, ki haifa mun su da yawa kamar dozen su zama kannen Waheedah takwarar ki, kin ji ko Maijidda?”

Daga haka ya koma lallashinta, da kalamai masu taushi da alkawarin bai aureta don ya wulakantata ba, bai aureta don y araba ta da farin ciki ba, bai aureta don ya raba ta da iyayenta ba, lallashi dai irin na namiji mai wayo, ilmi, wayewa da dabarar a saurareshi, har ya samu Hauwa ta yi shiru da kukan. Ta ki karbar hancikin da yake bata, amma kuma ta gyada kai kan nafilar da ya umarce ta da yi, sannan ya yi mata sallama kan zai koma gida a shirya mata dakin da za ta zauna kafin a gama yi mata visar tafiya tare da shi da Sumayyah zuwa Jeddah.

Da ya kai bakin kofa sai ya juyo yace "ki cigaba da kwalliya, da shafa hodar dana taba gani kinayi a asibiti, tayi min kyau ranar, ina son gayu fa ni Maijidda dan gayu ne, matata ma ‘yar gayu ce sai kin shirya da zama 'yar gaye". Yayi murmushi cikin kallonta, ta saki baki da kunne tana jin sa, sannan ya fita da murmushin a fuskarsa. A ranta tace ba hodar da zan shafa, inna gumbuda tayi yawa ba lallai a gayamin ba. Karshenta ma sai dai yayi min dariya shi da Inna. Allah yasa matar tasa balarabiyace karewa kenan. Ji take da dai Jamilu ne da kuwa tayi duk abinda yake so ba hoda kadai ba. 

Tayi maza tayi istigfari akan wannan tunanin don ta san yanzu akwai igiyar aure a kanta.

*****            ******              ******

                  

MADINAH

Bayan Usman ya dauko ta. A kan hanyarsu ta zuwa gidan iyayenta daga filin jirgi kawai ta samu kanta da canza shawara. Ta ce a ranta macen kwarai ba ta yaji. Tsayawa ta ke ta fuskanci ‘challenges’ din gidanta dana mijinta ‘in general’ komai tsaurinsu in masu gyaruwa ne ta gyara. Zuciya mafi rinjaye na gaya mata Sarham wasa yake yi, domin ba zai taba iya hada ta da wata mace a zuciyarsa da duniyarsa ba.

Da wannan tunanin Dr. Madina ta canza shawara, ta ce da Usman ya wuce da ita gidanta ba gidansu ba. Tana gaya wa kanta wataqila akwai ta inda ta ragi Sarham tunda har ya fara yi mata wasan son karin aure.

 Abin da ya kamata ta yi shi ne ta tsaya ta binciki ta ina wannan gibin nata yake, ta yi gaggawar cike shi. Ta ga dai ko aiki bata yi duk don ta samu lokacin sa da kyau shi da diyarsu. Ba kuma za ta gane ta ina ta rage shi din ba idan ba ya bude baki ya gaya mata ba.

Ta sa a ranta za ta yi magana ta gemu da Sarham din idan ya dawo, ta ji ta ina take kuskure shi da har tunanin karin aure ya yi crossing mind dinsa, dole ruwa ba ya tsami banza.

Da wannan Madinah ta baiwa kanta nutsuwa ta shiga gidanta ta bude ta soma gyare-gyare, bayan sun yi sallama da Yayanta Usman da cewa ya gayawa Hajjah Ramlah sai wajen gobe za ta shigo gidansu. Ta kawo sakonnin Hajjah Ramlah da ta taho da su daga Kano ta ba shi.

Amma me? Bayan ta manta da komai ta ci gaba da harkokinta cikin gidanta tana share-share da goge-goge, tana kuma kula da Waheedah, sai ga wayar kanwar Sarham wato Surayyah ta shigo mata.

Madinah ta amsa wayar Surayyah tana tsokanarta da amaryar Engnr. ta Aliyu ba da kanki a sare".

Tun daga nan Surayyah ta fahimci Madina ba ta san me ake ciki ba, don muryarta ras! Babu alamun damuwa a cikinta. Surayyah ta ce, cikin damuwa.

"Aunty Madinah kina ina?"

Madina ta amsa, "Na koma Jeddah Surayyah".

Surayyah ta ce, "Ga dukkan alamu ba ki san me ke faruwa da ke ba, kuma ni ba zan iya shiru ba, duk da an ce babu ruwana.

Ta nisa. "Aunty Madina ba zan taba manta tarin alkhairinki gare ni ba, har ma da wannan butulalliyar Allahn Sumayyah, hakika kin mana alkhairi mai yawa don haka ni ba zan ga inda za’a cuce ki in yi shiru ba.

Gaban Madina ya yi mugun faduwa, amma haka ta daure ta ci gaba da sauraron Surayyah ba ta katse mata hanzari ba, duk da a tsarinta ba a kawo mata gulma, kamar yadda ba ta zama ta yi gulmar wani ita ma, amma yau ta kasa tsayar da Surayyah sabida curiosity da ya ziyarceta irin na dan Adam.

"Yaya Doctor ya yi aure!".

Wadannan kalamai sune 'shock of her life' duk da cewa ta yi anticipating dinsu ko makamantansu, bayan zuciyarta ta gama karyata su daga bakin da ta tabbatar bai taba yi mata karya ba wato (bakin Sarham din da kansa).

Surayyah na jin irin numfashin da Madinah ke yi, sai taji tsoro, amma haka ta ci gaba da cewa, "Aunty Madinah, I am sorry to say, kuma yar talakawa fa ya dauko miki irin ‘yan cikin Badalar nan ‘yan tallan abinci, makauniya, almajira, basu da cin yau basu da na gobe sai abinda ya dauko ya basu, don talauci ubansu ya gudu ya barsu shekaru bakwai. Suka koma sayar da abinci a Tasha. Ko gidan zama ba su dashi, shi yake ciyar da su tun da jimawa.......". maganganu dai na gulma rututu

wadanda Madinah ba ta iya ta karasa ji ba ta saki wayarta a kasa ta rabe gida biyu.

Surayyah a can bangarenta ta ce, "Allah ya bi miki hakkinki Aunty Madinah, karshen wulakanci da kaskanci Yaya Doctor ya gama yi miki".

Mama ta gama shirin karbar amarya a dakin Sumayyah inda Madinah ma a nan aka karbe ta, don Malam Bilyaminu ya ce, ko kare kada a gayyato masa don biki, ya aurar da Hauwa ne ba don ya gaya wa duniya ba, sai don cika umarnin ubangiji na in 'ya'yanku sun kai munzali ku aurar da su.

Ya kuma gaya wa Abba Prof. duk wani abu na kayan daki da ake yi wa ya mace a bashi muhalli, zai yi wa Hauwa. Sai Abba ya ce, Sarham bai gama ginin gidansa na Kano ba har yau, za ta zauna tare da su ne kafin wucewarsu Jeddah. Sai dai ya bari sai can gaba, wato ranar da suka dawo kasar Kano da zama gaba daya sai ya saka mata kayan dakin. 

Amma hakika wannan abu da Malam Bilyaminu ya fada na sayawa Hauwa kayan aure ya kara sayawa Hauwa mutunci a idon Abban da Mama, shi abu daya ke bata masa rai, in ya tuna Hauwa da uwarta sun sayar da abinci a tasha. Wannan kalma ta ‘yar tasha ya kasa daina ganin su Hauwa da ita. A cewar Sarham hakan yana cikin kaddarar su, sannan ba kowa da ya zauna ko yake sana'a a Tasha bane mutumin banza. Duk da haka dawowar Malam Bilyaminu a daidai wannan lokacin ya yi wa aibunsu wanka da soso da sabulu a idanun Farfesan.

Mama ta shirya masu zuwa taho da Hauwa kanwarta dake aure a Kaduna da kanwar Prof. Daga Shanono, amma Malam Bilyaminu ya ce don Allah su koma, Sarham ya zo ya tafi da matarsa da kansa shi wannan ne policy dinsa. Ba ya son kowacce irin bidi'a a auren Hauwa-Kulu albarka kawai yake nema mata.

 Bai ki ba bayan kai ta gidan in sun so su yi walima kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya koyar.

Daren yau ne ya kama Sarham zai tafi dauko Hauwa, tun safe yake gwada wayar Madinah ta ki shiga. Yana so ne yaji lafiyarta ya kuma gaya mata komai ya tabbata kafin Hauwa ta tare, ya kuma tabbatar yayi mata lallashin da za ta fahimce shi a kan aurensa da Hauwa. (Bai san tuni Surayyah ta kwaba masa aiki ba).

Duk da haka Madina ba ta bar gidanta ba, saboda a wurin ta karshen tozarta aure shi ne "yaji". A wurinta yaji ga macen aure wadda ta san abin da ta ke yi zubewar aji da zubewar kima ne. 

Ita kuma Madina duk abin da zai zubar mata da aji da kima da martaba tana gudunsa a sittin, exactly yadda ta ke kallon auren da Sarham ya yi yanzu da makauniya ‘yar tasha, ‘yar talakawa ya zubar mata da aji, ya zubar mata da kima ya kaskantata ya wulakantata a idon tsararrakinta da duniya bakidaya.

A duniyar Subhana ta san tana son Dr. Sarham Abbas, tana kuma da wani irin kishi mai radadi a kansa, wanda hankali da tunani ba zai dauka ba, amma yau ji ta ke SON bakidayansa yana narkewa, yana zagwanyewa yana dalala kamar narkakkiyar dalma a kasa yana bin rariya.

Sai dai abu daya da ba zata yarda ta taba yi ba a rayuwar aurenta shi ne, "YAJI". Za ta jure ta zauna har Sarham ya dawo, in ya so in ta tabbatar da abin da Surayyah ta labarta mata a kan matar da ya aura daga bakinsa, to fa zamanta da Sarham ya kare. Ita ba ta saurin yanke hukunci a kan abin da ba ta da hujja kuma bata tabbatar ba. Wato dai bata yanke hukuncin one sided (daga bangare daya). 

Wane irin makauniya irin yaran cikin BADALAR Kano da ke sayar da abinci a Tasha ana zaune kalau, miskiniya ce kenan ko Musaka? Duk ba wannan ba Makauniya fa? Shi kuma daga likitancin ido sai ya bige da auren makauniya, ‘yar talakawa? Shi kuwa Sarham me yake nema a rayuwarsa wannan faduwa kasa har yaushe??

 Madinah ji take kamar ta dora hannu aka tayi ta kururuwa ita kadai. Sau tari tana jin ana fadin. Wani namijin in ya tashi karo aure in kayi duba da irin matar da yake da ita a gida, sai ka dauka hau ce ta hau kansa.

Madina ta yarda da Sarham matukar yarda, ta amince da shi da soyayyarsa iyakar amincewa, don haka wannan auren nasa da aka kara maimaita mata ya zama 'shock of her life' kuma in har Sarham ya tabbatar mata da hakan da bakinsa, to fa ta taho daga rakiyar duk wani Da namiji, ba Sarham kadai ba.

Maganar tafiya daga gidansa alhalin bai sake ta ba, ba shi ne solution ba, gara ta zauna su fuskanci juna idan ya dawo, don ta san matsayinta. Ta kuma tambayeshi hakikanin menene flaws dinta data cancanci wannan tozarcin.

 Yanzu kam bayan ta ji irin matar da ya aura din, sai ta ki yarda wai gazawarta ta wani bangare ne ya sa Sarham yin wannan auren, za ta fi yarda in ya ce kawai ya daina sonta ne (short and simple).

Amma shin anya soyayya irin tasu wadda aka yi shekaru goma cur ana fafutukarta ta kuma samu actualizing ba jimawa don ko shekaru biyu ba su rufa da aure ba, za ta iya karewa a farau-farau din banza irin haka cikin dan lokaci???

Yanzu dai ta yarda ba gazawarta ba ce, ba kuma aibinta bane ko wani gap data bari, duba da irin matar da aka ce ya auro din.

Madinah a wannan gabar, ta kasa jure wani irin bakin ciki da ke cin ranta, tun farkon maganar bata ji kuka yazo mata ba sai yau, ta kifa fuska cikin tafukanta ta soma rera kuka na sarewa a kan mijin nata, dama duk wani da namiji mai numfashi, tana yi tana karyata soyayyar maza ko wacce iri ce, a yau Madina ta la'anci duk wata yarda da soyayyar da ta yi wa Sarham tsayin shekaru goma sha daya a baya.

        ****         ****     ****

Maimakon irin shigar da angwaye ke yi ta manyan kaya ranar tarewar amarensu, abokai kuma su rako su dakin amarya. Dr. Sarham nasa salon daban ne, don wata farar T. Shirt ya saka samfurin 'Burberry' da bakin wandon 'Givenchy Jeans' mai kauri matuka, ya kuma taje sumar kansa sosai ya shafe ta da man da yake amfani da shi na musamman (Argan Oil for men), kowa ya san a dabi’arsa dama bai cika yin askin sumar kan shi ba sai tara suma da kykkyawan sajen (man’s pride) da baya gajiya da kula dasu. Sai kamshin turarensa na (Oud Abyad) da ‘Sandalia' na musamman yakeyi.

Dakin Mama ya fara zuwa ya same su ita da Sumayyah suna shirye-shiryensu su ma, ya ce, "Mama zan je in zo da ita yanzu, ina fatan Sumayyah ta gama gyaran dakin?"

Mama Mai Shari'a ta daga kai ta dubeshi, sai ta ga Baban na Waheedah ya koma mata yaro sabon jini, kuruciyar sa ta karu, kamar yanzu ne aka daura masa auren fari, wani boyayyen annuri ya fito sarari ya kayatar da idanun sa.

 Da karsashi Sumayyah ta amsa,

"Komai fa ya kammala Bhaiya, har abincin da za ku ci na dare na kammala, na gasa maka kazar amarci da wani irin ‘french grill’ mai ruwa-ruwa dana koya online, sai jiran isowar kanwata, amarya, Hawwa-Jiddan Bhaiya, Yaya Sarham mai Jidda mai Madinah, bari in je in turare dakin da turaren 'hawii' yanzun nan”.

Murmushi kawai Sarham ya yi yana mamakin Sumayyah, in ya tuna tsiyar da ta shuka masa lokacin auren Madinah.

Mama ta ce, "Ai Sumayyah ko ita aka auro wa Hauwa sai haka, yau ko na minta daya ba ta zauna ta huta ba, duk abin da ta san Hauwa'u za ta bukata ta nemo ta ajiye mata a dakin nan har brush da maclean ba ta manta ba.

Sarham ya fadada murmushin sa zuwa dariya, ya ce, "Summy, mai abun mamaki, wanda ranta yake so ya ji dadinsa!".

Duk zancen nan da suke yi Surayyah da ke toilet din Mama tana jinsu, waya ta ke da Madinah a bandakin tana gaya mata cikin takaici mai yawa "Anti Madinah yanzu Yaya Doctor zai je ya dauko makauniyar nan fa, anya kin dauki matakin da ya dace? Ga ‘yar banzar yarinyar nan Sumayyah sai rawar kafa ta ke kamar ta fi shi son auren ma".

Madina ta kasa shiru wannan karon sabida a rayuwarta ta tsani gulma da daukar zance, ta kuma fahimci Surayyah halinta kenan, ta ce, "Surayyah please, in kin sake kirana mu yi magana wadda ta shafe mu, kada ki kara yi min zancen auren Sarham ko na yarinyar da ya aura, I may be intolerant, besides, is none of my business, in ba so kike kuma in samu ‘heart attack’ ba. 

Ni wannan ba taimako na kike yi ba cutar da ni kikeyi a zuciyata da kwakwalwa ta".

Daga yadda ta ke maganar muryarta na daukewa sama-sama kamar mai fama da ciwon asthma, sai da Surayyah ta ji tsoro. Madina ta kashe wayarta daga nata bangaren, ta koma ta jingina da fuskar gadonta, ta lumshe ido tana ambaton sunan Ubangiji da neman daukinsa, na sanyayawa da tausasawa a gareta cewa ta ke a fili, idanu a rufe, hannu dafe da kirji; 

           "Ya Salamu-Sallim".


****             ****              ****

A nan layin shiga gidan Malam Bilyaminu ango Sarham ya kashe motarsa, ya dan zauna a ciki kadan na wasu mintuna dafe da sitiyari yana karanto addu'a a zuciyar sa, addu'ar Allah ya sa aurensa da Hauwa shi ne alkhairin da kullum yake nema a wajen Ubangijin sa da neman zabinSa da yayi ta yi kafin ya furta amincewa da yin sa. Ya kuma bashi ikon yi mata adalci tsakanin ta da matarsa.

Ya fito ya shiga gidan da kyakkyawar sallama a bakinsa da murya mai karsashi, Malam ne ya amsa daga dakinsa, ya kuma fito suka hade su duka a falon Inna. 

A lokacin Inna tana can dakin Hauwa tana tsaye a kanta tana fama da ita a kan shiryawa da sabuwar atamfar da ta dinka mata, dinkin doguwar riga akayi mata daidai jikinta. Hauwa ta kasa tsaida hawayenta haka ita ma Inna amma duk da haka bata fasa karfafa kanta tana lallashinta ba, lallashi irin wanda ba ta taba yi mata ba. Babbar damuwar Hauwa ita ce, jin cewa nan da kwanaki uku Babanta da Innarta za su koma kasar Ghana su barta a Kano hannun mijinta, wannan abu shi ya fi komai daga hankalin Hauwa fiyeda auren da ake ikirarin an yi mata da likita Sarham.

Malam ya leko dakin Hauwa yana fadin, "Har yanzu ba a gama shiryawar ba ne? Ko bankwanan bai kare ba tsakanin Hauwa da Innar ta? Naga dai jiya baku rintsa ba kuna hirar bankwana. Har gashi angon ya iso, tun dazu yana jiranku".

A lokacin Inna ta yi wa Hauwa lullubi da sabon mayafin da ya shiga da atamfarta ta fesa mata turaren Binta Sudan, ta kamo hannunta suka fito falon. Inna da kanta ta saka hannun Hauwa cikin na Sarham tana faman kokawa da hawayenta.

Addu'a ta musamman Malam Bilyaminu ya karanto duk suka shafa, ya baiwa Sarham amanar Hauwa kamar yadda ya baiwa Abba Prof, Inna kuma da aka zo jin ta bakinta cewa ta yi ita ta san in dai Sarham ne ba sai ta jaddada masa amanar Hauwa ba, ita Hauwan ta ke baiwa amanar danta (SARHAM), don ta santa wani lokacin hutsuwa ce, musamman (in ka nemi raina mata wayo), tace ta yi masa biyayya fiye da wacce take yi musu don yanzu aljannarta ta tashi daga yardarsu su iyayenta ta koma kasan dugadugansa.

Kan Sarham a kasa, hannun Hauwa cikin nasa, ya rike hannun sosai da riko mai karfi, suka fito daga falon Inna, Malam da Inna suka raka su har bakin motarshi ya budewa Hauwa ta shiga gidan gaba, ya maida kofar ya rufe, shima ya zaga ya shiga mazauninsa ya tada motar a hankali suka bar BADALAR KOFAR NA'ISA.

 Hauwa na jin 'feeling' na rabuwa da mahaifarta, inda ta rayu shekarun rayuwarta gabadaya, ba’a jikinta kadai take jin kewar BADALA ba, har a cikin zuciya da ruhinta take jin kewar.

****              ****           ****

Suna tafe a hanya jin kukan na Hauwa ya ki karewa Kuma yana taba masa zuciya ba kadan ba. Dr. Sarham sai ya samu gefen titi ya tsaya ya kashe motar, ya kuma yi sama da glassan motar wadanda dama tinted glasses ne.

Hauwa jin ya tsaya tsayin lokaci ya kashe mota kuma ko tari bai yi ba, bayan kashe motar da yayi, sai ta rage sautin kukan nata, har daga karshe ta yi shiru gaba daya tana ajiyar zuciya.

Sarham yayi kyacci, ya ce, "Maijiddah kin san me? Wannan kukan da ki ke ta yi mun yau, da wanda aka ce kin kwana yi, yafi min kama da irin kukan nan na an miki auren dole. 

Ni na tabbata da Dan Polonki aka aura miki ya daukoki zai kaiki gidan Baba Zakari, ba za ki yi ta yin wannan banzan kukan ba. 

A'ah, inada yaqinin farinciki zakiyi tayi na kin auri wanda kikeso yake son ki, wanda har masoyanki sai sun taya ki wannan farin cikin. Sai gashi ni din da ba ki so kuma kike kullace dani sabida wani dalili naki na rashin Tawhidi ni Allah Ubangiji ya ga damar baiwa.

Don haka ki ci gaba da kuka son ranki Maijidda, ina taya ki bakin cikin auren tsoho, mai mata, har da 'ya, ba yaro dan Polo sabon jini ba".

Hauwa ta dauke numfashi, ta daina hadiyar zuciyan da take yi don tana iya karantar irin (bitterness) din da ke cikin muryarsa akan Jamilu da halin da ya shiga a sanadin kukan nata a sautin cool muryarsa. Me ya sa yake son yi mata wannan fassarar da wannan habaicin ne kullum a kan Yaya Jamilu? A ganinta koma dai yaya ne, zancen ta da Jamilu ne koma waye) ya wuce, tunda an riga an daura musu aure itada shi, ai zance ya zama past, tana so ko ba ta so, sunanta matar Sarham yanzu, bai kamata ya yi ta yi mata gori, yarfe da mita a kan Jamilu ba.

"Ka yi hakuri". Kawai ta iya cewa cikin dusassar muryar data gaji da kuka.

Ganin kamar ban hakurin nata bai gamsar ba, domin har zuwa lokacin bai ja motar sun cigaba da tafiya ba, ta cigaba da sauke ajiyar zuciya sannan ta dora da.

"kayi hakuri don Allah. Na daina kukan Yaya Sarham, kuma ba don shi nake yin kuka ba, a'a, don kewar Malam da Inna ne.

 Kada ka manta fa kasar zasu bari gabadaya babu ni".

Ta fada cikin rauni, da jin kamar cewa ta zama ita kadai kwal ta rage a fadin duniya tunda babu Inna jagorarta, wadda itace garkuwarta, karfinta, sannan kwarin gwiwarta a kan komai tun bayan da ta rasa idanunta.

 Sannan babu Baba a tare da ita yanzu, wanda shima ta kwashe shekaru ba tareda shi ba, bata mori komai na dawowarsa ba an yi mata aure, wannan tunanin ya sa wani sabon kukan ya dawo mata ta soma kokawa da shi ta hanyar toshe bakinta kada ta kara laifi wa Sarham.

Sarham ya rasa inda zai sa ransa, sabida kuka irin wannan musamman na mace na kassara shi ba dan kadan ba, koda kuwa ace baida alaqar komai da ita, da hannunsa biyu ya bugi sitiyari sannan ya kifa kansa akan sityarin, yana sauraron yadda Hauwa ke rera kukanta wanda ya zarta na rabuwa da iyaye yanzu kuma, ya koma na tunanin yadda rayuwa zata kasance mata a gidan surukai da kishiya in general, alhalin bata da idon ganin su, kuka take tukuru, mai fita tun daga kasan ruhinta.

A baya ya saka a ransa Hauwa ba abun tausayi ba ce, Hauwa za ta iya yi wa kanta  jagora a duk inda ta samu kanta saboda karfin halinta da ki-fadinta, ya san ita ko lalube irin na makafi da son a taimaka a kamata a yi mata jagora ba ta cika yi ba, saboda zuciyarta dakakkiya ce, tsayayya kwarai, ya san Hauwa na da taurin zuciya mai sawa ta ji cewa za ta iya komai da mai lafiyar ido zai iya, amma wannan kukan da ta ke yi a yau, da iyayenta suka damka ta hannun sa bisa igiyar aure ya karyata duk wata jarumtakar ta, da duk abinda ta yarda da shi akan karan kanta. Ta koma ganin bazata iya komai ba yanzu tunda babu Inna. A yau ta yarda duk wani mai nakasa yanada rauni, da dole wani lokacin sai ya bukaci kusanci da tallafin wani nasa. 

Ya yarda Hauwa abun tausayi ce yanzu, tana bukatar tausayinsa, kaunarsa da adalcinsa, da kauna daga iyayen sa da dukkan ahalinsa da sadaukarwar su suma, hakan ne kadai zai karfafeta daga karayar data yi a halin yanzu. 

Ya lura ta gama karaya da nakasarta yanzun, ta gama sarewa da rashin Inna a tare da ita. Ta gama sarewa da cewa ada tana da confidence. (tabbas aure yakin mata).

Dr. Sarham ya ja motarsa a hankali, suka ci gaba da tafiya sannu sannu, yana mai kokawa da zuciyarsa da ke cewa, dole ya koyawa kansa soyayyar HAUWA. Tunda aure ya riga ya gitta kuma babu jin qai a cikinsa idan babu soyayya ko yaya take, zai kuma tsaya wa rayuwarta daga yau kamar, koma fiye da da yadda Inna ta ke kula da ita, zai kula da ita ya tsare mata mutunci da martabarta wadanda sune makasudin dalilan da suka sa ya aure ta. Abun da zai mayar da hankali akai yanzu shine koyawa zuciyarsa soyayyar wata macen bayan Madinah a inda hakan ya zama dole.

A kofar flat din gidan su Sumayyah suka tarar tsaye tana jiran isowarsu. Daga isowarsu bakin Sumayyah ya gaza rufuwa, ta karasa ta bude barin Hauwa, sannan ta kama hannunta ta fito daga motar fuskarta rufe ruf cikin mayafinta.

Har dakin Mama Sumayyah ta isa da Hauwa, Mama Mai Shari'a ta daga ido a hankali tana kallon Hauwa-Kulun, Kuluwa, AKA Maijidda (ta bakinsa), HAUWA'U kuma Hauwa-Jidda tana shigowa dakinta, da tafiyarta cikin nutsuwa da tsentseni, duk da ta rufe fuska da mayafi za ka gane akwai nutsuwa mai yawa a tattare da ita.

Har gefen gadon Mama Sumayyah ta kai ta, Mama ta yi murmushi ta ce, "Barka da zuwa cikinmu Hauwa'u, cikin iyalin Abbas Shanono, nan gidanku ne, don haka bude fuskarki ki daina kukan haka. Ajiye mayafin ki sha iska kin ji? Mu duka nan yan uwanki ne da iyayenki daga yau.

Ga abincin barka da zuwa kannenki sun shirya miki, sauko bisa ledar cin abinci mu ci abinci tare har Sarham din kin ji? We are family, insha Allahu ba za ki yi nadamar shigowa cikinmu ba".

Hauwa sosai ta ji dadin maganganun Maman Sarham, taji duk rabin damuwarta ta yaye nan take, a lokacin Sarham din ma ya shigo dakin ya zauna a kujerar da ke fuskantar gadon Maman, Sumayyah ta sauke mata lullubin sai Mama ta samu damar ganin kyakkyawar fuskar Hauwa sosai. Da manyan fararen idanunta masu kama da an diga musu zaiba ma'abota kayatar da idanun duk mai kallonta.

Mama ta yi tazbihi cikin ranta, ta kuma tabbatar bayan son taimako, shakuwa da son yin jihadi ga rayuwar HAUWA KULU, danta Sarham zai iya auren Hauwa (on the ground) na so da kauna, domin ta isa mace ga kowanne namijin da ba kyale-kyale yake so a macen aurensa ba.

Sumayyah ta zaunar da Hauwa kusa da Mama a kan ledar cin abincin. Ita kuma ta zauna gefen Sarham. Sannan ta zauna tayi serving kowannensu, Surayyah cewa ta yi cikinta na ciwo, don haka za ta je ta sha magani ta kwanta, ba ta jin yunwa.

Kwarai kyawun Hauwa ne da kamalarta har ma da kwarjininta ya razanata, duk da kasancewar ta 'yar talakawa din bata zaci ko kusa ilhamarta ya kai haka ba, hakika Surayya ta razana da ganin Hauwa don haka ta ki zaman dakin Mama ta kuma kasa cin abincin taredasu, duk da yunwar take ji ta yi karyar ciwon cikin, gulma na cinta kamar me. Tana so kwarai ta kira Madinah a wannan lokacin ta labarta mata yadda taga Hauwa da yadda Mama ke rawar jiki da ita sannan ta gargadeta kan ta sake lale, tayi babbar dammara in har tana son korar HAUWA sai ta yi da gaske ba kamar yadda ta bata labara kafin ta ganta ra’aayal aini ba, sai ta mike akan Sarham da Mama, kada wankin hula ya kaita dare, domin gabadaya yadda suka zaci abubuwan da Hauwar kanta a kalar 'yan tallen cikin gari ba haka take ba, a nitsenta take, ta tuna gargadin da Madinah ta yi mata na cewa, kada ta kara yi mata zancen Sarham, ko na matar da Sarham ya aura. In ba so take ta samu (heart attack) ba.

Da kyar Mama da Sumayyah suka lallaba Hauwa ta ci abincin da suka shirya dominta, amma kadan ta iya ta ci, sannan Mama ta kai ta dakin Sumayyah har bisa gadon da yaji shimfidar sabon zanin gado da sabon quilt, inda a can suka shirya mata sauka.

Ta barta tare da Sumayyah, ita kuma ta hada mata ruwa mai zafi a toilet ta ce ta shiga ta yi wanka ta ji dadin yin barci, ta kamata ta kai ta har bandakin ta nuna mata duk abin da za ta yi amfani da shi har saida ta gane kan komai na bandakin, sannan ta fito.

Sau biyu Sarham yana lekawa dakin don yayiwa Hauwa sallama zai je ya kwanta, Sumayyah na cewa ba ta fito daga wanka ba. Ita kuma Hauwa sulbi da taushin kumfar da kuma kamshin 'bath gel' na 'Fà' da kamshin turaren wankan da Sumayyah ta zuba mata a cikin ruwan wankan su suka sa ta kasa daina wankan, yi take tana sakewa jikinta na santsi don ba ta taba jin kamshi mai dadi irin su ba. da sabulun da ke dirje fata ta fita sumul kamar wannan ba. Su turarensu ita da Inna daga Dan Duala ne sai Binta Sudan. Sabulunsu kuma dan yanka ne wanda har wanki da shi suke yi, shi ya sa ta dauki lokaci tana saba jikin tana karawa, tana jin kamar bata taba yin wanka a duniya ba sai yau.

Ta kwashi wajen mintuna sittin kafin ta gamsu cewa fatar jikinta ta fita sumul, ta lalubi tawul faffada wanda Sumayyah ta aje mata ta ce shi za ta daura a jikinta in ta gama wankan, ta kuma rufa karaminsa a kanta ta tsane kai dashi ta fito. 

Sumayyah na jin motsin fitowarta ta mike ta kamo hannunta zuwa stool ta taya ta goge ruwan jikinta da karamin tawul din. 

Gashi daman Maman Salele ta rangada mata sabon kitso kanana da ake kira (weeving) a gashinta baki mai cika, na asalin Hausawa-Kanawa. 

Sumayyah na taba jelunan kitson da sha'awa tana ce da Hauwa.

"Hauwa Jidda kina da kai mai cika, haka kuma mai karfi, wanda baya breaking, amma kamar ba ki taba saka masa 'relaxer' ba".

Hauwa ta ce, "Umh, can baya ina yarinta na taba karambanin saka masa danjangabu da sunan zanyi shamfo gaba daya gashin ya sauka kasa, tun daga lokacin ban kara gwadawa ba, don kaina tal kwabo ya koma Aunty Sumayyah".

Sumayyah ta dinga dariya, wait tal kwabo, ta ce, "Danjangwabo ai 'traditional relaxer' ne, wa ya aike ki?

 Insha Allahu da mun sauka a Jiddah zan kai ki saloon din dana ke zuwa a yi miki na amarci wanda zai burge Bhaiyana".

Hauwa ta rufe ido tana jin kunya. Sumayyah tace "ah toh! Don in gaya miki gaskiya Bhaiya Dan kwalisa ne na gani kasheni, kuma yana so ‘yar kwalisar matar shi".

Sumayyah ta dauke mata damuwa da hirarrakinta masu ban dariya, duk na Sarham da irin gayunsa, nan da nan ta rage mata kewar Inna.

Sabuwar rigar barci fara kal, tsayinta iya kauri Sumayyah ta dauko ta bata ta saka, ta bata lotion mai kyau na neutrogena tana shafawa tana mata hira.

Sosai Hauwa ta sake da Sumayyah, ta jita (at home) don Summy ta maida kanta sa’ar Hauwa, duk da cewa ta girme ta da shekaru uku kwarara.

Mama da Abba na babban falo, Abba Prof. na cin abinci, Sarham na gefensa suna hira shi ya sa ya kasa tsallake su ya je don ya ga yaya Hauwa ta ke coping a gidansu, ya san dai zuwa yanzu ta fito daga wankan. Sumayyah kuma bazata barta ta nemi komai ta rasa ba. 

Sarham duk da kasancewarsa dan bokon zamani hakan bai cire masa dattaku da halin kawaici akan mata irin na manya ba. Bokonsa bai cire masa wasu daga halayen kawaici irin na mazan da a gaban iyayensu ba, duk kuwa da kasancewar iyayen nasa yan zamani ne kuma 'yan boko suma. Banbancin tashin yaro a kasar musulunci irin Saudiyya da kasashen turawa kenan 

Abba ke tambayarsa ko yaushe 'annual leave' din nasa zai kare? Kuma yaya ya tsara zaman iyalin nasa? Kafin Sarham ya shirya amsar bashi kuma yace.

In zaka bi shawarata, to Hauwa ka barta tare damu a nan, ta fara karatun degree a nan BUK tunda tana da WSSCE certificate, Jamb kawai zata zana a samar mata gurbi a duk tsangayar da take so”.

Abba Prof. ya kara da cewa, “bana so ta je Jeddah mata biyu su hada maka zafi, a matsayinka na likita mai bukatar nutsuwa wajen gudanar da ayyukan sa, Hauwa na bukatar (special care) in kun tafi kullum kana asibiti, matarka na jego, wa zai kula da ita? Tunda Sumayyah a makaranta ta ke zaune ba'a gidanku ba, don haka in har shawarata kake nema, to Hauwa'u ta zauna tare da mu a gidannan, Mamanku ta kula da ita, ni kuma in sa ta cikin jami'a zuwa gaba kadan mu ga me Allah zai tsara muku. For the mean time".

Sarham kansa na duke a kasa ya kasa dagowa balle Abba ya ga irin yanayinsa, da irin karbar da yayiwa shawarar sa. A da kam ya so ne ya tafi da Hauwa. Amma shawarar Abba Prof. ma abar dubawa ce, bai auri Hauwa don yayi rayuwa ta soyayya da ita ba, ko don biyan bukatar ransa, ko don ya yi auratayya da ita nan kusa, har gobe kallon kanwa yake yi wa Maijidda kanwar ma ta jini abar kulawa a gareshi, cikin dalilan da suka sa ya aureta harda dalilin zamowarsa sanadin nakasar idonta, da har gobe ya kasa yafewa kansa da kuma sauran dalilai masu tarin yawa, da bazau lissafu ba, ciki har da kaunar sa ta hakika ga Inna, da kuma alkawarin da yayiwa kansa na gina rayuwarta positively da tallafar ilminta koda idonta bai gyaru har abada ba.

Da kyakkyawan burinsa na ganin cewa ta zama wani abun amfani ga alumma, kuma abin alfahari ga iyayenta da duniyar masu nakasa. He wants to become HER PACESETTER in life! In haka ne kenan shawarar Abbansa tana kan hanya, kuma ita ta fi dacewa da Hauwa. 

Bai auri Hauwa don sha'awa ko soyayyarbukatar gangar jiki ba irin wadda za’a kasa controlling ba, ya auri Hauwa ne don ya tallafi rayuwarta ya zame mata, ya ginata ta kowanne bangare ya kuma nema mata lafiya.

Da wannan tunanin Dr. Sarham ya amince da shawarar Abbansa na zai tafi Jiddah ya bar Hauwa tare dasu, ya dago a hankali ya ce, "Abba na amince da shawararka. Hauwa ta zauna karkashin kulawar ku, na tabbata sai tafi samu kulawa har fiye da a hannunmu".

Abba ya ce, “To masha Allah lelan Abba, haka nake so ka dinga fahimtata a komai, yanzu sai a samar mata karamar yarinya daga Shanono cikin yaran family dinmu, wadda za ta zama mai aikinta ita kadai ta kuma dinga raka ta cikin makaranta kullum, ko’ina ya zama suna tare, ko ni in zan fita in fita da su in kai su department dinsu. 

In yaso sai su dinga dawowa da kansu in ta gama lectures su dawo gida tare da mai aikin nata. Zan yi wa Babanku na Shanono magana ya bamu aron 'yar sa Mardiya tunda ba su kai ga yi mata aure ba.

 Yarinyar nan Mardiyya na lura tana da hankali sosai ga nutsuwa.

Har suka gama hira shi da Abba Sarham bai tsallake su ya je dakin Sumayyah gun Hauwa ba. Har sai da Abba ya tashi ya shiga turakar barcinsa, bayan ya gaya masa sati mai zuwa zai koma Jeddah, hutun nasa next week zai kare, kuma zai sayo mata (JAMB form) ya cike mata komai kafin ya koma in sha Allahu, don a lokacin Mama ta ke gaya musu an fara sayar da jamb form na wannan shekarar.

Bayan wucewar Abba bedroom dinsa ya rage daga shi sai Mama suka ci gaba da hira. Mama ta ce,

 "Yanzu da gaske iyayen nata jibi za su koma Ghana? Su kuwa me yayi zafi hana da bazasuyi hakuri su zauna a mahaifar su ba?"

Ya ce, "Eh Mama, ni ma abun yana tayar min da hankali sosai don wallahi na saba da Innar Hauwa yadda ba kya zato. Saidai ko ke kika ji cikakken labarin Malam Bilyaminu da dan uwansa Zakari, zaki bi bayan hukuncinsa na yin nisa dashi shine mafi alkhairi gareshi da iyalinsa, ga dukkan alamu arzikin sa yana can".

Ya ba ta labarin irin yadda Inna ke sonshi da kula da cikinsa da abincinta mai dadi da tsafta, da yadda ta ke yawan yi musu addu'a su iyayensa ba dare ba rana. Da halin da Zakari ya janyo musu na shan wahala da sayar da abinci a tasha, sakamakon rushe gidansu da yayi, ya ce, “Mama, in na tuna hakan sai in ga hukuncin da Malam Bilyaminu ya yanke na barin Kano ya fi masa alkhairi fiye da ci gaba da zama da irin wadannan ‘yan uwan, kuma a haka dan sa na cikinsa ya dage ya kafa kahon zuka sai sun aura masa Hauwa. 

Wallahi Mama ban yi niyyar auren Hauwa ba Allah ya sani, wadannan dalilan da wasu masu yawa suka sa na yanke shawarar auren nata kawai, don Jamilu da gaske yake auren Hauwa zai yi ko ta halin kaka, ya manta da ko waye ubansa garesu".

Mama ta jinjina kai, abun ya tsuma ta, a karshe kuma ta yi ‘yar dariya ta ce, 

"kenan Jamilu ya tado tsohuwar boyayyar soyayya daga barci, kishi ya sa an yi gaggawar yin abin da ya dace".

Sarham ya yi wani basakkwacen murmushi, ya yamutsa fuska ya ce, 

"Mama ni fa, ni fa in zan gaya miki ki yarda ba son Hauwa nake ba, I mean so na soyayyah, Mama ni Hauwa kanwa nake kallonta har gobe, kwatankwacin yadda nake kallon Sumayyah cikin idona".

Mama ta tsuke fuska sannan ta mike tsaye don tatsuniyar tasa ta fara isar ta, ita bazata taba yarda wai namiji zai iya kashe kudinsa da lokacinsa ya auri macen da baya so ba, ta ce,

 "ka je ka gayawa wani maho din wannan tatsuniyar kanzon kuregen naka, ba ni mai shari’ah Maimunatu ba".

"Mama ki yarda da ni, ban taba yi ma wata mace kallon so bayan Madinah ba, ba don so kadai maza irina ke aure ba Mama. Dalilai da yawa sun fi komai saka maza kashi 90% yin aure ba soyayya ba, wallahi Mama dalilai ne suka rinjayi zuciyata na yi wannan auren amma ba so ba".

Mama ta ji wani irin babu dadi a ranta, kamar ita ce ta haifi Hauwa, mijin da ya auri Hauwan ya tareta yana gaya mata haka, ta kuma ji matsanancin tausayin Hauwa ya kama ta kan abinda Sarham ke fada a kanta.

  Tun daga wannan lokacin Mama Mai Shari'a ta kudiri aniyar zata taimaki Hauwa-Kulu, za ta zame mata UWA kamar Inna, amma ba uwar miji ba, zata zame mata Uwa, kamar yadda Innarta ta zamewa Sarham ba tareda su sun sani bama. Ko albarkacin abincin da ta dinga bashi. An ce mai Da wawa…inda ake son dan sa anan yake.

Mama tace a ranta. Insha Allahu watarana sai Sarham ya furta SON nan da yake ta musawa da bakinsa. Sai ya so ta kamar, ko ma fiye da yadda yake son Madinah dinnan.

Mama ta mike ta ce masa, "Ma'assalam Sarham zan shiga daga ciki, don na ga tatsuniyar taka ta yau ba mai karewa ba ce, mu kwana lafiya. 

In kun yi waya da “MATAR SO” din ka ce ina gaida Waheedah, tun safe nake gwada layinta (tana nufin Madinah) na kasa samu, in ya shiga sai ya katse, ban san me ya samu wayar tata ba, kwatakwata an daina samun ta. Naso ne dama in rarrashe ta akan maganar auren ka da Hauwa.

Ina fatan ka lallashe ta da kyau Sarham, ka san mu mata a irin wannan lokacin lallashinku da hakurinku da juriyar ku kan canjin halinmu da dabi’unmu kowanne iri ne kadai muke bukata, ka yi hakuri da dukkansu, ka kuma zamo mai adalci a tsakaninsu. 

Kada ka kara fada min wai dalili ne yasa ka auri Hauwa, raina baci yake yi".

Mama ta dade tana yi masa nasiha mai ratsa jiki da bargo, akan zama da mata biyu, sannan suka yi sallama ta bi bayan Abba. Shi kuma har zai wuce dakinsa sai kuma ya taka zuwa dakin Sumayyah don ya yi wa Hauwa sai da safe, ya kuma ga halin da ta ke ciki, ya san har yanzu tana nan cikin kukan nata na shagwabar an rabo ta da Inna. 

Amma ga mamakinsa a kan stool din madubi ya same ta cikin farar rigar barci mai kyan gaske wadda Sumayyah ta bata ta saka, ta dau wanka tayi wani irin fresh da ita, bai taba ganin ta zahirin irin yau ba da tsabar kuruciyarta ta ‘teenager’ data fito fili, sannan bai tsammaci wannan yanayin a tare da ita ba, dakin sai kamshin amarci mai dadi da sanyi yakeyi, kanta da ya sha ‘weeving’ yiri-yiri babu kallabi, ta gama shafa lotion wanda ya sa fatarta yin taushi sosai. Tana daga kan stool Sumayyah na daga gefen gado suna ta hira suna dariya, fararen hakoranta a warwaje kamar mai tallan sensodyne.

Bai taba ganin Hauwa-Kulu cikin kyakkyawan yanayi da kyakkyawar shiga irin wanda ya ganta ciki a yanzu ba.

Ita Sumayyah ta ga shigowarshi, da yake kofa take fuskanta, amma ba ta fada wa Hauwa ba. A lokacin Hauwa na tambayar Sumayyah, "Karatun likitanci nada wahala?”

Sumayyah ta dubeshi tayi murmushi mai sauti ya kasha mata ido, ta ce mata, "Aah babu, ba wani wahala".

Sai ta ce, "Kin ga da idanuna ba su rufe ba, da a bude suke kamar na kowa har yanzu, nima da irin karatun Yayanki zan yi, Ina sha'awar inga ana aikin fidar ido, kasancewar sa wani kwayar halitta mafi hatsari da muhimmanci ga jikin dan adam, ba ki san yadda likitoci suke burge ni ba, shi ya sa har wasu lokutan nake DAKACEN ina ma… in ga Yaya Sarham! Inama in ganshi cikin kwayar idona, in ga yadda kamanninsa na zahiri suke? Ko daidai suke da yadda nake kintata shi ina fasalta shi a raina? 

Anti Sumayyah wallahi haka kawai kyawawan kalamansa SUNA BURGENI!!!”.

Sarham sai kawai ya juya da baya cikin mutuwar jiki, tare da yi wa Sumayyah alamar kar ta ce ya shigo.

Yana shirin kwanciya kamar yadda ya saba ya samu kansa da yin addu'ar Allah ya cika wa Hauwa burinta watarana ta sanya idanunta cikin nasa, ya gaya matai do da ido shima tana burge shi”.

Yana addu’ar Allah ya bashi ikon yi mata adalci ta kowanne bangare, ya kuma ba shi tsawon ran da zai sauke duk alkawururruka da kudirin da ya dauka a kan rayuwarta na zame mata PACESETTER.

Sai washegari ya shiga dakin Sumayyah suka gaisa, ya baiwa Sumayyah kwalin waya, ya ce, ta hada wa Hauwa.

Sumayyah har ta fi Hauwan murnar mallakar tsaleliyar wayar nan. Nan da nan ta hada ta, ta saka layin da ya hado da shi na mtn, ta saka a caji tana gaya wa Hauwa sunan wayar da Bhaiya ta saya mata.

Hauwa wadda kanta ke sunkuye tun shigowarsa dakin, tana iya jin idanunsa all over her, da kyar ta iya furta masa kalmar godiyarta gajeriya.

A lokacin bata dade da yin wanka ba. Mama ta kawo shadda dinkakkiya dakakkiya 'yar Mali ta bata ta sanya, shaddar orange colour, tasa ta yi sharr da ita, amarya sosai mai jini a jika. Sumayyah ta fice daga dakin don dai ta ba su wuri su gaisa, ganin cewa tun jiya basu gaisa ba. 

Sarham ya tako ya zauna a gefen Hauwa. Dab da kafadunta. Hauwa na iya jin sanda ya zauna din, da kamshin balaraben turarensa 'sandalia' daya nasheta, ta lumshe ido ba shiri, inama zata gan shi a lokacin, hakika da ta kara godewa Allah a bisa ni'imar da yayi mata na bata Dr. Sarham Abbas a matsayin mijinta kuma abokin rayuwar ta na har karshen rayuwa. Wani sassaukan yadi ya sanya mai matukar tsada ruwan Madara shara-shara da shi har kana iya hango sabuwar farar singlet dinsa dake ciki. Sannan yadin baida nauyi ko kadan sai tsada. Hannun Dr. Sarham Hauwa ta ji ya ratsa a cikin hannunta na dama for the first time a rayuwarsu, wanda hakan yasa ta dan firgita, tsigogin jikinsu gaba daya suka tashi a lokaci guda. Sarham ya yi crossing fingers nashi da na Hauwa tareda rufesu da daya hannun nasa yana murmushi ya ce, 

“Maijidda matar likita ina kwana? Yaya kuma kwanan bakunta? Ina fatan kinyi barci mai ni'ima kin warware gajiya”.

Hauwa, wadda yau ta ji duk duniya ba wanda ta ke jin kunya sai Dr. Sarham, kasa amsawa ta yi, gashi yana kara karfin matsar da yayiwa hannunta da nasa hannun mai tsananin taushi, ya ce, "Ina gaishe ki Maiji....”.

Ta dan motsa baki cikin dabarar son janye hannunta daga nasa, sabida kasalar da taushin hannun nasa ke saukar mata, da kyar ta iya ta ce, 

"Ni ya kamata in gaishe ka ai Yaya Sarham, ina kwana?"

 Bai yarda ya saki hannun nata ba duk da yadda ta ke son zameshi cikin dabara, ya ce,

 "Na kwana ina tunanin cikin halin da ki ka kwana yau ba tare da Inna ba. 

Na fi ki damuwa da rabuwa da Inna, amma wannan ita ce 'reality' din kowacce diya mace, cewa ita din yar gidan wasu ce kin ji, mai lafiya ko mara lafiya in dai ta isa aure to Allah ya yi umarnin iyayenta su yi mata, ko a birnin Sin ne, so ko ba ni ba ki sa a ranki wai don rashin ido ba za ki dauwama a gaban Inna ba matukar Allah ya kawo miki mijin da ya dace dake yake kuma son ki tsakani da Allah, amma banda Jamilu, ba don komai ba sai don kwanciyar hankalin ki da zaman lafiyan iyayen ki da hakan zai wargaza. Ki yi hakuri kin ji???

Ni na san na saka gaggawa a cikin aurenmu, amma dai ai ba yau muka san juna ba ko Maijidda, kuma in har na kara jan lokaci bayan wanda Ubangiji ya ara min, Jamilu ba zai rabu da ke ba, da gaske yake.

Ni kuma ba zan taba barin wani abu ya kara taba zuciyar Inna ba da izinin Allah, balle aurenki da Jamilu wanda shi ne babban tashin hankalinta”.

Hauwa bata san sanda ta katse Sarham ba, cikin rishin kukan da ya taso mata.

 "....... Yaya Sarham, kana kokarin gaya min ne cewa saboda Inna ka aure ni kai, saboda kwanciyar hankalinta daga Baba Zakari, don ka raba ni da Yaya Jamilu, amma ba don kai a karan_kanka kana sona ba ko?"

Maganar Hauwa ta firgita Sarham yadda bai yi zato ba, don a tunaninsa Hauwa ba ta ma san wani abu wai shi SO ba. kuma bata da tsinkaye mai zurfin haka.

Shirun da ya yi ne ya ba ta damar zare hannunta daga cikin nasa a hankali, tareda matsawa gefe daga jikin sa, ta ce cikin dauriya da hadiye kuka.

"Na san ka aure ni ne saboda kana jin tausayina, kana kuma son ka wanke dattinka da ke cikin raina, sannan don ka dorar da dangantakarka da Innata. Amma kayi mantuwa, ka manta cewa ka riga ka gina zuciyata a kan wani ilmi na kada nakasa tasa in dauki kaina abar tausayi, ko inferior, ko mara amfani a cikin al’umma, ko wadda matsayinta bai kai ga samun kaza ba saboda nakasarta. Ka hore ni ne akan in zama jajirtacciya, cikakkiyar mutum, kuma in nemi ilmin da isheni hada kafada da kowa, ka koya min tsayuwa da kafafuna, in haka ne aurenmu cikin gaggawa ka yi ne don wani abu daban, amma ba don SO ba. 

In haka ne ai da ka bar ni a gaban Inna ta, na ci gaba da bin koyarwarka as my Pacesetter, na ci gaba da rayuwa da iyayena a gefe na. Koda kuwa ban auri Yaya Jamilu ba zan iya cigaba da rayuwata daidai, saboda ba'a aure babu soyayya a iya sanina.

Ashe shiyasa ko amincewata baka tsaya nema ba kafin ayi mana auren, Yaya Sarham ba ka taba tambayata ina so ko bana so ba, tunda ka san da ka furta Inna da Baba amincewa za su yi koda basa so.

 Hakan bai yi kama da fin karfi ba? Tunda ni dai ban ce inaso a aure ni don a taimakeni ko a ji tausayina ba?".

Hauwa ta saka fuska cikin tafukanta tana kuka mai tsuma rai, tana fadin, "Yaya Jamilu ba don tausayi ya yi niyyar aurena ba, ba don ya taimakeni ko ya sani a makaranta ba, zai aure ni ne saboda So, da gittawar Kalmar so da kauna, da kuma niyyarsa ta gyara gurbataccen zumuncin iyayenmu, shi ne ka yi maza ka hana shi, ba don kai din so na ka ke yi ba.

 Already you have your life and your love, kana da macen da kake so daidai kai; wadda tayi daidai da rayuwar ka, meyasa nima baka barni na auri daidai ni ba? Na gina nawa gidan kamar yadda ka gina naka da so da kauna, a maimakon inda za'a dan raba ni da sunan tausayi da taimako??

 Sabida bana gani? Ko saboda iyayena sun ce neman kai suke da ni? Ko kuwa saboda ni ban cancanci a so ni so na soyayya kamar sauran mata?" Ta kara tsananta kukanta harda jiniya kamar tayi masa tumami a kasa.

Yau dai Hauwa na shayar da Dr. Sarham matsanancin mamaki, wonders shall never end! Wato abin mamaki baya karewa. Mamakin ma irin wanda bai taba sha a kanta ba. Rikicin sosai yau Hauwa ta tubure tana yi masa, akan don me ya aureta ya rabata da mai sonta na hakika, tana kuka tana sharbe tana da ya barta ta auri Jamilu ya fiye mata alkhairi.

 Haka ya tabbatar masa da cewa Hauwa ta San 'yancin ta, nan gaba kadan in ta kara shekaru da zurfin ilmi ba za ta taba yarda a danne mata hakki wai don tana makauniya ba.

Ya nisa ya sake nisawa, a wahalce ya ce, "Meji... Maijiddah don Allah ki saurare ni, Maijidda nine fa, Ya Sarham dinky, kin san dai babu namijin da zai auri macen da ransa ba ya so ko kadan.

Tukunna ma ki gaya min wane irin so ne wannan da ki ke ikirarin ni ba na yi miki? Sai kin gayamin kowanne iri ne kuma a ina kika san shi?"

Ya tsattsare ta da ido kamar tana kallonsa, sosai taji idanun sa a jikinta kamar suna mata bulala, kuma wai sai ta ji duk kunya ta kamata, ta rufe ido ta ki budewa, har zai kama hannunta ya kai kirjinsa, don ta ji yadda kirjinsa ke bugawa akan rigimarta da rikicinta da ya daga masa hankali, da yadda kalamanta suka firgita shi, sai kuma ya fasa. Baya so ya zamo touchy a kanta. A ganinsa Hauwa ta yi kankanta ya zauna yana bayyanar da ‘inner feelings’ dinsa gareta bari dai ta kara hankali zuwa can gaba, watakila shi ma zuwa lokacin ya samu ya fahimci kansa da kansa, don shi kansa a halin yanzu bai san wane irin so ne zuciyarsa ke yi wa Hauwa ba, bai san alqiblarsa ba, ya san dai ba irin na Madina bane, ba kuma irin na Sumayyah kanwar da suka fito ciki daya ba kamar yadda yake kuskuren ikirari.

Ganin ta rasa inda zata sa kanta don kunya don ya dage shima sai ta gaya masa wane irin so ne take nufi da baya yi matan. Shi bai san wane iri bane. Mikewa ya yi yana ce da ita,

 "tunda bazaki gayamin ba bari in tafi sabgogi na. Zan shiga AKTH Haj. Soyayya, na rantse sai kin gaya min da bakinki wane irin so ne wannan don ni ban san shi ba ko ba yau ba, akwai abin da ki ke so in zan dawo in taho miki da shi?"

Hauwa ta kara kuluwa, tunda kuwa abin da ta ke son ji din daga bakinsa Sarham bai fade shi ba har zuwa lokacin. Sannan ya maida zancen rainin sense. Bai kuma musanta kalamanta na cewa ba don Inna ya aure ta ba, har ila yau, bai musa cewa don yana jin tausayinta ya aure ta ba, haka bai ce ba don kada Jamilu ya aure ta ne ya sa shi yin gaggawar aurenta ba, haka bai yi mata karyar da take son ji ba, wato ya karkace kai yace da ita yana mata so ne irin wanda Jamilu ke mata ko fiye, wato na zallar ‘I LOVE YOU’. 

Hakan ya sa Hauwa ta kara tsananta sautin kukanta. Don ta tsani a raina mata hankali.

"Cry more!" In ji Sarham. Yana takawa zuwa kofa. Tunda ni din dai da ba ki so ni Allah ya bai wa ba Jamilun da ki ke so ba, wanda ya iya kalaman I love you da ni ban iya ba".

Ya dawo ya russuna daidai fuskarta har tana iya jin sanyin numfashinsa a saman fuskarta kamar zai sumbaci hannayen da ta rufe fuskar da su, sai kuma ya fasa. “Kiss”. Abu ne mai nauyi da sai da Madinah kadai yake iya shi. A ganinsa Hauwa is too young a yanzu ya tsaya yana sumbatarta. Tunda kuma ta yi masa gorin Jamilu ya fi shi sonta, ya kara sanya shi shiga taitayinsa da ita, yasa a ransa ba zai barwa Hauwa kofar sanin zuciyarsa a kan kowaccen su ba ita da Madinah, wadda tun ba'a je ko ina ba ya gane Hauwa irin matannan ne masu son soyayya, da son miji ya zauna yana gaya musu yadda yake son su a ran sa, koda karya zai musu to yafi musu dadi akan ya ki furtawa, shi kuwa duk wata kalma ta ‘I love you’ da ire-irenta da dangoginta ai ya gama fadawa Madinah su a can baya, ‘in his twentieth’ ba yanzu da ya fara zama Uba ba.

Har yanzu yana nan a kan bakansa na cewa, ba auren soyayya ko son sauke sha'awa yayi da Hauwa-Kulu ba, a'ah, auren dalili ne, kuma auren jihadi da kawo maslaha cikin rayuwarta data iyayenta.

"Sai na dawo Maijidda, me zan kawo miki?"

Hauwa tayi masa shiru, tana jan hanci, ya ce. "Ko kina son ‘ice cream?"

A nan ne ta ce a dan fusace, "Ban san shi ba, kuma ban iya sha ba".

Ya ce, "Zan sayo ki koya?".

Da sauri tace.

"Wallahi bana bukata".

Murmushi ya yi, a ransa yace "oho dai, ba zan ce I love you din ba". Ya juya zai fita, sai ga Sumayyah na shigowa dakin.

Ya ce, "Summy, na ce zan sayo muku ‘ice cream’, sarkin rigima ta ce ba kwa sha".

Sumayyah ta yi dariya ta ajiye tray din da ke hannunta a gaban Hauwa, ta ce, "Bhaiya, ka fa yi babbar mantuwa, shin ka kawo kazar amarci ne kafin ice cream din? Ko ka fara zuwa zance ka kafa gwamnatin ka yadda ya kamata???


Sarham ya shafa ‘man’s pride’ din shi (sajen shi) yana gyada kai, kafin yace “wato akace dama sai hali ya zo daya ake abota, yau kam na yarda da wannan zaurancen”, ya gyada kai ya fice yana cewa,

 "Lallai Sumayyah kin raina ni da yawa. Watakila ma ke kike koya mata. Ke da ita ki gayamin me ye marabarku? Ai ni kanwa nake da Maijiddah, don haka na girmi kazar amarci da wani zuwa zance".

Wannan magana ta kara kular da Hauwa-Kulu, yadda baya zato, Sumayyah na ta dariya ya fice ya rufo musu kofar.

Bayan fitarsa Sumayyah ta takura mata sai ta ci abinci duk da fushin da ta samu kanta tana yi dole ta ci abincin tare da Sumayyah, sai da suka kammala Mama ta shigo tana jaye da akwatuna daya bayan daya ta shigo da su har guda shida, ta ce,

 "Sumy ga nan lefen Hauwa'u ne, da Babanta ya hana a kai. Da ma na ce sai ta zo nan zan ba ta da kaina".

Kan Hauwa na kasa sabida nauyin Mama da ta ke ji. Sai Sumayyah ce ke yi wa Mama godiya. Ta soma bubbudewa tana fiddo su, kaya ne masu daraja, tsala-tsala kowanne a diddinke da mayafi mahadinsu, sai akwatin takalma da jakkuna duka flat shoes ne, da karamin akwatin kayan shafa dana wanka, Mama da kanta ta zabo kayayyakin don haka komai ya bada kala da ma’ana.

Mama ta zauna tare da su suna magana da Sumayyah kan sha’anin makarantarta da abubuwan da ta ke bukata da za'a hada mata na komawa, dama duk sanda zata koma hutu sai ta sayi abubuwan bukata da babu a Jeddah irin su maggi da sauran kayan girkin kasar Hausa, don tare za su koma ita da Sarham, ta canza booking dinta ya koma daidai da nasa. 

A nan ne Sumayya ta ji hukuncin da aka yanke daga bakin Mama, cewa Hauwa ba za ta bi su ba. Tana tare da Mama, makaranta za ta fara zuwa itama.

Sumayyah ba ta so hakan ba, amma sai ta ga Abba ya fi su hikima da tunani mai kyau. Ina Hauwa ina iya zama da Madinah? Ita kanta ta san ba wai mugunta ke da Madinah ba, ba boka ba malam, amma wutsiyar rakumi ce ta yi nesa da kasa, kuma Hauwa ba za ta taba sakewa a tsakaninsu shida Madinah ba, haka Sarham din ko yadda yake kula Hauwa a yanzu, a gaban Madinah ba za ta samu hakan ba. Sai ta ga Mama da Abba sun fi su gaskiya, gara Hauwa ta zauna a tsakaninsu inda za a kula da ita ta kara ilmin zama da Madina koda watarana Allah zai hadasu zama tare.

A rana Sarham ya kan shigo dakin Sumayya wajen sau uku don kawai ya ga Hauwa, ko wannan yana faranta ran Sumayyah, amma tun ranar da ya ce ita da Sumayyah ba maraba bai kara ganin murmushin ta da kalar hakorinta ba. Ko Madina sanda aka kawo ta gidan bai yi zaryar dakin Sumayyah irin wadda yake yi a yanzu ba saboda Hauwa na fushi dashi kadai. Yadda ya kasa samun ko murmushi bayan gaisuwa daga bakin Hauwa, duk irin zaman da zai yi a dakin da irin lallashin da zaiyi mata bazata tank aba abun yana damunsa. Shi ba abun ya kwantar da kai ta hanyar janyota jikinsa ya lallasheta ba, girman kansa bazai bari ba, kada ta ga gadon barcinsa tun yanzu. 

Ga shi jibi insha Allah za su tashi zuwa Jeddah shi da Sumayyah. Amma har zuwa lokacin ya kasa samun kan Hauwa.

Ana i-gobe zai koma Jeddah ya zo ya same su ita da Sumayyah a kitchen wai girki suke yi tare. Amma sumayyah ta kafa mata kujera ta zauna suna hira tana daga zaune tana yanka mata salad. Ta sha wani tsadadden cotton lace mai laushi ruwan jinin kare riga da zani da aka kawo kasan lace din aka yi adon wuyan rigar da shi. Sosai Hauwa ta yi wani irin kyau, sai kyallin amarci take ga daurin kan yayi mata cif-cif a kai, kai ba za ka ce babu idanun ba, don har mascara Sumayyah ta zizara mata. Ta yi mata daurin kallabi mai tsari.

Sanda Sarham ya sako kai kitchen din ya ji Hauwa na ce wa sumayyah, “Gaskiya in kun tafi zan yi kewarki Aunty Sumayyah, tunda Aunty Surayyah ba ta zama a gidan nan”.

Sumayyah ta ce, “Ta fi son zaman gidan kakarmu tuntuni, ita ta raineta, amma Mama ta gaya mun yau za'a dauko miki ‘yar Baffanmu na Shanono mai suna Mardiyyah, yarinyar na da hankali, na tabbata sai kin fi jin dadin zama da ita fiye da Ya Surayya”.

Kamshin turaren Sarham ne ya sanar da Hauwa shigowarsa kitchen din, sai ta nutsu, ta daina maganar da ta ke yi. Wayarsa ya mika ma Hauwa ya ce, “Ga nan Inna na miki sallama sun sauka a kasar Ghana lafiya. Saura ki min kukan naki”.

Ya sa mata wayar cikin hannunta, jikin Hauwa har rawa yake jin muryar Inna. Ta kankame wayar tana kiran sunan Inna, sai ta sa kuka.

Inna ta ce, “Shi ya sa fa tuntuni na ki yarda likita ya hada ni da ke, na ce sai mun sauka lafiya. Don na san hakan ce za ta faru. 

Likita Sarhamu ya saya mana tikitin da ya kawo mu Kumasi, Hauwa ba ki ga gidanmu ba masha Allah, yayi ukun namu na Kano, ki yi biyayyar aure Hauwa, ki yi biyayya ga iyayensa da shi kansa, su ma iyayenki ne. ki gode wa Allah da ya hada ki da surukai na arziki ki zauna lafiya da kowa. Kin ji Hauwa-Kulu na?".

Hauwa ta gyada kai kamar Inna na kallonta. Inna tace "madallah, ya gaya min a nan gidansu zai barki tareda Mamansa, za ki fara makarantar jami'a, hakan ya fi min kwanciyar hankali fiye da kina tare da kishiya alhalin babu idanu a tare da ke. Allah ya zama gatanku, Ya jibinci al’amarinku. Allah yayi muku albarka”.

Malam Bilyaminu ya karbi wayar, shi ma nasiha sosai ya yi mata, kafin su yi sallama har lokacin Hauwa ba ta bar share hawaye ba.

Mama ta shigo kitchen din tana cewa, har yanzu ba su gama girkin ba? Me ya samu Hauwa’u ta ke kuka haka?”

Sarham ya juya zai fita don shi ma zuciyarsa ta tabu da hawayen Hauwa, har sai da ya gwammace da ya sani bai hada ta dasu Innar ba.

Da kyar Mama ta samu ta yi shiru, ta saka hannu aka karasa abincin yau har dakinta ta ja Hauwa, inda suka zauna daga ita sai Hauwa.

Mama ta ce, “Na san ba zan maye miki gurbin Inna ba, amma zan kula da ke kamar yadda nake kula da nawa yaran.

Na san ana cewa iyayen miji basu da kirki, but I want to be an exception!

Ki bani damar zama Uwa a gareki Hauwa, saboda inason Sarham, inason duk abinda zai zama kwanciyar hankali a gareshi, ki ga yadda zan zame miki uwar goyo da zani”.

Da ire-iren wadannan kalaman Mama ta lallashe ta suka ci abinci a dinning har da ita. 

Sarham na idar da sallar la’asar ya soma hada kayan tafiyarsa. Haka Sumayyah tun jiya ta hada nata kowannensu jiki a sanyaye, kuma ba don komaijikinsu yayila’asar ba sai don barin Hauwa da zasu yi ita kadai sai Mama dake wuni a chamber.

Bayan isha ne Sarham ya zo yin sallama officially again da Hauwa. A lokacin ita har ta yi shirin bacci. Sumayyah na can falo suna kallon talabijin da iyayensu.

Hauwa na karanta addu’ar kwanciya ta ji zaman Sarham a gefen gadon, har jikinsa na gugar kafafunta. Koda ma can turaren shi da sallamarshi sun riga shi isowa gare ta.

Da wayo da dabara ya kama hannunta ya dora bisa saitin zuciyarsa.

 Hauwa na iya jin yadda kirjinsa ke dagawa yana sauka. "To haka fushinki ke azabtar dani kwana da kwanakin nan Nana Hauwa'u. Ba zan dai iya bayyana miki bane don kin yi kankanta kuma kinga nan gidanmu ne, banida sakewa a cikinsa". 

Wannan kyakkyawan kawaicin na Dr. Sarham har gobe yana tare da shi, ba ya hada girman iyayensa da girman idanunsu da komai na rayuwarsa.

“Maijidda zan tafi, ba zan samu dan abin da zan ke tunawa da irin wannan lokacin ba? Dana tafi na bar mata ta HAUWA karkashin kulawar aurena da iyayena ba? Ko da kuwa sallama mai kyau ta fatar baki ce???

Na san kina fushi da ni, amma exactly ina son sanin laifin da na yi miki Maijidda. Honestly speaking bansan laifina ba”.

A hankali Hauwa ta janye hannunta daga saman kirjinsa, don ta kasa jure sauyukan da hakan ke haifar mata cikin jikinta da ruhinta, da kyar ta ce,

 “ni ba ka yi min laifin komai ba, hasali ma sai tarin alkhairi ni da iyayena, irin wanda baki ba zai iya furtawa ba. Sannan babu kalaman da za su isa godewa. Ina rokon Ubangijiya fini godewa.

Idan har na yi fushi da kai a kan wani abu Yaya Sarham, to ya zama rashin adalci da butulci irinna an adam, domin ka yi min komai and beyond, da ya cancanci in gode maka ba inyi fushi da kai ba. 

Kawai in na tuna cewa ni ba SO ne ya sa ka aure ni ba, tausayi ne da son kyautata rayuwata sai in ji komai na duniya ya daina yi min dadi…, burikana na shekara daa shekaru sai inji sun fita kaina”.

Sarham ya ce cikin daga murya, “Shi tausayin ba SO ne yake yin sanadinsa ba?

Ko kuwa in tausayi ne ashe duk masu lalurar ido na aibitin Murtala na Kano dana yiwa aikin ido sai in bisu in aure su, bana son ki zan kawo ki cikin gidanmu, in hada ki cikin iyalina Maijidda?

 Bana sonki zan miki takwara da diyar cikina? Tun ma baki zama matata ba?”

Kawai sai Hauwa ta ji kukan dadi ya kwace mata, ta sa tafukanta ta rufe fuskarta tana yinsa riiiii-riiiii.

A hakan ba ta yi aune ba ta ji numfashin Sarham daf da fuskarta, ya ce, “kin yi kankanta in tsaya ina gaya miki abinda kike son ji daga gareni. Amma duk da haka ina so ki saka a ranki, ba wai furta kalmar so ne kadai yake sakawa a yi aure ba, sannan aure ba ya taba samun muhalli a inda babu so. Ko na ce, ko ban ce ba Maijiddah, ba zan aure ki alhalin ba ki da muhalli ko yaya a zuciyata ba. 

Da wannan nake cewa. Maijiddah ki yi hakuri ki bani lokaci, ki taya ni mu taru ni dake mu raini wannan burbushin SOn, wanda dalilai da hujjoji suka fi shi karfi, daga ni har ke ba mu san me gobe za ta haifar ba, Allah daya halicce mu shi kadai ya san sirrin da ya boye a tsakaninmu.

 Ina fatan ki taya ni rainon wannan burbushin son, har zuwa sanda zai girma ya zama mashahuri, abin buga misali beyond our expectations”.

Sarham ya yi shiru yana nazarinta hawaye sun ki tsayawa a idanunta, amma ta kare fuskarta da tafukanta.  Ta sani cikin abubuwan da yake fada duka babu karya, gaskiyar zuciyarsa yake gaya mata,

 “suyi nurturing dan burbushin son tare har ya girma ya zama mashahuri”.

 Wanda ita kuma gaskiyar ce ta ke mata daci, ta cewa ita an aure ta ne ba don so ba, sai don wasu dalilai masu karfi.

Sarham ya fada ya maimaita a kunnenta, ya fada har a bayan idon ta, wanda shi a wurinsa ba komai ba ne face gaskiyar da ke zuciyarsa kasancewarsa frank person, kuma a wurinsa ya girma da yin karya, wai don ya farantawa mace. 

Bai sani ba, ita wannan gaskiyar bakanta shi ta ke yi a zuciyarta, har gara ya barwa ransa ita, koda kuwa bai yi mata irin zancen da ta ke son ji din ba kamar na Jamilu mai nuna tsantsar tsagwaron soyayyah muraran.

Duk yadda Dr. Sarham ya so su yi kyakkyawar sallama abu ya faskara, shi kuma yana jin nauyi da pride din ya rungumo ta cikin jikinsa ya lallashe ta irin lallashin da yake yiwa Madina in ya bata mata rai, Madinah ai sa’arsa ce, ta kuma mallaki hankalinta, sannan soyayyar ce zallah ta hada su. A wautarsa Hauwa-Kulu ba ta san da irin wannan duniyar ba, ba kuma zai koyar da ita ba balle har a zo gejin da wani abu makamancin nasa da Madinah zai samu mabubbuga tsakaninsa da Hauwa. 

Hauwa za ta ci gaba da cin matsayinta na tudu biyu, na kanwarsa kuma matarsa. 

Yayin da Madina ke kan tudun muntsira na masoyiyar romansiyya.

Matsayin da ya bata na kanwa kuwa ai ya fi na masoyiyar soyayya, tunda matsayin kanwar jini ya ba ta, kuma dai Hausawa suka ce jini ya fi ruwa kauri, wato soyayyar jini da yake yi wa Hauwa-Kulu kaurin ta yafi na romantic soyayya tasiri, irin wadda ke tsakaninsa da Madinah.

Sallamar dai ta ki dadi tsakanin Sarham da Hauwa, ta ki kula shi, ta ki daina kuka. Ta ki yafe furucinsa. Har cewa tayi cikin subutar baki. 

"Ita da ma ya barta tare da su Inna sun tafi Ghana, ya fi mata alkhairi a kan wanan kaddararren auren nasa, (wadannan kalaman da ya gama gaya mata yanzu sun mata da banzan ciwo), na cewa da yayi ta taya shi su yi nurturing ‘yar burbushin soyayyar da yake yi mata, su girmar da ita tare, har su samu ta zama mashahuriya, wanda in anbi salsala kalamansa na nufin ba ta da muhallin soyayya a zuciyarsa. 

Wannan ya kara tunzura kuka da rikicin Hauwa. Abinda bata sani ba harda na kewar tafiyarsa.

Abin da ba ya son yi wato rungumar Hauwa ya lallasheta shi ya yi a bisa dole, jikinsa yana ’yar kyarma ya hade jikinsa da nata wuri guda suka dunkule cikin ‘tight hug’. Hauwa tana sakin kuka a hankali bata daina ba, wani abu tamkar 'electrical shocking' ya bakunci jiki da zuciyar Hauwa, dana Sarham as well, ta yi kokarin janye jikinta daga cikin nasa, amma yaki saki, ya tallafo fuskarta da hannu daya, kallon hawayen da ke bilbila daga kyawawan idanunta suna sauka akan kundukukinta sumul sumul dashi kawai Sarham ke yi, kafin ya kai dan yatsansa manuni yana kawar dasu one by one daga kan kuncinta, sai kuma yasa fuskarsa a cikin tafukan Hauwa, wato ya tallafi fuskar shi da hannuwanta biyu ya sanya fuskarsa a tsakiyar tafukanta, murya na dan rawa kamar yadda ilahirin jikinsa ke shaking and vibrating da ya hadu dana Hauwa, Sarham ya ce.

  “Zan tafi Hauwa-Jiddah, sai nazo, ban san yaushe zan samu dawowa ba. Anyway ki kula da kanki, ki kula da ibada kin ji?”

Kai kawai ta gyada masa don dai ta samu freedom daga rikon kazar kukun da yayi mata, zai sumbaci tafukanta da ke kan sajensa, idanunsa a lumshe, Hauwa kamar ta san hakan zata faru ta yi maza ta janye hannayenta daga sajen fuskarsa, tsigar jikinta na tashi amma a wannan lokacin ji take bata bukatar irin wannan rarrashin yaje can yayiwa matar so. 

Duk yadda Sarham yake so sallamar tayi dadi da armashi tsakaninsa da Hauwa, ta yadda bazai tafi tana ajje dashi da kalamansa a ranta ba, hakan bata samu ba, Hauwa ta dauki fushi mai ban mamaki wanda shi a iya saninsa bai da dalili. Meye laifi don ya gaya mata hakikanin gaskiyar da ke zuciyarsa cewa ba soyayya ce ta sa ya aure ta ba? Dalili ne, kuma har gobe zai kara maimaitawa dalili ne mai kwari da karfi ya yi mujazar auren nasu. Ta tayashi su raini wannan dalilin har ya koma ingantaccen SO, Shima zai so hakan. Ko don ya zamo mai adalci tsakanin ta da Madinah. Ya gama gane Hauwa so ta ke ya zauna yana mata karerayin samari ‘yan I love you? Ya karkace kai yana ce mata ‘I can’t do without you, bayan Madinah ce kawai ‘he can't do without’.

  A ganinsa ya wuce wannan ‘stage’ din tun a can baya, kuma ba zai iya maimaita shi da kowacce mace a yanzu ba, bayan Madinah.

Ya tsura ma Hauwa ido daga tsaye, hannayensa biyu zube cikin aljihunsa, ya kasa fita daga dakin, kalma kuma ta kare masa don ta ki tsaida hawayen idanunta, kukan da bai ga dalilin yin sa ba, don ba za ta ce don kewarsa ta ke yin shi ba. Don yana da tabbacin Hauwa bata wani saka shi a ranta ba.

Lokaci na ta tafiya, Hauwa na sheshsheka, wadda ke saka Sarham tsuma daga tsaye, kukan nata na huda shi sosai, ya kasa fita daga dakin har sai da Sumayyah ta dawo, ba ta san cewa har lokacin yana dakin ba. 

Ta yi niyyar komawa da baya ganin yanayin da suke ciki, ya ce murya na sarkewa “Summy, kina iya shigowa, wucewa zan yi in kwanta, kin san gobe asubanci za mu yi.

 Ina fatan kin sayo ma Maijidda duk abin da za ta bukata din wanda zai yi mata akalla watanni uku?”

Sumayyah ta idasa shigowa dakin cikin sanyin jiki na yanayi mara dadin data gansu aciki, ta ce, “Ba abin da ban sayo mata ba, duk da cewa akwai komai a cikin akwatin lefenta, irin su pad, macleans da listerine na karo mata da sauran tarkacen da babu cikin akwatunan".

 Sarham ya soma taku daya, biyu zai bar dakin har zuwa lokacin hannayensa biyu cikin aljihunsa ya ce, “Maijidda sai mun yi waya, take care”. Da wani irin karfin hali ya bar dakin ba tareda ya jira jin amsarta ba.

Hauwa ta ce, “Allah ya tsare, Allah ya sauke ku lafiya”.

Wani irin tausayi mai tsanani ya kama Sumayyah ganin cewa, ai Sarham ba irin sallamar da ya dace a ce ya yi da Hauwa ba kenan, za ta iya rantsewa in Madina zai tafi ya bari a wata kasa ba irin sallamar da za ta samu kenan ba. 

A halittarsa ‘he's very romantic’ ga matar aurensa. Me yasa yake ja baya da Hauwa?

Ta hade rai sosai cikin taya Hauwa kishi, ta yi kwafa ta bi shi da harara yana ficewa.

Sumayyah ta zauna a gefen Hauwa wadda ke gyara filo don ta kwanta, ta ce, “Aunty Hauwa saboda Allah haka ake sallama da miji ana cin magani ana faman sharar hawaye da sharbe majina? 

Da me zai tuna ki ya yi dokin sake zuwa gare ki?

Hauwa sai fa kin sake lale, in ba haka ba wallahi za su kai ki su baro a ‘yar jiran dakinsu. 

Ki tashi ki kwato wa kanki ‘YANCIN SO, dana lura anaso a take miki da gangan, don ni ban ga soyayya a wannan auren naku ba, ya fi kama da zallar ‘yan uwantaka. 

Ni ko yadda na ga ana magana da Madinah ana kashe murya da Ido ba haka na ga ana magana da ke ba.

 Ke ni fa bana karbar ‘defeat’ na a so wata mace ‘yar uwata fiye da yadda za a so ni, don ban yarda ta fi ni da komai ba, dukkanmu mata ne a halitta, sai dai a ce kowacce da kalar tata fatar. Amma da irin kissar ta, na rantse mai mata irin Madinah, sai kin yi da gaske kafin ki samu gurbin da ya dace da ke a hannunsa, don wallahi Madina ta gama shan gaban Bhaiya daga sama har kasa, har kudu da arewa”.

Hauwa ta ce, “Aunty Sumayyah kenan, ta ya ya zan zo in same shi da matarsa in ce lallai sai na hada kafada da ita a zuciyarsa?

Nasan irin gwagwarmayar da sukayi tare kafin su kai ga wannan matakin? Kamar zan fi yarda da nasa ‘perception’ din fiyeda naki, da yace in taya shi mu raini nawa son har in samu ya girma a zuciyar sa. 

Soyayyah ta Allah ce, ba’a mata dole, shi yake sanya ta a zuciyar da ya ga dama, ni ba wani ‘effort’ da zan yi don a so ni, ban da maida al’amurana ga Allah da yin abin da zai amfane ni duniya da lahira. 

Ban shigo rayuwarsu don in hada kafada da ita a komai ba kamar yadda ban taba tsarawa kaina aure da mai mata ba. na shigo ne ta hanyar kaddarata.

To amma ya zanyi tunda Yayanki Allah ya rubuta min? Kuma shi iyayena suka zaba min? Na shigo gidansa ne da sunan shi ne mijin da Allah ya zabar min, kaddara kuma ta rubuta min, ba ruwana da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da matarsa”.

A takaice Sumayyah ta gama gane Hauwa, sune irin matan da ake kira ‘naive and innocent’ a zamantakewar aure. Ba ta da wani ‘proper experience’ na zama da miji balle da kishiya, don haka duk yadda za ta kwatanta mata ta tashi tsaye ta kwaci soyayya a zuciyar Sarham ba za ta gane komai ba.

 Ita kuma sai inda karfinta ya kare wajen kwato wa Hauwa ‘yancin so, sannu-sannu ba ta hana zuwa aka ce sai dai a  dade ba a je ba. An yi mai wuyar ai tunda har Hauwa ta amshi sadakin Sarham, shi kuma ya amince ta amsa sunan matarsa, har ya bata dafin Mrs. Shanono.

Babban abin da ya taba zuciyar Sumayyah ko irin dokin nan na amarci babu a tare da shi, a tsayin zamansu da Hauwa za ta iya tuna ko sau nawa ya kira ta a waya daga sanda ya mallaka mata wayar hannu. Amma Madinah fa? 

Sanda aka kawo ta gidan bata manta ba Sarham baya awanni biyu bai kira ta a waya ba, ga wani munafikin ‘midnight’ call da suke yi kullum dana yammaci da yake tafiya bakin layinsu yayi duk don tana cikin gidansu ba tare dashi ba, har sai da suka bar gidan zuwa inda suka fito, sannan suka samu lafiyar su.

Duk wannan ba ya gaban Hauwa, ba don komai ba sai don cewa Sarham bai koya wa Hauwa soyayya ba, bai bi matakan da suka dace wajen aurenta ba, don ko tadi bai taba zuwa officially ba, kalmar so ba ta taba giftawa tsakaninsu kamin su yi aure ba, haka ba ya jin wai a gaba za ta gifta. Duk abin da yake nema a diya mace yana da shi a Madina, don haka aurensa da Hauwa ba zai daina kiransa da auren dalilai da sanadi masu yawa ba.

A daren Sumayyah ta koya wa Hauwa amfani da abubuwa na tsaftace jiki kamar su mouth wash da mouth freshner, wanka da bath gel maimakon sabulu. Turarukan lefenta ta jere mata su a kan madubinta, ta nuna mata yadda za ta dinga amfani da komai har abubuwan toiletries din duk ta koya mata amfani da su.

Tun a daren suka yi sallama da Sumayya cike da kewar juna, haka Hauwa  ta kwana cikin sake-saken yadda rayuwa za ta kasance mata a gidan iyayen mijinta babu mijin, babu Sumayya mai debe mata kewar Inna.

Sarham da kanwarsa Sumayyah, sun tashi zuwa Jiddah a washegari. Gida ya rage daga Mama sai surukarta Hauwa da yarinyar da aka dauko mata daga Shanono.

Hauwa na jin dadin zama da Mardiyya, nan kasan kafafun gadonta Mardiyya ke saka katifarta ta kwanta. Duk wani motsi da Hauwa ta yi za ka ga Mardiyya ta mike tana tambaya, “Aunty Hauwa kina son wani abu ne? ko bandaki za ki shiga in taimaka miki?”

In bandaki za ta shiga sai ta ce, “Ai ba sai kin raka ni ba Mardiyya, ko ma barcinki zan iya kai kaina”.

Mama koyaushe in ta dawo aiki sai ta fara shigowa dakin da Hauwa ta ke, ta zauna su yi hira, tun Hauwa ba ta sakewa har ta gane Mama fa ba ta surukuta da ita. In Abba Prof ya dawo kullum Mama cewa ta  ke, Mardiyya ta fito da Antinta falo ta ji labaran tara, su daina kulewa a daki su kadai.

Surayyah tuni ta bar musu gidan, ta koma gidan Hajiyar Gadon Kaya.

A kullum abincin Hauwa na musamman Mama ke sa wa a shirya mata, kuma sai ta zabi abin da za a dafa mata. Mama ba ta dawowa gida ba tare da ta kawo wa Hauwa tsaraba ba, musamman da ta gane tana da son cin gugguru (popcorn) kullum sai ta sawo mata shi.

Kafin ka ce me ye wannan, wata irin shakuwa irin ta Uwa da Da mai ban mamaki da ban sha'awa ta samu muhalli tsakanin Mama Mai Shari'a da surukarta Hauwa.

A wasu lokutan Barr. Haj. Maimuna Shanono in tana hira da kawayenta na jiki  su Barr. Hannatu a chamber dinsu, za ka ji Mama tana fadin musu, “ita kam yanzu ne ta san Sarham ya yi aure daidai da shi. Inda zai fada aji, inda ba'a raina arzikin shi ba. Yanzu ne ta san ta yi surukar da in ta ce ta yi kaza za ta yi ba girman kai ba dagun kai, ita yanzu ta san ta yi suruka da take da ‘high influence’ a kanta". 

Kuma in za ka tsire ta ka ce meye aibun Madinah Sorondinki, kome tayi mata da har gobe bata bata yardarta da amincewarta 100% ba, kamar yadda ta bai wa Hauwa-Kulu farad daya, zaka tarar Mama ba ta da amsar ba ka. 

Bata da wata hujja kwakkwara ta son Hauwa fiyeda Madina. Daidai gwargwado Madina ba ta gaza da su ba, ko bata musu biyayya ko tana da wani nakasu da za'a iya bugun gaba a soketa da shi ba, illa hakan halin Dan Adam yake musamman a inda soyayyar miji ta kasa boyuwa akan mace, wasu iyayen mijin nada halin dan Adamtaka in ‘ya’yansu na mutuwar son matansu, to su kuma za ka samu ko me matar za ta yi ba zai burge su ba. Kuma a kasan ransu suna jin zafinta, babu gaira babu dalili. 

To hakan ce tsakanin Mama da Madina. Koda bata taba nuna mata Hakan ba. Balle dama Madina wadda tun asali tana da fenti a idon Mama na wulakancin da mahaifinta ya yi musu duk da cewa (eventually) ya yi (repenting), ita kam har gobe in ta tuna sai da ya fara bada ta ga maikudi irin su, ya rasa shi, sannan ya nemo Sarham ya manna masa abin yana ragewa Madina tagomashi a idanunta. 

Musamman data san cewa auren da Madina tayi bai rage komai daga soyayyar da Sarham ke mata ba.

Maganar auren Sarham  da Hauwa kuwa, Mama ta dade da sakawa a ranta, watarana zai faru. Duk da Sarham ya yi ittifakin ba son Hauwa yake ba a gabanta, amma ita ta dade da sanin akwai babbar kaddara a tsakaninsu. Tana biye da al’amarinsu tun daga ranar da ya yi wa Hauwa aikin ido, har zuwa yau.

 Mama ta yarda ta zama uwar Hauwa, tunda har Sarham ya rabo ta da uwa da ubanta, alhalin babu idanu a tare da ita. Tana lura da cewa, tun tafiyarsa bai kara kiran Hauwa a waya ba, sai dai ita in ya kira ta ya ce a gaida masa Maijidda.

Wannan abu yana yi mata ba dadi, ita kuma ba ta taba ce masa don me ba ya kiran Hauwa ‘direct’ tunda yana da lambarta ba? Ko musuluci bai yarda da wannan ba, kuma hakan tauye ‘yanci ne. Ta kwana da sanin Sarham ba zai iya kiran wata mace alhalin yana tare da Madinah ba.

Abin da ba za ta taba kira tsoro ba, don a policy din Sarham ba shi da tsoro ba shi da shakka tun yana dan karamin sa, don haka ba ta san dalilinsa na kin kiran Hauwa ba, bata masa fatan soyayyar da yake yi wa Madina ta kai ga matakin tsoro, tunda ai yana fita, zai iya kiranta in ya fita in ma idon matarsa yake gudu, bata fatan soyayyarsa da Madinah ta yi yawan da za ta saka shi zabar tashi ranar lahira da shanyayyen barin jiki na tauyewa Hauwa hakki. 

A karshe ta gode wa Abba Prof. da bai bari Sarham ya tafi da Hauwa Jiddah ba, hakika da ta ga rainin wayo, da rashin adalci, amma ai ba za'a dauwama a haka ba tunda Hauwa-Kulu, ko da ta ke makauniya, aurenta ake kamar yadda ake auren kowa.

Lokaci Mama ta bashi don ganin kamun ludayinsa a kan auren Hauwa, don ba zai yiwu ya auri ‘yar mutane a gaban shaidu ya bata sadaki sanan ya maida ita kanwarsa ta jini Sumayyah ba.

(Da a ce Mama ta san halin da Sarham ke ciki tun bayan komawarsa Jiddah hakika da ta tausaya wa masa, data ji tausayin tilon dan nata namiji daya tamkar da maza dubu, wato (Likita SARHAM)!!!




Post a Comment

0 Comments