TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 18

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____18💎



  Dariya shima yayi sannan ya tako gaban kantareren gadon 


"Batool kutashi kufita yanzun nan zakuga papi yashigo kuma kar kunsan halinsa inya iskoku, ku kyale hajiya kaka kutafiyarku wajen mom, indai itace nasan bazata tashi baccin nan yanzu ba" yana rufe baki sai ga papi yashigo yana takawa ahankali, rufe k'ofar da zaiyi ya juyo ya hango masoyiyarsa a tsakiyar gado zaune tana faman gyan gyad'i sukuma sun sata agaba suna faman dariya, murmushi yayi had'e da tak'ara sandarsa yana takowa a inda suke kamar irin shima abun yabashi dariya, ganin haka yasa gaba d'ayansu suma suka sake kece da wata dariyar, yana isowa bakin gadon Mahmud yaja baya yayinda papi ya d'a sandarsa ya dokawa Batool a gefen kafad'a  yana fad'in


"Malfar iyayenku, kunjimun shashashun yara, babyn ku keyiwa haka, yau duk sai kunci k'wakwarku agidan nan" zagayen d'akin suka farayi da gudu suna dariya shikuma yana binsu don yabugesu, ya matuk'ar shan wahala bai kama ko d'ayan suba saida Mahmud ya rik'e masa Batool a bayanta ya doka mata sandar tayi tsalle tabar d'akin aguje dama tuni su Bassam suka samu damar bud'esa suka fece Mahmud nata yimasu dariya



"Kun ganemun ja'iran yara daga zuwa suna neman tayar mani da hankalina dana baby"


"Yihak'uri papi kaga harma babyn taka tariga da tashi" Mahmud ne yafad'i haka had'e dayi masa nuni da gefen da hajia kaka ke neman saukowa daga kan gado, juyowa papi yayi yana murmushi tare da takowa har inda take


"Baby kikoma kikwanta, nizan tsareki babu wanda zai dawowa anan har sai kingama baccinki" cikin muryar da zata tabbatar maka da cewa tabbas hajia kaka bata yau bace tace


"Inaaa, ai wannan bacci bazai yuyu yanzuba tunda suka iso, kuka tafashe dashi tana fad'in ina baccina mai dad'i suka tadani" wurinta Mahmud ya k'araso cike da ladabi yana gaisheta, saida ta amsa sannan tak'olomasa idanuwa had'e da rik'e masa kwalar riga,


"Kagansu nan haddashi aka tadani bacci da kuma ja'irar amaryar nan taka"


"A'a baby wannan fa mommodi d'inkine , Sam shibaya cikinsu Batulu dai ce da k'annenta su Bassam da Bilal"


"Haba kakaa! To kicikamun riga tunda kinji bana daga cikin su, irin wannan cacuma haka sai kace kura tasamu nama adawa" gaba d'aya suka kwashe da dariya tana mai shafa gefen fuskarsa had'e da sanya masa albarka, saida suka sake gaisawa sosai cikin kamala tare da ajiye wasar jika da kakanni a gefe suka fara zayyano masa matsalolin mahaifiyarsa da dady ya fad'amasu, ko kad'an baiyi musun abu d'aya daga cikiba kuma ya tabbatar masu da faruwar hakan saidai shi baisan ya zaiyi da mom tafahimcesa ba shiyasa yakasa kawo k'arshen matsalolin, shiru hajia kaka tayi kafin tajuyo ta rik'e hannun papi tana kallonsa,


"Wlh ni har tsoro yarinyar nan take bani, bansan a ina takoyo wannan zazzafan kishi haka ba, ta isko matar nan agidanta tabi tahanata sakewa ita da yaranta don tsabar mugun hali, kadubi yanda yaronta yafita hankali.." 


Cikin kuka tak'arasa maganar had'e da fad'awa ajikin papi, bubbuga bayanta ya dingayi yana bata hak'uri tare da nemawa 'yar tasu shiriyar Allah, Mahmud dake gefen su zaune yashiga tunani tare da lalubo kota ina mom d'insa tasamo halinta amma ya gagara samu, muryar hajia kaka yaji tana fad'in,


"Kahutar da kanka maigidana ni kaina nayita wannan tunanin amma bansamo amsar tambayar ba, haline kawai Allah ya halicceta dashi, saboda haka sai kuyita hak'uri kuna lurar da ita har Allah yasa tagane"


A b'angaren mom kuwa Basmah tasa agaba tana tambayarta abunda ke faruwa acikin gidan hadda tambayoyin da basu kamata ba tayi mata ba, ita kuma ta daddage tanata bata labarin k'arya da gaskiya, hadda cewa ai agabansu idan dady yadawo Ummi ke rungumesa ko kunyarsu bataji, shikuma yata biye mata ko damuwa dasu dake yimasa sannu da zuwa bayayi, gaba d'ai yanzu babu ruwansa dasu saidai Ummi da yaranta, wani zubinma fita yawo sukeyi a mota sukuma abarsu agida bazasu dawo ba sai kusan sha biyun dare" muryar Batool suka jiyo abakin k'ofa tana fad'in,


"Laa ilaha illallahu, kai yayya Basmah kiji tsoron Allah, kefa ba agidan kike kwana ba balle wuni taya akayi kikasan haka, wlh Allah mom kada kiyarda da zancenta k'arya takeyi" yatsine fuska mom tayi had'e da d'agawa Batool hannu alamun tazo, tana zuwa takama kunnenta ta murd'e sosai cikin fad'a tace


"Kina nufin Auntyn takice ke k'arya? Wannan abun data fad'a tabbas yafaru da basuyi ba taya zata gani harta fad'a inbanda rashin sanin ciwon kai irin na dadynku da rashin kunya agaban 'ya'yansa zai zauna yana wud'annan abubuwa ko kunyar Allah basaji" cikin dask'ararriyar muryar dake neman saka Batool kuka saboda rad'ad'i da zafi da kunnenta da mom ta rik'e keyi tace


"Kada kiyarda da kalaman yayya Basmah, wallahi mom ba gaskiya tafad'a makiba, kuma idanma hakanne meye laifi aciki Ummi fa matar sace duk abunda suka aikata a tsakaninsu ko agaban waye har ga Allah basada laifi, meye wani abun aciki da za'ace ko kunyar Allah bayaji, bakiga yanda indiyawa, turawa harma da larabawa keyin abunda yafi runguma agaban 'ya'yansu ba, yin hakan samfa ba laifi bane soyayyace.." Buge bakinta mom tayi cikin zafin rai tana cewa


"Rufemun baki samnar yarinya, kice kema Aisha ta b'ata mani rayuwarki ta asirce manike kamar yanda tayiwa yayanki, asheko tajawowa kanta dala ba ganwo" mere baki Basmah tayi tana kallon Batool


"Kinji ko mom, ai dama nafad'a maki Ummi gaba d'aya gidan yanzu juyashi takeyi babu mai girgiza mata ko ganin laifinta, tazubawa kowa a abinci ya cinye sai yanda tayi dashi" fitina mom tafarayi da maseefar don mema dady ya d'aukar mata 'ya'ya yabawa Ummi gashinan yaja mata suna neman lalace mata to wlh ita bazata yaddaba dole yamaido mata yaranta ahannunta sannan tafice tabar d'akin har lokacin tanaci gaba da banbami, kallon Basmah Batool tayi cike da jin haushinta tace


"Yayya Basmah shikenan kinyi farinciki ganin yanayin da mom tashiga?, shin meye ribarki acikin wannan k'aryar da kika shimfid'a?, meye Ummi takeyi maki datayi deserving all dis from you? Saida ta tashi daga inda take zaune sannan tace


"Banida lokacin amsa wud'annan tambayoyinki domin inada abinyi"


"A'a yayya kidawoma hanyar gaskiya domin ad'an zaman da nayi da Ummi na fahimci cewa tanada kyakkyawar manufa akanmu"


"And so what? Wannan fa duka munafuccine, taya zata nufi alkhairi damu bacin bata k'aunar mahaifiyarmu tana nema tarabata da dady"


"Baki fahimta bane yayya kyawawan halayentane ke neman fifita akan na mom awurinsa amma ba rabasu take son yiba, duk da mom mahaifiyar muce kidubi gaba d'aya yanda tafiye son kanta da yawa, wlh da Ummi fitinanniyace mai biyewa kausasan kalaman da mom keyi mata da tuni gidammu ya watse gaba d'aya, kuma bazata tab'a yadda tazauna damu ba har tabamu kulawar da itakanta mom saida taga canji ajikin mu, don Allah yayya Basmah kifito gurb'atacciyar duniyar da muke ciki kifahimci gaskiya" 


"Mtssssss...am tired of ur noise, kirik'e gaskiyarki" Basmah tafad'a tare da ficewarta, wani irin dogon iska Batool tafitar had'e da cewa


"Allah kaganar da mom d'inmu da kuma yayya Basmah, nikam nagane sharrin da zuciya keyi mani domin itama Ummi uwace agareni, su Billy kuwa tabbas 'YAN UWANA NE na jini kuma makusanta, tun ranar da Yaya yaganni zaune ina kuka akan Ummi tayi mani fad'an yin sallah akan lokaci ina ganin kamar tana takura mani ne yalurar dani cewa don tana sona yasa tayimun fad'a bawai takuranine take yiba yayita yimun nasiha nafahimci cewa Ummi alkhairi ce arayuwarmu amma kash duk da haka har yanzu yayya Basmah takasa gano hakan,


 

A asibiti kuwa Ummi ce zaune bakin gadon da Bilkisu ke kwance tana faman bacci hankali akwance bayan sun dawo daga wajen scanning ta rabka tagumi hawaye na zubar mata a idanuwa akan halin da take ciki na matsalar abokiyar zamanta gashi har yakai ga 'yarta  nason itama tadinga yimata rashin mutunci, izuwa yanzu tafara tsorata da alamurran Basmah yanda take nunawa tamkar itace kishiyar tata, itakam ko kad'an bazata iya cigaba da zama da itaba gwanda dady yaje ya dawo da mom d'insu hakan zai fimata kwanciyar hankali, a hankali Bilkisu tabud'e idanuwanta akan fuskar Ummi da hawaye suka yimata kwance akai, firgigit ta tashi zaune don gasgata abunda tagani, yatsa tasa ta lakuto hawayen sannan ta kalli Ummi


"Ya salam! Umminah kuka kikeyi?, miyafaru dake?" Batare da tace mata komai ba tajawota ajikinta tarungume 


"Ba komai Bilkisu amma ina so infad'a maki cewa aduk inda kika tsinci kanki ki kasance mai tsoron Allah a rayuwarki, ban yarda kicutawa matar mahaifin kiba domin itama uwace agareki, ban yarda kiguji 'ya'yanta ba komai rintsi komai wuya domin su 'yan uwanki ne, ina jin zafi sosai idan Basmah tayimun wasu abubuwan fiye da zafin da nakeji idan mahaifiyarta tayi mani, sau da dama akan yimaka abune idan kayi amma ni Allah shine sheda ban tab'a yiwa matan mahaifina rashin kunya ba balle hakan tafaru dani, amma nad'auki abun a matsayin jarabtani ne Allah keyi, don haka kigujewa aikata hakan gudun kema haka tafaru dake"


Hannu Billy tasa tagoge mata hawayen ta sannan tace 


"Zanyi yanda kikace Ummi, amma bazan samu damar aikata hakan ba matuk'ar zandinga ganin hawayen ki, hakan zaisa inji nayi loosing courage d'in yin hak'uri har inyi k'ok'arin kasa rama abunda akeyi maki"


"Bilkisu zuciya batada k'ashi fitar hawayen shike kashe rad'ad'in da nakeji a zuciya, amma ina tabbatar maki da babu komai duk abunda sukayi mana ko zasu yimana to nayafe masu fatana dukkaninmu Allah ya ganar damu kuma ya d'oramu akan gaskiya"


"Amin Ummi, yanzu yaushe zasu bamu sallama? Allah ni nagaji da kwancin asibitin nan" takardar sallama da akaba Ummi tajawo acikin jikkarta ta mik'a mata


"Nakira dadynki na sanar dashi, yanzu yayanki muke jira yadawo, amma sunce banda gobe mudawo karb'ar result"




Post a Comment

0 Comments