TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 23

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____23💎



  Da sauri suka dakatar da ita, "a'a hajia Aisha akan hanya muke zamuje   legas ne wajen d'auko kayayyakin mu sai hanya tabiyo damu ta wajen gidanki shine mukaga bai kamata muwuce batare da mun kawo maki ziyara ba,


"Kai amma naji dad'i sosai wlh, yau sha rabo? Gaskiya duk da haka yakamata ace kun shigo daga ciki ko ruwane kusha ko?"


"Kiyi hak'uri hajia Aisha sauri mukeyi next time idan munzo zamu yimaki wuni" duk da bahakan tasoba cikin murmushi tace "shikenan na fahimceku dama 'yan kasuwa haka suke basada lokacin kansu" dariya sukayi had'e da tafewa "yo kinga laifinmu? Kema ai bayadda bamuyi dake akan ki shigo adama dake ba kikak'i"


"Ai very soon zaku jini but not now? Lokaci nazuwa" dariya sukayi gaba d'ayansu tare da komawa cikin mota ita kuma Ummi ta koma cikin gida had'e da cewa ina zuwa kud'an jirani pls


Bayan minti biyu sai gata tadawo rik'e da 'yan matsakaitan ledoji guda uku a hannunta, d'aya snacks ne masu yawa da takeyi tana ajewa saboda irin bak'in dake zuwa unexpected ta biyun kuma drinks ne aciki sai kuma ta ukkun turarukkane masu k'amshi da tsada, gambun motarsu na baya tabud'e ta ajiye ledojin sannan tadawo wajen da hajia maijidda kezaune a sit d'in driver tace


"To matafiya ina godiya da wannan ziyara taku, Allah ya tsare hanya" juyawa tayi takalli ledojin data ajiye masu sannan tasake juyo tana kallonta


"Amin ya Allah hajia Aisha ke kullum bakya gajiya da yimana hidima"


"Haba nothing much fa? Ai yiwa kaine"


Daga haka sukayi ban kwana da ita zuciyoyinsu na masu yabon kirki da kuma kyawawan halayen Aisha,


Ummi nakomawa cikin gida tanufi kitchen aduk  tsawon lokacin nan Basmah na nan zaune tana kuka a inda tabarta taye Ummi tayi cike da mamaki sannan tasa hannu ta rik'o hannun Basmah ta mik'ar da ita tsaye ahankali take janta har suka isa dining table, hannunta ta saki tajawo kujera, ta sake rik'o hannunta ta zaunar da ita akai, plate d'aya ta d'auko ta ajiye a gabanta tabud'e ferfesun kifin tazuba mata sannan  ta sake d'auko cup shima ta cikasa da kunun ta ajiye mata, da sauri Basmah ta d'ago kai tana kallon Ummi dake tsaye akanta tayi folding hannayenta tana kallonta, murmushi tayimata had'e da lumshe idanuwanta tana nuna mata plate d'in dake gabanta


"Bismillah, yimaza kici kar yunwa ta tab'a munke" idanunta na hawaye tace


"Ummi ni bazan iyaba" 


 Su batool dake zaune afalo tare da yaya mahmud suka dinga yimata dariya, cikin b'acin rai Ummi tajuyo 


"Gaba d'ayanku  kub'acemun da gani ko ranku ya b'aci, Babana kaje ka shirya akwai inda nake son aikinka" suna fita tajawo kujerar dake kusa da Basmah ta zauna, kallonta tayi had'e da d'ora hannunta akan nata dake saman table d'in ta rumk'e  sannan tace


"Basmah banyi maki fad'a saboda bana sonki ba balle kizauna kina kuka har na kusan minti 30, nayi makine saboda kuskuren da kika aikata, ba lallene kiyarda da abunda zanfad'a ba shiyasa na zaunar dake kici abincin da hannunkine ya sarrafashi kiji yanda yake kozaki yarda da cewa kuskurenne yajawo nayi maki fad'an"


"Ni nayarda nayi kuskure amma ni banason fad'a, saboda mom d'ina bata saba yimani shiba ko kad'an" shiru mom tayi tana kallon yanda take fad'a mata wannan maganar ido da ido kafin can ta sake wani dogon numfashi tace


"Shikenan Basmah bakyason fad'a ko? Naji bazan sake yimaki ba, tabbas bazan sake yimaki fad'a agidan nan ba, to amma ke kuma yazame maki dole kinatsu kibi duk wasu k'a'idojin dana shimfid'a maki ba tare da rashin kunya ba, if not kuma bazan dena yimaki fad'aba ta k'arasa maganar had'e da mik'ewa tabar falon zuciyarta na rad'ad'i, har ga Allah bataso faruwar haka tsakaninta da itaba, amma ya zatayi idan har bazata jurewa ganin Billy acikin yanayi irin wannan ba to don me zata k'yale  Basmah acikin wannan halin, koba komai amana take agareta kuma dole Allah zai tambayeta akan amanar daya bata, 'yar mijin tace hakk'ine akanta takula da tarbiyarta koda mahaifiyar ta nanan balle kuma da batanan.


Tana wucewa Basmah tagoge hawayenta 


"Wallahi babu wanda ya isa yasa inbi k'a'idojinshi tunda bashi ya haifeni ba kuma indai rashin kunyace yanzu aka fara ganinta"


Tunda sassafe mom ta tashi cikin wani irin farin ciki tana jiran isowar 'yar uwarta kuma aminiyarta wato hajiya kilishi, sosai su papi sukayi mamakin yanda take fara'a saboda tunda tadawo gidan cikin bak'in rai take amma sai gashi yau takasa zaune takasa tsaye saboda tsabar farinciki, kallon hajia kaka papi yayi yace


"Baby anya yau lpy 'yarki ke wannan farincikin, shin kodai addu'ar muce takarb'u"


"Ga alama domin yau tunda safe na lura da yanayin da take ciki na farinciki, Allah yasa sauyawar mummunan halintane zuwa kyakkyawa zai bayyana"


"Amin ya Allah" juyowa papi yayi yana kallon mom dake tsaye abakin window tana jiran isowar hajia kilishi karaf suka had'a ido dashi


"Zonan usain", saida tasake kallon windown sannan taje gabansu ta zauna"


"Gani papi"


"Dama cewa nayi lpy kike wannan zagaye zagaye cikin farinciki?, ko alhaji ne ketafe" cikin farinciki tace


"Lahhh...papi na manta bangaya maku ba, ai jiya mukayi waya da 'yar uwata kilishi tace yau tana nan isowa harma tace ingaisheku sosai" cike da farinciki daya bayyana d'auke a fuskokinsu sukace


"Shine baki fad'aba sai yanzu, eh lalle dole zakiyi farinciki yaushe rabo?, Allah ya kawota lpy kotasa kidena wannan shashanci kikoma gidan mijinki ki rungumi 'ya'yanki" sanin yanda take da ita yasa suka dena mamakin farincikin da takeyi.


_WAYE HAJIA KILISHI_


'Yace ga aminin papi kuma shak'ik'in abokinsa wanda yarasu tun tana k'arama, hakan ne yasa papi yanemi alfarmar mahaifiyar ta da kuma 'yan uwan mahaifinta da abashi ita tadawo hannunsa da zama tare da yimasu alk'awarin zai rik'eta amana tamkar 'yarsa, kasan cewar kowa yasan halin papi mutumen kirkine kuma ansanshi tare da mahaifinta yasa batare da wani dogon tunani ba aka bashi ita shikuma ya karb'eta hannu biyu ya had'ata da 'yarsa Hussaina, kasan cewar halinsu yazo d'aya sai sukayi matuk'ar shak'uwa da junansu ta yanda hatta baccima baya rabasu, suna son juna sosai kuma duk abunda zasuyi atare sukeyin abunsu batare da sun bari kowa ya sani ba, a tsawon rayuwarsu babu abunda ya tab'a rabasu sai aure wanda hakan ne ya sanyasu rabuwa da juna badon sun soba, amma duk da haka babu wanda ke iya zartar da wani abu agidanta batare da taimakon d'an uwansa ba, duk abinda d'aya zaiyi sai yanemi shawarar d'aya akai hakan yasa akoda yaushe suke mar

ari da d'okin ganin junansu, hajia kilishi tun tana k'aramarta fitinanniyar yarinyace ta iya makirci da tuggu kala-kala, sam bataso taga anzauna lpy arayuwarta kuma bata shakkun kowa akan duk abunda tasa agaba, hajia kaka kad'ai da papi take d'an shakkar yin abu a gabansu koshi don tasan taka mata burke zasuyi, agabansu tana nuna halayen kirki ko kad'an bazata tab'a yin abun asshaba, shiyasa suke matuk'ar ganin mutuncinta da kimarta fiye dana 'yarsu da suka haifa domin bakad'an take girmamasu ba, wannan shine tarihin hajia kilishi.


Tsayawar motar da sukaji yasa su yin shiru daga fad'a da nasihohin da suka fara yimata akan maganar  abunda yafaru na gaskiya tsakaninta da dady da Mahmud yafad'a masu,


Cikin hanzari mom ta tashi tanufi bakin k'ofa don tarbota, tana fitowa cikin motar suka rungume juna cikin farinciki saida sukayi kusan minti uku ahaka kafin can hajiya kilishi ta d'ago had'e da rik'e hannun mom tana yimata wani kallo tun daga sama har k'asa



"Tafd'i jam qawata anya kece kuwa? Kinganki yanda kika rame kika lalace kamar bake ba, to wlh badon muryarki danaji ba aguje zan ingijeki in wuce abina"


Wani irin takaicine da bak'in ciki suka rufewa mom zuciya wanda d'acin kalamanta yasa hawayen ta zubowa batare data ankara ba, da sauri taja iska a hancinta tare da goge hawayenta


"Bari kawai 'yar uwa akwai labari" tak'are  maganar tana kallon yanda jikin hajiya kilishi yayi wani irin haske da kyau gaba d'aya ta canza tayi fresh ga wata irin qiba data k'ara kamar ba itaba tana mamakin yanda tasamu wannan hutun ita dake auren mai mata uku itace ta hud'u kuma mijinta ko kad'an bai kamo ko rabin arzik'in dady ba, dariya tayi mata had'e da jujjuyawa ahankali tana fad'in "dubeni da kyau kigani babu abunda ke damuna yanzu saboda remote control d'in gidan alhaji dashi kansa yana hannuna sai yanda nayi dashi"


Baki bud'e mom ke kallonta tace


"Ke kina sha'aninki, muje daga ciki kihuta ki shafa mani ko meye sirrin"


Tafewa sukayi suna dariya har suka isa falo, adaidai bakin k'ofar shiga hajia kilishi tawani gyara mayafinta had'e da marairarice fuska kamar tak'warai tashiga bakinta d'auke da sallama, cike da ladabi ta isa inda su papi kezaune taduk'a har k'asa ta gaishesu sannan taje ta rungume hajia kaka tana fad'in


"Hajiya ta nayi kewarku dayawa"


"Allah sarki yarinyar kirki muma munyi kewarki, ya maigidan naki da abokanan zamanki duk lpy kuke ko?"


"Lpy klw hajia duk sunce agaishe daku sosai tare ma mukaso zuwa dasu to sai Allah bai nufaba saboda wasu dalilai amma sunce zasuzo suma sugaisheku insha Allah"


"Madallah! muna amsawa ya hanya ya hanya?"


"Alhmdulillah papi, ashe ita kuma Hussaina abunda yafaru kenan?"


"To kindai gani, abunda tun k'urciya ba'ayiba sai yanzu" papi ne yafad'i haka yana kallon mom dake gefe tsaye


"To papi k'addarorine Allah yatsare gaba"


"Amin, kidai yimata fad'a inzataji, yakamata ace takoya daga gareki yanda kike zaune lpy da abokanan zaman ki, amma ita ace ko yaushe gatanan cikin zargi da son zuciya tahana abokiyarta zama lpy kuma tafitini kanta" Kallonta tayi sannan tace


"Allah dai yakyauta papi, abubuwan ne babu dad'inji gaskiya"


"Tashi kije daga ciki ki nemi ruwa kiwatsa sannan kici abinci kihuta kinji ko? Allah yayi maki albarka yajikan mahaifinki" hajia kaka tafid'i haka itama tana k'ok'arin tashi


Suna shiga d'aki mom takai mata duka da wasa, tace 


"Ke kam bakida kirki, bazaki dena k'aryannan takiba ko? Hadda wani zancen da atare zakuzo da duka kishiyoyinki don d'ai neman suna agurin papi ni kuma kijamun zagi ko?" saida tayi dariya sosai sannan tace


"Eh mana, bagashi har papi ya yarda ba, halinshi dai nanan yanda yake be chanza ba, gaskiya akwai gyara cikin rayuwar shi, ace wai da kanshi ke fad'ar wai kin takurawa kishiyarki, cab ashe da zaiga yanda nake da nawa kishiyoyin wlh sai ya tsaneni don kokad'an dasu har 'ya 'yansu babu maijin sanyina bugu da k'ari ko wanda ya ajiye su wlh indai ina kusa basu isa suji sanyin shiba, ke nifa nan zan iyayin komai don inga nike taka bani ake takawa ba"


"Hmmm barka da arzik'i aini kam k'asa nake war was ana takani dani har yarana sai yanda akayi damu"


"Hhhh ki kwantar da hankalinki nesa tazo kusa yanzu ke zaki taka duk wanda kikeso don nazo maki da maganin matsalar ki"


"Da gaske 'yar uwa?"


"Sosai kuwa kedai kawo kunnenki kiji...



Post a Comment

0 Comments