TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

DIYAM PAGE 45

 By


Maman Maama


Episode Forty Five: Fauziyya


Murja tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba'a cigaba da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace "wallahi Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa samarin nan ina dasu, kuma duk wanda nacewa ya turo a cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi ba mu auren mu ke so kawai" na jinjina maganar nace "amma biki fa? Gara fa?" Tace "wannan kuma mijin ki zaki yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana. Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi abincin biki da shi" nayi dariya nace "kai murja, hadda sharri kuma?" Tace "wallahi ba sharri bane ba kayan da yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin su. Amma ya bar alhajin da yar shara".


Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su ya kira ni ya zazzage min bala'i. Bance masa komai ba har ya gama sannan nace "ni dai bani na kar zomon ba, ni ratayar ma ba'a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya gansu ba" ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya.


Tun ana gobe zai dawo yakira yagaya min "ke yanzu ko dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba. Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai kin tana de ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo" sai naji ma abin ya bani dariya nace "duk wanda ka gama samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar Diyam?" Bai musa ba yace "naki special ne. Da gaske nayi missing dinki fa" sai na kashe kawai. A raina ina jin inama yayi zamansa a can kar ya dawo?


Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe da taji tantakwashi. Na hada masa lemom kankana. Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa ya kaimu airport ni da Subay'a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai dai suje da Subay'a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana na gida nayi kwanciya ta a kan gado. 


Ina jinsu suka zo, kawai naji wani bacin rai ya sauko min nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay'a ta shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo min kaya da jirgi da mota" nace "kice kin gode, sannan kice masa ga abinci nan a dining" ta fita na koma nayi kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune ina kallonsa shima yana kallona, ya kara fari har da kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace "shikenan? Babu oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan welcome back hug ba zai samu ba?" Nace "na dafa maka abinci, nace maka sannu da zuwa sai menene kuma?" Ya saki hannun Subay'a ya hawo kan gadon sai nayi sauyi na sauka na fita na bar musu dakin. 


Na tarar da lodin kayansa a palo, na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana shirin wanka, na dauko abincin da nayi masa na kawo palon sama na ajiye sannan na koma kasa muka zuba ni da murja muna ci tace "ke ba zaki tafi gurin mijin ki ba ya dawo daga tafiya? Ke ana neman mijin ke kina wulakanta naki?" "Humm" kawai nace mata sai ga kira kuwa Subay'a tana yi min inzo inji Daddy. Yana zaune a kujera ya hade rai "ki zo ki zuba min abincin tunda ba zakiyi min wankan ba" bance komai ba na zuba masa na kawo table gabansa na ajiye masa. Yace "wai ke ciwon rashin magana ne ya same ki? Na fi so ina fada kina mayar min yafi dadi" nace "ba ciwon rashin magana bane ba, 拼ata ce ta girma shi yasa nake shiru a gaban ta" yayi dariya yana kallon Subay'a data zauna ta zuba mana ido. Na juya zan koma kasa sai ji nayi yace "kai! Matar nan wani duwawu naga kina yi fa" nayi saurin kallon Subay'a naga tana dariya sai kawai na girgiza kai na tafi.


Muna kasan Subay'a ta jawo wani karamin akwati da kyar, murja ta tashi ta taimaka mata suka sauko dashi tana cewa "Mommy kinga kayan da Daddy ya siyo min" tana ta bubbuda wa, kayan sawa ne masu kyau da takalma, sai toys, murja tana ta yabawa, sai kuma Subay'a ta koma sama da gudu sai gata da karamar travelling bag mai kyau ta kawo min. "Inji Daddy, wai irin kayan da turawa suke sakawa ne ya siyo miki kema kike sakawa. Ki koma irin su" na bata rai nace "to sarkin surutu" na karba na ajiye, murja ta dan dake ni tace "tashi zaki yi kije kiyi godiya sosai" na mike na tafi amma sai nayi kwana na shiga dakina nayi kwanciya ta.


Sai bayan magrib ya shigo dakin yana kallona ina ninke sallaya yace "zan fita, zan tafi zance" na dauke kaina nace "ba gidan Alhaji ya kamata kaje ba? Ka gaishe su kuma kaga abinda aka yiwa gidan?" Sai kawai naga yayi murmushi yace "au kishi kike dan zanje zance ko?" Na zauna a bakin gado nace "Saghir, na riga na gaya maka tun kafin kayi tafiyar nan ni ko mata goma zaka aura ba zanyi kishin ka ba. Ni da son samu nane ma hudu nake so kayi, yadda zaka bani takarda ta in kara gaba" ya karasa shigowa yana cewa "wato kin ganshi ko? Alhaji ya tura ki kin ganshi ko? To bara kiji, in shi yake zuga kima ki gaya masa, auren ki yanzu na fara. In kinga na rabu dake to mutuwa nayi" ya juya ya fita. 


Ranar da wuri na yiwa murja sallama na hau sama tana tsokana ta "wato miji yazo shine zaki tafi turaka ko?" Nayi dariya kawai na tafi, na shirya Subay'a na kwantar da ita sannan nima na shirya na rufe kofa ta nasa key nayi kwanciya ta. Cikin bacci naji karar wayata, na dauka na ga Saghir ne sai na saka ta a silent na juya na cigaba da bacci na, sai kuma naji shi yazo yana knocking, ko kallon kofar banyi ba har ya gaji yayi tafiyar sa. Da sassafe ya bar gidan, a raina nace "Allah ya raka taki gona".


Da yamma sai ga Mama tazo, ni na dauka zuwa tayi gani na sai da naji ta kama yi min fada sannan na fahimci Saghir ne ya kai kara ta. "Diyam me kike nema wa kanki? Kin manta abinda annabi ya fada cewa mata sunfi yawa a wuta? Kuma mafi yawansu sun shige ta ne sakamakon rashin bin aure? Abinda kike so kenan? Wuta kike so ki kai kanki? To wallahi ki nutsu kiyi wa kanki fada. Ganin Sadauki ya dawo ne zaki kuma dorawa kanki kulafucinsa ko? So kike a lahira shi Sadaukin da kike yi saboda shi idan ya aikata aiyukan alkhairi ya kasance a aljanna ke kuma kina wuta saboda shi?" Nace "Mama ni ba dan Sadauki bane ba, Sadaukin da ko kula ni baya yi?" Tace "to ya zaiyi ya kula ki? Matar aure ce fa ke. Ke ai har yanzu ba hankali ne ya ishe ki ba shi kuwa da hankalinsa. Saghir yace shi yana sonki, yana son zama dake, me yasa ke ba zaki so shi ba? Shima Sadaukin nan fa dole watarana aure zaiyi, yadda yake da kudin nan ma sai ki ga ya auri hudu a rana daya. In haka ta faru kuma ya zakiyi?.


Sai dare Saghir ya dawo gida. Yana shigowa palo murja ta gaishe shi ya hade rai yace "ki shirya gobe ki koma gida" tace to sai ya wuce sama. Murja ta kalleni pleadingly, ni kuma na daga mata kafada. Kamar bazan tashi ba musamman ganin ko kallon inda nake baiyi ba kuma dai sai na tashi na bi bayansa. Ina shiga dakinsa naga yana kokarin cire kaya sai na kama masa ya cire nayi hanging rigar sai yace "Mama tazo gidan nan kenan" na rike kugu nace "tunda ka kai kara ta ba dole tazo ba?" Ya zagayo hannayensa a waist dina yace "naga kina neman ki kaini lahira ne shi yasa na nemo taimakon gaggawa" ya shafa fuskata yace "you really are beautiful" na ture hannunsa nace "bararojin kuma?" Sai yayi dariya yace "wai baki manta ba, ai bararoji suna da kyau so it was a compliment" ya saka fuskarsa a cikin gashina yana shakar kamshinsa yace "tell me duk abinda kike so inyi miki" nace "ka bar murja ta cigaba da zama a gidan nan" yace "done. Sai kuma me?" Nayi shiru, yace yana zuge zip din rigata "ba zaki ce in fasa aure ba? Say it and it will be done" na sake shiru na rufe idona ina jin daci a bakina yace "kice 'hamma Saghir Please kar kayi min kishiya" bance komai ba ya daga ni ya dora akan gado, hawaye ya fara bin fuskata yace "kice hamma Saghir ina sonka" nayi shiru sai yayi ajjiyar zuciya yana hawowa gadon yace "watarana zaki fada, ina nan ina jira".


Ina kallon sa yana ta shirye shiryen sa, ni ko su inna ban gayawa zancen auren sa ba sai da suka ji daga gidan Alhaji Babba, Hajiya ta kira ni a waya "yanzu Diyam da gaske Saghir auren nan zaiyi? Shi yanzu kudin da zai kashe gurin auren ya bawa Alhaji su mana ko shago ya bude ya fara dan kasuwanci. Yanzu kina ganin kofar gidan nan ma da kyar Saghir ya saka ta shi ko a jikinsa ma wannan cin mutuncin da akayi wa gidan nan" "sai hakuri Hajiya" shine kawai abinda nace mata.


Har dani akaje aka kai lefe, aka saka rana akayi komai aka fara hidimar biki. Kowa sai mamaki na yake yi wai ni ko a jikina mijina zaiyi aure. Shi kuma Saghir kullum sai ya ce ince masa ya fasa aure ni kuma naki fada. Sai yayi fushi ya daina yi min magana sai kuma dan kansa ya sauko. Sadauki kuma bai kuma bi ta kaina ba, sai dai yakanje ya gaida Inna, kudin gidan gona kuwa account ya bude wa Asma'u ake zuba mata a ciki sai dai kawai su dauko suyi amfani da abinsu".


Satin bikin Saghir yana kamawa Hajiya ta kirani tace ita fa babu wani taro da zata yi, ni kuma sai nace zanyi walima ranar kawo amarya anan gidan Saghir, yadda kowa yazo in an kawo amarya sai ya ganta. Saghir yana ji ya fara fadan wai za'a bata masa gida. Ranar kafi suka zo suna ta daddaga hanci, na saka murja ta nuna musu spare dakin da yake sama suka ce "dama yace ba sai anyi mata komai ba ya saka komai a gidan, gadon ma da cewa yayi kar ayi mune muka ce sai anyi saboda kar a mata gori". Ina jinsu suna gulmar "wannan yar karamar yarinyar ce uwargida?".


Aka daura aure Saturday, Sunday kuma aka kawo amarya. Duk yan uwa sunzo walimar dana shirya, anci ansha sai kuma aka karbi amarya. Ni dai ina dakina basu kawo ta ba nima banje ba har aka gama kowa ya watse. Na shirya Subay'a nima na shirya muka yi kwanciyar mu sai na jiyo hayaniyar maza a waje, ni na manta ma ashe ana siyan baki. Sukayi ta hayaniyar su suka gama suka tafi ninina ta karanta novel din da Rumaisa ta turo min kafin ta tafi, sai ga Saghir ya shigo dakin. Ya hawo kan gadon ya karbi wayar daga hannuna yace "uwargida ran gida" sai abin ya bani dariya ma, yace "ki fito kiga amaryar ki. In ba kyason ta kuma kinyi alkawarin kula dani yadda ya kamata a yau zata koma gidan su" na mike ina saka hijab nace "ta sha zamanta. Tunda ba'a kaina zata zauna ba ni kuwa ina ruwana da ita?" Sai na wuce na barshi a nan. Ina shiga palo na ganta a xaune tana kallon kofar dakina. But unlike abinda Saghir yace na cewa nafita komai ni sai naga kamar ta fini komai except kyawun fuska. Ta fini shekaru, daga gani ta fini ilimin boko, ta fini girman jiki dan duk abubuwan da Saghir yake yawan complain cewa bani dasu ita tana dasu sosai. Tasha heavy make up da wani uban attach har gadon baya. Rigarta kusan rabin kirjinta a waje, na tambayi kaina "a haka akayi siyan bakin?" Na zauna nace "sannu amarya" ta kalleni tana yamutsa fuska tace "yauwa, sannu" Saghir ya shigo ya zauna a kusa da ita, kamar jira take yi sai ta dora kanta a kafadarsa hannunta kuma a kirjinsa. Nayi murmushi ina kallonsu, yace "Halima ga Fauziyya, Fauziyya ga Halima" ya kama jawabin zaman lafiya, baya son hayaniya waye da waye ya gama sai yace "to yanzu amarya zata gama kwana bakwai dinta da musulunci ya bata a matsayin ta na budurwa, daga nan sai kuma ayi maganar rabon kwana. Sai dariya taso kubce min na rufe baki na juya fuska, yace "kina da magana ne, Diyam?" Na girgiza kai, yace "no ki fadi abinda yake ranki, naga kamar kina dariya" nace "kawai dai naji kace budurwa ne, ni kuma da na ganta na dauka bazawara ce" sai tayi sauri ta mike zaune sosai tace "excuse me? Shi da zai aure ni bai gaya miki budurwa zai aura ko bazawara ba?" Nace "ba muyi wannan maganar dashi ba kuma to be frank bani da problem da koma wacece, Allah ya bada zaman lafiya, aci sati daya lafiya, sannan akan sati dayan na kara muku shekara daya kyauta from me to you" sai na mike nace "Allah ya bamu alkhairi".


Ina shiga daki yana shigowa shima, ya jawo ni tace "what? What was that? Wacce maganar banza naji kinyi a gurin can?" Nace "kyauta nayi maka ko ba ka so? Ji nake mai kula da kai a gado kake nema kuma gashi ka samu, ko shekarar tayi kadan ne in kara muku wata?" Sai na kwace jikina nace "and don't touch me kasan ba kwana na bane yau" na haye gado naja bargo. 


Ya tsaya yana kallona sai yace "yanzu har tsanar da kika yi min ta kai haka? To shikenan, saki kike nema na sani kuma ba zaki samu ba. Naji, Fauziyya zata kula da gado na amma duk abinda ya danganci aikin gida ke zaki ke yi, wanke wanke, shara, girki da komai" na gyara kwanciya nace "done. Shekara ta nawa ina wanke wanke da shara da girkin? Dan dai karin kwano daya ai ba zai gagare ni ba". Na rufe ido nace "in zaka fita dan kashe mana fitila Please".




Post a Comment

0 Comments