TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 55

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕

Page 5️⃣5️⃣

_______

Tun bayan da ta girka dinner tayi setting table ta koma ɗakinta dan bata ma son haɗuwa dashi bare wani abu ya haɗasu, tun kusan tara na dare ta kwanta tayi bacci dan gajiyar aikin gyaran ɗakinsa da tayi da yyi wa kaca kaca, tana yin wanka ta saka kayan bacci masu laushin gaske ta kwanta abunta bacci yyi awon gaba da ita. 


Yana shigowa cikin gidan ya zauna a dinning table yyi serving abincin da kansa ya zauna yana ci cikin sanyin jiki, a hanyar sa ta dawowa gida,cMG da kansa ya kirashi yake sanar masa da cewar situation ɗin Kenya da Somalia ƙaruwa yake yi so dole su tafi a daren zuwa 12 zasu wuce squadron jirgi zae jira su, team members ɗin ya kira ya sanar musu kasancewar sa leader, a hankali yake tauna abincin kamar shine abincinta na ƙarshe da zae ci duk cikin sanyi, yana gama ci yyi clearing table ɗin ya wuce ɗakinsa yyi wanka, camouflage uniform ya saka ya saka boot ɗinsa kafin ya ɗauki backpack ɗinsa ya kai parlour da yake a shirye already, sosai yake son yyi mata magana kafin ya tafi amma wani nauyi yake ji a ƙirjinsa kamar an ɗaura masa wani abu mae nauyi, duk da ba laifinsa bane ya kasa samun natsuwa a zuciyarsa. Gashi tun kafin ya tafi har ya fara kewarta har yana fatanya sake jin ɗumin jikinta a ƙirjinsa, kuma ya san ba hali ya tafi bae yi mata sallama ba hakan yasa ya fara zulumi. Da kyar dae ya tsinci ƙafafunsa suna nufar ɗakinta cikin rashin kuzari, a hankali ya tura ƙofar ɗakinta ya shiga ɗakin duhu sae dae hasken wata da ya ƙayata ɗakin da haske sa ga wani ƙamshi mae daɗi shaƙa dake fita daga ɗakin, a kan gado ya ganta tana bacci cikin kwanciyar hankali, gaban study table ɗinta ya ƙarasa ya samu pen da paper yyi rubutu dan dama haka yyi niyya, gaban gadon ya ƙarasa ya zauna a gefenta yana kallon sleeping face ɗinta ga yanda lafiyayyun eyelashes ɗinta suka kwanta kan kumatunta, sosai yake so ya ƙare mata kallo kafin ya tafi. Murmushi yyi kafin ya kai hannu yana shafa fuskarta cikin ƙauna yana murmushi, tana cikin bacci taji kamar ana shafa mata fuska yin tunanin ko shine yazo ya sake cutar daita yasa ta farka a zabure cikin tsoro, ganinsa a gabanta ba ƙaramin ƙara firgita ta yyi ba, matsawa tayi baya tayi da saurinta cikin murya mae rawa cike da tsoro tace, "Me..ya ..kawo..ka?" Shiru yyi yana kallonta cikin yanayin tausayi yace, "I came to say goodbye.." kallon banza tayi masa tana kallon agogo, kusan sha ɗaya da rabi na dare ne, matsowa yyi ya rungumeta wanda bata yi tsammanin hakan ba, fusge fusge ta fara tako cize masa kafaɗa da ƙarfin gaske yaji zafi amma haka ya fuske ya ƙi sakinta, ita kanta ganin ta cize shi da ƙarfi kuma bae sake ta ba yasa tace, "Ni ka kyaleni ko me kazo ka yi mani yau kuma?" Yana jin haka ya sake ta jiki a sanyaye yace, "I'm sorry Safeerah, bana cikin hayyacina lokacin, kiyi haƙuri!" Taɓe baki tayi bata ce komai ba, kanta ya tallafo da hannayensa biyu yace, "Wallahi da gaske I wasn't in my right mind, kiyi haƙuri!" A rayuwarsa bae iya bada haƙuri ba amma tunda ta shigo rayuwarsa ya koma bada haƙuri, wani motsi ta fara da bakinta kamar tana son magana amma tayi shiru dae, shi da yake kallonta sae abun ya birgeshi lokaci ɗaya ya manne lips ɗinsu ya fara aika mata da kiss da zafi zafi, tureshi tayi da dukkan ƙarfinta ta kalleshi, tissue ta fallo ta goge bakinta tace, "You disgust me Zayn, I thought you're better than this! Bana son ganinka ka tafi kawai ka bani guri!" Yana jin haka yasan there is no going back da halin taurin kanta, a sanyaye ya miƙe ya fice daga ɗakin bbu ko waiwaye shknn tunda tace ta bata son ganinshi, sosai yaji takaicin hakan ace wai ko mutum ɗaya ya kasa fahimtarsa musamman mutum biyu da yake ƙauna sosai Umma da ita amma gaba ɗaya sun juya masa baya, yana sauka daga steps ya zaro kwalin taba daga aljihun wandonsa ya kunna, a bakinsa ya maƙaleta ya ɗauki backpack ɗinsa ya fice daga gida, karon nan bbu wanda yyi wa sallama daga gidansu har Sadique bae gaya wa kowa ba, ɗaya daga cikin soldiers ɗin dake guarding gidan ya kaishi squadron. Yana shiga aircraft suka tashi, kowa ya kalli Team leader yasan bae baro gida lafiya ba amma ba wanda yyi magana har wasu suka fara bacci amma Abideen na zaune  banda tunani kala kala bbu abunda yake yi. 


Washe gari...

Bata tashi da wuri ba sae kusan sha ɗaya na safe, ta fita tayi breakfast amma bata ji shi ba ko alamarsa, ɗakinsa ta nufa ta duba amma shiru kuma ga gadonsa a gyare, sae a lokacin abunda ya faru jiya ya fara dawo mata, taɓe baki tayi ta cigaba da harkarta har sae lokaci ta kalli papern akan dressing mirrorn ta tana buɗewa taga rubutunsa a jiki.


# I'm sorry about what happened, zanyi miki bayani idan na dawo! I love you so much. 

Kallon papern ta tsaya yi tana taɓe baki cikin ko in kula amma deep down taji bbu daɗi gashi ita kaɗai a gida bbu zuwa makaranta bare wani abu ya ɗauke mata kewa, dunƙule paper tayi ta cillar dashi tana binsa da tsaki. 




Somewhere in Somalia...


Boxes ɗin bullets da grenade kawai sojojin nan suke unloading daga motarsu, suna aikinsu amma hankalinsu gaba ɗaya yana kan Team Leader da tunda suka iso yake smoking cigarette kuma by now ya shanye kusan packet ɗaya, duk bayan wani lokaci yake ciro wayarsa yana dubawa amma shiru bbu message bare kira kuma shi baze iya kira bah tunda she made it clear bata so ya kirata.


Cikin kwanakin nan sosai ya rame saboda ko wani abincin kirki baya ci, aikinsa ɗaya na shan taba yana jin shi kaɗai zae iya ɗauke masa hankali daga damuwa da kewarta da ya shiga, zaune yyi akan wani dutse ya zauna yana kallon full moon da ta haska ko ina kuma tayi kyau sosai, haka kawai ya kallo fuskar Safeerah tana murmushi cikin fara'a, kwanciya yyi kan dutsen yana murmushi. Zaune tayi riƙe da wayarta a hannu tana contemplating ko ta kirashi ko kar ta kira, da kyar ta danna call ta zauna shiru tana jiran ko zai ɗauka, yana kwance yaji wayarsa tana vibration a cikin rigarsa, zaro wayar yyi bae kawo komai ba da yake ya aiki wasu yaransa su shiga cikin gari su yi masa stocking packets of cigarette ɗinsa da ya ƙare kuma tun ɗazu suke kira suna yi masa shirme, a fusace ko kallon wayar ya ga wanda ya kira bae yi ba yyi picking yace, "Dalla ko wani kalan brand ku siyo, taba taba ce ai simple instruction kun kasa bi, kuma wallahi idan kuka dawo bbu cigarette ɗin nan, I'll deal with you mercilessly." Shiru tayi cikin kiɗima tana jin abunda yake faɗa, har ya sauke wayar daga kunninsa zae kashe yaji tace, "Basu bane, Safeerah ce!" 


* Toh... inji mae tallan totuwa...🫠

* Kar ku manta da vote da comments! 🥂✨️

* Wattpad @_khanoum_


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments