TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 11

 👭❤ *'YAN UWA NA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____11💎



 Yana shigowa yaci karo da Billy kwance akan cinyar Ummi tana tsefe mata kai, cike da kasala ya k'araso cikin falon, dak'yar yake takawa tamkar wanda akayiwa duka ya fad'a akan kujerar dake facing d'insu  zaune yayi wata iriyar ajiyar zuciya had'e da rufe idanuwansa, tsoron dake hannun Ummi ta saki tana kallonsa yare da karantar yanayin da yake ciki, 



"Babanah meke faruwa da kaine na ganka a haka?"


"Babu komai Ummi" ya fad'a ba tare daya bud'e idanuwan saba, murmushi tayi sannan tace


"Allah yasa haka"


"Amin Ummi, lil sis ina abokin rigimar naki"


"Gashi can a kwance, inagan yayi bacci tun d'azu da muka dawo"


"Ayya! Yawwa ya naga ke ranki bai b'aci ba da aka fasa fita" turo baki tayi kafin tace


"Allah ne bai nufaba amma raina yab'aci kuma ba sabida rashin fitar da ba'ayi ba sai don don dukan da kayiwa yayyah Basmah"


"Dagaske?"


"Sosai kuwa Yaya har cikin raina don wlh da nice, k'ilan saina kusa kuka"


"Tab! Allah ya tsare ranar da zakiyi irin abunda basmah tayi don na tabbata yankata zanyi!" Zaro idanu Billy tayi yace


"K'warai kuwa"


Duk firar da sukeyi ita dai Ummi na saurarensu har ta ida kammala tsifar da take yimata, kanta ta d'ago tana kallonsa yanda yake fitar da maganganun sa cikin natsuwa 


"Babana wai sai yaushe zaka fiddo da matar aure" da sauri ya wartsake daga yanayin da yake ciki har yana neman sauko wa akan kujerar da yake zaune


"Haba Ummi! Wane aure kuma nida na keda 'yan uwa mata agabana,  ai idan kikaga nayi aure to tabbas naga nakai autarsu Billy agidan mijine"


Tunda Ummi tayi magana Billy ke b'ab'b'akar dariya saboda yanda taga yayan nata yayi shock da jin zancen, amma tanajin amsar daya bayar ta d'aure fuska kamar ba itaba, dariyar shima yayi 


"Billy Japanese kenan! Wato ke kinga k'eta bari kiyi dariya ko?, to kima ajiye wannan fushin naki agefe don ko bakyaso tabbas sai lokacin da kukayi aure zanyi"


"A'a Babanah kabar wannan zance domin kaine babba acikin su don haka kai zaka farayi  daga nan sai su kuma su biyo ba yanka"



"Don Allah Ummi mubar zancen nan, ni banason wani aure billy tafad'a tare tana bubbuga k'afafuwa ak'asa kamar zatayi kuka tabar falon"


Sosai Ummi tayi dariya ita da Mahmud da yabi bayan ta da kallo yana fad'in


"Ai kuwa saidai ki koma Japan ba agidan nan ba"


Bayan kwana biyu dady ya tarasu a main palour d'insa saboda wani makirci da small mom ta shirya akan tana so dady ya raba masu gida, wannan maganar ba kad'an ta tayar masa da hankali ba wanda shine dalilin da yasa yatarasu waje d'aya, sai da yayi gyaran murya sannan yashiga yiwa Allah godiya bisa tarin arzik'i da samun iyali daya azur tasa dasu, bayan haka ya d'ora da cewa


"Hak'ik'a Allah yayi mani tarin ni'ima wacce bazan iya biyan saba, amma nayi alk'awari agaresa zan dage dayi masa biyayya har izuwa lumfashina na k'arshe, ni mutumne kamar Ku bana son shiga hak'k'in d'aya daga cikinku, banason tauye kowanen ku hakan yasa na taraku don neman sasanci a tsakanin ku, hajia Aisha da hajia Hussaina dukkaninku matanane kuma ina matuk'ar sonku wanda hakan shiyasa nake fatar komai tsanani komai wuya murayu atare kuma mu mutu atare, amma kash yau d'ayarku ta bijiro mani da buk'ata mafi k'ololuwar cutuwa agareni wacce jureta abune mai wahala da nake tunanin bazai yuyu ba don bana buk'atar hakan amma kafin na yanke hukunci ina so inji meye ra'ayin ke hajia Aisha da kuma 'ya'yanah akai" shiru yayi na kusan minti biyu kafin yaci gaba da cewa 


"Hajia Hussaina ta nemi da araba wajen zama saboda bazata iya jurewa cin fuska da munafurcin da ake yimata agidan nan ba don haka me kun kace akan wannan buk'ata tata" 


"Alhaji indai ta b'angare nane wlh banida ja duk hukuncin daka qudurta aranka zan bishi matuk'ar zai sama maka farin ciki" tana rufe baki basmah tace


"Bawani mudai munyarda araba wurin zama saboda musamu natsuwa muda mom d'in mu, ana takura mana a gidan nan don haka mu bana buk'atar zama dasu"


"Haba yayya Basmah kada kice haka mufa 'yan uwan junane, kar mubari son zuciya da kuma sharrin shaid'an ya b'ata mana zumunci"


"Dady fita batun Billy wlh Allah mudai muna amince, tsabar munafuncine ya hana sununa amincewarsu suma" cewar Batool dake zaune kusa da small mom tana taunar cingam. 


Tunda ake zancen nan Mahmud baice komai ba sai da yaji fitsarar k'annen tasa na nema ta wuce gona da iri, cikin damuwa yace


"Dady ni kwata kwata  bana goyon bayan wannan shawarar domin hanyace ta wargaza zumuncinmu, yakamata ace mom tafad'i abubuwan da akeyi agidan nan da bataso sai anemi hanyar gyarasu bawani ace lokaci d'aya araba wajen za.."


Kukan mom ne da yaji ya hanasa k'arasa maganar sa tana cewa


"Shikenan Aisha kin cuceni, Allah ya isa tsakanina dake tunda kika juyamun k'wak'walwar yaro, alhaji dubi yanda yaron nan kejuyawa muradina baya saboda yaci gaba da ganina cikin bak'in ciki da b'acin rai, yazab'i wacce batasan zafin saba akaina dama ni nasan bazaka tab'a canzawa ba matuk'ar muna wuri d'aya da wannan munafukar" tanuna Ummi dake zaune tana kallon ikon Allah, daga yaro yafad'i gaskiya shikenan sai abu ya juye akanta, a hankali tace "Allah ya sawak'e"


Cikin zafin rai dady yace 


"Rufemun baki kafin na sab'a maki, wannan wane irin abun kunyane kikeyi agaban 'ya'yanki, kina jifar 'yar uwarki da munanan kalamai donki cimata zarafi" ai kamar jira takeyi tafara zuba masu balbalin bala'i wanda hakan yasa Mahmud ya sallami k'annensa daga d'akin shi kuma yadawo yana lallashin dad d'insa daya dena biyewa mom, kallon Ummi dady yayi had'e da yimata umurnin itama ta tafiyarta ya sallameta, ta gefen mom tabi zata wuce ta fizgota da k'arfi



"Munafuka wlh babu inda zakoje har sai ankai k'arshen matsalar nan, bana buk'atar zama dake don haka dolene murabu" murmushin takaici Ummi ta saki tare da kallon ta tun daga sama har k'asa


"Hajia Hussaina ki tabbata kinyi na farko kuma kinyi na k'arshe, kada ki kuskura hannunki ya sake ya k'ara tab'a jikina, zaginki, k'azafin ki da sauran miyagun kalamanki basukai ga baki matsayin da zan tanka maki ba amma ranar da duk kuskurenki ya aikeki da sake tab'a jikina, ranar zaki samu matsayi aguna da zaisa in canza maki kama" hannu mom tad'aga da niyar marin Ummi dady yayi saurin rik'eta tana d'ago fuska ya d'auketa mari, zai mayar mata da na biyu Mahmud ya rik'e masa hannu hawaye na zubowa daga cikin idanuwansa


"Kayi hak'uri dady, uwa nada matuk'ar muhimmancin da akwai zafi a daketa agaban 'ya'yanta, dady ba momy kad'ai ba ni kaina ina buk'atar araba wajen zama saboda farincikin mahaifiyata, Ummi kifahimci buk'atar mom idan har kin duba musulunci ma ya amince da haka sai idan lalurar rashin wani zaman ta gitta kad'ai ya bada damar azauna waje d'aya"


"Mahmud wlh ni banida matsala tunda nima aurena akeyi duk hukuncin da dadynka ya yanke daidai ne, ni bance abijirewa buk'atar mahaifiyar kaba!" Jirine ya d'ibi dady dake tsaye Mahmud yayi saurin zaunar dashi akan kujera, ita kuwa mom tunda tasha mari bata sake cewa k'anzil ba.


"Shikenan hajia Hussaina kinyi nasarar raba mani gida, kije na amince kizab'i d'aya daga cikin gidajena ki koma, Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" wasu zafafan hawayene suka zubo a kumatun Mahmud don har ga Allah baiji dad'in rabasa da 'yan uwansa da mom tayi ba, kawae ya zab'i hakane don samun farincikin iyayensa ko ba komai shi kansa dady yasamu farin ciki.


Nan kowanensu yafita yanajin wani irin sabon yanayi acikin zuciyarsa, daidai inda kowacensu zata nufi part d'inta sukaci karo da Batool itada Billy suna fad'a ga Bassam can agefe ya haye Bilal yanata faman dukansa shi kuma yana kuka Basmah kuwa ta koma gefe sai fad'in take 


"Yawwa Batool sauya mata kama, banza dubi yanda Bassam ke lallasa Bilal amma ke kin tsaya wasa, wlh kika bari billy ta jibgeki kin zama samna. Tana rufe baki Allah yaba Billy sa'a ta d'aga Batool sama ta nane (mayar) k'asa.


Da gudu mom dake farincikin cin zalinsu Bilal da 'ya'yanta keyi ta nufi wurin yayin da itama Ummi ta nufi inda Bassam ke dukar mata yaro don kai masa d'auki.




Post a Comment

0 Comments