TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 53

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love 

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 5️⃣3️⃣

_________

Washe gari...


Tunda ta dawo daga asibiti kowa a ɗakinsa yake kwana separate, shi kansa baya son yin mistake ɗin cewa su kwana tare tun bayan daya kusance ta da kyar yake iya ɗauke kansa daga gareta, ya ƙosa sosai ta sake sakin jiki dashi ya koma dan ya gane yaren yanzu shiyasa Laylah ta dage ta manne masa, tun daya fara saukowa daga stairs ta kafe shi da ido daga inda ta zauna, kansa na ƙasa yana faman ɗaura agogo amma har ya ƙaraso dinning table bae iya ɗaurawa ba, tashi tayi daga zaunen da tayi ta ƙarasa gurinsa kai a ƙasa ta sa hannu ta karɓa agogon ta daura masa, idanu ya zuba mata yana kallon yanda morning face ɗinta yake sake sheƙi, murmushi yyi shi kaɗai kafin ya ƙarasa ya zauna, ido ta ƙura masa ganin yadda yyi kyau cikin ƙananun kayan dake jikinsa gashi sae baza ƙamshi yake yi kamar an ciro shi daga kwalban turare, serving ɗinsa tayi amma ko yunkurin fara ci bae yi ba, sae ma tsura wa abincin ido da yyi kamar wani abun aka zuba masa.


 Ta ga ya shirya da wuri zae fita amma kamar ba sauri yake yi ba tunda ya fara iyayi tun safiyar Allah ƙarfe sha ɗaya saura, kallon abincin tayi taga kome yake kallo, Irish ce soyayye da farfesun offals. Tashi tayi ta ƙaraso kusa dashi ta zauna a gefen kujerarsa, kallonsa tayi tace, "Aren't you hungry?" Kallonta yyi da fuska kamar zae yi mata shagwaɓa yace, "Ina ji manaaaa!" Kallonsa tayi tace, "Toh meye matsalar? Ko baka son wannan ne? Na dafa wani?" Ta faɗa tana nuna plate ɗin gabanshi, kai yyi saurin ɗaga mata yana smirking yace, "Eh banason shi, ni ke nake so.." juya ido tayi da sauri zata miƙe dan kunya ce ta sake koro ta, hannunta ya kamo ya jawota zuwa kan cinyarsa yace, "Please baby, just once. Sau ɗaya kawai zanyi!" Kallonshi tayi tace, "Akwai zafi kuma ni wallahi ban warke ba...." kusa da kunnenta ya matsa yace, "Ai dan wancan da farko ne yau baza kiji zafi ba, abun da kika ji jiya shi zakiji yau ma wanda ya fishi daɗi ma..." kallonsa tayi tana sake jin kunya, zumbur zata miƙe ya kamo waist ɗinta yana jiran answern ta, turo baki tayi tace, "Wallahi idan baka sake ni ba sae na faɗawa Aunty Jamilah..." ba shiri jin ta ambaci Ya Jamilah yace, "Toh shknn na haƙura, feed me!" Yana faɗan haka ya gyara mata zama a cinyarsa nan ta ɗibo abincin a fork ta miƙa masa, buɗe baki yyi ya karɓa yana ci a hankali, ganin rigar baccinta ita guiwa yasa hannu ya ɗage ya fara mata yawo da hannunsa akan cinya, kallonsa kawai tayi amma bata ce komai ba tunda fuske ya nuna kamar bbu abunda yake yi, tana cikin bashi taji yana ƙoƙarin zame mata pant ga caressing ɗinta da yake yi, wani zabura tayi kamar allura ya soke ta, take abubuwan da su Umma da Aunty Luba suka faɗa ya fara dawo mata cikin kai, kuka ta saka mishi tana faɗin, "Ni wallahi ka kyaleni.." ganin da gaske kukan zata yi masa yasa ya cire hannunsa ya cigaba da karɓan abincin da ta dage tana bashi, can ya kusa tayar da plate ɗinsa yace, "Ke baza ki ci bane?" Wani ta ɗauko ta kai bakinta, kafin ta zura duka cikin bakinta ya kamo gefen Irish ɗin yanda fuskarsu ta haɗe kamar suna kiss, hakan yasa ta sake mishi irish ɗin gaba ɗaya jin wani irin yanayi na ziyartar ta. Ɓata rai tayi ta miƙe tsaye ta kawo masa ruwa sannan ta fara kwashe kayan tana kaiwa kitchen, ya lura da ita sae ta sake jiki dashi sae wani abu yasa ta zabura. Ruwan yasha kafin yyi hanyar kitchen ɗin, jin motsinsa yasa tayi saurin share hawayenta, bae ƙarasa ba yace, "Zan fita, do you want anything?" Bata juyo ba tace, "Aah ba abunda nake so sae ka dawo" har ya juya zae fita tayi saurin cewa, "Yawwa dan Allah ga saƙon Hajiya ka wuce mata dashi.." wata jaka ta miƙa masa, yana leƙawa ya hangi kula a ciki, yana karɓa yyi mata kiss a goshi ya juya ya fice daga gidan, dinning table ta koma ta zauna tana sake jin zafin abunda su Umma suka gaya mata amma ba wanda zata iya faɗawa tunda bata da mahaifiya a raye.


Tun safiyar Allah message ɗin Umma ya shigo wayarsa cewar tana son magana dashi, yana shiga cikin gidan ya wuce part ɗin Hajiya saboda saƙonta, yana isa ya ganta a parlour a zaune tana hira ita da mae aikinta, da sallama ya shige nan mae aikin ta gaishesa ta miƙe ta fice daga ɗakin, a kan carpet ya zauna ya gaishe da Hajiya kafin ya miƙa mata jakar hannunsa, buɗewa tayi nan ƙamshi ya cike ɗakin murmushi Hajiya tayi tace, "Ɗannan kayi sa'ar mata, Allah Ya baku zuri'a ɗayyaba.." murmushi yyi yace, "Ameen!" Tamboyoyin daya saba jera mata yyi akan maganar magani kafin ya miƙe ya fice daga part ɗinta zuwa gurin Abba, bayan su gaisa da Abba ne ya raka Abba gurin parking space, "Yaushe kake son a ɗaura auren?" Sosa ƙeya yyi kafin yace, "Abba ai ko yaushe kace yyi amma nafi son sae na dawo daga Mission sae ayi..." ashe Umma na laɓe tana ji kuma hakan bae yi mata ba, motar Abba na fita daga gidan tayi sauri ta koma part ɗinta inda Aunty Luba ke jiranta, tana shigowa Aunty Luba ta miƙe tace, "Gashi nan ki san yadda zaki tursasa shi yasha ruwan maganin nan! Ta haka ne kawai zamu samu abunda muke so!" Karɓa Umma tayi ta ajiye akan table inda Aunty Luba ta miƙe ta fice daga part ɗin simi simi, Abideen yana shigowa ya tarar da Umma a zaune ta tusa gora kan table tana kallo.


Guri ya samu a ƙasa ya zauna tunda sun gaisa a parlourn Abba, goran Umma ta miƙa masa shi ko hannu yasa ya karɓa tareda zubawa Umma ido, ganin bata yi magana ba yace, "Umma na meye?" Ɓata fuska tayi tace, "Zan baka abunda zae kashe ka ne?" Saurin girgiza mata kai yyi ganin tayi masa fahimta abaibai, tsaki tayi tace, "Maza maza ka buɗe ka shanye shi naga magauta sun sako ka gaba!" Ganin ta kafe shi da ido yasa ya buɗe goran ya kai baki, wani wari yaji kamar zae yi amai amma yaga Umma ta kafe shi da ido tace, "Ko baza ka sha bane?" Da saurinsa yace, "Zan sha!" Yana faɗin haka yyi bismillah ya ɗauke numfashinsa ya fara sha, sae daya kwankwaɗe ya ajiye gorar yana yamutsa fuska duk da ruwan goran baya da taste amma akwai wari kuma ga yanda yaji tsikar jikinsa na tashi, murr kawai yasha ya daidaita fuskarsa jin Umma tana gyaran murya, bata ji daɗin Bismillar da yyi ba amma kuma take roƙon Allah Ya sa maganin yyi aiki.


Tana kallon yanda yake ta yamutsa fuska amma ko a jikinta dan fatan ta ɗaya maganin yyi aiki, gyaran murya tayi tace, "Yaushe za'a ɗaura auren?" Ajiyar zuciya ya sauke yace, "Umma nafi son idan na dawo daga Somalia sae ayi auren!" Tsaye Umma ta miƙe tace, "Wallahi baze yiwu bah, sae dae ko a ɗaura auren kana can idan ya so idan ka dawo sae ka ɗauki amaryar ka!" Sam bae ji daɗin maganar Umma ba yace, "Umma na fi son na gyara mata gidan da zata zauna ne idan na dawo!" Kallon banza Umma ta watsa masa tace, "Wallahi baka isa ba, a gidan da waccan mayyar take nan zaka saka Zaytoona. Wato ma har haka ta shanye ka?" Shiru yyi wa Umma ganin ranta ya ɓaci sosai, cigaba tayi da, "Wato ta shanye ka ita kaɗai, ka yi yawo da pant ɗinta a mota kuma ka siyan mata mota! Kai wani kalan shashasha ne?" Shiru yyi yana jin kunyar maganar pant da ta sake yi masa, baya son Umma na ganin laifin Safeerah hakan yasa ya ɗago kansa yace, "Umma ba ita tace na siya mata ba ni ne..." ai bae ƙarasa ba Umma ta wanke shi da wata wawiyar mari, giransa ne suka haɗe guri ɗaya kansa kuma ya ɗauke wuta baya ganin komai sae duhu, wani marin ta sake wanke sa dashi tace, "Mutumin banza da baka san ciwon kanka ba..." sinnar da kansa ƙasa yyi bae sake cewa komai ba, wani huci ne kawai ke fita daga hancinsa yana jin kansa na wani sarawa, ga yanda ransa ya ɓaci yana ji kamar yabi duka abubuwan parlourn yyi wurgi dasu ko zae huce, lokaci ɗaya idanunsa suka chanza suka yi ja dasu ga jijiyoyin kansa da hannayensa da suka fito, dunƙule hannayensa yyi yana ƙoƙarin controlling kansa, da kyar yake fahimtar surutan da take yi masa ƙarshe dae ji yyi tace, "...duk ɗakunan dake gidan ka wato mayyar can ne kawai zata mori babban gida ko toh baka isa ba itama a gidan zata zauna. Tashi ka bani guri mutumin banza!" A fusace ya miƙe ya fice, duk da yasan ransa ya ɓaci ji yyi wani baƙon abu yana mamaye masa ƙirji kamar an ɗaura masa dutse a ƙirji, burinsa ɗaya ya isa gida yanzu kawai ya kife akan gadonsa baya son ganin kowa, kamar wani mahaukaci haka yake jin kansa dan kamar ya fasa kansa da kanshi yake ji ko zae samu relief ɗin abunda ke damunsa. A fusace ya cilla motar kan titi duk da har wani dishi dishi yake gani amma a haka ya ƙarasa gida, jinsa yake yi kamar yyi ya, hannayensa a dunƙule ya shiga cikin gidan ya haye steps zai wuce part ɗinsa. 


Fitowarta daga ɗaki kenan ta ganshi yana hawowa da alama part ɗinsa zae wuce, ita kanta yanda ta ganshi ta tsorata sosai, jijiyoyin kansa duk a tashe ga idanunsa sunyi jajaye, ga wani huci da yake yi kamar shanu, haƙoransa kansu a haɗe suke ga yana tafe hannayensa a dunƙule da jini a jiki, tsoronsa taji ya kamata matuƙa amma deep alaƙar da suke dashi yasa ta bi bayansa, juyowa yyi ransa a ɓace yace, "DON'T YOU DARE FOLLOW ME!!!" ya san me zae iya faruwa ko yaushe idan yyi outburst yana jin tausayin yyi mata illa amma yau yaji koma meye zae iya yi mata dan ba ta ita yake yi dan shi kansa bae san meke damunsa ba....



©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments