TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 56

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕

Page 5️⃣6️⃣

________


A firgice ya kai hannunsa baki ya rufe kafin ya sake jin tace, "Muryarka ta dashe cigarette kk ta sha ko?" Shiru yyi kafin ya fara in'ina yana faɗin, "A'ah... ba.. ba sha.. nake..yi ba" taɓe baki tayi kafin tace, "Ko ma meye dae, ba dan shi na kira ba" sosai abunda ta faɗa ya kashe masa jiki, hakan yasa muryarsa tayi sanyi sosai sae ji yyi tace, "Ina so naje gidan Aunty Jamilah so I called to ask for your permission!" Kallon watan dake haske duka sararin samaniya yyi kafin yace, "Okay sae kin dawo, take care!" Yana faɗan haka ta kashe wayar, hannunta ta kai ta dafe zuciyarta dake bugu da sauri sauri sosai tayi kewarsa amma taurin kai baze barta ta sanar masa ba dan sarai taji yadda muryarsa bata ɓoye cewar yana cikin damuwa ba, ta daɗe a zaune tana murmushin jin muryarsa da tayi bayan lokacin da suka shafe ba tare da taji muryarsa ba, ta jima a zaune kafin ta miƙe ta wuce ɗakinta. 


Around ƙarfe ɗaya bayan sallar Azahar ta shirya ta fice daga gidan, ba dan taso ba Daniel ya kaita gidan Ya Jamilah sae dae dan tasan umarnin Abideen kawai yake bi kawai kuma bbu yanda ta iya. Tana shiga gidan Aunty Jamilah suka gaisa kafin suka fara hira cikin ƙauna nan Ya Jamilah tace, "Ina da wata ƙawa a Sudan kuma kinsan suna da likitoci sosai acan, tace mun sun samo wani magani da take son ki gwada kuma tana sa ran InshaAllah za ki samu lafiya completely!" Wani daɗi ne ya taso zuciyar Safeerah nan ta yi mata godiya, can bayan sallar Laasar suna zaune a parlour suna taɓa hira sae jin sallamar Umma ita da Yusra suka yi, suna gama gaisawa Umma ta kalli Safeerah tace, "Saurin me kike? Dama daga nan gidanki zan wuce na samu shi yaro da kika shanye!" Shiru Ya Jamilah tayi tana kallon Umma ga Yusra a gefe sae dariyar mugunta take yi a faƙaice, can Ya Jamilah ta samu bakin magana tace, "Umma wacce magana kike yi haka?" Kallon banza Umma tayi mata tace, "Kema ina zuwa kanki dan haka kiyi mini shiru, wato sae nace kizo gida amma shiru sae ki ƙi zuwa saboda kin raina ni ko?" Saukar da kai ƙasa Ya Jamilah tayi tace, "Umma idan bae bani izinin fita ba ai bbu hali na fita!" Tsaki Umma tayi tace, "Ke kika sani, ke kuma ina kika kai mun yaro ko kin shanye shi ne har ta kai baya iya fita?" Kai a ƙasa Safeerah tace, "Umma ai an kirashi a gurin aiki ya tafi, baya gida" tsaki Umma tayi tace, "Munafuka ko ma meye dai, ba auren ne baya so ba toh gashi nan nasaka an saka rana nan da wata shida komai bin bokayenki baki isa kisa a fasa ɗaura auren nan ba!" Rau Safeerah tayi da ido tana jin gabanta na faɗuwa, da sauri Ya Jamilah tace, "Umma wacce kalar magana kike yi haka na bin bokaye ana zaune lafiya?" Taɓe baki Umma tayi tace, "Shashasha kina ina ta shanye shi Abideen ɗin, nan ya siya mata mota kuma yake yawo da ɗan pant ɗinta a motarsa idan ba wanda aka shanye ba waye zai yi haka!" Cikin takaici da sanyin murya da shagwaɓa Ya Jamilah tace, "Kai Ummaaaaaaa!" Juyawa Umma tayi tace, "Ku kuka sani ai auren Abideen da Zaytoona bbu fashi, gashi nan alawa ne da cingam na kawo muku ai baku cin goro dan haka ban haɗo dashi ba!" Tana faɗin haka ta juya ta fice abunta, harara Ya Jamilah ta watsawa Yusra tace, "Kin zama munafuka ko?" Turo baki Yusra tayi tace, "Wallahi Yaya ba haka bane!" Leƙo kai Umma tayi tace, "Ina Yusran take ko suna nan suna yi miki huɗubar banza ne?" Da sauri Yusra ta miƙe ta bi bayan Umma abunta, ajiyar zuciya Safeerah ta sauke ta jawo ledar ta ciri Chewing gum ɗin ta tura a baki tace, "Allah Ya sanya alkhairi kuma ya kai mu lafiya!" Cikin mamaki Ya Jamilah ta zuba mata ido ganin ko kishi bata nuna ba, nan kuwa deep down Safeerah ji take kamar zuciyarta aka saka wa wuta, idan ma tayi tunanin cewa zatayi sharing mijinta da wata ji take kamar ta kurma ihu amma ganin Ya Jamilah a zaune yasa ta kame steeze and composure!🫠🤭


*****

Tun lokacin da ta kirashi bata sake kiransa ba har kusan wata biyu suka shuɗe, Abideen da yake can kuwa sae ƙara lalacewa yakeyi a kullum ranar Allah dan baya da aiki sae shan sigari sae kallon wata gashi ya rasa focus gaba ɗaya dan ko attack suka kai sae Beta ya rinƙa kula da komai idan ba haka ba tsab za'a harbeshi. Tana zaune a parlour tana kallon wani show a makeken TVn dake manne da bango wayarta ya hau ringing, da saurinta ta ɗauka ganin numbern Abideen yake kira, ajiyar zuciya ta sauke ta gyara murya tana jin wani farin ciki na rufeta, tana ɗauka taji ance, "Hello madame!" Haɗe girarta tayi tace, "Where's my husband?" Daga jin muryarsa ma wani yare ne, da sauri wani ya karɓa yace, "Madame, ya fita amma kiranki mukayi mu roƙe ki!" Shiru tayi tace, "Roƙo kuma?" Da sauri yace, "Eh madam! Idan akwai abunda ya haɗa ki da Boss dan Allah ku shirya wallahi yana affecting ɗinsa da mu gaba ɗaya!" Ta tsorata da jin haka sae tace, "How?" Shiru Beta yyi kafin yace, "Tun da nake cikin SFT ban taɓa ganin an harbi Boss ba sae yau" a take idanunta suka fara zubar da hawaye tace, "Me ya same shi?" Ajiyar zuciya ya sauke yace, "wallahi yyi losing focus gaba ɗaya ko abinci baya son ci, he's not in his right mind kwata kwata baya iya yin komai dan Allah ki kira shi ku shirya wallahi at this rate ma za'a iya kashe shi a battle, ki taimaka, please ma!" Shiru tayi tana goge hawayen idanunta kafin tace, "Is he alright?" Shiru Beta yyi yace, "He is always smoking tunda muka zo" da sauri Bravo ya ƙaraso yace, "He's coming, let's go..." da sauri Beta da yake magana da ita yace, "He's coming, give it a second thought please!" Yana faɗin haka ya kashe wayar suka gudu kafin Alpha yazo ya tarar dasu dan kamar jira yake ayi masa abu ya fara masifa, zuwa lokacin da ya ƙaraso bbu kowa a ɗakin duk sun tafi, kwanciya yyi akan airbed ɗinsa yana sauke numfashi a hankali.


Bae daɗe da kwanciya ba yaji wayarsa na ringing, zaro wayar yyi daga ƙasan pillow ganin sunanta kawai ya saka shi saurin yin murmushin da shi kansa ya manta last time da yyi, yana picking muryarta ya fito tana faɗin, "Yaaa Abi-deen...!" Shiru yyi yana murmushi ga farin cikin jin muryarta a kunnensa bayan lokaci mae yawa daya shuɗe, jin bae amsa ba yasa ta sake faɗin, "Yaaa Abideen, are you there?" Murmushi ya sake yi amma sae kuma ya lura kamar kuka take yi can dae ya samu ƙarfin gwiwar cewa, "Uhm, ina jinki!" Jin haka yasa ta kashe wayar tana jin wasu sabbin hawaye suna kwace mata dan sosai taji muryarsa ta dashe kuma tayi deep sosai kamar wani wahalallen mashayi, wani zafi taji zuciyarta na yi mata jin baya son cin abinci kuma an ya samu harbi a hannunsa. Kuka kuwa ta fara hajaran majaran kamar zata shiɗe, tana cikin kukan taga ya dawo mata da kiran amma video call, saurin picking tayi nan ta sake ganin abun da ya sake tayar mata da hankali, shi yana farincikin jin muryarta da ganin fuskarta amma gaba ɗaya ita kuka takeyi, ganin hawaye a fuskarta yasa a tsorace yace, "Me ya faru? Meysa kike kuka? Ki faɗa mun, me aka yi miki?" Sheƙan kuka tayi tace, "Ba kai bane!" Murmushi kawai yyi jin cewar Safeerar shi ce har yanzu kamar zata yi masa shagwaɓa, kansa ya sosa a faƙaice kafin yace, "Me nayi?" Hawaye ne ke sake zuba daga idanun nata ganin yanda ya rame yyi baƙi ya lalace gaba ɗaya, share hawaye tayi tace, "Me...yasa... ka ...rame haka?" Sosa kai ya sake yi yace, "Aiki ne yyi mun yawa!" Saurin ɗauke kansa yyi yana gyara zama a nan ne ta hango bandage ɗin dake a hannunsa inda aka harbeshi. Sabon kuka ta fara tace, "Kaji ciwo ma!" Taɓa gurin yyi ya kalleta yana yi mata murmushi, yace, "Ai bbu zafi bae kai rashinki zafi ba!" Wasu sabon set ɗin hawayen ne suka sake zubowa daga idanunta nan yace, "Kiyi shiru ki dena kukan haka ko so kike ki tayar mun da hankali kinsan bana son kina kuka!" Kai ta fara ɗaga masa kafin ta share hawayen tace, "Ka ci abinci?" Girgiza mata kai yyi kafin ya jawo abincinsa da yake a takeaway ya fara ci yana yi mata murmushi, ɓata rai tayi bayan ta sake lura da yadda muryarsa tayi deep sosai gashi ta dashe, kallon yanda ta ɓata rai yyi yana mamakin me zata ce yanzu, tamau ta ɗaure fuska tace, "Have you been smoking?" Zare ido yyi yana neman ƙaryar da zai yi mata amma in'ina ce ta fita yana cewa, "A...ah..ka..kawai..dae.." juya ido tayi tace, "You better quit it!" Saurin ɗaga kai yyi ya sara mata yace, "Yes Ma!" Dariya suka kwashe dukansu biyu kafin ta zauna tana kallon yanda yake cin abincin tana tayin murmushi cikin farinciki, daga baya bayan ya gama tace, "You know I love you right?" Cikin farin cikin jin furucinta yasa yace, "Really?" Kai ta ɗaga masa kafin tace, "I do, so come home safe, okay?" Kai ya ɗaga mata cikin farin ciki yace, "InshaAllah!" Dariya tayi tace, "I saw your letter, me zaka faɗa mun?" Sosa ƙeya yyi kafin yace, "Sae na dawo zan gaya miki!" Dariya tayi kafin tayi kissing screen ɗin wayarta tace, "Naka ne! Good night?" Kai ya ɗaga mata nan tayi ƙit ta yanke wayar, sosai ta fara yin kuka tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda tsabar takaicin ganin yanda mijinta ya lalace inda shi kuwa abincinsa ya ci mae kyau yana ta murmushi da farincikin ganin matarsa da yyi da jin furucinta na tana sonshi. 



#Team Safeerah, say hello!🫠🔥

#Team Zaytoona, say hi!🫠🥂


* Don't forget to vote lovelies! 😘🥂


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments