TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 57

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 5️⃣7️⃣


________

Washe gari da sassafe Abideen ya fitar da kwalayen tabarsa yana ta murmushi ga annushuwa da ta ƙawata fuskarsa, da suka gama operation da yamma kuma yyi aike cikin gari, drinks ya siyo musu suka kwalbe suka yi party abunsu kowa yyi farinciki, sosai suma suka yi farincikin ganin Boss ya dawo cikin hayyacinsa kuma ya fara aiki tuƙuru kamar yanda ya kamata. 


Bayan wata biyu...

Zaune tayi a parlour da dare tana safa da marwa, tun ɗazu take kiran Abideen amma baya shiga dan sunfi wata ɗaya basu yi waya ba kuma ko ta kira layinsa baya shiga, ajiyar zuciya ta sauke ta samu guri ta zauna ko abu kaɗan tayi sae ta riƙa haki tana jin kasala. Goga kuwa yau da kansa ya shiga cikin gari ko zae samu network yyi waya da madame ɗinsa ko zae samu ɗan sanyi a zuciyarsa, wani café ya samu ya shiga ya zaro wayarsa ya sake gwada numbern madame, cikin sa'a kuwa ta shiga, lokaci ɗaya wata kyakkyawar murmushi ta ƙawata fuskarsa, cikin farinciki ta zauna a kujeran dake gefenta tace, "Yaa Abi-deen!" Murmushi yyi yace, "Uhmm Baby, kina lafiya?" Kunya ta ɗan ji ta kawar da kanta gefe kafin tace, "Ina wuni! Ya aiki?" Murmushi yyi mata yace, "Alhamdulillah!" Dai dai lokaci wata Somalian waitress ta ƙaraso gurin Abideen tana tambayarsa me za'a kawo masa, take mood ɗin Safeerah ya chanza, coke da burger yyi order kafin ya juyo ya kalla Safeerah, ganin ranta a ɓace yasa shi cewa, "Naga kin ƙara kyau ne!" Ƴar dariya tayi kafin ta ɗaure fuska tace, "Muryar wa nake ji?" Dama yasan sae ta tambaya hakan yasa yace, "Waitress ɗin café ce!" Ta ɗan ɓata rai da jin haka amma ya zata yi tunda network ya fito dashi, a haka dae suka ƙare waya cikin farin ciki. 


Tun bayan da Ya Jamilah ta aiko mata da maganin da tasa a kawo mata ta daena jin ƙirjinta na yi mata yanda yake yi da, sosai tayi farinciki nan Dr Reedah tazo har gida ta duba ta tayi mata congratulations da cewar ta warke completely, sosai tayi farinciki ta kirawo Safna take faɗa mata, sosai sukayi farinciki da jin wannan zancen mae daɗi. 


****

Tun da suka yi waya jiya ya faɗa mata cewa zae dawo gida gobe InshaAllah tunda da daddare zasu yi last operation ɗinsu, wani daɗi ne ya rufeta tana jin kamar bazata iya jira ba amma bae gaya mata cewa zasu yi operation da dare ba, tana gama abunda zata yi ta kwanta da wuri saboda ta tashi tana son yi masa surprise amma baza ta gaya masa ba. 


Somalia...

Kenyans da kansu suka kawo attack dama haka STF suke jira dan su buɗe musu wuta, Abideen da sauran ƴan team ɗin na office suna sake planning strategy sae ƙara suka ji, "This is Wolf! Enemies spotted! Over!" Kafin Abideen yyi wani abu mataimakinsa ya ɗauki walkie-talkie ɗinsa yace, "This is Beta! Say again, your location!" Yana faɗan haka Abideen yace, "This is Alpha, Stand by for further instructions!" "Roger that!" Ajiyar zuciya Abideen ya sauke suka yi magana ƙusƙus kafin suka kwashi bindigoginsu suka fice da Bravo a gabansu suna biye dashi a baya dan sae yyi confirming gurin is clear yake yi musu sign da hannu du taho. 


"This is Beta, cover the Alpha, I repeat Alpha is shot!" Cover aka yi wa Abideen amma ba hakan ya hanashi cigaba da buɗe wuta ba, sae can Beta ya ƙaraso gurin da Alpha yake a zaune yace, "You're bleeding Boss!" Lumshe idanu Abideen yyi yana jin yanda jini ke zuba daga cikinsa, fincikewa Beta yyi ya buɗe rigar Abideen nan yaga jini caɓa caɓa, "This is Beta, the Alpha is shot, I'm calling for the medic! Over" Muryar wani ne ya shigo, "This is Charlie, roger that!" A wani guri suka laɓe, Abideen na leƙawa ya hangi Leadern Kenyans yana ta harbi, muryar wani ne ya shigo, "This is Bravo, we lost signal from Danger!" Cikin fushi Abideen ya miƙe daga cover ya fice, ajiyar zuciya Beta ya sauke yana gudun a sake harbar Alpha tunda an riga an harbeshi, a cewarsa yasan Abideen ya iya dodging bullets sosai amma yau bae san ya aka yi ba ya samu bullets har biyu ba, daga inda Abideen ya tsaya Leadern Kenyans ya hango shi, puff kke ji wata bullet tasake shiga hannun Abideen, yatsine fuska Abideen yyi kafin ya matse gurin da ɗayan hannunsa, ajiyar zuciya Abideen yyi ya sake yin saiti tunda sniper ce a hannunsa, kafin kace kobo yyi wa Leader biyu a ƙahon zuciya a ta ke ya faɗi matacce, ƙaran walkie-talkie ne ya shigo, "This is Bravo, K leader shot, enemies retreating! Over!" Daidai lokacin kuma idanun Abideen suka rufe ya zube a gurin. 


"This is Beta, the Alpha is out!"

"This is Tiger, Mission completed! Out!" 

"This is Bravo, enemies retreated, sight cleared!" 

"This is Charlie, location of the Alpha, over!"

"This is Beta, roger that!" 

"This is Wolf, three soldiers confirmed dead!" 

"This is Beta, 3'o clock!"

"This is Wolf, bodies cleared!"

"This Beta, CHARLIE I'LL KILL YOU IF WE LOSE THE ALPHA!!!" 


Hannu da hannu suka haɗa aka ɗauki Alpha aka kai shi Medi cube, ana kwantar dashi akan gado jini ne kawai ke zuba daga jikinsa dan harbi har uku ne a jikinsa kuma duka bullets ɗin suna cikin jikinsa. Ihu Beta ya bugawa Charlie yace, "He's losing so much blood, do something!" Ɓata rai Charlie yyi ya tura Beta waje ya rufe ƙofarsa, da kyar ya cire bullets ɗin daga jikin Abideen amma ko daya gama Abideen baya motsi, can dae yyi abubuwan da zaeyi ya saka masa drip ya fita daga ɗakin, yana fitowa ya tarar da Beta a bakin ƙofa yana gadi cikin camouflage ɗinsa dake ɓace da jini, aikuwa collar Charlie Beta ya kama yace, "Why isn't he moving? Eye, meysa baya motsi?" Shiru Charlie yyi kafin ya fusge collarsa yace, "The bullets are poisonous, nayi abunda zan iya ya rage ga sa'ar shi ya tashi, amma zae iya tashi tunda sae nan da 15 hours poison ɗin zae fara aiki!" Charlie na gama faɗan hakan yyi tafiyarsa tunda ya gama aikinsa, a ƙasa Beta ya zauna daɓas yana jin takaici tunda shi aka yi aiming za'a harba amma Abideen ya tare masa  tun a na farko kenan kuma tun lokacin ya fara zubar da jini. Matar Boss kawai yake gani a idanunsa tunda she's young bae kamata ace ta zama bazawara ba tun yanzu. Da kyar Beta ya miƙe ya bar gurin, har dashi suka tattare kayansu tunda da sassafe kafin rana ya fito za'a zo ɗaukansu, a haka dae suka yi abunda ya kamata tunda mission ɗinsu is completed. 


Can dare Beta ya kwanta amma ya kasa samun sukuni, medi cube ya wuce ya leƙa nan ya hango Abideen akan darduma yana sallah, wata ajiyar zuciya mae nauyi Beta ya sauke ganin Abideen ɗin ya tashi amma kuma idan ya tuna bullet ɗin poison ne sae yaji bbu daɗi da kuma cewar ta kusa ta fara cin jikin Alpha...


*Don't forget to vote!🥂❤️🔥

*Follow me on Wattpad @_khanoum_


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments