TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE 1-46

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHIM INA MAI FARINCIKIN SAKE HA'DUWATA DAKU MASOYANA ACIKIN WANNAN SABON LITTAFI NAWA MAI SUNA A SAMA👆 TARE DA ROK'ON UBANGIJINA DAYA BANI IKON KAMMALASA CIKIN K'OSHIN LAFIYA DA AMINCI, WANNAN LITTAFI HAKK'IN MALLAKA TANE BAN YARDA WANI/WATA A SARRAFASHI TA WATA SIGA DABAN BA, YIN HAKAN KUSKURE NE KUMA LAIFINE, LABARIN DAKE CIKI GASKIYANE YAFARU KUMA YAKAN CIGABA DA FARUWA ACIKIN AL'UMMA DON HAKA IDAN YA DACE DA HALINKI SAI KIYI GAGGAWAR CHANZAWA FATANA SHINE DANI DA KE 'YAR UWA MUTARU MUGYARA DON KYAUTATA GOBEN RAYUWARMU A CIKIN ZAMANTAKEWAR AURATAYYA...INA KIKE QAWAR ARZIKI *SAINAH ABUBAKAR (UMMU MINAL)* DUKKANI WANNAN LITTAFIN DON FARINCIKIN KINE, INA ROK'ON ALLAH DAYA HA'DAKI DA ALKHAIRANSA ADUK INDA KIKA SHIGA👏 INA SO KISANI BILLY S FARI NA K'AUNARKI HAR ZUWA LUMFASHINTA NA K'ARSHE, *MOM HAFSAT RANO, YA HAJJA CE,  MOM HAFSAT XOXO AND MY LITTLE PRINCESS SALMAH ABALI* INA SO KUSANI DUK WANI ALK'ALAMI NAWA DA ZAN 'DORA WAJEN RUBUTU CIKE YAKE DA ALFAHARI DAKU TARE DA TSANTSAR K'AUNARKU  FISABILILLAH!, BURINA ARAYUWA SHINE ALLAH YABAKU FARINCIKI MAI 'DOREWA ACIKIN RAYUWARKU HAR IZUWA AL-JANNAH FIDDAUSI👏



💎Page______1💎



    Wata 'yar kyakkawar yarinya ce mai yanayi da k'irar mutanen Japanis, wankan tarwad'a ce da baxa ta wuce 'yar kimanin shekara goma sha hud'u 14 da haihuwa ba. Ita na hango zaune akan matattakalar da zata sadaka da babban falon gidansu dake nan k'asa, ta buga uban tagumi hawaye na zubar mata a idanunta biyu, in ban da tunani da kukan bak'in ciki ba abunda take yi.


"Billy..!Billy..!!...Billy..!!!" 


Ta jiyo muryar yayan tah mahmud yana kiranta, kyakkyawan saurayi ne d'an kimanin shekara 27 dake tafe daga abayanta yana kiran sunanta cike da shauk'in dake nuna tsantsar k'auna, shak'uwar dake tsakaninsa da ita, tsananin k'unci da bak'in ciki da suka tarar mata a zuciya yasa ta kasa amsa kiran yayan nata da take matuk'ar k'auna. Mahmud ya kasan ce shine babban d'ah acikin familyn alhaji Bashir mai furniture, yana da k'anne guda biyar uku mata biyu maza Batool, Bilkisu, Basmah, Bilal da kuma Bassam.


A hankali ya k'araso wajen ta tare da dafa shoulder d'inta fuskarsa cike da damuwar yanayin da ya ganeta a ciki yace.


"Sister me yake faruwa dake ne kika zo nan kina kuka, ko wani abun ne aka yi maki? fad'amun don ku 'YAN UWANA NE! bana son abunda zai tab'a mani ku" 


Kallonsa Bilkisu tayi tare da kallon gefe gefensu taga babu kowa, turo labenta na k'asa tayi tana neman sake fashe masa da wani sabon kukan, da sauri Mahmud yasa yatsansa akan labbanta, 


"Shiiiiii....bana son kukan nan sister, fad'amin waye ya tab'a min ke?" ya Karashe maganar yana mai goge mata hawayen dake neman gurbin zama  a fuskarta.


"Yaya don Allah kafad'a mun wane laifi na yiwa small mom da ta tsaneni, ko ince ta tsane mu a rayuwar ta please yaya fad'amun me yasa take yi mana haka..?!"


"Ke Billy!..ba dai d'an na wane kika zaunar kina fad'a masa cewa na tsaneku ba, saboda iya makirci har kina fitar da wasu k'walla tsabar munafurci ko?"


Muryar small mom ce suka jiyo fitowar ta kenan daga bedroom rik'e da hannun bilal ta turo k'eyarsa tare da hankad'a shi har sai da ya fad'i k'asa tana fad'in haka, 


Da sauri Mahmud ya k'araso wajen ya d'auke bilal dake k'asa yana kuka ya rungume sa a jikinsa ransa a b'ace yana kallon mahaifiyar tasa kamar zaiyi kuka, Bilkisu na ganin haka ta ruga aguje wajen mahaifiyarta don ta sanar mata,


"Haba mom..! fisabilillahi meye haka kika yi? yanzu d'an wannan yaro me yayi maki da kike neman saukar masa da b'acin rai shima?" 


Mahmud ya k'arashe maganar had'e da kallon bilal da yayi lamo (kwance) a jikinsa yana shasshekar kuka, cike da masifa small mom take cewa...


"Banda iskancin yaron nan taya za'a yi yaje har k'uryar d'aki na ya watsarmin da kayan dake kan madubi na, gashi duk sun farfashe don tsabar k'eta da muguntar da aka koya masa shima.."


"Yanzu mom bilal d'in da iya karsa shekara uku yasan wata k'eta da mugunta?" kallon bassam dake gefen small mom yana dariya yayi tare da d'aukesa mari kawau!


"Hey.. stupid boy dariya ma kake yi min don ubanka? wallahi mom yanzu haka wannan shed'anin yaron ne yayi maki b'arnar kika yi zaton Bilal ne"


"Kai Mahmud bana son sharri da yarfe, bassam d'in ne zai fasa mani kaya? In banda kana shashasha taya zaka yiwa d'an uwanka sharri kaso bare kuma kafifita shi akansa?


"A'a mom sumafa 'YAN UWANA NE don me ba zan so suba?, idan har kince sharri na yiwa Bassam dake da shekara biyar ba zai iya yi maki b'arna ba taya zakice Bilal ne yayi mom? don Allah mom kidena yin irin wud'annan abubuwan bana so, Bilkisu da Bilal 'YAN UWANA NE ko kad'an bana farin ciki da abunda zai cutar mani dasu"


 Yana rufe baki sai ga Ummi ta fito tare da Bilkisu biye da ita, murmushin k'arfin hali ta yiwa Mahmud ba tare da takalli inda mom d'insa take tsaye ba ta karb'i Bilal, cike da takaicin abunda mom tayi Mahmud yace


"Ummi kiyi hak'u...." Be k'arasa ba Ummi hak'uri ba yaji k'arar Bilkisu dake gefen ta, juyowar da zai yi kenan ya hango Batool rik'e da gashin kanta billy tana ja tama fad'in.


"Munafuka meye na zuwa ki wani kirawo Ummi sai kace kashesa aka yi? wallahi mom yarinyar nan taji bak'in hali, yanzu haka ma ita ta turasa ya fasa maki kwalab'en turare dake kan mirror, nikam ban san ya aka yi wud'annan mutanan suka zamo jinin muba, na tsanesu mom don nikam ba 'YAN UWANA NE ba...!"


A fusace Mahmud yayo kanta "Batool dama ba kida hankali? jinin namu kike cewa haka? to idanke ba 'yan uwanki bane ni 'YAN UWANA NE kuma don ubanki yau sai kin fad'amun ko 'yan uwan waye a gidan nan" 


Belt d'insa ya cire tare da yowa kanta, sanin halinsa yasa ta saki Bilkisu ta ruga aguje tana ihu yana binta, ganin da gaske ya keyi yasa ta shiga k'eta ihu tana fad'in,


"Wayyo yaya don Allah karka dukeni da zafi wlh, mom kiceceni, wayyo na bani wlh yaya 'YAN UWANA NE su...!, YAN UWANA NE...!! su yaya, wlh na tuba suma 'YAN UWANA NE....!!!


Mahmud babban yaron Alhaji Bashir Mai funitures mutunen da yayi suna wajen rik'ongaskiya da amana yanada mata biyu da yara shidda ukku maza ukku mata yana matuk'ar kula da iyalansa yanda yakamata babu wani abu da zasu nema surasa indae aduniya ne haka kuma yana kwatanta adalci atsakanin matansa da 'ya'yansa yanda yakamata, Amma kash har yanzu abuguda ke damunsa, shine yanda  matarsa kuma amaryarsa bata son a zauna lafiya wanda yayi iya k'ok'arinsa yasan ko meye dalilinta yagagara, lokutta da dama yakan tambayeta meyasa takeyin hakan sai tace masa Bakomai, Hajia Aisha itace uwar gidansa mace mai hakuri, juriya da kuma K'ana'a abu mafi burgewa atare da ita shine gaskiya macece  kaifi d'aya Nata son munafurci arayuwarta shiyasa alhaji bashir KE matuk'ar k'aunarta aransa Sunyi aurena da ita bisa zab'in iyaye kuma sae Allah yasa akadace da suna k'aunar junansu sosae, Bayan sunyi aurena da shekara bakwae Hajia Aisha ko b'atan wata bata tab'ayi ba balle asa ran haihuwa mahaifin alhaji bashir ya auro masa 'yar amininsa mai suna hussaina, haka alhaji bashir yayiwa mahaifinsa biyayya yazauna da hussaina bisa amana badon yana Sontaba, Hajia hussaina macece mai son mulkar duk wani wanda take tare dashi kasancewar mahaifinta sarkine yana mulkar wani gari acan cikin birnin kano, ko kad'an tatsani taga fifikon wani akanta tanada matuk'ar izza daji dakai wanda sune suke

taimakonta wajen walak'anta natare da ita harma dana nesa, in kaga tana son mutum to tabbas yana bintane yana yimata yanda take so abunda Hajia Aisha Kenan takasa d'aukar mata shiyasa zamansu yakasa dai daita duk da kuwa mijin nasu na iya k'ok'arinsa. 


Wata tara cikin na goma da kawo Hajia hussaina ta haifawa alhaji bashir 'yarsa kyakkyawa sosae Hajia Aisha tanuna farincikinta afili duk da ana kyararta akan yarinyar hakan besa tayi fushi ba takoma gefenta,  Kwatsam ranar suna Alhaji bashir ya rad'awa 'yarsa sunan hajia Aisha sbd tausayinta da yakeji na bata haifa ba kuma yayi hakan ne saboda ya faranta mata kamar yanda take k'ok'arin faranta masa acikin dukkanin alamurransa,


Haka kuwa akayi Hajia Aisha tayi farincikinki sosai tare da yiwa mijin nata godiya tana kuka don tsabar jin dad'i, 


Lokacin da Hajia hussaina taji sunan 'yarta ba k'aramin bakin ciki tayiba duk da soyayyar da akeyiwa Yarinyar hakan bai hanata fatar inama bata haifeta ba, kwanaki biyu da suna yarinyar ta koma sanadiyar Typoid data yimata mugun kamu, a maimakon Hajia hussaina tadamu sai tanuna ita k'arama da yarinyar takoma duk da ko tanajin radadin rashin 'yar tata azuciya,  sosai Aisha tayi kukan rashin takwarar tata tare da fatar Allah yabasu wata mai albarka haka ta fannin alhaji bashir ya damu matuk'a da rashin yarinyar saboda son da yake yimata daga karshe dai duk suka tattara suka  barwa Allah ikonsa, Bayan shekara d'aya hussaina tasake haifo yarinya kamarta sak da alhaji bashir amma cikin ikon Allah ko minti goma batayi aduniya  ba itama tarasu, wannan karon kam Hajia hussaina tafi kowa shiga tashin hankali tayi kuka sosai rungume da yarinyar bayan tarasu halin d'ah da mahaifi saida akayi dagaske sannan akarabata da gawar yarinyar, bayan wash kwanaki Hajia hussaina ta fara b'ullowa da makircin wai Hajia Aisha ke kashe mata yara don ita bata haihuwa haka tabi dangin alhaji tana cewa ai asirine Hajia Aisha keyimata yaranta namutuwa don ita bata haihuwa, nan take Aisha tafara samun matsaloli da dangin mijinta ciki Kuwa hadda mahaifiyarsa dake matukar sonta, k'aunarsa k'waya d'aya kad'ai takejin sanyinta wato hafsat itama saboda jininsu ya had'u da ita tun kafin akawo Hajia  hussaina tariga tasan halinta kuma tasan mezata iyayi da wanda bazata iya ba shiyasa bata shiri da Hajia hussaina ko kad'an,


Alhaji bashir najin suruttan dake yawo acikin danginsa wai Aisha nakashe masa 'ya'ya saboda ita bata haihuwa amma daidae da rana d'aya betab'a bari sukayi tasiri azuciyar saba, wannan abun ya matuk'ar k'onawa hussaina rae don haka tafara kukan wai Hajia Aisha tarigata shanye alhaji baya ganin laifinta dole itama ta tashi tsaye, wannan karon wata goma hussaina tayi bayan haihuwarta tasake haifo santalelen jaririnta kyakkyawa kamar ba ita ta haifeshi ba,  kowa farinciki a fuskarsa baya misaltuwa Anata fad'in alhaji yasamu magaji, Aisha kuwa duk yanda taso taga yaron ta d'aukesa aka hanata acewarsu wai  umurnin mahaifiyar alhaji ne tace kada abari ta d'auki yaron, ran alhaji ya matuk'ar b'aci akan wannan abun da akayi  mata don haka ya riko hannunta suka bar d'akin tunda Aisha take bata tab'a kukan rashin haihuwaba sai yau...kuka maitsanani da ban tausayi tafashe dashi tana cewa


" _Ya rabbhi habli minasswaliheen_"


Cike da tausayawa ya rungumota


"Amin.... Aisha kiyi hakuri komai yanada lokaci insha Allah kema naki nazuwa"

 

Anan taci gaba da KIMANTA Tana tambayarsa metayi da Hajia tahana tadauki dansa jininsa shidae hakuri kawae yadinga bata tare da kalaman da zasu kwantar masa da zuciya aransa kuma yana jin rad'ad'in zafin kukan da Aisha keyi da kuma abunda akayi mata tun  daga ranar yad'au alkawarin ko dukiyarsa zata k'are tun daga nan k'asar har zuwa k'asashen waje sae yakai Aisha an nema mata  maganin matsalar data hanata haihuwa itama tahaihu, haka akaci gaba 

da hidimar biki Aisha bata tab'a d'aukar jaririnta ba, ga wani irin maseefar son yaron da Allah ya azo mata ana gobe suna saega hafsat kanwar alhaji ta iso wajen buki da yake acan borno tayi aure har da yaranta biyu shiyasa bata samu isowa da wuriba.


Nan yayan nata ya zayyana mata abunda hajiya tace da yake shima bayada abokin kaiwa kukansa ko shawara sai ita kasancewar tanada hankali da tsinkaya gashi itace auta ad'akinsu.


Cikin b'acin rai tace "haba yaya wlh kabani mamaki yanzu don sunce haka Saeka biye masu tanaji tana gani jininka yayi mata wahalar d'auka da gani to wlh tun daga hussaenar har zuwa munafukan dake tare da ita basu isaba" Cike DA isa tabar falon nasa tanufi d'akin hussaina ko kallon wud'anda ke wurin batayi ba ta d'auko jaririn

tafitowarta dashi  Tana hucin tab'ani inka isa, Kai tsaye tashiga dashi d'akin Hajia Aisha dake kwance akan gado tunanin duniya duk yabi ya isheta ta kwantar dashi dai dai fuskarta had'e da cewa 


"Ga d'anki nan nakawo maki kigani kuma kid'aukesa injini babu wanda zai hana"


Rungumesa Aisha tayi  cike da soyayya tana tofa masa addu'o'in kariya fuskarta d'auke da farincikinki tamkar ance yazama nata, man hafsat tayita bata hak'uri da fad'an tacirewa kanta damuwa komai yanada lokaci, sosae Aisha taji dad'i  tayi mata godiya, alhajine ya shigo d'akin yana kallon yanda Aisha tayi kyau da jaririn a hannunta yace


"Masha Allah kema Allah ya kawo maki naki rabo mai albarka"


Duk suka amsa da amin


Anan hafsat  tacewa yayanta ta rad'awa yaron suna mahmud sae kuma akaci sa'a da sunan mahaifin Aisha kenan shiyasa takarajin son yaron aranta har take kiransa da babana. 


Tunda aka haifi mahmud   hussaina bata sake haihuwar saida ya shekara goma da wata biyar sannan hussaina ta samu ciki ta hafo 'yarta har lokacin Aisha na shiru  bata haihuba sun karad'e duk wasu kwararrin asibitotan dake k'asarnan amma ba'a dace ba, Ranar suna aka rad'awa yarinya Basmah.


Ba'ajimah da haihuwar basmah ba wajen aikinsu Alhaji aka turashi k'asar Egypt yayo couse d'in shekara biyu hakan yasa yafara tafiya da Aisha shima saida akayi daru da hussaina kafin ta amince ai kuwa suna isa Alhaji yamaida hankali sosae wajen kai Aisha asibitota ana duba lafiyarta, duk da haka dae  ba'a dace ba har shekarar ta k'are bayan sun dawo kuma saega hussaina tafara laulayi lokacin basmah nada shekara d'aya da wata biyu da haihuwarta don haka tacireta ga nono,


Alhaji yaso barin hussaena gida ya komawarsa shikad'ai tunda cikin nabata wahala ga kuma k'aramar yarinya agabanta abun zai zame  masu lalura idan yatafi da ita don haka sai yayi tunanin yabarta gida, Aishace ta nuna masa illar da abun zai haifar k'ara yatafi da ita inyaso itama ya kaita asibiti har tasamu lpy nan yake tambayarta to ya zayayi jinyarta ga basmah da batayi wani wayo ba, Murmushi tayi tace idanka amince itama momynsu ta amince to kubar babanah da basmah awurina insha Allah zankula maka dasu kafin kudawo, koda alhaji yafad'awa hussaina cewar za'abar mahmud da basmah hannun Aisha k'in amincewa tayi saeda yanuna mata idan har bata amince ba toshi ba inda zaije da ita tazauna gida saboda bazae iya kwasar yara yaje dasu wata qasaba gashi ita da zata kula dasu batada isassar lpy sannan ta amince badon ranta yaso ba. 


Bayan tafiyarsu hussaina qaddara Egypt Aisha ta rungumi yaran hannu biyu kamar ita ta haifesu suna samun kula da tarbiya awajenta sosai, watansu biyu da tafiya kwasam Aisha tafara ciwo tana zuwa asibiti aka tabbatar mata da cewa tana d'auke da  juna biyu d'an kimanin wata hud'u sai taji abun kamar a mafarki saboda lokacin shekararta goma sha tara da wata bakwai kenan bata haihuba, saida Aisha taje kusan asibiti biyar saboda ta gasgata cewa tanada ciki ana tabbatar mata da cewa tanada juna biyu sannan tayadda, tayi farinciki sosae don har da kuka tayi sannan tayita yiwa Allah godiya da ni'imar da yayi mata, hafsat tafara yiwa albishir ita kuma tace takama bakinta karta fad'awa kowa sai dae idan yafito agansa hatta yayan nata cewa tayi kar tafad'a masa sae inya zo  mata nan da three months yaga kyakkyawar tarba, haka kuwa akayi saeda yazo yaganewa idonsa, tsabar farinciki har d'aukarta yayi kamar k'aramar yarinya yana dariya tare da yiwa Allah godiya daya nuna masa wannan ranar, Lokacin da  labari yaje kunnen hussaina ba k'aramar tsanar Aisha tak'araji aran taba, itadai Aisha tazame mata qadan garen bakin tulu gashi dama hausawa nacewa _hasada ga mai rabo taki ce_


Bayan wata biyu  hussaina tahaihu tahaifi 'yarta da aka rad'awa suna Batool bayan sati uku itama Aisha ta haifo santaleliyar 'yarta da akasha buki bidiri taci suna Bilkisu, daga lokacin hussaina tasake dage damtse wajen karfafa k'iyayyar da take yiwa Aisha da ganin cewa sai taraba Aisha da alhaji, amma da yake Aisha ta rik'e Allah sosai babu abunda yafaru da ita, 


Bayan haihuwar Batool da Bilkisu saeda hussaina tayi haihuwa uku yaran basa zuwa da rai kafin tasake samun wani cikin lokacin su Bilkisu nada shekara takwas da haihuwa tahaifi d'anta aka rad'a masa suna Bassam,


Bassam nada shekara uku da haihuwa sukuma su Bilkisu nada shekara goma sha d'aya Aisha tasamu ciki ta haifi d'anta Bilal ganin yanzu Aisha nada yara biyu ita kuma hud'u yasa hussaina tafara k'orawa Aisha jawabi da hantarar yaranta Amma Aisha bata tab'a tanka mata ba sai dai tayita haushinta inta gaji tabari, yanzu kam alhaji bashir yatara familynsa gwanin ban sha'awa yayinda Hajia Aisha wato Ummi uwar gidansa kenan take da 'ya'ya biyu Bilkisu da Bilal ita kuma Hajia hussaina small mom kenan wato amarya take da yara hud'u, Mahmud, Basmah, Batool da kuma Bassam.

Mahmud shine babba yanada shekara 27 sai Basmah dake bimasa tanada 16years sai Batool da Bilkisu 14-15years sai Bassam 7years Bilal kuma 3years.


_Back to the story_
































Mr's huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page______2💎



Kafin batool ta rufe baki taji saukar belt ajikinta, cikin wata irin kasalalliyar murya ta samu damar yin ihun da yasa small mom rugowa aguje ta ture Mahmud gefe tana fad'in 


"Amma wannan yaro baka san ciwon kanka ba wallahi! Yanzu akan waccan munafukar yarinyar kake nema kajiwa 'yar uwarka ciwo?, to Wallahi tunda naga rashin hankalin naka na nema ya wuce gona da iri saina sab'a maka rai, shashasha da baisan inda keyi masa ciwo ba" Cikin dak'ilalliyar murya dake nuna k'ololuwar b'acin rai mahmud yace.


"Amma mom kinajin maganganun da take fad'a fa, ko kad'an basu dace ba, don me zata yi hakan?" 


Sake da baki small mom ke kallonsa kafin ta jefa masa wata irin muguwar harara tare da sakar Masa dakkuwa tana cewa,


"Ungo nan marar kunyar yaro, Anya mahmud nina haifeka kuwa? Anya ba musayarka akayo mani a asibiti ba?  har wani tambayana kake don me take yin hakan, to don ubanka take yi, nace don ubanka take yi kaji ko?  Meye abun b'acin rai da har zaka kaiwa 'yar uwarka duka?, idan kace su 'yan uwanka ne ita d'in meye taka da zaka nemi ka illata min ita akan wud'an can zuri'ar da basu gaji arzik'i ba sai dai suci  banza..."


Da k'arfi mahmud dake duk'e da kansa k'asa ya d'ago yana kallon gefen dasu Ummi ke tsaye saboda yanda take nauyin maganar da mom d'insa kefad'a don ya san da gangan small mom ta fad'i haka saboda kawai a b'atawa ummi rai, Cikin Sa'a yaga ummi bata wajen, tunda ummi taga small mom ta fara fad'a taja hannun Billy har Lokacin bilal na sab'e akafad'arta ta bar falon, wata irin ajiyar zuciya mahmud yayi tare da cewa.


"Alhamdulillah" sannan ya jefawa batool dake tsaye a abayan small mom tana shafar shoulder d'inta tana hawaye na belt d'in daya shimfid'a mata a jiki yace,


"kuma kitabbatar kinkai mini abuna d'akina, pls mom kiyi hakuri kidena fad'ar irin wud'annan kalaman saboda samu da rashi duk na Allah, wannan abun da kike yi babu kyau tamkar training ne kike yiwa wannan dak'ik'iyar yarinyar" Mahmud ne ya sake fad'ar haka Bayan ya maida kallonsa ga mom da tun d'azu ta k'ara hasala da kalamansa, azuciye ta d'auko belt d'insa daya jefawa Batool dan ta kai masa a d'akinsa ta nufo wurinsa dashi,


"Kai yaron nan bari nayi maganinka tunda naga kana nema karenani sannan banza da wofi tun kafin kazo duniya nake shan wa'azi"


Da gudu mahmud ya bar falon yana dariyar kalaman mom d'insa a zuciyarsa kuma yana rok'on Allah daya sauya mata rayuwa ta gane cewa sumafa su bilkisu 'yan uwansu ne bai kamata ta dinga neman raba masu kai ba saboda zafin kishi, da wannan tunanin ya nufi part d'in Ummi, Zaune ya tarar da ita tana yiwa su Bilkisu fad'a akan sudena zuwa suna yiwa small mom abunda zaisa ta dinga dukansu ko kuma ta hantaresu, cikin sheshshekar kuka Billy tace


"Ummi Bafa abunda muke yi mata kawae dai ita ta tsane mune bata sonmu bata son murab'i 'yan uwanmu shi yasa take mana haka"


"Kashh! sister ba haka bane, kawae baki fahimci mom bane kamar yanda itama wani dalili yasa ta kasa fahimtar matsayinku awurinmu" Mahmud ne ya fad'i haka tare da dafa kafad'ar Billy, 


"Ummi don Allah kuyi hakuri, kufahimci mom d'ina kuma kuyi mata uzuri, wlh ni kaina bana son abunda take yi" ya k'arasa maganar tare da zaunawa gefen da ummi take ya rok'i hannun Bilkisu yana cewa,


"Plz sister ...ku 'YAN UWANA NE kada kurik'i mom d'ina amatsayin mai laifi ku d'auka tana yin kuskure ne wit time zata gyara insha Allah" yatsansa yasa ya gogewa Bilkisu hawayen da suka zubo mata "smile my Billy japanis" dariya ce takuccewa Billy  ta d'an kai masa Duka cikin shagwab'a had'e da rungumesa  cike da tsantsar so irin na d'an uwa da 'yar uwa.


"Allah yaya bana son sunan nan da kake yimun dariya yake bani wai Billy Japanis Inani inasu wajen kyawun duk da dai ance suma ba wani kyau ne dasu ba"


"Hhhhh lallai Billy ai japanis nada kyawu shi yasa ma na iya had'a kyawunki dasu sbd yanda kike Kama dasu...ni kam na san sai nayi yanga wajen aurar dake don ked'in kyakkyawa ce" kallon ummi yayi da tun d'azu itama take kallonsa tana mamakin yanda Allah ya fiddashi na musamman acikin 'yan uwansa sannan yace.


"Ai ina ganin garin yawon shak'atawar da Ummi sukaje ita da daddy aka samo cikinki acan agarinsu shi yasa kikayo kama dasu"


Murmushi Ummi tayi tare da shafa kansa.


"A gaida babanah Allah yayi maka albarka, yanda kake kula da farin cikin mu ko mahaifinka iya yanda zai yi kenan, indae mom d'in kace ni bana ganin laifinta tunda nice babba dole nayi hak'uri da duk abunda zata yi agidan nan dama shi babba a duk inda yake dole ya kasance mai hak'uri don da shine na k'asan sa zasuyi koyi, but plz kaima karage fushin nan naka yanzu da anbarka sae kajiwa batool ciwo saboda ta tab'a maka 'yar uwa kai mai 'yar uwa ko?"


"Amma Ummi ai laifin tane bata da Kunya wlh"


"To kade rage fushin zuciyan nan kaji babanah"


"shikenan Ummi Allah ya bani ikon ragewar, Ummi bari naje ga kiran sallah can naji anfara yi a masallatai" muryar bilal dake can gefe kwance yajiyo yana fad'ar


"Yaya nima zan bika nayi sallah" hannu mahmud yasa ya d'ago bilal daga kwance yana cewa,


"Yawwa my lil broth taso muje Daga nan in mun dawo mubiya insai maka sweet zaka sha ko?"


"Wayyo yaya nima zansha kasiyo mani har da chaculate"


"Baza'a siyo dake ba kinyi girma da yawa"


"Ummi kin deji bilal ko? Ina ruwansa ai ba dashi nake ba saina kamashi zan dokesa Ummi kice nazama babbar banza bacin shike fara jana"


   Billy tak'ara she maganar cikin shagwab'a tana neman kamo hannun bilal dake sauri mahmud yaja baya yana dariya ita kuma Ummi tarike hannunta cikin dariyar yanda 'yar shekara sha hud'u ke neman yin fad'a da d'an shekara uku tace,


"Haba Bilkisu ai da gaskiyar bilal wai bacin sweet d'in a had'o maki da chaculate, yo ai kece chaculate d'in"


Bubbuga k'afa Billy ta shiga yi tana neman yin kuka ganin yanda Ummi tayi siding bilal kuma ga yaya mahmud nayi mata dariya da sauri ya ajiye bilal cikin zolayarta donta huce yana fadin,


"jid'a ajikina nafasa d'aukar ka, a hannu zan jaka mutafi tunda kake tsokanar aunty Billy, k'yalesa my sister ba chaculate kad'ai zan siyo maki ba hadda duniya bisa tsinkenta (lol pop)"


 Wani irin tsallen jin fad'in tayi da yasa bilal tsorata ya b'uya abayan mahmud   yazata akansa Billy tayo ta dukesa, 


"Thank you yaya" Ta fad'a tare da rugawa tayi d'akinta tana Murmushin jin dad'i,


Shikuwa sake d'aukar bilal yayi suka bar part d'in, girgiza kai Ummi tayi tana dariyar shirme da quruciya irin na 'yar tata sannan itama tawuce bedroom d'inta don yin sallah.


'Dauke da bilal mahmud ya nufi part d'in momynsa yana basa labarin yanda suka yiwa mom b'arna, Ashe bassam ne ya taka gefen gadon mom suna wasa shida batool garin ta kamasa ya fad'owa madubin mom shinefa kwalaben humrorinta da turarukka suka fashe shi kuwa bilal na ganin haka yaje ya ta yasu d'auke wud'an da suke kwashewa da basu fashe ba sai ga mom shine da tana fad'a sukace ai bilal ne yafasa kwalaben.


"Ayya srry lil broth me yasa kaki fad'awa mom gaskiya...." dai dai nan suka iso k'ofar shiga d'akin mom kafin ya basa  amsa, tirjiya bilal ya fara yi saboda tsoron mom ba yaso ya shiga d'akin, ajiye shi a k'asa mahmud yayi tare da rik'o hannunsa suka shiga d'akin, cikin d'ari d'ari  bilal ke shiga yana rirrik'e mahmud tare da b'uya a bayan sa abun har yaso ya bawa mahmud dariya.


Zaune ya hango mom d'insa tana gyaran kayansu bassam dake kan gado an baje kamar wani d'an k'aramin boutique, kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai alamun haushinsa takeji marairaice fuska yayi tare da kneeldown agabanta yana fad'in.


"Na tuba my mom kiyafe mini indai akan na doki batool kike fushi dani barina kirata tunda belt d'in na hannunta saita rama"


Saboda son da take yi masa yasa ba zata iya jurewa ba ta d'ago kanta karaf suka yi ido biyu da bilal dake  tsaye abayansa a tsawace tace.


"Uwar me ka dawo kayi a d'akin nan ko kazo ka karasa fasa sauran ne?" had'e da banka masa wata irin muguwar harara "maza ka ficemin a d'aki ja'irin yaro"


Tsabar rud'ewar da bilal yayi tasa ya saki mahmud da gudu ya nufi wajen madubin yana kuka kafin mom ta sake sakar masa wata irin tsawa yabaro wurin aguje sannan yana mean k'ofar da zai fita, dafe kai mahmud yayi yana kallon momynsa yana so yayi dariyar abun Amma ba dama,


"Mom kiyi hakuri don Allah ni bana so in dinga ganinki cikin irin wannan yana yin plz"


"Ai kuwa ka dinga ganina Kenan matuk'ar baza kafita harkar wud'annan can matsiyatan ba, ina yanzu saeda kajeka lallaso su sannan ka shigo d'akin nan har kake cewa bakaso kaganeni cikin wannan yanayin"


"Pls srry mom kinga har za'a tada sallah banje masallaci ba"


"To ai sae kayi sallarka agida Allah zai karb'a"


"Subhanallah mom kinsan illar dake cikin rasa jam'i ga baligin namiji Kuwa? ai babbar asarace dake kai Mutum ga dana sani, Bari in tafi ina bassam yake ne?"


"To sarkin malamai ai sae ka dubashi a guarding Ina ga yana can yana wasa shida batool"


Girgiza kai yayi yana mamakin halin mom indai mahaifinsu baya gida ba zata tab'a damuwa da tasa k'annensa suyi sallah ba, Gashi yanzu salloli ake yi amma su suna can suna wasa kuma ko ajikinta,


"Allah ya kyauta" ya fad'a afili kafin ya bar d'akin mom na fad'in.


"To kuma me aka yi kake kiran Allah ya kyauta"


"Ba komai mom" yace ba tare da  ya juyo ba.


Yana fitowa yaci karo da bilal gefen d'akin yana jiransa Ashe duk tsoratar da yayi be tafi ba, Murmushi mahmud yayi yace


"Bilal kayo sallarka? "


"A'a yaya kai nake jira"


"Agaida takwaran ladanin annabi kayi dai-dai muje ko...?!"


_The more u coment the more updates u will get🤷🏻‍♀ ina godiya da ruwan addu'o'in da kukayi Mani,  tabbas natabbata cewa  koda yaushe masoyana na man atare dani💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻alhamdulillah kun matukar sanyani farinciki in my previous update da nayi nagode sosai Allah yabar k'auna🤝🏻_  LUV YOU ALL MAH FAN'S❤














Mr's huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT STORY AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____3💎



   Suna fitowa sukaci karo da Bassam aguje Batool ta biyo shi yana kwasar dariya, ganin yaya mahmud yasa suka shiga taitayinsu cike da fargabar kar yayi masu wani abun, wata uwar harara ya watsawa Batool had'e da cewa.


"Ke ko? Hmm! zaki zo hannuna ne, wato ana sallah ke kuma kintsaya yin shashanci da k'anenki don rashin sanin ciwon kai ko?, zaki wuce kiyi sallah ne ko saina makeki awurin nan?"


Cikin sigar shagwab'a Batool ta fara bubbuga K'afafuwan ta,


"Ni yaya Mahmud ba yanzu zanyi ba sai.... "


Kafin ta rufe baki Mahmud yayo kanta fuska a d'aure, tana ganin haka takwasa aguje ta shige wajen small mom tana qunquni had'e da tura baki shi kuma yaja hannun Bassam suka d'auro arwala a famfon dake cikin guading d'in sannan suka nufi masallaci. koda sukaje har an kusa sallame sallah saura raka'a d'aya, haka Mahmud yabi jam'in bayan an sallame ya tashi ya cika sauran taka'o'in da yarasa sannan ya baro masallacin hannuwansa rik'e da Bassam da Bilal yana koya masu addu'ar da ake yi idan anfito daga cikin masallaci...,


_"Bismil-lah wassalatu wassalamu ala rasoolil-lah, allahumma innee as-aluka min fadlik, allahumma iaasimnee minash-shayta nir-rajeem."_


Yana yi suna mai-maitawa  har suka isa wurin wani mai shago dake saida sweets dasu biscuit, d'ari biyar ya mik'awa  mai Shagon yace ya had'o masa biscuits da sweet amma yayi masa Leda leda kowanne na d'ari har guda biyar. Bacin angama had'a masa ya sake mik'a masa naira d'ari yace ya bashi chaculate  da lolipop, cike da jin dad'in cinikin Mai shagon ya had'o masa ya mik'a masa yana dariya wannan karon hadda gyara yasa masa yana fad'in,


"An gaida malam Mahmud shalelen alhaji kaga farin saurayi mai farar aniya, ranka ya dad'e yayi k'arko yayan Billy jepenese godiya nake yi"


Dariya Mahmud yayi don inda sabo ya saba da halin mai shagon duk lokacin da zaizo siyayya shagon mutumin sai yayi mashi wannan banbad'ancin kallonsa yayi kafin yace.


"Uh'umm..malam shehu kwalelanka akan sunan nan dan idan sister Billy taji wannan suna yana fitowa a bakin ka, ina tabbatar maka daga ranar ta dena son kayan shagon nan naka kuma zan dena siya saboda dama saboda ita nake saya" 


Yana gama fad'ar haka ya mik'awa Bassam da Bilal kowanen su leda d'aya tare da yiwa malam shehu mai shago sai anjima, Murmushi ya sake yi wanda ya k'ara fiddo masa da tsantsar kyawon da Allah yayi masa ganin yanda malam shehu yasa hannu biyu-biyu ya toshe bakinsa tare da turo idanuwansa waje saboda jin abinda ya fad'a, hannuwan su Bilal yaja suka nufi gida suna shiga yaci karo da Basmah k'anwarsa dake bimasa ta rako qawayenta earpiece lik'e a kunnenta ko d'an kwali batada shi balle mayafi kuma a haka take shirin fita har wajen gate, qawayenma nata kowanen su babu shigar kirki ajikinsu kaida ka gani su kasan k'awayen ban zane, tsuke fuska yayi tare da sakin hannuwan su Bilal..


"Oyah! Maza kushiga ciki gani nan shigowa" 


Suka bar wajen aguje hannuwansu rik'e da ledar sweet d'in daya siya masu,


Basmah na ganin haka gabanta ya fad'i don ta riga da tasan kwanan zancen, amma saboda kafuwa da k'arfin hali irin nata sai ta basar tare dayin kamar bata ganesa ba, cikin fad'uwar gaba tace da qawayenta.


"khady, shapsy bye-bye sai mun had'u gobe ko?"


 Tana k'ok'arin fita. Wata muguwar damk'a ya yiwa gashin kanta da ta sakawa ribon d'in acuci maza tare da jawota baya, 


"Ke wace irin wawuyace zaki fita a haka? Bakya ganin ko wud'annan dak'ik'an qawayen naki da basa iya sanya suturar k'warai ajikinsu sun d'an yafo abunda yarufe masu kansu, shine ke zaki fita haka" 


Sai alokacin khady da shapsy suka juyo suna kallonsa cike da son yi masa rashin mutunci saboda jin abunda ya fad'a akan su, tsantsar kwarjininsa yasa a maimakon suyi masa masifa sai gashi sun tsinci kansu da gaishe sa. 


Kallonsu yayi tun daga sama har k'asa tare da yatsine fuska yace


"Idan har zaku dinga irin wannan shigar banzar a matsayinku na 'ya'yan musulmi to kar in k'ara ganin k'afarku ta tako da sunan zuwa gidan nan, Infact idan ma ba zaku iya sauya irin muguwar shigannan ba kar nasake ganinku da qanwata if not i will make sure dt nasa kowacen ku tayi nadamar saninta."


k'arasa maganar yayi had'e da nuna Basmah da d'an yatsansa, har lokacin hannun sa rik'e yake da acucinta, cikin tsawa yace dasu.


"Get out now..."


Kallon Basmah suka yi da tuni idanuwanta sunyi jajir suna neman kawo k'walla saboda azabar da takeji, Kafin yace wani abun ya kaiga sake daka masu tsawar da tasa jikinsu na rawa suka bar gidan ba tare da sun yi mata maganar da suka tashi yi mata ba ita kuma yaja k'eyar kanta har cikin gida yana zuba mata masifar karya sake ganin kanta ba d'an kwali balle tayi tunanin fita haka!,


Basmah najin muryar small mom ta saki wani irin azababben kukan da yasa mom k'arasowa wajen aguje tana sallallami cikin sauri ta rik'o Basmah daya hankad'e can gefe yana cigaba da yi mata fad'a, kallonsa mom tayi a hasale tace.


"Amma Kai anyi mugun yaro anan, kai kenan kullum cikin cin zalin yaran nan ko tausayin su baka yi"


"Mom sune suke yin abubuwan da basu kamata ba wallahi duk da 'YAN UWANA NE SU banajin dad'in d'abi'un da suke yi, don Allah mom dubeta, a haka fa take shirin fita cikin gidan nan kanta babu d'an kwali sai kace ba d'iyar musulmai ba, ko Bilkisu da take k'anwar ta bata yin irin wud'annan mugayen d'abi'u sai su, to wlh kwanan nan idan basu dena ba jikinsu zai gaya masu"


Yana gama fad'ar haka yasa kai yabar part d'in ransa a b'ace,


"Eyyeeee...! lallai Mahmud wuyanka ya isa yanka, 'yan uwan naka kake cewa suna mugayen d'abi'u har kake cewa wata ta fisu? to ka canza wasu 'yan uwan mana tunda kanada wacce tafisu kyawawan d'abi'un, Jimun fitinannen yaro zaibi duk ya takurawa yarana, yi shiru ki k'yalesa zai dawo ya sameni idan ma turosa aka yi zanyi maganinsa, maza kishare hawayenki"


Mom ta fad'a tare da rad'awa Basmah wata magana akunne.


Hararar mom Basmah tayi had'e da langab'e kanta tace


"Da gaske?"


"Ha'a Basmah zan maki k'arya ne?"


"Yeee sai mom! Shi yasa nake masifar sonki"


Aguje Basmah ta wuce d'akinta kai tsaye ta nufi wardrobe d'in kayanta, tana bud'ewa taga wasu had'add'in kaya jins da t-shart har kala uku da mom tasiya mata, tsalle tayi had'e da yin ihu sannan taciro wayarta..


"Hello khady"


"Inaji basmah me kuma zaki fad'a mana bayan agabanki brother naki yaci mana mutunci amma kika kasa cewa komai"


"Haba khady Wlh yaya Mahmud matsalarshi ya wace da ita, ni bakiga wak'i'ar daya sani bane? wlh har yanzu kaina ciwo yakemun, abeg kimanta kawai kinji qawata"


"Hmm! Shikenan ammafa banji dad'in abinda yayi mana ba, don har nace keda ganina sai baba ya gani"


"Hhhhh matsoraciya"


"Naji d'in irin wannan red-face da yaya Mahmud yayi ai dole na tsorata, ammanfa ba k'arya basma yayan nan naki ya had'u ba kad'an basu don yafiki kyau sosae"


"mtsss manta kawai, naji yafini kinsan me?"


"A'a Basmah sai kin fad'a"


"Akwai chilling! Mom ta had'o min wasu had'addun kaya shine nace yaushe ne birthday din qawar nan taki sai mukece raini dasu"


"Haba bab da gaske? Wow kice akwai corrumboling"


"Yes woo....dama kala uku ne kinga sai na d'auki d'aya na baku sauran"


"Ok..shikenan Zanyi checking up naji ko yaushe ne I will call you back "


"Shikenan bye-bye sai najiki" daga haka tayi hanging wayar sannan tafad'a kan gado tana rera 'yan wak'ok'i cikin jin dad'in kyautar da mom tayi mata, 


Kai tsaye Mahmud ya wuce falon Ummi bakinsa d'auke da sallame yanemi wuri ya zauna, ganin babu kowa a falon sai k'amshin girlie dake tashi ya tabbatar masa da cewa suna kitchen, jin muryarsa tasa Ummi ta fito hannunta rik'e da cup d'in ruwa ta mik'a masa


"Babanah an dawo masallacin?"


"Eh Ummi me kike dafawa naji falon ya gauraye da k'amshi" Mahmud yafad'a tare da karb'ar cup d'in ruwan, dariya Ummi tayi sannan tace


"Kai babanah wane k'amshi kuma, Bilkisu ce ke dafuwar indomi" tana rufe baki sai ga Billy ta shigo falon d'auke da plate d'in indomien a hannu Bilal biye da ita yana kuka tana fad'in


"Yaro k'ara volume indai indomien nan ce bazaka cita ba"


Dariya Mahmud yayi had'e da girgiza kai


"Billy!.Billy!!..baki da dama wato ya k'ara volume  d'in kukan ba zaki basa ba ko?..Toh nima bari chaculate d'ina ya sha zamansa ba zan baki ba"


"Sorry yaya gashi na ajiye, Bilal zo muci" Har Bilal ya fara kokarin zaunawa ta jaye plate d'in tace "To kaje ka wanko hannunta ko malam"


Zaune shima mahmud yayi tare dasa hannunsa sukaci indomien yana yaba k'ok'arin Billy data iya girki haka.


"Lallai idan daddy ya dawo zance ya yiwa Billy aure tunda ta iya girki"


"Hmm Allah dai ya tsare wanda zae aureta a haka da shan jagwalgwalo, ai kaima daurewa kad'ai kayi don tana ta hannun damarka nasan da bazaka iya ciba" Bilal ne yake fad'i yana d'ago kai yana sud'ar hannu yace


"Hiynnmmm... su aunty Billy Japanese an iya dafa indomi" 


Dariya suka kwashe da ita har ummi na rik'e ciki


"Wato indomien tayi dad'i  Bilal?, ashe kaima karage iya fad'an Billy jepenese d'innan?" cike da k'warewa Billy ta d'aga hannu zata doke sa yaya mahmud yayi saurin rik'eta yana dariya


"Bafa shi ya fad'a haka ba malam..." 


Sai kuma yayi shiru tare da jawo ledar sweet da biscuit d'in da ya siyo mata ya mik'a mata har ya turo baki zatayi k'orafin chaculate d'inta taga ya mik'a mata had'e da lolipop, cikin jin dad'i tayi masa godiya tare da cewa


"yaya ina nasu aunty Basmah da batool? "


Nuna mata nasu yayi tare da mik'ewa yana cewa ummi.....






















Mr's huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____4💎



 Ummi sai anjima, wai yaushe daddy zai dawone?,  d'azu nayita trying number sa but it's switch up!, 


"Babanah kenan! yanzu nake cewa bari na tambayeka naji ko kunyi waya da Alhaji yafad'a maka ranar da zai dawo,ni kaina nata kiran wayarsa a kashe, Ashe kaima baka samesa ba"


"Eh wlh...Allah dai ya dawo mana dashi lpy, Ummi bari intafi ina so ind'an fita wajen sulaiman"


"Amin babanah, to adawo lpy ka gaidashi inkaje"



"Yaya Mahmud inzo muje wurin su yayya batool muyi hawasa"


"Eh taso mutafi, Bilal kaima zakaje?"


"A'a ya'ya ni bazan jeba mom zata koroni"


Cike da jin kunyar hali irin na mom Mahmud yasosa qeyar kansa tare da cewa


"To bari naturo maka Bassam kuyi wasa ko?"


"o'oh shima dukana yakeyi shi dasu yayya Basmah"


"Dukan ka kum..... "  Ummi ce tayi saurin katseshi saboda ta yanke maganar


"Babana idan zaka dawo kabiyo mani da lemun tsami naga na guiding be nunaba kuma ina buk'atarsa anjima zanyi had'in bama"


"To Ummi" ya fad'a had'e da rik'o hannun Billy suka  bar falon


Suna fita ummi tajawo Bilal ta rik'e masa kunne had'e da murd'ewa ta yanda zaiji zafi ta d'aure masa fuska sosai kamar ba ita ba


"Bilal mena fad'a maka? ban cemaka bana son yawan surutu da k'orafi ba? shine har kamanta kake nema ka d'auko mani fitina, kanaso yayanka yaje yata dukan maka 'yan uwane?" tasake murd'e kunnen har saida ya saki 'yar k'ara..



"Awwsh... A'a Ummi, nadena bazan k'ara ba..amma ai yayya Batool tace muba 'yan uwansu bane!"



"Itama mantawa TAYI shiyasa tafad'i haka Amma ku 'yan uwansu ne haka suma 'yan uwanka ne bakuda kamarsu aduniya kaji ko?"


"Eh Ummi kenan su 'YAN UWANA NE nida aunty billy?


"Sosae kuwa, saboda haka kar insakeji kana fad'awa wasu ko yayanka cewa sunyi maka kaza da kaza, kazamo mai hak'uri da rik'e sirrin 'yan uwanka!"


"To ummi" Murmushi tayi sannan ta sakar masa kunne had'e da cewa 


"Good boy, Allah ya albarkaci rayuwarka kai da 'yan uwanka"


Suna shiga part d'in mom suka tarar da ita zaune cikin falo itada yaran gaba d'aya zaune suna kallo, Billy ce tafara shigowa bakinta d'auke da sallama amma babu wanda ya amsa saida suka jiyo muryar yaya mahmud a bayanta shima yayi sallamar sannan suka amsa atare kamar sun had'a baki, dariya Billy ta kwashe da ita saboda kai da kaji yanayin da suka amsa sallamar kasan atsorace suke, kallon d'aya ummi tayi mata mai had'e da tsana ta d'auke kai, rufe baki tayi tare da k'arasowa cikin falon tagaida mom,  batare da mom ta kulata ba tace


"Lpy" koshi don taga Mahmud ba wurin ne kuma tasan halinsa yanzu sai ya cika mata kunne da zancen 'YAN UWANA NE se kace garesa farau 'yan uwa!..


kallon mom yayi kamar yasan metake tunani yayi murmushi had'e da girgiza kai sannan ya nemi guri a falon yazauna, 


Atare k'annen nasa suka sake had'a baki suna gaishesa...saida yayi murmushi sannan ya amsa had'e da cewa


"Batool d'in mom zoki karb'a yana hararar Basmah data quro masa idanuwa tana jiran taga abunda zai ba Batool"


Mik'amata ledar sweet da biscuits din daya siyo  masu yayi 


"Kid'auki d'aya kiba waccan marar kunyar d'aya"


Godiya sukayi masa fuskokinsu d'auke da fara'a, mom kuwa da tunda suka shigo bata d'aure fuska batare data kula saba dashi har Billyn  saboda haushin abunda yayiwa Basmah sai gashi ta saki fuska tana fad'in 


"To ko kaifa amma ka zauna kullum cikin kyarar 'yan uwanka najini babu wata kyautatawa sai fifita wasu kakeyi akansu, koda yake ba laifinka bane anriga da anshanye mani kai kamar yanda aka yiwa babanka, me akeyi da zuriar Sammu da sihiri nikam... "


Katseta Mahmud yayi cikin raunin murya


"Haba mom! wai meye haka?  Shikenan ni babu yanda zan rab'i mahaifiyata naji sanyi batare da naji tana fitar da kalaman da zasu b'ata mani rai akan 'yan uwana ba!?"


Kallon Bilkisu yayi da tuni kalaman mom suka tab'a zuciyarta amma sai tayi kamar batajin abunda suke fad'a maida kallonsa yayi ga mom dake taunar cingum tana fad'in


"To ai saika canza uwar dama nasan indai Aisha na raye bazan tab'a samun girmamawa awajenka ba sai ranar da tamutu"


A wannan karon kukane yaci k'arfin Bilkisu dama tuntuni idanunta cike suke tab da hawaye tabar d'akin aguje tanajin wata irin tsanar mom nasoma shiga zuciyarta,  wai yanzu agabanta mom keyiwa mahaifiyarta fatan muyiwa. 


"Haba mom meye haka wai yanzu babu damar Bilkisu ta shigo cikin 'yan uwanta tazauna sai ansata kuka?  Kitunafa ba ita yakamata ace kina yiwa wud'annan abubuwan ba, Wallahi Allah mom bakya kyautawa" Cikin takaici yabar falon kamar zai tashi sama, mom takalli Basmah da Batool suka bushe da dariya tace


Indai akan waccan munafukar matar ce dake neman rabaku da d'an uwanku gab nake da yimasa iyaka akanta



"Wayyo mom har yayya Billy tabani tausayi" cewar Bassam


Tangad'o k'eyarsa Basmah tayi dad'i duka, itama Batool takaina masa ran k'washi akai tace


"Samnan yaro zauna garin tausayinta kaima ahad'a da kai a asirce kamar yanda akayiwa yaya mahmud yafi sonsu akanmu" 


"Gud girl shiyasa kike burgeni batool"


"Ai Wlh mom kinmun dai dai, ita munafuka tazo tayi mana zaune don tsabar gulma da lek'en asiri" 


Basmah ce tayi saurin cewa


"Hmmmm..mom wama yasani ko Ummi ce ke turota shak'ar sirrin mu"


"Tabbas Basmah kinyi gaskiya, inko hakane sai natabbatar nasa Aisha nadamar daga ita har 'ya'yan nata"


Billy na fitowa part d'in mom ta hango bilal rik'e da ball d'insa yana bugawa, cikin gudu-gudu tanufi wurinsa had'e da rungumesa tana kuka,


"Aunty Billy me akayi maki kike kuka"


"Bilal mun shiga uku 'yan uwanmu basa son mu, mommy ta tsanemu..."

da sauri Bilal ya rufewa Billy baki


"Aunty Billy kiyi shiru kuma kidena fad'a kar ammie tajiki zata murd'e maki kunne nima haka tayimun d'azu"


"Bilal me kake tunani akansu da yasa suke yimana haka"


Shiru Bilal yayi kamar wani babban mutum yana tunani kafin ya kalli billy yace


"'YAN UWANA NE! haka Ummi tace"


Dariyar yaya Mahmud suka jiyo da tund'azu yake tsaye bayansu yana sauraren abunda suke fad'a, d'ago kan da zatayi suka had'a ido dashi, murmushi yayi tare dasa hannu ya goge mata hawayen dake zubowa daga idanuwanta. 


"Am srry my Japanese sister, abunda Bilal yafad'a shiya kamata ace kema kina tunawa aranki, mu daku 'yan uwan junane, muyi hak'uri da halayen juna da sannu komai zai wuce, karki d'auki zancen mom azuciyarki har yazo yadameki kinji ko?"


Shiru Billy tayi tana tunanin kalamansa har Lokacin hawaye basu dena zubowa a fuskar taba..


"Haba Billy Japanese" yafad'a had'e da jan hab'ar bakinta kafin ya rufe baki shima bilal yakai bakinsa a kunnenta ya hura mata iska sosai dama d'abi'ar da yake yimata kenan inyana son tsokanarta sai bata sakar ba ya hura mata iska a kunne suyita fad'a don yasani bata so, aikuwa yana ganin ta zabura ya ruga aguje guading yana dariya bayansa tabi itama tana fad'in


"Allah yau sai kagane tunda kiyimun wannan abun, Kama tsaya in kamaka don ko Ummi taji saita rik'e munkai tunda tace ka dena tsokanarta" ganin yana bata wahala yasa Mahmud ya zagayo tacan gefa ya rik'e matashi...ihu bilal yafara had'e da dariya yana zille zillen tserewa amma ina saida Billy ta riskesa, hannu tad'aga da niyar dukansu taji Mahmud ya rungumesu suduka yana fad'in


"We're srry aunty Billy luv you much" batasan lokacin da itama  ta saki dariya ba had'e da cewa


"Luv u too brother, always proud of you yaya"


Da haka Ummi ta iskosu wajen saboda ihun bilal da taji mai had'e da dariya, salati ta rafka tana tafa hannuwa



"Fitar kenan anan babana?, dama kana wurin atsaye suke tafka wannan uban rashin ji, ka kama ka biye masu fisabilillah kamar bakada abunyi?"


Kafin yace wani abu ya jiyo muryar mom d'insa dake tsaye abakin k'ofar part d'inta tana kallonsu tana fad'in


"Dama ya za'ayi yayi abunyi bacin an maidashi susutacce sai yanda akayi dashi, toni bazan lamunci wannan akan yarona ba, shikenan  tsabar mugunta an mayar mani da yaro bayajin maganata sannan baya son 'yan uwansa, mutum ko tsoron hakkin haihuwa bayayi akansa ai wannan mugun tace wlh"


Baki bud'e Ummi ke kallon mom batare da tace mata komai ba Don babu kalamin datayi mamakin jin fitowarsa daga bakinta, sai dai takai aya sannan ta kalleta sama da k'asa tace


"Allah ya sawak'e"


Cikin k'ufuwa mom tafara masifa


"Allah a fuska fir'auna azuci kin raba mani kan yara kuma nayi magana waike ustaziya kina fad'in Allah ya sawak'e, to ai yasawake abunda yafi haka tunda duk qulle-qullenki bai rabani da mijinta ba"


mahmud baice mata uffan ba yaja hannun 'yan uwansa da niyar barin wajen mom ta fincike hannunsa


"Lallai yaron nan asiri yayi tasiri kanka, yanzu kana gani tana neman cimani mutunci zaka rab'ani ka wuce? " kawai sai tafashe da kuka tana cewa


"To wlh bari alhaji yadawo sai yayi maka tsakani da matannan tunda ba ita tahaifeka ba,  shikenan k'irik'iri ana neman rabani da yarona"


Tsoron Allah ne yakama bilal jin wai mom ke fad'in yana kallon za'a cimata mutunci bacin ita kecin mutunci wasu 


Basmah ce tafito tana kiran mom uban waye yasaki kuka


Bud'e bakin da Mahmud zaiyi yabata amsa yaji tarasss.. saukar mari afuskar Billy Basmah tayi  mata Tana fad'in



"Wato ke 'yar iska tunda yaya ya d'aure maki shine  zakiyiwa mom rashin kunya har kisata zubar da hawaye? Idan ita uwar ki...."


Kafin tarufe ida itama taji tass-tass saukar marora afuskarta har sau biyu, wuyanta ya shak'o yana neman illatata Ummi tayi saurin b'anb'are hannunsa 


"Enough babana ai batasan meke faruwa ba, dirar mikiya tayiwa abun shiyasa tayi haka, k'yaleta kaji ko?"


Wani irin jiri ne ya d'ebi mahmud nan take yafad'i k'asa dafe da kansa , Ummi ce tayi saurin rik'osa tana fad'in 


"Subhanallahi babana lafiya?"


Tureta mom tayi had'e da  cewa


"Shikenan kin sabatta mun yaro, wayyo nashiga uku shima so kikeyi ki kasheshi kamar yanda kika kashemun sauran yarana.........

































Mr's huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____5💎



    Baya Ummi taja had'e da rik'o hannuwan Bilkisu da Bilal ta nufi part d'inta idanuwanta na zubar da hawayen tausayin Mahmud, ko shakka babu tasan tana matuk'ar  k'aunarsa aranta shi yasa bata iya jurewa idan ta gansa cikin damuwa, gashi yanzu tanaji tana ganinsa awani hali amma an haramta mata taimakonsa. Har ta kusa shiga part d'inta sai kuma ta juyo, 


Kallon inda su mom suke tayi har lokacin suna kan mahmud sun kasa bashi taimakon daya kamata. Goge hawayen idanuwanta tayi had'e da cewa.


"Bilkisu maza shiga ciki keda Bilal ina zuwa"


"Ummi ina zakije?"


"Kuje nace ina zuwa bakwa ganin d'an uwanku ba lafiya"


Wurin gate ta nufa ta yiwa maigadi knocking da saurinsa ya fito ya russana agabanta yana fad'in.


"Allah yatsareki hajia ina gaisuwa, me kike buk'ata ne yanzu nayi maki"


"Am malam habu ina saleh driver yake?"


"Bai jima da fita ba ya raka abokinsa da yazo wurinsa d'azu..." kafin ya rufe baki sai ga saleh driver ya iso yana rera 'yan wak'ok'insa, yana hango Ummi ya rugo aguje yana gaisheta.


"Yawwa saleh maza ka fiddo da mota ga Babana can ba lafiya kukai sa asibiti pls kayi sauri"


"Angama hajia" saleh ya fad'a tare da nufar wajen da motoci suke ajiye ita kuma ummi ta wuce part d'inta da nufin gyarawa tabi bayansu.


Saleh na fitowa da mota sai ga batool, cikin gadara tace,


"Kai saleh ina zakaje ne? to kajira zamu kai yaya Mahmud asibiti inji mom" 


Tana gama fad'a  masa tabar wajen. A wani private hospital _Jiddah specialist  hospital_ suka nufa kasancewar acan family doctor d'insu yake kuma a can duk 'yan gidan suke da folder, suna isa ba tare da b'ata lokaci ba aka shiga duba Mahmud, nan likita ya tabbatarwa da mom ba kome ke damun saba illah damuwa daya sa a ransa itace ke haifar masa da tsananin ciwon kai a duk lokacin da wani abun ya b'ata masa rai, don haka akula adena barinsa cikin damuwa domin hakan na iya tasiri ga zuciyarsa har yasa zuciyar ta fara yi masa ciwo.


Jikin mom ne yayi sanyi jin abunda likitan ya fad'a, kallonsa tayi kafin nan tace.


"Dr. toh ya jikin nasa yanzu?"


"Ki kwantar da hankalinki babu wata matsala yanzu haka anyi masa allurai tare da sanya masa drip bacci ya d'aukesa yana farkowa zaku iya wucewa gida, Amma dai ku kula sosai!"


"Insha Allah dr mun gode"


Rufe bakin mom keda wuya saiga Ummi ta shigo asibitin cikin damuwa ta nufi inda mom take,


"Momyn yara ya jikin baban nawa ina fatan da sauk'i ko?" ko kallon inda Ummi take mom ba tayi ba balle ta samu damar amsa mata. Hakan yasa Ummi ta samu kujerar dake gefe ta zauna, bata jima zaune ba sai ga family dr d'in su ya shigo,


"Ah...Hajia sannunku ina wuni,"


"Lpy klw dr" 


"Ya na ganku anan, waye ba lafiya?"


"Babana ne Mahmud ba lafiya"


"Ayya why not da ba'a kirani nazo har gida ba? me ya samesa?"


"To nima dai ban sani ba, amma muna tsaye kawai  mukaga ya fad'i k'asa had'e da dafe kansa..."


Kafin Ummi ta rufe baki mom ta Katseta da masifa,


"Ta yama za'ayi kisani kina nema ki kashe mun yaro to wallah....."


"Hajia hussaina!, hajia hussaina!! me nake shirin ji a bakin ki?, wannan sakarcin ne har cikin bainar jama'a?" muryar daddy ce suka jiyo da dirowarsa kenan ya samu labarin suna asibiti shine ya biyo baya, cike da b'acin ran abunda yaji mom na fad'a yake kallonta tare da narka mata harar mai tsanin nuna b'acin rai. Da sauri dr ya mik'a masa hannu yana fad'in


"U're welcm sir"


"Thank you dr jamil ya aiki?"


"Alhamdulillah how was the journey"


"Fine and good wallahi Dr isowata kenan yara ke fad'a mun my son is at hospital"


"Eh yanzu na keji ga hajia har nake tambayar don me ba'a kirani nazo gida ba, saboda tun d'azu ina gida yanzun nan na shigo urgently duba wata patient tawa"


"Nima da aka fad'amun haka nace why not daba akiraka ba"


Kallon mom dady yayi ta wani d'aure fuska had'e da kauda Kai gefe kafin ya maida kallonsa ga Ummi, Murmushi tayi tare da cewa,


"Sannu da hanya, an iso lafiya?"


"Lafiya lau hajia Aisha ya gidan?"


Wani murmushin ta sake sakar masa kafin tace.


"Gida kam yanzu ba dad'i tunda babana ba lafiya Amma kasan cewarka a nan yanzu nasan insha Allah komai zai dai-daita"


Wani mugun tsaki mom taja tabar wajen a hasale, Girgiza kai dady yayi sannan ya shiga room d'in da aka kwantar da Mahmud wanda ganin mom ta shiga ciki ya tabbatar masa da hakan, ita Ummi da dr sukabi bayansa.


Bayan an sallami Mahmud sun koma gida, da safe yana zaune ya jingina da jikin gadonsa cike da farin cikin dawowar mahaifinsa yace,


"Mom dama jiya daddy zai dawo shine baki fad'a mun ba" tab'e baki tayi had'e da mik'a masa cup d'in tea data gama had'a masa tana cewa,


"Ya za'a yi na sani bacin munafurci ya hana a sanar mani nima, tsabar rainin hankali ma dadyn naka kama wayoyinsa yayi yasa rufe tun shekaran jiya nake trying nasa ban samu bs ashe yasan me ya shirya tunda a wancan part d'in zai sauka..."



"Haba mom!, haba mom!!...yanzu dadyn ne kike cewa ya munafucceki bacin kinsan duk abunda zai yi agidansa baya nuna ban-banci, to wlh ni kaina saida na tambayi Ummi yaushe zai dawo, the same thing itama haka ta fad'a mani cewa bata sani ba don bata samun wayoyinsa idan ta kira, mom to meye ribar dady da Ummi idan sun b'oye maki wani abun? pls mom don Allah kidena irin wannan abun bai dace ba"


"Oho dai suma suka san dalilinsu ni idan ma ancuceni nida yarana wlh Allah ba zan yafe ba"


Shiru mahmud yayi yana kallon mom idanunsa cike da k'walla ya kasa ce mata komai, tunowa da kalaman likita ya sata sakin Murmushi tare da cewa.



"Sorry yayan B3 nadena dama da wasa nake yi maka"


Turo k'ofar d'akinsa da sukaji anyi yasa Mahmud ya kasa bawa mom amsa, Bilkisu ce ta shigo bakinta d'auke da sallama hannunta da k'aton tire da abinci ummi ta aikota ta kawowa mahmud d'in.


"Mom ina kwana, ya Mahmud ina kwana, sannu ya jiki, gashi ummi tace akawo maka tana gaisheka" 


Billy ta fad'a tana kallonsa, Dariya Mahmud yayi sannan ya ce


"Washhh...billy jepanis wannan surutu Mai had'e da tambayoyi to wace kike son na fara amsawa daga ciki?" saida ta turo baki jin sunan da yayi mata amfani wajan yi mata magana sannan ta duk'a da niyar ajiye tiren abincin mom da tund'azu ta cika tayi fam tasa hannu ya buge tiren duk abincin ya watse a k'asa ita kuma Billy ya b'ata mata jiki.


"Uban waye ya kawoki d'akin nan, anfad'a mata cewa bana iya kula da d'ana ne da har zata wani dafo wannan k'azamin girkin nata ta kawowa d'ana? maza kibar d'akin nan kafin nab'ata maki rai da wasu shegun idanuwanki kamar k'wayar gero!"


Da sauri mahmud ya taso ya rik'e hannun Bilkisu tare da cire rigar jikinsa yana goge mata kayanta inda abinci ya zubar mata bayan ya gama ya duk'a ya tattaro abincin daya zube a plate  sannan ya koma kan gado yasa hannu ya fara ci, sai da yayi kusan loma uku sannan ya d'ago kai yana Murmushi ya cewa billy.


"Sister kicewa Ummi na gode kuma abincin yayi dad'i sosai"


Kad'a masa kai tayi sannan ta duk'a da nufin gyara wajen yace


"Sister jeki zansa a gyara wajen"


 Jiki ba k'wari tabar d'akin yanzu kam inda sabo tafara sabawa da abubuwan da mom keyi mata, tana fita taci karo da Bilal zai shiga d'akin da sauri ta rik'o hannunsa,


"Bilal karka shiga mom na ciki" duk'owa tayi tana gwada masa yanda jikinta ya b'aci "kagani daga shiga in kaiwa yaya abinci shine ta kifar da abincin k'..."


Rufemata baki yayi tare da cewa 


"Aunty Billy kidena fad'a Ummi tace mudinga hak'uri idan anyi mana wani abun tunda 'yan uwan mune"


"Shikenan Bilal yanzu duk  abunda aka yi mana hak'uri zamu yi tayi babu wanda zamu fad'awa? Ai wannan basu suka yi ba mom ce tayi"


"Aunty ai itama mom 'yar uwar muce tunda mom tace k'anwar tace"


Rungumesa tayi "Bilal kai yaro ne k'arami amma kana da fahimtar da nikaina bani da ita" bata ankara ba taji ya hura mata iska a kunne ya ruga aguje yana dariya, binsa itama tayi aguje tana dariya don izuwa yanzu ta fahimci ko meyasa yake yi mata haka,


A b'angaren mahmud kuwa Billy na fita ya kirawo wayar Basmah.


"Hello yaya mahmud  ya jiki?" ba tare da ya amsa mata ba yace.


"Kizo d'akina yanzu" sannan ya kashe wayarsa, kallon mom yayi yace



"Mom for Godness sake me yasa kika zubar da abincin da Ummi ta aiko min dashi?"


"Saboda bana so kaci kuma ka watsan kasa a ido, waya san ko meta saka maka a ciki don ta kashe ka tunda bata son ganin 'ya'yana a raye"


"Kamar ya kenan mom?, kinsan adadin ko sau nawa inacin abincinta? Idan Ummi na son kashe maki 'ya'ya da tun-tuni muna yara zata kashemu, ko kin manta lokacin da kukaje egypt da daddy kika barta mu a hannunta har na tsawon shekara d'aya, meyasa lokacin bata kashemu ba sai yanzu da muka girma, duk da bawani wayo ne dani ba, bana manta wahalar da tayi da basmah lokacin ko shekara biyu bata yi ba a duniya, ko kad'an bata barin Ummi bacci da tsohon cikin Billy haka Ummi ke goyon Basmah abayanta idan tana rigima har sai tayi bacci me yasa bata kashe mu ba sai yanzu....? pls mom ko ba zaki so Ummi ba  Atleast ya kamata kiso yaranta kamar yanda take son mu"


Wata muguwar harara mom tayi masa had'e da maka masa pillow ajiki.. 


"Rufemin baki shanyayye ai gashinan garin kwad'ayinka an shanyeka zaka dameni da wani tsohon labari, bari in fad'a maka over my died body bana son Aisha da yaranta Don haka kaima tun wuri kasama ranka haka, dole ne karabu dasu don bana son tarayyarka dasu ko kad'an" sannan ta fice daga d'akin tana cigaba da masifa, dariya Mahmud yayi 


"Mom kenan ikon Allah!, kinsan gaskiya Amma bakyaso a fad'a, to nidai bansan ya za'a yi na rabu dasu ba don su d'in 'YAN UWANA NE na jini!"


Mom nafita taci karo da Basmah ko kallonta bata tsaya yiba saboda masifar da take yi ta wuce abinta, binta da kallo Basmah tayi had'e da tura k'ofar d'akin ba tare da tayi sallama ba


"yaya me aka yiwa mom naga ta fita tana masifa kamar irin rikitaccin tsofaffin nan?"


"Stupid koma kiyo sallama kafin na tashi na b'abb'allaki a gurin nan"


"Oh! yaya Allah ya baka hak'uri daga tambaya"


Komawa tayi tayo sallama ya amsa sannan yace ta shigo 


"Yawwa Basmah maza ki harhad'a kayan nan dake k'asa kishare abincin kiyi moping wurin sannan kishiga toilet d'ina ki wanko kwanonin Ina jiranki"


"To yaya amma waye yayi b'arin abincin?"


"Basmahhhh...! nifa shine yake had'ani dake wato yawan tambayar da kuma Shan batu, to mommy ce ta zubar da abincin shikenan?"


Had'e rai Basmah tayi don Ita bata son fad'a arayuwarta balle gwasalewa, aikin ta farayi tana qunquni har ta kammala.


"Yaya Nagama ga kwanonin"


"OK thank you Basmah ajiye munsu akan bedside zuwa anjima na kaisu"


"Yaya Mahmud kwanonin waye?"


"Na ummi ne" wani irin takaicin wanke su taji yataso mata aria, murmushin mugunta tayi  kafin tace.


"Bari na kai mata tunda ba kada lafiya"


"Ok sister say  a big thanks to her"


Jiki na rawa Basmah ta nufi part d'in Ummi tana qiyasta rashin mutunci da zata yi idan taje ciki....



  _SORRY FOR THE LATE UPDATE, AM TOO BUSY👏 yanzu ma nayi manage ne don d'ai naga cewa na faranta maku saboda zab'en da ake yi😍_






Mr's huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____6💎



     'Tana isowa part d'in Ummi ta tadda Bilkisu da Bilal suna wasan 'yar b'uya Billy ta d'aure masa idanunsa, garin ya lalabota saiga Basmah takawo kai ai kuwa ya rik'eta hannu biyu-biyu yana ihu yana fad'in.


"Yeeeeee...Aunty Billy na kamoki wallahi, no cheating bud'emun idona"


Speechless Basmah tazama tana kallon Bilal dake kulle da idanuwa duk yabi ya cukurkud'e mata doguwar rigar dake jikinta, muryarsa ta jiyo yana kuma cewa.


"Please Aunty Billy karki ce ba hakan bane Allah na kamaki kicire mun k'yallennan a fuskata"


Cikin jin haushi ta ajiye trey d'in kayan dake hannunta ta cire masa k'yallen, d'ago kan da zai yi ta d'aukesa da mari had'e da turesa ya fad'i k'asa, 


Wata irin muguwar k'ara yayi da tasa Billy fitowa daga inda ta b'uya da gudu ta k'araso wajen ta d'aga Bilal tana kallon basmah.


"Haba yayya Basmah wannan wane irin d'aukar  alhaki ne?, meye ribarki cikin cutar da d'an uwanki kuma jikinki?, Allah fa bazai barki ba idan kina hakan!" 


"OK Billy nuna mun d'an uwan kine kinji, kinga saiki rama masa ko?"


Kuka Bilal keyi jikinsa na rawa yace,


"Sorry yayya Basmah bansan ke bace, na zata aunty Billy ce shi yasa nayi maki haka"


"Rufemun baki munafukin yaro kawai Billyn ce ta kai girmana in ba iskanci irin naka ba" ta sake d'aga hannu zata kai masa duka da sauri Billy ta rik'e hannunta,


"A'a yayya Basmah gaskiya ba zaki sake dukan saba ai wannan cin zali ne, yaro bai yi maki komai ba kin maresa, ba tare da kinji tausayin saba kika hankad'esa ya fad'i, amatsayinki na 'yar uwarsa ko tsoro bakya yi ya ji ciwo, shine duk bai isheki ba kike nema ki k'ara dukansa, a gaskiya bazai yuyuba is enough."


Sake d'ago d'ayan hannunta tayi da nufin marin Billy tana fad'in,


"To bari na nuna maki koke baki wuce in duke kiba da mari ba balle kuma shi"


"Kul..karki kuskura kifara...!" 


Muryar Ummi ce suka jiyo dake tsaye abakin k'ofar shiga Parlourn tun lokacin da taji kukan Bilal ta fito tana kallon abunda  kefaruwa, a hankali ta k'araso wajen  ta cire hannun Billy data rik'e hannun Basmah sannan tace 


"Bilkisu me yasa zaki yiwa auntynki rashin kunya? Oyah say srry to her"


"Ummi ita fa..."


"Kibata hak'uri nace"


"Yayya Basmah kiyi hak'uri"


"Good maza kushiga daga ciki Ummi ta fad'a"


Bayan sun wuce Ummi ta kalli Basmah da sai faman kumburar baki take yi ta rik'o hannunta.


"Basmah don Allah kidena biyewa yarannan kuna sa'insa dasu, kece babba akansu kamata yayi ace kina behaving very matured ba wai ace komai kid'aga hannu kice zaki yi duka ba, kinsan yau da gobe sai Allah shaid'an zai iya sa watarana surama duk da bana fatan hakan ya faru tsakaninki da k'annanki!"


Da k'arfi Basmah ta k'wace hannunta daga rikon da Ummi tayi mata tabi takan trey d'in kayan abincin da tazo dasu aguje tana kuka suka tarwatse treyn ya fashe.


Murmushin k'arfin hali Ummi tayi cike da mamakin Basmah had'e da cewa.


"Allah ya sawak'e miki!"


Aguje Basmah ta shiga wajen mom tana kuka, nan take shirya k'arya da gaskiya ta fad'a mata, ana haka sai ga daddy ya shigo, ko gaisuwa babu mom ta fara zuba masifa tana sheda masa abunda Basmah tazo ta fad'a mata.


"To wallahi alhaji nagaji da wannan nuna banbanci da ake yimun cikin gidan nan, yanzu kenan babu dama Basmah ta hukunta yaran nan idan suka yi mata laifi sai Aisha tasa baki don tanuna cewa 'ya'yan tane, wai har da cewa idan Basmah ta dokesu surama suma!"


Shiru dady yayi yana nazarin maganganun ta kafin yace.


"Zanyi bincike, amma ke Basmah kin tabbatar da haka aka yi? don idan naji ba haka bane to saina sab'a maki saboda bazan lamunci shashanci agidana ba"


Nan Basmah ta fara fik'i-fik'i da idanuwa saboda tasan kwanan zancen, ko kad'an dady baya lamuncewa ayi masa shashanci, dady naganin haka yayi tsaki had'e da cewa mom


"Kin gani ko, bansan me yasa kike d'aukar k'ananan maganganun yaran nan ba kina bari suna tasiri azuciyarki ba, tazo ta shirya maki k'arya kin kama kin haye, to yanzu meye amfanin wannan? daga yau karki sake zomani da irin wud'an nan maganganun idanko ba haka ba saina mugun sab'a maki"


Haba!, mom najin haka  masifar tak'aru kamar an zubawa wuta fetur tana cewa,


"Dole kafad'i haka mana tunda Aisha da 'ya'yanta sune 'yan gata, to tunda kace haka ka raba d'aya biyu ka nuna kafi sonta akanmu to wlh saina tabbatar maka d'auki matakin da sai dai ran kowa yab'aci a gidan nan, Acuci yarinya sannan kazo kabud'e mata ido don karka b'atawa 'yan gwal rai"


mtssss dady yayi tsaki sannan yafice daga d'akin ya barta tana cigaba da surfa masifar ta. 



_Dukkanin k'orafinku ya iso a kunnuwana AKAN rashin samun update d'ina har na tsawon kwana biyu ina mai baku hak'uri akan haka, Amma ina so kusani banyi alkawarin yin update kullum ba saboda inada abubuwan yi agabana, just dt ina iya k'ok'arinane naga nayi abunda zai faranta raina da kuma naku, saboda haka masoyana kuyimun uzuri a duk lokacin da kukaji shiru nagode 👏LUV YOU ALL❤_







Mr's huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____7💎



    Part d'in Ummi dady ya nufa ransa duk ab'ace, ya rasa wace irin rayuwace mom take son ake yi a cikin gidan sa, ita ko kad'an bata fahimtar me ake cewa kishi da kishiya ta yiwa kalmomin mummunar fahimta ta yanda ba zata tab'a barin a zauna lafiya ba a cikin gidan. Har ya iso cikin falon Ummi yana wannan tunanin, Bilal ne ya rugo da gudu yana fad'in, 


"Oyoyo dady" Cabesa dady yayi tare da kissing forehead d'insa shima yana cewa,


"Oyoyo my Bilal kana lpy?"


Kai ya d'aga masa yana wasa da buttle d'in jallabiyarsa. Ummi kuwa dake cikin bedroom fitowarta wanka kenan ta jiyo muryar dady, agurguje ta shirya sannan ta bud'e bedside fridge d'inta ta d'auko gorar ruwan faro mai sanyi tare da cup ta nufo parlon fuskarta d'auke da murmushi, Bilal na ganin Ummi ta shigo ya sauka daga jikin dady tare da barin parlon aguje yana k'walawa Billy kira.


"Aunty Billy, aunty Billy kizo ga daddy"


Wani irin lafiyayyen murmushi dady yayi ganin Ummi ta nufo inda yake fuskarta d'auke da murmushin da ako yaushe ke haskaka masa zuciya,


A hankali ya bud'e mata hannayensa ta yiwa kanta  mazauni bisa ki'rjinsa shi kuma ya zagaye hannayensa abayanta, a lokaci guda suka lumshe idanuwansu suna jin wani sanyi da natsuwa na saukar masu acikin zuciya, sun jima a haka kafin can suyi breaking hugging d'in da suka yiwa juna, ruwan Ummi ta tsiyaya masa a cup sannan ta mik'a masa cike da girmamawa, karb'a yayi tare da had'owa da hannunta ya kai ruwan abakinsa yana sha yana kallonta a hankali har ruwan ya k'are. Ajiye cup d'in tayi tare da cewa.


"Barka da rana dadyn su B, ya gajiyar hanya?"


"Yawwa Rabba'atul baiti, gajiya takau tunda gani ga iyalina, Abu mafi burgewa na same su cikin k'oshin lafiya sai dai kash...da alama ko tunanina basa yi tunda kowacensu hankalinsu kwance yake kunyi wani fresh daku..!"


Da sauri Ummi d'ora yatsansa akan lips d'inta tace,


"Babu bukatar canzawar zuciyar dake samun kyakkyawar kulawa ga wanda ya ajiyeta, jarumtar da kake da ita wajen bamu kula da cire mana kewar rashinka atare damu bazata tab'a barin tunani yayi tasiri akan mu ba balle har yasa mucanza daga yanayin da kake k'ok'arin son ganin mu akoda yaushe, Idan kuwa hakan tafaru to tabbas rashin adalci da godewa jaruminmu ya tabbata akan mu"


"Rabba'atul baiti kenan! Bakya gajiya da kiran jarumtaka ga jaruminnan da ya kasa daidaita gidansa, Shin bakya tsoron ace wata rana ya samu rauni agabanki!?"


"Ko kad'an bata haufi akan haka idan kuma har ta faru zanyiwa jarumin nan nawa uzuri, in d'auka cewa Allah ya jarabce sane ko kuwa nice nakasa wajen iya wasashi shi yasa hakan ta faru bawai don ya gaza ba"


Murmushin jin dad'i dady yayi tare da yiwa Allah godiya daya mallaka masa Aisha a matsayin matarsa


"Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya mallaka mani ma'abocin fitar da kyakkyawan murmushi a fuskarsa, dukkanin murmushin da zaka yi yakan k'ara mini k'warin guiwa da kuma dalilan da zasu k'ara mani sonka da k'aunar ka tare da zama a cikin gidan ka cikin ko wane irin yanayi"


Yayi murmushi tare da cewa "Idan ko haka ne zan kasance mai k'ara yalwar murmushi na don intabbatar kin soni fiye da adadin numfashinki da nawa"


Sosai dady ya samu natsuwa da farin cikin da suka nemi kwace masa a part d'in mom, fira take yi masa wacce kesa idan har zai iya mantawa da kansa saboda tsananin dad'inta to tabbas zai manta dashi, 


Billy ce ta shigo bayan ta biye da Bilal aguje yana dariya ya yi saurin b'uya bayan dady, Billy naganin dady tayi tsaye cak had'e da duk'ar da kai k'asa,


"Dady ina wuni"


"Lpy klw Bilkisu ya aka yi naga kin biyo k'anin naki ko laifi yayi ne?" 


"Eh dady wai cemun yayi..." Bilal na dariya ya katseta yana fad'in.


"Dady wai don d'ai nace mata Billy Japanese yanda yaya mahmud kecewa shinefa take son dukana"


Gaba d'aya dady da Ummi sukasa dariya,


"Haba Bilkisu d'an wannan abun shine ya kai ayi duka akansa...Bilal yama ake cewa.. Billy Japanese  ko?" kukan shagwab'a ta fara yi tana bubbuga k'afa, A hankali ummi ta zagayo bayan dady ta damk'o hannun Bilal tana cewa.


"Zo gashi Bilkisu narik'e makishi tunda dadynku yayi siding d'insa"


"Wayyo ammi ki cikani da zafi zata yimun"


"Ban fad'a maka kadena cemata haka ba? Yau saika gane kuskurenka tunda bakaji"


"Ummi da wasa fa nake yi mata ko aunty Billy na?"


Saida ta hararesa sannan tace


"Eh Ummi, amma kice kar ya sake"


"Aww ni zaki bawa kunya? Shikenan zaki sameni ne"


Dariya suka yi harda daddy dake kallon su, abinda sam yaran Mom basa yi wato wasa da dariya ga junansu sai dai son girma kamar su suka yi kansu....



   *Assalamu alaikum 'yan uwa da abokan arziki, ina muku fatan alkairi a duk inda kuke. Ayi min afuwa na jina kwana biyu shiru da aka yi hakan ya samu asali ne daga wayar, yanzu ma zakuji ni shiru sai yadda hali yayi sabida taki yin dai-dai ko nayi typing dana bud'e data zai goge ayi min afuwa see you next insha Allah na gode....*😘










Mrs Huss@in✍🏻 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_*Gisuwa mai yawa tare da fatar alkhairi ga d'aukacin masoya wannan littafi, ngd bisa jajircewarku da k'aunar da kuka nuna agareni da kuma wannan lbri mai suna 'YAN UWA NANE! kuma ina yiwa kowa barka da sallah tare da fatar kowa yayi sallah lpy, in sha Allah zaku cigaba da jini akai akai*_


💎Page_____8💎



   Da sauri billy tanufi wajen Ummi rik'e da kunnuwa har lokacin tana dariya


"Sorry ummina nice fa, Bilkisunki ta annabi mai gadon zinari" Cikin soyayya Ummi ta d'aga hannunta kamar zata doketa dady yayi saurin jawota har lokacin shima yana dariya


"Haba madan ayimata hak'uri kar asa jinin dady ya hau" kafin ummi ta amsa har dady ya maido kallonsa ga Billy fuskarnan tasa ad'aure kamar bashine yagama dariya yanzu ba, cikin natsuwa yake tambayarta 


"Bilkisu me yafaru tsakaninki da auntynki basmah" shiru billy tayi kanta sunkuye ak'asa kafin tajiyo muryar dady yana sake jefo mata tambayar da k'arfi, nan take tayi masa bayanin duk abunda yafaru batare da tayi k'ari ko ragi ba, hannunta dady ya saki had'e da jawo hannun bilal dake rungume ajikin Ummi


"Bilal! Shin gaskiya ne auntynka ta fad'a?"


"Eh dady, amma mun bata hak'uri ko aunty billy" ya k'arasa maganar yana kallon 'yar uwarsa da nan take ta gyad'a masa kai.


Murmushi dady yayi had'e da cewa


"Very good! Amma ina so daga yau Bilkisu dake da bilal karku sake musayar magana da 'yan uwanku hakan d'abiace Marar kyau kunji ko?Ke Bilkisu Basmah Auntyn kuce bakyau ace kina mayar mata da magana akan zata yiwa qanenta hukunci, amma duk lokacin da kikaga tayi abunda ya cutar daku to kifad'amun kinji ko?


"Eh dady, kayi hak'uri bazan k'araba in sha Allah"


"That's my dota, haka nake so, Allah yayi maku albarka"


"Amin dady"


"Oya  jeki kishiryawa bilal kema kishirya kafin ingama magana da umminku zamu fita" tsalle Bilkisu tayi tare da cewa dady hadda Yaya Mahmud zamuje?


"Eh idan kunshirya kije kifad'a masa duk da nasan dak'yar inzai iya tunda jikin nasa ba mafita" da gudu billy taja hannun bilal suka nufi bedroom d'in Ummi shi kuma dady ya dawo sit d'in da take zaune kanta ak'asa tana tunanin matsalolin da suke fuskanta agidan na rashin zama lafiya, hannu yasa akan hab'arta tare da d'ago fuskarta tana kallon tasa, lumshe idanunsa yayi ya rufesu tare da bud'esu ya d'age mata gira yana murmushi yace



"Me uwar gidana ke tunani ne?" Murmushin itama tayi sannan tace


"Abunda zai faranta farincikin mai gidanta" 


Dariya dady yayi tare da d'ora yatsansa akan lab'b'anta ganin tana k'ok'arin yimasa bayani akan maganar da yagamayi da yaransa


"A'a Aisha kibar maganar a haka, nadad'e da fahimtar komai, nasan bazaki tab'ayin abunda zai raba kan 'ya'ya naba indai ba sharrin shayd'an ya gitta ba"


"Nagode da fahimtata da dyn Mahmud"


Tana rufe baki sai ga Mahmud yashigo falon, ganin yanda suke zaune so close ya sashi saurin juyawa da sauri


"Come in my son" dady yafad'a da k'arfi had'e da mik'ewa tsaye yana mai farincikin ganin d'an nasa da yake matuk'ar k'auna da kuma alfahari a zuciyarsa, kansa duk'e a k'asa ya k'araso d'akin had'e da gaida Ummi


"Ummi ina wuni?"


"Lafiya k'alau yayan B, ya karfin jikin naka?"


"Alhmdulillah Ummi naji sauk'i ya k'ok'ari?"


"Allah ya k'ara lafiya"


"Amin Ummi, inasu lil sis ne naji gidan shiru" yana rufe baki sai gasu billy sun fito cikin shirinsu suna k'amshi, da gudu bilal ya rugo Mahmud ya cab'esa sama yana fad'in


"Eyyee yaron Ummi, wannan gayu sai ina haka?"


Hannu dady yasa a kafad'ar Mahmud dake k'ok'arin sauke bilal ya lak'amo Mahmud yana fad'in...








Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____9💎



 My son ya jikin naka? hope kasamu sauk'i?


"Alhmdulillah dady it's just a little worry dake damuna"


"Being patient my son, in sha Allah komai zai wuce, abunda nakeso dakai shine kaje ka gyaro zamu fita da kai da kuma k'annenka"


"OK dady bari nashiryo" part d'insa ya wuce shi kuma dady yanufi part d'in Small mom, yana shiga ya tadda batool zaune Small mom na gyara mata gashinta shi kuma bassam yana kallon k'wallo gyaran murya yayi bayan ya shigo, cikin gadara Small mom tad'ago kanta tace


"Alhaji kaji tsoron Allah, yanzu abunda kakeyi daidai ne?, ka dubi tun lokacin da kabar part d'innan kanufi part d'in waccan algungumar munafuka ace sai

 yanzu zama fito kusan awa d'ayafa kenan kana can kabiyewa k'ananan yara kuna faman dariya sai kace mahaukata, wlh alhaji baka kyautawa"


Batare da dady ya kalli inda takeba ya k'wallawa basmah kira, da sauri tafito daga cikin bedroom d'inta daga ita sai bes da mini siket kanta babu d'an kwali, dady na kallonta ya d'auke kansa sannan yace


"Ki gyara keda qannenki zamu fita"


"Dady ina zamuje ne?" Kallon ta ya sakeyi cikin jin haushin shigar da take ciki yace


"Idan baza kujeba kwa iyayin zaunenku, shashashar yarinya, bassam maza jeka gyara kafin in fito"


"Dady ban iya gyarawaba momy ke gyarani" bassam ne ya fad'i haka har lokacin hankalinsa na akan TV da yake kallo, tsananin takaici yasa dady juyawa yabar part d'in, dariya basmah tayi had'e da cewa


"Cab wlh mom dady ya iya fitina yanzu, daga tambaya shikenan sai ya rufeni da fad'a, shin waima ina zamu jene?"


"Kema dai kyafad'a basmah! ai kune abokanan fad'ansa amma kar kiso kiji yanda yake k'yak'yata dariya da wud'an can jinin mayu" da sauri batool tace


"Cikamun kai nidai mom, wlh Allah idan bamu gyara da wuriba dady tafiyarsa zaiyi kuma munaji muna gani zai fita dasu billy yabarmu gida kuma nikam da haka tafaru k'ara shegen gashin can na yayyah basmah ya tsittsinke" cikin zafin rai basmah tanufo batool tare da finciko gashin kanta


"Bari nafara tsinke naki gashin kafin nawan da kikeyiwa fatan tsinkewa ya tsinke, muguwar yarinya kawai" nan fa suka kacame da rigima suna faman zagin junansu, ana haka saiga Mahmud ya shigo rik'e da hannun bilal, da gudu bilal yanufi wurin bassam yayinda shi kuma Mahmud ya nufi wajen dasu batool ke rigima yana fad'in


"Ke, ke me kuke yine haka, mom dube su kigani sai kace kaji kuma kinsa masu ido, wlh basmah idan baki cikataba saina zazzaneki agidan nan, wannan wane irin rashin mutuncine, kizauna kina fad'a da k'anwarki?" Turo baki tayi tana fitar da lumfashi dakyar kamar wacce tayi wasar athletic s competition 


"Yaya aradu wannan yarinyar batada kirki, wai ni take yiwa fatan gashina ya tsittsinke don tana marar kunya"


"Keep quite, stupid girl nizan ida cika fatan da take yimaki tunda bakyason zama da head tied, banda iskanci dubi yanda jikinki yake amma har kya iya fitowa ahaka wlh mom gab nake da b'ab'b'alla yarinyar nan, zaku wucene ku shirya ko sai na b'ata maku rai" gwalo batool tayiwa basmah had'e da dariya sannan kowace ta nufi d'akinta har sun wuce ya jawo batool ta baya yace


"Ke ko? idan na rik'aki zaki game kurenki tunda kin zama marar kunya" soko ya sakar mata had'e da tureta da kad'an ta fad'awa mom, da gudu tabar falon shi kuma mom ta jefo masa harara cikin b'acin rai


"My son kamaida hankalinka, wai meyasa kafiye son takurawa Yaran nan, shikenan kai kullum bakada aiki sai cin zalinsu" a hankali ya tako har inda take zaune shima ya zauna tare da rik'o hannunta


"Mom ya kamata kifahimci cewa su 'YAN UWA NANE ina matuk'ar sonsu shiyasa  nake yimasu haka, duk wannan abun da nake yimasu inayine saboda in daidaita rayuwarsu badon in takura masu ba"



"Shikenan naji amma meyasa baka lallaahinsu idan sunyi laifi kamar yanda kake yiwa waccan ma...." Da sauri yarufe mata baki saboda bayason kalmar da zata fad'a mararsa dad'i akan qanwarsa Bilkisu


"Kiyi hak'uri mom in sha Allah suma zan dinga lallashinsu matuk'ar sun gyara in kuma sukak'i dukane zai rabani dasu" kunnensa mom ta murd'e yayi saurin cewa 



"Washhh...mom harkin manta da yaronki ba lafiya shine kike neman ciremun kunne?" Sai a lokacin mom ta tuna da rashin lafiyarsa saboda abunda yafaru d'azu data tafito wajen ganinsa ba k'aramin b'ata mata rai yayi ba.


"Ayya sorry my son, ya jikin naka?"


"Am ok mom, nasamu sauk'i alhmdulillah, zamu fita da dady kuma tuwon alkama nake son ci"


"To ku tsaya a restaurant kaci mana kafin kudawo don bazan iya dafashi ba, kannen kama ka nema masu abunda zasuci ni bacci nakeji" 


"Pls mom kitaimaka kinsan bazan iya cin abincin waje inba dole ba"


"Haba my son baccifa nace maka zanyi, ko kana son takura nine?"


"Noo..shikenan mom bari mutafi" rai ab'ace yabar falon har yana cin karo da Billy dake k'ok'arin shigowa da gudu


"Washhh.." Tafad'a tana k'ok'arin fad'uwa, da sauri ya tarota 



"Sannu lil sis, meyasa kike son gudune ko nauyin jikinki bakyaji, nakusa fara dukanki idan baki dena wannan d'abi'ar ba"


"Sorry dady ne yace in kiraka" tana rufe baki suka had'a ido da mom dake bakin k'ofa rik'e da hannun bilal tana shirin ingizo k'eyarsa waje, sunkuyar da kanta tayi yayinda mom tayi kamar batasan da itaba tace



"Maza wuce kabar nan munafukin yaro, shine zakaje ka tsaresa kuna kallo don bak'in hali bacin kaga ba'a shirya masa ba ga dadynku najiransa" baki abud'e Mahmud ke kallon mom kafin yaje yakamo hannun bilal subar wajen,


Cike da tsana mom ta sake dallawa Billy hararar datasa tabar wajen itama da sauri


Kusan mintuna ashirin su dady sukayi suna jiran fitowar su basmah, can Mahmud ya hangosu tafe basmah saye da wata pitet street gown an tsaga rigar tabaya gashi ta matseta tako ina sannan ta yafo wani siririn mayafin da ko wuyanta bai ida rufewa ba ita kuma batool, a tsorace dady ya kalleta sannan ya maido kallonsa ga Mahmud fuskarsa d'auke da ayar tambaya. Duk'ar da kai Mahmud yayi sannan yafito cikin mortar ransa ab'ace ya nufi inda suke, batool da bassam na ganin haka suka rugo suka shiga cikin mota yayinda basmah taci gaba da tafiyarta cikin hankali kwance duk da zuciyarta cike take da tsoron yanayin da tagansa amma saboda yanayin rigar dake jikinta kotaso tayi gudu hakan bazai yuyuba shi yasa taci gaba da tafiyarta, kafin ta k'araso taga yafara ciro belt d'in dake jikinsa da baya da baya tafara ja amma ina kafin ta ankara har ya cimmata, dukanta yakeyi har saida tafad'i k'asa tana ihu, mom ce tafito aguje tana fad'in.....





















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWA NA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Tabbas d'aid'ai kun mutanen k'warai ne kad'ai  zasuga kayi wani kuskure acikin alamurranka suyi k'ok'arin yimaka gyara don cigabanka, hak'ik'a zuciyata na matuk'ar alfahari da samunku acikin rayuwata MOM XOXO, SANAH S MATAZU da kuma KHAIRAT UP nagode sosai bisa gyaran da kuka yimun na sunan littafina daga *'Yan uwa nane* zuwa *'Yan uwa na ne* saboda haka readers zamuci gaba da littafinmu da wancan sunan da muka gyara👆 ubangiji Allah ya tabbatar da alk'alummammu akan dai dai amin_👏🏻



💎Page_____10💎



  Amma kai Mahmud yaron banza ne, zaka k'yalemun yarinya ko saina sameka wajen, gaba d'aya idanunsa sun rufe ko sauraren abunda mom ke cewa batayi sai jibgarta yakeyi, ihun da Ummi taji yayi yawa yasa itama tafito part d'inta aguje tana kawowa mom na kawowa, cikin fushi mom ta finciko sa tare da d'aukesa wani zazzafan mari ita kuma Ummi ta duk'a ta d'auke basmah dake kwance k'asa lagyagya tana kuka.


"Wlh Mahmud ina kusa da in yafeka akan yarana, inyaso kaje ka sake wata uwar an fad'a maka cewa ita jakace da zaka rufeta da duka haka, meye tayi makane inba tsabar tsana da kake yimata ba, an riga ansa maka tsabar 'yan uwanka baka sonsu baka k'aunarsu" afusace ta jiyo ta anshe basmah dake rungume ajikin Ummi tana kuka ta hankad'e Ummi har saida takusa fad'uwa Mahmud yayi saurin tarota.


"Duk abunda yafaru kece sila don kece kika rabamun kan 'ya'ya, kuma wlh sai na tabbatar da nasakaki nadamar aikata haka, kin sawa uba tsanar 'ya'yansa yanaji yana gani za'a illatata gashi zaune amma tsabar k'iyayya ya  kasa magana" ta k'arasa maganar tana kallon dady dake zaune cikin mota yana kallon duk abunda ke faruwa,


"Haba mom wai me kike fad'a hakane, yanzu meye laifin Ummi ko kina tunanin ita zatasa in aikata haka?, to kinyi kuskure kullum bata fatar taga Allah ya had'a kanmu, Amma kidubi shigar da basmah tayi sai kace ba d'iyar musulmi ba, shin hakan da tayi mom tarbiyace, shin me kike tunani idan tafita maza suka kalleta, komaifa na iya faruwa, masha fad'a mata tadena shigar banza batada amfani zata iya haifar mata da matsalar da sai tashafi kowa agidan nan especially ku iyayenmu.."


"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, yanzu Mahmud lalacewar taka har takai haka, da kanka kake kamanta 'yar uwarka da arniya, kake yimata muguwar fata to da yardar Allah baza kaga haka ba, mugun bakinka ya sauka akan munafukar dake son rabaku"


Jin miyagun suruttan da mom keyi sunyi yawa yasa dady fitowa cikin motar a fusace ya buga gambun da k'arfi ya rufe sannan yabar wajen ya nufi part d'insa ransa a b'ace.


"Kin gani ko mom, duk hak'urin dady saida kika fusatasa, kidena d'aurewa basmah abunda takeyi is not good at all"


Hannun Ummi yaja suka nufi part d'inta yana bata hak'uri akan abunda mom tayi mata


"Bakomai Babanah rashin fahimta ne  ya kawo haka in sha Allah with time nasan zata fahimci komai tadena aibatani da yarana"


Saida ya tabbatar Ummi bata tare da damuwar abun ko kad'an sannan ya nufi d'akin mahaifinsu, kamar dai yanda yayita lallashin Ummi haka yayi tayi da dady har sai da yaga shima damuwarsa ta rage sannan yace


"Dady zamu iya tafiya yanzu?"


"No..kabarshi nafasa fitar kaje kafito da k'annenka dake cikin mota"


"Shikenan dady don Allah kak'ara hak'uri da halin mom"


"Tun yaushe kasan nake yin hak'uri da ita tun kafin kazo duniya, bansan meke damun mom d'in kaba, Sam bata son zama lafiya narasa me hajia Aisha tayi mata data d'ora mata karan tsana, babban bak'in cikin dake damuna bai wuce yanda taraba mani kan 'ya'ya ba ta tusawa yarana tsanar 'yan uwansu sannan kuma tana neman b'ata masu tarbiya, tabbas na tafka babbn kuskure arayuwata dana kasa daidaita gidana bazan tab'a yafewa kaina ba matuk'ar namutu da bak'in cikin mamanka"



"A'a dady kadena wannan tunani, Allah shedane akan yanda kake tsaye da sha'anin gidanka,  kana k'ok'ari sosai, kana matuk'ar kamanta adalci agidan nan wanda ba duk namiji ke iyayin hakaba sai jajir tacce, in sha Allah zan tayaka kula da 'yan uwana har sai na tabbatar kayi farinciki da alfaharin samunmu, mom kuma kaci gaba da addu'a zata canza da yaddar Allah"



"I hop so my son" da haka ya nufi part d'in mom maganganun dady nayi masa yawo a k'wak'walwarsa, yana shiga ya iske basmah kwance akan 3sitter idanunta arufe fuskarta ta kumbure saboda kukan da tayi, duk sai yaji ba dad'i cikin zuciyarsa gefenta ya zauna tare da d'ora hannunsa bisa kuncinta, 


"Basmah!" A hankali tabud'e idanuwanta suna had'a ido dashi ta kauda fuskarta, sake juyo da fuskar tata yayi sannan ya d'ago da ita daga kwancen da take


"Am sorry basmah don't mean to hurt you at all, ked'ince kin fiye kunnen k'ashi ni bana son irin wud'annan shigar da kikeyi, zata tab'a maki mutunci na har abada but Yaya is sorry kinji? Ku 'YAN UWA NA NE ina matuk'ar sonku kawai d'abi'unku da halayenku sune bana so da zaran kun dena zaku fahimci yanda yayanmu ke matuk'ar ji daku"


A hankali takoma ta kwanta ba tare data furta masa kalma ko d'aya ba saboda yanda take jin haushinsa, murmushi yayi sannan ya nufi kitchen inda ya jiyo motsin mom tana girki yana shiga yayi hugging d'inta


"Mom me kike dafawa ne?" Shiru tayi bata cemasa komai alamun fushi takeyi dashi


"Haba mom! Ur son d'inki ke maganafa kiyi hak'uri nagane ban kyautaba dana doki k'anwata, nayi maki alk'awari daga yau bazan sake dukan taba duk abunda kike tunani bahaka bane ina matuk'ar son 'yan uwana fiye da tunaninki kuma in sha Allah zan basu kulawa ta har abada, kicire komai aranki babu mai rabani da 'yan uwana" jin kalamansa yasa ta juyowa tana kallonsa fuskarta ba yabo ba fallasa tace


"Zanyi farinciki sosai idan kalamanka suka tabbata, but nasan haka abune mai wahala matuk'ar kana tare da Aisha, tariga ta shanye.." Hannunsa yayi saurin d'orawa abakinta


"Karki fad'i haka mom, ke mahaifiya tace, banida kamarki kuma banida wanda ya kaiki aduniya, zan tabbatar maki da cewa ni yaron kine, abunda nakeso dake mom shine kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki"


"Shikenan ammafa ka kula wlh idan ka sab'a alkawari sai na baka mamaki don wlh kowa sai yaji ba dad'i agidannan"


"A'a mom banda dady, ya kamata ace izuwa yanzu kin kula da farincikin sa, dady na matuk'ar sonki shiyasa yake jurewa matsalolin dake faruwa don Allah ki janye munannar fahimtar da kike yi akansa"


"Dallah rufemun baki kar kasa raina ya sake b'aci"


Gudun kar tasake birkice masa yasashi fitowa yana fad'in


"Mom mai duniya Allah dai yaja zamaninki, kiyi rai kiyi k'arko mamanah"


Girgiza kai tayi had'e da sakin murmushi tsabar jin dad'in kalamansa


Batool ce ta shigo falon ranta a b'ace tana faman turar baki kamar wacce akayiwa duka, mayafin hannunta tafara jifa dashi kafin can tacire takalmin k'afarta ta watsar dasu a tsakar d'aki, inda basmah take kwance ta nufa a afusace had'e da kai mata wani irin mugun duka a cinya tana fad'in


"Muguwa kawai, wlh Allah ya isana, kurum kinyi mana asarar fita don tsabar iskanci, kin jamana asarar abunda dady zai siya mana"


Cikin zafin nama da rad'ad'in dukan da tayi mata ta tashi ta kaimata naushi abaki nan fa suka kacame da fad'a, kadan cewar Basmah na cikin b'acin rai yasa Allah ya azata akan Batool tayita dukanta, dak'yar Mahmud ya fincikota akanta yana dariya



"Enough Basmah yi hak'uri kinrama dukanki shikenan har lokacin bai dena dariyar da yakeyi ba saboda yasan dama inda zata fanshe dukan da yayi mata take nema sai gashi cikin sauk'i ta samu, fizge hannunta tayi tana faman nishi tace


"Wlh kwanan nan sai kunci duka a hannuna saboda na lura gidan nan ba'a notice d'in dukan mutum sai dai yaji saukar na jaki ajikinsa don haka sai kunsha wahala a wurina keda wancan d'an iskan yaron ta nuna Bassam da ya shigo yanzu yana tuk'uburi, wata irin muguwar harara ya watsa mata shima tare da nuna ta da d'an yatsansa


"Kece 'yar iska bani ba tunda kika ja aka fasa fita don mugunta, shikenan yanzu kinja narasa ball d'in da nakeso dady ya siyamun"


Afusace tayo kukan kura akansa Mahmud ya sake saurin rik'ota


"Kai Basmah yanzu da Bassam d'in zakiyi fad'a, sorry nasan wannan rigimar duka laifina ne amma kiyi hak'uri kinji ko?"


"But yaya Mahmud..."


"Shhhh..ko meye ai nace kiyi hak'uri ko?"


Haka dai suka dinga yimasa rigima inya lallashi wannan ya koma ga waccan har mom ta k'arasa girkinta, cikin jin dad'in yanda taganesa cikin 'yan uwansa tace



"Yau kam nayarda duk tasirin asiri sai yakarye, dubeku gwanin ban sha'awa amma don tsabar hasada ake nema araba mani kanku, dole intashi tsaye nima saboda bazan juri haka ba"  Mahmud ne yace 


"Mommmm..."


"Rufamun baki samna kazo kazuba abinci kaci"


"Mom kizubo mana mana muci tare"


"Bazaka iya cin abinci da Yaran nan ba don nasan halinka"



"Zan iya mana tunda su 'YAN UWA NA NE"


 A tare mom tazubo masa abinci da k'annensa sukaci sannan yabar part d'in, d'akinsa ya nufa ya watso ruwa yayi sallah ya haye gadonsa don ba kad'an yakejin bacci na d'ibarsa ba, acan cikin bacci ya hango lil sis d'insa tana gudu cikin wani makeken daji tana kiran sunansa, mom d'insa kuma na gefe tana faman dariya, a firgice ya tashi baccin duk ransa ab'ace yana fad'in


" _Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, a uzubillahi minashhaid'anirrajim ya fad'a har sau uku ya tofa a hannunsa na hagu sannan ya k'ara da a'uzu bikalimatillahi tammaat, min ghadabihi, wa ik'aa bihi, wa sharri ibadihi, wamin hamazatishhayad'ini, wa anyahduruun_"


Ya matuk'ar tsoratata yanayin da yaga lil sis d'insa aciki don haka ya sauko kan gadon yasa doguwar rigarsa jalabiya sannan ya nufi part d'in Ummi zuciyarsa cike da son ganin halin da 'yar uwarsa take ciki...













Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWA NA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____11💎



 Yana shigowa yaci karo da Billy kwance akan cinyar Ummi tana tsefe mata kai, cike da kasala ya k'araso cikin falon, dak'yar yake takawa tamkar wanda akayiwa duka ya fad'a akan kujerar dake facing d'insu  zaune yayi wata iriyar ajiyar zuciya had'e da rufe idanuwansa, tsoron dake hannun Ummi ta saki tana kallonsa yare da karantar yanayin da yake ciki, 



"Babanah meke faruwa da kaine na ganka a haka?"


"Babu komai Ummi" ya fad'a ba tare daya bud'e idanuwan saba, murmushi tayi sannan tace


"Allah yasa haka"


"Amin Ummi, lil sis ina abokin rigimar naki"


"Gashi can a kwance, inagan yayi bacci tun d'azu da muka dawo"


"Ayya! Yawwa ya naga ke ranki bai b'aci ba da aka fasa fita" turo baki tayi kafin tace


"Allah ne bai nufaba amma raina yab'aci kuma ba sabida rashin fitar da ba'ayi ba sai don don dukan da kayiwa yayyah Basmah"


"Dagaske?"


"Sosai kuwa Yaya har cikin raina don wlh da nice, k'ilan saina kusa kuka"


"Tab! Allah ya tsare ranar da zakiyi irin abunda basmah tayi don na tabbata yankata zanyi!" Zaro idanu Billy tayi yace


"K'warai kuwa"


Duk firar da sukeyi ita dai Ummi na saurarensu har ta ida kammala tsifar da take yimata, kanta ta d'ago tana kallonsa yanda yake fitar da maganganun sa cikin natsuwa 


"Babana wai sai yaushe zaka fiddo da matar aure" da sauri ya wartsake daga yanayin da yake ciki har yana neman sauko wa akan kujerar da yake zaune


"Haba Ummi! Wane aure kuma nida na keda 'yan uwa mata agabana,  ai idan kikaga nayi aure to tabbas naga nakai autarsu Billy agidan mijine"


Tunda Ummi tayi magana Billy ke b'ab'b'akar dariya saboda yanda taga yayan nata yayi shock da jin zancen, amma tanajin amsar daya bayar ta d'aure fuska kamar ba itaba, dariyar shima yayi 


"Billy Japanese kenan! Wato ke kinga k'eta bari kiyi dariya ko?, to kima ajiye wannan fushin naki agefe don ko bakyaso tabbas sai lokacin da kukayi aure zanyi"


"A'a Babanah kabar wannan zance domin kaine babba acikin su don haka kai zaka farayi  daga nan sai su kuma su biyo ba yanka"



"Don Allah Ummi mubar zancen nan, ni banason wani aure billy tafad'a tare tana bubbuga k'afafuwa ak'asa kamar zatayi kuka tabar falon"


Sosai Ummi tayi dariya ita da Mahmud da yabi bayan ta da kallo yana fad'in


"Ai kuwa saidai ki koma Japan ba agidan nan ba"


Bayan kwana biyu dady ya tarasu a main palour d'insa saboda wani makirci da small mom ta shirya akan tana so dady ya raba masu gida, wannan maganar ba kad'an ta tayar masa da hankali ba wanda shine dalilin da yasa yatarasu waje d'aya, sai da yayi gyaran murya sannan yashiga yiwa Allah godiya bisa tarin arzik'i da samun iyali daya azur tasa dasu, bayan haka ya d'ora da cewa


"Hak'ik'a Allah yayi mani tarin ni'ima wacce bazan iya biyan saba, amma nayi alk'awari agaresa zan dage dayi masa biyayya har izuwa lumfashina na k'arshe, ni mutumne kamar Ku bana son shiga hak'k'in d'aya daga cikinku, banason tauye kowanen ku hakan yasa na taraku don neman sasanci a tsakanin ku, hajia Aisha da hajia Hussaina dukkaninku matanane kuma ina matuk'ar sonku wanda hakan shiyasa nake fatar komai tsanani komai wuya murayu atare kuma mu mutu atare, amma kash yau d'ayarku ta bijiro mani da buk'ata mafi k'ololuwar cutuwa agareni wacce jureta abune mai wahala da nake tunanin bazai yuyu ba don bana buk'atar hakan amma kafin na yanke hukunci ina so inji meye ra'ayin ke hajia Aisha da kuma 'ya'yanah akai" shiru yayi na kusan minti biyu kafin yaci gaba da cewa 


"Hajia Hussaina ta nemi da araba wajen zama saboda bazata iya jurewa cin fuska da munafurcin da ake yimata agidan nan ba don haka me kun kace akan wannan buk'ata tata" 


"Alhaji indai ta b'angare nane wlh banida ja duk hukuncin daka qudurta aranka zan bishi matuk'ar zai sama maka farin ciki" tana rufe baki basmah tace


"Bawani mudai munyarda araba wurin zama saboda musamu natsuwa muda mom d'in mu, ana takura mana a gidan nan don haka mu bana buk'atar zama dasu"


"Haba yayya Basmah kada kice haka mufa 'yan uwan junane, kar mubari son zuciya da kuma sharrin shaid'an ya b'ata mana zumunci"


"Dady fita batun Billy wlh Allah mudai muna amince, tsabar munafuncine ya hana sununa amincewarsu suma" cewar Batool dake zaune kusa da small mom tana taunar cingam. 


Tunda ake zancen nan Mahmud baice komai ba sai da yaji fitsarar k'annen tasa na nema ta wuce gona da iri, cikin damuwa yace


"Dady ni kwata kwata  bana goyon bayan wannan shawarar domin hanyace ta wargaza zumuncinmu, yakamata ace mom tafad'i abubuwan da akeyi agidan nan da bataso sai anemi hanyar gyarasu bawani ace lokaci d'aya araba wajen za.."


Kukan mom ne da yaji ya hanasa k'arasa maganar sa tana cewa


"Shikenan Aisha kin cuceni, Allah ya isa tsakanina dake tunda kika juyamun k'wak'walwar yaro, alhaji dubi yanda yaron nan kejuyawa muradina baya saboda yaci gaba da ganina cikin bak'in ciki da b'acin rai, yazab'i wacce batasan zafin saba akaina dama ni nasan bazaka tab'a canzawa ba matuk'ar muna wuri d'aya da wannan munafukar" tanuna Ummi dake zaune tana kallon ikon Allah, daga yaro yafad'i gaskiya shikenan sai abu ya juye akanta, a hankali tace "Allah ya sawak'e"


Cikin zafin rai dady yace 


"Rufemun baki kafin na sab'a maki, wannan wane irin abun kunyane kikeyi agaban 'ya'yanki, kina jifar 'yar uwarki da munanan kalamai donki cimata zarafi" ai kamar jira takeyi tafara zuba masu balbalin bala'i wanda hakan yasa Mahmud ya sallami k'annensa daga d'akin shi kuma yadawo yana lallashin dad d'insa daya dena biyewa mom, kallon Ummi dady yayi had'e da yimata umurnin itama ta tafiyarta ya sallameta, ta gefen mom tabi zata wuce ta fizgota da k'arfi



"Munafuka wlh babu inda zakoje har sai ankai k'arshen matsalar nan, bana buk'atar zama dake don haka dolene murabu" murmushin takaici Ummi ta saki tare da kallon ta tun daga sama har k'asa


"Hajia Hussaina ki tabbata kinyi na farko kuma kinyi na k'arshe, kada ki kuskura hannunki ya sake ya k'ara tab'a jikina, zaginki, k'azafin ki da sauran miyagun kalamanki basukai ga baki matsayin da zan tanka maki ba amma ranar da duk kuskurenki ya aikeki da sake tab'a jikina, ranar zaki samu matsayi aguna da zaisa in canza maki kama" hannu mom tad'aga da niyar marin Ummi dady yayi saurin rik'eta tana d'ago fuska ya d'auketa mari, zai mayar mata da na biyu Mahmud ya rik'e masa hannu hawaye na zubowa daga cikin idanuwansa


"Kayi hak'uri dady, uwa nada matuk'ar muhimmancin da akwai zafi a daketa agaban 'ya'yanta, dady ba momy kad'ai ba ni kaina ina buk'atar araba wajen zama saboda farincikin mahaifiyata, Ummi kifahimci buk'atar mom idan har kin duba musulunci ma ya amince da haka sai idan lalurar rashin wani zaman ta gitta kad'ai ya bada damar azauna waje d'aya"


"Mahmud wlh ni banida matsala tunda nima aurena akeyi duk hukuncin da dadynka ya yanke daidai ne, ni bance abijirewa buk'atar mahaifiyar kaba!" Jirine ya d'ibi dady dake tsaye Mahmud yayi saurin zaunar dashi akan kujera, ita kuwa mom tunda tasha mari bata sake cewa k'anzil ba.


"Shikenan hajia Hussaina kinyi nasarar raba mani gida, kije na amince kizab'i d'aya daga cikin gidajena ki koma, Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" wasu zafafan hawayene suka zubo a kumatun Mahmud don har ga Allah baiji dad'in rabasa da 'yan uwansa da mom tayi ba, kawae ya zab'i hakane don samun farincikin iyayensa ko ba komai shi kansa dady yasamu farin ciki.


Nan kowanensu yafita yanajin wani irin sabon yanayi acikin zuciyarsa, daidai inda kowacensu zata nufi part d'inta sukaci karo da Batool itada Billy suna fad'a ga Bassam can agefe ya haye Bilal yanata faman dukansa shi kuma yana kuka Basmah kuwa ta koma gefe sai fad'in take 


"Yawwa Batool sauya mata kama, banza dubi yanda Bassam ke lallasa Bilal amma ke kin tsaya wasa, wlh kika bari billy ta jibgeki kin zama samna. Tana rufe baki Allah yaba Billy sa'a ta d'aga Batool sama ta nane (mayar) k'asa.


Da gudu mom dake farincikin cin zalinsu Bilal da 'ya'yanta keyi ta nufi wurin yayin da itama Ummi ta nufi inda Bassam ke dukar mata yaro don kai masa d'auki.














Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWA NA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____12💎



 Saida ta d'auke Bassam dake saman jikinsa yana duka kafin ta d'agosa yana kuka, lallashin tashiga yi had'e da kakka b'e masa jiki, a hankali tad'ago kanta tana kallon Bassam dake faman nishi sai kace wanda yayi wasan tsere,


"Bassam don me zaka yiwa d'an uwanka wannan duka, baka ganin kafishi girma, ko kana son kaga yaji ciwo ne, haba! Kudinga tausayin da k'asa gareku don Allah"


Hannunsa Basmah tazo taja tana qunquni k'asa k'asa ita marar kunya, girgiza kai Ummi tayi tare da cewa 


"Allah ya shirya manaku" hannu tasa ta d'auki Bilal dake kuka sannan tajuyo da niyar barin wajen, juyowar da zatayi taji Billy tasaki wata irin muguwar k'arar data sa both ya Mahmud da dady fitowa aguje saboda tashin hankali, kwance suka hango Billy a some kanta na zubar da jini a sanadiyar hankad'eta gefe da mom tayi lokacin da ta iskota bisa jikin Batool tana duka shine tafad'a akan d'aya daga cikin kujerun dake harabar gidan da yake irin na stones ne sai kanta ya bugu, speechless mom tazama  takasa karasawa wajen wasu zafafan hawaye na  zubo mata a idanu yayinda Mahmud ya d'auki Billy idanunsa ko gani basayi tsabar takaici shima hawayen ne ke zubar masa, bakin gate ya nufa da nufin samun abun hawa sai ga dady yafito da mota suka nufi asibiti, sosai jini ya zuba akan Billy don haka aka nemi a k'ara mata jini, nan take Mahmud yaje aka aunasa jininsu yazo d'aya, dafarko dady yaso a ibi jininsa kasan cewar Mahmud bai dad'e da tashi ciwo ba amma shi yak'i amincewa da haka, sai da likitoci suka tabbatarwa da dady babu wata matsala don and'ebi jininsa tunda ya samu sauk'i sannan hankalinsa ya kwanta, dady na ganin komai ya daidaita a asibiti ya d'auki motarsa ya kama hanyar gida, yana isa ko parking mai kyau bai yiba ya nufi part d'in mom, yana shiga ya taradda ita tana kallon wani season film (king of the heart) hankalinta kwance tamkar bata aikata komai ba, yaran tane kad'ai suka d'an shiga damuwar abun da yafaru don dukkanin su zaune suke kamar ruwa ya cisu, cikin kakkausar muryar da mom batasan dady da ita ba taji yace


"Enough hajia Hussaina, nace enough is enough, basai kin kashe mani 'yaba zan gane bakya son jinina, ba sai kin nuna cewa Bilkisu ba 'yarki bace zan gane bakya da asara idan tamutu, Allah yasani ina matuk'ar son 'ya'yana gabaki d'ayan su, bazan iya jurewa cutuwar d'aya daga cikin suba matuk'ar ina raye, nayita k'ok'arin tausar zuciyata wajen ganin banyi abunda zaisa yaranki suji ba dad'i aransu amma ke kin kasa fahimtar haka har saida kika kaini bango, saboda haka kitafi gidan ku bana buk'atar ganin ki agidan nan, kin fita raina tun lokacin da ida nuwana sukaga yanda kika illata mani yarinya, kika raba tsakanin d'aya da biyu don haka kibar gidan nan kafin indawo, sannan karki kuskura kibar gidan nan da yaro ko d'aya"


"Kasha k'arya, wlh tunda kakoreni cikin gidanka to kamar ka kori yaran kane, ai 'ya'ya nane ba ubanda ya haifa mani su don haka ba ubanda ya isa ya hanani tafiya da abuna da kuma ke cewa naraba d'aya biyu to ina naga d'ayan balle narabata biyu, babu wanda baisan cewa Aisha bata haihuwa ba , amma tsabar muna furci tunda taga inayi shine taje ta samo wud'ancan shegun aka k'ak'a ba maka, da yake kai kuma anriga an wanke an baka ka tara kai ka amsa shine kake nema ka mai dasu d'aya da 'ya'yanka to hakan bazata sab'uba wallahi"


"Tir Hussaina! tir da halinki, karki kuskura kisake sheganta mani yara, maza ki fice mun daga gida Allah ya shiryeki"


"Mtsss aikin banza, ance..." Kafin ta rufe baki dady ya shak'e mata wuya had'e da matseta ajikin bango idanunsa sunyi jawur tamkar garwashi,


"Ki maimata abunda kike son fad'a in kin cika, am tired of ur stupidity" da gudu yaran suka fito d'akunansu jin kakarin da mom d'insu keyi suna bawa dady hak'uri amma yak'i sakinta, ganin haka yasa Basmah tarik'e k'afafunsa tana kuka,



"Don Allah dady kayi hak'uri, ka saketa dady zafa ta mutu" sai da yaji gaba d'ayansu sun fashe da kuka sannan ya jefar da mom gefe yabar d'akin ransa a b'ace yana mai da na sanin aurenta, da sauri suka nufi kanta Batool ta d'ebo ruwa suka bata, dak'yar take shan ruwan sannan ta koma takwanta,


"Mom kitashi kitafi, wlh bakiga yanda fuskar dady tayi ba kada ya dawo ya iskoki, kitafi mu zamu biyoki daga baya" Basmah ce kefad'ar haka cikin kuka, saida mom tad'an dawo hayyacinta sannan tafara had'a kayanta tana jin wutar tsanar Aisha tare da yaranta na dad'a ruruwa acikin zuciyarta.



Ummi kuwa tunda abun yafaru tashige d'aki tana kuka, ko kad'an bata zaci tsanar da mom keyi mata ba takai ga har ta iya cutar mata da yara ta hanyar zubar masu da jini, ga Bilal a gefenta shima sai faman kuka yakeyi wai


"Ummi ina aunty Billy, meya faru da itane?, Ummi akaini wajen ta" Jawosa tayi ajikinta ta rungume hawayen ta na d'iga akan fuskarsa,


"Kayi hak'uri, auntynka na asibiti ba tada lafiya"


"Me yasameta Ummi? Itama 'YAN UWA NA NE suka yimata duka? Ummi ni basu jimin ciwo ba, sune suka jimata ko kuma mom ce? Ummi me yasa basa son mune?"


"Ya isa haka! nafad'a maka cewa ba tada lafiya ne, kayi hak'uri yanzu zamuje wajen ta kaji"


Mik'ewa Ummi tayi ta d'auko mayafinta, hannun Bilal ta rik'e suka nufi kofar fita saiga dady ya shigo, ganin yanayin da yake ciki yasa ta koma ta cire mayafinta, fridge ta bud'e ta d'auko ruwa masu sanyi a gora ta tsiyaya masa ga cup ta mik'a masa, kasa karb'a yayi yana kallon yanda idanunta suka rine saboda kukan da tayi, Bilal ta tura bedroom sannan takai ruwan abakinsa, a hankali yake shan ruwan yana kallon idanuwanta dake k'ok'arin sake kawo ruwa, bayan ta janye ruwan abakinsa, cikin sanyin murya yace



"Kiyi hak'uri rabba'atul bai..." Kafin ya iyar ta rufe masa baki, 


"Ba komai dama Allah ya tsaro yau jinin Bilkisu sai ya fita saboda haka muyi hak'uri mu rungumi wannan qaddara Allah ya tsare gaba, saidai naji ba dad'i naji zafi sosai araina" rungumeta yayi tana kuka yana cigaba da bata hak'uri


"Nayi kuskure sosai arayuwata rabba'atul baiti! Wannan duk ni najawo dana kasa tantance wace irin mata yakamata in d'auko gidana gashi yanzu..."



"Shhh...kadena fad'ar haka, ya jikin ita Bilkisu?" 


"Da sauk'i amma tarasa jini saida aka d'ibi na yayanta aka saka mata, yanzu haka bacci takeyi"


"Haba alhaji! Saboda me za'a d'ibar masa jini bacin kasan bashida lpy so kakeyi ayi biyu babu ne?" Muryar Mahmud tajiyo daga bakin k'ofa yana fad'in 


"Saboda ni yayan tane kuma au 'YAN UWA NA NE!...."



















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWA NA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____13💎



  Da sauri dady ya nufi inda yake


"My son ya akayi kabaro asibitin? Bilkisun ta farfad'o ne?"


"A'a dady har yanzu, bacci nabaro tanayi shine nadawo in karb'i kayayyakin da za'a iya buk'ata don gaskiya dr kamal yace sai ta kwana biyu anga yada jikin nata yayi kafin su bata sallama saboda da alamu tana d'an jin jiki"


"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, Allah yasa bawani abunne ya faru da ita ba" Ummi ce tafad'i haka tana mai dafe hannun kujerar dake gefenta saboda jirin da taji yana shirin d'ibarta"


"Ki kwantar da hankalinki Ummi babu abunda zai sami lil sis in sha Allah, suna so ne sai an yimata scanning d'in k'wak'walwar ta anga buguwar da tayi bata haifar mata da wata matsala ba shiyasa zasu d'an rik'emu na kwana biyu"


"Shi kenan kaje ka watsa ruwa kafin nan ta shish shirya kayan"


"A'a dady babu buk'atar hakan yanzu nasan gab take data tashi, Ummi kije ki had'a mani kayan bari inje indawo"


"To Babanah sannu kaji, Allah yayi maka albarka"


"Amin Ummi"


Nan yafita yabar dady zaune akan kujera ya dafe da kansa da alamu har yanzu yana cikin b'acin ran abunda ya faru.


Part d'in mom ya nufa yaci karo dasu Basmah abakin k'ofa d'auke da akwatuna guda biyu biye a bayan mom, wani irin kallo mai d'auke da alamar tambaya ya watsa masu da sauri suka ja baya tare da sakin akwatunan, kai mom ta d'ago cikin b'acin rai tana kallonsa tun daga sama har k'asa


"Dallah matsa kabani wuri in wuce, lpy zaka shigo ka tsoratamun yara haka"


"Yi hak'uri mom amma ina zaki jene?" Ba tare data kallesa ba tace


"Kaje katambayi mahaifinka" sannan taci gaba da tafiyarta, da sauri yasha gabanta


"Don Allah karki tafi mom, ya kike so muyi idan kin tafi, ko kina so ne murasa gatar da muke da ita agareki, ko kad'an bazamu juri rashin kiba, don Allah mom kiyi hak'uri" cigaba da tafiyarta tayi tana fad'in


"Ai sai kaje ita waccan daka fifita akaina ta maye maka gurbina, tabaka gatar da duk kake buk'ata, ammafa ina so kasani yazama dole ka kula da k'annenka kuma kayi masu duk abunda suke so tamkar inanan" cikin muryar kuka yake binta yana cewa


"Kiyi hakuri mom, babu wanda zai iya bamu gatar da takai taki, kefa uwace ita kuma uwa tanada matuk'ar karamci da tausayawa ga 'ya'yanta, inada tabbaci akan babu wacce takaiki ko tafiki awurinmu, don..." Da sauri ta katsesa had'e da d'aga masa hannu


"Ya isa haka..ka kula da 'yan uwanka shine kad'ai abunda zan fad'a maka idan kuma suma kazab'i wasu 'yan uwan akansu basai kayi hakan ba" saurin tarar gabanta ya sakeyi yana hawaye tare da rik'o Bassam dake gefensa


"Mom ki dubesa ki gani yana matuk'ar buk'atar ki a kusa da shi ko ba don muba kiyi hak'uri ki koma don sa, bana son kina fad'in wud'annan maganganun domin babu wanda zai iya maye mana gurbinki aduniya" sosai mom kejin tausayinsa azuciyarta, har ga Allah tana matuk'ar son sa fiye da sauran 'ya'yanta shiyasa duk lokacin da taga hankalinsa ya karkata a wajen Ummi da yaranta takeji tamkar anrabata dashi kallonsa tayi cike da kulawa


"My son!, ai shi mahaifinku bai san da haka ba saboda haka kamar yanda ya buk'aci in tafi  in bar masa gidansa, to zan tafi in yaso ita wacce ya zab'a yasa tamaye maku gurbina" Runtse idanuwansa yayi, sauran hawayen dake lak'e a idanuwansa suna bin layi a fuskarsa, duk daya san cewa komai yafaru laifin mom d'in sane hakan bai hanasa jin d'aci acikin zuciyar saba, sosai yakejin ba dad'i akan hukuncin da mahaifin nasa yayi, hannayensa yasa ya goge hawayen dake kwance akan fuskarsa tare da kallon mom, kafin yace wani abun yaji muryar batool data hango dady na fitowa daga part d'in Ummi shida ita nacewa 


"Ya..ya. Yaya don Allah kabar mom ta tafi ga dady can yafito karya sameta anan, zai iya yimata fiye da abunda yayi mata d'azun" akwatunan hannuwansu ya karb'a yana fad'in


"Shikenan maza ku shiga daga ciki, mom zo mutafi ko?" Gaba d'ayansu suka rungumeta yayinda itako hankalinta nakan dady da Ummi dake tsaye wajen motar da dady ke hawa aranta tana ayyana irin ja'izar (musibar) da zata saka Ummi da duk wani nata aciki, muryar Mahmud ta katse mata tunani dataji yana fad'in "mom mutafi"


Bud'e mata d'aya daga cikin motocin da key d'inta ke hannunsa yayi ta shiga sannan ya zuba akwatunan a bayan boot, wajen su dady ya nufa batare da ya kalli inda yake ba yace 


"Ummi don Allah kuwuce keda dady ya ajiyeki asibitin akwai inda zanje yanzun amma idan nadawo zan sameku acan"


"Shikenan Babanah amma ina mom d'inka zata jene?" Murmushin karfin hali yayi yana kallon yanda dady ya juya bayan sa jin abunda Ummi tafad'a, tabbas yau mom takaisa bango, cikin sanyin murya yace


"Kayi hak'uri" sannan ya nufi motar da mom keciki ya tayar suka fita"


A gaban dady Ummi takoma tana kallon fuskarsa, hannunta tasa ta d'ago fuskar had'e da cewa


"Dadyn yara meka aikata" batare da amsa mata ba ya bud'e gaban gambun motarsa yace


"Shiga muje"


"Ka am samun tambayata mana, ashe bazamu kasan ce masu yadda da k'addara ba, Allah yariga daya tsaro hakan tafaru don me zakayi hakan, kenan idan nima da nake mahaifiyarta tsotsayi yasa hakan tafaru sai kace sai ka hukun tani"


"Ba haka bane, ki kwantar da hankalinki kinsan kowaye ni, bazanyi abunda ba daidai ba, kawai kishiga mota kinji rabba'atul bait?" ya k'arasa maganar yana k'ok'arin dafa kafad'arta, cikin rashin jin dad'i ta d'aga masa hannu.


"Shikenan ya isa, amma kadubi yanayin da Babanah ya shiga, ashe bai cancanci yasamu farinciki daga gareka ba, ita uwa fa uwa ce duk yanda take d'anta bazai tab'a jurewa ganin ta cikin b'acin rai ba, don Allah kasake tunani"


"Rabba'atul bait kenan! Ai kema uwace ya akeyi kike jurewa damuwar da akae saka yaranki dake kanki aciki, ya kamata ak'alla ko sau d'ayane innuna mata kuskuren da take aikatawa, ina so mugudu tare kuma mutsira tare don haka dole tasan tayi kuskure beside wlh ba abunda ya faru akan Bilkisu yasa nace ta tafi ba, ta matuk'ar yin gangancine cikin kalaman da tayi mani wannan dalilin yasa nayi mata wannan hukunci" jin yanda yayi rantsuwa yasa jikinta yayi sanyi, tashiga cikin motar had'e da cewa 


"Allah ya sawak'e" 


A b'angaren mom kuwa ta madibi Mahmud ke kallonta kafin yace


"Mom ina zan kaiki?"


"Gidan mahaifina mana"


"A'a mom kituna koma da daraja irin ta papi, anya kina ganin zuwanki bazai tab'a masa kima ba, yakamata ace izuwa yanzu kinfitar da duk wani abu da kikeji aranki gameda Ummi, yanzu meye dad'in wannan abu da yafaru tsakaninki da dady agaban yara? Abunda tun kuna da k'uruciya bai tab'a faruwa ba sai yanzu da kuka manyanta" 


"Tabbas kuma wannan abun ba abunda ya k'ara mani illa tsana da k'iyayyar matar ubanka, saboda adalilinta komai ya faru, wlh wlh matuk'ar inada rayuwa saina salwantar da rayuwar Aisha zuriarta" da k'arfi ya taka burki yana fad'in


"Wa'iya zubillahi meye haka kike fad'a mom?"








Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWA NA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____14💎



 Wani irin sarawa yaji kansa yayi saboda munin maganar da yaji mom d'insa tayi, dafe kan nasa yai na kusan minti biyar kafin can muryar ta dake faman masifa tadawo dashi duniyar tunanin daya shiga.


"Nifa nagaji da wannan zaman motar in zaka kaini inda nafad'a maka ka kaini idan kuma ba zakaje ba sai infita in hau napep, kabi duk kawani b'ata rai sai kace karasa wani naka"


"Mom kiji tsoron Allah kidena fad'an mugayen maganganu akan Ummi, wlh Ummi mutuniyar kirki ce batada wata mummunar manufa akanki" 


"To ubana yimun wa'azi!, bari kaji tunkan ahaifeka nake zaune da ita, shin kasan ko saunawa ta salwantar mani da 'ya'ya?, don haka in kasake shiga maganganu na sai ranka ya b'aci"


"Ya salam! Mom duk duniya fa idan tataru bazata iya cutar dakai komai ba sai abunda Allah ya nufa akanka, ina da tabbaci akan Ummi bazata iya salwantar da yaranki ba Allah ne yayi cewa su ba rayayyu bane kuma wannan bazai zamo hujja agareki ba kice zaki salwantar da tata rayuwarta data zuriarta, yin hakan kuskure ne agareki" tsananin b'acin ran abunda yake fad'a yasa ta fita cikin motar had'e da bugo gambun motar da k'arfi, napep tafara k'ok'arin tara tana sabbatu


"Ya zama dole in d'au mataki akanki Aisha, yama za'ayi ace d'ana dana haifa ke k'ok'arin juyamun tunani akanki, inaaa doleni kisan cewa kinyi k'ok'arin shiga gonata" da sauri ya qaraso wajen cikin girmamawa yace


"Kiyi hak'uri mom, idan bakyaso in koma magana shikenan nayi shiru amma kiyi hak'uri ki koma cikin mota lokaci na qurewa" sai da yayi ta mata magiya kafin ya samu ta koma cikin motar tana huci kamar damisa.


'Daya daga cikin gidajen dady dake unguwar igala ya kaita, gida ne mai matuk'ar kyau da tsaruwa, kallon gidan mom tayi sannan ta maida kallonta ga Mahmud dake k'ok'arin bud'e marfin motar ya fita


"Kai a ina ne nan ka kawoni" 


"Gidan dady ne daya gama ginawa las two month ago"


"To sai akayi me?"


"Eh to, dama na kawoki nanne kizauna kafin dady ya sauko daga fushin da yayi"


"Kutumar ubancan! Sai aka cemaka ni banida gidan iyaye, wlh Mahmud kashiga taitayinka"


"Don Allah mom kirufa mana asiri kizauna warki anan, nasan yanda dady yake da sanyin rai bazai wuce kwana d'aya ko biyu ba zai nemi ki koma, kinga daga nan ma sai ki dawo warki nan gaba d'aya tunda dama kin buk'aci araba maku gida ke da Ummi"


"Kaji na rantse maka bazan zauna a wannan gidan ba, wan can gidan dai nake da buk'ata tunda yafi girma kuma ni nake da 'ya'ya masu yawa, idan ma zaka kaini gidan ubana ka kaini don yafi maka"


"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, wannan wace irin sabuwar rigimar ce kike shirin d'au kowa mom?, kefa kika nemi araba maku gida ba zaki zauna da ita ba, to taya za'ayi kuma kice ita zata fita tabar maki gidan, don Allah mom kicire son kai da yawa"


"Aikin banza, dalla malam ni wuce muje, bazan zauna anan d'in ba"


Shiru yayi kafin ya tayar da motar cikin b'acin rai, da gudu yabar wajen yanajin tamkar ya kurma ihu,


"Eyyeee.. Lallai ka girma da yawa Mahmud, ai sai kayi maza ka kasheni tunda na fad'i son raina" ba tare daya kalli mom d'in ta saba ya rage gudun da yakeyi har suka isa gidan papi wato mahaifin mom.


Tunda suka fita ba wanda ya cewa wani k'anzil, murmushi dady yayi had'e da kallon Ummi data juyar da kanta gefen glass, hannunsa ya d'ora akan nata dake saman cinyarta yana d'an matsawa ahankali, juyowa tayi tana kallon fuskarsa dake fitar da wani annuri saboda murmushin da yakeyi, a hankali ta lumshe idanuwanta, juyar da kanta tasakeyi tana kallon yanda motoci ke wucewa d'aya bayan d'aya, a hankali tafara motsa bakinta lokacin da taji ya sake rumk'e mata hannu sosai


"Maganar gaskiya dadyn yara inajin ba dad'i araina, bana son ganin Babanah a yanayin da na ganesa hakan na matuk'ar tab'a mani zuciya sosai"


A daidai nan dady ya shigo da kan motarsa cikin asibitin, sai da ya daidai ta tsayuwar motarsa sannan ya kalli Ummi


"Rabba'atul bait mun iso" juyowa tayi fuskarta ba walwala


"Wlh bana jin dad'in wannan shurun naka, kanaji nake magana ka shareni"


"To ya kike so nace?, Kiyi hak'uri zamuyi magana anjima kinji ko?" Gad'a masa kai tayi sannan ta bud'e marfin gambun motar tafito, aminity ward ya nufa tana biye dashi har suka iso room 5 in da aka kwantar da Bilkisu... Kwance Ummi ta hango ta bisa gadon jinyar marasa lafiya har lokacin bacci takeyi hankali kwance duk da da zaran ka kalleta zaka gano tana jin jiki sosai,


Da gudu Bilal dake rik'e a hannun ummi ya nufi gadon, Aunty Billy, Aunty Billy kitashi, Aunty Billy me yasa mekine, dady ne ya rik'o hannunsa dake neman ya rik'o hannun Bilkisu,


"Zo nan autana, Auntyn ka bata lpy ne, kayi mata addua kaji" gyad'a kansa yayi had'e da cewa


"Allah yaba Aunty Billy lpy dady, kullum abunda take cemun shine ina Bilal muso juna karka yadda kabarni, dady kace ta tashi nima bana so tabarni" dafa kansa dady yayi had'e da cewa


"Bazata barka ba kuna atare in sha Allah" ahankali Ummi ke shafa kan Bilkisu tana tofa mata addu'ar samun sauk'in rad'ad'in ciwo


 _BISMILLAHI ARK'IK', WALLAHU YASHFIK, MIN KULLI DA'IN MAUDU'I, WAMIN KULLI AINI AU ANI HATIM ALLAHU YASFIK, ALLAHUMMA RABBAN NAS, ASHFI BIL BA'AS, WASHFI ANTASH SHAFI'I LAA SHIFAA'A ILLA SHIFAA'UKA, SHIFA'ALLAHU LAA YUGADIRUSSAK'AMA, AS'ALALLAHUL AZHIM, RABBIL ARSHIL AZHIM AN YASH FIKA/KI_


Sosai Ummi ke maimaita wannan addu'ar tana tofamata, cikin Ikon Allah sai gashi tafara bud'e idanuwanta ahankali, 


"Ummi" ta furta ahankali, murmushi Ummi tayi sannan tace


"Sannu Bilkisu, Allah yabaki lpy" maida idanuwanta tayi ta rufe sannan ta sake bud'e su ahankali hawaye na zubowa daga ciki, k'ok'arin tashi tayi da sauri ta koma had'e da dafe kanta dake d'aure da bandage,


"Washhh..."


"Yi a hankali" Ummi tafad'a tana k'ok'arin gyara mata kwancinta, d'ayan hannunta ta mik'awa Bilal tana yimasa alama da kai da yazo, hannunsa dady ya saki 


Da gudu ya k'ara wajen ta "sannu Aunty Billy, bazaki barni ba ko?" A hankali ta d'aga masa kai hawaye na zubar mata, 


"Eyyee..alhmdulillah my lil sis ta farfad'o" idanunta ta d'ago tana kallon Mahmud dake a bakin k'ofar d'akin yana murmushi, k'arasowa yayi daga ciki tare da jaye Bilal dake rik'e da hannunta


"Jaye daga nan autan Ummi inga lil sis d'ina" kallon dady yayi cikin farincikin ganin 'yar uwarsa ta tashi yace




















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____15💎



  Dady yaushe tafarka ne? Gaskiya am so happy  "yanzun bada jimawa ba" dady yafad'a yana d'an Sosa k'eyar kansa, sai a lokacin yake jin ba dad'i bisa abunda yafaru tsakaninsa da mom saboda gaba d'aya sai yaji kunyar yaronsa  yake ji, ganin yanayin da dady ya shiga ya sashi saurin juyar da fuskarsa yana murmushi don dama yariga da yasan ko waye mahaifinsa, Sam shi ba mutumne mai taurin rai ba yana da matuk'ar sanyin hali fiye da tunani, duk da baisan meke ransa ba yafahimci cewa izuwa yanzu har yafara jin ba dad'i akan abun da yafaru, murmushi ya sakeyi wanda har sai da kyawawan hak'oransa suka bayyana had'e da shafa gefen fuskar Billy yana fad'in "sannu ko my lil", murmushin itama ta mayar masa tare da nuna masa gorar jinin da ake k'ara mata dake batun k'arewa, d'ago kansa yai yaga kad'an yarage jinin ya ida shigewa sannan yafita domin ya kirawo likita, bayan kamar minti biyu sai gashi ya dawo tare da wata nurse a bayansa. Sai da tacire mata gorar jinin dake lak'e a hannunta ta tambaye ta shin ko akwai inda keyi mata ciwo yanzu tace a'a sannan ta juyo cikin natsuwa tana gaishe dasu Ummi dake zaune, cikin 'yar siririyar muryarta da tayi daidai da tsarin jikinta ta maido kallonta ga Mahmud tana fad'in


"Za'a iya nemo abinci a bata taci"


"OK nurse mungode" batare da tace masa komai ba tajuya tabar wajen tana murmushi, daidai k'ofar fita taci karo da dr kamal yaturo gambun k'ofar d'akin zai shigowa, sunkuyar da kanta tayi cikin girmamawa tana gaishesa,


"Lpy klw faraaha, ya aiki?"


"Alhmdulillah"


"Dama kece on duty today"


"Yes sir,"


"OK, very good naji dad'in haka don dama ina tunanin acikinku wanda zanba foler patient d'ina a kula mani da ita before indawo saboda d'azun aka kirani zamu tafi wurin seminar na tsawon two days, to tunda kece on duty nasan no trouble zaki kula fiye da yanda zan buk'ata kiyimun" ya k'arasa maganar had'e da rufe k'ofar suna tafiya yana cigaba da yimata bayani har suka iso wajen gadon, hannu ya mik'awa dady suka gaisa yana kallon fuskar Billy da tayi wani irin haske sosai, tafin hannunta ya duba sannan yasa hannu fad'an bud'a cikin k'asan idanuwanta kad'an don ya tabbatar da jinin ya isa yanda suke buk'ata


"Yawwa 'yar gidan dady! Yanzu komai  yayi daidai alhmdulillah, babu ciwon kai da jiri ko?"


"Eh dr. Amma ina jin zafi cikin kaina sosai"


"Eh dole zakiji haka saboda anyi maki d'unki a inda kikaji rauni amma insha Allah shima zai dena" nurse d'in yafara gabatar masu cikin nuna k'warewarta da sanin yakamata ga aikinta...


"Alhaji wannan d'aya daga cikin jajirtaccin ma'aikatanmu ce mai suna faraaha, duk da Bilkisu tasamu sauk'i bazaku samu sallama yauba har sai nan da kwana biyu anyi mata scanning akanta an tabbatar babu wata matsalar data shiga acan ciki, don haka duk abunda ya kamata ayi mata anyi photon shi kad'ai ake jira da kuma dawowar k'arfin jikinta, yanzu zan mik'a folder d'inta a hannun sister faraha zataci gaba da kula da ita saboda kiran gaggawa da nasamu yau d'innan akan zamuje wajen seminar, na yarda da k'warewar faraaha sosai ina fatan bazaku samu damuwa ba, faraaha ina so kibawa patient d'ina kula yanda ya kamata domin su d'in tamkar 'YAN UWANA NE"

 

"Shikenan dr. In sha Allah zanyi" sai da ya sake yiwa Billy checkup da kyau ya tabbatar babu wata matsala sannan yayi sallama da dady ita kuma faraaha ta koma bakin aikinta, hannun bilal dady ya rik'o suka fito shida dr. suna k'ara tattaunawa akan yadda abun yafaru, acan cikin d'akin kuwa wayar ummice tayi k'ara da sauri ta d'auka ganin lambar wacce takira had'e da barin d'akin shikuma Mahmud ya koma inda Billy ke kwance yana tambayarta ko me zataci,


"Bana son komai Yaya" 


"Ai kuwa kinsha k'arya dolene kifad'i abincin da za'a nemo maki kici"


"A'a Yaya ni bazanci ba"


"Zancen kike so lil sis, idan baki fad'a ba zanje inkawo maki duk abunda na samu kuma dole zakicisa in kuma kink'i inyi maki d'ure"


"A'a to zan fad'a, kasiyomun chaculate" zaro ido yayi cike da mamaki, 


"Lallai Billy kin renani da yawa, chaculate d'in ne abinci?" K'efta idanuwanta tafarayi alamar zatayi kuka, goshinsa ya dafe


"Oh! Sorry shikenan ina zuwa bari naje nakawo maki, enough ki kwanta kihuta kinji ko? kai ta d'aga masa had'e da rufe idanuwanta"


A b'angaren mom kuwa tayi abu ya shamata kai, don tsabar kishinta tunda ta isa gida takasa samun natsuwa babu abunda take ayyanawa aranta sai hango dady da Ummi suna buga sabuwar soyayya ga wata irin kula ta musamman da yake bata da 'ya'yanta ita kuma nata 'ya'yan sun wofantar mata dasu hatta bacci idan takwanta kyakkyawan murmushi take hango dady yana yiwa Ummi abu mafi munin data tsana taga yayi mata, da zaran taga haka cikin bacci a firgice take tashi kuma baccin da bazata koma ba kenan, yau kwana d'aya kenan da komawarta gidansu amma dady bai tab'a yunk'urin nemanta koda awayane haka yasa Basmah dole ta koma asibiti wajen jinyar Bilkisu sukuma Batool da Bassam yasa suka kwashe kayansu suka koma part d'in Ummi, duk abunda uwa keyiwa 'ya yiwa 'ya'yanta Ummi nayiwa su Bassam daidai gwargwado duk da ba k'aramin hak'uri takeyi da yanayin tarbiyar tasu, kullum tana kalle da Batool in lokacin sallah yayi bata tashi tayi haka safe ko rana gaba d'aya bata iya gaishesu ga rashin kunya kala-kala da take yimata agidan, dafarko Ummi na hak'uri amma ganin abun yayi worst yasa tazaunar da Batool tayi mata fad'a sosai sannan ta nuna mata matuk'ar bata gyara ba to tabbas sai ta sab'amata, hakan yasa Batool tashiga taitayinta amman kullum cikin kuka take wai Ummi na takura mata, shi kuwa Bassam bawata matsala da yakeba ta inba cutar Bilal da yake yiba, har mamakin kalolin k'etar da yakeyi take koda yake kullum cikin kallon wrestling yake shiyasa, Basmah kuwa zuwan asibitin kad'ai take amma babu wata jinya da takeyi, hatta abinci bazata iya zubawa Billy taci ba saida tagaji tazuba ma kanta ko kuma idan Yaya Mahmud yazo yazuba mata duk da ba wani ci sosai takeyi ba, kullum basmah na kwance akan caution d'in dake d'akin  rik'e da waya tana latsa tana tamnar cingum, sallah ma sama sama take yinta takomawarta kwance tana cigaba da latsar waya tana dariya, saboda yawan dariyar da takeyi yau sai da sister faraaha tayi mata magana akan tadena tana damun marasa lafiya amma tsabar rashin kirki irin na Basmah ta zauna ta zagaeta tass tare da buga mata warning akan karta sake shiga gonarta, tun alokacin taji ta tsani faraaha, duk abunda takeyi babu wanda ke iya da katar da ita inba Yaya Mahmud ba shikad'ai ne ko muryarsa taji zata shiga taitayinta, gashi yau tun safe bai samu lek'owa asibitin ba, shigowar sister faraaha d'akin yakai sau goma duk don tasamu ta gansa amma hakan ya gagara, tun ranar da idanun sister faraaha suka sauka akan fuskar Mahmud taji ya matuk'ar kwanta mata arai, duk abunda yayi na matuk'ar burgeta wannan dalilin ne yasa idan ta kammala duba lpyr patient d'inta sai tadawo d'akin suyita fira da Billy, baza tabar d'akin ba sai lokacin da taga shigowarsa, cike da jin dad'i da fara'a sun gaisa da juna tanajin wani irin shauk'in soyayyarsa na fisgarta sannan zatabar d'akin, maganar gaskiya faraaha tafad'awa son Mahmud son da bazata iya misil tashiba, turo k'ofar tayi bakinta d'auke da sallama tashigo tana kallon Bilkisu cikin fara'ah tace


"Sisto kishirya anjima zamuje wajen scanning kinji ko"


"Eh Aunty faraaha" har ta juya zata fita sai kuma tajuyo


"Yawwa sisto nace har yanzu yayanki bai zoba? Injin dai ko lpy?" Kafin billy ta bata amsa taji Basmah taja wani ubantsaki


"Mtssss..munsan komai anji haushi wlh ace ina macce in kwarewa namiji har ina zuwa neman sa tirr, wai sunan malamar asibiti kenan to kota soyayya?" Kokad'an faraaha bayani mamakin kalaman dake fitowa daga bakin Basmah ba domin tasan ko zata girmeta kad'anne, ga yanda yanayinta ke canzawa idan ta ganeta ta tabbata duk cikakkiyar budurwa irinta zatasan halin da take ciki akansa, don haka itama sai tayi murmushi cikin natsuwa tana kallonta tun daga sama har k'asa sannan ahankali itama taja nata tsukin.


"Mssss..Aikin banza harara cikin duhu, ai shi malam bahaushe yace iya ruwa fidda kai" tana rufe baki sai ga Yaya Mahmud ya iso tare dasu Bilal da bassam da kuma batool ta rik'o kulolin abinci wajen, daga ciki ta shige ta sakar masu hanyar da zasu shigo daga ciki, suna shigowa tajuya zata fita batare da tace masa komai ba Bilal ya rugo ya rik'eta yana fad'in


"Oyoyo aunty faraaha" cikin sakin fuska ba sosai ba itama tace "oyoyo aunty Bilal kana lpy?"


"Lpy klw Ummi tace agaisheki da k'ok'ari" duk'owa tayi daidai tsawonsa taja hancinsa


"Yawwa Ummi kace mata nagode" wani tsakin Basmah tasake ja acan k'ark'ashin mak'oshi yanda Mahmud bazaiji ba tace


"Munafuka" ko kallonta faraaha batayi ba taja hannun Bilal zasu fita, da sauri Mahmud dake k'ok'arin mik'ewa Billy ledar ice cream da chocolate daya siyo mata yana fad'in lil sis ya jiki ya juyo yana kallon faraaha da zata fita


"Malamar asibiti yau ba magana ne?" Batare data juyo ba cikin 'yar siririyar muryarta tace


"Naga ko 'yar k'anwata Basmah data gaisheka bakaji ba balle ka amsa mata shiyasa nima nahutar da kaina" faraaha nasane da ko sallamar da sukayi bata amsa ba balle ta gaishesa tayi hakanne don ta nunawa Basmah kuskurenta kafin ta rufe baki taji tana fad'in


"Eh.eh.Yaya inata magana bakaji ba, ina wuni?" Wani irin mugun kallo ya watsa mata had'e da cewa


"Munafuka yaushe ki kayi mani magana keda inji ko sallama kasa amsawa kikayi kina can kina latsar waya, keda aka kawo jinyar marar lpy kin koma shashanci idan bakiyi hattara ba saina karb'e wayar nabawa mai gadin asibitin nan stupid"


Murmushi faraaha tayi tana kallon Basmah dake kallonta rai ab'ace ta kashe mata ijiya d'aya tare da jan Bilal suka fita, shi kuwa Mahmud bayan faraaha dake tafiya yabi da kallo cike da jin dad'in ganinta"


Batool kuwa kallon Billy tayi tace






















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____16💎


  

  Ke Billy wai meye tsakanin waccan nurse d'in ne da Yaya, 'yar dariya tayi tana kallon Basmah dake tsaye abinta har lokacin zuciyarta na tuk'uk'i akan fad'an da faraaha taja akayi mata, da hannu tanuna Basmah tare da maido kallonta ga Batool daidai kunnenta ta rad'a mata.


"Bansan komai ba kije kitambayi yayya Basmah don naga alamar ita tafahimci ko meye ko kuma intambayar maki yaya yabaki amsar da kansa.." Da sauri ta zaro idanuwa waje had'e da sakar mata rank'washi akai tana nunata da hannu,


"Ke rufe baki so kike ya b'abb'allani nima abani gado a asibitin nan?, kawai manta dashi idan tayi tsami zamuji" tana rufe baki taji an rik'e mata d'ayan kunnen da k'arfi tamkar zai cire ashe duk abunda suke fad'a akunnensa yana jinsu,


"Bari nafad'a maki tunda so kikeyi kiji magulmaciya"


"Awshhh..Yaya cikani don Allah wlh da zafi" sake rik'e kunnen yai sosai ta yanda zafin zai d'ara wanda taji daga farko,


"Pls am sorry Yaya" sakinta yayi tare da mak'alo wuyanta a k'ark'ashin kafad'arsa yana dariya


"Kura ga tsoro ga ban tsoro, to ya kika ganta kuwa tayi?" Turo baki tayi hannunta d'aya na saman kunnenta dake yimata rad'ad'i.


"Gaskiya batayi ba, mace sai kace muciya" tana rufe baki kafin yayi k'ok'arin d'aukar wani action ta zille masa tabar d'akin aguje tana dariyar k'eta don tasan tayine kawai don ta k'waga masa akan abinda yayi mata, dariyar shima yayi had'e da shafa kansa, hatta Billy da Basmah dake faman kumburar fuska saida sukayi dariyar yanda ta zunduma da gudu, juyowa Basmah tayi donta koma mazauninta taga Bassam rik'e da wayarta sai faman game yakeyi, ak'ufule tayo kansa shi kuma ya yadda wayar ya ruga abayan Mahmud ya b'uya, jawo hannunsa yayi yace


"Zo gashi narik'e maki" ai kuwa ko kunya bata jiba tayo kansa cikin b'acin rai da nufin kai masa duka, da sauri Mahmud ya rik'e hannunta yana dariya


"Kai Basmah yanzu saiki dukesa akan ya tab'a maki waya ke ko kunya bakiji ba"


"To don me zai tab'amun, game fa yakemun kuma banida enough charji"


"Oh sorry!...bazai k'ara ba ko? mahmud ya fad'a yana kallonsa, kad'a masa kai yayi yace


"Eh Yaya"


"To kinji yace ya dena saboda haka tunda gani nazo kije gida kigyara idan dady da Ummi zasu zo sai kudawo tare muje gaida mom" hakan da yace ba k'aramin dad'i yayi mata ba, nan take cikin farinciki tahau har had'a kayanta, wayarta da ear piece da kuma charger tad'auko tasaka a cikin 'yar mini hand bag d'inta dake gefenta sannan tabar d'akin ba tare data kalli ko inda Billy ke zaune ba balle tasa ran zata cemata wani abun.


Bayan tafita yayi murmushi yace 'YAN UWANA kenan ko wannenku da kalar tasa rayuwar ya Allah kasa muso juna.


"Amin" yaji Billy tafad'a tana k'ok'arin tura chaculate d'in data kwand'are acikin baki, gefenta ya zauna akan gadon yace 


"Billy ya jikin naki?"


"Alhmdulillah naji sauk'i Yaya, wai sai yaushe zasu bamu sallama wlh ni nagaji da kwancin gadon nan"


"Ai kuwa hak'uri zakiyi har sai lokacin da aka yimaki scanning result ya nuna ba wata matsala sannan, gashi har yanzu basusa date d'in yin scanning d'in ba kinga kuwa indan zama yanzu kika fara"


"Kai Yaya hadda wani yanzu nafara zama don bakaso ka dena ganin aunty faraaha ko?, to thank good ance bayan sallar la'asar za'ayi scanning d'in" mintsili ya kaimata a kumatu had'e da cewa


"Kema biyewa Batool zakiyi ko? Nifa babu wani abu tsakanina da faraaha, the way yanda ta gwane ga aikin tane da kuma kulawar da take baki yanda ya kamata shiyasa kikaga nadamu da ita"


"Dagaske Yaya ba sonta kake yiba?"


"Eh mana baki yarda bane?"


"No..amma meyasa kacewa Batool..." Kafin ta iyar yace


"Common.. da wasafa nakeyi, sincirely ni babu wani tsarin soyayya ko aure agabana, faraaha kuwa burgeni ne kad'ai alamurranta keyi amma babu soyayyar ta aziciyata"


Sun jima da ita tana nuna masa irin alkhairan da faraaha take tartare dasu zaifi dacewa ace ya mallaketa amatsayin masoyiyarsa amma fir  Mahmud ya nuna mata shi ba sonta yakeyi ba, abunda ya matuk'ar d'aure mata kai shine yanda yake matuk'ar farinciki idan suka had'u  da ita da irin kallon da yake yimata amma wai yace shi ba sonta yakeyi ba kawai burgesa takeyi, yatsunsa ya murza akan fuskar ta har saida sukayi k'ara, firgigit Billy tafarka daga duniyar tunanin data lula, girarsa ya d'aga kafin yace


"What?"


"Nothing Yaya just dt ina mamaki ne"


"Believe me lil sis dama kindena"


Sai gab da sallar la'asar su Ummi suka shigo cikin asibitin tare da Basmah, kai tsaye dady ya nufi wajen faraaha don bincikar cigaban da aka samu game da lafiyar 'yarsa ita kuma Ummi da Basmah suka wuce room d'in da suke jinyar Billy, cikin girmamawa dady daya isko faraaha zaune dasu Bilal da Bassam tamik'e tana gaishesa, sun d'auki kusan mintuna biyar tana yimasa cikakken bayani daga k'arshe tafad'a masa cewa yau d'innan za'aje da ita wajen scanning da zaran anyi sallar la'asar, godiya yayi mata sosai tare da sanya mata albarka sannan ya nufi d'akin, Billy na ganinsa ta washe baki cikin farinciki tace 


"Dady sannu da zuwa" cikin fara'a shima ya amsa mata da "yawwa Bilkisu ya jikin naki"


"Alhmdulillah dady naji sauk'i sallama kad'ai nake jira" Ummi ya kalla cikin sigar tsokana yace


"Umminsu mekike bawa Japanese d'innan tawa naga tak'ara haske da k'iba dubi fa yanda idanuwanta suka k'ara shigewa" gaba d'aya d'akin aka hau dariya banda Basmah data koma gefe tana kallon duk abunda ke faruwa da gefen idanuwanta, wata irin muguwar harara ta aikawa Billy dake faman yiwa dady kukan shagwab'a wai yadena fad'a yasa suna yimata dariya had'e da cewa


"Munafuka" Billy kam da batama san tanayi ba ta kalleta tace


"Wlh Allah dady yayya Basmah tafini k'iba, d'ibeta fa" gaba d'aya kowa ya juyo yana kallonta, indai k'ibace  ba wanda bai yitaba agidan nan sai ni Mahmud yafad'a yana dariya, hannu Ummi tasa akuncinta tana shafawa ahankali fuskarta d'auke da murmushi


"Babanah aikai da wuya idan zakayi k'iba don kai gaba d'aya jikinka sak irin na abbatine" wato mahaifin dady Allah ya jik'an rai, hannunsa shima ya d'ora akan nata yarike  


"Ummi aikuwa ni bana son irin jikin tsohon nan na fulanin rugga, nafison inyi irin jikin dadynah.." Kafin ya rufe baki dady yad'an rank'washesa akai


"Ai anriga angama, ja'irin yaro" haka dai suka yita firarsu cikin farinciki da walwala a lokacinne da dady yafahimci irin k'ibar da kowannensu sukayi, wani irin farinciki ne ya rufesa duk da cewa yana kewar mom amatsayin sa na mijinta hakan baisa kwanciyar hankalin data bayyana agidansa tab'oyu ba, sunanan  zaune aka kira sallar la'asar dady da yaransa suka nufi masallaci yayin da Ummi da 'yan matanta suka shiga toilet d'in dake nan cikin d'akin sukayo arwala don gabatar da sallah, bayan duka sun sallame su Billy da Batool suka gaida Ummi ita kuma Basmah takoma gefe abunta tazauna, da gudu Bilal da Bassam suka rugo suka fad'a jikin Ummi dake zaune a inda ta ida sallah, suma d'in gaisheta sukayi Bilal na fad'in Ummi muda Yaya zamuje wajen Small mom zakije? Kafin tabashi amsa sai ga Mahmud yashigo shima har k'asa ya duk'a ya gaida Ummi had'e da cewa


"Ummi zamuje wajen mom, idan faraaha tazo tafiya da lil sis wajen scanning saiki rakata, dady ya riga da yafita shida abokinsa yanzu?"


"Shikenan Babanah babu damuwa zaku iya tafiya, kugaisheda mom d'in taku sosai" 'Dan tsaki Basmah tayi


"Yaya nidai ina waje zan jiraku bazan iya zama ina saukar maganganun da basu kai ciki ba" a hasale Mahmud yayi kanta cikin b'acin rai da nufin falla mata marora Ummi ta dakatar dashi,


"K'yaleta Babanah! Babu komai Allah ya shiryeta" juyowa tayi ta kalli Ummi sannan ta bud'e d'akin tafita cikin b'acin rai. Shi kansa baisan lokacin da yakaiwa bangon d'akin naushi ba saboda yanda zuciyarsa ke tafarfasa, tsabar yanda launin idanunsa suka canza zuwa jajaye zaka d'auka barkono aka watsa masa aciki, baisan meyasa Basmah bata shakkar kowa ba, yazama dole ya taka mata burki takowace hanya, matuk'ar halinta yamik'e haka zata matuk'ar shan wahala arayuwa shi kuma abunda baya fata kenan, wurin Ummi ya dawo yana bata hak'uri bisa abunda Basmah tayi mata, shafa gashin kansa tayi had'e da cewa


"Kamanta Babanah ita yarinya ce, maza katashi kutafi marece nayi ko acan zasu kwana"


"A'a Ummi gaisheta kad'ai dady ya amince muje muyi"


Akan hanya ne Batool ta kalli Basmah


"Yayyah Basmah" basmah dake rufe da idanu ear piec lik'e akunnenta d'aya tace 


"Meye?"


"A gaskiya abunda kikayi d'azu baki kyautaba" har lokacin idanunta na arufe tace


"Meye kuma damuwarki tunda ba mom nayiwa ba"


Da k'arfi Mahmud yataka burkin mota cikin b'acin rai yace


"Fitarmun a mota kafin na k'irga uku" ko kallonsa batayi ba tabud'e gambun motar tafita abunta tana taunar cingam, ya dad'e kansa kwance a staring mota kafin ya tayar da motar suci gaba da tafiya,


"Yaya kayi hak'uri mukoma a d'aukota"


"K'yaleta Batool, tafiyar Rabin kilometer yarage ak'arasa, wannan shine punishment d'in da ya kamaceta, yanzu idan za'ace kifad'i halin Ummi miye matsalarta data cancanci nuna k'iyayya daga wajenmu, yakamata ace munbar matsalar su can atsakaninsu bawai murik'a saka kawunanmu aciki ba, inajin zafi da rad'ad'i idan naga matsaloli na faruwa acikin gidanmu, shin kin tab'ajin Billy tayiwa mom rashin kunya?, yazakiji aranki idan ki kaga ta aikata haka ga mahaifiyarki wacce ta haifeki, ya kamata ace izuwa yanzu dukkaninku kun canza Batool! ku 'YAN UWANA NE kuma suma su Billy 'YAN UWANA NE, ina so muso junanmu, mubar su mom da abinda ke a tsakaninsu muyita yimasu addu'a har zuwa ranar da suma zasu so junansu, amma kina kallo 'yar uwarki kullum shashancinta sai k'aruwa yakeyi,


"Kayi hak'uri Yaya nadad'e da fahimtar Ummi ada ina yimata kallon munafuka wacce bata son mu amma fad'an zaman nan danayi da ita sai nafahimci tamafi sonmu akan mom" jawo Bilal tayi ajikinta sannan taci gaba da cewa nafahimci su Bilal 'YAN UWANA NE kuma ina sonsu, zance gaba da lurar da yayya Basmah har zuwa lokacin da ak'idar da mom tasaka mana arai zata fita cikin zuciyarta" wasu zafafan hawaye ne suka fito masa a idanu saboda jin dad'in canzawar Batool, yatabbata da sannu matsalolin gidansu sunfara ragewa, saita madubinsa yayi suka had'a ido da ita ya sakar mata murmushi


"Nagode sosai da fahimtar ta 'yar uwa....
















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____17💎



 Daidai k'ofar gidansu mom yayi parking motar Batool tafito aguje tana kiran mom, mom dake zaune bisa d'aya daga cikin kujerun dake falon mahaifinta ta d'ora kanta bisa kan kujerar idanuwanta arufe azahiri zaka d'auka bacci takeyi amma idanunta biyu kawai tashiga duniyar tunanin hanyar da zata d'auki fansar wannan zaman da  Ummi tajawo tanayi agidansu, muryar 'yar tata da tajiyo yasata saurin bud'e idanuwanta ahankali tace


"Batool" tare da dubon k'ofar da tajiyo sautin muryar ta, hangota tayi aguje Mahmud na biye da ita hannayensa rik'e da Bassam da Bilal yana dariyar gudun da Batool keyi, tana isowa inda take suka rungume juna tamkar sun dad'e basu had'uba cikin farinciki mom ta d'ago ta tana kallon yanda ta canza, Batool na dariya ta sake rungumeta


"Nice mom, nayi matuk'ar kewarki da yawa" wasu hawayen dad'ine suka zubowa mom tace


"Nima haka 'yatah, ina auntynki ne?" Ganin Bassam yasa bata jira amsar da Batool zata bata ba tasa hannu ta  d'aukesa had'e da cillasa sama tana fad'in


"Oyoyo autana" shafa kansa tayi tana dariya"Auta bakayi missing mom d'inka ba gaskiya, dubi yanda ka canza lallai aunty Basmah tana kula mani daku yanda ya kamata ko Yaya Mahmud zance?"


"A'a mom Ummi ce ba yayya Basmah ba ko Yaya Mahmud?" Yak'arasa maganar yana kallon gefen da suke tsaye shida Bilal, d'ago kan da mom tayi sukayi ido biyu da Bilal dake gefen Mahmud yayi saurin b'uya a bayansa, kallonta Mahmud yayi sannan ya jawo hannun Bilal dake bayansa ya durk'usa daidai tsawonsa tare da d'ora hannuwansa akan kafad'unsa,


"Bilal! kai bazakaje kayiwa mom oyoyo bane?, dubi yanda Bassam yaje yayi mata ta d'aukesa kai baka so ne ta d'aukeka?" kad'a masa kai yayi ahankali yaje saitin kunnensa yace


"Yaya inajin tsorone"


"Karkaji wani tsoro, ka saki jikinki ba abunda zatayi maka saboda haka yimaza kaje kajiko?" juyowar da Bilal yayi yaga yanda mom ke dariya saboda farincikin ganin 'ya'yanta datayi yasa shima sai ya samu courage d'in rugawa ya rungumeta kamar yanda Mahmud ya umurcesa da yayi, yana kaiwa mom tasa hannuwa biyu biyu zata ingijesa cikin tsorata yayi saurin rintse idanuwansa zuciyarsa nabugawa, sai ga papi nafitowa daga bedroom d'insa, mom na ganinsa saita waskewa ta d'aga Bilal sama tana fad'in


"Oyoyo autan dady kana lpy?" zuciyarta na rad'ad'i don bahaka tasoba gudun cin mutuncin da papi zai yimata idan yaga abunda tayi niyar aikatawa yasa tayi hakan, wata irin muguwar harara ta watsawa Mahmud dake dariya har kyawawan hak'oransa na bayyana da sauri ya juyar da kansa gefe had'e da shafa k'eyar kansa yana mai gintse dariyar dake neman sake fito masa da gudu su Batool suka nupi inda papi ya zauna akan kujera suna gaishesa shi kuma Mahmud ya k'araso inda mom yana Sosa k'eyar kansa


"Mom ina wuni" batare data amsa gaisuwar tasa ba tace "ina 'yatah Basmah?" Cikin rashin damuwa akan amsar da zai bata yace "tana kan hanya nan da minti ashirin nasan zata k'araso" zaro idanuwa wajenta awaje tayi sannan tace "kamar ya? Halama ita wa zai kawota ne?"


"Haba mom kowa kinyi masa tarba mai kyau hatta d'an autanmu Bilal yasamu kyakkyawar tarba daga wajenki saini ne zaki tarbeni ta hanyar wud'annan da tambayoyi"


"Ka amsamun abunda natambayeka yanzun nan koka fuskanci fushina"


"Ehh to ita dai zata kawo kanta da k'afafunta don nasan girman kanta bazai barta tahau napep ba" ya k'arasa maganar yana d'an sosa bayan kunnensa, suna had'a idanuwa da mom baisan lokacin da yafara yimata bayanin abunda yafaru ba shine shikuma da ransa ya b'aci yace tafitar masa a mota, 


"What? Kana nufin atiti kabaromun yarinya? Wlh minti biyar nabaka ka koma ka d'aukota" hak'uri yabata sannan ya nufi wajen papi dake rungume da Bilal agefensa na dama yayinda ya tokare sandarsa da hannunsa na hagu, cikin girmamawa tare da tsokana Mahmud ya karb'i sandar tare da ajiyeta gefe yana fad'in


"Yallab'ai yo ai sai ka ajiye wannan sandar tunda kazauna, irin wannan abu haka sai kace tsohon daya fara rud'ewa " saida papi yayi dariya sannan yace


"Uwarka gatacan ita tafara rud'ewar da takasa banbance gaskiya da kuma rud'in zuciya"


Ya k'arasa maganar had'e da nuna mom dake can gefe zaune, don tun ranar da tazo yakira dady yaji abunda yafaru tsakaninsu yake fushi da ita kuma baya shiga alamurranta dashi har hajiya kaka wato mahai fiyarta,


"Allah yabaka hak'uri papi abun baikai haka ba" gaishesa Mahmud yayi tare da tambayar ina hajiya kaka, ai kuwa da sauri papi ya d'ora yatsansa akan baki yana kallonsu Bassam dake wasa suna d'aga murya


"Shiiiiii.....kuyi shiru karku tadamun da masoyiya bacci" kafin yarufe baki Batool da Bilal da suka fahimci tana bedroom d'insa suka rugo aguje shima Bilal yabi bayansu suka shige d'akin suna fad'in


"Hajiya kakaaaa.."


Sandar papi dake gefe ya d'auko yana kwalar Mahmud da ita wai duk shi yaja zasuje sutayar da ita, dariya Mahmud ya kwashe da ita had'e da tashi zaibar wajen papi ya rik'e masa riga 


"Ba inda zakaje sai kafito mani da ja'iran k'annen can naka masu zubi da aku" ba Mahmud kad'ai ba hatta mom dake cika tana batsewa saboda abunda Mahmud yayi saida tayi dariya, aranta tanaji inama ace itama ita kad'ai take ga dadynsu Bassam yayi mata irin son da papi keyiwa hajia kaka ya bata kula kamar yanda papinta ke bawa hajia kaka.  Muryar Basmah ce tafito da ita duniyar tunanin data lula da sauri ta iso inda take tana dudubata.


"Sannu Basmah ashe haka yaron nan yayi maki? Kibarni dashi sai yagane kurensa, injin k'afafunki basa yimaki ciwo" 


Batare da Basmah ta lura da papi dake falon ba tace


"Wallahi Allah mom Yaya mugune, badon Allah yasa inada wani guy dake da motaba nakirasa yazo ya d'aukeni da saidai ink'araso gidannan ak'afa, kinga ma ice cream yabiya dani ta ten 'o seven ya siyamun" ta d'ago ledar tana nunawa mom


 "Allah sarki yaron kirki, dubi yanda yayi maki abunda yayanki ya kasa yimaki, Allah dai yayi masa albarka"


Mom narufe baki taji saukar sandar papi ajikin Basmah jikinsa har cira yakeyi yanata doka mata ita a duk inda yasamu, duk da yake bawani k'arfine da papi ba sosai take jin zafin dukan da yake yimata hakan yasata b'uya a bayan mom da yake idanunsa sunrufe ya had'a harda mom d'in yana dukansu, hakan yasa mom taja Basmah suka bar falon shikuma papi Mahmud yarik'asa ya zaunar dashi akan kujera yana faman nishi d'aya bayan d'aya kamar wanda yayi wani ja aiki, tafa hannuwa Mahmud yashigayi yana fad'in 


"Sannu papi, gud job" da sauri papi ya d'aga sandarsa shima ya doka masa a k'afa har saida yayi d'an tsalle "washh papi ni kuma meye laifina"


"Tirr...... ai wannan duka laifin kane da baka tsawatar mata tunda kaine babba agidan, nasan shi dadyn naka yafiye sanyin hali da yawa ba lallaine taji tsoron saba ita kuma mahaifiyar taku shashashace ko kanta batayiwa fad'aba balle tayiwa 'yarta, kai yakamata ace kasa ido akan k'annenka amma dubi yanda tsabar rashin kunya yanda take fad'ar wani namiji ya d'aukota hadda biyawa wani wajen da ita, ita kuma sakaryar harda wani samasa albarka allah ya tsare bata damu da sanin koshi ya dad'e da samun albarka 'yar tataba"


"A'a papi kadena fad'an haka wlh muna iya k'ok'arin mu Basmah ce tacika rawar...." Sandar papi yasake d'agawa kafin ya iyar da maganar sa da nufin sake doka masa yana fad'in


"Maza fice kabani wuri kafin kalma na nuna maka naka kuskuren"


Aguje Mahmud yanufi wajen hajiya kaka yana dariyar yanda papi baya shakkar dokawa kowa sandarsa, yana shiga ya tarar dasu Batool gaba d'aya akan gadon sun tada ita suna faman yimata surutu amma dayake baccin bai ishetaba sai faman gyan gyad'i takeyi sukuma suna yimata dariya...



  *_A BIG HAPPY JUMA'AT TO ALL MY FANS😘😘 LUV U SO MUCH❤_*
















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____18💎



  Dariya shima yayi sannan ya tako gaban kantareren gadon 


"Batool kutashi kufita yanzun nan zakuga papi yashigo kuma kar kunsan halinsa inya iskoku, ku kyale hajiya kaka kutafiyarku wajen mom, indai itace nasan bazata tashi baccin nan yanzu ba" yana rufe baki sai ga papi yashigo yana takawa ahankali, rufe k'ofar da zaiyi ya juyo ya hango masoyiyarsa a tsakiyar gado zaune tana faman gyan gyad'i sukuma sun sata agaba suna faman dariya, murmushi yayi had'e da tak'ara sandarsa yana takowa a inda suke kamar irin shima abun yabashi dariya, ganin haka yasa gaba d'ayansu suma suka sake kece da wata dariyar, yana isowa bakin gadon Mahmud yaja baya yayinda papi ya d'a sandarsa ya dokawa Batool a gefen kafad'a  yana fad'in


"Malfar iyayenku, kunjimun shashashun yara, babyn ku keyiwa haka, yau duk sai kunci k'wakwarku agidan nan" zagayen d'akin suka farayi da gudu suna dariya shikuma yana binsu don yabugesu, ya matuk'ar shan wahala bai kama ko d'ayan suba saida Mahmud ya rik'e masa Batool a bayanta ya doka mata sandar tayi tsalle tabar d'akin aguje dama tuni su Bassam suka samu damar bud'esa suka fece Mahmud nata yimasu dariya



"Kun ganemun ja'iran yara daga zuwa suna neman tayar mani da hankalina dana baby"


"Yihak'uri papi kaga harma babyn taka tariga da tashi" Mahmud ne yafad'i haka had'e dayi masa nuni da gefen da hajia kaka ke neman saukowa daga kan gado, juyowa papi yayi yana murmushi tare da takowa har inda take


"Baby kikoma kikwanta, nizan tsareki babu wanda zai dawowa anan har sai kingama baccinki" cikin muryar da zata tabbatar maka da cewa tabbas hajia kaka bata yau bace tace


"Inaaa, ai wannan bacci bazai yuyu yanzuba tunda suka iso, kuka tafashe dashi tana fad'in ina baccina mai dad'i suka tadani" wurinta Mahmud ya k'araso cike da ladabi yana gaisheta, saida ta amsa sannan tak'olomasa idanuwa had'e da rik'e masa kwalar riga,


"Kagansu nan haddashi aka tadani bacci da kuma ja'irar amaryar nan taka"


"A'a baby wannan fa mommodi d'inkine , Sam shibaya cikinsu Batulu dai ce da k'annenta su Bassam da Bilal"


"Haba kakaa! To kicikamun riga tunda kinji bana daga cikin su, irin wannan cacuma haka sai kace kura tasamu nama adawa" gaba d'aya suka kwashe da dariya tana mai shafa gefen fuskarsa had'e da sanya masa albarka, saida suka sake gaisawa sosai cikin kamala tare da ajiye wasar jika da kakanni a gefe suka fara zayyano masa matsalolin mahaifiyarsa da dady ya fad'amasu, ko kad'an baiyi musun abu d'aya daga cikiba kuma ya tabbatar masu da faruwar hakan saidai shi baisan ya zaiyi da mom tafahimcesa ba shiyasa yakasa kawo k'arshen matsalolin, shiru hajia kaka tayi kafin tajuyo ta rik'e hannun papi tana kallonsa,


"Wlh ni har tsoro yarinyar nan take bani, bansan a ina takoyo wannan zazzafan kishi haka ba, ta isko matar nan agidanta tabi tahanata sakewa ita da yaranta don tsabar mugun hali, kadubi yanda yaronta yafita hankali.." 


Cikin kuka tak'arasa maganar had'e da fad'awa ajikin papi, bubbuga bayanta ya dingayi yana bata hak'uri tare da nemawa 'yar tasu shiriyar Allah, Mahmud dake gefen su zaune yashiga tunani tare da lalubo kota ina mom d'insa tasamo halinta amma ya gagara samu, muryar hajia kaka yaji tana fad'in,


"Kahutar da kanka maigidana ni kaina nayita wannan tunanin amma bansamo amsar tambayar ba, haline kawai Allah ya halicceta dashi, saboda haka sai kuyita hak'uri kuna lurar da ita har Allah yasa tagane"


A b'angaren mom kuwa Basmah tasa agaba tana tambayarta abunda ke faruwa acikin gidan hadda tambayoyin da basu kamata ba tayi mata ba, ita kuma ta daddage tanata bata labarin k'arya da gaskiya, hadda cewa ai agabansu idan dady yadawo Ummi ke rungumesa ko kunyarsu bataji, shikuma yata biye mata ko damuwa dasu dake yimasa sannu da zuwa bayayi, gaba d'ai yanzu babu ruwansa dasu saidai Ummi da yaranta, wani zubinma fita yawo sukeyi a mota sukuma abarsu agida bazasu dawo ba sai kusan sha biyun dare" muryar Batool suka jiyo abakin k'ofa tana fad'in,


"Laa ilaha illallahu, kai yayya Basmah kiji tsoron Allah, kefa ba agidan kike kwana ba balle wuni taya akayi kikasan haka, wlh Allah mom kada kiyarda da zancenta k'arya takeyi" yatsine fuska mom tayi had'e da d'agawa Batool hannu alamun tazo, tana zuwa takama kunnenta ta murd'e sosai cikin fad'a tace


"Kina nufin Auntyn takice ke k'arya? Wannan abun data fad'a tabbas yafaru da basuyi ba taya zata gani harta fad'a inbanda rashin sanin ciwon kai irin na dadynku da rashin kunya agaban 'ya'yansa zai zauna yana wud'annan abubuwa ko kunyar Allah basaji" cikin dask'ararriyar muryar dake neman saka Batool kuka saboda rad'ad'i da zafi da kunnenta da mom ta rik'e keyi tace


"Kada kiyarda da kalaman yayya Basmah, wallahi mom ba gaskiya tafad'a makiba, kuma idanma hakanne meye laifi aciki Ummi fa matar sace duk abunda suka aikata a tsakaninsu ko agaban waye har ga Allah basada laifi, meye wani abun aciki da za'ace ko kunyar Allah bayaji, bakiga yanda indiyawa, turawa harma da larabawa keyin abunda yafi runguma agaban 'ya'yansu ba, yin hakan samfa ba laifi bane soyayyace.." Buge bakinta mom tayi cikin zafin rai tana cewa


"Rufemun baki samnar yarinya, kice kema Aisha ta b'ata mani rayuwarki ta asirce manike kamar yanda tayiwa yayanki, asheko tajawowa kanta dala ba ganwo" mere baki Basmah tayi tana kallon Batool


"Kinji ko mom, ai dama nafad'a maki Ummi gaba d'aya gidan yanzu juyashi takeyi babu mai girgiza mata ko ganin laifinta, tazubawa kowa a abinci ya cinye sai yanda tayi dashi" fitina mom tafarayi da maseefar don mema dady ya d'aukar mata 'ya'ya yabawa Ummi gashinan yaja mata suna neman lalace mata to wlh ita bazata yaddaba dole yamaido mata yaranta ahannunta sannan tafice tabar d'akin har lokacin tanaci gaba da banbami, kallon Basmah Batool tayi cike da jin haushinta tace


"Yayya Basmah shikenan kinyi farinciki ganin yanayin da mom tashiga?, shin meye ribarki acikin wannan k'aryar da kika shimfid'a?, meye Ummi takeyi maki datayi deserving all dis from you? Saida ta tashi daga inda take zaune sannan tace


"Banida lokacin amsa wud'annan tambayoyinki domin inada abinyi"


"A'a yayya kidawoma hanyar gaskiya domin ad'an zaman da nayi da Ummi na fahimci cewa tanada kyakkyawar manufa akanmu"


"And so what? Wannan fa duka munafuccine, taya zata nufi alkhairi damu bacin bata k'aunar mahaifiyarmu tana nema tarabata da dady"


"Baki fahimta bane yayya kyawawan halayentane ke neman fifita akan na mom awurinsa amma ba rabasu take son yiba, duk da mom mahaifiyar muce kidubi gaba d'aya yanda tafiye son kanta da yawa, wlh da Ummi fitinanniyace mai biyewa kausasan kalaman da mom keyi mata da tuni gidammu ya watse gaba d'aya, kuma bazata tab'a yadda tazauna damu ba har tabamu kulawar da itakanta mom saida taga canji ajikin mu, don Allah yayya Basmah kifito gurb'atacciyar duniyar da muke ciki kifahimci gaskiya" 


"Mtssssss...am tired of ur noise, kirik'e gaskiyarki" Basmah tafad'a tare da ficewarta, wani irin dogon iska Batool tafitar had'e da cewa


"Allah kaganar da mom d'inmu da kuma yayya Basmah, nikam nagane sharrin da zuciya keyi mani domin itama Ummi uwace agareni, su Billy kuwa tabbas 'YAN UWANA NE na jini kuma makusanta, tun ranar da Yaya yaganni zaune ina kuka akan Ummi tayi mani fad'an yin sallah akan lokaci ina ganin kamar tana takura mani ne yalurar dani cewa don tana sona yasa tayimun fad'a bawai takuranine take yiba yayita yimun nasiha nafahimci cewa Ummi alkhairi ce arayuwarmu amma kash duk da haka har yanzu yayya Basmah takasa gano hakan,


 

A asibiti kuwa Ummi ce zaune bakin gadon da Bilkisu ke kwance tana faman bacci hankali akwance bayan sun dawo daga wajen scanning ta rabka tagumi hawaye na zubar mata a idanuwa akan halin da take ciki na matsalar abokiyar zamanta gashi har yakai ga 'yarta  nason itama tadinga yimata rashin mutunci, izuwa yanzu tafara tsorata da alamurran Basmah yanda take nunawa tamkar itace kishiyar tata, itakam ko kad'an bazata iya cigaba da zama da itaba gwanda dady yaje ya dawo da mom d'insu hakan zai fimata kwanciyar hankali, a hankali Bilkisu tabud'e idanuwanta akan fuskar Ummi da hawaye suka yimata kwance akai, firgigit ta tashi zaune don gasgata abunda tagani, yatsa tasa ta lakuto hawayen sannan ta kalli Ummi


"Ya salam! Umminah kuka kikeyi?, miyafaru dake?" Batare da tace mata komai ba tajawota ajikinta tarungume 


"Ba komai Bilkisu amma ina so infad'a maki cewa aduk inda kika tsinci kanki ki kasance mai tsoron Allah a rayuwarki, ban yarda kicutawa matar mahaifin kiba domin itama uwace agareki, ban yarda kiguji 'ya'yanta ba komai rintsi komai wuya domin su 'yan uwanki ne, ina jin zafi sosai idan Basmah tayimun wasu abubuwan fiye da zafin da nakeji idan mahaifiyarta tayi mani, sau da dama akan yimaka abune idan kayi amma ni Allah shine sheda ban tab'a yiwa matan mahaifina rashin kunya ba balle hakan tafaru dani, amma nad'auki abun a matsayin jarabtani ne Allah keyi, don haka kigujewa aikata hakan gudun kema haka tafaru dake"


Hannu Billy tasa tagoge mata hawayen ta sannan tace 


"Zanyi yanda kikace Ummi, amma bazan samu damar aikata hakan ba matuk'ar zandinga ganin hawayen ki, hakan zaisa inji nayi loosing courage d'in yin hak'uri har inyi k'ok'arin kasa rama abunda akeyi maki"


"Bilkisu zuciya batada k'ashi fitar hawayen shike kashe rad'ad'in da nakeji a zuciya, amma ina tabbatar maki da babu komai duk abunda sukayi mana ko zasu yimana to nayafe masu fatana dukkaninmu Allah ya ganar damu kuma ya d'oramu akan gaskiya"


"Amin Ummi, yanzu yaushe zasu bamu sallama? Allah ni nagaji da kwancin asibitin nan" takardar sallama da akaba Ummi tajawo acikin jikkarta ta mik'a mata


"Nakira dadynki na sanar dashi, yanzu yayanki muke jira yadawo, amma sunce banda gobe mudawo karb'ar result"

















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_A rayuwar kowane mutum yanada wahala yamanta da mutane masu tarin d'inbin alkhairi acikin ta da kuma alamurransa😍 to nima kamar hakane awurina, dukkanin mataki da cigaban da zan samu arayuwata bazan tab'a mantawa da irin k'warin guiwar da akoda yaushe nake samu daga wajen ki ba *AUNTY MAIJIDDA MUSA* fatana Allah ya dawwamar da amincinsa acikin rayuwar aurenki, yaraya maki zuriarki ya albarkaceta sannan yayi maku kyakkyawan sakamako da aljannah fiddausi bi gairi hisabin wala ik'abin👏🏻ina mik'o gaisuwa mai tarin yawa da kuma jinjinata agareki Allah yabar tare🤝 much luv aunty mj😍_


💎Page_____19💎



 Shikenan Ummi bari nafara harhad'a kayanmu kafin su dawo, sister faraaha ce tashigo cikin d'akin fuskarta ba yabo ba fallasa cikin sauri Billy ta ajiye blanket d'in dake hannunta tana ninkewa ta rungume faraaha


"Congratulate me sis anbamu sallama yau zanje gida, missing home  sosai wlh" murmushi tayi had'e da rik'o hannunta suka dawo inda Ummi take "Ummi kinga lil sis d'in Yaya Mahmud sai farinciki takeyi tunda tayi nasarar tirsasani anbata sallama" tana kallon Billy take maganar, zaro ido Ummi tayi


"Faraaha dama had'a baki kukayi aka sallameta lokaci beyi"


"A'a naga mutuniyar tawa tagaji da zaman kuma gashi result ne kad'ai zai zaunar daku na tsawon kwana biyu shiyasa kawai naga bari ayi hakan, inyaso bayan kwana biyun idan yafito saiku dawo saboda ina tsoron tayi mana absconding" tak'arasa maganar tana dariya, girgiza kai Ummi tayi tana murmushin irin wayon yaran zamani shine Bilkisu tayi mata kamar batasan da maganar ba hartana tambayar ko anbasu sallama, kai yara Allah dai ya shirya mana tafad'a cikin zuciya, kallon Billy faraaha tayi cikin damuwa tace


"Sisto bakida kirki k'irik'iri kike nunamun farincikin ki zaki tafi gida abunki batare da ko irin zakiyi missing d'ina ba" 


"Kai aunty faraaha zaman asibitinne babu dad'i ko kad'an kinga kuwa dole inyi farinciki da samun sallama kuma kema kinsan ko ban fad'a ba zanyi kewarki sosai"


"Hmmm kamar da gaske"


"Aikuwa dagaske nakeyi, Ummi aramun wayarki na copy number ta aciki don ta tabbatar" mik'amata wayar Ummi tayi tana fad'in


"Maza ki kwafa kibani ink'arasa azkar d'in kafin magrib tayi na manto da hisnil Muslim d'ina agida" da sauri ta fad'a mata digit d'in tayi copy akan wayar sannan tafita d'akin saboda akwai statement d'in da take son cikawa ita kuma tamik'awa Ummi wayar sannan taci gaba da shirya masu kayansu.


Cikin b'acin rai mom ta sauko k'asa tare da nufar d'akin papi saida tayi knocking sau uku sannan aka bata izinin shigowa, yanayin da sukaga tashigo ya tabbatar masu da akwai abunda yafaru, d'aure fuska sosai papi yayi sannan yayi mata nuni da tazauna akan kujerar dake acan gefen wardrobe, anyi kusan mintuna biyar yana kallonta kafin can yace da ita


"Lafiya kuwa"


"A'a papi maganar gaskiya da akwai matsala" tashi Mahmud dake zaune agefen hajiya kaka yayi daniyar fita papi dake k'ok'arin gyara zamansa akan gado don sauraren abunda tazo dashi yace masa ya koma ya zauna,


"Inajinki meke faruwa ne?"


"Papi nidai so nake kayiwa dadyn yarannan magana ya maido mani da yarana hannuna bana buk'atar suzauna tare dashi ab'ata masu tarbiya" ba papi ba hatta hajia kaka da Mahmud saida suka zaro idanu had'e da bud'e baki suna mamakin kalaman dake fita abakin mom, kallonta papi yayi yana dariyar Ikon Allah sannan yace


"Meye dalilinki da kuma hujjarki akan abunda kika fad'a" aikuwa kamar jira mom keyi tabud'e baki bakunya ta zayyane masu duk abunda Basmah tafad'a mata k'arya da gaskiya kumafa papi inba son ab'ata yara ba har rungume rungume sukeyi agaban yaran, ni dai..." Katseta yayi cikin b'acin rai "ubangiji Allah ya rabaki da wahala Hussaina, yanzu meye amfanin wud'annan maganganu da kike fad'a agaban yaronki?,"


"Saboda suma hujja papi.."


"Rufamun bakinki, tir da yawanki ai wannan ba hujja bace shirmene, atafi suna aikata hakan shin haramunne? Sannan wayakai idanun yaran harsukai ga gano abunda bai shafesu ba"


"Papi kafahimta mana, agaban su akeyi"


"Mtsssss..wannan shi ake kira da bakin wahala, duk da banda tabbas akan abunda kefa ruwa yallab'ai natabbata wlh k'aryane hakan bai faruba don yanda nalura da halin hajia Aisha da shikansa maigidan nasu bazasu tab'a aikata hakan ba wlh, wannan duk k'ullalliyar yaran tane da gurb'atawa tunani ta b'ata masu tarbiya" hajia kakace ke fad'ar wannan maganar cikin fushi tare da b'acin rai, Mahmud dake zaune ya sadda kansa k'asa tunda mom tafara magana yace


"Mom wlh kiyarda dani wannan magana ba haka takeba, taya Ummi tasamu aikata duk wud'annan abubuwa ita da kullum cikin aikin kulamaki da yaranki take itada ko yaushe tana hanyar zuwa asibiti wurin jinyar 'yarta, na tabbata wannan matsalar Basmah ce tahaifar da ita, to bari kiji gaskiya mom ita kanta Basmah a asibiti take kwana, saida safe idan naje ita kuma saita jegida tayi wanka taci abinci lokacin Ummi tagama gyara komai sai sudawo tare kuma lokacin dady baya gida shin taya za'ayi tasan abunda yake faruwa, kiyi tunanin wannan maganar mom"


"Rufamun bakinka dama nasan kai bazaka yadda ba tunda ko yaushe bayanta kakebi tariga ta gama da kai da mahaifin naka" murmushin takaici papi yayi yana kallonta yace


"Tabbas muma d'in bamu yadda ba sannan kafin inrufe idona in bud'e inaso kibar d'akin nan shashashar banza da batasan ciwon kanta ba, inyaso muma d'in kice tagama damu kinji ko?"


Sumui sumui mom tabar falon zuciyarta na zafi da k'una akan rashin samun goyon bayan iyayenta aranta takai k'arshe akan cewa daga wannan karon bazata koma k'unsar bak'in cikin Aisha ba dolene bak'in yanayi ya juya akanta.


Tana fita papi ya kalli Mahmud dake kuka yace


"Kayi hak'uri kaima jarabawa ce Allah yayi maka da mahaifiya mai murd'ad'd'en hali kamar yanda muma ya jarabcemu da ita amatsayin 'ya" shafa kansa yayi tare da cigaba da lallashinsa har saida yaga yayi shiru sannan ya cigaba da cewa


"Dama Bilkisu bata da lafiya shine baka sanar damu ba kuma shima dadyn naku koda mukeyi magana dashi bai fad'a manaba abu har ankai ga kwanci asibiti gaskiya duk kanku baku kyautaba"


"Papi ni nazata tunda kunyi magana dashi yafad'a maku abunda kefaruwa" nan Mahmud ya zayyane masu duk abunda yafaru ranar da silar kwanciyar Bilkisu a asibiti, "Allah sarki Mahmud mahaifinka mutumne nagari, wlh gaba d'aya bai fad'a mana wannan maganarba amatsayin abunda yasa yace ummanka tayo gida, sab'anin da ya had'asu har takai ga sheganta masa 'ya'ya don banata bane shi kad'ai yafad'a mana, ya Allah kishirya mana wannan yarinya, gaskiya bata kyautaba ko kad'an kuma tayi kuskure sosai"


Shiru Mahmud yayi yana mamakin hali irin na mahaifinsa, tabbas duk hak'urinsa dole ya hukunta mom akan wannan abunda tayi masa,


Sunjima suna tattaunawa akan matsalolin mom tare da baiwa Mahmud shawarwarin yanda zai dinga lurar da ita, daga k'arshe papi ya tabbatarwa da Mahmud insha Allah gobe zasuzo suduba Bilkisu da jiki kuma yabawa dady hak'uri kafin suzo yafad'a masa basusun cewa Bilkisu batada lpy ba sai yau daya fad'a masu, sannan kafin sutafi ya kira Basmah da Batool yayi masu fad'a sosai tare da nuna masu suso 'yan uwansu domin ita duniya batada tabbas, babu yanda mom batayi ba don tasake keb'ewa da Basmah amma da hajia kaka talura da haka ta kasa ta tsare afalo har saida taga sunbar gidan sannan itama tanufi hanyar bedroom d'in papi ta d'ibo masa ruwa abuta saboda sallar magrib data gabato kuma dama shi bayason yin arwala a toilet yafiso yayi ta awaje hakan yafi sama masa natsuwa,


Ana kiraye kirayen sallar magrib suka isa asibiti don haka Ummi tace yaje yayo sallah kafin nan suma sunyi sannan sai suwuce, 


Bayan sun iso gida yana yin parking da mota Billy tafito aguje tana fad'in.


"Home sweet home, missing u so much" tana maganar tana bud'e hannayenta asama tare da shak'ar iskan dake kad'awa, hasken fitillun dake zagaye da bangon gidan su suka taimakawa Mahmud wajen hango farincikin dake shimfid'e a fuskarta, dariya yayi tare da fad'in


"She's always different, dt's my lil sister" 


Gaba d'ayansu part d'in Ummi suka nufa agajiye kowanensu yazube akan kujera ita kuma direct d'akinta ta nufa cikin zumud'i tana shiga taci karo da manyan akwatuna guda biyu wanda kemata nuni da anan 'yan uwanta suke zaune, ko kad'an ranta bai b'aciba ta wuce toilet ta watso ruwa, wardrobe d'in kayanta tabud'a suna nan kamar yanda tabarsu agyare, taciro wata doguwar riga ta material amma cotton anyi mata d'inkin nan da ake kira A-shape ko kad'an yadin bayada nauyi kalar baby pink da touch d'in royal blue ta saka ajikinta sannan takoma falo anan inda tabarsu suna nan zaune abunsu kowa na harkar gabanshi, ita kuma Ummi tana kitchen tana tanadar masu abunda zasuci marar nauyi, Bilal da bassam kuwa tuni har sunyi bacci,


Kitchen d'in itama tanufa ta samu Ummi tasa dafuwar macaroni tana hik'ar arish, hannu ta mik'a da niyar karb'a Ummi tace


"A'a Bilkisu jeki kihuta"


"Kai Ummi wane irin hutu zanyi tunda nasamu sauki" 


"Allah dai yak'ara sauk'i, ungo to bari nad'ora dafuwar k'wai kafin ki k'arasa fek'ewar"


Billy bata jima da wucewa kitchen ba itama Batool tabi bayanta, tana shiga tace 


"Ummi sannu da aiki, me za'a rik'a?" Saida Ummi tayi murmushin jin dad'i sannan tace


"Ai da kinbarshi batool kije kihuta, kuda kukasha tafiya"


"Lahhh bakomai wlh idan har Billy da batada lafiya zata iya aiki to mezai hana nima inyi Ummi?"


"Kai yayya Batool nifa na warke don bana tunanin zaki fini lafiya yanzu" dariya Ummi tayi


"To nidai bana son musu ungo nan kihad'a waccan stew d'in dana d'ora yanzu ga mai nan da nik'akkin kayan miya bari ni naje nawatso ruwa 'ya'yan albarka" har Ummi takusan fita Batool ta Sosa k'eyar kanta had'e da d'an yatsina fuska tace


"Ummi a gaskiya ban iyaba" shiru ummi tayi fad'an lokaci tana mamakin yanda kamar Batool ace bata iya had'a stew ba, murmushi tayi sannan tadawo cikin natsuwa ta dinga nunawa Batool yanda ake had'awa har suka kammala cike da jin kunya tayiwa Ummi godiya, shafa kanta tayi tace ba damuwa kijira ta ida nina sai ki kwashe a cikin waccan warmer d'in ke kuma Bilkisu kitsane macaronin da arish shikuma kwan kiyankashi shape d'in ball kamar yanda kika yiwa arish d'in saiki saka a wannan bowl d'in ku gyara kitchen d'in kafin nafito,


Kallon Basmah dake latsar waya Mahmud yayi sannan yace


"Ke bazaki tashi kije kuyi aikin ba"


"Bacci nakeji" 


"Ohh! Bacci kikeji amma kike latsar waya, zaki tashi kitafine kosai na mammakeki awurin?" Cikin b'acin rai ta tashi tanufi kitchen d'in har lokacin tana latsar wayarta wanda hakan yasa da kad'an ta bangaje Ummi dake k'ok'arin fitowa, jabaya tayi Ummi ta wuce abunta batare da ko kallonta tayi ba, mere baki tayi sannan ta lek'a kitchen d'in 


"Hi gusz abincin ya nina ne?" Kad'a mata kai Billy tayi tana murmushin da baikai ciki ba tace "eh yayya Basmah" ita kuwa Batool ko kallonta batayi ba taci gaba da aikin gabanta,


"Ke Billy ki kawomun nawa afalo don yunwa nakeji" tana gama fad'a tawuce abinta


To Billy tace tare da d'aukar d'aya daga cikin plates d'in dake sagale ajikin kitchenware Batool tayi saurin rik'e mata hannu


"Stop it Billy wlh Allah baza'a zuba matashi ba sai Ummi tafito, wannan ai rainin hankali ne..

















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____20💎



 Saida suka gyara kitchen d'in sannan suka kwashe kayan abincin suka jerikke akan dining table suka dawo falon suka tada Bassam da Bilal dake bacci suka wanko masu bakinsu sannan suka dawo falo suka zauna suna jiran fitowar Ummi, dady suka gani ya turo k'ofar falon bakinsa d'auke da sallama, da gudu su Bilal sukaje wurin sa suna oyoyo dady, ciki hanzari Mahmud ya tashi ya karb'i jakar hannunsa yana fad'in


"Sannu da dawowa dady"

 

"Yawwa Mahmud kun dawo?"


"Eh dady su papi na gaishesheka sosai" k'arasowa daga cikin falon yayi d'auke da Bilal d'ayan hannunsa kuma rik'e da hannun Bassam, kamar 'yan matan sun had'a baki gaba d'ayansu suka yimasa sannu da zuwa atare cikin girmamawa, cikin zolaya da barkwanci dady yace


"Yawwa 'yan matana, Basmah shin ko kin gano min Batool da Bilkisu" gaba d'ayansu sukayi dariya Mahmud na fad'in


"To gadai Batool nan a zaune dady amma Billy ina tunanin munbarota asibiti.." Kafin yarufe  baki cikin shagwab'a Billy tace


"Ehnm..ehnm kai yaya bagani anan zaune ba, ni kadena yimun fatan zaman asibiti banaso" dariya dady yayi had'e da k'ok'arin wucewa bedroom d'in Ummi sai gashi tafito cikin riga da plane zane na atamfa super England ash and maroon colour tayi matuk'ar kyau sosai sai k'amshi takeyi, sannu da zuwa tayi masa sannan takarbi Bilal dake hannunsa cikin lowering voice tace


"Yallab'ai ko zaka fara da abinci kafin wanka naga kamar yaranka yunwa sukeji" batare daya tanka mataba ya kashe mata idonsa d'aya sannan ya nufi gefen da dining table yake, murmushi tayi don tafahimci abunda yake nufi sannan ta juya tana kallonsu 


"Babanah kutaso kuyi dinner ko?"


"To Ummi sannu da k'ok'ari"


"Yaukam ai k'ok'arin na k'annen kane saboda haka kataso ka kwashi Batool delicious ko Batool?" Sosai suka shiga yin dariya har da dady dake can zaune shida su Bassam inbanda Basmah da ta kalli Ummi da gefen ijiya sannan ta mere baki, Mahmud ne ya tsaida dariyarsa yana fad'in


"Kai Ummi wannan irin kambamawa haka wai Batool delicious inama laifin kice Billy delicious don indai batool ce nasan bata iya komai ba"


"Lallai yaya aikuwa yau zakasha mamaki domin d'and'anon girkin natane," Billy ce tafad'i haka tare da rik'o hannun Batool data turo baki jin abunda yafad'a, murmushi Ummi tayi ta rungumota ajiki suka nufi dining table yana biye dasu Ummi tace


"Fita batun yaya ko yayi aure bazakije gidan saba balle yasa ran zakiyi masu girki" 


Bayan kowa ya zauna Mahmud ya juyo yana kallon Basmah dake kwancenta a inda take ko motsawa batayi ba yace


"Ke bazaki taso kici abincin bane?"


Juyowa tayi takallesa sannan ta sake maida idanuwanta tarufe, zuciyarta na rad'ad'i, muryar dady tajiyo again yana fad'in 


"Basmah meke faruwane da bazaki taso kici abinci ba?" 


"Dady tun d'azufa nakejin yunwa aka hanani" juyowa dady yayi yana kallon Ummi da itama ta d'ago kanta da k'arfi tana kallon Basmah cike da mamakin abunda tafad'a, shiru dady yayi tare da ajiye cokalin abincin dake hannunsa, Batool da tun d'azu maida hankalinta ga cin abinci da takeyi ta d'ago kanta ahankali tana kallon Dady da Ummi tacire hannunta daga abincin da yake ita batason cin abinci da spoon tace


"Dady Ummi, kufita batun yayya Basmah kuci abincinku, nice nan na hana Billy ta zuba mata abinci lokacin bamu ida kammalawa ba tazo tayi mana tsaye wai yunwa takeji, bacin tana zaune Ummi tashiga kitchen amma ta kasa tashi tarik'a mata aikin sedai mu damuke k'annenta mukaje, don haka idan zata taso taci abincin ta taso idan kuma bazata tasoba ita yunwa zata wahalar" tana gama maganar ta maida hankalinta ga cin abin cinta haka shima dady ya d'auki chokalinsa yaci gaba da cin abinci, Ummi ma haka, d'agowa Mahmud yayi saboda jin dad'in amsar da Batool tabaiwa dady bayan yakai lomar spoon abakinsa ya had'e 'yan yatsunsa biyu ya d'agawa Batool alamun girkin is so test sannan ya k'ara d'aga mata babban yatsansa alamar jinjina tayi daidai, wani irin takaicinsu ya rufe Basmah ta tashi da gudu tabar fallon tana kuka, kamar dady da mom sun had'a baki atare sukace


"Allah ya shirya" gaba d'ayansu suka amsa da amin.


Kwance mom take tana juye juye akan gado tarasa meke yimata dad'i a rayuwarta, ba abunda take da buk'ata aduniya irin kota halin k'ak'a taga ta salwanta rayuwar Aisha data zuriarta, wayar tace tayi k'ara tajawo had'e da karawa akunne, hello suka fad'a atare ita da wacce takirata,


"Hello, hajiya kilishi"


"Na'am mutuniyata kar dai ince har kingane muryata"


"Sosai kuwa bagashi kin gani ba, ya ake cikine"


"Daidai wlh..alhajinki yazo biko kuwa?"


"Hmm bari kawai hajia kilishi ina cikin matsala wlh har yanzu banga k'afarsa ba, ke inma tak'aice maki koga waya bai nemeni ba"


"Tafd'i jam shine kuma kike zaune abunki hankali kwance!? Yo ai bakiga tazama ba don anriga ankautar masa da hankali akanki bakya gabansa"


"Nasani hajia kilishi yanzu haka tunanin da nakeyi kenan akan yanda zanb'ullowa al-amarin, ina mafita yanzu?" Wani irin shu'umin murmushi tayi aranta tana fad'in anzo wajen!!!


"To kibari har insamu dama zan shigo sai muyi magana, ya papi da hajia kaka lpy suke? Saboda nakwan biyu ban kirasu awaya ba"


"Eh lpynsu klw wlh"


"Kigaishe dasu kafin inzo"


"Zasuji insha Allah" daga haka suka d'an tab'a hira sannan sukayi saida safe, tana gama waya da hajiya kilishi saiga kiran Basmah yashigo awayarta, dasauri ta d'aga wayar had'e da cewa "hello Basmah" cikin muryar kuka ta amsa da "hello mom, don Allah kibawa dady hak'uri kidawo, ni bazan iya zama gidannan ba idan bakya nan" 


"Me akayi ne Basmah, kiyimun bayani duk kintayar mani da hankali" nan tafad'a mata k'arya da gaskiya tak'ara da cewa hatta Batool yanzu anhure mata kunnuwa rashin kunya take yimata, iya k'ololuwar b'acin rai mom takai tace 


"Shikenan kyalesu duk saina ganar dasu kurensu, yanzu inashi yayan naki?"


"Yana d'akinsa"


"OK inazuwa" katse wayar tayi takira lambarsa lokacin yana k'ok'arin kwantawa, cikin girmamawa ya d'aga wayar


"Assalamu alaikum, mom..."


"Maza karufemun baki, wato don kana samna za'a tozarta 'yar uwarka agaban idanuwanka kayi shiru, to yanzu da aka hanata abinci da yunwa kake so takwana?"


"Mom metace maki anyi mata?, ya za'ayi a hanata abinci haba mom meyasa bazaki fahimci matsalolin Basmah ba"


"Ni bana son jin komai daga gareka maza kaje ka d'ibi abinci ka kaimata idan kuma babu kafita kayo mata take away"


"Haba mom dubafa kigani pass 11:00 yanzu ina zanje in nemo mata abinci" cikin b'acin rai tafara yimasa fad'a


"To idan bazakaje ba, bari ni infita insiyo mata sai kazo bakin gate ka karb'a ka bata tunda ni ban isa gareka ba"


"A'a mom kiyi hakuri zanje Allah ya huci zuciyarki" suna gama wayar yaciro doguwar jalabiyarsa dake sagale a jikin hanger, d'akin yarufe ya nufi part d'in Ummi, yana shiga ya k'wallawa Batool kira, cikin gigin baccin daya soma d'au karta tafito tana fad'in


"Yaya lpy?"


"Lpy klw akwai sauran abinci"


"Eh amma Ummi ta sakasa a fridge don karya lalace"


"OK shikenan zaki iya tafiya ki kirawomun Basmah"


Kai tsaye yanufi wajen fridge ya d'oko abincin sannan ya shiga kitchen ya d'oko plate ya yad'ibi abincin har saida plate d'in yayi soro yazuba stew asama sannan ya maida kingin acikin fridge, fitowa tayi da rigar bacci ajikinta earpiece lak'e akunnuwanta tace


"Yaya gani" kallonta yayi daga sama har k'asa kasancewar rigar nada d'an kabri kuma ta gota guiwowinta shiyasa bai yimata fad'a ba


"Zauna ga abinci kici" kasancewar tanajin yunwa girman kai yahanata zuwa tad'iba taci yasa tazauna batare data yimasa musu ba tafara cin abincin shikuma yadawo agabanta ya zauna kai hannunta keda wuya taji abincin da mugun sanyi ai kuwa tab'ata fuska tare da cire hannu tana kallonsa


"Ni bazanci wannan abincin ba yayi sanyi da yawa" wata irin muguwar harara ya jefamata had'e da cewa


"Ai wlh sai kin cinyesa tas, ba yunwa kike jiba, yau senayi maganinki intak'amarki rashin kunya" adole yatasa ta agaba tanaci tana kuka gashi babu damar d'aga waya balle takira mom......





















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

 

_Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar alkhairi marar misaltuwa agareku 'yan group d'in *BILLY S FARI NVLS GROUP* u people are always made me happy especially you guyz AFRAH, MAMAN ABBULKHAIR, AISHA ABUBAKAR, SADIYA SANEE, MMN HANAN, MMN IHSAN dama sauran wud'an da ban ambata ba sincerely inajin dad'in yanda kuke zuba mun ruwan comment domin hakan na k'aramin k'warin guiwa sosai, ngd ubangiji Allah yabaku farinciki mai d'orewa duniya da lahira👏🏻 luv u more than how word can say❤stay bless🤝_


💎Page_____21💎


 Tun tana kukan a hankali har takoma yinsa sosai tana fad'in "yaya nak'oshi", ko kad'an kukanta bai dame saba balle ya saurari abunda take fad'a sai ma cigaba da dannar wayarsa da yakeyi, saida ta cinye abincin nan tas saiga kiran mom awaya ya shigo a wayarsa, murmushi yayi had'e da d'aga wayar,


"Mom bakiyi bacci bane?"


"Kaji shashanci! Taya zan iya bacci 'yatah najin yunwa bataci abinci komai ba, kasan Allah kashiga taitayinka don naga baka damu da 'yan uwan kaba" sai da ya harareta ta gefen ido sannan ya danna hands free d'in wayar yana dariyar k'eta,


"Tuba nakeyi mom, ki kwantar da hankalinki ganinan tare da 'yarki nabata abinci kuma saida na tabbatar taci ta k'oshi, yanzu haka bakiga yanda cikinta yayi ba sai nishin kwad'd'i takeyi, ki kwanta kiyi baccinki cikin farinciki mom zan kula da 'yan uwana yanda ya kamata"


"Katabbata?"


"Sosai kuwa mom, sufa 'YAN UWANA NE taya za'ayi inbari su tozarta hakan bazai tab'a yuyuwaba min sha Allah"


"Yawwa my son haka nake son ji Allah yayi maka albarka"


"Amin mom seda safe" ya kashe wayar had'e da kallon gefen da Basmah take zaune har lokacin hawaye na zubar mata a idanuwa, baran ma dataji muryar mom da tasan zai shafa mata lafiya wlh anan zata k'arya tashi kuma tafad'iwa mom muguntar da yayi mata nasata cinye cikin plate d'in abinci da sanyin sa, 


"Maza ki d'auke plate d'in kikai kitchen and make sure gobe da sassafe na iskoki kitchen kinfara had'a breakfast kafin Ummi tafito kuma idan kin isa kikira mom kifad'a mata wlh in tattakaki agidan nan wawiya kawai" yajuya yabar falon yana mai addu'ar Allah ya shirya masa 'yar uwarsa dake nema tazame masu trouble maker acikin gida, yana fita ta turo baki had'e dasa hannuwa tagoge hawayen da suka zubo mata tana fad'in


"Wlh Allah ya isana, mugu kawai kuma bazan d'auke plate d'inba" had'e da shuresa gefe, dariya Batool dake lab'e a k'ofar d'akinsu tana sauraren duk abunda ke faruwa tayi sannan ta gyara muryarta tayanda zatayi irin ta yaya Mahmud tace


"Eyye..Kikace me?" Da sauri Basmah ta d'auke plate d'in takai kitchen tafito tana waige waigen inda zata hangosa tunda tasan yafita, shin kodai yaya Mahmud na ajikin k'ofa  ya lab'e da gudu tanufi d'akinsu don kar inyana kusa ya shigo ya mammaketa garin haka tayi karo da kujera tafad'i twuiii kakeji kamar ba jikin mutumba, dariya Batool ta tintsire da ita had'e da fitowa daga mab'uyarta rik'e da ciki tana cewa


"Gwai Allah yayya Basmah, bake rashin kunya ba? ai maganinki kenan!" Ta k'arasa maganar tanaci gaba da dariyarta hadda hawaye, matse fuska Basmah tayi kamar bataji zafin fad'uwar ba wai ita aunty bata son rainin Batool tace


"O.o.o ki kwantar da hankalinki bazan fad'awa kowa ba babu wanda yaganeki sai ni hattafa yaya Mahmud baiga komai ba don yariga daya tafiyarsa, muryar sama da kikaji nice nan na kwaikwaya, ba waike irin big girl d'in nan ba hadda wani yimasa Allah ya isa kuma bazaki d'auke plate d'in ba?, shine nikuma nayi maki haka,kuma sai nafad'a masa abunda kikace, wato yayan ne mugu ko? Tabbas saina fad'a masa" cikin fushi da b'acin rai had'i da rad'ad'in da takeji tayo kan Batool, da gudu tashige d'aki tana biye da ita idan tayi nan tayi can tana dariya, kan gado ta haye ta b'uya a bayan Billy da hayaniyarsu ta tada ita zaune a tsakiyar gado tana murzar idanu, kan gadon tahau tare da ture Billy gefe tayi kanta da duka, pillow ta dinga karawa ga duk naushin da zata kawo mata tana dariya, acan cikin pillow tasake lank'washe muryarta zuwa ta yqyq Mahmud tace


"Shin wai ke bazaki natsu bane Basmah?" da sauri taja baya da kad'an tafad'o daga kan gadon saboda yanda take tsoronsa, ba Basmah kad'ai ba duk wanda zaiji muryar zai d'auki Mahmud ne dama can muryar batool nashige da tasa sosai banbancin kawai tata tafi tasa sirantaka saboda ita macece shi kuma namiji, to idan ta d'an kaurara muryarta sai kaji tafito sak irin tasa, yanda ta razana ya k'arasa Batool dariya ita kuma ta gano still itace ba yaya Mahmud d'inba nan ta d'auki pillow itama tanata dukanta dashi  tun tana dariya har sai da tafara kuka sannan ta k'yaleta, tana nishi d'aya bayan d'aya tace "gobema kya k'arya", Cikin kuka Batool tace


"Muguwa kawai, wlh Allah ya isana banyafe ba, matsoraciyar banza" sake buga mata pillow tayi


"Wa kike cewa muguwa Allah ya isa?"


"Dake nake ai kamatu dini tadana" Billy dake zaune a k'asan gado tana kallonsu cikin yanayin baccin da takeji ta d'anyi murmushi gefen baki had'e da cewa


"Wlh yayya Basmah kundai shiga hakk'ina.." Kafin tarufe baki Batool tace


"Kema Allah ya idan maki" wata irin muguwar harara Basmah ta watsa mata sannan tajuyo tana kallon Billy


"Mtsss yo ai sai kizo kidakeni" sannan ta wuce toilet tana d'ingisa k'afa, gyara gadon daya cukuikuye Batool ta sakeyi sannan ta maido hankalinta ga Billy dake zaune tana gyan gyad'i tayi murmushi


"Ina ruwan hajia kaka, wannan da nikeyi da nace nayo gado kam sosai, ke Billy we're sorry taso ki kwanta" ganin kamar baccin yaci k'arfinta yasa tarik'ota ta kwantar da ita a tsakiyar gadon sannan itama ta koma bayanta takwanta, saida ta watso ruwa sosai ajikinta sannan tafito ta canza rigar bacci itama tahaye gadon ta kwanta daidai filin dake akwai a gaba lokacin kusan k'arfe d'aya da kwata 1:15am na dare


Duk da kasancewar basu kwanta da wuri ba jakan baisa Basmah ta manta da gargad'in da yaya Mahmud yayi mata ba, tana ida sallar asuba tanufi kitchen ita kuwa Batool takoma kan gado abunta ta kwanta, Billy kuma tazauna tana karanta azkar d'in safiya tana idawa tahau gyaran d'akin, kan gadon tahau tana fad'in


"Yayya Batool kitashi in gyara gadon kinga garin yafara haske"


"Ehmmmm..don Allah Billy ki kwanta kihuta mana" ta k'arasa maganar had'e da jawo Billy ta kwantar da ita "yawwa Billy i baccinki" tafad'a cikin muryar dake nuna alamun bacci takeji sosai, cikin jin dad'i da farincikin yau gata ga 'yar uwarta tana nuna mata soyayya tace


"Yayya Basmah Ummi fa batason baccin nan na bayan sallar asuba, shiya bana komawa idan naga azkar sai in cigaba da 'yan gyare-gyare da d'ora breakfast har sai rana tafito,


"Karki damu yau yayya basmah zata had'a mana breakfast"


"To bari naje nayi share-share da mopping idan yaso inkin tashi kya gyara gadon" k'ok'arin saukowa tayi daga gadon ta rik'e mata hannu "help me Billy in tashi in rik'a maki aikin" murmushi tayi had'e da jawo hannunta ita kuma ta biyota a hankali ta d'ora kanta akafad'arta, 


"Oh my God! Wake up yayya Batool kafin Ummi tashigo ta haumu da fad'a" d'ago fuskarta tayi tana kallon tata tace


"Billy am so sorry da yanda nayi treating d'inku a baya, na matuk'ar gano hakan ba daidai bane, nafahimci ku 'YAN UWANA NE kuma ina matuk'ar sonku" yatsanta tad'ora akan lab'b'anta


"Shiiiii...Yayya Batool! Babu komai a tsakaninmu yanzu, Allah ya gafarta mana zunubbanmu, dama kullum fatana shine naga 'yan uwana na sona kamar yanda nake sonsu" rungumeta tayi had'e da cewa


"Nagode sosai, amma zakiyi hak'uri da halin yayya Basmah ko? Bazaki d'auki fushi da itaba akan abubuwan da takeyi ko? Na d'aukar maki alk'awarin cewa da sannu itama zata gyara halinta in Allah ya yarda, zamu zamo kamar yanda yaya Mahmud keso muzama wato tsintsiya mad'aurinki d'aya"


"Sosai kuwa, Allah ya yadda" breaking hug d'in sukayi sannan suka hau gyara gadon, bayan sun ida suka cigaba da sauran gyare-gyaren gidan. 


Koda Basmah tashiga kitchen tsaye tayi takasa gano abinda ya kamata tad'ora kamar ance ta juya gefen fridge d'in dake bakin k'ofar shigowa kitchen d'in ta hango wata takarda mak'ale ajikin bango wacce ko baka tambaya ba kasan time table d'in abunda yakamata adinga cine kullum ajikinta saboda komai na Ummi a tsare yake kuma tana aiki da planning, mere baki tayi had'e da duba takardar taga yau Wednesday za'aci yam balls da kunun gyad'a da kuma farfesun kifi, rik'e k'ugu tayi had'e da cewa "Tab wlh akwai aiki kuwa breakfast d'in har sai anyi kusan girki kala uku sai kace restaurant" itakam gaskiya bata iya komai daga cikin su ba, kuma bazata iya tambayar Billy ba tare nata, don haka tanemi tukwanenta guda uku duk ta cikasu da ruwa ta d'ora akan gas tasamu wuri abunta tazauna, k'arfe shidda da rabi sai ga yaya Mahmud ya shigo, kitchen d'in yafara lek'awa ya hango Basmah zaune ta k'urawa tukanen ido kai kace wani abun kirki ta d'ora take jiran ya nina, gyaran murya yayi da sauri tamik'e tsaye,


"Morning yaya Mahmud" k'ura mata idanu yayi yana son gano wani abu ganin yanda tayi fik'i-fik'i da idanuwa tana wani nonnoce kai k'asa yace


"Lpy klw ai nazata zan iskoki kina vaccine"


"A'a gashima har na d'ora"


"Gud girl" yafad'a sannan yabar wajen, murmushi tayi had'e da cewa


"Hmmm gud girl ko? zako kuga gud girl wlh donni ba abunda na iya acikin abunda za'ayi breakfast dashi yau"


Ummice tsaye agaban wardrobe d'in dake lak'e ajikin bangon d'akin dady tana gyara masa kayansa bacin sun gamo sallar asuba shikuma yana cikeciken wasu document a laptop d'insa, gyaran murya tayi lokacin da take ninke wata T-shirt tace


"Dadyn yara ina son muyi wata magana idan har ba damuwa"


"To madam ina saurarenki," yafad'a har lokacin hankalinsa na akan aikin da yakeyi


"Da zaka bani aron wasu mintoto daga cikin lokacinka da zaifi, amma idan aikin da kakeyi urgent ne sai inbari sai wani lokacin" saida yayi saving rubutun da yakeyi a laptop d'in sannan ya rufe yajuyo yana kallonta,


"Gani ranki shidad'e ba lokacina kad'ai ba har ni kaina gashi kinsamu, kiyi maganar ki ina sauraren ki natabbata zanyi maki kyakkyawar fahimta aciki"


"Godiya nakeyi, Allah yak'ara d'aukaka mana kai" shiru tad'anyi sannan tace dama akan maganar hajia Hussaina ne, duk daba hurumina bane ina so inbaka hak'uri da kaje kayo bikon matarka don Allah, ka tausayawa yarannan ko donsu kaje kadawo da ita, bai kamata ace cikakken magidanci irinkaba ace yasamu tauyuwar ladarsa tahanyar rashin d'ayar matarsa akusa dashi ba, kayi hak'uri shi Allah yana son mutane masu hak'uri da kuma kyautatawa" cike da mamakin kyakkyawar zuciya irin ta Aisha da kuma yanda ta iya sarrafa harshenta wajen furta kyakkyawan kalaman da zasu lank'wasa zuciyar mutum tayi sanyi yace


"Aisha me yarannan suka rasa da bakya yimasu"


"Soyayya mana irin ta uwa da d'a wacce duk abunda zanci basu duniya bazan iya basu itaba" yasan halinta sosai idan yabiye mata yanzune zata sanyawa zuciyarsa raunin k'wak'k'waran adadin hukuncin data d'ibarwa mom don haka yace


"Shikenan zanyi tunani insha Allah"


"A'a dadyn...."


"Shiiiii....no more word again, kibarshi ahakan tunda ni nace zanyi tunani to zanyin kinji ko?"


Da haka tabaro part d'in nasa zuciyarta cike da fatar Allah yasa yahakura kenan...



_Tofah!🤔 koya za'a kwashe da Basmah dake kitchen tana had'a breakfast😋😋 aunty maijidda da aunty fareeda m Abbas ina gayyatarku wajen cin breakfast d'in Basmah's delicious💃🏻💃🏻💃🏻😃_











Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Gaisuwa tare da fatar alkhairi agareku 'yan *RANO ONLINE NOVEL GROUP* bisa yanda kuke k'ok'arin bibiyar wannan littafi nawa, musamman ga FARIDA MOH'D ABBAS, OUM AFAF, OUM FARHAN,BEEYAM, KUBRA, AISHA SURAJ, RUKAYYA KHADIJA, NUSAIBA BEBEJI, BESTY ZARIA, BABY LEEMERH, AMINA ina jinjina maku bisa yanda kukeyin comment cikin farinciki, inaso kusani hakan nak'ara mani k'warin guiwa fiye da tunaninku , ngd ngd ngd sosai inayi maku addu'a ubangiji Allah yabaku aljannah da rahamarsa👏🏻 I do luv you always❤_  



💎Page_____22💎


  Tana bud'e gambun k'ofar shiga falon taji wani irin sanyayayyen k'amshi yabugi hancinta tana shiga ta tarar angyara ko ina anyi mooping sai k'yalk'yalniya falon keyi k'amshi da sanyin AC na rab'aka tako ina, jin motsi a kitchen ya tabbatar mata da cewa har and'ora breakfast saboda tariga tasaba koda zata baro part d'in dady zata tarar har Billy ta gama shirya ko ina ta d'ora masu breakfast, shiyasa yauma batayi tunanin komai ba tawuce bedroom d'inta don ta tabbatar zata iya girka masu duk abunda yakamata agirka ba tare data rik'amata komaiba,


Batool kuwa na ganin Billy tanufi hanyar kitchen da zimmar rik'awa Basmah aiki bayan sun gama nasu tace


"A'a Billy kar kije kinsan halin yayya Basmah yanzu ne zaki shiga tab'ata maki rai ga banza, ashawarce kije kinemi ruwa kiwatsa idan kifito nima nashiga"


"Kai yayya Basmah aikin zai yimata yawa saboda breakfast d'in yau kusan abu kala uku za'a had'a, don Allah kema kitaso muje mud'an rarrage mata wasu abubuwa, inyaso sai mubarta ta ida k'arasa abinta" shiru tayi nad'an lokaci tana tunani irin gwatsilewar da zatayi masu.


"Plssss.yayya Batool kitaso mana"


Tare suka shiga kitchen d'in lokacin Basmah na k'ok'arin fera doya, juyowa tayi tana kallonsu had'e da tsuke fuska


"Malamai lafiya kukazo kuka yimun tsaye bisa kai?" 


"Yayya Basmah dama naga aikin kamar zaiyi maki yawa shine mun kazo mu tamaki" har ga Allah tana son surik'a mata aikin amma tasan halin Batool da tsarguwa beside ita bata son raini don haka ta fuske tace


"To ban gayyace kuba kufice kubani wuri bana son sa ido" dariya Batool tayi had'e da cewa Billy


"Kinga abunda nake fad'a maki, ai yanzu saiki wuce muje ko?" Ta k'arasa maganar had'e da dafa kafad'un Billy zasu fita, batare data juyo ba ta d'ago mata hannu tabaya tana fad'in


"Byeee..the great cooker" wani irin tuk'uk'i da takaicine suka tasowa Basmah kamar tayi ihu tace sudawo amma ko kad'an bazata iya hakan ba, tsaki ta d'anyi tare da gallamata harara "Asauka lpy" takusa minti biyar a zaune tana tunanin ta inda zata fara gashi 8:00am  har takusa, tukwanen ta shiga bud'awa d'aya bayan d'aya taga gaba d'aya ruwan da tasa sun tafasa  har sunfara k'onewa, nan hankalinta ya sake tashi tashiga bud'e kitchen cavinage tana neman abunda zata zuba masu, can taci karo da busashen kifin da Ummi ke amfani dashi idan zatayi miyar tuwo irin k'ananun kifin nan da akecewa crayfish sai dai wud'annan ba laifi don ba k'anana bane sosai , lumshe idanuwa tayi had'e da cewa "Alhmdulillahi" da sauri taciro kifin, ko wankewa bata tsaya yiba ta rutatashi a d'ayar tukunya sannan ta d'auko tattasanta da albasa mai uban yawa ta yankasu manya manya tazuba aciki, magunan data gani Jere acikin wasu bowl masu marfi tabud'e kowane tasaka k'waya d'aya "bari inbarsu haka kada suyi yawa" tafad'a tana k'ok'arin goge hannuwanta arigarta, dubawa tayi taga idan akwai curry da tyme ai kuwa cikin Sa'a taga dakakkin spices d'in da mom ke amfani dasu kowane ajiye, da sauri tad'ibi curry da tyme da tafarnuwa tazuba can tasake hango dakakkar daudawa tazuba kai tsabar nuna gwanewar Basmah hadda kdakakken kanumfari tasaka, kamar ance ta duba gefenta daga k'asa taga gyad'a cikin wani d'an bokiti k'arami tun jiya ummi ta jik'ata bayan sallar magrib saboda tajik'a sosai ya zamana yau blanding d'inta kad'ai za'ayi. Da sauri Basmah tarufe tukunyar ferfesun kifinta ta d'auko jik'akkar gyad'ar ta tsameta sannan ta zube cikin tukunya ta biyu da ruwan ta ke tafarfasa tarufe, fridge ta bud'e ta d'auko ruwan da zata sha don cikinta yafara neman abunda za'a saka masa saita hango gansarar kunun gyero da Ummi ke kunu da ita, d'au kowa tayi tad'ibi kusan rabinta tazuba a cikin tukunyar data zuba gyad'arta a hankali tasa ludayi tana motsawa nan take yayi kabri saboda yawan gansarar ammafa yayi k'olallai sosai ga kuma k'olallan gyad'a sun fito b'aro b'aro. Murmushi tayi had'e da sauke tukunyar ta aje gefe tayi wata irin ajiyar zuciya tace


"Kunun gyad'a!, dama ashe sauk'i ne dashi, ko kad'a bayada wata wahala" Juyowa tayi gefenta ta d'auko k'aton flaks d'in data gani ajiye cikin kayan jere tajuye kunun aciki sannan ta koma ga fik'ar doya, ganin lokaci na k'urewa yasa ta ajiye fik'ar doyar ta tashi tabud'e tukunyar ferfesun kifinta, "yawwa nasan dai ya nina haka yanzu bari na kwasheshi duk da dai akwai ruwa acikinsa ai zaifi dad'i ana d'an d'ebowa da ruwan da kifin anaci" kula mai kyau ta d'auko tazube farfesun aciki sannan ta d'auko bowls d'in miya da spoons ta d'orasu duka akan k'aton trey, hannu tasa tagoge zufan daya taran mata agoshi sannan ta d'auka tanufi wajen dining table dasu, jeresu tayi tsaf abun gwanin ban sha'awa kai kad'auka abun arzik'ine aciki sannan ta d'auki treyn takoma kitchen dashi, flaks d'in data zube kunun gyad'arta ta d'auko tare da tea cups suma takai ta ajiye akan dining,


Cikin tsiwa Batool tashigo kitchen d'in tana fad'in "wai har yanzu yayya Basmah baki gama had'a breakfast d'innan ba, nifa yunwa nakeji wlh"


"To munafuka ai nagama, yam balls d'in kad'ai ya rage" fridge ta bud'e ta d'auko garar ruwa har zata rufe sai ta hango kifi aciki, kuma tasan Billy tace hadda ferfesun kifi za'ayi


"Yayya Basmah kikace kingama? Hadda ferfesun kifin duka kinyi"


"Eh mana" tace batare da kalli inda Batool take ba, "Amma naga ai ga ki..."


"Abeg don Allah get out kar kisa nayi confusing abunda nake sonyi" Basmah tafad'a had'e da had'a hannuwanta kamar yanda indiyawa keyi, "ok! No wahala am out" itama tafad'a tare da d'aga kafad'unta tabar wurin, 



Ummi ce tafito cikin doguwar rigarta royal blue anyimata k'awa da Cristal stone, rigar tayi mata matuk'ar kyau sosai saboda yanda ta d'an kama jikinta, pink vail ne ta d'auro akanta abun ba'a cewa komai don indai kyaune tayishi sosai, "Bilkisu..Bilkisu.." ta kwala mata kira tana gyara zaman agogon dake sanye ga tsintsiyar hannunta,


"Na'am Ummi ganinan zuwa"


"Haba what is the time now ace har yanzu baki gama had'a breakfast ba, kinaso yunwa takamamun yarana ne" cike da mamaki take kallon Billy dake fitowa cikin d'akinsu gashi tanajin motsi cikin kitchen, 


"Ummi gani" saida takalleta irin kallon nan mai d'auke da alamar tambaya sannan tace


"Motsin waye nakeji a kitchen?"


"Yayya basmah ce"


"Ok kingama had'a komai ne?"


"Ummi yau bani nake had'in breakfast ba yayya Basmah ce keyi" gaban Ummi ne yafad'i don rashin sanin mezata isko, kitchen d'in tanufa ta isko Basmah nazuba doyar data fera acikin tukunya, kallonta tayi sannan tayi murmushi had'e da dafa kafad'arta, 


"Sannu da k'ok'ari Basmah dama kece a kitchen d'in, ai tund'azu nazata Bilkisu ce, agaisheke Allah yayi maki albarka, yanzun kin kammala ko akwai abunda yarage"


"Eh yam bolls d'inne kad'ai ya rage shima yanzunnan zan k'arasa"


"A'a jeki kiyi wanka nina k'arasa tunda kin gama mai wuyar kinji ko? Wani irin dad'ine ya rufeta don tund'azu tunanin yanda zatayisa kawai takeyi, azuciyarta kuwa cewa tayi ashe dai ko Ummi tasan aikin nada wahala, murmushi tayi sannan ta wuce d'aki ita kuma Ummi ta k'aro wutar gas d'in saboda doyar tayi saurin nina batare da tabi takan abunda Basmah tahad'a ba taci gaba da aikinta,


Cikin mintunan da basufi sha biyar ba Ummi tagama had'a yam ball d'inta takawo kan dining da tund'azu kowa ya hallara itakad'ai ake jira, cikin soyayya da yaba shigar datayi dady yace


"Weldone madam, yau kam anso asa mumakara"


"Am sorry dadyn yara, weldone yau ai na basmaty ne saboda ita ta shirya breakfast ida k'arasa mata kad'ai nayi, beside laifin ma duka na Bilkisu, sun shige d'aki sun barta ita kad'ai da aiki aidole tawahala sosai"


"Kai Ummi itafa Bilkisun da kike bari ita kad'ai tayi kuma naga akan lokaci take gamawa, ita dai d'in ce laziness" Mahmud ne yafad'i haka yana kallon Basmah data wani fuske ita ala dole yau ayaba mata da aikin datayi,


"What ever dai yakamata ace sunfito sun kamamata koba haka ba dadyn su" saida dady yayi murmushi sannan ya kalli Basmah yace


"Weldon Basmah 'yar gidan dady, yanzu dai a ajiye wannan zance afara zubomun ferfesun kifin in new test and aroma na 'yatah"


Ummi na bud'e kular ferfesu gabanta yafad'i saboda k'amshin kanunfari daya fara dukan hancinta, bata tsorata ba saida taga d'iyan k'anan kifi nayawo asaman ruwan ferfesun, k'walo idanuwa Ummi tayi ta juyo tana kallon Basmah, murmushi basmah tayi irin wow d'in nan tazata Ummi zatace, kallon dady tayi sannan ta kalli Mahmud, wani farincikine ya mamaye zuciyar har tana fad'a aranta yau ba reni tsakaninta da yaya Mahmud saboda yanda taga Ummi na kallonsu ta tabbatar sak'one take isar masu na yanda taga had'uwar ferfesun.


Bassam ne dake kusa da Ummi ya lek'a kular da ferfesun keciki shima ya k'walo idanuwa awaje


"Kai..! Dady kaga yanda grasshoppers (fara ko fari) suka mutu acikin ferfesun, gaskiya ni bazanci ba gasunan duk suntaso sama, Bilal zoka gani"


Rufe kular Ummi tayi tana d'an murmushin yak'e sannan tajawo flaks d'in kunu, cup ta d'auka tana zubowa ahankali aikuwa k'olallan da yayi dana gyad'a suka dinga fad'awa acikin cup d'in da wani yafad'o saida kunun yayi tsalle yafad'awa Ummi a fuska, rufe kunun tayi ta d'auki plates ta zubawa kowa yam ball d'in cikin zuciyarta kuwa b'acin raine kwance ace wai k'atuwar budurwa irin Basmah bata iya girki ba, batare da tace k'anzil ba tajawo hannun Basmah tayi kitchen da ita, suna shiga takai mata d'an rank'washi akai tace


"Wannan wace iriyar kwamacala ce kika had'a Basmah? Idan baki iyaba meya kaiki yi? Ina kika tab'a ganin anyi ferfesun crayfish" turo baki Basmah tayi hawaye na neman zubo mata a idanuwa ita kuma Ummi ta kunna gas had'e da d'ora ruwan zafi akai tana cigaba da yimata fad'a cikin b'acin rai,


"Kamata yayi ace tunda baki iyaba kin yimun magana sai narik'a maki muyi tare kiga yanda akeyi, ko kuma kitambayi Bilkisu tasan duk yanda akeyin komai sai tafad'a maki, yanzu dakin natsu yanda ya kamata ko kin tambaya baga kifinan acikin fridge ba, yakamata mirage wannan girman kai naki da shashanci kinatsu ki koyi girki domin gidan wani zakije, babu namijin da zai iya tolerating wannan noisens da kikayi, at least kodon kizama isassar mace awurin mijinki yakamata ace kin iya abubuwan da suka shafi rayuwar ki data zaman gidan auren ki amma ke kenan kullum cikin bak'in rai da sauraren wak'e wak'en banza a earpiece tare da rashin kunya, to kicanza wannan ba rayuwa bace kuma ba tarbiya mai kyau bace da zata zaunar dake d'akin ki idan Allah ya gwadamana, 


Ruwan zafin natafasa Ummi ta d'auko sauran gansarar data rage tana girgiza kai tazuba mata ruwa ta d'auraye sannan ta dama wani kunun amma shi wannan normal kunun gyerone,


Tana juyewa ta kashe gas d'in sannan takoma inda su dady ke zaune d'auke da kunun ita kuma tayi zaunenta kitchen tana sharb'ar kuka, cup's ta d'auka tazubawa kowa tare da sugar sannan ta maido da kallonta ga dady dake cin yam ball d'insa hankali kwance


"Am sorry dadyn yara kayi manage da wannan kunun, wud'annan bazasu ciwu ba" murmushi yayi sannan ya karb'i cup d'in kunun data mik'o masa, a hankali yake sipping saboda zafin da yake dashi har yasha fiye da rabi sannan ya ajiye, 


"Thank you rabba'atul bait, am going saboda nayi latti sosai" Allah ya kiyaye gaba d'aya suka yimasa ita kuma Ummi tarakasa har bakin mota sannan tayi masa addu'ar Allah ya kiyaye hanya kuma yasa adawo lpy, hugging nata yayi tare da yimata light kiss a forehead d'inta yana fad'in


"Amin ya rabbhi, Allah yayi maki albarka" tace "amin" yana shiga motar ya tayar had'e da zuge glass d'in dake gefenta ya duk'o da kansa yana fad'in 


"Ki kula mani da kanki sosai rabba'atul bait, luv you more than how word can say it" 


"Luv you too dadyn yara" tafad'a cike da jin kunya shikuma yaja motarsa yana dariya kasancewar drivern sa yayi tafiya k'auyensu shiyasa yanzu shike driving kansa zuwa office wata rana kuma Mahmud ne ke kaisa,


Yana fita saiga wata motar ta kunno kai ta shigo cikin harabar gidan tayi parking, har zata juya sai ta hango babbar aminiyarta hajia maijidda tare da wata k'awarsu hajia fareeda nafitowa daga cikin motar, farincikine ya rufeta lokacin da suka iso inda take tsaye tana murmushi, Rungume su tayi cikin soyayya da shak'uwar da zata nuna maka cewa aminantane na rai da rai tun suna 'yan k'anana, manyan matane masuji da kansu daka kallesu zaka tabbatar wayewar ilimin addini data boko sun ratsasu, bayan sunyi breaking hugging d'in da suka yiwa juna suka mik'amata hannuwansu dake d'auke da zobbunan zinari suna fad'in


"Assalamu alaikum hajia Aisha" cikin farincikin ganinsu ta amsa masu tare da rik'o hannunsu tana fad'in 


"Mushiga daga ciki...."


_Yau ake yinta ga aunty maijidda ga Basmah delicious, to asha dad'i lpy duk da kince baki amshi gayyataba amma rabo ya rantse sai maishi inji malam bahaushe..lol😃_

















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____23💎



  Da sauri suka dakatar da ita, "a'a hajia Aisha akan hanya muke zamuje   legas ne wajen d'auko kayayyakin mu sai hanya tabiyo damu ta wajen gidanki shine mukaga bai kamata muwuce batare da mun kawo maki ziyara ba,


"Kai amma naji dad'i sosai wlh, yau sha rabo? Gaskiya duk da haka yakamata ace kun shigo daga ciki ko ruwane kusha ko?"


"Kiyi hak'uri hajia Aisha sauri mukeyi next time idan munzo zamu yimaki wuni" duk da bahakan tasoba cikin murmushi tace "shikenan na fahimceku dama 'yan kasuwa haka suke basada lokacin kansu" dariya sukayi had'e da tafewa "yo kinga laifinmu? Kema ai bayadda bamuyi dake akan ki shigo adama dake ba kikak'i"


"Ai very soon zaku jini but not now? Lokaci nazuwa" dariya sukayi gaba d'ayansu tare da komawa cikin mota ita kuma Ummi ta koma cikin gida had'e da cewa ina zuwa kud'an jirani pls


Bayan minti biyu sai gata tadawo rik'e da 'yan matsakaitan ledoji guda uku a hannunta, d'aya snacks ne masu yawa da takeyi tana ajewa saboda irin bak'in dake zuwa unexpected ta biyun kuma drinks ne aciki sai kuma ta ukkun turarukkane masu k'amshi da tsada, gambun motarsu na baya tabud'e ta ajiye ledojin sannan tadawo wajen da hajia maijidda kezaune a sit d'in driver tace


"To matafiya ina godiya da wannan ziyara taku, Allah ya tsare hanya" juyawa tayi takalli ledojin data ajiye masu sannan tasake juyo tana kallonta


"Amin ya Allah hajia Aisha ke kullum bakya gajiya da yimana hidima"


"Haba nothing much fa? Ai yiwa kaine"


Daga haka sukayi ban kwana da ita zuciyoyinsu na masu yabon kirki da kuma kyawawan halayen Aisha,


Ummi nakomawa cikin gida tanufi kitchen aduk  tsawon lokacin nan Basmah na nan zaune tana kuka a inda tabarta taye Ummi tayi cike da mamaki sannan tasa hannu ta rik'o hannun Basmah ta mik'ar da ita tsaye ahankali take janta har suka isa dining table, hannunta ta saki tajawo kujera, ta sake rik'o hannunta ta zaunar da ita akai, plate d'aya ta d'auko ta ajiye a gabanta tabud'e ferfesun kifin tazuba mata sannan  ta sake d'auko cup shima ta cikasa da kunun ta ajiye mata, da sauri Basmah ta d'ago kai tana kallon Ummi dake tsaye akanta tayi folding hannayenta tana kallonta, murmushi tayimata had'e da lumshe idanuwanta tana nuna mata plate d'in dake gabanta


"Bismillah, yimaza kici kar yunwa ta tab'a munke" idanunta na hawaye tace


"Ummi ni bazan iyaba" 


 Su batool dake zaune afalo tare da yaya mahmud suka dinga yimata dariya, cikin b'acin rai Ummi tajuyo 


"Gaba d'ayanku  kub'acemun da gani ko ranku ya b'aci, Babana kaje ka shirya akwai inda nake son aikinka" suna fita tajawo kujerar dake kusa da Basmah ta zauna, kallonta tayi had'e da d'ora hannunta akan nata dake saman table d'in ta rumk'e  sannan tace


"Basmah banyi maki fad'a saboda bana sonki ba balle kizauna kina kuka har na kusan minti 30, nayi makine saboda kuskuren da kika aikata, ba lallene kiyarda da abunda zanfad'a ba shiyasa na zaunar dake kici abincin da hannunkine ya sarrafashi kiji yanda yake kozaki yarda da cewa kuskurenne yajawo nayi maki fad'an"


"Ni nayarda nayi kuskure amma ni banason fad'a, saboda mom d'ina bata saba yimani shiba ko kad'an" shiru mom tayi tana kallon yanda take fad'a mata wannan maganar ido da ido kafin can ta sake wani dogon numfashi tace


"Shikenan Basmah bakyason fad'a ko? Naji bazan sake yimaki ba, tabbas bazan sake yimaki fad'a agidan nan ba, to amma ke kuma yazame maki dole kinatsu kibi duk wasu k'a'idojin dana shimfid'a maki ba tare da rashin kunya ba, if not kuma bazan dena yimaki fad'aba ta k'arasa maganar had'e da mik'ewa tabar falon zuciyarta na rad'ad'i, har ga Allah bataso faruwar haka tsakaninta da itaba, amma ya zatayi idan har bazata jurewa ganin Billy acikin yanayi irin wannan ba to don me zata k'yale  Basmah acikin wannan halin, koba komai amana take agareta kuma dole Allah zai tambayeta akan amanar daya bata, 'yar mijin tace hakk'ine akanta takula da tarbiyarta koda mahaifiyar ta nanan balle kuma da batanan.


Tana wucewa Basmah tagoge hawayenta 


"Wallahi babu wanda ya isa yasa inbi k'a'idojinshi tunda bashi ya haifeni ba kuma indai rashin kunyace yanzu aka fara ganinta"


Tunda sassafe mom ta tashi cikin wani irin farin ciki tana jiran isowar 'yar uwarta kuma aminiyarta wato hajiya kilishi, sosai su papi sukayi mamakin yanda take fara'a saboda tunda tadawo gidan cikin bak'in rai take amma sai gashi yau takasa zaune takasa tsaye saboda tsabar farinciki, kallon hajia kaka papi yayi yace


"Baby anya yau lpy 'yarki ke wannan farincikin, shin kodai addu'ar muce takarb'u"


"Ga alama domin yau tunda safe na lura da yanayin da take ciki na farinciki, Allah yasa sauyawar mummunan halintane zuwa kyakkyawa zai bayyana"


"Amin ya Allah" juyowa papi yayi yana kallon mom dake tsaye abakin window tana jiran isowar hajia kilishi karaf suka had'a ido dashi


"Zonan usain", saida tasake kallon windown sannan taje gabansu ta zauna"


"Gani papi"


"Dama cewa nayi lpy kike wannan zagaye zagaye cikin farinciki?, ko alhaji ne ketafe" cikin farinciki tace


"Lahhh...papi na manta bangaya maku ba, ai jiya mukayi waya da 'yar uwata kilishi tace yau tana nan isowa harma tace ingaisheku sosai" cike da farinciki daya bayyana d'auke a fuskokinsu sukace


"Shine baki fad'aba sai yanzu, eh lalle dole zakiyi farinciki yaushe rabo?, Allah ya kawota lpy kotasa kidena wannan shashanci kikoma gidan mijinki ki rungumi 'ya'yanki" sanin yanda take da ita yasa suka dena mamakin farincikin da takeyi.


_WAYE HAJIA KILISHI_


'Yace ga aminin papi kuma shak'ik'in abokinsa wanda yarasu tun tana k'arama, hakan ne yasa papi yanemi alfarmar mahaifiyar ta da kuma 'yan uwan mahaifinta da abashi ita tadawo hannunsa da zama tare da yimasu alk'awarin zai rik'eta amana tamkar 'yarsa, kasan cewar kowa yasan halin papi mutumen kirkine kuma ansanshi tare da mahaifinta yasa batare da wani dogon tunani ba aka bashi ita shikuma ya karb'eta hannu biyu ya had'ata da 'yarsa Hussaina, kasan cewar halinsu yazo d'aya sai sukayi matuk'ar shak'uwa da junansu ta yanda hatta baccima baya rabasu, suna son juna sosai kuma duk abunda zasuyi atare sukeyin abunsu batare da sun bari kowa ya sani ba, a tsawon rayuwarsu babu abunda ya tab'a rabasu sai aure wanda hakan ne ya sanyasu rabuwa da juna badon sun soba, amma duk da haka babu wanda ke iya zartar da wani abu agidanta batare da taimakon d'an uwansa ba, duk abinda d'aya zaiyi sai yanemi shawarar d'aya akai hakan yasa akoda yaushe suke mar

ari da d'okin ganin junansu, hajia kilishi tun tana k'aramarta fitinanniyar yarinyace ta iya makirci da tuggu kala-kala, sam bataso taga anzauna lpy arayuwarta kuma bata shakkun kowa akan duk abunda tasa agaba, hajia kaka kad'ai da papi take d'an shakkar yin abu a gabansu koshi don tasan taka mata burke zasuyi, agabansu tana nuna halayen kirki ko kad'an bazata tab'a yin abun asshaba, shiyasa suke matuk'ar ganin mutuncinta da kimarta fiye dana 'yarsu da suka haifa domin bakad'an take girmamasu ba, wannan shine tarihin hajia kilishi.


Tsayawar motar da sukaji yasa su yin shiru daga fad'a da nasihohin da suka fara yimata akan maganar  abunda yafaru na gaskiya tsakaninta da dady da Mahmud yafad'a masu,


Cikin hanzari mom ta tashi tanufi bakin k'ofa don tarbota, tana fitowa cikin motar suka rungume juna cikin farinciki saida sukayi kusan minti uku ahaka kafin can hajiya kilishi ta d'ago had'e da rik'e hannun mom tana yimata wani kallo tun daga sama har k'asa



"Tafd'i jam qawata anya kece kuwa? Kinganki yanda kika rame kika lalace kamar bake ba, to wlh badon muryarki danaji ba aguje zan ingijeki in wuce abina"


Wani irin takaicine da bak'in ciki suka rufewa mom zuciya wanda d'acin kalamanta yasa hawayen ta zubowa batare data ankara ba, da sauri taja iska a hancinta tare da goge hawayenta


"Bari kawai 'yar uwa akwai labari" tak'are  maganar tana kallon yanda jikin hajiya kilishi yayi wani irin haske da kyau gaba d'aya ta canza tayi fresh ga wata irin qiba data k'ara kamar ba itaba tana mamakin yanda tasamu wannan hutun ita dake auren mai mata uku itace ta hud'u kuma mijinta ko kad'an bai kamo ko rabin arzik'in dady ba, dariya tayi mata had'e da jujjuyawa ahankali tana fad'in "dubeni da kyau kigani babu abunda ke damuna yanzu saboda remote control d'in gidan alhaji dashi kansa yana hannuna sai yanda nayi dashi"


Baki bud'e mom ke kallonta tace


"Ke kina sha'aninki, muje daga ciki kihuta ki shafa mani ko meye sirrin"


Tafewa sukayi suna dariya har suka isa falo, adaidai bakin k'ofar shiga hajia kilishi tawani gyara mayafinta had'e da marairarice fuska kamar tak'warai tashiga bakinta d'auke da sallama, cike da ladabi ta isa inda su papi kezaune taduk'a har k'asa ta gaishesu sannan taje ta rungume hajia kaka tana fad'in


"Hajiya ta nayi kewarku dayawa"


"Allah sarki yarinyar kirki muma munyi kewarki, ya maigidan naki da abokanan zamanki duk lpy kuke ko?"


"Lpy klw hajia duk sunce agaishe daku sosai tare ma mukaso zuwa dasu to sai Allah bai nufaba saboda wasu dalilai amma sunce zasuzo suma sugaisheku insha Allah"


"Madallah! muna amsawa ya hanya ya hanya?"


"Alhmdulillah papi, ashe ita kuma Hussaina abunda yafaru kenan?"


"To kindai gani, abunda tun k'urciya ba'ayiba sai yanzu" papi ne yafad'i haka yana kallon mom dake gefe tsaye


"To papi k'addarorine Allah yatsare gaba"


"Amin, kidai yimata fad'a inzataji, yakamata ace takoya daga gareki yanda kike zaune lpy da abokanan zaman ki, amma ita ace ko yaushe gatanan cikin zargi da son zuciya tahana abokiyarta zama lpy kuma tafitini kanta" Kallonta tayi sannan tace


"Allah dai yakyauta papi, abubuwan ne babu dad'inji gaskiya"


"Tashi kije daga ciki ki nemi ruwa kiwatsa sannan kici abinci kihuta kinji ko? Allah yayi maki albarka yajikan mahaifinki" hajia kaka tafid'i haka itama tana k'ok'arin tashi


Suna shiga d'aki mom takai mata duka da wasa, tace 


"Ke kam bakida kirki, bazaki dena k'aryannan takiba ko? Hadda wani zancen da atare zakuzo da duka kishiyoyinki don d'ai neman suna agurin papi ni kuma kijamun zagi ko?" saida tayi dariya sosai sannan tace


"Eh mana, bagashi har papi ya yarda ba, halinshi dai nanan yanda yake be chanza ba, gaskiya akwai gyara cikin rayuwar shi, ace wai da kanshi ke fad'ar wai kin takurawa kishiyarki, cab ashe da zaiga yanda nake da nawa kishiyoyin wlh sai ya tsaneni don kokad'an dasu har 'ya 'yansu babu maijin sanyina bugu da k'ari ko wanda ya ajiye su wlh indai ina kusa basu isa suji sanyin shiba, ke nifa nan zan iyayin komai don inga nike taka bani ake takawa ba"


"Hmmm barka da arzik'i aini kam k'asa nake war was ana takani dani har yarana sai yanda akayi damu"


"Hhhh ki kwantar da hankalinki nesa tazo kusa yanzu ke zaki taka duk wanda kikeso don nazo maki da maganin matsalar ki"


"Da gaske 'yar uwa?"


"Sosai kuwa kedai kawo kunnenki kiji...



















Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

 

_Jinjina had'e da gaisuwa ta musamman ga dukkanin members d'in *MUSHA KARATU NA..YBK GROUP* hak'ik'a zuciyata na alfahari da kasan cewata atare daku domin kud'in mutane ne masu tsananin karamci da halaccin dake samar da nishad'i atare da ita, fatana Allah ya tsarkake dukkanin gabb'anku ya kuma albarkaci ahalinku, ina so kusani cewa aduk bugun zuciya d'aya nawa d'auke yake da miliyoyin k'aunar ku fisabilillahi❤💘_



💎Page_____24💎



  Zaro idanuwa mom tayi tana mai kallon hajia kilishi sannan ta kwashe da dariya


"Ke 'yar uwa da gaske kikeyi?"


"Hmmm kina wasa wallahi ba itaba hatta shi kansa sai ya zame maki tamkar raqumi da akala, kedai kawai kisha kuruminki, kina zaunenki zakiga aiki da cikawa ba boka ba malam"


"Haka nake so domin naci alwashin salwantar da rayuwar Aisha da zuri'arta saboda na tsaneta fiye da yanda natsani shed'an"


"Hhhh kai k'awata shed'an fa kikace!" hajia kilishi tafad'a had'e da jefa cingum abakinta tana tauna, hannunta tasaka acikin jakarta tafiddo wata 'yar k'aramar kwalba kamar ta turare tamik'awa mom "ungo wannan ruwane aciki da basu wuce 3 drop ba amma sunada tsananin k'arfi, zakiyi amfani dasu kamar sau uku bayan sallar isha'i, zaki samu kad'a kid'an dangalo ruwan kad'an sai kiyi inserting acikin jikinki har na tsawon kwana uku amma ki tabbatar ranar alhajinki zai kusanceki, azahiri wannan kayan ni'imar matane ga duk wanda ya gani amma abad'ini sirrin mallakane mai k'arfi, ina tabbatar maki da cewa matuk'ar kikayi amfani dasu kuma alhajinki ya kusanceki to tabbas babu wata macce da zai koma kallo a matsayin macce aduniya idan ba keba" sake d'auko wata gumba tayi cike da k'aramin d'an bokiti fari irin wanda ake saka turarukkan wuta aciki ta mik'awa mom tace


"Ita kuma wannan gaba d'aya zaki dame kishanyeta, da kanki zaki bani bayanin kyautar da zaki karb'a a wurinsa don duk abunda kikace ya baki to wlh sai ya mallaka makishi"


Zaro idanuwa tayi had'e da cewa "kai dagaske kikeyi?"


"Sosai kuwa kigwada kigani"


"To amma ni k'awata har yanzu banji kintab'o abunda nafi buk'ata ba, matarnan fa tazamo mani tamkar ciwon ido" 


"Kash matsalata dake Hussaina gaggawa, ai kifara mallakar mijin tayanda duk wani tuggu da makirci da zaki had'a mata zai yadda dashi"


"Nifa nafison ayita tak'are, bana son ganinta gaba d'aya agidan" dafa kafad'arta tayi tana dariya


"Kai k'awata wai wannan tsana da kike yimata dame tayi kama? Ki kwantar da hankalinki abu komai a sannu kada garin gaggawa k'aik'ayi yi koma kan mashek'iya, abunda yakamata yanzu kiyi shine kisan yanda zaki jawo hankalin mijinki kibashi hak'uri in yakama har kuka kiyi masa ya maisheki d'akin ki hakan zai taimaka mana wajen yin aikinmu yanda ya kamata, amma kina nan azaune gida bana tunanin aikinmu zai yuyu kin fahimta" Shiru mom tayi tna nazarin magani ganunta sannan tace 


"To shikenan, yanzu kitashi ki watsa ruwa kafin hajia ta k'wallo maki kira"


Basmah kuwa Ummi na shiga d'aki ta kira wata k'awarta awaya, suna gama magana tafita abunta batare da kowa ya sani ba,


A b'angaren Ummi kuwa  bayan ta kammala abincin rana ita da 'yan biyunta wato Batool da Billy ta umurcesu dasu tafi part d'in mom su dubo mata Basmah idan tana can don tunda tagama yimata fad'a tabarta afalo zaune bata sake ganin taba ta d'auka tana d'akinsu kwance amma ga mamakinta koda taduba d'akin bata gane taba gashi har k'arfe biyu ta wuce, tafe suke suna firar breakfast d'in Basmah suna dariya har suka iso part d'in mom nan ma bata ciki saboda part d'inma akulle yake ba kowa aciki nan suka shiga dudduba ta tako ina gefe gefen gidan basu ganeta ba, wajen Ummi suka koma suka fad'a mata bata can, nan take hankalinta yatashi tafita tana duba ko ina a compound d'in gidan ba Basmah ba labarinta, innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta dinga fad'a in tayi nan tayi can, wajen maigadi tanufa tana tambayarsa shin ko yaga fitar Basmah, shiru yayi ya kalli yanda hankalin Ummi ya tashi, cike da tausayinta yace


"Tuba nake uwar d'akina banso nafad'a makiba saboda har kud'i aka bani na toshiyar baki, amma ganin yanda kika tada hankalinki zan fad'a maki gaskiya, d'azu ina  anan zaune saiga wata k'awarta tazo ita da wani acikin mota, basu cemun k'alaba ni kuma ban cemasu ba naga ta fiddo wayarta tayi kira, ba'a jima ba saiga  Basmah tafito, shine har ta shiga motar sai tafito ta mik'o mani d'ari biyar tace ko antambayeni naga lokacin data fita ince a'a ya k'are maganar had'e da nunawa Ummi d'ari biyar d'in, ki gafarceni hajia nasan konayi yunk'urin hanata walak'anci zata yimani shiyasa nayi shiru, hawayene suka zubo a idanuwanta da sauri tasa hannu ta shafo bakinta daya kasa furta komai sannan tajuya takoma cikin gida, wayarta tajawo takira Mahmud cike da damuwa tafad'a masa halin da ake ciki, saida ya kwantar mata da hankali sannan ya kashe wayar.


Lambar Basmah ya shiga lalubowa ajerin contact d'insa had'e da danna mata kira, Basmah naganin kiransa amma tak'i d'agawa har sau uku, ganin haka yasa yafita batun kiran yaja motarsa da yake yana wajen abokansa yabar wajen aguje cikin matsananciyar damuwa.


Ita kuwa Basmah dake zaune bisa wata katifa ita da suby k'awarta tayi dariya tana nuna mata gaban wayarta kafin tace


"Kinganshi ko? Sai wani faman kirana yake don ya takuramun, gaba d'aya gidan sun tsaneni, mom d'inmu kad'ai ke sona yanzu kuma bata gidan dadynah ma baidamu dani ba agabansa za'ayi tayi mani fad'a akan d'an k'aramin laifi idan nayi amma bazayace komai ba, hatta k'anwata dake bimun tagujeni taya kike zaton zansamu farinciki agidan?" Murmushi suby tayi sannan tace " ki kwantar da hankalinki anan zaki samu farinciki kawai abunda nake so dake kiyarda dani"


"Taya zan yarda dake suby bacin bakida maganin matsalolina" wata kwalba suby tafiddo ta mik'awa Basmah


"Karb'i wannan kisha da kinsha shi zakiji gaba d'aya matsalolin ki suntafi koba haka ba bab's" tak'are zancen tana kallon saura yin dake gefe yana zuk'ar shisha" cikin maye Bab's yace


"Tabbas haka yake suby, idan kuma bata buk'atar sa, to tasha wannan don yafi k'arfi sosai" ya mik'o mata wata kwalbar dake ajiye acikin kwalaben da suka daza agabansu.


Karb'a Basmah tayi tana yatsina fuska


"Meye wannan Bab's"


"Hhhh Basmah Basmah kenan, wannan shi ake kira da sabuwar duniya kawai kisha zaki tabbatar da abunda nake nufi" har tad'aga kwalbar zata sha  saiga kiran Ummi ya shigo a wayarta, bataso d'aga wayar ba amma saboda tanason yiwa Ummi fitsara tad'aga 


"To kuma meye? Ko fad'anne kika kirani kik'ara yimun" da wuri Ummi tagoge hawayen daya zubo mata a idanu'


"A'a Basmah, kiyi hak'uri kidawo gida, ina kika shigane, kuma waye ya d'aukeki amota?"


"Meye damuwarki aciki, kawai ki ajiye waya"



"Basmah kiji tsoron Allah a duk inda kike kidawo gida, kada kiruguza rayuwarki abanza, kib'ata tarihinki na har abada" tuni kalaman Ummi suka tunzura Basmah ta d'aga kwalbar dake hannunta tashanye abunda keciki tas sannan ta bubbuga kanta da hannu tace  


"Kikace me? To koma mezai faru ai rayuwatace babu abunda ya shafeki aciki don haka sai anjima"  Ummi kuwa tanajin zata katse wayar takama fad'in "hello hello Basmah, Basmah" amma ina tuni takashe wayar tana kallon suby tace


"Kinji 'yar rainin wayon matar nan ko?"


"Kawai ki manta da ita Basmah yanzune zaki samu farincikinki da 'yancin kanki" saida tayi dariya sannan taci gaba dacewa welcome to the new world"










Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Ina kuke 'yan group d'in *HOME OF NOVELS* gaisuwa ta musamman zuwa agareku saboda muhimmancin da kuke dashi agareni bazan tab'a iya misaltashiba, tabbas kuna sakani nishad'i tare da k'aramun k'warin guiwa aduk lokacin da naga kuna comment idan nayi update, wannan dalilin ne yasa bazan iya wuce wannan page d'in ba har sai na isar da jinjina had'e da fatar alkhairi agareku, especially you people UMMIE, ZULAIHA SAMINU ELJIBRIL, MALKALFRED966 da kuma OUM RUQAYYAT, nagode nagode sosai Allah ya faranta maku zuciyoyinku fduniya da kuma lahira, *luv you all to the square of infinity*💋❤_



💎Page_____25💎



  Daga nan fa Bab's da suby suka dinga mik'awa Basmah kayayyakin dake sa maye kala kala tana sha wai don duk su sama mata farincikin da take tsammanin tarasa acikin agidansu,


Tunda ummi tagama waya da ita tafad'a akan kujera zaune hannunta na rik'e da wayar yayin da idanuwanta suka kasa dena zubar da k'wallan bak'inciki da takaicin rashin sanin halin da Basmah tajefa kanta aciki, haka Mahmud ya gaji da yawace yawacen nemanta ya dawo gida ya tarar da ita cikin wannan halin, har ya k'araso gabanta ya duk'a had'e dasa hannayensa akan hannunta dake rik'e da wayar bata san yana wajen ba sai lokacin da taji ya rumk'e hannun nata sosai sannan ta farga dashi awajen, hannunta d'aya ta d'aura akan hannayensa dake kan nasa had'e da kallonsa cikin muryar kuka tace


"Basmah..!" da sauri ya lumshe idanuwansa yace "ki k'yaleta Ummi, duniyace ta isheta wando da riga hadda mayafi, rayuwar da tazab'awa kanta kenan babu yanda zamuyi da ita sai addua, babu inda banjeba cikin gidajen 'yan uwa da wasu k'awayenta dana sani amma ban sameta ba, abun takaicima ko wayata tak'i ta d'aga saboda d'ai tasan mezai faru idan ta d'aga" yak'arasa maganar shima hawaye nafita daga idonsa.


"Bazai yuyu a k'yale taba, itafa 'ya macece dake buk'atar killacewa, wallahi zaifi ace aure aka yimata da a k'yaleta cikin wannan rayuwar sam hakan bai dace ba Babanah kayi tunani mana"


"To Ummi yanzu me za'ayi?, tunda bamu ganeta ba"


"Sake komawa zakayi ko Allah zaisa ka ganta"


"A ina kuma awane wajen, natabbata bata area nan, amma bari na sake komawa" tashi yayi yafita yana gogur idanuwansa da sukayi masa jawur saboda tsananin b'acin rai da yake ciki, har yakai bakin k'ofar fita Ummi takira sunansa,


"Babanah ka kula da kanka sosai" gyad'a mata kai kad'ai ya iyayi sannan yafita,


Tunda hajia kilishi ta d'ora mom akan hanyar salo da yaudarar da zata bijirowa dady da ita don ya maisheta d'akinta tafara shire shiren yanda zatayi yanzu haka kusan minti biyar kenan tana kiran wayarsa amma yak'i d'agawa, hakan ba k'aramin b'ata mata rai yayiba cikin takaici tajefar da wayar tana maseefa


"Lalle mutumennan yamatuk'ar walak'antani, yanzu nike kiransa yak'i d'agamun waya, wlh duk randa yashigo hannuna sai nasa yayi nadamar wannan abun da yayimun" dariya hajia kilishi dake zaune a gefen gado tana buga game da wayarta tayi ba tare da tad'ago kan taba tace


"Saifa kin kai zuciyarki nesa yanzu don da alama uwar gidansa ta cikashe masa duk wani gurbi da kika kasa cikashewa acikin gidansa, mezai hana ki gwada tura masa text message, natabbata zai gani kuma zai karanta, ki kula banda rawar kai ko kuma kushe  masa mata acikin alamurranki ai kingane ko?" Sai da mom tad'an bata rai tare da gallawa kilishi harara sannan tajawo wayar, message tafara rubuta masa kamar haka cikin zafi da k'unar zuciya


_Alhaji natabbata kana ganin kirana ka kak'i ka d'auka saboda yanzu banice agaban kaba, to koma dai meye yakamata kasaurareni kona minti d'aya ne saboda kasan ko meye dalilin da yasa nakiraka, alhaji kenan inaso kasani fa har abada babu wacce zata iya maye maka gurbina matuk'ar ina raye saboda nice uwar 'ya'yanka wacce tafara baka farincikin da aka kasa baka na tsawon shekaru don haka kuwa kasan ban cancanci walak'antawa daga gareka ba, idan kayi tunani ina jiran kiranka domin mu magantu_ tana gama rubutawa ta tura masa had'e da jefar da wayar ta dafe kanta da duka hannayenta.


"Wlh alhaji na neman sa in zubar da matsayina agunsa" kallonta hajia kilishi tayi sannan tasake maida hankalinta ga game d'in da takeyi tana fad'in


"Abune da yazame maki dole kiyi inhar kina so kikoma d'akinki don cikar burinki to dole kisauke wannan girman kan da jijji dakan da kike yimasa",


"Shikenan! He most to pay fo all this wlh" k'arar shigowar message a wayarta taji da saurin ta d'auko wayar tana duba amsar da dady yaturo mata,


" _Hmmm kice har yanzu da sauran zama kenan!_" 


Da k'arfi mom tace "what?", kingani ko ai duk ke kika jamun wannan rainin, anfad'a masa cewa gidan namu isata yayi ne?"


"Cool k'awata" hajia kilishi tafad'a


"Mik'omun wayar naga mekika rubuta kuma wacce amsa kika samu da kika buga man wannan uwar tsawar acikin kunne"


Duk jahilcin hajia kilishi saida ta bud'e baki cike da mamakin kalaman da taga mom ta turawa dady, dafe goshinta tayi da tafin hannunta tana kallonta


"Ai kuwa da gaskiyarsa baki gaji da zaman gida ba, taya zaki tura masa wannan sak'o mai cike da isa da kuma izgilanci kuma kiyi tsammanin zai tsaya ya saurareki? Kash wlh so kike kib'ata mana tsari gaba d'aya, keda zaki yita lallashinsa da kalamai tausasa masu dad'i har kisamu ya saurareki amma shine zaki tura masa wannan shirmen? Cab...to wlh da sake indai baso kikeyi ki ida tsofewa agidan nan ba sukuma suna can suna bugun ingantacciyar rayuwarsu cikin soyayya ba"


"To yanzu ya kikeso nayi? nifa gaskiya bazan juri wannan sabon walak'anci nasa ba"


"Ai kuwa yazama dole kijure don cikar burinki idan kuma kin safe tun yanzu kin barwa Aisha shi sai intattara inawa inawa gobe inbar garin nan" da sauri takame hannunta


"Haba k'awata karki yimun haka, yanzu me kikeso ayi ko nace masa kuma?" shiru tayi ta kalleta ta kalli wayar sannan ta jefa mata ita ajiki,


"Maza kisake tura masa wani kuma kibasa hak'uri" jiki na rawa ta d'auki wayar don tana matuk'ar buk'atarta atare da ita domin batada wata madafa idan ba itaba, wani message d'in tafara rubutawa cikin jin haushin k'awar tata.


" _pls kayi hak'uri bahaka nake nufi ba, gaba d'aya narasa natsuwatace atare dani saboda rashinka akusa dani, nayi kewarka don Allah kayafe mani nayi nadamar abunda nayi kuma ashirye nake nagyara kuskurena_


 Tana gama rubutawa ta mik'awa hajia kilishi wayar tana tuk'uburi domin taduba tagani idan yayi, murmushi tayi tana kallonta bayan tagama karan ce message d'in had'e da rubuta _I LUV YOU SO MUCH & AM MADLY MISSING YOU_ ak'asan rubutun sannan tayi sending message d'in wa dady tare da mik'a mata wayarta tace 


"Shak'iyiya ana so ana kai kasuwa, to sai kijira amsa kigani yanzu"


A wannan karon kam dady dake zaune akan kujerar office d'insa yana duba wasu takardu tashi tsaye yayi cikin sauri kamar wanda aka tsikara da allura, lokacin daya gama karanta sak'onta, domin a iya saninsa tunda suke bata tab'a bashi hak'uri ba idan tayi masa laifi ba saidai yagaji da fushinsa sudawo su daidaita, amma sai gashi da kanta take basa hak'uri had'e da dad'ad'an kalamai, Allah sarki miji da mata sai Allah ko yanzu dady baisan badon karan kanta tayi hakan ba sai don ta cimma mummunan manufarta tare da taimakon k'awarta hajia kilishi" wani irin farinciki ya tsinci kansa aciki wanda ya haifar masa da nan take ya manta da kaidi da kuma makirci irin na mom, har zai kiranta sai kuma yafasa shima ya sake rubuta mayar mata da sak'on a takaice


_Da gaske kikeyi hajia Hussaina_


Tana karantawa tayi dariya tana cema hajia kilishi 


"Kinga sokon har ya yadda, bari zakayi idan kazo hannu, dama indai wajen sanyin zuciya ne nasan babu kamar alhajina kuma ai inada tabbacin yana matuk'ar sona ransa ne yab'aci har yayimun haka" wani sak'on tasake tura masa


_Sosai kuwa alhajinah don Allah kasake bani dama zaka fahimci rashinka yasa na canza dukkanin halayyata nidai fatana kayafe mani kai da Auntynah_


A wannan karon cikin zumud'i dady yakira wayarta tana d'agawa tafashe da kukan makirci


"Kayafemun alhaji wlh nayi nadamar duk abunda nayi, nayi maka alk'awari zanbika zanbi aunty Aisha bazan sake yin abunda zai haifar da damuwa acikin gidan kaba" wani lumshe idanuwa dady yayi yanajin kukan nata har cikin ransa.


"Karki damu komai ya wuce, kiyi shiru bana son jin kukan nan naki yana azabtar da zuciyata" mom najin haka tasake fashewa da wani kukan dak'arfi har tanayi kamar tana sharar majina


"Kabarni inyi kuka mana, na zalinceka da yawa don Allah kayafeni" haka dady yayita rarrashin mom yana fad'a mata dad'ad'an kalamai har saida yaji muryarta ta daidaita sannan sukayi sallama


Kallon hajia kilishi data saki baki tana kallon ta cike da mamaki tayi ta sakar mata murmushi had'e da ajiye wayar akan gado tashige toilet abunta, saida tafito hajia kilishi ta iyayi mata magana,



"Hussaina dama shak'iyancinki da makircinki yakai haka shine har kike neman taimakona kina yimani kamar bakisan mekike yiba, to plan A yak'are tunda kun daidaita da mijinki nima gobe komawa zanyi yarage naki ki aikata plan B yanda yakamata inyaso idan kingama dashi saiki nemeni musan yanda zamu b'ullowa plan C.


Dariya mom tayi tana goge jikinta da towel tace


"kad'an kika gani, dama can fashiyar bak'i ke wahalsheni amma ana nunamun hanya shikenan anwuce wurin"


"Eh naga alama kuwa irin wannan makirci haka!"


Muryar hajia kaka suka jiyo tana doka sallama abakin k'ofar d'akin, bayan sun amsa mata ta shigo cikin shigarta irinta nagartaccin tsofaffi dake nuna shirin fitane tayi tace


"Muzamu fita nida papinku don Allah kuje kud'ora dinner kafin mudawo" da yake ba'a jima dayi sallar la'asar ba a lokacin,


Atare suka amsa da "adawo lpy hajia"








Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____26💎


 

 Dady nagama waya da mom ya tattara takardu da laptop d'in dake gabansa yasa acikin jakar da yake zuwa office da ita dama lokacin tashinsa yayi, don haka batare da b'ata lokaciba yabar office d'in cikin farincikin dashi kansa bazai iya misal tashiba, yarasa dalilin da yasa duk irin rashin mutunci da mom keyi masa yakan tsinci kansa cikin farinciki aduk lokacin da yaji muryarta kuma yake samun tsananin damuwa da damuwarta.


Basmah kuwa ta shawu iya shawuwa, gaba d'aya halittarta ta canza kamar ba itaba, cikin awanni k'alilan tafita daga cikin hayyacinta takoma 'yar maye inbanda suruttai wud'an da basuda kai da ma'ana babu abunda takeyi har tagaji bacci ya soma d'aukarta, ganin hakanne yasa Bab's da suby suka d'aukota a mota sukazo da ita gida, koda suka iso anguwar su Basmah marece ya somayi don haka sai suka tsaya a farkon shigowa area su suka ajiyeta, cikin muryar dake nuna tatil suke suby tace


"Baassmah.... anan zamu ajiyeki fa..kitashi mana munzo layinku, ahh bazaki bud'e idanuwanki bane?..Allah mubazamu iya zuwa k'ofar gidanku ba saboda nasan dad d'inku ya dawo" cikin dak'ilalliyar muryar da bazaka iya fahimtar abunda take cewa ba ta lumshe birkitattun idanuwanta tace


"Indai ta dadyne mai sauk'i ne, kawai ni yayane banaason had'uwa dashi mugun kubcyne" gambun motar tafara bud'owa sannan ta sakko k'afarta a hankali tana faman tangad'i tayi kusan minti uku tana kokuwa da marfin motar sannan tasamu dak'yar ta turasa ya rufe da k'arfi, hannu ta d'agawa suby had'e da cewa,


"Mukamaaa gobe" daga nan suka tada motar sukabar layin aguje, wanda duk mai hankalin da yaga yanda ake tuk'in motar dole ya kauce don yasan ba lafiyayyune acikiba, kasancewar riga da sket ne a jikinta na atampa d'inkin yad'an kamata sai takasa tafiya yanda yakamata saboda yanayin tangad'in da takeyi hatta mayafinta kasa rufowa tayi saidai ta rik'osa ahannu, tafiya takeyi tana had'a hanya basu jima da wucewa ba sai ga motar yaya Mahmud ta kunno kai,da farko horn yafarayi don gaba d'aya b'acin ran da yake ciki ya hanasa gano ko waye agabansa, iya abunda yasani shine akwai mutum a gabanai, yayi minti biyar yana yimata horn amma ko kad'an hankalinta bai tashiba kuma bata razana ba kai kace titin na gidan sune, hakan ba k'aramin dad'a masa b'acin rai yayi ba akan wanda yake ciki, afusace yafito cikin motar da niyar sauke mata ruwan fitina amma abunda idanuwansa suka gane masa yasashi razana yaja baya da sauri yana nunata da d'an yatsa saboda duk wanda yaga yanayin da take ciki kobai san taba sai yagane abuge take, balle shida take k'anwarsa, Basmah na ganinsa ta turo idanuwa awaje tare da watsa hannuwanta gefe tace


"Shikenan ai najawa kaina, kawai kayi hak'uri" ta k'arashe maganar had'e da nufatosa, idanuwansa na hawaye ya duba gefe gefensa yaga babu kowa a layin saboda quite area ce irin ta masu kud'i babu ruwan kowa da kowa kuma da wuya kaga gittawar mutum awaje, cikin sauri ya rungumota ajikinsa had'e da nufar inda motarsa take, turesa shigayi cikin yanayin muryarta na irin mashaya tace


"A'aa...kada ka yimun wayo, idan zaka dokeni kadokeni anan idan kuma bazaka dokan ba kawai ka k'yaleni zan k'arasa da k'afafuwana" kallon k'afafuwqn nata yayi yaga ko takalma bata dasu hannu yasa ya sake goge hawayen da suka zubo masa yace,


"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, wannan wace irin musiba ce" dariya tayi had'e d'ora yatsanta akan lab'b'ansa,


"Shiiiii....musibace ko?" Tana waige waige ganin zata b'ata masa lokaci yasa yaja hannunta da k'arfi ya turata cikin mota sannan ya tayar suka nufi gida,


Yana shiga ya hango motar dady ya dawo don haka kai tsaye ya sake rik'ota ajikinsa ya shigo part d'in Ummi da ita, akan kujera ya ajiyeta, Billy ce tafara shigowa sannan Batool suna ganinta suka k'araso wajen aguje suka rungumota suna kuka, da alama abunda tasha yanada k'arfi sosai ko kuma batada k'arfin jinine saboda har yanzu bai sake taba, k'urawa Billy idaniwanta dake lumshe tayi kamar mai son gano wani abun sannan ta maido kallonta ga Batool dake tambayar sa cikin kuka,


"Yaya me yasami yayya Basmah!" Goge hawayen sa yayi batare daya bata amsaba saima cemata da yayi,


"Ina Ummi take" Billy ce ta amsa masa itama cikin kuka


"Tana part d'in dady"


"Ok Batool kije ki kirasa, ke kuma Billy jeki kid'auko mun gwangon peak milk da man zaitun" a hankali suka mayarda kanta akujera sannan  suka tashi, kamar antsinkili Basmah ta rik'o hannuwansu su biyu da sauri tana fad'in


"Kudawo ba inda zakuje ku 'YAN UWANA NE!" kafin subud'e baki suyi magana sukaga tafad'o masu luuu ajiki, kallon Billy Batool tayi itama ta kalleta, atare suka d'ago fuskarta sai sukaga ashe vaccine ya ziyartota. Kallon ya Mahmud dake dafe da kansa sukayi, 


"Yaya..." Alama yayi masu da hannu gefen kujera


"Ku kwantar da ita"



_*Manage pls, yau unguwa natafi kuma nagaji sosai, luv u all💋💋*_













Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


    *HAPPY JUM@T TO ALL MY FANS, MUCH LUV😍❤🥰*



💎Page_____27💎


    A haka Ummi tashigo falon cikin rashin walwala bakinta d'auke da sallama, hango Basmah da tayi a hannunsu Billy suna k'ok'arin kwantar da ita yasa tak'araso wurin da sauri takarb'eta had'e da rungumota ajikinta ta zauna akan kujera, hannu tasa tana d'an bubbuga kumatunta ahankali tana kiran sunanta cikin tashin hankali,


"Basmah, Basmah, Basmah kibud'e idanuwanki mana, lpy kike? Wai meke faruwa dakene basmah bakyajina? Basmah!" tak'arasa maganar had'e da girgiza hab'ar bakinta tana kallon idanuwanta data bud'e a hankali sannan ta sake kullesu saboda baccin da yayi mata nauyi, a hankali ta kwantar da ita akan kujerar sannan tajuyo tana kallon Mahmud daya tsura masu ido, dafa kafad'arsa tayi


"Babanah a ina kaganta? Kuma me yasameta hakane?" hannunsa ya d'ora akan hannunta dake saman kafad'arsa yana k'ok'arin maida wasu hawayen dake son zubo masa yace


"Ummi akwai matsala!, Basmah tafara shaye shaye, duk inda nayi tsammanin ganinta ba'a can na ganeta ba, daidai farkon shigowa layin nan naganeta abuge tsakiyar titi tamkar wacce batada gata, gaba d'aya tafita hayyacinta ko takalmi babu ak'afafunta, Ummi Basmah ta d'auko hanyar da bazata b'ulle ba kuma natabbata miyagun k'awayen dana hanata mu'amala dasu suka d'ora ta akanta" d'ora kansa yayi akafad'ar Ummi dake k'ok'arin goge masa hawaye yaci gaba da cewa,


"Ummi ina matuk'ar son 'yan uwana bana son wani abu yafaru dasu, duk da mugun halin Basmah bana fatar rayuwarta ta d'ore a hakan domin suma 'YAN UWANA NE! don Allah kiyi wani abu akai Ummi" a hankali Ummi keshafar sumar kansa tana rarrashinsa,


"Kayi hak'uri Babanah, komai na duniya mai wuce wane kuma babu wanda ke kaucewa k'addararsa, banida iko akan Basmah amma zanyi iya k'ok'arin da zan iya akanta, tsangwama da fad'a ko duka bazasu canza taba, haka kuma nuna mata soyayyr da take buk'ata ba abunda zai jawo illa sake jefata a had'arin rayuwa, don haka ka kwantar da hankalinka kukan beda wata fa'ida muyi hak'uri kuma mukarb'i k'addara, natabbata da sannu idan ana yimata nasiha da addu'a zata canza kamar yanda muke buk'ata kaji ko?" Bata jira amsar da zai bata ba tayiwa Batool umurni data zubo masa abinci takawo masa, Billy dake gefenta zaune itama ta mik'e ta d'auko gorar ruwa da fresh Orange juice d'in da Ummi tahad'a aka saka a fridge yayi sanyi sosai sannan ta d'auko glass cup takawo ta aza akan center table d'in dake gefen kujerar da suke zaune tajawosa agabansu ta ajiye, lokacin itama Batool takawo abincin da tad'ebo a plate ta ajiye akai, kallonsa Ummi tayi had'e da cewa "yanzu kadaure kaci abinci idan ka k'are saika watso ruwa kaji ko Babanah?"


"Ummi bazan iyaba, gaba d'aya yunwar dake cikina tafice mun" b'ata fuska Ummi tayi tace


"Bazai yuyu ba so kakeyi rashin lafiya yataso makane?" Bata jira mezai ceba ta d'auko Firar ruwan ta'ud'e ta tsiyayo a cup takai masa abakinsa batare da yayi mata musu ba yafara shan ahankali yana kallonta, sai da cup d'in yayi rabi sannan tajaye masa ta mayar ta ajiye, hannunta ta wanko tare da d'auko plate d'in abincin ta yamutsa tana basa abincin abaki, ciyakeyi yana kallonta hawayen nasake zubo masa afuska, ji yake azuciyarsa inama itace mahaifiyarsu ya tabbata da yau ba'a wayi gari ba 'yar uwarsa na cikin wannan halin, amma yazaiyi da tsarin Allah yana fata akoda yaushe shima Allah ya gyara masu halayen mom d'insu, saida Ummi ta tabbatar ya k'oshi sannan tace yaje part d'insa yayi wanka sai ya d'an kwanta ya huta kafin akira sallar magrib duk da tasan kwancin beda fa'ida amma k'ara yasamu rest of mine ko kad'anne,


Har zaifita yadawo yana kallon Basmah cike da tausayinta aransa yanaji inama yanada ikon cirewa Basmah zuciyarta marar tunani ya sakamata wata wacce zata lurar da tunaninta  akan dai dai,


Allah sarki wato shi d'an uwa daban yake komai lalacewarsa za'a so shi, juyowa yayi ya kalli su Billy yace


"Sis kada wanda yayi mata magana idan tafarko kuma kada kushiga sha'aninta kowa yasa mata ido kuyi har kar gabanku, hakan zaisa tafahimci kuskuren data aikata" suka amsa masa da to jikinsu duk a sanyaye,


"Ummi nagode" yafad'a lokacin da yake k'ok'arin barin falon, lumshe idanuwanta tayi alamar bakomai sannan ya wuce ita kuma tayi zaune tana tayiwa su Batool nasiha akan ko meye duniya da kuma rud'anin dake cikinta. Sallamar su papi ce ta maido da hankulansu abakin k'ofar,  bayan gabaki d'ayansu sun amsa sallamar  Batool ta tashi taje ta bud'e k'ofar don tabbatar da muryar wud'an da suka jiyo, tana bud'ewa taga hajia kaka da papi a tsaye cikin farinciki ta rungumeta tana fad'in


"Oyoyo babyn papi" tana dariya, gaba d'aya suma dariyar sukayi papi ya d'aga sandar,


"Cikata kada ki b'allata ja'irar yarinya" Batool na dariya tashigo dasu daga ciki tana fad'in


"Oh ni d'iyar Ummi wannan tsofon nagano bakada buri irin kaga kana dukana da wannan k'afar taka da ta uku, Billy zoki tayani mu karb'eta sai muga yanda zaiyi tafiya balle har ya iya dukan mutane da ita" murmushi Ummi data k'araso wajen da sauri tana yimasu sannu da zuwa tayi jin bakantar da take yimasu had'e da yimasu iso acan gefen wasu kujerun na musamman dake k'arshen falon, cikin girmamawa ta duk'a tana gaishesu 


"Hajia ina wuni, sannunku da zuwa, ya hanya?"


"Lafiya lau Aishatu uwar muminai, ya gida duk lpy kuke?" 


"Lafiya lau alhmdulillah" Ummi tafad'a tare da juyowa inda papi yake zaune ta russuna kai kad'an


"Sannu papi da k'ok'ari, ina wuni, anzo lafiya?"


Cikin sakin fuska da nuna tsantsar soyayyar da yakeji akanta yace


"Lafiya lau 'yatah, alhmdulillah, ya naki k'ok'arin?' Ubangiji Allah yayi maki albarka, ga yara nan duk sun canza masha Allah aci gaba da hak'uri dasu wata rana sai labari in sha Allah" ita dai Ummi batace komai ba sai murmushi da takeyi kanta nak'asa a sunkuye, Billy da Batool ne suka iso wajen hannuwansu d'auke da treys d'in abinci da abunsha, Billy tafara gaishesu sannan Batool itama suka k'ara gaisawa, ruwa suka tsiyayo masu a cup suka mik'a masu cikin ladabi da girmamawa, bayan sun karb'a sun sha, hajia kaka takalli Ummi


"Sannu da k'ok'ari Aisha, ashe abunda yafaru da Bilkisu kenan shine ba'a fad'a mana ba sai jiya dasu mommodu (Mahmoud) sukaje yake fad'a mana, ashe abun har saida aka kwantar da ita asibiti?, to don Allah kiyi hak'uri, d'ane inka haifesa baka haifi halin saba, inba don shashanci irin nataba banga dalilin shiga sha'anin yaraba wai har ace tajima d'aya ciwo, wlh ko kad'an bamuji dad'i ba kuma munyi mata fad'a sosai ai ba'a haka d'an uwa da d'an uwa sai Allah ba'a shiga tsakani, yanzu dubesu atare gwanin ban sha'awa har sun manta da abunda yafaru a tsakaninsu kai kace tagwayeni, shin idan da kunya intaga yanda suke yanzu ai tajita, to don Allah kiyi hak'uri, Allah kashiryeku baki d'aya kuma yayi maku albarka kuma Allah yaganar da ita damu baki d'ai" duk suka amsa da amin, shima dai papi haka yayita ba Ummi hak'uri ita har kunya tafara kamata, 


"Don Allah papi kudena wlh babu komai ai 'yar tace itama, don haka tafaru bakomai dama Allah yatsaro haka zata faru gareta koda kuwa a hannuna ne"


Rungumo Billy papi yayi ajikinsa yana kallonta


"Amaryata sannu kinji? meyasa bakiyi mun wayaba nazo jinya?"


Kallon hajiya kaka dake murmushi tayi tace "saboda nasan bazaka jurewa rabuwa da babyn nan takaba shiyasa nahutar da kai" dariya sukayi gaba d'ayansu har Batool nafad'in 


"Ai kuwa dai my sister kin huta don nasan yana zuwa jinya itama hajia kaka zata biyo bayansa, kinga daga nan amaimakon yayi jinyarki sai yakoma kiwon babynsa don duk abunda aka kawo maki ita zai bawa tacinye" hajia kaka dake faman dariya tace


"Oho dai ku kuka sani, tunda kuncinye abunku ba zancen ayi mani gori" Ummi na murmushi tabar wajen cike da sha'awar rayuwar su papi, cikin zuciyarta kuwa addu'a takeyi Allah yasa ta tsufa lafiya cikin soyayyar juna itada mijinta, k'ofar d'akin dady taturo yana zaune shida su Bilal da Bassam dake faman k'ilbasa shikuma yana kallonsu yana dariya, murmushi tayi sannan ta k'arasa cikin d'akin tace dasu


"Oya Bassam, Bilal kuje gasu papinku can sunzo" ko kafin tarufe baki har sun bar d'akin aguje, suna shiga Bilal ya rungume hajia kaka shikuma Bassam papi, cike da sha'awar yanda suka gansu tubarkallah masha Allah hajia kaka tafad'a tana kallon Bilal dake gaisheta


"Lpy lau mai gidana takobin daga kana lpy?" Dariya Bilal yayi had'e da cewa


"Lpy klw, papi mai sanda ina wuni?" adai dai nan sai ga Mahmud da tund'azu ya hango tsayawar motarsu lokacin da yafito wanka yashigo d'akin jikinsa duk ba k'wari, murmushi yayi tare da duk'awa ya gaishesu cikin natsuwa had'e da mik'awa papi hannu sukayi musabiha, nanfa suka kacame da fira abun gwanin ban sha'awa, 


Allah sarki uwa da d'a sai Allah lokacin sai da mom tafad'owa hajia kaka cikin rai tanajin wani irin abu makamancin rashin jin dad'in ganin 'yar tata awurin, koba komai zata so ace izuwa yanzu dady yayi hak'uri tadawo cikin 'ya 'yanta duk da babu abunda suka rasa awajen Ummi kusan ma inta fahimta kamar yaran sunfi natsuwa yanzu akan da, 


Sosai Mahmud ya fahimci yanayin da hajia kaka tashiga ciki,  murmushi yayi had'e da dafa cinyarta da yake gaba d'ayansu zaune suke ak'asa su kuma akan kujeru yace


"Ran hajia kaka yadad'e yayi k'arko, babyn papi mekike tunani?"


Murmushi tayi masa sannan takalli papi da tund'azu shima ita yake kallo ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa sannan sukaci gaba da firarsu, sai alokacin papi ya lura da Basmah bata wurin, kallonsa ya maido wajen Mahmoud yace


"Kai dakata wai inama bak'auyar matata take ne, tunda muka shigo ko wulgawarta bangani ba ko bata nanne" sai alokacin itama hajia kaka ta ahamo da tunda suka shigo bata ganta ba, amma kamar ta lura da mutum kwance a falo kan kujera, Ummi dake k'ok'arin shigowa dady na biye da ita abayanta tanajin papi na tambayar ina Basmah, gaban yafad'i saboda rashin sanin amsar da zata fito daga bakinsa gashi gaba d'aya ko zancen b'atanta bata sanarwa da dady ba balle halin da take ciki saboda bai dad'e da dawowa ba sai tabari sai zuwa anjima tafad'a masa, da sauri tak'arasa wajen tana murmushi, amma ina har Mahmud yafara fad'in


"Gatacan kwance papi..."


"Eh wlh papi yanzunnan muka samu bacci ya d'an d'auketa, tun safe take fama da matsanancin ciwon kai amma alhmdulillah tasamu sauk'i" Mahmud yaji Ummi tayi saurin katsesa lokacin data k'araso wajen, kallonta yayi cike da mamaki don shi so yayi yafad'a masu abunda yafaru ita kuma ummi tayi kamar bata gane saba. Durk'usawa dady yayi cikin girmamawa yana gaisheda su papi sukuma yaran gaba d'aya suka tashi suka bar falon, 


"Ashha injin da sauk'i? ai da antada ita tunda marece ya gabato, kuma kunsan vaccin bashida kyau alokacin" hajia kaka tafad'a tana kallon Ummi shi kuma papi yace "Allah ya sawake" hakan yasa Ummi ta tashi taje ta rik'o Basmah ahankali hannunta akan kafad'arta ta maida ita d'akinsu batare datayi k'ok'arin tashe taba saboda rashin sanin yanayin da zata tashi aciki,


Nan shi kuma papi da hajia kaka dake matuk'ar jin kunyar dady suka shiga bashi hak'uri akan abubuwan da suka faru tare da nuna masa rashin jin dad'insu, sosai shima dady yaji kunyar abunda yafaru tsakaninshi da mom d'in don koba komai yanda iyayenta suke da matuk'ar mutunci da yanda suke darajjashi amatsayinsa na surikinsu yaci ace yahak'ura mom tadawo d'akinta.


Saida su papi sukayi sallar magrib sannan suka koma gida, suna yaba kirki da mutunci irin na hajia Aisha data had'osu da sabulayye da turarukka masu tsananin tsada bayan tabasu shadda da atamfa masu kyau sunata sanya mata albarka. Koda zasu tafi still Basmah bacci takeyi da suka sake tambayar ta sai Ummi tace masu ai ta tashi, harma  tayi sallar magrib tana gama wane baccin ya sake d'aukarta, k'ilan saboda maganin data shane, hajia kaka taso ta fahimci wani abu amma saita basar tace "Allah yabata lpy" suka amsa da "amin"


Mom kuwa suna dawowa har ta kammala girkinta tayi sallah ita kuma hajia kilishi tana kwancenta akan gado,


"Tashi muje gasu papi can sun dawo" 


Afalo suka tarar dasu zaune akan kujeru suna firar kyawon halin Ummi, gaishesu sukayi tare da yimasu barka da dawowa sannan mom tace


"Papi wai ina kuka jene haka kuka dad'e?" cikin basarwa dady dake k'ok'arin mik'e yashiga d'aki yace


"Daga gidan mijinki muke" cikin jin haushi mom tace


"Kai papi me kuma kukaje yi acan bacin kunsan bani ciki asalima 'yar taku da don ta zakuje kun barota agida, ai wannan saiku saimun reni wlh, haba papi meyasa kuka yimun haka, gaskiya banji dad'i ba" 


"Ke dalla rufemun baki, shashasha to munjene mubada hak'urin shashancin da kika tafkawa abokiyar zaman ki ga yarinyar ta, kewai sai yaushe zaki hankali ne?, shikenan saboda bakya nan bazamuje ba? Duk da d'inbin rashin mutunci da kika aikata" Shikam papi juyowa kawai yayi ya kalleta had'e da girgiza kai sannan ya wuce abinsa batare dayace mata uffan ba,


Cikin fushi mom tabar wajen tana fad'in,


"Wlh nidai hajia baku kyautamun ba, yanzu gashi kun jamun gori ko nakoma gidan Aisha tace mijina baya sona sai da iyayena suka rok'amun ya maisheni" Baki abud'e hajia kaka ke kallonta kafin tace













Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____28💎



  Tafd'i jam Hussaina ashe bakyada hankali, mu kike cewa haka? To shikenan munje d'in, kizo ki dokemu, wannan rashin mutunci har ina, fad'a hajia kaka tadinga yimata ita kuma jin bazata iya tsayawa ta saurara ba yasa tawuce abunta tabar hajia kilishi nan tanata faman bata hak'uri, jin fad'an yak'i ci yak'i canyewa yasa papi fitowa daga cikin d'akin yadawo ya zauna kusa da ita, kallonsa tayi idanuwanta cike tab da k'walla tana fad'in


"Don Allah kaji abunda take fad'a sai kace itace ta haifemu" ta k'arasa maganar tana nuna hanyar da mom tawuce da hannu hajia kilishi na ganin haka itama tabar falon,



Rungumeta yayi ajikinsa yanajin kamar ya kamo mom yayita duka saboda yanda tasa ran babynsa ya b'aci,


"Kiyi shiru haka baby, d'ago fuskarki ki kalleni sai kija numfashinki sosai sannan kifitar dashi ahankali kinji ko?" kamar yanda papi yace tayi haka tayi sai ga hawayen da take nefan fitowarsu tund'azu suka mak'ale sun fito, cike da tausayinta yadinga shafa kanta data d'ora akafad'arsa ahankali sannan yaci gaba da cewa


"Babynah kiyi shirunki, bana son kina yawan fad'a da ita tunda batada hankali, abunda yafi kawai shine muyi mata addua Allah ya shiryeeta, kinsan halina idan nabiye mata sai inyi abunda zandawo ina nadama da kaina, shiyasa kikaga na k'yale ba tare dana tanka taba" 


"Nifa nafara tsorata da halinta alhaji, yarinya sai kace akanta shed'an yake zaune, bata tab'a yin abunda zai faranta zuciyar wani sai dai tata, wannan irin son kai da me yayi kama?"


"Muyi addu'a Allah ya canza mata halayya insha Allah zata dena"


"Allah yasa, amma wannan abubuwan ta sunfara wuce wuri" haka papi ya zauna yanata lallashi da lurar da babynsa yanda zasu dinga hak'uri da halin 'yar tasu har akayi kiran isha'i, papi bai fita masallaci ba da yayo arwala saboda har antayar da sallah sai ya jagoranci hajia kaka sukayi abussu tare.


Shikuwa dady bayan su papi sun wuce d'akinsu Bilkisu ya shiga don yadubo halin da Basmah ke ciki jin cewar da yaji anyi batada lafiya, sosai yake kallonta daya shiga shima kamar yana son gano wani abun amma da yake bacci takeyi bai fahimci komai ba yakoma part d'insa yana fad'in 


"Allah yasawak'e" bayan yayiwa Ummi umurni data biyoshi yana son magana da ita.


Sun kusan minti biyar zaune a falonsa batare da kowanensu yace uffanba, azahiri dukkaninsu kallon makekiyar TV dake jikin bangon d'akin sukeyi amma abad'ini ba haka abun yakeba kowane da abunda yake tunani aransa, gyaran murya dady yayi wacce ita tamaido da Ummi aduniyar tunanin data shiga, ahankali tajuyo tana kallon fuskarsa da haryanzu take kan TV yana kallo...murmusawa tayi kad'an sannan gaba d'aya tajuyo jikinta tana kallonsa, shima hakan yayi bayan ya tsaida kallon da sukeyi waje d'aya, hannayenta biyu yarik'o da hannuwansa yana kallonta yace 


"Rabba'atul bait, inaso insanar dake shawarar da nayanke akan maganar da mukayi dake yau da asuba, sai dai bansan yanda zaki kalli abun ba ina fatar zaki yiwa abun kyakkyawar fahimta" d'an muskutawa yayi ya gyara zamansa  sannan yaci gaba da cewa


"D'azu hajia Hussaina takirani tana bani hak'uri akan abunda yafaru kuma har tayi alk'awarin cewa idan tadawo zata baki hak'uri akan abunda yafaru sannan zakuyi zaman lafiya kamar yanda nake buk'ata, tabbas nafahimci tayi nadama don haka nake son bayan sallar isha'i zanbi bayan su papi inje inyo bikonta, naso ace idan har zata dawo to awani gida cikin gidajena zata tare amma saboda wani dalili nafiso kuyi hak'uri kuci gaba da zamanku atare hakan zaifimun dad'i, to amma ke mekike gani akan haka?" Murmushi Ummi tayi wanda zai tabbatar maka da cewa har cikin zuciyarta tayi farinciki da abokiyar zamanta zata dawo d'akinta sannan tace


"Alhmdulillah dadyn yara, Allah yak'ara maka hak'urin zama damu, kuma kayi daidai da kayanke shawarar zuwa ka dawo da matarka, d'azu bakaji irin kunya da nauyin su papi da suka rufeni ba, gaskiya naji dad'in haka Allah ya zaunar damu lpy kuma ya yafe mana laifukan da muka aikata, saidai wani hanzari ba gudu ba, mezai hana ka tambayeta idan tanada ra'ayin dawowa nan gidan tunda tanuna tanada buk'atar arabamu tunfarko sai kaji ko me zatace akan haka" kwanto da kanta yayi ak'irjinsa sannan yace


"Karki damu da wannan rabba'atul bait ni ra'ayinki shine nawa kuma na tabbata shine nata don haka feel free kifad'amun abunda yakamata kinji ko?"


"Shikenan dadyn yara tunda haka kace to nima ra'ayinka shine nawa"


Cike da jin dad'in amsar data bashi yazagaye bayanta da hannuwansa had'e da manna mata kiss agoshi


"Allah yayi maki albarka rabba'atul bait, ngd da zamowarki always by my side" dariya tayi tana k'ara shigewa jikinsa "wannan abune da yazama dole akaina don haka babu buk'atar godiya" sosai sukayi tighting d'in juna suna jin bazasu iya rayuwa ba idan basa tare.



Ana gama sallar isha'i dady yanufi gidan papi tare da rakkiyar amininsa alhaji Usman, suna isa maigadi yabud'e masu gate suka shiga, bayan sun fito cikin mota da gudu maigadin yak'araso yana gaishesu kasancewar yasan dady kuma duk sadda yazo gidan sai yayi masa alkhairi mai tsoka, bayan sun amsa dady yace yaje ya sanarwa da papi zuwansa, sosai papi yayi mamakin zuwan surikin nasa saboda basu dad'e da baro gidan ba, "Allah dai yasa lafiya" hajia kaka tafad'a tare da mik'ewa tashige d'aki, umurni papi yayi masu da su shigo ciki, bayan sun shigo sun zauna suka gaisheda papi sannan dady ya gabatar da dalilin zuwansu, sai da papi ya kira hajia kaka ya sanar da ita sannan yasa takira masa mom.


Tun fushin da mom keyi har yanzu bata sauko ba sai faman kmbure fuska takeyi, hajia kaka naganin haka tayi tsaki had'e da kwab'a ta maida kallonta ga hajia kilishi,


"Kelishi dama mijin wannan saunarce yazo wajenta, amma naga alamar kamar ita batada buk'atar ganinsa, don haka kifad'a mata zanje na sanar da papinta cewa tace ya sallamesa bazata zoba" mom najin haka tasaki fuska tana kallon hajia kilishi dake kallonta itama tayi murmushin da baikai cikiba tace


"Haba hajia ai ganinan zuwa yanzu, yama za'ayi haka so kike papi ya cimun mutunci?" Sake kallonta mom tayi tare da kwab'a tabar d'akin ranta ab'ace duk da dai k'asan zuciyarta cike yake da farinciki, mom d'ince idan ba haka tayi mataba sai tafito tana faman kumbura masa fuska, cike da zolaya hajia kilishi tace


"Ja'ira anaso ana kai kasuwa, ai nazata fushinki bazai bari kije kigansaba" 



"Hmmm ina zanyar da hajia tamaido mana da aiki baya, ai zanyi yak'i da zuciyata intirsasata yin abubuwan da bata so don cimma burin rayuwata" da sauri ta d'auki wani zumbulelen hijabi tasaka sannan ta feshe jikinta da turarukka masu k'amshin gaske, juyowa tayi had'e da cewa


"Sai nadawo k'awata"


Tunkan ta iso wajen tafara acting d'in marairaice fuska har ta iso falon, kallon dady tayi da tunda ta doso wajen yake kallonta yana so suhad'a ido, wani irin shu'umin murmushi ta sakar masa wanda ya sashi saurin lumshe idanuwansa tare da saukar dasu k'asa gudun kar yayi abun kunya agaban surukansa, gaishesa tayi cikin girmamawa ya amsa tare d'ago kansa yana sake kallonta, a wannan karon labarine ya canza tab'an garenta ganin yanda yayi fresh sosai hadda 'yar k'iba ya k'ara, tsananin kyawon da yayi mata yasa ta lumshe idanuwanta sannan tabud'esu ahankali ta saukar akansa, murmushi yayi mata yana k'ok'arin motsa bakinsa yaji, papi ya fara yimata bayanin abunda ketafe dasu, sannan ya d'ora dayi mata fad'a sosai har hajia kaka na tayashi, bayin sungama suka juyo ga dady da abakinsa suka yimasu nasiha sosai akan muhimmancin aure da kuma kula da hak'k'ok'an juna, sosai jikinsu dady yayi sanyi mom hadda k'ak'alo kukan munafucci tana neman yafuwar dady agabansu. Hakan datayi ya matuk'ar faranta zuciyoyin iyayen nata dama shi kanshi dady, umurni papi yayi mata da tajeta d'auko kayanta tabi mijinta, taso tayi masu musu akan haka saboda bata shiryaba ga kuma maganin da takeso tayi amfani dashi bata sakaba, amma saitayi shiru, har zata mik'e sai taji dady yace


"Papi inba damuwa ina rok'on alfarma idan bata gyaraba abari sai gobe sai inzo ind'auketa saboda kocan ba'a kimtse wajen yakeba sai nasa angyaggyara wajen"


"Shikenan alhaji amma ai da kunwuce tare tunda ga yara goben sai surik'a mata tagyara" ji mom tayi kamar ta watsa ihu ganin papi naneman wargaza mata shirin da takeyi....












Mr's huss@in✍ 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


*_ASSALAMU ALAIKUM, INA MAI MIK'O SAK'ONNIN GAISUWATA GA 'YAN UWANA WRITERS DA SUKA NUNA MUN KARAMCI DA HALACCI TARE DA KULAWA TAMUSAMMAN ALOKACIN DA NARASA MAHAIFINA😭 LOKACIN DA NAKE BUKATAR RARRASHI DA BAN MAGANA SAI GASHI SUNYI TURURUWA SOSAI WAJEN MIK'A TA'A ZIYARSU AGARENI HA'DI DA KYAWAWAN ADDU'O'I ZUWA GA RUHINSA😭, WASU SUN KIRANI AWAYA, WASU KUMA TEXT MESSAGE SUKA TURO, WASU KUMA TROUGH INBOX 'DINA NA WHATSAPP SUKA AJIYEMUN DA'DA'DAN KALAMANSU DA BAN HAKURI AKAN RASHIN DA NAYI, WANDA DUK DA INA CIKIN ALHINI HAKAN BAI HANANI YIN FARINCIKI AKAN KULAWAR DA SUKA BANI BA, SUKA NUNA MUN DAMUWATA DA RASHIN MAHAIFI DA NAYI SUMA TASUCE, NAGODE MAKU SOSAI 'YAN UWANA WRITERS, HAKIKA NARASA MAHAIFIN DAYA ZAMA JIGON RAYUWATA😭 WANDA SHIKA'DAINE KE RARRABE DAMUWATA DA FARINCIKINA BATARE DAYA TAMBAYENI BA "KIYI HAKURI BILKISU KINJI KO?" KODA YAUSHE ITACE KALMAR DA YAKE RARRASHINA DA ITA DON GUSAR DA DAMUWATA,😭 UBANGIJI ALLAH KA RAHAMSHEKA ABBIE,😭😭WANNAN KALMAR DA KAKE FA'DAMUN "KIYI HAKURI" BATA TSAYABA ABBIE SABODA GUSHEWARKA, NASAMU 'YAN UWAN DA SUKACI GABA DA NANATAMUN ITA BAYAN NA RASAKA "'YAN UWANA WRITTERS" KUMA ZANCI GABA DA AMFANI DA ITA HAR K'ARSHEN RAYUWATA ACIKIN DUKKANIN AL'AMURRANA,😢 BAN MANTA DAKU BA READERS KUMA KUNNUNA SOYAYYA DA KULAWA AGARENI SABODA YAWAN KIRAYE KIRAYEN  DA NASAMU AGAREKU HAR SAI DA WAYATA TAYI SHUTDOWN AMMA HAKAN BAI HANA SAK'ONNIN DA KUKA TUROBA TURURUWAR SHIGOWA ALOKACIN DANA KUNNA WAYAR BA, A GROUPS DA PRIVATE DUKA NAYI RECEIVING CONDOLENCE NAKU, NAJI DA'DI SOSAI KUMA HAKAN YA QARA MANI KAUNARKU AKO WANE LUMFASHI NA RAYUWATA KUMA ADDU'O'IN DANAYI AGAREKU TSAKANINA NE DA UBANGIJINMU SHINE KA'DAI YASANI, KUN NUNA MUN SO DA K'AUNA INA FATAN ALLAH YA 'DAUKAKA KOWACE WRITER DAGA CIKINMU, READER'S KUMA ALLAH YA KARE MANA RAYUWARKU DATA AHALINKU YA BAMU ALJANNA DA RAHAMARSA, WU'DAN DA MAHAIFINSU KE RAYE ALLAH YA TSAWAITA MASU RAYUWARSU CIKIN AMINCINSA👏🏻 MUKUMA DA NAMU SUKA RASU ALLAH KAJIK'ANSU DA RAHAMA😭😭 ALLAHU AKBAR SUN RASU ALOKACIN DA MUKE TSANANIN SONSU YA ALLAH KA HA'DA FUSKOKINMU DA NASU A AL-JANNAH FIRDAUSI_*😢👏🏻



💎Page_____29💎



  Tun fitar dady daga gidan bayan sallar isha'i Ummi kefama da Basmah ta tashi amma ina baccinta takeyi hankali kwance, Billy da Batool dake gefe suna kallon yanda Ummi kefaman tarai rayota ajiki tana bubbuga gefen fuskarta ahankali tare da ambatar sunanta, kamar sun had'a baki sukace "Ummi kibarta idan ta tashi zamu kiraki", juyowa tayi fuskarta d'auke da damuwa tace " Anya kuwa kina tunanin lokacin da zata tashi bacci bai d'aukeku ba, kuna gani ko abinci bataci ba, ni ko lunch ma bana tunanin tayi, gaba d'aya babu komai acikin ta wanda ya danganci abinci" tak'arasa maganar kamar zatayi kuka, rufe bakinta keda wuya taji Basmah dake rungume ajikinta tana yunk'urin yin amai kafin ta d'agota tuni ta wanke mata jiki dashi, ko kad'an Ummi batayi k'ok'arin d'agata daga jikin taba saima k'ara rik'ota datayi sosai cike da tausayinta, da sauri su Billy suka nufo wajen suma fuskarsu babu walwala suna yimata sannu, saida tagama a man tsaf sannan Billy ta bud'e wardrobe taciro wani d'an madaidaicin towel Ummi takarb'a tafara gogewa Basmah bakinta ta ajiyeta gefe sannan itama ta goggoge jikin ta, kallon Batool tayi tace


"Kuzo kugyara 'Yar uwarku kafin nadawo" kallonta ta maido ga Basmah data matuk'ar jigata kafin nan tamik'e tafita tana tunanin rayuwar data saka kanta aciki,


Cikin tausayawa suka tada ita zaune, Batool taciro towel d'in wanka suka cire mata kayan jikinta da suka lalace, a gefen gado da take zaune Billy ta rik'eta ita kuma Batool ta shiga toilet tahad'o mata ruwan wanka masu d'an zafi da zata iya gasa jikinta, ita dai Basmah gaba d'aya sai taji tamuzanta acikin su duk laifin da ta aikata baisa suka tsaneta ba sai ma jawota ajiki da sukayi, kallonsu takeyi tanajin k'aunarsu cike azuciyarta, Rirrik'ota sukayi gefe gefe har cikin toilet d'in sannan suka fito, wajen suka fara gyarawa sannan suka fiddo mata doguwar rigar bacci cikin kayanta bayan sun feshe d'akin da turaren room freshners masu k'amshi, 


Ummi ma tana Shiga d'akinta toilet tafad'a tayi wanka, k'aznin da jikinta bai daina yibane yasa takoma toilet d'in ta had'a turarukkan wanka masu ka'amshin gaske ta sake wanke jikinta dasu, sannan ta d'auko burner tajona ga wutar nepa tasa wani turaren itace mai k'amshi ta turare jikinta dashi, kasan cewar dare yayi yasa bata b'ata lokacinta dayin kwalliya ba, kayanta tasa bayan tashafa mai sannan tawuce kitchen ta tad'ora ruwan zafi cikin mintuna biyar suka tafasa tajuye a flaks wasu ta d'iba a cup ta had'ama Basmah tea mai kabrin gaske da yasa madarar sannan tazuba zuma aciki amaimakon sugar kasancewar ita zuma maganin ko wace irin cutace.


'Dakin tanufa hannunta d'auke da cup d'in saiga yaya Mahmud yashigo shida su Bassam da Bilal yana dariyar firar shirmen da suke tayimasa ahanya, sai da gaisheda Ummi daya lura fuskarta na d'auke da damuwa sannan ya juyo yana cewa su Bilal suwuce d'akinsu fuskar nan d'aure kamar ba shine yagama dariya ba, kallon Ummi yayi cikin damuwa da yanayin da yaganta yace



"Ummi lpy kuwa?," cup d'in hannunta yakarb'a kafin tabashi amsa yana mai k'ok'arin bin bayanta zuwa d'akin su Basmah data nufa, cikin sanyin murya take fad'a masa cewa 


"Basmah tafarko amma amaine ya tayar da ita,kuma ba kad'an a man ya galabaitar da itaba, ina tunanin koza'a kira dr. Yazo yasamata drip don natabbata run breakfast d'in safe data tsakura har yanzu bataci komai ba, bana son wannan abun yacutar da ita ko kad'an" dai dai lokacin da suka shigo sukaci karo da Basmah dake fitowa daga cikin toilet d'in idanunta na zubar da hawaye da alama taji duk abunda Ummi ke fad'a, wani irin jirine yasoma d'ibarta da kad'an tafad'i.


Da sauri Ummi tak'arasa wajen tarik'ota tazaunar abakin gado tana jefawasu Billy harara da duk sun mik'e tsaye suna k'ok'arin kaiwa 'yar uwarsu d'auki dake neman fad'uwa,


"Me kukeyi haka da yasa bazaku iya jira tafitoba, to ynzo daban isoba tafad'i taji ciwo fa? wannan ai sakarcine" sosai take yimasu fad'a Basmah nabinta da kallo, azuciyarta tana cewa


"Allah sarki yanzu dama soyayyar da Ummi keyi mani har takai haka, muguwar hud'uba tasa nakasa fahimta, dubi yanda nab'ata mata jiki d'azu amma gaba d'aya bata samu ba saima tausaya mani da takeyi" tunanin tane yakatse lokacin da taji Ummi najero mata sannu ita da yaya Mahmud, dak'yar tabud'e baki tana goge hawayen da suka zubo mata da hannu tace


"Hinm" tana kallon yaya Mahmud da tund'azu ita yake kallo.


Taimaka mata Ummi tayi tasaka rigar da suka fiddo mata sannan takarb'i cup d'in dake hannun yaya mahmud ta kai mata abaki, ko kad'an bata yimata masu ba don ita kanta ta tabbatar da tanajin yunwa sosai, kafin kace me har tashanye tea d'in gaba d'aya, jaye cup d'in tayi daga bakinta sannan tace su Billy suje sukawo mata abinci, nanma Basmah batayi musu ba taci abincin sosai don tacinye fiye da rabin plate sannan tace tak'oshi, kwashe kayan su Batool sukayi suka kai kitchen daga can suka shige d'akin su Bassam don yimasu addu'o'in bacci yayin da Ummi da Mahmud suka shiga bincikar Basmah abunda yafaru.


Saida tayi kukanta mai isarta sannan tashiga labarta masu gaskiyar abunda yafaru bayin fitarta gida. Sosai sukayi mata fad'a tare da nuna mata illar hakan da tayi da kuma cutarwar da zai yimata, Basmah na kuka tarungume Ummi tana rok'onta tayafe mata abubuwan da tayi mata. 


Ba Ummi kad'aiba hatta ya mahmud yayi mama kin sauyawar Basmah lokaci guda tare da godewa Allah daya ganar da ita gaske, lallashinta Ummi tayi tayi fuskarta d'auke da farinciki tace


"Bakomai dama ni band'auki  abun komai ba, duk abunda kike yimun ina kallonsa amatsayin kurciya wanda indai zan iya hak'uri da k'urciyar Bilkisu dole kema sai nayi hak'ur da taki don duk abu d'aya kuke gareni, fatana akoda yaushe Allah yayi maku albarka kuma ya shirya munaku"


Sosai Basmah taji dad'in kalaman Ummi, tanajin kanta awata sabuwar rayuwa tajin dad'i Marat misaltuwa.


Yaya Mahmud kuwa ya qudurta aransa idonsa idon mugayen abokanan Basmah da suka so ruguza mata rayuwa wlh sai yayi qasa qasa dasu. Hannunta yarik'o yana fad'in don Allah Basmah kirik'e wannan gaskiya da Allah ya nuna maki kada kibari shed'an yakoma ribantuwa dake na tabbatar inkikayi haka bazaki tab'a nadama ba har abada kinji ko?, Ummi da kike gani itama wata ni'imace da Allah yabamu ita agurbin da zamu rik'eta amatsayin uwa, matuk'ar mukabita to zamu samu ingantacciyar rayuwa har agidajen aurenmu" jinjina masa kai tayi alamar tabbatar masa da zatayi abunda ya fad'amata. Alokacin suma su Batool suka shigo da niyar kwantawa don bacci ya soma d'ibarsu,


"Yayya Basmah sannu" suka yimata had'e da cewa


"Ummi saida safe"


"Aw. babu arwalar zaku kwanta?" Ya Mahmud ne yafad'i haka tare da mik'ewa zaifita shima yana yiwa Ummi saida safen.


"A'a yaya ai zamuyi, Yayya Basmah kin rama sallolin dake kanki kuwa?" Batool tafad'a tare da shigewarta toilet , dafa kafad'un Basmah Ummi dake gefenta zaune abakin gado tayi tace


"Yawwa tunda kinsamu sauk'i kitashi Bilkisu ta taimaka maki kiyo arwala kirama sallolin dake kanki" ta k'arasa maganar tana kallon Billy.


"To Ummi" dukkaninsu suka fad'a sannan itama tafice tana jaddada masu  karwacce ta sake takwanta batare da tayi addu'aba.



Mom kuwa tunda tasamu dady ya lallab'a su papi suka amince akan zata koma gobe tasaki wata irin ajiyar zuciya da tasa kowanensu juyowa suna kallonta, ficewa tayi daga gurin papi ya girgiza kai yana fad'in "Allah ya shirya mana zuri'a" su kuma suka amsa da amin.


Sallama su dady sukayiwa papi bayan sun ajiye masa kud'i masu yawa suna godiya, k'in karb'ar kud'in papi yayi yace Allah dai yayi masu albarka amma Sam bazai karb'a ba. Dole tasa abokin dadyn yad'auki kud'in cike da yaba dattako irin na surukin aminin nasa.


Bayan sun fito fuskar dady cike da fara'a yace


"Alhmdllh Alhaji kaga yanda hajia Hussaina ta canza ko?"


"Eh wlh masha Allah, idan kam haka yad'ore zaka samu natsuwa sosai acikin gidanka, babban abunda yafi burgeni shine yanda mahaifanta suke da dattako gaskiya kayi sa'ar sarakanan k'warai"


Murmushi dady yayi ba tare da yace komai ba na tsawon mintuna kafin suci gaba da tattaunawa akan wasu harkokinsu na yau da kullum.


Mom nashiga d'akinsu ta cillar da hijab d'inta gefe had'e da sakin wani  shu'umin murmushi tana kallon hajia kilishi, hararar ta tayi kafin tace


"Shifa wannan murmushin tawajena?"


"Hmm kibari kawai, Kinga yanda alhajina ya koma, sai kace irin 'yan 30yers d'in nan yayi wani irin fresh kaman bashi ba, hmmm har zan yadda ace shearing d'ina nakeyi da wata! Wlh yanzu yak'in zai soma don sai na tabbatar da cewa koda kissa koda munafurci alhajinah yazama mallakina nikad'ai, ashirye nake dana sadaukar da komai nawa akansa don nikaina nahango tsantsar soyayya da kaunar da yake yimun, kawai shiga tsakanin mune akayi, kinga yanda yake nunamun irin missing d'ina da yayi?" 


Wata irin dariya hajia kilishi tayi da tasa papi da hajia kaka dake palou zaune juyowa suna kallon b'angaren da sutin kefitowa girgiza kai papi yayi kafin yace "Baby bari nashiga daga ciki kafin wud'annan shashashun sufasa mani dodon kunne" mik'ewa itama tayi tana fad'in 


"Ai saidai mutafi tare don idan naci gaba da zama anan zan iya shiga d'akin nacicci masu mutunci, yaran wofi kawai da basusan sun girma ba"


Hannunta tamik'awa papi yarik'e sannan ta tashi suka nufi d'akin baccinsu tanaci gaba da mitar irin abubuwan da sukeyi kamar wud'anda basa da 'ya'ya agabansu....






 









*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____30💎


 

  Yanzu ke har kina tunanin cewa Aisha zata iya saken da zaki mallaki alhaji ke kad'ai ranki? Kar kimantafa itace first wife d'insa, idan har ke da kika shiga gidan amatsayin matarsa ta biyu kina jin haushin shearing d'insa da wata mekike tunani ga wacce ita yafara sani arayuwarsa kuma ita tafara saninsa, gaskiya son kanki yayiwa qawata ina laifin kema kinemi aza taki kujerar acikin zuciyarsa ta yanda zaki samu matsayin da bazai iya musawa duk wani muradinki ba,


'Bata fuska  mom tayi kamar maishirin yin kuka "Haba taya zakice nacika son kai don nanu maki ina buk'atar alhaji yazama mallakina nikad'ai?, A gaskiya naji zafin kalamanki sosai don sun b'ata raina matuk'a" tak'arasa maganar cikin jin haushin hajia kilishi, mere baki itama tayi kafin tace "ikon Allah naga ai gaskiyace nafad'a ko?, nifa duk tugguna da makirci basa hanani fad'in abunda ke raina don haka inzaki iya to ki had'iyi bomb saiki fashe da alama bakyada buk'atata yanzu, dama donki na iso garinnan kuma gobe tunda sassafe zan tafi abina" tana gama fad'ar haka itama tamik'e cikin fushi tana k'ok'arin har had'a kayanta, ganin da gaske takeyi yasa mom ta sauka daga nata fushin sanin da tayi akan wannan maganar aminiyar tata zata iya fushi da ita natsawon lokaci, kuma bata buk'atar haka ayanzu, kamo hannunta tayi tana fad'in.



"Kai aminiya! Nifa ba haka nake nufi ba, taya za'ayi alamurrana su iya tafiya dai dai bisa tsari idan babuki, to shikenan kiyi hak'uri" dakatawa da had'a kayan tayi tana harararta da wutsiyar ido, mom tayi dariya


"Nadaiji kuma nagode, yanzu zauna sai muyi magana ko?" Zaunawa tayi tana kallonta kafin nan su tuntsire da dariya had'e da tafa hannuwa,



"Ja'ira ai nazata tunda nafad'a maki gaskiya fushi zakiyi dani" kilishi tafad'a tanaci gaba da tuntsirar dariya"


"Kome ma zakice naji, ai mai so gawani yaga takansa, yanzu dai so nake kid'orani a hanyar da zata taimakona, wlh nidai natsani Aisha da 'ya'yanta har ga Allah nidai bana son ganinsu" shiru hajia kilishi tayi tana kallon mom sannan tamatso kusa da ita tana rad'a mata wasu maganganun a kunne na tsawon lokaci kafin tad'ago tace


"Don haka kiyi k'ok'arin aiwatar da plans d'in da muka tsaro cikin lokaci sannan wannan dana fad'a maki su biyo baya" tsabar jin dad'in abunda kilishi tafad'a mata yasa tarungumeta tana yimata godiya kamar wacce akayiwa abun arzik'i daga bisani kuma suka shiga kimtsa kayansu kafin gobe kuma kowace tayi gidan mijinta.


Cike da fara'a dady yadawo gidan, a lokacin gaba d'aya yaran sunyi bacci Ummi kad'aice zaune a d'akinta bayan tagama shafa'i da wutiri  tana tilawar qur'ani, saida ya lek'a duka d'akunan yaran sannan ya shigo d'akin Ummi, da sallama abakinsa ya k'araso cikin d'akin tare da zaunawa gefen gado yana sauraren daddad'ar k'ira'ar Ummi dake k'ok'arin ganin takai k'arshen aya saboda shigowarsa.


Bayan takammala karatun tarufe Qur'anin had'e da juyowa tana kallonsa fuskarta d'auke da murmushi tace


"Sannu da dawowa dadyn yara"


"Yawwa rabba'atul bait, meyasa kika katsiye karatun, sai nakejin salon k'ira'arki tamkar ta sheik Abdul-basid Abdus-samad dake su'udiya, gaskiya nakan k'ara jin k'aunarki araina saboda yanda kike rik'o da addininki, ya Allah kada kabani damar sake rayuwa aduniya matuk'ar babu rabba'atul bait atare dani..."


Cikin hanzari Ummi tayi k'ok'arin rufe masa baki saboda gudun kar ya k'arasa maganar dake fitowa daga cikin bakinsa, amma ina!.  har ya k'arasa yana dariya had'e da d'an ciza tafin hannunta dake rufe da bakinsa, shagwab'e fuska Ummi tayi kamar wata yarinya tana yarfi da hannun, kyakkyawar runguma dady ya kaimata har lokacin yana dariya, k'amshin jikinta da yake shak'a ya sashi lumshe idanuwa yana fad'in "dadyn bb is sorry" shima wani marairaice muryar tasa yayi alamun ban hak'uri, hakan yasa ta tintsirewa da dariya tare da tighting d'insa sosai tana fad'in "kai ko!"



Sunjima ahaka suna warming d'in jikin junansu kafin Ummi ta tashi tana cewa


"Yaa salaam kagani ko dadyn yara gaba d'aya kasa na shagaltu batare da nabaka dinner kaciba, am so sorry plz made mistake" ta k'arasa maganar tare da barin d'akin.


Tunda tafara magana ya kwantar da jininsa akan gadon k'afafuwansa ak'asa yana binta da kallo har tafice, a hankali ya rufe idanuwansa yana tunano karamci, halacci da hak'urin da Ummi take dashi, tabbas idan har yardarsa zatasa Allah yabata aljannah to baya tantama da cewa ita 'yar aljannah ce d'ari bisa d'ari domin ya yarda da ita fiye da kansa aduniya, ahaka Ummi tadawo ta samesa, murmushi tayi kafin ta k'arasa wajen, gadon tahau cikin natsuwa tare da hura masa iskan bakinta ahankali afuska, batare daya bud'e idanuwansa ba yasa hannuwansa gaba d'aya ya rungumota ajikinsa, k'ok'arin zillewa tayi cikin wata irin kasalalliyar murya yace


"Relax rabba'atul bait!, so nake kifad'amun, wace irin baiwace dake wacce tasa zuciyata bata gajiya da soyayyarki haka kuma gangar jikina kullum take mararinki?" Wani irin farincikine ya mamaye ilahirin zuciyar ummi dajin wud'annan dad'ad'an kalamai dake fitowa daga bakin maigidanta, sassanyar ajiyar zuciya tayi kafin tace 


"Ai wannan baiwar kaine sirrinta domin akanka kad'ine take tasirantuwa" tana gama fad'ar haka tayi sauri mik'ewa daga jikinsa cike da jin kunya.


"Ka taimaka kataso kaci abinci kada yunwa takama mani kai" 


"Ai idan dai har ina tare dake babu wata yunwa data isa taziyarci rayuwata" 


"Gaskiya fa dadyn yara?" 


"Sosai kuwa rabba'atul bait" yafad'a yana dariya tare da biyo bayanta zuwa parlour, 


Saida Ummi ta tabbatar tacikawa dady tumbinsa sannan takwashe kwanonin takai kitchen, dawowa tayi tana kallonsa tace 


"To yallab'ai sai da safe ko?, nafara jin bacci naziyar toni" a hankali yamik'e tare da rik'o hannunta suka nufi bedroom d'inta, kallonsa tayi ya wani matse fuska,


"Dadyn yara ya haka?"


"Anan yau zan kwana"


"Amma kasan...." 


"Shiiiiiii" yayi saurin rufe bakinta da d'an yatsansa, turo bakin tayi tayi tare da had'e girarta ta sama, murmushi yayi batare da yace mata komai ba don yafahimci kome take nufi, shikam ak'ida irinta Ummi nabashi mamaki, duk da yasan don gyara tarbiyar yaransu takeyi amma ai shima yaci ace tabarsa yanayin yanda yake so a part d'in ta.








 



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Where are u my Tee-tee *{Teemah gabs}* here are my greeting goe's to u, u're such a wanderful, kindness and a lady with classy💁🏻 dt i will never ever forget in my entirely life. Thanks for been by my side, with u i will be always being bless in my writing, sincerely u're so nice and am proud of you. JAZAKILLAHU KHAIR👏🏻_



💎Page_____31💎



    Yau kam Ummi tasha mamaki sosai da yanda dady ya sarrafa dukkanin soyayyar da yake yimata don ganin ya isar da sak'on acikin k'undin zuciyarta, kuma alhmdllh sak'o ya isa don yanda Ummi tasha soyayya da tarairaya awajen dady yak'arawa mas kima da daraja sosai acikin zuciyarta ta yanda take jin duk duniya babu wani namiji dake iyayin tasirin da yayi acikin zuciyarta idan bashi ba, wata irin sabuwar duniya take jin kanta aciki wacce ta sakata cikin farinciki marar misaltuwa adaren jiya. Da asuba dady ya tashi shima cikin yanayin farincikin da bazai iya misiltashi ko fassarawa ba, murmushin da baisan lokacin daya kucce masa ba ya saki tare da mik'ewa yafad'a toilet, wanka yayi tare da d'auro arwala akai, yana fitowa ya tasheta itama, saida yaga tashiga toilet sannan ya fito yatada yaransa suma sukayi arwala, hannun Bilal da Bassam yarik'o suka nufi sashen yaya mahmud dake k'ok'arin rufo k'ofar d'akinsa da zimmar zuwa masallaci, gaba d'ayansu suka wuce cikin sauri kasancewar har liman ya tayar da sallah.



Itama Ummi koda tafito d'akin su Bilkisu tafara lek'awa ta tarar suma sun tashi har sun tada sallah sannan itama takoma d'akinta, bayan tagama sallah tadinga kwararo wa kanta da maigidansu da 'ya'yansu addu'o'in neman tsari da samun nasara da zaman lafiya acikin zamansu da rayuwarsu.


Koda dady suka dawo masallaci kai tsaye ya wuce part d'insa yayin dasu kuma su Bassam sukabi yaya mahmud d'akinsa yanayi masu tilawar azkar d'in safiya da marece.


Bilkisu kuwa tana ganin safiya tafara wayewa ta tashi don yin aikace aikacen da suka sabayi, juyowa tayi tana kallon Basmah da sallame sallarta kenan tad'ora kanta agefen gado tace


"Yayya Basmah morning, ya k'arfin jiki?"


"Alhamdulillah Billy" tafad'a tana murmushi, itama Batool gaisheta tayi tayi mata yajiki sannan suka soma da gyaran d'akin, duk aikin da sukeyi Basmah nakalle dasu gwanin ban sha'awa yanda suke taimakekeniyar junansu wajen aikin, suna kammalawa suka nufi hanyar fita d'akin don cigaba da aikace aikacensu, muryar Basmah suka tsinkayo tana fad'in,


"Ina kuma zaku tafi kubarni 'YAN UWANA?" Cike da mamaki duk suka juyo suna kallon fuskarta dake d'auke da wani d'ankarqmin murmushi dake nuna nadamarta bisa abubuwan dake faruwa, 


"Kada kiyi mamakin jin wannan kalma abakina matuk'ar ba wariya kuke son yimun ba, nayi nadamar dukkanin abubuwan da nakeyi kuma nagane cewa ku 'YAN UWANA NE na hak'ik'a, especially ke Billy danake d'auka kamar babu alak'a atsakaninmu, ina rok'onki daki manta da duk abunda yafaru kirik'eni a amatsayin 'yar uwarki dake matuk'ar sonki" tak'arasa maganar had'e da bud'e mata hannuwanta.


Lumshe idanuwa Billy tayi suna kallon kallo ita Batool tanajin wata irin sabuwar soyayyar 'yar uwarta kwance fal azuciyarta, da gudu Billy tak'arasa wajenta tare da shigewa cikin jikinta, wasu zafafan hawaye suka zubo mata ahankali tamaida hannayenta tarungume Billy tana jin sanyi azuciyarta, "kiyi hakuri kiyafemun duk.." take fad'a hawayen naci gaba da zubo mata afuska, da sauri Billy takatseta ta hanyar cewa "Ya isa haka Yayya Basmah, ni bantab'a jin cewa kunyimun laifin daya kai kinemi yafiyata ba, akullum ina kallon ku ''YAN UWANA NE  da kuka isa gareni da kuma d'an uwana, komai yawuce yayya  abunda ya kamacemu shine mufuskanci gaba"


Cikin jin dad'in kyawawan kalaman Billy Batool tayi tafi tace


"Gaskiya kun matuk'ar burgeni, to nikuma da kuka bari agefe waye zai rik'emun hannuna" Basmah na murmushi tayi mata alama da idanuwa tazo tana mai  mik'o mata d'ayan hannunta, da sauri itama tak'arasa wajen tarungume su tana fad'in


"Ku 'YAN UWANA NE da banida kamarku, kuma ina matuk'ar sonku sosai"


Ummi da taji har yanzu bataji motsin yaran taba tafito don jin ko lafiya suke, sai gashi tatarar dasu cikin yanayin da yasa lunkuwar farin cikin da take aciki, gyaran murya tayi kafin gaba d'ayansu sujuyo suna kallonta tace


"Agaisheku yaran dady Allah dai yayi maku albarka, shine kuka zo kuka tasa auntynku agaba kuma neman karyamun ita baccin kunsan batajin dad'i, murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta cike da jin kunyar ummi kafin tace


"Ai alhmdllh naji sauki sosai Ummi"


"K'arasowa daga ciki Ummi tayi ta zauna gefen gadon kusa da inda Basmah ke zaune ak'asa sukuma su Batool sun koma acan gefenta suna gaisheda Ummi, Dafa kanta tayi lokacin da itama tabud'e baki tana gaisheta, cike da fara'a ta amsa masu gaisuwar sannan takalli Basmah.


"Basmah kin tabbatar kinsamu sauk'i babu abunda ke damunki yanzu?"


"Eh ummi naji sauk'i sosai sosai"


"Masha Allah" tafad'a tare da juyowa tana kallon su Billy


"Maza kuje ad'ora breakfast ganinan zuwa yanzunnan, Basmah ke kuma ki kwanta kid'an huts kafin anjima kinji ko, Allah yak'ara sauk'i?" Tana gama fad'ar haka bata jira amsarsu ba tafi ce su kuma suka nufi kitchen don cika umurninta, ganin haka yasa itama Basmah tabi bayansu bayan tacire hijabin dake jikinta batare da takoma baccin kamar yanda Ummi taceba, har ga Allah Basmah bata iya girkiba don haka batasan mezata fara dashi ba, batare dama tashiga kitchen d'in ba tawuce store ta d'auko tsintsiya da moper tafara gyaran falon duk da shima d'in bawani iyawa tayi ba tunda mom basasu takeyi ba.


Kai tsaye Ummi nafitowa tawuce part d'in dady, zaune ta iskoshi gaban computer dake can gefen gado yana wasu 'yan cike cike ta e-mail, sallama tayi ya d'ago kansa had'e da amsa sallamar yana mai jifarta da wani irin murmushi dake tabbatar mata da yalwatuwar farinciki atare dashi, murmushin itama tamayar masa tana mai k'arasowa inda yake tare da zaunawa agefen gado.


"Barka da safiya dadyn yara, antashi lpy?" Tafad'a cikin wata iriyar muryar dake d'auke hankalin duk wanda ke sauraro, a hankali dady ya juyo da kujerar da yake zaune akai ya matso kusa da ita da yake irin kujerar nance mai taya da ake amfani da ita amafi yawancin offisosa, hannuwanta biyu yarik'o da hannayensa yace "yawwa rabba'atul bait, tashin safiyata kuwa alhmdllh, ya jikin 'yarki Basmah gaba d'aya jiya nashafa'a da intambaya, injin tasamu sauk'i"


Sai da ummi kad'an b'ata rai kafin tace "tasamu sauk'i sosai, amma dady yayi laifi tunda bai tambaya ba sai yau kuma dole yakarb'i hukunci ahannun umminta" turo idanuwa yayi kafin ya kama kunnuwansa duka biyun yana fad'in


"Dady is sorry, ayimai afuwa don bazai iya jurewa hukuncin da rabba'atul baiti d'insa zata yimasa ba" wani irin far ummi tayi da idanu sannan tace "za'a duba idan k'orafi zai karb'u" anan take sanar dashi addu'ar da yakeyi tare da burinsa akan yaransa to  Allah yakarb'a masa, ayanzu tana tabbatar masa da 'ya'yansu sun zama abu d'aya, wato tsintsiya mad'aurinki guda, no more problems or crasis a tsakaninsu, ta labarta masa yanayin da tariskesu aciki da wasu maganganun da tad'anji sunayi dake nuni da sulhun da suka samu.


Tsabar farinciki yasa dady ciro mak'uddan ku d'in da baisan ko nawa bane agefen aljihunsa ya damk'awa Ummi ahannu "ungo wannan tukuicin albishir da kika bani, idan hakan ya tabbata ko ayanzu Allah yakarb'i rayuwata alhmdllh, nasan banbar matsala abayana ba, kuma inada yak'inin nabar ingantacciyar zuri'ar da zata sakani alfahari" ya k'arasa maganar yana goge hawayen dake fita tare da dariya lokaci guda afuskarsa, hannunsa itama tarik'o tana jinjina kanta alamun tabbatar masa da abunda tafad'a, sannan ta mayar masa da ku d'in acikin tafin hannuna, "Aa dadyn yara kabarsu iya farincikin da naga kasamu ya wadatar dani agurbin tukuicin da zakayimun, sunjima suna tattaunawa akan maganar nan yake damar da ita barin dawowar mom yau, murna da fatan alkhairi tayi masa kafin nan su sake shagala cikin duniyar soyayya ta ma'aurata, ummi kam matuk'ar mamaki tashashi da irin wannan salo da dady ya b'ullo dashi tsakanin jiya da yau, 


Ummi nadawowa har sun kammala gyara ko ina tare da had'a breakfast ko waccensu tayo wanka suna jiran fitowarsu, Ab'angaren mahmud ma haka akayi saida ya tadasu Bilal daga baccin da suka koma yayi masu wanka sannan shima ya shiga yayo wankan, yana kammala gyarawa ya rik'o hannuwansu suka nufi part d'in Ummi, suna shiga suka hango kowa akan dining table suka d'ai ake jira sai dady, gida ummi sukayi sannan suma suka samu wuri suka zauna akan dining table d'in ana d'an tab'a fira kafin dady yafito, shigowarsa yasa kowanensu yayi shiru har ya k'araso wajen shima yajawo kujera yana kallonsu d'aya bayan d'aya, cikin natsuwa suka shiga gaishesa yana amsawa had'e da mik'awa 'yan mazan hannu, plate Ummi tad'auka tafara sieving d'insa, pancake ne da yasha zuma a samansa, sai had'in ruwan coffee data yimasa a cup sannan ta d'auko wani d'an k'aramin bowl tazuba masa ferfesun Neman kaza da yasha kayan yaji sai k'amshi ke tashi ta ajiye masa agabansa, kallonta yayi had'e da cewa "thank you rabba'atul bait, Allah ya saka maki da alkhairi" Amin ta amsa masa dashi tana k'ok'arin cigaba da zuzzuba masu abincin Billy tayi saurin mik'ewa had'e da karb'ar sarving spoon d'in dake hannunta tana fad'in,


"Ummimu kizauna kihuta kema bari nak'arasa" sai da Billy ta tabbatar da tazubawa kowa nasa yanda zai ishesa ta ajiye masa sannan takoma tazauna, dadyne ya d'ago kai yana kallonta cikin yabawa da natsuwar da Allah yayi mata yace "Agaisheki Allah yayi maku albarka amma ke ina naki banga kinzuba ba?" Gaba d'ayansu suka amsa da amin Billy ta amsa masa da cewa "Dady nida my twiny zamuci" tana mai saka cokalinta a plate d'in Batool dake kusa da ita, tunda aka fara cin abincin babu wanda yakoma cewa uffan har aka kammala, nan take Billy da Batool suka kwashe kayayyakin da akayi amfani dasu suka kai kitchen bayan sun dawo, dady yayi gyaran murya alamun yana son yin magana dasu mai muhimmanci, nan take kowanensu yanatsu had'e da tattaro hankalinsu agaresa, cikin jin nauyin abunda keson fitowa daga bakinsa yayi masu bayanin dawowar mom yau tare da nasiha mai ratsa zukatansu akan suji tsoron Allah suso 'yan uwansu kuma suhad'e kawunansu hakan zaisa hankalinshi ya kanta kuma asirinshi yarufu duniya da lahira, sosai kalamansa sukasa ummi jin tausayinsa kuma yaran suka yimasa alk'awarin cewa zasuyi yanda ya umurcesu da yardar Allah wanda hakan ya matuk'ar k'ara masa natsuwa sosai.


Dubu d'ari ya fiddo ya mik'awa ummi dubu hamsin yace tayi 'yan wasu saye saye da gyare gyare da take da buk'ata, karb'a tayi tana mai godiya da yimasa addu'a sannan ya mik'awa mahmud dubu hamsin yace yaje ya kaiwa mom d'insa itama idan akwai abunda take buk'atar saye. Makullan part d'in mom ya mik'awa mom yace tabawa Basmah suje su gyaggyarawa mom part d'inta tare da sake ciro wasu dubu hamsin yaba mahmud yace ya d'auki dubu ishirin dubu talatin kuma yaje da Basmah da k'annenta su siyo duk abunda suke buk'ata. Godiya sukayi masa sosai tare da addu'o'i sannan yamik'e don wucewa office, har mota Ummi tarakasa yayi mata bye bye kiss sannan ya shige cikin motar tana yimasa Allah ya kiyaye, Allah sarki uwa da d'a sai Allah wani irin farincikine yabayyana a fuskokin yaran mom wanda yakasa b'oyuwa saboda jin dad'in mahaifiyarsu zata dawo.


Mom kuwa safiya na wayewa ko sallah batayi ba ta d'auko gumbar da hajia kilishi takawo mata da tazo ta sirrin mallaka ta dameta tsaf tashanye tana faman nishi saboda yanda cikinta yacika da ita har yana neman d'ad'ewa.


Dariya hajia kilishi tashiga yimata tana yimata kirari "kaga amaryar alhaji da kanta, yau sai gidan alhaji akwan kwad'i amarci, wayyo alhaji daga yau kazama na Hussaina basa kanka asare aduk inda kashiga..."


Murmushin k'arfin hali mom da ko motsi mai k'arfi bataso tayi saboda yanda cikinta ya babbak'e mata.


"Kai wlh Allah ji nake da bansha abunnan ba, kinji yanda zuciyata ke tashi kuwa? gashi ko shed'ar kirki bana iyayi Allah sa dai bazata sakani zawo ba wannan sheri har ina, wlh Allah badon alhaji ba da kud'i bazan iya shanye wannan abun ba!"


"Banza kya fad'i haka mana, yo ai naga kezai amfana bani ba, idan ma baki shaba ai don kanki, ni bari ma natambayeki ina kika kai d'ayan na ruwa? Yafi wannan gumbar fa aiki kuma kinsan yau kike da tabbacin zaiyi maki amfani don nasan dole alhaji ya kwashi amarci, kinga daga nan karagar tadawo hannunki sai yanda kikace agidan"


"Hmmm bari kawai k'awata yana nan har namatsu isha'i tayi wlh, ki nake kamar ma nasakashi yanzu don zaifi aiki ko?"


"Aa ban fad'a ba, inkikayi bansaki ba, wannan irin gaggawa har ina, kiyi amfani da wannan lokacin kafin dare kije anyi maki qunshi da kitso mana, in kuma ba haka ba kyaji da rawar kanki ke kad'ai"


Allah sarki mom indama kin raba kanki da wahalar wannan shaye shaye da ture ture don kam dady yariga daya d'an d'ashi amarcinsa da tsohuwar zumarsa kuma rabba'atul baiti d'insa.


 















 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_ALHMDLLH I feel so bless to have u my fans, u made me so happy for ur sweet and amazing comment in my previous page, ubangiji Allah ya albarkaci kowannenku tare da ahalinsa, MOM luv's u 🤣🤣🤣🤣 tana mik'o gaisuwa da babbar murya, STAY ALWAYS BLESS MY FANS😘💋😘_



💎Page_____32💎



   Mom dai ba haka tasoba atunaninta idan tasaka maganin yanzu zaifi mata aikin don haka da taji abunda kilishi tafad'a sai takaici yasa tabar wajen cike da jin haushi, ita kuma hajia kilishi ta shareta ba tare data kula taba taci gaba da ida har had'a 'yan kayanta,


Ummi kam ya mahmud tabawa kud'in da dady yabata tace idan yafita yabiya ta banki ya kaimatasu, tunda akayi maganar mom zata dawo yau cikin Billy ya murd'a tare da fad'uwar gaba amma saboda kada tanuna yanayin da take ciki 'yan uwanta suji ba dad'i yasa tadanne dukkanin damuwarta tana tayasu murnar dawowar mom d'insu,  shikenan ta tabbata daga yau farincikin da suke ciki ita da umminta da d'an uwanta zai tawaya, gefen da takoma tayi shiru tana wannan tunanin yasa yaya Mahmud fahimtar halin da take ciki, matsowa yayi akusa da ita tare da kallon fuskarta yana had'a girarsa tasama.


"Meyake damun 'yar qanwa tane?" Yafad'a cikin yanayin da yasa Billy sakin murmushi, lumsa idanuwanta tayi sannan tabud'e tana kallonsa tace


"Me kuwa zai dami qanwar nan taka matuk'ar tana tare da kai?"


"Hmm! to idan hakane tunanin me takeyine? Kodai tasamu wani saurayinne daya d'auke mata tunani"


"Tab...hakan ba abu bane mai yuyuwa ba, domin babu wani saurayin da zai iya fara tunkarata matuk'ar bata hannun yayana ya biyo ba" dafe goshi mahmud yayi had'e da game hannuwansa waje  d'aya yana begging d'inta.


"Narok'eki kisanar dani damuwarki my sis kada kisa nayi tunanin ko k'anwata aure takeso" duk da yasan dalilin shiga wannan damuwar tata yafad'i hakan ne don yasan yanzunnan zata saki damuwar saboda bata son zancen, ai kuwa yana rufe baki tab'ata fuska had'e da turo baki, dariya yayi yana nunata da d'an yatsa kafin yace "Bilal, Bassam kuzo kuga fuskar auntyn nan taku, kufad'amun da metayi kama" da gudu Bilal ya rugo yana turo idanuwansa awaje kafin yace


 "Lahh yaya kamar fuskar baby Japanese d'innan da muka kalla yau da safe...kai kuma k'aryane da chaki chan tayi kama" muryar Bassam daya k'araso wajen sukaji yana fad'ar haka, 


Rufe idanuwa tayi ta rumk'e hannuwanta tasaki wata k'arar da tasa Bassam da Bilal guduwa suka b'uya a bayan yaya Mahmud dake kwasar dariya har da tuntsirawa yana rik'e ciki, ganin haka yasa suma suka biye masa sunata faman yimata dariya, cikin jin haushi da takaici tajawo throw pillow d'in dake kan kujera ta nad'awa ya Mahmud shi agefen kafad'a, mik'ewa yayi tare dasu Bassam suna zagayen kujerun ita kuma tana biye dasu tana neman  duka masu pillown har lokacin basu dena yimata dariyar ba, ganin bazata k'yalesu ba yasa suka shige kitchen wajensu ummi dake tsane plates d'in dasu Basmah ke wankewa, kallon fuskokinsu yayi yaga suma dariyar sukeyi don duk suna sauraren abunda kefaruwa tund'azu, Billy na shigowa taga gaba d'ayansu suna dariya har da Ummi aikuwa a fusace tayo kansu Bilal, Ummi dake k'ok'arin b'oye tata dariyar tayi saurin dakatar da ita, kunnuwan Bassam da Bilal takamo mata takawo agabanta tana fad'in 


"Maganar gaskiya yaya baka kyautaba, yanzu har Bilal nada bakin kiran Bilkisu da baby Japanese, shi bakaga tashi fuskar bane?, shi kuma wannan hadda wani cewa chaki chan don tsabar rashin ji"


Maburkakin dake gefenta tad'auko tamik'a mata tana dariya


"Allah ungo wannan kizazzane su"  ai kuwa kamar jira Billy takeyi, tana karb'a tafara tsalawa Bilal shi a d'uwawu da sauri ummi ta sakesa ya fice aguje haka shima Bassam so biyu ta tsulamasashi ajiki zatayi na ukku ummi tasakesa shima yafice yana fad'in, 



"D'aya na fuskar chaki chan dana fad'a shi kuma d'ayan dukan na fuskar jet-li ne daban fad'a ba"


Ai kuwa gaba d'aya suka sa dariya, girgiza kai ummi tayi tace "Bassam, Bassam Allah dai ya shirya" kan yaya Mahmud tayo dake gefe rik'e da maburkakin shima zata doka masa yayi saurin tsayawa da dariyar had'e da rik'e kunnuwansa yana fad'in "wayyo aunty Billy am sorry natuba" jump frog yafarayi yana cigaba da fad'in sorry aunty Billy, yanda yakeyi sai yabata dariya ai kuwa da wayo da wayo yasamu yafice daga kitchen d'in.


Kallonta Batool tayi kafin tace "To jet-li ai seki zubar da makaman fad'an tunda yayi maki wayau ya gudu" tana dariya takarb'i aikin da Yayya Basmah keyi tana fad'in "kinjita ko ummi?"


"Tsakanin kune ai kunfi kusa" ummi tafad'a, kallon Basmah tayi alamun takawo mata k'ara itama tabud'e hannuwanta alamar baruwana, 


Cike da nishad'i suka kammala aikin, bayan sun gyara ko ina tsaf sannan gaba d'ayansu suka nufi part d'in mom don su gyara kamar yanda dady ya umurta. Kallon Billy Batool tayi tace


"Twiny kishiga bedroom d'in mom kigyara tunda kinsan bawani gyaran gado na iyaba, muje in d'auko maki sabon bedsheet d'in da zaki shimfid'a akai, ke kuma yayya Basmah sai ki shiga kitchen kigyara ni kuma sai ingyara d'akunanmu da palour ko kuwa?" kasan cewar Basmah bata fiye son surutu ba yasa ta gyad'a mata kai kawai batare data tanka taba.


Cikin gwanewa Billy tagyarawa mom d'akinta gwanin ban sha'awa, bayan ta wanke toilet d'in dake cikin d'akin shima, fitowa tayi tasamu itama Batool ta kammala gyaran d'akunansu tana gyaran palour, sannu my twiny har kin fito, "Eh bari naje nataya yayya Basmah tunda naga kema kin kusa idawa"


"Ok babu matsala" da haka Billy tawuce kitchen ta rik'awa yayya Basmah suka k'arasa goge goge, suna fitowa ko ina ya gyaru tsaf yanda ake buk'ata suka nufi hanyar ficewa zuwa part d'in ummi, kallonsu Billy tayi tace


"Yayya Basmah banga an gyara store ba, kuma baku canza cuttings ba" rausayar dakai tayi kafin tace "Billy am totally tired, kawai abarshi gobe magyara" kallon Batool tayi itama dai hakan d'in tafad'a tana k'ok'arin zaunawa.


"To kuzo kujirani ni bari ingyara don gaskiya bai kamata abar wajen ahaka ba." Da sauri da sauri tashiga store d'in suna biye da ita ta dinga jaye kwalayen abinci da buhu huwan tana sharewa, ganin haka yasa suma adole suka taimaka mata aka gyara wajen sannan suka rufe part d'in, suna koma wa part d'in ummi kowacensu tayo wanka, bayan sun kimtsa yaya Mahmud shima yafito cikin shirinsa da yayi mugun kyau kai kache shuwa arabne, wata bugaggiyar shaddace sanye ajikinsa kalar ruwan kwai sai shining da d'aukar ido takeyi, tasha design d'in d'unki brown colour, sai takalmi suma brown colour k'irar Italy da hularsa itama Brown colour cikinta anyi masa design da zare shima kalar ruwan k'wai, yayi matuk'ar kyau sosai.


Da sauri da sauri ya shigo, yana gyara zaman agogonsa a tsintsiyar hannunsa,


"Kuma inane? Basmah, Batool, my sis kufito mutafi sauri nakeyi, so nake idan nakaiku inbiya wajen mom inkaimata sak'on dady, wai kuna inane? Wlh zantafi abina" yak'arasa fad'ar haka lokacin da yagama daidaita zaman agogon a hannunsa. Yana rufe baki suna fitowa kowaccensu masha Allah, Ummi ce tafito biye da su Bilal data gama gyara su cikin wasu k'ananan kaya masu d'an karen kyau, wani irin farincikine ya rufeta data kallesu gaba d'ayansu sunsha kyau bata san lokacin da bakinta yafara fad'in,


"Masha Allah yaran dady, _i'izukuma bikalimatillahi tammat, minkulli shayd'anin wa hammah, wamin kulli ainin lammah_" tadinga rik'o fuskokin kinsu d'aya bayan d'aya tana shafa masu, sannan suka fice suna yimata byebye, azuciyarta sai fad'in take Allah ya tsare manaku yasa kudawo lpy.


Misalin k'arfe tara da rabi hajia dake zaune afalo tare da wasu 'yan mata su biyu zaune agefenta ta k'walawa mom kira, da dawowarta kenan daga wajen rakiyar k'awarta kuma aminiyarta hajia kilishi bayan tasake d'orata akan salon makirce makirce da kissar da zata b'ullo da ita idan takoma, wajen ta iso hannunta rik'e da wayarta tana lallatsawa, harararta hajia kaka tayi kafin tace


"Hayn..aikinfa kenan, wannan shashanci naki narok'i Allah ya rabaki dashi, yanzu wane shireshiren kika yiwa kanki kafin maigidan naki yazo?" Batare da mom tad'ago ba tace nikad'ai nasani hajia tanaci gaba da latsar wayar" cike da takaici hajia kaka ta wafce wayar ahannunta tana fad'a.


"Samnar Banza da wofi ke kad'ai kika sanme bayan kin kasa gyara kanki, dubeki kamar wata ballagaza babu kitso ba k'unshi, wlh Allah kigyara halinki kafin duniya magyara makishi, zaki zauna ne yaran nan su taimaka maki ko sai nakira papinki yaci mutuncinki tukuna" cikin jin haushin fad'an da hajia kaka keyimata agaban yara yasa tab'ata fuska ta kumbura tana hararar 'yan matan tanaji kamar ta dokesu. 


Ganin hajia tamik'e tsaye yasata zaunawa ak'asa, sukuma 'yan matan sukayo kanta d'aya tacirewa mom d'an kwali tahau tsefe mata kai, d'aya kuma tafara yimata zanen siffa (lallen hydrogen) a k'afafuwa da hannuwa, nan take itama wacce ke saman kanta tana kammala tsifar tafara yayyafa mata kitso, cikin mintunan da basu wuce hamsin ba sai ga mom ankoma tamkar amarya har wani k'yalli takeyi.


 

















*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Thanks for being my shadow. That i really don't wan'na leave me, because somewhere in my life i know that you ure shining a light on it, *AUNTY FARIDA MOHAMMED* thanks for incouraging me with ur  warmest comments, jxkillahu khair_👏🏻



💎Page_____33💎



   A bakin wata katafariyar super market yaya Mahmud yayi parking d'in motarsa adai dai inda aka tanada don ajiye motocin, sai da yagama daidai ta zaman motar sannan suka fito, su Bassam ne agaba sai su Billy da suka biyo bayansu, shi kuwa Mahmud babban yaya biye dasu abaya ya wani matse fuska kamar bashi ba, duk wani motsi da 'yan uwan nasa zasuyi yana akan idonsa, cikin natsuwa suka dinga kwasar abubuwan da suke so wanda mafi yawancin abunda 'yan matan suka kwasa kayan kwalliyane su kuma yaran kayan wasa suka dinga jida suna sakawa cikin basket d'in dake jaye a hannunsa, shidai kallonsu kawai yakeyi batare daya d'auki komai ba kuma har lokacin yana biye dasu abaya, wani gefe sukabi dake Jere da underwear's kala kala amma ga mamakin sa babu wacce ta kalli wajen balle tasa ran d'auka, ganin haka yasa ya tsaidasu yana fad'in "Anan fa? Babu abunda kuke buk'atane naga zaku wuce?" Cike da jin kunya kowaccensu ta duk'ar da kai k'asa sannan sukaci gaba da tafiya, da sauri ya sake dakatar dasu yana merar baki, hannuwansa dake cikin aljihu ya fiddo d'aya ya dinga d'auko unders d'in yana jefa masu cikin basket saida ya kwatanta yad'ibi kowanne adadin saiti ukku kaloli daban daban sannan yawuce abunsa gaba batare da yakallesu ba yana sake matse fuskar nan alamun ba reni.


Kallon kallo aka shigayi tsakanin Basmah dasu Billy kafin suba juna hannu sukashe suna dariya, jin dariyar da sukeyi yasashi tsayawa had'e da juyowa lokaci guda yana watsa masu wani irin kallon da yasa cikannansu murd'awa, da sauri suka rufe baki tare da wucewa ta gabansa suna sake danne dariyar dake neman fito masu, sai daya kalli gefensa sannan ya sakebi bayansu yana murmushi,



Room fresheners masu k'amshi Billy takwasa kusan kala goma kuma kowane k'waya biyu biyu su Basmah suka bita da idanuwa suna kallo,


"Ke duk ina zakije da wud'an nan turarukkan haka sai kace ke kikafi kowa son k'amshi?" Yaya Mahmud yafad'a yana waro ido, sai data shagwab'e fuska sannan tace 


"Kai yaya aishi k'amshi rahamana, babu wata kyauta aduniya mafi tsadantuwa kamar k'amshi" turo idanuwansa yasakeyi yace


"Injiwa yafad'a maki, lalle son k'amshinki yayi yawa, to yanzu wud'an nan duk ina zaki kaisu?"


"Su ummi da mom na d'aukarmawa" Mahmud bai sake cewa komai ba, suna gamawa suka nufi wajen payment akayi masu total kud'in da zasu biya almost 40thousand naira, kuma kusan duk turarukkan ne sukafi yawan kud'i, gashi kud'in dake hannunsa gaba d'aya 50thiusand ne har gami da nasa, dole yaciri 10thousand acikin kud'insa yak'ara akan nasu 30thousand da dady yabasu yabiya aka saka masu kayan cikin jikkuna suka wuce, bayan sun fito ya d'auki hanyar da zata sadashi da titin da GT bank yayiwa ummi depositing d'in kud'in data bashi ya kaimata, yana fitowa bankin yatayar da motarsa aguje ya mai dasu gida, yana ajiyesu batare da yashiga ba ya tayar da motar yanufi gidan papi cike da d'okin ganin mom d'insa. 


Papi ne yasamu zaune bisa wasu kujeru shida amininsa daya kawo masa ziyara a harabar gidan suna fira, duk'awa yayi har k'asa ya gaishesu cikin natsuwa har yana tsokanar papi da cewa "sannu da hutawa gayen baby hajia kaka" dariya papi yai kafin yace


"Ja'irin yaro injin dai zuwa kayi katafi da mom d'in taka dake neman ta sanyawa babyn tawa ciwon kai"


"Aa papi ai wannan aikin dadyne ni sak'o nazo kawo mata daya bani" Mahmud yafad'a tare da mik'ewa yabar wajen, murmushi abokin papi yayi yana fad'in


"Ikon Allah yaran zamani kajifa abunda yake cewa, Allah dai ya shirya manasu" papi ya amsa da amin.


"Yawwa alhaji niko nace kaddai kacemun wannan d'an wajen 'yatace Hussaina!"


"Sosai kuwa shine, domma yaranta nafarko da na biyun basu tsaya ba, ai wannan shine yaronta na ukku "


"Masha Allah gashi tubarkallah duk inda saurayi ke kaiwa yakai, gashi da natsuwa har naji ina yiwa jikanyar wajena sha'awar had'ata dashi" murmushi papi yayi kafin yace


"Allah sarki ko 'yar wajen Ibrahim da Allah yayiwa rasuwa shida matarsa"


"Eh ita nake nufi, kasan har ta kammala karatunta nagaba da secondary a b'angaren kiwon lafiya (nurse) har tafara aiki awata asibitin kud'i dake nan garin"


"Kai madallah abu yayi, Allah yataimaka kuma yajik'an iyayenta, zan yiwa shi Mahmud d'in magana, idan ya amince sai yaje su daidaita da ita" wani irin farincikine ya bayyana a fuskar alhaji hamza wato aminin papi wanda koba'a fad'a makaba kasan yaji dad'in fitowar wud'annan dad'ad'an kalamai daga bakin aminin nasa, haka dai sukaci gaba da tattaunawa cike da fatar Allah yasanya qudurinsu yazamo alkhairi kuma yasa yaran su amince da juna.


Lokacin da Mahmud ya shigo paloun kasa gane mom d'insa yayi saboda yanda yaga tagyru k'asa da sama, gaisheda ita yayi yana fad'in


"Momynmu kingaki kuwa? Masha Allah gaskiya kinyi kyau sosai, nikam ina zanga maik'unshin nan kitso inyi masu kyauta" yak'arso wajen hajia dake marar baki tana fad'in


"Hmm andaiji kunya tsabar rashin gyaran jiki har d'an cikinki kinsaka shi cikin mamaki, adai san angirma adena shashanci" b'ata fuska Mahmud yayi yana gaisheda hajia kaka, bata tankashi ba saida tagama yiwa mom fad'a sannan tajuyo fuskarta d'auke da murmushi,


"Ahh..mommodu yanzu kake tafe? Ina k'annen naka suke da umminku, inace dai duk lafiya kuke ko?"


"Lafiya klw suke, yanzun nan na ajiyesu gida mundawo daga wajen sayayya"


"Kai malan mommodu!, shine kak'i kazo dasu, ko gudu sukeyi ink'wace masu kayayyakin da suka sawo inyiwa papi kwalliya dasu, don nasan sayayyar tasu bata wuce ta kayan kwalliya"


"Aikuwa kamar kinsani babyn papi suka d'ai suka kwaso" kunnensa tarik'e 


"Dama aini babyn sace ba takaba, tukuna barima intambayeka kai sai yaushe zaka kawomun taka babyn ko so kakeyi saina mutu sannan?"


"Awwshh...fara cikamun kunne tukuna sai infad'a maki ko!" Yafad'a yana rik'e da hannunta data rik'e masa kunne, Sakin kunnen nasa tayi ai kuwa kafin tayi wani k'wak'k'waran motsi har yabar wajen yana fad'in,


"Kunjimun tsohuwa da neman magana, tunda nashigo kinbi kin nanik'eni wuri d'aya ko bari bazakiyi naje wurin momynah naji d'imin jikinta ba" kitchen yanufa wajen mom dake faman sarrafa abunda za'aci da rana, rungumota yayi tabaya yana fad'in


"Momynah sannu da aiki, mekike dafawa tsofaffin nan dake neman su wahalshemuna dake?" Juyowa tayi had'e da dungura masa ludayi akai, "kaima nan kad'an iyayenka za'a kirasu da tsofaffi haddai dadynka" dariya yai tare da fiddo kud'in dake aljihunsa ya mik'a mata, "Allah sarki dadynah yayi matuk'ar kewarki sosai, ga wannan yace akawo maki ko akwai abunda zaki siya kafin yazo"


Karb'ar kud'in tayi tad'an juyasu sannan tad'ora akan fridge d'in dake cikin kitchen d'in, "kace masa ngd" tafad'a sannan taci gaba da abunda takeyi. Wani irin ba dad'i Mahmud yaji ganin yanda mom tayi da kud'in sai yatuna yanda Ummi takarb'i kud'in cikin girmamawa tanata kwararowa dady godiya da dad'ad'an addu'o'i tabbas ko anan kad'ai aka tsaya akwai banbanci tsakanin Ummi da mom d'insa ssai, kallonsa tayi taga yanda ya canza fuska sai itama taji ba dad'i aranta, murmushi tak'ak'aro don tafaranta ransa tace


"Wato dadynka kad'ai yayi missing d'ina kaida k'annenka da kuma umminku bakuyi missing d'ina ba ko?"


Hakan da tafad'a sai yaji wani irin sanyi aransa haddai da tace da umminku, arayuwarsa bait tab'a jin mom takira ummi amatsayin wacce zasu iya zama mallakinta ba sai yau, ko yaushe in abu yashafi Ummi saidai takirata da sunanta wato  Aisha amma sai gashi yau da bakinta take kiranta da umminsu, addu'a yayi azuciyarsa akan ubangiji Allah yasa mafarkinsa yazamo gaskiya, yana fatan Allah yasa ummi ta zubar da duka makaman yak'inta kenan, azahiri kuwa cewa yayi


"Munyi missing d'inki sosai, haka itama ummi da kullum take k'ok'arin kulawa damu tare da yimuna addu'a" Runtse idanuwa mom tayi saboda yanda kalaman suka daki zuciyarta, da ace Mahmud zai gane halin da take shiga aduk lokacin dataji yakira sunan ummi ko yayi mata zancenta to da baiyiba, don rad'ad'in hakan zai iya tsaida numfashinta. K'arfin hali tayi zuciyarta nayi mata zugi tace


"Ayya 'yar uwata Allah yabiyata, gaba d'aya kulawar da kuke samu tasaka baku ba har abbanku ya canza sosai, a gaskiya sai yanzu nakejin rashin da cewar abubuwan da sukata faruwa tsakaninmu" tsabar farincikin da yaji yasa yasake rungumeta "Momynah ba komai ai wannan abun duk yawuce, indai ummice natabbata babu komai aranta"  ji mom takeyi kamar takamasa ta mammake saboda yanda taji yana siding d'in ummin, haka dai sukaci gaba da firarsu ta d'a da uwa bayan taci nasarar canza firar, Mahmud baibar gidan ba sai bayan la'asar ranar tare da papi, hajia kaka, mom d'insa sukayi lunch cikin soyayya da k'aunar juna a tsakanin d'a da iyaye.


Bayan Mahmud yawuce papi ya zaunar da mom yayi mata nasiha sosai sannan itama hajia ta d'ora da tata akai, sosai mom tayita kuka kai kace zata sauya daga mugun halinta.


Ummi kuwa bayan fitarsu saiga kiran dady awaya, kasan cewar tak'are duk wasu aikace aikace daya kamata tayi tare da taimakon yaran nata yasa tasamu d'aya daga cikin kujerunta ta zauna tare da d'aga wayar, cikin wata iriyar zazzak'ar murya tace


"Hello abu Bilal!" Murmushin da saida taji fitar sautinsa dady yayi har hak'oransa nabayyana saboda dad'in sunan da tayi masa dabata tab'a kiransa dashiba, shiru yayi yakasa amsa mata saboda yanda yaji wata irin kasala ta saukar masa, jin baice komai ba yasa tasake cewa


"Hello, assalamu alaika abu Mahmud" akasalance ya amsa da


"Wa'alaikissalam rabba'atul bait oum bilqees"


"Ya aiki dadyn yara, hop dai ka isa lpy"


"Lpy klw, alhmdllh tsantsar kewarkice kawai ta uzzurawa zuciyata shiyasa nakiraki, ina fatar kina kula mani da kanki yanda yakamata ko"


"Matuqar kana kula mani da kanka to tabbas nasamu kula ta musamman domin kai d'in ne ni"


"Oum Bilqees kenan, in dai a fannin dad'ad'an kalaman dake kwantar da zuciyane kullum d'an koyo nake komawa agabanki, ke gwanace domin kinkai mak'ura wajen iya sarrafa zuciyata dani kaina wajen dad'ad'an kalamai"


"Hmm abu mahmud kenan, nikuwa gani nake ai kaine malamin kuma koyarwar takace, gwanewarka ita tahaifarwa da d'alibarka fahimtar karatun cikin sauk'i har tasamu kwarin guiwar iya karatun fiye da yanda ka koyar da ita, shiyasa har kake kallon kanka amatsayin d'an koyo akanta" dariya dady yayi kafin yace


"Idan kuwa hakane yazama dole nayiwa wannan d'aliba tawa kyauta, domin na tabbata duk inda nashiga da ita zata sakani farinciki da alfahari"



"To shikenan ina maraba da wannan kyauta taka ko yaushene domin itace zata k'aramun k'aimi da kwarin guiwa naganin cewa nasaka farincikinka da alfaharinka lillinkuwa akowane lokaci"


"Nabaki dukkanin zuciyata amatsayin kyautarki, domin na tabbatar da kalamanki" muskutawa ummi tayi daga zaunen da takoma akwance tana fad'in


"Madallah da wannan kyakkyawar kyauta maigirma data sanyani fita zakaran gwajin dabi acikin 'yan uwana mata, nayarda da cewa nafi kowacce macce sa'ar samun adali kuma nagartaccen miji, dukkanin maza da kake gani aduniya ina yimasu kallon matane, kai kad'aine namiji awurina dake haskamun duniyata da kuma lahirata..."


"Kibarni haka oum Bilqees kada kisa nakasa attaka komai" wata irin ajiyar zuciya sukayi atare har suna rigegeniyar fad'awa juna "I LOVE YOU" dukkaninsu dariya sukayi cikin jin dad'i sannan dady ya yimata bayanin cewa yaturo yaronsa akawo masu kayan abinci ita da mom, nan take sanar masa da cewa sai dai akaisu gaba d'aya part d'in mom saboda tana dasu sosai har yanzu basu k'are ba, godiya tatayi masa da addu'a yana amsawa da amin sannan ya kashe wayarsa cike da alfaharin samunta a amatsayin matarsa. Ummi nagama waya da dady saiga su Bassam sun dawo, gaba d'aya suka wuce d'aki suka ajiye jikkunan kayan da suka sawo, jikkar turarukkan kad'ai Billy ta d'auko tana nunawa Ummi,


"Ummi dubi turarukkan dasu yayya Basmah da Batool suka d'ebo maku keda mom" kasancewar Ummi ma'abociyar son k'amshice yasa tad'ago tana kallon Basmah da Batool da sukayi galala suna kallon Billy tace


"Wow....Basmah, Batool da kanku kuka zab'o mana wud'annan? Kai gaskiya sunyi kyau sosai, kuzonan yarana Allah dai yayi maku albarka" tak'arasa cike da murna tana bud'e masu hannuwanta suzo, rungumesu tayi sosai tanaci gaba dayi masu addu'a


"Nida momynku muna godiya kunji ko?" Billy dake gefe tsaye tahard'e hannuwanta akan k'irji sai kallonsu takeyi tana murmushi, azuciyarta tana fad'in "Allah sarki 'yan uwana, abun gwanin ban sha'awa, inama ace duka umminah tahaifeku!"


Koda dady ya kammala waya da ummi mom yakira, itama fira suka d'an tab'a da ita, ba laifi yasamu had'in kanta saboda qudurin da tasawa aranta sun d'an tab'a soyayya, duk da rabin soyayyar k'orafice akan yarage sonta, bata samun kulawarsa nan yayita bata hak'uri tare da tabbatar mata da cewa bahaka bane har yanzu yana matuk'ar sonta kuma yau zai tabbatar mata da hakan. Nan dai yafad'a mata cewa tagyara da anyi sallar isha'i zaizo ya d'auketa. 


Ana gama sallar isha'i mom ta d'auko abunda hajia kilishi tabata jikinta har rawa yakeyi tayi inserting kamar yanda tace, murmushi tayi tana kallon madubi, cikin isa da gadara da kuma yak'ini akan maganin tace


"Rest in peace Aisha dake da 'ya'yanki" sannan tabushe da dariya, tana cikin dariyar ne hajia kaka takirata tab'akkata wata dalleliyar atamfa super exculusive wax da tasha d'unki sosai tare da wasu sababbin kaya data d'unka mata kala hud'u, ga takalmi, jikka, 'yankunne da sark'a, mayafi duka sababbi ta siyomata, Allah sarki uwa rahamace, fad'a tasake yimata sosai sannan tace taje tagyara kafin alhajin yazo,


Dady na isowa aka bashi izinin shigowa ya gaida papi da hajia cikin girmamawa sannan aka kirawo mom papi yasake yimasu nasiha, godiya dady yayi masu sosai sannan ya d'auki matarsa kuma amaryarsa mom suka nufi gida...







 




 













 
















*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


🤣🤣 _Bana kyautar page ni Billy s fari saboda already nariga da nabada kyautar littafin ga wacce kukaga sunanta Asama👆🏻 don haka banida sauran ikon da zan iya kyautar da wani yanki daga ciki sai idan ita taga damar yin hakan, but idan muhimmancinka agareni yakai mak'ura nakan mik'o sak'on gaisuwa tamusamman agareka, saboda haka kusani yau gaisuwar takuce GHOST READER'S na littafin 'YAN UWANA NE! Ina fatar alkhairin Allah yakai gareku aduk inda kuke, duk da cewa bakwayin comment balle godiya kunada matuk'ar muhimmanci agareni domin ko kad'an rashin yin hakan baya damuna😃, lada nake neman samu tahanyar ilmantarwa da fad'akarwa kuma natabbata idan kunkaranta zan samu gwargwadon abubuwa masu kyau da kuka tsinta aciki kuma kukayi aiki dasu don haka jinjina agareku tare da fatar kowacenku na cikin k'oshin lafiya, Billy s fari na sonku over😘😘_


💎Page_____34💎



   Tunda dady yad'auko mom yake kallon tsantsar kyau da kuma kwarjini da tayi masa, tuk'i yakeyi amma duk bayan sakon biyar sai yajuyo yana kallonta, da mom talura da haka sai tasaki murmushi tana fad'a acikin zuciyarta cewa tabbasa hak'ata gab take data cinma ruwa, ai wajen kagani alhajina wani shagalin ma sai aiki ya kankama, hannunsa taji ya d'ora akan nata dake saman cinyarta yana d'an mammatsawa ahankali, lumshe idanuwa tayi kafin taji muryarsa ta dakan mata dodon kunnuwa.


"Ranki yadad'e wannan murmushin fa?, kinga yanda kikayi kyau kuwa?"


"Hmm anya wannan maganar dagaske kakeyi?"


"Sosai ma kuwa" yafad'a yana d'an matso da jininsa ga starring mota" wani irin murmushi tayi da yabayyanar da hak'oranta da yasa lokaci guda dady ya danne burkin mota yana fad'in "Ma sha Allah, irin wanna murmushin zai iyasa na saki titi batare dana ankaraba, a gaskiya bazan iya jurewa ganin kina yinsa awajeba don duk namijin daya gansa toya matuk'ar cutar da zuciyata ya k'arasa maganar cikin yimata rad'a akunne" ai nan take mom taji wani abu yarr acikin jikinta, soyayyar dady mai tsanani tak'ara nink'aya acikin zuciyarta, ji takeyi tabbas bazata iya jurar had'a alhajinta da kowace irin macce ba, wani kuzari tasamu azuciyarta naganin cewa duk yanda zatayi takori Aisha agidanta sai tayi don tabbatarwa kanta da cewa shi natane ita kad'ai kuma ita kad'aice wacce zai dinga yiwa irin wud'annan kalaman. K'arar 'yan yatsunsa daya murza taji a fuskarta yana fad'in,


"What? Mekike tunani kobaki yarda bane?"


"A'a nayarda mana kawai shakku nakeyi akan anya inada matsayin da zakayi irin wannan kishi akaina kuwa" murmushi yayi daidai lokacin da yakaryo layin gidansa tare da juyowa yana kallonta,


"Tabbas yau zan cire maki wannan shakkun, natabbata haka zai fahimtar dake zunzurutun son da nakeyi maki yakai matsayin da zanyi kishin da nakeyi maki fiye da tunani"


"Allah yasa haka" tafad'a daidai lokacin da yake k'ok'arin tura kan motarsa cikin gidan nasu da maigadi ya wangame masa gate yana kwasar gaisuwa, yana ganin mom da sauri yaja baya tare da d'ora hannuwa akai yana fad'in


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'unn, shikenan annobar gidan nan tadawo, wayyo 'yar dimirmiyar yarinya Bilkisu da Bilal natausaya maku kuma nima na tausayawa kaina don wallahi natabbatar wannan karon bak'in halinta zai iyasa inkasa tura gate agidannan saidai gate d'in yaturani, bayan tafiyarki banida matsala da kowa, inci mai kyau insha maikyau, babu tsawa balle zagi ko harara, alhaji badon kar ince wani abuba da nace wallahi Allah bakasona da alkhairi, Haba wannan wace iriyar musibace?" Ya k'are maganar yana goge guntayen hawayen da suka fito masa a idanuwa, zai sake sakin wata maganar kenan yaji muryar dady yana k'wallo masa kira, dagudu ya isa wajen lokacin dady na k'ok'arin bud'ewa mom gambu tafito, juyawa yayi da sauri yana fad'a cikin muryar da shi kad'ai ke iya jinta.


"Wayyo alhaji, walh kana cikin matsalar jarabtuwa da wannan muguwar mata" juyowa yayi tare da cewa gani alhaji batare da yakalli inda mom takeba, 


"Yawwa kafiddowa hajia kayanta ka kaimata aciki" dady yafad'a tare da wucewa gaba mom nabiye dashi abaya, sai alokacin maigadi yakalli mom yace


"Sannu da dawowa" wata uwar harara ta watsa masa batare da tace komai ba tawuce abunta.



Ita dai ummi tunda dady yadawo bayan la'asar take lura da yanayinsa duk da yana k'ok'arin b'oye mata nuna damu warsa akan dawowar mom amma dole saida yadinga yin wasu abubuwan dashi kansa baisan sun bayyana ba, saboda miji da mata sai Allah duk yanda basajin dad'in zama da juna aduk lokacin da suka nisanta da juna nawani tsawon lokaci to tabbas idan zasu had'u sai kaga suna d'oki da mararin had'uwa da juna, ummi naganin hakan tayi murmushi tare da danne kishin dake k'ok'arin motsamata ta hanyar addu'a


" _Rabbhi a'uzu bika min hamazatish shayad'in, wa a'uzu bika rabbhi anyahdurun_" ita tayita maimaitawa cikin ikon Allah taji komai ya lafa mata azuciya. Bayan sallar isha'i daya fito zai tafi d'auko mom ita tarakosa da kanta har bakin mota tana gyara masa zaman hular kansa had'e da yimasa fatan Allah ya kiyaye kuma adawo lpy batare da tasake jin komai aranta ba.lokacin da tadawo paloun ta tarar da yaran gaba d'aya zaune itama tazauna acikinsu suna ta fira, nan tafara surko nasiha da wa'azi acikin firar tana nuna masu muhimmancin rik'e 'yan uwantaka da zumunta tare da nuna masu illar dake k'unshe cikin b'atawa iyaye rai da nemawa junansu duk abunda suke so akansu, jajircewa bisa kaifin takobin gaskiya tare da juriya da kuma hak'uri, sosai nasihar takama zukatansu suna sake yiwa Allah godiya daya basu Ummi acikin rayuwarsu kuma a matsayi na uwa, mahmud da yashigo lokacin da Ummi ke k'ark'are nasihar, yace


"Laaah..gaskiya banyar daba ummi anyimun wayau asako baya, ko so kikeyi 'yan uwana sufini k'aruwa da baiwar da Allah yabaki" murmushi ummi tayi lokacin da yake k'ok'arin zaunawa agabanta tare da nad'e k'afafuwansa yana kallonta "A'a babanah saidai in son kai zakayi amma nasan bazasu fikaba don kai kake da baiwar da Allah yasa 'yarka ta gadoka, babu zancen asako baya domin kai kadad'e da kiyaye wannan karatun harma da aikatashi" bud'e baki yayi zaiyi magana ummi ta katsesa ta hanyar cigaba da cewa


"Maza ka tasa k'annenka agaba suje su d'orawa mom d'inku abincin duk da kasan tafiso natabbata suna gab da isowa" haka kuwa akayi batare da sunyi mata mu suba suka nufi part d'in mom hadda Bilkisu da zuciyarta ke cike da fargabar dawowar mom d'in har sun fita ummi takira Basmah tabata turarukkan da suka sawo masu d'azu bayan taraba ta d'auki nata.


Saida suka kammala girkin tsaf wanda fiye da rabinsa Bilkisu ce tayi dayake dafadukan makaronice da tasha kifi  sosai da wake, sosai mom kesonta shiyasa yaya Mahmud yace sudafa mata ita sannan suka feshe ko ina da turarukkan masu matuk'ar k'amshi suka kunna A.C sai part d'in yakoma tamkar na wata sabuwar amarya. Zaunawarsu kenan sukajiyo tsayawar motar dady, da gudu Bilal da Bassam suka rugo suna fad'in "Dady oyoyo" ganin mom yasa Bilal tsayawa batare da yak'araso ba, juyawa yayi yakoma daga ciki yana fad'in


"Aunty Billy kifoto ga mom nan kada ta iskoki" jikinsa har rawa yakeyi, da sauri ya Mahmud ya d'aukosa yana fad'in ya kwantar da hankalinsa babu abunda zata yimasa, "duba kagani ga yayya Basmah, ga yayya Batool, ga aunty Billy itama a zaune duka bazamu bari mom tayi maka komai ba kaji ko?" Bilal da har lokacin jikinsa bai daina rawa ba ya kalli Batool yace


"Yayya kikaini toilet zanyi fitsari" ganin yanda yarud'e yasa gaba d'ayansu suka taru suna rarrahinsa cike da kulawa suna jin ba dad'i a zuciyarsu.


Mom ce tayi sallamah a daidai k'ofar paloun had'e da d'ago labule, Allah sarki uwa uwace komai mugun halinta, cikin jin dad'i gaba d'ayansu suka rugo aguje hadda yaya Mahmud suka rungumeta, ai kuwa kamar jira Bilal keyi yaruga aguje cikin toilet har fitsarin na kuccikke masa.


👏🏻 _sorry fd late update naje anguwane u should manage with dis_













*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____35💎



   Bayansa Billy tabi tasamu har fitsarin ya gama fitowo a wandonsa, tsarki tayimasa sannan tarik'o hannunsa suka fito tare, tsaye tayi tana kallon yanda mom kebin yaranta d'aya bayan d'aya tana rungumesu tare da yimasu sunbata agoshi tana kawowa kan ya Mahmud tace


"Kai kam kayi girma da yawa kabari har sai Allah ya nuna mana nakawo maka matar da zaka aura inyaso ta wakilceni" bubbuga k'afa ya shigayi tamkar k'aramin yaro kafin yace "A'a ni mom bazan yarda da wannan wayon ba" rungumeta yayi saurinyi tare da cewa "welcome back, we missed you so much mom, home with out you is like a field of war with out no body" cikin farinciki tadinga kallon yaranta d'aya bayan d'aya tanajin wani irin nishad'i nak'ara bayyana k'arara a fuskarta, "I luv you so much my kids and i missed you too, life with out u and ur father is like missing my whole life, my Allah bless you for ever mom lovers" gaba d'ayansu suka amsa da amin suna dariya tare da rungumeta atare. Billy dake gefe rik'e da d'an uwanta taji inama ace mom zata iya gwada masu ko kad'anne daga cikin irin wannan soyayyar da take nunawa tsakaninta da 'ya'yanta, tabbas ta tabbata babu wani sauran bak'in ciki ko damuwa dazata samu gurbi acikin gidan su, amma kash tasan inba ikon Allah ba wannan abune mai matuk'ar wuya agareta, cike da Sha'awa taci gaba da kallon yanayin da mom takasance ciki ita da 'ya'yanta kafin tafara yunk'urin takowa cikin tsoro da fargaba, ahankali ta k'araso wajen har lokacin hannunta narik'e dana Bilal wanda takun tafiyar suce tasa hankalinsu yadawo ga 'yar uwarsu, cikin jin kunyar abunda sukayi na mantawa dasu suka k'araso wajen gaba d'ayansu kamar sun had'a baki inbanda Bassam daya kame hannun mom tamkar za'a k'waceasa ita suna fad'in


"We are sorry sister" tare da rik'o hannunta suka k'araso wajen mom datayi sororo tana kallonsu, cikin i'inar murya Billy kefurta "san..nu. da zu.wa mom" har mom ta d'auke kai cikin d'aure fuska sai kuma ta tuna da wani abun, juyowa tayi tana murmushin da baikai cikiba ta rungumo Billy ajiki tare da rad'a mata akunne "maza kija k'anenki kubar nan kafin inbayyanar maku da sabon halina da baku sani ba, ina son naganni dagani sai jinina donnayi kewarsu" d'ago Billy da jikinta yafara rawa tayi cikin lokaci guda tana dariya "thank u dota" tafad'a tare da duk'owa tarik'a hab'ar Bilal dake faman ja da baya yana b'uya abayan 'yar uwarsa tace "kai yaron Ummi yau ba magana" sannan tawuce batare data kalli kowanensu ba, murmushi sukayi cikin jin dad'in ganin yanda mom d'insu takarb'i 'yan uwansu batare da tsangomaba. Murmushin itama Billy tayi tana k'ok'arin danne damuwar dake neman taso mata alokaci d'aya kuma hawaye na neman bayyana a idanuwanta, da sauri ta duk'ar da kanta tana fad'in


"Ya Mahmud, yayya Basmah, twiny bari naje na sanyowa Bilal wando sai nadawo" batare da tajira mezasu cewa ba tayi saurin ficewa daga falon hawayen dake kokuwar fitowa a idanuwanta suka gangaro mata afuska, da gudu tabar part d'in tanufi d'an guarding d'in dake tsakanin part d'in mom, ummi da kuma dady.


Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun take fad'a tana kuka, Bilal ya rungumeta yace


"Aunty Billy kidena kuka ai muma muna da umminmu, mutafi muma tayi mana yanda mom tayiwa su yayya Basmah, kuma ni bazan koma wasa da ya Bassam ba tunda yak'yaleni don yaga mom d'insa, ALLAH yasa ma tasake komawa ko?"


Murmushi ne yakucce mata jin abunda Bilal kefad'a har lokacin tana kuka, rungumesa tayi na wani d'an lokaci sannan takunna fanfon dake can gefe ajikin d'akin ya Mahmud tawanke fuskarta. Juyowa tayi tana kallon Bilal "Bilal kada ka koma yin irin addu'ar da kayi d'azu, idan 'yan uwanmu sukaji baza suji  dad'i ba kuma zasuyi fushi damu, kana son haka?" Girgiza kai yayi tace


"Good boy itama ummin muce kuma suna sonta yanda suke son umminmu don haka dolene muma musota kamar yanda muke son ummi kaji ko?"


"Eh amma ni nafison ummina akanta"


"Shikenan yanzu sai muje ko? Zaka fad'awa Ummi nayi kuka" girgiza kai yayi tare da langab'esa gefa sannan yace


"A'a bazan fad'a ba banaso ranta yab'aci"


"Good give me five" tafad'a bayan sun tafe tarik'o hannunsa suka nufi part d'insu suna wasa kamar babu abunda yafaru.


Dady kuwa part d'in Ummi ya wuce ya tarar da ita zaune tayi shiru tana tunanin yanda kuma zaman nasu zai kasance yanzu, jin sallamarsa yasa tafito daga duniyar tunani, murmushi tasakar masa tare da tasowa ta rungumesa.


"Sannu da dawo angon mom, hope kunzo lpy?" Shiru dady yayi yana tunanin wai ummi wacce irin macece da bazata tab'a barin damuwa ko b'acin rai suyi galaba akantaba. d'agota yayi tare da manna mata kiss a forehead yace


"Rabba'atul bait meyasa baki kishi a kaina ko kad'an?" Murmushi tayi bayan tasakesa had'e da juyowa tadawo kan kujera sai ga hawaye suna biyar kuncinta, cikin rikicewa da tashin hankali yak'araso wajenta tare da yin neal down agabanta cikin damuwa tare dayin nadamar abunda yafad'a yace


"Ki gafarceni oum Bilqees idan abunda nafad'ane yasa kika shiga cikin wannan hali, natuba rabba'atul bait, kiyi hakuri kiyafeni" runtse idanuwa tayi hawayen suka ida fitowa kwance a fuskarta,


"Abu Mahmud kanemi tsarin Allah da infara bayyana tsantsar kishin da nakeyi akanka, domin zai sanya adalcin da kake dashi a tsakanin nida matarka yayi rauni saboda tsoron kada karasani, kamanta sunan da nake dashi ne? AISHA fa akace, wlh dajin sunan zakasan cewa tanada matuk'ar kishi akan duk abunda take so, amma kuma Allah daya sanya kishin a kirjina sai yayi mani kyauta da ilimi da zai dinga jagoranci akaina, kayi hak'uri ina sonka kuma ina matuk'ar kishinka fiye da yanda kake tunani abu Mahmud"


Rungumeta yayi shima hawayen nazubo masa saboda tausayinta akan tsantsar hak'uri da kawaici da take dashi "sorry rabba'atul bait, u're the best among the betters wife in d world, am lucky to have u oum Bilqees"


"Me too, dadyn yara" suna ahakane su Billy suka shigo suna dariya, da gudu Bilal yarugo yana "oyoyo dady"


Dariya dady yayi tare da cewa "ka kuru my boy dana biyoka bashi, d'azu ina kallonka bakazo kayimun oyoyo ba sai dai Bassam yayimun" "sorry dady" yafad'a yana kallon Ummi dake dariya.


Mom nashiga d'aki taciro waya takira hajia kilishi, ringing biyu tayi ta d'auka "hello amarya agidan alhaji miye lbari"


"Daidai wlh qawata ya kika isa kin isa lfy dai ko?"


"Lafiya k'alau keni shafamun naji injin dai baki mantaba" 


"Hhh bari kawai qawata kinga yanda alhajina ya rikice, hmm wlh shi kansa idan yazo hannu yau sai yagane bayada wayau, ita kuma waccan banzar dazaran yau munkeb'e da alhaji wlh k'aryarta tak'are don da ita har yaranta saina gasa masu aya ahannu kafin na salwantar da rayuwarsu" Batool ce dake lab'e tund'azu da tazo shigowa tacewa mom tazo taci abinci taci karo da kalaman da ke fita daga bakin mahaifiyarta tayi saurin rufe baki tana hawaye fuskarta d'auke da mamaki tadinga ja da baya har tabar wajen ta nufi d'akinsu cikin tashin hankali, ita kuwa mom hankali kwance tadinga wayarta da hajia kilishi tana cigaba da d'orata akan muguwar hanya.


Batool nashiga d'akinsu tafad'a jikin Basmah tana cewa "yayya Basmah munshiga ukku wlh mom bata canzaba ko kad'an, har yanzu zuciyarta nanan cike da tsanar Ummi da 'yan uwanmu, nan ta zayyanawa Basmah duk abunda taji mom nafad'i awaya, sosai hankalin basmah itama yatashi,



Kasancewar Basmah tafita shekaru yasa tafahimci cewa har sai matuk'ar dadynsu ya samu keb'ewa da mom hakan zai iya faruwa don haka yazama dole sudakatar da faruwar hakan, d'ago Batool tayi tace


"kiyi shiru 'yar uwa bazamu tab'a bari hakan yafaru ba, zamu dakatar da mom don kautar da ita daga bala'i alokaci d'aya kuma don mutaimaki Ummi da 'yan uwanmu daga cutuwa" hannu tasa tagoge hawayen idonta kafin tace 


"Taya yayya Basmah?"


"Yawwa aikinsan jiya dasu papi sukazo ummi tace masu banida lpyne nayi fama da ciwon ciki ko? Kuma dady yasan da haka, don haka da zaran munga mom tatafi part d'in dady zanfad'i ak'asa nadinga murje murje ina kuka, ke kuma saiki ruga ki kirawota, haka zandinga kuka sosai har safe tayanda hankalinta dana dady zai tashi, kinga daga nan dole mom zata dawo takula dani tsorona d'aya kada bacci ya kawomun ziyara " rungumeta Batool tayi tana fad'in


"Wow..nice idear yayya, Allah kasa kada yaya mahmud ya kwafsa mana tunda baisan abunda ke faruwa ba, kinsan zai iya cewa zai kula dake ko kuma yakai ki asibiti"


"To amin in sha Allah hakan ma bazai faruba, idan kuma yace zai kaini asibitn to wlh rirrik'e mom zanyi in tayi mata kuka ina neman gafararta kinga kuwa bazata yardaba k'afarta k'afata za'aje asibitin" dariya sukayi tare da tafewa cikin farincikin samun mafita da sukayi......











 




 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Gaisuwa ta musamma tare da fatan alkhairi agareki *UMMIE* dake group d'in rano online novel, inajin dad'in yanda kike bibiyar littafin 'YAN UWANA NE, thank you sister am really appreciate, another greatng from Ummi ur name sake to you, tace kici gaba da k'arfafa mata hakan zaisa tayi nasara, keda ita abu d'aya ne don haka zaku cinma buri kuma tanayinki over🤭💃🏼🤣_



💎Page_____36💎



    Mom nagama waya tafad'a toilet tayo wanka, simple make up tayi ta saka wata doguwar riga marar nauyi lemon green ta yaga k'aton black vail asama shima dai d'in marar nauyi tayi kyau sosai, fitowa tayi don jiran tsammanin kira daga dady, jin motsin fitowarta yasa suma su Batool fitowa, fuskarsu d'auke da fara'a sukace "mom sannu da fitowa, ur favorite food is ready"


"Wow are u serious?"


"Yeh! Suka fad'a tare da yimata iso akan dining table"


Dady kuwa bayan su Bilkisu sun shige d'aki, kallon ummi yayi yace


"Rabba'atul bait yunwa nakeji, zansamu abani abinci inci?"


"Gaskiya bazaka samuba tunda ga amaryarka can tadawo kuma yara sun shirya maku abunda zakuci, don haka katashi kaje tanacan tana jiranka karka shiga hakk'kinta" shiru dady yayi cike da jin kunyar yanda zai mik'e yafita, sosa k'eyar kansa yai tare da shafo kansa yarasa mezai cemat, can yasamu wasu kalmomin da basuda tushe suka fito abakinsa "Rabba'atul bait yau abun hadda kora da kuma horon yunwa" dariya ummi tayi cikin d'an basarwa tace


"Ko kad'an babu maganar horo anan don natabbata 'yar uwata shirye take data baka tarbo na musamman tare da cika maka ciki yanda ya kamata, kaga kuwa maganar Aisha tayi maka horo kamanta da ita" shiru dady yai ya zubawa Ummi idanuwa yana kallo, shi baice k'anzil ba kuma bai tashi ba, ganin haka yasa Ummi zuwa wajensa ta kamo hannuwansa ta mik'ar dashi,


"Katafi mana dare nayi" zaiyi magana tayi saurin d'ora d'an yatsanta akan bakinsa.. "Shiiiiii...ya kamata kayi abunda ke daidai kajiko?" Tafad'a rik'e da fuskarsa sannan tayi masa kiss agefen kuncinsa, galala yayi yanajin wata irin qaunarta na fisgarsa, hannunsa yaji takamo tanufi hanyar fita dashi sai da suka kai bakin k'ofar sannan tasaki hannunsa tarik'e gambun k'ofar tana fad'in,


"Saida safe abu Bilal" bayada zab'in daya wuce illa rungumeta da yai "I luv u so much rabba'atul bait, kayi daddad'an bacci tare da kular mani da kanki"


"Yanda kace hakan za'ayi da yaddar Allah matuk'ar zaisa kayi farinciki" kiss yai mata a forehead ta lumshe idanuwa sannan tayi breaking hug d'in takoma daga ciki tarufo k'ofar zuciyarta cike da tsantsar soyayyar mijinta, yajima a wurin tsaye kafin yanufi part d'insa yana cewa "Allah yayi maki albarka yakare aduk wani motsi da zakiyi rabba'atul bait, there will be no me with out u Aa'ishhh." Ikon Allah da yawan maza kanyi sabbatu akan hanya saboda rashin da cewa da mata nak'warai, amma akaro nafarko danaga mijin dake tafe yana sabbatu saboda soyayya, kulawa tare da kirkin matarsa.


Yana shiga kai tsaye ya wuce bedroom d'insa ya cire kayan jikinsa sannan ya fad'a toilet ya watso ruwa, kasancewar har 12 takusa yi yasa ya zuba jallabiyarsa seagreen sannan ya feffeshe jikinsa da turare, wayarsa yajawo da niyar kiran mom sai kuma yaji sha'awar saukowa ya iskota part d'inta, tasowa yayi yana zuba k'amshi a hankali yake saukowa akan matattakalar zuwa babban falon dake k'asa sannan yafito had'e da rufo k'ofar, part d'in mom yanufa amma a zuciyarsa tunanin Ummi kenema yahanasa sukuni.


Mom da zaunawarta keda wuya ita da yaranta akan dining suna bud'a  mata yummy d'in da suka had'a mata tace


"Wow...daji wannan food special ne can't wait to eat my fav delicious" tafad'a tana mik'a hannu zata d'auko plate, muryar dady da shigowarsa kenan taji yana fad'ar.


"Anya kuwa anyi missing dady da aka manta dashi har ana zancen cin  abinci batare dashi ba?, Basmah kuna ganin momynku ko?" Dariya sukayi sannan suka kalli mom data tsayar da hannun cak ita bata d'auko plate d'in ba, ita bata ajiye hannun ba tana sauraren abunda yake cewa, ganin duk suna kallonta yasa tayi saurin ajiye hannun itama tana dariya ta bud'e hannuwan had'e da d'aga kafad'u tana kallon dady daya k'araso wajen shima ita yake kallo tace "what to say?", d'aya daga cikin kujeru suka jawo mada ya zauna ya juyo ya kalli Basmah dake tsaye a gefenshi nadama yace


"My dota, ya jikin?" 


"Da sauk'i dady" tafad'a tana maijin dad'in wannan tambayar, juyowa yayi ga Batool data gama zuzzuba masa abincin a plate shida mom tana k'ok'arin rufe warmer d'in yace


"Thank you dota, ina yayanku da Bassam ne?"


Yana rufe baki sai gasu sun shigo ya mahmud har yaiwa Bassam wanka ya shiryasa cikin shirin kayan bacci, k'arasowa yai had'e da gaida Iyayen nasa cikin jin dad'in ganin su atare, kujerar dake gefen dady Bassam yahaye "Nima yayya azubomun nawa inci bacci nakeji" zuba masa Batool tayi sannan ta d'auki plate ta zuba wani aciki mai yawa sosai, kallon ya Mahmud tayi tace


"Ya Mahmud, kaje kaci abincin ko" sannan tayiwa Basmah nuni da sutafi, har sun kai tsakar falon rik'e da abincin data rufo da wani plate asama kamar dady da mom sun had'a baki sukaji sunce,


"Ina zakuje kuma?" cak  suka tsaya lokacin ya Mahmud nak'ok'arin zaunawa bisa kujerar dake kusa da dad yana facing d'in Bassam yayinda ta mom ke facing d'in ta dad, 


"Wajen 'YAN UWANMU" suka fad'a babu alamun tsoro a fuskarsu" mom najin haka nan take ta k'ware da abincin dake neman wucewa abakinta, da sauri dad ya bulbulo ruwan dake ajiye a gorar faro gefensa a cup ya mik'a mata yana fad'in "sorry" kallon juna su Basmah sukayi yayin da Mahmud yace dasu


"Dan Allah kuwuce" don kar mom tasamu damar hanasu shi kuma dady dama cin abincinsa yaci gaba dayi don har ga Allah maganar tayi masa dad'i shiyasa baibi takanta ba, b'ata rai mom tayi amma da tatuna shirinta sai tace


"No ai da kunje kunce suzo nan sai kuci ko gaba d'ayanku, ai laifin kune da run farko kuka k'i kirawosu anan kuci abincin?" 'Dagowa dady yayi da mamaki, lallai mom ta canza dakanta take cewa akirawo su Bilqees suzo nan suci abinci, koda mom taji shiru saita juyo dama taba falon baya saidai ganin falon wayam tayi ashe sun dad'e da tafiyarsu tun lokacin da ya Mahmud yace su wuce. Dole yasa ta hak'ura badon ranta yasoba, Mahmud nagama cin abincinsa yayi masu sai da safe shi kuma Bassam tuni har bacci ya d'aukesa ko gama cin abincin beyi ba, d'aukar sa mom tayi takai d'akinsu ta kwantar dashi batare da ko addu'a ta tsaya tayi masa ba don gaba d'aya hankalinta na akan dady, sosai take jin maganin yafara aiki ajikinta don jitake kamar ana mitsilarta acan k'asanta, tana fitowa tawani fara fari da idanuwa tana jujjuya jiki, nan take dady shauk'i yad'ibesa, hannu ya mik'a mata alamar ta iso garesa a hankali tafara takowa tana wata kwarkwasa da tasa tatafi da hankalin dady gaba d'aya, mazauni yayi mata akan cinyarsa yana faman shinshinar jikinta saboda k'amshin turaren dake tashi,


Batool kuwa suna shiga sun samu har Billy tafara bacci mom kuwa tana d'akinta tana tilawar Qur'ani, haka yasa basu katseta ba. Dukan da bazai cutar da Billy ba Batool takai mata acinya, da sauri Billy ta tashi tana murzar idanuwanta, wata irin harara Batool ta balla mata tana fad'in


"Lallai twiny bakida kirki, daga kizo kisakawa Bilal wando shine kikayi zamanki batare da kunje munyi takin dinner ba" langab'e kanta tayi ta d'ora akan kafad'ar yayya Basmah dake zaune gefenta cikin muryar baccin da bai ida sakintaba tace



"Kinganta ko yayya Basmah?" tana turo d'an k'aramin bakinta, shafo gefen fuskarta dake saman kafad'arta tayi da hannu sannan tace "k'yaleta sweety je kiwanko bakinki muci abinci kinji ko, ina Bilal ne?" 


"Yana wajen ummi k'ilan yayi bacci" tafad'a tare da mik'ewa tashiga toilet cikin sigar tsokana Batool nakira mata baby jepanise, murmushi tayi batare data tankata ba, 


Anatse sukecin abincin har suka kammala, sabuwar firar rayuwarsu tabaya suka d'auko sunata dariya, mafi yawancin firar tsakanin Batool da Billy akeyinta Basmah nacan gefe abunta. Yaya Mahmud ne yashigo part d'in jin yanda suke k'yak'yata dariya, "kai sisters wannan irin dariya haka dare fa yayi" nan Ummi tashigo tace 


"Kabarsu babana tund'azu nake son yimasu magana hankalina ne yad'auku, kuduba agogo kugani quarter to 1:00am fa amma kunata faman d'aga murya" jin haka yasa Batool da Basmah mik'ewa suna kallon Ummi.


"Ummi sai da safe" sosai Ummi taji ba dad'i ganin ba'anan zasu kwanaba amma yazatayi tunda suma suna buk'atar mahaifiyarsu akusa dasu, d'an murmushi tayi tare da fad'in


"Allah yatashemu lpy, kutabbatar kinyi arwala da addu'a kafin ku kwanta" "to ummi" sukace had'e da hugging nata sannan suka fita.


Tun abu na wasa wasa tsakanin mom da dady har yazama gaske domin kuwa mom takashe masa jiki da duk wani salon d'aukar hankali da jan ra'ayi, ganin abun na neman wuce wuri gashi basusan lokacin da yaran nasu zasu iya dawowa su riskarsu ba aciki yasa dady yayi k'ok'arin daidaita natsuwarsa, ahankali yake rad'awa mom magana akunne.


"We should stop all this Momyn yara kada su iskomu, bari naje na watsa ruwa, ina jiranki" sakinta yayi tare da nufar part d'insa cikin wata iriyar kasala, mom kuwa gaba d'aya labari yafara canza mata don jitake kamar ana mintsilarta tare da fizgarta ak'asanta, sosai take jin buk'atar mijinta atare da ita, d'aki tashige jikinta narawa ta d'auki abubuwan da take buk'ata sannan tanufi part d'in dady batare da tajira dawowar yaranta ba.


Su Basmah nafitowa part d'in ummi sukaga shigar mom part d'in dady.


Da sauri suka k'arasa part d'insu, Batool tace


"Yayya yazamuyi, intafi yanzu" cikin miskilanci tace


"A'a Batool wlh ganomu mom zatayi kawai mubada minti biyar, amma duk sai nakejin badad'i hakan da zamuyi wlh ina son mom, it been long time fa bata cikin gidan nan"


"Ohhh my God yayya kimanta da wannan, muyi abunda ya kamata, wlh yayya idan mom ta kwana part d'in dady akwai matsala, zata cutu, ummi ma zata cutu, mafi munin abu sa 'yan uwanmu zasu cutu, kitunafa 'YAN UWANMU NE, Idan bazaki iyaba to nidai 'YAN UWANA NE, yazama dole inkula da duk abun da zai cutar dasu, kinga tafiyata u should know what to do idan sukazo, bata jira amsar da Basmah zata bataba tafice d'akin aguje.


Mom da tuni jikinta yafara tsuma jira kad'ai takeyi taji tabbacin cikar burinta sai kawai suka jiyo an banko k'ofar falon k'asa da k'arfi,


"Wayyo dady mom kufito yayya Basmah zata mutu, dadyyy..." Gaba d'ayansu tashi sukayi cikin firgicewa tare da gyara jikinsu, bil-hakk'i Batool tak'ak'aro kukan k'arya tanaci gaba da takowa bisa matattakalan sama da zasu sadata da d'akin dady dake can sama, cikin kukan taci gaba da cewa


"Dady don Allah kuzo kada in rasa 'yar uwata...yayya Basmah zata iya mutuwa gatacen tana bille bille"


Tana kawowa step d'in k'arshe taci karo dasu sun fito, cikin rashin kuzari dady yace "meke faruwa da itane Batool?"


"Bansani ba dady nima dai naji tana fad'in cikinta, dady muje ataimaketa wlh bana so narasa 'yar uwata" 


"Subhanallahi ko ciwon jiyane yadawo mata" tsaye Batool tayi tanaci gaba da matsar hawaye alokaci guda kuma tana kallon mom dake safa da marwa saboda yanayin da take jin kanta aciki, juyowa tayi tare da cewa Batool "kije wurinta gamunan zuwa yanzu" aikuwa tafashe da kuka tana haba mom ni mezan iya yimata plz tanajin jiki sosai fa, kasawa tayi ta tsare har saida ta tasa dady agaba batare data jira ganin ko mom zata biyosu ba.


Suna fita mom ta'aza hannu akai, nashiga uku ni husaina ya zanyi da wannan alamari, Batool da kinsan bala'in da nake ciki da baki katseman hanzari ba , k'afafuwa tashiga matsa kafin itama tabiyo bayansu, ganin yanda bala'in yayi mata yawa yasa tadinga rarrafowa akan step d'in har tasamu tasauko "wayyoni Hussaina meke shirin faruwa da nine?" tafad'a tare da nufar part d'inta cikin wani hali mai wuyar fassarawa.


Koda dady ya shigo ya tarar da Basmah kwance k'asa tsakar falo tana kuka, tana ganinsa tarirrik'e shi "dady kataimakeni cikina" rungumeta yayi yana fad'in 


"Sannu Basmah bari muje asibiti" wata irin k'ara tasaki da tasa mom dake k'ok'arin shigowa firgicewa da gudu mom tak'arasa wajen


"Basmah, Basmah.. Me kikaje kikacine, wayyoni Allah naboni, Allah ya isarmun? Amaimakon tayi ta Basmah dake cikin wani hali sai faman nanik'ar jikin dady takeyi ko zataji suk'in abunda takeji, ganin babu wani sauk'i yasa tatashi tana zagayar falo tana buga ciyoyinta sai kuma ta mammak'e jiki kamar irin tanajin fitsarin nan sosai surutai ta dingayi wud'an da azahiri kamar don yanayin da 'yarta take ciki yasata yin hakan amma abad'ini da kanta take akan yanayin da take ciki,


"Shikenan tawa tak'are, Allah kawomun d'auki kafin narasa raina, yanzu me zanyi, menene mafita, wash, wayyo Allah na yi hoho"


"Hussaina meye haka, kidena wud'annan maganganun mana meye fa'idarsu" fashewa da kuka mom tayi tare dafad'uwa zaune dab'al tace


"Alhaji kabarni in fad'a, idan kuma bakaso infad'ane kazo muje ciki mana, wlh zan iya mutuwa" cike da mamaki da rashin fahimtar maganganun ta dady yace


"Anya kanki d'aya" 


"Wlh Allah indai zanci gaba da ganin wannan yanayin ahaka kaina zai koma uku bama d'aya ba" mom tafad'a tana cije baki tare da share hawaye kamar k'aramar yarinya, itadai Basmah da Batool nagefe suna kallon alajabi ga mom d'insu da hankalin dady yadawo kansu sai suci gaba da kukan ita kuma Basmah na juye juye tana wayyo cikina, tashi mom tayi tajawo Basmah ajikinta tana cewa "Basmaty kiyiwa Allah kitashi, narok'eki kiwarke da wannan ciwo, ganinki da nakeyi ahaka na daidai da bugawar zuciyata don nima zan iya mutuwa, ganin Basmah nak'ara birgima yasa mom cigaba da bubbuga fuskarta, Basmah kijure ai ciwon ciki shahada yake sawa kinji ko 'yata tashi mana. 



Ganin azaba da masifar wannan magani sunyi mata yawa yasa tayanke shawarar yin aljanun k'arya ko itama tarage zafi.


Wata irin k'ara mom tasaki tare da sakin Basmah gefe kan dady tayo dake k'ok'arin rik'eta suka fad'i k'asa aikuwa mom tasamu yanda takeso ta k'ank'amesa sunata birkid'a tsakar d'aki da sunan itama batada lafiya sai gumza takeyi, gaba d'aya burinta yanzu bai wuce tadena jin abunda takeji ajikinta ba, da zaran dady ya yunk'ura yatashi sai mom tajawosa sufad'i tare ganin haka yasa Billy ta rik'o Basmah tana kukan k'arya, " yayya Basmah sannu don Allah kitashi kinga har kinsa mom itama cikin wani hali"


Saida dady yayi da gaske yasamu ya kucce hannun mom ai kuwa da gudu yabar falon yacire makullin k'ofar yarufo d'akin tare da sa makulli tanan waje ya rufesu. 


Da sauri Batool taja Basmah suka shige cikin d'aki suna dariyar mulmular da dady sukayi afalo, Batool takalli Basmah tace


"Yayya dama mom nada aljanune?" Bansani ba kije kitambayeta.


Dady kuwa da duk jikinsa keyi masa ciwo yanufi d'akin ya Mahmud, karo yayi dashi yasanyo riga birkice cikin tashin hankali yace


"Yawwa my son, ungo makullin nan kaje part d'in mom d'inka Basmah batada lafiya sanadiyar haka itama mom d'inka inaga aljanu sunshigeta sune suka tasar mata, amma sunada matuk'ar had'ari don masu kayarwane da mulmula, kabi ahankali kuma kafara saka karatu awayarka kafin kashiga, maza kaje ganinan dawowa zand'auko habbatussaudane da nake amfani da ita sai asamata...















*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____37💎



   Kamar ya 'yar uwa tafad'a tana kai kallonta ga k'afar tata, duk'awa tayi arud'e had'e da tallafo k'afar, "Ayya Allah ya sawak'e banzata ciwon zaiyi haka ba, sorry, bari narik'aki kisamu kiyo arwala lokacin sallah na wucewa, sak'alo hannunta tayi awuyanta tana takawa ahankali, cikin k'arfin hali take taka k'afar tana hawaye har suka isa toilet d'in, da taimakon Basmah tayo arwalar sannan suka fito, sallarma azaune tayita saboda zugin da k'afar keyi mata. Tun tana daurewa har tafara kuka da gaske da gaske,


Ummi kuwa tana gama sallah ita da Billy suka nufi part d'in mom cike da fargabar yanayin da zasu isko, sallamar suce tsaida Basmah daga rarrashin da takeyiwa Batool dake faman kuka sharkat, da sauri ta tashi tanufi bakin k'ofar palourn da suke faman doka sallama, bud'ewa tayi tare da fad'in "Ummi kece a safiyar nan, ina kwana?" Murmushi tayi tare da jawota ajikinta "aidole ne tasa, tunjiya nadamu da sanin wane hali kike ciki, but alhmdllh naga kinji sauki" shiru tayi batare da tace komai ba wannan ne yaba Ummi damar jiyo kukan da Batool keyi, cikin rashin fahimta tare da neman k'arin bayani don tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyo mata tace


"Basmah kukan wa nakeji kaman na Batool?"


"Eh Ummi itane" 


"Aww.dama itace ba lafiya naji kamar dadynku yace momyn kuce ba tada lafiya?"


"Eh itama mom batajin dad'i, daga bayani itama Batool taji ciwo ak'afa"


"Subhanallahi agarin yaya?" Ganin zancen na nema yayi tsayi yasa Basmah cewa


"Ummi kishigo daga ciki mana, sister shigo ko?" Tak'arasa fad'a tare rik'o hannun Billy, ko kad'an Ummi bataso shiga d'akin ba saboda sanin halin mom amma donkar Basmah taji ba dad'i kuma kamar tanuna less care yasa ta tsarkake zuciyarta ta shiga, mom kuwa adai dai lokacin da Ummi ke fad'in ta zata dady momce yake fad'in batada lafiya tafito daga toilet, maganar kad'ai ce tadaki kunnenta aikuwa taji kamar tafasa ihu, wato dady zuwa yayi yana tallarta awajen Ummi yana fad'a mata duk halin da take ciki, lallai dady yayi kuskure daya aikata hakan, tana wannan tunanin ne Basmah tashigo d'akin, gaisheta tayi tare da yimata ya jiki sannan tafad'a mata cewa Ummi na a palour tazo ganinta, amsawa mom tayi tare da tambayarta itama ya nata jikin?


"Alhmdllh mom naji sauk'i Batool dai ce kefaman kuka k'afarta ta e, da sauri mom ta tashi daga ita sai towel d'aure ajikinta wanda iyakarsa giuwarta tanufi d'akin su Batool, a palour taci karo da ita zaune ak'asa ta d'ora kanta ajikin Ummi dake zaune akan kujera har lokacin tana kuka, burki mom taja kafin ta maida kallonta ga k'afar Batool data kumbure sannan ta kalli Ummi dake shafa kanta ahankali, cikin takaici tayi saurin komawa d'aki ta sanyo doguwar riga tadawo falon, ita dai Basmah biye take da mom tana kallon ikon Allah, shin wai koda gaskene aljanu sunfara shafar mom d'insu? Batasha mamaki ba saida ta hango mom tana sakarwa Ummi wani shu'umin murmushi kamar ba itaba, cikin natsuwa suka shiga gaisawa da Ummi dake yimata yajiki tare da jajanta abunda yafaru da Batool d'in, hakama Billy itama gaisheta tayi tayimata yajiki sannan tajuya tana rarrashin twiny d'inta dake kuka. 


Azahiri babu wani abun da mom ta nunawa ummi na Allah ya waddai amma abad'ini wani takaicine da bak'in cikin ganin fuskar Ummi kwance acikin k'asan zuciyarta kecinta. Ba kad'an Ummi tayi farincikin ganin canji daga wajen mom ba wanda har saida fuskarta ta bayyana hakan,


Allah yak'ara sauk'i Ummi tayi masu sannan tafice zuwa part d'inta, wani irin mugun kallon tsana tabita dashi wanda Billy kad'aice ta lura da hakan koshi don tajuyone tana yiwa Batool Allah yabida lpy, girgiza kai tayi bayan sufita aranta tace


"Mom kin zama zulwajahaini, meyasa koda yaushe take sakawa mutum yarda da ita agabansa amma tabisa da k'ulli tana cutar dashi abayan idonsa...hmmm ya Allah kashiryar da mom tagano gaskiya" tak'arasa zancen zucin daidai lokacin data turo k'ofar d'akin yaya Mahmud. Kwance yake shi dasu Bilal akan gado suna bacci dama tunda suka dawo sallah da asuba dady ya wuce part d'insa sukuma sukabi yaya Mahmud d'akinsa. Tilawar azkar sukayi kafin rana tafito sannan suka koma suka kwanta do kowanensu akwai bacci kwance a idonsa. Knocking ta shigayi da d'an k'arfin kafin tace


"Wakeup yaya" tafad'a da k'arfi cikin yanayin damuwa, 


"Pls katashi mana, wlh k'afar my twiny ta kumbure sosai sai kuka takeyi"












 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_ina mai baku hak'uri bisa rashin samun update d'ina jiya hakan yafarune bisa rashin lpy data d'an bijiro mani, haka kuma idan zaku lura mun samu doublecating na page 37 don haka kar wannan ya rud'aku yanzu zamuci gaba daga page 38 yazamana kenan munsamu page biyu masu numbering iri d'aya, hop kun fahimta?, thanks all_🤝🏻



💎Page_____38💎



    Tashi yayi had'e da dafe kansa yana kallon Bassam da Bilal dake gefensa sannan ya maida kallonsa gareta, "shikenan kije ganin zuwa kinji ko?" k'in yarda tayi tatafi saboda yanda taga yana k'ok'arin komawa ya kwanta da alama dai baccin bai ishesaba "pls Broth don Allah katashi muje, sosai fa take kuka" adole tasa yatashi yafad'a toilet, ganin haka yasa takoma part d'in mom wajen 'yar uwarta, tana shiga tasamu mom na zaune akusa da Batool d'in tana faman rarrashinta, hakan yasa Billy takasa k'arasawa wajen ta tsayawarta daga bakin k'ofa tana yiwa 'yar uwarta sannu, wata irin harara mom ke jefota da ita wacce tasata saurin noce kai k'asa ba tare da tasani ba. Basmah kuwa dake kitchen tana k'ok'arin had'a breakfast don yanzu ba laifi tad'an iya k'ananun girki da basuda wahala kamar ance tafito tahango Billy ajikin k'ofa tsaye, kallon mom tayi kafin tanufi wajenta tana fad'in "laahh...sister ashe baki wuce ba, mekikeyi anan shigo daga ciki mana" tak'arasa maganar had'e da rik'o hannunta, jawota tayi amma taga tak'i shigowa sai ma kallon mom da takeyi, ganin haka yasa tajawota da d'an k'arfi tana cewa


"Wai meye haka sister, kishigo mana, kina nufin mom d'ai zata zauna zaman jinyar twiny d'inki ba dake ba?"


"A'a yayya Basmah ai nakira ya Mahmud yazo sai akaita asibiti, bari inje Ummi kejirana" sallamar da yaya Mahmud yayi ce taba Basmah k'warin guiwar ida shigowa palourn rik'e da hannunta, cikin girmamawa suka gaishesa shima ya gaida mom had'e da yimata yajiki.kai dubansa yayi ga k'afar Batool data kumbure lokaci d'aya kuma yana kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tayi, sosai tabashi tausayi alokaci daya kuma sai ya tsinci kansa da jin haushin kansa na zamowa silar faruwar haka agareta, da ace bai kirata ba da duk haka bata faruba, kitchen Basmah tashiga ta kawo masu breakfast d'in data had'a, ruwan tea ne masu kabri sunsha kayan k'amshi sai biredi da soyayyen k'wai. Bata wahalda kantaba da d'orasu bisan dining table ba, anan falo inda suke zaune ta shimfid'a darduma mai d'an girma sannan ta d'ora kayan akai, Mik'ewa Billy da tund'azu take tsarge da kallon da mom ke watsa mata tayi zata fita, saurin dakatar da ita yaya Mahmud yayi lokacin da take k'ok'arin bi tagabansa, hannnunta ya rik'o yana fad'in "my sis ina kuma zakije bayan ga breakfast ankawo?"


"Am.ehm..dama ina son tashi tund'azu, Ummi ke jirana muhad'a breakfast"


"Koma kizauna tariga taga abunta, kafin in shigo saida na biya, acanma su Bassam nabarosu suna karyawa" ji mom tayi kamar tawatsa ihu, wai yanzu ita shikenan duk wani tsari nata data shirya ya watse, wannan bala'i da meyayi kama, ada tana tunanin mahmud kad'ai Ummi ta rabata dashi amma yanzu talura gaba d'aya 'ya'yan nata so take tarabata dasu, ace d'anta data haifa da cikinta in safiya tawaye sai yafara zuwa yadubo Aisha ya gaisheta kafin yazo itama ya gaisheta, duk da yasan cewa takwana cikin rashin lpy, wlh haka bazata sab'uba bindiga aruwa dolene tasakar mata mara tayi fitsari, ganin har lokacin yana rik'e da hannunta tayi tsaye batare data juyoba yasa mom ta ida hasala, a d'an tsawace tace


"My son cikamata hannu ta tafi tunda ni ba uwarta bace, tsoro takeji taci abinci anan kada azuba mata abunda zai kasheta ko, wato tana tunanin bak'in asirce asircen da uwarta keyi dabin bokaye shi nakeyi, ka cikata nace kosai naci mutuncinka, kada Allah yasa taci ita tasani. A take Billy tafashe da kuka ta k'wace hannunta daga rik'on da yayi mata tabar part d'in aguje zuciyarta na k'una, rai ab'ace Mahmud ya juyo yana kallon mom, har zaiyi magana sai kuma yafasa saboda tunanin rashin lpyr datake ciki amma ya qudurta aransa koyaushene sai yanunawa mom wannan kuskuren datayi, dubon Basmah da Batool dayaga suma fuskokinsu sun canza akan abunda mom tayi yayi sannan yace


"Batool kufito muje inkaiki asibiti, ina jiran ku awaje!" daga haka bai k'ara cewa komai ba yabar paloun ransa ab'ace batare da ya karya ba. Haka itama Basmah tarik'a 'yar uwarta suka koma d'akinsu suka shiryo, suna fitowa mom takallesu "Aw..kuma fitar zakuyi baku karya ba"


"Idan mundawo zamuci, bana son k'afar nan taci gaba da kumbure mata" Basmah tafad'a tana cigaba da tafiya rik'e da Batool dake tafiya dakyar ko k'afar bata iya takawa" mere baki mom tayi kafin tace


"Mtsss...aikin banza ku kuka sani, kada Allah ma yasa kuci masu bak'ar zuciya, ai tunda natab'a waccan manyar dole kud'au fushi dani, wawayen yara kawai, kuje kawai ko bakwaso dai nice nan uwarku"


Suna jin kalamanta amma babu wacce tayi yunk'urin tsayawa balle suyi abunda take so.


Daidai k'ofar fita sukaci karo da dady zai shigowa, gaisawa sukayi yana yimasu sannu dayake yaya Mahmud yafad'a masa zancen zuwa asibitin, yayi masu adawo lpy sannan yawuce daga ciki sukuma suka fito suna d'an waige waigen inda zasu hango yaya Mahmud d'in.


Lokacin da yafito shi kuma part d'in Ummi ya nufa saboda ya rarrashi 'yar uwarsa amma sai ya tarar bata can dady kad'ai ya isko suna gaisawa da ummi sai su Bassam dake game d'innan da ake had'a mota ko gida ko shape d'in wani abu da wasu pieces d'in abubuwa, duk inda yake tsammanin ganinta acikin gidan yaduba amma bai ganeta ba, tsaye yayi had'e da rufe bakinsa da hannu yana shafowa har zuwa hab'arsa, gaba d'aya yarasa dalilin da yasa mom d'insa keyiwa 'yar uwarsa haka, tunowa yayi da wurin da take yawan zama idan irin haka yafaru da ita, da d'an sauri sauri yanufi part d'in dady ya bud'e k'ofar saman upstairs d'in ya hangota kamar yanda yayi tsamnani ta kifa kanta saman cinyoyinta tana kuka. Ahankali ya k'arasa wajen ya nemi wuri akusa da ita ya zauna, saida yaji kukan yad'an tsagaita sannan yafara magana cikin muryar dake nuna lallashi da tausayinta "kiyi hak'uri! Tabbas nasan mom d'ina bata kyautatawa, amma inaso kisani kowane mutum da halinsa ake zama, sannan wannan abun da takeyi nasani wani gurb'ataccen tunani kesakata yin hakan, wlh nikaina natsani wasu abubuwan da takeyi, shin kiyi tunani dani dakeda mom dake dake da Ummi wayafi kamata yayi kuka?, ina so kifahimci cewa bake kad'ai hakan kefaruwa akankiba akwai dubbanninki dake da irin matsalarki wasun suma tafi taki, amma sukayi hak'uri sai abun yazama tarihi, kisani duk abun d'a yanaso yaga mahaifiyarsa cikin salihan bayi domin shine zai sakashi alfahari, idan  kuma yaga mahaifiyarsa a akasin haka dolene yazamo maitakaici da b'acin rai, ina son mom kullum fatana Allah ya sauya mata wannan mummunan tunani izuwa kyakkyawa, to amatsayin ki na 'yar uwata kema haka yakamata kiyi bawai kinuna damuwarki akan kalamanta ba, tunda kinsan bahaka bane,


Kafad'unta ya dafa sannan yace


"Don Allah kiyi hak'uri kiyafewa mom d'ina ko don karamci da Allah yayi maki na samun nagartacciyar mahaifiya kamar Ummi" sosai kalamansa suka saka jikinta yayi sanyi, sai taji tabbas haka maganarsa take shiya kamata yayi kuka da jarabawar da Allah yayi masa na samun uwa mai tsananin zargi, zato, munana kyawawan abubuwa izuwa qazafi irin mom ba ita ba, nan da nan tausayinsa da kuma kanta na muzgunawar da take fuskanta daga wajen mahaifiyarsa ya kamata, d'ago kanta tayi suka had'a idanuwa ta sakar masa murmushin da yasa 'yan k'ananan idanuwanta k'ara shigewa saboda kukan da tayi tace


"Shikenan yaya babu komai na hak'ura" rungumeta yayi yana mayar mata da murmushin tare da cewa


"Thank you my sis, jazakillahu bikhair" yak'arasa fad'a yana d'an matse mata kumatu, sannan yace taje ta karya wajen ummi sai tazo sukai Batool asibiti, tare suka fito suna tafiya zuwa hanyar da zata rabu izuwa part d'in Ummi shi kuma ya wuce parking space ya fiddo da mota, hango su Basmah sukayi suma sun nufi wajen parking space d'in ya juyo yana kallonta


"Oyah maza kifito kije kiyi breakfast d'in sai mutafi"


"Nooo.bari kawai nashiryo idan mundawo nakarya" tafad'a had'e da d'an rugawa da gudu zuwa part d'insu.


K'arasawa shikuma yayi inda suke ya bud'e masu motar suka shiga sannan shima ya shiga ya tayar da motar, saida yaba motar wuta na tsawon mintuna biyar sannan yayo reverse da ita ya tsaya, dai dai nan Billy ta iso tsaye tayi agaban motar batare data shi gaba, zuge glass d'in yayi ahankali yana kallonta,


"Billy Japanese ya akayine?, kizagayo mana kishigo" yafad'a yana dariya don yasan duk duniya ba abunda ta tsana kamar shiga gaban mota, ji take kamar idon kowa na akanta.


"A'a yaya ni gaskiya bana son gaba sai dai in squatting zamuyi abaya" tafad'a tana k'ok'arin bud'e gefen da Batool ke zaune, yana kallo har tabud'e ta zauna, Batool da Basmah suka sakar mata murmushi had'e da cewa "sisto we are sorry for what happened"


"Kai auntys nothing much fa" had'e da maido hankalinta garesa, "yaya muje ko?" "Ina!?, tab ai wlh bako Mahmud ba, sai kace wani drivern ku" kashe motar yayi gaba d'aya sannan yakoma jikin seat d'insa ya lumshe idanuwansa, turo baki Batool tayi had'e da cewa


"Allah duk don bakusan me nakejiba da baku tsaya wannan kace nace d'in ba, waike twiny meye laifin ma gaban mota da bakyason zamansa?"


"Tsoro kawai nakeji don bana son yawan kallo" tabata amsa atak'aice "mtsss...shikenan idan k'afar ta rub'e aka cire ai sai kuji dad'i" tafashe da kuka, duk abunda suke cewa yana jinsu murmushi kawai yakeyi abunsa don tabbas in d'ayansu bata dawo gaba ba, ba inda zaije dasu, sanin halinsa yasa Basmah tabud'e takoma agaban motar tana dariyar kukan da Batool kefamanyi, ada dai bata santa da shagwab'a ba amma d'an zaman nan da sukayi awajen Ummi duk takoya saboda kulawar da Ummi kebasu. Tayar da motar yayi suka fice maigadi na zuba masu kirari,


_Kaga babban yaya d'an gaban goshin alhaji, shalelen uwar d'akina, gaba salamun baya salamun 'yan ukun Ummi atafi lafiya adawo lafiya, gabanku alkhairi bayan ku alkhairi Allah dai yafidda mugu da duk wani mai mugun nufi acikinku_ maganar yak'arasa yana lowering voice d'insa gudun kada ya tonowa kansa bakin galma, abincinsa kuwa yak'are agidan, shigewa d'akinsa yayi yana cigaba da cewa "ato, aishi alkhairi dank'one kowa yayisa dole tafad'a don ko yaushene sai ya bayyana, amma nikam dole in iya bakina, ya na'iya da abunda yafi k'arfin wuta..."


Tunda taji muryarsa gabanta yafad'i abubuwan da suka faru jiya suka dinga dawo mata akai shikenan tasani yanzu kimarta da class d'inta da take tunk'aho dasu agabansa sun zube, abunda kuwa bata sani ba shine, gaba d'aya wannan tunanin baizo akan dady ba, shi kawai abunda ya d'auka aljanune suka shafeta, k'arasowa yayi tare da zaunawa kusa da ita


"Sannu Momyn yara ya jikin naki?"


"Alhamdulillah naji sauk'i" tafad'a kanta na ak'asa, duk'owa yayi yana kallonta sannan yace


"Kintabbata?" "Sosai kuwa" tabashi amsa had'e da yin murmushi, breakfast d'in dake gabanta ya shiga bubbud'ewa kafin yafara had'a tea d'in a cup yafara sha, kurb'awa yayi kad'an sannan ya maido kallonsa gareta "hope kinyi taking break d'in kema" girgiza masa kai tayi batare da tace komai ba, shi saima abun yabashi dariya wai yau mom ce dajin kunyarsa haka, anya kuwa ba wani salonne aljanun suka b'ullo mata dashi ba!. Cup d'in ya ajiye gefe ya sake d'aukan wani ya had'a tea mai kabri ya mik'a mata tare da zuba mata soyayyen k'wan ya ajiye agabanta sannan ya d'auki nashi tea d'in yaci gaba da sha, ahankali yata kanta da fira har tagano bai fahimci komai ba akan yanayin da tashiga jiya hakan yabata damar sakin jikinta dashi sukasha fira sosai sannan yabar falon zuciyarsa cike da tambayoyi akan abubuwan da suka faru da ita tsakanin jiya da yau, yana fita takoma d'aki ta d'auko wayarta takira hajia kilishi, bayan sun gaisa ta dinga kora mata bayanan abubun da suka faru da ita da kuma rashin cimma nasarar da basu samu ba, dariya hajia kilishi tayi sosai har tana fad'owa akan gado wanda hakan ya hasalar da mom takashe wa yarta, hajia kilishi na hawaye takira har sau biyu amma tak'i d'agawa saida takirata akaro na ukku sannan ta d'aga, gimtse dariyar tayi tare da cewa


"Sorry k'awata ai dole inyi dariya, cewafa kikayi kinyita birgima da alhaji a tsakar parlour wai izuwan aljanu duk don kirage zafi ai kinga dole inyi dariya, a gaskiya yaran nan basu kyauta makiba amma ai ba matsala tunda akwai sauran a ajiye ko?" Cikin wata irin murya mom tabugi gaba tace "sai inyi maki u....me dashi ai wlh ba alhaji ba ko duniya zan mallaka nabashi baya, tun jiya na yanke shawarar jefashi acikin masai na manta amma yanzu kin tunamun"


"Ke.ke..ke qawata wlh ajiyemun abunda inaso, da tsada nakarb'osa yanada kyau sosai wlh kawai kema don baku had'u bane, duk wannan yanayin da kika jiki wlh da alhajinki yazo hannu to shi zai tsinci kansa ahaka, tayanda kullum yana tare dake kuma bazai so b'acin rankiba don karki yimasa k'walele.."


"Mts..yo anfad'a maki ni jakace da zanjuri haka?, wlh ba tsinanniyar da zan ajiyewashi tayi amfani dashi, banza wai tukuna ma u..meye kika had'ani dashi?" Dariya hajia kilishi tasakeyi kafin tace


"Hmmm... Desire fluid ne da kuma sperm d'in ayu, ke banza na manta da sauran, kawai kibarshi tunda kinyi missing ushe mai aljanu"


"Mtsss..kidena wannan sakarcin kinemomun mafita, can da yawarki dake da maganin kuma wlh bazan ajiye maki Shiva"


"Shikenan naji tunda plan A and B kin ruguje mana su bari muje Plan C, kice alhajinki bai fahimci komai ba yagama yarda cewa aljanune ko?"


"Eh mana haka nake tunani"


"Good, da kanki kinsamo mana mafita, kuma natabbata zaiyi working, da wannan damar zakiyi amfani ki dinga sak'a mata makirci kala kala, ince dai tasan da wannan zancen?"


"Eh, don har tazo dubani"


"Wow, kinga saiki san tuggun da zakiyi mata awurinsa ta yanda alhaji zai tsaneta"


"Kamar ya?"


"Hmmm kiyi tunani, natabbata da kanki zaki shirya hakan, sai anjima zankiraki daga baya" sai da mom tayi wata irin dariyar shak'iyanci sannan tace


"Ai har nagama gano shirin da zanyi, kihuta qawata sai nakiraki" suka ajiye wayoyin atare mom najin wani irin nishad'i atare da ita.


Allah sarki Ummi da bata san me ake k'ullawa akan taba, ganin sauyin datayi a fuskar mom yasa tayi tunanin sake zuwa ta dubota anjima, ita kuwa gaba d'aya tagama shirya plan d'inta akan yadda zata soma had'ata da dady akan maganar da tayi d'azu cewa tabata mom d'in ce ba lafiya da taji dady nafad'i. 


A hankali tafito d'aki hannunta sargafe da hand bag d'inta cikin fararen kayanta na aiki, tsohon dake zaune akan kujera tsakar gida yana karanta jarida takalla tana murmushi taje ta rungumesa,


"Ina kwana Jaddi, ni zantafi nasoma yin latti"


"Oh nikuwa gashi ina son muyi wata magana maimahimmanci dake faraaha, amma shikenan idan kindawo mayi"


"To jaddi shikenan natafi"


"Adawo lafiya" cikin natsuwa take tafiyarta har ta isa bakin titi, mai adaidaita sahu tatara tafad'a masa inda zai kaita


A jidda specialist hospital yaya Mahmud yanufa, yana kaiwa yayi parking motarsa daga ciki, yabud'e masu suka rirrik'o Batool suka shiga da ita ciki tana takawa ahankali.





 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____39💎



   Suna shiga suka nemi wuri suka zauna, yaya Mahmud ya shiga lallatsa wayarsa don ganin family Dr. d'insu wato Dr. jamil, kusan ringing uku tanayi bai d'aga ba, da alama wani abun mai muhimmanci yakeyi, ganin haka yasa yadena kira yashiga waige waigen ta inda zaifara, dr.kamal ya hango wanda ya kula da case d'in Billy lokacin da batada lpy, da sauri yaci gabansa yana murmushi tare da mik'a masa hannu.


"Assalamu alaikum, morning dr." Cike da fara'a dr kamal yacire glass d'in dake idonsa shima yana mayar masa da murmushin da yake yi masa "wa'alaikassalam malam Mahmud yau kaine a asibitin namu"


"Wlh kuwa dr. Sister nace ba lafiya" tak'are maganar yana nuna masa inda suke zaune da hannu,


"Ayya kaddai ace 'yar gidan dady ce, don nalura k'anwar nan taka shagwab'abb'iyace shiyasa take yawan jima kanta."


"No bahaka bane, wannan karon Auntyn tace Batool, kuma nayita kiran dr. Jamil but not answer" 


"Eh to! Dayake gaskiya muna gudanar da wani muhimmin tarone anan ciki nak'arawa juna sani, nima yanzunnan nafito daga ciki zand'oko wasu takaddu da ake buk'ata awurin, but bari na had'aku da nurse faraaha idan ba serious case bane, idan kuma zaku iya jira nan da 1hr in sha Allah mun k'are kaga ni ko dr jamil we should handle the case" hannu yaya Mahmud ya mik'a masa had'e da cewa "noo..thank you very much, ko sister faraaha d'in muka samu gani is OK, am sorry na tsayar dakai" shima mik'a masa hannun yayi tare da cewa


"Habaa!..nothing much, u're welcome" sannan ya wuce, agurguje ya d'auko takardun a office d'insa sannan ya shiga wani office sai gashi sun fito tare da ita abayansa yana fad'a mata magana had'e da nuna mata inda su Mahmud suke zaune, murmushin ta mai k'ayatarwa tasake tana comperming d'insa cewa  babu wata matsala, wucewa yayi ita kuma ta doso wajen cikin tafiyar dake tabbatarwa duk wanda ke kallonta irin natsuwar da take da ita, mutuwar tsaye Mahmud yayi wajen kallonta har ta iso wajen ba tare da ya ankara ba, da gefen ido ta kallesa kafin ta d'auke kanta tana cigaba da murmushi, sallama tayi tana kallon Billy data ware idanuwa had'e da rufe baki 


"Laah aunty faraaha" ta taso da sauri ta rungumeta, 


"Lil sis kece kika k'ara zama 'yar lukuta haka, masha Allah, inasu ummi da Bilal lpy suke?"


"Lafiya klw aunty faraaha ya aiki kwana biyu kin b'uya, gaskiya nayi missing d'inki sosai" Billy ta fad'a tare da d'ago kai tana kallonta, harararta tayi tana fad'in 


"Ni cikani kafin raina ya b'aci, keda gaba d'aya tunda kuka bar asibiti nan kika manta dani, tukunama dai waye ba lafiya acikinku?" Tak'are maganar tana kallon gefen da mahmud ke tsaye ya shagala da kalonnta, Sai alokacin yadawo hayyacinsa, d'an sosa k'eyarsa kansa yayi kafin yace


"Am..sannu sister faraaha!, dama sister nace muka kawo tasamu 'yar matsala a k'afarta" yana mai nuna mata Batool dake zaune ta jingina kanta a kafad'ar Basmah, kallonsa tayi cike da yaba kyawon da yayi mata kafin tad'an basar tana fad'in.


"Sannu yaya Mahmud" tare da duk'awa tarik'o k'afar Batool


"Ayya sorry sister, me yasamekine?" Kamar jira Mahmud keyi yayi carab da maganar gudun kar Batool tafad'i cewa mom d'insu ce ta taushe mata k'afa yace


"Ammm..dama garin sauyawa fridge wajen zamane a kitchen ita da Basmah to ashe ita Basmah d'in bata rik'a dakyau ba sai tasakar matashi ak'afa" tun daga yanda Mahmud ke bayani faraaha ta tabbatar da bahaka bane d'ago kai tayi ta kallesa alamar ka tabbatar kuwa, batare da yace mata komai ba yabar wajen yana d'an murza saitin zuciyarsa, don har ga Allah d'ago kan da tayi tana kallonsa ba kad'an yaji wani abu ya dirar masa azuciya ba, mik'ewa tayi tacewa Billy sujirata yanzu zata dawo, orthopedic clinic d'in dake cikin asibitin tanufa,

bayan kamar minti biyar sai gata tadawo tare da wata messenger ta turo irin kujeran nan da ake gungura marar lpy, rik'o Batool tayi da taimakon Basmah suka d'orata messenger d'in tajata tare da bin bayan sister faraaha, ganin haka yasa suma su Billy suka rufa mata baya, kasancewar asibitin kud'ice nan take ake ciro folder Batool k'wararren likitan dake on duty ya dubata da yake dama faraaha tariga tayi magana dashi, sosai ya duba k'afar had'e da d'an messaging d'inta, ihu sosai Batool keyi tana kiran "wayyo yaya Mahmud kataimakeni zanmutu, twiny kizo kusa dani don Allah wlh mutumennan ba yada imani, yayya Basmah don Allah ina kike kuzo kutai makeni" cikin kwanciyar hankali matashin dr. Dake sanye da glass ke aiwatar da jikinsa batare daya damu da ihun da takeyi ba, "wayyo yay..." da sauri ya katseta tare da d'ago kansa yana fad'in


"If you shout again i will cut ur leg" sannan yaci gaba da murza k'afar, kuka take rerawa tamkar wacce akayiwa mutuwa shi abun ma sai yabashi dariya. Aransa kuwa cewa yake lallai wannan yarinya duk wanda ya kwasheta zaisha fama da rakin tsiya, shi alokacin da yaga an gungurota cikin keken mararsa lafiya ya d'auka wani serious injury ne da ita, ashe waima d'an targad'ene tayi shine ake wani gungurota akeke, to inata ace kariyace tayi ko gwabcewa, wai! Yafad'a afili batare da yasan maganar tafitoba, wani haushine ya kama Batool jin abunda yafad'a, wato ita da ciwo shida fad'in wai!, tattakewa tayi ta rafka wani uban ihu tare da kiran Ummiii, tsabar yanda ihun ya firgita dr. Saida ya tashi fad'uwa da sauri ya rik'e gefen gadon wanda har saida yabuge goshinsa da gefen wata drower da ake ajiye takaddu aciki, faraaha ce tabud'o gambun office d'in da k'arfi tashigo don ganin ko lafiya Batool ke zabga wannan uban ihu da yawuce ace na treatment ne. Tsaye ta iskosa yana k'ok'arin daidaita zaman curt d'insa tasama had'e da necktight d'insa yab'ata fuska sosai, akan kujerarsa yakoma ya zauna sannan yajawo wata takarda dake saman table d'in dake gabansa ya d'anyi rubuce rubuce akai sannan ya kalli Batool da har lokacin tana kwance tana sharb'ar hawaye ak'asan zuciyarta kuwa dariyace take sosai tare da jin dad'in yanda ta rama cutar da yake yimata. Ad'an tsorace faraaha takallesa tace


"Dr injin dai lafiya naji patient d'in taka nata ihu" da yake suna d'an wasa tsakanin su shiyasa tasamu damar yimasa wannan tambayar.


Cike da jin haushin ta da tazamo solar had'ashi da wannan muguwar patient yace


"Ai sai kije kitambayeta, ungo takardar maganinku, insha Allah babu wata matsala d'an targad'ene taji" tare da mik'a mata takardar ta karb'a sannan tanufi inda Batool d'in ke kwance, haushin sane yak'ara rufeta lokacin dataji yace wai d'an targad'ene taji, wato don baisan irin zafin da takeji ba shiyasa yake kiransa da wai d'an, k'wafa tayi tana k'ok'arin saukowa daga kan gadon suka had'a ido dashi ta zabga masa wata irin harara dake nuna kaima Allah ya had'aka da irin wannan targad'en da kake kira wai d'an, kallo yabita dashi ganin yanda faraaha tarik'ota tana faman tsilga k'afa sai kace wata gurguwa, juyowa faraaha tayi tace "Thank you dr. Ahmad" murmushi kawai yayi mata kafin ya cije baki had'e da girgiza kai "yarinya Allah ya sake maidoki anan kuma muhad'u wlh sai kin yabawa aya zak'i" yafad'a acikin zuciyarsa yana k'ok'arin ajiye folder d'inta gefe, har ya ajiye sai kuma ya sake d'auko wa yana karanta sunan da aka rubuta ajiki,  _FATIMA BASHAR MAI FURNITURES_ sunan ya sake maimatawa afili sannan ya maida folder d'in ya aje.


Suna fita Batool takalli faraaha tace


"Sister don Allah ko ciwo zai kasheni kada ki k'ara had'ani da wannan dr.wa naji kince masa? Wlh he's very wicked, kinji yanda yake murzammun kafarnan kamar yasamu busashshiyar gyad'a? Wlh Allah zai isarmun mugu kawai!" Dariya faraaha tayi had'e da sakinta tace


"Ok, tunda zaginsa ma zakiyi duk wannan taimako da yayi maki ni bazan rik'a kiba, sai kiyi tafiyarki da kanki" turo baki tayi tana d'an k'ok'arin takawa da kanta, aikuwa kamar wasa taji tana iya tafiya da kanta duk da tana d'an jin zafi kad'an ak'afar, juyowa tayi tace da ita


"Laa..sister duba kiga ina iya tafiya da kaina" 


"Eh mana ai duk waccan muguntar da kike cewa yayi maki itace silar iya tafiyarki, kinga dr. Ahmad mutumne mai kirki da sauk'in hali sosai, kawai shidai bai fiye son tsiwa da rashin kunya bane, ko nice shi zanyi maki fiye da yanda yai maki, irin wannan ihu da kike yimasa ai sai kisa masu k'aramar fahimta su zargesa" turo baki Batool tasakeyi sannan tace "yo ai da zafi yakemun kuma hadda cewa wai zai yankamun k'afa idan ban rufe masa baki ba" saida faraaha tayi dariya sosai sannan tace


"Baki sanshi bane, ai haka yake da son zolaya, kawai yafad'ane don kiyi shiru amma ba yana nufin haka ba" k'ok'arin wata maganar tayi takatseta "kinga muje kada kisa kafara nemana awurin aiki, Mahmud kam yau kasa b'oye abunda keransa yayi har saida ya furtawa faraaha yana k'aunarta, duk da yakasa samun kyakkyawar kulawa da amsa daga wajenta saboda yanayin aiki da take ciki saida ya nace mata sosai yabarsu Batool can acikin mota, dak'yar yasamu ta bashi lambarta koshi don taga yana son takura mata awajen aikine.












 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____40💎



  Sosai faraaha kebin farinciki aranta saboda cimma burin soyayyarta datayi wajen yaya Mahmud, tun lokacin da aka sallamesu asibiti take d'awainiya da soyayyarsa azuciya kuma dai dai da second d'aya bata tab'a fitaba, taso taja masa aji sosai lokacin daya furta Kalmar so agareta amma tsoron kada ajin ya tsinke takasa samun tudun dafawa ya sata bada kai bori yahau, a natse take aikinta fuskarta d'auke da murmushi tana tunano kyakkyawar fuskar her first luv d'inta, haka tab'an garen Mahmud shima bakinsa kasa rufuwa yayi tsabar farincikin samun soyayyar da yake tunanin ta kucce masa ada duk da cewa ko yanzu bayada tabbaci akan  amsa tayin soyayyar sa, cike da farinciki ya saki stearing motar had'e da murza tafin hannunsa yana fad'in " Thank you ya rabh for making us together again" Murmushi Basmah dake gefensa tayi don tagama fahimtar hak'ar faraaha ta cimma ruwa, gefe ta maida kanta tana kallon yanda motoci kewucewa kan titin, yayinda ita kuma Billy tamatso inda suke ta tsakanin kujerar ya Mahmud da kujerar Bassam tadafa kamar yanda yara keyi sannan tace


"My broth wai mekake yiwa wannan sabbatun haka, pls don Allah karik'e motarnan kada kasa mubuga" dafe stearing d'in yayi yana dariyar da saida gaba d'aya fararen hak'oransa suka bayyana kafin yace "Bari kawai my sister abun sirrine, zamu magantu anjima, yawwa bari natambayeki wai tunda aka sallamoki asibiti kinyiwa sister faraaha godiya kuwa?, kinsanfa ta taimaka maki sosai lokacin" Billy tace "a'a ni kwata kwatama na manta da ummi nada nombert balle inkirata nayi godiya" juyowa yayi tare da d'aga hannunsa kamar zai doketa yace "ke ko!, kinfiye mantawa da alkhairi dole yau d'innan kikirata kiyi mata godiya" wata irin dariyace ta kuccewa Basmah har tana rik'e cikinta, juyowa tayi tana kallon Billy tace "Gaskiya sister yayankin nan ya fola (Teemah gabs word🤣) da yawa, irin wannan zance haka ai zai iya shek'eni wajen dariya" gaba d'ayansu suka kwashe da dariya suna fad'in "Gaskiya ne" rank'washi yakai mata akai daidai lokacin da yake k'ok'arin parking abakin wata had'ad'd'iyar restaurant "gulmammiya! wato tun yanzu zaki fara yimana putting eyes ko?" raurau tayi da idanuwanta da suka cika da hawaye don ita abu kad'an kesakata kuka kafin tace "Kai yaya da zafi fa" sorry yafad'a tare da bud'e gambun motar yana fad'in "kufito muyi breakfast yau yajin aiki zamuyiwa girkinsu Ummi" turo baki Basmah tayi tana d'an goge hawayen da suka zubo mata, ahankali tayi k'asa da muryarta tace "Bawani can kai dai kawai kace 'yar k'aramar liyafa zaka had'a mana, tamurnar samun soyayyar faraaha"  yana jinta ya saki murmushi kawai ya wuce abunsa batare da yace komai ba sannan suma suka fito suka rufa masa baya, kowace abunda takeso tafad'a aka kawo masu, sunci sun sha sunyi nak sannan yaje dasu shop d'in dake gefe a cikin restaurant d'in, chaoculate ya kwasar masu sosai da biscuit biscuit sannan yaje ya biya kud'in suka kamo hanyar gida, Batool kam Alhamdulillah tasamu sauki a k'afarta sosai duk da har yanzu tana d'an d'ingishi da ita, suna isa suka fito motar da gudu suka nufi part d'in Ummi suna dariyar yanda yayan nasu duk yabi yarud'e akan faraaha yanata zuba masu kyauta, dariyar shima yayi tare da rik'o Batool dake tafiya ahankali don bazata iya guduba "sannu Batool d'in mom" yafad'a sunaci gaba da tafiya ahankali hannunsa rik'e da ita har suka iso part d'in Ummi tana bashi labarin yanda faraaha ta taimaka mata d'azu, wani irin farinciki yak'ara tsintar kansa aciki yanaji a wannan karon bazai tab'a yadda nauyin bakinsa yakaisa ga rasataba.


A  parlour suka tadda ummi zaune tana yanke wa su Bassam akaifa (qumba), Basmah tazo tabayanta ta sagalo hannuwanta a wuyan Ummi tana fad'in "Ummi sannu da aiki" had'e da bugo k'eyar Bassam dake zaune ana yanke masa yatsan k'arshe nak'afarsa "kai d'an lukuti tashi kabamu waje tsogumi zanyiwa Ummi" d'ago kai yayi zaiyi kuka Billy dake zaune kan kujera gefen da Ummi kezaune k'asa tajawo hannunsa ta d'orasa akan cinyarta tace "k'yale yayya Basmah nafahimci 'yar k'ibar nan tamu ta tsole mata ido, magani yakan farcen da Ummi tayi maka gayuuu" da haka ta badalar dashi daga kukan da yake shirinyi, ita kuwa Ummi dariya tayi tace 


"A'a..nifa dad'ine dake kenan Basmah bakya girma, yanzu da kinsa na yanke masa farce da kika fad'omun haka, cikamun wuya tunda kina neman samun yaro kuka" sakinta Basmah tayi tana dariya had'e da cewa


"Kai Ummi sorry irin wannan gwatsilewa haka ai sai kisa yaya yimun dariya idan yana wajen" "ai kuwa baki tsiraba tunda gani awajen ko yanzu" taji muryarsa da shigowarsa kenan yana dariya shida Batool, juyowa tayi takalli Ummi "Kin gani ko Ummi dama nafad'a maki" hannu ummi tasa tashafo fuskarta sannan tace "K'yaleshi fad'amun wane labarin kika kawomun yarinyar momy" da sauri ya k'araso wajen yatureta gefe "pls Ummi kada kisaurareta, wannan alk'awarinane ko meye da kaina zan sanar dake in lokaci yayi"


"Wlh kada kiyarda Ummi wayau zaiyi maki, kawai kabari infad'a idan kai kunya kakeji, Ummi wlh yaya ya.." Filo ya d'auka throw pillow yad'auka ya jefeta dashi takasa k'arasa maganar,


"A'a babanah wai meye haka kake b'oyewa 'yar taka ko ba'a sone inji" ummi tafad'a tana murmushi


"Ummi zakiji amma ba yanzuba" saida Basmah takai bakin k'ofar fita parlour tace "Ummi yaya Mahmud da nurse d'innan faraaha sun fola" tana gama fad'a taruga aguje tayi wajen mom tana dariya, sosai ummi kedariyar itama tana tambayar Basmah data dad'e da barin wajen wai meye fola. "Babana wannan yaren fola a ina Basmah ta samoshi, wai sun fola" tafad'a cike da mamaki, Billy ce tayi saurin cewa "waifa sun fad'a soyayyar juna take nufi ummi" 


"Allah sarki, da gaskene babana?

Mahmud da gaba d'aya kunya tarufeshi ya sosa kansa yana kallon Batool dake can gefe zaune itama tana yiwa su Bilal wasa abunsu tayi kamar bata san suna firar ba.


Murmushi Ummi tayi "ah to madallah, aiki yarinyar nada hankali sosai Allah yasa matarkace idan alkhairi ce agareka, nikam naji dad'in wannan folawar, shin haka ake fad'a ko Bilkisu?" tak'arasa zancen tana kallon billy dake faman dariya,


"Kai ummi haddake ke fad'in haka kuma?, nifa kalmarma dariya take bani, Basmah bataji wlh awajen wata qawarta Teemah gabs ta d'auko wannan yaren"


"Aw.. ashe kema Billy fad'a kawai kikayi bakisan meye ma'anar  saba" ummi tace haka tana dariya, anan dai suka zauna suna cigaba da yin firarsu hankali kwance abun gwanin ban Sha'awa kai kace Ummi ce tahaifesu gaba d'aya.


Duk wani shiri da mom zatayi ga Ummi idan dady yadawo part d'in taga abunta, ai kuwa yana dawowa ko sannu da zuwa mom bata yi masa ba lokacin da yashiga part d'inta, tanajin sallamarsa zai shigowa d'akin tafashe da kukan munafucci, da sauri ya ida shigowa d'akin yana tambayarta kome kefaruwa da ita amma tak'i tankasa sai kukanta take rabka, tagumi yabuga yana kallon ikon Allah kafin can yasake cewa "Momyn yara don Allah kidena wannan kukan, kifad'amun menene yafaru idan kuma laifi nayi makine ai saiki fad'a mani ko?" Cikin kukan tace


"Haba alhaji kaduba kagani tunjiya dana sanyo k'afata cikin gidannan nakasa samun kwanciyar hankali da natsuwa, yarana duk sungujeni saboda tsorata da sukayi da yanayin da suka ganni jiya aciki wanda nikaina ban tab'a tsintar kaina acikiba sai jiya, yau kuma ina tunanin babu wanda yasan da haka daga mijina sai 'ya'yana ashe kaje kafad'awa aunty Aisha, har nan part d'in tazo tana yimani sannu wai tunjiya daka fad'a mata banida lpy taso tazo dubani amma kace tayi zamanta muggan aljannune dani, haba alhaji ashe kai bamai rufe asirina bane, har take cewa Allah yasa ba nagadone nakwaso ba, kenan so take tayi mun anan maganganu ga iyayena don taga nadawo daga wajensu" wani irin kuka mom tasake fashewa dashi wanda dole dady yayarda da cewa bak'in ciki da munin kalaman da Aisha tayi matane yasata cikin wannan k'uncin da yakaita ga zubar da hawaye shiru yayi yana nazarin kalaman da shi kad'ai yasan zuciyarsa ta raya masa cewa mom aljanu sun shafeta sai kuma Mahmud daya fad'ama, kuma ya tabbata mahmud bazai fad'awa Ummi halin da mom d'inshi tashiga ciki ba saboda yasan irin hankali da tunanin da yake dashi, dole sai in fitowa Ummi tayi taji yana fad'a masa shine tayi amfani da wannan damar don ta muzguna mata, wani b'angaren zuciyarsa tace ko kad'an wannan ba halin rabba'atul bait d'inka bane ba zatayi hakan ba, yayin da wani b'an garen kuma yabashi cewa ai ajizancin d'an Adam na iyasa tayi haka tabbas in hakane Aisha bata kyau taba don tasani baitab'a zuwa yafad'a mata sirrin dake tsakaninsa da matarsa ba kamar yanda itama baitab'a fad'in nataba awurin mom, to don me zatayi masa haka bayan tasan yana kamanta yimasu adalci, wato so takeyi ta sakashi cikin damuwa kenan" mom kuwa dake lek'ensa tana ganin yanda fuskarsa ta sauya zuwa alamun b'acin rai tak'ara volume d'in kukanta hadda wata sheshshekar kuka takeyi tanajan numfashinta, gudun kar tashiga yanayin data shiga jiya yasa dady yafara lallashinta yana bata hak'uri tare da tabbatar mata da zaid'auki k'wak'k'waran mataki, da haka yafito part d'in cikin b'acin rai zai shiga wajen ummi sai gashi yaga mota tashigo tayi parking cikin harabar gidan, da guda yaga junior d'an wajen k'anwarsa hajia hafsat dake aure borno yafito yayo wajensa yana fad'in "unclee..", cike da fara'a ya taromasa hannu ya chab'esa sama yana fad'in "oyoyo my son"


Wani kyakkyawan saurayi dako zai girmi yaya Mahmud bazai wuce da shekara uku ba naga yafito daga cikin motar tare da zagayawa tacan gefe yabud'e murfin motar, hajia hafsat ce tafito tana murmushi da farincikin ganin yayan nata, takowa takeyi zuwa wajensa shi kuma saurayin ya take mata baya yana sissinne kai k'asa, Mahmud kenan! yaro d'an kwalisa mai cikar zati da kuma kamala, farine sosai yanada dogon hanci sai dai bayada idanuwa sosai, bakinsa kuwa zaka d'auka jambakine aka shafa masa saboda yanda yake d'auke da k'ananun lab'b'a da ake kira pink lips, yanada matsakaicin tsawo kuma d'an kakkabrane saidai ba sosai ba. Yanada matuk'ar jinkunya ga magabatansa yayinda yake zama miskili cikin tsararrakinsa, awurin 'yan mata kuwa zaka d'auka shi kurmane, suna matuk'ar kama da Billy tayanda zaka d'auka shi yayantane, tunda yataso yake matuk'ar son Bilkisu saboda yanda ummansa kefad'in kamarsa da ita. Ko kad'an baya wasa da yaran gidan duk da zamowarsu taubasansa (cousins) amma indai Billy na awuri babu wanda yarena da zolaya kamarta, ita kuma hakan yasa bata fiye son suzo ba saboda d'aukar abun amatsayin takuratane yake, Mahmud shine first born d'in hajia Hafsat tana matuk'ar sonsa sosai saboda sunan mahaifin sane ya gada wato sunan mijinta kuma abbansa, sun tsaya masa sosai wajen karatunsa wanda saboda k'wazonsa yasa shima yake shallake duk wani matakin karatun da suka d'orasa akai cike da nasara, yanzu yanada shekara 30 cicciccif arayuwarsa, kuma yayi nasarar had'a degree ukku a wannan lokaci tafanni daban daban, yahad'a degree d'insa tafarko ne afannin computer science ta biyu kuma a fannin marketing ta ukku kuma a fannin koyon tuk'in jirgin sama wato pilot wanda yanzu haka ya samu aiki da wani kamfanin dake kula da zirga zirgar matafiya da 'yan kasuwa daga wata k'asar zuwa wata k'asar.


Cike da girmamawa hajia Hafsat suka gaisa da yayan nata dake d'auke da Junior yana fad'in 


"Oyoyo marabanku mutanen borno, barkarku da isowa" yana mik'awa mahmud hannu suka gaisa shima cike da girmamawa


"Yawwa yayana mun sameku lpy?" Tafad'a tana k'ok'arin bin bayan dady daya nufi hanyar part d'in Ummi da ita hannunsa na rik'e dana Mahmud d'in "mutanen sararin samaniya ya aikin injin babu wata matsala, murmusawa Mahmud d'in yayi kansa na duk'e ak'asa yace "Eh uncle Alhamdulillah za'ace" 


"To madallah Allah ya taimaka" ya amsa masa da amin


Ummi na kitchen tajiyo muryar dady na shigowa kuma da alama bashi kad'ai yake ba da mutane yake tafe, da sauri tad'aurayo hannunta a sink tasa k'aramin towel d'in dake sargafe acan gefe jikin bango tagoge hannunta tafito muryar hajia Hafsat tajiyo tsakar falo tana fad'in "kina ina matar yayana kuma aminiyata k'awar arzik'i, kifito uwar gida sarautar mata, tumin tsakar gida shaluguden mahassada, anbuga dake anbarki" kunyace tarufe ummi lokacin da tafito ta tarar da qanwar maigidanta kuma masoyiyarta tana kwararo mata wannan washi, da hanzari ta iso gareta cikin fara'a tana cewa "lale marhaba biki tsohuwar albarka ummu babanah gwaggon Babanah" dariya Hajia Hafsat tayi suka rungume juna.


Juyowa tayi tana k'ok'arin gaisheda dady da amsar junior dake hannunsa ya kauda kai gefe yana amsa mata ciki ciki, karb'ar yaron tayi cike da mamakin abunda yayi sai kuma tabasar akaci gaba da gaisawar yau sharabo, duk firar da suke dady na gefe abunsa yanata wasa da hannuwan junior, d'ago kai ummi tayi takalli Mahmud dake gefe tsaye yana raba idanuwa tace "Babana barka da hanya kazauna mana" kujerar dake facing room d'in su Bilkisu ya zauna yana cewa ummi


"Ummi wai ina su Bilkisu ne naji tsit" "suna ciki babana bari nakirata ku gaisa tashi tayi tashiga d'akin tasamu har tasoma yin bacci, bubbuga k'afarta tayi " ke Bilkisu wakeup, meke damunki zakiyi baccin marece bayan kinsan bashida kyau"


"Jina nakeyi so lonely saboda su yayya Basmah da suka tafiyarsu shiyasa baccin yasoma d'aukata"


"To ai sai kitashi gasu umman borno can sun iso sai kugaisa" zaro idanuwa waje Billy tayi had'e da d'an rufesu kad'an tabud'e "um.m.i injin batare da yaya Mahmud sukazo ba" tafad'a cikin i'iniya. 


"Mtss...ai sai kiyi zuwa kam don shima yafara tambayarki shine dalilin kiran danazo nayi maki" in zaki tashi kitafi kitashi kinga ni inda nayi. K'afafuwa tashiga shuahurawa tana murje murje akan gadon kafin tadafe kanta tana fad'in "wayyo ni Billy damuwata yazo, don Allah yaya mahmud kashafamun lpy?" Tajima zaune kafin ta tashi tashiga toilet, fuskarta ta wanko had'e da bakinta sannan ta zubo k'atoton hijabinta mai hannu har k'asa, ummi nafitowa ta d'auki waya takira yaya mahmud, yana d'auka tasanar dashi isowar su umman borno, da sauri ya matse wayar tare da wucewa part din mom d'insa ya sanar da ita, d'akinsu Basmah ya shiga suma yafad'a masu sannan yajuya zai fita rik'e dasu Bassam dake faman tsalle wai umman barno tazo zasuga junior da yaya Mahmud. Da sauri Basmah ta dakatar dashi fuskarta d'auke da farinciki "yaya tare da yaya Mahmud sukazo?" Kallonta yayi kafin yace


"Eh ina tunanin haka" wani irin tsalle tayo daga kan gado tace "jirani yaya" harararta yayi yana fad'in "hmmm yarinya kice kema kin fola" don nadad'e da fahimtar son yayancan naki kikeyi" yana gama fad'ar haka yawuce abunsa cike da shauk'in son ganin d'an uwansa da kuma gwaggonsa.


Tunda Billy tafito Mahmud ya tsareta da idanuwa ganin yanda ta canza cikin 'yan shekarunnan dabasu had'u ba, don sharabonsa da ganinta tun haihuwar junior gashi yanzu shekararsa biyu harda 'yan watanni, tafe take kanta aduk'e tana kallon k'asa shi kuwa hakan yabashi damar k'are mata kallo, duk da kasancewar bazasu shekarune da itaba tanada girman jikin da yabayyana surarta baisha mamaki ba saida tak'araso wajen tad'ago fuskarta tana gaida ummin borno da dady, sosai yashafa'a da kallon yanda d'an k'aramin bakinta kemotsawa wajen fitar da zazzak'ar muryarta da yakeji tamkar ana kad'ai sarewa, sau biyu tana gaishesa amma baijiba har saida ummansa tace


"Ikon Allah, Mahmud halama bakaji 'yata nagaisheka, kodai ka lorane" shafa sidebars d'insa yayi da hannu tare da sake kallonta kafin yace


"A'a ummanah ganin 'yar taki nayi kaman kajinnan naturawa shiyasa nake mamaki mutum da k'irar buloras"


Dariya dady yayi da tund'azu sai faman ciccije fuska yakeyi sannan yace


"To ai dukkunne yarona" gaba d'aya palourn sukasa dariya jin abunda dady yafad'a


Ita kuwa Basmah jiki narawa takalli Batool tace "sister don Allah kitashi muje, namatsu inga fuskar yaya Mahmud, fuskar da nadad'e ina mararin son gani, wai kinsan me nifa ina matuk'ar sonsa kuma wannan karon duk yanda zanyi in nuna masa zanyi  har yafahimci hakan" rungume pillow tayi had'e da runtse idanuwanta tace "ina matuk'ar k'aunarka yayanah"...



_Tirk'ashi, this is just d beginning, yanzu ma'anar Kalmar *'YAN UWANA NE* Zata bayyana afili, idan kun amince da cigaba da typing, ina jiran *comment* d'inku_


# *Team mahbasmah*#💋

            ❤❤

# *Team mahBilqees*#💋



👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_ina kike tawan *MEAMAH* dake group d'in rano online, gaisuwa tare da fatar alkhairi agareki, ina matuk'ar jinjina maki wajen bi biyar wannan littafi da kikeyi tare da sharhin a kowane page, tabbas hakan nabani nishad'i tare da k'warin guiwa sosai, ngd ngd jazakillahu bikhair am really appreciate💋Allah yabar tare_



💎Page_____41💎



   Tirk'ashi! Anya yayya Basmah zaki iya da wannan miskilanci na yaya Mahmud kuwa? Batool tafad'a tana turo idanuwa awaje, "hmmm shi so baya dubin yanayin rayuwar mutum kafin ya shigesa, dacewa ko rashinta, cancanta ko akasinta duka baya dubawa, kwatsam yake shiga azuciyar da Allah yanufi hakan atare da ita, ni bandamu da irin yanayin rayuwar saba, a Mahmud d'insa nake k'aunarsa tsakani da Allah acikin zuciyata, kuma rasashi zai iyasa nima narasa rayuwata, ina k'aunarsa irin k'aunar da bansan taya akayi nayi sakeba har tayi yad'on da zaiyi wuyar cirewa acikin zuciya taba, kawai fatana Allah yasa shima zai soni kamar yanda nake sonsa" ajiyar zuciya Batool tayi had'e da cewa amin ya Allah yayya Basmah ni har kinsa jikina yayi sanyi.


"Kidena zancen jikinki yayi sanyi kawai kitayani addu'a kuma kitashi muje mugaida umman borno kinsan halinta bata fiye son raini ba"


Tashi sukayi suka fara lek'awa wajen mom dake kwance abunta tana latsar waya "mom zamu tafi wajen umman borno mugaisheta"


"Ok sai kundawo, kuma ku kula da kanku tunda abokiyar tsibbon nata tazo kada acutarmun daku" batare da sun amsa taba suka wuce part d'in mom cike da takaicin wannan zargi da take yiwa Ummi, 


Tashi Billy tayi zata koma d'aki Ummi tace "ina kuma zuwa? Kije kitchen ki kawo abun tab'awa kafin inzo" kitchen tawuce tashiga har had'a fruit akan wani k'aton tray, sannan ta azo gorunan ruwa masu sanyi tare da lemun hollandia asaman wani madaidaicin tray sai kuma cups da wani tray data d'ora snaks akai, wani bowl tasamu ta zubo soyayyen naman rago da yasha kayan yaji da k'uli shima ta azo agefe. Tray d'in data d'ora ruwa had'e da cups da lemuna tafara d'aukowa tanufo palourn dasu tana shigowa saiga yaya Mahmud shima yashigo tare dasu Bassam, da gudu suka rugo suka rungume ummin borno suna yimata oyoyo, gaisheta shima yayi cikin girmamawa tare da nuna yanda sukayi kewarta sosai sannan ya gaida dady da ummi, juyowa wajen d'an uwansa yayi yana fad'in


"Welcome my big broth" tare da mik'a masa hannu suka gaisa sannan ya rungumesa yana murmushi, don kuwa ba kad'an sukayi farincikin ganin junan suba, 


Agaban umman barno Billy ta ajiye tray d'in, cup ta d'auka ta tsiyaya mata ruwan ta mik'a mata "sannu da hanya Umma" tafad'a tana k'ok'arin mik'ewa bayan ta karb'a.


"Yawwa Bilkisu sannu kinji ko? Allah yai maki albarka"


"Amin Umma" k'ok'arin komawa kitchen tayi don kwaso sauran kayan ummi tace "Aww Bilkisu dama haka ake tarbon bak'i? Kin bawa ummanki ruwa shine kika barmun d'a k'isar da yakwaso ahanya tasan yanda tayi dashi?" Kallonsa tayi ya sakar mata wani irin miskilin murmushi tare da cewa "ki k'yaleta Ummi kinsan bak'auya ce"


"Aikuwa naga alama, a ina natab'a ganin haka raba d'aya biyu"


"A'a nikam 'yatah wayayyace tunda tasan karrama iyaye" umman borno tafad'a daidai lokacin dasu Batool suka turo k'ofa tare da shigowa,


"Ai shikenan Umma taje abunta Allah yasa ba ita kad'aice k'anwata ba dana sha haushi" dariya gaba d'aya sukayi harda dady dake latse latsen wayarsa amma da alama hankalinsa na kansu, k'arasowa su Batool sukayi tare da duk'awa har k'asa suka gaida umman borno, cike da mamaki ta amsa ganin sauyin tarbiyar da tayi atare dasu da bata san da itaba, kallon Ummi tayi tace "are they my child" lumshe idanuwa ummi tayi umman borno tamik'o masu hannuwa tana fad'in "kumatso kusa dani 'yan matana, ahh lalle girma da hankali sunzo sai aure" haka ta dinga tsokanarsu cikin irin wasarnan ta uwa da d'ah dake nuna soyayya mai tsanani, juyowa sukayi suka gaida yaya Mahmud pilot ya amsa shima cikin sakin fuska tare da cewa


"Allah yayi ruwa tsiya tawanke, sister Basmah zubomun ruwa nasha k'auyancin qanwarki na nema yasa k'ishirwa tak'arar mun da yawu" yak'arasa zancen yana kallon Billy dake k'ok'arin ajiye tray d'in fruit d'in data kawo tana murmushi, wani irin farincikine marar misaltuwa yadira azuciyar Basmah lokacin da taji yanda sunata kefitowa daga bakin yaya Mahmud pilot, sai takeji tamkar yafi kowa iya fad'ar sunan, murmushin ta mai sanyi tasaki had'e da d'aukar cup tabud'e gorar ruwan ta tsiyaya masa ta mik'o masa kanta na sunkuye ak'asa saboda kwarjinin da yayi mata bazai barta ta iya had'a idanuwa dashi ba, shikuwa da hankalinsa na akan firar da sukeyi da yaya Mahmud koda yamik'o mata hannu tazata ya karb'a ta sakar masa, ashe shi kuma hannunsa bai ida kawowa ga cup d'in ba, kawai sai dai sukaji k'arar fad'uwar cup d'in yafashe ruwan suka zube akan tyles wasu kuma ajikinsa, da k'arfi yajuyo yana kallonta cike da jinhaushi yace "Another bak'auya, waccan tahanani ruwan, ita kuma wannan datazo bani saita jik'ani" yanda yake maganar sai yabawa kowa dariya haddai Billy da keyi da k'arfi tana faman rik'e ciki, d'ago kai yayi ya kalleta tayi saurin gintse dariyar kamar ba itaba, d'an k'aramin tsaki yayi sannan yabar palourn Umma da har lokacin dariya takeyi tace "ina kuma zakaje, ai kinmun daidai Basmah, bashine ciwon baki ba"


"Wlh Umma bada gangan nayi masa ba nazata yarik'a cup d'inne shiyasa nasaki" Basmah tafad'a kamar zatayi kuka, 


"Nasani Basmah da gangan nafad'i haka don yaji haushi tun d'azu yasaka k'anwarki agaba yana tsargata shiyasa nayi masa haka" gaba d'aya Basmah bataji dad'in abunda ya faruba duk sai taji badad'i aranta ganin haka yasa Umma ta dinga janta da fira don tad'an saki, anan take tambayarta ina mom d'insu injin dai lafiya take, so take tad'an huta sannan taje sugaisa, nan suke sanar da ita ai batajin dad'i amma da sauk'i, suna gama fad'ar haka suka wuce guading abunsu su uku suna firarsu tare da su bilal dake biye dasu abaya rik'e da hannun junior dama shi yaya mahmud tun d'azu yabi bayan d'an uwansa yana masa dariya had'e da tsokanarsa yana fad'in (another bak'auya, gaskiya broth kerenamun k'anne da yawa), duk da bawani shiri umman barno keyi da mom ba saida taji ba dad'i aranta, cikin kulawa da tausayawa tace


"Ayya Allah yabata lafiya, bari natashi naje na dubota,hajia Aisha ko zaki yimun rakkiyane?" murmushi Ummi tayi kafin tace


"Anya kuwa!, dak'yar gaskiya d'azu nashiga nadubota nida 'yarki duk da naso komawa ko yanzu amma zaifi dacewa ace kitafi ke kad'ai saboda kisamu ku soyewarku yanda ya kamata keda amaryar taki ni kuma sai na kula da yayan naki don da alama yana buk'atar magana dani" kasan cewar babu kowa afalon sai su ukun kuma dukkaninsu babu mai b'oyewa wani damuwarsa yasa dady ya d'ago kai yana kallon Ummi kafin yace


"Wace maganar zanyi dake bayan wacce nariga nafad'a maki jiya akan rashin lafiyar matata" kallon rashin fahimtar inda maganganunsa suka dosa Ummi tayi masa sannan tace


"Kamar ya abu Bilal?"


"Kamar yanda kikaje kika cemata nafad'a maki wai aljanune da ita kuma miyagu" dady yafad'a yana kallon cikin idanuwan ummi murmushi Ummi tayi don tasan dama za'a rina, ko kad'an batayi mamakin jin kalaman saba,hak'uri tasoma basa cikin natsuwa kafin tafara fayyace masa yanda akayi taji zancen mom batada lafiya da zuwan datayi ganinta da duk maganar data fad'a, sannan tace 


"Abu Bilal har ga Allah nazata cewa hajia Hussaina tacire tsabar da take yimun araina tadawo da nufin muyafi juna muzauna lafiya kamar yanda kafad'amun shine dalilin dayasa na amincewa zuciyata har naje part d'inta amma tunda abun yakasance kuma har kayarda umman yara muje narakaki daga nan sai nabata hak'uri" tana gama maganar tamik'e tsaye tana jiran tasowar umman borno data saki baki tana kallon dady.


A hankali yataso daga inda yake zaune yarik'o hannunta,


"Kiyi hak'uri rabba'atul bait, ko kad'an banyarda da abunda tafad'a ba kawai nayi hakan ne don nagano gaskiya kuma natabbatar da alk'awarin da tayimun na canza warta"


"Wlh karki yarda dashi k'awata, dad'in bakine yake son yimaki da kuma borin kunya, taya inhar bai yardaba zai dinga wane fuffuskewa ai tund'azu ina kalle dashi, hmmm yaya kabani kunya wlh kamarka ace har yanzu baka banbance munafuki da mumini abayyane, Allah ya kyauta dama tunda mukayi waya kace zata dawo nasan da wani abun aranta, oh ni hafsa wlh albasa batayo halin ruwa ba, Allah dai ya isarwa su papi da b'ata masu tarbiyar da suka bata datayi" umman borno ce kefad'ar haka cike da takaicin yayan nata,


"Haba hajia Hafsat, meyasa zaki fad'i haka nifa gyaran aure nasanki dashi ba b'atawa ba, kuma kinsani badon naso kamanta adalciba bazan fad'a mata komai ba sai dai na cigaba da fushi da ita kuma nad'auki hukuncin da naga dama akanta, plz rabba'atul bait kifahimceni kada kibiyewa zugar 'yar uwata har ga Allah ban gama yarda da zancen ba" ganin yanda dady yad'an marairaice mata yasa tace "shikenan komai yawuce amma daga yau zanci gaba da tsayawa a'inda Allah ya ajeni, inaso kafahimci cewa bana son fitina shiyasa banabi takan matsalolin matarka don Allah tabarni insamu natsuwa plz" katseta umman borno tayi "Ai kuwa yau sai kinso fitinarnan don dole kuhad'u part d'insa tamaimaita abunda tace kinyi mata agabanki inta isa"


"Shiiiiii... Ya isa Hafsat meye ribar yin hakan? Kawai mu manta da komai da alama yanzu yadawo ko hutawa baiyiba, dadyn yara komai yawuce kaje kahuta, ke kuma kitashi kije ku gaisa kafin akira magrib in kuma sai kinyi sallah zakije shikenan"


"Ba inda zanje wlh nama fasa zuwa ganin nata munafuka kawai da bataso azauna lafiya" murmushi Ummi tayi lokacin da taji dady yayi hugging d'inta had'e da cewa


"Thank you for given me a wanderful Peace in my entirely life" hararar umman barno yayi tare da cewa "kid'au darasi 'yar uwa" sannan ya ficewarsa zuciyarsa cike da farinciki sab'anin d'azu da yafito part din mom zuciyarsa a cunkushe anan kad'ai akwai zallar banbanci tsakanin Ummi da mom.


Yana fita Ummi tadawo tazauna akan kujerar da umman borno kezaune tasa hannu ta dafa kafad'anta, cire hannun nata umman borno tayi tana cewa


"Don Allah meye ribarki cikin kwantar da kan da kikeyi akan waccan matar, ke kenan cikin b'acin rai akan matsalolinta wlh ni hak'urinnan naki yafara tunzurani"


"Hmmm Hafsat kenan! Yanzu ke bakiga ribar haka da nake yiba?, dubi yanda mijina yafita yana farinciki, dubi yanda mijina ke lallashina da bani hak'uri abunda bakowace mace kesamun wannan matsayin acikin gidan taba, dubi yanda mijina ya gasgata zancena fiye da nata duk da kasancewar yanada damar k'aryata zancen kamar yanda yak'aryata nata yanzu, ai ko ahaka aka tsaya natabbata naci riba, balle a idanuwansa nahango tsantsar soyayyar data lunku azuciyarsa tawa, bazaki iya fahimtar hakan ba saboda sak'on akaina yayi tasiri shiyasa kike ganin laifina"


"Hmmm! Tabd'i jam dole yaya yace nad'au darasi, tabbas wannan itace kissa a ilmance, saita ingizo maki rigima kekuma saikiyi amfani da ita takoma makamin d'aukaka soyayyar ki azuciyar sa, dole na nemo sabon littafin d'aukar darussa ba darasi ba, madallah da samun nagartacciyar mace da yayana yayi kamarki" rungumeta tayi aranta tanajin cewa babu wanda yakai yayanta sa'ar mata kamar yanda tad'aya b'angaren take ganin babu wanda yayi rashin sa'ar k'arin aure kamarsa.


Tunda faraaha tadawo asibiti take jiran ganin call d'in first luv d'inta amma shiru, bini bani zata d'auko watarta tak'urawa nombarsa ido kozai kira, sai kuma tayi murmushi tare da dukan goshinta tana fad'in "kai faraaha kaffa kizubar da gp d'inki, irin wannan zak'ewa haka da yawa har ina" da zaran taji shigowar kira awayarta zata zata shine sai tad'auka da sauri sai taga ashe bashi bane,


A b'angaren dr. Ahmad kuwa yana dawowa daga asibiti kai tsaye yawuce d'akin maminsa agajiye ya fad'a kan gado tare da runtse idanuwansa, fuskar Batool ce tafad'o masa arai lokacin da yake murza mata k'afar da taji ciwo tana ihu, dariya yadingayi yana dafar cikinsa yana kwaikwayon ta "wayyo yaya Mahmud kataimakeni zan mutu, twiny kizo kusa dani don Allah...." Haka yadinga maimaita suruttan da takeyi yana dariya, mami dake acan bayan d'akin tana shanyar kaya tashigo aguje jin yanda yaron nata kefaman dariya alokaci guda kuma yana ihu, a d'an tsorace ta tsaya bakin k'ofar d'akin tana kallonsa cike da mamakin abunda yakeyi, ganin baida lokacin tsagaita dariyar tasa yasa tayi gyaran murya had'e da shigowa ciki fuskarta ad'aure tarik'o kunnensa tana fad'in.


"Kai meke faruwa da kaine? Bana son irin wannan banzar d'abi'a, meye haka kakeyi?" Tafad'a tana k'ara murd'e kunnensa da take rik'e dashi,


"Awshh...wayyi mamie bani bane, fatima ce, ita takeyi hakan" 


"Kai wato kafara shashanci a wajen aikin naka ko?, har ka manta yanayin da muke ciki, tukunama fad'amun waye fatima kafin inzane maka jiki" tana d'an kaimasa duka da hannu a kafad'a,


"Mami fatima itace trouble maker, wacce tasa yau jarumin d'anki yakoma soko agabanta, tasa goshinsa ya kumbura saboda tsananin rakinta, alokaci d'aya kuma tasa ya afka a ramin dake da matuk'ar wahalar fita..." 


Baki abud'e mami ke kallon yaron nata kafin tace...




 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FAR.  I💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Miliyoyan gaisuwa marar adada agareku masoyana, bakina bazai iya kwatanta godiyar da zanyi agareku ba saboda girmanta, all i say gaba d'ayanku Allah yabaku aljannah da rahamarsa, ina matuk'ar samun kuzari da k'warin guiwa bisa comment d'inku, Allah shine sheda ina sonku gaba d'ayanku harda wud'anda karantawa kad'ai sukeyi basa comment, ina fatan aljannah tazamo wurin had'uwar fuskokinmu aranar k'arshe, aciki gaba da hak'uri dani still mun sake samun page 40 har sau biyu don haka yau a page 42 zamu tashi insha Allah sai akula wud'ancan 2pages sun zama page 40 da 41_



💎Page_____42💎


 

    "Iko sai rabbana, Ahmad yanzu mekake so kafad'amun, kadai san yanayin da muke zaune aciki, kana ganin soyayya tanada muhallin da zaka iya bata yanzu?" Hannuwan mamy yarik'o cikin damuwa yace


"Yazanyi mamy harga Allah bntab'ajin ina son wata mace ba kamar yarinyar nan, narasa ko meye dalilin dayasa nakamu da soyayyarta baccin nasan yanayin da nake ciki, amma abu d'aya nasani samu da rashi duka na Allah ne, natabbata albashina zai taimaka mani wajen ganin nabiya dukkanin basosan dake kan mahaifina, jarabawar rayuwa babu ta yanda bata zowa bawa, fad'awa soyayyata bayana nufin karya alk'awarin mahaifina bane, da yardar Allah saina sauke wannan hakk'in nasa daya rataya awuyana, nidai fatana ki amince mani na nemi auren yarinyar nan don kai tsaye nake so inje da nufin aure bawai nema ba" mamy dake hawaye tace "Shikenan Ahmad, 'yar wane gidace yarinyar? Kuma ta amince tana sonka itama?"


"Ban sani ba mamy yau nahad'u da ita asibiti ankawota taji ciwo ak'afa nadubata, banyi mata zancen soyayya ba, amma naduba file d'inta 'yar gidan alhaji Bashar mai furnitures ce" dafe k'irji mamy tayi tana fad'in 


"Haba Ahmad, haba Ahmad, ina kai ina 'yar wannan gidan da babu wanda yasan iya adadin tarin yawan dukiyar da yake da itaba, karufa mani asiri kada kad'auko mana abunda yafi k'arfinmu" tak'arasa maganar hawaye cike tab a idanuwanta, ganin yanayin da mamynsa tashiga yasa ya rungumeta cike da tausayinta yace


"Shikenan, mamy zan barta innemi daidai dani idan hakan zai saki farinciki, amma inaso kisani mom arana d'aya naganta kuma arana d'aya naji k'aunarta araina amma wlh banajin zan iya fishsheta azuciyata cikin rana d'aya" d'agowa yayi daga jikinta yaci gaba da cewa "mamy kinsan meyasa nafad'a son yarinyar? Kawai jikinane yabani cewa zata kula mani da mahaifiyata fiye dani kaina, yanayainta tsarinta sun tabbatar mani da zata sakaki farinciki, zata cire maki kewar abbana daya rasu, amma idan kince in hak'ura da ita zan hak'ura mana tunda dama nikad'ai nake kid'ana kuma nake rawata" rik'o fuskarsa tayi tana hawaye "Aa my son dama ni walak'ancin masu kud'i nake jiyema, amma indai zakayi farinciki da samunta to kaje ka sanar da ita kuma katabbata kanemi aurenta ka kawo mani ita kaji ko, Allah ya dafa maka kuma yayi maka bud'i mai albarka kafin lokacin yayi kuma itama Allah yasa ta amince dakai?" Magana takeyi har lokacin hawaye na zubo mata a idanu, alokaci guda kuma tana murmushi, sake hugging nata yayi yace


"Nagode mamynah, ina sonki" da haka sukaci gaba da fira yana bata labarin abunda yafaru tsakaninsa da Batool tare da nuna mata inda yabugu a goshi har yad'an kumburo kad'an tana tayi masa dariya. 



'Dakin yaya Mahmud Mahmud pilot yanufa  cike da jin haushin dariyar da aka azamasa, kayansa yafara cirewa sannan ya shige toilet dama yanajin gajiya ya watso ruwa yana fitowa yaci karo da jikkar kayansa yaya Mahmud yashigo masa da ita, bud'ewa yayi yaciro black trouser da sea green d'in shirt yasaka fuskarnan tasa ad'aure, kallon yaya Mahmud dake zaune bisa kujera yana dannar wayarsa yayi yace


"Broth, muje ko?" Batare da ya kallesaba yake tambayarsa ina zasuje ina batun kiran sallar magrib don dama yasan halinsa idan yazo ba shida burin da yawuce sufita sud'an zazzagayo gari, cigaba da dannar wayarsa yayi ganin yaficewarsa batare daya amsa mashiba, dariya yayi had'e da cewa "kaji dashi indai gidannan ne bakaga komai ba wlh, dama ka ajiye wannan d'aurar fuskar agefe" koma shigewarsa yayi cikin kujera yaci gaba da kiran faraaha da tund'azu yake kira ba'a d'aga ba..ita kuwa faraaha dama tana waje wayar nacikin d'aki sai can tajiyo k'ararta, shiga d'akin tayi tare da d'aukar wayar tana murmushi saida takusa tsinkewa sannan ta d'aga had'e da karawa a kunnenta saita tsinci kanta da kasa furta kalma ko d'aya, "hello" yafurta masa aya b'angarensa yana mai sauke wata irin ajiyar zuciya. Lumshe idanuwanta tayi sannan tabud'esu tana murmushi batare da tace komai ba, jin haka yasa yaya Mahmud cigaba da cewa


"Hello my fa..raah!" Ya fad'a cikin wata sigar da dole yasa ta amsa masa da "Na'am" atak'aice.


"Hmmm!...ayiwa raguwar zuciyar nan dake da nacin tsiya, so da kaunar da nakeyi maki shi yajawo mata wannan raunin da bazata iya rabuwa dake ba, keyimun kowane irin hukunci bisa damunki da nakeyi amma banda hukuncin rashin kulawa da kuma hanani jin zazzak'ar muryarki" Murmushin da saida yaji sautinsa akunnensa tasaki sannan tace


"Wannan zuciyar dake tunanin tanada rauni tadad'e da samun tallafin wata zuciyar kamarta, wanda a yanzu yakamata tasani tasamu k'arfin da zata iya yak'ar kowane irin hukunci da zai iya gittowa akanta, bazan hukuntaka ta hanyar rashin kulawa ba ko hanaka jin muryata, amma zantabbatar da nahukuntaka ta hanyar nacewa zuciyarka da kuma ruhinka, zan sakaka azuciyata sannan inbuga maka takunkumin da babu wanda zai iya fiddoka aciki" d'ora kansa yayi ajikin kujera tare da rufe idanuwansa, yana jin wata mahaukaciyar soyayyar ta nafizgar kowane sashe daga jikinsa, a hankali ya furta


"Idan kuwa haka tafaru to tabbas nasamu cikakken adalci wajen hukuntawa, kiyarda dani faraah! sonki nakeyi da gaskiya kuma zan aureki matuk'ar kin amince dani" zaunawa tayi daga tsayen da take saboda yanda taji kalamansa sun yimata dirar mikiya acikin zuciya" cikin wata irin miskilar murya tace dashi,


"Bazan k'ikaba ko don zamewarka mutum nafarko da yayi dashe acikin zuciyata, amma inaso kabani dama innemi zab'in wanda ya halitto mana zuciyoyinmu don tabbatuwa bisa sirad'in da zai kaimu a ingantacciyar rayuwa"


"Na'amince faraah! Allah yazab'a mana duk abunda yafi zama alkhairi, zanjira amsarki tare dafatar zaki bani dama inci gaba da kiranki don bawa dashen danayi kulawa yanda yakamata"


"Bakada matsala indai akan wannan ne k'orafi yariga daya karb'u" dariya yaya Mahmud yayi kafin suci gaba da firarsu cikin so da k'auna.


A b'angaren Mahmud pilot kuwa yana fitowa ya nufi guarding don yarasa ina zaije yarage zafi, can nesa dasu Billy dake firarsu ta 'yan uwan juna ya zauna yana satar kallonsu d'aya bayan d'aya, Basmah da Batool kyawawan 'yan mata ne da babu namijin da zai kallesu baiji ya fad'awa sonsu ba, kusan kamar su d'aya amma Basmah tad'ara Batool haske sosai duk da itama d'in ba bak'a bace, ko kad'an basada wata k'iba ajikinsu amma hakan bai hana shape d'insu fitowaba, yayinda ita kuma Billy wankan tarwad'ace tanada jiki amma irin na lukutayen yaranda da zaran kadubesu zaka tabbatar da akwai hutawa atare dasu, tanada k'irar matan nan da ake kira da masu shape d'in coca cola, duk da kasancewar tanada k'ananan idanuwa da suka alak'anta yanayinta da mutanen Japanese hakan bai hana kyawon da Allah yayi mata bayyana ba. Murmushi Mahmud pilot yayi kafin yace


"She's very different and unique also she mean something something" yad'an d'ora hannunsa saiti da zuciyarsa yana k'ara k'aremata kallo.


Batool ce talura da hakan, tad'an kizgini Basmah da kafad'a tana nuna mata inda yake da idanuwa, murmushi tayi tana kallonsa tace "sisters kozaku rakani nabashi hak'uri akan abunda yafaru d'azu naga kamar ransa yab'aci sosai"


"Tab babu inda zanje, kiga mutum sai wani shan k'amshi yakeyi akan d'ai an watsa masa ruwa ajiki, sai kace wanda aka watsawa wuta!" Batool tafad'a tana k'ara gyara zamanta akan stone chair d'in da suke zaune, dukanta Basmah tayi cike da jin haushi aka fad'a tace "kinga matsalata dake rashin fahimta amma ai naga dai ko k'ak'ane an b'ata masa kuma yakamata abasa hak'uri ko Billy" tak'arasa maganar tana kallon Billy dake sakace 'yar dattin data shige mata a akaifa da yatsanta.


 

"Eh" Billy tafad'a atak'aice tana satar kallonsa. Hannunta Basmah tarik'e suka nufi wajensa kanta na sunkuye ak'asa har suka iso, itadai Billy ko kallon inda yake batayi ba, yayin da Basmah tace


"Yaya mahmud don Allah kayi hak'uri da abunda yafaru d'azu, banyi hakan da wata manufa ba, kuskurene kawai" d'ago kansa yayi yana kallonta sannan yayi murmushin da yasa banda Billy dake gefen Basmah da tuni jire ya d'ebeta tafad'i "kimanta kawai sister, komai ya wuce dama ni bake kika b'atamun rai ba, wannan damammiyar k'anwar takice mai fuskar Japanese data azamun dariya tafi b'atamun rai, zo zauna anan kibani labari kuma kice mata ta tafi kafin in mamaketa anan" farincikine ya bayyana a fuskar Basmah wanda alokaci d'aya taji duk damuwar da tashiga ta yaye mata, ita ko Billy najin haka tajuyawarta ba tare da tace masa komai ba don inda sabo tasaba da irin tsarguwar da yake yimata, hakan da tayi sai ya bak'anta masa rai cikin jin haushin halin ko inkula data nuna masa yasa mata k'afa aikuwa tayi baya da baya tafad'i k'asa, da sauri Basmah taduk'o tare dasa hannu biyu ta d'agota shikuwa yayi kamar bai ganetaba, kallonsa tayi idanuwanta cike tab da hawaye ya wani fuske tare da kauda kai gefe. Rik'eta Basmah tayi cike da kulawa tana tambayarta "sisto sannu injin baki jimuba" cije baki Billy tayi sannan ta wafce hannunta daga rik'on data yimata ta wuce abunta rai ab'ace. Mik'ewa yayi had'e da cewa "sister bari naje naji ankira sallah" 


"Shikenan yaya sai anjima" 


Batool kuwa dake kallon duk abunda kefaruwa dariya ta azawa Billy lokacin data k'araso wajen tana duba hannunta daya d'an tulb'e daga ciki, "sannu twiny wlh kinban dariya, kin kuwa ga yanda kika fad'i? Hhhh wlh yaya ya iya mugunta, shiyasa kikaga nace ba inda zanje koda yake ai duk laifin yayya Basmah ne data wani jaki bataje ita kad'ai ba" tana rufe baki taji an tallafo k'eyar kanta da duka ana fad'in


"To zuga zugi ai dai 'YAN UWANA NE dukansu baki isa ki had'ani dasu ba" d'ago kan da zatayi taga ashe Basmah ce ke fad'ar haka had'e da sakar mata harara, turo baki tayi da niyar magana itama Billy ta sakar mata rank'washi akai tabar wajen aguje tana dariya had'e da fad'in "ko akanki narage zafi" dariya Basmah tabushe da ita lokacin da taga Batool tabi bayanta itama tana fad'in


"Ai baki isaba, kumburi ga doki sakkiya ga jaki, Allah bazan yardaba sai na rama"...


 








 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 




👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____43💎



    Bayan umman borno dake zaune tana gyarawa Ummi yakuwa Billy taje tab'uya saiga Batool tashigo tana faman haki, dube dube tafarayi ta inda zata hangota amma bata ganetaba, kallonta umman borno tayi had'e da cewa "'yan matana daga ina haka kike faman haki, Allah sa dai bagudune kikayi ba?"


"Umma kibarni da Billy ita tasakani wannan gudun shine kuma tazo tab'uya"


"Au dama keta jawo shine tazo tab'uya abayana kuna 'yar gudedeniy?, Iko sai Allah" fitowa tayi daga bayan nata tace


"Plss sorry aunty Batoolu.." Kafin tarufe baki batool tashiga bubuga k'afa tana fad'in


"Umma kinji ta ko?, nafad'a mata banason wannan sunan amma bazata dena ba, wlh Allah zunubinki yazama biyu, gana dukan da kika yimun kuma gana wannan sunan da bana so" ya isa haka Ummi tafad'a lokacin data fito daga kitchen hannunta d'auke da warmer d'in da ta kwashe tuwon semolinan data tuk'a


"Allah ya shiryeku wlh yarabaku da wahala, yanzu Bilkisu tsabar tsokana auntyn taki kike duka, ga shidai alamu sunnuna kungirma amma ko kad'an babu jin magana atare daku, nasha fad'a maku bakyau gudu ga 'ya mace idan ba bak'ar doleba amma bazaku dena ba, ai sai kuyi tayi ga wanda zaiyi maganinku nan ya iso"


"Ummi duk laifin aunty Batool ne, dariya fa tayimun"


"Au ashe dariya babu dad'i kika azama yayanki ita d'azu" Ummi tafad'a tana k'ok'arin karb'ar yakuwar da umman borno tagama yankawa sannan ta shige kitchen tana cigaba da yimasu fad'a. Kallonsu Umma tayi d'aya bayan d'aya sannan tacewa Billy "to mai gadon zinari kije kibata hak'uri sai kuje kuyi sallah, kinji ko? don gaskiya kece mai laifi kuma kudena irin wud'annan wasannin bakyau da haka shed'an kesamun hanyar shiga tsakaninku sai ya ribaceku" rik'e kunnuwa Billy tayi bayan tadawo wajen da Batool take tsaye had'e da cewa "Am sorry my twiny, never repeat it again" d'aga hannu tayi kamar zata doketa ita kuma ta runtse idanuwa saboda yanda take da matuk'ar tsoron duka sai tayi dariya had'e da lak'amo kafad'ar ta suka nufi part d'in mom tana fad'in "matsoraciya kawai, ga tsoro ga ban tsoro!"


Yaya Mahmud kuwa saida yaji ankira sallar magrib sannan ya katse wayar da sukeyi da faraaha yana jinsa cikin wani irin shauk'i da bazai iya kwatantasa ba, kissing d'in wayarsa yayi tare da yin tsalle yana fad'in "yes nasamota" wanda yayi daidai da shigowar Mahmud pilot, cike da mamaki yake kallonsa tare da d'an turo idanuwansa sannan ya mere baki ya wucewarsa toilet yayo arwala, yana fitowa shima ya shiga yayo tasa suka nufi masallaci, dady kuwa yana shiga part d'insa ya samu d'aya daga cikin kujerun dake nan falon k'asa yazauna, jingina jikinsa yayi ajikin kujerar ya lumshe idanuwansa yana tunanin wai yaushene hajia Hussaina zata canza wud'annan mugwayen halayenta, menene matsalarta da rabba'atul bait d'insa da take neman kullum tahad'asu fad'a, tabbas idan za'aci gaba da tafiya haka baya tunanin zai iya jurewa k'arasa rayuwarsa da ita matuk'ar bata canza ba, haka yaci gaba da tunani kala kala azuciyar sa, idan ya sak'a wannan ya kwance wancan babu abunda yake buri arayuwarsa irin yasamu mafita akan wannan matsalar dake cimasa tuwo a k'warya, har aka kira sallar magrib yana wurin zaune batare da yasamu tudun dafawa ba akan wannan matsalar tasa. 


A b'angaren Basmah kuwa kai tsaye d'akinsu tanufa lokacin da tabar wajen cike da farinciki, toilet tashiga tayo arwala ta gabatar da sallah tare da addu'ar Allah ya sanya yayanta yazamo miji agareta kuma  farincikinta uban 'ya'yanta, tana kammala wa tawuce kitchen, mom d'inta ta tarar aciki tana k'ok'arin sauke couscous d'in data dafa, gaisheta tayi had'e da cewa "mom ya jikin sannu da aiki" 


"Yawwa Basmaty, jiki nawarke tunda gani kitchen ina k'ok'arin had'a maku abunda zakuci kuda dadynku"


"Allah to yak'ara sauk'i momyn mu, yanzu mezan rik'a maki muk'arasa" dariya mom tayi kafin tace


"Kinji ki da abun dariya, ke mekike iya in banda latsar waya, kawai jeki abunki zan k'arasa" wani irin tuk'uk'in bak'in cikine yarufe Basmah had'e da takaicin wai yanzu momyn tace da kanta kegoranta mata haka, kenan badon Allah ya taimaketa da zaman da sukayo wajen Ummi tafara nuna mata wasu abubuwan ba shikenan haka mom zata k'yaleta bata iya girkiba har tayi aure taja mata matsaloli gidan mijinta, gashi tun ba'aje ko inaba ita da kanta keyimata gori da bata iya komai ba sai latsar waya, sai alokacinma tatuna da wayarta bata hannunta ranar tabarota a d'akin da sukaje ita dasu suby da babs, 'yan guntayen hawayen da suka zubomata tasa hannu tagoge sannan ta kalli mom dake k'ok'arin nik'a tattasai a blender tace,


"Mom zan fara koyar girki daga yau, insha Allah bazaki koma shigowa kitchen kekad'ai ba, atare zamu dinga yi har saina iya nima"


"Kai! inaaaa haba Basmah ai bazan yarda kilalatamun abinci ba kasa dadynku yakasa ci, kedai kawai kije abunki, inkyayi auren kya koya acan" cike da mamaki Basmah ke kallon mom, wannan wace iriyar maganace haka takeyi, mahaifiyarta da kanta keneman durk'ufe rayuwarta taya zaka koyi girki agidan miji bacin kamata yayi ace kakoya tundaga gida, shiru tayi bata sake cemata komai ba tanemi gefen fridge d'in dake kitchen d'in tayi tsaye tana kallon yanda take had'a miyar k'wai with kidney har ta kammala, tayata gyara wajen tayi duk da sai faman gwatsileta takeyi tana fad'in taje tazauna abunta ita bata fiye son  idan tana aiki adinga takurata ba.


Kimanin kwana uku kenan yau kullum dr Ahmad cikin tunanin Batool d'insa yake kuma aduk lokacin da yatuna da ita sai yayi dariya sosai had'e da cewa Yaa Allahu kabani fatima! Yauma dai kamar kullum zaune yake yana duba wata marar lafiya sai idanuwansa suka kai ga d'an gadon da ake duba patient dake cikin office d'in sai yatuna da ihun da Batool tadingayi tana neman taimako, baisan lokacin da yafara kwasar dariya ba harda rik'e ciki, patients d'insa naganin haka ta tashi sad'ab sad'ab tabar office d'in, so yakeyi ya tsaisheda ita amma yakasa magana sai faman d'aga mata hannu yake aikuwa tafice abunta rik'e da hannunta daya sundule mata sosai, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru had'e da k'urawa wajen idanuwa yace


"Fateema kidena wahalda zuciyata haka, ina matuk'ar azabtuwa da soyayyarki, ina zanganki ta ina zanfara fuskantarki da d'imbin k'aunarki dake cikin zuciyata, gaba d'aya na zauce akanki, na susuce akan sonki sosai fateemah! Ya Allah nunamun tahanyar da zansamu fateemah" kamar daga sama yaji an amsa masa da amin, d'ago kansa yayi yana kallon wacce ke tsaye gabansa tad'ora hannuwa ak'irji itama tana kallonsa fuskarta cike da murmushi da alama taji duk abunda yafad'a, d'an sosa k'eyar kansa yayi alamun yaji kunya, ita kuma tajawo kujera ta zauna sannan tace


"Dr. Ahmad kenan! Kace yau ruwa sunk'arewa d'an kada, irin wud'annan sabbatu da kake zubawa ai sai mufara tunanin kaikai kaga likitan sychartric, tukunama wai wannan fatimar wacece ita, wace mai sa'arce data sace zuciyarka arana d'aya?" Shafa kansa yayi kafin ya kalleta ya nuna gadon dake facing d'insa tajuyo ta kalli gadon itama, ahankali yace "a wancan gadon ne nayi arba da ita, kyawonta, tsarinta, muryarta duka a cikin wannan ranar suka daki zuciyata, a wannan ranar da bazan manta da dafin data sakarmun ba, kuma acikin wannan ranar ne nakamu da soyayyarta wacce kece silar shigata wannan yanayin da kuma babu wanda zai iya taimakona idan bakeba sister faraaha!"


"Tofah! Dr kace abun naka azhimun ne, kafito Filo kayimun bayanin da zan iya fahimta ko Allah yasa nazamo silar magance wannan yanayin da kake ciki na neman taimako" dariya yayi had'e da juya biron dake hannunsa sannan ya ajiye ya sark'e yatsun hannuwansa wuri d'aya yana kallonta, anatse yafara fad'amata fatimar da yake nufi da kuma ranar da sukazo da ita da abunda yafaru tsakanin shi da ita har zuwa yanayin daya shiga akanta cikin 'yan  kwanakinnan, ya k'are da fad'ar "natabbata kingane ko wace fatima nake nufi don nasan alak'ar da kike da ita dasu yasa kikazo kika nemi in taimaka maki nadubata ko bahaka ba"


Wata irin ajiyar zuciya faraaha tayi kafin tace....







*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_A wasu lokutan samun nagartaccin abokanan tarayya acikin rayuwa kansa su shallake gurbin akirasu da abokanai ko kuma k'awaye saboda kirki, mutunci da karamcin da suke dashi saidai akirasu da 'YAN UWA, a 'yan uwanma irin najini da ake very close dasu, gaisuwa tare da fatan alkhairi agareki *FATEEMA SHI'ITU BUNGU'DU* (Maman arfat) ina so kisani ke 'yar utace dake da gurbin da baya kankaruwa ko musanyawa acikin zuciyata, fatana Allah yakare mani rayuwarki data ahalinki kuma yabaki mafi ingantacciyar rayuwa agidan aurenki tare da mafi girman sakamako agobe k'iyama wato aljannah fiddusi, ur *BIL-SAN* luvs you more than how word can say it_💋❤



💎Page_____44💎



    Dr.kenan yanzu akan wannan 'yar k'aramar matsala kazauna kana sabbatu a office? Kadena nauyin baki acikin burin zuciyarka kadena b'oye damuwarka gameda abunda kakeso, kuma kada kayi jinkirin bayyana muradinka ga wanda kake fata yazama abokin rayuwarka domin hakan zai iya cefaka amatsalar da zakasha wahala arayuwa idan yagudu yabar ka ko kuma yayi nisa dakai matuk'ar ba Allah yatausaya maka yasake maido maka da abunnan izuwa gareka akaro na biyu, tabbas nafahimci fatimar da kake cikin magagin sonta domin 'yah ce ga alhaji bashar mai furniture's wanda Dr.Jamil shine family doctor d'insu, kuma shine silar shigar wata alak'a tsakanina dasu, kuma ta dalilin ganinsa ranar yasa kahad'u da ita, yayanta abokinane sosai wanda da sannu kuma zai zamo abokin rayuwata nahar abada idan Allah yaso, saboda haka ka kwantar da hankalinka zaka samu fatimarka da yardar Allah saidai kuma a gaskiya kayi sonkai da yawa don yarinyace sosai, she's just 15years" tak'arasa maganar had'e da mik'ewa tsaye zatabar office d'in, da sauri ya tsaisheta cikin rawar murya yace


"Haba sister faraaha, ina kuma zakije, kizauna muk'arasa magana mana, wannan ai tamkar kin k'arawa fetur ruwane idan kika tafi kika barni  with out finding the solution" turo idanuwa tayi awaje hannuwanta na cikin aljihun rigarta ta irinta nurses da suke sawa tace "aikifa nake dashi dr., nakawo wata patient ne anan EPDU sai nace bari nal'ek'o office d'inka mu gaisa" agogon hannun dake d'aure a tsintsiyar hannunta ta kalla tace "it's more dn 20m fa ina cikin office d'in nan, gaskiya am going ka kula da patient d'inka inyaso next time zamuyi magana" tun kafin tarufe baki taga yafara har had'a inashi inashi dake saman table d'in dake gabansa yace "Shikenan muje kifara dubani ai nima patient d'inne in yaso daga baya nadawo nadubasu, haba sister faraaha ai kamata yayi kabani taimakon gaggawa da zai ceto rayuwata, bawai kawai kizo kidubani kiwuce ba, haka aka cemaki ana kula da marar lafiya" cike da mamaki faraaha tace "kamarya dr. Bakada lpy?" 


"Kin manta mekikace lokacin da kika shigo, zaku kaini naga sychatric doctor, to ai wannan yanayin da yasa kika fad'i haka shine rashin lpyr tawa, plsss sister faraaha yakamata ko akan hanya kid'orani kafin kiwuce, idan kuwa ba haka ba nadinga bibiyarki kenan duk inda kikayi har sai kinsamu lokacin da kike tunanin zaki iya taimakona, ina matuk'ar jin pain anan d'ina kuma duka dalilin fateemah ne!" ya nuna saiti zuciyarsa fuskarsa kamar zaiyi kuka, sosai yabata tausayi ta kalli yanda yake da kyau ga kwarjini da yanda 'yan matan asibitin ke ribibinsa yana wani feeling tare da shan k'amshi akoda yaushe don ko a ward d'insu kusan mace biyu ke sonsa amma yak'i ya basu fuska balle susa ran samun kulawa daga garesa, tabbas shi so babu ruwansa dako kai waye, yau gashi dr. Ahmad da kansa yake begging ataimaka masa akan soyayyar wata mace kuma 'yar k'ank'anuwar yarinya, tsayuwarta tagyara sannan tace "yanzu ya kake so ayi dr?" 


"Ki had'ani da ita" 


"Idan nayi maka haka shikenan?" 


"Eh..in sha Allah" wayarta tajawo takira lambar danaga tarubutawa *All I have* akai sau biyu tayi ringing ana ukkun ya d'aga.


"Hello golden heart" Mahmud da yafad'a da fitowarsa wanka kenan yana tsane jikinsa yaji k'arar wayar, murmushi tayi tamkar tana agabansa tace


"Barka da hutawa ranka ya dad'e, injin dai katashi daga baccin haka"


"Eh natashi amma dak'yar saboda yanda hatta acikin mafarkina kika hana zuciyata sukuni ina neman rasa raina akan sonki, d'aukin da kika kawomun alokacin tare da dad'ad'an kalamanki su suka hanani wucewa har nasamu nafarka daga baccin da nakeyi"


"Hmmm kace nakuru yallab'ai dana zama k'aramar bazawara aduniyar mafarkai" dariya yaya Mahmud yayi kafin yace


"Ya ake ciki my Golden heart, yanzu nake mararin kiranki idan nagama shiryawa sai gashi naga kiranki ya shigo"


"Eh dama ina son yin waya da Batool ne idan kuna kusa"


"Lallai ma kice saboda ita nasamu kira yau daga wajenki, tabbas yazama dole inyi mata kyauta tamusamman ayau, bamu tare amma bari nakai mata wayar"


"Noo..kahuta abunka anjima zankira sai kabani ita duk da dai urgent nake son magana da ita." Dagashi sai dogon wando da farar singlet dake jikinsa yabar d'akin yana fad'in,


"Karki damu gashima nafito zan kaimata" d'an hararar dr Ahmad daya zuba mata idanuwa yana kallo cike da mamakin yanda ta iya soyayya haka tayi kafin ta shagwab'e murya k'asa k'as tace "sorry All have nabaka wahala ko? Nima dai kamawa tayi but i will pay for it anjima kaji ko?" Murmushi yayi daidai lokacin da ya isa part d'in mom Batool na kakkab'e kujeru da alama gyaran palourn take yajawo hannunta, "golden heart karkiji komai ga Batool d'in" yafad'a had'e da manna mata wayar akunne sannan yawuce bedroom d'in mom don ya gaisheta.


"Helloo, assalamu alaikum" Batool tafad'a cikin muryarta mai d'an karen dad'i tana yamutsa fuska saboda rashin sanin wa yaya Mahmud ya had'ata dashi suyi waya, faraaha najin muryarta sai tayi saurin mik'a masa wayar bayan tasa hannu tad'an rufe speaker d'in wayar tace "Gud luck dr Ahmad, iya ruwa fidda kai gaka ga fateemah nibari najiraka daga waje" karb'a yayi hannunsa narawa yakara wayar akunne tare da sassauta d'aurin neck tight d'insa, dai dai lokacin Batool tasake cewa


"Hellooo." Dak'yar yasamu yayi kokuwa da lumfashinsa dake neman d'aukewa ya amsa mata da "He.l.l.o fateemah" had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya.


"Na'am ina kwana!" tafad'a cikin mamakin yanda aka kirata da sunan da duk duniya bata tab'a jin ankirata dashi ba, ta amsane kawai don tasan cewa asalin sunanta fateemah ne!, shi kuwa wani irin jirine yafara d'ibarsa jin yanda ta amsa masa amutunce had'e da girmamawa, wata irin sabuwar soyayyarta mai girman gaske yaji tak'ara shiga zuciyarsa cikin sanin murya ya amsa mata da "lpy klw fateemah, hope kintashi lpy" "eh alhmdllh tafad'a atak'aice cike da zak'uwar jin koda wa take waya "kar kisamu damuwa fatima, yanzu zangabatar maki da kaina tare da dalilin da yasa nanemi yin waya dake saboda shine abu mafi muhimmanci daya kamata kifara sani akaina, sunana Ahmad Bashar kuma ni d'an haifaffen wannan jaharce gaba da baya, ina zaune a anguwar G R A tare da mahaifiyata, fateemah tun ranar da Allah yasa nad'ora idanuwana akanki nayi sha'awar nazamo bawa agurinki, tayanda duk wata d'awainiya taki aduniya zanzamo nine wanda zaiyi maki ita, fateemah ina sonki irin soyayyar da bazata barni yiwa kaina uzuri ba aduk lokacin da tunaninki yak'aurace mani, nayi alk'awari zan bauta maki har iya k'arshen rayuwata matuk'ar kika amincemun, kiyarda dani fateemah so nakeyi maki tsakanina da ubangijina kuma zan aureki idan kin amince kuma kinbani damar yin hakan. Don Allah karkicemun A'a fateemah domin hakan zaisa nazamo marar sa'a nafarko acikin sabuwar duniyar dana tsinci kaina" tirk'ashi Batool tafad'a acikin zuciyarta, wannan wane irin mutumne da Allah yayima baiwar iya tsara kalamai, bama wannan ba yanda yake furta asalin sunanta abakinsa shine abunda yafi burgeta dashi, bata sani ba ko zuciyarta zatayi na'am da wannan sabon mutum mai sabon al'amariba amma tabbas taji kalamansa sun burgeta.


Jin shirun yayi yawa yasashi cewa "kiyimun uzuri kuma kiyafeni inhar kalamaina sun bak'anta zuciyarki, zamowarki mace tafarko data b'alle murfin zuciyata tashige batare da saninaba shiya haifar da fitar wud'annan kalaman masu tsauri agareki" 


"Babu damuwa, zanyi tunani inkuma auna gaskiyar kalamanka kafin nan in amshi uzurinka" Batool tafad'a had'e da cigaba da kakkab'e kakkab'en kujerunta"


"Godiya nakeyi mai zarkakakken suna zarah!, natabbata tsarkakakkar zuciyarki zata amshi uzurin bawan dake neman agaji daga wajenta, zanjiraki nan da anjima, gobe, jibi ,sati, wata, shekara kai harma nan da zuwa tsayawar lumfashina, fateemah !i do luv you forever, nabaki lafiya, inayiwa kaina fatar kizamo cikin amincin Allah akoda yaushe"


"OK nagode, sai anjima" kafin yace wani abun har takatse wayar tare da kiran yaya Mahmud tamik'a masa abussa, yana amsa saiga kiran faraaha yasake shigowa, d'agawa yayi fuskarsa d'auke da murmushi "hello matar" murmushi tayi kafin itama tace


"Hello mijin, am sorry pls don Allah ka sake baiwa Batool wayar"


"Angama ranki yadad'e" yamik'awa Batool wayar, karb'a tayi wannan karon zaune tayi bisa hannun kujera kafin tace hello atak'aice, muryar sister faraaha da taji yasa tafad'ad'a murmushinta  tana fad'in "laa...aunty faraaha morning, ya aiki" dariya tayi tace


"Yau kam aiki yasamu tsaiko daga wajen dr. Ahmad d'inki"


"Kamarya aunty?"


"Eh bayanzu kika gama waya da wani ba, ina dai kingane kowaye ko?"


"A'a aunty faraaha amma dai yacemun sunansa Ahmad Bashar, dama kin sanshine?"


"Hmmm sosai Batool shine dr.Ahmad d'in da ranar yadubaki, har kin manta nafad'a maki sunansa" dariya Batool tafashe da ita kafin tace


"Kice Allah aunty!, lalle dr. Nan ya shammaceni, wato ranar yagama zalintata, shine yau zai kirani yace wai yana sona, no wander zai kuwa gane kud'insa"


"Pls Batool keep joke aside, wlh da gaske yakeyi, wace irin shammata zaiyi maki bayan wacce ke kika yimasa na sace zuciyarsa gabaki d'aya, nidai nahango tsantsar soyayyar da yake yimaki a idanuwansa kuma ina shawartarki daki manta da wancan abun daya faru tsakaninku, inada yak'ini akan in sha Allah zaki samu farinciki awajensa don haka, kibawa Allah zab'i akansa kuma kinemi shawara awajen mutanen k'warai kamar yayanki, nan da kwana ukku zan sake kiranki kinji ko" 


"In sha Allah aunty amma wlh Allah ya iya Mugunta" Batool tafad'a tana turo baki kamar tana gabansa.


"Amma ai naga Mugunta ta taimaka maki don ina da tabbacin izuwa yanzu tafiyarki takoma normal" haka dai faraaha tayi ta convincing d'inta akan dr Ahmad kafin nan tace tabawa yaya Mahmud wayar, agaban dr Ahmad tayi masa bayanin abunda kefaruwa da dalilin dayasa tanemi yaba Batool waya, kaf tafad'a masa komai akansa ta yanda zai fahimta batare data b'oye masa ba, murmushi kad'ai yaya Mahmud yayi yace


"Allah yazab'a masu abunda yafi zama alkhairi damu baki d'aya" da haka ya tsinke wayar yana mai tsokanarta da wai tazama mai dalili sunata dariya sannan ta jefa wayarta a aljihu, kallon Dr Ahmad tayi tace


"To dr.shikenan ko? Ina fatar nad'oraka akan hanya, kuma nabaka maganin da inhar kakula dashi da kyau zaka samu lpy, ammafa jarumar taka sai k'orafin kayimata mugunta takeyi, don haka arage cutar patient dr" Dr Ahmad da zuciyarsa kecike da farinciki ya dirko akan taburin da yake zaune yana fad'in


"Sosai kuwa sister faraaha, zankula da maganin har sai yazamo warakar cutata,kuma ina godiya sosai wacce batada adadi, koda fateemah tayi rejecting d'ina kin kincini tukuici domin kin yimun abunda bazan tab'a mantawa dakeba"


"Kar kaji komai dr haka Allah yatsaro zai faru don haka dole nima nayi abunda kebisa tsarin da Allah yayo.ni zan wuce, amma idan o.c ya rufeni dafad'a to Allah kai zance kasani kula maka da wata patient" 


"Ai ba za'ayi haka ba, muje nataka maki" 


"A'a nahutar dakai wannan ai hurumin all I have ne" tana gama fad'ar haka tafice abunta shikuma yaci gaba da aikinsa.


Mom kuwa tun ranar da umman borno tazo take jiran jin sakamakon k'ullin data yiwa Ummi awurin dady amma taji shiru gashi tun daga ranar taga dady yad'an sauya mata, yau tak'uduri niyar zata yimasa magana akan dalilin wannan sauyi daya yimata, bayan yadawo daga wajen aikinsa dama ak'a'idarsa inya dawo yakan shiga part d'in kowaccensu yaduba halin da take ciki ita da yaranta, yana shiga ko gaisawa basuyiba tana faman d'ad'd'aure fuska da hurar hanta tace


"Wlh nagaji da wannan walak'anci da tozarcin da akeyimun acikin gidannan, azalinceni in fad'a maka kuma ka kasa d'aukar kowane mataki akai, kuma tsabar cuta a shirya makircin da zaka dinga d'ad'd'auke mani kai, haba alhaji ai wannan ba adalci bane" tafashe da kuka kamar wadda aka cutawa kamar yanda tace. Murmushin takaici dady yayi kafin yajawo hannunta ya zaunar da ita gefen gadon da yake zaune, rarrashinta yadingayi yana bata hak'uri har saida yaga tayi shiru sannan yak'walawa Basmah kira,


Cikin girmamawa Basmah ta amsa ta taho, abakin k'ofar d'akin tatsaya tayi sallamah, dady yabata izinin shigowa, gaidashi tayi sannan tace


"Gani dady" saida ya kalli idanuwan mom da kamar ba ita bace tagama kuka yanzu sannan ya d'aure fuska sosai yana kallon Basmah.


"Basmah so nake intambayeki shin wai umminku tazo duba momynku dake ranar da bakwada lafiya ko kuwa?, don ni abunne yaban mamaki saboda ranar banga alamun tazoba, sai umminku kefad'amun wai tazo shine nace bari dai inkira 'yatah intambayeta don intabbatar da hakan, shin da gaskene tazo?" D'ago kai Basmah tayi suka had'a ido da dady tace 


"Laaa...eh wlh dady tazo ita da sister da safe lokacin ma ina d'aki ina rarrashin Batool dake kuka, naji sallamarsu, ina zuwa na tarar dasu abakin k'ofa, nace su shigo, shine da ummi taji kukan Batool take tambayata dama nida Batool ne ba lafiya taji kamar kace nida mom, to nan nake sanar da ita mom d'in daice Batool daga bayane itama tajimu, nan naje nakirawo mom suka gaisa har ummi na lallashin Batool data dawo itama nan falo, saidai bata wani jima ba tayi mana Allah yak'ara sauk'i suka tafi ko mom?" Tak'arashe maganar had'e da kallon gefen da mom take zaune tun d'azu tana faman k'yak'yaftawa Basmah idanuwa akan tayi shiru amma bata masan tanayi ba, don bilhakki Basmah tazata fad'a dady zaiyiwa Ummi shiyasa ta tak'ark'are tana koro masa bayani, ikon Allah kenan, idan kazamo mai maida alamurranka ga ubangiji to kana zaunenka Allah zai dinga yimaka fighting da kansa ga duk wanda keda niyar cutarka, kana nan zunenka ana cinno maka wuta sai wani yayita ingije maka ita batare da sanin kaba, da gangan dady yayiwa Basmah wannan tambayar saboda ya nunawa mom kuskurnta idan zata gyara. Dady na murmushi ya kalli mom yace


"Tabbas kinyi gaskiya Momyn yara, saidai yanzu da 'yatah tayimun bayani nafi samun gamsuwa, hak'ik'a kin burgeni da kika kasance mai yiwa 'yar uwarki shedu nak'warai, Allah ya shirya kuma yaci gaba da ganarwa" Basmah ta amsa da amin sannan dady yace zata iya tafiya sannan taje takirawo masa yaya Mahmud da kuma Mahmud pilot. 


Tana fita shima dady yamik'e tsaye had'e da kallon mom yana fad'in 


"shin yanzu zaki iya fad'amun tsakanin ke da ita waye aka cutar kuma waye wanda aka zalinta waye aka shiryawa makirci acikinku, sannan kuma inaso kifad'amun tsakanin ke da ita waya cancanci ayiwa abunda kika lissafo ana yimaki agidannan?" yana gama fad'ar haka yafice abunsa batare da jin wani d'ar azuciyar saba.


Kwance yake akan gado sai faman juye juye yakeyi yana buga tsaki don gaba d'aya wayar da yaya Mahmud keyi da faraaha sake tsananta masa ciwon dake zuciyarsa takeyi, kimanin kwana biyu kenan baisa Billy a idanuwansa ba wanda hakan ke matuk'ar cin zuciyarsa fiye da tunani, ji yake bazai iya rayuwa idan babu billy atare dashi ba kuma shi yanzu yagama yanke shawarar aurenta zaiyi don bazai zauna da damuwa aransaba amma taya hakan zai faru bayan yakasa fuskantarta ido da ido yafad'a mata sirrin dake ransaba, gashi yanzu tunda tafara tsanar alak'ar dake tsakaninsu saboda gwatsileta da yake yawanyi yasa tadena yadda suhad'a hanya da ita, mezai yi yanzu ya gyara wannan kuskure taya za'ayi ya fahimtar da ita tsagwaron k'aunarta dake ransa kuma azuciyarsa tuntana 'yar k'ank'anuwa, rashin samun amsarsa yasa zuciyarsa tafara yimasa zafi yana fitar da wani nishi da k'arfi da k'arfi kamar wanda za'a zarewa rayuwa. Tsananin ciwon da yakeji ne yahaifar masa da fashewa da kuka yana juye juye, afirgice yaya Mahmud ya katsiye wayar da yakeyi yayo kansa yana fad'in


"'Dan uwa, meyake faruwa da kaine?, fad'amun meke damunka d'an uwa" dak'yar Mahmud pilot yabud'e baki yana hawaye yace


"Bazan rayu inbabu keba 'yar uwata, ina matuk'ar sonki, amma duk hanyar da zanbi tafahimceni takasa, kullum gani take kamar tsarguwar tace nakeyi hakan yasa taharamta mani ganinta gaba d'aya, d'an uwa sonta ajinina yake don Allah kataimaka ka fahimtar da ita" wani irin farincikine yarufe yaya Mahmud sanin cewa 'yar uwarsa Basmah kad'aice kenuna tana sonsa kuma yatabbatar da ita yake nufi amma don yaji da bakinsa yafad'a ya tallofo kansa had'e da d'orawa ak'irjinsa yana goge masa hawaye.


"'Dan uwa ban fahimceka ba wai wace yarinyar ce kake nufin ta jefaka acikin wannan hali fad'amun ko wacece nayima alk'awari zansa tasoka koda hakan zaisa narasa farinciki atare dani"


"Broth 'yar uwa tace ba..." Kasa iyarwa yayi had'e da rik'e hannun yaya Mahmud sosai saboda wani irin tari daya taso masa ba k'ak'k'aftawa.....






 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Ban manta dakuba qawayen k'warai, abokanan kirki, akowane lumfashi da zanyi kuna nan mak'ale acikin zuciyata❤ gaisuwa mai tarin yawa da fatar alkhairi agareku, *SA'ADATU SHEHU BUNGUDU, SARATU ADAMU, ZAINAB 'DAN MALAM, MOM HAFSAT BARUMI, FARIDA MOH'D GUSAU, MARYAM BELLO, SADIYA M LADAN, RUK'AYYA BELLO KARIKKAI, ASMA'U UMAR GUSAU, ZARA'U MOH'D MARADUN* ina matuk'ar alfaharin zamowarku atare dani Allah yaraya maku zuria kuma ya sanya masu albarka, ina so kusani BIL-SAN KAURA takuce kuma tana sonku irin sosai d'innan💋🤝🏻_


💎Page_____45💎


   Dady nafitowa yaci karo da Basmah zata shiga kitchen yace


"Bacewa nayi kije kikirawomun yayun kiba, mekuma ya tsaishekine? Maza kije kice susameni a falon umminku ina jiransu.cikin hanzari tanufi d'akin yaya Mahmud, wanda nan take sai taji gabanta nafad'uwa, bakin k'ofa tatsaya tare da rik'e handle d'in k'ofar da niyar yin sallama sai kuma tafasa jin kalaman dake tasowa daga d'akin, har ga Allah taji dad'i lokacin dataji Mahmud pilot ya ambaci cewa 'yar uwarshi ce yakeso wanda gaba d'aya tagama yarjewa zuciyarta cewa hak'ar tace ta cimma ruwa, jiki narawa tamatsu taji ya ambaci sunanta amma kash sai tarin da yakeyi ya hanasa iyarwa, hannayenta ta had'e waje d'aya kamar mai addua tana kallon sama yayinda zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, sai da tarin ya tsagaita masa sannan yabud'e baki ahankali yace


"'Yar uwa tace Balkisu, ina matuk'ar sonta fiye da komai d'an uwa, rasata tamkar rasa rayuwata ne!" Tsaye chak Basmah tayi jin abunda yaya Mahmud pilot yake fad'a wai 'yar uwarta Bilkisu yakeso! Wani irin kukane da bata san lokacin daya zomataba ta kucce dashi, hannu tasa tayi saurin to she bakinta tana bin jikin bango da take jingine dashi har takai k'asa, ta kusan minti biyar awurin duk'e tana kuka kafin da sauri ta tashi da guda tabar wajen tanufi cikin guarding tana kuka mai tsuma zuciya.


Yaya Mahmud kuwa gaban sane yayi wata irin muguwar fad'uwa wanda har sai da yasa kansa sarawa, innalillahi wa innalillahi wa'inna ilaihirrajiun yake fad'a acikin zuciyarsa, saida yayi dagaske sannan wani irin kuzari yazo masa tare da k'arfin halin cewa 


"Enough d'an uwana, akan wannan zaka tashi hankalinka har kake nema kasa kanka cikin wani hali? Hala ka manta cewa kai d'an uwane, kuma dady namatuk'ar sonka fiye da tunani babu abunda zaka nema karasa indai a gidannan ne, pls don Allah kasa aranka tamkar Billy tazama taka, kawai kafara ba Allah zab'i sannan kanemi soyayyarta natabbata dady zai aura maka ita kaji ko?" Haka yadinga yimasa kalaman da zasu kwantar masa da hankali har saida yaga yazama normal. 


Basmah kuwa kuka tayi sosai har saida kanta yasoma ciwo sannan taje ta wanko fuskarta ga fanfo amma duk da haka hawayen basu daina zubowa a idanuwan taba, komawa guarding d'in tayi tazauna tana tunano abubuwan da suka faru ranar da tajata suka tafi tabasa hak'uri wanda tun alokacin yakamata tagane cewa yana son Billy amma saboda yanda so ya rufe mata ido sai tadinga yaudarar kanta dacewa 'yan uwane shiyasa hakan kefaruwa. Rufe rabin fuskarta tayi da tafin hannuwanta idanuwanta na tsiyayar da hawaye tace "wa ufawwidu amri ilallah, ina matuk'ar sonka yaya Mahmud soyayyar da banida tabbaci akan zata fita azuciyata amma yazama dole zan hak'ura dakai koda hakan na nufin zan rasa rayuwata, bazan koma nuna maka soyayyar danake yimaka ba, zan jure zafin rashinka, zan sadaukar da farincikina agareku domin kud'in 'YAN UWANA NE!, shiko yaya Mahmud fitowa yayi shima yanajin wani bak'on yanayi atare dashi, yanaji aransa cewa yafi kowa shiga tsaka mai wuya saboda yanda yasan irin son da Basmah keyiwa Mahmud ba kad'an bane kuma zata iya shiga damuwa idan tasan da wannan maganar, kuma bayaso yarasata, sannan  kuma gashi yanzu mahmud yanuna masa irin tsantsar son da yake yiwa Bilkisu wanda yatabbatar masa da rasata zai iyasa shima yarasa tasa rayuwar, kuma yaga hakan atattare dashi, goge hawayen da suka zubo masa a idanuwa yayi ahankali ya furta "ya Allah kawarware wannan matsala cikin sauk'i domin dukkaninsu 'YAN UWANA NE banaso narasa ko guda daga cikinsu" wayar sace tayi k'ara ya d'auko yana duba sunan wanda ke kiransa, ganin dadyne yasa yad'aga da sauri kafin ta tsinke had'e da daidaita muryarsa yace


"Hello dady barka da rana"


"Yawwa my son, tun d'azu naturo Basmah takira maniku kuma naga lokacin data wuce amma har yanzu banganku ba, lpy kuwa?" gaban Mahmud ne yafad'i cike da tsoron Allah yasa bata k'araso ba taji abunda ke faruwa cikin rawar murya yacewa dady 


"Dady Bas.ma.h kuma!?"


"Eh ko batazo bane?" d'ago kan da yaya Mahmud zaiyi yagoge zufan daya keto masa sai ya hango Basmah zaune cikin guarding ta tura kanta cikin cinyo yinta wanda hakan ya tabbatar masa da kuka takeyi. da sauri ya amsawa dady da 


"Aa tazo dady gamunan zuwa" katse wayar yayi aransa yana fad'in shikenan tafaru tak'are don yanayin daya hangota aciki ya tabbatar masa da cewa taji komai, ahankali ya dinga takowa zuwa inda take zaune, gefenta yazauna tare da sa hannuwansa ya d'agota, 


"Basmah lpy kuwa?"


Juyowa tayi tana k'ok'arin maida hawayen dake son zubo mata had'e da yin murmushi tace "lpy klw yaya Mahmud, dadyne ya aikoni inkiraku sai naji kaina yad'an sara mun shine nazauna anan har yakwanta sai intafi, amma tunda gaka nagani kafad'awa yaya Mahmud dady na neman ku yace kusameshi a part d'in Ummi, mik'ewa tayi tare da goge hawayen da suka zubo mata zata bar wajen"


hannunta ya rik'o "Basmah fad'amun gaskiya, shin ko wani abunne yafaru" girgiza masa kai tayi batare data juyoba hawayen naci gaba da zubo mata, "idan gaskiyane to kijuyo ki kalleni mana, fad'amun su hawayen da kikeyi na meye idan har babu abunda yafaru?" Juyowa tayi had'e da fad'owa kan jikinsa tana kuka "yaya am too late, ashe zuciyar yaya Mahmud tadad'e da zamowa mallakin k'anwata bansani, gashi nayi nisa sosai a soyayyar sa, yaya ya zanyi nafiddashi acikin tawa zuciyar?" Sosai 'yar uwarsa tabasa tausayi amma shikansa baisan amsar da zaibata ba, idan yace tacire Mahmud aranta baiyi mata adalci ba, idan kuma yace tabayyanar da soyayyarsa ga iyayensu shima baiyi masa adalciba tunda yafad'a masa wacce yake so, haka yabarta ajikinsa tayi kukanta mai isarta sannan ya d'agota, kallonsa tayi da rinannin idanuwanta da sukayi jawur duk shacin jini  ya kwanta aciki saboda kasancewarsu manya, murmushi ya sakar mata had'e da sauke ajiyar zuciya sannan yace


"Basmah kiyi hak'uri, bansan yanda zamuyi da wannan al-amari ba, amma inaso kisa azuciyarki Billy'yar uwar kice kuma duk wani ciganta nakine, kibarwa Allah dukkanin al-amurranki natabbata bazai tab'a bari ki wofantaba, be strong Basmah nasan zaki iya kinji ko?" Jijjiga masa kai tayi tana murmushi alokaci guda kuma hawaye nazubo mata "I will yaya, but fore sure ina matuk'ar sonsa, kuma bazan iya denawa ba amma zan tirsasa zuciyata tarage k'aunarsa don natabbata narasashi"


"Karkice haka Basmah _laa taqnad'u min rahmatillah_ Allah da kansa yace kada mud'eba k'auna daga rahamarsa, kuma yak'ara da cewa _faswabrun jamil_ wato hak'uri abune mai kyau, don haka kidaiyi hak'uri kuma kiyiwa addua kinji ko?"


"Zanyi in sha Allah yaya Mahmud, kaima katayani addua"


Da haka yata janta da labarai masu dad'i da kuma faranta zuciya har saida yaga tad'an saki abun sannan ya mik'e yana fad'in


"Yau kinsa nayiwa dady laifi, dole inazuwa infara da bashi hak'uri na rashin amsa kiransa da banyi ba cikin gaggawa" murmushi dai tayi masa sannan tawuce shi kuma yakoma d'aki ya sanar da Mahmud pilot kiran da dady keyi masa, jikinsa ba k'wari yarik'asa suka nufi part d'in Ummi, suna shiga dady zai fitowa Ummi ta rakosa rik'e da jakarsa da yadawo office don dama yau ita keda girki, gaishesu sukayi cikin girmamawa bayan sun amsa Ummi ta mik'awa yaya Mahmud jakar tana kallon dady daya zuba mata idanuwa ganin abunda take shirinyi tana dariya tace


"To abu Bilal ga 'ya'yanan sun hutar dani da wannan rakiyar, bari nakoma wajen k'anwata" murmushi sukayi had'e da karb'ar jakar suka bar wajen. Speechless dady yazama yana kallon yanda take dariya, ya nunata da makullin motar dake hannunsa shima yana dariyar yace


"Ke koh!" "Afuwan dadyn yara Allah kad'aici ba dad'i shikenan ni dad'i miji saina barta itakad'ai azaune"


"Shine kuma ni za'a sakani zaman kad'aici bacin ansan bayada dad'i, shikenan kije amma ina tabbatar maki da duk bayan sakon d'aya sai nazo acikin tunaninki tayanda firar ma bazata yimaki dad'i ba sai kinzo inda nake" 


"Hmmm to shikenan, ai natabbata nikuma 'ya'yana bazasu bari hakan tafaruba tunda suna tare dakai bazasu bari kad'aici ya ziyarto kaba"


"Haka kike tunani oum Bilqees amma ko mutanen duniya zasu zo suzauna atare dani matuk'ar bakya kusa dani to bazasuyi tasirin da zaisa kad'aici ya kasa ziyar toniba, kije abunki amma wannan qanwar taki ta matuk'ar takurani da yawa"


"Nagode abu Mahmud, shiyasa nake sonka da yawa" tafad'a tare da juyawa tabar wajen sannan shima yawuce abunsa zuciyarsa nak'ara jin soyayyar matarsa kuma uwar gidansa.


Zaunawa dady yayi akan kujera, sukuma suka zauna k'asa suka k'ara gaishesa, yaya Mahmud yabashi hak'uri akan rashin zuwansu da wuri, "bakomai" dady ya amsa masu dashi atak'aice tare da sanya masu albarka sannan ya kalli Mahmud pilot yace


"Kaine babba kuma akanka zanfara, yakamata ace izuwa yanzu ka fiddo da matar da zaka aura don iya rufin asiri Allah yayi maka shi, ka kammala karatu kanada gidansa nakanka gashi kuma kanada aikinyi shin to mekake jira da bazakayi aure ba? Ko so kakeyi sai kagama tsofewa sannan zakayi auren? don haka ina shawartarka daka taimakawa kanka kazamo cikakken namiji bawai tazuru ba kaji ko?" Eh Mahmud ya amsa masa dashi yayinda zuciyarsa ke ingizasa daya fad'awa dady cewa Billy yake so wata kuma zuciyar na hanasa akan yabari har sai yasamu soyayyarta sannan yafad'a masa. Juyowa dady yayi ga yaya Mahmud yace


"Kai kuma magana biyu nakeda ita dakai tafarko shawarace kaima tabiyu kuma umurnine!" Gaban yaya Mahmud ne yayi wani irin fad'uwa na rashin sanin wane umurnine dady keshirin bashi, muryar dady ce yaji yaci gaba da cewa "a matsayina na mahaifinka ina baka shawara daka ajiye kula da shagona na furniture's da kakeyi ka koma makaranta ka had'o master's d'inka ta fannin business  in yaso kana dawowa saika fara neman aiki daga nan sai batun aure sannan kuma sai inbud'a maka naka shagon da zaka dinga kula dashi ranakun dabaka aiki, sauran ranaku kuma sai azuba maka yaran da zasu kula maka dashi, sai abu nabiyu ina so kaje gidan aminina alhaji Usman akwai yarinyarsa da mukayi maganar had'aku aure Fareeda idan tayi maka shikenan sai asa rana inka gamo karatu sai ayi auren, don yanzu SS1 take a makarantar secondary, ga d'an uwanka nan anjima sai yaraka ka" Wani irin zufane ya ketowa Mahmud ya k'walalo idanuwa awaje yana kallon dady yace


"Dady wa kace?  faraaha ko Fareeda?"...





 








 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____46💎



   Yaushe nafara wasa dakai my son Fareeda nacema ko har yanzu bakaji bane, durk'usawa yaya Mahmud yayi agabansa yana fad'in,


"Tuba nake dadynah amma inaso kabani dama inyi magana idan ka amince" "go ahead" dady yafad'a yana mai gyara zamansa akan kujera.


"Dady kai mahaifinane kuma nasan bazaka tab'a zab'amun abunda zai cutar dani ba kaine ka tarbiyantar dani yanda zanyi kyakkyawar mu'amala acikin mutane kuma nake koyi da kai wajen d'abi'u masu kyau tare da cika alk'awari, dady akwai yarinyar da nakeso kuma mukayi alk'awarin aure da ita, idan kace inbarta inbi zanb'inka to zan barta koda hakan nanufin zansaukane bisa tarbiyar daka bani da koyin da nakeyi dakai wajen cika alkawari don tabbatar dana farantamaka" shiru dady yayi yana kallonsa da nazarin kalamansa daki daki kafin yace


"Shikenan my son nafahimceka, kuma na amince kaci gaba da neman yarinyar amma inaso kasani kai mijin mace hud'u  ne zan samu alhaji Usman nafad'a masa abunda kafad'amun idan har jin hakan baisa ya jaye muradinsa akankaba to ina tabbatar maka da cewa nima bazan watsa masa k'asa a idanuwa ba saidai kahad'asu su biyun ka aura ka fahimta." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke dake nuna kalaman sunyi masa nauyi azuciya ya koma zaune daga duk'en da yake had'e da cewa


"Amma dady ni bana sha'awar ajiye mata biyu, bazan iya zama da suba ko kad'an!"


"Haka zakayi hak'uri sai dai kayi addu'ar Allah yasa alhaji Usman yajaye qudurinsa wannan kad'ai zai hanaka auren mata biyu but idan ba haka ba dole ka hak'ura kahad'a da ita Fareedar!"


Mahmud pilot da kansa ke duk'e k'asa yana tunanin ta hanyar da zai soma maganin tasa matsalar kafin dady yace shi mata hud'u zai aura ya d'ago kansa yana kallon fuskar yaya Mahmud data koma kalar tausayi baisan lokacin da dariya ta kucce masa ba, kallonsa dady yayi yace "zanzo takan kane!, idan har baka fitar da matar da zaka auraba kaima zannemo maka auren yayar Fareeda yama sunan da suke kiranta dashi? yawwa Meamah! Itace daidai kai saboda this year zatayi graduating SSCE d'inta" Dariyar da yaya Mahmud baisan da zuwan taba shima ta kuccemasa yana nuna Mahmud pilot daya kumbure fuska da hannu, dariya shima dady yayi yana kallonsa, murya can k'asa k'asa yake fad'in "ni Bawata meamah wlh sai Billy" ko kad'an dady baiji abunda ya fad'aba saboda bakin sane kad'ai yaga yana motsi, shikuwa yaya Mahmud da har yau baidena dariyar ba kallonsa yayi yace


"Ah abu yayi d'an uwa Allah yasanya alkhairi" had'e da mik'amasa hannu, buge hannun yayi ya mik'ewarsa zai fita dady dake dariyarsu yace "koma kazauna ai ban sallameku ba ko?" makullan mota guda biyu ya mik'amasa, "Gashi kazab'i d'aya kaba d'an uwanka d'aya, yau aka kawomun tallarsu guda biyu iri d'aya k'irar BMW amma different colours ne, golden da kuma ash sai kuje kamfanin al-ikhlas kuce agwada maku manager wurin zai nuna maku motocin saiku d'auka" tunda dady yafara magana suka saki baki suna jujjuya makullan motar cike da mamakin irin wannan kyauta daya yimasu tabazata, godiya suka yimasa sosai suna zuba masa addu'o'in neman tsarin Allah daga abun k'i tare da fatar samun tsawon rayuwarsa cikin amincin Allah, murmushi dady yayi sannan yace


"Karku damu ubangiji Allah yayi maku albarka kuma kukula sosai kutsare mutuncinku da namu aduk inda kuke"


"In sha Allah dady" da haka yasallamesu fuskokinsu d'auke da tsantsar farinciki shi kuma ya haura sama domin ya huta.


Suna fitowa yaya Mahmud ya kalli Mahmud pilot cike da tsokana yace


"Ahh lallai angon meamah tazo a Sa'a, sabuwar amarya sabuwar mota, daga yin zancenta saimu samu kyautar dank'areriyar mota haka, gaskiya inatayaka murna d'an uwa to inata daka aureta, ahhhh..mukam wlh mun amince dady yaje yayi magana da gani zata shigo da farar k'afa, kai masha Allah congrat" tsabar takaici baisan lokacin daya ja wani dogon naushi zai kai masaba da sauri ya kauce tare da barin wajen yana yimasa dariya.


"Au! ashe kai k'aramin shak'iyine ai da katsaya na zubar dakai k'asa can ka k'arasa wajen wannan nurse d'in taka da kuke damun mutum da d'an banzan surutu"


Dr Ahmad dai yau kam jiyake yafi kowa farinciki saboda yasamu jin muryar masoyiyarsa, tun kafin ya isa gida yakira mamy yasanar da ita yanda sukayi da fatimar sa kuma tayi farinciki sosai tare da fatan Allah yasa ta amince da soyayyarsa, koda yatashi office seda ya tsaya kan hanya ya siyo kaji d'anyu guda biyar tare da kayan miya sannan ya sayi katam d'in lemun roba na coca-cola sanan ya isa gida, cike da fara'a mamy ta tarbesa ana fad'in


"A'ahh d'an gidan mamy yau me ka kawowa mamyn taka ne?" tak'arasa karb'ar kayan dake hannunsa, bud'ewa tayi taga naman kaji aciki ta d'ago kai tana kallonsa bayan fuskarta ta sauya zuwa kalar tausayi tace"haba Ahmad har yaushe zaka dena wahalda kanka haka, kace kai kullum sai ka takura kanka don ka faranta mani, nafad'a maka banida damuwa ga duk abunda zaka kawo mani komai rashin dad'insa, babban burina shine naga ka sauke nauyin hak'k'in mahaifinka dake kanka"


"Mamy ki kwantar da hankalinki, duk abunda nakeyi inayinsa ne bisa tsari, zancika maki burinki nan bada dad'ewa ba, ruhin Abbanah yana gab da samun salama fiye da wacce yake ciki, kiyi hak'uri kuma kici gaba dayimun addu'a domin itace makamin da nake yak'ar duk abunda zai tari gabana, kuma akoda yaushe farincikin ki shinake son gani shiyasa nakeyi maki duk abunda nasan kinaso, ko kinmanta da amanarki da Abbana yabani" goge 'yan hawayen da suka zubo mata agefen idanuwa tayi sannan tace


"To madallah nagode, yaron Abba, ubangiji Allah yayi maka albarka kuma yajik'an mahaifinka"


"Amin mamynah haka nakeso inji kin fad'a" d'aki ya wuce yarage kayan dake jikinsa sannan yadawo tsakar gidan yayi zaune yana kallon yanda take k'ok'arin gyara kayan daya shigo dasu, "mamynah kawo narik'a maki wani aikin"


"A'a kabarshi nagode Allah yayi albarka, ga abincin ka can akan fridge kaje ka d'auka kaci inka gama saika d'an samu waje ka kwanta kahuta, wannan aikin ai namatane" murmushi yayi yana tuni rayuwarsu tabaya.


_WAYE DR. AHMAD BASHAR_


'Dane tilo awurin mahaifinsa Alh bashar mai fulawa, mahaifinsa cikakken d'ankasuwane dake da k'aramin jarin saida fulawa, wanda ananne yasamo lak'anin da ake yimasa, yanada matarsa k'waya d'aya da ake kira mamy amma asalin sunanta Hauwa'u, macece mai tsananin kawaici da hak'uri kuma shima haka halinsa yake, wannan dalilinne yasa zaman nasu yayi dad'i fiye da tunani, tunda suke ba'a tab'ajin muryar d'ayansu da sunan fad'aba, suna matuk'ar son juna da kuma mutunta juna, aurensu da shekara uku Allah yabasu k'aruwar haihuwar d'ah namiji wanda yaci sunan Ahmad kuma ta dalilin haihuwar sane mamy tahad'u da lalura ga mahaifarta da bazata sake iya haihuwa ba, sosai mamy tayi kuka wanda saida ya tashi zamemata damuwa, Abba yadinga bata hak'uri data barwa Allah komai kuma surok'i wannan yaro daya basu yaraya masu shi kuma ya sanya masa albarka, dole mamy tahak'ura tafawwalawa Allah alamarinta sukaci gaba da renon yaronsu cikin kulawa, akoda yaushe ciwon dake damun mamy ga mahaifa yakan tashi akai akai amma bata bari Abba yasan da haka don sai yanuna yafita shiga damuwa, haka mamy tayita fama da ciwon har Ahmad ya girma, abunda mamy bata saniba shine barazana da k'alubalen da Abba ke fuskanta daga wajen 'yan uwansa akan sai yak'ara aure amma shi kuma yakafe ya cije akan alk'awarin daya d'aukarwa kansa cewa bazai tab'a auren wata mace ba aduniya matuk'ar matarsa naraye, wannan dalilin yasa maganganun da sukeyi masa suka haifar masa da damuwa maitsanani data zame masa ciwon zuciya, haka sukaci gaba da rayuwarsu kowa na b'oye wa d'an uwansa ciwo da damuwar dake ransa don gudun tayarwa da junansu hankali, Ahmad yataso cikin gata da kulawar karatu har zuwa lokacin daya kammala karatunsa amatakin degree a inda yayi specializing a b'angaren likitan k'ashi, ranar daya dawo itace rana mafi muni da bazai manta da itaba ranar da tazamo silar fad'uwa katangar da suke jingine da ita wato mutuwar mahaifinsa,


Cike da farinciki yanufo gidansu don tabbatar wa da mahaifinsa samun nasarar da yayi wajen karatu domin shine d'alibi nafarko amakarantar da yafi kowane d'alibi maki ashekarar wanda har saida aka karramashi da lambar yabo, yana isowa unguwarsu ya hango cincirindon taron mutane a k'ofar gidan tsaitsaye, da sauri yak'arasa wajen ya hango wani alhaji tukur tsaye yasa ana firfitowa da kayansu ana jehowa waje, hango  Abbansa yayi durk'ushe agaban alhaji tukur shida mamynsa suna bashi hak'uri amma ina ko kallonsu beyiba balle susa ran zai karb'i hak'urinsu, aguje yak'araso wajen tare da sa hannuwansa ya d'ago mamy da Abbansa idanuwansa na zubar da hawaye yace 


"Haba Abba meyasa zaku k'ask'antar da kanku agaban wanda yake mutum irinku bayan Allah yayi maku daraja, waima meyake faruwane Abba?" Kasa magana yayi saima k'wace hannunsa da yayi yanufi wajen alhaji tukur yana k'ara yimasa magiya akan yayi hak'uri ya rufa masa asiri amma yak'i saurarensa har saida yasa kwad'o yarufe gidan sannan yajuyo cikin fad'a yace


"Alhaji Bashar! Alhaji Bashar! Wlh Allah idan kaga nabaka makullan gidannan ka koma ciki to tabbas ka biyani kud'ad'ena danake biyarka gaba d'aya! Idanko ba haka ba baka ba komawa cikin wannan gida matsiyacin banza matsiyacin wofi" a k'ufule  Ahmad yayo kansa had'e da cin kwalar rigarsa idanuwansa sunyi jawur saboda tsananin b'acin rai ,Abba dake duk'e yana sharb'ar kuka yayi saurin dakatar dashi "sakeshi Ahmad gaskiya yake fad'a bayada laifi" sakinshi yai yana wani irin huci sai kace kububuwa sannan yadawo wajen mahaifinsa shima yana kuka, haka itama mamy kukan takeyi kamar ranta zaifita, yunk'urawa Abba yayi zai tashi had'e da d'ago kansa yana kallon mamy dake faman kuka yana girgiza mata kai alamun tayi shiru kawai sai sukaga yafad'i k'asa jini nafitar masa ahanci, da sauri Ahmad yayo kansa ya d'agosa lokacin yana goge jinin dake zubo masa da hannunsa, kallon mamy data k'araso wajen tana kuka yayi tare da rik'e hannunta sosai, wata irin ajiyar zuciya yayi bayan yasake goge jinin dake zubo masa sannan yakai kallonsa ga Mahmud dake fad'in Abba tashi muje asibiti yana kuka, cikin k'arfin hali yabud'e baki yace


"Kuyi hak'uri, sannan kuyafemun wannan abun fad'i dana bar maku, ni nasan bazan tashiba a wannan karon, mamyn Ahmad akwai abubuwan dana b'oye maki baki sani ba, kimanin shekaru 7 kenan ina fama da ciwon zuciya wanda nayita boyewa gudun kada kusani in sakaku cikin damuwa, sau biyu yana yimun tsanani har inkwanta asibiti jinya na tsawon kwanaki amma sai inb'oye maki akan nayi tafiyane idan kika kira saboda ban dawo gidana, likita ya tabbatarmun da cewa kada inkoma bari hakan tafaru akaro na ukku domin barazana ne ga rayuwata, amma kinga yanda Allah yanufa" wani irin tari yayi da yasa saren jinin fitowa daga cikin bakinsa da hanci yana zuba" Ahmad na kuka ya ciccib'i Abba suka nufi titi amma sai ya dakatar dashi,


"Kabarni Ahmad bazan rayuba, kawai kasaurari abunda zanfad'a maka idan Allah yabani iko, ga amanar mahaifiyarka nan kakula mani da ita sosai, kabata farinciki, kuma kayimata duk abunda takeso idan Allah ya hore maka kada kabari ta tab'a yin kuka dakai domin tamatuk'ar shan wahalar rayuwa a dalilin haihuwar ka, wata biyu da suka wuce mamynka tayi fama da ciwo sosai lokacin kana makaranta wanda yakaita ga kwanciyar asibiti, anan aka buk'aci cewa ciwon dake mahaifarta zai iyasa tarasa rayuwarta matuk'ar ba'ayi mata aikiba aka cire mahaifar, kimanin kudin aikin naira dubu d'ari biyar da hamsin sukace suna buk'ata kafin suyimata aikin gashi ina kallonta rai ahannun Allah, gashi alokacin dubu uku ne kad'ai acikin aljihuna, sanin kankane sana'ar da nakeyi karb'a nakeyi in aza tawa ribar idan nasa yar sai inmayar da kud'in ga maisu don haka banida kud'in da zasu isa ayimata aikin, ganin bazan iya zuba idanuwa inrasata ba yasa naje wurin alhaji tukur rancen kud'i amma fir yace bazai bani ba har sai inzan bashi jinginar gidana dafarko dai banyarda ba amma ganin banida mafita yasa nakoma nafad'a masa na amince, inaji ina gani yasa aka kawo takardar yarjejeniya nasa hannu shima yasa abun takaici dubu d'ari uku kad'ai yabani da k'yar ina kuka narok'esa nasamu yacikaman dubu hamsin yarage saura dubu d'ari biyu har yau, hakan yasa nakoma shago na kwashe sauran buhuhun fulawar mutane dake hannuna kusan buhu arba'in da biyu nasa akasuwa nasayar, na har had'a kud'in suka kama dubu d'ari hud'u da tamanin yazamana saura dubu sittin in had'a kud'in aikin mahaifiyarka, da qyar nasamu likitocin suka amince zasuyi mata aikin bisa sharad'in baza'a bamu sallama ba har sai mun biya sauran kud'in, gudun kar inrasata yasa nasake amincewa nan da nan aka shiga da ita wajen tiyatar bayan and'ibi gorar jinina biyu, duk inda yakamata inje neman taimakon sauran kud'in da zanbiya naje amma bansamuba, hatta 'yan uwana hanamin sukayi wai indai da kudinsu zata rayu to saidai tamutu inyaso dole na auro wata, alokacin naso kiranka infad'a maka amma dana tuna semester k'arshe kake bai kamata abari hankalinka yatashiba alokacin saina hank'ura, nabawa wani mak'wabcina aron shagona akan ya aramani dubu sittin d'in inyaso shi sai yaci gaba da sana'a acikin shagon ni kuma duk lokacin dana biyashi sai yabani abuna. Da haka nabiya kud'in kuma alhamdulillah ga mahaifiyarka nan tasamu lpy, wa'adin daya kamata nabiya alhaji tukur kud'insa yacika har yawuce amma banida zarfin biyansa shiyasa ya aikata hakan kuma yanada gaskiya tunda munyi arubuce, inaso in Allah yakarbi raina katabbatar kabiya kud'ad'en da mutane kebiyata ka karb'o makullan gidannan don shi kad'ai na mallaka aduniya, kuyafemun bisa wannan yanayi da zanbarku aciki, gaba d'ayanku Allah yayi maku albarka"


Yana gama fad'ar haka rai yayi halinsa atake mamy tasome wajen, duk mutanen dake wurin sun matuk'ar tausayawa mamy da Ahmad kasancewar mahaifinshi mutumen kirkine kuma ba'a tab'a jin yayi fad'a da wani ba, nan take limamin anguwar yasa aka kwashe kayansu aka kai gidansa sannan aka d'auki gawar Abba Ahmad nakuka aka suturcesa akayi masa sallah sannan aka kaishi gidan gaskiya, mamy kuwa har aka kauda Abba bata farfad'o ba, nan take mutuwarsa ta karad'e garin ta ko ina gaisuwa ake zuwa saboda ansan shi da mutunci sosai, lokacin da alhaji tukur yaji zancen mutuwar Abba gaba d'aya jikinsa yayi sanyi don harda kuka yayi da dana sanin abunda ya aikata masa har yazama silar rasa rayuwarsa, makullan gidan ya d'auka yakaiwa liman tare da bada hak'uri yace suzama sheda yayafewa Abba kud'in da yake bisa duniya da lahira, murmushin takaici Ahmad yayi batare daya ce komai ba amma yasa aransa matuk'ar Allah yahore masa zai biyasa kud'insa kamar yanda Abba ya umurcesa, tunda tun yana raye bai yafe masa suba to babu buk'atar yanzu ya yafe masa, wannan dalilin yasa yana fara kwasar albashi ya biya wanda ke biyar Abba dubu sittin da kuma kud'in fulawar da Abba yasayar ta wanda ke bashi yana sayar masa yacire ribarsa. Yanzu kuma saura dubu d'ari uku da hamsin kud'in alhaji tukur yabiya suma yana kan har had'a masa abunsa. Goge hawayen da suka zubo masa yayi yana kallon mamy dake wanke naman kajin zata zuba atukunya ta d'ora kanwuta, sai yaji wani irin tausanta ya mamaye zuciyarsa, aransa yace Allah sarki mamynah yanzu asanadiyata akacire maki mahaifa badon hakaba da yanzu kin haifi wasu 'ya'yanki kuma k'annena dazan dinga kalla inji sanyi, tasowa yayi had'e da rungumeta yace


"Ina sonki mamy, ina sonki sosai fiye da rayuwata mamynah" murmushi tayi itama tace


"Nima haka amadidinah" duk suka kwashe da dariya atare.


Tun ranar da mom ta koma papi yayi niyar kiran Mahmud tasanar dashi zancen auren da yake son had'awa da 'yar wajen amininsa amma hajia kaka tahana tace yabari har sai ankwana biyu tukuna, yau kam papi yalashi takobin sai ya fad'awa jikansa qudurinsa don haka ya d'auki waya yakirasa akan yazo yana son ganinsa, bayan asa d'aya saiga Mahmud ya iso gidan bakinsa bud'e yana fara'a shida yaya Mahmud pilot dayake dawowarsu kenan sunkarb'o motocin da dady ya saya masu saiga kiran papi yashigo wannan dalilin yasa sukayo nan tare kafin su wuce gida , bayan sun gaggaisa an d'an tab'a wasannin jika da kaka papi yayi gyaran murya cikin dattako yafad'awa Mahmud cewa yaje gidan amininsa da suka gaisa dashi ranar akwai jikanyarsa da sukayi magana dashi akan zasu had'a aurensu idan sun daidaita shikenan sai ajira ranar buki ya huta da zaman gwauran taka papi yak'are maganar cike da tsokanarsa, sanin halin papi da yayi akan magana d'aya yasa yad'ago kai kamar zaiyi kuka yace


"Don Allah papi kayimun rai, wlh da akwai wacce nakeso kuma munyi alk'awarin aure da ita, kai da kanka kasha fad'amun babu kyau karya alk'awari idan kuma nabarta na auri zab'inka ai kaga siffofin munafukai sun tabbata akaina, idan yayi alk'awari ya sab'a koba haka ba papi?" tunda Mahmud pilot yaji zancen papi dariya ta cika masa ciki amma ba halin yinta saboda yanda papi yatsare gida, hajia kaka kam dariya tadingayi tana fad'in to banda abunka mommodu ai kai mijin mace hud'u ne saika had'a duka su biyun ka aura, 


"Kai hajia kaka kiyimin adalci kice ni mijin mace hud'u ne to idan nagado papi fa"


"Aaahaf..nafa  ganoka yaro, bama zaka gado shiba inkuwa so kakeyi ka gadoshi saidai in zabinka zaka hakura dashi kabi zab'insa kaga shikenan kayo gadonsa" hajia kaka tafad'a cike da tabbatar masa da maganarta. Kad'an yarage yafashe da kuka don gaba d'aya yau ancaza masa kai alamurransa gaba d'aya sun hargitse masa, 


"Mahmud katashi katafi ni bashawara nake nemanka ba umurnine kawai nabaka kuma cikin satinnan nakeso katafi kaji ko" papi yafad'a yana kallonsa.


Jiki ba k'wari Mahmud yamik'e yana fad'in "to papi" sai anjima sukayi masu sannan suka fita batare daya nuna masu kyautar motar da dady ya siya masu dayake ta d'aukin zuwa yagwada masuba.


Suna fita Mahmud pilot yakece da dariya hadda rik'e ciki yana cimasa "kaiii gaskiya natayaka murna d'an uwa irin wannan farinjini haka, mata uku ajere congrat Allah ya tabbatar mana da hakan" cike da b'acin rai yaya Mahmud yajuyo dak'arfi yace


"Ba amin ba! Ba amin ba kai bakada tausayine?" d'an ja da baya yayi had'e da cewa


"Cool...d'an uwa 1-1 katuna ko?"


"Mtssss badai cool ba d'an uwa saidai hot....





Post a Comment

0 Comments