TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 5

 D. Auta ce✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA BIYAR.*


       Dawowa ta gidan babu daɗewa, na jiyo muryar Firdausi tana rangaɗa sallama a tsakar gida. Su Ummu Salma suka ƙara tabbatar mini ita ce saboda ihun murnar ganin ta, da suke yi suna faɗin, 


      "Oyoyo Maman Khadija."


       Da sauri na fito na tarbe ta fuskata cike da annuri, saboda farincikin ganin ta a wannan lokacin. Ita ma babu yabo babu fallasa take kallo na, sannan ta gaishe da Inna Kulu da Umma. Na ja ta muka shige ɗaki bakina har kunne na fice bayan ta zauna. Na kawo mana abinci na dire a gabanta duk da kallon da take bi na da shi, hakan bai hana ni yalwata fuskata da murmushi ba, tare da faɗin,

    "Hajiya ga abinci da abin jiƙa maƙoshi!"

      Wani kallo ta yi mini sannan ta ce,

       "Ba shi ya kawo ni ba, don haka ki bari na fara yin abin da ya kawo ni, kafin ki yi mini tayin komai."

       Kafaɗa kawai na ɗaga mata, na fara cin abincin saboda masifaffiyar yunwar da na kwaso. Sai da na gama na kora da kunun ayar Umma, sannan na dawo natsuwata ina kallon yadda take shan kunun ayar kamar ba ta so. A ƙarshe ma rufe gorar ta yi ta ajiye gefe tana goge bakinta. Hakan ya sa na yi hanzarin haɗe fuska tare da faɗin,

      "Malama ki ƙara kunun ayar idan ma ba ki ƙoshi ba akwai ƙari, tun da kin ƙi cin abincin Inna Kulu."

     "Ba ƙin ci na yi ba!"


     "To mene ne? Ai sai na faɗa mata domin ta san zaman da za ta yi da ke, tun da ƙyamar abin hannunta kike yi."

      "To maganaɗisu. Ki rufa mini asiri kada ta ɗauka gaske kike yi." 


      Murmushi na yi mata mai sauti sannan na ce,

     "Ai gaskiya ce! Don yanayinki ya nuna abincin nata ne kawai ba kya so! Inna Kulu kina ina!!!!"

      Na ƙare zancen cike da tsokana cikin ɗaga murya, don na san abin da ta tsana kenan a duk lokacin da ta zo gidan; idan ta ƙi cin abu na haɗa ta da su Umma na ce su take ƙyama. 

      Cikin sauri ta toshe bakinta idonta a kan Inna Kulu ta ce, 

       "Ƙyale ta Inna! Sharrinta ne kawai da ta saba yi ba ta gajiya. Amma ni azumi ma nake yi."

    Baki buɗe na fara nuna wa Inna Kulu gorar kunun ayar da ke hannunta. Kuma aka yi dace ta tana ƙoƙarin kai wa bakinta. Daga ni har su Umma dariya muka yi mata. Ta fara goge bakinta bayan ta ajiye gorar tana faɗin,


    "Astagfirullahi! Azumina!"


    Mun ɗauki lokaci muna taɓa barkwanci a tsakaninmu, sannan Inna da Umma suka fice suka bar mu. Hakan ya ba ta damar ƙura mini kallo, cike da damuwa a kan fuskarta ta ce,

      "Ashe abin da ya faru kenan ba ni da labari?"


     "Bari ke dai, an sha artabu!"


      "To Ubangiji ya sa hakan shi ya fi alheri. Ni ma ban san me ke faruwa ba sai jiya da dare, lokacin da nake tambayar Abban su Khadijah da nufin zuwa gidanki."

      Murmushin yaƙe kawai na yi cike da ƙarfin hali na ce,

      "Ashe ya ji labarin?"


"Ai kuwa dai! Kin san mutane da bin rayuwar mutum sau da ƙafa. Kana bacci ana yi maka minshari."

      "Tabbas! Don ga shi ke ma da kike kusa da ni ba ki ji ba, amma ga shi har zance ya fara karaɗe gari, ana yamaɗiɗi da shi lungu da saƙo."


  "Allah dai ya kyauta kawai. Amma gaske ne Haidar yana hannunsa?"


     "E yana can! Sai fatan Allah ya yi masa garkuwa da abin ƙi."


     "Allahumma Amin Ya Rabb!"


     Daga haka muka yi shiru kowa da tunanin da yake yi. Ƙarar shigowar saƙo a wayata ya sa na miƙe ina ƙwala wa Umma Salma kira. Umurni na ba ta kwashe kayan abincin, sannan na ɗauko wayar ina dubawa. Babu shiri na kai zaune gefen gadon Umma cikin sanyin jiki.


   'Ban san me ya sa kike son azabtar da zuciyata ba!'


    Kallon saƙon na dinga yi, ina ta maimaita karatunsa a raina. Ba tare da na ɗauke idona a kan fuskart wayar ba, balle na yi wani motsin kirki. Cike da kasala na ajiye wayar a gefena na yi tagumi, saboda har cikin raina saƙon ya ratsa zuciyata da gangar jikina. Duk da ban san me na yi masa ba, balle na nemi azabtar da zuciyarsa a banza.

     'To me na koma yi masa bayan laifin da ya faɗa mini kafin mu rabu?'


    'Babu!' 


Ita ce amsar da wata zuciyar ta ba ni kai-tsaye, domin iya sanina ban yi komai ba, wanda zai ɓata wa wani ma balle shi da ba ma kusa.

      Kaina a ƙulle na kai kallona ga Firdausi, wacce ita ma ni take kallo cike da son ƙarin bayani. Murmushin na yi mata mai sauti, cike da ƙoƙarin na basar abin kada ta fahimci komai. Kamar ta karanci abin da ke cikin zuciyata ta ce,


     "Wai ina mutuminki?"


"Wan ne kenan?"


    Sai da ta gyara zamanta sannan ta ba ni amsa a gajarce ta ce,


 "MD mana!" 


        Guntun tsaki na yi mata sannan na ce,

      "Yana nan, yana ƙoƙarin ɗora mini laifin babu gaira balle dalili."


     "Laifi kuma?"

"E!"

      "To a kan me?"


"Shi kaɗai ya sani."


    "Ke ma ya dace a ce kin sani."


    "Ta wace hanya?"


"Ta hanyar fahimtarsa da kyau, da abin da ke janyo miki laifin."


    "Fito da ni a hanya!"


"Idan kin fara gano shi, ke da kanki za ki fahimci inda na dosa."


     "Kin ƙara jefa ni cikin ruɗu."


    "Babu wani ruɗun da Firdausi ta jefa ki! Kina sane sarai da biyar diddigin da yake yi miki tun kina da aure. Kuma ya yi ya gama duk nacin shi sai ya bar ki kamar yadda barci ya bar ido!"


   Zancen da Ummata ta yi kenan a sama tamkar ta dake ni. Bakina yana rawa na ce,

     "Wallahi Umma duk abin da yake yi yana yi ne don Allah ba don komai ba."

    "Kada ki mayar da ni wata gaula Zaituna! Don tun kafin a haife ki na san So da alamunsa. Saboda haka nake ƙoƙarin yi miki iyaka da shi tun ba yau ba. "

    Kai na shiga girgizawa idon a zare ina ta faɗin

       "Ba so na yake yi ba! Asali ma ko maganar banza ba ta taɓa haɗa ni da shi ba!"

      "Ja can! Kada takaicin ku ke da shi ya sa na kai miki duka! To bari ki ji! Daga ke har shi na gano take-takenku. Kuma tun wuri ake shawara ba sai an dawo ba! Ki fita daga sabgar shi tun kafin a hango mu ni da ke tashar 'yan barkono. Domin ban ga haɗin kifi da kaska ba! Ban yi tsaye aka raba auren ki da wancan sokon don ki ba shi fuskarki ba! Domin a wannan karon Ina son ki yi auren farinciki inda hankalinki zai kwanta, ba inda ba kya da natsuwar zuciya ba. Saboda ba zan sake sayar da Akuyata ta dawo tana gugar mini danga ba. Abin da aka yi baya ma ba don mun so ba! Amma tun da Allah ya raba bai dace ki sake yi mana zaɓen tumun dare ba..."

       

       "Ki yi haƙuri Umma, ban so shiga maganar nan ba. Amma ya dace na ɗan yi tsokaci a kan abin da na san kin sani Umma. A yanzu ba fito-na-fito ya dace a yi da duk wani mai son Zaituna ba. Zaɓin Allah za a nema saboda ya fi mu sanin inda nagartaccen yake. Sannan shi kansa wannan mutumin yana da kirki sosai Umma..."


    Zancen Firdausi kenan a lokacin da ta katse Umma, daga zazzafan kashedi da hannu mai sandar da take yi mini. Kafin ita ma Kawu Sale ya katse ta da faɗin,

     

      "Allah dai ya yi miki albarka! Ban san me yaron ya tare wa Habi ba, da tun farko take ƙoƙarin yi mana katanga da aikin alherin da yake son yi mana!"

       Cikin sanyin jiki Umma ta ce, "Dukanku kun kasa fahimtar inda na dosa. Yaron nan fa tun tana da aure yake bibiyarta, bai dace a ba shi damar da ta wuce gaisuwar Musulunci a tsakaninsu ba! Saboda ina jin tsoron namiji mai neman mata musamman masu aure. Domin Allah kaɗai ya san iya adadin matan da ya yi wa hakan kafin ita..." 


     "Zato zunubi ne, ko da ya zama gaskiya! Idan kin san ba za ki kyautata masa zato ba, to barin maganarsa ya fi alheri da bitar abin da zai janyo miki lalura. Mutumin nan dai ko ɗan iskan ne da gaske a yadda kike nufi; dole ne ki ɗaga masa ƙafa. Saboda bai fito da maitarsa a fili ya nuna muka gani ba. Don haka ko lahira ba a yanke wa mutum hukunci da laifin da bai riga ya aikata ba. Amma tun da ke kin ji kin gani ga fili ga mai doki, ita gina daman idan ta yi ruwa ne ake kiran ta da rijiya, idan kuma ba ta yi ba dole ne ta koma masai ko ba a so"


        Shiru ya ratsa tsakaninmu bayan maganar Kawu Sale da tafiyarsa. Kafin Inna Kulu ta kawar da shirun da cewa,

       "Shin mutumin ya fito ya ce yana son ta ne?"


     Girgiza kaina na yi cikin sauri, kafin na sauke ajiyar zuciya na ce, 

       "Idan ma ya ce, ni ba zan iya auren shi ba!"


      "Saboda me?"


Tambayar da Firdausi da Inna Kulu suka jefo mini kenan, idonsu a kaina cike da son ƙarin bayani. Cikin sanyin jiki na ba su amsa,

       "Saboda na ji an ce matarsa masifaffiya ce!"


      "Mitsssss! To ki jira ki samu wanda matarsa za ta roƙe ki da Allah ki auri mijinta."

        Cewar Inna Kulu kenan a ƙufule tana aiko mini harara. Kafin ta shigo ɗakin kai-tsaye ta samu wuri ta zauna. Idonta a kaina ta ce,

       "Karkaɗe kunnuwanki da kyau ki ji ni. Ko ba yau ba, ina so ki riƙe wannan karatun har ma ki yi wa wasu bita. Duk macen da kika ga mijinta zai yi aure ta ɗaga hankalinta tana masifa. To ki tabbatar da cewa abin kirki ne mijin, shi ya sa take kishin wata ta zo ta raɓe shi. Kuma duk rintsi kada ki ɗaga, ki kafe ki manne har sai kin ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Kada ki kuskura ki ji tsoron duk wata barazanar da za ta yi miki. Saboda ba ta so ki shigo ne shi ya sa, gudun ya raba kulawar da yake ba ta ya ba ki rabi. Don haka da kin ga irinsu; ki saka wa ranki kin yi mijin nuna wa sa'a. Sai dai idan Allah bai ƙaddara ba ki rungumi haƙuri."


      "Zancen ki gaskiya ne Inna Kulu! Ni ma na ƙara ɗimama karatuna."


     Firdausi ta ƙare maganar tana 'yar dariya, Inna Kulu ta nisa sannan ta sake cewa. 

      "To ku riƙe da kyau! Ko bayan ranmu ku karantar da wasu. Sannan zance na biyu; duk macen da kika ga za a yi mata kishiya hankalinta kwance ko kaɗan ba ta damu ba. Musamman masu faɗin, 'Ta zo ga gidan nan ta zauna ta ji in da daɗi, tun da dai ba a kaina za ta zauna ba ga ta ga gidan!' To da kin ga ire-irensu yi ta kanki tun da jajayen sawu ki ari na kare. Idan ba haka ba amaryar sai ta zamo goro ko kuɗin sayen goro gidansa. Domin kuwa sai ta gwammace zamanta gidansu, da shiga irin wannan gidan. Don mugunta wata makira murna ma za ta dinga yi da zuwan ki, ko babu komai za ki kwankwaɗi mugun halin mijinta kamar yadda yake zuƙa, ta yadda za a gano irin haƙurin da take yi da shi tsawon lokaci. Musamman a lokacin da kika yi ƙara, kashi ya game miki."

       "Hmmmmm! Lalle Inna Kulu kin gama gane ta kan tsiyoyin mata. Domin wannan zance naki gabaɗaya yana kan gaskiya. Saboda haka ke mai gudun wani saboda matarsa ki buɗe kunnuwanki da kyau, ki naɗe karatun Inna, ko don gaba ya yi miki amfani."


    Zancen Firdausi kenan tana maka mini harara tamkar wata Yayata. Kafin Umma ta saka mana shakku da fargaba a cikin zukatanmu duka. Domin a faraɗ ɗaya na gano zancenta bai yi wa Inna Kulu da Firdausi daɗi ba. Saboda maganar da ta furzo mai kama da kashedi ta ce,


   "Ummm! Kuna ƙoƙarin janyo sabgar mutumin nan a cikin rayuwar Zaituna. Bayan ni har ga Allah ko kaɗan bai kwanta mini ba."


     "Idan ita ya kwanta mata ai shi kenan. Don ba ke za ki yi mata zaman auren ba!"


     Zancen Inna Kulu kenan, wanda ya sa Umma miƙewa tana faɗin,

       "To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta!"


     Tana ƙare faɗar hakan ta fice ɗakin tana waƙar BARMANA CHOGE. inda take cewa,

        "Ku tashi sana'a mata, domin nema yana hana ciwon zuciya"



       




     Akwai ƙura hwa!😓





Ku yi haƙuri da ni na shiga rububi kwanan nan. Idan kun ji ni shiru akwai uzurin da ya ɓoye ni. 




Post a Comment

0 Comments