TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

DIYAM PAGE 49- END

 By


Maman Maama


Episode Forty Nine : The Utterance


Inna taga ta kanta a gurin jama'a jiya. Duk inda na shiga kowa kokawa yake yi da abinda Inna tayi. But to me, laifin Inna a yanzu guda daya ne, rashin sauraron Diyam kafin ta yanke hukunci bawai hada Diyam da tayi da Sadauki ba. Wannan kuma shine halin kusan 70% na northern mothers. Kullum su dai burinsu shine yarsu ta zauna a gidan mijinta kar ta kashe auren ta dawo gida ta zauna a gabansu. But what if the marriage is not working? What if she is buying her ticket to hell fire instead of paradise a cikin auren?


And Saghir, Saghir yayi laifuffuka da dama a baya but a yanzu laifinsa shine dukan Diyam. Nothing, nothing gives a husband the right to hit his wife. Duk kuma namijin da yake dukan matarsa to ba mijin aure bane ba, ballantana mata mai ciki? Hmmm


Then Sadauki. Na lura Sadauki ya zama shafaffe da mai a gurin readers, sam basa ganin laifinsa komai yayi daidai ne dan ina jin few mutane ne naga sunyi comment akan laifin Sadauki. Sadauki is rather rude and very authoritative. Ba shi da right din da zai sa a rufe Saghir, yes Saghir yazo gurin aiki drunk kuma ya fadi maganganu wadanda babu wanda ya gane in banda shi Sadauki da ake magana a kansa. Abinda ya kamata Sadauki yayi shine yasa ka security su fitar dashi waje, in ya ga dama ya hada masa da takardar kora daga aiki. But bashi da right din kaishi station a rufe shi kuma wai without bail, saboda yana da kudi?


Let's continue


Na rufe fuskata ina girgiza kaina da sauri. "Inna kar kiyi min haka dan Allah. Inna ki tsaya ki saurare ni ki fahimce ni kar ki mayar dani gidan Saghir in na koma wallahi mutuwa zanyi" tace "da baki mutu ba shekara da shekaru sai yanzu da Sadauki zaiyi aure shine zaki mutu?" Sai ta mike zata shige daki nima na mike da sauri na rike hannunta da hannu na daya dayan kuma na daga mara ta da shi nace "Inna nayi bari jiya" sai ta juyo tana kallo na ido a bude, ta taba fuskata da hannunta tace "bari Diyam? Ya akayi kika san bari ne kinje asibiti?" Na gyada kaina nace "naje Inna, su suka tabbatar min da cikin jikina ya fita Inna. Saghir ya fitar min dashi" ta dan bata rai cikin rashin fahimta tace "Saghir? Ta yaya Saghir zai fitar miki da ciki?" Nace "dukana yayi Inna, dukana Saghir yayi ya buga ni da jikin bene ya kashe min baby na, kamar yadda shaye shayensa ya jawo mutuwar yan biyu".


Sai ta kama hannuna muka zauna tace "Diyam, kin tabbatar abinda kike gaya min gaskiya ne? Me ya hada ki da Saghir har ya dake ki haka?" Na shafa fuskata sai itama ta saka hannu ta taba fuskar tawa, side din da Saghir ya mare ni, na dan yamutsa fuska alamar zafi sai naga idonta ya kawo kwalla amma sai tayi sauri ta mayar da ita. Tace "me ya ha蓷a ku nace" sai na bata labarin messages din Sadauki. Tana girgiza kai tace "me yasa? Me yasa zaki ajiye sakon Sadauki a wayar ki har mijinki ya gani bayan kuma kinsan yasan tsakanin ki da Sadaukin" nace "inna na fada miki menene a cikin sakon nan, babu wata kalma ko daya data kauce hanya a ciki kuma in na goge su ai kamar bani da gaskiya kenan. Ina son Sadauki na sani, amma Allah ne shaidata cewa ko sau daya ban taba tunanin yin sabon Allah da Sadauki ba. Kuma ke kece shaida, Sadaukin nan tamkar dodanniya haka nake a gurinsa, ko kallon inda nake baya yi. Shi dai ya zarge ni ne saboda shi din yasan shi mai laifi ne, abinda yake cikin tasa wayar idanuwa ma ba zasu iya gani ballantana hankali ya dauka" Inna tace "akan wannan maganar ne Sadauki ya sa aka kama shi?" Nace "ni ban sani ba, amma ina jin akanta din ne. Ya dai fita a fusace yace sai ya wulakanta Sadauki, tun daga nan kuma bai dawo ba sai da safe Kabiru abokinsa yazo yace mana yana hannun yan sanda" Inna tayi shiru tana tunani sannan tace "yace za'a sake shi gobe, Allah ya kaimu goben, ya fito sai yazo yayi bayanin dalilin da yasa ya dake ki. Kar ki goge messages din ki barsu saboda shaida a gani cewa babu abin duka a cikin su".


Sai naji raina yayi min wani irin dadi, babu abinda yafi dadi irin a fahimce ka babu kuma abinda yafi ciwo irin ace kana da gaskiya amma a hana ka tsarawa ballantana a fahimce ka. Ina ma dai iyaye zasu ke bawa yayansu wannan damar? A fahimci kowa sai a hada both parties ayi wa kowa fada dai dai da laifinsa? Ba wai ace da mace ki komaki cigaba da hakuri ba tare da ko murya an daga wa shi namijin da yake maltreating dinta ba, wannan tamkar ana ce masa ka cigaba da maltreating dinta ne.


Amma dana fara tunanin abinda zai iya faruwa gobe sai naji duk hankali na ya kuma tashi. Nasan halin Saghir sosai nasan zai iya jujjuya maganar gabaki daya ta koma laifina kuma na tabbatar iyayen mu musamman mazan bayansa zasu bi, musamman in nayi la'akari da irin kiyayyar su ga Sadauki, da kuma soyayyar da suka san ina yiwa Sadauki, tabbas komai Saghir ya gaya musu yarda zasuyi. Ni kuma ba yardar su ko rashin yardar su ce problem dina ba a'a tirsasani in koma gidan Saghir shine problem dina. Na gama auren Saghir, ba zan koma gidan Saghir ba. Wannan is my decision. Ni a yanzu auren Sadauki ko rashin auren Sadauki ko shi kansa Sadaukin basa gabana. Abinda yake gabana shine rabuwa da Saghir.


Inna tace inje in kwanta in huta a daki. Na tashi na shiga ina jin Asma'u tane cewa "Inna amma ba za'a mayar da Adda gidan can ba ko?" Inna tayi shiru bata ce komai ba. Na kwanta kawai sai hawaye ya fara zubo min ina lissafin abin da zanyi in akace sai na koma. A ciki har da guduwa na lissafa amma inna gudu inje ina? Yan uwan uwata dai sune yan uwan ubana sune kuma yan uwan mijina. Sai kawai na yanke shawarar in aka matsa min akan in koma gidan Saghir to zan gudu gurin Sadauki, inje in tuna masa da amanar da Baffa ya bar masa ta kula damu, sannan in tuna masa cewa ni ma fa yar Baffa ce ba wai Asma'u ce kadai yarsa ba. In kuma roke shi daya shige min gaba in kai karar Saghir court alkali ya raba auren mu. Yes, wannan shine abinda zanyi. 


Ina kwance Subay'a ta shigo ta kwanta a kusa dani. Sai naji tana sheshshekar kuka, na jiyo nace "Subay'a? Lafiya kike kuka? Wani gurin ne yake yi miki ciwo?" Sai tace "Mommy ki daina kuka kema" na jawo ta jikina nace "ba kuka nake ba Subay'a ido nane yake min ciwo" tace "kuka kike yi ai na sani, naji kuma aunty Fauziyya dazu da tana shirya ni zan tafi school tana waya tana cewa kunyi fa蓷a da Daddy shine ya dake ki kike kuka, kuma naji dazu kina fada wa Inna Daddy ya dake ki" sai na kasa ce mata komai, lallai yara duk abinda ake yi a gabansu suna sane. Ta goge min fuskata tace "kiyi hakuri Mommy, in Daddy ya dawo zance masa kar ya kara dukan ki".


Sai na dage da addu'a sosai ina rokon Allah ya shiga lamari na ya kawo min agaji. Dan nasan in na koma gidan Saghir to ba rayuwata ta duniya ba har ta lahirar ma tangadi take yi, two zero kenan. Saboda ni dai nasan a rayuwar auren da nayi da Saghir a baya ba karamin zunubi na lodar wa kaina ba ballantana in na koma nasan bazan iya yi masa koda rabin biyayyar da nayi masa ada ba. In kuma haka ta faru to nice a ruwa dan Ubangiji babu ruwansa, laifina daban a gurinsa laifin Saghir shima daban. Kowa littafin sa daban. Dan haka sai na kwana ina kaiwa Allah kuka na.


Washegari tun safe nake saka ran wani abu ya faru amma shiru, ko ya naji anyi motsi sai in tsorata in dauka Saghir ne zai shigo gidan. In naji wayar Inna tayi kara kuwa dai inji kamar zan saki fitsari a wando saboda tsoron ko kira ne a kaina amma shiru. Da safe Inna tayi min farfesun hanta mai romo tace in cinye, na cuccusa da kyar naci dan bani da appetite sam, sai kuma ta fita da kanta taje kasuwa sai naga tayo cefanen green vegetables kala-kala tazo ta hada min miyar ganye mai naman rago ta sani naci da tuwon shinkafa tace zai kara min jini. Daga ni har ita babu wanda yayi zancen Saghir amma dai nasan duk maganar tana ran mu.


Shiru shiru har dare. Har gayi ya waye wani daren ya sake yi. Har aka kwana biyu sannan aka kwana uku, hudu, biyar, sai akayi sati daya. A ranar ne Inna tace "to ni ko Alhaji Babba zan kira ne akan maganar Saghir din nan ne? Kar dai ba'a sake shi ba har yau. Ni kuma bana son in sake kiran Sadauki kar yaga kamar ina damunsa akan sirikina yaji babu dadi" Asma'u tace "dan Allah Inna ki rabu dasu, yayi ta zama mana a cell din wa ya damu ne wai? Itama yanzu ba gashi ta samu kina kulawa da ita ba da yana nan kuwa ba vari zaiyi kije gidan ki kula da ita ba kuma ba lallai bane ya barta tazo nan" Inna tace "Asma'u kenan, ke yarinya ce ba zaki gane ba. Maganar nan fa tana kara jimawa ne tana kara karfi. Dole ya kamata in bincika inji halin da ake ciki" sai ta dauko waya ta kira Hajiya Yalwati, suka gaisa sai take tamayarta ko taga Saghir kuwa? Nan take Hajiya Yalwati tace "dama yanzu nake niyyar in saka kati in kira ki. Me ya hada Saghir da Diyam da tsohon saurayin ta kuma? Tun jiya naji ana ta maganar a gidan nan ni dai ba'a yi min cikakken bayani ba amma na fahimci kamar ko sunyi rigima ne harda su yan sanda" inna tace "Saghir din yazo gidan kenan" Hajiya Yalwati tace "yazo gidan fa, jiya nan ya kusan wuni sai dare ya tafi".


Tunda suka gama wayar Inna ta zauna ta zabga tagumi, sai ajima tayi ajjiyar zuciya ta sake wani ragumin duk tabi ta damu kanta. Nima kuma na damu din amma ba kamar inna ba, ni damuwata shine bansan zurfin sharrin da Saghir yake shirya min ba. Muna zaune kuwa, Asma'u ta kawo mana lunch kenan sai gasu sunyi sallama. Na ajiye spoon din abincin kawai na fara ambaton Allah dan ji nayi zuciyata kamar ta dawo wuyana.


Daya bayan daya suka shigo palo, Alhaji Babba, Kawu Isa, sai kuma Saghir. Inna ta tashi tana musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa ta suka zauna. Ta gaishe su babu wanda ya amsa mata, dan haka sai naja bakina naji shiru ban gaishe su ba kaina a kasa. Kawu Isa ne yayi magana "gamu munzo Amina, mun sauke girman mu mu da muke manya munzo mun same ki tunda haka kike so. Kin bamu kunya Amina, Allah yaji kan hardo da inno, Allah yaso ba zasu ga wannan rana ba ba zasu ga wannan bakin ciki ba na abinda suka raina suka rike kamar abinda suka haifa kuma yazo yana yi musu bita da kulli. Amina yanzu ke wato duniya ta bude miki ido ko? Yanzu wato kudi sunfi miki yan uwanki ko?" Nace "Kawu...." Inna ta daga min hannu tace "kar ki sake inji bakin ki" sai ta juya tace "hamma kudi ba komai bane ba akan zumunci da halacci. Amma yanzu ni me nayi da har kake cewa na zabi kudi?" Alhaji Babba yace "me kika yi?" Ya nuna ni yace "wannan bata gaya miki abinda ya faru ba?" Inna tace "ta gaya min, ta gaya min komai har dukan da Saghir yayi mata da barin da tayi ta gaya min" Kawu yace "kuma ta gaya miki labarin cin amanar Saghir din da take yi tare da wannan tsinannen yaron? Ko kuma dama kin riga kinsan wannan labarin?" Inna ta girgiza kai tace "shi Saghir din ne yace Diyam tana cin amanar sa da Sadauki? Zai iya rantsewa da Allah cewa ya gansu suna cin amanar sa? Ko kuma zai iya rantsewa cewa sakon daya gani a wayarta ya nuna wata alama na cewa suna cin amanar sa" Alhaji Babba ya dubi Kawu Isa yace "kaji ba? Na gaya maka dama ta sani sarai. Da hadin bakinta ne akeyi komai. Ba dai yaron yayi kudi ba? Ni kuma na talauce" Inna tace "in kuka ce haka baku kyauta min ba. Yaron nan, duk cikin ku babu wanda ya kuntata rayuwarsa kamar ni. Tun yana cikin zanin goyonsa bana binsa da komai sai harara da muguwar magana amma me? Shine ya dauke ni a lokacin da Saghir ya watsar dani. Ya baku labari? Naje gidansa duba Diyam ya kore mu ni da Asma'u cikin dare ana ruwan sama. Badan Allah ya bude mu ba badan Allah ya kawo mana Sadauki ya taimake mu ba da yanzu babu Asma'u a duniya. Sadauki ne ya taimaka mana. Tun daga ranar kuma nayi nadama mai tsanani na kuma yi alkawarin yin rikonsa tamkar yadda zanyi rikon dana. Wannan ne yasa tun ranar da Diyam tazo min da maganar na kira shi nace ya sa a saki Saghir, sannan kuma na zauna ina jiran shi Saghir din yazo yayi min nasa bayanin inji" Kawu Isa yace "to mu yaje yayi mana bayani, ya gaya mana komai har yadda shekara da shekaru Diyam take tare da tsohon saurayinta, ta saka ya bashi aiki dan suji dadin cin amanar sa, yanzu kuma mun kuma tabbatar cewa duk abinda ake yi da sanin ki Amina. Wato ke naki salon sakayyar kenan a bisa dukkan alkhairan mu a gareki ke da yayanki. To gasu nan mun bar miki su, gaki nan ga duniyar nan ga kuma Sadauki nan. Ba dai kudi ba? Kamar yadda nawa ya kare haka nasa shima zasu kare sai kuma muga wanne sarkin za'a bi. Saghir dai kam ya gama auren Diyam. Dama tursashi muka yi ya aure ta ba'ason ransa ba saboda muna son mu karfafa zumunci da iyalin dan uwanmu kuma muna so mu rufa muku asiri. Taje ta auri Sadaukin mu gani, ba dai mune masu daurin auren ba?" 


Na dago kai na kalli Saghir wanda tunda suka shigo yake tsaye a bakin kofa ya rungume hannayensa ya zuba min ido, ina jin idonsa a kaina amma ban kalle shi ba har saida Alhaji ya gama maganar sa sannan na kalle shi.


Sai ya tako yazo gabana ya durkusa yana kallon cikin idona yace "tunda nake a rayuwa ta ba'a taba yi min wulakanci irin wanda akayi min akan ki ba Diyam. Zan rabu dake, amma ba wai dan na hakura na yafewa Sadauki abinda yayi min ba sai dan wadanda suka ce in aure ki sun ce in sake ki. Na sake ki saki daya." 


Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya mike da sauri. Har yakai bakin kofa kuma sai ya dawo yasa hannu ya dauke Subay'a da take kwance kan kujera tana bacci ya dora a kafadarsa ya yi waje. Na mike da sauri kamar wadda aka mintsina nace "Saghir ka bani yata" ya juyo yace "in da ita kika je gidan ba sai ki karbeta ba in gani?" Na bi bayansa da sauri. "Ka bani yata Saghir, Subay'a! Subay'a!" Sai ta farka firgigit a hannunsa ta sauke idonta a kaina. Ganin ina kuka yasa itama ta saka kuka tana miko min hannu "Mommy! Mommy" yana fita waje ya saka ta a mota ya rufe ya shiga da sauri yaja ya bar gidan tun kafin su Alhaji su karasa fitowa".

[2/22, 9:21 PM] Ummy Gugah LING: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty: The Utterance 2


Assalamu alaikum my dear fans. Baki ba zai iya bayyana muku irin godiya ta a gare ku ba a bisa karbuwar da littafi na ya samu a zukatan ku. Nagode Nagode sosai kuma nima ina sonku a duk inda kuke.


A duk lokacin da marubuciya ta dauki biron ta dan rubutu, to tabbas da akwai wani topic a ranta da take son yin rubutu a kansa. Dan haka duk abinda zata rubuta will be akan wannan topic din. Sanda nayi niyya kuma na fara rubuta Diyam abinda yake raina guda biyu ne, na farko shine illolin auren dole na biyu kuma karfin soyayya ta gaskiya. Dan haka duk abinda nake rubutawa akan wadannan abubuwan ne.


So aim din bawai na koyawa mata yanda zasu gyara aurensu bane ba, aim din na nunawa iyaye da sauran al'umma illar auren dole ne. Allah yasa za'a fahimci manufa ta, ba wai ina nufin rayuwar da Diyam tayi a gidan Saghir itace dai dai ba, a'a, ina nuna akwai possibility na samun irin wannan rayuwar a auren da aka gina shi da tubalin kiyayya. 


A kodayaushe rubutu na is open for corrections, criticism and suggestions. Duk abinda ka gani wanda kake ganin ba dai dai bane ba zaka iya tuntubata ka nuna min ko kayi dropping comment yadda zamu hadu mu tattauna har a samu fahimta. Amma kuma, ita fahimta hausawa sunce fuska ce kowa da irin tasa.


Godiya ga wata baiwar Allah data yi min wani gyara a last episode, akan maganar da nayi ta cewa "nothing gives a man the right to hit his wife" what I should have said a gurin shine "nothing gives a man the right to hit his wife the way Saghir did" saboda munsan cewa an bawa maza damar horon disobedient wife da bakin sutturar su, shima kuma sai akace kar su taba fuska. Nagode baiwar Allah duk da bansan sunan ki ba. Lol


Kar in cika ku da surutu, ga Diyam...........

Na tsaya a gurin tamkar wadda aka dasa ni, ina kallon bayan motarsa, ina nan tsaye su Alhaji Babba suka fito suka shiga motar Kawu Isa suka tafi ba tare da sun ko kalli inda nake tsaye ina kukan rabani da yata ba. Asma'u ta fito da tazo ta kamani "Adda kiyi hakuri kizomu koma gida, ki rabu dashi yayi ta tafiya da ita din, Allah zai baki wadansu kuma ita din ma da kafafuwanta zata dawo gurinki" ta kama ni muka shiga ciki. Muka tarar da Inna ta zabga ragumi idonta yayi ja, Asma'u tace "dan Allah Inna kar ki wani tayar da hankalin ki, ance musu in babu su ba zamu iya rayuwa ba ne ba? Ai mu kwallon mangwaro muka yar muka huta da kuda wallahi. Da auren Saghir ba gwara babu ba?" Inna tace "hmmm. Asma'u ke yarinya ce. Ba zaki gane ba".


Ni dai sai na wuce su na shiga daki na zauna a bakin gado. All I have ever wanted tun da aka daura aurena da Saghir shine inji sanda zai furta da bakinsa yace ya sake ni. To gashi na samu amma kuma yanayin da sakin yazo min sai yasa naji sam banji dadinsa yadda nayi tunanin zanji ba. Hakan kuma yana da dangantaka da abubuwa da dama. Na farko zargin da Saghir ya sake ni saboda shi, wanda kuma ba gaskiya bane ba, na biyu zumunci daya karasa lalacewa tsakanin mu da yan uwanmu, na uku Subay'a I can't even imagine yadda rayuwar Subay'a zata zamo a gidan Saghir ba tare dani ba. In banda mutuwa menene yake raba uwa da yar karamar yarta? Amma ni gani a raye amma an raba ni da tawa yar. And I asked myself then, shin Saghir yana da wannan damar?


Ranar haka na karasa wuni raina babu dadi. Da nazo sallah kuwa ina dora goshina a kasa sai kuka, zuciyata ta cunkushe gabaki daya, na idar na daga hannuna da niyyar yin addu'a amma sai na rasa me zan roka kuma. Sai kawai na roki Allah daya dubi zuciyata tunda ya fini ni kaina sanin abinda yake cikin ta, na roke shi ya daidaita min lamurana zuwa ga abinda yake shine dai-dai bawai abinda ita zuciyar tawa take so ba, ya saka rabuwar nan da mukayi da Saghir ta zamanto mafi alkhairi a gare mu baki daya, sannan ya bayyana gaskiya ya goge zargi ya kawo daidaito tsakanin mu da yan uwan mu. Na kuma roke shi daya kasance tare da Subay'a a duk inda take.


 My life had been full of challenges so far, na fuskanci kaddarori iri iri wadansu naji dadin yadda na dauke su wasu kuma I have made a total mess of them. Amma a cikin regrets dina babu rabuwa da Saghir, na daiyi regretting irin zaman da mukayi amma banyi regretting kuma bana jin zanyi regretting zama na dashi. For more than eight years muna tare dashi amma dai dai da rana daya ban taba jin zuciyata tana sonshi ba, ko da kuwa a cikin ranakun da yake kyautata min ne sai dai inni kiyayyar sa ta dan kwanta min amma ba dai ta tafi ba ballantana sonsa ya shiga. Nayi addu'ar kuma kullum, kullum nayi sallah sai nayi addu'ar idan zamana da Saghir ne mafi alkhairi Allah ya rage min kiyayyar sa a zuciya ta. Dan haka da akayi rabuwar sai nayi taking that as shine zabin Allah kuma ma roke shi ya cigaba da zaba mini.


Na fara zaman iddah a nan gaban inna, ba inda nake zuwa sai kewayen maman iman sometimes inyi kallo musamman in Asma'u ta tafi makaranta, sometimes kuma in zauna anan dakin Inna inyi ta karatu wanda shine yake kara nitsar min da zuciyata ina jina ina zama at ease. Inna ta gayawa Mama abinda ya faru, kuma tazo har gida ta ganni ta kuma yi min nasihohi sosai akan karbar kaddara da kuma shirin facing rayuwar da zata zo min. Tace "in kin gama iddah Diyam makaranta zaki koma. Kar ma kiyi tunanin aure gwara kiyi karatu ki huta kema jini ya dawo jikinki sosai. Sannan ki samu exposure. Kuma ki koma islamiyya ki karasa saukar ki dama kin kusa ko?" Na daga mata kai, tace "sai ki karasa kuma ki fara hadda, ki cigaba da bin sauran littattafan addini suma kina kara buda kwakwalwar ki" nace "insha Allah Mama". Washegari sai ga Rumaisa amarya tazo gurina. Muka wuni tare muna ta hirarrakin mu sai naji hankalina ya kwanta sosai.


Monday Sadauki yazo kamar yadda ya saba zuwa. Last Monday bai zoba ya kira Inna yace wani issue ne ya rike shi a Maiduguri amma tayi hakuri. Wannan Monday din kuwa tun safe naga tana ta ha蓷a masa kunun aya wai taga yana so, ta dama masa fura itama ta saka a fridge ni dai ina ta kallonta. Yamma tana yi, dama nasan da yamma yake zuwa sai na saka hijab dina na tafi gurin Maman iman muka kafa hirar mu. Bana son ganinsa yanzu kuma nasan kona zauna a cikin daki in yazo sai Inna tace in fito in gaishe shi. Amma muna zaune kawai sai ga baban iman da baki sunzo, dan haka dole nayi musu sallama na fita na koma gurin Inna. Ina shiga naga takalmin namiji a kofar palo, sai na jawo farar kujera na zauna a tsakar gida amma ina zama inna ta kira ni, na bata rai kamar zanyi kuka na tashi na shiga. Yana zaune a kasa, Asma'u kusa dashi da wata takarda a hannun ta tana nuna masa wani abu suna magana a nutse. Ga kunun ayansa nan a cup a hannunsa yana sha. Na zauna a gaban Inna nace "sannu da zuwa" ya dago ya min kallo daya ya mayar da kansa yace "sannu maman Subay'a" sai ya cigaba da yiwa Asma'u bayanin wanda na fahimci kamar takardar jamb ce take kokarin cikewa. Na mike na shiga daki nayi kwanciya ta. Sai naji Inna tace masa "Diyam fa sun rabu da Saghir" naji yace "rabuwa Inna" cikin mamaki, Inna tace "rabuwa fa, ya sake ta" yayi dan shiru sannan yace "ya Salam. Subhanallah. Abu baiyi kyau ba. Allah yasa hakan shi ya fi musu alkhairi" Inna tace "ameen" Asma'u tace "ai rabuwar ma itace alkhairi hamma, wannan auren na Adda ai dashi gwara babu" Inna tace "rufe min baki sarkin magana. Waye ya tambaye ki? Tashi ki fita" ta tashi ta fita. Sadauki yace "na dauka ai ko ganin ku tazo yi" Inna tace "uhm uhm, ai satinta biyu kenan anan. Tun sanda nayi maka wayar nan ai bata koma ba dama. Nan yazo har gabana ya sake ta yasa hannu ya dauki yarsa" yace "Subay'a? Ita ta bashi ita ko kuma shine kawai ya dauke ta?" Inna tace "ina kuwa zata bashi ita? Gata nan tunda ya dauki yarinyar nan kullum sai na ganta tana kuka kuma nasan kukan yarta take yi amma ya zanyi?" Yace "a'a in dai ba ita ta bashi ita ba to zata iya karbar yarta. Ai both islamically da constitutionally bashi da right din daukar yarinyar" Inna tace "to ta yaya za'a karbo ta kenan?" Yace "ba wahala ai. Ko hisba akaje akayi reporting zasu karbo yarinyar a hannunsa su kawo mata" Inna ta jinjina kai tace "mutanen nan sunyi mana ba dai dai ba daga ni har yaran nan, amma yanuwan mune. Bana son cigaba da rigima dasu so nakeyi a samu fahimta a tsakanin mu. Amma zabin Diyam ne" sai ta saka baki ta kira ni. Na gyara hijab dina na fita, sai na ganshi a zaune yana daddanna waya kamar ba shine yanzu suke magana rai rai da Inna ba, na zauna a gabanta nace gani, tace "Sadauki yace za'a iya karbar Subay'a a hannun Saghir in aka gayawa hisba. Kina so a karbo miki ita?" Na juya na kalle shi busy with his phone, at least a matsayin da yake dashi na yayana da muka tashi tare kuma Inna ta bashi wannan labarin ai ya kamata ko magana mai dadi ce yayi min, sai na dauke kaina nace "ina son karbar Subay'a Inna, kuma zan karbo ta insha Allah amma bana bukatar taimakon sa. I can do it on my own" sai naga yayi sauri ya dago kai yana kallona. Yace "how?" Nace "ba kace hisba ba? Ai nasan hanyar hisba din kuma ina da bakin da zanyi musu bayani in naje" Na daga kafada na mike na komawa ta daki.


Daga nan babu wanda ya sake maganar karbar Subay'a ni kuma kullum yarinyar tana raina, kullum zan kwanta bacci sai nayi tunanin ko tayi bacci? In ina cin abinci sai na tunanin ko taci in na tashi da safe sai nayi tunanin ko an tashe ta an shirya ta zuwa makaranta? Kullum kuma a kowacce Sallah sai nayi mata addu'a amma kuma kamar yadda Inna ta fada bana son cigaba da rigima dasu Alhaji Babba, so nake a samu daidaito. Amma daidaiton da baiyi involving komawa ta gidan Saghir ba.


Lokaci ya cigaba da tafiya, har nayi wata biyu a gida. Duk sati ranar Monday sai Sadauki yazo gidan da yamma, in kuma ba zai samu zuwa ba to zai kira Asma'u ko Inna yace musu ba zai zo ba amma ni ko zuwa yayi gaisuwa ce kawai a tsakanin mu, sai sometimes ya kan tambayeni ko da abinda nake so to which I always reply "babu komai. Nagode".


Su Alhaji basu sake kallon inda muke ba ballantana Saghir. Ni kuma sosai na kwantar da hankali na babu abinda yake damuna sai kewar Subay'a. Har yar kiba ta nayi na kara haske. 


Ranar nan na hada kayan Subay'a da muka taho dasu gidan, nima kuma ina bukatar kayan amfani dan wadanda nazo dasu sunyi min kadan ga kuma har phone dita tana gidan Saghir. Amma sam bana son zuwa gidan Saghir, duk kuwa da cewa ina son ganin Subay'a amma bana jin zan iya taka gidan dan haka sai na bawa Asma'u ta kai mata sannan na lissafa mata abubuwan da zata dauko min kafin a debo kayana. Tunda akayi sakin inna take cewa za'a debo kaya amma jin su maman iman suna shirin tashi saboda sun kammala ginin su yasa Inna tace a bari sai sun tashi tukunna saboda a samu gurin ajiye kayan.


Asma'u ta shirya taje ta dauko min duk kayan da nake bukata, amma sai tace min Subay'a bata gidan, daga alama gurin Hajiya Babba ya kaita. Sai na fara tunanin to chanza mata school yayi ko kuma dai tana gida kawai? Sai kuma tace min Fauziyya tace in na kunna waya ta zata kirani. Kuma ta bani labarin cewa "kinga gidan nan kuwa Adda? Gaba ki daya ya lalace har wani karni yake marar dadi. Kayanki kuwa in ba'a je an debo su ba to kuwa sai dai a wuce dasu bola. Na tarar da Saghir a gidan ma, yana kwance a palo ni ko kallon sa banyi ba na shiga na dauko abinda zan dauko na fito".


Da yamma nayi charging wayata da daddare kuma na kunna. Fauziyya ta kirani few minutes after na kunna. Muka gaisa tace "Halima yanzu wai da gaske ba zaki dawo ba?" Nayi dariya nace "my fight is over Fauziyya. Na gama. Bai gaya miki ya sake ni ba?" tace "ya gaya min amma ai saki daya ne dan haka akwai chance na zaki dawo din. Ya gaya min komai bayan kin tafi, kuma ni zanji dadi in kika dawo gidan nan. He loves you da gaske, in ma da baya sonki yanzu gaskiya yana sonki. Ya gaya min dalilin da yasa ya aure ni. Ni kuma na aure shine saboda ina son inyi settling down sai yazo da maganar aure ni kuma na karba. But a yanzu halin da yake ciki bayan tafiyarki I don't think Saghir is the right person to settle down with. Sun daura abota shi da shaye shaye. Most of the time ma baya kwana gida, kullum masifa kullum zage zage. Shi ne na kira in gaya miki, for the sake of your only daughter ki dawo maybe zai dawo hankalinsa in kina nan". 


Nace "kiyi hakuri Fauziyya, but kamar yadda na fada miki. Na gama. For more than eight years nake tare da Saghir amma babu abinda muka tsinta a ciki auren mu daga ni har shi in banda wahala. Rabuwar insha Allah itace alkhairi. And kar kice baya sonki, tunda har ya zabeki a cikin sauran mata ya aure ki to kuwa tabbas yana sonki. Ki ci gaba da kokarin ki, it will be okay with you insha Allah".


And then one day, lokacin har nayi period biyu ina jiran daya. Monday, ranar da Sadauki yake zuwa sai Rufaida tayi rashin lafiya dan haka Mama ta tafi dubata ta barmu gida ni da Asma'u. Ni nama manta ranar Sadauki yake zuwa dan haka ina zaune a palo ina kallon wani film din hausa da na aro a gurin maman iman kawai sai jin sallamar sa nayi. Na tashi zaune sosai na gyara hijab dina sai gasu sun shigo shida Asma'u tana ta zuba masa surutu shi kuma yana mata dariya. Ya zauna ta gaishe shi ya tambaye ta ina Inna ta gaya masa bata nan. Sai ya dafe kai "kash, yau kice bani da kunun aya kenan" Asma'u tace "lah, sai da tayi maka ai kafin ta fita" sai ta tashi ta dauko masa ta zuba masa yana sha sannan na gaishe shi "sannu da zuwa. Ya office?" Ya kalle ni yace "yauwa. Lafiya lau" and that was all. Naji wani makokon takaici ya tokare ni. It really does hurt to be ignored, especially by someone da kuka saba sosai. 


Sai kawai na kara volume din kallo na a raina ina fatan karar zata dame shi ya tashi ya fita amma sai ma naga sun dauko takardu shida Asma'u suna dubawa suna ta magana, kallo nake amma hankali na yana kansu sai na fahimci maganar ssce suke yi tana cewa "ni dai dan Allah hamma ka cire ni daga makarantar mu ka saka ni a government school in yi exams dina a can, wallahi government anfi ci, private basa bayarda da amsa" yarike baki "au kenan amsa kike so a baki? Maimakon kiyi karatu kici da kanki?" Tace "chaf, wadanda ma suka fini kokari basa ci ballantana ni? Yanzu kuma kaga in banci ssce din nan ba jamb dina ta tashi a banza kenan fa sai na sake wata" yayi dariya yace "kinsan kuwa sau nawa na zana jamb? Kuma a karshen karshe dai ban samu admission din dana ke nema ba" sai ta juyo ta kalle ni tace "Adda kema da kin sani kin cike form din jamb din. Kinga sai muyi tare in ba haka ba sai next year kuma" nayi kamar ban jita ba sai naji yace "in kina so sai a kawo miki gobe" na juyo na kalle shi naga yana kallona sai na kalli sides dina kamar me neman wani abu sannan na nuna kaina nace "are you talking to me?" 


Sai yayi kamar zaiyi dariya amma ya wani maxe ya dauke kai yace "kina so ko ba kya so?" Nace "ina so, amma karka wahalar da kanka gurin kawo min, zan kira yaya Mukhtar ince ya siyo ya kawo min" ya daga kafada yace "duk daya. Tunda kinci waec dinki ba sai kin sake ba" sai na kalle shi da mamaki, I don't remember telling him cewa nayi waec ballantana zancen naci, nace "ya akayi kasan naci waec?". Sai kawai ya zauna yana kallona. And then all of a sudden sai ganin Saghir mukayi ya shigo palon hannunsa rike da Subay'a. He looked at me then at Sadauki and then at me again. Subay'a ta saki hannunsa ta taho gurina da gudu na bude hannuna na rungume ta ina jin dadi har cikin raina. 


Saghir yace "what the f....." Sai nayi sauri na mike nace "Asma'u dauki Subay'a ku fita" dan nasan halin Saghir zai iya fadin komai ko yin komai a gaban Subay'a shi babu ruwansa. Ai kuwa tun kafin su fita ya fara "wato na matsa na baku dama ko? Shine wato zaku cigaba daga inda kuka tsaya? Ba kwajin kunyar duniya ba kuma kwajin ta Allah ko?" Sai Sadauki ya gyara zamansa ya dora kafa daya akan daya yayi folding hannunsa yana kallon Saghir. Ni kuma sai na mike, gabaki dayan su basa gabana dan haka baxan tsaya su bata min raina a banza ba. Nazo zan wuce Saghir ya kamo hannuna "ina zaki je? Munafuka kina wani saka hijabi kamar mumina" nayi kokarin kwace hannuna nace "don't touch me" ya maimaita "don't touch me, don't touch me kullum don't touch me." Sai ya juya yana kallon Sadauki yace "but I did touched her. Dan haka gwanjo nace. Duk inda zaka shiga babu inda ban shiga na fita ba and I left my foot print there" raina ya kai kololuwar baci, ban ma san me zance ba sai ji nayi Sadauki ya danyi dariya yace "are you sure about that?" Na kama kokawar kwace hannuna daga rikon Saghir zuciyata tana tafasa, zan so ace na fisu karfi in hada su duk su biyun inyi ta duka, how dare they talked about me like that.


Saghir yace "of cause am sure kasan a ledarta na bare ta. Sabuwa fil aka kawo min ita and I took her virginity" I froze. What? Ba zan ma iya kallon side din da Sadauki yake ba amma sai naji yace "ita nake so, not her virginity so...." Na kwace hannuna da sauri nayi bakin kofa hawaye yana bin fuskata, kafin in fita Saghir ya finciko hijab dina ya dawo dani cikin palon, ya hada ni da jikinsa muna facing Sadauki, Sadauki ya mike tsaye, Saghir yace "me yasa zaki gudu ne? Dan ke fa ake wannan taron ai ya kamata ki tsaya ki saurara kema ki tofa albarkacin bakinki a ciki. For example, tell him about our first night, tunda yace bai damu ba tell him how I did it maybe zai damu" na fara girgiza kaina da sauri. It is either Saghir is drunk ko kuma kwakwalwar sa ta fara tabuwa. And he said it. "I raped her" and then I saw a flash of fire a idon Sadauki. Saghir ya sake maimaita wa "I raped her the first night da aka kai min ita gida na. That was how she got pregnant for me har ta haifa min twins". 


Sadauki took one step sai nayi saurin kwace jikina daga Saghir na tari gaban Sadauki na daga masa hannu "don't. Kar kace wani abu kar kayi wani abu just go" Saghir yace "yeah. Just go. But before you go, listen to this. Na mayar da ita dakinta." Na juyo da sauri ina kallonsa zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina nace "no, no" yace "yes. Na mayar dake tunda dama saki daya nayi miki kuma shima bada son raina ba. Na mayar dake saboda ina son ki sannan kuma saboda I want him to think of you every night of every day when laying on his empty bed har zuwa ranar da zaki bar duniya ko kuma shi zai bar duniya. Sai inga karshen soyayya".


Inna ce ta shigo dakin da sauri, daga alama taga motocinsu a waje kuma tayi sensing something is wrong. Tana zuwa bata ce komai ba sai ta kama hannun Sadauki ta ja shi da sauri ta fitar dashi daga palon. Kafin su fita ya juyo ya kalleni and I saw a look on his face similar to wanda na gani ranar da zamu rabu a gidan Alhaji Babba. Na juya da gudu na shige bedroom din Inna na rufe kofa.

[2/23, 9:26 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty One : The Will


A jikin kofar na zame na zauna ina jin zuciyata tana wani irin bugawa, ji nake yi kamar zan mutu, kaina yayi wani irin zafi kuma hawaye ya tsaya a ido na. Ban taba tunanin it's possible ka tsani mutum kamar yadda naji na tsani Saghir a lokacin ba. Na fara girgiza kaina ina cewa "no no no" kamar mahaukaciya. I can't even imagine komawa gidan Saghir a matsayin mijina, I can't imagine him touching me again. I would rather die. Ina jiyo maganganu a palo kamar muryar inna amma bana gane me take cewa, sai naji ta taba kofar amma da yake ina jikin kofar sai ta kasa bude wa sai naji tana kiran Asma'u. Sai kuma naji ana knocking kofar. Da kyar na bude idona na matsa daga jikin kofar sai suka bude suka shigo su biyu sannan Subay'a ta shigo itama tana kallo na sai naga Asma'u tayi sauri ta dauke ta sun sake fita.


Inna ta durkusa gabana tana taba wuyana tana magana a hankali amma ni bana jin ma me take cewa. Sai kuma naga ta kama ni ta mayar dani kan gado ta kwantar dani ta juya na riko rigarta sannan cikin muryar da naji kamar ba tawa ba nace "Inna bazan koma ba. In na koma mutuwa zanyi" ta juyo tana kallona sai ta zauna tace "komawa ina?" Sai kawai na bita da kallo, wato Saghir saboda bai daraja ta ba bai ma gaya mata cewa ya mayar dani ba? Sai ta gane me nake nufi tace "cewa yayi ya mayar dake?" Ban iya bata amsa ba sai kuka, sai ta mike tsaye "wannan wanne irin abu ne? Wanne irin ya mayar dake kuma? Suzo nan su kare mana cin mutumci sannan kuma ya mayar dake bayan babu wani mataki da aka dauka? To babu inda zaki koma. Yanzu fa Hafsa take bani labarin wai kawun ku Isa ya bashi Suwaiba" Suwaiba yar kawu Isa ce itama kuma kusan set din mu ce, mun dan girme ta kadan. Lokacin muna yara ita da Rumaisa ne suke crushing on hamma Saghir, murja tana yawan gayamin cewa har yanzu suwaiba tana son Saghir amma ni ban taba ko saka abin a raina ba. 


Inna tace "wato su suna can suna kokarin yi masa huce haushi shine shi kuma zai zo nan yace ya mayar dake? To ku biyu yake so ya hada a gida daya ko kuma ya yake so ayi? Ai indai kinga kin koma gidansa to ki tabbatar an zauna ne an hada ku anyi muku fada kowa an bashi laifin sa bawai kullum ace kece da laifi ba" tayi ta fadanta ni dai ina jinta kawai. Amma ni a raina nasan ko anyi mana fadan bana jin zan iya sake zama da Saghir, not after what he did today, not after what he said a gaban Sadauki.


Tuni da Sadauki da nayi sai naji wata irin fargaba ta shige ni. Tsoro nake ji sosai, tsoron abinda Sadauki zai iya yi akan furucin da Saghir yayi a gaban sa. Ina tsoron zuciyar Sadauki, ina tsoron zafin sa, ina tsoron rashin tafiyar sa, considering abinda yaji da kuma yanayin da ya fita a ciki, bansan hukuncin da zai dauka ba. Sai na samu kaina dayi masa addu'ar Allah ya taushi zuciyarsa Allah ya hane shi ga aikata abinda zaizo yayi nadama. 


Sai magrib na tashi. Nayi alwala nayi sallah nayi kuka sosai a cikin sujjada ta na roki Allah ya kawo haske a cikin al'amura na. A lokacin ne Asma'u suka dawo ita da Subay'a. Subay'a ta taho gurina da gudu ta fada jikina tana kallona tace "Mommy kin daina kukan? Dazu naga kina kuka" nace mata "na daina subis" sai tayi dariya tace "Daddy ya tafi ko? Dama cewa yayi zai kawo ni gurinki in kwana biyu sai mu koma gidan mu tare" bance komai da akan wannan sai tace "Mommy kullum sai nayi kuka nace da Hajiya ta kawo ni gurinki ita kuma taki. Mommy dan Allah ni kar a mayar dani can gidan gwara in zauna a gurin ko kuma mj koma gidan Daddy na tare" sai na daga ta nace taje tayo alwala tayi sallah. 


Na lura ta rame, ta fada sosai tayi baki. Kamar ba'a kula da tsaftarta sosai sannan idonta ya nuna alamar damuwa. Sai na yanke wata shawarar, bawai ni kadai ce bazan koma gidan Saghir ba har da Subay'a ma ba zata koma ba, tazo kenan. 


Da dare ina jin Inna tana cewa Asma'u ta kira mata Sadauki, kamar tasan ina son in tabbayda lafiyar sa. Asma'u ta kira switched off, a raina nace nasan za'a rina, amma ban furta komai ba nayi shiru kawai. Nan fa hankalin Inna ya tashi tace "wai me ya faru ne mai zafi a tsakanin su? Ni sam banji dadin yadda naga Sadauki ba tunda kuma ya fita hankalina yana kansa wallahi" ta juyo tana kallona tace "me Saghir din ya gaya masa me zafi haka?" Na sunkuyar da kaina kawai, ni ba zan iya gaya mata kalaman Saghir ba. Jin nayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "Allah ya kyauta".


Washegari babu kunya babu tsoron Allah sai ga Aunty Fatima nan da Hajiya Yalwati da kanwar Hajiya Babba wai Alhaji Babba ya turo su su gaya wa Inna cewa Saghir ya mayar dani, a gaya min in shirya sai mu saka rana ni da Saghir din sai yazo ya dauke ni. Ni kawai kallon su na tsaya ina yi cike da mamaki. Inna tace "yanzu Fatima har da ke? Har dake za'a ci amanar marigayi dan bashi da rai?" Aunty Fatima tace "me akayi Amina? Yanzu mayar da auren shine cin amana?" Inna tace "ba mayar da aure ne cin amana ba, rashin kulawa da nuna son kai shine cin amana" sai ta lissafa musu dukkan laifuffukan Saghir wanda ni na gaya mata tace "ni ba wai goyon bayan Diyam nake yi ba ko kuma bana so ta koma dakinta ba, a'a, so nake a zaunar da Saghir shima ta fadi laifin Diyam din sai a hada su kowa ayi masa fada a bashi laifin sa. A ja masa kunne akan dukanta dan ni abinda yafi komai daga min hankali kenan" sai Aunty Fatima ta nuna itama bata ji dadin abin ba tace "ni duk fa bansan wannan ba, ni cemin sukayi Diyam tana kula Sadauki shi kuma Saghir yaji haushi ya saketa. Kema yadda muke dake ai kamata yayi duk abinda ya faru ki kira ni ki gaya min. Da Diyam da Saghir duk yayana ne ai". Amma ita kanwar Hajiya sai ta kama fada, ita wai lallai nayi wa Saghir sharri "babu wani shayeshaye da yake yi balle neman mata" sukayi ta bugawa da inna har tayi zuciya ta tashi ta tafi Aunty Fatima ma ta tafi sai Hajiya Yalwati ta zauna tace sai anjima zata taho. Daga jin haka nasan tsegumi ta zauna yi. 


Tace "wallahi Amina karki mayar da yarinyar nan. Yaron nan fa bawai gyaruwa yayi ba. To yaron da baiji kan iyayensa ba ina zaiji kan wani. Shaye shayen nan fa munsan yanayi amma sai a rufe ido ace bayayi. Neman matan nan kuwa yinsa yake yi kamar babu gobe. Ita kanta Fatima da take wannan maganar rannan a gaba na naji tanayiwa Minal yarta fadan kar ta kuma kula shi. Dama Suwaiba ce tasa kuma yanzu sunce sun bashi dan haka ku rabu dasu, in dai abinda Diyam ta fadi gaskiya ne in ya auri Suwaiban ai zasu gani" Inna tace "za kuwa su gani. Ai ni zanso ayi auren nan ma ko dan gaskiya ta bayyana" Hajiya Yalwati tace "gaskiya kam zata bayyana. Tun yanzu ba gashi nan muna gani yana zuwa yana daukan ta a mota ba? Ahau, lokaci kadai muke jira".


Har tana shirin tafiya kuma sai cewa tayi "ni Diyam kuma ta wani zubin banji dadin tahowar nan taki ba. Dama ke ce mai dan saka shi yana dan kawo mana abinci gidan. Yanzu kuwa shiru. Rannan har ya fara zancen aurar dasu murja yanzu kuwa yadda yake a rikicen nan nasan ba lallai ne yayi ba". Inna ta dauki yan kudade ta bata tace ta siyawa yara sabulu.


Da dare sai ga wayar Saghir. Na kalli wayar kawai na dauke kai. Yayi ta kira sai na saka a silent sai ya turo min message "ki shirya. Rana ita yau zan zo mu tafi". Sai na kashe wayar gaba-daya na ajiye.


Washegari wai dan rashin kunya sai ga Hajiya Babba da kanta. Ina ganin ta nayi wa Asma'u text. "Ki dauki Subay'a ku bar gidan nan, sai na kira ki zaku dawo". Ina kallon su suka fice. Tazo ta saka inna a gaba "yanzu ya za'ayi ace kince ba zata koma gidan taba? Yanzu zumuncin kenan? Koma menene ya faru a tsakanin su shi ya hakura ita me yasa ba zata hakura ba?" Inna tace "tace ba zata koma ba. Ni kuma baxan matsa mata ba, matsantawar da nayi mata a wancan karon ma da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi ba". 


Sai ta kama hannuna ta jani daki muka zauna a bakin gado tace "yanzu Diyam ke kinsan halin Saghir. Kinsan cewa ya chanja sosai saboda ke kuma ya chanja din. Yanzu da kika barshi Diyam Saghir duk ya koma yadda yake da koma fiye da haka. Me yasa ba zaki je ki karasa abinda kika fara ba? Ko dan saboda Subay'a" nace "Hajiya Saghir fa ba wai chanzawa yayi ba. Indai har da gaske ya chanza bai kamata ya koma ruwa ba dan bana tare da shi. Hakan yana nufin saboda ni ya chanza kenan ba wai saboda kansa ya chanza ba. To yanzu kuma in mutuwa nayi fa?" Tace "a hankali ai yake gyaruwar, in kin koma zai cigaba da gyaruwa ne" nace "Hajiya tun farko ba kwa ganin kamar akwai son zuciya da zalunci a cikin dora mim alhakin gyaran Saghir? Ku da kuka haife shi baku gyara shi ba tun yana danyensa ta yaya zaku bani shi bayan ya bushe kuma ku saka ran in kare rayuwata gurin gyaransa?" Tace "saboda munsan zaki iya. Kin fara kuma zaki iya karasawa" na girgiza kaina nace "bazan koma ba Hajiya" tace "saboda me?" Nace "saboda bana son shi Hajiya" sai ta tsaya tana kallona. Sai na tuno da ranar da Saghir yazo gaban inna yace baya son aure na. Hajiya tace "ba kya son sa fa kika ce min Diyam. Yanzu har idonki yayi budewar da zaki kalle ni kice ba kya son Saghir? Koma dai menene Saghir din nan, koma da gaske ne maganganun da kike fada still Saghir dai danuwan ki ne kuma duk kin da kike masa ba zaki taba cire jinin ki daga nasa ba. Mijinki ne kuma, tunda dai yace ya mayar dake Sannan uban yarki ne, ba zaki taba chanja mata uba ba" nace "Allah zai raya ta ko ba a gidan sa ba" sai ta mike da fushi ta fita, ina jinta tana cewa da Inna ina Subay'a zata tafi da ita, sai inna tace "Diyam tace Subay'a ba zata koma ba. Zata rike yarta" nan tayi ta bala'i "wallahi bata isa ba, ita tace ba zata koma ba sannan yar tasa ma ta hana shi?


Da dare inna ta kuma saka Asma'u ta gwada number din Sadauki but still bata shiga. Inna ta kalleni tace "ke baki san inda yake zaune ba?" Na girgiza kai nace "ban sani ba Inna. Sai dai office dinsa na sani" Asma'u tace "ni dai nasan kamar a hotel yake zaune. Amma bansan wanne hotel din ba" Inna tace "to ko Asma'u zan tura office din nasa gobe ta gani? Ni duk zuciyata bata min dadi wallahi".


Washegari Asma'u tana dawowa daga school sai gashi ya kirata. Tace "Inna ga hamma yana kira" Inna tace "to kiyi sauri ki dauka mana kar ta katse kuma? Alhamdulillahi" Asma'u ta dauka tana gaishe shi sai naga ta kalleni tace "tana nan" sai kuma ta mike zata fita, Inna tace "ina kuma zaki je?" Sai Asma'u ta daga mata hannu ta fita kawai. 


Shiru shiru, ni dai ina zaune a kan kujera staring into nothingness har Asma'u ta dawo after like two hours. Ta zauna tace da Inna "yace ince miki yana lafiya kuma gobe zai shigo" Inna tace "shikenan? Duk wannan dadewar kuna waya shikenan abinda yace?" Asma'u tace "tambayoyi yayi ta yi min kawai. Akan Adda. Yanayin zamanta a gidan Saghir" Inna tace "ke kuma me kika ce masa?" Asma'u tace "everything. Duk abinda na sani na gaya masa sai dai kuma wanda ban sani ba. Abinda na fahimta shine duk shekarun nan shi ya dauka Adda lafiya take zaune a gidan mijinta" na dauke kai ina lissafin wanne ne abinda Asma'u ta sani wanne ne kuma wanda bata sani ba?


Washegari da safe muna breakfast yazo. Fuskarsa babu annuri ko digo a cikinta ya gaishe da Inna muma muka gaishe shi. Ya kalli Subay'a yace da inna "an dauko tane?" Inna tace "tunda uban ya kawo ta Diyam tace ba zata koma ba" yace "good. Ba zata koma ba. Ita ma kuma Diyam din ba zata koma ba sai dai in har ita ce take son komawar" ya juyo ya kalle ni yace "kina son komawa gidan Saghir?" Na sunkuyar da kaina ina girgiza kaina da sauri, yace "good. Then ki dauki wayarki ki kira shi. Ki gaya masa ba kya sonsa ba zaki koma gidansa ba. In yana son rabuwa ta arziki to ya kawo miki takardar ki within the next three days, in kuma ba haka ba kice masa zaki kaishi kara in yaso alkali ya raba ku".


Ya juyo yana kallon Inna yace "Baffa uba ne a gurina. Dan yadda nake jinsa a zuciyata har yafi yadda nake jin shi kansa wanda ya haife ni saboda Baffa ya bani abinda shi din bai bani ba. Baffa ya bani soyayya, ya bani kulawa, ya bani tarbiyya. And he used his last breath a duniya to tell me in kula daku, and that's what I have been trying to do, and that's what I will continue to do sai inda karfi na ya kare".

[2/24, 8:22 PM] Ummy Gugah LING: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty Two : A Little Game


Inna ta fara sharar hawaye, ita dama kwana biyun nan komai sai kaga ta fara hawaye. "Allah ya ji kan baffan ku. Babu abinda bai gaya min ba sai kace yasan abinda zai faru bayan babu shi. Abinda na wulakanta shine yanzu gatana ni da yayana, wadanda kuma na daukaka fiye da komai sune muka zama abin wulakanta wa a gurin su." Sai Asma'u ta tashi ta koma kusa da ita tana rarrashinta, Sadauki ya mike tsaye yana kallona yace "ki kira shi yau. Gobe ki gaya min yadda kuka yi dashi". Na gyada kaina sai ya juya ya fice. 


Ina kallonsu suka gama kukansu amma ni ko hawaye banji a idona ba, maybe ko kukan ya kare ne oho, nidai abu daya da na sani shine baxan koma gidan Saghir ba and that's final. 


Sai yamma na samu courage din kiransa. Bugu daya ya dauka yace "ha! Finally. Kin shirya inzo mu tafi?" Na lumshe ido na na bude, ina bitar abinda Sadauki yace min nace "ba wannan dalilin da yasa na kira ka ba. Na kira ne in tabbatar maka da abinda na gayawa Hajiya sanda tazo. Aure na dakai ya kare Saghir. Ba zan koma gidan ka ba saboda rabuwa a tsakanin mu tafi alkhairi akan zaman. Ina neman ka sawwake min. Ka kawo ko kuma ka aiko min da takarda ta nan da kwana uku in kuma ba haka I will have no other choice than in kai karar ka alkali ya raba auren mu" ya yi shiru amma nasan bai ajiye ba, sai yace "are you threatening me Diyam?" Nace "ba threat bane ba, option ne na baka kamar yadda nima Allah ya bani option na ko in hakura in zauna da kai ko kuma in kai karar ka in baka kudin yin wani auren kai kuma ka sawake min" yace "ohh, abinda ya tsara miki kenan ko? Abinda yace ki gaya min kenan? To ki bude kunnen ki kiji sosai nima nawa sakon zuwa gurinsa. Kice masa nace bazan sake ki dinba, idan akwai abinda yafi court ya kai ni can. Amma kafin ku tafi court din bara in fara gaya muku abinda zai fari a can din. Muna zuwa zan zayyana wa alkalin cewa shi wanda ya taimaka miki kika kawo karar tawa tsohon manemin ki ne, na kama ku na hana ku harka shine kuka yi deciding kawo kara ta saboda in sakar masa ke. How about that?" Nace "kai kanka da kake fadar maganar kasan cewa ba gaskiya bane ba. Kuma duk inda alkali yake ai mutum ne mai ilimi wanda zai zai saurari kowa. Ni fa 拼a ce Saghir ba baiwa ba, tunda nace bana sonka set me free please" yace "in nayi haka Diyam ai na bashi abinda yake so kenan, na baku abinda kuke so. Ni kuma nayi alkawarin tunda kuka making fool of me for years sai na dauki fansa. Plus wulakancin da yasa police suka yi min. So here is another message to him. Tell him nace I want my job back, I am kind of out of money yanzu. In ba haka ba kuma zan fara spreading rumors a cikin ma'aikatan sa, and this time around I won't be drunk yadda zanyi passing clear message har su fahimci wanene real Mr Abatcha, suma su fara boye matansu. Kuma harda gishiri zan kara wa maganar" ya karashe maganar yana dariya. 


Na cire wayar daga kunne na saboda yadda maganganun sa da dariyar sa suke kara huta ga already wutar da take ci a kirjina. Shin anya kuwa Saghir yana tsoron Allah? Shi karya bata yi masa wuya. Sanda ya dake ni a gida ya nuna yana zargina da Sadauki banji haushin sa ba kamar wanda naji akan maganganun da ya fada ranar nan akaina a gaban Sadauki, it shows cewa abinda yayi din ma bashi da remorse akan sa tunda har fada yake yi proudly a gaban third party. Yanzu kuma maganganun sa sun nuna min cewa ba wai ya mayar dani bane ba saboda yana son aurena ba, ya mayar dani ne to get back at Sadauki. Am not a toy, am a person with zuciya a kirjinta da kuma jini a jikinta. Am not going back.


Da dare na gwada wayar Sadauki dan in gaya masa abinda Saghir yace amma naji har yanzu bata shiga. Haushi ya ishe ni na ajiye ta kawai. Amma sai na gayawa Inna duk abinda Saghir yace akan maganar Sadauki. Ta juya kai tace "wannan yaron baya kyautawa. Shi bai san hukuncin wanda yayi wa wani irin wannan sharrin ba? In kotun za'a je fa shine a kasa dan bashi da wata shaida" sai kuma tace "ni bana son zuwa kotun nan wallahi, zuciyata bata so, yan'uwan mu ne mutanen nan, so nake ayi sulhu a tsakani ba sai kowa yaji ba. Ba ga Suwaiba nan ba an bashi, kuma yana da wata matar a gida me yake nema kuma. In kudin yake so sai a bashi shima in dai za'a rabu lafiya. Ni kotun ce bana so, kuma bana so ya bata wa yaron nan suna a gurin mutanen da suke ganin girmansa".


Nima kuma bana son court din, amma kuma bana son komawa gidan Saghir kuma bana son in watsawa Sadauki kasa a ido ince bazan je ba. Dan haka ranar sai naki bacci na kwana ina gayawa Allah. Kuma na tabbatar ya jini kuma na yarda da cewa zaiyi hukuncin da ya dace.


Washegari da safe Asma'u ta tafi school ni kuma na koma na kwanta in danyi bacci sai naji karar wayata. Na dauka ina kallon number din Sadauki. Sai na jujjuya wayar a hannuna dan in tabbatar da cewa tawa ce bata Asma'u ba. Sai data kusa katsewa sannan na dauka da sallama na gaishe shi yace "ya kuka yi?" Sai da bashi labarin duk abinda Saghir ya fada. Sai kawai naji yayi dariya, yace "that man is so predictable. Ya fadi exactly abinda nake so ya fada. Tell him, na tsorata na tuba nace yayi hakuri kar ya zubar min da mutunci a gurin mutane, kice nace ya dawo ya cigaba da aikinsa ai dama ni ban kore shi ba shine ya daina zuwa. Sannan kice masa kema kin hakura ba kya son zuwa court dashi dan haka zaki koma gidan sa amma kina so please ya baki wata biyu saboda kina so ki shirya sosai" nayi saurin cewa "bazan koma ba" yace "I know. But just tell him that" nace "saboda me?" Yayi shiru sannan yace "do you trust me?" Nayi shiru nima ina lissafa lamarin sannan nace "yes, amma ina bukatar bayani" yace "okay, let me break it down for you. Bana son ke ko Inna ku shiga court dashi saboda kamar yadda Inna ta fada yan uwanku ne babu yadda zakuyi dasu. Sannan kuma ko an kaishi court din karshe kawai raba auren za'ayi and to get even that sai anyi ta faman cecekuce ana saka ki kina bayar da labari kina kara maimaita wa. I don't want to put you through that emotional trauma. You have had enough of your share of emotions. Still kuma in nace zamuyi sueing dinsa for abinda ya fada a kunnena yayi, ba lallai ya samu wani sentence mai kyau ba saboda a lokacin da yayi din akwai aure a tsakanin ku dan haka iyayenki za'a jawo cikin case din for marrying you off that young. Bana son insa Inna cikin wannan maganar. So option dina shine ya zama tsakani na dashi ne kawai ku kuna gefe. And I promise you ba zaki koma ba but for that I need you to call him ki gaya masa abinda nace".


Nace "okay, zan gaya masa" yace "thank you. But please kar ki gayawa Inna. Let it be our little secret".


Ban gayawa Inna din ba kuma ban kira Saghir ba sai washegari. Ji nayi bana son kiran nasa dan haka sai na tura masa text message na fada masa abinda Sadauki yace in fada. Sai kuwa gashi nan ya kira ni na dauka da kyar, yace "it wasn't so hard now was it? Dama nasan zamewa zaiyi ya barki. Ai mutane irin su babu abinda suke so irin su gyara public picture dinsu, ina komawa kuma zanyi requesting karin albashi kuma sai inga in zaiyi denying" yayi ta maganganun sa ni dai bance komai ba har ya gama sannan yace "and you? Mai zakiyi da wata biyu?" Nace "shiryawa nake so inyi sosai" yace "wacce irin shiryawa kuma? Ba kayanki kawai zaki zuba a akwati ba?" Nace "ina so in shirya emotionally, bayan abubuwan da ka fada ranar nan a gaban Sadauki ai you should be greatful da nace zan dawo din ma" sai na katse wayar kamar nayi fushi na kashe ta ma gaba daya.


Daga nan komai ya lafa a bangaren mu. Two weeks after that Sadauki yazo yayi wa inna sallama yace zaiyi tafiya zuwa Canada. Yana shigowa Subay'a ta zagayo ta dawo bayan kujerar da nake zaune. Muka gaishe shi ya amsa sai ya mika mata hannu "Subis come here" sai ta makale. Yayi dariya yace "inna na kawo karar Subay'a, bata gaishe ni" Inna tace "ke! Ba zaki zo ki gaishe shi ba?" Still taki zuwa, zanyi mata fada yace in rabu da ita, yayi wa Inna bayani "dama family na na Maiduguri kusan duk suna Canada, zan danje in yi musu kwana biyu. In naje zan kira ku da number din da za ku same ni da ita should in case ko wani abun zai tashi" Sai Inna ta nuna irin bata ji dadin tafiyar tasa ba, Asma'u harda matsar kwalla yace "ko wata daya fa ba zanyi ba. Just hutawa nake so inyi saboda ina aiyuka da yawa a nan". 


Yana fita Subay'a ta zagayo cinyata tace "Mommy bana son mutumin nan" Inna ta kwade ta da muhuci tace "kar in sake jin kince ba kya sonsa, kuma in na sake ganin yazo kin ki gaishe shi ni dake ne. Babanki ne shi, tunda yayan babarki ne".


Sai bayan tafiyar sa Inna ta tambayeni "wai ya kuke ciki ne maganar Saghir? Ni baki ce min komai ba" nace "na gaya masa abinda Sadauki yace in fada masa, shi kuma yace ba zai sake ni din  ba sai dai aje court din. Shi kuma Sadauki yace vaya son muje court dasu" inna tace "nima bana so, to amma ai ba zaki yi ta zama da aure aka ba. Dole dai cikin biyu za'ayi daga. Bara ya dawo daga canadan muji".


Sati daya da tafiyar Sadauki muka je gidan Mama gabaki dayan mu. Anan ne muke samun labarin ashe rigima ake tayi a sharada tsakanin Alhaji Babba da kawu Isa. Kawu Isa yayi wa Saghir huce haushi na da suwaiba, har Saghir ya karba ya an fara shirye shirye sai kuma yaxo yace ya fasa ni zai mayar sai kawu Isa ya nuna cewa ba'a kyautawa yarinyar ba, amma as usual, Alhaji Babba ya goyi bayan dansa. 


Mama tace "ni tsoro nake ma Allah yasa bai lalata musu yarinya ba, dan labaran da muke ji basu da dadi".


Bayan dawowar mune nayi bakuwa. Fauziyya. Ni ban san ma tasan gidan mu ba sai yau. Na karbe ta sosai muka shiga daki nayi serving dinta abinci da drinks. Sannan tace "muna ta jira kuma har yanzu shiru" nayi dariya kawai, sai tace "ko sai za'a koma sabon gida sannan zaki dawo?" Nace "sabon gida kuma?" Tace "eh mana, ko bai gaya miki ba ya siya mana sabon gida? Sai ta fara yi min bayanin girma da kyan gidan "kowa da part dinshi, part din kowa yayi girman gidan da muke ciki. Yayi order komai na gidan next week za'a kawo su" sai ta nuna min key din mota "kinga ya siya min mota, kema ina jin kina komawa za'a siya miki taki. Shima ya sake wata" na gyara zama ina nazarin ta nace "why are you here Fauziyya?" Tace "ziyara na kawo miki mana. Kuma in gaya miki alkhairin da ya samu mijin mu dan in kwadaita miki komawa gidan. Hausawa sunce the devil you know is better than the angel you don't know. Na zauna dake lafiya, gwara ko dawo akan a kawo min wata wadda ban sani ba".


Bayan tafiyar ta na zauna tunani. Kudi? Lokaci daya? Saghir? Ina ya samu kudi? And I remembered lokacin daya samu aiki yazo yake bani labari yace "financial secretary aka ce miki. Ni nake kula da duk harkokin shige da ficen kudi a companyn".[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty Three : Check up


Sai naji tunani na ya tsaya. I just want to make a sense of wannan abin but na kasa believing abinda nake thinking. Is Saghir helping himself out of Sadauki's money? Ko kuma yana blackmailing Sadauki ne akan wannan maganar? But anya Sadauki zaiyi paying Saghir irin wannan kudin saboda empty threats dinsa? Tun sanda yayi threat din ni ban ji ko alamar tsoro a voice din Sadauki ba. Menene ma kuma dalilin da yasa Sadauki ya mayar wa da Saghir aikinsa? In dai kuwa har Saghir kudin Sadauki yake dauka then he is dumber than I thought.


Koma dai menene ni abinda na sani shine ya kamata inyi warning Sadauki akan ya kula da kudinsa tun kafin Saghir ya debi wanda zai kassara Sadauki ko kuma shi wanda ba zai iya biya ba. Kamar yadda na tabbatar zan mutu haka na tabbatar Sadauki ba zai bar masa ba.


Wayar Asma'u na nemo na dauki number din da naga Sadauki ya kira ta rannan na saka a tawa wayar nayi dialing amma sai taki shiga, naji kamar in jefar da wayar saboda bakin ciki, wato a wannan number din ma sai da yayi blocking dina? Wai me yake tunanin kansa ne? Ni ma na damu, sai sune suyi tayi ai daga shi har Saghir din.


Washegari Saghir yazo gidan. Ya ci kwalliya fiye da yadda yake da sai sheki yake yi kamar tarwada. Sai naga rashin kunyarsa da har zai iya shigowa palon Inna bayan duk abinda yayi mata da kuma sakinna da yayi a gabanta. Subay'a ta tafi da gudu ta rungume shi ya daga ta sama yana juya ta kamar yadda yake yi mata sanda muna gidansa. Asma'u tayi tsaki ta fita. Sai ya dan rissina ya gaida Inna ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Sai ta dauki mayafinta tace min zata je unguwa. Ya zauna yana kallona yace "babu gaisuwa gimbiya" na kalle shi nace "yaushe babana ya zama sarki ballantana ni in zama gimbiya?" Yace "ai ba gimbiyar gari bace ba, gimbiya tace ni kadai. Kinsan cewa an bani kyautar budurwa naki karba saboda ke? Ke kinsan wanne irin so nake miki kuwa Diyam?" Nayi shiru ina tunanin irin maganganun daya fada a nan palon a gaban Sadauki, is that his version of love? 


Yace "wata biyun nan yayi min yawa please. Ki rage. Ko kuma ince na rage miki da kaina. Na sayi sabon gida, you are going to like it. Zanyi tafiya zanyi two weeks kafin nan komai na gidan ya kammala ina dawowa zamu tare. So, I want you to get ready kafin nan kafin lokacin dan har dake din zamu tare a lokaci daya. Kinga da kin koma ma da dake zamuyi tafiyar nan. Am taking Fauziyya to the honeymoon I promised her, but in kin koma kema sai muyi fixing time ki zabi kasar da kike so mu tafi" na gyada masa kai kawai a raina ina jin haushin Sadauki da yace ince da Saghir zan koma. I don't like this idea at all.


Ya fara duba kayan jikin Subay'a "wannan kayan duk sun tsufa a zubar dasu Diyam. Ga kaya nan na taho mata dasu suna mota sai ta cigaba da amfani dasu" sai ya dora ta akan cinyarta tana ta zuba masa surutu yana dariya, ina jinsu ya fada mata zaiyi tafiya ita kuma ta fara lissafo masa kayan da zai siyo mata. Sannan tace "Daddy dan Allah ka dawo da wuri mu koma gidan mu ni nafi son zama tarr da kai da Mommy" yayi pecking dinta a cheeks yace "ina dawowa zamu koma kinji princess? It is going to be sabuwar rayuwa for us".


Sai naji a raina cewa tunda har yanzu ni matarsa ce then it is my responsibility inji source din kudinsa. Sai nace "kudi ka samu ne masu yawa haka? A ina?" Sai ya watso min wani mugun kallo yace "matse ni sai in gaya miki, kinsan dai tunda kika sanni da arziki na kika san ni ko? Ko kin taba gani na ina gyaran matattun motoci? Wanda ya samu dukiya sama ta ka shi ake yiwa tambayar inda ya samu dan zata iya yiwuwa yankan kai ko fashi da makami yake yi". 


Sai da yasa na raka shi har bakin kofa, ya fito da kayan Subay'a jaka guda ya mika min sannan yace "I will be seeing you soon, sweet pie".


Washegari jirginsu ya daga shi da Fauziyya, I didn't even know ina suka tafi sai ya suka sauka ya kira ni yace min sun sauka a Miami, yace in ajiye number din saboda zai ke kira na da ita. 


Bayan tafiyar Saghir ne Asma'u ta kammala jarabawarta, tayi candy, sannan kuma hakan yazo dai dai dayin saukar Alqur'anin ta. Wannan yasa ta shirya walima a nan gidan mu ita da kawayenta. Inna ta aika wa duk yan'uwa aka gayyato su kuma ga mamakin mu sai gasu sunzo, sai dai abinda muka lura dashi shine babu jituwa tsakanin iyalin Alhaji Babba da kawu Isa. Aka gabatar musu da abinci iri iri wanda su kansu sai da sukayi mamaki, daga abincin da aka ci har zuwa sutturar da muka saka daga mu har Inna duk sun nuna cewa ba a cikin kunci muke ba. Su Murja sai tambayata suke yi "yaushe zaki koma gidan hamma?" Murja ta jani gefe "dan Allah Diyam in baki koma bama kiyi masa magana ko zaiji maganar ki. Kinga maganar auren nan fa ta tsaya duk uban kudin da yake samu kwanan nan amma yace ba zaiyi ba. Shi kuma kawu isa da muke tunanin tura masa samarin mu shi kuma gashi yanzu ko magana basa yi da Alhaji" nace "wai me ya hadasu ne?" Ta rufe baki tace "ba za'aji a baki na ba".


Kwana biyu da yin walimar Asma'u sai ga Kawu Isa a gidan mu. Mamaki ya ishe ni na tuna ranar da yace sun cire mu a cikin zuri'a ranar da sagjir ya sake ni a gabansu amma yanzu gashi few months after ya dawo da kafafuwansa. Muka gaishe shi ni da Asma'u muka fita muka basu guri da inna. Sun jima suna maganganu kafin muji ya fita sannan muka dawo dakin. Asma'u ta saka Inna a gaba da tambaya "me yace? Me ya faru" Inna tace "ina ruwanki? Suda mai bakin magana" 


Sai da Asma'u ta tafi islamiyya sannan inna ta bani labari. "Zuwa yayi yace min wai dan Allah duk yadda za'ayi kar mu mayar dake gidan Saghir. Ashe abinda Yalwati take fada min rannan gaskiya ne, Suwaiba dai har da cikin Saghir a jikinta. Alhaji Babba yace shi lallai sharri aka yiwa dansa, shi ma kuma Saghir din yace ba nashi vane ba kuma yama fasa aurenta ke zai mayar. Shine shi kuma hamma Isa yazo yace kar mu mayar masa da ke in yaso yayi biyu babu kenan. Su yanzu likitan da zai cire cikin suke nema". Nayi shiru ina jin hawaye yana bin fuskata. Na tuno zafin da naji sanda Saghir yayi min sharri a gaban yan'uwan mahaifina amma duk babu wanda yayi komai a kai. Ga zina nan ta kare a gabansu, yanzu sai su ware ni da Saghir waye mazinaci.


Bayan sati ya kuma zagayowa sai ga malam iliya maigadin gidan Saghir ya kirani hankali a tashe. Na tambayeshi sai yace "yan NDLE ne suka zo gidan, sun yi filla filla da komai na gidan wai suna neman kayan maye" cikin tashin hankali na tambayeshi sun samu sai yace "sun samu, a dakin mai gidan sukayi ta fitowa dasu sannan suka samu wasu kuma a motarsa. Yanzu tafiyarsu kenan nima guduwa nayi da ina jin dani zasu hada. Shine na kira ki tunda su basa nan in gaya miki halin da ake ciki" nayi masa godiya na kashe wayar, ina kokarin bawa inna labari sai ga kira ya shigo wayarta daga Hajiya Yalwati tana ta kuka "Amina mun shiga uku. Wai yan drugs ne suka zo zasu tafi da Alhaji. Alhaji Babba fa? Me ya hada shi da shaye shaye?". Nan take Inna ta rikirkice ta saka mu muka shirya muka tafi gidan gaba daya, muna zuwa muka tarar har an tafi dashi ga yan gidan nan sun fito sunyi chirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi, yan unguwa kuma ana tsaye ana kallo. Mukayi ta basu baki muna mayar dasu cikin gida har muka samu suka koma ciki sannan aka fara tunanin ta inda za'a bullowa lamarin. Ni dai na fada musu abinda mai gadin gidan Saghir ya fada, dan haka sai muka fahimci cewa neman Saghir suke yi shi yasa suka kama Alhaji. Aka kira Kawu Isa aka gaya masa amma yace shi babu ruwansa "tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka".


Dan abin kunya sai surukan gidan aka nema, ciki harda wanda yake neman auren Murja, su sukayi ta zirga zirga Inna kuma ta saka Asma'u taje ta ciro kudi a account a bawa wancan cin hanci a bawa wancan amma sai da Alhaji Babba ya kwana biyu a garkame sannan suka sake shi da yarjejeniyar Saghir yana shigowa kasar zai danka musu shi a hannun su.


Ranar da Alhaji ya dawo gida haka ya zauna yana ta kuka kamar karamin yaro "ban taba ganin cin mutumci irin wannan ba, wannan yaro mai ya janyo min haka ni Muhammadu. Ankwa hannu da kafa haka aka saka min ana jana a titi kamar wanda yayi kisan kai" sai kuma ya fara yiwa Inna godiya a kan kokarin ta da karfin ta da kudinta gurin ganin an fito dashi. Yana ta kuka har ciwonsa yana kokarin tashi dan haka akayi masa allurar bacci mu kuma muka tafi gida.


What remains a mystery shine yadda akayi yan drugs suka yi suspecting Saghir yana ta'ammali da kayan maye har suka kaiwa gidansa ziyara.


Two weeks after tafiyar Saghir sadauki ya dawo. A gurin Asma'u naji zancen dawowar tasa sai kuwa gashi nan yazo gidan. Ina jin shigowarsa na shige cikin daki na lulluba kamar mai bacci. Ina jin su suna ta hirar su a palo, ya kawowa Asma'u graduation gift na wata desighner handbag da takalmi, ya kawo wa Subay'a yar karamar computer ta yara mai kyau. Ta shigo da murna tana nuna min "Mommy kinga abinda wannan yayan naki ya kawo min, amma ke yace bai siyo miki komai ba" na karba ina dubawa nace "to kije kice kin gode madallah" ta fita na koma na kwanta. 


Ina ta so dai inyi masa maganar kudin companyn sa, amma bana son ganinsa dan haka bayan ya bar gidan sai na kara dauko waya ta ban kirashi ba dan nasan ba shiga zata yi ba amma sai na rubuta masa message. "Ka sa ido a kudaden kamfanin ka. I might be wrong. Just taking precautions". Na tura masa. Na zauna da wayar a hannu ina jiran reply, shiru shiru babu. Har na gaji na ajiye ta na tashi na cigaba da harkoki na. Aka jima na sake dubawa babu reply, nayi tsaki a raina nace "ku kuka sani" Sai kuma nake jin haushin kaina for caring a inda ni ba'a damu dani ba. 


Saghir yakan kira ni sometimes, in ya kira sai in bawa Subay'a suyi magana. Ko da wasa ban bashi labarin case din drugs ba dan nasan ba karamin aikinsa bane ba yaki dawowa dan ba damuwa yayi da abinda za'ayiwa Alhaji in bai dawo din ba. Ranar nan ya kira na bawa Subay'a suka gama maganganun su sai yace ta bani, na karba yace min "jibi zamu dawo. Ina son ki kawo Subay'a airport ta tare mu. Tace tana son zuwa" nace "okay Allah ya kaimu jibin. Allah ya kawo ku lfy" yace "ameen. Hope kin gama shiryawa dan daga airport sabon gidazamu zarce" na sake cewa "Allah ya kaimu" na kashe. I didn't have the energy or the patient to argue.


Muna gama wayar sai naga Asma'u ta dauki tata wayar tayi kira sannan tace "jibi zai dawo" ta kashe. Ta kalleta nace "what was that?" Tace "Hamma yace in gaya masa ranar da Saghir zai dawo" na saki baki kawai ina kallonta. What was that about?


Ranar dawowarsu na shirya Subay'a tana ta murna muka tafi malam Aminu Kano international airport. Muka tsaya a gurin da aka tanada dan taryar matafiya. Subay'a tana ta tsalle ta kasa tsayawa a guri daya yayin da ni kuma nake ta lissafe lissafen halin da nake ciki. Ni har yanzu ban gama fahimtar kudurin Sadauki na mayar da Saghir aiki sannan da kuma hanani gaya masa cewa ni ba zan koma gidansa ba. Na fahimci kamar yana buying time ne but for what? Me yasa kuma yake son jin lokacin dawowar Saghir?


Muna tsaye akayi announcing saukar jirgin su Saghir, muna tsaye kuma har suka gama checking out suka fito. Na hango shi, as handsome as ever, hannunsa cikin na Fauziyya suna fitowa daga revolving door din gurin. Subay'a ta fara murna "Daddy, Daddy" ya dago mata hannu yana murmushi. 


And then as he steps his feet out of the door, police surrounded him. Police, not NDLE officers. Fauziyya ta matsa baya da sauri tana ihu, Subay'a ma ta fara ihun kiran Daddy yayinda shi kuma ya fara demanding dalilin kamashi. Na daga Subay'a na rungume ta a kirjina, muna kallo daga inda muke tsaye aka garkamawa Saghir ankwa a hannayensa aka wuce dashi police car da take gefe tana jira. 


Subay'a ta fara jera min tambayoyi "me yasa yan sanda suka tafi da Daddy na? Ina zasu kai shi?" A lokacin naji karar shigowar text cikin wayata. Na dauko ta na duba naga number din Sadauki. Sai yanzu yayi replying message dina. Na karanta "check up" it said.

[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty Four & Five : The Games We Play


"Check up" na maimaita a fili. Nasan wannan kalmar amma a ina? Sai mind dina ta koma baya, back in time lokacin muna yara a gida muna playing game of cards ni da Sadauki a incomplete benen Baffa a lokacin da nake gudun islamiyya ya rama min duka ance in na koma sai an zane ni. A cikin game din ana cewa check up. And it means game over.


Amma wanne game din ne over bayan ni bansan sanda game din ya fara ba? Ya akayi ya turo min wannan text din a dai dai wannan lokacin? Ko dai Sadauki yana da hannu ne gurin kama Saghir?


Kamar ance min in juya baya sai na juya. And I saw him. Yana tsaye ya jingina da jikin motarsa with dark glasses a idonsa and a broad smile on his face yana kallon motar police din da aka saka Saghir a ciki, sai da yaga sun ja sun tafi sannan ya bude motarsa shima ya shiga shima ya tafi.


Da sauri na koma taxi din da nayo shutter nace masa mubi bayan police car din data fita. A hanya drivern yake ta surutai "ai haka police suke yiwa irin wadannan bata garin, in sunyi abu sai su gudu su bar kasar sai a shammace su ranar da zasu dawo azo ayi gaba dasu. Ai wannan commissioner din baya wasa" jin ban kula shiba sai yayi shiru kuma muka cigaba da bin su a baya har na tabbatar cewa bompai zasu tafi dashi sannan nace da drivern ya kaini badawa layout, gidan Mama, muna zuwa na ajiye Subay'a na gayawa Mama briefly abinda ya faru, naci sa'a yaya Sadiq yana gida sai ta hadani dashi muka koma police station din dan muji takamaiman abinda ya faru, for what charges aka kama Saghir. 


But ni already jiki na ya gama bani charges din ina dai so ne in tabbatar da zargi na. Ina kuma bukatar wasu amsoshin daga Saghir. Da kyar muka samu desk officer din ya kula mu, amma da muka nemi ganin Saghir Muhammad da aka shigo dashi yanzu sai kawai yayi mana dariya irin mun ma bashi dariya din nan, yace "wannan ai ko uwarsa ce take son ganinsa sai dai ta hakura. Ku koma gida kuyi taja masa charbi dan yau ne za'ayi masa tambayar kabari ta duniya" ya fada yana dariyar mugunta.


Nace "to zamu iya sanin dalilin da yasa aka kama shi?" Yace "ke wacece a gurinsa?" Nace "matarsa" yace "kinsan inda yake aiki?" Na hadiye wani abu a kirjina Nace "eh. Abatcha Motors" yace "to can zaki je ki tambayi abinda yayi, zasu yi miki bayani dalla dalla".


Haka muka hakura muka fito. Yaya Sadiq yana jan motar mama ni kuma ina gaba nayi shiru ina juta lamarin a raina. My deepest fear have come true, wannan case din bana drugs bane ba kuma wani ne daban, case din Sadauki ne, Saghir ya debi kudin companyn Sadauki yayi facaka dasu Sadauki kuma ya saka an kama shi. But what was Saghir thinking?


Gidan Alhaji Babba nace Yaya Sadiq ya kaini, dole inje in fada musu halin da dansu yake ciki in yaso a hadu a san yadda za'ayi tackling lamarin. Ga kuma wancan case din NDLEA da yake jiran Saghir. Sai kawai naji ina jin tausayin iyaye da yan uwan Saghir. 


I also needed to talk with Sadauki. Bana ko raba daya da biyu nasan tarko ne Sadauki ya dana wa Saghir shi kuma ya fada head over heels. Wato wannan shine time din daya nema in yi masa buying kenan. Sai kuma na sake tambayar kaina "menene hadin Sadauki da case din NDLEA? I really do hope bashi da hannu a ciki.


Da muka je gidan kuma sai na kasa gaya musu, musamman ganin da nayi suna ta fama da kansu, an dafa wake da shinkafa ana ta lissafin yadda za'a samu kudin mai, sai da naje na bayar aka siyo musu. Sai na ja Hajiya Yalwati gefe na labarta mata. Ta rike baki tana salati tace "gurin aikin sa kuma? Ba companyn Sadauki bane yake aikin ji nake ya kore shi?" Nace "bai kore shi ba, ga kuma abinda ya faru. Yanzu yana bompai. Naje an ma hanani ganinsa" haka na tafi na barta da jimami nace ta gayawa Alhaji da Hajiya. Ni ba zan iya ganin wannan heart break din ba.


Daga nan gida yaya Sadiq ya kaini, na bar Subay'a gidan Mama in yaso gobe in na koma station din sai in biya in taho da ita saboda nasan yanzu in muka he gida ta saka ni a gaba kenan da tambayar ina daddyn ta? Ina police suka kai shi?. Ina shiga gidan Inna tana sallamar wani yaro da yazo siyan kankara ta gane something is wrong, sai data sallame shi tace min "lafiya? Ina Subay'a? Rigima kuka sake yi da Saghir?" na zauna ina cire hijab dina nace "inna Saghir yana bompai" ta saka salati tana tafa hannu tace "masu neman nasa ne suka kama shi? Dama sun san yau zai dawo?" Nace "basu bane ba Inna. Wani case din ne daban, basu gaya min menene ba amma sunce case ne daga gurin aikinsa" na fada ina kallonta cikin ido, nan da nan sai naga ta fahimta tace "Sadauki? Me ya kuma hada su kuma?" Na daga kafada nace "ban sani ba. Sai gobe zan sake komawa inji ko zasu yi min bayani" tace "to ki kira Sadaukin mana ki tambayeshi shi?" Na kwanta a kujera ina cewa "ba zai dauka ba Inna. Dama can baya daukar waya ta ballantana yanzu". 


Na jima kwance da idanuna a rufe har aka fara kiran magrib. Ni dai va bacci nake ba kawai ina ta lissafe lissafe ne, Sadauki should have just let me take Saghir to court shikenan a wuce gurin. In na rabu dashi ba dai shikenan ba?


Ina ji da dare Inna ta saka Asma'u tana ta bugawa Sadauki waya amma yaki dauka, daga baya ma sai ya kashe wayar gabaki daya. A raina nace dai dai kenan.


Washegari tun da wuri na tashi na shirya inna ma ta shirya tace gwara muje tare, muka bar Asma'u a gida muka tafi bompai amma muna zuwa muka tarar Hajiya Babba ta riga mu zuwa ita da wani kaninta. Idanunta sun kumbura alamar tayi kuka harta gode wa Allah. Muna shiga ta taho gurina da sauri "Diyam sharri yake masa wallahi, wallahi sharri yake yi masa ina yaron nan zai kai wadannan uban kudade?" Inna ta rike ta tana lallashinta ni kuma na karasa gurin desk officer din da yake on duty. Ya miko min wata takarda wacce take dauke da case statement na case din Saghir, a jiki naga bayanin cewa ya yi transfer din kudi ne daga account din company zuwa private account dinsa. Amount din dana gani sai daya saka kaina ya sara naji kamar zan fadi, mai Saghir yake tunani ne wai? A jiki kuma naga cewa Saghir din ya karbi laifinsa tun a jiyan da aka kawo shi dan haka har an fara shirin tura shi court. Na ajiye takardar nace da officer din "can I see him please" ya kalle ni da mamaki yace "are you sure? He went through some questioning so an dan sassama shi kadan" ya karasa yana grinning. Na juya na kalli inda Hajiya har yanzu take zaune tana kuka Inna tana rarrashinta. Nace "zan ganshi, amma ni kadai" sai ya miko min wani form yace in cike. Na karba na tafi gurin su Hajiya nace musu "sun hana ganinsa, gwara ku tafi gida kawai. Ni zan zauna in cike wasu takardu yanzu zan biyo ku" kamar ba zasu tafi ba sai kanin Hajiya wanda dama tunda muka zo naga yana ta nuna alamar ya gaji yace "in mun zauna ma babu abinda zasuyi mana fa, zasu iya wulakanta mu gwara mu koma gida sai asan yadda za'a bullowa lamarin" sai naci sa'a suka bishi suka tafi ni kuma na koma ciki na cike form din da aka bani, aka kaini wani daki na zauna ina jira, shiru shiru tun ina kallon agogo gar na fara zama frustrated ina jin tamkar na shekara a dakin sai aka bude kofa aka shigo.


Saghir ne, amma kamar ba Saghir ba. Daga shi sai singlet da gajeren wando, fuskarsa babu inda bai kumbura ba dan idanuwansa da kyar suke budewa. Sai kawai naji zuciyata ta karye na rufe baki na kama kuka. Officer din daya shigo dashi yace "na gaya miki ai" sai ya zaunar da Saghir akan benchi ya juya ya fita. Na tsaya kawai muna kallon kallo. Sai can yace cikin wata irin murya "kinzo ne dan ki sakani a gaba kiyi ta kallo kina cewa Allah ya kara ko kuma kinzo ki karasa aikin da tsohon saurayinki ya fara?" 


Na zauna ina facing dinsa nace "Saghir me yasa ka daukar masa kudi? Why? In zaka dauki kudin kowa a duniya me yasa zaka taba na Sadauki bayan kasan abinda yake tsakanin ku?" Yace "menene a tsakanin mu din? Ke? Dan ke akayi min wannan abin na sani kuma yayi da dan halak. Sai na rama duk ranar da na bar gurin nan sai na chanja masa kamanni kamar yadda yasa aka chanja min nawa" na girgiza kai cike da takaici, he is still being arrogant, nace "ni so nake in tabbatar, ka daukar masa kudi ko ba ka daukar masa ba? Ina so insan gaskiyar maganar nan saboda in san ta inda zan bullo mata" ya dauke kai yace "I don't need your help. Kiyi tafiyar ki kawai. Ki je ki gaya masa cewa tarkon daya kafa ya kama shaho" na girgiza kaina a raina nace 'he have no idea how much trouble yake ciki' sai na bashi labarin case dinsa da yan drugs. And that broke him down.


Hannu biyu yasa ya dafe kansa, ya jima a haka sannan ya dago yana kallona yace "wannan duk yana cikin irin kiyayyar da kike yi min Diyam? Me yasa baki fada min ba kika barni na dawo kasar? Me yasa kika barni na fada tarkon da makiyana suka kafa min" naji tausayinsa har cikin raina, nace "Saghir, ko daya ba naki gaya maka ne saboda bana sonka ba, naki gaya maka ne saboda nasan in na gaya maka ba zaka dawo ba and that means trouble for Alhaji, wanda babanka ne shi mahaifi dan haka dawowarka yafi maka alkhairi akan kin dawowarka" yace "really? To case din Sadauki fa? Shima kamanin da yayi yafi min alkhairi akan rashin kamani? Waye ya gaya masa zan dawo da har yasa aka tare ni a airport?" Nace "duk abinda zan gaya maka ba lallai ka yarda ba. Amma duk da haka zan gaya maka. Bani da idea akan abinda ya faru tsakanin ka da Sadauki. Na san dai yana buying time for something but bansan menene ba. Kuma ina so kasan cewa zanyi iya kacin kokari na na ganin ka fita daga gurin nan but for that ina bukatar ka gaya min gaskiya. Ka dauki kudin Sadauki ko baka dauka ba? Drugs din da aka samu a dakin ka da motar ka, naka ne ko ba naka ne ba?"


Ya jima shiru kamar ba zaiyi magana ba sannan kuma sai ya danyi murmushi yace "that former boyfriend of yours is smart, na bashi credit anan. Tunda yaron nan ya dauke ni aiki, ina jin ma ai na taba gaya miki, babu aikin da nake yi. Sai ya dauki wani a matsayin assistant dina to duk aikin da ya taso shi ake bawa yake yi and I tot 'huta roro' tunda dai ana bani salary na mai kyau ai bani da problem. Shekara da shekaru, ko banje gurin aiki ba bani da matsala, I should have known tun a lokacin that something is off but ni ta constant monthly income dina nake yi. And then lokacin da na koma aiki, suddenly it was all work for me. A lokacin ne nasan ma how much money ne a cikin account din Company and it was a huge money. Kullum kudi suna shigowa wadansu suna fita, kudi masu yawa. Shi yayi tafiyar sa, and duk takardar da aka kawo zaiyi signing sai a kawo min ace yace inyi a maimakon sa. Duk kudin da za'a fitar ni za'a saka in fitar dasu haka duk kudin da za'a shigar. It was like cewa ake yi Saghir dauki kudin nan. And I saw my chance. Mutumin nan yaci amana ta yayi making fool of me for years, dan haka dole ce ta saka ni na cigaba da aiki under him saboda babu inda zanje in samu din. Dan haka sai na dauka as a revenge for what he did to me kuma dan in kafa kaina nima in daina aiki under him. Nasan zai gani amma kuma nasan yana tsoron kar in bata masa image dinsa with that scandal so I expected him to keep quiet. Da kudin na sayi gidan dana gaya miki na kuma saya mana motoci ni da ke da Fauziyya and I gave some part of the money to Kabir da niyyar zamu hada share muyi business tare. Sauran kuma dasu nayi wannan tafiyar wadansu kuma suna account dina da niyyar su zasu rike mu kafin business din da zan fara ya kankama".


A gyada kai, my mind already thinking ta yadda za'a harhado kan wadannan kudade. Ya cigaba:


"Drugs kuma, wadanda aka samu a daki na, a kasan gadona, ba nawa bane ba. You know I don't do drugs. Na Kabir ne ya bani ajjiya saboda yana da iyali karsu taba masa ni kuma tunda zanyi tafiya shine yace in ajiye masa, a mota ta kuma alcohol zasu samu".


Na gyada kai nace "so, where is Kabir now?" Ya daga kafada yace "ta yaya zan sani tunda ina nan a rufe?" Nace "but ta yaya akayi suka kai mamaye gidan ka?" Yace "I have no idea. Ask that smart boyfriend of yours maybe shi yana da idea".


Na mike tsaye nace "thanks for telling me the truth. Zan je gidan Alhaji zamu zauna muga ta yadda za'a bullowa lamarin. Insha Allah, you are getting out of here. Zamuyi reporting cewa stuffs din Kabir ne ba naka ba." Na juya zan fita sai yace "why?" Na juyo ina kallonsa nace "why?" Yace "why are you trying to help me bayan duk abinda nayi miki? I tot ke celebrating zakiyi ma cewa you are finally getting rid of me" nace "kamar yadda Hajiya ta gaya min rannan. Kai dan'uwa na ne, mijina, kuma uban yata".


Daga bompai gidan Alhaji Babba na koma, a can na same su harda inna duk sunyi jigum jigum har aunty Fatima itama tazo. Na zauna na lissafa musu tas abinda ya faru. Saghir dai ya dauki kudi ba sharri ne akayi masa ba, ya kuma admitting to ajiye drugs a gidan sa amma yace ba nasa bane ba na Kabir abokin sa ne. 


Nan take Alhaji Babba ya dauko waya ya kira Alhaji Murtala mahaifin Kabir yana tambayarsa in yasan inda Kabir din yake amma sai yace shima nemansa yake yi bai san inda yake ba, ya dauka ma tare suka fita da Saghir, da yake duk halin daya ne. Nan fa hankalin Alhaji ya sake tashi. In ba'a samu Kabir ba Saghir ne a ruwa.


Out of the confusion na fita waje na zauna a compound. Sai na dauko wayata nakira Fauziyya. Tunda na ganta a airport sanda aka kama Saghir ban kuma waiwatarta ba kuma babu wanda ya kuma kiranta. Bugu biyu ta dauka. "Halima ya ake ciki?" Naji haushin da bata kirani taji ya ake ciki ba sai yanzu? Amma sai nayi mata bayanin duk abinda na fahimta da kuma halin da ake ciki a yanzu. Sai ta tabbatar min da cewa tabbas taga sanda ya ajiye drugs din a day to tafiyarsu yace ajjiya aka bashi but bata san menene ba a lokacin kuma bata san waye ya bashi ajjiyar ba. Sai na ce mata ta shirya ta taho gidan Alhaji itama ayi komai da ita.


Sai can yamma ta zo, tana ta dari dari dan duk yan gidan ba sonta suke yi ba kar ma Hajiya taji labari, tace tsohuwar karuwa ce. Ita ta sake tabbatar musu da cewa Saghir shi ya ajiye drugs din da hannunsa, ta kuma gaya musu zancen gidan daya siya wanda su sam sam basu san da zancensa ba. Tace gidan yana unguwar rijiyar zaki dan haka muka yi shirin gobe zamuje a ga gidan sai kuma a nemi mai siya. Za'a karbi motarta da tasa a hada da wadda yace ya saya da sunana duk a siyar, sai a hada kudin da sauran kudin da yake account dinsa aga abinda za'a tayar kafin a nemi inda Kabir yake a dankashi a hannun NDLEA a kuma karbi kudin Saghir na hannunsa. Sauran kudaden kuma da Saghir ya riga ya kashe bansan inda za'a same su ba. Da Fauziyya zata tafi tace min "Mr Abatcha, ai yana jin maganar ki ko? Zaki iya sakawa ya saki Saghir ko?" And I didn't answer her. 


Muna komawa gida na kira shi da wayar Asma'u tunda ba zai dauki tawa ba amma still sai yaki dauka, I guess yayi tunanin Inna ce take nemansa da gaske. Amma ita inna tunda taji zancen cewa Saghir ya dauki kudin Sadauki da gaske sai tayi shiru bata kuma cewa komai ba. But like I told Saghir, zanyi iyakacin kokari na gurin fito dashi so I decided to see Sadauki the next morning. 


Da safe muka sake komawa gidan Alhaji Babba, Fauziyya ma tazo za'a tafi sabon gidan Saghir sai nace musu suje kawai, na gaya musu inda zanje. Abatcha Motors.


Na tarar da gurin kamar wancan zuwan nawa ana ta hada hada, sai dai yau kamar gurin yafi cika kuma motocin gurin sunfi nada yawa har bazan iya kirgasu ba, na samu receptionist din nace masa "ina son ganin ogan ku" sai ya tsaya yana kallona yadda na hade rai ya dauki waya yayi magana a ciki sai kuma ya kalle ni yace "ya ga shigowar ki ta CCTV. Yace kije office dinsa. In kika bi nan...." Na daga masa hannu nace "nasan inda office dinsa yake thank you" sai kuma na tafi inajin haushin kaina for being rude ga wanda bashi yayi min laifi ba.


Na ga wannan kyakykyawar secretary din nasa, ta yi min sannu da zuwa sannan tazo ta bude min kofa kamar ranar nan na shiga but sai na bar kofar a bude na tsaya ina kallonsa a zaune yana kallona shima.


Nace "let him go" sai ya taso ba tare daya ce min komai ba yawuce ni majestically ya rufe kofar dana bari a bude. Ya juyo ya samu kujera ya zauna yace "he took, or rather stole my money" nace "kudi, kudi, kudi dai? Shikenan abinda yake da muhimmanci a gurin ka kudi? Look at what you have, lokacin da naga amount din kudin da Saghir ya dauka I tot ya kassara ka but ni banga alamar anyiwa companyn nan ko da scratch ba" yayi murmushi yace "you are right. Amma dai ya dauka. So, dole zai biya in kuma ba zai iya biya ba sai ya tafi gidan maza har zuwa ranar da iyayensa zasu samu kudin da zasu biya masa" na tako nazo gaban table dinsa na tsaya, ina jin kamar in rufe shi da duka. Nace "me yasa? Tarko ne ka dana masa na sani but why? Me yasa? You could have just let me take him to court kamar yadda nayi niyya ya sake ni and that'll be all. Zumuncin dama ai a lalace yake menene saura. Why do you feel the need to lock him up?" Yace "kamar yadda kika ce in kika kai shi court ya sake ki that will be all. Meaning duk abinda yayi miki yayi a banza kenan? What he did to you and said to my face shikenan yayi a banza kenan?" Ya fada with bitterness in his voice, ya cigaba "wannan abinda yayi, kuma ya gaya min yayi, shine greatest mistake dinsa a rayuwa kuma shine abinda zai paying for in prison for as long as possible" na zauna a kujerar da take facing dinsa nace "ni yayi wa, ba kai ba...." Yace "da ni yayi wa da sai abin yafi zuwa masa da sauki" naji zuciyata ta karye nace "Sadauki.....komai ya faru fa ya wuce. Ni duk na yafe kowa saboda a yanzu kowa yayi paying price dinsa. Tun daga ranar da aka kaini gidan Saghir nake addu'a cewa Allah ya saka min akan duk wanda ya zalinceni, kuma a yanzu bayan shekaru duk wadanda suka zalinceni din babu wanda bai karbi hukuncinsa ba. Inna, tun ranar da aka kaini gidan Saghir har yau Inna cikin regret take, har yau bata samu peace of mind ba saboda bana jin akwai abinda yafi ciwo irin ace uwa tayi destroying rayuwar yarta da kanta. Alhaji Babba a yanzu fa bashi da komai, ka tuna dukiya da izza irin ta Alhaji Babba amma yanzu rigar da zai saka ma sai in na debo na Saghir da baya sakawa na aika masa saboda shi ba zai bashi din ba. And Saghir, Saghir fa ta kare masa, ko da bakayi trapping dinsa ya daukar maka kudi ba Saghir already yana da case, NDLEA sun samu drugs a dakinsa dan haka suna nemansa. So you see? You don't have to do anything Allah yana planning komai accordingly" yace "na yarda, kamar yadda na yarda cewa Allah yana using people to furnish other people. Alhaji Babba da kike magana fa har yanzu baiyi regret ba, ko ya taba kiranki ya baki hakuri akan abinda yayi? Har yau da zaki tambayeshi cewa zaiyi taimaka miki yayi ya aura miki Saghir, dukiyarsa kuma cewa zaiyi makiyane suka saka masa hannu. So dole ya cigaba da zama gida daya da kaji da raguna ya cigaba da having sleepless nights for as long as I had, which will be like forever tunda har yau ba baccin nake yi ba" 


Na mike tsaye ina jin haushinsa nace "how thick is your skull? In kana furnishing Alhaji su kuma iyalansa fa? Me sukayi maka? Makota fa? Me sukayi maka? Gidan gona tunda ka bawa Asma'u zan saka ta ta chanja masa guri. Batun Saghir kuma za'a biya ka kudinka, za'a siyar da duk abinda ya siya da kudaden sannan a nemo sauran a cika maka a baka kayanka ba shikenan ba?" Ya mike tsaye yana murmushi yace "me da me za'a siyar, gida da motoci? You are kind of late because I already bought the house and one car about two weeks ago" na juyo da sauri nace "what?" Ya gyada kai yace "bayan ya debi kudina I asked someone to track duk abinda zaiyi da kudin, naji ya sayi gida da motoci and I became worried cos zai iya siyar dasu ya biya ni. Luckily for me, sai ga report cewa one of his friends..." Ya duba wata takarda a gefe yace "Kabir, ya saka gidan da mota daya a kasuwa zai siyar, he was in a kind of hurry sai na taimaka masa na siya, yanzu har na zuba yan haya a gidan. Shi abokin daya siyar din yanzu ance min ya gudu ya bar kasar" ya sake murmushi "hard luck for him".


Na dafa kujera na zauna ina kallonsa. Na fahimci lissafin sa tsaf kuma na gane mai ya faru. Saghir ya saci kudi, Kabir set him up with the drugs sai ya siyar da gidan ya hada da sauran kudaden ya gudu. Meaning yanzu Saghir bashi da abinda zai biya ga kuma case din drugs a kansa. Sai na mike ba tare dana sake cewa komai ba har nayi hanyar waje kuma sai na tuna abinda ya faru rannan dan haka na juyo nace masa "open the door" yace "Please Diyam, stay out of it. Let him take the fall. He more than deserve it" na dawo gabansa nace "tell me something. Me yasa ka yafe wa Inna? Inna tafi kowa musguna maka a duniya amma ita mai yasa ka yafe mata?" 


Ya dago kai yana kallona yace "she gave birth to you".

[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty Six : A Walk To Freedom


"She gave birth to you" 


Maganar ta daki kunnuwana sannan ta wuce har cikin zuciyata, sai naji tamkar ta kunno min emotions din dana ke ta kokarin dannewa a cikin zuciyata, sai hawaye yazo idanuna ya fara zuba kan kuncina a hankali na fara rera kuka sai ya taho inda nake da sauri yace "Diyam....." sai kuma ya dakata ya juya ya koma bayan table dinsa ya danna button din bude kofa yace ba tare daya kalleni ba "good bye Halima".


Na juya nima da sauri na fita ina kokarin goge hawayen fuskata. Na sauka daga stairs din cikin sauri na fita daga building din. So nake kawai in samu seclusion din da zanyi kuka na son raina har in gode Allah. Na tsaya a bakin kenan naga mota tayi packing a gaba na sai driver din ya fito ya zagayo inda nake ya bude min kofar baya yace "oga yace ki shigo a kaiki gida" har nayi tunanin kin shiga sai kuma nayi lissafin gwara inyi kukana a cikin mota ni kadai da ac akan inyi a cikin napep mutane suna kallona.


Na shiga ya rufe kofar ya zagayo gurin driver sannan na masa kwatancen gidan Alhaji Babba muka tafi. Na jawo hijab dina na rufe fuskata nayi kuka na na koshi amma ni kaina bansan kukan menene ba, kukan tausayin kaina ne ko na Sadauki? Kukan abinda ya faru da ne ko kuma wanda zai faru nan gaba? Ko kuma kukan abinda yake faruwa yanzu ne?


Nayi bitar maganganun Sadauki ina son inyi placing dinsa a scale din dai dai da rashin dai dai. A iyakacin fahimta ta tun muna yara nasan kafiya da zuciya sune manyan flaws din Sadauki. And he seemed to be harder yanzu. Ya nutse sosai a cikin kogin revenge yadda har yana kokarin yayi loosing kansa, and I won't allow that.


Nasan duk abinda yayi akan gaskiyar sa yake, babu inda ya kaushe wa shari'a but still Allah da kansa yace yana son bayinsa masu hakuri ni kuma ina so Sadauki ya kasance a cikin jerin mutanen da Allah yake so. 


Muna zuwa gidan Alhaji Babba na sauka, drivern ya tambayeni in shikenan inda zai kaini na amsa masa da eh. A dakin Alhaji na same sun yi tsuru tsuru har da Fauziyya. Ina shiga Alhaji ya mike yana tambayata "ya kuka yi Diyam?" Na girgiza kaina kawai na zauna a raina ina cewa 'you are in for a bad news' duk da daga yanayin su na fahimci sunje gidan Saghir sun tarar da yan haya a ciki. Alhaji ya zauna shima, yanayinsa kawai ya isa ya saka mai raunanniyar zuciya kuka, yana cewa "wannan wacce irin mummunar kaddara ce ta afkawa yaron nan? Wallahi ni ko da wasa bai gaya min ya dauki wadannan kudade ba, ballantana ya gaya min ya karbi wannan ajiya. Ba wanda yake neman shawara a gurinsa shi kadai yake al'amarinsa shida abokansa. Yanzu gashi gidan munje mun tarar da mutane sunce su haya suke yi a hannun wani agent suka karba" sai na basu labarin duk abinda na fahimta da maganar, a lokacin da Saghir yake can yana honeymoon dinsa shi kuma babban abokinsa Kabir ya saka gidan da kuma motar da Saghir din ya siya da sunana a kasuwa, ya karbe kudaden ya hada dana wajensa ya gudu ya bar kasar bayan ya bawa Saghir ajjiyar drugs kuma yayi masa chunen NDLEA.


Kowa yayi shiru a dakin har na gama bayani na, sannan na kara da cewa Sadauki yana kan bakansa na cewa sai an biya shi kudinsa. Har na gama babu wanda ya samu damar bani amsa. Sai dana gama sannan Hajiya Babba tace "Allah, Allah mun tuba. Allah in laifi muka yi maka ka dube mu ka yafe mana ka kawo mana sassaci a lamarin nan. Allah ka dubi yaron nan ka fitar dashi daga wannan matsala" ni dai nace "ameen" amma a raina nasan a inda matsalar take. Alhaji ne yayi deciding cewa zai je yaga Saghir kuma zai gaya masa halin da ake ciki. Sai naji dadi dan ni kam I wasn't looking forward to breaking the news to Saghir cewa best friend dinsa ne yayi framing dinsa dan ya cinye masa kudi. 


Daga gidan Alhaji gidan Mama na tafi. Ina shiga Subay'a ta taho da gudu ta tarye ni tana cewa "Mommy ina daddy? Kin dauko shi daga gurin yan sandan?" Na jawo ta na rike fuskarta a hannuna nace "Daddy ya sake yin wata tafiyar, amma zai dawo very soon" sai ta saka kuka ita gurin Daddy zata je ita in kira mata shi a waya. Sai da Mama tayi barazanar dukanta sannan na samu tayi shiru. 


Muka zauna na bawa Mama labarin duk abinda ake ciki tace "ki fita cikin maganar nan Diyam. Ki barshi shi da iyayen sa suyi ta fama ai tsuntsun daya ja ruwa hausawa suka ce shi ruwa kan doka. Duk halin da Saghir yake ciki iyayen sa ne suka jawo masa dan haka ki barsu su girbi abinda suka shuka da hannun su" sai nayi shiru ina kallon Subay'a tana wasa ina tunanin ko zata daina tambayata daddyn ta?


Sai yamma sosai na shirya Subay'a muka koma gida, muna zuwa na tarar Inna itama dawowar ta kenan sai Asma'u take bamu labarin Sadauki yazo yiwa Inna sallama zai tafi 'business trip'. Na kwanta kawai na rufe idona amma nasan babu wani business guduwa yayi dan kar inyi breaking dinsa. 


An saka ranar shari'a Saghir sati biyu bayan kama shi, na shirya na koma bompai gurinsa amma sai yaki yarda ya ganni, officer din yace "ya zama very emotional kwana biyun nan yace baya son ganin kowa" sai na fahimci cewa Alhaji yazo ya bashi labarin cin amanae da Kabir yayi masa, and it broke him, finally.


Tun da aka saka ranar shari'ar Saghir ban zauna ba, nice gidan Alhaji, nice bompai, nice NDLEA, kuma nice kiran Sadauki. Kullum sai na kira shi da yawar Asma'u amma itama sai ya daina dagawa. Sai in zauna in tsara masa message, duk abinda nasan zai saka ya sauko in tura masa amma ko reply daya ban taba samu ba. 


During one of my visits to NDLEA ne na samu rannan suka saurare ni, nayi musu bayanin abinda ya faru nayi mentioning sunan Kabir and that cought their attention, ashe dama suna suspecting dinsa amma basu da hujjar kama shi dan haka sun yarda zai iya framing Saghir din but still there is a case, kuma dole someone has to take the fall, Saghir kenan, dole zasuyi convicting Saghir suyi sentencing dinsa har sai an kama Kabir ya kuma karbi laifinsa.  I felt relieved, duk da ba wani important improvement bane ba but at least it was a step further.


An siyar da gidan Saghir inda muka zauna, an siyar da tsohuwa da sabuwar motarsa sannan an siyar da motar daya siyawa Fauziyya itama. Sai aka hada da kudaden daya bari account din sa but all that only raised one third of kudin da ake binsa. A lokacin ne na kuma fahimtar cewa Saghir bashi da kowa, bashi da brother dama, cousins din kuma da brother in laws din duk babu wanda yayi zaman arziki dasu ballantana su tsaya masa, uncle din kuma yayi wa yarsa ciki dan haka ko sau daya bai taba shiga maganar ba, daga ni sai Hajiya da Alhaji, ga Alhaji babu isasshiyar lafiya ga kuma tsufa daya kara saukar masa. Yan uwan Hajiya ma duk sun zare hannayensu sunce wannan abin kunyar ba da su ba. 


Nima rannan na dawo gida a gajiye Inna ta kalleni tace "daga yau babu inda zaki kuma fita akan maganar nan. In dake ce wani abu irin wannan ya same ki da daga Saghir din har iyayensa babu wanda zai daga ko dan yatsa ne ya taimaka miki, dariya ma zasu yi miki" na zauna kawai nayi shiru, sai tace "ko kin chanja shawara kuma Saghir din zaki komawa?" Nayi saurin girgiza kaina. Bana son Saghir kuma na gama aurensa, that's a fact, but still har yanzu mijina ne, nayi kurakurai da dama a rayuwar auren mu bab sani ba ko wannan kokarin da nake masa zai taimaka min wajen goge wadancan laifukan. Sannan kuma, Subay'a, bata da wani uban daya wuce Saghir duk wani wanda zai rike ta sai dai ya zama uban kara amma ba mahaifi ba, and I am not looking forward to telling her that babanta yana prison, what will happen kuma inta fahimci cewa Sadauki yayi playing role a saka babanta a prison din? 


Another dalilina kuma shine Sadauki. Sadauki loves me, for that bani da dobt, wannan kusan shine dalilin da yasa ya gudu saboda kar yaga na damu ya kasa abinda yayi niyya. And I love him, shima bani da dobt a kan wannan dan haka nake so in chanja ra'ayinsa zuwa forgiveness, for his sake, saboda ina gudar masa daukan alhakin wadanda basu da laifi, ina kuma gudar masa dana sani a nan gaba.


Ranar sharia tazo and we all went to the court, na bar Subay'a a gida, wadda a ranar ma sai da tayi min complain din neman daddyn ta. Na samu seat a farko farko na zauna bracing myself for duk outcome din da za'a samu. Muna zaune aka shigo da Saghir, looking very down and defeated, ban taba ganin sa a haka ba. Ya zauna a gurin zaman accused looking down at his fingers. 


Sai aka fara gabatar da kara, aka lissafa all charges against him sai lawyers suka fara maganganun su da ba ganewa ake yi ba, nayi ta stressing 茩wa茩walwa ta ina so in gane mai suke cewa amma sam bana fahimta sai dai in sunyi magana inga alkali ya gyada kai har suka gama. Sannan ya juyo yana kallon Saghir ya tambaye shi "how do you plead?" Ba tare daya kalle shi ba yace "guilty" and my heart went out to him. 


A take alkali ya yanke masa hukunci, for the crime of kudin Abatcha Motors daya ci, za'a rike shi a prison har sai familyn sa sun biya kudin, for the crime of drugs, shima zai zauna har sai an kama Kabir.


In both cases he is doomed for life.


Aka gama karanta masa sentence dinsa amma bai dago kansa ba, na fara jin koke koke a baya na. Na waiga naga Hajiya tana kuka ita da kanwarta, sai Fauziyya daga can gefe, sai su Murja sun hada kai ita da sauran yan'uwanta suna yin nasu, and then a can karshen room din na hango wadda banyi tunani ba. Suwaiba. Itama tana nata kukan.


Sai aka taho dashi za'a wuce dashi, ya tsaya yana kare mana kallo daya bayan daya, sai muka hada ido and he smiled. Da sauri na mike na tari abin hawa zuwa gida. 


Ranar kwana nayi banyi bacci ba. Washegari Mama tazo suka wuni anan ita dasu Rufaida da Muhsina. Bayan sun tafi da yamma sai naga Subay'a ta shigo da banki irin na kasar nan na yara ta saka a kasan gadon Inna. Nace mata "Subay'a? Banki kika siyo mana?" Tace "eh, kudi zan ringa tarawa a ciki in biya wannan yayan naki kudin sa da yake bin Daddy na" I was stoned, nace "Subay'a? A ina kika ji wannan maganar?" Tace "Mama naji suna hirar da Inna, wai Daddy na yana gurin police sai an biya yayanki kudi sannan za'a fito dashi".


The next day na tashi da wuri na shirya, Inna ta tambayeni inda zanje sai nace "prison" sai ta shirya min abinci a basket tace "ki kai masa". 


Da yake anan kano central prison yake, dan haka da kafa na tafi tunda babu nisa da gidan mu. Na jima ma'aikatan prison din suna ta ja min aji kafin su yarda zan ganshi. Sai suka kaini wani guri suka ce in zauna. After waiting for like eternity sai gashi sun fito dashi. He looked very different. Older but calmer. Suka zaunar dashi a kujerar gaban table din da nake sannan wanda ya kawo shi ya matsa baya but yana kallon mu. 


Na sunkuyar da kaina ina lissafa fingers dina shi kuma yana kallona yace "my God, you really are beautiful" na dago na kalle shi and he smiled. Nace "ga abinci nan inji Inna" yace "thank you. Dama kinga azumi nake yi" nayi shiru ina tunanin ban taba ganin Saghir yana azumi ba in ba Ramadan ba. Sai yace "ya kika ga sabon gida na? Yayi kyau?" Na kalli surrounding din gurin nace "nan ba gidan ka bane ba Saghir. I am going to get you out of here" yayi dariya yace "how? Zaki saka ni a jaka ne mu tafi gida tare?" Nayi shiru. Yace "nasan maybe, just maybe, zaki iya convincing your lover boy ya yafe min kudinsa, but zaki iya kamo Kabir ki danka shi a hannun hukuma ki saka yayi confessing cewa shi yayi framing dina?" Nace "maybe, just maybe, zan iya convincing Sadauki ya yafe maka, sannan in saka shi yayi amfani da power dinsa to get you out. Nigeria ce fa, with few phone calls an gama komai".


Yayi dariya "not even in your dreams. Ba zaiyi ba. Mutumin da yake son ganin baya na ta yaya zai taimaka min?" Nayi shiru, nima kaina bansan ta inda zan bullowa wannan lamari ba but i am going to try.


Yace "I really did mess up ko? Nayi messing up auren mu. It would have been a great one" nace "not 'you' but 'we'. Tare muka hadu muka rusa auren mu. Ina fatan kuma zaka yafe min my part of the mess" yace "oh, you mean the closed doors ko?" Nayi murmushi. Na juya hannunsa yace "na yafe" nace "thank you".


Sai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardu guda biyu yana kallona sarcastically yace "ya sunan ki ma? Ke ce Halima ko kece Fauziyya?" Bance komai ba sai ya miko min daya, naga sunana baro baro a jiki na bude na karanta


Ni Saghir Muhammad Kollere na saki matata Halima Usman Kollere saki daya, in ta samu miji tayi aure


Na dago ina kallonsa yace "daya ne ba yawa, in kika hada da wancan sun zama biyu kenan. Ni kuma na rike daya a gurina with hope that maybe, just maybe, zaki zauna ki jira ni" nayi murmushi yace "not even in my weirdest dream ko? I will just have to keep hoping".


Mutumin daya rako shi ya matso yace "time up" na gyada kaina na mike kamar zan tafi sai kuma na dawo na tsaya a gabansa nace 


"For raping me, na yafe maka. For the twins, na yafe maka. For everything, na yafe maka. And I am going to get you out of here" 


Yayi murmushi yace "thank you. Goodbye Halima". 


Sai na juya da sauri na fita daga gurin, na kuma fita daga cikin prison din, hannuna rike da takarda ta.


Na fara tafiya a kafa ina jin iskar yanayin damina tana ratsani. Wani abu naji ya yaye daga 茩wa茩walwa ta. I felt a sense of freedom wanda rabon da inji shi tun ranar da aka aura min Saghir. Hatta hanjin cikina ji nayi yana warwarewa tamkar da a nannade yake a guri daya, wani abu daya tokare a makogwarona naji ya sauka at last ina sha茩ar numfashi freely. 


And I decided that I am going to do the right thing.

[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty Seven: Moving On


A hankali nake tafiya, enjoying my own company, feeling as free as a bird. Wannan feeling din da banji ba lokacin da Saghir yayi min sakin farko sai yanzu nake jinsa. Nayi murmushin da ya shiga har cikin zuciyata sannan a hankali na fara tariyo rayuwar auren mu da Saghir a kaina. 


Shi dai Saghir, babban abinda yayi dooming rayuwar sa har ya kai shi ga stage din da yake ciki a yanzu shine rashin tarbiyya. Makauniyar soyayyar da iyayensa suka nuna masa tun yana jariri ita ce silar komai. Sai ya taso a matsayin sangartacce, mai son kansa kuma marar yawo saboda bai san yadda zaiyi ya kula da kannasa ba kwata kwata ballantana har ya kula wani, that including su kansu iyayen nasa. Rashin yawon sa shine ya bawa Sadauki da kuma Kabir damar kai shi inda yake a yanzu.


Na tuno ranar daya ce min bararoji a palon Hajiya, na tuno sanda ya shigo daki a gaban Inna yace baya sona, na tuno abinda ya faru a first night din mu da kuma abinda ya biyo baya, na tuno haihuwar twins, zama na a gida da kuma komawa ta gidansa. Inda ace zan zauna zan iya lissafa sau nawa muka yi magana ni  shi inus our first year of marriage. Har zuwa haihuwar Subay'a bata chanja zani ba. Na tuno da yawan comments din da yake yi akaina cewa bani da body parts din daya ke so a gurin mace, year after year, then suddenly lokaci daya ya chanja after ya gama gasa ni for about seven years sai kuma ya dawo yana bani kulawa always commenting on my beauty and the so called body parts din daya ke so wadanda a lokacin na fara developing dinsu. A duk lokacin da naga yana wannan care da comments din nasan inda maganar zata kare, his bed. I remember yadda yake yawan comment cewa I tasted different than sauran matan da yake sharing bed dinsa dasu. And then he said he loves me.


But that got me thinking, it that really love? I mean zaka iya cutar da wanda kake so? Ka dake shi ka aibatashi a gaban mutane ka aibata iyayensa masu rai da marasa rai sannan kace 'you are really beautiful' ka ja shi zuwa gadonka? It that love or something else?


Duk wanda yace baya sonka, ya wulakanta ka a lokacin da baka da physical appearance din daya ke so, sai daga baya kuma daka samu sannan yazo yake kulaka, to me that is not love, that is lust.


Nasan so kuma I don't think I can hurt wanda nake so intentionally. Ko a gurin da ake aibata shima ba zan iya zama ba ballantana ni inyi da kaina. In na bata masa ransa kuwa to tabbas akan wani abu ne da nasan is for his own good. Kamar abinda na kudurce a raina cewa ina so yayi.


A tsakar gida na tarar da Inna da Asma'u suna ta gyaran gida saboda tashin su Maman Iman shekaran jiya. Na gaida ta sannan na mika mata takardar da Saghir ya bani na shige daki, ina jinta ta saka Asma'u ta karanta mata. Sai na zauna a gaban kujerar da Subay'a take kwance a kai ina kallonta a raina ina lissafin whats next a rayuwar mu ni da ita, Allah ne kadai masani amma ni nasan zanyi duk abinda ya kamata inyi a matsayi na na uwa dan ganin cewa ta samu farin ciki koda kuwa hakan yana nufin yin gibi ga nawa farin cikin. The first thing da zanyi shine in mayar da ita school, already tayi missing term guda gashi har anyi hutu ana shirin komawa sabon session. Dan haka na yanke shawarar nema mata school a arear gidan mu in saka ta wadda nasan Inna zata iya biya dan ni koboless nake a yanzu, hatta kudin recharge card ma bani akeyi.


Inna ta shigo ta zauna tana kallona da takardar a hannunta tace "na kira Hajiya Yalwati na gaya mata, nace ta gaya wa su Alhaji" na gyada kai kawai, sai kuma tace "Allah yasa hakan shi yafi miki alkhairi Allah kuma yasa karshen wahalar ki kenan" nace "ameen Inna. Nagode".


Washegari da wuri Asma'u ta fita saboda tana ta harkar neman admission, ina jinsu suna waya da yayanta da sassafe a raina nace "kaga masu business trip". Bayan ta fita nima na fita naje nayi mana register ni da Subay'a a islamiyyar bayan layin mu wadda ake yi safe da yamma. Sai a lokacin nayi dana sani dana yi jamb din nima maybe da yanzu nima ina neman admission din amma yanzu ya wuce ni sai next year. Bayan na dawo ne na tarar da bakuwa a palo tana jirana. Fauziyya. Sai naga duk ta chanja duk babu gayun nan, ga hijab a jiki, the first time da naga Fauziyya da hijab. Daga yanayin fuskarta na gane itama ta karbo tata takardar sai na maze muka gaisa tana ta yiwa Subay'a wasa, ni kuma sai na kira Subay'a na aike ta gurin Inna dan yanzu sam bana son yin hira a gabanta. 


Sai Fauziyya ta miko min wata takarda tace "kinga Halima" na karba na bude a raina ina saka ran ganin irin tawa takardar amma sai naga report ne daga asibiti da yake nuna cewa Fauziyya tana dauke da juna biyu. Na ninke na mika mata ina kokarin kakalo murmushi nace "well congratulations" sai ta fara share hawaye tace "zubar wa zanje inyi Halima. Ya zanyi dashi? Na gaya miki nayi aure ne saboda ina son inyi settling down a gidan miji, wannan cikin would have been a good news da ace abinda ya faru bai faru ba, yanzu ta yaya zanyi inyi raising baby alone babu miji babu mataimaki? Kinsan iyayena basu da rai, kuma yanzu ba kowa ne zai aure ni da baby ba, Saghir kuma...." Sai ta rufe fuskarta tana kuka, na taso na dawo kusa da ita ina rarrashinta tace "jiya da yamma naje ganinsa, ya bani takarda wai ya sake ni saboda bashi da ranar fitowa. Bai ma san da cikin ba ban gaya masa ba saboda so nake in zubar dashi" nace "to yanzu ni me yasa kike gaya min? Ba kya ganin cewa kina gaya min ne saboda deep down ba kya son zubarwar kina so wani ya baki shawara yace kar ki zubar?" Ta dago kai tana kallona sai ta gyada kai tace "haka ne, ina son baby na amma ya zanyi" nace "ni ba gashi yanzu an barni da Subay'a ba? Ke da kinyi karatu, ni fa secondary school kadai na gama da kyar, ba zaki iya ki nemi aiki da takardun ki ba ko dan teaching ne ko da private school ce ki ke yi kina samun kudin da zaki rike kanki da abinda Allah ya baki ba? Ni ina ganin in dai ba gani kikayi zaki takura ba to gwara ki ajiye batun aure a side ki samu abinyi first, in mijin yazo along the way shikenan, who knows? Maybe kiga Saghir ya fito nan bada dadewa ba" sai naga hope yazo fuskarta tace "da gaske? Zaki taimaka masa?" Na gyada kai nace "zanyi iyakacin kokari na, amma babu guarantee. Sai dai ina so kiyi min alkawarin ba zaki zubar da cikin ba" ta gyada kai da sauri tace "na fasa zubarwa insha Allah. Allah kuma ya baki sa'a akan abinda kika saka a gaba". Mun jima muna hira sannan na raka ta bakin hanya ta tafi. 


Kwana biyu bayan nan da sassafe ina bacci naji ana ta haya niya a tsakar gida, na leko ta window sai naga ma'aikata ne suke ta shigo da kayan gini, na tashi na fito palo na gaishe da Inna na tambayeta "aikin menene za'ayi a gidan nan?" Sai tace "can dakunan za'a gyara sai a zuba kayanki da aka kwaso" ban wani damu da aikin ba da yamma zan tafi islamiyya na leka naga kusan sabo ake mayar da gurin. Hatta plaster da floor an kankare ana sake wasu, an cire ceiling da electric wiring duk za'a sake sai na dawo gurin Inna nace "wannan aikin Inna a ina aka samu kudin yinsa haka?" Bata kalle ni ba tace "matse bakina sai in gaya miki" ban sake cewa komai ba na juya na fita. 


Washegari da safe aka sauke katangar da akayi a tsakiyar gidan mu ya koma kamar yadda yake ada. Kwana biyu ana aikin aka mayar da tsofaffin dakunan inna tamkar brand new dan in ba sanin su kayi ba ba zaka gane suba. Maimakon inga an kawo kayana da aka debo daga gidan Saghir sai naga ana shigo da wadansu kayan wadanda ko a ido ka kalla kasan ba class dinsu daya da wadancan nawan ba. Sai na sake komawa gurin Inna "Inna ina wadancan kayan da aka dauko?" Bata kalle ni va tace "na siyar dasu na kara jari" sai na mayar da bakina na rufe.


Asma'u tana shigowa na jata gefe daya yadda Inna ba zata jiyo ba na fara zazzaga mata masifa "ke ce kika ce da mutumin can ya gyara mana gida?" Ta daga kafada "wanne mutumin kuma?" Nace "kar ki raina min hankali kinsan wanda nake nufi ai" tace "the last time I checked shima gidan su ne. Menene laifi a ciki dan na gaya masa masu haya sun tashi za'a zuba kayanki a ciki shine yace a bari azo a gyara gurin tukunna. Daga nan kuma sai ga kaya ya aiko dasu a zuba" na bita da harara nace "kice masa......" Tace "ince masa an gode? To zan gaya masa" sai na dauki katako kamar zan dake ta ita kuma ta fice da gudu.


Wasa wasa ana gama wa da dakunan inna nada muka koma ciki muka tare. Inna da Asma'u daki daya ni da Subay'a daki daya. Na dauko akwatunan kayan sawar mu da muka debo daga gidan Saghir na jera mana abin mu. Subay'a tana ta murna wai munyi sabon gida. "In Daddy ya dawo anan zamu zauna tare dashi".


Daganan kuma aka fara gyaran dakunan Baffa. Aka gyare su tas suma aka saka sababbin furnitures aka barsu a matsayin gurin saukar baki. Inna tayi ta gayyatar yan uwa su zo suga sabon guri, kowa yazo ya gani yayi ta sam barka. Lokacin ne Adda zubaida itama tazo dai ta jani gefe tace "Alhaji ne ya turo ni gurinki. Yace inyi miki godiya sosai akan irin kokarin da kika yi tayi a lokacin shari'ar Saghir. Allah yayi miki albarka Allah ya bar zumunci kuma Allah yaji kan baffanku" nace "ameen. Shi kuma Allah ya fito dashi" "hmmmm" kawai tace, sannan tace "ki samu lokaci kije ki dubo alhajin" nace "to". Sai kuma na kawo mata shawarar da nake ta sakawa a raina tuntuni nace "Adda, a shawarce ku manyan mu tare da Aunty Fatima dasu Inna ku ya kamata ku shiga cikin maganar Alhaji da Kawu. Ya kamata su daidaita haka nan tunda wanda ake rigimar a kansa ma yana can a rufe" tace "zasu daidaita ne, amma ba nan kusa ba kinsan cikin suwaiba ya ki fita har yau, shegen jika za'a ajiye musu, yarinyar ma an kaita Kollere a can zata haihu" na dafe kaina ina jin babu dadi, ina taisayawa yarinyar nan wallahi Saghir ya shafa mata bakin fenti marar goguwa. Yanzu dai yaya biyu za'a haifawa Saghir kenan. Sai na bata labarin cikin jikin Fauziyya, ta rike baki tace "to ai kuwa bana jin mutan gida sun sani".


Duk wannan abinda ake yi shi oga mai gyaran gida ko keyarsa ban gani ba. Ban san ko ya dawo daga so called tafiyar ba ko kuma bai dawo ba. Amma kusan kullum ina jinsu suna waya shida kanwarsa kuma nasan suna gulmata dan sai inga ana maganar ana kallona ana dariya. In naga haka sai in tashi in bar gurin. 


A haka har akayi resuming school. Nayi wa inna maganar Subay'a sai tace in bincika makaranta mai kyau sai na gaya mata har na bincika ma na samu wata anan kusa damu wadda zata iya zuwa da kanta. Sai tace da safe in je inji fee dinsu da sauran abubuwa. Amma da safen ina tashi sai naga Asma'u ta tashi itama tana shiryawa nace ina zata je wai "hamma yace in shirya in shirya Subay'a zai zo da wuri muje a sata a school" cikin fada nace "oh dama yana gari kenan. In shi ya haifar min yar ba sai yazo ya dauke ta ba in gani" sai naga duk sun tsaya suna kallona sannan na fahimci nayi rashin kunya a naganar. Nace "amma inna sai ya fara gaya min ai ko? Kulawa ma ai yabawa ce" Asma'u tace "yace ai fushi kike yi dashi. Wai in yayi miki magana ma ba zaki kula shi ba" nace "ya gwada ya gani? Ni ina na ganshi ma balle inki kula shi?" Sai tace "to ki shirya sai kuje tare ku kaita" na tashi nace "bazanje ba ai bai gayyace ni ba".


Ina kallo suka fita, sun jima sannan suka dawo Subay'a tana ta bata rai amma suna zama sai ta fara bani labarin sabuwar makarantar ta, ta nuna min uniform dinta da books din da already aka riga aka bata. Gobe zata fara zuwa fresh. Sai kuma naji dadin kula Subay'a da yayi har ya tuna cewa sabon session za'a shiga ya kamata  sata a school. Daganan kuma sai ya ajire driver wanda kullum yake zuwa ya kaita school sannan in an tashi ya dauko ta.


Asma'u ta samu admission a northwest university ta fara karatu. A lokacin ne nima na gayawa Inna kudirina na shiga computer school kafin shekara ta zagayo in nemi admission, harda karawa da cewa "irin wadda Sadauki yayi lokacin da baici jamb ba" wai duk dan ta bari saboda naga yanzu shine favorite person dinta. Amma sai ta tabe baki tace "wato ke lissafin karatu ma kike yi kenan, auren kuma fa?" Naji kamar zan saka kuka nace "aure kuma Inna? wanne irin aure dan Allah dan Annabi?" Sai tace "au baki san wanne irin aure ba? Ai kin kusa gama idda zaki sani a lokacin"  kamar ta fada da bakin mala'iku kuwa a ranar sai ga third period dina tazo. Ina cikin saka pad a daki sai gata ta shigo ta kalleni tace "to alhamdulillah!" sai naji duk kunya ta rufe ni. A raina nace "shin wai Inna auren dole zata sake yi min ne?" 


A ranar na shirya nace gidan Mama zan tafi in kwana biyu, amma inna ta hana ni tace "islamiyyar fa?" Haka naja jakata na mayar daki na dawo palo na cigaba da zama. 


Two weeks bayan nan, ina zaune zaman kallo zaman kashe wando kamar kullum sai jin muryar Sadauki nayi a tsakar gida yana tsokanar Subay'a da sunan da yake gaya mata "Subis" sai na mike da sauri har da dan guduna na shige daki na rufo kofa. Sound proof ne dan haka bana jiyo mai suke yi a palon sai daga baya Subay'a ta shigo ta turo baki, ta zauna a gefe na tace "wannan yayan naki ne yazo" nace "kin gaishe shi?" Ta gyada kai. 


Dan rashin ta ido sai ganin kiran sa nayi a waya ta. Na kalli wayar a raina nace "lallai ma Sadaukin nan" ina kallon wayar wannan kiran ya shigo ya katse wani ma ya shigo har ya gaji ya daina. Sai na dauki wayar ina kallon number din. Finally dai anyi unblocking dina kenan. Ya kamata dai inyi saving number din nan, amma wanne suna zan saka masa? Sadauki? Ko hamma kamar yadda naga Asma'u ta saka?


Sai kawai na bude keyboard dina nayi typing "Aliyu" nayi saving. Asma'u ta budo kofa ta shigo tun kafin tayi magana nasan me zata ce "ki zo inji Inna" na dauki hijab dina na saka na fita. Yana zaune can carpet a gefen kujerar da Inna take zaune, an cika masa gabansa da kayan ciye ciye, yayi kwalliyarsa cikin normal kananan kayansa. Nayi saurin dauke kaina daga kansa saboda zuciyata da naji tana kokarin barin kirjina. Na zagaya naje na zauna can nesa dasu nace "Inna gani" tace "baki ji Sadauki yazo ba? Ai dai kya fito ki gaishe shi ko?" Na kalleshi muka hada ido, har da wani langwabar da kai kamar wani abin tausayi. Na dauke kaina nace "sannu da zuwa" yace "yauwa. Ya gida ya makarantar?" Asma'u ta fara bashi labarin school dinsu, yana ta tsokanar ta wai jambite ni dai sai na mike zan bar musu gurin sai yayi sauri ya tashi yace "Inna zan wuce, Allah ya bamu alkhairi" tace "ameen, Allah yayi albarka" sai da ya je bakin kofa sai ya juyo yana shafa kai "ammm, Diyam. Akwai sakon Subay'a a mota ko zaki zo ki karba" nace "Asma'u, bi shi ki karbo mata" sai ta mike tayi hanyar daki tana waka "you know I love it when you call me senorita" ta shige daki ta rufo kofa. Na cigaba da zama na shi kuma yana tsaye a bakin kofa yana kallona sai kawai gani nayi Inna da dauko mafici tayo kaina dashi sai na tashi da sauri na fita. 


A garage na same shi a tsaye yana dariya. Na hade rai nace "ina sakon?" Yace "yanzu ke baiwar Allah sai Inna ta biyo ki da mafici sannan zaki zo gurina?" Nace "akwai sakon da zan karba ko babu?" Ya jingina a bango ya rungume hannayensa yace "babu, just want to see you, that's all" nayi shiru, trying so hard not to look at him, yace "ba kya son gani na yanzu ko?"

[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Fifty Eight : Murjanatu


Na dauke kaina gefe nace "tunda babu sakon da zaka bani, Allah ya bamu alkhairi" na juya zan tafi sai ya zagayo ta gabana ya tsaya yace "look into my eyes and tell me ba kya son ganina and I promise you I will leave you alone" na daga ido na kalle shi amma muna hada ido sai nayi saurin sunkuyar da nawa idon kasa saboda wani zazzafan sako daya iso gare ni daga cikin idanunsa, sai na jawo fuskar hijab dina na rufe fuskata dashi, amma ina ganin duhunsa, sai naga ya sunkuyo dai dai fuskata yace murya can kasa "open your eyes and look into my eyes kice 'sadauki bana son in sake ganin ka" sai na juya fuskata daya side din nace "ka bani hanya in wuce, ko ka manta na baro 拼ata a daki ita kadai? And she needs me saboda babanta bayanan yana prison" sai ya gyara tsayuwar sa yace "hmmm. Gori zaki yi min kenan ko? Wai '拼ata'" ya fada yana kwaikwayon magana ta. Bance komai ba sai kuma yace "Subay'a will be fine, nayi miki wannan alkawarin. Na san ba zan taba replacing mahaifinta ba, amma zanyi duk iya kacin kokari na inga na bata duk abinda ya kamata uba ya bawa yarsa. Kar ki manta ina da training din rikon 蓷an wani. Ban tashi da ubana ba duk kuwa da cewa yana raye, and still I have gotten the best fatherly care and love"


Na fahimci zancen Baffa yake, sai na bude fuskata ina kallonsa nace "hakane, amma banbancin ka da Subay'a shine shi Baffa bai rufe mahaifinka a prison ba sannan bai yi gidan gona a cikin gidan grandfather dinka ba. No child will ever forget that". Ba tare dana kalleshi ba na wuce shi na koma ciki. 


Ina shiga na wuce Inna a palo na shiga daki ina jin zuciyata tana yi min zafi, haushin Sadauki nake ji kuma haushin kaina nake ji. Ji nake kamar wani dan karamin yaki akeyi tsakanin zuciyata da 茩wa茩walwa ta ko wanne yana gaya min abinda zanyi. Sai na sake jawo jakata na kuma hada kayana kamar rannan na fita na samu Inna a dakinta tana sallah sai na zauna na jira ta sai data idar sannan ta juyo tana kallona, daga yanayin zaman da nayi tasan magana ce a bakina dan haka tace "ya akayi?" Nace "Inna, alfarma nake nema a gurin ki. Dan Allah Inna ina so ki fita daga maganar Sadauki" ta kalle ni da mamaki tace "ban gane ba? In fita daga maganar sa kamar yaya? Wacce maganar kenan?" Sai nayi shiru na kasa bata amsa sai tace "ba kya sonsa ne yanzu kuma?" Na girgiza kaina nace "kawai dai Inna ina son ajiye maganar sa a gefe sai zuwa lokacin da muka sake fahimtar juna tukunna. Kinga shekaru da yawa, abubuwa da yawa sun chanja. Ba lallai ne halayyar sa ta da ita ce a yanzu ba. Ni so nake ki bar mu ni da shi kiyi ta mana addu'a in Allah yasa muka fahimci juna sai mu sanar muku ku saka mana albarka" a juya kanta gefe tace "fushi kike dashi akan maganar Saghir ko?" Nayi shiru, sai ta cigaba "ruwansa ne in yaga dama ya yafe masa, ruwansa ne kuma in bai ga dama ba kuma yaki. Ni ba wai ina matsa miki ki kula shi ko ki aure shiba, ina kokarin gyara abinda na bata ne a baya, ina kokarin bashi abinda na hana shine a baya tare da fatan ko hakan zai rage min laifuffuka na a gurinsa da kuma a gurin ubangiji. Dan haka ni dai shi nake so ki aura, amma zabi yana gurinki in kince a'a bazan ji dadi ba amma ba zan matsa miki ba".


Nace "Nagode Inna" sai kuma na gabatar mata da bukata ta tason zuwa gidan Mama. "Kwana biyu" ta ce min, naso ta barni inyi sati ko ma sati biyu amma taki, haka na hakura na dauki kaya set biyu da safe na tafi tunda ina son zuwan saboda ina so muyi shawara. 


Ina zuwa na tarar Rumaisa tazo, na saka ta a gaba da tsokana mai ciki mai ciki ita kuma tana ta jin kunyar Mama, sai da muka kebe tace "wai dama haka ake ji in ana da ciki?" Hmmm kawai nace mata a raina ina cewa wannan kukan dadi take yi, na tuna cikin twins ina 14 years, babu abinda na sani, ga babu miji babu iyaye. Na tuna cikin Subay'a yadda na sha wahalar laulayi, da gorin da Saghir yayi min wai daga an taba ni sai ciki. 


Sai da muka samu zama sannan na bawa Mama labarin cewa Sadauki fa ya dawo, bai dai furta direct ba amma ya nuna. Ta daga kafada tace "so? Ji nake murna zakiyi kuma naga kin bata rai" sai na gaya mata kuduri na akansa. 


"Ba wai bana son aurensa bane ba Mama, so nake ya kunce kullin da yayi da kansa, saboda jin dadin kansa kuma Subay'a" tace "so kike ya yafewa Saghir kudin da yake binsa?" Na girgiza kai nace "ba wannan kadai ba, so nake ya taimaka masa yayi solving drug case dinsa. Sadauki yana da power, zai iya jan wasu strings ayi closing case din Saghir na drugs, ko kuma ayi tracking Kabir a kama shi asaka shi ya amsa laifinsa. Bayan ya fito dashi kuma ina so ya bashi aikin yi, saboda nasan with that reputation babu ma'aikatar da zasu dauki Saghir aiki ballantana ya samu abinda zai rike yayansa". Mama tace "anya kuwa Diyam wadannan sharadan naki basuyi tsauri ba? Wane ne zai je neman auren mace kuma tace masa sai ya fito da tsohon mijinta daga prison kuma ya bashi aiki? Anya kuwa kina ganin zai amsa?" Na girgiza kaina nace "ban sani ba Mama, shine kuma shawarar da nake so ki bani yadda zan saka Sadauki ya karbi wannan maganar. Ni dai abinda na sani shine zuciyar Sadauki tayi tauri da yawa, ya kasa yafewa wadanda yake ganin sun cutar dani da shi. Kuma nasan  gurin Sadauki Saghir yafi kowa ba茩i, shi yasa nake so ya yafe masa kuma ya taimaka masa. Nasan in dai har ya iya yafewa Saghir to babu wanda ba zai yafewa ba, in dai har ya taimaka wa Saghir to babu wanda ba zai taimaka wa ba".


Mama tayi shiru tana kallona sannan tace "zuciyarsa tana da tauri tabbas, ke ai kinsan haka tun kuna yara haka yake kuma sai rayuwa ta kara taurara shi. To ni a shawara ta ba juya masa baya zaki yi ba jawo shi kijinki zakiyi. Ki nuna masa irin son da kike masa ki bashi dama ya nuna miki nasa, to shi kansa ba zai san sanda zuciyar tasa zata rissina ba, abinda zaiyi ke kanki sai ya baki mamaki".


Kwana na biyu gidan Mama na shirya zan koma gida Inna ta kirani. "Sadauki yazo dazu, na gaya masa kina nan gidan yau zaki dawo sai yace zai zo ya dauko ki" nace "to" a raina ina jin haushin mai yasa ba zai kira ni ya gaya min ba.


Sai bayan magrib sannan yazo, har na gaji da jira na kwanta a palo ina game a wayata sai ga kiransa "Aliyu" nayi tsaki sai kuma nayi murmushi na daga nayi sallama, ya amsa yace "na dauka ba zaki dauki wayar bama ai. Kin san ni yanzu tsoran ki nake ji fa" nace "naga alama kam. Amma ai ba yanzu ne ka fara tsoran nawa ba dama ka dade kana yi" sai yayi dariya, and I couldn't remember the last time da yayi dariya irin haka. Nima sai nayi murmushi. Yace "ina waje, Please kar kice da Mama ni nazo dan kunyarta nake ji"  na tashi na shiga dakin Mama zan mata sallama tace "da daren nan" sai na sunkuyar da kaina nace "Sadauki ne yazo zamu tafi tare" tace "kuma babu gaisuwa? Ki ce masa ya shigo mana" na dauki waya na kira na gaya masa yace "ke ba'a sirri dake? Ban taba zuwa na gaishe ta ba sai kuma in zo in fitar mata da 拼a? Ni kunyar ta nake ji" nace "to ai in bance kai ne ba ba zata barni ba cewa zata yi dare yayi" a dolen sa ya shigo, yana ta sunkuyar da kai yana shafa keya, and I asked myself "wai me yasa maza in suna jin kunya suke shafa keyar su?".


Bayan ya fita nayi wa Mama sallama na bishi a baya. A cikin mota na same shi a zaune a seat din driver. Sai ya bude min kofar gaba yayi min alamar in shigo da hannunsa. Na shiga na rufo kofar sai ya juyo yana kallo na, na sunkuyar da kaina kasa ina feeling uncomfortable. Motar naga kamar tayi mana kadan, space din tsakanin mu yayi kadan, ga motar ta cika da kamshinsa mai shiga har cikin ruhi. Sannan kuma gashi yana min murmushi.


Naji kamar in bude motar in fice. Bai kunna motar ba ya juyo yana kallona Yace "wai ke duk fushin ne haka? Me zanyi ne wai ayi min murmushi ko guda daya ne" sai na kara bata rai na turo baki yace "okay rashin kunyar tana nan ashe kenan. Na dauka an barwa Subay'a" sai ya tayar da motar muka bar gidan.


A hanya yace "kinsa naji kunyar Mama fa, banzo na gaishe ta ba sai da nazo zance" na kalle shi nace "zance? Gurin wa kaje zancen? A kano muke fa ba'a Maiduguri ba" ya dan bata rai kamar mai tunani sai kuma yayi dariya yace "ohhh okay, yanzu na gane wannan fushin na menene. Ai na gaya mata zan zo gurinki dama kuma tace in gaishe ki" nace "kar ma kayi tunanin da nake tunanin kana yi. It is not what you are thinking" yace "yes it is. Hausawa sunyi karin magana suka ce kishi kumallon mata, amma ke naki kishin aman gaskiya yake saka ki. Daga jin muna magana da Inna sai ki kama amai?" Na gane maganar da yake yi nayi saurin cewa "ba fa abinda kake tunani bane ba, bani da lafiya dama a lokacin. To ni ina ma ruwa na da aurenka" yace "okay idan rashin lafiya ta saki amai ita ce kuma ta saka daga nayi miki sannu kika rufe ni da fada?" Nace "kaga nifa bana son ake juya min magana ta" yace "shikenan, an daina" muka cigaba da tafiya sannan yace "na bata labarin ki. I told her ina son aurenki first and she agreed" ya fada yana kallona, nayi kamar ban jishi ba ina jin bacin raina yana karuwa, amma sai ya sake cewa "tana sonki sosai. Tace zata zo Nigeria karshen week din nan purposely saboda ta ganki" na saka hannuna na toshe kunnuwa na ina jin zaman motar duk ya ishe ni. Nace "stop the car" yace "why?" Nace "ko dai ka daina wannan maganar ko kuma ka tsayar da motar nan in fita in karasa a kafa" sai ya kama dariya yace "an daina your highness".


Muna zuwa gida nayi masa godiya, kafin in bude kofar ya kira suna na "Diyam" na juyo ina kallonsa yace "Please in na kira ki ki dauka kinji. Say whatever you want to say in kin dauka din but please kar ki 茩i dauka".


Ranar na jima banyi bacci ba ina juyi. Feeling a familiar warmth a cikin zuriya ta wanda a da naje tunanin ko ba gushe yanzu baya nan. Zuciyata da 茩wa茩walwa ta suka cigaba da battle dinsa ni kuma na zama confused dan bansan wanne daga cikin su zan bi ba. My heart was telling me in kira Sadauki a waya, in bude masa zuciyata in gaya masa irin zurfin da soyayyar sa tayi a ruhina, while my mind was asking me to hold on, reminding me cewa ba lallai ne in Sadauki ya samu abinda yake so ni kuma ya bani abinda nake so ba.


Washegari da safe bayan na dawo daga islamiyya ya kirani, daga alama a office yake "kinci abinci? Me kika ci?" Nace "kosai Asma'u ta soya mana" yace "yan gayu. Ni kuma kinga yunwa nake ji babu wanda ya damu yace Sadauki ga abinci" nace "Sadauki ko Mr Abatcha?" Yayi dariya yace "all the same" nace "ni banga same ba. Sadaukin dana sani is different from this rich Mr Abatcha" yace "really? To fada min menene bambancin" nace "da farko dai Sadauki baya taba yin abinda zai bata ran Ummah ko Baffa. Ita kuwa Ummah a cikin masu hakuri ma ita daban Allah yayi ta, bata taba fada ballantana har ta kasa yafewa wadanda suka bata mata. Na tabbatar kuma zata so ace yayanta, ni da kai, munyi koyi da ita, ko da bamu zama irin ta ba sai mu kwatanta ko yaya ne" 


Ya jima shiru sannan yace "she was a good woman. The best. Bata bata wa kowa, in mutum ya bata mata ma sai tayi kamar bata gani ba duk kuwa da cewa ta gani 蓷in. Har gida har daki za'a zo aci mutuncin ta ba tare data yi laifin komai ba and she will always looked at me and said "kar kayi magana, kar kace komai" and I will keep quiet. Amma ranar data mutu kinsan me Alhaji Babba yace? Cewa yayi ba za'a shigar da gawarta gidan mijinta ba as if she were some kind of trash" na goge hawayen daya taru a idona ina tuno wa da abinda ya faru a ranar data chanja gabaki dayan rayuwata. 


Nace "sai menene kuma? Hakan ai bai rage ta da komai ba a wajen ubangijin ta, kuma muna saka mata ran cewa yanzu tana gurin da yafi gidan nan kyau da daraja. Kuma nasan da ace zata kalle ka a yanzu zata ce "kar kayi magana, kar kace komai" saboda tana son ka zama mai hakuri mai yafiya irin wanda Allah yake so, Annabi kuma yake alfahari dasu" yace "nasan abinda kike so ki ce, so kike yi kice in yafe musu gabaki dayan su, amma abinda kika manta shine, su fa basu yi nadama ba har yau. Yes, Alhaji ya bani hakuri ranar nan amma daga ni har ke har shi munsan cewa tuban muzuru yayi, na saka shine a corner babu yadda zaiyi shi yasa ya bani hakuri amma a lokacin da yana da dama da ina juya bayana zai da蓳a min wuka" 


Nace "na sani, amma wannan shi da ubangijin sa, ni da kai na damu ba dasu ba, zuciyarka nake fatan gyarawa and maybe a kokarin haka kaga tasu itama ta gyaru. Kasan abinda na fahimta? Babu abinda yafi saukarwa da mutum nadama irin idan wanda akayi wa sharri yayi sakayya da alkhairi. Take Inna as an example. Ba karamar nadama ce Inna tayi ba kuma a yanzu babu wanda take kaunar farantawa sama da kai" ya ajiye numfashi yace "kina so in yafe musu?" Nace "yes, amma badan ni zaka yafe ba. Dan Allah zaka yafe. Take your time and think over it. Kai da kanka zaka yanke shawarar yin abinda ya dace". Sai ya chanja maganar "yanzu ya za'ayi a kawo min kosan nan zuwa office?"


Kamar wasa few days bayan nan da daddare ina shirin kwanciya ya kira ni "me kike shirya wa bakuwar ki ne?" Nace "wacce bakuwar kuma?" Yace "kin manta nace akwai wadda zata zi gurinki?" Naji duk nishadin dana ke ji ya kau, nayi shiru yace "gobe zata sauka. Jirgin safe. Ni ina da meeting about that time. Ki shirya sai in turo miki da mota kije ki dauko ra a airport" nace "ni kuma? To ni da bansan ta ba  ta yaya zan gane ta?" Yace "ki saka bakar doguwar riga ita kuma zata saka milk. You will know her when you see her" na hadiye abinda ya tsaya a kirjina nace "ya sunanta?" Yace "Murjanatu".


Not edited. Sorry for the typos.[3/4, 8:20 PM] +234 703 589 5826: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episodes Fifty Nine & Sixty : The Answers


Da safe na gayawa Inna sakon Sadauki. Tace "to fa! Sai kije ki dauko ta din. Anan zata sauka ne ko kuma a wani gurin daban?" Nace "nima ban sani ba inna" sai tace "to ki kira shi ki tambayeshi mana, in nan zata sauka ai gwara mu sani dan ayi mata abinci ko?" Na kasa kiransa saboda ji nayi duk haushinsa nake ji, sai na tura masa text "a nan zata sauka?" Sai da na fito daga wanka naga reply dinsa, "bakuwar ki ce ba tawa ba. Besides, ni gwauro ne bani da gurin da zan sauke ta".


Karfe goma da rabi yace min jirgin su zai sauka. Karfe goma driver yazo yana jirana. Asma'u tana school Subay'a ma haka, dan haka dole na shirya ni kadai na fita ina ta bace bacen rai. Sai 10:30 muka je airport din a raina ina cewa 'in sun sauka ma ta jira, da waye ya gayyace ta zuwa wajena?" Sai kuma nayi rashin sa'a jirginsu yayi delay dan haka sai da muka jira ma sannan suka sauka. Ina tsaye da bakar rigata da ya umarce ni in saka idona akan kofa ina ganin masu fitowa, mostly turawa ne maza da mata, sai few blacks suma kuma yawanci maza ne sai kuma wasu family da suka fito tare. Sannan na hango ta ta taho, tun daga nema na ganeta saboda kalar rigar jikinta. Waya a makale a kunnenta tana magana tana murmushin da yake bayyana hakoranta, naji kirjina ya buga da karfi a lokacin da zuciyata ta ayyana min wanda suke wayar dashi. 


Ta fito waje sosai tana dan dube dube, idonta ya sauka a kaina sai naga ta sake fadada murmushin ta ta katse kiran sannan ta taho inda nake. I was suppose to like nima in tafi inda take sai mu hadu a hanya amma sai nayi tsayuwata pretending as if ban gane taba har ta karaso gaba na tana murmushi tace "Diyam?" Sai kuma na kirkiro murmushi nayi mata ina studying dinta. Baka ce, mai matsakaicin jiki kyakykyawar gaske and every part of her was screaming "I am rich" dan kallo daya zaka yi mata kasan cewa bata san wata kalma wai ita wahala ba. And something caught my attention, kalar skin dinta, manyan fararen idanuwanta, shape din fuskarta da kuma yanayin murmushin ta irin na Sadauki ne. Na tambayi kaina "are they related? Ko hadin gida za'ayi musu?"


Na kirkiro murmushi nace "Murjanatu?" Sai tayi dariya, ta saka phone dinta a cikin karamar jakar da take rataye a kafadarta sannan sai kawai naga ta rungume ni, ta sake ni tana kara kallona tace "wow, you are even more beautiful in person than yadda aka kwatanta min ke" na danyi dariya ina tunanin tsaurin ido na Sadauki da zai zauna yayi wa budurwarsa description dina. Nace "welcome to kano, fatan dai baki sha wahala sosai ba" ta yarfe hannu tace "zafi, haka kullum in muka je Maiduguri nake fama. Kamar ace an ciro mutum daga cikin freezer ne an saka shi a cikin oven. Na kan tambayi Adama, wai haka kaji sukeji in ana gasa su? irin frozen chicken din nan kuma a saka su a oven" nayi dariya a raina ina cewa wannan surutu ne da ita. 


Drivern da muka zo dashi ya zo ya fara jan akwatin ta ni kuma sai na mika hannu da niyyar in karbi jakar hannunta amma sai taki bani tace "rufa min asiri, so kike yaya ya gasa ni kamar gyada?" Na maimaita kalmar yaya a raina. So they are related da gaske.


Muna tafiya veil din kanta ya fado kafadarta ya bayyana gyararren gashin kanta, but sai naga bata damu data gyara ba har sai da ni da kaina na gyara mata. She just thank me casually muka cigaba da tafiya.


A hanya muka dan taba hira, duk da dai da yawa daga hirar ita takeyi, a lokacin take gaya min cewa wannan ne zuwan ta kano na farko "in munzo Nigeria gida muke zuwa, Maiduguri, sai Abuja sometimes, mun dai taba zuwa Kaduna once" jin haka sai na fara yi mata bayanin guraren da muke wucewa a hanya, and she looked very interested. 


Da muka je gida ina kallonta ina jiran inga tayi wa gidan mu wani kallo haka, ko kuma in an bata abinci inji tayi wani comment marar kyau amma sai naga sam babu abinda ya dame ta, she is the most down to earth person I have ever met. Ta zauna ta harde kafa tana ta cin tarin abincin da Inna ta jera mata tana kuma yiwa Inna hira. Sai tace "ina 'yar Asama? Kullum sai an bamu labarin Yar Asama da Diyam, Diyam this Diyam that. Ko kaya muka saka sai yace "ku kun mayar da kanku turawa, kuyi ta saka kananan kaya, why can't you dress like Diyam?" Ta fada tana kwaikwayon yadda Sadauki yake maganar sa.


Na kai mata kayanta dakina sannan na hada mata ruwan wanka a toilet nace tayi wanka ta huta. Bata tashi ba sai da Asma'u ta dawo daga school, ina jin Inna tana yi mata bayanin bakuwar da akayi sai kuwa naga ta tura baki tana kunkuni, Inna tayi mata warning kar ta sake tayi mata wata magana marar dadi.


Na shiga daki na tarar ta tashi daga bacci tana sallah, na zauna ina jira har ta idar sannan na tambayeta ko da akwai abinda take so. Kafin ta bani amsa Asma'u ta shigo tace "nazo gaishe da matar yayana" sai naga Murjanatu ta kalle ni sai ta cigaba da nineke abin sallah. Asma'u ta sake cewa "matar yaya barka da zuwa" sai Murjanatu ta kalle ni tace "ana miki magana" nace "ke take gaisarwa fa" sai tace "matar yaya naji tace, wanne yayan?" Na gyara zamana ina so inyi confirming suspicio dina Nace "Sadauki mana" ta dan bata fuska tace "waye Sadauki?" Na sunkuyar da kai nace "Aliyu, mu anan Sadauki muke ce masa" cikin mamaki tace "yaya Aliyu? Nice matar tasa kuma?" Nace "well, not legally yet, yace dai an bashi ke an kusa biki" sai ta zauna a bakin gado ta dafe kanta tana dariya tana kallona tace "tsokanar ki yake, he is my brother, my half brother, baban mu daya". 


Har dare Murjanatu tana ta tsokana ta. Ina jinsu suna waya da Sadauki tana bashi labari suna dariya sai na harare ta daga ita har wayar tata, ina jinta ta gaya masa wai ina hararar ta sai naga ta saito ni da wayar kamar zata min hoto sai na rufe fuskata ita kuma tayi ta min hotuna a haka.


Sosai Murjanatu ta sake a gidan mu, nan take muka kulla kawance mai kyau a tsakanin mu. Tana ta yimin hirar gidan su, Papa, Mama, Adama, Sa'adatu, Yani. Amma ban taba yi mata tambaya a kansu ba, na saka a raina cewa Sadauki ne ya kamata ya bani labarin su. Na fahimci kuma tana tsoron Sadauki, duk da kuwa na kanga suna yin waya suyi hira amma kamar bata taba ketare maganar sa, bata yi masa musu, kuma tana bani girma sosai saboda shi.


Ranar nan bayan Murjanatu ta kwana uku da zuwa muna waya dashi tace gobe mu shirya gabaki daya zai zo mu fita yawo "mu zagaya da Fanna taga garin Kano" nace "Fanna?" Yace "yes, Murjanatu. We call her that a gida". 


Ina gaya musu sai murna, nan da nan Asma'u ta fara making list na guraren da zamuje, aka fara ware kayan da za'a saka da irin kwalliyar da za'ayi. Murjanatu ta kalleni ina yi musu dariya tace "gobe sai na yi miki kwalliya. Asma'u zata rike min ke in kinki tsayawa".


Na dauka wasa suke sai washegarin na fito daga wanka sai gasu da make up kit, nace bana so amma haka suka tilasta min suka yi min kwalliya. Na dauko abaya ta na saka sai Murjanatu ta tsaya tana kallo na tace "wannan rigar is too loose, bai fitar da duk abinda ya kamata ya fitar ba bayan kuma akwai abin" sai ta dauko wani belt a kayanta ta daura min, na kalli kaina a mirror naga yadda hips dina suka fito sosai, ni kaina bansan ina dasu har haka ba, sai na girgiza kaina nace "bazan iya fita haka ba. Mutane zasu ke kallona fa" sai ta dan dake ni a kafada tace "dalla in sun kalle kin sai me kuma? Ke wallahi halin ku daya da yaya Aliyu yanzu zaku fara wa'azi" nayi dariya kawai amma na hakura ne kawai dan bana so in gwale ta amma ni nasan bazan iya sakewa ba sam. 


Muna gamawa yazo, muka fita ni dai ina ta rabe rabe a bayansu. Muna fita muka hango motarsa duk da bama ganinsa but I felt his eyes on me sai na kara buya a bayan Murjanatu ina jin kamar zan gurde in fadi har muka karaso inda yake, Murjanatu ta bude min kofar gaba tace "entere" nayi murmushi na shiga ina jin still idanuwansa a kaina amma na kasa kallon side din da yake, sai naji yayi gyaran murya yace da Murjanatu "koma ciki ki samo mata hijab" sai ta kama bubbuga kafa a kasa kamar mai shirin kuka sai yayi mata tsawa "are you still there?" Da sauri ta koma cikin gida.


Nayi kasa da idona ina wasa da fingers dina, still feeling his eyes on me. Sai yace "kinyi kyau sosai Halima. But I can't let people see you like this. Ina da kishi da yawa I might end up fasa wa wani hanci akan hanya. In son samu nane ma bayan hijab har nikab zaki saka ki rufe fuskarki" tunda ya fara magana nake murmushi, ina jin feeling mai dadi a raina cewa nima ina da value. Sai na tuno da ranar da Saghir yake fito min da gashina "let's show them abinda matansu basu dashi".


Ta kawo min hijab din na saka ya saka hannu ya gyara min fuskar hijab din sannan yace "that's much better" sai kuma ya leka waje yace da Asma'u da Murjanatu "duk wadda bata shigo ba zamu tafi mu barta" da sauri suka bude baya suka shigo suna dariya.


Yawo mukayi sosai a garin kano, har gidan sarki sai da muka je muka shiga ta kofar gudu muka fito ta kofar arewa muka ga grand central mosque. Muka je gidan mesium muka je gidan makama da gidan mutan da. Muka hau badala, muka hau dutsen dala da gwauron dutse. Muka je har government house muka yi zagaye a ciki muka fito sannan muka tafi Abatcha Motors.


Murjanatu tace "yau dai finally zanga wannan precious Abatcha Motors din da yake rike yayana a Nigeria. Ko da yake ban sani ba ko ba shi kadai bane yake rike shi ba" ta fada tana mintsini na ta baya. Na juya na harare ta shi kuma yana mana dariya muka shiga building din. 


Da yake weekend ne duk babu ma'aikata sai security kamar zasu ci mutum. Muna zuwa suka taso kamar zasu durkusa mana ni dai duk sai naji inajin nauyin su. Ya saka su bude ko'ina a gurin sannan yace dasu Murjanatu su zagaya duk inda suke so mu kuma sai ya saka aka kawo mana kujeru gaban wani fountain muka zauna. 


Sannan ya dauko waya yayi kira, da alama abinci yayi mana order. Sai kuma yace min "ranar nan, you asked me some questions. Are you ready for the answers?" Na tuno tambayoyin da nayi masa farkon zuwa na office dinsa. Sai nace "eh. Ina son sani please". Yace "okay. Let's start from the beginning".


"Tun farko na san cewa Alhaji Bukar ne ya hada auren Ummah da mahaifina, amma bamu taba maganar dashi ba saboda ganin kamar umman bata so".


"Sunan mahaifina Alhaji Umar Mustapha Abatcha" nayi saurin cewa "Alhaji Umar Mustapha dai wanda muke jin labarin sa?" Ya gyada kai yace "shifa. Family din Mustapha Abatcha family ne da yayi suna ba'a Maiduguri ba kadai har ma da sauran Nigeriya. Suna da kudi tun asalinsu but kudin Umar Mustapha daban ne dana sauran. Tun yana saurayi ya mallaki kudin da shi kansa mahaifinsa a lokacin bashi da su. Harkar man fetur yakeyi yi, tun yana yin gidajen man fetur a gari gari har ta kai shi ga fara siyan rijiyoyin man fetur din gabaki 蓷aya. Bashi da lokacin aure, dan haka ya jima baiyi ba, wannan yasa yan'uwansa, musamman da yake duk yan uba yake dasu dan shi kadai ne a gurin mahaifiyarsa, suka sako shi a gaba, suna saka ran in ya mutu suci kudi. A lokacin ne Alhaji Bukar, tsohon amininsa da sukayi secondary school tare yayi masa tayin auren bafulatanar yarinya Zainab. Shi kuma sai ya karba yana ganin tunda ba auren soyayya bane ba ba zata ke demanding time dinsa ba. Ta gaya masa labarin wanda take so aka raba su and he was sympathetic, yana nuna mata kulawa sosai ita kuma ta kwantar da hankalin ta sukayi zamansu lafiya a nan family house dinsu dake Maiduguri. A haka har ta samu ciki. A lokacin ne kuna ya fara business da Canada yana exporting crude oil daga Nigeria zuwa Canada wanda har yanzu shine sana'arsa, a yanzu yana daya daga cikin manyan dealers na crude oil a kasar Canada. 


Tunda zainabu ta samu ciki shikenan kuma sai al'amurra suka cabe mata, gashi lokacin baya zama a kasar ita kuma taji duk duniya babu inda ta tsana irin gidan aurenta, babu wanda bata son gani kamar mijinta, babu kuma abinda take son rabuwa dashi irin cikin jikinta. Ta zama kamar mahaukaciya, sai ta fita da gudu sai an bita ana kamota ana dawo da ita gida, wani lokacin kuma sai ta zauna tayi ta dukan cikin wai sai ta kashe abinda yake ciki. Alhaji Umar yana zuwa ya ganta a wannan halin yasan asiri ne dan haka ya hada malamai aka zauna addu'a da magungunan karya sihiri akayi tayi mata, in abun ya lafa kwana biyu sai ya dawo. Ta sha wahala sosai. Ranar nan cikin dare suna bacci ta tashi tafita ko dan kwali babu ta kama doguwar katangar gidan da aka zagaye da waya da kwalabe amma a haka ta haura ta var gidan cikin jinin ciwuwwukan da taji, Alhaji Umar yana tashi yaga bata nan ya fito yayi ta nema babu wanda ya ganta sai ya dauki mota ya fita hankali a tashe. Cikin ikon Allah sai ya samo ta tana ta tafiya kamar zautacciya a kamata da kyar ya saka a mota daga nan sai airport. A can ya samu yayi mata adduoin ta dawo hankalinta ya sako ta a jirgi ta taho Kano ya kira Alhaji Bukar ya gaya masa, shi kuma sai ya koma ya nuna cewa bai same ta ba. Akayi ta nema har da cigiya a gidajen radio daga baya aka hakura.


Ita kuma ta dawo gurin yaya ladi ta zauna a kano. Har ta samu lafiya sosai aka tabbatar duk sihirin dake jikinta ya fita. Anan ta haife ni, Alhaji Umar yazo da kansa yayi min huduba da suna Aliyu "saboda ka zama jarumi ya sa na saka maka Aliyu" daga nan sai ya datse igiyar aurensa da zainabu, ya kuma roki Alhaji Bukar cewa ya nemo wannan wanda take so din yayi kokarin hada su aure, bayan an samo Baffa kuma Alhaji Umar da kansa ya bashi amana ta. "Dan Allah ka rike shi tamkar kai ka haife shi. 茒a na kowa ne ai, wata kila ma kai zaiyiwa rana bani ba. Ni dai kawai ina son shi da mahaifiyarsa su kasance safe". Through all those years da nake gurin Baffa ashe duk Alhaji Umar yana biye da rayuwata, kuma yace ko da sau daya Baffa bai taba neman wani taimako daga gare shi ba.


To bayan rasuwar Umma da Baffa, bayan na koma gidan Alhaji Bukar, sai yake gaya min cewa ya gaya wa mahaifina zancen rasuwar, amma baya kasar a lokacin yasan da zaizo gaisuwa ma amma yace a gayamin in saka rana da kaina sanda na ke ganin am ready in gaya masa zaizo Nigeria sai mu hadu a Maiduguri. I fixed the date, sai muka tafi. But cikin rashin sa'a sai ya zamanto shi din wani abu yarike shi a can kasar da yake zaune, Canada, dan haka bai samu tahowa da wuri ba. Ban sami kowa a Maiduguri ba sai step grandmother dina a uncles dina. A lokacin ne kuma kika kirani da maganar za'a hada aurenki da Saghir. Nan take naso in yi musu dan karamin hauka a gidan na dage akan lallai sai an taho anzo Kano an nema min auren ki. Duk kallona suke kamar tababbe, irin suna ganin ban isa aure ba ai. Aka kira Papa aka gaya masa yace a rabu dani, wanne irin aure kuma? Sai na karbi wayar na gaya masa ko dai ya ajiye koma me takeyi yazo ya nema min aurenki ko kuma in kama gabana kuma babu wanda zai kuma jin labari na. Sai na gaya masa ko wa cece ke da dangantakar mu. Wannan ne ya ja hankalinsa. Sai ya bani hakuri akan cewa ba zai iya zuwa ba sai dai mu taho tare da Alhaji Babagana, daya daga cikin uncles dina. Muka taho din kuwa and you know what happened a gidan Alhaji Babba. Sanda muka fita I was beyond broken. Sai nace bazan koma Maiduguri ba, a gidan Alhaji Bukar zan zauna. Na zauna gidan Alhaji Bukar trying to find a solution amma na rasa ko daya, babu irin tunanin da banyi ba ciki kuwa har da in shirya mana visa tare zuwa Canada sai in dauke ki mu tafi can mu cigaba da rayuwar mu. But sai na tuno da kalaman Baffa da yake cewa ba yaso ya bani aurenki in dai babu amincewar Inna a ciki, nasan kuma yadda Inna bata sona in na dauke ki zata hada daga ni har ke ne ta tsine mana kuma ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwa. And I didn't want to put you through that. Sai na fara bincike ta karkashin kasa, Alhaji Babagana ya bani kudi sosai kafin ya koma Maiduguri dan haka bani da matsalar kudi, I followed Alhaji Babba, I watched him a lokacin da ya siyar da garejin Baffa, I also watched him lokacin da ya siyar da filina, I watched him lokacin daya siya wa dansa gida na bishi har gidan na gani. But bayan ya tafi sai na tsaya ina studying gidan, bai yi min ba kwata kwata. Unguwar was deserted dan haka babu security kenan, ko menene zai samu mutum a gidan babu wanda zai sani. Na haura na shiga har cikin gidan sai naga locks din kofofin ba masu kyau bane sosai sai naje na siyo wasu na dawo na cire wadancan na saka sababbin da kaina. But still ban gamsu ba dan nasan wannan mijin naki ba lallai yake zama a gida bake kadai zai ke bari so I hired a gate man for you. Malam Iliyasu" na kalle shi da sauri nace "Malam Iliyasu dai maigadin gidan Saghir?" Yace "yes. Tsohon soja ne yana gadi anan kusa da gidan Alhaji Bukar to sai wanda yake yi wa gadin ya rasu. So I took him zuwa unguwar na nuna masa gidan, mukayi sa'a Saghir din yazo sai na nuna masa shi nace yaje ya nuna masa cewa gurin zama yake nema, yana son zaiyi masa gadi free of charge abinda yake so kawai a bashi dakin mai gadi ya zauna anan. And he took the bait. Nace yace masa free ne dan na fahimci babu yaren da Saghir yake ganewa sosai irin na kudi. So, Malam iliyasu yayi muku gadi, ni nake biyansa duk wata, in return shi kuma yana supplying dina with information musamman abinda ya shafi lafiyar ki"


Ban bar kano ba sai da nayi attending daurin aurenku da Saghir. Daga nan airport na wuce straight na tafi Maiduguri ina zuwa kuma na tarar takarduna sun gama haduwa zuwa Canada dan haka kwana na daya a Maiduguri na tafi Ottawa, capital din Canada inda anan ne mahaifina yake zaune da iyalinsa. 


I had been holding on, ina ta gayawa kaina cewa ba gaskiya bane ba, cewa ban rasa ki da gaske ba, but sai a jirgin nayi loosing din sauran hope dina. Gani nake yi na rabu dake kenan har abada and I couldn't picture my life without you, gani nake babu wani sauran meaning a rayuwata. Daga airport maimakon gida sai asibiti aka wuce dani, ji nake kamar tsaga kirjina akeyi da wuka ana yankar zuciyata sala sala. Mahaifin da naci burin gani sai a asibiti na ganshi and the first thing da ya fada min shine "are you this weak? Do you really want to die saboda mace?" Nace "she is not just any woman. She is mine and they took her from me" yace "to me zakayi akai? Zaka kwanta ka mutu ne while tana can tana sabuwar rayuwa da wani ko kuma zaka tashi ka rayu and show them that abinda sukayi is wrong?" And I decided, maybe gwara in rayu din, maybe one day I will be able to see you again, and get you justice from whoever wrong you. 


But it was easier said than done. A watannin farko na aurenki I spent more time in hospital than at home. In ina gidan ma kuma ina daki a rufe. Bana kula kowa bana yi wa kowa magana. All I kept thinking about was you, you and you. Kullum tunani na a wanne hali kike ciki? Kinyi missing dina ko kuma kinyi accepting auren ki kin cigaba da rayuwarki da mijinki. Na kira Malam Iliyasu sai yake gaya min cewa Saghir yayi tafiya sai ke kadai a gidan tare da wata mata. And the agonizing months suka wuce, the most terrible times of my life. Ranar nan ina gida da rana kawai sai ga wayar Malam Iliyasu, nayi mamaki dan nasan cewa dare ne ku a wajenku na dauka sai naji cikin tashin hankali ya na gaya min wai baki da lafiya, shi yana ganin ma kamar kin mutu dan yaga maigidan ya dauko ki cikin jini ya saka ki a mota ya fita dake. Papa yana office dan haka message kawai na tura masa na dauki kudi da passport na tafi airport. Ban samu jirgi zuwa kano ba sai Abuja. Sai dana shiga Abuja sannan na samu wani zuwa kano ina shiga kano na kira Malam Iliyasu yace min shi bashi da wani labari tunda kuka fita shiru, sai na wuce gidan Alhaji Babba, na shiga har compound din gidan saboda yadda nake jin raina I was beyond caring akan me zai faru in aka ganni. Amma sai na tarar da gidan a hargitse, hankali na ya tashi and I asked wani mai kula da flowers sai yace min ai gobara ce Alhaji yayi duk shagunan sana'arsa sun kone kurmus babu abinda ya tsira dashi. Sai na tambayeshi game da matar Saghir, sai yace haihuwa ce kika yi amma yaran sun mutu, ke kuma an kaiki asibiti amma baisan wanne asibitin ba. Muna cikin magana Inna ta shigo gidan, ta wuce mu ba tare da ta ganni ba kuma na lura hankalinta a tashe yake, ta shiga cikin gidan ta sake fitowa sai na tura wanda muke tare nace yaje ya tambaye ta ya mai jiki? Anan naji sunan asibitin da kike, ana bukatar jini kuma ita ta rasa kowa duk gidan suna gurin Alhaji da yake asibiti shima. Sai na fice ba tare data ganni ba, na je asibitin da kike na nemo dakin da kike na shiga har ciki na ganki. You were sleeping, kamar allurar bacci aka yi miki. Kin kumbura sosai kinyi fari tas. I stayed a dakin for a while ina ganin kamar in na fita bazan dawo in tarar dake da rai ba but i knew dole inyi wani abu sai na tafi nace Inna ce ta turo ni in biya kudi kuma a dauki jini na, akwai wadda a gurin ta tambayeni ko nine mijinki and it pained me to say no. Aka gwada jini na and luckily sai yayi matching da naki" 


Na katse shi "wait, wai kai ka bani jini ranar nan a asibiti?" Yayi murmushi "naki fadar kaina ne saboda nasan yadda Inna bata sona zata iya cewa ba za'a karba ba dan kar in shafa miki maita or something like that"


Kullum ina zuwa in duba ki. Na tabbatar kina samun sauki sosai, ranar nan saura kadan Mama ta ganni na buya duk I doubt ko ta ganni ma zata gane ni saboda ni kaina nasan I looked terrible. Ranar nan nazo sai akace min a ranar za'a sallame ki. Sai na tsaya and I saw you sanda kuka fito, ke da Inna da Saghir da wadansu mata. Kuka shiga motar Saghir ke da Inna kuka tafi and I kept following you a kafa sai danja ta tsayar daku har na karaso inda kuke and I did what I shouldn't have done, nayi miki magana"


Da sauri nace "I knew it. Nasan kai na gani amma inna tace wai aljanu ne suka bude min ido". Yayi murmushi. Ban kyauta ba na sani bai kamata inyi wa matar wani magana ba but I did it. 


A ranar na koma Abuja daga nan kuma na koma Canada. A cikin jirgin nayi making decision cewa it is time to move on, tunda ke gashi har kin haihu, seven months after the wedding har kin haihu. Dan haka ina zuwa gida na samu Papa nace "am ready to move on yanzu" yace "good. Sai ka tafi makaranta kayi mechanical engineering dinka" sai nace "ina son karatu amma nafi son business, in yaso sai in hada da karatun da business din duka" yace zai saka ni a harkar Mai, but sai nace masa bana son aiki under him, I want something of my own, yadda zan making name for myself ba wai in jingina dashi ba. Na dauka zaiji babu dadi but sai naga yayi murna, yace wannan ya nuna masa how strong I am. Sai yayi signing check ya bani yace in cike kudin da nake ganin zasu ishe ni in kafa kaina. Na rubuta na mika masa sai ya yaga check din yace "wannan kudin da zan bawa wani ne in tazo neman taimako gurina. Ba kudin da zan bawa tilon dana ya kafa business ba. Sai ya sake signing wani ya miko min yace "multiply that by hundred, ka rubuta kaje ka karba. Allah yasa albarka a ciki".


That was the beginning of Abatcha Motors. I chose Kano saboda in samu damar keeping eyes on you. Cikin few months aka gama komai na fara hiring ma'aikata. A lokacin ne Malam iliyasu yake gaya min cewa kuna cikin matsalar kudi dan yaga aba ta fitar da kayan gidan ana siyarwa. So, I talked to someone who talked to someone har aka gayawa Alhaji Babba cewa ga sabon company nan ana daukan ma'aikata and luckily shi kuma Saghir ya dauko takardunsa ya fito neman aiki a lokacin sai aka turo min shi. A gurin interview din dana yi masa ne na tabbatar cewa bai sanni ba. I gave him a job. Amma ba job bane ba dan baya ma cikin list of staff dina. Salary dinsa daban nake bashi and his salary was just like me giving you money. Ina bashi kudin dana san ya isa ya kula dake. 


Ina gab da komawa Canada ne sai yazo office dina yana ta complain wai matarsa ce zata haihu kuma doctors sunce ba zata iya haihuwa ba sai dai ayi mata aiki, gashi sunyo masa bill na kudi da yawa. I was scared kar yazo yaki biyan kudin ki zo ki samu matsala so I paid the money. Har na kara masa da kudin ragon suna da sauran hidima, ranar da za'ayi aikin na kwana ina miki addu'ar nasara, I wanted to go and see you but nasan hakan ba dai dai bane ba sai na hakura nace ya kirani in anyi and I asked him ya sakawa yarinyar Subay'a hoping hakan zai faranta miki ranki.


Daga nan na koma school. Carleton University of Canada. Anan nayi karatu tsahon shekaru biyar na fita da matsayin mechanical engineer. A wannan shekarun ne muka yi bonding sosai da yan uwana. My four sisters, Sa'adatu, Yani, Fanna da auta Adama, wadanda Papa ya bani task din koya musu hankali dan zaman kasar turawa ya saka duk sun koma suma kamar turawan. Yanayin shigarsu da yanayin mu'amalar su. I treated them with fire, but sometimes kuma sai inyi musu sanyi muyi ta wasa da dariya. Maman su kuma ta bani goyon baya sosai gurin koya musu hankali dan dama yanayin nasu duk yana damunta itama turancin ne yasa bata iya tsawatar musu.


All those years, nayi iyakacin kokari na dan ganin na cire ki a zuciya ta amma abin ya faskara. Nayi addu'a, nayi azumi nayi sadaka duk da wannan niyar, daga baya sai na saka a raina cewa wannan shine kaddara ta, zan rayu da sanki a zuciyata amma bazan rayu dake ba. Ban dauka cewa babu abinda ya ragu na sonki a zuciyata ba sai dana dawo, ranar da staff dina sukayi surprising dina da party, I saw you there, I tried pretending but then I saw him holding your hand and I couldn't take it, nasan in ban bar gurin ba zan iya rufe shi da duka dan haka na gudu"


Then one day ina dakina na hotel ana ruwan sama, har na fara shirin bacci sai ga wayar Malam Iliyasu yace min mamanki da kanwarki sunzo gidan Saghir ya kore su, ga dare gashi ana ruwa yana jin tsoron kar wani abu ya faru dasu. I left everything na hau mota na taho unguwar ina tafiya ina dubawa, hankalina a tashe ina tsoron kar in zama too late, sai gasu nan kuwa na gansu already har sun fada hannun mugaye. I couldn't imagine me zai faru da Asma'u idan da Allah bai sa Malam Iliyasu ya kirawo ni ba. That was when I decided to sue Alhaji Babba for garejin Baffa da filina. Tunda rashin mutumci suke ji I decided to show them rashin mutunci".


"Wannan shi yayi stating chain of events din da har suka kai ga rufe Saghir"


"Ina so ki fahimci cewa ban rufe Saghir dan in aure ki ba. Yes, I loved you, I love you and I will take your love with me to my grave but da ace zaman lafiya kuke yi da Saghir da babu abinda bazanyi ba dan ganin cewa zamanku ya dore a tare. I would have given everything in dai zakiyi farin ciki. But after na fahimci irin zaman da kuke yi, after what he said a gaba na ba tare dako digon nadama a muryarsa ba, after ke da kanki kin gaya min cewa ba kya son komawa gidansa then I won't let you. Yes, na barwa Saghir kudina intentionally saboda ina so ya dauka, saboda ina son in samu hujjar rufe shi yayi paying for abinda ya aikata. But I didn't force his hands. Shi yayi making decision din dauka da kansa. And that's what took him to prison bani ba".


"Yanzu na dawo gurinki Diyam. Ina neman aurenki bisa yardarki. Yes, nasan shekaru sunja ba lallai ne kina da feelings for me a yanzu ba. Amma ina so ki fada min abinda yake ranki, in kika karbi offer ta ta aure I will surely be the happiest man on earth, in kuma kika ki karba I will be heart broken maybe fiye ma da wancan karon but I will respect your wish. Bazan matsa miki ba ba kuma zan bari a matsa miki ba".


Ina jiran amsar ki.

[3/5, 10:12 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Sixty One: The Decision


Nayi kokarin dago kaina in kalleshi amma na kasa, tun daya fara magana nake hawayen tausayin rayuwata da tasa, wani gurin kuma inyi murmushi ina jin soyayyar sa tana kara ninkuwa a zuciyata. A karshe sai na samu kaina da tambayar kaina. Shin tsakanin ni da Sadauki waye yafi son dan'uwansa? 


But can I tell him that? Anya zan iya gaya masa cewa babu abinda ya ragu a zuciyata dangane da soyayyar sa sai ma karuwa da yayi. Sai jin murtarsa nayi a hankali yace "should I start crying? Ko kuma in durkusa a kan guiwa ta?" Na yi murmushi ina karasa goge sauran hawayen ido na, na bude baki sai maganar ta makale, sai kawai nasa hannayena na rufe fuskata. Ya kama dariya yana cewa "you must be kidding me. Yanzu ni in zauna in gama bude miki zuciyata amma ke sai ki rufe fuska? In ba zaki gaya min bama at least let me look at your eyes in karanto amsa ta a can" na girgiza kaina nace "I can't" yace "wait, wai kunya ta kike ji?" Na bude fuskata nasan "mu fulani kunya ce damu" yayi dariya yace "maybe kin manta, nima bafulatani ne" nace "half ba. Mun bar musu kuma" yace "ni ban yarda ba, ko bani da jinin fulani my heart is fulani. Zuciya kuma itace rayuwa" nayi murmushi ina tuna ranar daya fara fada min nice zuciyarsa a Taura. Yace "I still need to hear it. I need to hear you say you love me. In kika fada then I have tukuici for you. Happiness insha Allah, till eternity. Through thick and thin".


Ina sunkuyar da kaina kasa, murmushi a lips dina, ruwan hawaye a idona, nace "kalmar love can't even begin to describe yadda nake jinka a zuciyata. Sometimes ina jin soyayyar ka kamar tayi waya a kirjina Kamar zuciyata ta cika har tana zuba da sonka. Da sonka aka haife ni Sadauki kuma nasan da shi zan koma fa mahalicci na. Bana jin kalmomi zasu iya bayyana soyayya ta gare ka dan duk abinda na fada ji nake yi kamar yayi kadan" sai yayi sauri yace "okay, will you marry me? Please? Sai a nuna min soyayyar a aikace ko zan fi fahimta sosai" sai nayi saurin jan hijab dina na rufe fuskata saboda nauyin maganar sa da naji. Ban san me yasa yanzu nake jin tsananin kunyar Sadauki ba bayan kuma sanda nake karama bana ji kamar haka. Ina jinsa ya sake jawo kujerar sa kusa dani yace "Please say something Diyam. Am dying here".


Hayaniyar su Asma'u ce tasa na bude fuskata amma ban kalli inda yake ba sai na juya inda na jiyo muryoyinsu. Murjanatu tazo da sauri tana cewa "yaya, wallahi naga irin motar da kayi min alkawari as my birthday gift. Please, please yaya ka bar min ita" sai ya dafe kansa da hannu daya yace "zaki saka min ciwon kai Fanna. Please go and make the noice somewhere else" sai na mike tsaye nace "yauwa an kawo abinci, dama yunwa nake ji".


An jera mana abinci iri iri akan shimfidar da akayi mana akan grass carpet din gurin. Muka tafi mu uku muka fara saving kan mu muna ci muna hirarrakin mu amma hankali na tana kansa yana zaune har yanzu a inda muka zauna da waya a hannunsa. Naji shigowar text cikin waya ta sai na duba naga "Please ki ajiye abincin nan kizo mu karasa maganar mu" sai na juya na kalle shi nace "me za'a zubo maka?" Ya bata rai yace "am not hungry". 


Anan mukayi sallolin mu, Murjanatu tana ta yi masa nacin mota sai yace ta bari sai birthday din nata. "Ke ba iya motar ma kika yi ba. In na baki me zaki yi da ita?" Tace "koya min zakayi ai" yace "ni bani da lokacin koya miki mota akwai driving schools ki shiga ki koya a can". Sai da magrib ta gabato sannan muka tafi gida. A hanya Asma'u da Murjanatu ne kawai suke ta hirarrakin su amma ni da Sadauki kowa yana hira ne da zuciyarsa. Ni ina rarrashin tawa ne akan ta yarda da hukuncina a kan Sadauki, ina gaya mata cewa hakan shine abinda ya kamata gare ni, gare shi ga Subay'a, ga kuma zuriar dazamu haifa in muna da rabo. But my heart was weeping tana ganin banyi mata adalci ba. Tana gaya min hukuncina ni zaifi affecting ba wai shi wanda nayi wa ba.


Muna zuwa gida yayi packing a kofar gida su Asma'u sukayi masa sallama suka fita, ina hango Subay'a ta fito da gudu sai kuma ta tsaya tana kallonsa sai ta juya ta koma gida. Ya juyo yana kallona, nasan maganar da zaiyi min kuma kirjina bugawa yake da karfi ina tattaro courage din amsa masa, yace "baki bani amsa ta ba Diyam. In kin amince min ina son zanje gurin Kawu Isa" na juyo ina kallonsa, ina tunanin irin smartness ne Sadauki. Gurin Kawu Isa. Yasan a yanzu in ya nemi aurena a gurin Kawu Isa da gudu zai bashi ko dan ya kara bakantawa Alhaji Babba rai tunda har yanzu basu shirya ba. Sai kuma nayi tunanin hakan da Kawu Isa zaiyi shi zai kara rusa yar guntuwar zumuntar da take tsakanin uncles dina guda biyu. Sai nace "ina son aurenka Sadauki. Zan iya cewa shine greatest burina a yanzu. But, ina son muyi shi akan dai dai. Ina son muyi shi ta yadda nan gaba ba zamu zo muna nadama ba" yace "nadama kuma? Akan me zamuyi nadama?" Nace "have you thought about maganar da mukayi ranar nan? Akan forgiveness?" Sai ya dauke kansa gefe yana kallon waje nace "nima da akayi wa laifin nan na yafe musu. And I felt good lokacin da na yafe din ji nayi tamkar na dauke wani abu ne mai nauyi daga zuciyata. Wannan feeling din shi nake yi maka kwadayi. And Subay'a, 拼ata ce at the same time 拼ar Saghir ce duk yadda bana son Saghir bazan taba cewa ba shine ya haife ta ba. She will come in between us ko da munyi auren ma she will never forget cewa kai ka rufe mata mahaifinta and that may affect me nima a gurinta zata iya tunanin da sani na akayi komai" yace cikin dacin murya "I didn't lock up her father. Shi yayi signing takarda da hannunsa babu wanda ya tilasta masa" nace "but intentionally ka bar masa ai. Kuma kudin ka ne. You can just walk to the court a yanzu kace ka yafe masa a d that will be all" ya girgiza kansa yace "you seem to be forgetting something. Ba kudina ne kadai yake rike da your precious Saghir a prison ba. Ko drygs din ma ni na daka masa a dakin sa?" Naji zafin kalmar 'precious Saghir' din daya fada amma nasan kishi ne yake yi, sai nace "ba kai ka saka masa ba. Abokinsa ne yayi framing dinsa amma yayi framing dinsa ne saboda ya samu damar guduwa da kudinka da Saghir ya dauka, so it circles back to you. Please Sadauki, you have the power, you can set him free. Saghir yayi nadama. I saw it in his eyes sanda naje gurinsa a prison" yace "nadama? Baki san hausawa sunce kowa ya tuba dan yuwa babu lada ba? Ko zaiyi nadama Saghir ba yanzu ba" nace "Sadauki, Saghir fa....." Sai ya daga min hannu yace "stop, Please stop mentioning his name" sai na fahimci wani abu. Duk maganar da nake Sadauki ba jina yake yi ba, kishi ya rufe masa ido gani yake yi kamar saboda ina son Saghir ne nake so ya fito da shi. Ban kuma cewa komai ba sai na dauki purse dina na bude kofa na fita. Ina jin yana kirana amma ban juyo ba duk kuwa da cewa ji nake tamkar tawa zuciyar tafi tashi jin zafin hakan.


Ina shiga na tarar Asma'u da Murjanatu sun saka Inna a gaba suna ta bata labarin guraren da muka je. Sai na wuce su na shiga daki da niyyar rage marata a toilet sai kawai naga Subay'a a kwance a kan gado, na karasa kisa da ita sai naga kuka take yi a hankali hawayenta yana zuba kan katifa. Naji hankalina ya tashi sai na durkusa na jawo ta jikina nace "Subay'a? Kuka? Me ya faru?" Sai taki magana ta cigaba da kukanta ni kuma nayi ta rarrashinta har tayi shiru Sannan na sake tambayar ta sai tace "Daddy na nake son gani" sai nayi murmushi nace "dan kina son ganin Daddy sai kiyi kuka? Kiyi hakuri kinji? Da weekend zan kaiki ki ganshi" ta gyada kai kawai. Har zan tashi sai kuma na dawo na zauna nace "Subay'a, ranar nan da kika ce min kinji su Inna suna magana akan uncle Sadauki shi ya rufe Daddy ba haka bane ba, bakiji dai dai ba, uncle Sadauki shi yake kokarin fito da Daddy daga prison. Dazu ma maganar da muke yi dashi kenan" sai ta sake gyada kai kawai but she didn't looked convinced. Sai naji babu dadi saboda nayi mata karya amma kuma hakan ina ganin shine zai rage kiyayyar ta ga Sadauki. Ina kuma fatan komai ya dai-dai ta kafin tayi girman da zata gane komai.


Sai da nazo kwanciya naga text din Sadauki "am sorry Diyam, but I can't".


Sai nayi ta juya wayar a hannuna na rasa amsar da zan bashi. A karshe kawai na kasheta na ajiye. Cikin dare na tashi na gayawa Allah bukatu na. I want everything to turn out alright a gurin kowa da kowa. Ina kuma son zumuncin mu da yanuwan mu ya koma kamar yadda yake kafin a hada auren karfafa zumunci tsakani na da Saghir (ko auren bata zumunci ba), sai na roki Allah ya duba zuciyata yayi min zabi mafi alkhairi. Kafin safiya nayi making decision. Makaranta zan koma in cigaba da karatu. 


Da safe na samu inna da bukata ta. "Inna maganar makarantar da nayi miki ranar nan. In kin amince ina so in nemi makarantar in sayi form in fara kafin shekara ta zagayo in tafi jami'a" ta tsaya rana kallona, daga dukkan alama maganata bata yi mata dadi ba amma sai tace "Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" nace "ameen".


Da yamma sai ga Sadauki yazo gidan. Ya zauna kowa ya gaishe shi sai yake yiwa Murjanatu magana "Papa ya kira. Yace ki shirya ki koma saboda shirin tafiyarki school" ta bata rai, ya daga hannu yace "babu ruwana. Kinsan in baki tafi makaranta ba this year ba aure za'ayi miki" ta turo baki "Sa'adatu ma ba'ayi mata aure ba sai ni?" Yace "okay try me ki gani. Kin dauka wasa nake ko. Su Sa'adatu ai duk karatu suke yi ke kuma zaman banza kike yi zaman kula samari" sai tayi shiru fuskarta kamar an aiko mata mutuwa. Inna tana jin su tace "gwara kije karatun ki. Diyam ma tace makaranta zata koma" ya juyo yana kallona naki yarda mu hada ido sai yace "school? Very good. Ina zaki je?" Nace "computer school zan yi, kafin in samu admission. Tunda kaga yanzu an gama registration har an fara karatu sai next year kuma" ya daga kafada yace "ba duk universities bane suka rufe admission" nace "wacce ce ba'a rufe ba? Kasan kuma banyi jamb ba, so ko ba'a rufe ba bani da hope" yace a hankali "you can go to Oxford. Can nake nemawa Murjanatu, zaku iya tafiya tare" sai Murjanatu ta mike da sauri ta fara tsallen murna. "Haa, har naji dadi wallahi. Please Diyam say yes kinji? Please, please, please".


Sai nayi shiru ina kallon Sadauki wanda shima ni yake kallo, with so many unspoken words a cikin kallon namu ni ina jin haushin wato akan ya yafe wa Saghir ya gwammace ya tura ni wata uwa duniya karatu shi kuma yana jin haushin dan yaki yafewa Saghir na yi choosing in koma makaranta akan in aure shi. 


Ba yawa, kuyi manage.[3/8, 12:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Sixty Two & Three : The Bet


Inna ce ta yi magana "au biye mata zakayi? Wani irin karatu zata tafi har wata kasa tayi? Ba gwara ayi auren ba in yaso in ma alhuda huda zata zama sai tayi ta zama ba?" Na kalleta nace "Akwai wanda yazo yace yana son aure na ne Inna?" Sai tayi min dakuwa tace "ku raba ke da yan gidan ku, yanzu zama kike so yayi tayi yana jiranki har ki gama wani karatu? Ko wanne karatu ne ai za'a iya yinsa a gidan miji" sai ya mike yana kallon Inna, ban kalle shi ba but I sensed cewa ransa a bace yake, yace "in karatu take so Inna ki barta tayi karatun ta, in zata je Oxford din ta fada and I will take her there. In kuma bata son ta ta fadi duk wadda take so in dai ina da dama zan kaita" sai ya juya ya fita. 


Na mike da sauri nabi bayansa kamar wadda ake fusga ta zuwa gare shi na same shi a gareji nace "Aliyu" ya juyo da sauri yace "what?" Ina kallon yadda idonsa yayi ja nace "kar kayi fushi dani please" ya dawo gabana ya tsaya yace "nasan abinda kike trying to do, kinsan ina sonki da yawa ina son aurenki shi yasa kika yi shawarar tafiya karatu a tunanin ki hakan zai saka na fito miki da Saghir dinki, which I will never do. Na gaya miki kuma nace bazanyi ba, the more you keep mentioning him and showing that you care about him, the more zuciyata take gaya min in barshi yayi rotting there. In da kinsan kina son sa sanda na tambaye ki ko kina son komawa gidan sa sai ki gaya min, I would have supported you, kamar yadda a yanzu zanyi supporting dinki through karatun da kika ce zaki yi. You know why? Because I love you, and to me that's what true love is. In kana son mutum soyayya ta gaskiya shine you care about him and support him, you put his happiness a saman naka, you sacrifice everything just for him" 


Naji bacin rai nace "how can you accuse me of that? I don't love Saghir kuma ka sani, ka sani kai nake so, kuma..." Yace "ni kike so? Na dai ji a baki kin fada kin ce kina sona. But am not so sure about that. Saboda duk abinda kike yi is total opposite of abinda na fahimta a matsayin so. Yes, kin soni a da na sani, but yanzu ban sani ba because a yanzu Saghir dinki shine a gabanki, dashi kadai kika damu" nace "ka daina cewa Saghir dina, ba nawa bane ba, bana son Saghir kuma ban taba son Saghir ba kuma bana jin zan taba sonsa tunda har na zauna dashi a matsayin mijina for years amma ban so shi ba. Kai na so, kai nake so kuma kai zan cigaba da so. Son da nake maka ne kuma ya saka nake so ka fito dashi din for your own good, for peace a cikin rayuwar da nake mana burin shinfida wa dani da kai har mutuwa, and that's my version of true love. In jawo ka kan gaskiya even if that will hurt you and me".


Sai naga idanunsa sunyi softening, yana girgiza kansa yace "I can't, na gaya miki I can't".


Raina a bace na koma cikin gida. Why is he so stubborn? Amma ina zuwa gida na tarar inna ta na tsarawa Murjanatu dalilin rigimar mu ni da Sadauki, sai ta juyo tana kallona tace "why are you so stubborn?" Nace "ni? Au nice ma mai taurin kan bashi ba?" Inna tace "ke ce fa. Kuma ke zakiyi wa kanki, dan ni bazan goyi bayan yayi ta zama yana jiranki ba har zuwa sanda zaku gama rigingimun ku wadanda babu rana. Ke fa kece baki da gaskiya, shi waye yace ya daukar masa kudi? Ita kuma Subay'a ai ba'a kanta aka fara rufe uba ba, wasu ma uban nasu mutuwa yake yi ya bar su kuma haka suke hakura. Wadansu ma basu san iyayen nasu ba uwa da uba gabaki daya. Kowa da kaddarar sa". 


Ni dai bance mata komai ba saboda nasan ba fahimta ta zata yi ba. Sai naga ta saka mayafin ta tace mana ta tafi unguwa. Sai bayan ta tafi sai sannan na zauna nayi wa Murjanatu bayanin irin yadda Sadauki intentionally ya shirya wa Saghir trap din daya kai shi prison. Maimakon inga ta fahimce ni sai naga tayi dariya tace "kadan da aikin yaya na wallahi, Aliyu Haidar sadaukin sadaukai" na bude baki ina kallonta da mamaki "wato ke burge ki yayi ko?" Tace "waye yace ya daukar masa kudi? Ai kamar yadda ya fada ne shi ba shi yayi forcing hannunsa ba, ba kuma bindiga ya saka masa a kai ba, ya dai haka masa rami amma shi yayi deciding ya dauka dan haka shi ya jefa kansa cikin ramin".


Sai dare sannan Inna ta dawo daga unguwar tata. Lokacin kwanciya bacci yayi muka je muka kwanta ni da Murjanatu dan tun zuwanta na mayar da Subay'a dakin su Inna. Muna kwance Murjanatu tana ta chatting da sisters dinta da samarinta. Na dauki wayata ina ta jujjuyawa a hannu na. Sam bana jin dadin rabuwar da mukayi da Sadauki dazu, amma kuma banji dadin abinda ya gaya min ba akan wai ina son fito da Saghir ne saboda ina so sa. Zuciyata tana son in kira shi in ji muryarsa kuma in bashi hakuri amma kuma wani barin yana nuna min cewa shi me yasa ba zai kira ni ba? Na ajiye wayar nayi tsaki na kwanta na juya bayana, kusan awa daya ina kwance babu bacci babu dalilinsa, har Murjanatu ta gama yin wayoyinta da chatting dinta naji tayi addu'a ta kwanta. Sai na kuma dauko wayata na nemo number dinsa nayi dialing a raina ina cewa ba lallai ne ta shiga ba, amma sai ta shiga din, bugu dayakuma ya dauka sai kuma muka yi shiru gabaki daga muna sauraron numfashin juna. 


Nace "I tot ba zaka dauka ba" yayi ajjiya zuciya yace "ni na isa. Bayan kin hana ni bacci" nace "ta yaya zan hana ka bacci ina miles away from you" yace "yes, miles away but so close" sai na lumshe ido na ina jin dadi a raina, naji duk bacin raina yana gushe wa zuciyata tayi fes. Nayi murmushi nace "ko?" Yace "ke ma kin sani ai, ko sai na maimaita miki. Haliman nan dai ita ce a kirjin Aliyu. Itace a jininsa ita ce a tsokar jikinsa. Bana jin akwai abinda zakiyi min in ki daukan wayarki" a hankali nace "kayi hakuri. Na bata maka rai na sani amma tawa zuciyar tafi bakanta a kan taka" yace "nima na bata miki ai. I shouldn't have said what I said about Saghir. Matsalata ina kishinki da yawa Diyam" nace "Amma ka yarda cewa bana sonsa kai nake so?" Yayi dariya yace "kara fada min inji?" 


Mun jima muna hira har credit din yawa ta ya kare. Sai ya kira muka cigaba. Yana ta bani labarin rayuwar sa a Canada da University din da yayi. Sanyin da naji gari yayi yasa na fahimci dare ya ja sosai. Da kyar nayi masa sallama. "Zaka je office fa gobe" sannan dai yayi min sallama ya kashe. Ina yin addu'a ko minti daya ban kara ba nayi bacci.


Da safe Murjanatu ta tashi tana ta jera hamma. "An hana ni bacci jiya da I love You I Love You" na jefa mata pillow nace "zaki koma kwana a palo" tayi dariya tace "wai su yaya Aliyu an iya soyayya. Lallai in na koma gida akwai labari" sai na tambayeta in tana ganin Papa zai amince, ta bata rai tace "why not?" Nace "ni na taba aure. Aliyu kuma bai taba yi ba" tace "and so what?" Bazan iya miki describing Papa ba, but duk randa kuka hadu you will feel ashamed in kika tuna cewa kinyi min wannan tambayar".


Ranar ma inna ta sake fita unguwa. And I stated to suspect something. Har yamma bata dawo ba, a lokacin ne kuma Sadauki yazo. Na bude masa palon da yake a matsayin na baki muka zauna a ciki. Sai a lokacin na samu courage din yi masa tambayar da take raina nace "Sadauki baka gaya min labarin yaya ladi ba" yayi murmushi yace "sai yanzu kika tuna da ita? Na gaya mata ai nace kin manta da ita gashi kuma kin kwace mata miji" na zaro ido nace "tana raye? Tana ina? I tot ta rasu ne kuma bana son tuno maka da old painful memory, you are already bitter ba sai na kara maa wani ciwon ba" yace "tana nan. Tana damagun gurin wata cousin dinta. Bayan na tafi Canada ta tafi can ita kuma, kuma tunda na dawo taki dawowa gurina tana can sai dai inje in ganta, one day zamu je tare as a couple" na ture maganar gefe nace "baka kuma fada min ba, tuwo na na ranar nan, ka ci? Na jima ina son inji ko kaci ko baka ci ba" sai naga ya bata rai kamar ba zaiyi magana ba sannan yace "naci, sai da safe amma. I drove throughout the night" 


Muna cikin hira aka kira shi da kamar ba zai dauka ba kuma sai ya dauka yana cewa "Inna ce" naji sun gaisa sai yace "ina gidan ma. Okay bara in fito sai inzo" na yi masa alamar tambaya da hannuna sai yace "Inna ce tace inje in same ta a gidan Kawu Isa" ina jin haka nasan magana tace, amma ya inna zata yi min haka bayan mun gama magana da ita na roke ta kar ta shiga maganar? 


Sai dare inna ta dawo. Bata ce min komai ba sai ta shiga harkokin ta nima kuma ban tambaye ta ba amma sai na kira Sadauki na tambayeshi. Ya kukayi a gidan Kawu Isan?" Yace "babu komai. In tayi tsami zakiji ne ai" amma ni kuma ai bana son tayi tsamin. Nafi so in samu maganar a fresh dinta yadda zan iya tackling dinta. Amma Sadauki yaki gaya min. 


Da weekend Murjanatu ta koma gida. Sai naji duk babu dadi saboda na saba da ita a kwanakin da tayi a tare damu. Bayan tafiyar Murjanatu kamar yadda nayi wa Subay'a alkawari na shirya ta muka tafi central prison gurin Saghir. Amma sai da muka samu ganin sa sannan nayi nadamar zuwa gurin cos it really broke my heart to see him a wannan condition din. Ya rame sosai fatarsa tayi baki ta lalace. Yayi datti. Uniform dinsa na prisoners wandon ya yage daga gwuiwa. Sai na tuno wancan Saghir din dan gayu mai iya daukar wanka da kwalliya yana kyalli kamar tarwada. 


Ya dauki Subay'a ya daga ta sama ya rungume a jikinsa irin yadda yakeyi mata a gida. Sai ta kankame shi tana cewa "Daddy ka dawo gida gurin mu dan Allah" ya sauke ta yana lakuce mata hanci yace "Daddy zai dawo gida kinji princess, ki ringa yiwa Daddy addu'a kullum in kika yi sallah" sai ya juyo yana kallona yace "look at you. Kinyi wata kiba kamar wata Hajiya. Me Inna take baki kike ci ne?" 


Sun jima suna hira shida yarsa, tana bashi labarin sabuwar makarantar ta da sababbin kawayenta. Sai da zamu taho yace "Diyam ya labarin alkawarin mu? Wannan alkawarin da kika yi min shi kadai ne yake keeping dina going a gurin nan. The hope that one day zan fita shi yasa har yanzu banyi loosing sanity dina ba".


Na dauka Subay'a zatayi kuka amma sai naga bata yi ba. Muna zuwa gida tace min "Daddy yace zaki saka uncle Sadauki ya fito dashi ko?" Nace "mommy da uncle Sadauki zasuyi iyakacin kokarin su, amma sai kinyi min alkawarin kin daina maganar, ba zaki kara yiwa kowa maganar ba kuma ba zaki kara yin kuka ba".


Da yammacin ranar nayi baki. Kawu Isa aunty Fatima da Mama. Ina ganinsu naji hankalina ya tashi dan nayi guessing maganar data kawo su. Basu jima da zama ba sai ga Sadauki shima yazo, naji haushinsa for not telling me abinda ake shiryawa. A gaishe su, shima ya gaishe su sannan sai na gaishe shi sama sama. 


Kawu Isa ya fara magana. "Diyam innarki ta same ni da maganar ki da yaron nan. Tace yazo yana neman aurenki amma ke kin dauko wasu sharadai marasa tushe kin gindaya masa. Menene dalilinki nayin hakan?" Na dago kai ina son hada ido da Sadauki amma ya sunkuyar da kansa. Na fahimci lallai ni ake jira inyi magana amma kuma ban fahimci me ake so ince din ba. Shin wai su basa ganin abinda nake gani? Sai dai na fahimci akwai banbanci a tsakani na dasu, su basu san gadar zaren da Sadauki ya saka wa Saghir ba, su basu san maganar siyan gida da motar Saghir da Sadauki yayi dan ya taimaka wa Kabir wajen guduwa da kudin da Saghir ya sata ba. Nace "ni ba cewa nayi bazan aure shi ba Kawu. Ni cewa nayi ya yafewa Saghir kuma ya taimaka masa yayi clearing case din drugs dinsa" Mama ta kara da cewa "Sannan kuma ya bashi aiki ko?" Sadauki yayi sauri ya dago kai ya kalle ni, shi baisan da wannan part din ba ma. Nayi niyya ne sai Saghir ya fito sannan zan gabatar masa da wannan kudirin. Na dauke kaina daga kallonsa yayinda Kawu Isa ya rufe ni da fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ni mamaki yake bani sosai musamman saboda nasan ba wai dan zumunci yake yin wannan abin ba, yana yi ne dan ya batawa Alhaji Babba rai kuma dan ya tabbatar da zaman Saghir a prison saboda abinda yayi wa suwaiba. Sai na tambayi kaina "anya kuwa akwai family din daya kai namu lalacewa?"


Sai daya gama yi min fadan sannan yace "kuma yaron nan yana iyakacin kokarin sa gurin ganin an fito da Saghir, jiya ma sai da muka je tare dashi har ofishin commissioner of police, kuma sun gaya mana suna iyakacin kokarin su akan maganar amma akwai rudani a cikin maganar sosai. Sunce zai fito amma sai ya dauki lokaci" Ya juya yana kallon Sadauki yace "shekara nawa ma suka ce mana?" Sadauki yayi gyaran murya yace "drug case is complicated. Kamar five years haka zuwa sama. Amma zai fito". 


Mama tace "to alhamdulillah. Wanda ake tunanin ya tafi kenan kuma aka zo aka samu sassaucin da har za'a saka ran fitowarsa? Ai babu abinda zamuyi sai godiya ga Allah. Kai kuma Sadauki Allah ya biya ka" suka ce ameen. Aunty Fatima tace "ai wannan commissioner Ahmad Muhammad yana kokari sosai" suka ci-gaba da hirarrakin su yayinda ni kuma hankali na ya tafi wani gurin daban. 


"Ahmad Muhammad" a ina nasan wannan sunan? Na dago kai muka hada ido da Sadauki sai na tuno inda nasan sunan and everything become clear to me. Ahmad Muhammad shine babban abokin Sadauki wanda suka taba zuwa min visiting makaranta tare, Ahmad Muhammad da yace bashi da buri irin yaga ya zama commissioner of police dan ya kama yan iskan gari ya rufe su a cell. That Ahmad Muhammad. Sai na tuno da kamun Saghir na farko, lokacin da aka je bail dinsa akace wai commissioner yace kar a bada bail dinsa. Sai nayi realising cewa Sadauki yana playing Kawu Isa ne, wato ya dauke shi ya kaishi office din abokin sa sun hadu sun ninke shi a bai bai da maganar cewa suna iyakacin kokarin su bayan kuma babu wani kokarin da suke yi. And I realized with a sinking feeling that Sadauki bashi da niyyar fito da Saghir.


"Ahmad Muhammad" na maimaita a fili. Duk suka juyo suna kallona sai muka hada ido da Sadauki a take kuma na fahimci cewa ya gane cewa na gane abokin sa ne. Nace "shekara biyar ko? Allah ya nuna mana shekara biyar din. Kawu kuyi hakuri kuyi min afuwa ku barni in tafi karatu, kafin shekara biyar din na dawo insha Allah. A lokacin in Saghir din ya fito sai ayi maganar auren".


Gaba-daya suka yo kaina da fada, har bama na jin abinda suke cewa ni kuwa na sunkuyar da kaina. Su basu san cewa decision din yafi yi min zafi a kansu ba amma dole ce ra saka ni. Sadauki bashi da niyyar fito Saghir bana jin kyma zai fito dashi ko da kuwa bayan na aure shi dinne. Option dina daya a lokacin shine inyi relying da son da yake min in hana shi cikar burinsa na aure na har sai ya warware daurin dayi da hannunsa.


Fada suke tayi min har saida Sadauki ya koma basu hakuri, inna kamar zata dake ni tana cewa "ya fasa auren naki to, aurensa zaiyi ya rabu dake. Yarinya sai shegen taurin kai" Aunty Fatima tace "ikon Allah, wai kamar ba Diyam din da take ta kuka an raba ta da Sadauki ba ce ba, yanzu kuma ita ake cewa ta auri Sadauki tana ki"


Ni kuma bana son in bayyana musu gaskiyar laifuffukan Sadauki saboda bana son in bata shi a wajensu. Gwara ni in dauki laifin shi kuma ya zauna fes.


Washegari da safe Sadauki ya kira ni a waya. Da kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka dan inji me zai ce min sai yace "Oxford din ce kenan" na danyi tunani. I need a break gaskiya, from Sadauki and from my family. Maybe in nayi nesa da Sadauki zaifi tabbatar wa cewa da gaske nake maybe rashina yayi breaking dinsa. Sadauki loves me, and that love shi nake relying on. Nace "Yes, Oxford din ce" ya danyi shiru sannan yace "na gaya miki tuntuni, I can't do abinda kike fada. Ki bar maganar Saghir, he deserves halin da yake ciki" nace "deserves? Sadauki Allah ne fa kadai yasan waye yayi deserving kaza wate baiyi ba, Allah ne kadai yake judging mutane akan laifuffukan su ba wai mu bil'adama masu tarin laifuffuka ba, Saghir yayi laifuffuka na sani, Alhaji Babba ma haka, amma Allah shi zaiyi judging dinsu bamu ba. Me yasa ba zamu zamanto masu yafiya ba saboda muma Allah ya yafe mana?" Sai yace "Allah yana judging wadansu ta hanyar wadansu. Wanne department din za'ayi miki applying for?" Nayi shiru. I had been thinking about that for years na kasa tsayar da shawara sai a ranar da Saghir ya bani takarda ta, a ranar da na samu freedom dina, a ranar ne na yanke shawarar abinda zan karanta. Law. 


"Law" na fada masa. Yace "wow. But why law" nace "nayi tunani, kusan duk abinda ya same ni a rayuwa, tun daga auren dolen da akayi min har zamana a gidan sa da rabuwar mu ta farko da karbar Subay'a da yayi da farko. Duk wadannan sun faru ne saboda abu guda daya. Saboda rashin sanin yancin kaina da banyi ba. Alhaji Babba a both musulunci da kuma a dokar kasa bashi da right din yi min auren dole. Ko da mahaifin daya haife ni ne bashi da wannan right din sai dai zan iya yi masa biyayya dan in samu lada amma ina da option din cewa 'no'. Zaman da nayi a gidan Saghir, wahalhalun da nasha wadanda suka yi kokarin lalata both rayuwata ta duniya da kuma ta lahira duk sun faru ne a saboda bansan yancin kai na ba balle in nemi rabuwa da Saghir, both matsayi na na musulma da kuma matsayina na yar Nigeria sun bani yancin zabin wanda nake so in zauna dashi a matsayin mijina, na tuna rabuwar mu ta farko lokacin da ya dauke Subay'a ya tafi da ita da irin halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashinta, shima wannan duk ya faru ne saboda bansan yancina ba, ba kuma ni da courage din fighting for my right dan shari'a ni ta bawa rikon 拼ata, ko da mutuwa nayi rikon Subay'a baya hannun Saghir sai dai a bawa Inna, wannan itace Shari'a ta gaskiya. Amma rashin sanin yancin kai da matan hausawan mu suke fama dashi shi yasa ake tauye musu islamic and constitutional rights dinsu"


"Wannan shi yasa nayi deciding in karanta law, dan in samu damar tsayawa duk wata yarinyar da iyayenta ko marikanta zasu tursasa ta gurin auren wanda bata so, dan in tsayawa duk wata matar auren da take zaune da abusive husband kuma take son rabuwa dashi, dan in tsaya in tabbatar iyaye mata sun samu right dinsu da ubangiji da kansa ya basu na karbar rikon yayayensu a lokacin rabuwar aure ko kuma lokacin mutuwar miji. Wannan shine zai zama role dina a society" 


Yace "Masha Allah. I am very proud of you Diyam. Kuma ki sani ina tare dake tun daga farko har karshe".


Na fahimci cewa Sadauki shi ko a jikinsa da nayi suspending auren mu nace sai na gama karatu. Shi dai kawai in dai Saghir zai cigaba da zama a prison shikenan. Da nayi kokarin yi masa complain cewa bama so nake tunda bai damu da aurena ko rashin aurena ba sai yace "you have no idea how much I want to marry you. This is just a phase we are going through. Am sure zaki chanja mind dinki along the way, in ma baki chanja ba I will wait har ki gama din ki dawo". 


Wato ni ina depending on son da yake yi min cewa zai sauko ya chanja shawara ya fito da Saghir saboda muyi aure shi kuma yana depending on son da nakeyi masa yana saka ran zan sauko in bar maganar Saghir muyi aure. Ni dashi aga wanda zai fasa.


Ya gama nema mana admission, kuma mun samu successfully. Anan na fahimci cewa su ba yearly suke bada admission ba kamar in batches suke yi kuma mu namu session din zai fara ne January. Daga nan kuma sai ya shirya ya tafi yaje yayi one week a can ya dawo yace "all set, an samo muku apartment a kusa da school din an kuma ajiye muku mota saboda zirga-zirga. Abinda ya rage miki shine koyan driving" shi ya koya min, ya ajiye duk harkokinsa yake zuwa yana dauka na muna fita koyon mota kuma cikin kankanin lokaci na iya sosai. Zamu yi ta hirar mu amma da zarar nayi masa maganar Saghir zai dauke wuta in ba hakuri na bayar da kuma to sai dai mu dawo gida ranar ba za'ayi koyon motar ba. 


Shi yayi min komai na harkar student's visa, muka je Abuja ni da shi da Asma'u. A embassy na UK na hadu da Judith itama tana neman student's visa, daga gaisawa naji yarinyar ta kwanta min muka yi ta hira har na fahimci scholarship ta samu daga program na African Initiative for Governance kuma session din karatun mu zai fara tare ne. Sai na roki Sadauki ya karbar mana visar tare da ita sannan kuma nace mata in mun hadu a can tazo mu zauna tare a apartment din mu.


Bayan everything ya zama set kuma sai na ji duk jikina yayi sanyi. Naji bana son rabuwa da gida, da Inna da Subay'a da Asma'u. Bana son rabuwa da Sadauki. Inna nasamu wadda har lokacin bata daina fushi dani ba akan kin auren Sadauki, nayi mata bayanin manufa ta akan hakan, na nuna mata nima bawai hakan naso ba sai dai hakan nake ganin shine dai dai, sai ta dan sauko, ta saka min albarka sannan tayi min nasiha a game da zaman da zanyi a can.


Ranar tafiya Sadauki ne yazo ya dauke ni muka tafi airport, su kuma yan rakiya ta suka biyo mu a mota daban. A hanya babu wanda yayi wa wani magana a cikin mu har muka je muka yi packing sai kuma muka ci gaba da zama a motar. Can ya juyo yana kallona yace "can you promise me something?" Nima ina kallonsa nace "what?" Sai kuma yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan yace cikin rikakkiyar murya "zaki tafi jami'a, Oxford, akwai mutane da yawa a can, maza, and you are very beautiful am sure some of them will ....... God, bazan ma iya fadar kalmar ba" nayi murmushi nace "soyayya? I won't. Nayi maka alkawarin Halima ta Aliyu ce. In ba Aliyu ba kuma to babu wani namiji a gaba na" yayi dan murmushi yace "Allah yasa ki rike alkawarin nan. Dan ni yanzu am not sure about you anymore. Tsoro nake ji. Gani nake anya kuwa zan iya wannan zaman jiran kar inje fa zuciyata ta buga" sai nayi dariya nace "tsoro da girmanka" ya juyo and for the first time ya kama hannuna a cikin nasa ya rike yana kallona yace "let's play a little game da zai making everything easier for everyone. Let's make a bet" na girgiza kaina nace "ni kasan bana son wadannan games din naka fa" yayi dariya yace "tsoro kike ji? Tsoro kike ji kar kiyi failing?" Nace "kaima kasan ko sanda muke games din bana faduwa" yace "yes, kina winning, saboda ina barin ki kiyi winning dan kar kiyi kuka" sai muka fara musun cewa ba barina yake ba ni nake winning da kaina sai yace 


"let's do this one mu gani. Yanzu in muka rabu a airport din nan in kika sauka a UK, through out your stay har zuwa sanda zakuyi hutu in dai har kika dauki wayarki kika kirani da kanki then nayi winning and I got to decide whether or not zan saki Saghir. In kuma baki kira ni ba har kukayi hutu kika zo gida then kinyi winning kuma zanyi duk abinda kika ce"

[3/10, 9:37 PM] +234 706 757 8042: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By 


Maman Maama


Epidode Sixty Four : A Little Advise


Na dan tsaya ina kallonsa ina assessing maganarsa, yana kallona with a broad smile a fuskarsa, na dauke kai ina lissafi, yes it will make everything easy amma anya zan iya kuwa? Not talking to him for months bayan a yanzu bana iya kwana daya ba tare dana yi magana dashi ba? But the result is really worth it, amma kuma in na fadi fa? In na kira shi fa?.


Na sake kallonsa naga har yanzu ni yake kallo yana murmushi with an unreadable expression a fuskarsa. Na girgiza kaina, it is too risky gaskiya. Sai ya langwabe kai gefe kamar abin tausayi, yana robbing palm dinsa a nawa yace "Please Diyam, shekara biyar tayi yawa. Ba kya tausayina wai ke?" Nayi saurin zare hannuna daga nasa ina yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani blood rush da naji ya taso daga hannun nawa cikin seconds ya zagaye duk jikina. Cikin sarkewar murya nace "okay, okay. Na yarda. It is a deal" ya lumshe idonsa ya bude yana kallon yadda nake yarfe hannuna sai ya miko min nasa hannun yace "let's shake on that" na boye nawa hannun a cikin hijab dina nace "nace na yarda ai, no need to shake kuma" ya daga gira yace "tsoro kike ji?" Sai na dauki handbag dina nace masa "goodbye Aliyu" yayi murmushi yace "till we meet again Halima".


Na fita da sauri daga motar ina harhada hanya, but I felt as if gangar jikina ce ta fito ta bar zuciyata a cikin motar. Nayi kokarin calming down kafin in karasa inda Asma'u take jirana rike da sobbing Subay'a. Na durkusa na rungume ta ina jin tafiyar duk ta fita daga zuciyata, tausayinta naje ji sosai zata zauna without uwa da uba kuma bayan duk suna raye. Sai da muka je bakin departure hall sannan na juya na kalli inda motar Sadauki take, har yanzu yana nan a zaune, bana iya hangoshi amma ina hango duhunsa. A smiled at him, waved my hand sannan na shige.


Murjanatu ce ta tare ni a airport a Oxford. Muka tafi gida tare da ita, sannan washegari ita ta fara kaini school duk da dai itama bakuwar ce amma kasancewar ta fini wayewa da sanin kan al'amurra sai ya kasance ita tayi guiding dina har na kammala duk abinda ake bukata cikin nasara. I tot about Sadauki alot, tun a jirgi nake nadamar taking wannan bet din nasa but what is done has already been done, sai kuma naja damarar ganin cewa nayi winning dan mu samu nutsuwa gabaki daya ni dashi. Nasan shima burinsa shine yaci, kuma yana ganin kamar zaici din saboda yana ganin rauni na, and I decided to show him am strong. At first abin da wahala, musamman in naga kiransa ya shigo sai inji kamar in dauka amma nasan halinsa in na dauka zai iya cewa duk is part of the deal dan haka kiran nasa ma bana dauka. And it really hurts. Kullum babu fashi zai kira ni first thing in the morning, sannan ina dawowa daga school zai sake kira sai dai in naki dauka ya kira Murjanatu ya tambaye ta lafiyar mu ko kuma in muna bukatar wani abu. Kudi kuwa kamar ruwa haka ya sakar mana su, ina so in masa complain ince kudin sunyi yawa amma ina tsoron kar yace yayi winning. 


Most of the times in suna waya da Murjanatu sai in yi ta straining kunnena wai dan in jiyo muryarsa, wani lokacin kuma shi da kansa zai ce ta saka a handsfree yayi ta yi min magana amma sai in ki yin maganar duk a tsoron kar yace yayi winning "please Diyam, please, please kiyi min magana" amma na daure na cije na cigaba da ignoring dinsa hoping wannan ta zama karshen wahala ta. Gani nake yi taimaka wa Saghir da nake so yayi shine zai gyara image dinsa a gurin family dina, kuma ina hopping hakan ya zamanto sanadiyyar daidaituwar al'amura a cikin family din. And Subay'a. Ina so in aure na ya kasance Sadauki Subay'a ta rike shi a matsayin uba ba wai matsayin enemy ba, wannan shine zai tabbatar da zaman lafiya a tsakani na da shi. Sannan taimaka Saghir zaiyi softening heart dinsa ya zamanto mai yafiya ga wanda ya munana masa sannan mai tausayi ga na kasa dashi, wannan kuma zai kara kusantashi da mahaliccin mu. Dan haka ni a ganina duk abinda nake yi ina yinsa ne domin Sadauki.


And then he tricked me into calling him and also found out about Bassam. And now he is angry. Nasan kishi yakeyi dan nasan yana da kishi sosai, ni kuma har cikin zuciyata ba wai ina kula Bassam bane saboda wata alaka ta soyayya, na fara kula shi saboda in goge haushina da yake ji, and we became friends, sai kuma na lura cewa shi Bassam din ya fara developing feelings for me wannan shi yasa nayi deciding in yanke alakar mu tun kafin abin yayi nisa but the decision was made late, dan already Sadauki yasan maganar Bassam ba kuma na son yazo yayi wani abinda ba dai dai ba. Ban kashe wata wutar ba bana son a kunno min wata.


Wannan ne yasa na yanke shawarar bawa Bassam labari ne dan ya fahimci dalilin yanke alaka ta dashi, dan yasan waye Sadauki da kuma alaka ta dashi, sannan kuma ina hoping labari na zai taimaka masa wajen solving family issue dinsa kuma maybe zai iya bani shawarar yadda zan bullowa crises din Sadauki da Saghir.


(Now, some people need to re-read episodes 1-10. Diyam is in love with wanda yake kiranta. Kuma ba labari take bawa Bassam ba, she is going over the story a kanta kafin ta bashi. Lol)


Bassam yace "ina jinki. Ina so inji labarin naki" ta dauke idonta daga kallon ruwan da yake tsiri a fountain, sai ta samu kanta da yin murmushi ganin yadda ya nutsu yana kallonta, tace "ba labari ne mai dadi sosai ba, and get your hanky ready cos you might cry at some point" yayi murmushi amma baice komai ba sai ta bashi labarin ta in summary, asalinta, soyayyar su da Sadauki, mutuwar su Baffa, aurenta da Saghir da yadda sukayi rayuwar auren tsahon shekaru, dawowar Sadauki cikin rayuwarta da kuma mutuwar aurenta ta farko data biyu. Ta bashi labarin a takaice but without missing all the main points da zasu saka ya gane manufarta sosai. Sai kuma ta gaya masa winning din da Sadauki yayi da kuma text din da yayi mata dazu akan Bassam din. Tana bashi labarin yana yi mata tambayoyi a gurin


Baiyi kukan ba kamar yadda ta tsokane shi da, amma idonsa yayi ja fuskarsa ta nuna bacin ransa akan abinda ya faru da ita, abinda bai taba tsammanin yana faruwa a kasar sa har a yanzu ba. Ya kuma jinjinawa jarumtarta dan he can't even imagine a girl of 14 years going through what she went through. 


But his heart breaks daya fahimci karfin soyayyar da take tsakanin ta da Sadauki. Yes, da gaske ya fara jinta a zuciyarsa har yana hoping alakarsu will lead to something da zai fitar da khausar daga zuciyarsa. But daga labarin ta ya fahimci cewa cigaba da rike soyayyar ta a ransa will be a wrong move. She is already in love, deeply in love with someone else, just like Khausar. 


Ta katse masa tunanin sa ta hanyar cewa "ina fatan ka fahimci duk abinda nake so ka fahimta" ya gyada kai yace "na gane, sosai. Kuma bana jin da akwai wata kalma da zan iya furta miki wadda zata nuna how sorry I am akan abinda kika yi passing through a rayuwarki. It was unfortunate. Kuma bazan iya misalta miki how happy and how important I feel right now da har kika zaunar dani kika bani wannan labarin. Naji dadi sosai, na karu sosai, nayi wa rayuwa kallon da ada ban taba yi mata irinsa ba" tace "thank you, thank you for understanding Bassam" ya sake murmushi yace "nine da godiya, you have no idea how this is going to change my life. My family, I have been taking them for granted duk da irin kauna da kulawar da suka yi kokarin gina min rayuwata a kai, a lokacin dani nayi watsi da supportive family dina nayi kokarin rusa zumuncin dake tsakanin mu saboda budurwar da bama ta sona a lokacin ke kuma kike against mutumin da ya ke miki soyayya ta gaskiya irin aliyu saboda family din da suka yi everything possible dan ganin sun rusa rayuwar ki. You truly are an angel. I now understand the real value of my family, kuma zanyi iyakacin kokari na inga na gyara kuskure na. And like you said, story dinki ya kara nuna min ma'anar true love, it is not feelings like I said. It is much more than that, true love means sacrifice. Kayi sacrificing happiness dinka dan wanda kake so yaji dadi, ka sa farin cikin wanda kake so a sama da naka. Na koyi wannan daga Aliyun ki kuma nima zanyi applying dinsa a case dina da khausar, ina sonta dan haka zan dora happiness dinta a saman nawa, happiness dinta kuma shine kasancewa tare da wanda take so. Am going to let them be, and hope to find my one true love nima watarana".


Tayi murmushi tana jin tausayinsa a ranta, tasan so tasan zafinsa dan haka tasan decision din nasa is not an easy one. But it is for the best. 


Tayi ajjiyar zuciya tare da gyara zamanta tace "to saura ni. Ina so inji menene view dinka a game da sharadin dana kafawa Sadauki" ya girgiza kai yace "ni a fahimta ta, daga ke har Aliyu kuna kan gaskiyar kune, dan haka sharadin da kika kafa masa from your point of view dai dai ne. But where you are wrong is on the approach, hanyar da kike bi wajen ganin yayi abinda kike so ne ba tayi dai dai ba. Mu maza a yadda Allah ya halicce mu shine bama son ake directing din mu, do this, do that. Wannan hikima ce ta ubangiji sai ya saka mu as heads of the family mata kuma yace kuyi submitting to us. Amma inda hikimar take shine indai mace tabi namiji sau da kafa yi nayi bari na bari to zata juya shi ba tare da shi yasan tana juya shi din ba. Musamman ace idan yana sonta. Duk mijin da zaki ji ance mijin tace to shi bai san ma yana yin abinda mutane suke tsegumin ba. Irin son da Aliyu yake miki if you submit to him ba fito da Saghir kadai ba, in yana da dama zai iya fito da duk mutanen prison for you".


Ta jinjina maganar sa, Mama ta taba fada mata something similar to this, tace in ta nuna wa Sadauki soyayya zaiyi duk abinda tace but ita a ganinta ai tayi ta fada masa tana maimaita masa cewa tana sonsa kuma gashi nan har yanzu baiyi abinda take so din ba. Sai tace "yanzu me kake ganin ya kamata inyi?" Ya daga kafada yace "Marry him. Aurensa kawai zakiyi to make him feel loved, pamper him, take good care of him, ki tabbatar masa da cewa you are his and his alone kuma ki daina o da mentioning sunan Saghir then shi da kansa zai dubi yarinyar da take tsakani ya sake shi ba tare da kin furta hakan ba".


Ayi hakuri da wannan. A kuma yi hakuri da jina shiru kwana biyu, abubuwa ne suka cushe min but insha Allah in komai ya warware za'a cigaba da jina akan kari.

[3/12, 1:05 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Sixty Five: The Unbreakable Love


Ta tsaya tana kallon sa for some seconds. Sai kuma tayi murmushi very brightly sannan tayi dariya, shima dariyar yayi and they laughed together sannan tace "thank you Bassam. Nagode sosai" yace "no, thank you. Nine da godiya" wayarsa tayi kara ya dauko ta yana duba prayer alarm dinsa, lokacin magrib yayi. Suka mike a tare sannan suka jera suna tafiya suka bar garden din, taking their steps together kamar yadda suka shigo but unlike yadda suka shigo kowa rai a bace yanzu da zasu fita kowa a cikinsu murmushi yake yi. A bakin kofa ya tsaya yace "wait a minute, naji kince Umar Mustapha Abatcha, Umar Abatchan dana sani kike nufi ko kuma wani daban?" Tayi murmushi tace "shi din dai da ka sani, do you know him personally?" Ya girgiza kai yace "sunanshi dai na sani. But the son, ya taba zuwa gidan mu ones. Last year lokacin auren Ya Ameen Daddyn mu ya gayyaci father din sai bai samu damar zuwa ba but he sent the son to represent him. Ko gaisawa ba muyi ba amma zanso mu gaisa wata rana" Diyam tace "am sure shima zai so haduwa da kai" sai kuma tayi murmushi ta kara da "idan ya huce".


Yayi murmushi yana kallonta yace "goodbye Halima" tayi murmushi tace "see you soon Sadiq". Sai ta juya ta tafi shi kuma ya tsaya yana kallon bayanta, sai kuma yayi murmushi yana girgiza kansa yana tunanin irony din rayuwa. 


Duk wanda ya shigo rayuwarka da akwai dalilin shigowarsa, some enter your life to teach you a lesson, some to take lessons from you, some enter to help you and some to accept a help from you. Duk wanda ka hadu dashi to ya shigo rayuwar ka ne for a reason. Da akwai point din da zaka hadu da mutum akwai kuma point din da zaka rabu dashi bawai lallai dan bakwason juna ba sai dan role dinku to each other ya kare. The only person that will stay from start to finish in your life is YOU and YOU are the only person responsible for your happiness.


People are not perfect, nobody is, so if you truly love a person you just have to accept him/her the way s/he is, accept both the good and the bad sides of them and together you can bring out the best in each other.


Ya juya da sauri ya koma cikin hotel din sannan ya hau zuwa dakinsa. Yana zuwa ya fara gabatar da sallah sannan ya jawo jakarsa ya fara zuba kayansa a ciki. It is time for a change a rayuwarsa, Nigeria zai tafi ya gyara rayuwarsa but before that he have to pay a visit to his Aunt first, yasan haduwarsu ba zatayi masa dadi ba but dole yayi clearing mess din da yayi creating da kansa.


Diyam tana zuwa gida itama sallar ta gabatar sannan ta tsaya a gaban mudubi tana practicing yadda zata fuskanci Sadauki gobe. Tasan akwai battle a tsakanin su dan ta tabbatar da daurarriyar fuska zai sauko daga jirgi. Sai ta fara making faces a mudubi tana zabar wacce zata fi melting frozen heart dinsa. Ta gwada fuskar tausayi, ta gwada fuskar shagwaba ta kuma gwada serious face amma duk sai taga basu yi mata ba. Ta binciko kaya tana zaben wadanda zata saka saka suma kuma taga duk basu yi mata ba, ta tuna ranar nan a Kano da Murjanatu tayi mata kwalliya ya yaba sosai dan haka gobe ma zata saka ta tayi mata. And she is going to wear dogon hijab kamar yadda yake so. 


Ta ajiye kayan ta fita da sauri zuwa dakin Murjanatu, ta tarar da ita tana waya sai ta tsaya har ta gama sannan tace "Murjanatu Please zo ki taya ni zaben kayan da zan zaka" Murjanatu ta ajiye wayar tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace "kayan da zaki saka yaushe? Biki zaki je?" Diyam ta harare ta tace "kakan biki ba biki ba. Malama ni fa yayarki ce kuma am ordering you to do something for me" Murjanatu ta hade hannayenta tace "to babbar yaya tuba nake yi, tunda yaya na za'ayi wa kwalliya dole in tashi". 


Haka sukayi spending the night preparing. Har takalmi da sarka sai da aka ware. Sannan suka yi plan din abincin da zasu dafa masa. Tuwo dai yafi so miyar yauki amma basu san inda zasu samo ingredients din ba dan haka Diyam ta yanke shawarar dafa masa farin couscous garnished with vegetables sannan kuma suyi masa farfesun kifi sai kuma suyi pepper meat. Drink tasan yana son kunun aya amma bata da aya dan haka zata yi masa banana smoothie.


Ta kira shi da niyyar tambayarsa sanda jirgin su zai sauka amma kamar yadda tayi tunani sai yaki picking, tayi masa text babu reply. Ta saka Murjanatu ta kira shi itama yaki dagawa duk sai taji babu dadi, shi wannan zuciyar tasa ce problem dinsa, yana da saurin hawa amma kuma yana da saurin saukowa dan haka ta shirya sauko dashi goben in yazo. 


Ta lura Murjanatu duk ta daga hankalinta sai ta zaunar da ita tace "kar ki wani damu kanki da fushinsa, zai sauko na gaya miki ki barni da shi kawai" Murjanatu tace "baki san halinsa ba, zai iya raba ni da makarantar nan fa wallahi. Akwai abinda ya taba yi min a gida Canada akan wani saurayi na an gaya masa bad abubuwa akan sa sai yace min kar in kara kula shi ni kuma na cigaba da kulashin. Ashe yasa a saka masa ido a kaina sai gashi an tura masa da videon mu tare a gurin cin abinci. Ba wani abin muke ba kawai muna hirar mu muna dariya. Akan haka ya karbe wayata kuma yayi grounding dina a gida for three months ko kofar gida bana fita. Papa da Mama kuma suka biye masa yanzu ma kuma nasan duk abinda yace biye masa zasuyi" Diyam tace "ba zai ce komai ba, ki barni dashi".


Suka duba suka tabbatar suna da abubuwan da suke bukata, abinda basu da shi kuma sai sukayi order online da niyyar a kawo musu da sassafe. Sai kuma suka shiga website din airport suka duba flights schedules na gobe, anan suka ga time din da jirgi zai sauka from Nigeria. Sai yamma. Wannan yasa suka yi baccinsu sosai sannan suka tashi a tsakane suka yi komai tare har da Judith itama ta taya su, suka ci abincin su sannan suka yi wanka aka zauna kuma yin kwalliya a shafa wancan a goga wannan a ja wancan suna ta rigima har aka gama sannan aka yi dressing aka kuma bi da turare. Murjanatu ce ta dauko hijab da kanta ta bawa Diyam tace "gwara ki saka tun kafin yayi ball damu tun daga airport har gida".


Tare suka tafi airport din a mota, suka bar Judith a gida tana gyara musu gidan. A hanya duk sukayi shiru kowa tana lissafe lissafen ta sannan Diyam tace "Murjanatu a tunanin ki ta yaya Aliyu yasan ina kula Bassam?" Murjanatu ta daga kafada tace "yaya Aliyu ne fa, ya iya bincike ta karkashin kasa I guess wani ya saka ya saka masa ido akan mu. The guy might have saw you two together and reported to him" Diyam tayi shiru tana tunani, she will have to talk to him about that, hakan kamar rashin yarda ne. Murjanatu ta katse mata tunanin ta ta hanyar cewa "there is nothing between the two of you, is there?" Diyam ta harare ta tace "in kina son shi just say so, sai in hada ku" Murjanatu ta tabe baki tace "bai yi min ba, he is definitely not my type. Daga ganin sa nasan lady's man ne, Allah kadai yasan yawan yammatan sa" Diyam tayi dariya tace "wai dama kura tana iya cewa da kare maye? Ke ma Allah ne kadai yasan yawan samarinki" Murjanatu ta yi murmushi ta fara bata labarin new catch din da tayi a school last week.


Suna tsaye suna jira jirgin ya iso, Diyam tana ta jujjuya hannun ta feeling nervous dan bata san da wacce zai zo ba sannan kuma ga zuciyarta da take neman betraying dinta saboda dokan tuwa da tayi gurin son ganinsa after almost three months of not seeing him. And then suddenly sai idonta ya sauka a kansa, yayi kyau sosai fuskarsa tayi fes gashinsa na fulani da sajensa sun kwanta lufluf suna daukan ido. The freshness of his dark skin alone zai tabbatar maka da cewa he is taking good care of his body, yanayin takunsa kuma da posture dinsa sun nuna yawan ziyarar da yake kaiwa gym. Their eyes locked, and everything in her stopped except bugun zuciyarta da yayi doubling. He walk straight to gabanta ya tsaya one hand inside pocket, his expression unreadable yace "hello Madam".


Ta bude baki zatayi magana amma sai taji duk rehearsal din da tayi na abinda zata ce masa ya gudu ya barta. Yayi mata kwarjini da yawa, and the fact that he called her madam have added to that. Sai ya dauke idonsa daga kanta ya mayar da dubansa kan Murjanatu da take kusa da ita tana mishi murmushin dole, suna hada ido tace "sannu da zuwa yaya, ya flight din?" "Fine" yace mata in short sannan ya zagaye su yayi hanyar fita, Murjanatu taja hannun Diyam da sauri suka bishi a baya. Suna fita suka ga cab tayi packing a gabansa Murjanatu tayi saurin cewa "ga mota munzo da ita fa" ya juyo yana kallon Diyam yace "thank you" sai ya shige suka ja suka barsu a wajen.


Murjanatu ta juyo tana kallon Diyam tace "you kept quiet, me yasa zaki yi shiru?" Diyam tace "he called me Madam. Kin san kuwa yadda nake jin haushi in yace min Madam?" Murjanatu tayi dariya tace "to menene na jin haushi? In yace miki Madam sai kice masa Sir, ba shi kenan ba? Now we have to follow him kuma" suka shiga mota suka bi bayan cab din data dauke shi but sai suka ga sunyi wata hanyar daban ba hanyar gidan su ba, Diyam zata yi magana Murjanatu tace "gidan Papa zashi. Inda muke sauka in munzo gari" sai Diyam ta juya kan motar suka yi hanyar gidansu. Murjanatu tace "ba binsa zamuyi ba?" Diyam tace "we cooked for him, dole kuma yaci abincin da muka dafa".


Suna zuwa gidan Murjanatu ta shiga ta hado kan girkin da suka yi masa ta jera a babban basket sannan ta dawo motar suka kama hanyar wajen gari inda anan ne gidan yake. Suna packing Diyam ta tsaya tana kallon gidan a ranta tace "wow, da gaske dai Umar Mustapha Abatcha ne ya haifi Sadauki" ba mutane a gidan sai security daya bude musu gate suka shigo, amma komai na gidan tsaf yake daga alama ana zuwa aba gyaran gidan akan kari. Kofar da suka hango a bude suka dosa, suka shiga wani palo madaidaici Diyam tana iyakacin kokarinta na ganin bata yi kauyanci ba. A kan dining suka hango shi yana zaune yana kallon kofar da suka shigo. He kept his eyes on them har suka karaso Murjanatu ta ajiye basket din hannunta ta gaishe shi ya amsa tare da tambayarta karatu, sai kuma tace da Diyam bara taje ta dubo wani abu a cikin gidan. 


Sai data fita sannan Diyam ta dauke idonta daga kansa ta sauke kan wata baturiya sanye da apron da hular cooks tana ta jera abinci akan dining table din gabansa. Diyam ta tako ta karaso gurin tana kallon baturiyar tace "thank you, I will take it from here" sai matar ta juya tana kallon Sadauki shi kuma ya yi mata alamar ta tafi da hannunsa sai ta juya ta bar gurin. Diyam tabi bayanta da kallo tana jin haushinta ba tare da matar tayi mata komai ba. Sai kuma ta fara tattare abincin kan table din tana ajiyewa gefe sannan ta dauko basket din da suka shigo dashi ta dora akan table din ta fito da abincin ciki ta jejjera sannan ta jawo kujera kusa dashi ta zauna. Tunda ta fara yayi folding hannayensa yake kallonta har ta gama ta zauna sannan ta jawo plate gabanta tace "banyi maka tuwon da kake so ba saboda bani da kayan hadi. Amma nayi maka something da nake tunanin zaka so" still idonsa akanta yace "how is he" ta gane maganar da yake amma sai ta cigaba da hada abincin ta, carelessly tace "how is who?" Sai ta debo abincin a spoon ta kawo bakinsa tace "ha" and she saw his lips curved in a smile amma sai ya juya fuskarsa gefe kar ta gani sai ta sake bin bakinsa da spoon din tace "ha muga ni" sai ya langwabar da kai sannan a hankali ya bude mata bakin ta saka masa abincin a ciki sai ta zauna tana kallon sa with wide opened eyes shi kuma yana taunawa a hankali sannan tace "please tell me yayi dadi. I spent hours ina shirya maka abincin nan kamar yadda nayi spending hour ina yi maka kwalliya amma gashi nan ko yaba wa ba kayi ba" ta karashe maganar kamar zata yi kuka. 


A hankali yace "waye yace miki ban yaba ba?" Ta turo baki tace "you called me Madam, kuma kaki shiga mota ta" ya danyi murmushin daya tsaya a iyakacin idonsa yace "to ba Madam din bace ba ke?" Tace "I am not Madam, in ka kara gaya min kuma nima Sir zan ke ce maka" and his smile widen to his lips. Ta sake dauko wata lomar ta kuma cewa "ha" ya bude ta saka masa yana ci ya kuma cewa "how is he?" Ta gyara fuskarta zuwa serious one tace "kana magana akan Bassam ko?" Ya daga kafada yace "bansan sunansa ba and I don't want to know" tace "he was fine as of yesterday, bansan ya yake yau ba. Kamar yadda bansan me yasa kake wani tunani akan sa ba. He is just my friend, department din mu daya muna lectures tare and he is a Nigerian" ya bata fuska yace "shi yasa kuke cin abinci tare?" 


Ta saka masa wata lomar a baki sannan tace "and how do you know that? Wani ka saka yake spying on me? Baka yarda dani ba?" Yace "babu wanda na saka yayi spying on you. Akwai mutumin da muka yi harkar admission da registration dinku tare. He saw your pictures then. A lokacin kuma na gaya masa ke matata ce then he saw you with that boy and thought ya kamata in sani. I told him bake bace ba cos I thought you would never do it sai ya tura min da picture of you two together" ta ajiye spoon din hannunta tana kallon yadda fuskarsa take nuna bacin rai, yace "do you like him?" Ta dafe kanta tace "I just told you, Bassam is my friend. Na bashi labarin ka ma na gaya masa zaka zo yau kuma har cewa yayi zai so ku hadu. There is nothing there. Please stop looking for something that isn't there" she saw him relax a little yana kallonta yace "he is handsome" tace "really? Ni ban gani ba. He may be one of the thousands of stars in the sky amma ni duk bana ganinsu, only one star shines brightly a ido na, you. Kai kadai nake gani a matsayin mai kyau sauran duk dusudusu nake ganin su. You are the only star in my sky". 


And he smiled. This time genuine smile yayi mata ya lumshe idonsa ya bude yace "I always remember that night duk sanda naga starry sky" ta sunkuyar da kanta kasa tace "me too".


Sai ya saka dogayen fingers dinsa guda biyu ya dago fuskarta yana kallon cikin idonta yace "feed me" ta hadiye wani abu a makogwaron ta amma taji yaki tafiya, sai ta yi sauri ta dauke idonta daga cikin nasa ta dauki spoon with shaking hand ta cigaba da bashi abinci. Bai kuma magana ba sai ido daya tsare ta dasu har sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta bashi drink ya sha sai kuma yace "thank you, this is the best food I have tasted for a while. Ko kuma yadda aka bani abincin ne ya saka naji yafi kowanne dadi?" 


Sai kuma ta danji kunya ta rufe fuskarta da bakin hijab dinta, suddenly sai taji babu abinda take so irin ta kuma jin wannan kalmar daga bakinsa but as her husband yadda zata ji dadi fiye da na yanzu kuma ta samu lada mai yawa. 


Sai ta zame daga kujerar da take zaune ta durkusa a gabansa tana kallon yadda yake kallonta da mamaki tace "Aliyu Umar Abatcha. Will you do me the honor of marrying me?" 


Please, duk wanda Allah ya bawa ikon karanta wannan page din ina barar a karanta min surorin Falaq da Nas. Da niyyar Allah ya gina mana katangar tsari tsakanin mu da duk wanda yake neman mu da sharri, Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi tsakanin mu da duk mai neman mu da alkhairi. Allah yayi mana jagora kar ya barmu da iyawar mu dan mu ba zamu iya ba. Allah ya tabbatar mana da alkhairi a kasar mu baki daya.


Nagode

[3/14, 10:49 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Sixty Six: The Unbreakable Love 2


Naga adduoin ku, nagode sosai.


For two seconds ya zauna yana kallonta da tsantsar mamaki a fuskarsa sai kuma yayi sauri ya mike tsaye ya kamo hannayenta duk biyun ya mikar da ita tsaye yana kallonta tana murmushin ganin duk yadda yabi ya rude sai yace cikin saurin murya "No! No".


Ta bude ido da mamaki tace "no?" Sai ya saki hannunta da sauri ya dafe kansa yace "ba wannan no din ba, I mean no karki durkusa please, karki bata kayanki" ya fada yana ciwo hanky da sauri ya kama goge mata hijab dinta, sai daya dago sannan ta daga gira tace "so? Yes ne ko No?" Maimakon ya bata amsa sai ya dora goshinsa a kafadarta, tana jin yadda ya sauke wata nannauyar ajjiyar zuciya wadda tasa hawaye ya gangaro daga idon Diyam sannan yace can kasan makoshinsa "Yes Diyam. Of cause I will marry you. You have no idea how much I want to marry you" 


Murjanatu ta bude kofa ta shigo, sai kuma ta tsaya tana kallon su sannan tace "wrong room. Ba nan zan shigo ba" sai ta kalli kofa tace "Na'am!" Ta juyo tace "they are calling me so I gotta go" sai ta juya da sauri ta fita. Diyam tayi dariya tana share kwallar idonta tace "she is funny. Babu wanda yake kiranta" ya danyi dariyar da Diyam taji vibration dinta a kirjinta yace "kika sani ko aljanun gidan ne suke kiranta?" 


Ta dan matsa baya forcing him to raise his head from her shoulder. Sai ya kalle ta da idon da suka fara chanja color yace "yaushe kika chanja shawara kuma? What about Saghir? Kin fasa fitar dashi din?" Ta zauna a kujera tayi dagumi but fuskarta da murmushi tace "you won the bet, I can't continue to deny myself freedom. Nayi kokari ai ko?" Ta fada da sanyin murya. Ya zauna opposite dinta yace "Subay'a fa?" Tace "in muka yi aure Subay'a ta zama yarka. And I trust you will do everything in your power to make your daughter happy" ya gyada kai yace "you bet. She is going to be the happiest girl ever".


Matar dazu ce ta shigo ta fara gyaran dining table sannan ta zo gurin su tana tambayar Sadauki in akwai abinda yake bukata in babu tana son tafiya. Ya sallameta ta tafi ya juyo yana kallon Diyam da take bin bayan matar da harara yayi murmushi yace "what?" Tace "fire her. Ita da wannan secretary din taka ta Kano" ya bude ido da mamaki yace "why?" Ta turo baki "ni bana son su" yayi dariya yana shafa kansa yace "and you accuse me of being heartless" ta bude hannu tace "sai ka basu wani aikin ai. Kai kuma ka samu maza suke yi maka irin wadannan aiyukan" yayi tagumi da hannu daya yana kallonta yace "yarinyar nan anya kuwa Baffa bada A'isha yayi miki huduba ba? Kishinki yayi yawa. Yanzu suna min aiki kince ba kya so, so tell me idan kuma kika gan mu tare muna cin abinci a cafeteria mai zaki yi? Hmm?" Ta gane inda ya dosa sai tayi saurin cewa "kayi hakuri, an gama ba za'a kuma sakewa ba" bai ce komai ba sai kallonta da yake tayi fuskarsa da murmushi. Ta jawo fuskar hijab dinta ta rufe fuskarta tace "ni kunya kake saka ni in kana kallona" sai ya koma ya jingina a jikin kujerar yace "kinsan tunanin me nake yi?" Ta bude fuskar ta tace "no" yace "tunani nake yi in koma airport a yau in koma Nigeria, gobe inga Kawu Isa jibi a daura mana aure in dawo gurin amaryata a jibin" tayi saurin mayar da fuskarta ta rufe tace "kai dan Allah. Ka dai bani lokaci in shirya dai ko?" Yace "wacce shiryawa kuma? Nasan a gida zasu ce zasu shirya wani abu amma koma menene sai dai su jira sai bayan na tare da amarya ta" sai ta mike da sauri tayi hanyar waje tana hada hanya tace "sai dai ka tare kai kadai" ya biyo bayanta yana cewa "dama ai ni kadai nake tarewa ta kullum on my empty cold bed, it is about time I get some warmth" ta karasa kofar da sauri tana hoping ba irin ta office dinsa bace ba. Tana murdawa taji ta bude ta fita tana raba idon inda zata hango Murjanatu, sai gashi nan ya fito shima ya rufe kofar ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa da kafafuwansa yace "run run little girl. Duk inda zaki je you will come back here" ya fada yana nuna kirjinsa yace "cos that's where you belong. A heart belongs to the chest".


Ta juya suka hada ido, feeling like yau ta fara ganin sa. She couldn't help but look at chest din daya nuna, very broad and very strong, sai taji babu abinda take so irin ta jita a gurin feeling the warmth and the strength that she so much miss. Ta hadiye wani abu tare da saurin girgiza kanta a kokarin ta na goge image din daga kanta tace masa "uhmmm. Lokacin Sallah. Murjanatu" yayi mata murmushin gefen baki sai ya nuna mata wata kofa da hannu" ta juya da sauri ta tafi can. Sai data bude kofar ta shiga sannan ta rufo kofar ta jingina da jikinta ta yi ajjiyar zuciya. Sai kuma tayi murmushi tana girgiza kanta. 


Daga gefenta taji ance "hmmm. Wato da can anaso ana kaiwa kasuwa akeyi ko?" Ta juyo ta harari Murjanatu tace "ke nifa yayarki ce, bana son rashin kunya". Anan tare sukayi sallah tare sannan suka fita Murjanatu tana zagayawa da ita gidan Diyam tana ta kashe kwarkwatar idonta. Komai na gidan abin kallo ne, exact lissafin da Diyam take yi na abinda ake cewa aljannar duniya. Suna cikin zagayen suka hadu dashi, yace da Murjanatu "thank you Fanna, zaki iya komawa daki" ta turo baki tana buga kafa amma yana yi mata wani kallo ta juya ta koma. Diyam tace "kai kuwa ka barta mana mu karasa" yace "a gabanta zanyi hira dake? Kina sone ma ta raina ni kenan" suka jera suka cigaba da tafiya tare, but ba kallon gida sukeyi ba hirar su kawai suke yi suna jin dadin iskar da take kadasu. 


Ta rungume hannunta tana jin sanyi amma bata son nunawa dan tana jin dadin hirar da yake yi mata, sai ya cire top dinsa ya saka mata, ya cigaba da bata labarin irin yadda ya yi ta kokarin ganin ta kira shi dan yayi wining amma taki. Yace "har halucination fa nake yi. In wani ya kira ni sai inga kamar ke. It was hectic. I almost lost it" tayi murmushi tace "kasan me? Wani lokacin sawa nake Murjanatu ta saka min kai a handsfree" ta fada tana rufe fuskarta, yace "laaa ila, that was cheating" ta bude fuskarta tana hararar sa tace "har zaka yi maganar cheating?" Yayi dariya yace "bature yace 'nothing is fair in love and war".


A lokacin suka kai karshen gidan sai suka juyo suna retracing steps dinsu sai yace "sanda zaku taho Papa cewa yayi ku zauna a nan gidan, but sai na nuna masa cewa yayi nisa zaku ke shan wahalar transportation. But ni personally ba wai dan haka na samo muku wancan gidan ba, ni a ganina you are my responsibility kuma nan ba gida na bane ba bana son matar gidan ko sauran siblings dina suzo gidan suyi miki wani kallo, gwara can nawa ne babu mai daga miki kai" tayi murmushi tace "bansan sauran ba amma Murjanatu tana da kirki sosai" ya gyada kai yace "tana da kirki, suma duk basu da problem amma hausawa sunce maganin kar ayi kar a fara".


Sai da sukayi sallar isha sannan suka bar gidan. Zuciyoyin su tas kamar takarda. Suna zuwa gida sukayi wanka suka yi shirin kwanciya saboda duk sun gaji. Diyam ta kwanta tana bitar maganganun su da Sadauki. Yes, ta karbi shawarar Bassam, Sadauki baya son tana maganar Saghir dan haka ta daina amma bawai ta bar maganar bane ba, zata jira taga if he will come around and do the right thing da kansa.


Watarta tayi kara ta dauka tana murmushi. Bai gaji da hirar ba kenan. Ta dauka da sallama yace "so nake in taho nan kin yarda?" Tace "nan kuma? Me zaka yi anan din?" Yace "hira zan yi miki kadai" tace "to kayi min a wayar mana, ai ina jinka a haka" yace "nafi son inke ganin ki as ina miki maganar. Nafi son in yi miki joke kiyi min murmushi in gani. Nafi son in tsokane ki ki harare ni in gani. Nafi son in fada miki sweet sweet words inga kin rufe fuskarki kina jin kunyata" sai taja abin rufa ta rufe fuskarta. Tace "ni dai kar kazo zuwa zakayi kayi ta sakani jin kunya" sai kuma tace "amma bada gaske kake ba zancen daurin aure jibi ba ko?" Yace "in da zan samu yadda nake so da ko gobe nema ina so. But nasan ba zan samu ba, Papa zai ce abokansa da sauran mutanen sa, Mama zata ce zasuyi biki, and you, I want you to have all the wedding things da baki samu ba ada. So, I will wait. Kinsan ni am a patient bird. Yanzu ki gaya min duk abubuwan da kike so for the wedding" ta lumshe ido tana tunanin childhood dreams dinta, but those are only dreams kuma yanzu sun zama past, dan haka tace "ni bana son komai fa. Sai dai ko in kai kana son wani abu" yace "ni ke nake so. I want only you, and that's the only thing that matters" taji ta tamkar tana narkewa tana shigewa cikin katifar da take kwance. Is it possible to love someone this much? 


Suka cigaba da hirarsu mai ratsa zuciya, tana bashi labarin makaranta da yadda tayi adapting, shima yana bata labarin lokacin da yake tasa makarantar. She told him about Bassam abinda ya hada su da yadda rayuwar su ta kasance tare but sai taki gaya masa cewa Bassam ya fara sonta. She told him yace ya taba ganinsa yaje daurin auren brother dinsa. Sai a lokacin yace "Abuja? Last year you said?" Tace "eh" ya danyi tunani yace "naje daurin auren gidan sarki. Maybe can yake". Sai da yaji alamar ta fara jin bacci sannan yace "kiyi addu'a ki rufe idonki. I will talk to you sai kinyi bacci saboda ina son kiyi mafarki na" 


Took my hand, Touched my heart, Held me close. You were always there, By my side. Night and day, Through it all. Baby, come what may.

Swept away on a wave of emotion, Oh, we're caught in the eye of the storm. And whenever you smile, I can hardly believe that you're mine, Believe that you're mine.

This love is unbreakable. It's unmistakable. And each time I look in your eyes, I know why.This love is untouchable. A feeling my heart just can't deny. Each time I look in your eyes, Oh, baby, I know why This love is unbreakable.

Shared the laughter, Shared the tears. We both know We'll go on from here. 'Cause together we are strong. In my arms: That's where you belong.

I've been touched by the hands of an angel. I've been blessed by the power of love. And whenever you smile, I can hardly believe that you're mine.

This love is unbreakable. Through fire and flame. When all this is over, Our love still remains.

This love is unbreakable. (Lyrics by Westlife)

Washegari Sunday, Diyam tayi baccin safenta sosai sannan ta tashi. Tana mikewa ta jawo wayarta ta tura masa message cewa tana gayyatarsa breakfast. Ta fita ta tarar duk su Murjanatu suma babu wanda ya tashi dan haka ta zarce kitchen ta fara shirya abinci. Tana cikin aikin Judith ta shigo suka cigaba tare har suka kammala sannan ta tafi ta tashi Murjanatu ita kuma ta shiga tayi wanka ta shirya sannan suka fito kusan a tare da Murjanatu. A palo suka hadu suka baje kayan breakfast suna yi sai gashi ya shigo. Suka gaishe shi gaba-daya ya amsa da sakakkiyar fuska tana bude warmers din gurin. "Me aka shirya mana ne?" Murjanatu ta tashi tana serving dinsa yayinda Judith tayi musu sallama ta fita. Ya jingina da kujera yana shan tea yana kallon Diyam yace "kin yi kyau sosai" ta sunkuyar da kanta tace "thank you".


Ranar wuni sukayi tare, ya dauke su a motar Diyam suka fita yawon zaga gari. Sai dare suka gama suka dawo gida ya ajiye su shi kuma ya tafi da motar. A daren Diyam ta kira Inna dan rabon da suyi waya tun sanda ta kira ta suna tare da Bassam. Inna ta dauka suka gaisa suka kuma gaisa da Asma'u da Subay'a. Sannan Inna ta karba tace mata "ya bakon naku?" Diyam tace "lafiya lau Inna" Inna tace "ya gaya miki abinda yayi? Naji bakiyi mana magana ba" Diyam taji gabanta ya fadi, me kuma yayi? Sai ta dake tace "me yayi kuma Inna? Ni bai gaya min komai ba" Inna tace "nasan dama bai gaya miki ba, na dauka zai gaya miki yanzu da yazo. Ya kwashe dabbobin nan daga gidan Alhaji Babba ya mayar dasu bayan gari tun kusan sati biyu da suka wuce. An buge katangar tsakiyar gidan Alhaji yace ya bar masa gurin kyauta".


Ga breakfast, ayi enjoying tare da oga.

[3/17, 12:15 AM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Sixty Seven: The Inheritance


Diyam ta ajiye wayar tana tunani, sati biyu da suka wuce Inna tace anyi relocating gidan gonar, sati biyu da suka wuce lokacin Sadauki bai ma yi winning bet dinsu ba. This means yayi abinda yayi ne on his own account ba wai dan yayi winning bet din ba. Shin hakan yana nufin Saghir yana da hope?


Washegari Sadauki ya koma Nigeria. A airport Diyam ta marairaice masa kamar zatayi kuka shi kuma ya rikice. "Ki taho mu tafi. Sai ki dawo next week" tace "school kuma fa?" Yace "share school din nan, ai baku fara exams ba" sai ta tuna sanda yake hanata zuwa islamiyya, tace "so kake ayi min bulalar fashi ko?" Yace "waye zaiyi miki bulalar? Gaya min shi in fara yi masa tun kafin yayi miki" tayi dariya kawai tana tuno jibgar da ta sha a gurin Saghir, sai tace "ni yanzu mai duka na ai sai dai ruwan sama, ruwan saman ma sai na tsaya" yayi kasa da murya yace "in kin tsaya din ma I will shield you from it, like an umbrella" sai ta tuno sanda Inna ta kama su suna saukowa daga sama tazo zata dake su ya kare ta shi akayi ta dukan sa. He had been shielding her all his life. Ya katse mata tunanin ta ta hanyar langwabe kai yace "Please kizo mu tafi" ta makale kafada tace "naki, sai dai ka zauna anan" yace "ai kinsan maganar da zata mayar dani Nigeria. So nake fa ayi lokacin hutun ku sai mu dawo tare" ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, sai kuma tace "Inna ta gaya min zancen Alhaji Babba. An gode madallah Allah ya kara arziki" yace "ameen" sai kuma ya dauke kansa gefe kamar yana tunani yace "ina yammatan gidan? Su Murja kawarki wadanda kika yi min maganar su rannan akan har yanzu basuyi aure ba?" Diyam tace "suna nan. Muna waya da Murja ma. Wani abin ne?" Yace "ya maganar auren nasu" tace "suna jira dai. Last wayar da muka yi tace min zata tura saurayinta gurin Baba Sa'idu (mijin anty Fatima)" yace "idan kun sake waya kice mata zakiyi musu kayan daki, ita da sisters dinta" ta bude baki tana kallon sa yace "ke ba yayarsu bace ba, ke zakiyi musu kayan daki ai" ya dauke kai yace "in place of their brother".


A kano bayan Sadauki yaje gurin Mama yaje ya gaya mata sun daidaita da Diyam, sai kuma ya nemi shawarar ta akan abinda ya dace yayi next. Sai ta nuna jin dadin ta sosai tace "ko ku fa, ai hakan yafi muku akan wannan zaman jiran da da kuka ce zaku yi" ya shafa kai yana murmushi. Tace "to yanzu abinda za'ayi shine zanje ni da kaina in samu Alhaji Babba, in yaso sai ya fadi ranar da za'a je a same su kai kuma sai ka fada a can gida sai su zo" yace "da nayi tunanin ko Kawu Isa, saboda kar a samu matsala da Alhaji Babba" Mama ta girgiza kai tace "babu matsala insha Allah. Shine Babba dan haka dole a bashi girman sa in ya karba shikenan in bai karba ba in yaso sai a je wani gurin a nema" suna cikin maganar sai Mukhtar yazo, suka yi hannu da Sadauki, Sadauki yace "ka yar dani Mukhtar, ko nema na bakayi" Mukhtar yayi dariya yace "ai ka zama yallabai ne yanzu, ka zama hukuma sai da lallashi" Sadauki yayi murmushi yace "sharri zaka yi min kenan ko? Zan samu time zaka ganni har gidanka".


A Oxford da Diyam taje school sai taji babu dadi saboda ganin seat din Bassam empty. But sai taji dadi dan hakan yana nufin ya tafi gida kenan, ya tafi yaje ya gyara tsakanin sa da family dinsa. She just hope ba zai dade sosai ba saboda kar karatunsa ya samu matsala.


Kamar yadda Mama tayi alkawari, washegarin da Sadauki yaje ya same ta sai ta tafi gidan Alhaji Babba. As usual, bata ji dadin yadda ta samu gidan ba duk da dai a yanzu matan gidan sun fara yan sana'o'i, Hajiya Babba tana siyar da ruwan sanyi, lemo da kankara. Hajiya Yalwati kuma tana yin snacks, da wannan sana'ar suke kokarin ciyar da kansu da yayansu dan Alhaji Babba har yanzu kusan dashi da babu duk daya a gidan sai ma jigilar asibiti da suke tayi dashi, shi bai mutu ba shi kuma bai cigaba da rayuwa normal ba. 


Taje suka gaisa da matan gidan sannan ta tafi dakin Alhaji. Yana nan har yanzu a dakin da Inna ta zauna bai koma part dinsa ba duk kuwa da cewa Sadauki ya saka an gyara part din tas batan an kwashe kajin. Ta gaishe shi ya tashi daga kwancen da yake ya amsa mata yana tambayarta lafiyar family dinta, kafin ta gabatar masa da abinda ya kawo ta sai cewa yayi "Hafsa ina Diyam, har yanzu bata zo gari ba?" Mama tace "bata zo ba. Basu samu hutu ba ai" ya mayar da kansa ya kwantar yace "Diyam yarinyar kirki ce mai son zumunci. Fatima ta gaya min abinda tayi wai taki auren shi wannan yaron da take ta nacin so tace lallai sai ya fito da Saghir tukunna zara aure shi. Banyi tsammanin haka ba, na dauka in ta juya bayanta ta bar Saghir a prison ba zata sake waigen inda yake ba, na dauka in ta samu cigaba a rayuwa ba zata sake tunanin halin da muke ciki ba. Ina so inga Diyam Hafsa, ina son in roki gafarar ta tun kafin lokaci na ya kare a duniya. Ina kuma son in roki gafarar Saghir. Ko ma menene Saghir ya zama ko ma menene Saghir yayi ko ake zargin yayi to laifi nane, nine na lalata rayuwar dana mafi soyuwa a zuciyata duk a tunanin soyayya ce nake nuna masa. Ina sane, ina sane da duk abinda Saghir yake yi nasan yana yi din amma sai in rufe idona in nuna tamkar ba zaiyi dinba saboda ina so in gaya wa kaina cewa ba zaiyi din ba. Banyi nadama a bisa tarbiyyar da nayi wa Saghir ba sai da na je gidan yari na ganshi tukunna" yayi shiru yana kokarin saisaita muryarsa saboda kukan da yaji yana neman ya kwace masa. Mama ta fara bashi hakuri "sai hakuri Alhaji, komai mukaddari ne komai rubutacce ne" yace "haka ne, amma komai yana da sila. Silar lalacewar Saghir kuma shine rashin tarbiyyar dani da mahaifiyar sa muka gaza bashi. Ba kuma mu tashi ganin sakamakon abin ba sai da ya zama babu abinda zamu iya yi akai. Bani da yadda zanyi in fito da Saghir daga inda yake, bani da kudi ko hanyar samun kudin da zan biya yaron nan kudinsa sannan bani da karfi na jiki dana aljihu da zan samo wannan yaron daya lika masa wadannan kwayoyi" 


Yayi shiru yana tunani sannan yace "Hafsa, idan kunyi waya da Diyam ki nemar min gafararta dan ban tabbatar da zanyi tsahon ran ganin ta in roke ta da kaina ba, sannan kuma ki ce ina rokon alfarmarta akan ta janye waccan maganar ta kin cikawa kanta burin zuciyarta na auren Sadauki, ta aure shi indai tana sonsa, shi kuma ruwansa ne ya yafe wa Saghir ko kuma yaki yafe masa wannan zabin sa ne".


Sai Mama taji dadi, dan haka sai ta rufe maganar sasantawar da aka samu tsakanin Sadauki da Diyam dan tana son alhajin ya ji dadi a ransa ya dauka tamkar shi ya sasanta su din, dan haka ta ki shigar masa da maganar auren da niyyar sai bayan kwana biyu sai ta dawo ta sake shigar masa da maganar. Ta kuma yi masa alkawarin kiran Diyam ta gaya mata sakonsa. 


Sai dai tana mike wa sai ga Kawu Isa ya shigo dakin hannunsa rike da jariri. Ya wuce ta yaje chinyar Alhaji Babba ya ajiye masa yace "ga sakon Saghir nan. Nayi masa huduba da sunanka dan haka ina yi maka murna ka samu takwara" ya juya da sauri ya wuce Mama ba tare da ya kula mai take cewa ba ya fita. Ta juyo ta dawo gaban Alhaji tana kallon jaririn da take kwance kan cinyarsa yana ta jujjuya kai da alama abincinsa yake nema. Ko ba'a yi mata bayani ba ra fahimci cewa Suwaiba ce ta haihu kuma wannan shine dan gaba da fatihar data haifawa Saghir. Ta saka hannu ta shafi kan yaron tana kallon fuskarsa mai kama data Subay'a. Tace "Allah yayi maka albarka" Alhaji ya dago kansa daga kallon yaron shima yace "ameen. Ki kira min Hajiya Saratu a ciki". Ga dai jika nan namiji Alhaji da Hajiya sun samu amma kuma shege.


Kafin Mama ta baro gidan sai data yi ta zarya zuwa gidan Kawu Isa akan ayi hakuri a mayar da yaron nan hannun uwarsa amma Kawu Isa yace sam bai san wannan maganar ba "ba zata shayar dashi ba" ya fada ya kuma maimaita wa. Ko samun ganin Suwaiba Mama bata yi ba, daga baya ma ta tabbatar bata gidan dan haka ta hakura amma tace "yaron dai jikan mune gabaki daya, kuma shi bashi ne yayi laifi ba dan haka bai kamata a hukunta shi akan laifin dashi bai san ma sanda aka aikata shi ba. Rashin shayar dashi ba zai goge cewa Suwaiba ce ta haife shi ba".


Sai taje ta siyo baby formula da feeder ta dawo ta kawo wa Hajiya Babba. Ta tarar da ita ta goya dan jaririn da ya rare baki yana ta kwarara kuka. Ta mika mata tayi mata barka sannan ta koma tayi wa Alhaji sallama, sai yace "ki turo min Amina dan Allah" daga haka sukayi sallama.


Bata koma gida ba kuwa sai da ta je gurin Inna, ta fada mata duk yadda sukayi da Sadauki da kuma yadda suka yi da Alhaji da kuma abinda ya faru a gidan alhajin. Inna duk ta tayar da hankalinta nan take washegari ta dauki kudi ta shirya ita da Asma'u da Subay'a taje tayo siyayyar kayan babies sukaje gidan Alhaji Babba, ta kaiwa Hajiya Babba ta kuma yi mata barka ta dauki yaron da yasha madarar sa yana ta baccinsa tayi masa addu'a sannan taje gurin Alhaji. 


Bayan sun gaisa yace mata "Amina idan kun yarda ke da yayanki ina so za'a zo a raba gadon usuman" Inna ta kalle shi da mamaki tace "wanne irin rabon gado kuma Alhaji?" Yace "an raba ne? Ai har yau ba'a raba ba. Kuma taba kudin da nayi ne ya haddasa min duk masifun da suka same ni. Tun da na shigo kano na fara neman kudi nake samun sa'a da nasara a rayuwata ban taba cin karo asara ba sai dana bi son zuciyata na taba kudin gadon nan. Kuma har yau ban biya ba, wannan shi yasa duk abinda nake dashi bashi da albarka, duk harkar neman kudi bana tarar da komai a ciki sai asara. Wannan kuma a duniya ne kadai, idan har ban biya ba to azaba tana can tana jirana a lahira. Na sani sarai, ina sane da duk abinda nakeyi son zuciyata kawai nake bi shi yasa na kasa gyarawa amma yanzu alhamdulillah rayuwa ta bani wata sabuwar damar gyara kurakurai na guda biyu. Zan fitar da hakkin usuman da yake kaina sannan kuma zan gyara kuskure na na tarbiyyar Saghir akan wannan yaron da aka haifa masa".


Inna tace "mu ai Alhaji mun riga mun yafe maka rabon mu ni da yara da yake cikin abinda ka dauka, shima kuma Sadauki yace ya yafe kason mahaifiyarsa, sannan kuma ai kaima da sauran yan'uwa kuma da rabo a ciki sannan....." Yace "muna dashi, hardo yana dashi, hatta yaya ladi mahaifiyar Zainab tana dashi. Yanzu bayan mutuwar hardo matar daya aura kafin rasuwarsa tana dashi. Mutanen da suke da hakki suna da yawa, wannan yafiyar ba zata sauke min nauyin nan ba".


Tayi shiru tana lissafa maganar sa, sai yace "ina so azo ayi rabon gadon a bisa ka'ida. Zan bayar da complete kudin dana dauka, sai ayi wa gidan da kuke ciki kudi sannan a raba a bisa tsarin da addini ya tsara a bawa kowa rabonsa ko zan samu rayuwa ta dan sassauta min kafin in bar duniya kuma in samu sassauci a lahira" tayi tagumi tace "to a ina zaka samu kudin nan Alhaji?" Yayi murmushi yace "nan gidan da muke ciki shine kadai abinda ya rage min a duniya. Shi zan siyar. Kollere zan koma in cigaba da rikon sarautar da hardo ya mutu ya bari muka ki karba. Sauran abinda yayi min saura kuma sai in samu sana'ar yi a can wadda zata rike min iyalina a can din". 


Inna ta girgiza kai tace "ba zai kai ga haka bama Alhaji, insha Allah ba zai kai ga haka ba".


Wasa wasa abu ya tabbata. Inna ta kira Diyam da Sadauki ta gaya musu abinda duk ake ciki, farko Diyam ta nuna rashin yardarta amma sai inna ta gaya mata cewa hakan shine dai dai "shima marigayin wannan wani sauke nauyi ne akayi masa". Aka yiwa gidan Baffa kudi, a take Sadauki ya siya. Aka kuma yiwa gidan Alhaji Babba kudi aka siyar, ana siyarwa Diyam ta aiko da kudi tace a kama musu ko rent ne su zauna kafin komai ya zama settled. Sannan Alhaji Babba ya ware kudin garejin Baffa daya siyar aka hada da kudin gidan Baffa aka raba kudin cash, kowa aka danka masa nasa a hannunsa hatta amaryar da hardo yayi kafin rasuwarsa sai da aka fitar mata da nata a cikin kason Hardo aka aika mata dashi har Kollere. 


Babu yadda Alhaji Babba baiyi ba akan son komawa Kollere amma yaya da yan uwa suka saka shi a gaba akan lallai ba zai koma ba. Dole ya zauna a gidan da Diyam ta aiko da kudi aka kama masa haya a unguwar Jaeen, suka koma gabaki daya shida iyalinsa. A lokacin ne kuma Diyam daga can ta aiko da kudurinta na son yiwa kannen Saghir su hudu wadanda suka isa aure kayan daki. Sai Alhaji Babba yace "ku gaya mata tazo sai a hada auren tare da nata".


A bangaren Sadauki, yana ta son ya tunawa Mama da maganar da suka yi amma kunyar ta yakeji, sai yayi ta cewa Diyam wai ita ta kira Mama ta tuna mata, tayi dariya tace "wato nice marar kunya ko? To babu ruwana, tunda kaji tayi shiru tana da dalilinta".


Sorry for keeping you guys waiting. Biki things. Enjoy your week.

[3/18, 11:02 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Sixty Eight : Save the Date

Yace "eh nasan tana da dalilin ta shi yasa ni kuma na kasa zuwa in tuna mata. Am just scared Diyam, tsoro nake yi kar a sake hana min ke a karo na biyu. Bansan me zanyi ba wannan karon" tace "babu wanda zai hana mu juna Aliyu. In har kaga ba'ayi ba to kuwa tabbas Allah bai rubuta za'ayi ba. Waliyai na ne su amma basu kadai bane waliyai na in sunki zamu iya zuwa Kollere mu......" Yace "no, no Diyam. Ba su kadai ne waliyan ki ba amma sune shakikan Baffa, kamar yadda kika fada haka ne Baffa zaiji dadi idan muka sasanta tsakanin mu da su. Kuma ni ba zanzo in zama sanadiyyar rabuwarki da yanuwanki ba but am not going to give you up, not now not ever. Dan haka zamu jira in ta kai ga cewa ni zan kuma durkusawa Alhaji Babba zan durkusa din" sai ya dan yi dariya yace "the table have been turning so past yanzu kuma na dawo ni nake nema a gurinsa" ta taya shi dariyar sannan tace "in lokacin durkusawar yazo, call me sai mu durkusa tare ni da kai because we are in this together".


Washegari sai ga wayar Mama. Ta gayawa Diyam duk abinda sukayi da Alhaji Babba tace "na bashi wannan damar ne saboda naga yadda yayi nadamar abinda yayi, so nake ya nemi Sadauki da kansa ya gyara kuskuren da yayi da kansa. Yanzu yace yana so kizo gari dan yana son neman yafiyarki, sannan kuma yace kice da Sadauki ya turo, in yaso sai a hada dana su Murja ayi gabadaya" 


Diyam ta lumshe idonta tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa a zuciyarta wanda har sai daya saka hawaye ya taru a idon ta. Mama tace "kinyi shiru kuma, me zance masa?" Ta dan goge hawayen idonta tana jin zuciyarta fari kal kamar takarda, rabon data ji wannan feeling din tun Baffa yana da rai, tun tana carefree teenager, tun lokacin da Sadauki yake zuwa gurinta a school suyi ta bayyana wa junansu abinda yake zukatan su. 


Amma sai taji kunyar Mama tace "mun kusa fara exams yanzu Mama, ba zan iya tahowa gida ba amma muna yin hutu zan taho sai in samu alhajin, duk da dai ni na riga na yafe masa tuntuni" Mama tace "to Allah ya bada sa'a. Maganar Sadaukin fa?" Diyam tace "duk yadda akayi Mama" Mama tace "ki gaya masa ya tura gurin Alhaji Babba, sai asa rana tare daba su murjan. Yaushe kuke so a saka?" Diyam ta sake yin shiru sai da Mama ta maimaita sannan tace "duk sanda aka ce dai dai ne" Mama tace "in aka saka lokacin hutun ku ai yayi ko?" Diyam ta sake yin shiru tana murmushi amma a ranta tana lissafa kwana nawa ya rage ayi hutun.Mama tace "shikenan tunda ba zakiyi magana ba, shi bara in kira shi in tambayeshi" s


Suna yin sallama Diyam tayi saurin kiran Sadauki ta gaya masa yadda sukayi da Mama, yace "tare dana su Murja kika ce?" Tace "eh, haka tace min" ya girgiza kai yace "I don't like that. Nafi son ranar bikinki ya kasance all about you not you and someone else, nafi son in an ganki ace 'ga amaryar can' kar ace 'ga daya daga cikin amaren nan' nafi son ki samu cikakkiyar kulawa daga kowa ba wai ki samu divided attention ba. Dan haka zan gaya mata ayi nasu first, later in an huta sai ayi namu" 


Tun da ya fara magana take murmushi har sai daya gama sannan tace "I don't need attention din mutane, attention dinka nake so, in nayi kwalliya ban damu da a yaba ko ayi comparing dina da wasu ba as long as kai ka yaba as long as a gurinka babu wadda ta kai ni. Besides, ni ba biki zanyi ba, daurin aure kawai za'a hada da nasu, ni a gida zanyi zamana kawai sai wanda ya shigo aka gaisa kawai shikenan. Ban damu da having a big wedding ba as long as kaine angon that's all that matters, tunda nasan a gurinka zan samu more than abinda na samu a wancan auren" a can kasan makogwaron sa yace "more of what?" Tace "everything" yace "like?" Tace "caring" yace "and?" Tace "tunda nace everything ai ina nufin everything ko? Sai na lissafa maka?" Yayi dariya yace "so nake ki fada da bakin ki, yadda in lokacin yayi zan tuna miki cewa ke nema da kanki" ta bata rai tace "abinda kake nufi fa ni ba shi nake nufi ba, we are not talking about the same thing" yace "zaki sha kwana ko? To gaya min ni abinda nake nufi" tace "ni ban san me kake nufi ba fa" yace "to in baki sani ba ya akayi kika san ba abu daya muke nufi ni da ke ba?" Tayi rolling eyes dinta tace "good night Aliyu" yace "ashe tsoro na kike ji tunda zaki gudu, ki tsaya mana" tace "ba tsoro nake ji ba bacci nake ji, ina da school gobe" yace "hmmm okay, Allah ya tashe mu lafiya, but I will still demand to know that 'everything' da kika fada, ko ba gobe ba ko watarana I will get the words out of you".


Suna gama wayar Sadauki ya ajiye phone din yana kallonta, sai kuma yayi murmushi sannan ya lumshe idonsa ya kwantar da kansa a bayan kujerar office dinsa yana dan jujjuya wa a hankali. Sai kuma ya mike zaune sosai ya jawo system dinsa yana duba calendar, yasan ranar dasu Diyam zasu fara exams ya kuma san ranar da zasu gama sannan yasan ranar da zasu koma  school, sai ya duba dates din da suke tsakanin hutunsu da komawar su school yana neman weekend mai perfect date for their wedding, sai idonsa ya sauka akan date din, his birthday. Ya dafe kansa yana fadada murmushin sa. He is going to have a perfect birthday gift for his 30th birthday.


Mama ta kira shi kamar yadda tace zatayi, ta kuma maimaita masa abinda already Diyam ta gaya masa sai ta tambaye shi shima akan date, sai ya maimaita mata abinda Diyam tace mata "duk sanda aka saka dai-dai ne Mama" ta tabe baki tace "ai shikenan, idan manyan sunzo ayi magana dasu".


Washegari ya hau jirgi daga kano zuwa Maiduguri ya samu Alhaji Babagana wanda yake kani ne a gurin Papa kuma shine dai wanda shekaru goma da suka wuce yazo ya nema masa auren Diyam aka hana shi. Yanzu ma shi zai sake dawowa tare da Alhaji Bukar su karasa abinda suka fara. Nan take shi kuma ya kira Papa ya gaya masa sannan ya bashi izinin ya dauki sauran yan'uwa suje su hadu da Alhaji Bukar suyi duk abinda ya dace. Sai da suka gama wayar sannan Sadauki ya gaya masa date din da ya keso a saka. Sai shi kuma ya tambaye shi "kana ganin ba za'a samu matsala ba? Kar azo ayi irin ta wancan karon" Sadauki yace "babu matsala in sha Allah, tunda wannan karon ai sune da kansu suka nemi azo din".


Daga Maiduguri sai yayi branching a Yobe yaje damagun gurin yaya ladi wadda take zaune a gidan cousin dinta da Sadauki ya gyara musu shi tas ya zuba musu kayayyakin more rayuwa kuma ya daukar musu yan aikin da zasu ke kula dasu. Bayan sun gaisa ta gama loda masa tuwo da fura sai ya sanar mata da duk abinda ake ciki, yana maganar yana murmushi. Sai ta rike baki tace "Diyam din dai Aliyu?" Ya dago kai yana kallon ta yace "Diyam din dai. Ko kina kishi ne?" Ta tabe baki tace "ni dai daka hakura da Diyam din nan da nafi jin dadi, kazo ga yammata nan birjik ka zaba ka darje in ma hudu kake so a tsakanin yau da gobe sai a samo maka su amma kai ka nace sai yarinyar da yan'uwanta suka wulakanta ka, suka wulakanta mahaifiyar ka, suka wulakanta ni kakarka?" Ya daga kafada yace "ita nake so, ita ma kuma tana sona kuma in anyi auren da ita zan zauna bada yan'uwanta ba" Hajiya Dije, cousin din Yaya Ladi tace "amma duk da haka Aliyu, ko bayan anyi auren ne ya kamata ka samu budurwa ka kara da ita" sai ya mike tsaye yana daukan hularsa a hannu fuskarsa da murmushi yace "kar ku damu, bayan anyi auren da sayi daya zan dawo nan sai in aure ku duk ku biyun a rana daya" yaya ladi ta tabe baki dan tasan shirishitar da maganar yake yi, tace "to ai shikenan, uwarka ma haka nayi ta fama har sai dana hakura" ya durkusa a gabanta yace "kisa mana albarka kawai ke dai. Kiyi mana fatan alheri" ta dafa kansa tace "Allah ya sanya alkhairi a ciki, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma kade duk wata fitina da zata taso sannan ya baku zuri'a mai albarka" yayi kyakykyawan murmushi yace "yanzu kika yi magana. Karki manta, ke ce uwargida ran gida a gurina, ita kuma amarya ta sannan kuma zuciyata".


A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri, aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da, Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa ba shida mahaifiyar sa?


Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa ya gyara masa yace "dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da damar" Alhaji Babba yace "mun bawa Aliyu auren Halima. Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana" Alhaji Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a gaban Alhaji Babba yace "a shirye muka zo. Kuma munzo da ranar mu amincewar ku kawai muke nema" sai ya fadi ranar da Sadauki ya gaya masa, yace "lokacin yarinyar tana hutu" babu musu kowa ya amince da hakan, sannan suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar tsokana dan mayar da abin wasa.


Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama jakar da aka bashi yace "ga abinda suka kawo" Mama ta bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace "wannan kudin sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi ba" Kawu Isa yace "nima dai naso ince haka, amma sai naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru" Inna tace "ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan sun mika masa ne saboda shine Babba" Abban Rumaisa ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace "tunda an riga an karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta saka musu ita mu kuma tayi musu addu'a shikenan". Sai Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi sannan ya tafi. 


Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message 


"save the date. 25th August"

[3/20, 10:04 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: DIYAM

By

Maman Maama

Episode Sixty Nine: Mrs Abatcha

Assalamu alaikum

Naga votes dinku, kuma kamar yadda nayi tsammani kusan 99% sun goyi bayan a fito da Saghir. Inda aka samu rabuwar kai shine akan lokacin da za'a fito dashi, kafin biki ko bayan biki. I followed the majority kamar yadda nayi alkawari amma na rubuta in such a way that suma minority din zasu samu satisfaction.

Thank you.

We are almost done insha Allah.

Ta lumshe idonta tare da jingina kanta da jikin kujerar da take zaune akai tana murmushi mai sauti wanda yafi kama da dariya. Murjanatu da take zaune kusa da ita tana cin abinci ta dakata da abinda takeyi tana kallon Diyam sai ta bude ido tace "what? Menene ya faru kike dariya ke kadai?" Diyam ta daina dariyar da take yi amma bata ce komai ba sai Murjanatu ta warce wayar daga hannunta ta karanta message din nan take ta mike tana tsalle tana kiran Judith, Judith tana fitowa tayi mata bayanin cewa auren Diyam za'ayi sai itama ta kama murna suna rawa a tsakiyar palon, Diyam tana zaune tana kallon su a ranta tana jin kamar ta tashi suyi rawar tare amma sai ta hana kanta.

Sai da suka gama tsallen murnar su sannan Murjanatu ta zauna tana haki ta jawo phone dinta, Diyam ta bude ido tace "hey, me zakiyi?" Murjanatu tace "su Adama zan gaya wa" Diyam tace "ai za'a gaya musu a can, ki barsu kawai saji a can" Murjanatu tace "yanzu su Adaman ma kunyarsu kike ji? To Papa zan gayawa ma, in ce masa gaki nan kin saka waya a gaba kina ta dariya kin kasa rufe baki kina murna zaki auri dansa" nan da nan Diyam ta mike ta murde hannun Murjanatu ta karbe wayarta ta tafi daki tana cewa "nayi seizing phone dinki, bazan baki ba sai anyi hutu".

Tana shiga dakin Murjanatu ta dauki tata phone din ta kira Sa'adatu wadda a lokacin suna tare da Falmata sai suka kira Adama da taje school a lokacin suka hada conference call sannan Murjanatu ta basu labarin abinda yake faruwa. Duk sunyi murna sosai musamman da yake wannan shine biki na farko da za'ayi a gidan su. Sa'adatu tace "oh su yaya Aliyu za'ayi aure, I wonder ta yaya suke magana da Diyam din da wannan turbunanniyar fuskar tasa" Murjanatu tayi dariya tace "wallahi in kunga dariyar da yakeyi mata ko, zaku dauka chanja shi akayi gaba ki dayan sa" sun jima suna hirarrakin su sannan suka lissafa kwanakin da ya rage kafin bikin sai kuma suka fara tsare-tsaren events din da zasu shirya. Sai da suka gama Murjanatu tace "Allah yasa ya yarda, zamu iya gama shirya komai yace shi ba za'a yi wa matarsa kwalliya a shiga da ita cikin mutane ba, kishi ne dashi kamar me".

Sai da suka gama Murjanatu ta dauki wayar ta kai wa Diyam har daki ta mika mata tace "thank you for letting me use your phone" sai ta ajiye ta fita da sauri tana dariya. Diyam ta dauki phone din ta duba numbers din da Murjanatu ta kira, sai tayi murmushi tana mamakin zumunci irin na wadannan mutanen, sam basa nunawa Aliyu yan ubanci ko dan akwai wayewa sosai a tare da su?

Daga gida ma Mama ta kira Diyam ta yi mata bayanin duk halin da ake ciki, sai kuma ta umarce ta data kira Rumaisa suyi shirye shiryen abinda zasu yi kafin tazo gidan.

Sanda sukayi waya da Sadauki kuma sai yace mata "guess what? Na sayi fili zan yi gini" tayi dariya tana rike baki yace "au, dariya ma na baki ko?" Tace "I tot zaka sayi gida ne kawai, ko kuma ma ka riga ka siya" yace "hmmm, nima na dauka zan siya gidan ne, but then an opportunity presents itself to me, na saka a nemo min gida sai dillalin ya gaya min akwai wani fili ma in ina so, sai na bincika na gano ashe fili na ne, filin mune Diyam da Baffa ya siya mana zamu gina gidan mu, all these years ba'a gina shiba har sai daya dawo hannun mu. And now I hired wani construction company da aka bani labarin sa a Abuja 'Moon Construction Company' sunce zasu gama komai within a month. Ina ganin ai yayi ko? Tunda muna da kusan watanni biyu nan gaba"

Diyam taji dadi a ranta tana jinjina hikima irin ta ubangiji. Tace "yayi sosai ma" yace "zasu turo min samples na building plans dinsu, sai mu zaba ni dake sannan sai su fara" sun jima suna hirarrakin su sannan suka yi sallama suka ajiye wayar. Sai ya cigaba da zama hannunsa rike da phone din yana kallon hotonsu shi da ita da yake kan screen din wayar, a Oxford suka dauka sanda yaje, selfie ne yayi musu suna tsaye a gaban motarta shi yana murmushi ita kuma ta turo baki tana hararar sa. Yayi murmushi saboda ya manta me yayi mata a lokacin take hararar sa kuma yasan itama kanta in da zai tambayeta ta manta. Ya saka babban dan yatsansa a hankali ya shafa fuskarta a jikin hoton sai kuma yayi sliding din hoton sama ya nemo number din one of his lawyers ya kira "barrister akwai maganar da nake so zamu yi Please, lets meet in my office in an jima. Okay, thank you".

Diyam har ta fara sabawa da rashin Bassam a school, duk da dai kullum in ta kalli empty kujerar kusa da ita sai taji babu dadi. Sai a lokacin tayi nadamar rashin exchange din numbers da basu yi ba at least da yanzu ta kira shi tasan halin da yake ciki. And then one day, suna gab da fara exams din su sai gashi ya shigo ana tsakiyar lecture. Yayi ignoring lecturer din da yake masa kallon yazo late yana distracting din class sai ya wuce empty seat din kusa da ita ya zauna ya juyo yayi mata murmushi sannan suka mayar da hankalinsu kan lecture din da ake yi. Sai da aka gama lecturer din ya fita sannan Diyam tace masa "welcome back prince Sadiq" ya juyo yana kallon ta da mamaki dan shi dai ba zai iya tuna sanda ya gaya mata daga inda yake ba, yace "Prince? Yaushe na gaya miki haka?" Tace "ba ka gaya min ba, Aliyu told me" yace "shi din ya akayi ya sani?" Tace "okay, ba direct ya gaya min ba, kace ka taba ganinsa a gurin daurin auren yayanka a abuja last year, shi kuma yace daurin auren da yaje abuja last year na jikan sarkin Abuja ne, so, in yayanka ya kasance jikan sarki to kuwa kaima jikan sarkin ne, ko ba haka ne ba?" Ya dauke kai yace "an baki A1 a fannin bincike" tayi dariya tace "tell me everything. Dame da me ya faru? I hope komai ya warware yanzu and you are back to your old self again"

Yace "well, bayan mun rabu naje gurin aunty Hafsat but she refused to see me. Nayi iyakacin kokari na amma abin yaci tura but sai na ci sa'a uncle Zayed ya dawo, dama yayi tafiya ne lokacin da muka samu sabani dan haka bai ma san abinda ya faru ba, I explained everything to him kuma na dauki laifina sai ya saka ni a gaba muka tafi Nigeria tare" ya danyi dariya yace "ba karamin taimako na Allah yayi ba da muka je tare dashi, da maybe in Daddy ya fara jibgata sai na kwanta a asibiti" Diyam tayi dariya tace "anya kuwa bakayi girma da duka ba?" Yace "not to my Daddy, ba ruwansa da girma na wallahi dukan tsiya zaiyi min Mami kuma ba zata hana shi ba. But Allah ya taimake ni Uncle Zayed ya shiga maganar, and my grandparents too, sai komai yazo da sauki musamman tunda na karbi laifina kuma na bada hakuri. And now Ya Ameen ne ya dawo dani tare da wife dinsa Humairah itama zata fara karatu. She is an artist, yana so ne ta samu qualifications din kawai" suka yi shiru Diyam tana tunanin ina ma dai itama nata family din zasu zama irin haka in 蓷a yayi wa wani family member laifi sai iyayensa su danne son da suke yi masa su hukunta shi har ya zamanto su ake bawa hakuri ma.

Bassam ya cigaba da cewa "Mommy, my grandma, tace wai in zabi budurwa a cikin cousins dina in place of khausar, but nace mata ta barsu duk na gode, saboda duk wadda na zaba din za'a iya forcing dinta dan a faranta min and I don't want to end up like Saghir dinki, in zauna da matar da bata so na, so I decided zan jira, rayuwar ai yanzu ta fara ko? Zan jira har Allah ya hada ni soulmate dina da zata soni kamar yadda kike son Aliyun ki" ya karashe da sigar tsokana. Ita kuma tayi murmushi tace "ka lallaba ni in baka kanwata" yace "wacce kanwar?" tace "Murjanatu" ya daga hannu yace "no, no, no. Thank you so much but no. Wannan yarinyar samarinta sun kai cikin container".

Suna tare har aka tashi. A lokacin ne ta bashi labarin itama cigaban da aka samu a nata bangaren, ya taya ta murna sosai da sosai sannan shima ya tambaye ta game da shirye-shiryen da take yi. Ta daga kafada tace "ba fa abinda zanyi ni, ina naga friends din ma da zan shiryawa event. Nasan dai Inna zata yi taron yan uwa da abokan arziki and that will be all" Bassam yayi shiru yana kallon ta sannan yace "kinsan wani abu? Matar yayana dana gaya miki mun taho tare zata fara school itama, zan hada ki da ita ina tunanin you two will like each other. Zaku iya zama friends" Diyam tace "no, ni bana son friendship da yayan masu kudi" yayi murmushi yace "babanta ba mai kudi bane ba, mai rufin asiri ne. Kuma bafulatana ce irin ki" tace "in babanta ba mai kudi bane ba ai mijinta mai kudi ne" Bassam yace "that makes the two of you" sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, the mare thought of Sadauki as her husband yana saka ta murmusawa.

Suna rabuwa da Bassam ta kira Sadauki ta bashi labarin dawowar Bassam. Wannan shine dai dai saboda boye boye shi yake kawo zargi in a relationship.

Kamar wasa sai ga Bassam ya kawo wa Diyam Humairah har gida. Sai Diyam taga cewa ashe duk abinda take tunani a game da Humairah ba haka bane ba, na farko she is young, dan Diyam tana ganinta ta san cewa ta girme ta. Ko kuma dan tana da baby face ne? Da suka zauna suka fara hira sai ta fahimci tana da saukin kai sosai da kuma addini. Ta karbi babyn da yake hannun Humairah tana yaba kyawunsa tace "masha Allah, ya sunansa?" Humairah tace "Abubakar, Ayman ake ce masa" Diyam tayi murmushi tana tuna mitar da Bassam ya taba yi akan cycling suna daya within a family. Amma ai honor ne ko? Kowa yana burin ya haihu yayi wa iyayensa takwara.

Nan da nan Diyam ta dauko zani ta goya Ayman, tana tuna sanda Subay'a take jaririya. Wannan yasa Humairah ta kara sakin jikinta saboda hausawa sunce mai 蓷a wawa ne. Sun jima suna hira, suka yi hirar similarities dinsu sannan suka yi hirar differences dinsu, a take kowacce a cikin su ta fahimci cewa tayi kawa.

Tare suka shirya abinci sannan suka zauna suka ci a plate daya, suna cikin ci Murjanatu ta shigo tayi joining dinsu itama. A nan ne take bawa Humairah labarin cewa an kusa auren Diyam da yayanta, sai kuma hirar ta koma kan hidindimun aure da kuma zamantakewa ta aure har sai da Murjanatu ta mike tace "wannan hirar tafi karfina kar kuje ku kona ni tun kafin in tafasa".

Komai ya tafi normal har Diyam ta kammala exams dinta, a cikin lokacin sau biyu Sadauki yana zuwa Oxford Diyam tana koro shi Nigeria saboda tace karatu yake hanata yi in dai yana can din. A dole ya hakura ya dawo Nigeria amma da sharadin cewa kullum zasuyi video call sau biyu.

Ranar da zata dawo Nigeria Sadauki ne yace zaije ya dauko ta, amma sai ya gaya wa Asma'u ta shirya Subay'a su tafi tare. Subay'a kam murna take tayi ta kasa rufe bakinta saboda farin cikin zata ga mommyn ta, dan haka bata damu bama da wate zasu tafi tare dashi. Shi ya fito da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga sannan ya zagaya ya zauna yana tsokanar ta "Subis yanzu duk wannan kwalliyar ta mommy ce? Dama ashe kin iya kwalliya haka shine ni ba kya yi min sai mommy ko?" Ta sunkuyar da kanta tace "bani nayi ba ai, aunty Asma'u ce tayi min" yace "to gaya min, me kika tanadarwa mommy?" Ta bude hannu tace "babu komai, ai ni bani da kudi" yace "to me kike so ki siya mata" tayi shiru sannan tace "sweets" yayi murmushi "wato kin san ta da shan sweet ko?" Sai tayi shiru bata ce komai ba. Yace "kina so in kai ki ki siyo mata?" Ta gyada kai kawai, sai yace "a'a, in dai kina so to sai kinyi magana da baki ba da kai ba. In kuma baki yi ba bazan siya miki ba" tace "ina so" yace "to sai kin fadi sunana tukunna. Ya sunana" a hankali tace "uncle Aliyu" yayi murmushi ya shafa kanta yace "good girl".

Suka biya ta mall suka ciko leda da kayan zaki sannan suka karasa airport. A airport din sai yaga duk walwalar data fara dazu ta ragu, tayi shiru kamar mai shirin yin kuka, sai ya durkusa a gabanta yace "menene kuma? Ba kya murnar ganin Mommy? Ko in kira ta a waya ince mata ta koma ba kya son zuwanta?" Sai tayi sauri ta girgiza kai, yace "to me kike so?" Tace "rannan da muka zo nan da mommy, sai police suka zo suka tafi da Daddy na kuma har yanzu basu dawo min dashi ba" sai hawaye suka zubo daga idonta ta dago tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta sake cewa "mommy tace zaka fito min dashi ko?" Ya saka hannu ya share mata hawayen fuskarta yace "daddyn ki zai fito little girl. I promise you" sai kuma yayi murmushi yace "amma sai kinyi min wani alkawari, promise me daga yau mun zama friends" ya fada yana mika mata dan karamin finger dinsa, ta goge hawayen fuskarta ta saka nata karamin finger din a ciki sannan ta gyada kai tana murmushi. Ya daga ta masa ya dora ta akan kafadarsa yace "now, let's wait for your mommy".

Diyam tana fitowa ta hango su, and seeing them smiling together ya saka taji wani irin joy a zuciyarta marar misaltuwa, tana kallonsa ya sauke Subay'a kasa ita kuma ta taho da gudu gurinta sai ta durkusa ta bude mata hannayenta ta shige zuwa kirjinta ta rungume ta taba ajjiyar zuciyar dadi, ta dago fuskarta tayi kissing goshinta tace "I miss you so much little girl" Subay'a tace "I miss you too mommy". Ya karaso ya tsaya a kansu yace "na gane matsayi na" ta mike tana kokarin daukan Subay'a yace "ke! Careful kar kisa a daga min biki" ta harare shi tace "wato bikinka ne a gaban ka ko?" Yace "a yanzu, yes" Subay'a tace "uncle bikinka za'ayi?" Ta fara tsalle, "zanje gidan ka inga amaryarka" ya daga ta sama yace "karki damu, kece yar zaman daki".

Daga airport basu yi cikin gari ba sai suka dauki wata hanya daban. Diyam tace "ina zamu je?" Bai kalleta ba yace "kawunan ku zanje in siyar" tayi dariya "ni kaina yafi karfin babarbare ya siyar" ya kalleta yace "siya na nawa kuma? Sai ya kalli Subay'a ta mirror yace "kinci sa'a we have company" ta murguda masa baki, yace "ki cigaba, ba dai rashin kunya ba, akwai ranar kin dillanci".

Titin bypass suka hau sannan suka shiga unguwa uku, suka sauka daga babban titi suka shiga wani layi sannan yayi packing a gaban wani gida yace "Mrs Abatcha, welcome to your home" ta bude vaki tana kallon gidan sa yake gabanta sannan tace "wow" yayi murmushi yace "shall we?" Kafin ta bada amsa Subay'a ta bude motar ta fita da sauri tana cewa "uncle gidanka ne wannan?" Ya fito yana cewa "gidan mu ne princess, ni da mommyn ki da ke" sai ta kwasa a guje ta kama gate din tana cewa "Mommy ki kira inna kice ta aiko min da kayana" Diyam da Sadauki suka yi dariya a tare.

Malam iliyasu ya fito yana bude musu gate. Diyam ta kalleshi sannan ta kalli Sadauki shi kuma ya daga mata kafada yana murmushi. Sai ta juya tana amsa gaisuwar da malam iliyasu yake yi mata amma bata ce masa komai ba sannan suka taka da kafa suka shiga gidan. Tsayawa bayyana tsari da kyawun gidan zai tsawaita labarin mu amma dai tabbas Moon construction company sun kure adakar su a wannan gidan. Daki daki suka bi a nutse Sadauki yana yi mata bayanin komai kuma tana neman gyaranta in akwai amma ita bata jin akwai wani gyara da za'ayi a wannan tsararren gidan. Bayan sun gama sun fito ne suka zagaya baya gurin wani dan karamin gurin shakatawa mai lullube da grass carpet da kuma madaidaicin swimming pool mai dan karen kyau wanda ganinsa kawai ya isa ya saka mutum yaji yana son yin wanka. Suka zauna a wasu daga kuherun gurin ita kuma Subay'a ta bazama tana zagaya gurin a kuje. Diyam tace "amma gidan nan yayi kyau, irin sosai din nan fa" yayi murmushi yace "am glad you like it. It will be our Kano home insha Allah. Zamu yi wani a Maiduguri saboda muke sauka in munje, and for Oxford we have to get a bigger apartment dan wanda kuke ciki yanzu yayi mana kadan".

Sai ta dauko wasu takardu ya mika mata sannan ya gyara zama yana kallonta. Ta karanta ta kuma karantawa, ta fahimci cewa wata yarjejeniya ce signed by Aliyu Umar Abatcha cewa ya yafewa Saghir Muhammad Kollere kudaden sa daya satar masa. Akwai saka hannun lawyers dinsa, akwai saka hannun alkalin da yayi waccan shari'ar sannan akwai saka hannun Saghir. A kasan inda Saghir ya saka hannun ya rubuta "thank you".

Ta dago da sauri tana kallon Sadauki, sai kuma ta kasa magana. Yaushe Sadauki yayi wannan shawarar? Shin hakan yana nufin Saghir ya fito ko kuwa bai fito ba?

Jin bata ce komai ba yasa yace "lokacin da Saghir ya fada min wannan maganar a kanki ba rufe shi nayi niyyar yi ba, zuciyata abinda take gaya min shine in kama shi inyi ta dukansa har sai ya daina numfashi sannan in kaishi daji in ajiye shi dabbobi su cinye shi da rai" ya danyi dariya ganin kallon da take yi masa yace "babu irin imagination din da bana yi that's why I decided to set a trap for him and luck him up, a hakan zaiyi paying for what he did and he will be out of my reach yadda bazan yi masa lahanin da duk zamuyi dana sani ba. I didn't know his friend will set him up for drugs. Niyyata shine a lokacin da naji zuciyata tayi sauki a kansa sai in yafe masa ya fito but as fate have it ba wannan ne kadai case dinsa ba, so, har yanzu yana can kamar yadda alkali ya fada har sai an samu nasarar kama abokin nasa kuma sai abokin ya karbi laifin shi ya bashi ajjiyar drugs din" Diyam ta gyada kanta tana kallon Subay'a da take wasa a can nesa dasu sannan take murya can kasa "thank you. Mun gode Allah ya kara arziki" baice komai ba shima yana kallon Subay'a sai zuwa can yace "zanyi kokarin ganin ya fito, dan Subay'a taji dadi. But bazan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata daga farko, ruwansa ne yayi hankali ruwansa ne kuma yayi akasin hakan. Na riga nayi magana da Ahmad, duk da dai kamar baya goyon bayan fito da Saghir din but yace zai taimaka min, matsalar shine su iyayen Kabir din sunki vada goyon baya su fadi inda dan nasu yake" ya juyo yana kallonta yace "naso ya fito kafin auren mu, naso yazo ayi dashi dan anan ne zan tabbatar da nadamarsa ko akasin hakan. But it is beyond me dan haka sai bayan

[3/22, 10:25 PM] +234 703 589 5826: 鉂� DIYAM 鉂�


By


Maman Maama


Episodes Seventy & Seventy One : The Wedding


The chance of you dying with COVID-19 is 1% while the chance of you dying anywhere anytime by any means by Allah's wish is 100%. Wanne ya kamata muji tsoro? Corona virus ko Allah? Then why the panic bayan mun yadda da kaddara munsan komai rubutacce ne? 


Mafita kawai shine mu koma ga Allah mu rungumi Alqur'ani da Azkar, mu  yawaita istigfari sannan kuma mu bi dokokin da ma'aikatan lafiya suka kafa.


Idan Allah ya riga ya rubuta cewa Corona virus itace sanadin mu muna rokon Allah ya karbi shahadar mu (mutuwar annoba shahada ce), idan kuma ba ita bace ba Allah ya bamu rayuwa mai albarka ya dawwamar damu cikin imani Ameen. Allah kuma ya kyautata karshen mu.


Diyam...............


Diyam taji dadi sosai a ranta. Tabbas ko da Sadauki bai fito da Saghir ba to kuwa yafe masa ma da yayi ya nuna cewa his stone hard heart is now soft. Yanzu ya yi part dinsa ya rage nasa kuma ya taimaka wa Saghir ko yaki duk ganin damarsa ne, taimakon yana da kyau sosai musamman saboda xuri'ar da aka riga aka hada, amma kuma ba wajibi bane ba. Dan haka ba zata sake yi masa magana ko kokarin tursasa shi zuwa haka ba dan in yayi din ya zamanto niyyarsa ta kyautata.


Tayi masa kyakykyawan murmushi tace "hakan ma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci" yace "Ameen, Mrs Abatcha" ta harare shi, "bana so" yace "okay, madam kike so?" Ta mike tsaye kamar zata yi kuka "bana so wallahi" ya mike shima yana mata dariya "gaya min to, me yasa ba kya so?" Tace "sai in ji na zama kamar wata katuwar 茩edara, wai Madam" yayi dariya sosai yana matsowa kusa da ita yace "to me kike so ince miki?" Ta juya ido tace "Diyam" yace "Sadiyam" tayi masa gwalo tace "sholoki" sai ta bar gurin da sauri ta tafi gurin Subay'a tana waigensa. Ya daga murya yace "zan kama ki ne ai, not now but on the 25th" bata waigo ta kalleshi ba but she blushed. 


Wayarsa tayi kara ya duba sannan ya taho gurinsu yana cewa "time off, Inna ta gaji da jira tasa yar asama ta kira mu" Diyam ta mike straight tana cewa "Allah sarki inna ta, nima nayi missing dinta sosai" ta mika masa takardun hannunta suka tafi Subay'a tana ta fushi wai ita ta dauka sunzo kenan.


A kofar gida ya ajiye su yace bazai shiga ba. Subay'a ta fita da gudu tana ta dokin bawa Asma'u labarin sabon gidan da suka je. Diyam ta yi masa sallama zata fita kenan sai ya miko mata wani card ta karba tana dubawa taga credit card ne sai yace "ki dauki kudin da zaki bukata a ciki, ki kuma dauki na su Murja da kika yiwa alkawari" kafin tayi masa godiya sai yace "birth year din ki shine pin din" ta gyada kai tana murmushi, ta sake bude baki zata yi godiya yace "bana son ji. Ko ki fita ko kuma in tafi dake kuma bazan dawo dake ba sai dai a biyo ki da kayan ki".


Bata san tayi missing inna har haka ba sai da ta ganta tukunna, ta tafi da sauri ta rungume ta tana dariya, itama innar dariyar take yi amma sai ta ture ta tana cewa "kar ki karya ni" Asma'u ma ta kankame ta tana cewa "nayi missing dinki, sosai Adda ta" Diyam ta kalleta tace "oh, Asma'u kin kara girma fa. Inna wannan ai itama kamata yayi a hada bikinta da nasu Murja" Asma'u ta fara buga kafa tana cewa "shikenan zaki kunto min ruwa, dama inna kiris take jira ta dawo kaina" ta karashe maganar tana tafiya daki. Inna ta bita da kallo tana cewa "yayanki ne ya daure miki gindi ai, daga ke har shi kun tsaya kuna ruwan ido amma ace yarinya kamar ki har yanzu bata da saurayi?" Diyam dai tana tayi musu dariya saboda ta fahimci wanne yayan ake nufi, shi har yanzu kallon Asma'u yake kamar wata jaririya.


Diyam ta lura da chanji a gidan su, an bude part din Ummah an kwashe kayan ciki sannan an gyara shi amma ba'a zuba komai a ciki ba. Ta shiga daki tayi wanka ta shirya tayi sallah sannan ta dawo palo suka zauna cin abinci da Inna, Asma'u da Subay'a da take ta zuba mata hira tana kokarin bata labarin duk abinda akayi a gidan sanda bata nan. Sai Diyam taji tamkar gidan yafi ko ina dadin zama.


Bayan ta kwana biyu ta huta sai shirya da niyyar zagaya gidajen yan uwa ta gaishe su. Inna tace "sai kiyi musu sallama kuma dan ba lallai ne ki sake samun zuwa gurin su ba". Tare da Asma'u suka fita, gidan Alhaji Babba suka fara zuwa, wannan shine zuwan Diyam gidan na farko kuma taji dadin yadda taga gidan, ba kamar dai nasu nada ba amma kuma basa cikin kuntata. Babban abinda ya kara mata jin dadi shine ganin Alhaji Babba ya chanja sosai ya samu nutsuwa fuskarsa ta saki ta rage nuna damuwa. At last ya daina blaming makiya da sauran al'umma for his misfortune. Da fara'a sosai ya amsa gaisuwar tata har da tsokanar ta da cewa "munji ki shiru har ina tunanin ko sai dai kawai mu daura auren anan in yaso angon ya biki can?" Ta rufe fuskarta tana jin kunyarsa. Sai kuma yayi mata godiyar kudin haya data biya masa sannan ya dora da bayanin neman yafiya a bisa abubuwan rashin adalcin da yayi mata. Ta katse shi da sauri "Alhaji ni na yafe ai, tuntuni na yafe muku tun ma kafin mu rabu da Saghir. Komai ya wuce sai fatan Allah ya kara gyara mana zumuncin mu" yace "ameen" ya dora da "ina son kuma ki sake yi min godiya gurin yaron nan Aliyu. Satin daya wuce naje na gano Saghir kuma ya gaya min abinda yayi masa, ya gaya min ya yafe masa kudaden daya daukar masa" ya fada yana dauke hawaye da babban yatsan sa. "Kudade masu yawa amma yace ya bar masa su. Kuma yace min ya hada shi da lauyoyinsa zasu taimaka masa akan maganar kwayoyin nan. Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yaji kan mahaifiyarsa, matar da har ta mutu Allah bai bamu ikon neman yafiyarta ba".


Ta shiga dakin Hajiya ta dauki Muhammad, kyakykyawan yaro har ya warware yana ta shan madarar sa. Sai kuma ta shiga dakin Hajiya yalwati inda acan ne tafi dadewa suna ta hira da Murja da sauran yammatan, suna ta competition gurin farantawa Diyam. 


A gidan Kawu Isa shima ya karbe ta sosai shi da iyalinsa. Sun jima suna hira yana tayi mata nasiha a game da aure, sai taga kamar wani chance ne ta samu na kokarin gyara tsakanin su da Alhaji Babba. Tace "Kawu, mu kuwa zamu ji dadi idan komai ya wuce tsakanin ka da Alhaji, kune iyayen mu, ta yaya zamuyi zumunci idan ku ba kwa yi?" Sai ya girgiza kansa yace "uwata shi zumunci yi min ne inyi maka, shi Alhaji Babba son kansa da son dansa ne ya jawo igiyar zumuncin sa da mutane duk ta gutsire. Ni fa wai kyautata wa ce na yiwa yaron nan na dauki yarinyar nan nace na bashi ita a daura musu aure saboda in gyara zumuncin da nayi tunanin kamar ya samu baraka, amma kinga sakayyar da ya saka min dashi. Dana je gurin uban na gaya masa ga abinda dansa yayi maimakon ya nuna alhinin sa kuma ya kira yaron nan ya nuna masa laifinsa sai ya shafawa idonsa toka yace shi ba dansa ne yayi ba, ko tambayar yaron ma fa baiyi ba. Yanzu gashi nan ya ga sakayya ai. Ni kuma gashi an barni da yarinya, ni ina ganin na kaita Kollere ta haihu a can ina tunanin kamar na rufe maganar ashe duk jama'a kowa ya sani. Jiya jiyan nan na fito daga masallacin unguwa naji ana maganar. Yanzu waye zai aureta da wannan tambarin? Menene makomar rayuwarta dana zuri'ar da zasu fito daga gareta?" Diyam tayi shiru tana tunani sai tace "Yanzu Kawu zaka hakura idan Saghir ya fito ya auri Suwaiba? Suka bude sabuwar rayuwa suka kuma rike dansu? Zaka yafe masa ka dawo da zumuncin ka da Alhaji?" Yayi shiru yana dan jujjuya kafa sai yace "yaushe Saghir din zai fito?" Diyam tace "very soon, insha Allah" sai yace "Allah ya fito dashi lafiya, abinda zasu yi shida mahaifinsa idan ya fito din shine zai zama tubalin cigaban alaka a tsakanin mu".


A cikin gidan sai Diyam taga bata ji dadin ganin Suwaiba ba duk ta rame, duk da cewa ita mai kiba ce amma yanzu duk ta sirance, farin ma ya ragu amma sai Diyam ta danganta hakan da haihuwar da tayi. Sai da Diyam tazo tafiya sannan Suwaiba ta biyo ta da niyyar rakata sai tace "Diyam kinga Jawad a gidan Alhaji?" Diyam ta gyada kai tana kallon ta, sai tayi murmushi kawai, anan Diyam ta fahimci problem din Suwaiba, kewar jaririnta take yi, sai tace "Diyam naga abban mu ya sakar miki fuska, dan Allah ko zakiyi masa magana ya karbo min Jawad" Diyam tayi shiru bata ce mata komai ba saboda ita dai ba zata iya wannan rashin kunyar ba. Sai dai kuma ta tausayawa Suwaiba saboda tasan zafin rabuwa da 蓷a musamman ma wannan da yake dan jaririn da ko nono ba'a barta ta bashi ba. But hausawa sunce idan bera da sata to kuwa daddawa ma tabbas da warinta. Tabbas Saghir yayi laifi amma kuma itama Suwaiba da akwai nata laifin da har ta bari dadin bakinsa da kyawun fuskarsa suka rude ta ta bude masa kafafuwanta yayi mata ciki. Abinda ta shuka ne itama take girba.


Sai Diyam tayi tunani akan lalacewar zumuncin zamani. Babban dalili a fahimtarta shine son kan mu da muke dashi da kuma nuna son yayan mu a fili. Yes, an sani kowa yana son dansa amma hausawa sunce kaso naka ne duniya ta kishi ka kuma ki naka duniya ta so shi. Duba misalin uwa in ta kama danta tana duka idan yayi laifi, sai kuga mutane sun tafi da gudu sun karbe shi a hannunta suna bata hakuri suna kuma lallashinsa. Amma idan da ace zaiyi laifin ta goyi bayansa ta nuna cewa ba laifi yayi ba sai kuga mutane suna yi musu tsinuwa daga ita har shi. Daga nan kuma zasu fara ja baya dasu, zasu yanke zumunci dasu, in yayi laifin ma babu mai kwabar sa babu mai hana shi. Wannan tsarin na daga ni sai yayana shine tsarin daya tarwatsa zumunci. 


A gidan Mama suka kai har dare. Diyam ta tambayeta shawara akan kayan dakin da zata yiwa su Murja, shin ta siya musu kayan ne ko kuma ta basu kudi kowa ya siya da kansa? Sai Mama tace "ina ganin ki sai musu furnitures, sai kuma ki basu kudin da zasu sai sauran kayayyakin anfaninsu tunda kowa da irin taste din ta" nan suka yanke shawarar irin kayan da za'a siya da kuma adadin kudin da za'a basu. Sannan Mama tace "to ke kuma fa? Menene naki shirin?" Diyam ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannayenta. Mama tace "ba kunya zaki tsaya ji ba fa, magana zaki yi sosai. Dan ba kya gari ne da tuntuni ya kamata a fara yi miki gyaran jiki da sauran abubuwa. Amma tunda kin dawo yanzu zamu fara insha Allah. Kinga akwai tsumin Maman Fareeda shine gatan da ake yiwa ko wacce amaryar da za'ayi aurenta a yanzu, ko matan auren ma zasu iya amfani dashi, very pure and natural babu algus. Ga number dinta nan zan baki ki kirata kiyi order zata kawo miki har gida kiyi ta sha kuma sai ki ajiye number din daga baya ma kya cigaba da karba" ta karantowa Diyam number din kamar haka "07033742833".


Sai kuma ta nemi Diyam ta sanarwa da Sadauki cewa zasu zo ganin gida ita da Aunty Fatima dan su san yawan kayan da za'a siyo. Amma da daddare da Diyam tana waya da Sadauki ta gaya masa sai yayi dariya yace "wanne kayan za'a siyo? Ki ce musu suyi hakuri nayi musu shigar sauri har na bayar da order kayan gida gabaki daya, za'a sa komai da komai, sai dai in an gama sakawa sai suzo su gani in akwai gyara suyi mana" da Diyam ta gayawa inna sai ta kama fada "wannan wanne irin abu ne? To wannan kudin da suka kawo a cikin jaka kuma me zamuyi dashi?" 


Rumaisa tazo har gida suna maganar gyaran jiki da Diyam. Tace "akwai Hajiya Hannatu Sokoto, mutuniyar Sokoto ce amma ta zauna a sudan dan haka ta iya gyaran jiki sosai kuma duk kayan ta ma daga sudan take zuwa da abinta, nima wata matar abokin abban Najma (babynta) ce take bani labarin ta, aikinta akwai tsada dan matan manyan mutane kadai suke iya hiring dinta amma kuma fa akwai kyau dan saita mayar dake tamkar jaririya, Sadauki kuwa in ya shigo hannun ki to kuwa ya kade har ganyensa" ta karashe maganar tana dariya. Diyam ta dungure ta, sai kuma tace "to kisa a hada ni da ita mana" Rumaisa ta harare ta tace "au, na dauka ai ba kya so".


Tunda aka hada Diyam da Hannatu Sokoto shikenan komai ya chanja mata, matar ta karbi kudade da yawa a gurin Diyam amma fa tana fara aiki akanta, Diyam tasan cewa she is worth it. Kullum sai tazo kuma kullum da kalar gyaran da take yi wa Diyam. Tun daga kan gashin kanta zuwa faratan yan yatsun hannayenta da kafafuwanta babu abinda gyaran bai shafa ba. Yau a shafe ta da wancan a wanke da wannan gobe a saka ta tsugunna akan wancan turaren jibi kuma a bata wannan ace ta li茩a ta kuma yi tsarki da wancan. Gata kuma a jika ta gabaki dayanta a wanke ta. Har bakin Diyam sai da akayi masa gyara na musamman yadda zai bada wani sihirtaccen kamshi. Ga kuma tsumin maman fareeda (07033742833) da Diyam ta kira aka kawo mata shi har gida, wanda tana sha sau daya ta tabbatar wannan bana wasa bane ba dan haka tayi wa number din kyakykyawan ajiya dan gaba.


A gefe guda kuma tayi dinkuna na fitar biki. Duk da dai ita har yanzu tana nan akan bakanta na cewa ba zata yi taro ba, wanda inna zata yi kawai ya wadatar.


Sadauki kuma a nasa bangaren baya samun zama sam. Kullum yana cikin zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Kano. Family dinsa duk sun taho daga Canada suna Maiduguri suna nasu shirin. Kamar yadda Murjanatu ta fada, lokacin da suka gabatar masa da jerin events din da suke son yi na biki sai yace "no, kuyi parties dinku ku kadai amma ni ba za'a fitar min da mata ana tallata ta a duniya ba" duk suka juya suna kallon Murjanatu ita kuma ta daga kafada tace "I told you so". Abinda kawai Sadauki ya yarda za'ayi shine wushe-wushe, wanda yake bikin al'ada na kanuri. Sai mother's eve da Mama zata yi washegarin kai amarya dan a nuna wa yan uwa amarya itama kuma ta san su.


On impulse Diyam ta kira Humairah, matar yayan Bassam ta tuna mata zancen bikinta. "Ban sani ba ko zaki samu zuwa?" Humairah tace "what are you talking about? Zan zo mana, ai ina lissafe da lokacin dama already na tambaya har an barni ma. Insha Allah kwana ma zanyi tare dani za'a kai ki gidan Mr Abatcha" sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Ana bugo kati Diyam ta sake tura mata, sannan kuma ta tura mata na daurin aure tace "ki nunawa Bassam ko zai samu damar zuwa".


Satin biki yazo, su Mama sunje sunga gidan Diyam kuma babu abinda suka gyara saboda babu abin gyarawar, sai dawowa da sukayi suna rike baki suna bada labarin aljannar duniyar da suka gani. Mama tace "har Subay'a anyi mata dakinta, da set din gadonta da komai na bukatar ta". Ranar talata Diyam tayi baki, Sa'adatu, Falmata, Fanna da Adama gabaki dayan su da akwatinan su "tunda yaki yarda muyi dinner da luncheon da bridal shower da cocktail party gwara mu dawo gidan su amaryar mu zauna muyi ta kallonta" inji Murjanatu tana turo baki. Diyam tayi murmushi tana taryen su with open arms, da alama shi kansa yayan nasu bai san da zuwan su ba tunda bai gaya mata ba. A ranar ne sauran sisters din Sadauki suka fara ganin Diyam a zahiri, gashi kuma dama tasha gyara sai abun yayi musu duka biyu. Adama tace "gaskiya pictures basa yi miki adalci Diyam, you are much more beautiful in person" Murjanatu ta kama hannunta tana shafawa tace "what's the secret? So kike ki kashe min yaya na ko?".


Part din Ummah Inna tasa aka shirya musu aka yi musu shimfidu aka saka musu duk abubuwan bukata sannan aka kai musu kayansu can suka sauka. Sai Diyam itama ta koma can tare da Subay'a da Asma'u suka barwa Inna da yan uwanta da suka fara zuwa daga Kollere part dinta. Wasa wasa sai ga gida yana kara cika. Kusan duk wanda yazo daga Kollere sai yace a nan zai sauka, da Asma'u ta tambayi wata mai yasa basa tafiya gidan Alhaji Babba shi da yake auren yaya hudu? sai tace "haba yar nan, kowa ai yana son dan maiko maiko ko?" Jin haka yasa Inna ta aikawa da Hajiya yalwati kudi da kayan abinci tace saboda baki.


Kamun amare (su Murja) an saka shi ranar Alhamis, juma'a kuma angwaye sun shirya dinner su da amaren su da kawayen amare. Assabar za'ayi daurin aure, wanda shine za'a hada dana Diyam, Alhaji Babba ya bawa Kawu Isa waliccin yaran duk su hudun shi kuma zaiyi waliccin Diyam. Ranar assabar din ne kuma za'ayi yini sannan da daddare akai amare.


A bangaren Diyam kuma babu kamu, babu dinner, sai wushe-wushe ranar friday sai daurin aure assabar da safe sannan inna tayi yinin ta anan gida da daddare kuma akai amarya. But, ranar laraba sai ga mutane daga Maiduguri wai sunzo kawo kudin cin-cin, aka tarye su sosai aka kuma karrama su amma kuma akayi ta mamakin wannan al'ada ta cin cin. Mama tace "to yanzu cin cin din zamu zo mu soya ko kuma me?".


Alhamis da safe Hannatu Sokoto tayi wa Diyam kunshi ja da baki mai dan karen kyau, sannan kuma tayi mata kitso shuku kanana kanana, duk a cikin aikinta ne. Da yamma Diyam ta shirya tayi simple kwalliyarta cikin atamfa riga da plain zani ta dauki in-laws dinta suka tafi gidan aunty Fatima inda a can ne za'ayi kamun wadancan amaren. Amma Diyam tana zuwa sai kallo ya koma sama, kowa ya kalle ta sai ya sake waigo wa "wai Diyam ce wannan?" "Diyam ke ce kuwa?" Har sai data gaji dan haka kafin a gama ma ta gudo ta dawo gida. Tun a daren Sadauki ya gaya mata zasuyi baki washegari.


Washegari Friday, da wuri Humairah tazo gidan, hakan ba karamin faranta ran Diyam yayi ba. Suka hadu da Rumaisa, Rufaida, su Murjanatu da kuma Asma'u. A ranar Kasusu (yan uwan ango) suka zo gari, gidan Alhaji Bukar suka sauka, daga nan kuma suka taho gidan su Diyam kawo kayan gaisuwar uwar amarya. Set guda akayo wa Inna na kaya tamkar wanda aka hado mata lefe, sai kuma kayan kunshi iri iri wadansu ma ko sunan su su Inna basu taba ji ba. Su kuma anan gidan suka hada musu goma sha tara ta arziki na nau ikan kayan ciye ciye, fura da nono kam ba'a maganar ta saboda tambarin su na fulani, sai gurasa ita kuma shedar su kanawa ne, sai kuma sauran abinciccika da kala kalar nama da drinks har sai da suka ci suka bari suka kuma yi takeaway. Da zasu tafi suke tsokanar su Sa'adatu "wato dan kunyi yaya shine kuka tare anan? To sai ku bita har gidan mijin kuyi mata zaman daki" Asma'u tayi saurin cewa "nice yar zaman daki ai".


Daga nan kuma sai aka fara shirye-shiryen wushe-wushe (bangajiya). A gurin taro na Meena event center anyi decorating gurin da traditional costume na barebari. Falmata, wadda take registered beautician ita ce ta zauna ta tsarawa Diyam kwalliya sannan suka nannade ta da flowery laffaya mai kalolin red and blue. Su kuma yammatan duk sunyi kwalliyar blue shadda da akayiwa dinkin riga three quarters da skirt, sai kuma suka yafa jan mayafi. Duk abinda suke yi Diyam tana jin sune kawai, amma ita hankalinta yafi tafiya ne akan murnar yau zata ga Sadauki, dan rabonta da ganin sa tun ranar Monday daya tafi Maiduguri zai taya Papa shirye shiryen saukar bakinsa da zasu zo daurin aure.


Bayan magrib motoci suka zo akayi ta diban mutane ana kai su, kowa cewa yake yi zaije saboda kowa yana son yaga wannan al'ada ta barebari sannan kuma kowa yana son cin dadi. Lol


Sai da aka gama kwasar mutane saura Diyam da yammatan ta sannan Sadauki yazo daukan ta. Aka kawo kuma wata motar da zata dauki kawayenta. Ya kira ta yace ta fito su tafi, ai kuwa duk su fanna suka taho rakiya da kuma tsegumi. Suka hango motar daya zo da ita, tun daga motar suka fahimci cewa yau a shiryen sa yake, Al- Mustapha ne a seat din driver, kuma dama yana daga cikin samarin Murjanatu dan haka ta bude seat din kusa dashi ta zauna. Diyam kuma aka bude mata baya inda Sadauki yake zaune ta shiga ta zauna kusa dashi aka rufe kofar. Adama ta zagaya side din da yake tayi knocking window, ya sauke glass yana kallon ta yace "ya akayi?" Tace "yaya Aliyu dan Allah in shigo? In zauna a tsakiyar ku kaga waccan motar kamar ba zata ishe mu ba" ta karashe maganar tana kokarin yin dariya, bai ce mata komai ba sai tayi winding up glass din yana murmushi yace "yaran nan so suke su mayar dani kakan......" Sai kuma maganar ta makale ya kasa kammalawa saboda juyo wa da yayi suka hada ido da Diyam da take kallon sa saboda kyawun da yayi mata ko kuma maybe dan bata saba ganin sa da manyan kaya bane ba?. Bakin sa ya motsa a hankali amma Diyam bata ji mai yace ba, sai ta tambayeshi. Yace "tasbihi nake yi ga Allah, mahaliccin kyawawan surori" ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta sai yabi hannun da kallo, idanunsa suka sauka akan tsararren kunshin da yake kwance akan farar fatarta. Yace "wadda tayi kunshin nan ko nawa aka biya ta taci kudinta" Diyam tayi masa fari da ido tace "harda kitso tayi min" yace "may I see it?" Ta makale kafada tace "not today" yace "gobe ne dai kadai ta rage min. Amma ban sani ba ko zan kai goben? Dan wannan abin da kike min da ido bana jin zai barni in yi bacci yau" dariya suka ji Murjanatu tayi daga gaba, Sadauki ya kalle ta yace "ko kiyi shiru ko kuma a sauke ki ki hau napep" Al-mustapha ya dan waigo yace "amarya, ni ko gaisawa ma ba'a bari munyi dake ba" Sadauki yace "hey! Juya ka kalli gabanka, don't go about looking at something that is not yours" Murjanatu tace "an fara, yau zanga yadda za'ayi wannan taron" Sadauki yace "kinyi shiru ne ko kuma ayi packing ki fita?" Al-Mustapha yace "in ka sauke ta sai dai ka zagayo ka ja motar ka da kanka" Diyam dai tana jinsu tana ta murmushi. Ita kanta tasan tayi kyau kuma tasan yau za'ayi rigima da Sadauki duk kuwa da cewa komai nata a rufe yake fuskarta da hannayenta ne kawai a bude.


Suna packing ya miko mata hannu yana murmushi, ta makale kafada sai ya langwabe kai yace "Please" sai ta saka hannunta a cikin nasa, ya juya hannun sannan ya saka fingers dinsa a tsakankanin nata yana kallon yadda hannayen nasu suka yi kyau sosai together,  perfect match for each other, kamar dama a haka aka halicce su.


Suka fita suka jera a tare suka tafi gurin da aka tanada saboda su, Diyam idanuwanta a kasa tana jin tsananin kunyar mutanen gurin. Tun daga bakin mota ake turara su da turaren wuta iri iri masu kamshi kala kala har suka je suka zauna sannan aka sake zagaye su da turarukan wuta. Nan take aka fara gabatar da shagali wanda ita Diyam ba fahimta take yi sosai ba saboda hannun da yake rike da nata kuma tayi dabarar kwacewa ta kasa. Ga kuma idanuwa guda biyu a kanta suna kallon duk wani motsi nata. Ta dan kalle shi tace "hey.......stop looking at me like that" ya daga gira yace "ko? Saboda me? Baki san ni maye bane ba? Ko baki da labari?" tayi murmushi tace "kar ka bari Inna taji ka" yace "am serious fa, kin dauka wasa nake yi ko? Ina tausaya miki ranar da zaki fahimci a inda tawa maitar take" ta sake kokarin karbar hannunta ta kasa. Yace "wannan hannun tunda kika bani shi kuma ya zama nawa, sai sanda nayi niyya zan baki aron sa" ta sake cewa "ni ka daina kallo na" ya bata rai yace "ba fa ke nake kallo ba, lips dinki nake kalla wondering what they taste like" taji kamar zata nutse a gurin, tace "wayyo Ummah". 


Anyi rawa sosai, rawar barebari, yan'uwa da abokan Sadauki ne suka fara yi sai kuma na Diyam sukayi joining dinsu suna koya, sai kuma suka koya musu suma irin tasu rawar ta fulani. Amma Diyam ko motawa daga seat dinta Sadauki bai bari tayi ba ballantana ta saka ran yin rawa. Duk wanda yazo gurin su daukan hoto kuwa indai namiji ne to Sadauki zai ce masa "zagayo ta side dina" sai suyi dariya gaba daya. And Diyam wondered, anya kuwa Sadauki zai barta ta koma school?


Sai after 11 suka tashi, shima dan dare yayi ne ba wai dan sun gaji ba. Da kyar Sadauki ya bar Diyam ta shiga gida, shi ji yake kamar su yi ta zama a mota har gari ya waye, gani yake kamar gobe ba zata yi ba. 


A ranar duk su biyun babu wanda yayi bacci. Kwanciya suka yi da wayoyinsu a kunnuwansu suna bitar rayuwar su, yarintarsu, rabuwarsu, da kuma sake haduwarsu. Diyam ta bashi labarin sanda take lekensa ta window lokacin da Saghir ya kawo shi gidan su. Yace "ohhhh, ashe shi yasa naji kamar zan fadi, ashe idanuwa ne suka yi min yawa". Sai da dare ya raba sannan suka yi shawarar gabatar da salloli da addu'ar neman alkhairi a cikin sabuwar rayuwar da zasu shiga gobe. A kan sallayinsu suka karasa kwana. Sai da suka yi sallar asuba sannan Diyam ta kwanta, amma kuma ba wai bacci tayi ba likimo kawai tayi tana jin su Humairah dasu Murjanatu suna ta hirarrakin su suna dariya har gari ya waye. Bata tashi ba sai da Hannatu Sokoto ta zo ta tashe ta tana cewa "gwara da kikayi baccin ai, shi bacci yana kara fito da kyawun mutum" sai ta ajiye mata special dahuwar kazar da tayo mata daga gida, ta zauna ta cinye tas sannan ta kora da tsumin maman fareeda (07033742833), tana ci suna hirar su da Humairah suna kuma jiyo hayaniya a tsakar gida maza suna ta shirye-shiryen  tafiya daurin aure. A lokacin Bassam ya kira Humairah ya gaya mata ya shigo gari amma ya zarce venue din daurin auren, Alfurqan Mosque.


Kafin ta gama Hannatu Sokoto ta shirya mata ruwan wanka dan haka ta shiga tayi wanka tafito, tana zama a gaban mirror message din Sadauki ya shigo wayarta.


Dear Mrs Abatcha

Alhamdulillah. I am now yours and you are mine.

Signed

Mrs Abatcha


Ai mun gama ko?

[3/24, 10:36 PM] +234 703 589 5826: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Seventy Two & Three :  A Perfectly Perfect Night


I was thinking about covid-19. Sai nake ganin da ace al'ummar duniya duk sun sani kuma sun bi umarnin fiyayyen halitta (S.A.W) a inda yake cewa idan annoba tazo guri, wanda yake ciki kar ya fita wanda kuma yake waje kar ya shiga, da an bi haka da cutar bata kai matsayin da take a yanzu ba.


Chinese basu san wannan umarnin na annabi ba, amma mu munsani dan haka me yasa mu ba zamu bi ba dan dakushe yaduwar cutar?

Stay safe

Stay at home


Hannatu Sokoto da muka yi magana a last episode wata member ce ta group dina na WhatsApp, amma bata gyaran jiki, na saka sunanta ne kawai to honor her and for fun.

But Maman Fareeda is real, duk mai so zata iya kiranta.


Ta dora wayar a kirjinta ta lumshe idonta taba jin hawaye yana taruwa a idonta, sai data fahimci da gaske kukan zata yi sai ta mike da sauri zata shiga toilet sai suka hadu da Humairah tana fitowa ita kuma, ta tsaya tana kallon ta tace "wai kuka kike yi?" Sai Diyam taji sauran kukan data rike ya taho gabaki daga, ta juya bayanta tayi facing bango tana kokarin share hawayenta. Humairah ta fara dariya, abinda ya jawo hankalin yammatan da suke dakin suka taso suna tambayar abinda ya faru. Hannatu Sokoto ta shigo lokacin da Diyam take kokarin ture Humairah zata shiga toilet sai Hannatu tace "wai shiga kike so kiyi ki zauna a kan sassanyan tiles kiyi kuka zaki a toilet din? To dakata, bara in kawo miki garwashin wuta in dumama miki tiles din sai ki zauna kiyi ta kukan" duk suka kwashe da dariya, tace "a to, ni ba kukan ne damuwata ba, ni damuwata shine zama a sassanyan guri". Da Diyam taga sun mayar da ita abar tsokana sai ta fice ta bar musu dakin. Daya dakin da yake kusa da inda suke ta shiga, wanda a da shine a matsayin dakin Sadauki sanda suna yara. Ta shiga ta rufe kofa ta jingina a jikin kofar tana kallon dakin da yanzu yaje a gyare tas amma babu komai a cikinsa sai carpet da akwatunan su Murjanatu da aka kawo dakin dan kar wancan ya cika da kaya. Ta rufe idonta hawayen yana cigaba da zarya a kuncinta, hawayen da ita kanta tasan na murna ne ba wai na bakin ciki ba. Sai yau ta tabbatar da cewa ana iya yin kukan dadi.


Ta bide idonta tana tuno lokacin da take shigowa dakin tayiwa Sadauki kaca-kaca dashi, ta yayyaga masa takardun sa ta hargitsa masa shinfidar sa, ko kuma tazo ta kwanta a shimfidar tayi ta baccin ta, amma bai taba ko daga mata murya da sunan fada ba. Da kuma sanda take zuwa ta saka shi a gaba yayi mata homework ko da kuwa shi baiyi nasa ba. She never thought da gaske one day zai zama mijint, duk kuwa da cewa tun kafin tasan ma'anar kalmar miji take cewa shine mijinta.


Anan dakin ta kwanta akan carpet. Ta lumshe idonta sai kuma tayi murmushi tana jin duk sauran problems dinta na rayuwa suna melting away. Ta zama matar Sadauki.


Tana nan kwance Rumaisa tazo gidan, ita ta shigo har dakin ta fita da ita palo sannan suka kafa tsokanar ta wai tayi kukan aure, sai kuma Falmata tayi mata kwalliya ta musamman aka shirya ta cikin tsadadden farin lace din da ta tanada saboda yau wanda tayi musu anko ita da Subay'a. Sannan suka fara daukan pictures, suka dauka anan sannan ta shiga part din Inna can ma suka daddauka da mutane ana ta taya ta murna da kuma yaba kyawun da tayi. Masu selfie nayi a waya, cameraman ma yana yin nasa.


Sai kuma ga sanarwar cewa ango yazo zasuyi pictures da amarya, nan kuma Diyam taji ita duniya babu wanda take kunya kamar Sadauki, ita sam bata dauka zaizo yin wani hoto da ita ba. Sai ta wayance ta koma part din Umma tayi zamanta amma tana jin alamar ya shigo kuma sai ta mike ta tsaya daga bakin kofa tana lekensa, yayi kyau sosai, a idon Diyam sai taga bata taba ganin mutum mai kyau irinsa  ba a rayuwar ta, yayi shigar farin yadi kal dashi tun daga hula har zuwa takalmi fuskarsa dauke da annuri wanda yake bayyanar da farin cikin da zuciyarsa take ciki. 


Tana kallo ya shiga gurin Inna, da alama gaisheta yaje yayi sai kuma gasu sun fito tare hannunsa rike da Subay'a, suka tsaya a tsakar gida suka yi pictures sai kuma Inna ta sa baki ta kira ta amma sai ta makale taki tafiya, sai Subay'a ta taho part din da sauri "mommy kizo kiga yadda uncle Sadauki yayi kyau, kizo kuyi hoto kafin ya tafi" Sa'adatu tayi dariya tace "chafdi, mai fitar da yaya Aliyu daga gidan nan ba tare da yaga Diyam ba ai babu shi a duniya". Diyam ta kama hannun Subay'a amma kafin tayi magana sai gashi a tsaye a bakin kofa yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da idonta tana mamakin rashin kunya irin ta Sadauki da har ya keto mutane ya taho gurinta. Sai ya tako cikin tafiyar kasaita ya zo har gabanta ya tsaya yace "my wife" sai ta saki hannun Subay'a ta rufe fuskarta da sauri tana murmushi, taji yammatan gurin sun dauki shewa sannan kuma wata mata a tsakar gidan ta rangada guda. 


Sai kawai ji tayi ya kama hannunta ya fara jan ta zuwa waje, a dole ta nutsu ta bishi amma fukarta a kasa, ta kasa daga ido ta kalle shi duk da yadda zuciyarta take son ganin cikin idonsa, balle kuma ta kalli sauran jama'ar gurin. A kayi ta hotuna, suna tsaye wannan yazo a dauka wancan ma yazo a dauka har saida aka gama sannan ya kuma jan hannunta zuwa dakin daya dauko ta ya zaunar da ita yace da Murjanatu "kar kuda ya taba ta" sannan ya juya ya fita, sai a lokacin ta dago kanta ta bi bayansa da kallo, tana kallon yadda yake taking steps one after the other.


Sai da ya fita sannan kuma suka zo suka zagaye ta suna tsokana 'mai tsoron miji' 'ta kasa kallon mijinta' 'dama fulani haka kuke?' ita dai bata kula suba sai ta karbi wayar Asma'u wadda ta lura tana ta daukan pictures "kawo inga pictures din da kika dauka" ta bude hotunan da sauri tana scrolling tana neman wanda yafi fitowa sosai har ta samu, sai ta kwanta ta dunkule a guri daya ta zuba wa fuskarsa ido tana murmushi.


Humairah ce ta katse mata daydreaming dinta, tace "Bassam yazo fa, yana waje" sai ta ajiye wayar ta mike da sauri, ta kira Asma'u "akwai bako a waje, ki bude masa dakin baki ki kai shi can, sai kizo ki kai masa abinci da ruwa" sai Asma'u ta saka mayafin ta ta fita, amma kuma wajen a cike take da mutane maza da mata na ta gaggaisawa, sai kawai ta tsaya tana bin su da kallo tana son ta gani ko zata iya gane waye jikan sarkin Abuja a cikin su. Yana cikin mota ya hango ta fito daga gidan da yake tunanin nan ne gidan su Diyam, farko ya dauka Diyam din ce amma kuma yasan Diyam ba zata fito kofar gida cikin mutane ba tunda yau aka daura mata aure, sai kuma ya lura wannan bata kai Diyam maturity ba amma suna kama sosai sai fari da Diyam ta fita. Yana ganin yadda take yamutsa fuska, dafa dukkan alama zata yi tsiwa. Nan sai zuviyar shi ta bashi cewa wannan Asma'u ce, only sister din Diyam. Sai ya bude kofar motar ya fita yana kallon ta, sai yaga ta juyo ta kalle shi kamar wadda aka kira, suka tsaya suna kallon kallo sannan sai yaga ta doso shi. He likes yadda take tafiya, ya tabbatar bashi kadai ba sauran mazan da suke gurin ma ta ja hankalinsu. Ta tsaya dan nesa dashi kadan tace "Bassam?" Ya gyada kai yace "Asma'u ko?" Bata amsa ba sai tace "Adda tace ka shigo ciki" muryarta tayi masa dadi, sautin fulani. Sai ta juya tayi gaba. A zuciyarsa baya son shiga dan shi da a son ransa ne daga gurin daurin auren zai komawarsa dan dai Humairah ta nace sai yazo yayi wa Diyam Allah ya sanya alkhairi "dan ita kazo fa, ai ya kamata ku gaisa ko minti daya ne". Amma yanzu da Asma'u take gabansa tana tafiya sai yaji cewa binta a baya ya zama wajibi a gare shi. Ya zare key din motar ya bita cikin gidan yaga ta tura kofar wani daki kafin a karasa shiga cikin gidan ta ce masa "Bismillah" sai ya shafa kai yana kallonta, shi ai ya dauka tare zasu shiga amma sai yaga ta juya ta shiga cikin gida ta barshi a tsaye. Wannan yasa dole ya shiga dakin ya zauna ya kama daddanna phone dinsa. Amma zuciyarsa tana tunanin ko zata dawo?


Bai jima ba sai gata ta shigo da sallama, tayi masa shimfidar abinci can gefe kadan sannan ta fara jera masa kayan ciye ciye iri iri har ta gama amma shi idanunsa a kanta suke ba wai a kan abinda take yi ba. Itama kuma tana jin idanuwan nasa akanta, dan kada ne ya rage bata yi barin abincin da take shiryawa ba. Sai data gama sannan ta mike, yayi saurin pretending kamar wayarsa yake dannawa tace masa "Bismillah, ga abinci. Adda zata fito ku gaisa" ya ajiye wayar sai kuma yace "thank you. Amma ki zauna mana kafin tazo din ko. Kinga ai sai ki tayani hira ko?" Sai ta dauke kanta, wannan mutumin neman magana yake yi kuma. Shi baisan zuciyarta bugawa take yi da wannan kallon nasa ba? Ga shi ya cika kyau da yawa. 


Ta girgiza kai tace "ina yin wani abu ne a cikin gidan" yace "Please, minti uku fa kawai. Kinga ni ban iya cin abinci ni kadai ba" he is a playboy, tayi deciding a zuciyarta, sai ta doshi kofa ba tare da ta kuma ce masa komai ba, har ta daga labule sai taji yace "an a lobbo sanne, Asma'u" sai ta juyo tana kallon sa, bata taba tsammanin bafulatani bane ba, mix din shi yayi yawa. Sai ta samu kanta da yin murmushi tace "miyetti" amma duk da haka bata zauna ba ta fita. Bata shirya yin wasa da zuciyarta ba.


Bai ci abincin ba tunda yaci a reception din da suka wuce daga gurin daurin aure. Aliyu ya gane shi kuma ya karbe shi sosai. Sai ya zuba juice ya sha, sannan ya koma ya zauna ana fatan Asma'u ta biyo yayarta su dawo tare. Amma sai ga Diyam tazo sanye da hijab tare da Humairah, suka gaisa tayi masa godiya shi kuma yayi mata fatan alkhairi sannan yace zai tafi. Yace "Asma'u tazo ta kwashe kayan abincin nan mana" Diyam tace "no, kar ka damu kayi tafiyar ka kawai, an jima za'a kwashe su" yace "a dauke dai yanzun ai sai yafi ko?" Ta tsaya kawai tana kallon sa sai yayi murmushi, ta daga gira tace "Asma'un?" Yace "sallama kawai zamuyi ba wani abu ba, dan Allah ki turo ta" Humairah tace "kar ka damu kani na, har phone number dinta zan karbo maka" yace "kash, shi yasa nake yinki over yayata". Suna shiga ciki Humairah ta kwalla kiran Asma'u "kije kuyi sallama da kani na" sai Asma'u ta tura baki tana kallon Diyam, Diyam ta daga kafada tace "ina ruwa na, in kina son zuwa kije mana" kamar ba zata je ba, sai kuma ta zari mayafi ta tafi.


Bayan sallar azahar sai ga yan kawo lefe. Anan gida ya hargitse gaba daya ashe wai al'adar bare bari ne sai an daura aure ake kawo lefe. Akwatuna akwatuna, ga kuma wasu kayan a jakankuna. Lefen yakunshi akwatunan amarya set biyar, akwatin maman amarya (inna), akwatin kannen maman amarya(innaso), akwatin yan uwan baban amarya (bawaso),  sai sisters (Asma'u) sai na kawayen innarta (ya samma soye) sai na matan waliyinta (su Hajiya Babba da yalwati),  sai matan kawunnanta (kamu rawaye. Matar kawu isa da kuma su Hajiya Babba again)sai na  yan bayarwa (na rabo) sune a jakankuna, sai na wadda tayi mata kiso (Hannatu Sokoto) an bata atampopi da kudi. Tun a kofar gida aka fara nunawa maza tukunna aka shiga dashi cikin gida gurin su Inna. Wannan duk al'ada ce ta barebari. Fulani sai suka tsaya kallo da mamaki, wanda baya kusa ma sai da aka kira shi a waya yazo ya kashe kwarkwatar idonsa masu video coverage suna yi masu dauka a hotuna suna yi. 


Diyam kuwa tana cikin daki ta rufe kanta, ita kunyar yan uwan Sadauki take ji gashi taji ance gar da Yaya Ladi da yan'uwanta aka zo. Ana cikin haka sai ga Fauziyya ta shigo gidan tana rarraba idanu, da goyon yarinya a bayanta. Irin yadda gidan ya chanza rake kalla ga kuma uban kayan data gani mutane suna ta gani wanda ko ba'a fada ba tasan lefen Diyam ne. Amma data tuna wanda aka ce shi ya auri Diyam din sai taga wannan ba komai bane ba.


Ta tambaya aka raka ta har dakin da Diyam take. Diyam tana zaune da waya a hannunta tana kallon kiran Sadauki yana shigowa one after the other amma ta kasa dauka. Sai ganin shigowar Fauziyya tayi, ta tare ta da fara'a sosai sai Fauziyya tace "fushi nake yi fa, kin manta dani kuma wayar ki bata shiga kwata kwata" Diyam tace "Allah sarki, ba haka bane ba wallahi. Bana kasar ne ina UK ina karatu" Fauziyya ta gyada kai kawai. Ta tuna lokacin da Saghir ya fita da ita honeymoon America, a lokacin tana jin kamar duk duniya babu ya ita, tana yiwa Diyam dariya a ranta tana ganin cewa Diyam din tayi asara ashe ita asara zata samu. Rayuwa ta juya mata baya gabaki daya, komai ya tsaya mata. Dama a gurin maza take karbar yan kudade tana biyan bu茩atar ta yanzu kuma tunda tayi deciding haifar cikin Saghir shikenan ta rasa costumers, bayan ta haihu kuma tana kallon fuskar jaririyar ta taji cewa ta gama yawon ta zubar kenan. Yan uwan Saghir sam basa taimaka mata kuma ta fahimci suma kansu taimakon suke nema, sun dai je sunga baby sanda ta haihu sai kuma Hajiya da take dan kiran ta tana tambayar lafiyar Anisa. Jin dadin ta daya ta samu aikin koyarwa a wata private school anan layin su. 


Diyam ta karbi Anisa tace "Masha Allah. Kinga dai yaran nan gaba ki dayan su kamar baban su suke yi". Fauziyya tayi murmushi jin an yabi hasken rayuwarta, tace "ni fa bansan ma zakiyi aure ba, Hajiya Babba ta gaya min ana bikin kannen Saghir shine na shigar musu to a can ne nake ji ashe tare da naki ake yi" Diyam tayi murmushi kawai. Fauziyya tace "Allah ya sanya alkhairi" Diyam tace "ameen". 


Ta dauko wayarta a karo na ba adadi tana kallon kiran Sadauki yana shigowa. Sai daya katse sannan tayi murmushi. Sai kuma ga Murjanatu ta shigo ta mika mata waya tace "yaya Aliyu yana kira" Diyam ta ture wayar tayi mata sighing "kunya" sai Murjanatu tayi dariya ta fita tana masa magana. Diyam ta kuma daukan wayarta sai sakon shi ya shigo.


Tunda Sadauki ya fita daga gidan yake kokarin ganin yayi waya da Diyam, yana so yaji muryarta. Da farko mutane ne suka hanashi samun sukunin yin hakan, daga baya kuma da ya samu ya kira sai taki dauka. Yayi yayi amma sai dai tayi ta ringing ta katse ba zata dauka ba. Da farko ya dauka bata kusa da wayar ne dan haka ya kira Murjanatu ya ce ta bata, amma sai taki karba, yana jin Murjanatu tana yi mata dariya sannan tace masa "yaya Aliyu kunyar ka fa take ji wai" sai yayi murmushi ya samu secluded guri ya zauna ya shiga WhatsApp ya tura mata "ke fillo" shiru at first, sai later kuma ta aiko masa da reply na emoji na harara. Yayi dariya shi kadai ya rubuta 

"wai da gaske kunyata kike ji? Tun yanzu?" 

"Kunya kuma? Wacce irin kunya?"

"Hmmm, really? So tell me, me yasa kika rufe idonki da na shigo gida? Me yasa kika ki yi min magana kuma me yasa kika ki daukan phone dina?"

"Bafa kunyarka nake ji ba. Fushi nake yi"

"Poor me, laifin me nayi?"

"Ba kai bane ba ka hanani rawa a gurin wushe-wushe" (imojin shagwaba)

Dariya "okay, yanzu dai rawa kike so ko?"

"Uhmmmm" 

"Shikenan. Kina bina bashin rawa"

"Da gaske?"

"Yes, but just me and you. Tonight."


Tayi logging out da sauri. Feeling very nervous. Ina ma dai za'a daga kai amaryar nan zuwa gobe? Ko jibi?


Babu abinda aka fasa. Magrib tana yi aka saka ta ta sake wani wankan, wannan karon babu kwalliyar da aka yi mata sai atamfar da ta saka blue mai adon pink and white flowers. Sannan aka nada mata laffaya fara mai shara shara da adon blue and pink flowers. Humairah da Murjanatu ne suka shirya ta tsaf, sannan suka kamo hannunta suka taho da ita dakin Inna inda anan iyaye suke, Mama, Inna, Hajiya Rabi (matar Kawu Isa) sai kuma step sisters din su Inna su biyu. Ta zauna a tsakiyar su ta nannade kafafuwanta suka fara yi mata nasiha, idan waccan tayi ta gama sai waccan ta dauka itama tayi nata. Suka gama sannan suka yi doguwar addu'a suka shafa. Lokacin masu daukan amarya suka zo, yaya ladi, Mama (matar baban Sadauki) sai kannen Papa mata su biyu. 


Suna zuwa aka fara nuna musu kayan garar da aka hadawa Diyam. Komai da komai na kayan abinci an siya in abundance, ga kuma kayan gara dangin su alkaki, nakiya dubulan, gireba, cincin da sauran su komai a cikin manyan containers. Sai daaka nuna musu kayan suka gani suka saka albarka sannan aka zuba su a mota aka tafi dasu gidan Alhaji Bukar.


Diyam tana jinsu suka zauna suna ta barkwanci dasu Mama, sai taji dadin yadda taji ana magana tsakanin Inna da yaya ladi. Sai da suka gama sannan aka sake feshe ta da turare sannan maman su Murjanatu ta kama hannunta ta mike. A lokacin Subay'a ta shigo "mommy! Mommy wai aunty Asma'u tace tafiya zaki yi ki barni, Mommy ai tare zamu tafi ko?" Mama tayi saurin dauke ta ta fita da ita daga dakin tana ta rusa kuka, wannan shi ya kawo hawaye idon Diyam. Tun sanda za'a kai kayanta gidan Sadauki ta fara hada na Subay'a amma Inna tace "ba ki da hankali. In ma zaki tafi da ita ba yanzu ba. Kuma ke da zaki koma karatu menene amfanin tafiya da ita?"  


Ta fara kuka a hankali maman su Murjanatu tana tsokanar ta. Ita kuma tsokanar kara mata jin kunya take yi. A haka suka fita tana jiyo kukan Subay'a suka shiga mota ita da maman su Murjanatu da Mama, almustapha kuma yana driving suka tafi, sannan sauran motocin daukan amarya suka biyo bayan su.


Duk da fuskar ta tana rufe amma tana gane inda suke har suka je, a lokacin ta daina kukan Subay'a, suka fito aka saka ta tayi basmala ta kuma shiga gate din gidan da kafar dama sannan ta sake repeating sanda zata shiga cikin gidan. Tana shiga kamshi ya kaiwa hancinta ziyara, kamshi mai dadi, kamshin Maiduguri. 


Sama suka hau da ita suka kaita har cikin bedroom din da yake nata suka zaunar da ita, suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi. Sanda Mama zata tafi sai tace "Diyam yau ba zaki rike hannuna kice kar in tafi in barki ba?" Sai Diyam ta samu kanta da yin murmushi tare kuma da jin kunya. 


Humairah ce ta fara zuwa tayi mata sallama saboda a daren zata bi flight zuwa Abuja, daga nan kuma mutane suka fara watsewa a hankali gidan ya fara yin shiru. Su Murjanatu, Rumaisa da Asma'u ne karshen tafiya, sai da suka gyara mata duk inda aka bata suka kara tabbatar wa ko ina na gidan yana kamshi sannan suka yi mata sallama. Murjanatu tace "wato ko dan tayin nan ba zaki yi mana ba ko? Irin ki dan ce 'ku zauna ku kwana mana tunda dare yayi?" Diyam ta matsa mata guri tace "Bismillah, zo ki kwanta a kusa dani" Rumaisa tace "har na tausaya miki Murjanatu. Ni dai kunga tafiya ta maigidana yana waje yana jirana tun dazu" Adama tace "kunsan wani abu? Yaya Aliyu fa yana cikin gidan nan duk wannan abin da ake yi. Naje part dinsa naji kofa a rufe kuma an bar key a jiki ta ciki" Murjanatu ta mike da sauri ta dauki handbag dinta "Allah ya bamu alkhairi" duk suka yi mata dariyar ta fiya tsoron Sadauki sannan suka fita gabaki dayan su a tare.


Tunda Diyam taji cewa Sadauki yana cikin gidan sai taji duk nervousness dinta ya dawo. Wayar ta har zamewa take yi daga hannunta tana faduwa kasa. Ta mike daga kan gadon tana karewa dakin kallo sannan ta kalli kanta a madubi kawai sai taga tayi wani irin kyau har kyalli fatarta take yi duk kuwa da cewa babu ko digon kwalliya a fuskarta. Ta gyara zaman laffayar ta sannan ta bude kofar balcony din daya ke cikin bedroom dinta ta fita tana kallon yadda sama tayi tas sannan taurari suka cika ta. Sai tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki a zuciyarta sannan ta koma cikin dakin ta murda kofar fita waje ta leka empty corridor sannan ta fita da sanda kamar marar gaskiya ta bude dakin da yake opposite nata taga shima irin nata ne sai girma da wancan dakin yafi wannan sai kuma banbancin colors. 


Shirun da gidan yayi ne yasa ta jiyo kamar motsin takun mutum yana tahowa inda take, sai tayi sauri ta karasa shiga cikin dakin ta haye can karshen gado ta rufe fuskarta da laffayar jikinta. Taji an bude kofar corridorn an shigo, sannan heavy footsteps suka taho zuwa dakin da take yayinda bugun zuciyarta ya karu, taji shigowarsa sannan taji kamshinsa. 


Ya dan jima a tsaye yana kallonta sannan ya karasa shigowa ya hawo kan gadon ya zauna akan kafafuwansa a gabanta yana kallon fuskarta ta cikin shara sharan laffayar ta sannan murya can kasa yace "Sadiyam"


Ta saka hannayenta da sauri ta kara rufe fuskarta tana murmushi. Sai ya saka nasa hannayen a saman nata yana shafa wa yace "hannayenki suna da kyau, kunshin yayi musu kyau sosai". Tayi sauri ta juya tana kallon side. Sai yayi dariya yace "yanzu ni fuskar matar tawa ba za'a barni in gani ba?" Tace "sai ka biya tukunna" yayi murmushi ya jawo rose flower da ya shigo da ita a soke a bayan wandonsa a jikin rapping din an rubuta "loving you is all I ever know" ya mika mata ta karba da hannun dama, sai kuma ta miko masa hannun hagu tana murmushi, sai ya tuna lokacin da suna yara in ya bata sweet a hannu daya sai ta miko masa daya hannun shima ya bata. 


Sai ya saka hannu a aljihu ya dauko chocolate din twix ya saka mata a hannun. Yace "shikenan na biya?" Bata ce komai ba sai ya saka hannu biyu ya bude fuskarta ya sauke laffayar har kafadun ta. Ta dago kai a hankali suka hada ido yayi mata murmushi mai kyau sai ta kuma sunkuyar da idonta kasa itama tana murmushi ta fara bude chocolate din daya bata amma maimakon ta kai bakin ta sai ta kai nasa bakin. Ya rike hannunta a cikin nasa ya juyar dashi zuwa bakin ta ta fara gutsira sannan ya juyo da hannun zuwa nasa bakin shima ya gutsira. 


Sai da suka gama cin chocolate din su sannan ya jata suka mike a tare yace "let's pray". Dakin da aka kaita suka koma, shi ya fara shiga toilet yayo alwala sannan itama ta shiga. Sai ya ja musu jam'i a gurin da aka tanada a dakinta musamman dan sallah. Sukayi sallar isha'i tunda duk su biyun basu yi ba, sannan kuma suka yi sallar raka'a biyu ta godiya ga ubangiji a bisa cikar burinsu sannan ya juyo yana kallonta suka fara jero adduoi. Farko sun fara gabatar da godiya ga Allah sannan suka yi salati ga fiyayyen halitta (S.A.W) sai kuma sukayi addu'a ga mahaifansu da suka riga mu gidan gaskiya, Baffa da Ummah, suka roka musu gafara da ragamar ubangiji, sannan kuma suka yi addu'a ga mahaifansu da suke a raye tare da fatan tsahon rai a cikin kyakykyawar rayuwa. Sai kuma sukayi wa kansu addu'a, suka roki tabbatar alkhairin dake cikin auren su sannan suka roki tsari daga sharrin dake cikinsa. Suka yi addu'a ga yayan su, twins da suka rasu da fatan su zamo masu ceton mahaifansu sukayi addu'ar rayuwa mai kyau ga Subay'a sannan sukayi doguwar addu'ar a kan neman zuri'a ta gari mai albarka a tsakanin su.


In Sadauki ya dauko addu'a Diyam tana amsa masa da ameen in ya gaji sai ita kuma ta karba ta cigaba shi kuma yana amsa mata. A haka har suka kammala suka shafa. 


Kanta yana kasa tana kallon hannunta amma tasan ita yake kallo duk da bata kallonsa, sai ta murguda masa baki, yace "ni ko?" Ta daga gira. Ya mike tsaye yana cewa "zakiyi bayani ne yarinya" sai ya zauna a kan gado sannan kuma ya tafi da baya ya kwanta rigingine ya lumshe idonsa, tana zaune still a inda ya barta tana kallon sa ya jima a haka sannan ya juyo inda take ya bude idonsa a cikin nata yace "na gama komai ko?" Ta mike tsaye tace "sauranka kaza" yayi kamar zaiyi kuka "Please ni kam a yafe min kazar nan mana. Kinga na gaji fa, ga kuma dare yayi" ta makale kafada tana kallon sa. Ya mike zaune sannan ya mike tsaye yace "shikenan, in na fita waje aka sace ni kar kiyi kuka" ya juya ya fita ya barta ita kadai. 


Kayan jikinta ta cire, ta shiga toilet tayi refreshing sannan ta fito ta zauna tana shafa mai me sassanyan kamshi a duk ilahirin jikinta, tana yi tana kallon kofa a tsorace har ta gama ta saka underwears dinta ta kuma saka riga da dogon wando na bacci, rigar a sake take sosai amma ta tsaya ne a saman cibiya, wandon kuma dogo ne har kasa sai dai ya kama saman sosai ya kuma bude sosai daga kasa,  sannan ta hau kan gado ta dauko wayarta tana duba pictures. A lokacin ne sakon Sadauki ya shigo wayarta. 


"I owe you a dance, da kuma kazar amarci. Meet me in the garden please" 


Ta rufe idonta ta bude tana jin kamar zatayi zazza蓳i. Sai kuma ta mike ya dauki hijab ta saka masa turare ta saka sannan ta fita a nutse. Ta sauka kasa ta cikin corridorn daya raba palonsa na kasa da nata, inda anan ne stairs din hawa sama suke kuma anan ne front door da back door na gidan suke. Ta murda back door din ta fita doguwar veranda sannan ta sauka daga kan steps guda uku ta shiga garden. A tsaye ta hango shi, ya chanza dogayen kayan jikinsa zuwa shirt da wandon. Yayi shimfidar karamin carpet akan grass carpet din gurin ya zuba throw pillows akan carpet din sannan ya zagaye shinfidar da candles masu kyalkyali, a gefe kuma ga food warmers guda biyu da fruits da aka yi arranging dinsu a shape din heart. Ya taho ya tarye ta yana murmushi, ya jawo ta zuwa jikinsa ya rungume ta ta baya yana saka fuskarsa a ramin wuyanta yace "ga kaza an siyo, sai me kuma?" Ta juyo tana kallonsa tace "saura rawa ta" yace "with pleasure" sai ya zare hijab din jikinta ya ajiye a gefe ya juyo yana kallonta lokaci daya ya dauke numfashi saboda abinda ya gani, ya sani cewa tana da good figure but bai san cewa it is this good ba, ya jima tsaye yana jin tamkar ya samu paralises ita kuma tana ta sussunne kai, sai ya saka hannunsa na dama a waist dinta ya jawo ta sosai ya hade jikin su, daya hannun kuma yana shafo tun daga kan kananan kitsonta zuwa gadon bayan ta zuwa hips dinta, ta kwantar da kanta a tsakiyar kirjinsa tana jin cewa tamkar a nan ne aka halicceta, ta zagaye shi da hannayenta, tare suka sauke ajjiyar zuciya. Sai ya fara taking steps tare da ita a jikinsa, tamkar jikin nasu guda daya ne, three steps forward, two steps back. 


Ta lumshe idonta tana jinta kamar tana floating a cikin iska, kakkarfan jikinsa like a shield to her, his heart beat like a music to her ear. And he sang to her a cikin kunnen ta:


I found a love for me, Darling just dive right in, And follow my lead, Well I found a girl beautiful and sweet, I always knew you will be the someone waiting for me......

'Cause we were just kids when we fell in love, Not knowing what it was, I will not give you up this time....

But darling, just kiss me slow, your heart is all I own, And in your eyes you're holding mine......

Well I found a woman, stronger than anyone I know, She shares my dreams, I hope that someday I'll share her home, I found a love, to carry more than just my secrets, To carry love, to carry children of our own

We are still kids, but we're so in love, Fighting against all odds, I know we'll be alright this time...

Darling, just hold my hand, Be my girl, I'll be your man, I see my future in your eyes

Baby, I'm dancing in the dark, with you between my arms, Barefoot on the grass, listening to our favorite song, When I saw you in that dress, looking so beautiful

I don't deserve this, darling, you look perfect tonight.

Songwriters: Edward Christopher Sheeran.


Lokaci daya ya tsaya, ya saka hannayensa biyu ya dago fuskarta daga kirjinta suna kallon juna for some seconds sannan ya sunkuya a hankali ya dora lips dinsa akan nata. Very slowly at first, very lightly that she hardly felt it, then it grows and it sends shiver data fara tun daga yatsun kafarta zuwa kwakwalwar ta tayi blocking dukkan tunanin ta, and she opens up to him, inviting him further in. 


A hankali hannayenta da suke sarke da juna a bayansa suka fara journey upward, daga bayansa zuwa wuyansa sannan zuwa kansa suna kara jawo shi closer, giving him more, accepting more.

[3/26, 10:19 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Seventy Four : The Birthday Gift 2


Ga masu tambayar abinda Bassam ya gayawa Asma'u. Fulatanci ne, amma kunsan kamar kowanne yare fulatanci ma yana da dialect da yawa. Yayi mata magana ne da dialect din fulanin yalleman. Idan bamu manta ba Maimoon mahaifiyar Bassam yar yalleman ce dan haka dialect dinsu ya iya. Abinda yace mata shine "you are so beautiful" ita kuma tace masa "thank you".


Diyam............


Wani irin feeling na emptiness ne ya farkar da Diyam daga bacci. Tana jin tamkar jikinta ne a kwance a kan gadon amma ruhinta is somewhere else. Ta bude idonta a hankali tana kallon bedside lamp din take ajjiye a gefen gadon feeling so lonely tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai kuma tayi murmushi tana lumshe ido yayin da tayi realizing abinda yasa take jin wannan feeling din shine saboda babu hannayen Sadauki a rungume da ita. Sai ta mike zaune da sauri tana kallon tafkeken bedroom din daya ninka nata a girma, sai kuma tayi sauri taja sheet ta rufe jikinta saboda tunawa da tayi babu komai a jikin nata, ta kama rarraba ido kamar wadda tayi wa sarki karya sannan ta jiyo motsin ruwa daga toilet, sai ta koma da baya ta fada kan gadon tana yar karamar dariya ita kadai kamar sabuwar shiga a gidan tababbu. 


But she is not sure ko ta tabu din ne dan bata da tabbas din cewa abinda take feeling yanzu da abinda tayi feeling jiya da daddare is possible. Can it really be this good? Can one night really be worth a lifetime?


It had started with a kiss, a kiss that lasted for like an hour a tunanin Diyam dan lokaci ya tsaya mata ne tamkar yadda tunanin ta ya tsaya. A kiss that loosen up everything na Sadauki, his heart, his brain and his entire body har ya sashi yayi realizing cewa ashe dai shi ba Sadaukin bane ba.


But suddenly sai tayi breaking up the kiss, wai kazar ta zata ci, tana so ne taja ajinta for as long as she can. Ji yayi shi haushin kazar ma yake ji, haushin dukkan kajin duniya yake ji. Ina ma dai bai siyo ba? But dole ya barta ta zauna cin kazarta amma kuma bai fi loma biyu ta samu tayi ba saboda ko da second daya hannunsa bai bar jikinta ba, nema yake yi yayi mata kuka dan haka dole ta hakura da kazar amma sai da yayi al茩awarin biyanta wata.


Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sanda ta tuna cewa she lost some of her clothing a garden din, shima kuma haka. Tayi addu'ar Allah yasa ya fita ya dauke musu kar masu aikin gidan su zagaya su gani. 


Daga garden suka fara slow journey dinsu zuwa daki, branching a palo wanda ba zata iya tunawa wanne palon bane ba kamar yadda ba zata iya tuna yadda akayi suka shigo dakin ba, amma abinda take da tabbas akai shine she didn't come in with any of her clothing, except for ribbon din data daure kitson kanta dashi.


Ya rikirkice mata ya susuce mata acting as if cinye ta zaiyi gabaki dayanta, burinsa kawai ya samu ya kai inda yake son kaiwa amma ita kuma ta hana shi, making him beg, har sai da ta tabbatar he can no longer take it ita ma kuma haka sannan ta sakar masa. 


The first round was wow, and it fused not only their hearts but their souls together. A gurin Sadauki it was mind-blowing and was much more than what he expected. Ya tuna da duk wahalar da yasha kafin ya samu abinda ya samu din, sai yaga cewa ashe bai ma wani sha wahala da yawa ba, ashe prize dinsa yafi wahalar da yasha yawa. He used to call her his heart, yanzu sai yaga cewa that is an understatement, kamar ya rage mata daraja ne dan ita zuciya ai a jikin mutum kawai take, ita kuwa ai ta hada ne da jikinsa da ruhinsa da kuma duk abinda ya mallaka a duniya. And then he called her his world.


A gurin Diyam mamaki abin ya barta a ciki. Dama haka abin yake? Dama haka ake ji? Can this really be possible ko kuma imagination dinta ne kawai. In haka feeling din yake me yasa ita bata taba ji ba sai yau? Bata taba jin koda kashi daya cikin goma na abinda taji yau ba. Duk rayuwar aurenta na baya ba zata taba iya tuna ranar da taje shimfidar mijinta ba tare da hawaye ya zuba daga idanuwanta ba saboda zuciyarta bata son abin. Saboda jikinta baya son abin. With every touch daya taba ta ji take kamar naman jikinta yake yanka and it hurts duk sanda ya kusanceta. Wannan yasa a lokacin take mamakin matan da suke neman mazajensu su makale musu kamar chewing gum saboda ita ta dauka yadda take ji din haka kowacce mace take ji. But now she knows better.


The second round was wow wow, much better than the first, after which bacci mai nauyi ya dauke Sadauki. Sai Diyam ta tashi ta tafi toilet da niyyar tsaftace jikinta, tana jin cinyoyinta kamar tayi tsallen kwado. Ta fara wanka kenan ya murdo kofa ya shigo, tayi saurin rufe idonta ta durkushe a gurin tana jin wata irin kunyarsa wadda dazun duk bata ji ba, ko dan yanzu ta dawo sense dinta? Baice mata komai ba sai ya sunkuya da dagata chalak ya mayar da ita daki ya dora ta a gado daga ita har ruwan jikinta sannan ya dora daga inda ya tsaya tamkar zakin daya kwana bai ci abinci ba, and she found out ita din ma ashe yunwar take ji.


Jin heavy footsteps dinsa ya katse mata tunanin ta, tayi saurin jan abin rufa ta lullube har kanta dan tana jin kamar ba zata iya hada ido dashi ba. Tana jinsa yazo ya tsaya a kanta sai kuma tayi sautin murmushin sa. Ya saka hannu ya gogo ruwa a jikin gashin sa sannan ya daga abin rufar ta ya goga mata a tsakiyar naked bayanta. Ta danyi kara tana matsawa tare da kara chukuikuyewa a guri daya. Ya zauna a bakin gadon yace "ko ki bude rufar nan ko kuma in shigo nima mu lulluba tare" tayi saurin girgiza kanta, yace "to bude in gani" ta sake girgiza kai, yace "Please, fuskarki kawai zan gani" ta fara bubbuga kafafuwanta a kan gadon cikin yana yi na shagwaba sai yace "hmmmm, baki san wannan abin da kike yi tamkar gayyata ta kike yi ba?" Sai ta daina sannan tace "ka tashi ka tafi" yace "ina zani? Dakina ne fa wannan. Ke ki tashi ki tafi" tace "dan Allah ka tashi. Na roke ka" yace "okay zan tashi amma sai naga fuskarki tukunna. Please just a glimpse" kamar ba zata bude ba kuma dai sai ta bude iyakacin fuskarta amma idonta a rufe gam. Ya jima yana kallon fuskarta sai kuma yasa hannu ya shafa doguwar jelar kitsonta and then bai san yadda akayi ba sai ganin fuskarsa yayi akan tata, hannunsa kuma yana cire abin rufar ta. Tayi saurin bude ido tana kwace bakinta daga cikin nasa "kai ba kayi wanka bane ba?" Yace da dasashshiyar murya "ban fita ba, wani wankan zan sake". Sai da kuwa ya sake din. Yana tayar da sallah ta mike ta nannade jikinta da bedsheet sannan ta fita da sauri ta tafi dakinta. 

Toilet ta zarce tayi wanka a gaggauce sannan ta fito ta saka doguwar riga da hijab tayi sallah. Tana son ta koma bacci amma kuma yunwa take ji sosai dan jin cikinta take yi kamar anyi mata yasa. Ta duba agogo taga karfe bakwai, a lokacin kira ya shigo wayarta daga Murjanatu. Ta dauka da sallama Murjanatu tace "amarya, wannan saurin daukan waya haka kamar wadda ta kwana ba tayi bacci ba?" Sai kuma ta kyalkyale da dariya. Diyam tayi rolling eyes dinta tace "kina da abin cewa ne ko kuma kirana kikayi saboda credit yayi miki yawa?" Murjanatu ta daina dariyar tace "Mama ce tace in kira ki in tuna miki cewa karfe goma jirgin mu zai tashi, ki shirya zamu biyo mu dauke ki" Diyam ta dafe kanta, shaf ta manta akwai mother's eve da Maman su Murjanatu ta shirya musu yau a Maiduguri. Lallai Sadauki ba karamin formatting kwakwalwar ta yayi ba. Murjanatu tace "kin manta ko?" Diyam tayi saurin cewa "no no no, ban manta ba, baki ji har na tashi na fara shiryawa ba?"........


Ta cire rigar da tayi sallah da ita ta mayar da wata doguwar rigar wadda bata karasa har kasa ba amma ta kama ta tsam-tsam like a second skin. Yadin rigar mai layi layi ne na kalolin black, dark ash, ligh ash da white. Wuyan rigar ya bude sosai har Diyam tayi tunanin ya zama too reveling, wannan yasa maimakon ta daura dan kwalin sai ta nade shi a wuyanta stylishly yadda ya rufe kirjinta. Ta bude kofa ta fito daga dakinta a dai dai lokacin da taji kara kamar ta faduwar wani abu, followed by another sound kamar ana 蓳ari. Ta dan kara sauri zuwa inda take jiyo sound din sai ta ga daga mini kitchen dinsu ne da yake a sama.


Ta tsaya a bakin kofa leka ciki, abinda ta gani shi ya saka ta rufe bakinta tana hana dariya fitowa. Sadauki ne daga shi sai singlet da short, kusan duk cabinet din kitchen din a bude su ke ga kasan tiles kaca kaca da egg shells da kuma 蓳awon dankali, ga mai cikin kasko a kan wuta shi kuma yana tsaye like three meters away from kaskon hannunsa da spatula yana leka cikin man. Sai kuma taga ya dauko wasu bowls guda biyu, daya ruwan kwai ne a ciki kusan rabin crete, dayan kuma danyan dankali ne guda gudan sa. Sai taga ya dauko dankali guda daya ya saka a cikin ruwan kwan sannan ya dauka da spatula ya jefa a cikin man daya riga yayi over heating. 


Dariyar da take rikewa ce ta kwace mata lokacin da yayi wani tsalle zuwa karshen kitchen din. Dariyar ta ce ta juyo hankalinsa gurinta. Yayi kamar zai yar da bowl din kwan da take hannunsa amma sai yayi saurin ajiyewa ya taho gurinta yana kallon ta tun daga kasa har zuwa sama. Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sannan ta juya masa baya, not realizing cewa ta juyo masa daya daga cikin abinda yake so a jikinta.


Yana zuwa inda take sai ya jawo ta ya hada bayanta da jikinsa, ya saka fuskarsa a wuyanta yana shakar kamshinta mai dadi sannan yace "good morning Sadiyam" bata amsa ba sai yace "wai kunyar ce har yanzu? I tot na cire ta tun jiya ashe da akwai sauranta. Ki gayawa kunyar nan ko ta rabu dake ko kuma inyi maganin ta" ta kara narkewa a jikinsa tana lumshe idonta.  Ya kai baki dai dai kunnenta yace "na dauka kunyar ta tafi lokacin da naji kina cewa 'sadauki more please" ya fada yana kwaikwayon muryar ta. Tayi saurin kokarin janye jikinta daga nasa tana bubbuga kafa tace "lahh! Ni wallahi ban fadi haka ba" yana dariya yace "nayi recording fa, in baki yarda ba mu koma dakina in kunna miki kiji" kamar zata yi kuka tace "ni bana son ji, ni ban fada ba" ya dawo da ita jikinsa yace "I had the greatest night of my life yesterday. And I had the greatest birthday gift. Yanzu wish dina guda daya a rayuwa shine every night na sauran rayuwa ta ya cigaba da kasance wa like yesterday night" ta juyo tana facing dinsa tace "lallai ma. To yau ma ba anan zan kwana ba" ya bata rai yace "ban gane ba" ta saka hannu tana gyara masa hannun rigarsa tace "biki zanje" ya sake bata rai "biki kuma? Bikin wa?" Tana murmushin fahimtar ba ita kadai ta manta ba tace "bikin mu ni da kai. Ka manta yau za'ayi event a Maiduguri? Mama har ta saka a kira ni a tuna min karfe goma jirgin mu zai tashi. Kuma nasan ba zan dawo yau ba, maybe sai jibi". Ta fada da yanayin tsokana. Ya kife kansa a kafadarta yace "bara inje in hada kayana nima" ta ture shi tace "ba fa a gayyace ka ba" yace "duk wanda ya gayyaci matata to kuwa tabbas ya gayyace ni. Anywhere you go I will also go".


Ta kalli kaskon da yake kan wuta tace "me kake dafa mana ne?" Ya kalli kaskon shima, har ya manta ma da cewa girki yake yi, sai yace "dankali da kwai" tayi murmushi kawai sai ya dan ja da baya yana kara kallon shigar jikinta, ya daga gira  yace "if you want to wear a dress like this, wear it with confidence" sai ya saka hannu ya zare dakwalin da ta rufe wuyanta da kirjinta da shi. Ta danji kunya ta sunne kai a kirjinsa sai shi kuma ya daga ta chak ya dora akan worktop, ta karbi dankwalin a hannun sa ta nada masa shi a nasa wuyan tana dariya, yace "ki zauna anan. Let me cook for you" sai ya koma ya leka cikin man sa, ya juyo yana kallon ta fuskarsa abin tausayi yace "ya kone" tayi dariya shi kuma ya harare ta ya dauko dankalin da ya zama kamar gawayi ya jefa a waste basket ya dawo gurinta ya zagaye ta da hannayensa ya dora kansa a kirjinta yace "ban iya girkin ba. I wanted to cook for you" tace "ka iya mana. Let me tell you what to do. Shi wannan dankalin you boil it first with a little bit of salt, sai ka yayyanka shi a kwance yayi shape din circles, shi kuma kwan sai ka zuba masa attaruhu da albasa da spices, sai ka juye dankalin a cikin kwan ka juya su sosai sannan ka dora frying pan akan wuta ka zuba mai kadan sannan ka juye dankalin da kwan ka soya su together on a very low heat, in side daya yayi ka juya dayan side din shima yayi, shikenan" sai ta sauko taje ta kashe wutar da har yanzu man yake kanta yana konewa. Tace "yanzu bara in hada mana, in ka gani yadda nayi kaga watarana kai ma sai kayi mana" sai ya sake daukanta ya mayar da ita kan worktop yace "you seat here, ni zanyi mana, ai na gane".


Har ya koma gaban cooker din sai kuma ya dawo gurinta yana langwabe kai yace "energy na ya kare. I need a refill" ta turo baki tana magana kasa kasa, yace "me kike cewa?" Tace "bayan yunwa nake ji tun jiya banci komai ba kuma kazar ma baka barni naci ba" yace "to ba nace zan biya ki ba, please" ya fara koma mata Sadaukin jiya, tayi kokarin ture shi "kitchen ne fa" yace "kitchen din waye? Gidan waye? Matar waye?" Ta sake makale kafada sai yace "okay, just a kiss then" ya fada yana kawo fuskarsa kusa da tata, ta saka fingers dinta tana tracing gashin girarsa ta zagayo har zuwa sajen sa, ya lumshe ido sai tayi sauri ta juya fuskarsa side tayi kissing cheek dinsa. Ya bude idonsa ya bata rai ita kuma tana dariya yace "gaskiya ban yarda ba. Ni bana son wannan" ta miko hannunta tace "bani kaya na to tunda baka so" yayi mata murmushin mugunta yace "with pleasure" sannan ya dora lips dinsa akan nata.


Hmmmm. Naga wadannan ba yunwar suke ji da gaske ba, kuma na fahimci basu da niyyar zuwa Maiduguri. Gwara in tafi kar jirgi ya tafi ya barni.

[3/28, 10:13 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Seventy Five : Maiduguri

Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din mota a waje, sannan ta ruga daki da gudu tayi refreshing. Tana cikin saka kaya Murjanatu ta shigo dakin tana kallon ta tace "wai sai yanzu kike shiryawa?" Diyam tace "da wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da zanyi amfani dasu tun a gida" Murjanatu ta shiga ta fito da  karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ya dauko hijab dinta tana checking contents din handbag dinta sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta rataya. Suna saukowa Murjanatu tace "baku da abinci a gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci yunwa nake ji" Diyam tace "nima yunwar nake ji, in kin samu nima ina so".


A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin maneman Murjanatu suna magana, ya dora jallabiya akan shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha yazo ya karbi jakar hannun Murjanatu ya je ya saka a mota, Murjanatu tana kallon Sadauki tayi wa Diyam rada tace "baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa masa?" Diyam tana dariya tace "kakan bleaching ba bleaching ba" amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he seems kamar ya kasa daina murmushi. 


Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace "to ya isa haka, shiga mota" ya nuna Murjanatu yace "kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?" Almustapha yace "kaji masu mata, muma dai mun kusa zuwa gurin" Sadauki yace "kun kusa, amma baku zo ba. Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma yanzu kana baya na" duk suka yi dariya, sannan su biyun suka shiga mota. 


Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, sai ya mika hannu ya kama nata, tace "zamu tafi" yace "Allah ya kiyaye hanya. I will be on the next flight insha Allah. Take care of yourself for me kinji? Sai nazo anjima" tayi murmushi tana gyada kai, sai kuma tayi 蓷age on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata hijab dinta ya manna mata kiss a palm dinta sannan ya rufe mata kofa. 


Suna jan mota Murjanatu tace "I will pretend kamar banga komai ba" Diyam ta harare ta tace "to ai dama babu abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi". Suna zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying maman su Murjanatu sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa. 


Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda akayi musu a airport, tun daga motocin da Diyam taga sun zo daukan su harda motar security, Diyam ta kara tabbatar wa lallai 蓷an Umar Mustapha Abatcha ta aura. Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da gidajen kakanni, iyaye da ya'ya. Gidan baban Sadauki a ciki yake, uncles uncles dinsa duk suna ciki, da kuma cousins dinsa da sukayi aure. Ko wanne gida ka gani a cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar kudi daga aljihunsa dan akwai su din.


Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Murjanatu ta ja ta suka tafi part dinsu su yammatan gidan wanda shi a kansa ma gida guda ne. Murjanatu tana ta tsokanar ta "wallahi in kika ce kunya zaki ringa ji ko? To wallahi a gidan nan sai an kusa mayar dake tababbiya" Diyam tayi murmushi, amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba. 


Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan, sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta jawo jakar kayanta zata saka sai Sa'adatu tace "Mama fa ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting" Diyam tayi godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu in yaso in an jima sai ta saka nata. Aka kawo mata kayan ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za'a dan buda mata. Nan take Sa'adatu tayi waya aka zo aka karba kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi. Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta, in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da dankwalin shaddar sannan ta saka bungles na danyen gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi ta rike clutch golden brown nan take ta fito a matsayin Mrs Aliyu Abatcha. Bayan suma su Murjanatu sun gama shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda Diyam tana zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din tayi. 


Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki, kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu, kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba.


Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe ba wai anan ne za'ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka ko kuma family meetings. Sai da akayi la'asar sannan aka fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da Sa'adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace "wow" Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta. Nan take ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun dazu da suka tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply

"Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa ce?"

"Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but not directly"

"To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki godewa Allah Diyam dan yayi miki komai" 

"Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the body.

Imojin heart mai beating

"I love you so much my husband"

"I love you more, my wife".


Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi. Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba'a tashi daga event din ba sai daaka fara kiran magrib.


Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo yake yi mata dan haka akan sallayar da tayi magrib anan ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su suka amsa mata da fara'a suka yi ta tsokanar ta tana rufe fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner mai kyau ta bata a matsayin gift sannan tayi musu sallama Mama ta tafi ta raka ta. Bayan Mama ta dawo ne sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma dabaru irin na zaman aure, wadansu maganar sai Diyam taji sunyi mata nauyi da yawa amma kuma duk tana ganewa kuma tana dauka. In dai Sadauki ne, she can and will do anything for him.


Suna tare su Murjanatu suka shigo, sannan aka gabatar musu da abinci suka hadu a dining din Mama suka ci tare sannan suka dawo palo suka cigaba da hira, Diyam tana ta mamakin yadda Mama take yi da yayanta kamar kawayenta. Suna nan tare Sadauki ya shigo, Diyam ta kalleshi sau daya suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya je ya gaida Mama sannan ya samu guri ya zauna yana amsa gaisuwar kannensa, Diyam ma ta gaishe shi ya amsa yana danna phone dinsa, Murjanatu tayi dariya Diyam ta harare ta.


Mama tace "kaje gurin babanka kuwa?" Yace "eh, muna tare dashi ai tunda nazo, sai daya shiga ciki sannan na shigo". Ya turo wa Diyam text "ki taso mu tafi" ta karanta sai ta dago kai ta harare shi. Ya hade hannunsa alamar roko sai ta gyara zamanta yadda bama zata ke kallon sa ba. Sai kawai suka cigaba da hirar su shida Mama, tana bashi labarin taron da irin matan da suka zo da kuma gifts din da Diyam ta samu. Sai yayi mata godiya sosai sannan ya mike tsaye yana cewa "Fanna kawo min abinci daki na Please" Mama tayi sauri tace "wacce Fanna kuma? Mu ai mun yaye ka yanzu. Halima tashi maza ki hada abinci ki bishi ki kai masa" bai ce komai ba yayi hanyar waje sannan ya juyo a wayence yana kallon Diyam, yayi mata gwalo.


Ta tashi ta hada masa duk abinda tasan zai so ta zuba a basket sannan tace da Murjanatu "tashi ki rakani" Murjanatu ta harare ta "kinga in kika fita daga gidan nan ki kalli gabas, gini na farko da kika gani a gurin shine part dinsa" Adama tayi dariya tace " me dakin gabas kenan, shi yasa mu a gidan nan bamu fiye kallon gabas ba sai in zamuyi sallah" Falmata tace "to ai dan kar mu kalla ace harara mukayi" Mama ta jefi Fanna da remote tayi mata magana da barbarci sai ta mike suka fita tare da Diyam.


Suna fita Diyam tace "kun takurawa bawan Allah nan. Mutum mai hakuri da kawaici irinsa, mutumin da ko hannu aka saka masa a baki ba lallai ya ciza ba" Murjanatu tace "waye hakan? Lallai so hana ganin laifi. To in gaya miki saboda muguntar sa kwanan baya sai da ya saka ni Murjanatu na share gidan nan gabaki daya, tun daga sama har kasa" Diyam tayi dariya tace "daga ji wani babban laifi kika yi masa, shi bawan Allah ne mai sanyin zuciya mai kuma hakuri da yafiya idan aka bata masa" a lokacin suka zo kofar part din Sadauki. Murjanatu ta bude kofa ta tsaya a gefe tace "wacce take fadar maganar tafi wacce ake fadawa sanin cewa ba gaskiya take fada ba. Good night friend" Diyam tayi dariya tace "yanzu zan dawo ai" Murjanatu tace "we will see about that".


Ta ajiye abincin a palo tana studying kyawun gurin, sai ta tafi kofar da jikinta ya bata yana ciki tayi knocking ta tura kofa, yana kwance a kan gado da yawa a hannunsa, dakin cike da sanyin ac da kuma kamshin sa, ya ajiye wayar yayi mata murmushi yana folding hannayensa yace "welcome wife" tace "ga abincin" ya dan bara rai "waye yace miki yunwa nake ji? Ni matata nake so" ya karasa maganar yana langwabe kai, ta fara bubbuga kafa a kasa "ni wallahi bacci nake ji, ni wallahi na gaji jikina ciwo yake yi min" ya mike zaune yace "good. Kinga sai inyi miki massage" ya fada yana tattare hannun rigarsa. Ya nuna gefensa akan gadon yace "come and lay down here inyi miki tausa. You will thank me tomorrow". Ta yi kamar zata yi kuka, ya miko mata hannunsa yana kara marairaice wa sai kuma tayi murmushi ta tafi tasa ka nata hannun cikin nasa.


Da safe sai da kowa ya tashi a gidan aka kuma gama komai har breakfast an gama shiryawa amma babu Diyam babu Sadauki babu kuma labarin su. Anyi ta kiran wayoyinsu kuma da suna shiga amma daga baya switched off. Sai da aka zo yin breakfast sannan Papa yace aje a kirawo su, yana son suci abinci tare gabaki dayansu saboda a yau yake son komawa Canada.


Cikin bacci Diyam taji kamar ana knocking kofa, ta bude ido da kyar saboda nauyin bacci, ta hannun Sadauki daga jikinta sannan ta juya tana kallon fuskarsa so deep in his sleep sai kawai ta dulmiya wajen kare masa kallo tana murmushi. Wani bugun kofar da aka sake yi shi ya dawo da ita daga duniyar kallon Sadauki. Ta mike tana gyara kayan jikinta sannan ta dauki hijab dinta ta saka still cikin baccin ta fita palo ta bude kofa. Murjanatu ta gani a tsaye, ta harare ta tace "kika ce min ba kwana zaki yi ba" Diyam tace "wannan ne dalilin da yasa kika dame mu muna bacci? To bara inje in kira wo shi sai ki maimaita a gaban sa" ta daga hannu tace "Papa ne yake kira, in kuma inje in gaya masa kunce kar a dame ku ne to?" Diyam bata ce komai ba ta koma da sauri ta tashi Sadauki ta gaya masa sakon kira sannan ta fita da sauri a ranta tana cewa "wannan wanne irin abin kunya ne nayi ni Halima".


Da sauri Diyam tayi brush ta wanke fuskarta ta chanza kaya sannan suka tafi part din Papa inda anan ake neman nasu. Tana shiga Sadauki shima yana shigowa, fatar idonsa a dan kumbure alamar bacci bai ishe shi ba. Shi ya fara zuwa ya durkusa ya gaida mahaifinsa sai bayan da ya zauna sannan Diyam itama ta karasa for the first time ta gaishe da surukinta. Ya amsa da madaukakiyar fara'a "Halima, ance min jira kinyi kyalliya da kayan fulani, ni kuma sai nace to lallai zamu yi miki zanen barebari dan mu tabbatar miki kin zama tamu yanzu" duk suka yi dariya har Diyam data rufe fuskarta da hijab dinta. Sai data zauna sannan ta samu damar ganin fuskarsa. Sai a lokacin tayi mamakin yadda akayi duk ganin da take yi masa a hotuna bata fahimci suna kama sosai da Sadauki ba sai data gan shi ido da ido tukuna. Bayan shekaru, banbancin fuskarsa data Sadauki shine hancin Sadauki yafi nasa tsaho sai kuma sumar Fulani da Sadaukin yake da ita. 


Suna zama masu aiki suka matso suna tambayar kowa abinda za'a zuba masa daga cikin menu, kowa ya fada aka fara saving, Sadauki kuma ya fadi nasa dana Diyam dan yasan ba zata yi magana a gaban su Papa ba. 


Sai da suka gama cin abincin sannan Mama ta sake yiwa Diyam barka da zuwa family. Papa kuma ya dora da cewa "ina so Halima ki saka a ranki cewa nan gidan ku ne ba wai gidan surukan ki ba, ki dauke ni a matsayin baban ki ba wai baban Aliyu ba. Saboda baffanki, malam Usman yayi min halaccin da babu wanda ya taba yi min irinsa a duniya. Ya rike min Aliyu tamkar shi ya haife shi dan haka nima zan rike ki tamkar ni na haife ki insha Allah. Wannan shine abinda zanyi in kwatanta abinda Usman yayi min".


"Nasan Aliyu ya baki labarin dana bashi akan rabuwata da mahaifiyar sa amma ban gaya masa dalilin da yasa bayan nayi bincike na gano wanda yake neman halaka su kuma na dauki mataki akan sa ban koma na dawo dashi gida gurina ba. Na barshi ya cigaba da zama a hannun Usman ba tare da yasan nine mahaifinsa ba saboda a lokaci nayi tunanin hakan shine dai dai a gurinsa, maybe I was selfish, but I wanted what is best for my son. Ni mutum ne mai harkoki da yawa wanda ban fiya samun lokacin kaina ba ballantana na iyali na, tarbiyya, nuna soyayya, nuna kulawa ga dan karamin yaro bayan kuma bana tare da mahaifiyar sa ba abu ne da zai samu a gurina ba. Wannan ne yasa na bar shi a hannun Usman da Zainab. Na kuma boye kaina daga  gare shi ne saboda ina son ya zama strong, bana son yasan nine mahaifinsa ballantana ya dora wani abu a ransa ko kuma ya raina marikansa. Sai na nemi alfarmar Usman nace ya koya masa neman na kansa tun yana karami. I used to go to the garage duk sanda na samu dama, I used to watch him work, drenched in oil and sweet, na kan ce a raina "good, yanzu zaka san darajar kowacce kwandala da ka samu". Usman kuma bai taba neman ko kwandala daga wajena ba saboda kula da Aliyu, sai lokacin daya kasa samun admission ne ya nemi in taimaka masa ni kuma nace ya barshi ya sha wahala ya samu da kansa, har yayi fushi dani a lokacin yana ganin kamar nayi tsauri da yawa. Amma yanzu gashi naga result din abinda nayi din, Aliyu yayi turning into more than yadda na saka rai. Yes, na bashi kudi nace ya juya, shekaru biyu bayan nan dana bincika sai naga already yayi doubling kudin da na bashi. A yanzu haka bansan adadin me yake dashi ba. Allah ne kadai yasan me ya tsara wa rayuwar sa amma ni ina saka ran cewa this is just the beginning for him. Allah yayi muku albarka gabaki dayan ku, Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuriya mai albarka".


Duk suka amsa da ameen. Diyam ta saci kallon Sadauki sai taga kansa a kasa amma fuskarsa tana nuna tsantsar farin ciki. Mama tace "a matsayin wedding gift, Papa and I decided to give you two, Aliyu da Halima, gidan mu na Oxford, mun bar muku shi duniya da lahira. Allah ya baku zaman lafiya" nan take gurin ya kaure da murna, siblings din Sadauki duk suka taho suka ringume Diyam suna taya su murna. Ta gefen idonta taga Sadauki ya durkusa gaban mahaifinsa yana godiya, sai taga ya dago shi ya rungume shi a jikinsa yana bubbuga bayan sa.

[3/30, 10:51 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Seventy Six and seven : Karma


Food for thought: Mun tuna da hadisin da Annabi (SAW) yake mana bayani akan healing power da take cikin habbatus sauda? Sannan da hadisin da yake gaya mana cewa nemon tsami yana maganin cututtukan annoba? Zam zam fa? Mun tuna cewa yana maganin duk wata cuta da aka sha shi da niyyar neman waraka daga gareta? Add that to bin ka'idodin kare ka kai daga wannan cutar, kar ki/ka fita daga gida indai bada wani kwakwkwaran dalili ba, in za'a fita din kuma a saka face mask da hand gloves. A guji taba mutane, doorknobs, railers etc a lokacin da ake waje, kar kuma aci ko a sha wani abu, a kuma guji taba fuska, in an dawo gida kuma a cire kayan da aka fita dasu a shanya su a rana sannan ayi wanka kafin a taba komai na gidan. 


Don't forget your morning and afternoon azkar. Insha Allah we will get through this together.

#Don't panic

#Stay safe

#Stay at home


A ranar da yamma su Diyam suka dawo Kano. Tun a jirgi Diyam take ramuwar baccin ta, sai Sadauki ya daga armrest din tsakanin kujerun su ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa shi gyara mata hijab dinta ya rufe mata har kafafunta. Sai da zasu sauka sannan ya tashe ta, suna fitowa already daya daga cikin office drivers dinsa yana jiransu ya dauke su ya kaisu gida. A gidan ma Diyam baccin ta ta cigaba, dan sai yau take huce gajiyar biki, Sadauki bai dame ta ba ya batta tayi baccin ta shi kuma yayi musu order ta abinci aka kawo musu har gida saboda ya tabbatar wa kansa cewa bai iya girki ba. 


Sati daya bayan tariyar Diyam Asma'u tazo ita da Subay'a, ranar Subay'a kamar zata zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman saboda ganin dakin da aka ware a gidan saboda ita. Diyam kuma sai ta dauko gift din data samu a Maiduguri ta ware wadanda take so sannan sauran ta hada da wasu daga cikin kayan lefen ta ta bawa Asma'u tace ta kaiwa Inna a raba wa yan'uwa, cousins dinta duk kowa sai daya samu wani abu. Asma'u kam sai data debi rabonta dama tun kafin a fara tabon. A lokacin ne Diyam ta fahimci cewa Asma'u suna waya da Bassam, she did not comment, idan hakan suke so to ita kam sai dai ta taya su da fatan alkhairi.


Sati biyu bayan bikinsu hutun su Diyam ya kare, ta dauka zasu yi drama da Sadauki akan komawarta amma sai taga shine ma mai taya ta lissafi. Da lokaci ya matso sai taga ya fara hada nasa kayan shima. Tace "aikin fa? In ka bini wa zai kular maka da companyn ka?" Yace "my dear Halima. Kin manta I managed my company for the five years din da nake karatu? Ko kin dauka zan barki tafi ki barni ne?" Tayi dariyar yadda ya fadi maganar kamar wani yaro. Amma kuma tana jin dadi a ranta dan ba karamin faduwar gaba take yi ba a duk lokacin da ta tuna cewa zata koma England school ta bar Sadauki a Nigeria. 


Ta zo ta zauna akan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta ta saka fuskarta a wuyansa tana dan bubbaga bayansa tace "kar kayi kuka, bazan tafi in barka ba kaji habibi" ya shafa mararta yace "habibi yana cikin nan gurin a kwance" ta zaro ido tace "ba wani nan" yace "to ni dai banga kinyi period ba" tace "sati biyu ne fa kadai" yace "koma kwana biyu ne, ni ai nasan irin shukar da nayi kuma nake yi so nake inga na fara girbi" ta boye fuskarta a wuyansa tace "kai dan Allah, sai kace wata gona? Ni bani da komai Allah. Kuma ma ai kaga karatu nake yi yanzu ko? Ko so kake in ke faduwa exams dina?" ya dago fuskarta yace "tare zamuyi karatun ai, muna yi kuma muna cigaba da planting seeds din mu, kafin mu gama in Allah ya taimake mu sai mu girbi ko da biyar ne" ta zaro ido "biyar fa kace? Sai kace kaza?" Sukayi dariya tare. Yace "biyar din ma rage miki nayi ai dan kar ki sha wahala da yawa, in za'a bani zabi twins nake so duk shekara. In akayi twin boys sai ayi girls, sai a sake boys a sake girls, kinga a shekara hudu anyi takwas kenan" ta mike da sauri tana cewa "in yaso a shekara ta biyar sai inga an shigo min da amarya ko" ya jawo ta ta fado jikinsa, ya gyara mata zama tana facing dinsa yana tracing jawline dinta da finger dinsa yace "kina so ta mutu ne amaryar saboda bakin ciki? Ko kuma kina so ranar lahira in tashi da shanyayyen barin jiki saboda na kasa adalci? Kina ganin zan iya jera wata dake a zuciyata Halima?" Ta turo baki tace "da蓷in baki" yace "au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi. Let's taste and find out na waye yafi dadi".


Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay'a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma'u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma'u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace "kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?" Asma'u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace "eh, Bassam da kuke waya dashi Asma'u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje" Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace "Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?" Diyam ta nuna ta tace "gata nan, tayi maka bayani". Asma'u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace "bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?" da sauri Asma'u ta gyada kai.


Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Murjanatu suka zo. Sun taho gabaki dayansu tare da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Murjanatu zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma'aikatan gidan wadanda dama suna nan already, masu kula da tsaftar gidan, masu abinci da masu gadi. A cikin kwana biyu aka gama settling komai, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a palo suna hira sai Sa'adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace "ke Sa'adatu dake Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba" duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace "yanzu haka baban nawa yake magana?" Falmata ta bude hannu tace "yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula yayan masu kudi" Murjanatu ta gyara zama tace "basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin maza" anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk sunyi tsuru tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace "hello Papa" ya gaishe shi yace "maganar nan da ka yiwa su Sa'adatu, ina ganin a hada harda fanna saboda duk tafi su samari. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too" ya juyo yana kallon fanna yace "ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa First, sai nayi approving sannan zasu je gida" bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa.


Murjanatu ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace "wallahi yau na kuma tabbatar wa yaya Aliyu baya so na" su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace "alhamdulillah. Zuciyata fess yau. Karyar tara samari ta kare. 


Satin su Sa'adatu daya suka koma. Su kuma su Asma'u sai da sukayi wata daya sai da hutun su ya kare sannan suka koma gida. Washegarin da suka tafi ne da assuba Diyam tana karatun Alkur'ani akan sallaya sai ga Sadauki ya dawo daga masjid. Ya zauna akan gado yana kallonta har ta idar sannan ta mike ta hawo kan gadon ta kwanta tana lulluba yace "ni fa har yanzu banga tazo ba" bata kalle shi ba tace "wacece zata zo? Bakuwa zaka yi?" Ya yaye rufar yace "yau ba zaki yi baccin nan ba sai kin gaya min akwai ko babu" ta fara yi masa shagwaba "ni me zan gaya maka. Ni babu abinda zan gaya maka" ya cire rigar da yaje masjid da ita yayi astriding dinta yace "ko ki gaya min ta lallami da lumana ko kuma ki gaya min in kinji wuya" ta fara dariya, ya sakar mata nauyinsa shima yana dariya, tayi kokarin ture shi ta kasa sai ya rike hannayenta duk biyun da hannunsa daya, yace "akwai ko babu?" Tace "to ni yanzu me kake so ince maka" yace "cewa zaki yi 'sadauki kayi min ciki" ta kwace hannunta da sauri ta rufe fuskarta tace "la ila, wai kai baka jin kunya ne?" Yana dariya yace "ina ji mana, ina jin kunyar mutane amma bana jin kunyar matata" tace "ni dai bazan iya fada ba" yace "to kinga, in akwai ki gyada kanki, in babu ki girgiza kanki" tayi shiru, yace "akwai ko babu?" Ta bude ido tana kwallon sa ta miko masa hannu tace "kawo tukuici" yace "say it, duk abinda kike so, anything" ta rufe hannun tace "in ka kawo tukuici sai kazo a gaya maka" yace "a bani bashi zan biya" ta turo baki "har yau fa baka biya ni bashin kaza ta ba kuma kake neman a kara maka wani bashin?" Ya dafe kai "wannan kaza, wannan kaza. Yanzu duk kajin gidan nan amma ban biya ba?" Tace "waccan special ce" ya mike yana saka rigarsa. "Zan siyo miki kaza yanzu, zan kuma kawo miki tukuicin ki".


Sai daya loda rigunan sanyi a jikinsa saboda sanyin da ake yi a waje, gashi kuma gari bai ko gama wayewa ba amma haka ya fita, da kyar ya samu kazar saboda duk eateries din kusa dasu basu fito ba sai da ya shiga cikin gari sosai sannan ya samu, ya siyo mata chocolates duk wadanda yasan tana so leda guda sannan ya dawo gida. 


A gado ya same ta har lokacin ta lulluba tana baccinta. Ya zauna a gaban gadon ya bude ledar gasassun kajin ya yanko cinya daya ya bude fuskarta ya kai naman kusada fuskata, ta motsa idonta sannan ta bude idon cikin nauyin bacci tana kallon naman sai kuma ta kai hannu da sauri zata karba sai ya janye yace "kwadayayyiya. In kina so sai kin fada min abinda nake son ji, akwai ko babu?" Ta tashi zaune ta leko tana kallon naman kajin daya bude ya cika dakin da kamshi ga kuma chocolates din daya zube a kasa suma. Sai ta kalleshi ta gyada kai da sauri ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta.


Wannan ciki na Diyam ya sha gata, gayu da soyayya a gurin sabon shiga Sadauki. Rigimar da tayi tunanin zasu yi akan komawarta school basu yi ba sai yanzu akan zuwa school da ciki. "Idan kuma kika fara rashin lafiya a can fa? Ko kuma in kina son ki kwanta ki huta babu gurin kwanciya? In zaki yi amai fa? Ko kuma kina sauri kin makara ki gurde ki fadi" tana dariya tace "baban baby kenan" yace "babies, kar ki rage min daraja mana" tace "okay Baban babies. Wannan cikin fa ba me laulayi bane ba, dame laulayi ne da ni da kaina zan nemi hutu. Ka barni in cigaba da zuwa please kaga yafi inyi ta zama a gida ko?" Amma fir Sadauki yaki, sai yayi enrolling dinta a online classes yadda zata zauna a gida tayi connecting da class dinsu online, duk abinda suke yi ko suke cewa tana ji kuma tana gani a screen din computer dinta, za kuma ta iya yin question a amsa mata, in bata kusa kuma zata iya saving lecture din sanda take free ta bude ta gani. Sai Murjanatu ta koma ita kadai take tafiya school sai Judith, dan ma dai ta samu at last ta koyi driving an kuma bata mota tana zuwa da ita.


Diyam babu abinda take yi sai dai taci ta sha ta kwanta tayi bacci sannan ta kula da mijinta, wanda sun rasa gane a cikinsu waye yafi kula da danuwansa. Kullum tamkar kara wa musu kaunar junansu ake yi. A lokacin ne kuma ya bayyana mata abinda yake shiryawa. "Branch nake so in bude na Abatcha Motors anan kasar, kinga sai inke siyan motocin daga nan ina aikawa dasu Nigeria kuwa zanke siyarwa anan din ma. Tunda muka zo nake processing abin amma saboda kasancewar ni ba dan kasa bane ba sai na kasa samun permit na bude Company, but alhamdulillah yanzu na samu" ya dauko takardar ya nuna mata, ta karba tana karantawa yace "har na sayi fili ma, yanzu zan fara gina gurin tukunna sai in dauki ma'aikata insha Allah" ta rungume shi cikin jin dadi tace "congratulations darling. Allah ya cigaba dayi maka jagora mijina" ya zagayo da ita gabansa yace "ameen. Yanzu problem din shine, bana son harkar bude wannan branch din ta saka ni in kasa saka ido akan wancan, though lafiya lau komai yake tafiya a can din but I need an assistant, someone that I can trust" tayi shiru tana tunani sai tace "Alhaji Bukar bashi da ya'ya? Kayi masa magana mana ya hada ka da mafi aminci a cikin yayansa kaga shima zaiji dadin ka karrama shi" yayi murmushi mai kyau sannan yayi kissing forehead dinta yace "that is one of the reasons I love you, saboda kina da tunani mai kyau. You know what? Kema na baki aiki" ta bata rai tace "wanne aiki kuma bayan wanda already nake dashi?, na matarka?" Yace "you are now my special advisor" tace "duk ka dai part of my job ne as your wife".


Koda yaushe Diyam tana lissafin Saghir a ranta, amma bata taba yiwa Sadauki maganar ba saboda bata son taba masa zuciya, duk kuma sanda suka yi waya da Subay'a sai tayi mata maganar sa, duk da cewa Inna tana yawan kaita ta ganshi. Shima Sadauki bai taba yiwa Diyam maganar Saghir din ba amma shima Subay'a bata barshi gurin tambaya ba. 


A lokacin dasu Diyam suka kammala second semester dinsu a lokacin cikinta yana da watanni biyar, a lokacin kuma Sadauki har ya kammala ginin sabon branch din Abatcha Motors. Cikin Diyam ya dan fito kadan amma baiyi girma sosai ba, abinda ya fito sosai shine kyawunta, dan sanda suka fito daga jirgi a malam Aminu Kano international airport ita da Sadauki hannayensu rike dana juna, duk wanda ya kalle su sai ya sake kalla. Gidan Inna suka fara zuwa, a can suka ci abinci suka huta Diyam tana ta jin kunyar cikin jikinta, anan Sadauki ya barta sai dare yazo ya dauke ta duk da tayi ta rokonsa ya barta ta kwana biyu a nan. Yace "ina garin zaki kwana gida? Ki bari in nayi tafiya sai kiyi zauna ko kwana nawa ne kiyi musu".


A week after that, ya dawo daga office sai taga mood dinsa ba shi da kyau, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera tare da lunshe idonsa. Ta zauna a hannun kujerar tana shafa fuskarsa tace "wanka ko abinci?" Ya dan bude ido ya kalleta yace "bara in dan huta tukunna" sai ta sauka ta durkusa a gabansa ta cire masa takalmi ta hada da briefcase dinsa ta kai sama ta dawo ta sake zama a gabansa ta cire masa safar kafa ta dora kafafun a kan cinyarta tana mammatsa masa ita, tana jan yatsun kafar. Ya dan janye kafar yana cewa "ke! Chakulkuli fa kike min" ta sake jawo kafar tace "tausa fa nake yi maka, haka ake chakulkulin?" Sai tayi masa chakulkulin gaskiya a tafin kafarsa, Yayi dariya yana tashi zaune sosai ya janye kafarsa, sai ta mike tayi kneel down tana murmushi ta faki idonsa ta saka hannunta cikin rigarsa tayi masa chakulkuli tana cewa "gana gaskiyar nan nayi maka to" ya kama dariya har da zamowa kasa ya jawo ta suka fadi tare, sai shima ya yi mata yana cewa "sai na rama wallahi" ta kama kyalkyata dariya tace "wayyo zan mutu, ka bari wallahi, chakulkuli fa kanin mutuwa ne" ya sake ta ta janye daga jikinsa tana dariya, yace "kinci sa'a bake kadai bace ba" ta murguda masa baki sannan ta dawo kusa da fuskarsa tace "wanne mai tsautsayin ne ya taba min lion dina" ya danyi tsaki yace "mutane, yanayin rayuwa, cin amana. Babu abinda wasu mutanen ba zasuyi saboda kudi ba. Babu wanda ba zasu ci amana ba akan kudi. I don't know mai mutanen mu suka mayar da kudi, abinda zaka iya samu yau gobe ka rasa, abinda zakayi bayani a lahira dalla dallar yadda akayi ka samu" tace "me ya faru?" Yace "Saghir zai fito next week insha Allah" taji dadi har cikin ranta amma sai ta boye ta danyi murmushi tace "alhamdulillah. An samu Kabir din kenan?".


Yace "tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba'a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, Nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?" Diyam ta gyada kai, yace "ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir ba kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za'a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money. Yau sai gashi ya dawo, can You believe ge got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa"


"Nayi submitting record din to Ahmad, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama kabir, and Saghir is coming out latest next week".


Not edited. Ayi hakuri da typos.鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍


By


Maman Maama


Episode Seventy Eight and Nine : Finale


Sai da Diyam ta gama da Sadauki sannan ta zauna ta kira Inna ta gaya mata labarin zancen fitowar Saghir. Inna tayi murna sosai tace "Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah yasa karshen wahalar sa kenan shi kuma Sadauki Allah ya saka masa da alkhairi" Diyam tace "ameen Inna" tace "bari in kira gidan Alhaji Babba inyi masu albishir". A ranar zance ya zagaya family, zuwa washegari yab uwa suka fara kiran Diyam suna confirming "da gaske Saghir zai fito?".


Ranar da aka kama Kabir kuwa Hajiya Babba har gidan Diyam ta zo tayi mata godiya ita da sister dinta, hawaye fal idonta, tana ta bata hakuri dan gane da rashin kyautawar da suka yi mata a baya. Diyam ta cika su da abin arziki kuma ta nuna musu babu komai ai yiwa kai ne. Sun so ganin Sadauki suyi masa godiya amma yaki fitowa yace ace musu babu komai. 


Ranar da Saghir zai fito, Friday kenan, a ranar Sadauki yace da Diyam ta shirya tare zasu je. Daga gidan su gidan Inna suka fara zuwa suka dauki Subay'a sannan sannan suka tafi prison din. Suka yi packing a tsallake, Sadauki yace musu su zauna a mota ya shiga shi kadai. Bayan ya tafi Subay'a tace "Mommy nan prison ce ai" Diyam tace "eh" "inda Daddy na yake" "eh" "to Mommy mu shiga mana muhe mu ganshi" "a'a ba shiga zamuyi ba Subay'a" "to Mommy mai uncle ya shiga zaiyi a ciki?" Sai kuma ta bude ido ta ja numfashi tace "zuwa yayi ya fito dashi, dama ya gaya min zai fito dashi, Mommy ki bude min kofa inje gurin su" Diyam ta rike hannunta, sai kuma tayi murmushi tace "Subay'a uncle zuwa yayi ya fito da Daddy, amma kiyi zamanki a mota tunda uncle bai ce ki fito ba, yanzu zaki gansu sun fito tare". Subay'a ta hakura bata fita daga mota ba amma kuma bata zauna ba, in ta leka ta waccan window din sai ta dawo ta leka ta wannan, in kuma taga motsi a bakin kofar gurin sai ta fara tsalle sai taga basu bane ba. Daga baya data gaji sai ta kwanta a backseat tana kuka wai sunki fitowa.


At last sai gasu sun fito. Sadauki ne fara fitowa tare da wadansu mutum biyu wadanda Diyam ta gane a matsayin lawyers dinsa. Sai kuma Saghir ya fito tare da wani wanda ya tsaya yana ta yi masa bayanai har su Sadauki suka karaso mota. Mutanen suka yi masa sallama suka tafi sannan wancan ma yayi wa Saghir sallama ya tafi.


Diyam ta zauna tana kallon shi ta cikin motar. Yayi baki sosai, ya kuma rame sosai, amma wannan kyawun yana nan sai dai babu gayun, kuma shekaru sun fito sosai a fuskarsa harda strings of furfura a gashin sa. Ta gane kayan jikinsa, sune kayan da yake sanye dasu ranar da aka kamashi a airport, she can remember yadda ya fito daga arrivals cikin yana taku dai dai yana jin duniya duk a tafin kafarsa ga kyakykyawar Fauziyya a gefensa but yanzu da ta kalle shi bata ga komai daga cikin characters din wancan Saghir din ba. He looked calm and very different.


Sadauki ne yayi knocking a tagar da Subay'a take, ta dago tana kallonsa sai yace "Subis ga Daddy nan" ta mike da sauri ta kalli kofar prison din, tana hangoshi sai ta kama kokawa da handle din motar sai Diyam ta bude mata central lock tana dariya. Ai kuwa nan take ta bude ta fice daga motar a guje, Diyam ma ta bude ta fito tana cewa "careful Subay'a akwai titi fa". Daga tsallake Saghir ya hango fitowar ta, ya kuma lura da yadda tayo kan titi da gudu dan haka sai shima ya taho da sauri gurin ta zuciyarsa tana bugawa. A tsakiyar titi suka hadu, ya daga ta sama amma sai ya kasa juyi da ita ya sauke ta yana haki yace "kinyi girma Subay'a, Daddy kuma bashi da karfi" sai ta rungume 茩afafuwan sa tana murmushi. 


Ya kamo hannunta suka karasa tsallako titin zuwa inda su Diyam suke a tsaye. Unintentionally hannun Diyam ya sauka akan cikinta tana kallon Saghir, sai taga ya kalli cikin sai kuma tayi sauri ta dauke hannun tana sunkuyar da kanta. Yayi murmushin takaici Yace "amarya" sai ta gaishe shi ya amsa yace "a sake min godiya gurin Mr Abatcha. Na goge sosai Allah ya bar zumunci" ta gyada kai a hankali tace ameen tana kallon Sadauki wanda yake ta danne danne a waya kamar baya jin me suke cewa. Sai ta kalli Saghir tace "congratulations. Allah ya kiyaye gaba" daga haka ta bude mota ta koma ciki. Sadauki ya dago kansa yana kallon Saghir ya  nuna masa mota yace "Bismillah, sai mu ajiye ka a gida ko?" Sai Saghir ya kalli Diyam, ya hadiye wani daci a ransa ya girgiza kai yace "no, thank you. Kar in takura muku maybe akwai inda zaku je. Bara in hau napep kawai" Sadauki ya daga kafada kawai, sai ya tare masa napep din ya kuma biya kudi sannan ya yi wa mai adaidaitan kwatancen sabon gidan Alhaji Babba, tunda Saghir din bai sani ba. 


Saghir yace da Subay'a "zaki bini gidan Alhaji?" Ga mamakin su sai ta kalli su Diyam ta kuma kallonsa sannan ta girgiza kai tace "no, Aunty Asma'u tace yau Uncle Bassam zai zo, kuma na bashi sakon abubuwan da zai taho min dasu in zai zo, ka ga kar yazo bai same ni ba" Sadauki ya bude ido yace "Subis akwai zarar magana sai kace wata babba" Saghir yayi murmushi yana kallon inda Diyam take yace "gado tayi ai". Har adaidaitan zai ja sai Subay'a tace "Daddy zan kawo maka ziyara gidan ka".


In silence suka bar gurin kowa yana lissafe lissafe a zuciyarsa. Sai can sannan Sadauki yace "ba zan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata. Bana son drama, nafi sonsa a nesa damu" bata ce komai ba, ya cigaba "amma zanyi masa komari ya samu kudin sa na gurin Kabir" Diyam tayi sauri ta kalle shi tace "kudin ka dai, ai kudinka ne" ya girgiza kai yace "nayi signing takarda cewa na bar masa kudina daya dauka, so legally yanzu kudin sa ne ba nawa ba. I have already talk to my lawyers, za'a siyar da kadarorin Kabir maybe za'a samu part of kudin amma nasan ba za'a samu gaba daya ba" Diyam taji dadi sosai a ranta tana yabawa kyawun zuciyar Sadauki, kamar yadda ya taba fada mata shi fire ne da ice, duk da wadda kazo dashi za'a tarye ka.


Tayi masa godiya sosai sannan yace "kin san wani abu? Ni da Saghir are alot alike" ta bude ido dan ita bata ga hadin su ba bayan kasancewar su musulmai kuma half fulani tace "ta yaya?" Yace "kinga ni da shi duk only sons ne a gurin iyayen mu. Kuma iyayen mu suna son mu sosai sannan sun nuna mana soyayya in their own different ways. Duk kanin mu iyayen mu sun bamu kudi, the only difference is yadda muka yi da kudin da suka bamu. Sannan kuma duk muna sonki" ya fada yana kallon ta, tayi saurin girgiza kanta tace "he doesn't" yace "he does. I saw it in his eyes yanzu da yana kallon ki" 


Tayi saurin kawar da maganar ta hanyar cewa "kuma duk ku biyun kuna da kanwa mai suna Murja" yayi dariya yace "ni kanwa ta Murjanatu sunan ta ba Murja ba, kuma ni nafi shi son kanwa ta" tace "ita kuma duk duniya gani take yi kafi kowa kinta" and they laughed together.


          *************************


Saghir ya juyo yana kallon Subay'a, yana kallo Sadauki ya kama hannunta ya bude mata kofa ta shiga mota sannan shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da pregnant Diyam. Yayi sauri ya rintse idonsa tare da dafe kansa yana jin hawaye yana zuwa idonsa. Bai dauka har yanzu Diyam tana da gurbi a zuciyarsa irin haka ba, ya dauka ba zaiji komai ba inya ganta musamman saboda kokarin da mr Abatcha yayi masa, amma ita zuciya bata da linzami dole ya ja baya dasu ya daina ganinsu, ko kuma abinda yaji din yana da alaka da yadda Diyam din ta zama? Irin kyawu da cikar halittar da tayi? Wai hakan na nufin da ace ya kula da ita tsahon shekarun da suka yi a tare da irin haka zata zama kuma maybe da zata so shi? Lallai gaskiyar hausawa da suka ce tun ranar gini tun ranar zane, shi kuwa nasan ginin ya bushe dole sai dai ya hakura da zanen ko kuma ta sake sabon gini, sabon ginin wata rayuwar. 


But with who? Wannan wata tambaya ce for another time. Maganar da Subay'a ta fada ta dawo masa zuciyarsa "zan kawo maka ziyara gidan ka" wanne gidan? Shi fa yanzu ko gidan kansa ba shi da shi, wayake ma maganar gida, shi ko kwandala bashi da ita. Bashi da komai sai freedom dinsa, kuma ya dauki freedom din nasa ya zama another chance at life. Chance din kuma da insha Allah zai yi amfani dashi sosai yadda har sai mutane sunyi mamakinsa. Yadda har sai iyayensa sunyi alfahari da shi. Iyayen da a wancan lokacin ya wofantar ya wulakanta, abinda yake tunanin shine dalilin zuwansa inda yaje ba wai Diyam ba.


Maganar mai napep ce ta dawo dashi hankalinsa, yace "yallabai munzo" ya leko dakansa yana kallon gurin yace "nan ne?" Mai napep yace "nan dai yayi min kwatance, yace jaen layin shago tara, gashi nan kuma har mun kusa fita daga layin tunda mun fara hango diga. Sai dai ka sauka ka tambaya" Saghir ya sauka yana kallon gurin, not that bad. Mai adaidaitan ya miko masa dari biyar yace "dubu biyu ya bani, ga dari biyar ka sha ruwa kai ma" Saghir ya karba harda yi masa godiya sannan ya tafi gurin wasu mutane su uku da ya hango a kasan bishiya ya gaishe su yace "dan Allah tambaya nake yi, gidan Alhaji Babba, bai dade da dawowa unguwar nan ba" duk suka ce basu sani ba, yayi gaba ya cigaba da tambaya amma babu wanda ya sani sai ya juyo ya fara retracing ta inda suka shigo yana yi yana tambaya, ga rana gashi dama jikin sa duk babu karfi. 


Da kyar ya samu wanda yace "inda akayi biki watannin baya?" Da sauri Saghir yace "eh" sai aka hada shi da yaro suka koma can inda ya baro, suka je har gaban wani gida sannan yaron ya nuna masa ya juya. Ya tsaya yana kallon gidan, a tsahon rayuwarsa bai taba tsammanin duniya zata yi juyawar da har nan gidan zai koma shine gidan baban shi ba, gidan ma kuma gidan haya, gidan hayar ma kuma Diyam ce ta ke biya masa.


Ya shiga soro yayi sallama, Hajiya ya hango ta fito daga wani guri daya ga kamar kitchen tana amsa sallamar hannunta rike da wuka tana goye da wani yaron da bai sani ba a bayanta. Ta yarda wukar tana kiran sunan Alhaji, Alhaji ya fito, Hajiya yalwati ta fito, sai ga yaran gidan suma sun fito daga wani daki duk suna binsa da ido. Shi ya karasa shigowa, ya tafi gaban mahaifinsa ya durkusa amma sai ya kasa gaishe shi sai kuka ya kwace masa. Alhaji ya sunkuya gabansa ya jawo shi jikinsa ya rungume shi shima yana hawayen yace "bansan yau zasu fito da kai ba Saghir, da ko ba zan iya zuwa da kaina ba da sai in gaya wa mahaifiyarka ta je ko ta tura aje a taho da kai" Saghir ya goge hawayen sa yace "Mr Abatcha ne yaje ai, dashi da Diyam da Subay'a" ya fada yana jin dacin zuciyar dazu yana dawo masa. Alhaji yace "madallah dasu. Allah yayi musu albarka ya jikan Usman". 


Nan fa gida ya rude da murnar dawowar Saghir, dan ma yanzu duk yaran babu saura kadan. Hajiya Babba ce ta kama shi ta kaishi daki, Hajiya yalwati kuma ta dora masa ruwan wanka, alhaji kuma ya aika a siyo masa nama da lemo kafin a gama abinci. Babu laifi suna cikin rufin asirin su duk da cewa alhaji har yau bai kuma gwada kasuwanci ba amma matansa suna yan sana'o'in su sannan yayansa mata da suke aikin gwamnati suna kokari gurin taimaka musu sosai, haka ma surukan gidan lokaci zuwa lokaci suna aiko musu da kayan abinci ko kuma suttura. 


A dakin Hajiya ya huta, naman da Alhaji ya siyo masa sannan yayi wanka ya chanja kaya zuwa wanda Hajiya ta ajiye masa akan gado. Sai ta kunto yaron bayanta ta mika masa. Kallo daya yayi masa yasan waye, sai kawai ya ajiye shi a gabansa ya sunkuyar da kai, tace "sunan babanku ne dashi, Jawad ake ce masa" yaron ya rarrafa da sauri yabi bayan Hajiya yana kuka alamar bai san shi ba.


Dakin da yake soro, wanda kuma yake da kofa a waje shi dama Alh yasa aka gyara tun sanda yaji labarin dawowar Saghir gida. Aka shimfida carpet aka saka katifa, wardrobe, da kuma standing pan. Nan ne ya koma dakin Saghir. 


Kwanan Saghir biyar ya warware, duk da dai babu inda yake fita sai yan'uwa da suke ta zuwa yi masa murna. Inna ma tazo ita da Asma'u da Subay'a, suka kuma bar Subay'a anan tayi weekend tare da mahaifinta da kakannin ta. A ranar ne Alhaji ya kira shi dakinsa. Suka zauna sai ya dauko wata leda ya miko masa, Saghir ya karba ya bude sai yaga kudi a ciki, ya zaro ido "Alhaji kudi ai, kudin menene wannan?" Alhaji yace "kudi na ne, sauran kudin gida na ne da kuma abinda na samu daga gadon Usman, su nake ta ajjiye dasu da niyyar duk ranar da ubangiji ya sake baka dama a rayuwa ya saka ka fito daga prison nima zan sake baka dama in baka su kayi jari" Saghir yayi saurin girgiza kansa hawaye yana bin idonsa yace "Alhaji kar kayi haka, ka bani kudi sau ba adadi ina salwantar wa, kai ma kana bukatar kudin nan alhaji, kana da iyali kaima. Ka rike kudinka alhaji ka kula da kanka da matanka da kanne na" Alhaji yace "da wanne karfin Saghir? Ni ai tawa ta kare, karfi na ya kare, dan haka kai na dora wa wannan nauyin ka juya wannan kudin ka kula da kanka sannan ka kula dani da iyayenka da kannenka, kuma ka cigaba da kula dasu ko bayan rai na ne".


Saghir ya karbi kudin ya rike yana jin nauyi a zuciyarsa "anya kuwa akwai soyayya sama data iyaye?"


Alhaji yace "akwai kuma wata magana da nake so muyi. Ina so ka kawo karshen rashin jituwar da take tsakani na da danuwana, ina son ka auri Suwaiba" ya dago kai yana kallonsa, Alhaji ya gyada kai yace "ta inda ake hawa tanan ake sauka. Tunda kuka bata dan haka ku zaku gyara". Sai Saghir yaji Fauziyya ta fado masa a ransa. Bayan ya bata takardarta sun rabu, daga baya sai ta koma tana gaya masa cewa tana da cikinsa, ta kuma ce zata haifi cikin za kuma ta jira shi as long as bata samu miji ba har ya fito sannan kuma yana da sha'awar mayar da ita. Bayan ta haihu kuma ta kai masa babyn ya gani. And after seeing Subay'a rike da hannun Sadauki, baya jin zai kuma barin wata yar tasa a wani gidan. Dan haka indai Fauziyya bata yi aure ba to sai dai ya hada su ita da Suwaiba. 


Wata daya bayan nan Diyam tazo yi musu sallama zata koma Oxford, England. Washegarin zuwanta kuma alert ya shigo masa. Ya bude ido yana kallon kudin cike da mamaki ya tafi da sauri ya nunawa Alhaji. Alhaji yayi murmushi yace "Diyam ta gaya min jiya, kudin da Kabir ya gudu dasu ne aka dawo maka dasu. Zabi kuma ya rage naka kasan me zaka yi dasu".


Abinda Saghir ya fara yi shine ya dauki kudin da Alhaji ya bashi ya sayi gida madaidaici amma me kyau. Ba shine ya tare a gidan ba, Alhaji Babba da iyalin sa ne suka tare. Sai kuma ya sayi karamin fili a kusa da gidan a matsayin nasa "sai in zauna a kusa daku yadda zanfi jin dadin kulawa daku" next sai yaje har gidan Kawu Isa ya durkusa ya bashi hakuri sannan ya nemi ya bashi auren Suwaiba. Sai kuma ya tafi gidan su Fauziyya itama ya nemi auren ta. Amma duk kan su yace sai shekara mai zuwa idan ya samu nutsuwa sosai.


Daga nan sai ya tafi kantin kwari, tsofaffin shagunan Alhaji wadanda wuta ta cinye babu komai sai ginin, shima ginin duk ya mutu an sace kwanukan. Cikin kwanaki kadan ya tayar da ginin su, yayi komai ya saro kayan duk da yasan Alhaji yana siyarwa ada da kuma kayan da yasan zamani ya zo dasu ya zuba a ciki. Sannan ya nemo tsofaffin yaran Alhaji wadanda suke kular masa da shagunan a da ya dawo dasu dan su suka san kan kasuwa, shi kuma ya zauna cikinsu dan shima ya fahimci harkar.


Watanni kadan abubuwa suka warware wa Saghir, ya hada kudin neman aure ya kai gida biyu aka saka masa rana watanni takwas masu zuwa za'ayi duk a tare, sannan kuma ya fara ginin gidan sa a hankali. Gidan da yake da yakinin zai zamanto tushen sabuwar rayuwa a gurin sa.


    ****************************


A lissafin Sadauki so yayi in sun bar Nigeria su fara tafiya Canada suyi kwana biyu tukunna, amma Diyam ta tubure masa ita bata son zuwa, ya gane abinda yasa bata so, ita kunya take ji ake ganin ta da ciki. Yayi dariya "to wai ke banda abinki, ni fa banga abin kunya anan ba, kowa ma fa yana yi" ta juya masa baya tana kallon Subay'a a cikin swimming pool tace "kuma kawai sai in je gidan inyi ta yawo da ciki suna kallona?" yace "baiwar Allah, idan baki je da ciki ba in kika haihu dai ai dole zasu ganki da dan ko? Ko shima cewa zaki yi ba ke kika haifa ba?" Tace "ai kuwa in naje gidan da baby to har in bar garin ba zan dauke shi ba" ya rike baki "to waye zaiyi feeding dinsa?" Tace "sai ya sha madara" ya kwanta akan camp bed din da yake zaune akai ya rufe ido yace "you are impossible Diyam, ke fulatancin kamar a kanki ya kare" ya sake cewa "kiyi addu'a to, kar a saka bikin su fanna kafin ki haihu, sai muga yadda zakiyi da cikin a gurin biki" tayi saurin cewa "Allah ya kiyaye, insha Allah sai na haihu". Sai ta jawo kujerar da take kai kusa dashi tayi tagumi tana kallon sa, ya bude ido yana kallon ta yace "what?" A hankali tace "I want to kiss you, kuma Subay'a tana kallon mu" yace "ohh, a wannan bangaren  kam kin ajiye fulatancin ko?" Sai kuma ta rufe ido tana dariya. 


Addu'ar Diyam dai bata karbu ba, dan suna komawa makaranta aka saka ranar bikin su Sa'adatu kuma wata biyu kadai aka saka, meaning cikin Diyam yana da wata takwas kenan za'ayi bikin. A dole Diyam ta taho Maiduguri lokacin bikin da katoton cikinta, Sadauki yana ta yi mata dariya amma sai ta maze da shiga harkokin bikinta sosai ta rike role dinta na matsayin babbar yaya. Da ita akayi shawarar komai, da ita aka sayi komai, wani abun ma in ana nema sai Mama tace azo wajen Diyam.


Su Inna da Mama da Asma'u ma duk sunzo gurin bikin sun kuma Kawo wa amaren gift sosai har sai da Maman su Murjanatu tace "kayan nan anya basu yi yawa ba Amina?" 


Aka daura aure aka kai amare gidajen su. Sa'adatu ta auri Aminu an kaita Abuja. Falmata kuma Saifullahi mutumin Kano amma mazaunin Canada dan haka can zasu koma, Fanna kuma ta auri cousin dinta Al-mustapha zasu zauna anan Maiduguri amma zata zauna a gurin su Diyam ta karasa karatun ta.


Bayan su Diyam sun koma England sai hankalinsu kuma ya koma kan haihuwa, Sadauki yana ta rawar kai, duk zuwa asibiti tare suke yi idan kuwa yaga namiji ne zai duba ta sai ya ja abarsa su bar asibitin. Twins ne kamar yadda Sadauki yake ta addu'a. Diyam tayi tunani sai taga cewa ba zata iya tuno yadda haihuwa take ba tunda bata yi labor a haihuwar Subay'a ba, haihuwar twins kuwa ba zata iya tuna yadda abin ya kasance ba dan haka sai ta shiga maternity classes, anan ta fahimci komai ta kuma yi browsing wasu abubuwan ta sake fahimta. 


Abinda take tsoro guda daya shine shigar Sadauki gurinta in tana labor, tasan kuma za'a bashi option din shiga kuma tasan zai shiga din. Sannan tasan in dai ya shiga sai ya hargitsa daga ita har me karbar haihuwar kuma in yaga wahalar da ake sha a gurin haihuwa sai sunyi rigima kafin ya barta ta samu wani cikin. Ta kuma san yadda yake son yaya, dan haka ta yanke shawarar yi masa dabara yadda ba zata haihu a gabansa ba saboda ta haifa masa yaya as many as yadda Allah ya basu.


Ranar data fara jin alamar labor da daddare sai taki nunawa Sadauki, da safe kuma sai tayi pretending as if bacci take yi har ya gama shiryawa a hankali dan kar ya tashe ta, ya zo yayi mata kiss ya fita. Sai bayan fitarsa sannan ta tashi ta dauko jakar tafiya asibitin ta wadda already ta riga ta shirya ta ta kuma yi driving kanta zuwa asibitin. Sai da taje suka aunata suka kuma tabbatar mata da cewa haihuwa zata yi sannan suka bata daki suka kuma nemi su kira mijinta amma ta hana su tace sai ta haihu tukuna.


Ta sha wahala ba kadan ba, Sadauki ya sha kira kamar sunan sa zai kare ta kuma yi nadamar kin gaya masa dan da yana kusa  ko ganin sa in tayi zata ji dadi. A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifi namiji first, sai data huta sannan labor ya sake dawowa ta haifi mace. Ana miko mata su taga fuskar babansu amma fatarta, sai dai namijin bai kai macen haske ba.


Sai da aka gama garata aka kuma gyara babies din ta kuma danyi bacci kadan ta huta sannan tace su kira shi. 30 minutes after kiran nasa sai gashi ya shigo asibitin hakan yasa Diyam ta tabbatar da cewa yayi breaking every traffic rule a hanya saboda sanin nisan asibitin daga office dinsa. 


A rikice ya bude kofar dakin da aka nuna masa ya shiga. A tsaye ya ganta a gaban window ta juya masa baya. T-shirt dinsa ce a jikinta, wadda ta kawo mata har zuwa rabin cinyarta, gashin kanta a barbaje wani ya sauka a bayanta wasu akan kafadun ta wasu kuma sun zubo kan kirjinta. "Diyam" ya fada cikin sarkewar murya. Ta juyo tana kallonsa, hannunta rike da jariri tana rocking a hankali, fuskarta da faffadan murmushi. Ya karaso cikin sassarfa ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yace "don't you ever do that to me again" ta kwantar da kanta akan kirjinsa tace "am sorry my Lion. Bana son in tayar maka da hankali ne" yace "kinsan tashin hankali da naji kuwa? Kinsan da yadda nazo asibitin nan kuwa? I tot karya suke yi min da suka ce lafiyar ki kalau, I tot ba zaki iya haihuwa ba tare da ni ba" tace "I missed you sosai, nayi ta kiran sunanka" ya danyi dariya yana dago fuskarta da hannun sa daya, taji kunya ta mayar da fuskar kasa.


Ta zaunar dashi akan kujerar da take dakin ta mika masa babyn hannunta, ya dan leka cikin diaper dinsa fuskarsa kamar zata yage dan murmushi. Ta dauko dayar da take bacci a kan gadon su ta mika masa itama. Ya rike su hannu bibbiyu inya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan ya kasa tantance wanne yafi kyau a cikin su. Yayi musu addu'a. Tana tsaye a gabansu tana kallon su sai ta fara buga kafa cikin shagwaba, ya dago kai yana kallon ta cikin alamar tambaya sai tace "ni a ina zan zauna, sun tare min gurin zama na" ya daga babies din da sauri yace "zo ki zauna akan cinya" ta tafi ta zauna tana karbar daya, ta rike ta da hannun ta daya dayan hannun kuma ta zagayo wuyansa dashi. Sun jima a haka suna kallon kyautar da Allah yayi musu sannan yace "Baffa ne da Ummah. Baki ga yadda suke ta kokarin rike hannun juna ba?" Diyam tayi dariya tace "babu ruwana sai na gaya wa Inna" yayi murmushi yace "so kike ta biyo ni da muciya?" Sukayi dariya a tare. Sai ta kwantar da kanta a wuyansa shi kuma yayi kissing forehead dinta tare da sauke ajjiyar zuciya. A hankali yace 


             "ALHAMDULILLAH"


Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya. Allah ya kara salati ga fiyayyen halitta (SAW) Allah kuma yasa muna da rabon ganin sa baki daya.


Godiya ga fans dina wanda na sani da wanda ban sani ba a duk inda suke, alkhairi ya kai muku har dakunan ku, ina sonku sosai da sosai, idan babu ku to kuwa tabbas babu ni.


#MyWattpadpeople, thank you for all the votes, the comments and the encouragement.


#MamanMaamaNovels na Facebook ina godiya da soyayyar da kuke nuna min a duk books dina, ina ji daku sosai mazan ku da matan ku.


#MamanMaamaNovels groups 1,2,3,4,5 na WhatsApp, ina ji daku tamkar nama daya a miya. Allahu ya bar kauna.


The ladies at #Shatuuskingdom, #zaurenBiebeeIsa, #KDM soldiers, #ZeenatNovel, #SameenaAliyuNovels, da sauran groups din da nake ciki da wadanda ma bana ciki, ina godiya kwarai da gaske. Allahu ya bar zumunci.


Zaku sake ji na da wani labarin, amma banan kusa ba, maybe sai 1-1-2021 maybe kuma kafin nan. In kuma babu rabo to Allah ya hada fuskokin mu a aljannatul Firdaus. Allahumma ameen.


Please pray for me a duk sanda labarin mutuwa ta ya riske ku.


ILYSM.




Post a Comment

0 Comments