TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 16

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____16💎


  

  Ke Billy wai meye tsakanin waccan nurse d'in ne da Yaya, 'yar dariya tayi tana kallon Basmah dake tsaye abinta har lokacin zuciyarta na tuk'uk'i akan fad'an da faraaha taja akayi mata, da hannu tanuna Basmah tare da maido kallonta ga Batool daidai kunnenta ta rad'a mata.


"Bansan komai ba kije kitambayi yayya Basmah don naga alamar ita tafahimci ko meye ko kuma intambayar maki yaya yabaki amsar da kansa.." Da sauri ta zaro idanuwa waje had'e da sakar mata rank'washi akai tana nunata da hannu,


"Ke rufe baki so kike ya b'abb'allani nima abani gado a asibitin nan?, kawai manta dashi idan tayi tsami zamuji" tana rufe baki taji an rik'e mata d'ayan kunnen da k'arfi tamkar zai cire ashe duk abunda suke fad'a akunnensa yana jinsu,


"Bari nafad'a maki tunda so kikeyi kiji magulmaciya"


"Awshhh..Yaya cikani don Allah wlh da zafi" sake rik'e kunnen yai sosai ta yanda zafin zai d'ara wanda taji daga farko,


"Pls am sorry Yaya" sakinta yayi tare da mak'alo wuyanta a k'ark'ashin kafad'arsa yana dariya


"Kura ga tsoro ga ban tsoro, to ya kika ganta kuwa tayi?" Turo baki tayi hannunta d'aya na saman kunnenta dake yimata rad'ad'i.


"Gaskiya batayi ba, mace sai kace muciya" tana rufe baki kafin yayi k'ok'arin d'aukar wani action ta zille masa tabar d'akin aguje tana dariyar k'eta don tasan tayine kawai don ta k'waga masa akan abinda yayi mata, dariyar shima yayi had'e da shafa kansa, hatta Billy da Basmah dake faman kumburar fuska saida sukayi dariyar yanda ta zunduma da gudu, juyowa Basmah tayi donta koma mazauninta taga Bassam rik'e da wayarta sai faman game yakeyi, ak'ufule tayo kansa shi kuma ya yadda wayar ya ruga abayan Mahmud ya b'uya, jawo hannunsa yayi yace


"Zo gashi narik'e maki" ai kuwa ko kunya bata jiba tayo kansa cikin b'acin rai da nufin kai masa duka, da sauri Mahmud ya rik'e hannunta yana dariya


"Kai Basmah yanzu saiki dukesa akan ya tab'a maki waya ke ko kunya bakiji ba"


"To don me zai tab'amun, game fa yakemun kuma banida enough charji"


"Oh sorry!...bazai k'ara ba ko? mahmud ya fad'a yana kallonsa, kad'a masa kai yayi yace


"Eh Yaya"


"To kinji yace ya dena saboda haka tunda gani nazo kije gida kigyara idan dady da Ummi zasu zo sai kudawo tare muje gaida mom" hakan da yace ba k'aramin dad'i yayi mata ba, nan take cikin farinciki tahau har had'a kayanta, wayarta da ear piece da kuma charger tad'auko tasaka a cikin 'yar mini hand bag d'inta dake gefenta sannan tabar d'akin ba tare data kalli ko inda Billy ke zaune ba balle tasa ran zata cemata wani abun.


Bayan tafita yayi murmushi yace 'YAN UWANA kenan ko wannenku da kalar tasa rayuwar ya Allah kasa muso juna.


"Amin" yaji Billy tafad'a tana k'ok'arin tura chaculate d'in data kwand'are acikin baki, gefenta ya zauna akan gadon yace 


"Billy ya jikin naki?"


"Alhmdulillah naji sauk'i Yaya, wai sai yaushe zasu bamu sallama wlh ni nagaji da kwancin gadon nan"


"Ai kuwa hak'uri zakiyi har sai lokacin da aka yimaki scanning result ya nuna ba wata matsala sannan, gashi har yanzu basusa date d'in yin scanning d'in ba kinga kuwa indan zama yanzu kika fara"


"Kai Yaya hadda wani yanzu nafara zama don bakaso ka dena ganin aunty faraaha ko?, to thank good ance bayan sallar la'asar za'ayi scanning d'in" mintsili ya kaimata a kumatu had'e da cewa


"Kema biyewa Batool zakiyi ko? Nifa babu wani abu tsakanina da faraaha, the way yanda ta gwane ga aikin tane da kuma kulawar da take baki yanda ya kamata shiyasa kikaga nadamu da ita"


"Dagaske Yaya ba sonta kake yiba?"


"Eh mana baki yarda bane?"


"No..amma meyasa kacewa Batool..." Kafin ta iyar yace


"Common.. da wasafa nakeyi, sincirely ni babu wani tsarin soyayya ko aure agabana, faraaha kuwa burgeni ne kad'ai alamurranta keyi amma babu soyayyar ta aziciyata"


Sun jima da ita tana nuna masa irin alkhairan da faraaha take tartare dasu zaifi dacewa ace ya mallaketa amatsayin masoyiyarsa amma fir  Mahmud ya nuna mata shi ba sonta yakeyi ba, abunda ya matuk'ar d'aure mata kai shine yanda yake matuk'ar farinciki idan suka had'u  da ita da irin kallon da yake yimata amma wai yace shi ba sonta yakeyi ba kawai burgesa takeyi, yatsunsa ya murza akan fuskar ta har saida sukayi k'ara, firgigit Billy tafarka daga duniyar tunanin data lula, girarsa ya d'aga kafin yace


"What?"


"Nothing Yaya just dt ina mamaki ne"


"Believe me lil sis dama kindena"


Sai gab da sallar la'asar su Ummi suka shigo cikin asibitin tare da Basmah, kai tsaye dady ya nufi wajen faraaha don bincikar cigaban da aka samu game da lafiyar 'yarsa ita kuma Ummi da Basmah suka wuce room d'in da suke jinyar Billy, cikin girmamawa dady daya isko faraaha zaune dasu Bilal da Bassam tamik'e tana gaishesa, sun d'auki kusan mintuna biyar tana yimasa cikakken bayani daga k'arshe tafad'a masa cewa yau d'innan za'aje da ita wajen scanning da zaran anyi sallar la'asar, godiya yayi mata sosai tare da sanya mata albarka sannan ya nufi d'akin, Billy na ganinsa ta washe baki cikin farinciki tace 


"Dady sannu da zuwa" cikin fara'a shima ya amsa mata da "yawwa Bilkisu ya jikin naki"


"Alhmdulillah dady naji sauk'i sallama kad'ai nake jira" Ummi ya kalla cikin sigar tsokana yace


"Umminsu mekike bawa Japanese d'innan tawa naga tak'ara haske da k'iba dubi fa yanda idanuwanta suka k'ara shigewa" gaba d'aya d'akin aka hau dariya banda Basmah data koma gefe tana kallon duk abunda ke faruwa da gefen idanuwanta, wata irin muguwar harara ta aikawa Billy dake faman yiwa dady kukan shagwab'a wai yadena fad'a yasa suna yimata dariya had'e da cewa


"Munafuka" Billy kam da batama san tanayi ba ta kalleta tace


"Wlh Allah dady yayya Basmah tafini k'iba, d'ibeta fa" gaba d'aya kowa ya juyo yana kallonta, indai k'ibace  ba wanda bai yitaba agidan nan sai ni Mahmud yafad'a yana dariya, hannu Ummi tasa akuncinta tana shafawa ahankali fuskarta d'auke da murmushi


"Babanah aikai da wuya idan zakayi k'iba don kai gaba d'aya jikinka sak irin na abbatine" wato mahaifin dady Allah ya jik'an rai, hannunsa shima ya d'ora akan nata yarike  


"Ummi aikuwa ni bana son irin jikin tsohon nan na fulanin rugga, nafison inyi irin jikin dadynah.." Kafin ya rufe baki dady yad'an rank'washesa akai


"Ai anriga angama, ja'irin yaro" haka dai suka yita firarsu cikin farinciki da walwala a lokacinne da dady yafahimci irin k'ibar da kowannensu sukayi, wani irin farinciki ne ya rufesa duk da cewa yana kewar mom amatsayin sa na mijinta hakan baisa kwanciyar hankalin data bayyana agidansa tab'oyu ba, sunanan  zaune aka kira sallar la'asar dady da yaransa suka nufi masallaci yayin da Ummi da 'yan matanta suka shiga toilet d'in dake nan cikin d'akin sukayo arwala don gabatar da sallah, bayan duka sun sallame su Billy da Batool suka gaida Ummi ita kuma Basmah takoma gefe abunta tazauna, da gudu Bilal da Bassam suka rugo suka fad'a jikin Ummi dake zaune a inda ta ida sallah, suma d'in gaisheta sukayi Bilal na fad'in Ummi muda Yaya zamuje wajen Small mom zakije? Kafin tabashi amsa sai ga Mahmud yashigo shima har k'asa ya duk'a ya gaida Ummi had'e da cewa


"Ummi zamuje wajen mom, idan faraaha tazo tafiya da lil sis wajen scanning saiki rakata, dady ya riga da yafita shida abokinsa yanzu?"


"Shikenan Babanah babu damuwa zaku iya tafiya, kugaisheda mom d'in taku sosai" 'Dan tsaki Basmah tayi


"Yaya nidai ina waje zan jiraku bazan iya zama ina saukar maganganun da basu kai ciki ba" a hasale Mahmud yayi kanta cikin b'acin rai da nufin falla mata marora Ummi ta dakatar dashi,


"K'yaleta Babanah! Babu komai Allah ya shiryeta" juyowa tayi ta kalli Ummi sannan ta bud'e d'akin tafita cikin b'acin rai. Shi kansa baisan lokacin da yakaiwa bangon d'akin naushi ba saboda yanda zuciyarsa ke tafarfasa, tsabar yanda launin idanunsa suka canza zuwa jajaye zaka d'auka barkono aka watsa masa aciki, baisan meyasa Basmah bata shakkar kowa ba, yazama dole ya taka mata burki takowace hanya, matuk'ar halinta yamik'e haka zata matuk'ar shan wahala arayuwa shi kuma abunda baya fata kenan, wurin Ummi ya dawo yana bata hak'uri bisa abunda Basmah tayi mata, shafa gashin kansa tayi had'e da cewa


"Kamanta Babanah ita yarinya ce, maza katashi kutafi marece nayi ko acan zasu kwana"


"A'a Ummi gaisheta kad'ai dady ya amince muje muyi"


Akan hanya ne Batool ta kalli Basmah


"Yayyah Basmah" basmah dake rufe da idanu ear piec lik'e akunnenta d'aya tace 


"Meye?"


"A gaskiya abunda kikayi d'azu baki kyautaba" har lokacin idanunta na arufe tace


"Meye kuma damuwarki tunda ba mom nayiwa ba"


Da k'arfi Mahmud yataka burkin mota cikin b'acin rai yace


"Fitarmun a mota kafin na k'irga uku" ko kallonsa batayi ba tabud'e gambun motar tafita abunta tana taunar cingam, ya dad'e kansa kwance a staring mota kafin ya tayar da motar suci gaba da tafiya,


"Yaya kayi hak'uri mukoma a d'aukota"


"K'yaleta Batool, tafiyar Rabin kilometer yarage ak'arasa, wannan shine punishment d'in da ya kamaceta, yanzu idan za'ace kifad'i halin Ummi miye matsalarta data cancanci nuna k'iyayya daga wajenmu, yakamata ace munbar matsalar su can atsakaninsu bawai murik'a saka kawunanmu aciki ba, inajin zafi da rad'ad'i idan naga matsaloli na faruwa acikin gidanmu, shin kin tab'ajin Billy tayiwa mom rashin kunya?, yazakiji aranki idan ki kaga ta aikata haka ga mahaifiyarki wacce ta haifeki, ya kamata ace izuwa yanzu dukkaninku kun canza Batool! ku 'YAN UWANA NE kuma suma su Billy 'YAN UWANA NE, ina so muso junanmu, mubar su mom da abinda ke a tsakaninsu muyita yimasu addu'a har zuwa ranar da suma zasu so junansu, amma kina kallo 'yar uwarki kullum shashancinta sai k'aruwa yakeyi,


"Kayi hak'uri Yaya nadad'e da fahimtar Ummi ada ina yimata kallon munafuka wacce bata son mu amma fad'an zaman nan danayi da ita sai nafahimci tamafi sonmu akan mom" jawo Bilal tayi ajikinta sannan taci gaba da cewa nafahimci su Bilal 'YAN UWANA NE kuma ina sonsu, zance gaba da lurar da yayya Basmah har zuwa lokacin da ak'idar da mom tasaka mana arai zata fita cikin zuciyarta" wasu zafafan hawaye ne suka fito masa a idanu saboda jin dad'in canzawar Batool, yatabbata da sannu matsalolin gidansu sunfara ragewa, saita madubinsa yayi suka had'a ido da ita ya sakar mata murmushi


"Nagode sosai da fahimtar ta 'yar uwa....




Post a Comment

0 Comments