TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 46

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 4️⃣6️⃣

______

A firgice Ya Jamilah ta faɗo cikin gidan inda sojojin suka bita da ido suna mamakin wannan lafiyarta kuwa, cikin gidan ta nufa kai tsaye ta wuce upstairs, jin motsi yasa Abideen fitowa daga ɗakin Safeerah ya tsaya a bakin ƙofa, ajiyar zuciya Ya Jamilah ta sauke ganin yanda idanun ƙaninta suka yi ja gashi duk ba cikin kwanciyar hankali ba, tana ƙarasowa ya kama hannunta yana faɗin, "Ya Jamilah dan Allah ki tai- taimake..ni, wal-wallahi ina so..son ta so..sosai.." tausayi ne ya kama Ya Jamilah amma yanzu ba ta shi take ba, tana ƙarasawa cikin ɗakin taga Safeerah a kwance rai a hannun Allah, sosai Ya Jamilah ta tsorata tace, "Abideen me kayi mata haka.." shiru yyi bae amsa ta ba sae hawayen dake ta zuba daga idanunsa inda yyi ta ƙoƙarin gogesu amma sun ƙi tsayawa.


 "Ɗauko ta mu tafi asibiti.." ƙarasawa yyi ya ɗauke ta cak suka fita daga ɗakin, jinin da Ya Jamilah ta gani malale akan gadon ba ƙaramin ƙara tsorata ta yyi ba, bedsheet ɗin gadon ta yaye ta ajiyeshi a gefe sannan ta fice ta rufa musu baya, a backseat ɗin motarsa ya sakata sannan ya jira fitowar Ya Jamilah, driver seat ta shige inda Abideen ya shige backseat tare da matarsa, cikin wani mahaukacin gudu Ya Jamilah ta tura motar kan titi sae zuwa asibiti...


A stretcher aka ɗauketa nurses suna turawa cikin sauri, cikin sanyin jiki Abideen ke binsu a baya yana roƙon Allah Ya sa ta tashi lpy, kowa ya gansa yasan ba cikin kwanciyar hankali yake ba, da kyar ya samu kujera ya zauna a gefen Ya Jamilah suna jiran doctors ɗin su fito daga ICU ɗin da suka shiga, sun kusa minti 30 kafin wata doctor ta fito tana cire white gloves ɗin hannunta da suka ɓaci da jini ta kallesu tace, "Is she a rape victim? Ya kamata kuyi filing rape suit.." kallon Abideen Ya Jamilah tayi nan duk ɗinsu suka ɗinke bakinsu, da kyar Abideen yace, "Is she alright?" 


Wata likita ce kyakkyawa black beauty ta fito itama tana cire gloves ɗinta kafin tace, "She's out of danger" wata nannauyar ajiyar zuciya Abideen ya sauke yana godewa Allah nan likitar tace, "Wanni kalan stamina ka saka mata haka Major Abideen" sinnar da kansa ƙasa yyi yana ɗauke idanu, ɗayar likitar tana jin haka tace, "Taji jiki ba ƙarya, ƙila bashi ta biya.." ƴar dariya likitar tayi kafin tayi tafiyarta, Dr Reedah da ta tsaya ne tace, "Zamuyi transfer ɗinta zuwa wani ɗaki yanzu, so I'll like to see you in my office.." yaso yaga lokacin da zaa fito da Safeerah daga ICU amma Ya Jamilah ta zare masa ido, ba shiri ya bi bayan Dr Reedah.


Bayanin da Dr Reedah tayi wa Abideen ba ƙaramin tsorata shi yyi ba wato bata da lafiya amma ta zaɓi ta ɓoye masa, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Dr ba yanda za'a yi ta samu lafiya yanzu.." murmushi Dr Reedah tayi tace, "She has been taking drugs for quite a while, so zan bata wasu magungunan, InshaAllah zata samu sauƙi.." tana faɗan haka tayi rubutu a paper ta miƙa masa, jiki a sanyaye ya karɓa ya miƙe ya fice, pharmacy ya wuce ya siyo drugs ɗin kafin ya kama hanya zuwa ɗakin da aka kwantar da Safeerahn a sashen VIP. Upstairs ya haye zuwa VIP ward, can yyi locating room ɗin ya shiga, zaune ya ga Ya Jamilah tayi akan darduma da alamar ta idar da sallah, dubansa ya kai ga Safeerah dake kwance, daga yanda ƙirjinta ke sama yana ƙasa a hankali ya tabbatar da tana jin daɗin baccin, ɗakin shiru sosai sae ƙaran AC dake tashi cikin sanyi, juyowa Ya Jamilah tayi ta gansa a zaune a gefen matarsa ya ƙura mata idanu, murmushi tayi sannan ta haɗe fuska tace, "Kayi sallah?" 


Ba wai kunyan yayarsa yake ji ba amma kawai sae yaji nauyinta, a hankali taji yace, "Sae nayi wanka.." juya ido tayi tace, "Toh kazo ka tafi gida.." shiru yyi mata hakan yasa ya ayyana ko baze iya driving bane, akan fridge ɗin ɗakin taga wayarsa hakan yasa ta miƙe ta ɗauki wayar ta dannawa Sadique kira, kallo ɗaya yyi mata ya ɗauke kansa ya cigaba da kallon matarsa, bata wani yi magana mae tsayi ba ta kashe wayar, ba'a wani ɗau lokaci ba ƙofar ɗakin ta buɗe nan Sadique ya shigo a tsorace, yana kallon abokinsa a zaune sae ya sauke wata ajiyar zuciya yana dafe ƙirjinsa, Ya Jamilah ya kalla sannan ya gaishe ta, sae a lokacin idanunsa suka sauka akan Safeerah dake kan gado tana bacci cikin kayan marasa lafiya na asibitin, a kiɗime yace, "Yaya me ya same ta?" 


Taɓe baki Ya Jamilah tayi tace, "Ai ga abokin naka a gefe sae ka tambayesa me yyi mata.." shiru Sadique yyi ya kai dubansa ga Abideen yaga duk ya fita hayyacinsa yyi kamar bashi ba, idanunsa ya runtse ganin Abideen ɗin kaca kaca, can Ya Jamilah tace, "Ka raka shi gida yyi wanka yyi sallah.." maganar da tayi kawai yasa Sadique ya shiga haske akan abunda ya faru, tsaye Abideen ya miƙe suka yi hanyar fita daga ɗakin, "Ku taho mun da wayarta idan zaku dawo.." cikin sauri Abideen ya juyo ya kalli Ya Jamilah inda ta watsa masa harara ta ɗauke kanta, cikin sanyin jiki suka fice daga asibitin suka shiga motar Sadique suka wuce gidansa. A main parlour Sadique ya zauna yana jiran Abideen yyi wanka yyi sallar sae su wuce, tunda ya fara driving har suka iso gidan bae cewa Abideen komai ba ganin damuwa ɓaro ɓaro a fuskarsa. 


Yana idar da sallar ya fito daga part ɗinsa cikin wata shirt blue and navy blue wando, idanu Sadique ya bisa da shi ganin ya shige ɗakin matarsa, murmushi Sadique yyi ya cigaba da latsa wayarsa, ko da Abideen ya shiga ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah tayi pushing through, bedsheet ɗin ɗakin da Ya Jamilah ta ɗage ya gani, a can ƙasa kuma rigarsa ce fara ta jiya da nata rigar baccin da pant ɗinta duk a ƙasa, hannu yasa ya tattare su ya wuce dasu laundry room dake a haɗe da bayin Safeerah, wardrobe ɗinta ya buɗe ya ciro mata wani riga doguwa material mara nauyi sosai ya haɗa da pant da hijabi. 


A wata ƙaramar jaka ya saka ya ɗauki wayarta suka fice daga gidan, Sadique take driving ya juyo ya kalli Abideen yace, "Ka riƙa bin yarinyar mutane a hankali Abideen.." bae juyo ya kalla Sadique ɗin ba yace, "A hankalin ai na bita.." dariya Sadique yyi yace, "Ba wani malam, a hankalin ne har tazo asibiti??" Juyowa Abideen yyi ya kalleshi yace, "Idan baza ka yarda ba ma kai ka sani.." kallonsa Sadique yyi yace, "Ba wai maganar kar na yarda bane, tsoron ka zata fara ji.." sae yanzu Abideen yyi tunanin haka kuma ba ƙaramin tsorata yyi da jin hakan ba. Har suka isa asibitin bbu wanda ya sake magana har suka kutsa kai zasu shiga cikin ɗakin, Sadique ne a gaba saboda shi ya riƙo ledojin abun breakfast daga restaurant.


Farawa da Bismillah🤭 shiga da Abideen zaeyi ya hango Safeerah a tsaye da taimakon Ya Jamilah da alama toilet zasu shiga, cikin muryar kuka Safeerah tace, "Aunty Jamilah na gaji ƙafataa ciwo take yi bazan iya tafiya baaa.." cikin kukan shagwaɓa take faɗin haka duk da sun kusa ƙarasawa toilet ɗin, "Kiyi haƙuri mu ƙarasa kinga lokacin sallah na wucewa kuma sae kinyi wanka.." cize leɓe Abideen yyi daga inda yyi mutuwar tsaye bayan daya ji haka, cikin sanyin jiki ya ƙarasa kan gadon ya zauna tareda ajiye ledar kayanta yana sauke numfashi da kyar. Sadique kam da ya ajiye ledar breakfast sae ya dawo gurin Abideen yace, "Toh bara na wuce, Allah Ya ƙara sauƙi.." kai Abideen ya ɗaga masa tareda miƙa masa hannu su kayi handsake, da kyar muryarsa ya fita yace, "Toh zamu yi waya.." kai Sadique ya ɗaga ya fice duk tausayin Abideen ɗin ya kama shi ganin yanda duk ya kiɗime, a haka dae Sadique ta tafi da tunanin Abideen a ransa.


 Abideen na a zaunen yaji Safeerah ta kwala wani ihu tana faɗin, "Wayyooo Allaaah... Aunty... da zaaafi.." yana jin wannan ihun zuciyarsa ta sake yin wani sanyi, da kyar ya kwashi ƙafafunsa ya fice daga ɗakin dan baze iya zama ba, a bakin ƙofar ɗakin ya zauna a kujerar da aka ta nadar. Cize leɓensa na ƙasa ya riƙa yi har sae da yaji ɗanɗanon jini a bakinsa ya bari, nadama ce fal a cikinsa amma toh ya zae yi. Ko da Ya Jamilah ta fito sae taga ledoji hakan ya tabbatar mata sun dawo amma bata gansu ba, ledan kayan Safeerah ta ɗauka ta koma toilet ɗin, ba'a jima ba sosai suka fito daga toilet Ya Jamilah ta taimaka mata ta saka kaya sannan ta tayar da sallah, tana idarwa suka ƙarya ita da Ya Jamilah akan carpet ɗin ɗakin, basu jima ba Safeerah ta koma kan gadon nan taji ƙamshin turaren Abideen hakan ya tabbatar mata yazo ɗakin amma bata ganshi ba, da sauri ta runtse idanunta tareda juyawa...


*Don't forget to ✔️ote and drop your comments!🥂

©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments