TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so 42

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 4️⃣2️⃣

______

Suna zaune a parlour suna kallo a parlour da rana bayan sallar Azahar suna maƙale da juna suna hira da raha, ƙaran shigan message ne ya shigo wayar su kusan a tare, ko data duba wayarta tsaki tayi inda shi kuma ya zuba mata ido bayan ya gama karanta nasa message ɗin, ajiyar zuciya yyi yace, "Meya faru?" Rolling eyes ɗinta tayi tace, "Message aka turo mun wai anyi suspending ɗina daga school till further notice!" Shi kuma wai ana son ganinsa a school ɗin haka ya gani a nasa email kasancewar sa guardian ɗinta kuma ummul aba'isin abin daya faru. Sosai yyi mamakin jin yanda tayi maganar kamar bata damu ba saboda yasan tana son school hakan yasa yace, "Why are you not worried?" Kallonsa tayi tareda sake matsawa kusa dashi tace, "I don't feel safe anymore, gara na zauna a gida na dinga kula da kai" kallonta yyi cikin rashin yarda yace, "Amma kina son school sosai.." wani murmushi mae sanya nutsuwa ta sakar masa sannan tace, "Amma bae kai yanda nake sonka ba ai.." wata kalar zurr yaji yana yi masa yawo a kai ga daɗi dake ratsa shi tun daga ƙafa har cikin brain ɗinsa sannan ya koma zuciyarsa yana jin kamar ya saka ta a cikinsa saboda murna da ƙauna. 


Hannunsa ta kamo ta ɗaura akan saitin zuciyarta amma tudun boobs ɗinta kawai yake ji hannunsa na taɓawa ga wani abu dake yi masa yawo akai, cigaba tayi da, "I'm saying this from the bottom of my heart that ka faye mani komai Ya Abi-deen, ka zamo garkuwa..." tun da ta fara magana shi yanda lips ɗinta ke motsi kawai yake kallo, shi kansa bae san lokacin daya manna lips ɗinsa da nata ba, kissing ɗinta ya fara yi a hankali inda ta fara mayar masa cikin shauƙi, har ya fara ɗauka da zafi zafi tayi saurin tureshi tace, "Ya Abi-deen..." dakatawa yyi yana mayarda numfashi masu nauyi, kallonta yyi bae ce komai ba nan ta cigaba, "Dan Allah ina so muje gidan Aunty Jamilah kafin dare yyi.." murmushi yyi mata kawai tareda ɗaga kai cikin amincewa, tsaye ya miƙe inda ta zuba masa ido ganin bulge ɗinsa daya cika masa wando, yana da saurin jaraba amma akwai dauriya da haƙuri. Haka ta bisa da ido har ya wuce part ɗinsa, ɗakin ta ta nufa tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa, ɗinkin yyi matuƙar yi mata kyau sosai, tana sauka ta tarar dashi ya fito dan har ya shirya cikin kaftan da suka karɓe shi sosai. 


Ya Jamilah ba ƙaramin farin cikin ganin Safeerah da Abideen tayi a gidan nata ba, ta kasance tana da yara biyu maza amma a abroad suke karatu, hakan ya saka ta cikin kaɗaici sosai. Bayan sun gama gaisawa Abideen yace, "Ya Jamilah zan fita amma zan dawo ɗaukarta anjima" ɗaga masa kai Ya Jamilah tayi tareda sauke masa murmushi, kai ya saka ya fice daga gidan da shirin zae ɗauke ta anjima. Yana fita Ya Jamilah ta gyara zama tace, "Ya jikin naki?" Murmushi Safeerah tayi tace, "Tun dana fara shan maganin da sauƙi sosai, duk da.." saurin zare ido Ya Jamilah tayi tace, "Have you done the deed?" Dariya Safeerah tayi tace, "Not yet amma ina tunanin zan iya coping since a lot of romance has been going on.." murmushi Ya Jamilah tayi nan Safeerah taji kunya na rufe ta bayan ta faɗa, kamo hannunta Ya Jamilah tayi tace, "Kar ki damu, ni ma kamar Yayarki naki and idan kina ganin baza ki iya ba I can always talk to him.." ɗaga mata kai Safeerah tayi nan suka fara hira har Safeerah ke bawa Ya Jamilah labarin Prof Tasiu, tsaki Ya Jamilah tayi tace, "Kin san lecturers ɗin nan wasu haka suke, hakan yasa suke ɓata wa na gari suna amma Allah Ya karemu daga sharrin su.." "Ameen" Safeerah ta rufawa adduar Ya Jamilah. Can bayan sunyi sallar Laasar Ya Jamilah tace, "Kinga ina da appointment ɗin gyaran jiki, I can't afford to miss it zo mu tafi.." shiri Safeerah da Ya Jamilah suka yi daga nan suka wuce gurin gyaran jikin, a can aka yiwa Safeerah fixing nata sannan aka fara yi masu tare.


Ko da Abideen ya bar gidan Ya Jamilah makarantar su Safeerah ya wuce, can a office ɗin sabon president ya tarar da committee ɗin makarantar suna jiransa su huɗu tareda President su biyar kenan, a dake Abideen ya shiga ya samu guri ya zauna, ba gaisuwa sukayi setting down to business inda President yace, "Me Prof yyi maka kayi masa rauni har hka?" Kallonsa har cikin ido Abideen yyi yace, "Meysa yyi trying raping wife ɗita?" Shiru President ɗin yyi nan wani dattijo yace, "Bae kamata ka ɗauki doka a hannunka ba, da kayi reporting da zamuyi tackling issue ɗin!" Kallonsa Abideen yyi ta taɓe baki yace, "Okay, go ahead ga President nan ka fara daga kansa.." saurin kallonsa President yyi numfashinsa na neman ɗaukewa, naɗe ƙafa Abideen yyi yace, "Ba za ku iya ba ko?" Taɓe baki yyi nan wani matashi yace, "Kayi wa Prof rauni sosai kasan zamu iya kai ka court?" Dariya Abideen yyi yace, "Rauni kamar ya?" Kallonsa matashin yyi tareda tura masa wasu papers, kallon papers ɗin Abideen yyi ko taɓa su baiyi ba nan matashin ya ɗaura da, "You fractured his skull, fingers ɗinsa ma a karye suke and hancinsa ma ya karye ga two missing teeth a bakinsa." Matsawa kusa dashi Abideen yyi yace, "Zuwa yaushe zai farfaɗo?" Ɗaya daga cikin wanda baeyi magana ba yace, "Three to six months zai ɗau kafin ya warke.." tsaki Abideen yaja yace, "I should have done more, at least baze iya cin zarafin wasu ba for the mean time" President ne yyi saurin ɗaga kai yace, "Kasan zamu iya filing suit against you, wannan ai zaka sa lecturers su dinga jin tsoro ne!" Taɓe baki Abideen yyi yace, "Idan har baza su ci zarafin ɗalibai ba then it's fine with me!" Lumshe ido yyi tareda warware ƙafafunsa, wanda bae yi magana ba kwatakwata ne yace, "Major Zayn Abideen.." kallonsa Abideen yyi tareda lumshe idanunsa nan mutumin ya cigaba, "Just because you're a soldier doesn't mean zaka iya assaulting civilian, we can file a report!" Dariya Abideen yyi jin ransa na ɓaci, fisting hannunsa yyi ya buga akan table ɗin dake gabansu nan ransu duk ya tsinke ganin ransa ya ɓaci yace, "Oh well MashaAllah! So nayi assaulting civilian when he was trying to rape my wife and I caught him right in the act!! Impossible, that's not possible! Go on, file a lawsuit against me and zanyi filing case akan rape and the whole damned school!" Rau rau President yyi da idanunsa ganin zae iya ɓata wa school ɗin suna idan yyi filing suit hakan yasa suka yi shiru, a fusace Abideen ya buge kujerar gefensa yyi tafiyarsa, yana fita matashin yace, "Yana bani tsoro!" Dattijon gefensa yace, "Ba kai kaɗai ba.." tsaki President yaja yace, "Ai ko baza ta dawo wannan school ɗin ba.." ko daya fita ya shiga cikin motar takaicin abun ya bashi wai mutane basu damu da yaran da Prof ɗin da wasu ke lalatawa ba, lafiyarsa da sunan makarantar su kawai su ji.


Su Ya Jamilah kuwa har bayan Magrib suna kwance sae gyaran jiki ake yi masu, ana shirin yiwa Safeerah gyaran kai wayarta ta fara ruri tana neman agaji, da saurin gaske Safeerah ta nufi jakarta ta ciro wayar ta kara a kunne. Ransa kamar a ɓace yace, "Mae gadi yace kun fita, ina kuka je?" Jiki na rawa tace, "Munje gurin gyaran jiki ne.." katseta yyi da, "Send the address, I'll head over.." ƙaran katse wayar taji hakan yasa ta sauke wayar tareda yi masa text ɗin gurin, Ya Jamilah ce ta kalle ta tce, "Meya faru?" Murmushin dole Safeerah tayi tace, "Zai zo ɗauka na wai.." murmushi Ya Jamilah tayi tana faɗin, "Abideen bashi da dama.." a haka dae Safeerah ta shirya ta kwashe kayanta, yana sake kiran wayarta tayi wa Ya Jamilah sallama tac  fice daga gurin, a mota ta tarar dashi ya haɗe fuska tamau babu ko alamar fara'a a fuskarsa. Tunda ta shiga wani ƙamshi ke ziyartar hancinsa amma dayake terror ne kuma ransa a ɓace sae ya fuske amma bae tsira ba tunda sae da ya ji fushinsa yana sauka, kallonta yyi yace, "Da izinin wa kika fita?" Tunani tayi bata so ta sake kiran Ya Jamilah cikin harkar hakan yasa tace, "Babu nisa shys ban tambaya ba amma..." haƙuri zata bashi amma lokaci ɗaya yaji fushinsa na ƙara tashi, wani tsaki yaja yace, "It doesn't matter, ko ina ne DOLE NE ki sanar dani kafin ki yi abu.." shiru tayi tana kallon fuskarsa dake lulluɓe da ɓacin rai tace, "Fushi kayi over this small.." bata ƙarasa ba kamo hannunta ya matse cikin fushi da ɗaga murya yace, "Don't you dare call it small, what of the dangers lurking..." bae ƙarasa ba tace, "Ya Abideen you're hurting me.." saurin sakin hannunta yyi yana kallon gurin kafin ya sauke ajiyar zuciya, he lost it again, guilt ne ya fara cinsa hakan yasa yyi shiru ta cigaba da driving ɗinsa cikin nutsuwa, juya masa baya tayi tana kallon mutane ta window tana jinta very suffocated zama a gefensa, ya cika fushi kuma idan yyi abun baya kyau ko kaɗan.


Suna isa gida ta sauka ta wuce ɗakinta, bayanta yabi zuwa room ɗinta bayan ya gyara parking, ko amsa barka da zuwan sojojin dake yi masa baiyi ba ya wuce ciki a gigice, ko daya shiga room ɗin nata sae handbag ɗinta da veil, ƙaran running tap daya ji ya tabbatar masa tana cikin bathroom. Lokacin salla na neman ƙurewa hakan yasa ya wuce part ɗinsa, a gida yyi sallar Magrib da Ishaa duka yana jin jikinsa duk bbu ƙarfi, ya daɗe a zaune bayan ya idar da sallar Ishaa ɗinma gashi lokacin tafiyarsa ta kusa dan kwanaki kaɗan ya rage, ga maganar auren Zaytoona duka, tsuka yaja sannan ya miƙe ya fice daga part ɗin nasa ordern dinner yyi masu bayan anyi delivering kuma ya ci nasa ya gyara gurin, room ɗinta ya nufa yyi knocking kafin ya shiga, ganin ta yyi a kwance ta juya masa baya, a hankali ya kirawo sunanta, "Safeerah.." shiru tayi masa hakan yasa ya sake kira, "Safeerah, ki tashi ki ci abinci.." daga can ƙasa yaji muryarta tace, "Na ƙoshi.." a dake yace, "Me kika ci?" Shiru tayi masa hakan ya tabbatar masa da cewa bata da niyyar amsa shi, jiki a sanyaye ya wuce ɗakinsa ya zare jallabiyar jikinsa ya kife a lallausar gadonsa, a haka dae bacci yyi awon gaba dashi da tunani kalakala cikin kwakwalwarsa...


Don't forget to vote, comment and share MUGUN SO to your friends!😘🥂✨️


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments