TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 12-END

 D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Yabo da jinjina gare ki Daughter Hanne Magaji. Har kullum idan na tuna alherinki gare ni ina jin daɗi har cikin raina. Ubangiji ya saka miki da mafificin alherinsa👏🏻*



*LAMBA SHA BIYU.*


       _Nan take raina ya ɓaci, saboda haushin yaudarar da yake yi mini. Daren ranar ba mu yi bacci mai daɗi ba daga ni har shi. Saboda ɗan banzan rikicin da muka tafka da shi, a kan cin amanar da yake ƙoƙarin yi mini ya raba ni da ƙawata. Bayan kwana biyu da wannan zancen Hafsa ta zo gidan. Babu kunya na sanar da ita abin da na ji kuma na fahimta, wanda ke tsakaninta da Mukhtar. Yanayin da ta nuna mini tare da rantsuwa a kan, ba za ta iya auren mijina ba; hakan ya sa na yarda da ita. Kuma na goge tsanar da na fara yi mata a raina, wacce ta sa na ci alwashin daina kula ta har ƙarshen numfashi. Haƙuri ta dinga ba ni tare da kalaman kwantar da kai a kan ko mutuwa na y; ba za ta iya auren mijina ba, balle ina da rayuwa._

      _Ba na mantawa akwai watarana da ta zo gidan tana taya ni aiki; Mukhtar ya shigo tare da abokinsa. Baki har kunne yake kallon mu yana 'yar dariya ya ce,_


    "Ina ma a ce ku matan mutum ɗaya ne? Wallahi kun dace sosai a kira ku da matan mutum ɗaya."


     "Ai kuwa gani nan bari nan dukiyar Alawa. Domin har abada ba zan yi kishi da ƙawata ba. Don haka ku gama tsegumin da ya kawo ku ku fice. Mukhtar nawa ne ni kaɗai, babu macen da ta isa raba ni da shi balle kuma ƙawata!"


     _Sumi-Sumi suka fice bayan sun gama borin kunyarsu, domin ita kanta sai da ta ce, su raba ta da wannan zancen. Domin ta san yadda nake kishin Mukhtar; ko kashe ta zan iya yi idan ta aure shi. Dariya suka saka sannan Abokin nasa ya ce, 'Ai Allah bai haramta ba' cikin ƙololuwar ɓacin rai na ce da shi; to ni na haramta masa auren wata ma balle ƙawata. Yanayin da suka ga na shiga ina ta zuba musu baƙaƙen maganganu ya sa suka fice bayan sun gama borin kunyarsu._

       _Domin ƙarfin zumuncin da nake da ita, har turmin atamfa na sa ya saya mata a wata sallah. Ashe ni suke yi wa kallon biri boko sun san abin da ke tsakaninsu. A lokacin wani sabon wulaƙancinsa ya tashi, ya yi ta mini abubuwan da ke ɓata mini rai, kuma ya san abubuwan da na tsana a rayuwata kenan. Ya tsiri wayar dare sai na yi bacci na farka na ji shi yana waya, haushi ya turnuƙe mini zuciya. Musamman kashe muryar da yake yi kamar na shaƙe shi ya mutu. Sai da muka yi gumurzun bala'i da shi sannan ya daina mini wayar tsakiyar dare cikin ɗaki._

       _Ina da tsohon cikin Iman, ya samu aiki a Community Bank. A lokacin likkafarsa ta fara cigaba, domin kuwa komai ya yalwatu Allah ya buɗe masa ƙofar samu. Hakan ya ba shi damar fantsama cikin neman matansa har da na aure. A ranar da na je gidansu Hafsa ina sanar da ita Mukhtar ya samu aiki; tsalle ta dinga yi tana murnar shi kenan sai ya aure ta. Mamaki ya sa na dinga kallon ta baki a sake tamkar wata wawuya, saboda tsabar mamakin maganar da na ji ta faɗa da bakinta._

   _Ban ji nauyin Mahaifiyarta da ke zaune tana sauraron mu ba, na ce; na rantse da Allah ba zai taɓa auren ki ba! Wata mata daga ke zaune ta ce saboda mi na ce haka, idona a rufe na ce da ita; ni da ita duka ɗaya ne a wurinsa. Don haka muddin ina tare da shi sai dai ita ta haƙura, idan kuma auren shi take son yi; to ni zan fita gidan na bar mata Ummu Salma da abin da zan haifa, sai ta ci gaba da rainonsu a matsayi uwa kamar yadda nake yi yanzu. Mahaifiyarta ta yi saurin faɗin; Allah ma ya kiyaye Zaituna! Ai da ki fita ki bar mata 'ya'ya, gara ta haƙura ki ci gaba da rainon yaranki._

       _Haka na fito gidan cike da mamakin zancen Hafsa, duk da daga baya ta ce da ni wasa ce take yi, domin ta ji abin da zan ce. Amma na ji zafin ta sosai, sai dai dole na haƙura saboda ba na son ƙawancenmu ya lalace sanadin hakan. Muka ci gaba da zama ba tare da na canza mata fuska ba, saboda iya fahimtar da na yi musu duka; na gano shi yake son ta ba ita take son shi ba._ 

        _Sai dai kuma har abada ba zan manta wani abu da ya yi mini ba. A lokacin da cikina ya shiga watan haihuwa, ya dinga yi mini abubuwan baƙƙan ciki iri-iri, wanda ban kawo dalilin faruwar su, balle laifin da na yi masa yake yi mini haka. Damuwa ta yi mini yawa ga haihuwa yau ko gobe, a gabansa zan ci kukana na ƙoshi; amma ƙanzil ba zai ce da ni ba balle na samu arziƙin ya ba ni haƙuri. Amma idan ta zo ya yi ta yage mata baki yana jan ta da surutu tana fuskewa._

       _Ranar da naƙuda ta kama ni gadan-gadan, ya kira mini wata malamar asibiti har gida ta duba ni. Ta ce ina da sauran awanni kafin na haihu, don a yadda ta ce zan ɗauki awa bakwai kafin kan Bbyn ya sauko ƙasa. Ta ba ni lokaci da nufin ta je ta dawo, tun misalin ƙarfe goma na safe nake ta shan wuya har zuwa yamma. Ganin ina ta fama da kaina ya kira Hafsa ta zo ta taya ni aiki, don ko shara ban yi ba ranar._

        _Jikinta yana ɓari ta fara aiki tana jera mini sannu, shi kuma sai tsokanarta yake yi da hira, ba tare da ya nuna damuwar halin da nake ciki ba. Asali ma yadda take nuna mini fuskar tausayi, shi ko rabin hakan ban samu a wurinsa ba. Bayan ta gama gyara gidan ta yi wa Ummu Salma wanka ta shiryata; ta dawo inda nake ta zauna, tana ta jera mini sannu a duk lokacin da marata ta murɗa. Ina ɗaukar lokaci cije da baki gumi yana tsattsafo mini kafin ta lafa na dawo sauke numfashin wahala. Amma a haka ya je ya siyo abinci a ƙatuwar kula. Ya zuba wa kansa ya zuba mata, ni kuma tun da ya ce zan iya ci na ce a'a, bai sake bi ta kaina ba.  Amma ita sai faman rarrashinta yake yi a kan ta ci abinci kada ta zauna da yunwa. Ni ko furar da na ce ina so na sha ma, tun da na kurɓa na ajiye bai damu da cewa dole sai na ƙara ba. Kuma a gabansa nake ta nishin wahala idan marar ta murɗa mini tamkar na shiɗe. Amma babu wata damuwa kan fuskarsa dangane da halin da nake ciki, saboda hankalinsa kacokam yana kanta sai faman kallon ta yake yi. Ita kuma tana haɗe masa fuska tana jera mini sannu cikin kulawa kamar ta yi kuka. Hakan ya sa na ƙara tabbatar da  shi yake haukarsa a kanta, amma ita ba ta damu da shi ba._


  




Na muku typing da yawa ya goge. Ku yi manage🧐





D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Masoya ABOKIN AIKINA a duk inda kuke ina ƙaunar ku. Alherin Allah ya kai muku har gadon baccinku. Farincikina yana linkuwa a duk lokacin da na ga ana rububin littafin. Raina yana haske, a duk lokacin da nake tarbon baƙin masoya littafin. Ina jin daɗin addu'o'in da kuke yi mini da fatan alheri. Rabbi ya biya da buƙatunku gabaɗaya, kuma ya saka muku da gidan aljanna maɗaukakiya!*



*LAMBA SHA UKU.*



         _Lokacin haihuwar yana cika malamar Asibitin ta dawo, ko minti talatin ba a yi da zuwanta ba na haifu. Na samu yarinyata fara, mai satar kamanceceniya da fuskar Mukhtar kwabo-dakwabo. A lokacin hidimar murnar haihuwar; na fuskanci abubuwan ɓacin rai da yawa a wurin Mukhtar. Domin komai za a yi ko a dafa; ba ya kasawa da ni, ba ya saka ni. Sai dai na ga ana yi, saboda komai Hafsa yake kira ko Yaya Maimuna. Sa da ragon da ya yanka wa Iman ma; ko shi ban san da zai yi ba sai dai na ji zancen a bakin Yaya Maimuna._

       _Hakan ya sa na sauya musu dukansu, sannan na ƙudurta idan aka gama bikin sunan; zan ba shi zaɓi a kan ya zaɓa ko ni ko Hafsa. Saboda na gaji da abubuwan da nake gani, waɗanda babu komai a cikinsu face kayan baƙinciki da ɓacin rai. Haka aka yi kuwa, bayan kwana biyu da suna ta zo gidan, yana tsaka da rawar kansa saboda ganin ta; na kira sunan shi tare da nata a wuri ɗaya cikin wata sarƙaƙƙiyar murya.Raina yana ɗaci na ajiye Iman da ke shan mama gefena a saman kujerar da nake kai. Sannan na kalle su ɗaya bayan ɗaya na ce da su,_


      "Daman magana ɗaya ce na nake son sanar da ku. Don haka kai Mukhtar ka zaɓa ko ni ko Hafsa a cikin gidan nan! Amma na gaji da ganin kayan takaicin da kake cusa mini saboda ita. Ko kuma na tattara sauran komatsaina na bar maka gidanka, sai ka auro ta ta dawo ɗakin nan da zama, domin ta maye maka gurbina" 

       _Kafin ya yi magana Hafsa ta riga shi da cewa,_

        "Haba Zaituna! Har sau nawa zan sanar da ke mijinki ya haramta gare ni? Idan ma kina tunanin zan aure shi na ci amanarki; wallahi ki daina! Ban da niyyar cin amanarki tuni da yanzu komai ya gama faruwa..."


     "Ki saka niyyar kawai ki aikata yanzu, saboda ba kanki farau ba! Kuma ba za a ƙare kanki ba"


       _Zancen da na faɗa kenan a zafafe saboda kalamanta na ƙarshe sun daki zuciyata. Fuskarta a a haɗe ta miƙe tsaye tare da gyara mayafinta tana faɗin,_

       "Don dai ina zuwa gidanki ne kike mini haka ko? To daga yau na daina in sha Allah! Zumuncin da ke tsakanina da ke kuma yana nan! Don ba dole sai na zo gidan nan zai ɗore ba! Ki yi haƙuri da duk abin da kike ganin na yi miki, domin ni kaina ba a son raina yake abin da yake yi ba!"


    _Tana ƙare faɗar maganar ta fice fuu! Ta bar mu ni da shi muna aika wa juna harara. Fuskarsa ya cure tamkar hadarin da ke gaf da ruwa, sannan ya nuna ni da hannu yana faɗin,_


      "Ke wace irin mace ce, da ba ta san arziƙi ba? Yanzu yarinyar nan duk wahalar da take yi miki ba ki gani ba; sai da kika yi mata kora da baƙin hali...?"


      "Na kore ta! Idan ka isa, kuma ka cika namijin gaske ka je ka dawo da ita a matsayin matarka! Ko an faɗa maka ban gano inda ka dosa ba? To na gama gano ka sarai da kalolin take-takenku daga kai har ita! Kuma na ji baƙincikin da ka mayar da ni wata sokuwa, kana saka ni ina ɗaukar abu ina ba ta da sunan ta kai wa Mamarta..."


     "Laifi ne don na siyo abu na ce a bai wa wani?"


      "Ba laifi ba ne! Amma yin kyautar a inda bai dace ba nake takaici. Saboda Ummata ta fi cancanta da ka saya wa abu, ka yi mata alheri ba uwar ƙawata ba! Domin ba su haɗa komai da kai ba face; ƙawancen da nake yi da su. To idan har abin ka don Allah kake yi, uwata ya dace ka yi wa abin da kake sa ana yi wa uwar ƙawata...!"


     "Ok! Yanzu na fahimci tsabar baƙinciki da hassadar da kike yi da abin da nake yi musu! To buɗe kunnuwanki da kyau! Duk abin da kika ga na yi, ina yi ne don ke da hidimar da Hafsa take yi a kanki da Ummu Salma. Amma tun da ba a miki gwaninta; daga yau komai ya ƙare, ko gidan nan ba za ta sake zuwa ba tun da kin kore ta! Sai ki ci kanki ta bar miki gidanki ki dafa shi ki cinye!"


    _Daga haka ya bar gidan, bai dawo ba sai da na yi bacci. Kuma tun daga ranar ya daina sake mini fuska. Sai ya tsiri Safa da Marwa tsakanin Runjin Sambo da Bafarawa Estate. Umma tun tana jin daɗin zuwa gaishe ta da yake yi, har ta fara zargin abin da ke kai shi unguwar koyaushe. Saboda yaran unguwar sun fara kai mata tsegumin; yawan ziryar da yake yi a gidansu Hafsa. Babban abin haushi, takanas yake shigowa da takardar kilishi ƙatuwa cike fam an yi rapping. Ya ce da ni saƙo aka ba shi na mutane ne kada na taɓa, haka zan zuba wa kilishin ido yana ta ƙamshi cikin ɗaki tun dare har safe. Ya kinkime shi ya fita da shi da sunan kai wa mai saƙon kayan shi, ashe ita yake kai wa har gida ita da Mamarta da ƙannenta._

        _Haka ma idan tafiya ta kama shi, duk lokacin da ya dawo; siyayyarta daban ce, kuma ta musamman ce! Ba na manta wata tafiyar da ya taɓa yi ya dawo, yara suka dinga shigowa da ledodi tun ina murna har na dawo mamakin yawan kayan. Yana shigowa tsakar gidan ya gan ni ina duba ledodin cike da jin daɗi, ya yi hanzarin faɗin na je na haɗa masa ruwan wanka a toilet ɗinmu. Tare da miƙo mini jakar kayansa na kai masa ɗaki. Ko da na dawo na tarad da babu rabin ledodin, cike da mamaki na dinga kallon kayan ina sanar da shi na haɗa masa ruwan wankan._

       _Bai bi ta kan ruwan ba har sai da ya gama kasa kayansa ya bai wa duk wanda yake so, sannan ya bar mana leda ɗaya ta Irish da wasu ƙwarorin gwaiba. Kallo ɗaya na yi wa kayan na ɗauke kaina na kwashe na kai Kitchen. A gabana ya bai wa ƙanensa kuɗi ya siyo masa lemu da ayaba masu kyau, ya haɗa da wani ƙaton biredi, ya ce yaron ya jira shi waje zai zo. Saboda yana so a kai wa Manajan Bankinsu kayan tun kafin ya zauna._

       _Tare suka fita ya bar ni da tunanin inda sauran ledodin suka yi, domin in da sabo na saba da wannan halin nasa. Wanda zai dawo da tsaraba himili guda, amma ya kwashe ya rabar. Idan danginsa suka tashi buga mini gora kuma; su ce komai ni yake kawo wa ina dannewa, ba na bai wa kowa sai abin da ya ba su. Kuma wannan ɗabi'ar kai wa Manajansu tsaraba; tun ba na jin haushi har na koma adawa da kyautar da yake yi masa. Saboda muna son abu ni da 'yata yake fita da shi a kai masa._

      _Ashe duk wannan hidimar da yake yi, Hafsa yake yi wa bauta ba Manajansu ba. Ni ma sai daga baya labarin ya dawo kunnena da na Ummata. Amma saboda tsabar ya mayar da ni wata shashasha! Da ya dawo ya gan ni zaune na yi tagumi, zama ya yi yana 'yar dariya ya tambaye ni lafiya, na ce da shi wani abu ne ya ba ni mamaki. Ya ce to na fara kawo masa abincinsa ya ci, kafin na sanar da shi. Babu musu na je na kawo masa na zauna gefen shi ina bai wa Iman nono. Yana cin abincin ya ce da ni,_ 


      "Me kike son sanar da ni?"


     Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce da shi,

       "Ledodin da ka shigo da su na yi mamakin ganin yawansu a farko. Amma ko da na gama haɗa maka ruwan wanka na koma na tarad da babu rabinsu. Shi ne nake ta mamakin inda sauran suka maƙale, domin na san ba su da ƙafafun guduwa balle su tsere, kuma ba su da fiffiken tashi balle su filfila sama su bar gidan nan!"


     _Sai da ya gama dariya son ransa, sannan ya ce da ni,_

      "Da alamu kin yi gamon da aka buɗe miki idanuwan ganin ledodin bibbiyu! Amma ni dai yadda kika ga yawan kayan, a haka na shigo da su garin nan, tun kafin na iso gidan nan a kawo miki su. Wataƙila dai, aljanu ne suka buɗe miki idon gani yau saboda murnar dawowata, shi ya sa kike kallon komai huɗu-huɗu."


       _Shiru kawai na yi ina kallon shi, zuciyata sai hasko mini yawan ledodin take yi a tsakar gidanmu. Da lokacin da yara suke ta shigowa da kayan suna ajiyewa tun kafin ya shigo. Domin idan ba idona bai gani daidai ba; kamar har da kwalin takalmi na gani a cikin wata leda da na buɗe. Hakan da na tuna ya sa na yi saurin cewa da shi,_

      "Su ma takalman da na gani a cikin kayan aljanun ne suka buɗe mini ido?"


     _Hanzarin miƙewa ya yi bayan ya ture plate ɗin abincin daga gabansa zuwa gefe, sosa kansa ya fara yi sannan ya ce da ni,_


      "Kin ga na sha'afa! Akwai ma wasu takalmin da na siyo miki suna cikin mota na bar su. Wai ko dai da gaske aljanun suna nuna miki abubuwan da ke nesa ban sani ba? To bari na je na kawo miki tun kafin su manna mini sharri, su haɗa ni faɗa da ke ranar da ya dace mu nuna kewar junanmu."


      _Mintuna a tsakani da fitar shi ya dawo da leda ya ɗora mini a cinya. Na gyara kwanciyar Iman a jikina saboda ta yi barci. Na fito da kwalin takalmin na buɗe, mamakin da na ƙara yi; ganin wasu kalar takalmi ba irin waɗanda na fara gani ba. Ban ce da shi komai ba na yi masa godiya, sai bayan ya shige toilet na ji raina ya yi ƙololuwar ɓaci. Saboda tunanin da zuciyata ta ba ni a kan; 'ko dai budurwarsa ya saya waɗanda na fara gani? To idan ma ita ya saya ma, wace ce ita?'_


      'Hafsa!'


_Wata amsar da na samu kenan daga wani gefen zuciyata. Zumbur na miƙe jikina yana rawa na goya Iman, bakin toilet ɗin na nufa kai-tsaye na buɗe na faɗa. A lokacin yana tsaka da wanka gabaɗaya jikinsa kumfa ne. Idona a kansa na ce,_


      "Wa ka kai wa takalmin da na fara gani?"


     _Salati ya fara yi, wani bayan wani yana sharce kumfan da ya cika fuskarsa da shi, ya buɗe idonsa cikin kumfan yana kallo na da ƙwayoyin idanuwansa, waɗanda suka fito tsakiyar kumfan tamkar wani zomo._


    "Wai ke! Wace irin mace ce da ba ta san yadda ake tarbon miji idan ya yi tafiya ba? Haka kika ga sauran matan gari suna yi wa mazajensu? To ban sani ba! Idan kina so na amsa miki tambayar ki shaƙe wuyana ki ji!"


     _Zuciyata tana tafarfasa na ce da shi,_


"Ba zan shaƙi wuyanka ba! Amma ka sani duk wacce na gani da su sai na ci ubanta. Saboda na gaji da abin da kake yi mini, wallahi na gaji! Idan kuma kai ma ka gaji da ni kawai ka sauwaƙe mini na huta! Domin har abada ba za ka canza daga Mukhtar ɗin da na sani ba! Idan taƙamarka ka yi kuɗi yanzu shi ne kake neman saita mini hanyar gidanmu; to ba sai ka yi hakan ba! Cikin sauƙi ka rattaba mini takardar sakina uku ka ba ni na ƙara gaba. Ba Hafsa ba ko uwarta kake son aure; na san ubanta zai sakar maka ita ka aura!"


   _Ina ƙare maganar na fito na fara haɗa kayana cikin wata jaka. Sai ga shi ya fito da sauti ya riƙe jakar, tare da kalaman borin kunyar na yi haƙuri cikin taushin murya kamar ya yi kuka. Kuka na fashe da shi wiwi tamkar wacce aka yi wa mutuwa. Saboda zafin da nake ji a zuciyata, ya fi ƙarfin na shanye takaicin a cikina. Da lallami da ban baki ya shawo kaina har na haƙura, a nan ya san yadda ya yi har ya karɓi haƙƙinsa bayan ya rufe ɗaki ya karɓi Iman ya ajiye ta falo._

       _Sai bayan komai ya hattama na dawo jin haushin kaina, a kan me ya sa na amince da shi ya kusance ni a lokacin. Ga shi ban yi satisfied ba kawai dai ya tsoma ya girgije ruwansa, duka na kai masa a cinya, sannan na miƙe cikin zafin nama saboda ganin jijiyarsa a leme tamkar ba ta taɓa tashi ba duniya._


    'Wasu maza dai sun ji haushi wallahi'


     _Abin da na faɗa kenan a zuciyata, kafin na ja tsaki a fili na faɗa toilet. Ina jin sautin ajiyar zuciyarsa da ƙarfi, a lokacin da nake kwarara wa kaina ruwan wankan dolen da ya saka ni, babu biyan buƙata. Amma kuma a hakan na nemi rabin haushinsa da nake ji; na rasa._


      _A taƙaice dai tun daga wannan lokacin Hafsa ta daina zuwa gidan. Ni ma na daina zuwa gidansu ko a waya na daina neman ta. Sai lokacin da ta kira ni da kanta tana sanar da ni an kawo mata lefe. Ban je ganin lefen ba, sai da na tabbatar da mijin da za ta aura wani ne daban ba Mukhtar ba. Ashe sun yi baram-baram da Ummata da Mamarta ba tare da na sani ba. Sanadin hakan suka daina sake wa Mukhtar fuska, suka hana shi zuwa gidan gabaɗaya. Domin Inna Kulu ta ce da ni, Umma har gidan ta je idonta rufe ta wanke Mamarta da zafafan maganganu. Waɗanda suka sa ta dawo ba ta haƙuri dole, tare da alwashin ko bayan ranta ba ta yafe ba idan Hafsa ta auri Mukhtar._

       _Dalilin da ya sa suka shirya kenan, don daman can ƙawaye ne ita da Ummata. Aka bai wa wani damar ya fito don daman can; hidimar da Mukhtar yake yi musu ce ta hana su hangen kowa. Ummata da kanta ta ba ni umurnin zuwa na gano lefen, domin na kafe a kan cewa ba zan je ba, kuma ni da ita har abada._

      _A ranar da na je ganin lefen nata ma sai da Mukhtar ya kira ta, ina zaune tana nuna mini kayan sai ga kiran shi a wayarta. Abban Ummu da na gani an rubuta a jikin wayar, hakan ya sa na zargi shi ne ya kira ta. Ban gasgata ba sai bayan ta gama wayar zuciyata ta tabbatar mini da shi ne suka yi waya. Saboda yanayin da ta shiga yayin wayar da irin maganganun da na ji tana faɗa. Raina a jagule na miƙe ina faɗin,_ 


    "To ni zan tafi, Allah ya sanya alheri"


      _Hankalinta a tashe ta riƙo hannuna ta ce,_


     "Ina za ki je, ba ki gama ganin kayan ba?"


     "Iman na tuna, sauri nake yi na koma kada ta tashi daga barci, gudun ta yi kuka Umma ta mini faɗa."


     _Sallama na yi wa Mamarta, ta tsayar da ni tana ba ni haƙuri a kan abin da ya faru. Na ce da ita babu komai ya wuce, Hafsa ta rako ni muka fito. Bakin ƙofar gidansu ta tsayar da ni tana faɗin,_


     "Don Allah Zaituna ki yi haƙuri! Abin da ya faru ma ƙaddara ce ki ɗauka komai ya wuce. Allah ya sani ina da masu sona da yawa, shi ya sa ban taɓa saka wa raina zan iya auren Mukhtar ba. Yanzu haka wannan kiran da kika ga an yi mini; wani tsohon mai sona ne ya kira ni. Yana zancen bai ji daɗin da wani ya kasa shi ba. Ya so ya aure ni amma tun da Allah bai nufa ba ya haƙura, duk da ya san da wuya ya samu wata wacce ta fi ni."


    _Murmushin yaƙe kawai na yi mata, saboda ganin ƙanwarta za ta shiga gidan, da talkamin da Mukhtar yake laƙaba mini aljanu a ƙafarta, har sun sha jiki. Kuma tun kafin sunan Abban Ummu ya fito a jikin wayarta, lambarsa na fara gani a lokacin da ya kira kafin sunan da ta saka masa. Saboda wayar ta fi kusa da ni, kuma ni ce ma na miƙa mata wayar da hannuna. Na shanye kukan da yake ƙoƙarin taso mini na ce da ita,_


     "Kada ki damu komai ya wuce!"


   _Daga haka na bar wurin ina goge hawayen da suka kangare mini, duk da ƙoƙarin dannar da nake yi musu a kan kada su fito a lokacin. Ban faɗa wa Ummata komai ba, saboda gudun wata sabuwar fitina ta tashi. Na sa a raina tun da dai ta samu wani mijin; babu amfanin ɗaga wata maganar da za ta sa a yi tashin hankali._

      _Mukhtar ma ban yi masa zancen ba, na bar shi da halinsa, da kuma ƙuncin da na ga yana yi shi kaɗai. Wanda kafin na ji zancen auren nata na sha fama da shi a kan me yake damunsa. Amma ya ƙi faɗa mini gaskiya ya fake da rashin lafiya, domin har da ciwo ya kwanta na kwana biyu ana masa allurori. Ashe duk na rashin Hafsa ne ban sani ba._

      _Lokacin bikin ma da ya kai ni gida, a gabana ya kira ƙanwar Hafsa ya ba ta kuɗi ya ce ta kai wa Mamarsu tasa gudunmuwa. Duk da na ji tsananin zafin abin amma ban tanka ba a lokacin, sai bayan an gama bikin, da dare  ya zo ɗauka ta za mu koma gida na fara sauke masa kwandon masifa. Ya ce da ni ai don na gani ya yi, da bai so na gani ba; ba zai bayar a gabana ba. Na ce da shi tun da ban kai darajar da zai ba ni kuɗin na bayar ba. Ai dole ya nemi wulaƙanta ni gaban ƙanwarta, domin da ya ɗauke ni mai muhimmanci ni zai bai wa kuɗin na kai musu. Babu doguwar jayayya ya ce da ni; duk yadda na ɗauka shi kenan, amma shi bai yi da wata manufa ba._ 


     Ƙwan-ƙwan-ƙwannn! Shi ne sautin ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da muka ji, daga ni har Amina muka kai kallonmu ga bakin ƙofar... 








D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



_*Ma sha Allah! Muna godiya ga Allah da ya ara mana rayuwa da lokaci. Domin mu taya ki murnar zagayowar wata shekara lafiya. Kina da kirki, kawaici, tsokana, barkwanci, tare da sanin darajar zamantakewa. Kina da matsayi mai girma a wurina, wanda duk tsawon lokaci ba zan manta tarihinki gare ni ba. Barka da ganin wannan rana, wacce ta zamo ƙari da ragin iskan numfashinki. Fatan Allah ya linka albarka a cikin sauran kwanakin da suka rage a rayuwarki. HAPPY birthday to you ƙanwata KHADIJA MUHAMMAD MRS BASAKKWACE😘*_



*LAMBA TA SHA HUƊU.*


         "Kash! Wannan abu bai mini daɗi ba! Daman fa abin da na yi wa gudu kenan, yaran nan su katse mana labar..."


     Zancen Amina kenan bayan ta buɗe ƙofar tana aika musu harara. Iman ta ɓata fuska tana cewa,

      

     "Shi ya ce mu zo wurinku"


     Dundu ta kai wa Yusuf tana faɗin, "Ai daman na san aikinsa ne! Maza ku je wurin Hajiya ku taya ta hira!"


      "Mun gaji da hirarta, ita da sai ana magana ta fara barci!"


     Gabaɗaya muka saka dariya, saboda zancen Yusuf da yanayin yadda ya yi maganar. Ganin Iman ce babba, na ce da ita,

    "Je ki koya masa karatu kafin na fito mu je gida."


     Hannunsa ta ja suka tafi, Amina ta yi hanzarin bin su da cewa,

     "Kada wanda ya dawo a cikinku har sai mun neme ku!"


     Rufe ƙofar ta yi, sannan ta dawo ta zauna ta yi tagumi, ta ɗauki ɗan lokaci tana kallo na ina mata dariya. Sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, 

       "Har kullum ba zan fasa jinjina miki ba! Domin kin yi namijin ƙoƙarin zama da Abban su Haidar. Saboda wallahi ni kwatar haƙurin nan ba zan iya yi ba. Yanzu ji don Allah ƙawarki ta ƙurciya ya yi ɗan waken zagaye, yana soyayya da ita a gefe. Idan ban da kina da ƙarfin zuciya ai da tuni ya manna miki ciwon hauka, ko ciwon hawan jini mai shanye sashe guda. Wannan masifa har ina? To ya aka yi da yarinyar da kika ce kin gano ya yi mata ciki?"


      "Hmmm!" Sautin ajiyar zuciyar da na sauke kenan cikin ƙarfi, sannan na gyara zamana na ce da ita,

         _"Bari na sanar da ke hotunan Hafsa da na gani a cikin kayansa, kafin mu je wurin Jamila. Saboda ina da hotunanta da yawa a wurina, wasu muna tare, wasu kuma ita da ƙannenta, sai waɗanda take ita kaɗai. To gabaɗaya waɗanda take ita kaɗai da ƙannenta duka a cikin kayansa na gansu._

        _Ya yi wata tafiya na ce bari na gyara masa kayan da ke cikin wata matsakaiciyar jakarsa. Waɗanda suka ƙumshi takardu, littafai da mujallu, tare da wasu tarkacensa da ya ba ya so su  salwanta. Domin a nan yake ajiyar abubuwansa masu muhimmanci. Zazzage kayan na yi ƙasa ina harhaɗa su, na gama haɗa su kenan na zo kakkaɓe jakar na mayar; kawai na ji abu cikin zif ɗin da aka rufe shimfiɗar jakar da shi. Cikin sauri na buɗe zip ɗin na fito da wani envelope da na yi tozali da shu, jikina yana rawa na buɗe shi ƙirjina yana luguden uku-uku._

       _Babu shiri na miƙe tsaye dafe da ƙirjina da ke barazanar tarwatsewa. Domin ƙarfin bugun da zuciyata ke yi; tamkar ta fasa ƙirjina ta fito waje. Saboda ganin hotunan Hafsa kala-kala, kuma bayan kowane hoto an yi rubuta zafafan kalaman soyayya. Babu shiri jiri ya kwashe ni na koma ƙasa daɓas, tare da yin zaman 'yan bori. Ranar na yi kuka, irin kukan da na ji ina ma ban taɓa sanin shi a duniyata ba. Ina ma ban san Hafsa ba balle mu ƙulla ƙawance, ina ma ban zo duniyar ba gabaɗaya, domin na huta da mummunan gani a cikin ɗakina._ 

      _Kuma babban abin haushin, ko da ya dawo na nuna masa hotunan ina masifa; bai ce da ni komai ba. Sai da na gaji don kaina sannan ya ce da ni, 'Da ma na daina wahalar da kaina a kan wacce na fi kowa sanin matar wani ce.' A fusace na ce da shi ya san matar wani ce; kuma yake ajiyar hotunanta a cikin kayan shi har zuwa lokacin. Buɗar bakinsa ya ce da ni,_


   "Daman can naki ne ba nawa ba, don haka tun da kin gani ki riƙe kayanki. Saboda babu amfanin da za su yi mini a yanzu!."


      _Yana ƙare maganar ya fice ya bar gidan, ba tare da ya damu da maganganun da nake jifar shi da su ba. Haka na kwashe kwanaki ina fushi da shi, amma ko a jikinsa. Dole na gaji na bari don kaina, saboda ganin bai damu da duk wata damuwar da zai gani kan fuskata ba._

      _Sannan zancen Jamila! Sai bayan ta yi aure na ji labarin shi ya yi mata ciki. Saboda Nura mijin da ya aure ta har dukan Mukhtar ya so yi, bayan bikinsu. Mutane suka taru ƙofar gidansu domin a nan ya zo ya same shi, yana ta zunduma masa zagi irin na tashanci. Kasancewar Mukhtar ma ba baya ba wurin faɗa, a nan suka dinga zagin juna har suka tara wa kansu mutane. Rikicin da na ji ya yi yawa na leƙa a nan na ji mafarin bala'in daga bakin Nura. Saboda tsattauran kashedin da yake yi masa a kan Jamila, tare da alwashin sai ya yi ajalinsa muddin ya sake zuwa kusa da ita, ko da sunan kallo balle ya kai ga taɓa jikinta._

       _Ban wani damu ba a lokacin, asali ma daɗi na ji da Nura ya yi masa rashin mutunci. Ko babu komai haƙƙina ya fita a kan abubuwan da yake yi mini. Amma da ya shigo gidan na rufe shi da bala'i ina tattara kayana zan bar gidan, Mahaifiyarsa ta zo ta dinga tausa ta da ƙyar na haƙura. Saboda gabaɗaya na ji ya fice mini a rai, kuma na ci alwashin ba zai sake kusanta ta ba. Sai dai ya je ya ci gaba da neman matan da yake yi a waje, kamar yadda ya saba. Kuma a haka muka zauna har tsawon lokacin da Allah ya kawo rabon cikin Iman._


      "Hmmm! Allah ya ƙara mana haƙuri!"


"Amin" Ita ce amsar da na bai wa Amina. Saboda ganin yadda jikinta ya yi laushi tun daga kan fuskarta. 

       "A cikin labarin Hafsa da kika ba ni, na ji kina zancen a lokacin da hanyoyin samu suka buɗe masa, ya shiga neman mata har da na aure. To ya aka yi kika san yana tare da matan aure?" 

      Murmushin takaici na yi mata a kan fuskata sannan na yi mere bayan na duƙar da kaina. Nan take na ji hawaye ya cika mini ido, saboda tuno komai da abin da ya faru.  Sai da na nisa sannan na ce,

      _"Ai mace biyu ne na san suna tare, ta farko wata 'yar gaba da unguwar ce. Ɗaya kuma ban san a ina take ba, kawai dai na kama saƙonninta a cikin wayarsa, sannan na kama shi yana waya da ita a gidan rijiya, wacce ke maƙale da gidanmu, kuma akwai ƙofar da za ta kai mutum har inda take. Ita nake bi a lokacin da nake buƙatar ɗebo ruwa. Sannan daga can ciki akwai wata ƙofar da 'yan gidansu suke shiga su ɗebi ruwan su ma._

      _Mafarin na sani a lokacin azumi ne, duk bayan shan ruwa yana shigewa cikin gidan, kuma ya kwashi lokaci bai fito ba. Tun ba na bi ta kai har na saka wa shigar da yake yi ido, saboda ina so na ga me yake yi a cikin gidan. Bayan shigar shi da ɗan lokaci na bi bayan shi,  saɗaf-saɗaf na dinga tafiya ina bin bango tamkar wata ɓarauniya. Saboda tashin muryarsa da nake ji ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa, cikin sa'a akwai duhu lokacin babu hasken farin wata balle ya gan ni. Haka na dinga lalube cikin duhun har na isa inda nake jin shi tar-tar yana magana tamkar da ni yake yi._


     "Cabɗijam! Ki ce da na haɗa faɗa... Um'ummmmh! To Allah ya ƙara tsarewa. E...haka ne, haka ne...to ya yi babu damuwa... Allah ya datar da mu...ok bye-bye sai kin kira..."


    _Ire-iren maganganun da na ji yana faɗa kenan, waɗanda gabaɗaya na fahimci da mace yake waya. Sai dai lafazin da ya yi a kan da ya haɗa faɗa, ya riƙe mini wuya. Ina nan tsaye a inda nake har ya gama wayar ya juyo zai fito, ya gan ni tsaye jikin bango na sha jinin jikina. Babu shiri ya zabura tare da yin ihu ya saki wayar a hannunsa ta yi ƙasa. Kallon shi na dinga yi a cikin duhu tamkar na rufe shi da duka. Fahimtar ni ce ya sa cikin ruɗu ya ce,_


     "Me ya.. ka..wo ki wurin.. nan!?"


    "Zuwa na yi domin na ji da wace shegiyar kake waya?"


     "Wai Allah! Yanzu a kan wannan abin ne kika biyo duhu kika zo don ki ji? To ba da kowa nake yi ba, shi kenan ko?"


    "Ba shi kenan ba! Sai ka faɗa mini wace ce kake zancen za ka haɗa faɗa? Idan kuma ba haka ba, wallahi a yanzun nan sai na bar maka gidanka tun da ba gidan ubana ba ne!"

       "Dakata! Abin fa bai kai can ba, in don wannan ne yanzu zan sanar da ke, ba sai kin ɗaga hankalinki ba. Wannan yarinyar da kika ga na yi waya da ita; a lokacin da na je Katsina ne muka haɗu. Shi ne fa wata tana ganin hotona a wurinta ta ce mata ita ma tana sona, shi ne abin ya zamo musu rikici, har sai da aka shiga tsakaninsu. To kin ji yadda abin yake, don haka don Allah ki daina mini haka. Ba ki ji yadda na ji ba a lokacin da na gan ki, irin haka sai ki sa zuciyar mutum ta buga saboda tsoro."


     _Wani malalacin kallo na bi shi da shi a cikin duhun, ya yi gaba na bi bayan shi ina faɗin,_


     "Ko ma wace ce! Ni na amince idan har son ta kake yi; ka aure ta kawai tun da har tana iya faɗa da wata a kanka."


     "Ba yanzu ba! Don tuni na faɗa mata ta yi auren ta kawai ta daina jira na. Kuma ta amince yanzu haka babu komai tsakanina da ita, face mutunci. Saboda ta riƙe ni matsayin Yayanta, domin ina ba ta shawara sosai a kan duk abin da ya shige mata duhu. Don haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai sake faruwa."  


     _Daga haka, ya baibaye ni da daɗin bakin da na yarda da shi kai-tsaye babu sauran shakku. Saboda Mukhtar gwani ne wurin iya magana, abu ko ba gaskiya ba ne; yana iya gyara shi ya yi masa adon da za ki rantse da Allah gaskiya ce tsagwaro._

      _Amma da yake Allah ba azzalumin Sarki ba ne, har bayan an mance da wannan zance. Na kama wayarsa da kalolin saƙonnin da suka so buga mini kwanya. Ba na mantawa ranar Sallar Layya ce abin ya faru, ya jona wayarsa caji ya fita waje suna hidimar raguna. Muna tsaka da gyaran hanji ni da Sajida, aka kira ni a waya, har Sajida za ta tashi ta ɗauko mini; na ce ta yi zamanta bari ni na je. Bayan na gama wayar ina ƙoƙarin mayar da ita cajin da take yi; na ga wayar mukhtar._

       _Mamaki ya kama ni, saboda sanin yadda yake ɓoyon wayarsa tamkar kuɗi. Ko wanka zai shiga da ita yake shiga, idan bacci zai yi tana ƙarƙashin filonsa. Ko da sunan haska fitila bai yarda na ɗauki wayarsa ba, domin ko ya ara mini ita; minti ɗaya ya yi yawa ya biyo ni baya gudun na masa bincike. Sai ga ta yau na gani a ɓagas, hidimar sallah ta sa ya ajiye ta ita kaɗai tana zuƙar caji._

      _Cikin sauri na ɗauki wayar na yi toilet, na shiga binciken saƙonnin da gani ɗaya bayan ɗaya, gumi ya shiga karyo mini ta ko'ina a jikina. Saboda jin abin da saƙonnin suka ƙumsa, ɗauke da rashin gaskiya ƙarara a cikinsu. Amma waɗanda suka fi ɗaukar hankalina guda uku ne, kuma su na yi ta maimaitawa a cikin zuciyata, sannan na kasa ɗauke idanuwana daga kansu da sunan A'isha wacce ita ce da alhakin turo saƙon._


     _'Kada ka kira ni, kada ka turo mini saƙo Oga yana gida.'_


     _'Wai ka san ranar nan oga ya gano abin da ya faru...? Ranar bai kwana gidan nan ba!  A çan ɗayan gidan shi ya kwana._


     _"Wani taimako nake so ka yi mini, domin babu wanda zai iya yi mini shi face kai. Don Allah ka sayi wani layi ka kira ni da shi zan tura masa lambar, saboda ya ce sai na ba shi lambarka. Ina so na ba shi ita a matsayin taka, ya ce zai kira ka ku yi magana, zan shirya maka abin da za ka faɗa masa idan ya kira. Saboda ba na so ya zarge ni, na fi son ko rabuwa zai yi da ni; ya sake ni ba tare da yana zargina ba!"_






     Wata sabuwa🤭na yi nan wallah🏃🏻‍♀️






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA BIYAR.*


         "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Gaskiya Maman Haidar kin ga abubuwa da yawa. Wannan masifa har ina? Daga wannan ta wuce sai wannan! To me ya ce da ke dangane da saƙonnin? Ko ba ki nuna masa kin gani ba?"


 _"Hmmmmm! Raina ya yi ƙololuwar ɓaci, saboda ganin saƙonnin da suka fi komai muni a cikin halayyarsa. Zuciyata a sama sai bugawa take yi da sauri da sauri, haka na dawo falo na zauna raina yana ƙuna. Kira na ƙwala wa Sajida cikin wata hargitsattsiyar murya, jikina yana tsima, bakina yana rawa na ce ta kira mini shi._

      _Mintuna a tsakani ta dawo tana sanar da ni ga shi nan zuwa. Kai kawai na ɗaga mata, amma ban iya cewa da ita komai ba. Saboda yadda nake ji a raina tamkar na kai wa iska duka. Ina nan zaune jikina yana ciccira ya shigo idonsa a kaina, yanayin da ya gan ni ya sa ya yi hanzarin zuwa wurin da ya saka cajin. Babu shiri ya juyo cikin hargitsattsen yanayi yana faɗin,_


     "Ina wayata da na saka caji!?"

 

    "Wayar da babu komai a cikinta face fasadi! To ga ta a hannuna, kuma duk wani bala'in da kake shirya wa a cikinta na gani tas! Amma ka sani wallahi haƙurina ya kai bango! Ba zan iya zama da mutumin da ke neman matan aure ba! Ko ka sake ni, ko na tona maka asiri wallahi..."


     "Dakata! Ke fa mummunar fassara gare ki koyaushe! Shi kenan daga ganin saƙo a wayata sai ki fassara shi yadda kike so?"


     "Saƙonnin da kansu su suka fassara kansu, babu buƙatar wani tambihi a cikinsu. Oga yana gida, kada ka kira ni ko ka turo mini saƙo! Amsa ce a bayyane wacce ko jahili zai fahimci inda zancen ya sa gaba balle ni. Domin ko a iya waɗannan kalmomin; na gama gamsuwa da abin da ka aikata, balle a je ga sauran saƙonnin da ke nuna tsantsar rashin gaskiya tsakaninka da matar wani. Yanzu Mukhtar matar aure kake nema a waje kuna aikata ɓarna?"


    _Na ƙare maganar cikin kukan da ya zo mini ba tare da na shirya wa zuwan sa ba. Cikin tashin hankali ya taso a ruɗe ya zauna kan kujerar da nake kai, janyo ni ya fara yi na buge masa hannu. Yana ta ƙoƙarin haɗa jikinsa da nawa cikin sigar rarrashi na ture shi cikin zafin rai na ce,_


       "Kada ka sake taɓa ni da hannun da kake taɓa matan banza! Na tsane ka Mukhtar! Na tsane ka!"


     _Kuka na fashe da shi wiwi saboda iya abin da zan iya yi kenan a lokacin. Domin idan zan biye abin da zuciyata take ingiza ni na aikata; to duka zan rufe shi da shi, har sai ya daina motsi yana gangar mutuwa sannan zan bar shi. Ko shi saboda gudun na kashe shi zunuban da ke kansa su juye kaina. A wannan lokacin ne kaɗai na ga weakness ɗin shi a zahiri. Domin bai taɓa karɓar laifinsa ba ko da ya san ya aikata, sai ya samu lagon da zai bi ya kare kansa, ta yadda zan yi saurin yarda da shi, ko kuma borin kunyar da zai sa mu hau sama mu faɗo ƙasa. Amma ranar rasa abin da zai faɗa ya yi, sai da ya bar ni na ci kukana na ƙoshi, yana zaune yana kallona ba tare da ya ce komai ba. Haushi ya sa na yunƙura zan tashi, ya yi hanzarin mayar da ni na zauna ina buge masa hannu. Saboda ina ji kamar na saka gatari na sare masa hannuwan gabaɗaya, ta yadda ko ni ba zai sake taɓawa ba balle ya je ƙetare iyakokin Allah inda bai dace ba._

      _Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya ce da ni,_

        "Allah shi ne shaidar; ban taɓa zina da ita ba. Asali ma ban taɓa ganin ta ido da ido ba. A facebook muka haɗu, a can muke zumunci da ita!"


      "To ya aka yi ta ce abin da Oga ya gani ransa ya ɓaci bai kwana gida ba?"


     _Na yi maganar cikin sanyi jiki, saboda ganin yadda ya dawo kalar tausayi a lokaci ɗaya abin ya tsaya mini zuciya. Shi ma sai da ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce da ni,_

      "Ni dai ki yi haƙuri, domin tabbas na san ban kyauta ba. Amma tun da har aikin gama ya gama kin gani; haƙurin kawai zan iya ba ki. Saboda ni kaina ban san matar aure ba ce har sai da muka shaƙu! Amma in Sha Allah daga wannan karon komai ya zo ƙarshe. Don tun kafin yanzu na daina kula ta, a dalilinta ma na daina facebook saboda ba na son muna haɗuwa da ita..."


     "A dalilin mijinta dai! Da yake ƙoƙarin binciko inda kake! Domin ba na raba ɗaya biyu a kan cewa; ita ce wacce kake waya da ita a lokacin da na kama ka gidan rijiya. Shi ya sa kake zancen za ka haɗa faɗa! To ka sani duk abin da ka yi sai an yi maka, kuma kada ka manta kana da 'ya'ya mata, kai ma ka haifa. Kuma ko babu su; ni akwai ni, shin ya za ka ji a lokacin da ka kama matarka tana hulɗa da wani namiji a waje?"


     "Ni dai ki bar zancen nan! Na dai faɗa miki gaskiyar abin da na sani, saboda haka ba na son kwatancen da kike yi a kanku. Laifi ne dai na aikata, kuma tun da na ce na daina; ba zan sake ba. Don haka ki daina mini kwatancen da zai saka mini ciwon zuciya..."


     "Ai duk abin da ka yi sai an yi maka Mukhtar! Saboda faɗar Allah da Manzonsa ba zai taɓa tashi ba! Fata na kawai kada Allah ya jarrabi 'ya'yana silar ta'adin da ka aikata. Ni ma ya kare ni shiga tarkon kowa domin na kauce wa abin da ka janyo mana. Sannan ka sani ka ƙara sani! Muddin ka yi sanadin aka lalata mini yarana; wallahi ko shi kaɗai ya rage ka shiga aljanna ba zan taɓa yafe maka ba! Kuma gidanka na gama zamansa tun da ba autan maza ne kai ba!"


     _Na tashi cikin sauri na figi hijabina na saka, ina ƙoƙarin fita ya sha gabana. Kokawa muka shiga yi da shi, har ya ci galabata ya rufe ni cikin ɗakin da makulli, sannan ya fita ya bar ni ina ta gurzar kuka wiwi tamkar wata ƙaramar yarinya._

      _Don tsabar ƙwarewa da kissa; Ummata ya kira a kan don Allah ta ba ni haƙuri, wai ya yi mini laifi kuma na ce sai na zo gida, don Allah ta hana ni zuwa shi ba ya son a ce ba na gidan ana hidimar sallah. Har da ƙarin ga nama nan ya ajiye tun ɗazu ba a gyara ba, kuma idan na tafi ba zai iya cin naman ba. Saboda ni kaɗai ce nake iya gyara masa shi yadda yake so. Duka na gano hakan ta hanyar faɗan da Umma take yi mini, tare da kashedin kada na kuskura na bar gidan. Idan kuma na fita ba tare da izinin sa ba; ba ta yafe mini ba!_ 


     "Cabɗijam! Lalle kin sha fama ba kaɗan ba! To ita ɗayar da kika ce 'yar unguwarku fa? Ita ma ya aka yi kika gane yana tare da ita?"


    Agogon hannuna na duba, ganin ƙarfe huɗu da minti goma; hakan ya sa na ce da ita ta bari mu yi sallah! Na miƙe na ɗoro sabuwar arwalla. Minti goma muka gabatar da sallar tare da addu'o'i, sannan na gyara zama na ce da ita,


    _"Ita ta unguwar; wasiƙa take turo yara da ita su kawo masa, duk lokacin da suka zo neman shi na ce ba ya nan. Kwatsam ranar na ce da su, 'wai wa yake aiko su?' Suka ce da ni Hassana ce take aiko su. Na ce wace ce ita, kuma wane saƙon ne take aiko su da shi wurinsa. Kafin su ba ni amsa ya shigo gidan, yana ganin su ya ja su suka fice waje. Suka bar ni da tunanin wace Hassana ce, da ya shigo na tambaye shi ya nuna mini babu komai. A ƙarshe ma mayar da ni wata 'yar dariya ya yi yana faɗin kishina ya yi yawa. Sannan ya koma gargaɗin na rage binciken abubuwan da babu ruwana a cikinsu. Har da faɗar, mace lauya ake so ta zamo wa mijinta ba 'yar sanda ba. Amma ni komai sai na yi binciken da ko 'yansanda ba su yi wa mutum irin shi._

      _Daga haka na ja bakina na tsuke, ban sake bi ta kan zancen ba, sai ranar da asiri ya tonu. Ko da yaran suka shigo neman sa, na rufe ƙofa na ce sai sun faɗa mini abin da ake aiko su wurin shi, ko kuma na zane su gabaɗaya. A nan suka fito mini da wasiƙa suka ba ni, cikin sauri na karanta ina aika musu harara na ce, a wane gida suke. Suka yi mini kwatance har na gane gidan da matar duka, sannan na yi musu ƙwaƙƙwaran kashedin,_


    "Duk na sake ganin ku a cikin gidan nan; sai na yi wasar kura da ku! Domin wallahi ta sake ba ku saƙo kuka kawo masa; na kama ku sai na lahira ya fi ku jin daɗi. Ita kuma ku sanar da ita, ta kiyayi lokacin da zan zo har gida na tona mata asiri a wurin mijinta!" 


    _Jikinsu yana rawa suka fice bayan na kora su da ice kamar wata mahaukaciya. Zama na yi ina ƙara bitar takardar, wacce babu komai a cikinta face tunatarwar neman ya cika mata alƙawarin da ya yi mata. Haka na yi ta juya wasiƙar cikin raina har ya dawo gidan, fuskata a haɗe na miƙa masa takardar, tare da rungume hannu a ƙirji ina aika masa harara._ 

     _Yana karanta wasiƙar yana satar kallo na tare da haɗe fuska, bayan ya gama ya tura ta aljihunsa zai bar wurin; na yi hanzarin jan rigarsa ta baya. Dole ya ja ya tsaya, na je gaban shi ido cikin ido na ce da shi,_


     "Mene ne haɗin ka da ita, da har za ta dinga turo yara suna ziryar kawo maka wasiƙu?"


    "Taimakon ta zan yi! Amma tun da abin ya zo da haka; dole na taka mata birki. Domin garin taimako ba za ta kashe mini aure ba! Amma tun da ta zaɓi hakan; ni bari na je wurin mijinta na sanar da shi komai. Kafin ta kashe mini aure ni na fara kashe mata nata..."


     "Babu ruwana, ban ce ka zamo silar mutuwar auren kowa ba! Amma wallahi muddin ta sake yi maka aike na gani; da kaina zan je har gidanta na faɗa wa mijinta abin da ke tsakaninku. Saboda ban ga ta inda haɗin ka da ita zai yi yiyuwa ba, ita matar aure kai mijin aure. Kai ko 'yar'uwarka ce tun da take da aure dole ta san yadda za ta tunkare ka; balle ita har gida don ta raina wa mutane hankali..."


     "Ki bar ni da ita! Ta yi na farko, ta yi na ƙarshe!"


   _Ya fice, ya bar ni da juya zantukan a cikin raina. Saboda lafuzzan da ya yi amfani da su; sun faranta mini rai, duk da ban gama yarda da shi ba. Don an yi wannan ne kafin na kama saƙonnin A'isha a cikin wayarsa. Shi ya sa ban ja abin da tsauri ba, saboda ban san shi da halin neman matan aure ba._ 

       _A lokacin ne kuma; bankinsu ya tura shi wani aiki Birnin Kebbi. Wanda ya ɗauke shi tsawon wata uku yana zirya duk bayan sati biyu. Ban san wainar da ya toya a garin ba, har sai da ƙawata Asma'u ta rasu sanadin haihuwar fari, saboda ta jima ba ta yi aure ba sai daga baya Allah ya kawo mata miji. Na je garin gaisuwa, ina zaune ɗakin Mamarta ina ta kuka ana rarrashina. A nan wata Yayarta ke cewa da ni,_

      "Ki yi haƙuri Zaituna, kowa ya san alaƙarki da Asma'u alaƙa ce irin ta 'yan'uwantaka. Wacce ba za a taɓa kwatanta ta da ƙawance ba. Dalilin da ya sa kenan; lokacin da mijinki ya zo neman aurenta ta ƙi amincewa. Domin ta sha faɗi, ko unguwar nan ta san yana neman aure; sai ta san hanyoyin da za ta bi; domin a fasa ba shi auren, gudun ki zargi da sanin ta ko da sa hannunta a ciki. Balle a ce ita da kanta ta aure miki miji ku yi zaman kishi a gida ɗaya. Duk da ya ce da sanin ki ya zo, amma hakan bai sa ta amince da shi ba." 


     _Sautin kukana ya ƙaru, saboda jin mummunan kisan gillar da Mukhtar yake ƙoƙarin yi mini ban sani ba. Har na fito gidan ban daina tunanin miyagun halayensa ba, waɗanda yake aikatawa ina gani, da ma waɗanda yake ƙoƙarin ɓoye mini Allah yana tona masa asiri._

      _Ban bari na dawo gidan ba, tun a cikin wayar na wanke shi tas, da soso da sabulu. Kuma na sanar da shi na gama aurensa har abada, kada ya sa ran zan dawo Sokoto balle na koma gidansa. Na samu wuri na yi zamana a gidan Baba Ali, tun ana sa ran zan dawo; har Baba Ali ya gaji da gani na ya ce yaushe zan koma. Saboda Ummata na yi mata ƙaryar Mukhtar ne ya ba ni kwanakin da yawa. Shi ma kamar ya gundura da ni, tun da muka yi haka da shi bai sake nema na ba._

      _Lokacin da Baba Ali ya yi mini zancen komawa na ce shi ya ce na zauna sai ya neme ni. Jin haka ya neme shi da kansa a kan me yake nufi da faɗar sai ya neme ni, ya dinga zuba rantsuwar bai ce da ni haka ba. Baba Ali ya fatattake ni na dawo ba don ina so ba. Amma kuma mun jima ban sakar masa fuska ba, saboda na kasa manta kalolin cin amanar da yake yi mini..._


    "Gaskiya Abban su Haidar ba ya yi miki adalci! Duk da a wasu wuraren kamar kina da laifi, amma duk abin da kika yi shi ya janyo komai. Saboda shi ne ya ba da ƙofar da zargi ya dinga shiga tsakaninki da shi. Ke kuma laifinki duka bai wuce binciken da kike yi masa ba, domin duk macen da ta ce za ta ɗauki ɗabi'ar binciken mijinta; to watarana sai ta binciko abin da zai yi silar ajalinta. Don a yadda kika ga yana yi miki ɓoyon wayarsa ba ya so ki ɗauka, ya dace ke ma ki taimaki kanki ki yi nesa da ita. Saboda duk abin da zai ɓata maka rai; bai dace ka buɗe ƙofarsa da hannunka ba. Ke ko da kin yi katarin an buɗe ƙofar domin ki gani, yana da kyau ki yi ƙoƙarin kawar da kanki, gudun a ɓata miki rai a banza."


     "Hmmmm! Na karɓi kuskuren, kuma in Sha Allah zan kiyaye faruwar hakan a gaba! Duk da dai yanzu komai ya ƙare a tsakanina da shi..."


     "Ban gane ba!"


Amina ta yi maganar idonta a zare tana kallo na cike da son ƙarin bayani. Murmushi na yi mata mai sauti sannan na ce,

      "Allah ya sahale mini kayan nauyin da nake ta faman ɗauka a kaina tsawon shekar..."


    "Kina nufin ku..."


"E! Mun rabu, kuma ba shi ya sake ni ba kotu ce ta raba mana auren..."


    "Innalillahi! Shi ne ban sani ba sai yanzu?"


   "A lokacin ke ma kina fama da matsalar Mama. Shi ya sa ban sanar da ke ba!"


     "To Ubangiji Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri. Amma ni ina jin tausayin su Haidar, musamman Ummu Salma da Iman. Waɗanda suka kasance mata, ba kamar Haidar da yake namiji ba."


   "Ai suna hannuna, Haidar ɗin ne a hannunsa."


      "Yawwa! Ma sha Allah! Ubangiji ya zamo gatansu duka!"


     "Amin Ya Allah!"


Haka kawai na tsinci zuciyata da ɓacin rai. Na miƙe ina ƙoƙarin gyara zaman doguwar rigar da ke jikina na ce,


      "Ni zan tafi, tun da na cika alƙawarin da na ɗauka!"


     "A'a gaskiya! Har yanzu da sauran abubuwan da kika lissafa mini a baya. Kuma alƙawari kika ɗauka dukansu za ki ba ni labari."


     Murmushin na yi mai sauti, saboda ganin yadda ta haɗe fuska alamun ba ta so na tafi. Cikin kwantar da murya na ce da ita,

      "Ko iya haka na sauke fiye da rabin alƙawarin. Saboda haka mu tara a gaba, yanzu time ya tafi Umma za ta yi mini faɗa, idan ta ga na daɗe ban dawo ba."


       "Ok tom! Na karɓi uzurin, amma da sharaɗin ranar Monday idan muka fito aiki; za ki ƙarasa mini"


     "In Sha Allah!" 


Daga haka na shirya tsaf kamar yadda na zo, na ƙwala wa Iman kira ta iso ɗakin tare da Yusuf. Kayan abincin na sa suka kwashe, sannan na biyo su na yi ɗakin Hajiya domin na yi mata sallama.

        Godiya ta yi mini sosai, tare da saƙon na gaishe da su Umma. Na fito gidan hannuna cikin na Iman Amina ta biyo mu. Wata leda ta miƙo mini na ƙi karɓa, ta ja hannun Iman ta saka mata ledar tana faɗin,


     "Ba ke na bai wa ba, don haka kada ki taɓa wa 'yata komai a ciki."


     Murmushi kawai na yi na sekonni, sannan na haɗe fuska tare da faɗin, "Idan har kina mini haka; kin kashe gobe na sake zuwa wurink..."


     "Yanzun ma ba wurina kika zo ba!" 


    "Oh! Haka ma za ki c..?"


     "E! Don haka a daina mini kashedi tun da ba don ni aka zo ba!"


    Ina ƙoƙarin mayar mata da raddi, motar MD ta doso mu, Wacce tun daga nesa bugun da ƙirjina ya yi ya tabbatar mini da shi ne ya zo. Cikin sauri na ja hannun Iman za mu bar wurin, Amina ta yi hanzarin faɗin,


     "Kin ga na sha'afa na manta da saƙon Maigida. Zumuɗin ganin ki ya sa na manta ban sanar da ke ya ce ku jira shi ba, domin shi ne ya ce zai mayar da ku gida."


    Dum-dum! Sautin dakan luguden da zuciyata ta yi kenan. Cikin tashin hankalin da ya bayyana kan fuskata na kai kallo na inda ya yi parking. Wanda alamu ya nuna zahiri mu yake jira mu ƙarasa inda yake, wani ɓacin rai ya daki zuciyata na kalli Amina na ce,

      "Ki ba shi haƙuri! Saboda wallahi ba za mu shiga motarsa ba!"


    Ina ƙare zancen na fisgi hannun Iman muka bar wurin tana ƙwala mini kira. Tafiya na dinga yi cikin sauri tamkar zan kifa, saboda tsoron abin da zai je ya dawo a lokacin da na shiga motarsa, ko kuma shi na ƙi shiga irin fushin da zai yi da ni.





Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Umma ko MD?🌝







D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA SHIDA.*


       Abin mamaki har na samu abin hawa bai biyo mu ba, zuciyata cike da tunanin,

      'Shin na tsayar da adaidaitasahun na koma na ba shi haƙuri; ko kuma na mazge kawai kamar ban yi komai ba?'

       Umurnin wani gefen zuciyata na bi da yake sanar da ni,

       'Share shi! Ai ba ke kika ce ya zo ba!i'


    Da wannan na hau kai na zauna, sai kallon gefe da gefen titi nake yi, amma zuciyata hasko mini shi take yi a cikin motarsa. Shigowar saƙo a wayata ya sa na yi hanzarin fiddo ta na duba. Ganin sunan shi a saman Notification ya sa jikina yana rawa na buɗe saƙon.


     _'Ni kike gudu ko? To na gode ki yi abin da kike so!'_


       Wani sabon tashin hankali ya ziyarcce ni, wanda ya sa na ji kamar na zura da gudu na same shi. Gumi ya shiga karyo mini, saboda dukan luguden da zuciyata ke yi.  Babu shiri na danna masa kira, amma har ta yi ringing ta ƙare bai ɗauka ba. Ban haƙura ba na sake wani kiran nan ma har ta katse bai ɗaga ba.

     Shiru kawai na yi babu zato na ji hawaye suna sauka a kan dandamalin fuskata. Cikin sauri na shafo fuskar kamar da wasa na ga ashe ruwan hawayen ne da gaske. 


      "Mama me ya faru?" 


Tambayar da Iman ta yi mini kenan, kuma na kasa amsawa, saboda ni kaina ba zan ce ga dalilin ba. Amma dai tabbas na so na ji muryarsa, kuma na ba shi haƙuri cikin tausasa harshe. Ko da zan goge rabin laifin da na yi masa,  amma kuma ya ƙi ɗaukar wayar. 


      "Wataƙila laifin da na yi masa ya sa ba ya son jin muryata.."


     Zancen zucin da na yi kenan,, amma amsar da Iman ta ba ni ya sa na gano a fili na yi zancen. 

       "Mama ki daina kuka, ai ya ce da ni tausayinki yake ji, kuma ni ma yana so na sosai har su Aunty Ummu da Haidar duka. Ya ce ma ɗauke mu zai yi ya kai mu gidansa, wai a can za mu dinga zama ya dinga kai mu makaranta."


     Baki a sake na dinga kallon bakin Iman, saboda mamakin magungunan da take fesa mini. Yarinyar da magana ma ba ta dame ta ba, amma har ya samu kanta yana zuba mata labari. Kuma shi ma a sanin da na yi masa ba mai yawan surutu ba ne, amma ya iya tarar ta da irin wannan magana mai girma. Ajiyar zuciya na fara saukewa kafin na ce,


     "To ke za ki iya zama gidansa ki bar ni?" 


       "Ai har da ke ya ce za mu je!"


    "Har da ni kuma?"

      

Na jefo mata tambayar a ruɗe, saboda jin maganar tamkar almara. Kai ta ɗaga mini tana 'yar dariyar jin daɗi, wacce alamunta ya nuna zahiri ya samu karɓuwa sosai a wurinta. 

       "Mama! Kuma fa ya ce na dinga kiran shi Daddy!"


     'Wata sabuwa!'


A raina na furta hakan, saboda gabaɗaya zantukanta sun rage mini kaso tara a cikin goman damuwar da na shiga. Sai kallon ta nake yi ina hango fuskarsa cikin tata farinciki ya mamaye zuciyata. Murmushi na dinga bin ta da shi jefi-jefi har aka ajiye mu ƙofar gidan Kawu Sale.

      Na biya mai adaidaitasahu kuɗinsa, ina ƙoƙarin juyawa na yi turus, saboda tozalin da na yi da motar Arma a gefen gidan sai ƙyalli take yi. Nan take gabana ya fara bugawa, saboda na san shi ne ya zo wurin Ummata.

      Hannun Iman na ja da ƙarfi, saboda yadda na tsinci ɓacin rai a cikin zuciyata nan take, wanda ban san dalilin faruwarsa ba balle abin da ya kawo shi. Illa ganin motar Arma, wanda jikina ya ba ni da gaske so yake a tuno da baya. 

     Da guntuwar sallamata na shiga gidan, saboda sautin dariyar shi da na ji shi da Umma suna hira. Idona a ƙasa na gaishe shi ba tare da na bari mun haɗa idanu ba. Na yi wa Umma sannu da gida, sannan na ce da Inna Kulu na dawo ina ƙoƙarin shigewa ɗaki. Umma ta yi hanzarin cewa da ni,


     "Ki zo ku gaisa da Armaya'u, saboda ke ya dawo gidan nan, domin ya ga jikinki!"


    Dariyar yaƙe na fara yi, sannan na miƙa wa Ummu Salma ledar da Amina ta ba mu, da niyyar ta kai ɗaki. Na dawo ɗan nesa da shi na tsaya ina faɗin,

      "Ai na ji sauƙi sosai! Da ba ka wahalar da kanka ka dawo ba."


    Na ƙare maganar ina aika masa murmushin dole. Saboda ba na so na yi laifi a wurin Umma, Kuma shi ma ba na so ya ga na yi masa wulaƙanci. Fuskarsa a washe ya ce da ni,

      "Ai dole na dawo na gan ki Zaituna, saboda da abin na kwana cikin raina har safe. Tun jiya na so zuwa Alhajinmu ya sa na wakilce shi zuwa wani taro. Shi ya sa na ci alwashin yau duk rintsi zan shigo na ga jikinki. To Allah ya bi da lafiya, tun da ga shi har kin samu ƙarfin yawo."


    Ya ƙare maganar yana aiko mini wani siririn kallo tare da murmushin da ya ƙi barin fuskarsa. Ni ma ina 'yar dariyar na ce da shi,

     "Alhmdulillah! Na murmuje"


     "To Allah ya ƙara afuwa!"


    "Amin" Na ce sannan na bar wurin zan shiga ɗaki, haka kawai na tsinci jikina yana sanar da ni kallona yake yi ta baya. Zama na yi kan gadon Umma ina jin yana faɗin,

      "To ni Umma zan tafi! Daman ita na zo gani. Allah ya ƙara sauƙi."


     "Amin-amin" na ji Umma tana ta faɗa, kafin na ji ya ce su Ummu Salma su raka shi waje su karɓo mini saƙona. Umma ta shiga faɗin,

     "Wai kai ba ka gajiya ne? Wannan hidimar ta yi yawa fa!"


       "Babu komai Umma, ai yi wa kai ne!"


    Shirun da na ji na gano ya fice, cikin sauri na fito ina faɗin,

      "Gaskiya Umma ki hana shi wannan wahalar da yake ƙoƙarin saka kan shi! Ba na so hankalin mutane ya dawo kanmu, a kan wannan ziryar da yake yi mana a cikin gida. Duka-duka yaushe ya zo amma shi ne ya kwaso ƙafafuwa ya dawo!"


    Wani kallon da Umma ta yi mini ya sa na ji hantar cikina ta murɗa. Kafin ta mayar da kanta gefe tana jinjina shi ba tare da ta ce komai ba. Sai da su Umma suka shigo da ledodi a hannunsu sannan ta washe fuska tana faɗin, 


    "Wannan yaro da ta ni yake bi da ya daina wannan almubazzanci. Abu idan Allah ya nufe shi da hidima ko babu sai an yi ai. Wannan kashe kai har ina! Kowa yana fama da kansa a wannan lokacin."

      

     Kallo na ƙura wa Umma kafin na maimaita zancenta a raina,

      'Abin da Allah ya nufe shi, da hidima ko babu sai an yi' 


Bakina yana rawa na yi hanzarin faɗin,


     "Umma me Allah zai nufa?" 


       "Auren ki da shi mana! Saboda jikina ya ba ni a kanki yake wannan hidimar. Kuma kyarkyara ce yake yi kafin zuwan lokacin da zai bayyana kansa. Domin na sanar da shi idda kike yi yanzu, wataƙila hakan ya dakatar da shi bayyana abin da ya kawo shi wurinmu!"


     "Aure! Aure fa Umma?"


"E, aure Zaituna! Ko kuma akwai hadisi ko ayar da aka kawo a kan haramcin auren ki da shi ne?"

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Umma ta ya za ki hasko zancen aure ya kawo shi wurinmu? To ko a faɗa cikin baki ma babu dacewa balle wani ya ji wannan maganar! Ko kin manta har yanzu saurayi ne bai taɓa aure ba?"

     "Ya sanar da ni, kuma ban manta ba! Amma ke da kanki kin san banza ba ta kai zomo kasuwa. Na sani ko a baya yana zuwa gaishe ni jefi-jefi, amma wannan zuwan ya sha bambam da na baya. Don haka ki daina ɗaga hankalinki a kan abin da daga ni har ke ba mu da iko a kansa, sai abin da Allah ya wanzar!"


     Cikin sanyin jiki na dinga kallon kayan da Umma take fito da su a ledodin, sannan na ce,

     "Hmmm! Babu haɗi tsakanin tsintsiya da ragga Umma. Ai idan hankali ya ɓata; wani hankalin ke nemo shi!"


    Ba ta ce da ni komai ba, har ta gama fito da kayan tana ƙwala wa Inna Kulu kira. Fuskarta na bi da kallo, domin ina so na tantance a wani matsayi zan ajiye yanayinta. Inna Kulu ta dinga yabon kayan tana Allah sanya alheri, ni kam tagumi kawai na yi, ina kallon kayan ɗaya bayan ɗaya ta wutsiyar idona. 

      Dogayen riguna biyu samfurin bugun ƙasar Sudan, sun yi kyau har sun gaji da ƙyallin ƙananan shuwari stone a gaban rigar, da gaban ɗankwalinsu. Sai takalma mahaɗin rigunan da agogon guda biyu, a gefe ɗaya kuma kwalin waya sabuwa dal bayan kayan fruits. Waɗanda suke nuna a zahiri dubiya ya zo yi a wurina, fuskar Umma ɗauke da mayalwacin farincikin da ke nuna jin daɗinta ƙarara. Sai lagudar kayan take yi tana jinjina kai alamun abin ya yi mata daɗi kuma kayan sun burge ta.

      Hakan ya sa na miƙe na yi ɗaki, zuciyata sai tafasa take yi. Saboda ganin da gaske Umma ta amince da Armaya'u ɗari bisa ɗari. Waton shi MD ƙaunar shi ce kawai ba ta yi, domin ba ta taɓa nuna jin daɗinta fili a kan wata bajintar da ya yi ba. Nan take na ji damuwa ta lulluɓe ni, domin na san za mu kwashi 'yan kallo tsakanina da ita; a duk lokacin da na sanar da ita ba zan auri Arma ba MD nake so.

     Kiran magrib ya sa na fito waje, ita da ke waje ta miƙe da ledodin kayan a hannunta ta yi ɗaki. Arwala nake yi amma zuciyata sai hango mini kalar rikicin da za mu yi da ita nake yi. 

      Bayan na gama sallah ina tsaka da cin abinci Umma ta shigo ta zauna, gabana ya ƙire ya faɗi saboda sunana da na ji ta kira cikin wata murya kamar ba ita ba. Kaina na ɗago tare da zare hannuna cikin kwanon abincin na amsa,


     "Na'am!"


Shiru ta yi na ɗan lokaci sannan ta ce da ni, "Shin kin san yaron nan Allah ne ya turo miki shi, domin ya wanke baƙincikin da Mukhtar ya bar ki da shi?"

     Kasa magana na yi, saboda ban san abin da zan ce da ita ba. Wataƙila gano hakan ya sa ta ci gaba da maganar ba tare da ta jira cewa ta ba.

      "Ki yi nazari da kyau, muddin kika aure shi kin kere sa'a, kuma kin wuce da sanin Mukhtar ta kowace fuska. Domin Allah ne zai kashe ya damƙa miki a cikin tafin hannunki. Kin ga ɗaya saurayi ne, bai taɓa aure ba balle ki yi fargaban wacce za ki taras. Na biyu, kowa ya san ubansa a faɗin jahar nan har ma da ƙetare, yana da usuli da nasaba mai kyaun da ya yi wa Mukhtar fintinkau. Abu mafi girma a cikin lamarinsa kuma shi ne; nagartarsa da kyakkyawan halinsa da muka sani tun a baya. Sannan idan za a yi duba da matsayinsa da namu ke ma kin san sun fi mu nesa ba kusa ba...ke ko don yadda ya dawo miki a yanzu, bayan doguwar tafiyar da ta mayar da ke uwa kuma bazawa; ya dace ki kalli irin wannan tarin ni'ima da baiwar da Ubangiji ya yi miki. Masoyin gaskiya ne kaɗai ake rabuwa da shi ya dawo, kuma duk rintsi kada ki bari damar da kika samu ta suɓuce miki a wannan karon."


     "Hmmmmm!" 


Ajiyar zuciyar da na iya saukewa kenan a farko, kafin na ture kwanon abincin gefe. Saboda yanayin da na tsinci kaina a ciki, ba zan iya dogon motsi ba, balle wata loma ta sake zuwa maƙoshina. Kallon da take yi mini mai nuna son jin ta bakina, ya sa na yi gyaran murya sannan na ce da ita,


      "Na gamsu da dukkan bayananki Umma! Kuma tun ba yanzu ba na san Arma masoyin gaskiya ne! Sai dai kuma, tazarar da ke tsakanina da shi a yanzu; ba za ta bar ni jin daɗin zama da shi ba. Saboda na yi masa nisan da duk gudunsa ba zai iya cim ma inda na je ba. Ina da yara har uku Umma, kuma a cikinsu akwai matashiya mai shekarun da suka haura goma. A tunaninki idan aka zo kwatancen matar da zai aura, ko kuma ya aura; ba za a kira ni tsohuwar mace ba? Shin ya kike hangen kallon da danginsa za su yi mini, a lokacin da suka ga Ummu Salma a matsayin 'yar matar da ɗansu, ko kuma wacce ɗan'uwansu zai auro musu a matsayinsa na matashi kuma saurayi? Sannan mu ta gefenmu nan, wane kalar kallo za a yi mana idan aka ji shi yake son aure na kuma mun amince? Ko ba a faɗa ba, mu da kanmu idan za mu yi wa kanmu adalci, za mu hango muguwar tazarar da ya yi mana, wanda yanzu ke ma kin faɗa ya fi mu nesa. To kai-tsaye za a mana fassarar masu kwaɗayin abin hannunsa. Ko da mun yi da zuciya ɗaya, sai an yi tunanin kuɗinsu ne suka ja mu. Saboda haka don Allah Umma ki dakatar da shi tun da wuri, kuma tun kafin ma wani ya san abin da yake ƙoƙarin aikatawa."


    Shirun da na ga ta yi ne, ya sa na fara tunanin ta gamsu da bayanan da na yi. Sai dai abin da ta zo da shi, ya rushe duk wani karsashin da zuciyata take ba ni a lokacin. Domin kuwa kai-tsaye ta ce da ni,


     "Ko da babu Armaya'u! Ba zan taɓa amincewa da auren ki da wannan mutumin ba. Don haka daga shi har shi duka mu ture su gefe, har zuwa lokacin da Allah zai kawo miki wani wanda ya fi su nagarta."






🤭🏃🏻‍♀️


D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Umma ta ce a gaishe ku duka, kuma a sanar da ku ta ji abin da kuke faɗa kanta.😹 Ni dai na ce kada ku manta da shaƙar wuyanku da aljanun Umma za su yi😛*



*LAMBA SHA BAKWAI.*


        Rasa me zan faɗa na yi, na ja bakina na tsuke. Saboda ina jin tsoron faɗar wata maganar, wacce za ta janyo ta yi mini bakin da ban san ina zan jefa kaina ba. Ko kuma ta yi maganganun da za su haramta mini MD kwata-kwata. Ita ma daga haka ba ta sake cewa da ni komai ba ta miƙe ta fice ɗakin.

      Daren ranar ma ban yi baccin kirki ba, saboda kukana da na kai wa Allah. Domin ya yi mini zaɓin abin da ya fi zama alheri gare ni da rayuwata. Na daɗa miƙa wuya ga Ubangiji, a kan ya zaɓa mini wanda ya fi alheri a tsakaninsu. Na ɓata daren duka domin neman biyan buƙatata, hakan ya sa da safe na tashi babu kuzari.

      A haka na yi ayukan da na saba, sannan na koma ɗaki na kwanta. Ban san lokacin da barci ya yi awon gaba da ni ba, ban tashi ba sai ƙarfe tara da rabi na safiya. Na miƙe jikina wasai na yi wanka, Ummu Salma ta kawo mini abin karina na karya. Ina ƙoƙarin miƙewa da kwanon na fito, da nufin wanke hannuna, na ji dirin mota a ƙofar gidan alamun mun yi baƙi. Haka kawai na ji ƙirjina yana dakan luguden da ban san dalili ba.  

      Na ajiye kwanon kenan ina tsaka da wanke hannu, na ji sallama su cikin ɗaga murya, alamun babu lafiya. Kafin na gama nazarin muryoyin har na gano mallakansu; sai ga Fatima matar MD na yi ido huɗu da ita, tare da Sara matar Basiru abokiyar aikina. Sai wasu mata biyu da na gane ɗayar ƙawar Fatima ce da suka je mini takakkiya har ofis. Ɗayar ce kawai ban waye ta ba.

      Kallon-kallo muka dinga yi wa juna a wulaƙance, yadda suke aiko mini nasu haka na dinga bin su da nawa ɗaya bayan ɗaya. Duk da  ganin su ya tsorata ni ainun, amma kuma ban bari fuskata ta nuna hakan ba. A gadarance na ce da su,


        "Malamai lafiya kuka shigo wa mutane gida haka kamar an koro ku?"


      "To ƙaramar ƙwaranya! Ba wurinki muka zo ba! Don kin mini kaɗan da na sake musayar yawu da ke! Wurin Uwarki na zo! Idan tana kusa kuma tana ji na ta fito na miƙa mata saƙon da ya kawo mu wurinta!"


     Ban yi mamakin jin abin da Fatimar ta faɗa ba, saboda ko a yanayinsu zai tabbatar da ba alheri ya kawo su gidan ba. Tattaki na yi cikin taƙama na isa gabanta muna fuskantar juna. Sai da na yi mata wani kafurin kallo sannan na watsar tare da buga mata tsaki mai sauti. Dariyar tura haushi na fara yi mata kafin na ce,

      "Ni nan na gagare ki balle Uwata? Kin yi gangancin da ba zai taɓa gyara shi ba a tsawon zaman da za ki yi duniya. Domin na sha gabanki a kan duk abin da kike taƙama da shi, kuma na wuce da sanin ki! Don haka tun wuri ke da karnukan farautarki ku ja tsummakaran ƙafafuwanku ku fice mana daga gida. Idan kuma kuna buƙatar ganin wasar kura a cikin tumakai, ku ƙara minti biyar ba tare da kun fice ba..."


       "Wai lafiya? Su waye waɗannan matan?"


     Tambayar da Inna Kulu ta yi kenan tana nuna su da hannu. Yamutsa fuska kawai na yi na ce da ita, 

       "Kamanninsu ma ai sun bayyana su waye Inna Kulu! Don ko a duba ɗaya za ki gano dukansu sakarkaru ne babu tunani mai kyau a cikin ƙwaƙwalensu. Domin da akwai cikakken hankali a kansu, da sun yi tunanin rashin amfanin zuwansu maƙurar rashin mutuncinsu. Saboda ban ga amfanin kawo kansu inda za su kwashi kashinsu a hannu ba..." 

      Na ƙare maganar ina aika musu harara, wacce alamu ya nuna maganata ta zafafa zukatansu. Domin kuwa Fatima a harzuƙe ta tare ni da cewa,


  "Ke ƙaramar ƙwaranya! Wurin Uwarki na zo, kuma tun da ga ta ta fito; ki ce ta matso na ba ta saƙon na juya. Saboda tun kafin a je ake shawara ba sai an dawo ba..."

       

      "Wai me ke tafe da ku ne? Da kuke wannan rashin darajar a cikin gidan mutane!"


    Inna Kulu ta ƙare maganar cikin fushi da ɗaga murya, Sara ta yi caraf ta ce, 

      "Kashedi muka zo yi mata a kan Maigida mijin Hajiya Fatima..."


      "Dakata Sara! Daina mini azarɓaɓin ci mini albasa da bakina! Idan har ke ce Uwarta da gaske! Na zo sanar da ku ki tanadi likkafanin 'yarki a cikin kwanan nan! Kuma ki sanar da masu kai ta maƙabarta su shirya akwai rakiya. Domin duk ranar da na sake kamata da mijina; sai na yi ajalinta! Sai na yi ajalinta! Sai na kashe ta Wallahi!!!"

        "Ƙarya kike yi! Uwar ubanki ma ta yi kaɗan! Zaituna ko 'yar tsana ce ta fi ƙarfin kisa a hannun magauta. Balle irinki tantiriya, 'yar tasha, haihuwar bariki mai tofin Allah tsine. Ki ji ki ƙara ji! Farcen 'yata ma ya fi ƙarfin ku taɓa balle ku kashe ta! Idan kuma kina musu ku taɓa ta ku gani. Wallahi! Wallahi! Raina fansa ne a kan 'yata Zaituna! Da ƙadangarun bariki irinta su taɓa ta gara a saita ƙirjina da bindiga a harbe ni!!!"

      Zancen Umma kenan wacce ta fito daga bayi tana ajiye buta ta yi kansu da masifa tamkar ta kai musu duka. Wanda ba su ba; har ni kaina na tsorata da jin manyan lafuzzan da ke fita daga bakinta. Amma saboda ƙarfin zuciya irin na  Fatima sai da ta gyara tsayuwarta ta ce,

 

     "To idan ba kya son faruwar hakan, kuma da gaske kina da sauran son 'yarki; ki ce ta rabu da mijina! Saboda nawa ne ni kaɗai, babu macen da ta isa na haɗa zaman kishi da ita. Idan kuma ba haka ba, zan aiwatar da abin da na faɗa a kanta ba tare da ɓata lokaci b.."


     "Ba ki isa ba! Kuma kin yi kaɗan ki raba abin da Allah ya haɗa. Auren shi kuma kamar ta yi ta gama, don haka ki shirya zaman kishi da ita. Don ko da bala'i sai ta shigo gidanki ta yi tarayya da mijinki! Munafukar banza 'yar baƙinciki, sai dai ki mutu amma sai ta kwana da mijinki  a gado ɗaya, kuma ya ba ta duk abin da yake ba ki! Baƙar almura, annamimiya, 'yar ƙasan wuta..."

      Cikin sauri na rufe wa Inna Kulu baki, saboda ganin da gaske ta haukace musu kamar wata zararriya. Ƙawar Fatima cikin ɗaga murya ta ce, 

      "Wallahi sai mun kashe ta idan ta aure shi! Tun da kunnuwan ƙashi ne da ku ba ku san arziƙi ba!"

      Babu zato muka jiyo sautin Umma tare da ice a hannunta tana faɗin,


 "Ihhhuuuu! Ba za a mana haka ba!!!! Ƙarya kuke yi tsinannu! gafalallu! la'annanu! jirgaggu! makakku!!!"


    Kafin ka ce me ta fara kai musu duka da icen, aguje suka fara rige-rigen  fita gidan suna turin juna. Cikin rashin sa'a Fatima ta faɗi ƙasa, a lokaci ɗaya ta riƙe ƙafa tare da fasa wata uwar ƙara. Amma duk da haka ba su juyo ba balle su taimake ta, ganin haka ya sa na yi hanzarin riƙe icen da Umma take ƙoƙarin kwaɗa mata a kai. Inna Kulu ta rirriƙe ta suka dinga kokawa, da ƙyar ta shigar da ita ɗaki ta rufe. A ɗakin ma Umma sai ihun take yi tare da faɗin sai sun kashe su, tun da suka zo har gida za su kashe ɗiyar goɗiyarsu.


     Kallon banza na yi wa Fatima da ke riƙe da ƙafarta tana ihu har lokacin, duk da ta ba ni tausayi matuƙa saboda gumin da na ga yana ta tsattsafo mata a goshi. Duƙawa na yi kusa da ita, ido cikin ido na ce da ita,


      "Ina miki albishir kin karye a ƙafa! Kuma kafin ki warke, zan auri Aliyuna. Kafin ƙafarki ta miƙe garas na samu ciki da Aliyuna. Kin ga ya zama nawa ni kaɗai daga yanzu. Tun da haukar ki ta janyo miki nakasa, a gaban idonki za ki ga komai, kuma ba za ki iya hana komai ba, balle ki yi komai.."


    "Kama ta mu fitar da ita waje, kada ta janyo mana musiba ba mu ji ba mu gani ba!"


Cewar Inna Kulu kenan, wacce hango ta ya sa na fasa ƙarasa faɗar abin da na yi niyya. Haka muka kama ta tana ihun wayyo ƙafarta muka fito da ita waje. Abokan tafiyarta muka hango bakin motarsu, kowace a hargitse suna mayar da numfashi a wahalce. 

      Hango mu da ita ya sa suka yo kanmu dukansu suna salati, dire ta muka yi ƙasa ta fasa ƙara. Inna Kulu ta dungure mata kai tana faɗin,

     "Gobe idan halinki ne ki koma zuwa takakkiya gidajen mutane! Don ko kashe ki aka yi ke kika janyo wa kanki baƙar almura. Ku kuma idan ba ku daina zuga ta ba; sai wutar Allah ta ci ɗuwawunku sakarkarun banza munafukai! Tun da ba za ku faɗa mata gaskiya ba sai dai ku ziga ta tana iskanci. Yanzu da bala'i ya tunkaro ku ai kowacen ku guduwa ta yi ta bar ta. Kuma da za a tona zukatanku dukanku, babu  wacce ba ta fatar ta samu auren mijin nata. Amma da yake ba kwa shuka alheri sai sharri, ga shi kun turo ta yin rashin mutunci ta karye a ƙafa. To ku kama ta ku kai ta gida, tun da jinya ta same ta!"


     Tana ƙare faɗar hakan ta juya, kallon-kallo muka dinga yi ni da Sara. Fuskata a haɗe na ce da ita, 

      "Munafuki dai bai ji daɗin halinsa ba, kuma a haka za a ƙare tun da hassada ta zamo abincinki ki..."


     "Ke zo mu shiga gida! Ƙyale sakarkarun banza marasa mafaɗa!"


   Na juya kamar yadda ta ba ni umurni, bayan na gama wanke su da tsaki na ce,

      "Kaɗan ma kuka gani, idan kun isa gobe ku dawo gidan ƙananun 'yan iska!"

    Zagi suka bi ni da shi kala-kala, daga ni har su Umma babu wanda bai sha zagi ba a bakunansu. Amma hakan bai sa na juyo ba balle na tanka, a ƙarshe ma yaran unguwar ne suka fatattake su kamar karnuka. Saboda dukan  da suka rufe motarsu da shi, har sai da suka buge musu gilashin gaba da ƙaton dutsi.

     Bayan sun kora su ne suka shigo gidan suna sanar da mu, da sun san rashin mutunci ya kawo su unguwar; da tuni sun zo har cikin gidan sun koya musu hankali. Godiya muka yi musu suka tafi, tare da cin alwashin duk lokacin da suka dawo; kada mu musu komai a nemo su kawai. 


    Ranar har marece Umma tana ta barci, sannan ta tashi idonta jawur tana faɗin ina suke ta ci ubansa. Kai-tsaye muka sanar da ita abin da ya faru da yadda aka ƙarge. 

     Kallona ta yi ko ƙyaftawa babu ta ce, "Matar abokin aikinki ce ko?"

    Na yi hanzarin ɗaga mata kai, cike da fargaban abin da za ta faɗa. Cikin sanyin murya ta ce, 

      "Ki kama kanki da ita! Don wannan komai za ta iya aikatawa. Sannan shi kan shi ki daina sake masa fuska, ki san hanyoyin da za ki bi ki toshe duk wata alaƙa da ke tsakaninku. Domin wannan matar, ba fata nake yi ba; amma ko aurensa kika yi masifar ta ba za ta bari ki huta ba!"

      "In Sha Allah Umma zan kama kaina fiye da zaton ki!"


     Murmushi na gani kwance a kan fuskarta. Wanda nake da tabbacin ta ji daɗin kalamaina, waɗanda suke nuni da  fita sabgar MD gabaɗaya. Dafa kaina ta yi kamar wata ƙaramar yarinya, ta tofe ni da addu'o'in da ban ji me take faɗa ba. Farinciki fal! Raina, ko babu komai na faranta mata rai, duk da abin da na faɗa iya kan harshena ne bai kai zuciyata ba.


 ***

   Da dare muka yi ta zanta abin har kowa ya shige barci. Daren ranar ma ban yi barci ba, na duƙufa neman zaɓin Allah cikin ƙanƙan da kai. Tare da addu'ar tsari ga 'ya'yana da neman musu miji nagari ba irin Babansu ba. Haidar ma na yi masa addu'o'in kariya da sharrin Mukhtar da matarsa. Saboda hankalina ya ƙi kwanciya a kan zaman da yake yi da su. 


       Da safe Monday, bayan mun ajiye su Ummu Salma, Najib ya juya adaidaitasahunsa zai kai ni wurin aiki. Ya sosa kansa yana cewa,


     "Aunty ban sanar da ke ba! Abban su Haidar 'yan sanda ya ɗauko mini har gida. A kan wai na je gidansa na ci zarafin matarsa. A taƙaice dai an sha gumurzu don har dukana ya so yi aka rirriƙe shi. An so kashe case ɗin a nan ya ce bai yarda ba sai an je station an yi mana iyaka. Yanzu an kai matsayar babu ni babu gidansa da Haidar.  Idan na sake shiga sabgarsu kuma kotu ce za ta raba mu, ban ji daɗin da Mahaifiyata ta taka mini birki ba. Amma wallahi Aunty ko ba yanzu ba, na ci alwashin sai na koya wa matar nan hankali."


    "Tun da aka ce ka bari, kawai ka bar su da Allah! Kowa ya yi nagari don kansa."


    Abin da na faɗa kenan raina a jagule, bai ce da ni komai ba har ya ajiye ni ya juya. Da sanyin jiki na shiga ciki zuciyata ɗauke da tunanin halin Mukhtar na rashin hankali a wasu lokutan. Saboda idan ya tashi yanke hukunci ba ya nazari kai-tsaye yake yin duk abin da ya shigo kansa.

      Kiciɓis na yi da MD ban sani ba, duk da ƙamshin turarensa ya sanar da ni shi ne; amma hakan bai sa na ɗaga kai na kalle shi ba. Saboda ina so na yi abin da zai faranta wa Umma duk da ba ta gani na, kuma ko da  iya kan fuskata ne.

      Sannan rashin mutuncin da matarsa ta yi mana har gida, ya sa na fara sanyi da lamarinsa. Ba wai don tsoro ba, kuma ba don na rage son shi ba; kawai dai ina so na koya wa zuciyata dangana. Saboda ban san abin da zai faru gaba ba, duk da ba na fatan rasa shi; amma ina ji kamar ba zan aure shi ba. 

      Ban damu da kallon da jikina ya ba ni yana mini ta baya ba, haka ma ban damu da tsayawa gaishe shi ba. Na buɗe ofishina na shige, na tarad da shi a share komai fes-fes, hakan ya tabbatar mini da Inna Taru ta yi mini shara da goge-goge. 

     Zama na yi ina sauke numfashi, daga shirun da na yi barci ya sace ni a zaune. Sai jin tatttausar muryarsa na yi a cikin kunnuwana, a hankali na buɗe idanuwana na sauke su a kan fuskarsa. Ban wani motsa ba balle na tashi daga ginciren da nake a kan kujerar, na sake lumshe idona na rufe kamar ban gano kowa ba.


       "Me ke damunki yau?"


      Ba tare da na buɗe idanuwana ba na ce,


    "Me ka gani"


Sautin ajiyar zuciyarsa kawai na ji a cikin kunnuwana, wacce ta sa na ji kasala ta sauka a jikina. 

        "Ban san me ya sa kika zaɓi ɓata mini rai a matsayin makaminki da za ki riƙa ba! Me ya sa ba kya jin tausayina ne?"


      Buɗe idanuwana na yi tarwai a kansa, kafin na ɗauke ganina daga kan fuskarsa zuwa wani gefen daban. Kaina na dafe saboda ina jin ya mini nauyi sosai, wanda ba na raba ɗaya biyu a kan bashin barcin da na ci ne.  A hankali na yi jarumtar furta,


      "Ka yi haƙuri! Ni ma ban san me ke damuna ba a cikin kwanan nan! Na san dai ba na jin daɗin yanayin kwata-kwata. Wataƙila hakan ya janyo sauyin wasu halayen da kake gani kamar ba daidai ba!"


     Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya rungume hannunsa a ƙirji ya sake jefo mini tambayar, 


"Me ke damunki?"


     "Babu komai!"

      

Abin da na iya faɗa kenan, tare da duba agogon hannuna na ce,

     "Sir! Idan akwai aikin a ba ni, time yana ta gudu kada na yi zaman banza."


    Wani kallo ya bi ni da shi, kamar ya yi magana kuma ya fasa. Juyawa ya yi kawai ya fice, mintuna a tsakani Baba Masinja ya kawo mini wasu takardu, sannan ya sanar da ni akwai customers ɗinmu masu jira na a waje. Kai-tsaye na ba shi umurnin shigo da su ɗaya bayan ɗaya ina karɓar kuɗinsu suna saka hannu. 


    ****

Bayan wata biyu da kwana sha uku, abubuwa da yawa sun faru a tsakanin waɗannan kwanakin. Cikinsu kuwa akwai samun sauƙin Baban Taufiƙ ya koma gidansa tare da amaryarsa Sajida. Sai fitowar Arma gadan-gadan da niyyar aure na cikin ɗan lokaci. Sannan akwai sauyin da na yi wa MD wanda ya so kama jikina, duk da ba ƙaramar wahala nake sha ba a kan azabtar da zuciyata da nake yi. A duk lokacin da na samu kaɗaici ina kuka ba tare da kowa ya sani ba, saboda na daina jin daɗin komai sai dai na yi dariyar yaƙe gudun Umma ta gano ni. Na fara rama har ƙashin wuyana ya fara fitowa, saboda ganin da gaske Umma Arma take so mini fiye da abin da zuciyata ke muradi.

       A ɓangare ɗaya kuma tausayin MD ya mamaye mini zuciya, duk da yana ƙoƙarin ɓoye mini damuwarsa, tun a lokacin da ya gama gano da gaske na sauya masa.  Shi ma ya daina shige mini, kuma ya daina saka ni yin abu dole. Sai dai hakan ba ƙaramin taɓa masa kuzari ya yi ba, domin ko aikin ma watarana ba ya fitowa. Wani lokaci na yi ta baza idon ganin shi, amma shiru kamar an shuka dusa na ji kamar na yi ihu. Sai saƙon da yake aiko mini a waya kullum safiya tamkar ibada. 

      

      'Ya kike? Fatan kina lafiya.'


      Amma duk da hakan, amsata gare shi ba ta wuce, 'fine' wani lokaci kuma ya dame ni da godiyar da ban san wani abin alherin da na yi masa ba. Ko wasu kalaman da ban san ta ina zan kamo fassararsu ba. Wani lokaci na share wani lokaci kuma na yi masa daidai da kalar zaurancen da yake yi mini mai wuyar fahimta. 

      Matarsa ma tun daga lokacin ban sake jin ɗuriyarta ba. Sai a bakin Baba Masinja da na ji yana tambayarsa ya jikinta. Bayan ya wuce na tambaye shi waye babu lafiya, ya ce da ni,

      "Matar Maigida ce ta yi hatsari, ba dai ba ki sani ba har wannan lokacin?"


    Na yi masa fuskar jimama sannan na ce, "Ai na ɗauka ta ji sauƙi, ashe har yanzu jikin?"


     "Karaya ce a ƙafa fa! Kin san irinta sai an sha fama kafin a wartsake! Ga shi ita abin ya zo da tsautsayi, sau biyu ana gyara ƙafar. An yi na asibiti bai yi ba dole sai da aka yi mata ɗorin gida, amma na ji ya ce yanzu an yi dace ƙafar har ta fara ƙanƙarewa."


     "Allah Sarki! Ubangiji ya bi da lafiya!"


Ya ce, "Amin."


    Daga haka na bar wurin zuciyata cike da tunanin ƙaryar da ta shirga wa mutane. Gudun asirinta ya tonu, kuma ya gano inda ta je aka yi mata aika-aikar. Murmushi mai sauti na yi a daidai lokacin da nake ƙoƙarin shiga adaidaitasahun da za ta kai ni gida.

      Mun fara tafiya kenan wayata ta fara ɓurarin neman agaji, na yi hanzarin ɗauka saboda ganin Sajida ce,


      "Aunty ki zo ga mu Uduth Haidar ne babu lafiya!"


    "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


 Iya abin da na faɗa kenan, saboda duk abin da ya sa Sajida nemana a kan matsalar Haidar ta ɓaci. Domin tun da suka koma unguwar ragamar komai nasa ta koma hannunta. Barci kawai ke sa ya koma gidansu, saboda dokar da Mukhtar ya gindaya mata kafin ya amince ta ja ragamarsa. Kuma tun lokacin hankalina ya kwanta a kansa, domin jefi-jefi tana haɗa ni da shi muna waya. Kuma a yanayin da nake jin shi cikin farinciki tamkar ina tare da shi. Hakan ya sa zuciyata ta samu natsuwa na daina fargaban abin da zai faru da shi mara daɗi. 


     Jikina yana rawa na ce da mai adaidaitasahun ya kai ni Asibitin Uduth. Cikin tashin hankali na biya shi kuɗinsa jikina yana rawa na isa emergencyn, inda Sajida ta sanar da ni Haidar yana can. Ganin su ƙofar ɗakin tana ta kuka, gabana ya ƙire ya faɗi. Bakina yana rawa na isa wurinta ina tambayar,


      "Me ya same shi?"





 


Hmmmmm! Wata sabuwar gwarama😪😢






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA TAKWAS.*


       Kallon da na ga Sajida tana yi wa Mukhtar da Barira; ya sa hankalina ya ƙara tashi. Saboda ta kasa ba ni amsa sai kallon su take yi ɗaya bayan ɗaya, kamar mai jin tsoron abin da za ta faɗa. A ƙarshe rungume ni ta yi tare da fashewa da wani mahaukcin kukan da ya sa na saki guntun fitari. Saboda jikina ya ba ni Haidar ya mutu shi ya sa take ɓoye mini.

       Cikin sarƙewar murya da ta numfashi, na ƙara jefo mata wata tambayar jikina yana tsima.


     "Wai..wai.. me samu Haidar ɗin..? Ko ya mutu shi ne.. kike gudun faɗa mini?"


     "Haidar bai mutu ba Aunty! Amma likitoci sun tabbatar mana da ya samu gagarumar matsala! Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


    Abin da ta faɗa kenan cikin kuka tare da ɗaga murya. Tashin hankalin da nake ciki ya sa ban san lokacin da na ture ta daga jikina ba. Aguje na faɗa ɗakin tamkar wata zararriya ina ihun kiran sunan Haidar. Kafin na isa inda idona ya hango mini shi a cikin oxegen; wasu nurse's suka rirriƙe ni tare da kokawar fitar da ni daga ɗakin ta ƙarfi. 

      Cikin ƙaraji na dinga nuna gadon da yake kwance da hannuna ina faɗin,

      "Ku bar ni na ga ɗana! Don Allah kada ku fitar da ni ya mutu ya bar ni. Wayyo! Haidar kada ka mutu don Allah! Wallahi ina son ka! Kada ka bar ni!"

      Na ƙare maganar a ƙofar ɗakin tare da durƙushewa ƙasa ina borin kuka. Saboda sun mini taro sun fito da ni waje sun ƙargame ƙofar ɗakinsu. Tamkar mahaukaciya sabon kamu na zabura, bazama na yi da gudu na zagaya ta bayan ɗakin. Inda ban sha doguwar tafiya ba na ja na tsaya bakin tagar da ke sautinsa, inda ya yi daidai gadon da yake kwance. 

      Ihu na fara fasawa, kafin na toshe bakina cikin sauri, saboda tsoron su ji Ni su ƙara hana ni ganin shi. Domin ganin shi a halin da yake ciki; ya ƙara firgita ni matuƙa, kuma hankalina ya ƙara tashi. Saboda hango bakinsa cikin na'urar zuƙo numfashi. Idonsa a rufe numfashin shi yana fita a wahalce, kasa haƙuri na yi na ƙara ɗaga murya ina faɗin,

   

     "Haidar kada ka mutu ka bar ni don Allah!"


Kamar ƙiftawar ido na ji an ba ƙofar 'karaf!' suka rufe tagarsu. Daga nan inda nake ina jiyo sautin faɗan da Likitan yake yi, saboda ganin da ya yi mini a bakin tagar da ihun da nake yi musu. 

      Mintuna tsakani ina nan duƙe wurin ina kuka, na hango lebarorin Asibitin sun nufo ni gadan-gadan, kamar waɗanda za su dake ni, kowanensu fuska babu annuri. Miƙewa na yi a fusace tamkar zakanya ina nuna su da hannu, bakina yana rawa na ce da su,

     "Kada wanda ya taɓa ni! Ku bar ni da abin da nake ji, na ganin yarona a cikin wannan mummunan hali. Idan kuma babu imani a ƙirazzanku!; To ku taɓa ni na ɗauki mummunan mataki a kanku gabaɗaya wallahi!"


     Turus suka yi suna kallo na tamkar an dasa su, yayin da wasu daga cikinsu suke ta aiko mini da mugun kallo tare da harara. Wata farar dattijuwa a cikinsu;  ta matso kusa da ni cikin sanyin murya ta ce,

     "Ki nemi wuri ki zauna, kuma ki yi masa addu'a, in Sha Allah zai samu lafiya. Sannan ki yi haƙuri ki zo mu je ki zauna inda ba za ki takura sauran marasa lafiyar ba." 


    Kamar wata doluwa haka na bi bayanta Sajida tana faman faɗin,


     "Ki yi haƙuri Aunty zai samu lafiya"


     Ina jin abin da wata guntuwar mace a cikin lebarorin ta faɗa, na ja na tsaya ina ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa. Domin a lokaci ɗaya na gama aune ta a sikilen fahimtar da na yi mata. Saboda bilicin ya gama heƙe mata fuska tas har ta fara glass. Bayan faɗin fuskar da take ɗauke da ita da bazajjen hancin da ya ƙara wa fuskarta faɗi. 


      "Wannan ai rashin tawakkali ne! Don ihunta ba zai hana yaron mutuwa ba idan Allah ya ƙaddara!"


     A fusace na wurga mata wata arniyar harara, raina yana tafasa na ce da ita,

      "Tun da aikin sharar asibiti bai hana uwarki mutuwa ba; ta ya ya ni ma zan hana ɗana idan kwanansa ya ƙare!"


     Ina ƙare maganar na yi gaba, alamun ko a jikina abin da na faɗa. Ina jin wata a cikinsu tana cewa, 

     "Don Allah Malama ki yi haƙuri! Ke kuma Inno ki san abin da kike faɗa, don ba kowa zai juri halinki ba!"


     "Daga 'yar wannan maganar za ta zagi uwata kuna ji kuma har ku ga laifina? To na rantse da girman Allah sai na faɗi abin da ke bakina! Mutuwa a kanta aka fara ne da za ta ɗaga wa mutane hankali? Ko kuma a kanta za a daina? Da za a nuna mata gaskiya ta ce za ta yi wa mutane ɗibar albarka! Billahillazi na fi ta rashin kunya da ciwon baki..."


     "Daman ta ya zan haɗa kaina da wacce take kwanan asibiti? Ana ba ta ɗari biyu, ɗari uku tana raya dare!" 

Na ƙare maganar ina ci gaba da tafiya ba tare da na waigo ba.


     "Kutumar bala'i! Ke ni za ki yi wa sharri? To wallahi sai na ga uban da ya ɗaura wa uwarki aure a garin nan!"


     Ta yo kaina da gudu za ta dake ni, aka rirriƙe ta ana ba ta haƙuri. Sai faman huci take yi tana kallo na kamar ta shaƙo wuyana. Kallon banza na wurga mata sannan na yi tsaki na kawar da kaina gefe, tare da neman wurin zama na zauna a kan wani dakali. 

      Da ƙyar aka ja ta suka  bar wurin, aka bar ni da dattijuwar da tun farko ta zo mini a mutunce. Sannan Sajida da ke ta sharar ƙwalla har lokacin, idanuwanta sun yi jawur tamkar wacce aka watsa wa barkono a cikinsu.

 

   Wayata na ciro a jaka jikina yana rawa na danna wa Umma kira. Tana ɗauka na ji wani kuka ya zo mini mai ƙarfi, a cikin muryar kukan na sanar da ita halin da Haidar yake ciki. Cikin tashin hankalin da muryarta ta tona, a ruɗe ta ce da ni,


     "Me ya same shi?"


Na goge hawayen da ke ta mini zarya a kan fuska na ce,

      "Ban sani ba Umma! Kuma sun hana ni zuwa wurin shi balle na gan shi, sai ta window na hango shi yana ta zuƙar numfashi a wahale! Don Allah ki zo, ko za su bari na gan shi tun kafin ya mutu ya bar n..."

       Katse kiran na yi saboda kukan da ya ci ƙarfina, dattijuwar Leburar ta kalle ni da kyau ta ce, 

     "Ki yi haƙuri! In shan Allah zai samu lafiya! Bari na je kada a yi nema na. Ki zauna a nan don Allah kada ki koma Doctor ya ga laifin mu!"


    Kai kawai na ɗaga mata, sannan na kalli Sajida cikin ƙarfin hali na ce da ita,

      "Ki daina kukan nan! Saboda babu abin da muka iya yi, sai abin da Allah ya yi mana. Zo mu je ki raka ni na yi sallah kafin su Umma su zo!"


     Tare muka miƙe jiri yana kwasa ta muka bar wurin. Daga can nesa na hango Mukhtar tsaye jikin wani ice, Barira zaune ƙasa ta yi tagumi. Tun da na yi musu kallo ɗaya na ɗauke kaina, saboda takaicin su da fargaban halin da Haidar zai kasance, tsakanin mutuwa ko rayuwa. 

      Bayan na gama sallar na ɓata lokaci ina yi masa addu'ar samun sauƙi, duk da har lokacin ban san me ke damunsa ba, balle dalilin ciwonsa. Sai da na shafa addu'ar, Sajida ta zuƙe majinar kuka ta ce da ni,

       "Tun kwana biyu da suka wuce, na ga wasu ƙuraje sun fito masa a baki. Da na tambaye shi ko ya yi ciwo ban sani ba,  ya ce da ni shi ma haka kawai ya gan su sun fito masa. Na nemo amplclox da vitamin c na shi ya sha, amma ban ga sun warke ba. A yau Monday na yi niyyar zan kawo shi asibitin nan a duba mana bakin. Kawai asubar farin sai ga Abbansa ya zo yana bubbuga mana gida, wai Haidar babu lafiya. Ko da na je gidan na gan shi riƙe da ciki yana ta murƙususu, sannan jikinsa ya yi zafi sosai kamar an kara masa wuta."


       "Hmmmm!"


 Ajiyar zuciyar da na sauke kenan, saboda abin da nake ji a raina dangane da ciwon nasa; ina ji kamar na yi ta zunduma ihu. Sajida ta ƙara goge hawayen fuskarta ta ɗora bayanin da cewa,


     "Da ƙyar muka ga safiya ta waye, saboda barcin da ya kwashe shi bayan an ba shi paracetamol ya sha. Bai tashi daga barcin ba har ƙarfe takwas na safe, ina gidan ya farka da ihu, riƙe da cikinsa yana ta kuka. Ganin idonsa suna kakkafewa ya sa muka kwaso shi jiki yana rawa muka yi Asibitin nan. Tun muna ganin abin da sauƙi har ya yi tsananin da dole na nemo ki. Gudun wani abu ya faru ba tare da an sanar da ke ba..."

      Ta fashe da wani sabon kukan da ya ƙara dagula mini lisaafi, kiran Umma da na gani ya sa na miƙe cikin sauri na ɗauki wayar, kakkaɓe ɗankwalina da na shimfiɗa na yi sallah da shi nake yi, ina kuma sauraron abin da Umma take faɗa. 


    "Kina ina? Ki zo likita yana neman ki!" 


    Ƙirjina ya buga cikin sauri na yi gaba ina cewa Sajida ta zo mu je ana son gani na. Sauri-sauri gudu-gudu muka isa bakin emergencyn, inda na hango Umma da Inna Kulu. Sai Mukhtar da Barira a gefe ɗaya tare da su Yaya Maimuna da sauran wasu danginsa. Idona a kan Umma kafin na yi magana wata nurse ta buɗe ƙofar ɗakin tana faɗin,

     "Iyayen Haidar Mukhtar su zo likita yana buƙatar ganin su!" 


    Da sauri na bi ta baya ƙirjina yana dakan luguden tara-tara, saboda jikina ya ba ni kamar Haidar ya rasu. Ni na fara shiga Ofishin, sannan Mukhtar ya turo ƙofar ya shigo. Wuri likitan ya nuna mini na zauna, sannan ya ɗauki lokaci yana nazartar file ɗin da ke gaban shi.

       Mintuna a tsakani ya cire gilashin fuskarsa ya kalle mu ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce,


    "A binciken farko da muka yi, mun gano ɗanku yana ɗauke da cutar Human papilloma virus 

(HPV) da Pelvic infection diseases (PID) tare da Toilet Infection. Kuma dukansu sun samu asali ne daga; tsotsar sperm ɗin da yake yi a bakinsa.


    "Sperm kuma!!!?"









To fa!😲








D. AUTA CE✍️


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



_*Ku yi haƙuri, ku ƙara haƙuri! Wannan abin da ya faru ga Haidar gaske ne zahiri an yi hakan. Kuma na saka matsalar ne saboda Iyaye su hankalta da ire-iren matsalar. Domin su ƙara ɗaukar wasu matakan tsaro ga tarbiyyar 'ya'yansu. Sannan a ƙarshe a bi da addu'a Allah ya ƙara kare mana abin da ba ma gani balle mu tsawatar. Fatan alheri gare ku duka, luv u all fans😘.*_



*LAMBA SHA TARA.*



      "E, tabbas babu makawa ya tsotsi sperm a bakinsa. Kuma sanadin hakan ya haɗu da waɗannan matsalolin. Duk da a zahiri  akwai wani Acid da ke fita a gaban mace lokacin sha'awa. Wanda babu wata hanya da ake samun shi face ta wannan hanyar. Kuma yana da kyau sosai a jikin mutum, domin yana ƙara lafiya da kuzari, har ma da kyawun fatar mai shan irin wannan Acid. Sannan akwai Vitamin K a gaban mace. shi kuma yana ƙara ƙarfin ƙashi, da ƙarfin haƙori. Sai Vitamin D. Shi ma kamar misalin Vitamin K. yake a jikin mai tsotsar ruwan gaban mace. Sai kuma Protein shi ma ana samunsa a cikin ruwan da ke fita yayin ƙololuwar jin daɗin mace da tsananin sha'awarta. Haka ma akwai kitse a cikin ruwan duka, don haka banu illa idan an sha, saboda yana gina jikin mutum matuƙa."


Sai da ya ɗan tsahirta, sannan ya nisa kafin ya ɗora bayanin da ya saka jikina mutuwa murus. 

       "Amma za a samu lafiya ne a jikin macen da ba ta ɗauke da waɗannan cutukan; Human papilloma virus 

HPV da Pelvic inflammatory disease. Saboda a cutukan za a samu wasu ruwa mai wari. Shi ma idan bakinsa akwai datti ko ya sha yaji zai iya saka mata wata cutar a yayin tsotsar gaban nata. Kamar yadda zai kwasa haka shi zai manna mata. Saboda ba a Oral sex da wanda yake ɗauke da cutar, domin  fatar da ke cikin bakin mutum, irinta ce a cikin farjin mace. Cutar da take kama fatar gaban mace, tana iya kama fatar bakin mutum. Saboda ita wannan cutar cuta ce wacce ke ɗauke da kwayoyin cutar da suke dangin *viruses.*  Kuma duk cutar *virus* kusan cuta ce da za a ce ba ta da magani har yanzu.  Misali HIV. Virus ne shi ma, shi ya sa ba ta da magani, sannan ita cutar virus, yadda ake maganin su shi ne magance wasu alamomi da ainihin cutar ta haifar.

     HPV ana iya daukar shi ta vigina, waton al'aurar mace, ko anal wajen bayan gida ko ta baki idan an yi oral sex. HPV cuta ce da ke ɗaya daga cikin STI *sexual transmitted infection.* Kuma Akwai low risk da high risk. Low risk din bai cika haifar da matsala sosai ba, sai dai yana kawo wrats on skin, throat mouth, vigina, etc.  High risk din kuma shi ne ke iya haifar da cancer, idan ya zama ya jima a jiki babu magani. Yana kawo cancer a genital areas e.g cervical cancer, anal cancer, vulva cancer etc. Ita kuma *oropharyngeal cancer* yana taɓa makoshi *throat* ko harshe. Daga cikin alamomin sa akwai *lump on d neck or sore throat* za ki ga kamar kumburi a maƙoshi. Magana ko haɗiyar abu ma yakan zamar wa mutum aiki. Don haka yanzu kun ji bayanin halin da yaronku yake ciki." 


    Amsar da likitan ya ba ni, da bayanan da ya yi cike da tabbaci a kan fuskarsa, sun sa na ji wani abu ya dira kaina yana sauka jikina, tun daga sama har zuwa tafin ƙafata. Nan take wani gumi ya rufe ni, sakamakon zugin da nake jin zuciyata tana yi tamkar ta tsage gida biyu. 

      Wataƙila halin da ya gan ni ciki ne ya sa, ya yi hanzarin faɗin,

      "Ku kwantar da hankalinku! Za a bi abin daki-daki domin mu san ta ina matsalar ta samo asali. Sannan mu yi gaggawar toshe ta, gudun matsalar da ke barazanar faruwa gare shi ta auku!"


    "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


    Ita ce kalmar da na ambata a bakina cikin ƙarfi, saboda numfashina da ke ƙoƙarin ƙwace mini a lokaci ɗaya. Ashe kuka ma wuri yake samu, domin kuwa gabaɗaya ruwan jikina sun ƙafe, balle na samu kuzarin fito da su a cikin kwarmin idona. 


    "Ya aka yi kuka bar yaronku babu kulawa? Me ya sa kuka yi sakacin kula da tarbiyyarsa? Har ya faɗa irin wannan ƙazamin halin da ke yi masa barazana da mutuwa!"

      Kallo na kai a hargitse bisa kan fuskar Mukhtar, wanda yake zaune kamar wani gunki mai siffar mutum-mutumi. Domin ko motsi ya kasa yi balle ya yi magana kamar yadda na yi jarumtar yi. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da goge gumin fuskarsa. Saboda Likitan ya maimaita mana tambayar kamar yadda ya yi a farko. Kasancewar ban san me zan faɗa ba ko da ina iya magana, balle ban san komai a kai ba. Haka ma ba zan iya doguwar magana ba a lokacin, domin ina ji a raina; ina ma mala'ikan mutuwa ya zo ya tafi da ni na huta da jin abin da zai fasa mini ƙirji ya ruguza zuciya...  


    "Ban san ya aka yi hakan ya faru ba, saboda ba na zama gidan idan na fita tun safe sai dare nake dawowa gida na kwanta. Ban san wa ya yi masa hakan ba, ban san ya aka yi abin ya faru da shi ba. Ban sani ba..ban.. sani ba.."


    Ya ƙare maganar cikin karyayyiyar muryar da kiris ya rage ya yi kuka. Amma ko kaɗan bai ba ni tausayi ba, haka ma ban ji ko ɗar a kan muguwar ƙiyayyar da ke ƙara narke mini a zuciya ba. Kallon da nake yi masa ma a idona; mai kama da na neman hanyar makasar shi nake yi a lokacin.

     Ban san lokacin da na miƙe tsaye na kwaɗa masa wani la'anannen mari ba, jikina yana tsuma na sake ɗaga wani na kai masa a ɗaya gefen. Likitan ya yi hanzarin riƙe mini hannun, haushi ya sa na rufe su da duka dukansu, tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu.

     Mugun riƙon da Likitan ya yi wa hannuwana, ya sa na fasa wata ƙara mai sauti na zube ƙasa. Saboda zuciyata da nake jin tana tsagewa tamkar ana yanka mini ita da reza. Na koma kokawa da numfashina da ke ta fisga ina ƙoƙarin magana dafe da zuciyar amma na kasa furta komai.

       Daga hakan ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bayan na farka na gan ni kan gadon asibiti da ruwa maƙale a hannuna. Kaina na ɗaga ina ƙare wa fanka kallo, wacce ke ta juyawa da gudu tana filfila fukafukanta da ke bayar da iska ta ko'ina. Tuno abin da yake faruwa ya sa na zabura tare da kiran sunan Haidar a lokaci ɗaya. 

     Muryar Ummata na ji tana salati, tare da wasu muryoyin da ban san masu su ba. Suka yi taron dangi wurin mayar da ni kan gadon suka kwantar. Sannan aka gyara mini allurar da ta kauce wa jijiya tana ƙoƙarin haɗa mini ƙoƙon jini. Kallo na bi Umma da shi ina yunƙurin furta abin da ke bakina, amma kuma ina jin ya mini nauyin da dole na koma kokawa da muƙamuƙaina. Domin su ba ni haɗin kai na ɗaga bakina na furta abin da zuciyata ke muradin jin gaskiyarsa a bakin Ummata.

     Cikin nasara na gagari danƙon da muƙamuƙina ya yi wa bakina, domin kuwa na samu damar rabe haƙorana ɗaya sama ɗaya ƙasa, daga ɗaurin huhun goron da aka yi musu tamkar an katse mini jijiyoyin bakin duka. Ta yadda na ɗaga harshena cikin wata raunanniyar muryar na ce da ita,


       "Haidar ya mutu ko?"


"Bai mutu ba! Amma yana buƙatar addu'arki. Domin ban ga amfanin ɓoye miki abin da za ki ji daga baya ba. Ki yi hanzarin ƙarfafa kanki, saboda mu yaƙi bala'in da yake ƙoƙarin tunkaro mu ta ƙarfi! Domin Mukhtar da matarsa sun gama kwashe kayansu daga gaban ma'aiki. Kuma har abada, ba za mu rama abin da suka yi mana ba. Sai dai idan mun je lahira; Allah ya yi musu hukunci daidai da abin da suka aikata mana."


     "Me ya faru? A cikinsu waye da alhakin halaka mini rayuwar yarona?"


   Umma ta miƙe cikin sauri ta fice ɗakin, wata nurse ta matso kusa da ni tana faɗin,

      "Ki yi haƙuri! In Sha Allah yaronki zai samu lafiya!"

      Kawar da kaina kawai na yi gefe, zuciyata cike da ɗokin son jin wane ne ya cutar mini da Haidar a cikinsu. Domin dukansu babu wanda ba zai iya aikata wannan rashin imanin ba. Duk da wani gefe na zuciyata yana sanar da ni Barira ce ba Mukhtar ba. Amma kuma ina ji a raina ko da ita ce; to su biyun suka aikata mini laifin, kuma su biyu zan yaƙa saboda shi aka damƙa wa yarona ba ita ba.

      Na daɗe ina ta jujjuya maganganun a cikin zuciyata, inda nake ta hasko abin da aka yi wa Haidar a idona tamkar a gabana ake yi. Babu shiri na rintse idanuwana cikin ƙarfi na furta,


   "No! No! No wallahi! Haidar ɗina ba zai aikata wannan mummunan aikin b.... Innalillahi wa inna ilaihirraji'un...!" 


    Muryar da na ji a tsakiyar kaina, ta sa na yi hanzarin kawar da kaina, tare da fashewa da wani sabon kukan da ban san dalilin yin shi a lokacin ba. Gaisawar da na ji yana yi da Inna Kulu faram-faram cikin mutunta juna, hakan ya sa na yi jarumtar saka ɗayan hannuna na goge gefen fuskata, wanda ke ta tsiyayar da ruwan hawaye daga kwarmin idona zuwa shimfiɗar filon da nake kwance.


     Ƙamshinsa, ya sa na ji wani zirr a jikina. Duk da ina ji a raina ba zan iya juyo da kai na kalle shi ba; amma tabbas na ji daɗin zuwansa, kuma na yi farinciki da jin motsinsa a kusa da ni. 


   "Ya jikinki?" 


Ita ce tambayar da na ji ya yi, wacce nake da tabbacin da ni yake ba da kowa ba. Amma ban iya amsawa ba balle na juya na kalle shi, saboda kunyar abin da Haidar ya aikata nake ji, wanda nake da tabbacin ya ji komai shi ya sa ya zo duba na. 

      

    "Zaituna an zo ganin ki, ko barci kika koma?"


   Zancen Inna Kulu kenan a saman kaina, bayan ta leƙo fuskata domin ta gani da gaske idan baccin nake yi. Haɗa idon da muka yi ya sa ta yi saurin kama ni da nufin tayar da ni zaune. 

    Ban ba ta kunya ba na miƙe kamar yadda take muradi. Sai da ta gyara mini zama na daidaita, sannan ta saita mini hannuna ta yadda ruwan za su shiga jikina da kyau. Ta shiga jera mini sannu kafin ta ce,


    "Bari na haɗa miki shayi ko babu yawa ki kurɓa. Saboda yunwar kwana biyu ba ƙanwar uwar kowa ba ce! Don ma kina zuƙar ruwan Bature; da ba a yi kiɗan da rawar ba!"


    'Kwana biyu?'



       Tambayar da na jefi kaina da ita kenan a cikin zuciya. Saboda ban san komai ba tun daga lokacin da na faɗi a ofishin Likitan, hannuna riƙe da zuciyata da ke barazanar watsewa. 


     "Karɓi ki sha! Ko na ba ki da kaina!"


   Inna Kulu ta dawo da ni daga duniyar nazarin da na lula. Idona a kan kofin  sannan na ce,

     "Ina so na wanke bakina, ba ya mini daɗi ɗacinsa nake ji!" 


    Ta yi mini brush da kanta, sannan na kuskure bakina na karɓi kofin da hannuna ɗaya ina ƙoƙarin ajiyewa gefena, cikin sauri MD ya tare kofin da ke ƙoƙarin faɗowa ƙasa har shayin ya fara zuba. 


     "Oh Allah! Sannu kin ji! Ubangiji Allah ya ba ki lafiyar ki Zaituna."


Inna Kulu ta faɗa cikin jimamin da ya sa ta riƙe haɓa tana kallon mu ni da shi. 


    "Amin." Ya ce da ita, kafin cikin sanyin murya ta ce da shi,


    "Don Allah ka ba ta shayin, ko za a dace ta sha kafin na je ganin Haidar na dawo. Don Habi tana can wurinsa kuma na san yanzu ya tashi daga barcin da na baro yana yi."


     Kansa kawai ya ɗaga mata yana murmushi mai sauti, wanda na saci kallon shi ta gefen ido kafin na kawar da kaina. Kujerar da ke gaban gadon ya janyo, ya ajiye ta daf da ni sannan ya zauna riƙe da kofin a hannunsa. 


    "Zaituna!"


Da sauri na kai kallona a kan fuskarsa, saboda mamakin jin sunana raɗau a bakinsa. Wani lum ya yi da idonsa, babu shiri na ɗauke ƙwayar idona da ke cikin na shi idon. Kawar da kaina gefe na yi saboda ba zan iya jurar haɗuwar idanuwanmu wuri ɗaya ba.

 

      "Karɓi ki sha kada ya huce!"


    Ya yi maganar cikin wani slow voice tamkar mai yin raɗa, kasa musawa na yi kai-tsaye na karɓi kofin na kai bakina. Ɗan kurɓa na yi a hankali sannan na nemi ajiye shi inda ya so faɗuwa farko, da hanzari ya kai hannunsa ya damƙe kofin da hannuna duka a wuri ɗaya. 


    'Yammm!' Na ji a jikina, ta yadda gabaɗaya ya hau rawa tamkar an jona mini shocking. Murmushi ya yi mai sauti, sannan ya zare kofin daga hannuna ya miƙe. Mamakin abin da zai yi ya sa na bi shi da kallo, ai kuwa babu zato ya tallafo kaina ya ɗora mini kofin a baki. Idona a kansa na fara ƙoƙarin ture kofin tare da datse bakina, kai ya fara girgizawa alamun kada na ƙi sha. 

       Muryar Umma da na jiyo ta sa na yi hanzarin zuƙe shayin ina mayar da numfashi a wahale. Saboda tsoro da fargaban abin da zai je ya dawo idan ta gan ni da shi a yadda muke. Bai koma ya zauna ba har ta iso jikin gadon tana cewa,


      "Idan ruwan sun ƙare, za ki je ki yi wanka. Kwana biyu kina fama yana da kyau ɗan watsa ruwa."


     A ladafce ya duƙa har ƙasa yana gaishe ta, sannan ya miƙe yana nuna mata ledodin da ke ajiye gefen gadon. Waɗanda ni ma ban lura da su ba har sai da ya nuna. Kallon kayan ta yi babu yabo babu fallasa, sannan cikin sauri ta ce da shi,

      "Da ma ba ka wahalar da kanka ba ai, saboda ta ji sauƙi. Kuma in Sha Allah da wuri za a sallame su duka ba sai an yi ta ɗawainiya ba." 


    "Babu komai Umma yi yi wa kai ne, fatan mu kawai Allah ya ba su lafiya."


     "Amin-amin mun gode sosai Allah ya saka da alheri."


    Cewar Umma kenan tana ƙoƙarin shigowa cikin gadon bayan ya fice. 

       Idona a kanta, ba tare da na nuna na gano canjin yanayinta ba na ce, 

       "Ya jikin Haidar ɗin? Ina so na gan shi Umma. Kuma don Allah ki sanar da ni a cikin Mukhtar da Barira waye ya yi masa wannan aika-aikar?"


     Zama ta yi a kan kujerar da MD ya tashi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,

    " Ko ba a faɗa ba ai kin san wannan la'ananniyar yarinyar ce! Ɗiyar tsiya haihuwar tsakiyar rana. Wacce da haihuwarta duniya gara ɓarin cikinta. Na rantse da girman Allah! Ko kashe ta na ga an yi gaban idanuwana ba zan taɓa daina jin tsanar ta a raina ba! Ke shi kan shi baƙin ɗan iskan lusarin mijin nata har duniya ta jingine; ba zan daina yi masa tofin Allah-tsine ba! Saboda duk abin da aka yi musu a duniyar nan; ba zai kai rabin abin da suka aikata ba! Don duk lalacewar matarsa ya fi ta laifi, saboda da ya tsaya ya kula da amanar da Allah ya ba shi; da hakan bai faru ba. Duk da ba a isa a raba bawa da ƙaddararsa ba, amma wannan siyenta aka yi da sakaci da rashin sa ido a kan wasu abubuwan da ke faruwa a cikin gida!"


    "To yanzu a wane hali Haidar ɗin yake?"


    "Da sauƙi za a ce, domin akwai bambancin yanzu da ranar da abin ya faru. Duk da ƙurajen da ke bakinsa sun hana shi magana, amma yana kallon mu da ido kuma yana gane komai. Abin zuƙar numfashin da aka saka masa ma yanzu an cire yana numfashin shi babu laifi."


     "Alhmdulillah! Ko iya haka aka bar mini shi; Allah na gode maka!"


    Abin da na iya furtawa kenan, kafin na sulale a hankali na koma na kwanta. Luff na yi kamar mai barci, amma zuciyata tafasa take yi mini tamkar ana dafuwa a cikinta. 

     






    Haƙuri Zaituna😢




Ku yi haƙuri da ni a yan kwanan nan. Laifin ba daga ni ba ne uzuri ne yake riƙe ni.😌




D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA ASHIRIN.*


      Muryar Inna Kulu na ji tana faɗin, 

"Ashe har ya tafi?"


       "Ya tafi!"


Iya amsar da Umma ta ba ta kenan, Inna Kulu ta iso inda nake ta dafa kaina tare da gyara mini zaman filon. Sannan na ji ta ce,


    "Babu abin da za mu ce da yaron nan sai godiya. Domin kuwa tun ranar da abin nan ya faru yake ta zirya asibitin nan. Ni ban ma san wanda ya faɗa masa ba."


      "Ummm! Allah dai ya kyauta, amma wannan binbinin na shi ko kaɗan ba ya burge ni. Sai kashe kuɗinsa yake yi a banza, bayan kuma an nuna masa ba a so ya daina amma ya ƙi"


     Amsar Umma kenan, wacce ta sa na ji wani siririn farinciki ya ɗan tsirga mini. Domin alamu ya nuna zahiri yana tare da ni kowane motsina. Sai dai ni ma na yi mamakin zuwan shi Asibitin. 

      Muryar Sajida na ji tana gaishe da su Umma bayan ta yi sallama. Ya jikina ta tambaye su sannan na ji ta a kusa da ni tana faɗin,

      "Allah ya ba ki lafiya Aunty."


     A raina na ce 'Amin' su Umma ma na ji sun amsa da hakan, kafin Umma ta ce da ita,

 "Zo ki zauna bari na koma wurin Haidar!"


     Bayan ɗan lokaci shiru ya ratsa tsakani, can na ji sauke ajiyar zuciyar Sajida a cikin kunnena kafin ta ce,

      "Inna ga abinci nan! Na zo muku da shi"


    "Haba Sajida! Ke shi kenan ba kya gajiya? Ke kenan ɗawainiya koyaushe?"


    "Babu komai Inna ai yi wa kai ne." 


     "To Allah ya saka miki da alheri, ina maigidan naki? Ko ba tare kuka zo ba?"


     "Amin Ya Allah! Shi ya kawo ni Inna, amma ya tafi wani wuri sai ya dawo zai shigo ku gaisa."


     "To Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Muna godiya sosai da ɗawainiyarku."


 Amin ta faɗa sannan shiru ya ratsa tsakani, kafin na ji Sajida ta ce, "Wai ni kam Inna har yanzu muguwar matar can ba ta amsa laifinta ba?"

      "Ina fa! Ta kafe kai da fata a kan ita ba ta san komai a kai ba. Kuma shi kan shi Kawun naki ya goya mata baya, don ya ce bai amince da za ta yi wa Haidar hakan ba. Asali ma ganin yake yi a waje ne aka yi masa abin ba cikin gidansa ba!"


     "Lalle ma Abban su Haidar! Ban san me ya sa Barira ba ta laifi a wurinsa ba! Yanzu duk wannan ta'asar da aka aikata wa ɗansa bai gani ba; sai goya mata baya yake yi yana ƙoƙarin kare ta? To Allah ya kyauta kawai za a ce! Amma wallahi ni dai na zargi ita ce da wannan zaluncin, kamar yadda Umma ta yi hasashe. Don Allah ku ce a ci gaba da hora shegiya, har sai ta ji wuya ta yi bayanin komai da kanta duniya ta ji. Don wallahi da za a bar ni ni kaina; sai na kusa kashe ta tsinanniya. Saboda Haidar ba ya zuwa ko'ina unguwar nan sai wurina, kuma ban da makarantar boko da Islamiyarsu da ke cikin unguwar; babu inda yake zuwa. Domin da an taso yana wurina sai an kira magrib sannan na tura shi masallaci. Kuma da ya dawo gidan na ba shi abinci ya ci yake komawa gidansu, sai kuma da safe ya idan zai je makaranta ya biyo. Sannan a ɗan zaman da na yi unguwar; na ga yadda 'yan iskan ƙawayenta suke zirya gidan. Domin duk aka zo yi mana barka da arziƙi na rako mutane; ina hango wasu za su shiga gidan ko sun fito. Ko kuma wani lokaci na gan ta bakin ƙofar gidan, tana hira da ƙawayenta har da  shewa. Kuma wallahi ya sha faɗa mini ba ya son kwana gidan tsoro ake ba shi. Idan na tambaye shi wa ke ba shi tsoro ya ce shi ma bai sani ba, na ce ya yi ta addu'a idan zai kwanta babu abin da zai same shi."


     "Hmmmm! Akwai Allah ai! Don tun a nan duniya sai ta girbi abin da ta shuka, kafin a je lahira ta iske sakamakon laifinta..."


    Sallamar Amina da na jiyo, ya sa na yi hanzarin buɗe idona. Babu shiri na ji wani kuka ya zo mini na yi hanzarin danne shi saboda ganin ta tare da wasu abokan aikinmu. Inna Kulu ta tarbe su bayan ta shimfiɗa musu tabarma suka zazzauna. Gaishe- gaishe suka fara yi a tsakaninsu kafin su tambayi jikina, tare da yi mini fatar samun sauƙi. Da ƙyar na iya buɗe bakina na amsa ya jikin da suke yi mini ɗaya bayan ɗaya.

     Zuwan wata nurse ya sa kowa ya mayar da hankalinsa a kanta, saboda zare mini ruwan da take ƙoƙarin yi cikin zafin nama. Ta ce idan akwai abin da zan yi na je na yi kafin a ƙara jona mini wasu ruwan. Ƙoƙarin saukowa daga kan gadon na fara yi, saboda zuciyata cike take da son ganin Haidar. Inna Kulu ta kama ni na sauko tare da tsayuwa a kan ƙafafuna.

      Jikina ya hau rawa saboda jirin da nake ji yana kwasa ta. Sajida ta miƙe cikin sauri ta ƙara riƙe ni tana faɗin,

      "Aunty ko ba kya iya tafiya ki zauna? Kada ki je ki faɗi fa!"


    Hannu kawai na ɗaga mata, ina ƙoƙarin tafiya Inna Kulu ta sagala hannuna a wuyanta. Kai-tsaye toilet ɗin da ke cikin ɗakin ta nufa da ni, cikin wata murya na ce da ita,

      "Wurin Haidar zan je Inna!"


"Ki bari ki yi wanka tukunna ko za ki ji ƙarfin jikinki."

       Ban musa mata ba muka shige toilet ɗin, a nan ta bar ni bayan ta kawo mini ruwa masu ɗimi da sabon soso da salubu. Shiru kawai na yi na kasa wankan, sai kukan da na cisga a cikin toilet ɗin tamkar zan shiɗe. Domin na yi fatan mutuwa ta zo mini cikin gaggawa ta tafi da ni a lokacin. Ko da zan rage jin abin da nake ji a cikin zuciyata.

     Wataƙila shirun da Inna Kulu ta ji na yi ne, ya sa ta dawo. Ganin ko ruwan ban taɓa ba, ta fara ƙoƙarin yi mini wankan da kanta. Daman ina tunanin yadda zan yi da kalular da ke hannun haguna,  domin ba na jin zan iya wani aiki da hannun idan ba cire mini ita aka yi ba. 

       Bayan ta ƙare cuɗa mini jikina tass; ta ɗauraye ni ta ko'ina, sannan ta taimaka mini na sake kayan jikina a nan. Riƙo ni ta yi muka fito, a lokacin har abokan aikinmu sun tafi an bar Amina da Sajida. Sai ƙarin Firdausi da na gani wacce ta zo daga baya. 

      Gani na ya sa suka taso suna ta jera mini sannu. Bakin gadon na zauna ina jin jirin yana ɗiba ta har lokacin, Inna ta zubo mini abinci a plate ta dinga ba ni a baki ina ci ina rintse ido. Saboda ɗacin da nake ji, da toshewar da maƙoshina ya yi sai da ƙyar loma ke wucewa.

      Ban ci abincin da yawa ba, na buƙaci ruwa ta ba ni na gora. Waɗanda suke cikin kayan da MD ya kawo mana. Ruwan na ɗan sha masu dama sannan na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Sannu suka dinga jera mini har abincin da na ci ya ɗan faɗa mini. Firdausi ta yi mini ya jiki na ce da sauƙi sannan na miƙe ina cewa da Inna Kulu,

      "Bari na gano Haidar!"


Ta saka hannunta cikin nawa muka nufi ƙuryar ɗakin. Firdausi da Amina suka biyo mu, Sajida ta tsaya tsare mana kayan dubiyar da ke baje cikin ɗan saƙon gadon.

     Tafe muke juwa tana kwasa ta har muka isa ɗan ƙaramin ɗakin. Inda tun kafin mu isa wurin na hango shi kan gado idonsa a rufe alamun barci yake yi. Nan take na ji kuka ya zo mini, babu shiri na toshe bakina tare da zuƙe shi ya koma cikin sauri.

     Kansa na tsaya ina ƙare wa fuskarsa kallo. Domin kuwa gabaɗaya ya sauya, sanadiyar ƙurajen da suka cika masa baki. Sannan ya yi baƙi saɓanin hasken da na san shi da shi, kuma ya rame irin ramar da za a gani tun a kallo ɗaya. 


    "Haka Allah ya mayar mini da kai Haidar...?"


    Kuka ya kufce mini, duk da ban so yin shi ba. Amma na kasa jarumtar da nake ƙoƙarin yi, ko don sassauta wa zuciyata zafin da take yi. Haƙuri suka dinga ba ni kowa da abin da yake faɗa. Saɓanin Ummata da ita ma kukan take yi, duk da ƙarfin zuciyarta da na sani, domin abu ne mawuyaci ya saka Umma kuka sai ta ɓaci.

     Na ɗauki mintuna ina dannar zuciyata domin na tsayar da kukan da nake yi. Hannunsa na riƙe idona a kan fuskarsa, kamar an ba shi umurni ya buɗe idonsa ya sauke su duka a kaina. 

  

    "Ma..ma.."


Abin da ya fara faɗa kenan cikin bakinsa da ƙuraje suka kumbura masa. Isa na yi daf da kansa na duƙa saiti da goshin shi na haɗa kaina da na shi wuri ɗaya ina rera kuka. Hannunsa ɗaya ya sa ya dafa kaina cikin sigar rarrashi. Babu zato na ji ya ce da ni,

       "Mama ki tafi da ni wurinki maciji nake tsoro..."


    Babu shiri na ɗaga kaina ina ƙare masa kallo cike son ƙarin bayani na shanye kukana na ce,

      "Maciji kuma Haidar?"


Kai ya ɗaga mini sannan ya rufe idonsa kamar mai barci. Ganin hakan ya sa na yi hanzarin kiran sunan shi na ce,


    "Haidar faɗa mini! Ina kake ganin macijin?" 


Idonsa a rufe ya ce, "Mama bakina ciwo yake yi, don Allah ki tafi da ni gidanku maciji zai cinye ni..." 

      Kuka ya fara yi, wanda ya yi daidai da zuwan babban Likitan da ke duba shi. Haƙuri ya dinga ba mu tare da umurnin a bar shi ya huta a daina takura masa da magana. Wasu allurori ya yi masa yana kansa har ya koma barci, dole muka yi jugum-jugum kowa da abin da yake kitsawa a ransa. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi tare da ƙura wa fuskar  Haidar kallon, tamkar ita ce za ta ba ni amsar da nake son ji daga bakinsa.


     "Ai yau an yi sa'a ya yi magana, don tun da aka kawo shi bai ce uffan ba. Sai bin mutane da ido kawai yake yi kamar mai neman wani abu." 


     Ganin babu wanda ya ce komai,  hakan ya sa na gano kukan da ke shimfiɗe a kan fuskokinsu duka.

    'Ashe ba ni kaɗai nake kukan ba har su yi suke yi.' 

      Zancen zucin da na yi kenan domin ban yi zaton ganin kukansu ba. Bayan Likitan ya ƙare da shi ya waigo ya kalle ni yana 'yar dariya ya ce,


    "Ya jikin naki ke?"


"Da sauƙi!"


Iya abin da na ce da shi kenan, ina goge fuskata da ta gama jiƙewa da hawaye. Cikin sigar kwantar da hankali ya ce da mu,

     "Ku yi haƙuri, in Sha Allah zai samu sauƙi cikin kwanan nan! Saboda magungunan da muke ɗora shi a kansu. Za su taimaka masa sosai wurin toshe cutar da ke jikinsa. Kuma idan an yi nasarar kashe ta, zai samu lafiyar har mugun ciwon da ake tsoro zai bar shi. Ku dai ci gaba da yi masa addu'a, da yardar Allah sauƙin zai samu."


 "Allah ya amince.."


 "Ubangiji ya shiga lamarin.."


 "Haka muke so ai, Allah ya zama gatan shi da mu bakiɗaya."


"Allah ya tayar da shi cikin 'yan'uwan shi."


Addu'o'in da suke yi masa kenan, kowa da kalar ta shi. Ni da Likitan muna ta faman faɗin, 'Amin-amin' 

     Kafin ya wuce ya bar mu a nan yana duba sauran marasa lafiyar da ke kwance cikin ɗakin. Ni kam sai juya batun maciji nake yi a raina, saboda ban gano inda zancensa ya dosa ba. Amma na sa a raina duk yadda aka yi, akwai abin da yake faruwa da shi, wanda ake ba shi tsoro da macijin domin a firgita shi.


     'Shin ko dai da shi ne ake saka shi yin abin da ake so, domin a samu ya aikata?'

 

   




🙆🏻‍♀️da an boni ko😱






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*ASHIRIN DA ƊAYA.*


      Luuu! Na yi zan faɗi, Umma da ke kusa da ni ta yi hanzarin saka ni jikinta. Su ma suka taso suka rirriƙe ni aka zaunar da ni kan kujera, tare da jera mini sannu. Amma na kasa amsawa sai bin su kawai nake yi da ido, tamkar wata sabuwar 'yar maye.


     "Haƙuri za ki yi fa! Don dole sai kin ƙarfafa zuciyarki. Saboda cuta ce an riga an yi mana ita, kuma babu halin dawo da hannun agogo baya. Da kotun duniya ma ba ta isa raba mu da shi ba, balle har wannan azal ta faɗa bisa kansa..."


    Zancen Umma kenan, cikin karyayyiyar muryar,  a ƙoƙarinta na son ɗora ni kan dakalin jarumtar.  Domin kawai na shanye damuwar, amma ta kasa juriyar ɓoye tata a fili, ta ƙarashe maganar tare da fashewa da wani sabon kuka wiwi. Ganin hakan ni ma na buɗe nawa sabon shafi, cikin wani shaƙaƙƙen sautin mara dadin sauraro. Wanda nake jin zuciyata tana bugawa da sauri da sauri, cike da mugun zugin da take yi mini tamkar tana darewa.


     "Don Allah Umma ku yi haƙuri..."

    "Zaituna ki daina kukan nan, kin san ba lafiya ta ishe ki ba."


     Zancen Firdausi kenan da Inna Kulu, saboda Amina ma taya mu kukan take yi. 

       "Tashi mu je ki kwanta, zamanki a nan zai ƙara gurgunta 'yar lafiyar da muke ganin kin samu."

       Inna Kulu ta yi maganar tare da kama ni iya ƙarfinta na miƙe. Jikinta ta saka ni cike da ƙarfin hali muka bar wurin zuwa gadon da aka kwantar da ni. Amina ta biyo mu aka bar Firdausi tana bai wa Umma baki a kan ta daina kukan da take yi.

      Shiru na yi rufe da ido, ina sauraron mugun gudun famfalaƙin da zuciyata ke yi, babu ƙaƙƙautawa balle sassauci. Kuma a hakan nake sauraron maganganun da Inna Kulu take faɗa, tare da Amina. 


      "Wannan masifa har ina?" 


      Cewar Inna Kulu, cikin wani amo mai nuna tsantsar damuwar da take ciki. Amina cikin kuka ta ce,

     "Inna don Allah kada a bar matsiyaciyar matar nan ta ci bulus. Tun da ta ƙi faɗi a saka mata hular kwano, ko da bala'i sai ta yi bayanin duk abin da ta san ta aikata masa. Amma idan ba haka ba, da wuya ta faɗa kai-tsaye, tun da ta san ba su shuka masa gaskiya ba."

      

    "Waton abin akwai sarƙaƙiya a cikinsa, saboda shi ɗan iskan mijin ya ce matarsa ba za ta aikata ba. Sannan shi an tabbatar ban da makaranta babu inda yake zuwa, to a makarantar ake saka shi, ko a hanyar gida zuwa makarantar?"


     "Ni fa wallahi Inna su biyu nake zargi, shi ko matarsa..."


      "Ba na zaton shi ne Amina, don duk lalacewar shi; ba zai aikata wa ɗan cikinsa hakan ba. Duk da dai, sanin gaibu sai Lillahi! Wanda ba a zaton zai yi abu; idan aka tsananta bincike za a same shi da hannu dumu-dumu a ciki. Allah dai ya ƙara kare mu da sharrin wannan lokaci."


       "Amin Inna! Amma kam an dai ga mutum. Sanin abin da ke zuciyarsa kuma sai Allah!"

       "Hmmmmm!" Sautin ajiyar zuciyar da na sauke kenan da ƙarfi, saboda zantukansu duka ba sa mini daɗin ji. In da hali na fi so a bar ni ni kaɗai na yi jinyar zuciyata. 

      Hakan ya sa na yi farincikin ganin nurse ɗin da za ta mayar mini da ruwa. Bayan ta gama saƙala mini gorar ruwan, na kalle ta da rinannun idanuwana na ce,


     "Don Allah ki mini allurar barci, ba na son jin motsin komai a kusa da ni."


      Murmushi kawai ta yi mini, sannan ta ce da ni,

      "Daman yanzu za ki yi barci, saboda zuciyarki tana buƙatar hutu sosai."


    Rufe idona kawai na yi, cike da fatan barcin ya ɗauke ni, ko da zan daina hango Haidar yana abin da ake faɗa. Saboda na kasa daina hango shi cikin hoton zuciyata da irin firgitar da yake yi a lokacin da ake tsoratar da shi.

      Ban san ya aka yi barcin ya mamaye ni ba, domin tun ina jin hirar Inna Kulu da Amina sama-sama, idona a kan rufin ɗakin. Har na koma hango duhu a idon nawa, kafin na tantance ɓarcin ya ɗauke ni.

      Ban tashi farkawa ba sai cikin duhun dare, lokacin da nake ta jin sautin kuka sama-sama yana tashi. A firgice na zabura, saboda mummunan mafarkin da na gama yi da Haidar. Gadon na diro ina zare allurar ƙarin ruwan, idona a kan Kawu Sale da ke ta rarrashin Inna Kulu. Bakina yana rawa na ce da su, 

      "Inna Kulu ina Haidar! Ba a dai tafi da shi ko'ina ba ko?"

        "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Ki yi haƙuri Zaituna, ki rungumi wannan ƙaddarar da ta same ki. Saboda babu mai rayawa da kashewa sai Allah, ki ɗauka aro aka ba mu Haidar. Kuma yanzu yana da kyau mu karɓi abin da aka zo mana da shi, ko da ba ma farinciki..."

    

      "Ina za ki je?"


Ita ce tambayar da na ji Kawu Sale ya yi mini cikin raunanniyar murya. Kallon sa kawai na yi kamar ban gane me ya faɗa ba. 

      Saboda babu abin da nake da muradin gani a lokacin face yarona, aguje na nufi ɗakin da yake kwance, saboda wani sabon kuzarin da nake ji a jikina kamar na jima da samun lafiya. Sai dai me, tun kafin na ƙarasa Umma ta sha gabana, amma daga inda nake; ina iya hango lulluɓin da aka yi wa Haidar da zaninta.  Hannu na fara nuni da shi a saitinsa, bakina yana karkarwa nake faɗin,

      "Ku buɗe shi bai mutu ba! Ya faɗa mini ba zai tafi ya bar ni ba, tun da yana so na! Umma a buɗe shi wallahi bai mutu ba..." 


    Maganar da na hattama kenan bakina yana rawa, tare da durƙushewa ƙasa ina wani irin kuka, mai ɗauke da ruwan hawaye da majina. 


       "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


   Ita ce kalmar da Umma ta faɗa, da hanzari na tashi tsaye, idona a kan wasu ma'aikatan asibitin. Saboda ganin sun ɗora shi a kan wani gado suna tura shi za su bar wurin. Cikin sauri na nufe su tare da riƙe ƙarfen gadon ina ƙoƙarin buɗe shi ina faɗin,

      "Ku bar mini ɗana don Allah! Wallahi bai mutu ba. Saboda ya sanar da ni ba zai tafi ya bar ni ba"


     Ji na yi an ɓanɓare hannuna daga jikin ƙarfen. Ina kallo aka tafi da Haidar, kafin wani sabon jiri ya kwashe ni na tafi luuu na zube ƙasa. 

        "Da gaske Haidar ɗina ya tafi ya bar ni? Don Allah ku ce kada ya bar ni a lokacin da nake da ƙisar kusanci da shi..." 


    Maganganun da na farka da su kenan a cikin bakina. A lokacin da aka ɗebe tsammani da samun rayuwata, saboda somewar da na yi tsawon kwana uku ban farka ba. Domin zuciyata ce ta kai matakin gajiya da aiki, kuma an ba da tabbacin da na wuce wasu awannin da aka ɗiba; sai dai a yi haƙuri da ni. Saboda tun kafin lokacin zuciyata ta kumbura, kuma Likita ya tabbatar wa da su Umma; ƙiris ya rage ta buga. Sai ga shi na rasa ɗana, mafi soyuwar zuciyata, a cikin 'ya'yana. 

      Sautukan mutane na dinga ji a cikin kunnuwana. Waɗanda suka ƙumshi muryoyin mutane da dama, kuma a faraɗ ɗaya ba zan iya tantance su duka ba. Amma tabbas na ji muryar Ummata, Kawu Sale, Inna Kulu da 'ya'yanta. Sai Firdausi, Amina, Arma, Baba Ali da matansa biyu, wasu 'ya'yansa mata da maza. Da sauran wasu da na kasa tantancewa. Waɗanda dukansu kalmar,


     "Alhamdulillah!" Ce take fita daga bakunansu. Sai masu faɗar, "Allah mun gode maka!"


    Kallo na dinga bin kowa da shi ɗaya bayan ɗaya, kafin na ɗora idanuwana a kan fuskar MD. Wanda ke tsaye ɗan nesa da su, yana ta faman goge fuskarsa da tissue, wanda a lokaci ɗaya na gano kukan da ya sha a cikin ƙwayar idonsa. 

      Hannu na miƙa masa, alamun ya zo, wanda hakan ya sa mutanen da ke wurin suka bi hannuna da kallo, mai nuni da inda yake tsaye. Kawu Sale ya yafito shi da hannu yana faɗin,


     "Matso kusa mu ji, me take son cewa."


    MD ya zo gaban gadon ya rusuna, hannunsa ya saka cikin nawa, sannan ya rintse su wuri ɗaya gam-gam! Idonsa cikin nawa yana ƙoƙarin yin magana amma ya kasa. Sai da na ƙare masa kallo tsawon sakonni sannan na ce da shi,


    "Ka kai ni wurin Haidar na gan shi. Ina son ganin shi tun kafin mutuwa ta tafi da ni..."


     "Ba za ki mutu ba! In Sha Allah za ki tashi ki sake samo mana wani Haidar."


    Hannuna da ke cikin nasa na zare a hankali. Sannan na juya kaina ina ƙoƙarin goge ruwan hawayen da ke bin gefe da gefen fuskata. Saboda zancen shi, ya tabbatar mini da mafarkan da nake yi a kan mutuwar Haidar. A hankali na juyo ina kallon Ummata, wacce ni take kallo ita ma tana goge hawayen fuskarta. Idanuwanta sun nuna zahirin kukan da ta sha a cikinsu, hakan ya ƙara raunata zuciyata matuƙa. Amma a haka sai da na yi jarumtar furta,


     "Ina su Umma Salma?"


    MD ya miƙe ya fice cikin dandazon taron, Umma ta matso kusa da ni ta riƙe hannuna. Tana so ta yi magana amma ta kasa furta komai sai sharɓen kukan da take yi. 


    Inna Kulu ta matso tana goge fuskarta da gefen zanin da ke jikinta. Sannan ta yi jarumtar zuƙe majinar kukan da ke cikin idonta ta ce,


    "Yaranki suna nan lafiya lau! Don haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same su da yardar Allah!"


    "Haidar kuma ai ya rasu..."


     Iya abin da na iya furtawa kenan hawaye yana ziraro mini. 

     "Ki kwantar da hankalinki, bari yanzu na je gida, na ɗauko miki su ki gan su."

  

    Kallo kawai na bi Kawu Sale da shi har ya bar cikin taron. Ƙarfin riƙon da na ji Ummata ta ƙara yi mini; ya sa na dawo da kallona kanta. Bakina yana rawa na ce,

     

     "Ki daina kuka Umma, tun da Haidar ya tafi ba zai dawo mana ba. Ko bayan na mutu akwai su Iman, za ku dinga ganin su kamar ni da Haidar..."


    Ruf na ji Umma ta rufe mini bakina, girgiza kai ta shiga yi kafin ta haɗiye wani abu muƙut a wuyanta ta ce da ni,


    "Idan kina son farincikina, ki daina ambatar mutuwar nan, kuma ki daina kiran sunan Haidar daga yanzu..." 


      "Ai tun da ya rasu, ko ganin shi ba zan sake yi ba, balle na kira shi Umma..."


     "Don Allah ku yi haƙuri ku ɗan bar mu da ita, akwai wasu magungunan alluran da za a yi mata. Ku fita waje sai bayan awa uku, zuwa lokacin za ta samu ƙarfin surutun da ake saka ta."


      Zancen wata nurse kenan, ina kallo, suka dinga ficewa ɗaya bayan ɗaya aka bar Ummata. Ita ma Likitan yana zuwa ya ce ta ɗan jira su waje idan sun gama ta dawo. Allurai aka sake zuba mini a gorar ruwan da ake zirara mini a hannu. Tare da wasu magungunan da ban san amfaninsu ba.

     A hankali nake bin Likitan da nurse ɗin da kallo, suna ta aikinsu har zuwa lokacin da ban gane komai. saboda barcin da ya ci ƙarfina.







    😭






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


     _*Ku yi haƙuri ina ba ku haƙuri, tabbas rashin Haidar ni kaina abin ya taɓa mini zuciya. Ina so na yi amfani da wannan dama, domin na nemi yafiyar ku a kan kukan da na saka ku.😢 Wanda ma ya tsinci zuciyar shi babu daɗi; shi ya yafe mini👏🏻. Ina jin daɗin yadda kuke nuna ƙaunar littafin nan a fili da zuciyarku. Ina son ku duka, kuma ina alfakhari da ku mutanena. Alherin Allah ya ziyarci ruhinku da ƙirazzanku, a duk inda kuke. Ubangiji ya ƙara kare mana yaranmu da sharrin abin ƙi komai ƙanƙantarsa. Mu ma ya ba mu ƙarfin gwaiwar ɗora su a kan daidai duk rintsi. Zaituna ta ce a gaishe ku, Umma ma ta ce 'Ashe haka kuke son ɗan Jikallenta?' Fatan alheri dukanku, much luv you my fan's💋*_


*ASHIRIN DA BIYU.*


        Satina ɗaya a Asibitin, ana ba ni kulawa ta kowace fuska. Likitoci suna iya yin su a kan lafiyata ta dawo na wartsake. Su Umma suna karakaina a kaina, suna ta ƙoƙarin faranta mini. Haka ma duk wani 'yan'uwanmu da abokan arziƙi, na kusa da nesa; sun zo duba ni Asibitin, kuma na ga tausayin da suke mini a cikin idanuwansu da fuskokinsu.

      Hatta Yaya Maimuna da dangin Mukhtar wasu da yawa sun zo duba ni. Yaya Maimuna ma duk da a muzance take har ta bar Asibitin; zuwan ta biyu duba ni. Amma cikinmu babu wanda ya yi mata rashin kirki ko kallon banza. Saboda darajar Sajida, da kalolin ɗawainiyar da take yi a kaina da su Ummu Salma. Domin ita ke ta ba su kulawar idan suka zo har sai ta bar Asibitin.

      Abin farinciki har da Ammin MD ta zo duba ni, na sha mamaki ƙwarai a lokacin da na gan ta. Farar dattijuwa, guntuwa mai fuskar kamala, saɓanin shi da yake tsaka-tsaki. Ba za a kira shi fari ba, kuma kai-tsaye ba za a ce da shi baƙi, sannan shi ingarman namiji ne dogo, mai ɗan jiki saɓanin ita da take guntuwa kuma mara jiki.

       A take na ƙiyasta komai na Babansa ya ɗauko, domin ban da satar kama irin ta uwa da ɗan da ta haifa; babu ta inda ya biyo ta a ƙirar halitta.  Na ji daɗin ganin yadda ta nuna mini ƙauna fili, sannan fuskarta a sake suka yi 'yar mutunci da su Umma, har ta bar Asibitin. Sai faɗin take yi, a kula da ni don Allah kada a sake ɓata mini rai.

      Likita ya sallame ni da tarin magunguna tare da dokoki. Sannan ya yi alƙawarin zuwa duba ni a gida lokaci bayan lokaci, ko da ban zo Asibitin ba. Domin a cewarsa mun zama 'yan'uwa, kuma yana mini kallon ƙanwarsa ta jini. 

       Umma da Inna Kulu sai godiya suke ta yi masa, yayin da MD ya miƙa masa hannu suka yi musabaha. Kai-tsaye ya yi gaba, bayan ya ce da su Umma zai jira mu waje domin ya kai mu gida. Kallon fuskar Umma na yi babu yabo babu fallasa, hakan ya sa na gano MD ya samu canjin hali a wurinta.

     Inna Kulu da Sajida suka yi ta ɗibar kayanmu suna kai wa motarsa. Ina zaune sai kallon mutane nake yi, cike da jin daɗin zan bar Asibitin. Domin duk na kai kallo na ɗakin da Haidar ya zauna; sai na ji ƙirjina ya buga. A ƙagauce nake da barin Asibitin, tare da cin alwashin ba zan sake zuwan ta ba har abada. 

        

      Tare muka fita da wasu nurse's ɗin da muka yi sabo da su, a ɗan zaman da muka yi. Sannan Likitan ma ya rako mu ina ji suna wata magana da Kawu Sale, wacce na ji kamar yana faɗin recording ɗin da ya yi yana nan a wayarsa, da laptop ɗin shi. 


    'To wane irin recording?'


Tambayar da na yi wa kaina kenan a zuciyata, wacce na so a ba ni amsar ta tun kafin ta zame mini aiki a zuciyata. Muna tsaka da sallama sai ga motar Arma ta doso inda muke, daidaita wa motar zama ya yi sannan ya fito cikin rawar jiki yana gaishe da su Umma. Kafin ya matso kusa da ni, idonsa a kaina bakinsa har kunne yana faɗin,


     "Ma sha Allah! Ashe an yi sallama? Tun ɗazu nake son zuwa na tsaya wani uzuri. Yanzu ya kike jin jikin naki? Da sauƙi ko?"


    Ɗaga masa kai kawai na yi ina murmushin yaƙe, saboda ganin gabaɗaya wurin ni ake kallo. Fuskar MD na hango a cure, kafin ya buɗe motarsa ya shiga ya zauna yana dannar waya.

      Ganin haka ya sa ni ma na nufi motar ina cewa Inna Kulu, 

    "Mu je Inna, jiri nake ji!"


Ɗuruwa muka yi a bayan motar, ni, Umma, da Inna Kulu. Kawu Sale ne ya zauna gaban motar,  yayin da yake ƙoƙarin gyara zaman rigarsa domin ya ji daɗin rufe ƙofa. Arma ya duƙo da kansa fuskarsa a sake yana faɗin,


     "Umma da wasu sun rage mun tafi a tawa motar."


     "Bar shi kawai tun da mun zauna. Kai ma, mun gode sosai da ƙoƙarinka. Allah ya bar zumunci, kuma ya saka da alheri."


    Zancen Umma kenan, cikin sakin fuska. "Amin." Ya ce sannan ya ɗan ja baya saboda wutar da MD yake bai wa motar. Ina hankalce da shi sarai ko da ya ja motar fuskarsa a haɗe, sai cizon haƙoran shi yake yi tare da ƙura wa madubin motar ido. Muna gaba Arma yana rufa mana baya, har muka fito gate ɗin Asibitin muka  kama namu titin ya yi na shi. 

      Jugum-jugum babu wanda ya yi magana har muka kusa isa gida, sannan Kawu Sale ya ce,


     "Yana da kyau gobe a yi zama na musamman a kan matsalar nan! Saboda Likitan ya ce komai yana nan a cikin wayarsa da computer'rsa. Tun da har Allah ya sa yaron ya yi bayanin da bakinsa, ai gardama ta kawo ƙarshe."


     Inna Kulu ta yi hanzarin faɗin, "Allah ya kai mu goben. Ai inda babu ƙasa, nan ake gardamar kokawa."


  Ajiyar zuciya kawai Umma ta sauke, a daidai lokacin da MD ya yi parking ƙofar gidan Kawu. Muka fiffoto motar, na so shigewa gidan, sai na ga rashin dacewar hakan na ja na tsaya. 

     Zagayowa ya yi ya buɗe bayan boot yana fito mana da kayanmu. Inna Kulu da Kawu sai godiya suke ta zuba masa. Umma ma kamar mai jin nauyinsa a bakinta, a haka ta gode masa cikin sanyin murya kafin ta ɗauki wasu kaya ta yi cikin gidan da su. Ni ma na ɗauki tabarma da buta zan bar wurin, MD ya yi hanzarin shan gabana ya karɓe. Harara ya aiko mini wacce ban san laifin da na yi masa ba, kafin ya yi gaba da butar da tabarmar a hannunsa zuwa gaban ƙofar gidan. Inna Kulu ta fito ta karɓa ta koma ciki tana yi masa godiya. Kawu ma ya ɗauki wasu ya yi cikin gidan, ni kam ban da kallon shi babu abin da nake yi.

       Saboda na kasa motsawa daga inda nake, balle na bar wurin. Takowa ya yi ya tsaya gabana, ido cikin ido muke kallon juna. Ni fuskata a sake, shi ta shi a cure, yana ƙoƙarin yin magana Kawu ya fito yana faɗin,


     "Ki shigo da shi ɗakina! Ya fi tsayin da kuke nan wurin!"


    Cike da mamaki, da jin wani nauyin MD, na kalli Kawu na ce,


 "Tafiya zai yi Kawu!"


     "To ya yi, amma idan ya dawo ko ba na gida; a buɗe masa ɗakin ya je can ku zauna! Don yanzu ya zama ɗan gida, ba za a sake barin shi tsayuwa ƙofar gidan nan ba."

      Har cikin raina, na ji daɗin karamcin da Kawu yake ƙoƙarin yi wa MD. Shi ma na hango siririn murmushi a kan fuskarsa, duk da yanayinsa bai yi kama da wanda yake farinciki ba. Bayan Kawu ya koma na yi masa wani kallo sannan na kira shi da sunan da nake faɗa a gabansa,


     "Sir! Ina ta ganin ɗawainiya fa! Bayan wacce na ji a bakin su Umma. Na gode sosai, Ubangiji ya saka maka da alheri, mun gode, mun gode sosai. Allah ya jiƙan mafari, kuma ya ƙara buɗi na alheri. Ita ma Hajiya a yi mata godiya, Allah ya hutar da gaji..."


    Yanayin kallon da yake yi mini ko ƙyaftawa babu, ya sa na yi hanzarin datse maganar ina turo baki kamar wata ƙaramar yarinya. Saboda fuskarsa ta nuna kamar ma ba ya jin daɗin addu'o'in da nake yi masa.

      Raina a jagule na juya zan bar wurin, ya yi hanzarin faɗin,


    "Ki ce da wancan yaron, kada ya sake zuwa kusa da ke daga yau! Idan kuma kika sake yi masa murmushi; Allah yana kallon ku!" 


    Yana ƙare maganar ya shige motarsa cikin zafin nama ya bar ƙofar gidan. Bayan motarsa na bi da kallo, cike da mamakin maganganun shi. Saboda daman na zargi ransa ya ɓaci tun a Asibitin. 


      'To amma me ya kawo zancen Allah yana kallon mu?' 


     Tambayar da na jefi kaina da ita kenan, wacce rashin gano amsar ta ya sa na ja ƙafafuwana na yi cikin gidan. Rashin ganin su Ummu Salma suna mini oyoyo; ya sa na tuno suna gidan babbar ɗiyar Inna Kulu. Domin a can suke zama tun lokacin da muka fara kwana asibiti. Kasancewar tana da yaran da suke kamar sa'o'in juna, hakan ya sa ake kai su gidan, tun da Umma da Inna Kulu duka sun tare Asibitin.

       Bayi na fara shiga, sannan na yi ɗakin Umma, saboda ƙarfe sha ɗaya na rana a lokacin. Kwanciya na yi a kan gadon Umma na mimmiƙe, ina jin ƙasusuwan jikina suna ƙara ƙas-ƙas! Sannan na sauke numfashi mai ƙarfi na ce da Umma,


     "Kin ga hannun nan nawa gabaɗaya ciwo yake yi mini."   


    "Dole ya yi ciwo, tun da kin sha suka. Murnarmu ɗaya ce; Allah ya shiga lamarin kin tashi lafiya." 


     Kiran da ya shigo wayata, ya sa na kasa cewa komai. Cikin sauri Umma ta miƙo mini wayar da ban san an saka mini ita caji ba. Sunan Sajida na gani, haka kawai na ji ƙirjina ya buga, saboda tuno ranar da ta kira ni tana sanar da ni ciwon Haidar.


     "Aunty ga ni Asibitin na zo, an ce an sallamo ki."

      "E, gani ɗakin Umma."


"To gani nan zuwa yanzu!"


     "Ok tom!"


Kashe wayar na yi da sanyin jiki na miƙa wa Umma. Saboda tunanin mutuwar Haidar, ta sa na ji damuwa ta yi mini lulluɓi. Zancen Kawu Sale da Likita ya faɗo mini a rai, cikin sauri na ce da Umma,


    "Wai Umma wanne recording na ji ana zance?"


     "Rukodin kuma?"


"E, Umma! Wanda na ji Kawu yana magana cikin mota!"


    "Kin san dai ba ki gama warkewa ba, don haka ki daina binciken abin da ba a sanar da ke ba. Don gobe da yardar Allah za a yi ta ƙare tsakaninmu da tsinannun mutanen can! Kuma don Allah ki yi haƙuri a kan duk abin da za ki ji an yi, ko an ce. Saboda abin da ya faru ya riga da ya faru sai bitar zance. Saboda da wannan abin, da babu shi, duk ba za mu hana Allah yin abin da ya tsara mana ba. Ki ɗauki cewa; Yaron nan Allah ne ya nufa zai rasu yanzu, saboda ya ƙaddara ba zai yi dogon zama ba tun a kafin ya zo duniya. Domin da ba a ƙaddaro masa hakan ba; ruwa da iska, ba zai raba shi da numfashinsa ba. Ubangiji ya ba mu aronsa, kuma ya karɓi kayan shi a lokacin da yake so. Mu yi fatan Allah ya sa shi zai ceci mu a ranar lahira."

  

      "Amin Umma. Tabbas! Na yi imani da haihuwa da mutuwa, kuma na san Allah ne ya ba mu kuma ya buƙaci abin shi. Ubangiji ya ba mu ikon jure rashin shi, da ture tunaninsa a zukatanmu."


     "Amin Zaituna, Amin Ya Allah! Karɓi ki sha"


    Zancen Inna Kulu kenan, tana miƙo mini fura a kofi. Na karɓa jikina babu kuzari na fara sha, yanayinta da na ji babu tsami ya sa na zuƙe nan take na ajiye kofin ƙasa.

      Saboda a cikin magungunan da ake ta ɗura mini har da na cin abinci. Kuma Alhmdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin har kumari na yi, sannan haskena ya ƙara fitowa sosai. Saboda  jinyar ta karɓe ni duk da ƙuncin da ke addabar zuciyata. Don ni kaina na san na ƙara cika, saɓanin watannin da suka wuce, a lokacin da nake jinyar horon da na yi wa zuciyata a kan MD.


     Komawa na yi na kwanta, shiru na yi ina ta tunanin abubuwa da yawa. Cikinsu har da tunanin rayuwar da na yi da Haidar, wacce kusan kullum bakinsa ɗauke yake da zancen; idan ya girma zai kai ni Makkah, ya dinga saka ni motarsa muna yawo. Har da nuna mini yadda zai yi tuƙin yake yi da hannuwansa biyu, yana faɗin,


    Zwinnn! Zwinnn! Ƙuuuu! 


"Allah Sarki yarona. Ubangiji ya kai ka kafala."


    "Amin" Na ji Umma ta ce sannan ta fice ɗakin, a lokacin na gano fili na yi zancen. Jinin jikina na sha ban sake motsin kirki ba, sai da na ji sallamar Sajida  na ɗan muskuta. 

      Ta shigo da fara'arta, wacce fuskarta ta nuna jin daɗin gani na zahiri. Kular da ke hannunta ta ajiye bakin gadon, sannan ta zauna tana faɗin,

      "Wash! Aunty! Da na sani da na kira ki a waya. Na ji haushin da ya ajiye ni ya tafiyarsa. Kuma sauri yake yi ya je wurin aiki na sa ya yi latti, dole na nemo adaidaitasahu ta kawo ni don ba zan sake takura masa ba."


     Murmushi na yi mata kafin na tashi zaune, saboda har zuciyata na ji daɗin jin maganganunta. Domin alamu ya nuna a fili, ta fara yarda da ƙaddararta, kuma tana samun natsuwa a zamanta da Baban Taufiƙ. Saboda daman can ba ragon maza ba ne, kuma ya san darajar aure, sannan ya iya tattalin mace. Shi ya sa Maman Taufiƙ ta haukace a kan kishinsa, domin bai rage ta da komai ba, sai auren da yake da burin ƙarawa, wanda take ganin bai mata adalci ba.


     "Aunty me kike tunani?"


   Sajida ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na lula, murmushi a kan fuskata na ce da ita, 


    "Rayuwarki ce ta fara burge ni Sajida. Na ji daɗin ganin kin rungumar ƙaddararki hannu bibbiyu. Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna, sannan ita ma Maman Taufiƙ; ya karkato da hankalinta ta dawo gida ko don yaronta."


      "Amin Ya Allah Aunty! Ni ma ina mata fatan ta dawo gidan mijinta. Saboda ɗan zaman da na yi da shi yanzu, na gano mutum ne managarci. Wanda kowace mace ta zauna da shi dole ta dinga kishinsa... Amma ni dai har yanzu ban fara ba Aunty..."


    Ta ƙare maganar tana 'yar dariya, saboda kallon da nake bin ta da shi; ya sa ta jin kunya. Duƙawa ta yi ta ɗauko kular da ta ajiye, tana ƙoƙarin buɗewa ta ce,


      "Bari na nemo miki plate. Saboda ina so ki ƙara murmurewa da wuri mu sha biki."


     Baki a sake na bi ta da kallo har ta fice. Mintuna a tsakani ta dawo da plate a hannunta tana faɗin,

       "Wallahi Aunty kun yi matching sosai ke da shi, domin yadda ya tayar da hankalinsa, kowa zai gano ba ƙaramin ji da ke yake yi ba. Musamman ranar da aka ce idan ba ki farka ba a lokacin shi kenan. Na rantse da Allah Aunty kamar wani zautacce ya koma, duk wanda ke wurin sai da ya ba shi tausayi."


     




      Allah ya sa MD ya ji kina tona masa asiri Sajida🏃🏻‍♀️






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*ASHIRIN DA UKU.*


      Ido na ƙura mata, bakina a sake kamar wata sakarai, saboda tsabar mamakin maganar da nake ji tana faɗa a bakinta. Miƙo mini plate ɗin take yi amma na kasa zura hannu na karɓa, saboda mamakin zancen da kunnena ya ji, duk da farincikin da na tsinci kaina a sanadin hakan; ba zai iya misaltuwa ba. 


     "Karɓi Aunty!"


Abin da ta faɗa kenan cikin marairaita tana ɓata fuska, idona na ɗora saman plate ɗin da ta shaƙe shi tas da dafaffiyar kaza. Wacce ta sha dahuwar ruwa-ruwa, ta yi luguf-luguf sai ƙamshi ke tashi. Yawuna ya tsinke na yi saurin haɗiyewa muƙut, kafin na karɓa idona a kanta ina faɗin,

      "Wai ke Sajida, me ya sa ba kya gajiya da ɗawainiyar nan haka nan! Shi ma har da Aminun da ya biye ki, yana ɓarnata kuɗinsa a banza..."


     "Wallahi ba a banza ba Aunty! Saboda babu abin da ba zan iya yi miki ba, domin kin cancanta, kuma ni ma kin yi mini a baya. Ai ɗan halas ba ya manta alheri komai ƙanƙantarsa Aunty. Ke dai kawai ki yi masa addu'ar fatan alheri da ƙarin buɗi, ko don na ƙara miƙe ƙafafuwana na ciyo muku arziƙi."


    Dariya ta suɓuce mini babu shiri, ina ƙoƙarin kai loma a bakina na ce,

      "Waton ki ciyo mana arziƙi? E, lalle abin  ki azimun Sajida. To mu ba arziƙi muke so ki ciyo mana ba, zaman lafiya da zuri'a mai albarka muke so. Idan kika wadatu da waɗannan biyun; mu kin gama mana komai a zaman aurenki da shi."


     "Ai in dai wannan ne Aunty ba zan ba ku kunya ba, saboda na ɗaura ɗambar zama da shi tsakani da Allah. Kuma zan kyautata masa daidai gwargwadon iyawata..."

       "Har ma abin da ba za ki iya ba, ki ƙoƙarta ki gwada yi masa, matuƙar kika san yana so."


     "In Sha Allah Aunty!"


Shiru ya ɗan ratsa tsakani ina nazarin zancen  zaucewar MD da na ji ta faɗa, kafin na kawar da shirun da cewa,

       "Dafuwar nan ta mini daɗi a baki. Lalle ba mu yi asarar kuɗin tarar da kika cinye mana a makarantar ba."

       "Ai Aunty rainonki ce ni, dole na haddace duk abin da kika koya mini tun ina ƙarama. Wai Aunty wannan bawan Allah shi ne Abokin Aikinki?"

       Ƙirjina na ji ya buga dam-dam! kafin na ɗago kaina na watsa mata idanuwana duka. Sakato na yi mata kafin na samu harhaɗa kalmomin bakina na ce,


     "Kin san shi ne?"


"A'a Aunty! Kawai dai na gan shi so kind and gentle man, kuma akwai soyayyarki da yawa a cikin ƙwayar idonsa. Jikina yana ba ni kamar shi ne Abban su Iman yake ta zancensa a baya.  Kuma na ji Amina tana kiran shi da Oga, shi ne na yi tunanin kamar shi ne..."


      "Shi ne wa..."


"Shi ɗin dai, shi ɗin nake nufi.."


    "Wallahi kina da abin dariya Sajida."


    Zancen da na yi kenan ina ajiye plate ɗin ƙasa, saboda fahimtar so take ta ji komai a bakina. Hannuna na fara lashewa ina faɗin,


     "Koma mene ne, tun da kin gama fassara shi ai shi kenan. Amma kuma ni har yanzu bai taɓa bari na gano inda ya dosa ba. Wannan zancen ma da kika ce ya tayar da hankalinsa, da a ce a farke nake ido biyu; ba zai taɓa nuna mini ya damu da ni a kan fuskarsa ba. Amma ban san miye zuciyar shi ba gaskiya, saboda bai sanar da ni ba balle na gasgat..."


     "To wallahi Aunty son ki yake yi, don da a ce kin ga yadda ya koma a ranar; da kin gano kin yi wa zuciyarsa muguwar mamaya."

       "Oh Allah! Abin har da mamaya a ciki? To ki rufa mini asiri, kada Umma ta ji kina wannan batu babu ruwana."


     Na ƙare maganar cikin sassauta murya domin ta bar zancen, don na san Umma ba za ta rasa jin hirar da muke yi ba. Amma ta ƙara amsa mini kamar ma ba ta ji kashedin da nake yi mata ba.

       "Yo ai gabanta aka yi komai Aunty, ita ma ta gani, kuma ta shaida ba ƙaramin so yake yi miki ba. Ni wallahi na gamsu da haɗinku, kuma ina fatar ya zamo mijin, ko da za ki fanshe ƙaddararren auren da kika yi a baya..."


     "Innalillahi! Sajiji kin fi ƙarfina. A bar zancen nan mu ɗauko wani, tun kafin ki ɗaure ni da jijiyoyin wuya."


       "Aunty tun da ba kya son maganar, a bar ta kawai. Amma ni dai na san gaskiyar abin da na gani nake faɗ..."


     Sallamar Firdausi ta sa Sajida yin shiru tana kallon ƙofa tare da amsa sallamar. Ni ma na miƙe da nufin wanko hannuna muka yi kiciɓis da ita a bakin ƙofa. Kallo ta dinga bi na da shi har da riƙe baki tana faɗin,


     "Lalle matar nan kin samu lafiya kin ƙi faɗi. Kin ga yadda kike sheƙi tamkar wata sabuwar a amarya?" 

        Ta gefenta na raɓa na fice, don na ga da gaske so take yi ta fasa mini kai da yawa. Ɗakin ta faɗa na nufi bakin fanfo na wanko hannuna, zuciyata cike da wani sabon shauƙi. Saboda zancen MD da Sajida ta yi, ya fama mini mikin son shi da ke danƙare a cikin zuciyata.

       Saboda ni kaɗai na san me nake ji a kansa, kuma na daɗe da sanin shi ma yana jin abin da nake ji ko ma ya fi ni. Amma ƙwauron bakinsa ya hana shi fito da komai ya huta ni ma na sarara, ban san me yake jira ba, ban san wane lokaci yake dakon faɗa mini ba. 

      Nan take na ji wata damuwa ta yi mini rumfa, na koma ɗakin cikin sanyin jiki, saɓanin yadda na fito cike da annushuwa. Zama na yi da tagumi ina ƙare wa kulolin Firdausi ido, saboda zuciyata ta tabbatar mini da ita ma ɗawainiyar ce ta yo mini kamar Sajida.

   

     "Malama lafiya dai, kike ta kalle mini kuloli haka?" 


     "Mamakin hidimarku nake yi kullum babu gajiya. Shi kenan don kun samu mazajen suna sake muku bakin buhu; shi ne za ku koma yi musu wasa da shinkafa. To ni dai wallahi ina ba ku shawara ku san yadda ake tattali. Domin alamunku ya nuna ba ku san zafin neman da suke yi a cikin rana ba." 


     Firdausi ta ƙura mini kallo baki a sake tamkar lefen bakantatta. Kafin ta samu damar faɗin,


     "Sannu 'yar kare maza! To ki yi ki gama ki ƙara gaba, don ba za mu fasa ci mu bai wa wanda muke so ba. Tun da ba jeren ɗaki ake so mu yi da shinkafar ba..."


     "Ni dai gaskiya na faɗa muku, ku koyi tattalin abin da miji yake kawowa. Saboda ƙarnin nan da ake ciki kowa ya san da wahalar neman da mazaje suke yi, kafin su kawo gida su ajiye."


     "Amma wallahi wuyanki ya yi kauri Zaituna! Ke yaushe kika dawo ta maza har kike kare su?"


     "Ko ma yaushe ne ni dai gaskiya na faɗi! Don haka zan faɗa wa Umma ta hana ku wannan almubazzancin da kuke yi wa mazajenku... Ummah!!!!!!"


    Na ƙare maganar tare da ƙwala wa Umma kira, ta shigo tana 'yar dariya alamu ta ji mu. Za ta yi magana Firdausi ta yi saurin faɗin,


      "Umma don Allah kada ki ce komai ki bar ni da ita! Tun da ta samu lafiya ai kuma rashin mutunci sai wanda ta mance." 


     Umma ta fice tana faɗin, "Ai kun sha ƙoƙari Firdausi, ku bari haka nan ku ma ku huta da ɗawainiya. An sha fama da mu asibiti, ya dace ku bari haka nan ku huta, hidimar ta yi yawa gaskiya!"


     "Shi kenan dai Umma kin goyi bayanta!"


    Zancen Firdausi kenan tana dariya. Gwalo na yi mata cike da tsokana na ce,

     "Idan mu manya mun faɗi magana, ya dace a ɗauki shawarar da muka bayar. Saboda abin da muka hango; irinku ko sun hau tsani ba za su gani ba.."


       "Kam bala'i! Ke irinmu ko dai irin Sajida?" 


    "Ni ai girma ɗaya nake hango ku..." 


     Dundu ta kai mini a baya na kauce ina dariya, Sajida ma tana dariya ta ce,

     "Aunty Firdausi ki daina dukan amaryar oga MD. Kin san tsautsayi ne da ita, kada ta koma mana kwance mu shiga uku. Bayan mun saka ranmu da shan biki mu kwaso shoki."


    Kallon Sajida na yi bakina har kunne na ce, "Wai sai yaushe zancen mutumin nan zai fita a bakinki?"


       "Ranar da muka kai masa ke Aunty!"


    "Ohhh Allah! Mu muka ga tsagwaron soyayya Asibiti. Wai matar nan tana cikin jinya ma hannunta bai daina nuna shi gaban dubban mutane ba. Wallahi da ni ake bi, kan gadon asibitin za a ɗaura auren da ta wartsake a miƙa ta gidan shi. Domin wannan rashin ta idon da ta aikata abin dubawa ne, yarinya a hannun Allah amma tana zambaɗa wa mutane soyayya!?"


   Kasa cewa komai na yi, sai siririn tsakin da na ja, wanda ya ƙi fitowa duka saboda kunyar da ta ba ni. Kwanciya na yi kan gadon ina faɗin,


     "Tun da kika samu abin faɗa, ai kuma an boni. To bari ki ji; idan ma an yi hakan, to ba a hayyacina na yi ba..." 


     "Aunty mu ai haka muke so! Saboda ni dai wallahi ina so masa ke da yawa. Domin ta ko'ina kun daidaita, kina mugun son shi, shi ma yana mahaukacin son ki..."


    "Yau dai, a kaina kuke neman sauke gajiyarku. To bari na bar muku ɗakin, kada ku janyo mini wani sabon ciwo."


   Tashi na yi ina dariya na fice waje, saboda kiran sallar da na ji ana yi. Ban koma ɗakin ba na shige ɗakin Inna Kulu, a can suka same ni bayan mun ci abinci; muka kora da wata sabuwar hira. Wacce duk rabinta shawara ce suke ba ni a kan na riƙe MD. Amina ta zo ita ma ta fara fashe abin da ke zuciyarta a kan jin daɗin tarayyata da MD. 

       Bakinta a sake ta dinga yabon halin shi gare su, tamkar wacce aka siye domin ta yi aikin. Dukansu sun yaba kuma sun yi na'am da cewa shi ne mijin da ya dace na aura. Ni dai ido da baki kawai nake saki, saboda ba na so na faɗi abin da zan fallasa kaina a wurinsu. Domin idan na biye ta zuciyata, zan yi ɓanɓaramar kwararo musu yadda nake jin shi a raina, har wata safiya ta waye ban gama ba. Haka suka bar gidan sai nanacin zancensa suke yi. Ni ma suka bar ni da kewar son shi da ke linkuwa a cikin zuciyata.


      *****

Daren ranar mutane suka dinga zuwa duba ni,  wasu suna fita wasu suna shigowa. Saboda har can asibitin wasu sun je, hakan ya sa suka gano an sallame ni suka garzayo gida.

      Bayan sau ya lafa na lula duniyar tunanin rayuwar aurena da Mukhtar. Wanda na gama haɗa kan komai na gano, bayan su Ummu Salma da na samu da shi; ban tsira da komai ba a cikin aurensa. Sai guzurin baƙinciki da ɓacin rai, wanda ya bar da mikin da nake jin ba zai goge mini ba iya rayuwa. 

     Ba tun lokacin ba, na sha da-na-sanin sanin shi a rayuwata. Na sha jin ina ma a ce ban taɓa sanin shi ba, ina ma a ce hannun agogo zai iya dawo mini baya. Domin  na goge shi kwata-kwata a cikin tarihin rayuwata. Saboda ina jin tsanarsa a kowane lungun zuciyata, ina ji da za a ba ni damar kashe mutum ɗaya a duniya, kuma a lamunce mini hakan ba tare da laifi ko zunubi ba, balle haƙƙin kisan shi ya rataya kaina. Da a tashin farko shi zan fara kashewa, irin kisan da zan dinga datsar naman jikinsa duk bayan kwana ɗaya, wanda zai ɗauki tsawon lokaci ina gana masa azaba. Domin ba zan iya kashe shi a tashi ɗaya ba, ba tare da ya ɗanɗani ƙunar kwatar baƙincikin da ya bar wa zuciyata ba.

      Ajiyar zuciya na sauke mai sauti, kafin na janyo tunanin MD ta ƙarfi. Saboda ina jin zuciyata tana yi mini ƙuna tamkar ana gasa biredi a cikinsa. Rintse idanuwana na yi ina hango Haidar a cikinsu, sannan  MD a gefe yana buɗe hannuwansa cike da jiran na faɗa jikinsa. Fuskarsa ɗauke da mayalwacin murmushin da ke ƙara masa haiba. Ni ma wani murmushin ya ziyarci fuskata, ban san lokacin da na furta kalmomin da nake ji a raina shi ne a gabana.


    'Ina son ka da yawa'


Zancen zucin da na yi kenan, sannan na juya kwanciyata. Na jima barci bai ɗauke ni ba, duk da magungunan da na sha akwai na barci a ciki. Amma tunanin da ke kaina, ya rinjayi barcin da ke cikin idon nawa. 


     ***

Da safe na tashi cikin sanyin jiki da mutuwar gaɓɓai. Umma da Inna Kulu ma sai da suka dame ni da tambayoyi a kan yadda nake ji. A tsammaninsu jikin ne ya motsa, na wayance musu da cewa; ba na jin ƙarfin jikina ne. 

      Sannu suka jera mini, bayan sun saka ni kari cikin lokaci tare da shan magungunana. Daga haka ban san lokacin da barci ya sace ni ba, ko da na farka na ga agogon ɗakin Umma ya nuna ƙarfe goma saura minti shida. 

      Da salati na miƙe ina kallon su Ummu Salma da ke zaune gaban gadon jugum-jugum, babu mai motsin kirki a cikinsu. Haka kawai na ji damuwa ta ziyarci zuciyata, saboda tun jiya na so a kawo su na gan su. Umma ta ce a bar su sai da safe a kawo su, duk da ban san dalilinta ba; amma na saka wa raina su ma suna cikin kewar rashin Haidar sosai.

     Sunansu na kira suka taso da gudu suka rungume ni, kukan da suke yi ya sa ni ma na fashe da nawa kukan. Saboda tsabar tausayinsu ya rufe mini zuciya, ganin da gaske mutuwa ta yi mana yankan ƙauna. Ta raba mu da sanyin idonmu mai saka mu nishaɗi da magantuwa ko ba ma so. 


    "Ku yi haƙuri kun ji, Allah ya fi mu son shi. Kuma daman can bai ƙaddara za mu yi tsawon rayuwa da shi ba. Yanzu ku ba ga ku nan muna ganin juna ba? Don haka ku gode wa Allah tun da ga ni da raina ban mutu ba, kuma ni da ku muna raye za mu dinga yi masa addu'a."

      "Mama Malamin makarantarmu ma ya ce, mu daina kuka Haidar ɗan Aljannah ne."


    Zancen Iman kenan tana goge hawayenta, cikin sauri na ce,

     "Sosai ma! Ai a ranar lahira shi zai cece mu dukanmu mu shiga aljanna."

      Daga haka babu wanda ya sake magana a cikinsu. Ummu Salma ma kukan da take yi bai bari ta yi magana ba, rarrashin su na shiga yi har Umma ta shigo tana faɗin,


      "Fitar nan da za yi kamar ki yi zaman ki."


    "A'a Umma bari na yi wanka ai na samu ƙarfi yanzu."


    Na ƙare maganar da janye su Ummu Salma a jikina, na miƙe tsaye. Wanka na faɗa a gurguje na dirje jikina na fito, a lokacin duk su Kawu sun shirya ni kaɗai ake jira. Ina tsaka da shafa mai na ji ƙarar saukar mota a ƙofar gidan, ƙirjina na ji ya buga dam! Saboda jikina ya ba ni motar MD ce. 

     Sai ga muryar Kawu yana faɗin, 


   "To ku fito fa! Ga shi nan ya zo mu yake jira."


     Cike da mamaki na saka kayana tare da goga ɗan turaren toch a jikina sama-sama. Umma ta leƙo tana faɗin,


     "Ki same mu waje." 


Bayan fitar ta Inna Kulu ta shigo ɗakin tana cewa,

 "To ku ku taso ku taya ni hira kafin su dawo!"

 

    Su Umma Salma suka fice, na zura dogon hijabina mai kai mini har ƙasa, sannan na rufe ɗakin na miƙa wa Inna makulli. Ina ƙoƙarin fita gidan na haɗu da Kawu zai shigo gidan, gani na ya sa shi juyawa yana faɗin,


     "Yawwa! Fito mu je."


Tun da na doshi motar, nake jin ƙirjina yana dakan lugude. Ban bari na kai kallona gare shi ba balle na haɗa idona da shi. Bayan motar kawai na buɗe na shige, na zauna gefen Umma, Kawu ya shiga gaba shi ma ya zauna. Kamar an ce da ni ɗago fuskarki, caraf idanuwanmu suka sarƙe wuri ɗaya a cikin madubi. Da hanzari na janye nawa idon jikina yana tsuma. Nan take na diririce, amma na jarumtar basarwa tare da ɓata fuskata ina kallon gefena. A hankali ya ja motar cike da ƙwarewa, sai dai har muka bar ƙofar gidan muka kama titi ban mayar da kallona cikin motar ba.



    

   Wannan tafiya..🤭




 



D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*ASHIRIN DA HUƊU.*


       Tafiya yake yi tiryan-tiryan daga wannan zuwa wancan. Amma duk na yi katarin ɗago kaina sai na ga fuskarsa cikin madubi, kuma ni yake kallo kamar ba tuƙin ne a gabansa ba. Zuciyata cike da fargaban kada ya buga motocin da ke gabansa, ko kuma ya watsar da mu mu shiga uku. 

       Addu'a na dinga yi a zuciyata cike da ƙaguwar mu dai isa inda muka nufa lafiya. Sai ga mu a bakin gate ɗin ma'aikatar hukumar kare haƙƙin ɗan Adam, wacce tun a saman allon bangonsu, aka rubuta HUMAN RIGHTS. 

     Babu wani jinkiri muka shiga harabar wurin, bayan ya yi parking muka fiffoto. Zuciyata cike da tambayoyin; me ya kawo mu, kuma wurin wa muka zo. Duk da jikina ya ba ni a kan case ɗin Haidar ne, sai dai kuma ban da masaniyar wainar da ake toyawa.

      MD da Kawu a gaba, ni da Umma muna bin su a baya har ofishin shugaban hukumar. Wanda wani ya yi mana jagoranci kai-tsaye ba tare da mun yi jira ba. Hannu ya bai wa wa su Kawu, suka yi musabaha, mu ma muka gaishe shi tare da mutanen da muka taras ofishin. Sannan ya nuna mana dogon benci muka zazzauna, tare da ba mu uzurin mu yi haƙuri yanzu suna kan hanya sun kusa isowa. A raina na ce,

      

      'Su waye?'


Shiru na ɗan mintuna sai ga sallamar Likita shi ma ya shigo, jakar da ke jikinsa na bi da kallo har ya gama gaisawa da kowa. Wurina ya zo fuskarsa a sake yake faɗin,


     "My facient! Fatar kin samu lafiya?"


    Ina murmushi na ce da shi,


     "Jiki ya warware"


"Haka ake so, Ubangiji ya ƙaro miki lafiya. Amma ki dinga shan magungunanki, in Sha Allah za ki samu ƙarfin jikinki sosai."


    "Ina kan sha. Kuma Alhmdulillah na fara dawowa normal..."


    "Ok, hakan yana da kyau! Amma idan kin ji wani canji kawai ki kira ni, ko me nake yi zan zo in Sha Allah!"


    "Na gode!"


Iya abin da na iya furtawa kenan, saboda fuskar MD da na hango ta ɗoro baƙin hadari cikin ɗan lokaci. Amma kansa a duƙe yana kallon ƙasa tare da ƙura wa wuri ɗaya ido, tamkar wanda aka bai wa aikin gano; simintin wane Company ne aka yi shafen tyles ɗin da ke malale cikin ofishin.


     Nan take na sha jinin jikina, duk da har raina na ji daɗin ganin sauyin na shi. Jugum-jugum babu wanda ya sake magana shugaban hukumar yana ta rubuce-rubucen shi. Sai ga jiniyar 'yansanda wiwi ta shigo harabar ma'aikatar. Ɗan lokaci a tsakani wasu 'yan sanda biyu suka fara shigowa, sannan Barira da Mukhtar da ke cikin ankwa a bayansu. Bayansu ma wasu 'yan sandan ne, aka durƙusar da su ƙasa, sannan aka katsa musu tsawa tare da kai musu faka.

       Ganin su ba ƙaramin fama mini mikin zuciyata ya yi ba, babu shiri na miƙe ina ƙoƙarin ficewa ofishin. Saboda muguwar tsanar su da nake ji a raina, ba zan iya jurar haɗa numfashi da su a muhalli ɗaya ba. Sai dai ko taƙa huɗu ban yi ba, bakunan mutane da yawa suka ce ina zan je. Umma ta yi hanzarin faɗin,


     "Dawo ki zauna! Ko za ki ga ƙarshen zalunci da munafukai."


      Na koma na zauna  zuciyata tana suya na dinga sharar hawayen da ban san  lokacin da suka zubo mini ba. Sallamar aka yi a bakin ofishin; ya sa hankalin kowa ya koma bakin ƙofar. Wasu daga cikin dangin Barira ne suka shigo, da Yaya Maimuna sai ƙannen Mukhtar maza. Su ma wuri suka samu suka rakuɓe, kafin shugaban Hukumar ya sa a fara videoting ɗin Mukhtar da Barira. Ana bayanin abin da ya faru da Haidar, da yadda ake so a ji ta bakinsu bayan an gama jin bayanin da ya yi a cikin waya.

      Nan take Likita ya fito da laptop ɗin da ke cikin jakar da ya zo da ita. Aka jona komai normal a ƙatuwar plasma tv'n da ke cikin ofishin, sai ga hoton Haidar a kan gadon Asibitin yana ta fisge-fisge, tare da kwarara ihu cikin muryarsa da ke fitowa raɗau, tana shiga kunnuwan duk wanda ke cikin ɗakin. Bayan dukan luguden da take mini a cikin zuciyata. 


     'Mamahhhh! Don Allah ki zo za su kashe ni! Wayyo maciji zai cinye ni! Maciji! Maciji ne... wayyo Mamata! Idan ba ki zo ba zai cinye ni...'


       Su Umma na hango da Likitan tare da wasu mutane bayan nurses, sun rufu kansa suna ƙoƙarin dannar shi kada ya faɗo daga kan gadon. Likitan ya zare masa ƙarin ruwan da ke jone a hannunsa, cikin sauri Umma ta yi nasarar rungume shi har aka samu ya lafa, sannan ya koma sauke numfashi ɗaiɗaya yana zarar idanuwa. 

       Mintuna a tsakani Likitan ya matso jikinsa ya riƙe hannunsa, cikin sanyin murya ya ce,


 "Me ya sa kake mana ihu!"


      Ya fara dube-duben gefen shi, sannan ya ƙara shigewa jikin Umma yana faɗin,

       'Tsoro suke ba ni. Kullum maciji suke saka mini a cikin riga. Kuma su ce idan ban yi abin da suka saka ni ba za su saka shi ya haɗiye ni da bakinsa. Kuma..kuma ni tsoronsa nake ji, don Allah ku ce su kashe macijin kada ya cinye ni ba na so na mutu....'


    Iya abin da na ji kenan na fashe da kuka wiwi, aka dakatar da videon aka koma ba ni haƙuri. Likitan kusa da ni ya dawo cikin kwantar da kai ya dinga rarrashina cikin siyasa tamkar wata ƙaramar yarinya. Da ƙyar na taushi zuciyata na daina kukan, ban bi ta kan MD ba balle na ga a wane hali yake a lokacin. Har aka sake kunna video'n, inda Likitan ya ƙara tambayarsa su waye suke saka masa macijin. Kai-tsaye ya ce,

       'Amarya da Babanmu ya aura, tare da ƙawayenta su suke saka mini macijin su ce da shi ya haɗiye ni na mutu...Da na faɗa wa Abbanmu ina jin tsoron zama gidan, ya yi ta mini faɗa har ya dake ni, kuma ya ce idan na je wurin Mamata sai  ya yanka ni da wuƙa ya saka ni rami ya rufe ni. Ita ma da ya fita ta ce duk na faɗa wa wani abin yake faruwa, sai ta saka macijin ya fasa cikina ya cinye mini hanji na mutu...' 

      Zumbur ya zabura kamar wani zautacce yana dubin gefe da gefensa, tare ƙanƙame Umma yana ta faɗin,

      'Wayyo macijin ne! Don Allah ku tafi da ni zai cije ni! Mamahhhh!! Wayyo... Innalillahi...ƙulhuwallahu Ahad..Allahussamad...yihhhhhh...ummmmh...'


     Luf ya langaɓe a jikin Umma da ke ƙanƙame da shi tana kuka. Kamar wasa, Lkitan ya karɓe shi cikin tashin hankali ya dinga aune-aune. Can ya koma dannar ƙirjinsa yana hura masa iska ta baki, da hanci har cikin kunnuwansa. Ya dawo taɓa tsintsiyar hannunsa, ya danne da ƙarfi ya kara hannun nasa a kunnen shi. A hankali ya ajiye hannun Haidar, sannan ya saka zanin Umma ya lulluɓe shi. Wurin ya bari kafin mintuna kaɗan duhu ya ziyarci hoton video'n. 

     Kasa ɗauke idona na yi daga kan tv'n, saboda mutuwar zaunen da na yi ba na jin zan iya motsa ko ɗan yatsana. Hawaye ne kawai ke mini zarya wani bayan wani, saboda gabaɗaya zuciyata a rufe take, ba na iya gane komai a lokacin face Haidar da nake gani a idona.

      Girgiza ni na ji an yi sannan na yi firgigit kamar mai barci, kallo na bi Ummata da shi bayan hawayen ya gama ɓalle mini tamkar burgaggen famfo.

      Bayana ta dinga bubbugawa ita ma hawayen suna mata zirya. Video'ting ɗin Barira aka fara yi bayan ganin video'n Haidar, inda mai gabatarwar yake buƙatar ta yi bayanin kanta da matsayinta ga Haidar. Sannan aka buƙaci jin ta bakina, dangane da  abin da ta sani da wanda da ta gani da idonta.

      Idonta fiƙi-fiƙi tana kallon mai video'n tana muzurai. Sai da wani ɗan sanda ya katsa mata tsawa, sannan ta zabura ta fara bayani tana sosa kai.

     "Daman ni ba ni na kawo shawarar a saka shi ba. Aunty Suby ce ta ce mu yi masa haka, tun da shi ba ya iya yi mini komai da dare sai minshari kamar wani rago."


     "Shi waye?"


Tambayar da mutumin ya jefa mata kenan, ta yi hanzarin nuna Mukhtar tana faɗin ga shi nan. Sannan ya ɗora mata da wata tambayar yana cewa,


    "Ita Aunty Subyn tana ina? Kin san gidansu?"


   Ta ce, "E, daman sun taɓa samun matsala da Auntyn shi ya sa ta ce mu yi masa hakan ko za mu rage jin haushin ƙazafin da ta yi mana. Wai mu nuna mata da gaske mu ɗin 'yan iska ne, musamman a lokacin da za ta gano shi ma yaronta ya lalace. Na nuna mata ba zan iya ba kada ya tona mana asiri, ta ce mu ba shi tsoro ta yadda ba zai iya faɗa wa kowa ba."


      "Daga nan sai kuka yi masa me? Sannan ita wacce ta ba ki shawarar daman akwai 'yar tsama tsakaninta da Maman yaron ne?"


      "E, sun taɓa rikici a lokacin da ta zo wurina. Kuma tun daga lokacin ta ci alwashin sai ta nuna mata da gaske ita ɗin tana abin da ta zarge mu da shi. Saboda ta yi niyyar a sace 'yarta Ummu Salma domin ta ɓoye ta, da nufin sai ta ɓata mata rayuwa, sannan ta sa a yi mata allurar barci a jefar da ita inda za a tsince ta. Ni ce na hana ta, saboda ina tsoron Auntyn idan ta gano mu ne muka aikata, don na ga kamar ko shi Romiyon yana tsoron masifarta. Shi ne ta ce da ni wai na cika tsoro da yawa, to a lokacin da zaman Haidar ya dawo gidan; shi ne ta zo da wannan abin da aka yi masa..." 

    

     "Aka yi masa ko kuka yi masa? Ko ita kaɗai ta yi masa ban da ke?""


     Kai ta fara sosaya tana kallona tare da haɗa hannuwanta biyu wuri ɗaya tana faɗin,

  

     "Don Allah Aunty ki yi haƙuri! Wallahi ba da son raina na aikata ba..."


     Ta ƙare maganar da kuka, ni kam ban da tagumin da na yi ina kallon ta; ko motsin kirki na kasa yi saboda jin har da Ummu Salma aka so cutarwa, gabaɗaya imani ya kama ni. Nan take na tuno zancen Subyn a lokacin da muka yi hatsaniya da ita har Yaya Maimuna ta shiga, ranar da na dawo aiki na ji suna masha'arsu ita da Barira. Inda take cewa da ni daidai take da zamanina, don ita ta ci dubu sai ceto. 


     'Waton da gaske ta ci dubun, amma ceton ne ya kasa zo mata a yadda ta yi tsammani, domin ta so su yi ta lalata shi har ya girma. Ta yadda zai taso cikin mugun hali da muguwar ɗabi'a ta ji daɗin cin bulus kamar ko yaushe. Sai ga shi Allah bai yi tsarin a yadda ita ta tsara ba.'


     "Hmmmmmm!"


Tunanin da na gama kenan tare da sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya. Sannan hankalina ya dawo na ji abin da ake tambayarta,


    "To me za ki ce da masu hali irin naki?"


    Tana sharɓar hawayen kuka ta ce,

       "Su ji tsoron Allah su daina, saboda gudun ranar da asirinsu zai tonu su ji kunya. Ko da ba sa tsoron haɗuwa da Allah."


    Wani mugun kallo na aika mata, wanda nake jin kamar na miƙe na yi ta dukanta har sai ta mutu.

       "Bayan ke da ita Subyn da kuke saka shi yana muku abin da kuke so, sai kuma wa? Ko kuma ku kaɗai yake yi wa aikin?"


        "Ba mu kaɗai ba ne, akwai wasu ƙawayenmu biyu da su ma suke zuwa gidan yana yi musu..."


    Babu shiri na zabura, jikina yana tsima na miƙe da nufin isa inda take kamar wata zakanya, cikin sauri Kawu Manu ya riƙe ni, sai jin na yi Ummata tana ihu da kururuwa bayan ta shaƙe wuyan Barira. Da ƙyar aka ɓanɓari Umma daga kanta don ta taushe ta da gwiwowinta biyu, sannan ta riƙe mata maƙogwaro da nufin aikata lahira cikin gaggawa. 

      Kawu Sale ne ya fitar da Umma waje da taimakon wasu, sannan Barira ta fara tari riƙe da wuyanta tana mayar da numfashi ɗaiɗaya. Ni ma zaunen da nake jikina sai ciccira yake yi ina huci, hannun MD riƙe da hannuna ɗaya gam-gam! Alamun ba ya so na tashi ko kuma na yi abin da zuciyata take ƙoƙarin saka ni aikatawa.

     Wurin Mukhtar aka juya, wanda haushin shi da muguwar tsanarsa suka hana ni kallon fuskarsa. Kaina na duƙar ƙasa, saboda jirin da nake ji kamar ƙuguna ba zai juri zaman bencin ba. Can na ji ya fara magana cikin rawar murya kamar ya yi kuka,


     "Babu abin da zance, illa na ba da haƙuri. Saboda ban ji daɗin mutuwar Haidar ba, kuma ban zaci abin da suke saka shi aikatawa ya kai hakan ba. Shi ya sa a lokacin da yake nuna ba ya son zama gidan tsoro yake ji, na ji zafin maganar sosai har na dake shi. A tsammanina wurin mahaifiyarsa yake son komawa shi ya sa ya tsiro da hakan. Domin a gaban idona ita azzalumar da ƙawayenta suke ta nuna masa so da kulawa. Wani lokaci ma har abu suke saya masa ya ci ko ya saka a jikinsa, hakan ya sa nake jin daɗin zuwan da suke yi gidan, suna taya ta hidimarsa. Na zata son tsakani da Allah ne suke yi masa, shi ya sa nake  masa faɗa tare da gindaya masa dokar; duk ya faɗa wa wani yana jin tsoro a gidan sai na yanka shi da wuƙa. Domin ba na so mutane su zargi ana cutar da shi ko, ana yi masa wani abu mara kyau a cikin gidan. Don da a ce na san da wannan ƙullalliyar; wallahi ni da kaina zan ɗauki mummunan mataki tun kafin a kai ga hak..."


    Ya ƙare maganar cikin muryar kuka, kafin shiru ya ratsa tsakani na tsawon mintuna. Wani sabon kuka na fashe da shi, aka shiga rarrashina na yi shiru, amma ban daina tsiyayar ruwan hawaye ba, wani bayan wani nake ji yana sauko mini kan fuskata.

     Mai gabatarwa ya nemi na ce wani abu bayan ya yi bayanin za a ji ta bakina. Amma kukan da nake yi, ya sa MD ya yi masa nuni da hannu a kan a ƙyale ni, sannan ya ce ya goge hoton fuskata da ya fara ɗauka. Babu musu ya ce da shi kada ya damu, ba zai fito da ni a ciki ba, nan take a wurin ya goge guntun video'n da ya ɗauka ina kuka.

     

     Shugaban Hukumar aka umurci jin ta bakinsa, ya yi bayanin case ɗin dalla-dalla. Sannan ya ƙara da cewa,

      '"Hukumar mu, a shirye take domin ta kare haƙƙin waɗanda aka zalunta. Don haka za mu saka wakilanmu, su yi aiki kafaɗa-kafaɗa tare da jami'an tsaro. Domin su binciko duk inda wannan Subyn take da sauran masu ruwa da tsaki a cikin case ɗin. Saboda a gurfanar da su a gaban kuliya, sannan a yanke musu hukunci daidai da laifin kisan yaron, wanda suka zamo silar ajalinsa. Shi kuma mahaifin yaron, tun da gaskiya ta bayyana babu saka hannunsa a cikin abin da aka yi masa; za mu nemi alfarmar hukumar tsaro, domin ta sake shi a bisa sharaɗin zai nemi yafiyar mahaifiyar yaron da danginta. Saboda ya ba da ƙofar da aka cutar da shi, silar rashin kularsa, da rashin saka idonsa a kowane motsin gidansa, domin komai da ya kasance wannan sanadi har mai aukuwa ta auku. Muna fatar wannan abin ya zame masa izina, da ma wasu magidanta masu irin halinsa na sakaci da kiwon 'ya'yan da Allah ya ba mu. Sannan ita matarsa, masu hali irin nata su hankalta su gano duniya ba ta da tabbas. Domin ga ta a hannunmu dumu-dumu da kuma hannun hukuma, kuma za mu yanke mata dukkkan hukuncin da ya dace da laifinta. A ƙarshe hukumarmu ta kare haƙƙin ɗan Adam, muna bai wa Mahaifiyar yaron da danginta haƙuri, tare da yi musu ta'aziyyar yaronsu da suka rasa. Allah ya ƙara ɗora mu a kan daidai, kuma ya hane mu aikata abin da zai zame mana da-na-sani. 


    "Amin"


Kowa ya ce, cikin sanyin jiki, sannan ya ƙara yi wa jami'an godiya, a kan aron su Barira da suka bayar. A gabanmu aka tasa ƙeyar su Barira da Mukhtar suka fice. Ina kallon Mukhtar ta gefen ido, ni da MD sai ƙare mana kallo yake yi ko ƙyaftawa babu. 

      Saboda tun lokacin da na so zuwa wurin Barira Kawu Sale ya hana ni, MD ya taso ya riƙo ni da kansa ya zaunar da ni. Sannan ya saka hannunsa cikin nawa ya matse wuri ɗaya alamun na yi shiru duk da bai ce da ni komai ba. 

      Tun daga lokacin jikina ya ba ni Mukhtar yana ƙare mana kallo, kuma aka yi dace duk na ɗago kai mu yake kallo. Muguwar harara kawai na aika masa, saboda idon mutane ya hana ni zuwa wurinsa na faffala masa mari sai fuskarsa ta tsattsafo jini. Haka ma Likita ina hankalce da sauyin fuskarsa tun lokacin da ya ga MD ya riƙe mini hannu.   

     Ko da muka fito harabar wurin, har 'yan sanda sun tafi da su Barira. Umma da Kawu Sale kawai muka gani zaune suna magana, ganin mu ya sa suka taso suka tarye mu. A nan Likitan ya yi musu bayanin yadda aka ƙarge, MD yana ƙara musu bayanin abin da Likitan ya manta bai faɗa ba.

     Godiya Kawu Sale ya dinga yi musu tare da addu'ar gamawa lafiya. Likita ya matso kusa da ni yana cewa,

     

    "Ki yi haƙuri ki bar komai ga Allah, in sha Allah zan zo har gida na duba jikinki. Ni zan tafi Allah ya ƙara lafiya."


    "Amin" Dukanmu muka ce, sannan ya tayar da motarsa ya fice ma'aikatar. MD ma ya yi gaba zuwa motarsa, muka dafe masa baya, zuciyata sai ƙuna take yi. Jiki babu kuzari na buɗe motar na shiga,  na jingina bayana da seat ɗin kujerar. Jefi-jefi ina sharar ƙwalla har muka isa gida, kai-tsaye na fito motar, ban jira komai ba na shige cikin gida ina ta kukana.

       Su Umma Salma suka yo kaina da murnar gani na, wataƙila fahimtar kukan da nake yi ya sa suka sake ni. Ɗakin Umma na shige tare da faɗawa kan gado ina rera kuka tamkar wata ƙaramar yarinya. Inna Kulu ta shigo da salati tana faɗin,


     "Daman na san muddin kika ga video'n nan; sai aiki ya dawo mana sabo. Don Allah ki daina kukan nan, ga yaranki can kin saka su kukan su ma."


    Su Umma suka shigo ɗakin, su suka dinga ban-baki har na samu kukan ya tsaya mini. Abinci Inna Kulu ta kawo mini, ta ce na daure na ci, sannan na sha maganina. Na ɗan tsakura kaɗan, saboda zuciyata ba ta mini daɗin da zan saki jiki na ci abincin. Maganin na kora sannan na bi gadon Umma na yi luff. Ganin haka ya sa suka fice suka bar ni ni kaɗai,  shigowar saƙo a wayata na ji, na so sharewa, wata zuciyar ta ba ni shawarar dubawa ko da saƙon MD ne.

     Zumbur na miƙe na ɗauko wayar, dubawar farko idona ya yi tozali da sunansa, tare da saƙon da ya so gigita guntun tunanin da ke kaina a lokacin.


     _'Baki ya yi kaɗan ya furta zahirin matsayinki a zuciyata, shi ya sa na zaɓi kalmar shiru a kan na furta abin da zan rage masa martaba, garin yunkurin sanar da ke ainahin yadda na ɗauke ki. Domin a rana ɗaya idan kika nisanta da ni, ina ji tamkar mun yi shekaru dubu ba ma tare, Kin riga kin zama fatar jikina, duk wanda ya raba ni da ke; tamakar ya raba ni da kyawun kwarjinin da ke haɗe da suturata. Ni da ke garkuwar juna ne, masu kare wa juna wasu manyan jiga-jigan matsaloli tari-tari. Ke hasken zuciyoyi ce, shi ya sa aka raɗa miki suna Zaituna. Saboda ki sanyaya rayuka da kamilar baiwarki. Dalilin haka na zaɓi damƙa miki farinciki da annashuwata, domon ki jiyar da ni daɗin da ke cikin tafukan hannunki. Ina ji a raina;  ko kaɗan ba zan iya nisa da ke ba, domin na daɗe da saka wa zuciyata wuya ko daɗi ba zan bar ki ba, duk rintsi. Sai dai idan Allah bai zana ƙaddarar zaman mu wuri ɗaya ba. Duk da ban taɓa ji a raina ko a mafarki za ki bar ni ba, balle ki suɓuce mini. Don haka ki shirya tarbon mijinki, angonki, kuma abokin rayuwarki, a yammacin gobe idan Allah ya kai mu.'_


    _'Ki kasance cikin aminci. Daga ni mijin Zaituna!!!'_




     Cabɗijam!😱






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*AM BACK MY FAN'S😘*


*Yabo da jinjina ga abokan zama nagari masu ƙoƙarin faranta mini ta kowace fuska. Ina alfakhari da samunku kusa da ni gwanayena; DAUGHTER SAFNA SANI JIBIYA, OUM NASS, DAUGHTER A'ISHA D. FULANI, ƘANWATA ASIYA, ƊIYATA UMMU MUHAMMAD. MY AMBASH, NAJIDEDENMU, MY OMEE. Alherin Allah ya ya lulluɓe ku gabaɗaya. Na gode sosai da bajintarku, Ubangiji ya saka muku da mafificin alherinsa👏🏻*



*ASHIRIN DA BIYAR.*


       Jikina ya hau tsima, nan take gumi ya wanke mini fuska. Karanta saƙon nake ta yi ina maimaitawa a cikin zuciyata. Mamaki, ruɗuwa, gigita duka sun kama ni a lokacin. Saboda ban taɓa sanin ya san ta kan soyayya ba, balle kalaman so masu zafi irin haka. 

       Babu shiri na kai zaune har lokacin idanuwana a kan saƙon, saboda tsantsar farincikin da ya lulluɓe mini zuciya. Typing na fara da zummar yi masa reply, domin ya shaida na ga abin da ya turo kuma na karanta. Sai dai inda gizon ke saƙar; duk abin da na rubuta sai na yi kamar na tura masa sai na fasa, a ƙarshe kuma na goge na sake rubuta masa wani. Saboda ganin nake yi kamar bai yi daidai da amsar saƙonsa ba. Kwanciya na yi da wayar a cikina ina nazarin abin da zan rubuta, wanda ba zai gano azarɓaɓina ba, kuma ba zai ga na kasa ba. 

      Dole na tsayar da zuciyata a bisa abin da nake ganin shi ne daidai. Wayar na ɗauka na rubuta masa gajeren reply na tura masa, cike da son fashin baƙi ga manyan zantukan da na ji ya faɗa a cikin rubutunsa.

 

     _'Sir, saƙon nan nawa ne kuwa, ko na amaryarka?'_


     _'Na amaryata ne! Wacce nake da burin zama muhalli ɗaya da ita a cikin ɗan lokaci.'_


Amsar da ya turo mini kenan bayan minti biyu tsakanin fitar saƙon a wayata, da isar shi wurinsa. Haka kawai na tsinci zuciyata da bugawa, tare da zuwan wani sabon farinciki da  kishinsa a lokaci ɗaya sun turnuƙe mini zuciya. Don sunana da na gani a cikin saƙon nasa; bai hana mini jin haushin maganarsa ba. 


    _'Congrats!'_


Iya abin da na tura masa kenan, kafin na miƙe na fara tuɓe kayan jikina da zummar watsa ruwa. Domin na rage jin abubuwan da nake jin sun damƙare mini zuciya. 


'Zuutt!' 


Sautin shigar saƙon da na ji a wayata kenan, kamar kada na duba saboda na san daga shi ne. Amma na kasa haƙura sai da na ɗauka na gane wa idanuwana abin da ya turo.


     _'Thank u so much Bby.'_


   Ido na zaro kamar a gabansa, kafin wata munafukar kunya ta yi mini bargo. Babu shiri na rufe idanuwana tamkar wata sakarai, haka na ajiye wayar a gadon Umma na koma na zauna tare da yin tagumi. Shiru na yi ina maimaita kalmar Bby a raina, har Umma ta shigo ta same ni a haka. 

      Idonta a kaina ta ce, "Har yanzu jikin? Ko kuma damuwar ce kike ƙoƙarin loda wa kanki?"


     Tagumin na cire sannan na girgiza mata kai don maganar ta yi mini nauyi a cikin baki, balle na samu kuzarin furtawa.


     "Kin dai ji abin da Likita ya faɗa kanki, don haka ki yi ƙoƙarin cire damuwar kowa a cikin ranki. Abin da ya faru dai ya faru kuma ba zai goge ba, wanda ya yi nagari don kansa, domin shi sharri ɗan aike ne, ko ya tafi sai ya dawo wurin wanda ya miƙa shi."


    Cikin sanyin jiki na ce, "Haka ne, Allah ya ƙara zama gatanmu gabaɗaya."


     "Amin" Umma ta ce, sannan ta ci gaba da sabgoginta. Ni ma na yunƙura cikin sanyin jiki da na gaɓɓai na fice ɗakin.

       Inna Kulu ta karɓi bokitin da na ɗauka, ta cika mini shi taf da ruwan wanka ta kai mini bayi. Na shiga dirzar jikina ina nazarin sunan Bbyn da MD ya ƙaƙaba mini. 


     'Wai ni ce Baby yau!'


Murmushi ya suɓuce mini tamkar wacce aka yi wa wata bushara. Har na shirya cikin wata doguwar rigar atamfa, ban daina tunanin tsadadden saƙonsa ba. 


    Marece sakaliya, na ji saukar motar Arma ina tsakar gida muna hira da Inna Kulu. Ina taya ta aikin abincin daren da take yi, wanda ta hana ni shiga Kitchen ta bar ni da aikim yanka kuɓewa.


     Su Ummu Salma suka shigo gidan suna cewa Umma ga Auncle A. Da mamaki na bi su da kallon murnar zuwansa da suke yi, sannan sabon sunan da suka raɗa masa, wanda ban san ina ya samo asali ba.

       

     "Je ki ce ya shigo!"


Saƙon da Umma ta bai wa Iman kenan, domin ta faɗa wa Arma da ke ƙofar gida yana jiran tsammani. Nan take na ji raina ya ɓaci, a hankali na dinga yankan kuɓewar, babu kuzarin da na fara yankan da shi a cikin karsashi. 

       Tun kafin mu gan shi sallamarsa ta fara isowa, Inna Kulu ta amsa suka gaisa da shi faram-faram. Ni kam kaina a duƙe ina aikina na gaishe shi muryata a ciki. Umma ma ta fito daga ɗaki suka gaisa, ta yi masa iso har cikin ɗakinta sannan ta fito ta nufo ni.

      Ba ta ce da ni komai ba ta karɓi kwandon kuɓewar da ke saman cinyata ta ajiye gefe. Ta sassauta murya a hankali ta ce,


     "Tashi ki je wurinki ya zo!"


    Kallon ta na yi ido cikin ido, zan yi magana ta yi mini kashedi da ido, babu musu na miƙe ina kakkaɓe jikina da sanyin ruwan da na wanke kuɓewar. Hijabin Inna Kulu da ke kan igiyar shanya na saka, raina babu daɗi na shiga ɗakin Umma na samu wuri na zauna ƙasa. 

      Ban jira komai ba na gaishe shi ba tare da na kai idona inda yake ba balle na ga yanayinsa. Sautin murmushin shi na ji yana tashi a cikin kunnuwana, kafin ya yi gyaran murya ya ce,


     "Alhmdulillah! Jiki ya warware. Ubangiji ya bi da lafiya. Kuma ya jiƙan yaronmu." 


     "Amin Ya Allah!"


Shiru ya ratsa tsakani kafin ya ɗan muskuta ya ce,

     "Abubuwa masu muhimmanci suka kawo ni Zaituna. Na so mun tattauna da ke tun kafin yanzu. Sai ga shi Allah ya  ƙaddara abin da ya faru, wanda ya ja mana tsaikon tafiyar da kullum nake kwana da ita ina tashi."

      Sai da ya ɗan tsahirta sannan ya sake cewa, "Kamar yadda kika san Arma a baya masoyin Zaituna ne, a wannan karon ma ya dawo da ƙoƙon baransa gare ta domin a gudu tare a tsira tare."

      Kaina na ɗago tare da ɗora idanuwana saman fuskarsa, shi ma nasa idon a kaina, ya ɗaga kansa tare da jaddada mini abin da kunnuwana suka ji ya faɗa.


    "Ko a baya, babu macen da na so sama da ke Zaituna. Allah ne bai nufi za mu yi aure tun a lokacin ba, sanadin karatun da nake yi kuma ban ajiye komai ba a lokacin, face biro da takardar da nake yi wa bauta. Dalilin hakan Alhajina ya toshe zancen auren, da na zo masa da zancenki. Yanzu kuma Alhmdulillah! Karana ya kai tsaikon da zan daki ƙirji na ambaci na isa da kaina. Don haka kada ki kalli 'ya'yan da ke gabanki, ki kalle ni a matsayin Armanki na baya, kuma uban Ummu Salma da Iman."


    Gabaɗaya kalamansa sun ɗaure mini jijiyoyin jikina, ta yadda na ji ba zan iya yi masa tsiwa ko nuna masa rashin ƙaunata a fili ba. Saboda mutum ne mai daraja a wurina, wanda ya so ni son da ba ya shayin nuna wa kowa matsayina. Sai dai tazarar da ke tsakanina da shi a lokacin ta rage kaifin alaƙarmu, musamman shi da ba aure ne a gabansa ba lokacin. Saɓanin ni da koyaushe zan iya aure, a matsayina na mace, wacce za a iya yi mata aure da ƙarancin shekaru, kuma kafin ta mallaki hankalin kanta. Hakan ya sa Mukhtar bai sha wuyar samuna ba, domin a lokacin da muka yi aure ma Arma ba ya ƙasar.


     "Ba ki ce komai ba Zaituna! Ina so na ji ta bakinki, domin shi kaɗai ya rage mini a yanzu. Saboda a matse nake da na sake gabatar da manyana da sadakinki, kamar yadda suka zo a farko nema mini izinin zuwa wurinki aka lamunce."


   Zancen da ya yi ya dawo mini da natsuwata, saɓanin tunanin baya da na lula. Ajiyar zuciya na fara saukewa kafin na ce,


     "Haƙiƙa kana da matsayin da ka fi ƙarfin yawo da hankali, ko na faɗa maka wata magana domin na yi maka daɗin baki. Dalilin da ya sa kenan zan sanar da kai farar gaskiya ba tare da na bar ka cikin kokwanto ba. Saboda kai masoyi ne na gaskiya, irin wanda komai nisan tafiya yana waiwayen baya."


     Shiru na yi ina tauna maganganun da nake ƙoƙarin furzarwa daga bakina, cike da tsoron Umma ta ji, ko kuma abin da zai biyo bayan faɗar maganar daga bakina. Amma sanin babu wata mafita sai ta hanyar, hakan ya sa na yi ƙundunbalar sanar da shi abin da na gama kitsawa tare da zuciyata.


    "Haƙiƙa ban da bakin da zan gode maka, balle na nuna maka zallar farincikin da ka zo mini da shi. Illa na yi maka addu'ar fatan alherin dacen mace tagari wacce za ku rufa wa juna asiri..."

      Kallon da ya wurgo mini fuskarsa a hargitse, hakan ya sa na yi hanzarin faɗin,

       

     "E, ina maka fatan mace tagari a ko'ina take. Saboda halin kirkinka ya fi dacewa da mace mai kirki da nagarta."


     "Kin ɗaure mini kai sosai Zaituna, me waɗannan zantukan naki suke nufi? Na kasa tantance matsayar da zan ajiye su. Shin ke ba macen kirkin ba ce, da kike mini fatar ta a wani wuri?"

     Murmushi na yi masa kafin na jefi shi da kallon ba ka san dawan garin ba. Sannan na sassauta muryata a hankali na ce da shi,

     "Kai-tsaye ba zan kira kaina da ta kirkin ba, amma dai na sani ban da munanan halayen da za a ƙi aure na saboda su. Abu ɗaya ne nake so na nusar da kai; aure na da kai kwata-kwata babu matching. Domin idan ban saka son rai da son zuciya ba; zan fito fili na sanar da kai budurwa ya dace ka aura a wannan marra ba bazawara mai 'ya'ya irina ba..."


    "Dakata Zaituna! Ba na son ki shata 'ya'ya ko zawarci a cikin maganarmu. Ina jin tun kafin na zo miki da wannan sifar; na san kin taɓa aure,kuma kina da yara. To ban ga amfanin bitar zancen da; ni da ke duka mun san da shi ba."


    "Ka fahimce ni Arma! Abin nan da kake ƙoƙarin aikatawa zai cutar da mu a gaba. Domin ko da na amince an yi auren; ni da kai duka ba za mu samu natsuwar da kake mana hasashe ba. Dalili kuwa shi ne; kai saurayi ne matashi mai jini a jika, kana da kuɗi kana da ikon auren mace har huɗu ba ɗaya ba. To me zai sa ka ɓuge ga auren bazawara mai haihuwa uku? Shin babu 'yanmata a garin ne? Ko kuwa taimako ne kake ƙoƙarin yi da jihadi?."


     "Kusan duka! Domin tun ranar da na ji labarin abin da ya faru da ke da auren ki; na ji ina kwaɗayin dawo da bara bana. Sannan zancen wasu mata ko 'yanmata; ba su ne a gabana ba, don ina buƙatar su da tuni na daɗe da ajiye mata biyu. Amma Idan dai ni ne ba kya so, ko kuma ba kya hango ni a matsayin miji; to ki yi gaggawar sanar da ni sai na janye. Saboda ba na son yi miki dole, tun da ba zaman wasar yara za mu yi ni da ke ba."


     Cikin sanyin jiki na ce masa, "Rashin so ba zai sa na guje ka ba! Amma tabbas ba zan bari na cutar da kai ba. Na yi alƙawarin zan taya ka addu'ar neman zaɓin Allah, domin ya yi maka zaɓin da ya fi wanda kake ƙoƙarin yi wa kanka."

      Shiru ya ratsa tsakani na ɗan lokaci, kafin ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa ya ce, 

     "Ni zan tafi, amma kada ki yi tsammanin zan daina son ki ko da mun tara ɗiya da jikoki. Ni da ke Ubangiji ya zaɓa abin da ya fi zama alheri. Domin babu wanda ya san inda rana za ta faɗi, domin tabbas ina kan bakana har zuwa lokacin da kika ga ya dace na zamo mijinki."


    Murmushi kawai na yi masa, ya fiddo da kuɗi a aljihunsa ya ajiye saman gadon Umma ya fice. Hannun Iman ya ja suka fice, na raka shi har ƙofar gida zuciyata cike da tausayin shi. Saboda na ga zahirin soyayyata a cikin ƙwayar idonsa, matsala ɗaya ce ta ɓangarena; da na rufe zuciyata ruf da kwaɗo. Ba na ji kuma ba na ganin kowa face MD, soyayyarsa ta rufe mini idon ganin kowa face shi kaɗai. Wanda nake hango shi yana shawagi a cikin farfajiyar birnin zuciyata.


    Leda ya miƙa wa Iman ta yi cikin gida, na dinga ɗaga masa hannu har ya bar ƙofar gidan. Sannan na dawo ciki na taras da Umma da Inna Kulu suna bitar zancen. Wuri na samu na zauna, ina kallon Umma da ke buɗe ledar da Arma ya bai wa Iman. Biscuits da sweet ne iri-iri har da waɗanda ban taɓa gani ba.

       Ganin kayan ya sa na tuno da sunan da na ji sun kira shi a lokacin da ya zo. Ina 'yar dariya na ce da Ummu Salma,


    "Ke kam yaushe ya zamo Auncle ɗinku. Na ji kuna faɗin Auncle A. Sai kace wani sani kuka yi masa kafin yanzu."


    Kafin ta yi magana Inna Kulu ta riga ta da cewa,

     "Ai sabon duka na asibiti ne idan ya je duba ki. Saboda ya yi ƙoƙari sosai a kanki da su, kafin a samu kanki."


    "Mama shi fa ya ce mu dinga kiran shi da sunan. Saboda ya ce shi ne zai aure ki, kuma da mu za ki je gidansa har ya yi mana aure."


     Dariya ta suɓuce mini babu shiri, Inno Kulu ta sake cewa, "Da a ce yana da mata kafin yanzu; da tabbas zai iya ɗawainiyar yara. Amma yanzu kam ta sabon aure ake yi kafin yaran su biyo baya. Allah dai ya zaɓa abin da ya fi alheri."


     Ni da Umma muka ce amin, amma daga haka ba ta sake cewa komai ba. Balle a san inda shirunta ya dosa, sai rabon sweet ɗin take yi ta bai wa yara nasu da Inna Kulu. Sannan ta miƙo mini na zura hannu na karɓa, saboda ba na so na yi wani abin da zai taɓa mata rai a kan abin da ya shafi Arman. Kuɗin da ya ba da ma dubu goma cas ita na damƙa wa su ko ficika ban ɗauka ba.


***

Daren ranar barci na yi ina tunanin zuwan da MD zai yi wurina. Domin ranar Jumu'a ta kama, kuma ina da tabbacin da an sauko daga masallaci zai zo gidan. 

     Hakan ya sa na yi sammakon tashi, zuciyata cike da tunanin yadda zan faɗa wa Umma zuwan shi. Sai ga shi ina tsaka da gyaran ɗakin Umma, na jiyo Kawu Sale yana faɗa wa Umma zuwan shi idan an sauko daga masallacin juma'a.

      Hamdala na yi, sannan na gode wa Allah da ya sa gare shi ta ji zancen ba a bakina ba. Ƙarin farinciki ya kira ni gabanta yana jaddada mini zuwan sa domin na shirya. Sannan ya kawo cefane na kama wa Inna Kulu muka yi masa girki mai suna girki, bayan na haɗa masa drinks kunun aya da na zaƙi. A gefe ɗaya kuma kayan jiƙa maƙoshi irin na mai jan kunne.

     Domin sauran kuɗin account ɗina na zare, na miƙa aka siyo masa duk abin da ya dace. Umma dai kallo ne nata, ba ta ce um ba balle um'umh. Daga ni sai Kawu muke ta zumuɗi duk da ina ƙoƙarin dannewa kada Umma ta gano ni. Sai Inna Kulu da ke taya mu duk inda aka ja bi take yi, babu musu. 

 

     Murje idanuwana na yi, na saki jiki na darzo wanka bayan mun gama aikin. Na shirya cikin sabon kayana da na ɗinka lokacin bikin Barira, na yi kyau sosai a cikin shaddar. Sai dai ban yi wani makeup da yawa ba, saɓanin wancan karon da aka fente mini fuska da hododi kala-kala.

       Daman can ba gwanar kwalliyar nake ba, simple makeup nake yi koyaushe. Lips gloves da hoda sun wadatar da ni, sai an yi dace nake ɗan zirara kwalli a idona. Yanzun ma shi na yi sha'awar gogawa wa idona, sai ga shi ya fito raɗau cikin ƙwayar idon nawa tarwai. 

     A madubi na dubi kaina ma sha Allah sharr da ni, bayan na yi ɓarin turaruka a jikina tamkar da gayya.

     Nan take ɗakin Umma ya ɗauki ƙamshi, abin mamaki sai ga ta ta shigo ɗakin tana haɗe fuska. Idonta a kaina tana mini wani kalar kallo cike da son ƙorafi, sai ga Kawu ya shigo yana faɗin,


    "Ki dai shirya yana kan hanya yanzun nan!"


    Umma ta yi masa wani kallo sannan ta ce, "Na rasa wanda ya fi wani rawar kai a tsakaninku. Tun safe kun addabi mutane da zance ɗaya sai ka ce abin da ba a taɓa gani ba. To ka dai faɗa mata; haramcin shafa turare ga namijin da ba muharraminta ba. Tun da ita zaƙin soyayya ya sa ta manta da sanin Allah."


     "Idan ma ta shafa ai ba laifi ta yi ba. Ke ƙaro wani har bayanki ki goga, idan ta kama ma ki barbaɗa shi har cikin gashin kanki."





     To fa!😳😂🏃🏻‍♀️




Ku yi haƙuri da ji na  shiru kwana  biyu,, wayata ce ta lalace, amma yanzu komai normal. Sai dai na so sai na gama sabgogin gabana kafin na dawo muku dindindin. Yawan neman da kuke yi, da masu ƙorafi a kan rashin motsina. Ya sa na dawo ba don na kammala uzurina ba, don haka ban yi alƙawarin posting kullum ba, sai lokutan da na samu kaina sannan za ku ji ni. Alƙawari ɗaya na ji zan iya yi; update sau uku a cikin sati har zuwa lokacin da zan ƙare rubutun gasar da nake yi. Fatan alheri gare ku koyaushe👏🏻 luv u all💖








D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*AM BACK MY FAN'S😘*


*Yabo da jinjina ga abokan zama nagari masu ƙoƙarin faranta mini ta kowace fuska. Ina alfakhari da samunku kusa da ni gwanayena; DAUGHTER SAFNA SANI JIBIYA, OUM NASS, DAUGHTER A'ISHA D. FULANI, ƘANWATA ASIYA, ƊIYATA UMMU MUHAMMAD. MY AMBASH, NAJIDEDENMU, MY OMEE. Alherin Allah ya ya lulluɓe ku gabaɗaya. Na gode sosai da bajintarku, Ubangiji ya saka muku da mafificin alherinsa👏🏻*



*ASHIRIN DA BIYAR.*


       Jikina ya hau tsima, nan take gumi ya wanke mini fuska. Karanta saƙon nake ta yi ina maimaitawa a cikin zuciyata. Mamaki, ruɗuwa, gigita duka sun kama ni a lokacin. Saboda ban taɓa sanin ya san ta kan soyayya ba, balle kalaman so masu zafi irin haka. 

       Babu shiri na kai zaune har lokacin idanuwana a kan saƙon, saboda tsantsar farincikin da ya lulluɓe mini zuciya. Typing na fara da zummar yi masa reply, domin ya shaida na ga abin da ya turo kuma na karanta. Sai dai inda gizon ke saƙar; duk abin da na rubuta sai na yi kamar na tura masa sai na fasa, a ƙarshe kuma na goge na sake rubuta masa wani. Saboda ganin nake yi kamar bai yi daidai da amsar saƙonsa ba. Kwanciya na yi da wayar a cikina ina nazarin abin da zan rubuta, wanda ba zai gano azarɓaɓina ba, kuma ba zai ga na kasa ba. 

      Dole na tsayar da zuciyata a bisa abin da nake ganin shi ne daidai. Wayar na ɗauka na rubuta masa gajeren reply na tura masa, cike da son fashin baƙi ga manyan zantukan da na ji ya faɗa a cikin rubutunsa.

 

     _'Sir, saƙon nan nawa ne kuwa, ko na amaryarka?'_


     _'Na amaryata ne! Wacce nake da burin zama muhalli ɗaya da ita a cikin ɗan lokaci.'_


Amsar da ya turo mini kenan bayan minti biyu tsakanin fitar saƙon a wayata, da isar shi wurinsa. Haka kawai na tsinci zuciyata da bugawa, tare da zuwan wani sabon farinciki da  kishinsa a lokaci ɗaya sun turnuƙe mini zuciya. Don sunana da na gani a cikin saƙon nasa; bai hana mini jin haushin maganarsa ba. 


    _'Congrats!'_


Iya abin da na tura masa kenan, kafin na miƙe na fara tuɓe kayan jikina da zummar watsa ruwa. Domin na rage jin abubuwan da nake jin sun damƙare mini zuciya. 


'Zuutt!' 


Sautin shigar saƙon da na ji a wayata kenan, kamar kada na duba saboda na san daga shi ne. Amma na kasa haƙura sai da na ɗauka na gane wa idanuwana abin da ya turo.


     _'Thank u so much Bby.'_


   Ido na zaro kamar a gabansa, kafin wata munafukar kunya ta yi mini bargo. Babu shiri na rufe idanuwana tamkar wata sakarai, haka na ajiye wayar a gadon Umma na koma na zauna tare da yin tagumi. Shiru na yi ina maimaita kalmar Bby a raina, har Umma ta shigo ta same ni a haka. 

      Idonta a kaina ta ce, "Har yanzu jikin? Ko kuma damuwar ce kike ƙoƙarin loda wa kanki?"


     Tagumin na cire sannan na girgiza mata kai don maganar ta yi mini nauyi a cikin baki, balle na samu kuzarin furtawa.


     "Kin dai ji abin da Likita ya faɗa kanki, don haka ki yi ƙoƙarin cire damuwar kowa a cikin ranki. Abin da ya faru dai ya faru kuma ba zai goge ba, wanda ya yi nagari don kansa, domin shi sharri ɗan aike ne, ko ya tafi sai ya dawo wurin wanda ya miƙa shi."


    Cikin sanyin jiki na ce, "Haka ne, Allah ya ƙara zama gatanmu gabaɗaya."


     "Amin" Umma ta ce, sannan ta ci gaba da sabgoginta. Ni ma na yunƙura cikin sanyin jiki da na gaɓɓai na fice ɗakin.

       Inna Kulu ta karɓi bokitin da na ɗauka, ta cika mini shi taf da ruwan wanka ta kai mini bayi. Na shiga dirzar jikina ina nazarin sunan Bbyn da MD ya ƙaƙaba mini. 


     'Wai ni ce Baby yau!'


Murmushi ya suɓuce mini tamkar wacce aka yi wa wata bushara. Har na shirya cikin wata doguwar rigar atamfa, ban daina tunanin tsadadden saƙonsa ba. 


    Marece sakaliya, na ji saukar motar Arma ina tsakar gida muna hira da Inna Kulu. Ina taya ta aikin abincin daren da take yi, wanda ta hana ni shiga Kitchen ta bar ni da aikim yanka kuɓewa.


     Su Ummu Salma suka shigo gidan suna cewa Umma ga Auncle A. Da mamaki na bi su da kallon murnar zuwansa da suke yi, sannan sabon sunan da suka raɗa masa, wanda ban san ina ya samo asali ba.

       

     "Je ki ce ya shigo!"


Saƙon da Umma ta bai wa Iman kenan, domin ta faɗa wa Arma da ke ƙofar gida yana jiran tsammani. Nan take na ji raina ya ɓaci, a hankali na dinga yankan kuɓewar, babu kuzarin da na fara yankan da shi a cikin karsashi. 

       Tun kafin mu gan shi sallamarsa ta fara isowa, Inna Kulu ta amsa suka gaisa da shi faram-faram. Ni kam kaina a duƙe ina aikina na gaishe shi muryata a ciki. Umma ma ta fito daga ɗaki suka gaisa, ta yi masa iso har cikin ɗakinta sannan ta fito ta nufo ni.

      Ba ta ce da ni komai ba ta karɓi kwandon kuɓewar da ke saman cinyata ta ajiye gefe. Ta sassauta murya a hankali ta ce,


     "Tashi ki je wurinki ya zo!"


    Kallon ta na yi ido cikin ido, zan yi magana ta yi mini kashedi da ido, babu musu na miƙe ina kakkaɓe jikina da sanyin ruwan da na wanke kuɓewar. Hijabin Inna Kulu da ke kan igiyar shanya na saka, raina babu daɗi na shiga ɗakin Umma na samu wuri na zauna ƙasa. 

      Ban jira komai ba na gaishe shi ba tare da na kai idona inda yake ba balle na ga yanayinsa. Sautin murmushin shi na ji yana tashi a cikin kunnuwana, kafin ya yi gyaran murya ya ce,


     "Alhmdulillah! Jiki ya warware. Ubangiji ya bi da lafiya. Kuma ya jiƙan yaronmu." 


     "Amin Ya Allah!"


Shiru ya ratsa tsakani kafin ya ɗan muskuta ya ce,

     "Abubuwa masu muhimmanci suka kawo ni Zaituna. Na so mun tattauna da ke tun kafin yanzu. Sai ga shi Allah ya  ƙaddara abin da ya faru, wanda ya ja mana tsaikon tafiyar da kullum nake kwana da ita ina tashi."

      Sai da ya ɗan tsahirta sannan ya sake cewa, "Kamar yadda kika san Arma a baya masoyin Zaituna ne, a wannan karon ma ya dawo da ƙoƙon baransa gare ta domin a gudu tare a tsira tare."

      Kaina na ɗago tare da ɗora idanuwana saman fuskarsa, shi ma nasa idon a kaina, ya ɗaga kansa tare da jaddada mini abin da kunnuwana suka ji ya faɗa.


    "Ko a baya, babu macen da na so sama da ke Zaituna. Allah ne bai nufi za mu yi aure tun a lokacin ba, sanadin karatun da nake yi kuma ban ajiye komai ba a lokacin, face biro da takardar da nake yi wa bauta. Dalilin hakan Alhajina ya toshe zancen auren, da na zo masa da zancenki. Yanzu kuma Alhmdulillah! Karana ya kai tsaikon da zan daki ƙirji na ambaci na isa da kaina. Don haka kada ki kalli 'ya'yan da ke gabanki, ki kalle ni a matsayin Armanki na baya, kuma uban Ummu Salma da Iman."


    Gabaɗaya kalamansa sun ɗaure mini jijiyoyin jikina, ta yadda na ji ba zan iya yi masa tsiwa ko nuna masa rashin ƙaunata a fili ba. Saboda mutum ne mai daraja a wurina, wanda ya so ni son da ba ya shayin nuna wa kowa matsayina. Sai dai tazarar da ke tsakanina da shi a lokacin ta rage kaifin alaƙarmu, musamman shi da ba aure ne a gabansa ba lokacin. Saɓanin ni da koyaushe zan iya aure, a matsayina na mace, wacce za a iya yi mata aure da ƙarancin shekaru, kuma kafin ta mallaki hankalin kanta. Hakan ya sa Mukhtar bai sha wuyar samuna ba, domin a lokacin da muka yi aure ma Arma ba ya ƙasar.


     "Ba ki ce komai ba Zaituna! Ina so na ji ta bakinki, domin shi kaɗai ya rage mini a yanzu. Saboda a matse nake da na sake gabatar da manyana da sadakinki, kamar yadda suka zo a farko nema mini izinin zuwa wurinki aka lamunce."


   Zancen da ya yi ya dawo mini da natsuwata, saɓanin tunanin baya da na lula. Ajiyar zuciya na fara saukewa kafin na ce,


     "Haƙiƙa kana da matsayin da ka fi ƙarfin yawo da hankali, ko na faɗa maka wata magana domin na yi maka daɗin baki. Dalilin da ya sa kenan zan sanar da kai farar gaskiya ba tare da na bar ka cikin kokwanto ba. Saboda kai masoyi ne na gaskiya, irin wanda komai nisan tafiya yana waiwayen baya."


     Shiru na yi ina tauna maganganun da nake ƙoƙarin furzarwa daga bakina, cike da tsoron Umma ta ji, ko kuma abin da zai biyo bayan faɗar maganar daga bakina. Amma sanin babu wata mafita sai ta hanyar, hakan ya sa na yi ƙundunbalar sanar da shi abin da na gama kitsawa tare da zuciyata.


    "Haƙiƙa ban da bakin da zan gode maka, balle na nuna maka zallar farincikin da ka zo mini da shi. Illa na yi maka addu'ar fatan alherin dacen mace tagari wacce za ku rufa wa juna asiri..."

      Kallon da ya wurgo mini fuskarsa a hargitse, hakan ya sa na yi hanzarin faɗin,

       

     "E, ina maka fatan mace tagari a ko'ina take. Saboda halin kirkinka ya fi dacewa da mace mai kirki da nagarta."


     "Kin ɗaure mini kai sosai Zaituna, me waɗannan zantukan naki suke nufi? Na kasa tantance matsayar da zan ajiye su. Shin ke ba macen kirkin ba ce, da kike mini fatar ta a wani wuri?"

     Murmushi na yi masa kafin na jefi shi da kallon ba ka san dawan garin ba. Sannan na sassauta muryata a hankali na ce da shi,

     "Kai-tsaye ba zan kira kaina da ta kirkin ba, amma dai na sani ban da munanan halayen da za a ƙi aure na saboda su. Abu ɗaya ne nake so na nusar da kai; aure na da kai kwata-kwata babu matching. Domin idan ban saka son rai da son zuciya ba; zan fito fili na sanar da kai budurwa ya dace ka aura a wannan marra ba bazawara mai 'ya'ya irina ba..."


    "Dakata Zaituna! Ba na son ki shata 'ya'ya ko zawarci a cikin maganarmu. Ina jin tun kafin na zo miki da wannan sifar; na san kin taɓa aure,kuma kina da yara. To ban ga amfanin bitar zancen da; ni da ke duka mun san da shi ba."


    "Ka fahimce ni Arma! Abin nan da kake ƙoƙarin aikatawa zai cutar da mu a gaba. Domin ko da na amince an yi auren; ni da kai duka ba za mu samu natsuwar da kake mana hasashe ba. Dalili kuwa shi ne; kai saurayi ne matashi mai jini a jika, kana da kuɗi kana da ikon auren mace har huɗu ba ɗaya ba. To me zai sa ka ɓuge ga auren bazawara mai haihuwa uku? Shin babu 'yanmata a garin ne? Ko kuwa taimako ne kake ƙoƙarin yi da jihadi?."


     "Kusan duka! Domin tun ranar da na ji labarin abin da ya faru da ke da auren ki; na ji ina kwaɗayin dawo da bara bana. Sannan zancen wasu mata ko 'yanmata; ba su ne a gabana ba, don ina buƙatar su da tuni na daɗe da ajiye mata biyu. Amma Idan dai ni ne ba kya so, ko kuma ba kya hango ni a matsayin miji; to ki yi gaggawar sanar da ni sai na janye. Saboda ba na son yi miki dole, tun da ba zaman wasar yara za mu yi ni da ke ba."


     Cikin sanyin jiki na ce masa, "Rashin so ba zai sa na guje ka ba! Amma tabbas ba zan bari na cutar da kai ba. Na yi alƙawarin zan taya ka addu'ar neman zaɓin Allah, domin ya yi maka zaɓin da ya fi wanda kake ƙoƙarin yi wa kanka."

      Shiru ya ratsa tsakani na ɗan lokaci, kafin ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa ya ce, 

     "Ni zan tafi, amma kada ki yi tsammanin zan daina son ki ko da mun tara ɗiya da jikoki. Ni da ke Ubangiji ya zaɓa abin da ya fi zama alheri. Domin babu wanda ya san inda rana za ta faɗi, domin tabbas ina kan bakana har zuwa lokacin da kika ga ya dace na zamo mijinki."


    Murmushi kawai na yi masa, ya fiddo da kuɗi a aljihunsa ya ajiye saman gadon Umma ya fice. Hannun Iman ya ja suka fice, na raka shi har ƙofar gida zuciyata cike da tausayin shi. Saboda na ga zahirin soyayyata a cikin ƙwayar idonsa, matsala ɗaya ce ta ɓangarena; da na rufe zuciyata ruf da kwaɗo. Ba na ji kuma ba na ganin kowa face MD, soyayyarsa ta rufe mini idon ganin kowa face shi kaɗai. Wanda nake hango shi yana shawagi a cikin farfajiyar birnin zuciyata.


    Leda ya miƙa wa Iman ta yi cikin gida, na dinga ɗaga masa hannu har ya bar ƙofar gidan. Sannan na dawo ciki na taras da Umma da Inna Kulu suna bitar zancen. Wuri na samu na zauna, ina kallon Umma da ke buɗe ledar da Arma ya bai wa Iman. Biscuits da sweet ne iri-iri har da waɗanda ban taɓa gani ba.

       Ganin kayan ya sa na tuno da sunan da na ji sun kira shi a lokacin da ya zo. Ina 'yar dariya na ce da Ummu Salma,


    "Ke kam yaushe ya zamo Auncle ɗinku. Na ji kuna faɗin Auncle A. Sai kace wani sani kuka yi masa kafin yanzu."


    Kafin ta yi magana Inna Kulu ta riga ta da cewa,

     "Ai sabon duka na asibiti ne idan ya je duba ki. Saboda ya yi ƙoƙari sosai a kanki da su, kafin a samu kanki."


    "Mama shi fa ya ce mu dinga kiran shi da sunan. Saboda ya ce shi ne zai aure ki, kuma da mu za ki je gidansa har ya yi mana aure."


     Dariya ta suɓuce mini babu shiri, Inno Kulu ta sake cewa, "Da a ce yana da mata kafin yanzu; da tabbas zai iya ɗawainiyar yara. Amma yanzu kam ta sabon aure ake yi kafin yaran su biyo baya. Allah dai ya zaɓa abin da ya fi alheri."


     Ni da Umma muka ce amin, amma daga haka ba ta sake cewa komai ba. Balle a san inda shirunta ya dosa, sai rabon sweet ɗin take yi ta bai wa yara nasu da Inna Kulu. Sannan ta miƙo mini na zura hannu na karɓa, saboda ba na so na yi wani abin da zai taɓa mata rai a kan abin da ya shafi Arman. Kuɗin da ya ba da ma dubu goma cas ita na damƙa wa su ko ficika ban ɗauka ba.


***

Daren ranar barci na yi ina tunanin zuwan da MD zai yi wurina. Domin ranar Jumu'a ta kama, kuma ina da tabbacin da an sauko daga masallaci zai zo gidan. 

     Hakan ya sa na yi sammakon tashi, zuciyata cike da tunanin yadda zan faɗa wa Umma zuwan shi. Sai ga shi ina tsaka da gyaran ɗakin Umma, na jiyo Kawu Sale yana faɗa wa Umma zuwan shi idan an sauko daga masallacin juma'a.

      Hamdala na yi, sannan na gode wa Allah da ya sa gare shi ta ji zancen ba a bakina ba. Ƙarin farinciki ya kira ni gabanta yana jaddada mini zuwan sa domin na shirya. Sannan ya kawo cefane na kama wa Inna Kulu muka yi masa girki mai suna girki, bayan na haɗa masa drinks kunun aya da na zaƙi. A gefe ɗaya kuma kayan jiƙa maƙoshi irin na mai jan kunne.

     Domin sauran kuɗin account ɗina na zare, na miƙa aka siyo masa duk abin da ya dace. Umma dai kallo ne nata, ba ta ce um ba balle um'umh. Daga ni sai Kawu muke ta zumuɗi duk da ina ƙoƙarin dannewa kada Umma ta gano ni. Sai Inna Kulu da ke taya mu duk inda aka ja bi take yi, babu musu. 

 

     Murje idanuwana na yi, na saki jiki na darzo wanka bayan mun gama aikin. Na shirya cikin sabon kayana da na ɗinka lokacin bikin Barira, na yi kyau sosai a cikin shaddar. Sai dai ban yi wani makeup da yawa ba, saɓanin wancan karon da aka fente mini fuska da hododi kala-kala.

       Daman can ba gwanar kwalliyar nake ba, simple makeup nake yi koyaushe. Lips gloves da hoda sun wadatar da ni, sai an yi dace nake ɗan zirara kwalli a idona. Yanzun ma shi na yi sha'awar gogawa wa idona, sai ga shi ya fito raɗau cikin ƙwayar idon nawa tarwai. 

     A madubi na dubi kaina ma sha Allah sharr da ni, bayan na yi ɓarin turaruka a jikina tamkar da gayya.

     Nan take ɗakin Umma ya ɗauki ƙamshi, abin mamaki sai ga ta ta shigo ɗakin tana haɗe fuska. Idonta a kaina tana mini wani kalar kallo cike da son ƙorafi, sai ga Kawu ya shigo yana faɗin,


    "Ki dai shirya yana kan hanya yanzun nan!"


    Umma ta yi masa wani kallo sannan ta ce, "Na rasa wanda ya fi wani rawar kai a tsakaninku. Tun safe kun addabi mutane da zance ɗaya sai ka ce abin da ba a taɓa gani ba. To ka dai faɗa mata; haramcin shafa turare ga namijin da ba muharraminta ba. Tun da ita zaƙin soyayya ya sa ta manta da sanin Allah."


     "Idan ma ta shafa ai ba laifi ta yi ba. Ke ƙaro wani har bayanki ki goga, idan ta kama ma ki barbaɗa shi har cikin gashin kanki."





     To fa!😳😂🏃🏻‍♀️




Ku yi haƙuri da ji na  shiru kwana  biyu,, wayata ce ta lalace, amma yanzu komai normal. Sai dai na so sai na gama sabgogin gabana kafin na dawo muku dindindin. Yawan neman da kuke yi, da masu ƙorafi a kan rashin motsina. Ya sa na dawo ba don na kammala uzurina ba, don haka ban yi alƙawarin posting kullum ba, sai lokutan da na samu kaina sannan za ku ji ni. Alƙawari ɗaya na ji zan iya yi; update sau uku a cikin sati har zuwa lokacin da zan ƙare rubutun gasar da nake yi. Fatan alheri gare ku koyaushe👏🏻 luv u all💖








D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


  _*Alhamdulillah! Na gode wa Allah da ya nuna mini wannan rana. Wacce na dawo bakin aiki gadan-gadan domin mu cinye taliyar da muka fara dafawa. Ina godiya sosai gare ku masu bibiyar littafin a kowace nahiya. Ina miƙa ɗinbin gaisuwa gare ku duka, saboda jin daɗin neman da kuke yi mini ruwa ƙoƙo sanadin wannan littafi. Masu kira a waya, masu turo saƙonni; duka ina yi muku ban gajiya. Alherin Allah ya yi muku rumfa a cikin kowane takun tafiyarku. Barka da sallah dukanku, Allah ya nuna mana wata shekarar lafiya.👏🏻*_


*ASHIRIN DA SHIDA.*


      Baki Umma ta buɗe har da riƙe haɓa, ga dukkan alamu zancen Kawu ba ƙaramin girgiza ta ya yi ba. Domin yanayin da take bin mu da kallo daga ni har shi ya nuna zahirin zallar mamakin umarnin da Kawun yake ba ni. 

       "Hu'umm! Lalle Sale abin naka ya wuce dokar Allah! Yanzu kai da kanka kake zancen ta zuba turare har cikin kai? To shi kenan, idan ta je ka ce ta cire ɗankwalinta ta dunguna masa kan ga bakinsa ya yi lasar turaren tun da abinci n..."


     "Wai ke Habi mene ne matsalarki a ciki? Kin yi lokacinki kuma ki ce za ki hana wasu rawar gaban hantsi?"


     "Ni dai faɗar gaskiya ne nawa! Tun da kai ma ka bi sawun Yarima kun fara shan kiɗan tare; zan zuba maka ido daga kai har ita, sai ka kwaɓe riga ku tiƙi rawar tare."


    "To ki zamo 'yar kallo kawai. Don wata rawar ta fi ƙarfin rawa sai dai a rausaya kai, a koma kaɗa ƙafafuwa. Ke Zaituna yi sauri ki kimtsa! Ki ƙara hoda da kwalli, kuma idan ya zo ni na ce ki masa fari da ido, don ranar bikin balbela; hankaka ba gayyar ta ake ba!"

      Dariyar da nake ƙumshewa ce ta fito fili babu shiri, saboda zancen Kawu da kallon da Umma ta bi shi da shi baki sake, har ya fice gidan. Sannan ta ɗora idanuwanta a kan fuskar Inna da ke tsaye tana dariyar ita ma, cike da jimami a cikin muryarta ta ce,


     "Kulu ko kin san wani abu dangane azarɓaɓin nan na Sale a kan wannan mutumin? Jikina ya fara sanyi fa! Saboda ina tsoron a haifi ɗan da babu idanu ni da shi idan rana ta ɓatar mana."

      Ƙirjina na ji ya buga dam-dam! Saboda zancen Umma da amsar da na ji Inna Kulu ta bayar. Wacce ta saka ni zama gefen gado ina juya zancen Innar a raina, da nazarin inda ya sa gaba.


      'Ko ma mene ne Habi; mu dai alheri muke roƙo. Idan ya amsa kuma sai mu bi su da addu'a!'


    Dirin saukar motar da na ji a ƙofar gidan; jikina ya ba ni MD ne ya zo. Ƙirjina ya shiga dakan lugude, sai dai hakan bai hana ni sauraron maganar da Umma take yi ba.

      "Wannan magana mai ɗauke da harshen damo fa Kulu? Ni fa ina tsoron Allah, ina tsoron Sale a wasu lokutan. Saboda nuna minin da yake yi ya fi ni sanin ta kan zaman duniya, kullum kallon ƙaramar yarinya yake yi mini. Amma tun da ya ce na zama 'yar kallo; zan zama, sai dai idan na ga abin zai wuce gona da iri zan tanka. Domin ba zan zuba musu ido su jangwalo mana abin magana b..."


     "Idan kin gama mitar; ga shi nan ya zo zai shigo ku gaisa."


    Abin da Kawu Sale ya faɗa kenan, duk da ba na ganin fuskarsa daga cikin ɗakin; amma yanayin muryar da ya yi amfani da ita wurin maganar ya sa na fahimci kamar ransa a ɓace yake. 

      Da sauri Umma ta faɗo ɗakin ta rarumi Hijabi ta saka, sannan ta nemi wuri ta zauna kan gado. Kallon ta na yi cike da mamakin zaman da ta yi, maimakon ta fita tsakar gidan a inda na hango Inna Kulu tana shimfiɗa sabuwar tabarma. 


    Sallamar MD da na jiyo; ta sa babu shiri na duƙar da kaina, saboda muryarsa ta sa na ji wani yarr a jikina. Kawu ya leƙo ɗakin yana faɗin, 


    "Habi ki fito ku gaisa!"


Tsam ta miƙe fuskarta babu yabo babu fallasa ta fice ɗakin, fuskarta ɗauke da murmushin da kallo ɗaya na gano yaƙe ne take yi. Daga cikin ɗakin ina jin gaisuwar da suke yi cikin mutumta juna. Mintuna a tsakani na ji Kawu yana faɗin. 


    "Ai ba sai ka fita ba, biyo ta ƙofar cikin gidan kawai tun da ka shigo."


     Ta ƙofar ɗakin Umma ya bi nan take ƙamshin turarensa ya daki hancina. Numfashi na ja kafin na lumshe ido, saboda shauƙin son shi ya fara tsima zuciyata. Shiru kawai na yi jikina gabaɗaya ya mutu, saboda wata sabuwar kasalar da ta sauko mini.  


     "Ina kike? Ke fito ke yake jira fa!"


    Zancen Kawu kenan, wanda ya sa na miƙe cike da jin kunya na fara gyara mayafina. Sannan na fito daga ɗakin kaina a ƙasa cike da jin nauyin haɗa ido da su Umma. Kamar ba ni ce nake ta zumuɗin zuwansa ba tun safiya har zuwa lokacin.

     Saboda zantukan su Umma ya sa jikina ya yi sanyi, musamman da nawa hasashen ya fara hasko mini alamar tambayar da Umma ta ɗora a kan Kawu da maganar Inna Kulu. 


     Har zan wuce ta gaban su Umma da ke kan tabarma; Na canza shawara na dawo na durƙusa har ƙasa na ce mata,


     "Umma zan tafi."


Kallon da ta wurgo mini ya sa na miƙe jikina yana rawa ina sosa kai. Tsaye na yi a wurin kamar an dasa ni, har zuwa lokacin da Kawu ya fito daga ɗakin Inna Kulu yana faɗin,


    "Wai ke me kike jira da ba ki tafi ba har yanzu?"


    Na kai kallona a kan fuskar Umma, Inna Kulu ta yi mini magana da ido a kan na tafi kawai. Sum-sum na wuce ko waigen ta ban yi ba, ballantana idanuwan Umma su ƙara tsoratar da ni. 

    Bakin ƙofar na ja na tsaya ina mayar da numfashi har na samu ya daidaita. Sannan na yaye labulen ɗakin na Kawu da guntuwar sallamata a baki na shiga. Idanuwana a ƙasa na samu wuri na zauna ba tare da na bari mun haɗa ido ba. 

     Mintuna a tsakani na yi jarumtar ɗaga kaina da niyyar gaishe shi, saboda na san halinsa wataƙila ni yake jiran na fara gaishe shi, kafin ya yi mini magana. A hankali na wurga idanuwana a gefen da yake, nan take a raina na ce,

   

    'Ma sha Allah!'


Saboda yanayin shigarsa ta burge ni, kuma sosai ya yaƙi zuciyata da shigar manyan kayan da ya yi. Domin ban taɓa ganin shi da irinta ba tun da na fara aiki wurinsu tsawon shekara da rabi. Farar shadda ce ƙal ta sha aiki ga babbar rigar tun daga sama har ƙasa. Sannan fatar agogon da ke tsintsiyar hannunsa baƙa ta fito da gayunsa, kansa ɗauke da hula zanna bukar, wacce aka yi wa adon aikin da fiye da rabin ta zare baki ne. Na gano haka tun daga kallon farko da na yi ƙoƙarin yi masa, kafin na sauke idanuwana ƙasan ledar da ke shimfiɗe a tsakiyar ɗakin Kawu.


    Saboda kallon da yake jefo mini ya sa na ji ƙirjina ya hau bugawa. Wanda nake jin duk bugun da yake yi tare da harafin sunansa yake tafiya.  

     Tsam ya miƙe daga mazauninsa zuwa inda nake ya ja ya tsaya a gabana. Ƙamshin turarensa ya shiga luguiguitar da zuciyata, rintse idanuwana na yi cikin sauri saboda ni kaɗai na san abin da nake ji a lokacin.  Kafin na tantance na ji numfashinsa gaf da fuskata, babu shiri na buɗe idanuwana saboda mamakinsa ya kusa daskare mini ruwan jiki. 

     Tsugunno ya yi gabana yana aiko mini wani siririn murmushin da ya ƙara fito da zatin haibarsa. 


     "I luv u!"


Ita ce kalmar da ya fara furta mini tun lokacin da na shiga ɗakin har zuwa lokacin. Manejin kallona na ƙure a kan fuskarsa,  domin mamakinsa ya hana ni furta komai, face kallon ido cikin idon da muke aika wa juna saƙonnin zuci.


     Hawaye na ji ya fara gangaro mini a kan dandamalin fuskata, waɗanda ban san lokacin da suka taru ba ballantana dalilin zuwansu. Hannu ya saka ya fara share mini hawayen yana girgiza mini kai ba tare da ya yi magana ba.

     Lallausan hannuwansa biyu ya saka ya tallafo fuskata, saiti da goshina ya kai bakinsa babu shiri na zabura. Saboda wani siririn kiss da ya kai mini a goshin, wanda ya sa na ji gabaɗaya tsikar jikina ta tashi yarr. Bakina ya nufa gadan-gadan yana ƙoƙarin kai bakinsa, na yi hanzarin kawar da kai tare da jan jikina baya ina ɓata fuska.

     Hannuwana biyu ya riƙe, ido cikin ido muke kallon juna saboda na kasa furta ko kalma ɗaya. Illa jikina da yake ta rawa, domin gabaɗaya wata muguwar sha'awa ta taso mini. 

 

      'Hasbunallahu wa ni'imal wakil!' 

    

    Ita ce kalmar da na furta a zuciyata cikin sauri, saboda na samu natsuwata ta dawo tun kafin na bayar da kaina gabansa ya gano ni. Shi ya fara miƙewa sannan ya miƙar da ni tsaye riƙe da hannuna yana aika mini wani munafukin kallo tun daga samana har ƙasana. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya ce, 

    "Kina da kyawu Zaituna! Na yi sa'ar samun mace ɗaya tamkar da goma. Ki daina kuka kina ɓata mini kwalliya, kuma ki kwantar da hankalinki Aliyu naki ne halas malas. Babu mai miki ɗan kallo ballantana ta yi miki ƙwacen abincin ruhinki."

     Wani kalar kallo na yi masa cike da jin nauyinsa na fara ƙoƙarin ƙwace hannuna da ke cikin nasa. Saboda ban san wace kalma zan faɗa ba, ballantana na wanke kaina daga muguwar cafkar da ya yi wa lagona. Zare hannuwana na yi a hankali na juya da nufin barin wurin, ya yi hanzarin dawo da ni na faɗa jikinsa. Rungume ni ya yi tsantsan cikin faffaɗan ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya wata bayan wata. Sannan cikin wata kalar murya ya ce,


    "Ina za ki je? Bayan tafiyar duka taki ce!"


     Shiru na yi na ɗan lokaci, kafin na haɗa kalmomi wuri ɗaya da ƙyar na furta,


    "Abinci.. da.. ruwa zan kawo..maka."


     Ɗago ni ya yi ya kai wa karan hancina sumba kafin ya ce, 


    "Ke ce abincina! Kuma ke ce za ki ba ni ruwan da zan sha ya ɗebe mini ƙishi. Ki bar ni na yi ta kallon ki, na yi ta jin numfashinki, na yi ta jina a cikin jikinki. Tun da Allah ya sa; kishin ki da son ki ba su zautar da ni ba kafin zuwan wannan lokacin! Ina son komai naki, musamman ƙamshinki mai daɗi. Wanda ke saka ni shiga wani yanayi a duk lokacin da na shaƙa. Hmmmm! Haƙiƙa kalmar ina son ki ta yi kaɗan ta bayyana irin yadda nake jin ki a zuciyat..."

      Harshensa da ya tura cikin kunnena ya sa babu shiri na zabura tare da ƙanƙame shi cikin jikina. Na ɗauki lokaci ina mayar da numfashi kafin na ƙwace kaina ta ƙarfi na yi nesa da shi, ba kuma don zuciyata ta so hakan ba. Saboda na kasa bin umurnin da take ba ni a kan kada na raba gangar jikina da nasa. Amma tuno laifi ne muke aikatawa ya sa na daƙile son zuciya na aro jarumta da tsoron Allah na yafa wa kaina.

     Harara na dinga aika masa kafin na saukar da idanuwana ƙasa saboda furucin da ya furta mini. Wanda ya sa na yi sadudar dole, don na gano ko gaba da gabanta. Saboda furucin da ya yi amfani da shi yayin furta,


     "MD ne fa!"


Ya sa na rungume hannuna a ƙirji kafin na haɗe rai alamun babu wasa. Murmushi ya yi mai sauti, kafin ya koma kan kujerar da ya tashi yana girgiza ƙafarsa ɗaya da ya ɗora kan ɗaya, tare da aiko mini wani kallon da ya ƙara tsima zuciyata.

      Ƙafuwana na ja a hankali na fice ɗakin, saboda ina so na nuna masa ni ma wata janwuya ce mai iya shanye komai a kan fuskarta. Tsaye na yi bayan fita daga ɗakin dafe da ƙirjina saboda yanayin da nake jin kaina ya fi gaban kwatance.

     Natsuwata na shiga sannan na fice tsakar gidan, inda su Umma suke zaune har lokacin suna hira. Kai-tsaye Kitchen na nufa na ɗauko sababbin kulolin da na gama tanadi don shi kawai. Gabansu Umma na wuce na isa ɗakin Kawu, ban tsaya komai ba ina ajiye kulolin na sake fitowa na kwashi sauran tarkacen kayan na ƙara dire wa gabansa. Shi ko ban da aikin kallo na babu abin da yake yi, domin jikina ne ya ba ni kallon da yake yi mini a duk lokacin da na shigo ko zan fita. Ina ƙoƙarin juyawa na sake ficewa da zummar ɗauko wasu kayan, na tsinkayi muryarsa yana faɗin,


     "Idan ba so kike yi na yi aika-aika gidan surukaina ba; don Allah ki bar ni.. haka!"


    Abin da ya faɗa kenan da ƙarfi, babu shiri na isa wurinsa. Saboda yanayin da na gan shi a ciki ya sa hankalina ya tashi matuƙa. Hannunsa na riƙe, na ƙura wa gumin da na ga tsattsafo masa a goshi kallo, shi ko yana ta faman gogewa da hankacif.  Fuskata a hargitse na ce da shi, 


    "Subhanallah! Me ke damun ka?"


     Hannuna kawai ya riƙe gam-gam idanuwansa a rufe zuwa ɗan lokaci, yana ta mayar da numfashi sama-sama har numfashin nasa ya daidaita. Idonsa ya buɗe da suka yi jawur cikin 'yan daƙiƙun da ba za su wuce biyar zuwa goma ba. Da mamaki fal raina, na zare hannuna da ya sassauta wa riƙo na dinga kallonsa tamkar mai son gano muninsa. 


    "Ki zauna kawai, na yafe sauran da za a kawo! Saboda jikina ba zai karɓi wannan zaryar da kike yi a gabana ba salun alun ba. Ko a baya; ni kaɗai na san halin da nake shiga a kanki, balle yanzu da nake hangen nesa ta zo mini kusa, haka kawai ki wargaza ɗan guntun haƙurin da nake yi tsawon kwanaki ina ta kawar da kai."


     Rufe idanuwana na yi, cikin sauri na zauna, saboda fahimtar inda zantukansa suka lula. Nauyinsa ya sa na kasa haɗa ido da shi, na fara buɗe kulolin ina ƙoƙarin zuzzuba masa komai da ya samu halarta ɗakin. Duk da na sa a raina zan yi dabarar ficewa na kawo sauran gudun na yi aikin banza. Domin shi na yi wa, kuma shi kaɗai nake so ya ci kafin kowa. 


    Kallon da yake yi mini ya sa na yi fuska na tura masa plate-plate ɗin gabansa ina faɗin,


    "Bisimillah Sir!"


Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗora idanuwansa a kan plates ɗin. Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce,


    "Da alamu so kike yi idan na gama ci na baje ɗakin Kawu."


Ni ma murmushin na yi sannan na ce, 


     "Ai gida ne ko ka baje akwai filo da katifa."


    "To idan haka ne, babu damuwa tun da kina gefena, don na san Kawu ba zai bar ni na kwana ni kaɗai ba."


    Bakina rufe ina 'yar dariya, saboda ya rufe mini baki ban san me zan sake faɗa ba. Bakinsa ya buɗe mini alamun na ba shi da kaina, na ciko spoon na kai bakinsa ya kauce. Na ɓata fuska ya sauko daga kan kujerar, ya janyo hannuna ya saka cikin abincin ya deɓo. Bakinsa ya nufa na yi saurin noƙewa tare da ƙoƙarin janye hannun, amma sai da ya kai lomar da ke hannuna bakinsa. Maimakon ya ci iya abincin kamar yadda ya shiga bakinsa, sai da ya haɗiye lomar sannan ya koma tsotsar yatsun hannuna yana sauke numfashi. 


    "Innalillahi!"


Ita ce kalmar da na faɗa, saboda yadda jikina ya ɗauki rawa gabaɗaya, har ina jin wani danshi yana fita cikin jikina. Haka ya dinga cin abincin yana tsotsar yatsuna har na langaɓe masa gabaɗaya a jiki ina miƙa. Saboda ya gama damalmala mini natsuwar da nake ƙoƙarin janyowa tana guduwa. 

     Ban tantance ba na ji bakinsa cikin nawa, harshensa yana iyo cikin yawuna. Ban da sauke nufarfashi babu abin da muke yi daga ni har shi, saboda ya kai ni maƙurar da ba zan iya kauce wa tayinsa ba kowane iri. 




     😱🤦🏻‍♀️🏃🏻‍♀️






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*


*Comments ɗinku sun saka ni dariya matuƙa. MD ya ce a faɗa muku ba halinsa ba ne.😢🤣*


     *ASHIRIN DA BAKWAI.*


     Mun ɗauki lokaci cikin yanayin da muke, saboda gabaɗaya mun fita hayyacinmu. Kafin na dawo hankalina babu shiri, saboda hanunna da ya ɗora saman jikinsa yana raɗa mini wata maganar da ta sa na janye jikina daga nasa. Na zabura jikina yana rawa na fara ja da baya tare da nuna shi da hannu amma na kasa furta komai.

      Kaina na shiga girgizawa hawaye yana mini zarya a kan dandamalin fuskata. Yanayin da na gan shi yana mayar da numfashi a wahale, dafe da jikinsa ƙam-ƙam ya sa na ƙara jin haushin kaina. Ƙafafuwana na fara ja a hankali na isa gabansa. durƙusawa na yi gwiwa bibbiyu na haɗe hannuwana wuri ɗaya alamun roƙo ina ci gaba da zirarar hawaye.

      Da ƙyar na tsayar da kukan sannan na cikin wata raunanniyar murya na ce da shi,

      "Ka yi haƙuri ka yafe mini, domin na san ni ce silar shigarka cikin wannan halin. Amma kada ka manta wannan mummunar hanya ce muke ƙoƙarin bi ta kanta. Wacce na san ka fi ni sanin illar da ke cikin tafiyar, domin hanyar za ta kai mu inda ba za mu iya ɓullewa ba."


    Kansa saman kujera fuskar tana kallon sama har lokacin tsawon mintuna, kafin ya ɗago da kan ya watsa mini jajayen idanuwansa duka waɗanda a lokaci ɗaya suka ƙanƙance.  


     "Haƙurin me kike ba ni? Bayan ba ki yi laifin komai ba. Don ni kaina ban san lokacin da na fara susucewa a kanki irin haka ba, duk da ina da tabbacin turaren da ke jikinki ya yi matuƙar tasirin wargaza mini natsuwata. Shi ya sa ko a baya nake ƙoƙarin kawar da kaina kanki, dalilin haka ya sa nake miki faɗan ki daina sakawa. Amma kuma wannan karon ya sha bambam da na baya, saboda kusancin da nake da shi yanzu ya yi wa na baya fintinkau. Babu laifi don kin saka turaren, amma kuma ni zan fi kowa cutuwa da hakan a yanzu. Don ga shi kin tayar mini da abin da nake ta lallaɓa kaina kansa gudun na yi aika-aika. Duk da ba na gudun faruwar hakan ko shayin duk abin da zan yi, ko a gano na aikata kanki, ko kuma da ke. Domin idan aka kai ni bango, zan yi abin da zai fallasa komai domin kowa ya san matsayina a wurinki.


    Ido na zaro masa cike faɗuwar gaba na ce, "Ni dai ba na fatar hakan ta faru tsakanina da kai. In dai turaren ne matsalar jira ni yanzu na je na sauya wasu kaya, kuma na dirje jikina ta ko'ina turaren ya fice na dawo."


     Har na juya jikina yana tsima ya yi hanzarin dakatar da ni ta hanyar faɗin,

      "Dakata! Ni ya dace na bar gidan tun da ba kya fatar faruwar hakan kamar yadda kika ce!"


    Ya miƙe dafe da kansa yana ƙoƙarin fita ta ƙofar waje, na yi hanzarin bin sa cikin sauri na riƙe hannunsa ta baya. Hannuna saka na share hawayena da ke kwaranya har lokacin suna fareti a kan fuskata. Ya juyo tare da sauke mini nauyin idanuwansa cikin nawa idon, kallon juna muka shiga tsawon mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya. Gabaɗaya ya juyo yana ƙare wa hannunsa da ke cikin hannuna kallo kafin ya zare nasa a hankali ya koma goge mini hawayen da ya jiƙa mini fuska.


     "Plss ki daina kukan nan ba na so! Ni ma ban san zan tsinci kaina a wannan halin ba; da tun kafin na zo gidan nan na yi wa abin tufƙar hanci. Gudun ki janyo a yi mana zargin da babu biyan buƙata, don da a ce na yi komai ba zan taɓa damuwa don wani ya san abin da muka aikata ba."


    Mamakinsa ya sa na kasa ɗauke kallona a kan fuskarsa, saboda ban taɓa zaton yana magana mai yawa ba balle irin wannan mai cike da confidence. Rungumar da na ji ya yi mini ta hanyar zagaye hannunwansa ta bayana ya sa na yi hanzarin zabura na ja baya. Sakato ya yi yana aika mini wani sihirtaccen kallon da na kasa jure haɗuwar idanuwanmu wuri ɗaya. A raina na ce, 


     'Wannan mutumin dama haka yake?'


    "Na wuce duk tunanin da kike yi a kaina Zaituna! Dalilin da ya sa na kasa ɗauke idanuwana a kan duk wani motsinki. Saboda ina so na ƙara tabbatar da abin da na ji domin na ga zahirin komai a kan idona. Don na san za ki sha mamaki sosai a lokacin da kika ji na dawo miki da wasu shuɗaɗɗun abubuwan da suka gudana a rayuwarki. Ina son mace irinki sak, domin komai naki ya yi mini daidai da tsarina."


    Babu shiri na rufe idanuwana, saboda amsar da ya ba ni kamar ya ji tambayar da na yi wa kaina a zuciya. Sannan kallon da yake aika mini saman ƙirjina ya sa na yi hanzarin ja baya, gudun ya yi abin da zai ƙara saka ni jin kunyarsa. Hannuna ya ja muka dawo kan kujerar da ya tashi muka zauna, kansa ya ɗora saman kafaɗa ya ce,


    "Sai kin yi haƙuri da ni, saboda ina buƙatar kulawa sosai fiye da wacce kike so ki samu. Ai za ki shayar da ni ruwan da zai ishe ni har na yi wanka ko?"


    Yarr! Tsikar jikina ya tashi babu shiri, saboda wuyana da ya dinga lasa tamkar wanda ke lasar zuma. Ture shi na yi tare da ba da tazara a tsakaninmu ina haɗe fuska na ce,


     "Me ya sa kake manta haramcin da ke cikin irin waɗannan abubuwan da kake yi?"


    Murmushi ya yi mini mai sauti kafin ya ce, "Koya miki nake yi, saboda ina so ki saba ta yadda za ki tarbe ni a yadda na zo miki."


    "Idan lokacin ya ba da hakan zan koyi komai a hankali."


     "To ni a zafafe nake so ki zo mini ba a hankali ba! Domin idan kika same ni a yadda kike za ki sha wuya kafin ki saba da halina. MD'n da kika sani daban yake da Aliyun da ke gabanki a yanzu, amma sannu a hankali za ki gano hakan idan tafiya ta miƙa. Tun da ba kya so ni zan tafi, sai dai kafin na je zan faɗa miki mafarkina ya tabbata. Shigar da nake ganin ki da ita cikin idanuwana koyaushe, ita ce yau kika yi mini kuma ta burge ni. Na so bayar da zazzafan tukuici, amma kin hana mu tari lokaci idan ya kama."


    Yana ƙare maganar ya ranƙwafo saiti da kumatuna ya yi mini kiss, sannan ya miƙe ya nufi bakin ƙofa. Sanin takalminsa ba su ta ƙofar wajen, na yi hanzarin zuwa na ɗauko masa idonsa a kaina na har na ajiye takalmin a ƙofar ɗaki. Gefen gyalena na saka ina goge ƙurar da ban hango ba, don ko da akwai ba ta kai darajar da za a bi ta kai balle a ce dole sai an goge. Amma shauƙinsa da ke fisgata ya sa na yi abin da ni da kaina na san bidi'a ce kawai. Na miƙe na tare ƙofar ina faɗin,


    "Ba za ka fita ba sai ka ci ka sha duk abin da na yi don kai kawai, ko da za ka jiƙa maƙoshin da tun da ka zo yake aikin magana."


    "Ki ce kawai yau na zama akun matata. Shi ne kuma za a mini ɗure bayan an hana ni na huta."

     "E, tun da ba MD ba ne a wurin, dole na bayar da umurni kuma a bi."


    Baki ya buɗe yana 'yar dariya, alamunsa ƙarara ya nuna mamakina. Bai musa ba ya dawo yana duba agogon hannunsa. Wanda ya yi daidai da kiran sallar Asr a Masallacin da ke unguwar, kansa ya dafe yana faɗin,


     "Ban san ya zan yi ba. Jikina najasa kuma lokacin sallah ya kama." Shiru kawai na yi masa kamar ban ji abin da ya faɗa ba. Na tsuke fuska sannan na sake zuba masa abin da nake so ya ci, sannan na ja gefe na bar zura masa ido. Kaɗan ya ci ya miƙe yana goge bakinsa da tissue, na miƙa masa abin sanyaya maƙoshi ya sha kaɗan babu gardama. Sannan ya ce da ni na ce da Kawu zai wuce, cikin sauri na fice ɗakin. 

     Ban ji ko ɗar ba wurin isar da saƙonsa ga Inna Kulu domin ta faɗa wa Kawu. Sai dai kallon da suke bi na da shi ita da Umma ya sa na ji na tsargu. Kafin Innar ta ba ni amsa da cewa,


    "Yana waje yana gadin motar baƙon, gudun yara su ɓata masa mota."


    "To ya ce a faɗa muku ya wuce."


    Abin da na faɗa kenan ina ƙoƙarin faɗawa ɗakin Umma. Saboda mugun kallon da na ga Ummar tana yi mini mai kama da tuhuma. Kayan jikina na shiga tuɓewa domin gabaɗaya na rasa natsuwata, a raina ina ji kamar sun gama gano abin da muka aikata ni da shi.

     

     "Maganata dai ta tabbata Kulu, kin gani da idonki zumuɗin soyayya ya sa ta ƙi kwashe sauran kayan wahalar da ta yi masa."


    Gabana na ji ya ƙire ya faɗi dam-dam! Kafin amsar da Inna Kulu ta bayar ta sa hanjin cikina ya kaɗa. "Shi ya sa na so kai mata, amma da na yi wani tunani dole na dawo gudun na shiga ba su san da zuwa na ba."


     "Yo ai sai da na ce ki bar su a yadda zumuɗin ya sa ta manta da su. Ai da kin shiga, ko babu komai za ki ga kalar wainar da suke toyawa. Don ni har ga Allah, da ta ni ake ba da tuni na yi masa iyaka da gidan nan, ki dubi yadda ta fito a hargitse kamar kazar Mayu, ke ko da gani kin san akwai abin da suke yi a cikin ɗakin. Tun da Sale ya ba su damar da za su aikata abin da suke so don taƙamar yana son ta da aure. Amma a yi dai mu gani idan tusa za ta hura wuta!"


     Babu shiri na kai zaune dafe da ƙirjina, saboda maganganunsu sun tabbatar mini Inna Kulu ta ga abin da muka yi da shi. Hannuna na ɗora a kai ina ji kamar na ce wayyo Allah, saboda tsabar kunyar Inna Kulu da ta lulluɓe ni. 

      Haka suka ci gaba da tattauna maganganun ina maƙale ɗaki na kasa fitowa. Inna tana kare ni Umma tana ƙara hawa har akayi kiran sallar magrib. Sai da na ga shigiwarta ɗakin bayan ta yi arwala sannan na fice da ɗaurin ƙirji domin na yi wanka. Saboda ina jin alamun rashin tsarki tattare da jikina.

     Tsarkake jikina na fara yi sannan na yi arwala na dawo ɗakin, kallon da take bin kaina da shi ya sa na yi hanzarin saka hijabi. Cikin kakkausar murya ta ce da ni,


    "Ba sai kin yi hakan zan kasa gano taɓargazar da kuka shuka ke da shi ba. In dai ingiza mai kantu ruwan da Sale yake yi miki ne a kan wannan mutumin nan; ki ƙara ɗaura ɗamara, don bayan ke da ya bi da aure; akwai wasu da ke tafe ko kin yi nasara ƙaddara ta haɗa auren ki da shi."



 


    😢😒





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*ASHIRIN DA TAKWAS.*


      Kaina na ji ya yi mini girma, saboda zancen Umma ya ƙona raina, kuma ya saka wata mahaukaciyar kunyarta ta mini rumfa. Nan take na ji hawaye ya sauko mini a kan fuska shaa. Sai da na zuƙe majinar kuka sannan na ce da ita,


     "Tun da nake a rayuwata, ban taɓa zina ba Umma. Yanzun ma turaren da na saka a jikina ne na ji ya hau mini kai. Dalilin da ya sa na yi wanka kenan, amma ba abin da kike zato na aikata ba. Saboda babu hakan a raina,, kuma ba na fatar hakan ko a gaba, ina roƙon Allah ya kare ni da aikata abin da zan ci amanar kaina."


     Ina ƙare faɗar maganar na yi hanzarin tayar da sallah, saboda fargaban ta kawo mini duka, don irin kallon da take jefo mini a lokacin, kai mini duka ba zai yi wahala a wurinta ba. Amma hakan bai sa na tsira da wata sabuwar gudumar da ta kwaɗa mini da harshenta ba, wacce na gwammace dukan da za ta yi mini, da irin zantukan da take fesowa mini daga bakinta cikin ɗaga murya. Wacce ta fito da zallar ɓacin ran da ke cikin ranta a zahiri.


    "Ita dai duniya, wanda bai zo ba ma jiran shi take yi! Don gyara kayanka ba zai taɓa zama sauke mu raba ba! tun da yau kaɗai idanuwanki sun yi buɗewar da za ki mayar mini da baƙa; to ki sani ko hannunki wannan mutumin ya taɓa; ban yafe miki nauyin cikinki da na yi dakon ɗauka ba, tsawon wata tara da kwana goma. Saboda na fahimci rawar kanki ta ƙaru saboda an ba ku ratar ku ci karenku babu babbak..."


    "Haba-haba Habi! Wai har yaushe bakinki zai daina faɗar ire-iren waɗannan maganganun ga 'yarki tilo a cikin duniya? Don girman Allah yanzu ki sakar mata mara ta yi fitsari haka nan! Abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tamkar ƙwan makauniya? Yanzu wannan ban yafen da kika yi mata ba ina amfaninsa, da za ki jefi 'yarki da shi a kan wannan 'yar ƙaramar matsala?" 


     Zancen Inna Kulu kenan kafin Umma ta ba ta amsa cikin ɗaga murya cike da mamakin abin da ta ce.


     "Ƙaramar matsala fa kika ce Kulu?" 


    "E! Ƙaramar matsala ce Habi! Don babu haramci a kan duk abin da suka aikata, ko da sun haɗa da kusantar juna kuwa balle taɓa hannu. Saboda matarsa ce ta sunna halas malas tun tana kan gadon asibiti. An zaɓi ɓoye miki ne saboda sanin wace ce ke, gudun ki tayar da wani ɓallin da zai sa a rasa rayuwar da ake ta fafutukar nemo mata lafiyarta ido rufe. Ban so sanar da ke a irin wannan lokacin ba, na so kin saduda kafin zuwan lokacin da za ta tare na yi miki bayanin komai a natse. Amma tun da kin zaɓi hakan ga shi nan yanzu na sanar da ke, sai ki daina ɗaga jijiyoyin wuyanki kina mata Allah ya isa a kan abin da Allahn bai haramta mata ba!"


     Cikin sauri na shafa addu'ar da ban san me nake roƙa ba, saboda tsananin tashin hankalin Allah ya isar da Umma ta sake yi mini a kan MD. Sai ga wani sabon bugun zuciyar da na ji daga bakin Kawu Sale, wanda  ya cafe zancen daga sama ya fito da amsar da ya dace a ce a bakin Inna Kulu ta fito.  Wacce alamunta ya nuna ƙoƙarin feso ta cikinta da take yi, amma fusatar da Kawun ya yi ta janyo ya shiga gabanta da zancen. Dole ta ja gefe tare da ba shi hanya ya shigo cikin ɗakin idonsa a kan Umma. Wacce ke ƙare wa fuskarsa kallo tamkar ba ta taɓa ganin shi ba. Kafin ta yi magana cikin raunanniyar murya ta ce,


     "Kana nufin har an ɗaura masa aure da ita ina cikin duniya ba ni da labari?"


    "Tabbas Zaituna matarsa ce! Shi ma mijinta ne! Don haka ki daina yi wa 'yarki baki a kan abin da Allah bai haramta mata ba. Saboda wata biyu Alhaji Ali ya bayar duk shirin da za ta yi ta kammala shi kafin zuwan lokacin. Don da an bi ta mijin nata ma da yanzu haka tana ɗakinsa. Yanayin jikinta da damuwar da ke ranta ya sa aka bar shi har zuwa lokacin domin ta ƙara samun lafiya da kuzarin jiki. Amma ki yi haƙuri idan mun miki katsalandan! Mun yi hakan ne saboda a kawo ƙarshen matsalolin da ke ta faruwa a tsakaninku, saboda kin fi kowa zama shaida kulawar da ya nuna mata a asibiti. Kuma ni da ke da kowa ma ya san ita ma tana son shi, dalilin da ya sa muka yanke hukuncin kenan. A ranar wata jumu'a bayan an sauko daga masallaci; dubban mutane suka shaida ɗaurin auren ta da shi, wanda Alhaji Ali ya yi jagoranci a matsayinsa na Yayan Mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya. Ni kuma na tsaya miki, kuma na amince da auren a matsayin ke. Sai dai idan kin ga ba a miki daidai ba kina iya ɗaukar matakin da duk kike so! Amma ban da raba abin da Allah ya haɗa, don kwanaki kaɗan suka rage ya karɓi matarsa ta koma gidansa gabaɗaya!"


     Kuka Umma ta fara yi wiwi har da salati, saboda ni kaina zancen ya dake ni ballantana ita da ke adawa da abin kowace safiya. Cikin tsananin tashin hankali na miƙe na isa gaban Kawu na durƙusa jikina yana rawa na fara magana cikin kuka na ce,


    "Don Allah Kawu ka taimake ni ka taimaki rayuwata! Na haƙura da auren nan ka ce ya sauwaƙe mini zan yi wa Umma biyayya na auri wanda take so! Don Allah Kawu don Allah..."


    "Yi mini shiru Zaituna!"


Tsawar da ya katsa mini kenan cikin ɗaga muryar da ta sa na zabura babu shiri. Nuna ni ya fara yi da hannu sannan ya ce, 


    "Kada na koma jin kalmar saki ta fito daga bakinki! Domin aure ya riga da ya ɗauru, ko ke kika ce kin fasa a yanzu ba zai fasu ba ballantana Habi da tun farko ba ta yi na'am da shi ba!"


     Jinin jikina na sha, ni ma na fara kukan, saboda sautin kukan da Umma ke yi ya tsima ni matuƙa. Nawa sautin kukan ya ƙaru a lokacin da Umma ta kalli Kawu fuskarta cike da ruwan hawaye ta ce,


    "Yanzu Manu ina da rai aka yi wa Zaituna aure ba tare da an ba ni haƙƙina na uwa ba?"

     

 Cikin sauri Kawu ya ce, "Ta ya za a faɗa miki, Ke da kullum ba kya hangen abin da ake hango miki? Ba kya zaton idan Allah ya tsaga rabo a tsakaninsu ba zai iya kashe ki ba? To ki ji da kyau! Mu gata muka yi miki, saboda muddin kika yi ƙoƙarin toshe hanyar alheri; to ke kuma za ki toshe wa kanki sauran rayuwa a zaman duniya. Don ko Hausawa sun daɗe da faɗar; rabo ajali ne. Idan ya ratsa dole ne ya fito ko ta daɗin rai ko babu!"


    "Gara ganin mutuwata da jin wannan maganar taka Sale!! Don da tun farko kun yi mini addu'ar mutuwar ta ɗauke ni tun wuri; ya fi da irin wannan tozarcin da kuka yi mini. Sai ku ƙulla musu auren cikin ruwan sanyi babu ni ballantana na kawo muku cikas. Don haka ka sani tun da har aka haɗa kai da kai aka mini rufa-rufa; wallahi sai na bar gidanka tun da ba ka ji kunyar watsa mini ƙasa a ido ba!"


     Abin da ta faɗa kenan tare da ƙarin sautin wani sabon kukan da ya fi na farko taɓa mini zuciya. Jiki na ja cikin tashin hankali na isa gabanta da zummar ba ta haƙuri. Ta miƙe tamkar wata zakanya ta kwaɗa mini mari, tana ƙoƙarin kai mini na biyu Kawu da Inna suka rirriƙe ta.  Ta sake yin cikina da duka Kawu ya yi ƙoƙarin janye ni daga gabanta yana faɗin,


    "Ni ya dace ki daka ba ita ba! Don ni ne na yi ja gaban auren ita ma ba ta san komai ba, kamar yadda kika ji a yanzu haka ita ma ta ji daga bakina. Saboda shi kansa mijin nata mun hana ya sanar da ita, amma mun ba shi damar ya kafa kansa gare ta a hankali har ta fahimci abin da ke nan. Saboda sanin ba ki sani ba, gudun ta ji ta sanar da ke ba tare da kin ji komai daga bakinmu ba. Amma tun da kin kira hakan da cin amana, ki yi duk abin da kike so. Kuma muddin kika dake ta a kan haka sai Allah ya saka mata tun da ita ma ba ta san komai ba!" 


  "Wallahi ban yafe muku ba Sale! Daga kai har Alhaji Ali da munafukin mijin nata duka sai Allah ya isar mini a kanku! Tun da kuka haɗu kuka ɗaura wa 'yata aure ba tare da na sani ba!"

    

  Kawu ya fice daga ɗakin a fusace yana faɗin, "To muna jiran abin da zai same mu a kan rashin yafiyarki! Aure kuma tun da Allah ya haɗa haukarki ba ta isa ta raba ba! Daman sanin halinki ya sa aka ɓoye miki gudun ki kawo mana matsala. Ke Kulu ni zan fita! Idan kuka ji ni shiru ku saya gidan!"


     Inna Kulu ta ce masa "To!" Sannan ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta tako zuwa inda Umma take zaune, wacce har lokacin kuka take rusawa wiwi. Sassauta murya ta yi cikin lafuzzanta masu sanyi ta ce,

      

     "Ki yi haƙuri Habi, ki ɗauka cewa Allah ne ya ƙaddara ba yin su Sale ba. Saboda dukanmu babu wanda yake da tabbacin abin da zai faru anjima ballantana gobe. Kuma tun ranar gini ake yin zane, Allah ya ƙaddara tun can Zaituna za ta aure shi, shi ya sa hakan ta kasance ba tare da an shirya wa lokaci ba. Sannan zancen barin gida ki ajiye shi ma, don babu inda za ki je ki bar gidan ɗan'uwanki a kan wannan matsala. Saboda kai-tsaye zai zargi don ba shi ya haifi Zaituna ba ne kike nuna bai isa da ita ba. Duk da kin ji Yayan Mahaifinta ne ya yi auren, shi nasa laifin rashin faɗa miki da wuri tun lokacin da aka ƙulla. Amma don Allah ina roƙon ki Habi ki yi haƙuri ki yafe musu duka, musamman 'yarki da ɗan'uwanki waɗanda suka fi kowa kusanci da ke. Domin ɓacin ranki nasu ne, duk yanayin da za ki shiga dole ne su ji ciwo. Addu'a ya dace ki yi a kan tabbatuwar alherin da ke cikin auren, tare da kawar da sharrin cikinsa komai ƙanƙantarsa. Amma wannan kukan da munanan lafuzzan duka ba za su kawo wa ɓacin ranki waraka ba. Illa su ƙara haifar da wata sabuwar matsalar da ba a san inda za ta tsaya ba. Na san abin da ciwo, amma ki yi haƙuri, ki ɗauka haka Allah ya ƙaddara ba yin wani ko wasu ba."


    Tsam Umma ta miƙe tana sharce majinar kuka ta shiga zuba kayanta a wata madaidaiciyar jaka. Wani sabon tashin hankali ya yi mini dirar mikiya, na zabura cikin rawar jiki na isa inda take na kai wa jakar cafka. Cikin zafin nama ta kai mini wani bahagon mari babu shiru na kai ƙasa tare da zuwan wani sabon kuka. 

    Inna ta iso inda nake da sauri ta tayar da ni na miƙe, rungumata ta yi jikinta muka fice ɗakin ina ta kuka. Su Ummu Salma da ke tsakar gidan ma kukan suke yi, zuciyata ta sake karyewa na yage baki ina ta rero kuka tamkar wacce ake duka. Ɗakinta ta kai ni bakin gadonta ta zaunar da ni, ta ce da ni na zauna nan kada na fito. Sannan ta fice su Umma Salma suka shigo ɗakin suka rungume ni, muka dinga rera sautin kukanmu daga ni har su babu mai rarrashin wani.


    Mintuna a tsakani na ji muryar Inna tana magiyar Umma ta zauna kada ta je ko'ina. Ture su Iman na yi na miƙe zumbur na fito tsakar gidan, inda na hango ta riƙe da jaka tana ƙoƙarin ficewa Inna Kulu tana riƙon ta.

      Aguje na isa wurinta ni ma na rungume ta ta baya, ina wani irin kukan da ban san yadda zan kwatanta shi ba. Gabanta na sha na durƙushe ƙasa na yi ƙoƙarin riƙe hannuwanta duk da tana gocewa. A haka na ɗora idanuwana saman kumburarriyar fuskarta da ta ɗoro hadarin gabas da na yamma. Idona yana tsiyayar ruwan hawaye na ce,


    "Don Allah Umma kada ki tafi ki bar ni, idan kuma kika tafi ni ma zan koma Birnin Kebbi da zama. Ko kuma na ɓace ɓat ta yadda za a neme ni cikin faɗin Nigeria ba a samu wanda ya gan ni b..."


    Kuka ya ci ƙarfina na kasa kai ƙarshen maganar, ita ma jakar ta saki ta juya tare da goge ruwan hawayen da ke cikin kwarmin idanuwanta. Inna Kulu ta ɗauki jakar ta yi ɗakinta da ita, ni kam ko motsi na kasa yi ballantana na samu ƙarfin miƙewa na bi su. 

     Na ɗauki minti talatin a wurin ina shesshekar kuka kafin su Umma Salma su kama ni mu koma ɗakin Inna Kulu. Kan gadon muka zauna suka shige jikina suna faman sharar ƙwalla jefi-jefi, har barci ya kwashe su duka a jikina.


     Daren ranar haka muka kwana a gidan zuciya babu daɗi, domin ko abincin ban ci ba, haka ma duk kiran da MD yake yi mini ban ɗauka ba. saƙonnin da suke shigowa cikin wayata ma babu ɗaya da na duba, duk da jikina ya ba ni shi ne ya turo su duka. 

   A ɗakin Inna muka kwana daga ni har yaran, asubar farin na fito sallah, lokacin Inna Kulu tana ɗakin Kawu. Kamar an ce na leƙa ɗakin Umma, da ƙumajina na ɗage labulen da zummar ganin halin da take ciki. Babu shiri na zaro ido saboda ganin babu kowa a ɗakin, kuma ban hango jakar da ta ɗibi kayanta a ciki ba. 

     Ɗakin na faɗa kamar an jefa ni, ina ƙwala wa Inna Kulu kira cikin ihu da ƙaraji. Cikin ɗan lokaci Inna da Kawu suka faɗo ɗakin suna tambayar lafiya, cikin muryar kuka na ce da su,


     "Ban ga jakar Umma ba! Ita ma kuma ba ta ɗakin nan. Don Allah ku ce kada ta tafi ta bar ni zuciyata za ta buga!"


    Salati dukansu suka saka, Inna ta yi hanzarin kama ni na miƙe muka fito waje, Kawu ya fice yana faman kiran sunan Umma a bakin ƙofar bayi. Shirun da muka ji ya sa aka shiga biɗar ta cikin gidan kungiya saƙo, amma ko'ina babu ta babu alamunta. 

     Tsakar gidan na zube ina wani irin kukan da nake jin kamar zuciyata za ta fashe. Inna Kulu da Kawu da yaran duka suka taru kaina, amma ban bakin da suke yi mini bai sa na daina ihun kukan da nake yi ba. Gaban Kawu na ja jikina na tsaya, hannuwana na haɗa tare da ɗaga su sama alamun roƙo na ce, 


     "Don Allah Kawu ka ce ta dawo! Wallahi na fasa auren MD zan auri duk wanda take so!"


    Kafin ya yi magana na zabura jikina yana rawa na yi ɗakin Inna, wayata na janyo jikina yana rawa tamkar mazari na fara kiran lambar MD. Amma har ta katse bai ɗaga ba, wani kiran na sake danna masa tana gaf da tsinkewa na ji ya ɗauka. Majinar kuka na zuƙe sannan na yi magana cikin karyayyiyar muryata da sha kuka, magana na yi masa kai-tsaye babu gaisuwa ballantana wata sallama.


     "Ka sake ni! Na fasa aurenk..."






     😳😿







D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*




   *ASHIRIN DA TARA.*


          Fisge wayar da na ji an yi; babu shiri na zabura tare da juyawa muka yi ido biyu da Kawu. Duk da zuciyata ta dake a lokacin, amma sai da na razana da irin kallon da Kawu yake yi mini.


 'Hello! Hello!  MD yake ta faɗa, hakan ya sa Kawu ya kara wayar a kunnensa yana cewa,


    "Kwantar da hankalinka! In Sha Allahu kai da ita aurenku mutu ka raba takalmin kaza! Abu ɗaya nake so gare ka; ka yi haƙuri a kan duk wani abin da za ka gani daga nan har zuwa lokacin da za ta bar gidan nan ta koma gidanka! Sannan akwai maganar da nake so mu tattauna da Alhaji Ali, duk abin da muka kai ƙarshe zan neme ka da kaina na sanar da kai." 


   Yana ƙare faɗar hakan ya datse kiran, tare da aiko mini hararar da hantar cikina ta kaɗa. Wayar ya miƙo mini yana cewa, 

     "Za ki cutar da kanki a banza, matuƙar kika biye sabgar Habi! Domin babu ta inda ta kamo hanyar gaskiya ballantana a mara mata baya. Saboda aure ne aka ƙulla miki ba zaman shashanci muka ce ki je ki yi ke da shi ba. Yaron nan kuma yana son ki tsakani da Allah! Amma idan kin ga za ki cuci kanki a kan boren ta ki je ga fili ga mai doki. Sai dai kada ki manta, ita dama sau ɗaya take zuwar wa mutum a rayuwa, kuma duk ƙanƙantarta ka yi amfani da ita cikin lokaci kada ka bari sai gobe. Gudun garin neman gira a rasa ido, ko kallon ruwa ya sa kwaɗo ya yi miki ƙafa! Iya gatan da za a yi miki kenan a yanzu kuma an yi miki. Domin ko budurwa ta samu wannan yaron ta more ballantana ke da ake ƙoƙarin rufa wa asiri Habi tana ƙoƙarin halaka ki. Don na yi imani da cewa; ko ba ki aure shi ba, ba za ki daina son shi ba. Kuma duk inda kika je ba za ku daina biyar juna ba, to da a haifi ɗan kan titi; gara a haife shi gidan sunnah. Saboda shi rabo ajali ne babu ruwansa, da ya rantse sai ya fito ko da tsiya ko da tsiya-tsiya!"


     Yana ƙare maganar ya fice daga ɗakin, Inna da ke bayansa ta ƙaraso ciki tare da jan hannuna muka yi ɗakin Umma. Saboda maganganun Kawu sun saka su Ummu Salma farkawa daga barcin da suke yi.

    Bakin gadon Umma ta zaunar da ni sannan ta tura ƙofar ɗakin ta rufe. Bayan ta gama bai wa su Iman umurnin su je su yi sallah. Zama ta yi kusa da ni tana faɗin,


     "Yanzu ke Zaituna kanki kike son ki yi wa salalan tsiya? To ban so sanar da ke na gan ku ido da ido kuna faranta wa juna rai ke da mijinki ba. Amma tun da ta kama zan fito miki a mutum domin ki yi saurin fahimtar inda na dosa." 


    Shiru ta yi na ɗan lokaci, wanda ya ba ni ratar tuno abin da ya faru tsakanina da MD. Nan take kunyarta ta rufe ni, amma hakan bai hana ni ɓata fuska ba, saboda halin da nake ciki ba na maraba da duk abin da zai ƙara wa zuciyata nauyi. 


    "A lokacin da na je kai miki kayan da na ce da Habi har na je na dawo; to na tsaya bakin ƙofar ina ƙoƙarin yin sallama na ga kuna shan bakin juna ke da shi duka kun fita daga hayyacinku. A tunaninki wannan abin zai bar ku idan ba ku auri juna, kuka zauna a mazauni ɗaya ba? Kin yi kuskure Zaituna, saboda yawunsa da kika sha, shi ma ya sha naki; ya ƙara danƙon soyayyar da ke tsakaninku. Kuma har abada ba za ku daina ɗokin kusantar juna ba, sannan maganar Sale ce, ko kin sa ya sake ki saboda ki faranta wa Habi; za ki ɓata mata idan ta fahimci kin kasa barin shi kuna aikata abin da bai dace ba. To da a yi ɓarna a kwashi zunubi; gara a yi abin da zai kawo muku lada daga ke har shi. Don haka ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah Habi da kanta za ta sauko har ta saka wa aurenku albarka. Amma hakan ba zai samu ba har sai kin nutsar da hankalinki wuri ɗaya, kuma kin kame mijinki kin riƙe. Don haka daga yau za ki fara gyara jikinki kafin zuwan lokacin tariyar da aka ɗiba, babu boka babu malam za ki mallake mijinki ba tare da ɓata lokaci ba. Yanzu ki tashi ki yi sallah ki dawo, idan na gama nema mana abin kari na ba ki wani abu ki fara da shi."


   Tsam na miƙe ba tare da na ce da ita ƙanzil ba, cikin nauyin jiki na dinga jan ƙafuwana har na fice daga ɗakin. Jiri yana kwasa ta na yi arwala na dawo ɗakin Umma na yi sallah. Ina kan sallaya zaune  ina ta lazimi,  har su Umma suka gama shirin makarantar islamiya. Daga nan ɗaki ina jin su da Inna a lokacin da ta ba su abin kari tana jan su da hira. Bayan sun gama suka ɗauki jakar makarantarsu suka yi mini sallama, ina ɗaga musu hannu suka fita.  Addu'ar a dawo lafiya na raka su da ita a cikin zuciyata. Saboda ko dogon motsi ba na so balle na yi wata magana mai ƙarfi. Domin na yi ta kiran wayar Umma tana ringing ba ta ɗagawa. MD ma sai kira na yake yi amma na kasa ɗagawa balle na nemo amsar da zan ba shi a kan sauyawata. Saboda ba na so na rage wa Umma girma a wurinsa, shi ya sa na saka wa raina ba zan taɓa faɗa masa gaskiyar Ummata ba ta son tarayyarmu da shi ba. Hakan ya sa na rufe layukansa duka, ta yadda ko ya kira ba zai same ni ba ballantana na ƙi ɗagawa na ƙara masa damuwa.


    Tagumi na yi da hannu ɗaya, hannuna ɗaya riƙe da carbi ina ja. Inna Kulu ta shigo ɗakin ɗauke da plate ɗin taliyar da na ji ƙamshinta ya cika ɗakin, tun lokacin da ta doso ni da ita. Gaba ta saka ni ina cin taliyar tana sanar da ni Umma tana Dunguza, Kawu ya kira ta yana sanar da ita ashe can ta nufa da jakar kayanta. Ban ce da Innar komai ba, domin a raina ina jin kunyarta tamkar wata surukata, saboda abin da ta ga na aikata, wanda nake tsoron ya goge ɗinbin yardar da ta yi mini a baya kafin ta gano ni.

      Na ɗan ci taliyar kaɗan na ture, ba ta matsa mini sai na ƙara ci ba, ta janye plate ɗin daga gabana. Ta ajiye mini wani jug kusa da ni tana faɗin,

   

      "Ki sha, kanunfarin da na jiƙa miki ne, ko shi kaɗai kika riƙe; za ki bambanta kanki da sauran mata a wurin mijinki. Saboda yana saka ƙamshin jiki, ta yadda ko fitsari kika yi sai ya yi ƙamshi, ballantana mijinki ya zo kusantar ki ƙamshi zai tashi a maimakon warin da mata suke futarwa a wani lokaci. Sannan kin ga kayan ruwa, (Fruit) idan kika laƙanci shan kankana ki haɗa da dabino ki tauna su wuri ɗaya, yadda zaƙinsu zai kama bakinki; haka mijinki zai dinga jin zaƙinki a lokacin da yake saduwa da ke. Ki fara shan kanunfarin kafin a nemo miki kankana da dabinon. Ina son ko da za ki je gidansa jikinki ya ƙara haɗewa, ta yadda zai ji ki tamkar sabuwar budurwar da aka fasa budurcinta, amma jikinta bai buɗe ba."


    Kaina na ji ya yi ƙato, saboda ganin Inna da gaske ta yaye kunyata gefe. Sai da na sha rabin jug ɗin, sannan ta ce na ajiye a firij idan anjima ta yi na ƙara sha, sai a sake zuba masa ruwa ya ƙara jiƙa kafin dare ya yi na sake sha.


    Ina ƙoƙarin miƙewa tsaye ta ce, "Ba ni na kai miki kofin, amma ki yi wanka za mu je Dunguza mu yo bikon Habi ta dawo. Sai dai ki tabbatar kin tambayi mijinki fitar, ko da ba ki sanar da shi inda za mu je ba. Don bai dace ya san da ƙiyayyar nan da Habi take yi masa ba. Gudun mutuncinta ya zube a wurinsa ya dinga yi mata kallon rashin daraja. Saboda duk yadda take; gaba take, uwa uwa ce, kuma duk rintsi babu wanda ya fi ta. Sannan ba za a samu wanda zai kamo ƙafarta wurinki ba. Sai haƙƙin miji da aka ce yana gaba da na kowa, amma ko shi ba zai miki fatan ki saɓa mata ba, matuƙar yana so ki gama da duniya lafiya. Ki faɗa masa za mu je dubiya Dunguza, idan ya bar ki sai mu je mu rarraso ta ta dawo. Idan kuma ta kafe mu baro ta har ta gano Annabi ya faku ta dawo don kanta."


    Ta ƙare maganar tana 'yar dariya, ni ma murmushin na yi mata sannan na fara cire hijabina, zuciyata sai hasko mini zazzafan kiss ɗin da muka yi wa juna ni da MD. Rintse idona na yi na zauna yaraf bakin gado dafe da kaina, na shiga bubbuga goshina saboda tsananin abin kunyar da nake ji a raina na aikata. Wanda zuciyata take ta hasko mini komai daki-daki domin na gano irin ta'asar da muka yi ni MD cikin idona.

      A gurguje na yi wanka, sai dai tun kafin na fito na ji muryar Kawu yana ƙwala mini kira. Inna ta sanar da shi wanka nake yi, ya ce to na yi sauri na fito tun da na tayar wa yaron mutane hankali. Ga shi can ya zo ni yake son gani.

     Raina a ɓace na shirya zuciyata babu daɗi, domin haka kawai nake jin a raina zan iya haƙura da shi, matuƙar Umma ta kasa saukowa daga dokin naƙin da ta haye. Duk da wani sashen zuciyata yana faɗa mini ƙarya nake yi, domin a kansa ko hauka zan iya yi matuƙar aka nemi raba ni da shi. 

     Inna ta leƙo tana sanar da ni ita kaɗai za ta je, tun da mijina ya zo na yi ta tasa kawai. Amma za ta jira su Ummu Salma idan sun dawo su tafi tare, ko da ganin su zai sa Umma ta saduda. Murmushin yaƙe kawai na yi mata ina saka dogon hijabina, saboda umurnin da zuciyata take yi mini a kan na killace kaina, ta yadda ba zai ga wata ƙofar da zai ce na tayar masa da hankali ba. Sannan ko ta kan turare ban bi ba ballantana na shafa ya jingina wa turarena laifi. 

     Na ja takalmina na nufi hanyar fita gidan, da zummar idan na shiga ɗakin Kawu ta waje na rufe ƙofar cikin gidan. Gudun a sake kwata abin da zai saka ni nutsewa cikin ƙasa saboda kunyar mutanen gidan. 


    Fuskata a haɗe na shiga ɗakin, ina ƙoƙarin bi ta gabansa na wuce ya yi saurin riƙo hannuna. Ban kalle shi ba na ƙwace hannun nawa na nemi nesa da shi, na yi wa kaina mazauni. 


    "Barka da safiya."  


Ita ce maganar da na fara taron shi da ita, tun kafin ya yi ƙorafin da nake da tabbacin shi ya kawo shi. Ban kalli inda yake ba, amma jikina yana ba ni ni yake kallo. Ajiyar zuciya na ji ya sauke sannan ya ce,


    "Laifin me na aikata kika tayar mini da hankali? Bayan kina sane da halin da na bar gidan nan, amma na kira ki da dare kika ƙi ɗauka. Kuma da safe kika bijiro mini da zancen da zuciyata ta tashi bugawa. Me na miki da zafi har haka Zaituna?"

  

    Ya ƙare maganar cikin raunanniyar muryar da ta sa na ji har raina ban kyauta masa ba. Amma na ƙara tsuke fuska na ce da shi,


    "Babu komai"


   "Ok, babu komai kika yi hakan?"


   Kai na ɗaga masa alamun 'e', saboda kukan da nake jin yana turnuƙo ni ba zan iya amsawa da bakina ba. Tsam ya miƙe ya nufo inda nake, cikin sauri na miƙe tsaye tamkar wacce aka tsikara na fara ja da baya zuwa ƙofar cikin gida. Amma bai fasa biyo ni ba, hakan ya sa na jingine da bango, hawayen da nake ƙoƙarin shanyewa ya sirnano mini shaa a kan fuska.


    Rumfa ya yi mini a jikin bangon, sannan ya saka hannunsa ɗaya ya tallafo ni ta baya ya haɗa da jikinsa. Cikin wata murya mai taushi ya ce da ni,


    "Wannan hukuncin da ake son yanke mini na mene ne? Ba na son rufa-rufa ki sanar da ni abin na aikata har ake neman yanke mini hukuncin kisa! Ina son ki da yawa Zaituna, idan kika guje ni a irin wannan lokacin za ki cutar da ni da yawa. Me ya sa za ki nemi watsa mini ƙasa a ido? Bayan na gama bugun ƙirjin ke daban ce a cikin matan da na sani a rayuwata."

     Hannuna ya janyo ya ɗora saman saitin zuciyarsa ya ce, 


    "Kin ji yadda zuciyata take gudu ko? To kowane bugun da take yi da ke take tafiya Zaituna! I luv u more than anything in this world. Ba zan iya kwatanta matsayin da kike da shi a cikin zuciyata ba. A tunaninki idan na bar ki zuciyar ba za ta buga ba?"


    Kalamansa sun saka zuciyata natsuwar dole, amma hawayen da ke cikin idanuwana bai daina zuba ba.


 'Shin me ke damuna ne wai?'


   Tambayar da na yi wa kaina kenan, saboda luguden da ake yi mini a tawa zuciyar, kwatankwacin yadda na ji tashi tana gudun famfalaƙi a cikin ƙirjinsa. Kaina ya ɗago saboda ganin na kasa furta masa komai. Kallona ya dinga yi tsawon mintuna sai ga hawaye ya fara tsalle daga cikin kwarmin idonsa zuwa saman fuskata. 

      Mamaki da tashin hankali duk suka dirar mini a lokaci ɗaya. Saboda ganin kuka a cikin idanuwansa, kuma kukan ma wai saboda ni Zaituna MD yake zubar da hawayensa. 

     Babu shiri na shiga goge masa hawayen, idona cikin nasa ƙur muna kallon juna. Kafin na saka hannunwana duka biyu na tallafo kansa ta baya. Bakina na kai saiti da nasa domin na faranta masa rai, ko da kwatar ɓacin ran da na saka shi ciki, wanda na saka shi zubar da ruwan hawayensa a kaina. Lebena na kai saman nasa, na ɗan tsotso a hankali har sau uku. Sannan na lumshe idona, tare da sauke ajiyar zuciyar da ban san me ya kawo ta ba na kwanta saman faffaɗan kirjinsa. Da hannunsa da ke zagaye da ni ta baya, ya yi amfani wurin ƙara mana kusanci da juna. Kansa ya ɗora saman kafaɗata yana faɗin,


     "Zan mutu Zaituna, matuƙar kika bar ni! Plss! Ki ce da ni abin da na ji ba gaske ba ne ko da hankalina zai kwanta."


    Nan take jikinsa ya fara rawa da sauri ya ɗago kansa, babu zato na ji ya fara lasar ruwan hawayen da ke kan fuskata da harshensa. Santsin harshen da yanayin lasar da yake yi wa furkar tawa; ya sa na shiga sauke numfashi sama-sama tare da gantsare masa. Jikinsa ya saka ni gabaɗaya ya tallafo ni, saboda ƙafafuwana sun yi sanyin da ba zan iya ɗaukar kaina ba. 

     A hankali ya fara zame mini hijabi kuma ko kaɗan ban yi tunanin hana shi ba. Saboda zuciyata ta gamsu da kalar son da yake yi mini daban ne, ko a cikin tarin masoyan duniya. Da kaina na taimaka masa ya gama cire mini hijabin ya ajiye, sannan ya fara kai mini kisses a saman ƙirji sannan ya dawo kunnena yana karkaɗa mini harshensa ciki. Miƙa na dinga yi, tare da sauke ajiyar zuciya wata bayan wata, kafin na ƙara baje masa sosai domin jikina ta ko'ina ya karɓi saƙon da yake ƙoƙarin aika mini. 


    Ya shiga lalube ni ta inda yake so, ni ko ban da aikin sauke numfashi kala-kala babu abin da nake iya yi a lokacin. Hakan ya ƙara masa ƙaimi a kan abin da yake ƙoƙarin aikatawa, babu shiri na riƙe masa hannu, saboda wuce gona da irin da na ji zai yi.  Cikin wata kasalalliyar muryar ya yi mini raɗa a kunne,


    "Ki taimaka mini..Zan mutu...Idan ba ki ba ni haƙƙina ba!" 


    





   🙈Oh ni😿







D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*


   _*Saƙon gaisuwa zuwa gare ku ɗaukacin masu bibiyar wannan littafi. A duk inda kuke yi muku fatan alheri gabaɗaya. Masu kukan tausayin Zaituna tana godiya matuƙa da karamcinku.🥰 Masu jin haushin Umma ma ku yi mata uzuri ku yafe mata. Daman kowane ɗan'adam yana da nasa kalar hali, ita nata haka ya zo a ɓauɗe ba a mata gwaninta duk girman kirkin da za a nuna mata; laifi kaɗan zai sa ta dinga yi wa mutum kallon hadarin kaji. Sannan kuma tana cikin iyayen da ba sa bai wa 'yarsu damar zawarci komai rintsi zaman auren kawai a mutu ko a yi rai. Ire-irensu duk yadda aka kai ga nuna musu hanya ko sun san ta suna kawar da kai gudun a saki ɗiyarsu. Duk hanyar da za ta bi in dai zaman zai ɗore za ta iya bi saboda kada auren ya guntule. Mai irin halin Umma sai an yi namijin ƙoƙari kafin a iya zama da ita. Saboda ko an yi gaba sai an dawo baya saboda zama a kan tsattsauran ra'ayi. Allah ya ƙara mana haƙurin zama da su sau da ƙafa, saboda mu samu rabauta a nan duniya da gobe ƙiyama. On luv😍*_



      *LAMBA TALATIN*


   Babu shiri na fashe masa da kuka, saboda sanin inda muke da tsoron abin da zai sake faruwa idan aka gano me muka aikata. Cikin rawar jiki ya kai wa bakina cafka jikinsa sai kyarma yake yi, alamun zaƙuwa da zalama duka sun bayyana gare shi a lokaci ɗaya. Ƙoƙarin shiga jikina ya fara yi na ƙara saitin kukana wiwi tamkar mu kaɗai ne a cikin duniyar daga ni sai shi.

     "Daina kuka, tun da ba kya so ba zan miki dole ba!"

      Shiru ya yi na ɗan lokaci bayan gama maganar, sannan ya zare jikinsa daga nawa a hankali ya miƙe. Bai ce da ni komai ba ya nufi ƙofar waje zai fice, ganin da gaske tafiya zai yi kuma a yadda yake yana buƙatar natsuwa kafin ya fice. Zumbur na tashi na dunƙule wuri ɗaya, daga nan inda nake na ce da shi,

    "Idan ka fita a haka; mutane za su gano ka."


   Juyowa ya yi a hargitse ya ɗora kallonsa saman fuskata sannan cikin wata shaƙaƙƙiyar murya ya ce,

    "Tun da ba kya tausayina, mene ne damuwarki idan na fita a haka?"


    Majinar kuka na zuƙe kafin na ce, "Yanzu laifina ka gani ko?" Na ƙare maganar da zuwan wani sabon kuka. A harzuƙe ya sake jefo mini wata tambayar cikin kaushin  murya ya ce


    "Ya ba zan ga laifinki ba? Bayan kin hana ni abin da nake ƙulafucin mallaka har a cikin barcina!"


    "Yanzu me za ka ce idan wani ya gan mu a irin wannan halin? A tunaninka mutuncinmu ba zai zube ba?"


    Wani kallo ya yi mini kafin ya ce, "Zina muka aikata?"


    Girgiza masa kai na yi alamun a'a, idona a kansa ina tsiyayar ruwan hawaye. Kafin na sunne kaina cikin cinyata na dinga sharɓen kuka. Ban ji takunsa ba, sai dai na ji shi kusa da ni yana ƙoƙarin ɗago kaina. Ban musa masa ba, na ɗago fuskata muka dinga yi wa juna kallon ido cikin ido tsawon mintuna, nan take saƙon da muke ƙoƙarin aika wa juna a zuciya ya yi tasiri. Domin kuwa janyo ni ya yi a hankali  na kwanta saman ƙirjinsa ya rugume ni tsantsan, tare da ɗora kansa saman fuskata. Tare muka sauke ajiyar zuciya daga zaunen, kafin ya miƙar da ƙafarsa na kwanta sosai a jikinsa. Sajensa ya fara goga mini a gefen fuska babu shiri na lumshe idona, ya saka ƙaramin gemunsa ya fara mini wasa saman fatar idon nawa. Shiru na yi tsawon mintuna ina ji da sauraron kalar soyayyarsa mai shiga jiki da ratsa zuciya. 

     Hannu na saka idona a rufe na shafi gemun nasa, zuciyata cike da shauƙin sonsa da ke fisgata. Ina ji a raina tamkar mu tabbata a yadda muke mu kaɗai, saboda sabon salon da ya zo mini da shi ya ƙawata zuciyata matuƙa. Hannuna ya haɗa da nasa wuri ɗaya ya damƙe tare da fesar da wani ƙaƙƙarfan numfashi a lokaci ɗaya. 


      "Ina son ki da yawa Zaituna, don Allah kada ki cutar da ni! Ba na zina kuma a rayuwata ban taɓa kusantarta ba. Dalilin da ya sa kenan ban fiye kallon mata ba ko da suna gabana, ina ƙoƙarin hana kaina kallon su saboda sanin wane ne ni. Ina da ƙarfin sha'awa, kuma matuƙar ta taso ina rasa natsuwata, ta yadda ba na ji ba na gani sai na samu abin da nake so kafin na dawo cikin hankalina."


     Shiru na yi masa tsawon sakonni ban iya furta ko kalma ɗaya ba, saboda kwarjininsa da kunyarsa gabaɗaya sun gama yi mini lulluɓi. Musamman da na ji harshensa saman leɓena yana lasa tamkar ya samu zuma. Ƙoƙarin tashi daga jikinsa na yi saboda tsoron ya sake ganin laifina, domin na saka wa raina ba zan taɓa bari ya same ni a arha ba, har sai lokacin da aka kai ni gidansa. Duk da na san ba ƙaramin artabu zan sha da shi ba, duba da yanayinsa da yadda yake saurin hargitsewa idan muna tare. 

     Miƙewa tsaye na yi ina ƙoƙarin barin wurin ya yi saurin riƙo hannuna yana faɗin,

     "Ina kuma za ki je?"


"Fita za mu yi da Inna, kada ta ga na daɗe bayan ni kaɗai take jira."


    "Ban yarda ba! Babu inda za ki je, don kullenki zan yi ta yadda ba za a cuce ni a dinga kalle mini ke ba. Wai ko kin san zafin kishina a kanki kuwa?"

     Murmushi a kan fuskata na girgiza masa kai, sai da ya ɓata fuska sannan ya sake cewa,


    "Ko wurin aiki, ba za ki sake zuwa ba sai kin tare gidanki. A can ɗin ma babu tabbas ɗin zan bari ki ci gaba da zuwa gaskiya. Ina fargaban wani ya kalle ki na hango shi; ƙaddara ta sa na tsire masa ido ya makance."


     Bakina na yi saurin rufewa saboda dariyar da ta zo mini kafin na ce, "Duk wannan kishin na mene ne? Bayan ni ba budurwa ba ce, sannan kuma ma'aikaciya ce ni. Ko ban fita don komai ba zan fita ko don aikina, gudun MD ya gano ba na yin abin da ya kai ni ya hukunta ni."


    Shi ma murmushin ya yi kafin ya ce, "Babban hukuncin da ya fi na MD; hana wa Aliyu haƙƙin matarsa! MD kuma ki bar shi can a ma'aikatarsu, Aliyunki kuma; ki ba shi irin kulawar da yake buƙata a wurinki."


    Ajiyar zuciya na sauke tare da rungume hannuna a ƙirji na ce, "Allah ya ba ni iko! Amma fa ina tsoron Aliyuna ya kasa yin adalci tsakanin matansa. Saboda gudun ya tashi da shanyayyen jiki a ranar gobe ƙiyama a dalilin rinjayar wani sashe!" 


    Shiru ya yi mini ba tare da ya ce komai ba tsawon mintuna, sannan ya sauke ajiyar zuciya idonsa a kaina ya ce, "Aliyu ya yi dacen matar da ta dace da komai nasa."

     "Ina taya shi murna, sai dai ita ma matar Aliyun; zan daki ƙirji na ce da ita ta yi matuƙar dace da mijin marainiya! Wanda yake saka ta farinciki yayin da take cikin ƙunci, ya saka ta dariya a lokacin da take rusa kuka. Ya hana ta bin ɓaragurbin hanya ya ɗora ta a kan tafarkin gaskiya. Wanda yake ƙoƙarin kawar da kai da haram ko da zuciyarsa tana so.   Mai kawo mata agaji a lokacin da take tsananin buƙatar ceto. I luv u so much Aliyuna, ina son ka sau ba adadi, irin son da ba na zaton akwai irin shi a kaf faɗin duniyata!"


    Ido ya lumshe ya buɗe, sannan ya ce, "Wowww! Daman matar Aliyu ta iya sarrafa harshe kamar haka?" 


     "Zama da kai ne ya sa na koya!"


    Na ƙare maganar ina 'yar dariya. Idonsa ya buɗe sannan ya ce,   

      

      "Yo ni da ba na magana?"


    "A haka na koya da yaren kurame!"


    Nuna ni ya fara yi da hannu yana cewa, "Kina da hira a bakinki, aka yi dace kin iya tsara magana tamkar a rubuce. Ni dai ba zan fasa faɗar komai naki ya yi mini ba. Kuma kin zo a yadda nake buƙatar ganin matata, sai fatan Allah ya ba mu zaman lafiya. Kuma ya ba ki ikon ɗauke ɗawainiyar Aliyunki, duk da ina ji a jikina za ki yi jarumta. Amma kuma hakan ba shi zai sa na kasa miki huɗubar juriya ba, saboda ina so ki ƙara mallake zuciyar Aliyunki!"


     Idona na rufe da tafukan hannuna saboda muguwar kunyarsa da ta kama ni. Da siririyar dariya ɗauke a kan fuskata na ce, 

     "Wai me ya sa ba ka jin kunyata?"


    "Saboda ke matata ce!  Kuma babu wani shamakin da ya ratsa tsakanina da ke a yanzu. Saɓanin baya da ko kallon ki ba na son yi sai dole. Amma kuma hakan bai hana ni saka wa duk wani motsinki ido ba, saboda amanarki da Baba Ali ya ba ni tun kafin ki fara zuwa aiki ma'aikatarmu."


    Ido na zaro cike da mamakin maganarsa, bakina yana rawa na ce, "Shi Baban ya ba ka amanta?"

     "E, ya ba ni labarinki tun kafin na fara ganin ki. Dalilin haka ya sa na yi ruwa da tsaki a cikin rayuwarki. Saboda ina masa kallon mahaifi tun kafin na rasa nawa a duniya. Abokantar da ke tsakaninsu mai ƙarfi, ta sa nake masa kallon uba, saboda ya riƙe mu matsayin 'ya'ya ni da ƙanwata tun ba mu mallaki hankalinmu ba, a lokacin da muke tsananin buƙatar wani bangon da zai taimake mu ni da Ammina. Shi ya sa na lashi takobin kula da amanar da ya damƙa mini. Ko motata da wancan mutumin ya ɓata;  ɗar ban ji ba, saboda na saka wa zuciyata yi don Allah duk tsanani duk wuya. Ban yi zaton kulawar da nake yi miki za ta rikiɗe ta koma so ba. Sai a lokacin da na fara jin hirar ku ke da Amina."

     

    "Amina kuma?"


Tambayar da na yi masa kenan bakina yana rawa, kansa ya ɗaga mini sannan ya ce,

       "Ki yi haƙuri! Saboda na ji abubuwan da bai dace na ji ba. Amma na yi hakan ne saboda na ƙara tabbabar da abin da Baba Ali ya faɗa mini dangane da wancan mutumin. Hakan ya sa na saka wa motsinsa da naki ido, aka yi dace ranar da kika fito cikin dare maigadin da na bar wa kula da ke a cikin unguwar ya ga lokacin da kika fito. Yana sanar da ni a waya na fito cikin daren, saboda tsoron wani abu ya same ki Allah ya tambaye ni amanar da na ɗaukar wa kaina. Aka yi dace Allah ya tserar da ke da shashashun mutanen da suka so keta miki haddi. Dalilin da ya sa na ƙi kai ki tasha kenan, saboda gudun ki je Kebbi ya zargi ba na kula da amanarsa da kyau. Sai ga shi ke kuma na yi miki laifi a sanadin hakan, maimakon nuna mini ƙaunar da ake yi; sai aka koma fushi da ni ana ta gudu na."


    "Gudu kuma?"


Tambayar da na jefe shi da ita kenan ina ƙumshe dariyata, saboda tuno artabun da muka yi da su Ummita, tare da badaƙalar da aka yi daren ranar har zuwa safiya lokacin da na ji motsi a gidan nasa kafin na fito.

     "E, gudu mana! Wanda ya janyo duk yaƙar zuciyata da ake ƙoƙarin yi aka zubar da makaman. Saboda na ba shi haushi, tun da na ƙi bari ki bar garin kamar yadda kika yi niyya."


     Amsar da ya ba ni kenan yana mini dariya, fuska na ɓata alamun ba wasa sannan na ce, "Ni dai faɗa mini, wace magana ka ji muna faɗa ni da Amina?"


    Agogon hannunsa ya fara dubawa, sannan ya ce,

     "Bari na gudu, yau Saturday akwai aikin da nake so na yi a gida, tun da aikinki da nawa duka yanzu ya dawo kaina. A dole nake bai wa Amina tana rage miki wani idan na ga zan haɗa wa kaina nauyi da yawa. Amma kuma ina so na saba da hakan, saboda ba na zaton za ki koma ma'aikatar nan da sunan aiki!"

     Tsaye ya miƙe, yana aika mini wani kallo kafin ya ce, "Zan tafi, tun da har yanzu ban yi sa'ar zama ango ba."


    Rai na haɗe kafin na turo baki, saboda ba na son ya tafi, kuma na so jin maganar da ya ce ya ji, wacce ta sa ya fara so na. Sannan zancen barin aikin da ya yi mini albishir bai mini daɗi ba. Don ko babu komai zan tallafi kaina da yarana, bayan su Umma da ko ba su roƙa ba ya dace na dinga kyautata musu lokaci bayan lokaci.


   Ban san me ya tuna ba, har ya yi gaba ya dawo ya rungumo ni jikinsa. Bai tsaya komai ba ya yi mini abin da ban yi zato ko tsammani ba. Saboda ƙirjina ya kai hannunsa babu shayin komai ya dinga yadda yake so da su. 

     A kiɗime na dinga ture masa hannuwa ina ƙoƙarin ƙwatar kaina. Amma hakan bai hana shi yin son ransa da su ba, sai da na ji zai sake dawo da mu ruwa na zille da gudu na bi ƙofar cikin gida na bar masa ɗakin. Ban san ya ya ƙarge ba na ji ƙarar tashin motarsa alamun ya tafi, ajiyar zuciya na sauke mai mai ƙarfi dafe da saitin zuciyata na ce, 


     'Ko ya zan yi da wannan bawan Allah idan aka kai ni gidansa?'


    ***

Su Inna ba su dawo gidan ba sai bayan Zuhur, domin ko abincin rana ni ce na girka. Ina ɗakin Umma kwance ina huce gajiyar sharar gidan da na yi; na jiyo muryar su Ummu Salma da Inna suna rafka sallama. Ina ƙoƙarin tashi daga kwancen suka shigo ɗakin dukansu da wata sabuwar sallama.

      Na amsa ina yi wa Inna sannu da zuwa kafin ta samu wuri ta zauna tana 'yar dariya. Kafin ta yi magana na riga ta da cewa,

     "Ina Ummar? Ba za ta dawo ba ne?"


     "Habi kam, ta kafe a kan ba za ta dawo gidan nan yanzu ba. Shi kuma Sale ya yi waya da Alhaji Ali sun rage kwanakin tarewarki. Maimakon wata biyun da aka saka ya dawo sati biyu masu zuwa. Don haka shiri za a yi a gaggauce domin a samu abin da ake buƙata, ungo wannan gumbar dabino ce da madara. Ko da gutsura za ki cinye ta ba sai kin tsaya damawa ba, sannan yanzu zan tashi na fara dafa miki tsimi. Tun da abin ya zo kusa dole ne mu tashi tsaye mu yi gyaran da ya dace." 


     Daga haka ta fice, ta bar ni da tagumi saboda haushin kafiyar Umma, da yadda za a ƙarge da hidimar bikin da ba ta so. Kuma yadda ta tsayu a kan duga-duganta, haka su ma suka lashi takobin sai sun ga komai ya kankama yadda suka tsara.

     Amma ni kam, zuciyata tsalle take yi, domin ganin ƙoshi da kwanan yunwa. Ina son MD da aurensa, amma ba ba na son fushin Umma a dalilina.





     🤗









D. AUTA CE✍🏼





*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



_*Commenters ina godiya sosai da ƙoƙarinku, sannan ku yi haƙuri da rashin reply ɗina a wasu lokutan. Amma duk wanda ya yi; matuƙar ina cikin group ɗin zan gani, kuma ina farinciki sosai da bajintar da kuke nunawa wurin sharhi babu gajiya. Mabiya daga wasu groups ɗin da ba na ciki; ku ma dukanku ina muku godiya sosai, tare da fatan alheri gabaɗaya. Thank you so much, luv u all😘*_


*TALATIN DA ƊAYA.*


      Tun daga ranar da Inna Kulu ta sanar da ni an dawo da tariya sati biyu; da dare MD ya kawo kwalayen cingom, biscuits da sweet kala-kala. Saboda a raba wa mutane kowa ya shaida ɗaurin auren, da lokacin da zan tare. Inna Kulu ta ce ba za a taɓa kaya ba sai an kai wa Umma ta gani sannan a raba.

     Kawu ya yi Tsalle ya dire a kan sam ba za ta saɓu ba. Sai dai a raba a kai mata nata tun da ita ce ta mayar da kanta saniyar ware. Ni da Inna Kulu shiru muka yi muna ta sauraron faɗan da yake yi tamkar ya kai wa iska duka.


    "Ko ban sani ba! Aka ɗauki kayan nan aka kai wa Habi da sunan ta raba; ban yafe ba Kulu! Saboda ban kori Habi ba ita ce ta kori kanta, kuma ban biye ta ba na taka da kaina har Dunguza na ba ta baki a kan ta yi haƙuri ta dawo; nan ma ta buga kanta ga ƙasa ta ce ba ta san zancen ba! To na gama bin Habi ko neman ta a kan abin da ya shafi auren nan na Zaituna! Kamar yadda ta faɗa ta bar mini ita na jiƙa ta na shanye; to na karɓa hannu bibbiyu! Kuma ba zan taɓa saduda a kan hakan ba! Aure dai ne mun ɗaura kuma ya ɗauru, ƙarshen zancen ma gidan mijinta za mu kai ta ko da izininta ko babu! Saboda haka babu abin da zan sake neman ta a cikin sha'anin auren nan! Baƙin bakin da take yi mana kuma ba zai taɓa kama mu ba! Alheri muka ƙulla kuma in Sha Allahu shi za mu gani!"


   Yana ƙare faɗar hakan ya bar wurin a fusace har yana ƙwallo da wata babbar robar Inn. Jugum-jugum muka yi ni da Inna da su Ummu Salma gaban kwalayen. Saboda faɗan Kawu ya sa mun kasa motsin kirki, domin yadda jikina ya mutu murus; haka na hango fuskar Inna Kulu ta yi tuɓus. Domin alamunta duka ya nuna ƙarara ba ta ji daɗin hukuncin da Kawun ya yanke ba, ni ma ban ji daɗi ba; amma kuma ban ji haushin shi ba ko kaɗan. Saboda batutuwan da na ji ya ce ta faɗa; ko ni ce a matsayinsa, abin da zan iya yi kenan. 

      Tun cikin daren Inna ta kira Ummar ta sanar da ita an kawo kayan da za a raba wa mutane. Amma Umma ƙanzil ba ta ce da ita ba, sai jin muka yi wayar ta tsinke alamun ta datse kiran. Inna ta ce na nemo su Firdausi na sanar da su, ita kuma ta kira 'ya'yanta da niyyar idan safiya ta waye a bai wa duk wanda ya dace. 


     Haka ta kasance, ko da ƙarfe sha ɗaya na safe ta yi har an gama ƙulli. Domin Firdausi da Sajida kusan tare suka zo gidan, Amina ce ba ta zo ba sai ƙarfe ɗaya da aka tashi wurin aiki, lokacin har an kai wa duk wanda Allah ya tsaga da rabonsa. 

     A ɗakin Umma muka yada zango, suka saka ni gaba da tsarguwar na ɓoye musu zancen auren, sai da na ga lokaci ya ƙure na sanar da su. Iyakacina da su bayanin ni ma ban sani ba sai a lokacin, amma sun ƙi karɓar uzurin kamar yadda nake so su yi. Har muka rabu ba su fasa ganin laifina ba, Amina kuma sai tsokana ta take yi da sunan matar Oga. Sajida kam baki har kunne take ta tsallen murnar hasashenta ya tabbata. Firdausi kuma da dare bayan mun raka su sun tafi; ɗakin Umma muka ƙule tana tambaya ta inda Umma ta je har lokacin ba ta dawo ba. Kasancewar babu ɓoyo tsakanina da ita, nan take kukan tausayin kaina ya zo mini, cikin kukan na yi mata bayanin duk rikicin da ake yi.

      Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce, 

"Ki ƙara haƙuri! In Sha Allah aurenki da MD alheri ne, saboda jikina yana ba ni Umma da kanta sai ta yi alfahari da wannan auren, ballantana ke da za ki je ki mori mijinki. Amma zan je da kaina na gani idan za ta ji maganata ta yi haƙuri ta dawo a yi komai gabanta. Saboda babu daɗi gaskiya a ce ba ta gidan nan za a yi hidimar auren nan! Ko ba ta shiga ba; gara a ce tana kusa, kafin ki tafi ki samu ta yafe miki. Sannan rashin ganin ta zai sa mutane su hankalta da abin da bai dace a ce kowa ya sani ba."

     Shiru na yi mata kafin na zuƙe majinar kuka na ce, "Na rasa me MD ya yi mata da ba ta son shi. Ƙiri-ƙiri take nuna ƙiyayyarta a kansa, irin ƙiyayyar da ko Mukhtar ba ta yi wa irinta ba! Har ga Allah ina kunyar a ce ya gano ba ta yi na'am da aurenmu ba, duk da na san ba ya rasa fahimtar rashin sakin fuskar da take yi masa. Amma bai dace ya gano komai ba a yadda yake ba, don Allah ki je Firdausi, kuma duk yadda za ki yi ki shawo mini kanta ta dawo, ko don ta yafe mini kafin na bar gidan nan. Saboda matuƙar aka kai ni ba ta yafe mini ba; wallahi hankalina ba zai taɓa kwantawa ba!"


    Firdausi ta yi mini alƙawarin za ta je, kuma duk yadda suka yi idan ta dawo za ta sanar da ni. A kan haka muka yi sallama da ita. Ni da su Ummu Salma muka raka ta har ƙofar gidan, sai da na gaisa da maigidanta sannan na dawo gida zuciyata cike da damuwa.

Tun daga ranar Inna take aikin gyara ni ciki da waje. Komai ta kwaso ba ni take yi ta ce na sha ko na ci, babu musu nake karɓa. Saboda na sa a raina ba zan taɓa ba ta kunya ba. Ko babu komai ni ma ina so na je masa a nutse, ta yadda zai sha mamakin ganin tsohuwar rijiya ta zama sabuwa.


      A gefen MD kuma kullum muna maƙale ta waya yana ƙara susuce ne da zazzafar soyayyarsa mai tsima rai da zuciya. Idan ba ma waya muna saman network muna chatting. Domin dare muke rabawa muna abu ɗaya, har sai da na nuna masa ba na so ya shiga haƙƙin matarsa, sannan muka rage hirar da muke yi da dare. Haka ma 'yar shaƙuwar da na samu da shi; ta sa na fahimci yana da sauƙin kai sosai idan ya so hakan. Kuma alamunsa ya nuna ƙarara ba zai yi wuyar ja ba, ta yadda zai zamar wa mace tamkar raƙumi da akala. Saɓanin kallon da nake yi masa a baya, mutum mai wuyar sha'ani da tsattsauran ra'ayi, a wasu lokutan mai wuyar ganewa.


      Ɓangaren Umma kuma, ko a waya na kira ta ba ta ɗagawa. Firdausi ma duk da ta je, amma ba ta yi mini bayanin yadda suka yi ba kamar yadda ta yi mini alƙawari, hakan ya sa na ce da Kawu zan je na ba ta haƙuri da kaina. Ya ce ba zan je ko'ina ba. Idan ta matsu da son gani na za ta dawo don kanta. Amma su Ummu Salma kacokam ya ce su koma can su taya ta zama. Duk da na ji haushin hakan, amma da na yi nazari sai na gano ya nemi su je ne domin ya ba ni fili na sakata na wala da MD a waya. 

     Domin wani lokaci idan ya kira ina tsakar gida tare da Inna, ko kuma suna wurin ba na sakewa. Shi ya sa nake ƙin ɗauka, idan kuma na kasa haƙuri na ɗauka kai-tsaye nake sanar da shi aiki nake yi, idan na gama zan kira shi. Idan Kawu yana wurin ya yi ta mini faɗan na daina haka wulaƙanci babu kyau. Har ma ya ce da su su ba ni wuri na yi waya.

      

     ***

 Ana saura sati ɗaya MD ya sanar da ni baƙi za su zo daga gidansu. Ban yi nauyin baki ba na sanar wa Inna Kulu zuwan su. Tun daren da za su zo aka tanadar musu duk abin da za a tarbe su da shi. Na gayyato su Firdausi duk da nake fushi da ita, saboda ban da wasu ƙawaye sai su, sai Hafsa da ta zo gidan taya ni murna a lokacin da aka kai mata cingom ɗin bikin. A bisa umurnin Mamarta ta zo kamar yadda ta sanar da ni da bakinta, a cewarta tun da na share ta tsawon lokaci shi ya sa ita ma ta kama kanta da ni. Ban wani sake mata ba amma ita sai ƙoƙarin shige mini take yi, a ƙoƙarinta na son nuna mini komai ya wuce a manta da baya, da kuma abin da ya faru. 

     Ranar Jumu'a da marece sakaliya, gidan Kawu ya cika da 'yan'uwa da abokan arziƙi. Saboda tarbon lefena da MD ya narke kuɗi domin kawai ya faranta mini, kuma ya fitar da ni kunyar mutane.

     'Ma sha Allah!' Kawai ke tashi, tun da da aka fara shigowa da akwatunan har zuwa lokacin da aka buɗe kayan ana dubawa. Guɗa da ayyururui ɗin wasu mata ta sa na yi hanzarin faɗawa ɗakin Inna Kulu tun lokacin da na ji dirin motoci a ƙofar gidan. Amma na sha jinin jikina ta tagar Inna, na ɗan ɗaga labulenta ta wata kusufa ina hangen dafifin da aka yi wa akwatunan ana kallo. Ihu da shewar da ake yi duka a cikin kunnuwana, kuma a kan idona. 

     Allah ya sanya alheri na ji ana ta yi kafin na bar jikin tagar na ja ƙafafuwana a hankali na kwanta kan gadon Inna. Zuciyata cike da tsantsar farinciki marar misali, saboda jin kaina da nake yi tamkar wata sabuwar halitta. Domin ko auren farko ba a yi mini irin gatan da MD ya yi mini ba. Saboda tun daga kan akwatunan dole ne a yaba masa, balle a zo kan kayan da na ga ana ta ɗagawa gwanin burgewa. 

     Sajida ta shigo ɗakin tana ihun faɗin, "Wayyo Auntyna! Yanzu za ki san kin yi auren kece raini!"


    Alamun shiru na yi mata da hannuna daga kwancen, saboda muryar da ta ɗaga mutane za su iya hankalta da ni, kuma akwai waɗanda za su dinga shigowa ɗakin su yi ta kallo na. Sai dai kuma hakan da na yi mata bai sa ta fasa ihun da take yi ba. Illa bi na da ta yi da zancen,


     "Aunty ki bar ni na ya murnata! Wannan abin farinciki har ina? Wallahi gara da aka yi, don ke gaba ta kai ki gobarar titi a Jos! Dole na yi guɗa duk da ban iya ba! Ayyururuiiiiiiii! Auntyna ta yi goshi!"


    Kaina na dafe tare da rintse idanuwana, saboda kwarantun da ta yi ya sa na ji kamar na zura da gudu tsabar daɗi. 


    "Ina amaryar take? A fito mana da ita mu gan ta!" 


    Sautin wata da na ji kenan a tsakar gida, hakan ya sa na yi hanzarin janyo mayafin da ke jikina na rufe fuskata ina salati Sajida tana mini dariya Muryar Firdausi na ji ta shigo ɗakin, kafin ta zo saiti da kunnena ta ce,


    "Taso mu je ki gaishe su, domin su gano ba mu da makusar da za a kushe mu! Domin na fahimci akwai 'yan bani-na-iya a cikin waɗanda suka kawo kayan."

     Noƙewa na yi na kasa miƙewar da take so na yi domin mu fitan, Sajida ta riƙo hannuna tana faɗin,


    "Aunty ki taso don Allah! Kuma ki rage kunyar nan kada a ce mana ƙauyawa." 


     Firdausi ta kama ni na miƙe tsaye, ta taimaka mini na rufa mayafina a saman kai. Kaina ƙasa muka fito daga ɗakin, fahimtar idanuwan mutane a kaina ya sa na yi hanzarin wayancewa ina fara'a na bi Firdausi da ke riƙe da hannuna, har zuwa wurin wasu manyan mata da ke ɗakin Umma zaune. 

     Har ƙasa na durƙusa na gaishe su fuskata ƙasa, don tun kallo ɗaya da na yi musu ban sake bari muka haɗa ido ba. 


   "Ma sha Allah! Zaituna ko?" 


    Abin da na ji wata dattijuwa ta faɗa kenan, na ɗaga mata kai ina murmushi. "Tabbas! Aliyu ya yi zaɓi mai kyau, Ubangiji ya ba ku zaman lafiya." 

    A zuciyata na amsa da 'Amin' amma a fili na ƙara sunne kaina, tare da jan gyalena na rufe fuskata. Firdausi ta miƙar da ni muka fito ɗakin, ina ƙoƙarin komawa ɗakin Umma na tsinkayo muryar wata 'yar Iya kamar tana ƙusƙus da wata.


    "Tsohuwar mace ce fa! An ce tana da manyan 'ya'yan da suka isa aure..." 


   Babu shiri na ja na tsaya, cike da son na waigo na ga wace ce mai maganar. Amma dole na basar na shige ɗakin, saboda sanin idanuwan mutane suna kaina. Zuciyata cike da son jin ci gaban gulmar da aka fara, bakin gadon Inna na zauna ƙirjina yana bugawa, saboda ɓacin ran da ya yi mini dirar ba zata. Kan gadon na koma na kwanta Firdausi ta fice tana faɗin,


    "Bari na je mu sallami baƙin, na dawo mu yi wata gulma!"


  Kallo kawai na bi ta da shi kafin na lumshe idona, kamar wacce ake busa wa usur, haka na dinga jin wata sabuwar hira a daidai bayan tagar Inna ta lungun da zai kai mutum ɗakin Kawu Sale ta ƙofar cikin gida. 


      "Gaskiya tana da kyau, kuma na yi wa Fatima hoton da ta ce, idan muka koma zan nuna mata. Amma kin san me; babu abin da Fatima za ta nuna mata wallahi. Saboda ko dirin jikin banza ta fi ta, sai dai ta nuna mata faɗin jik.."


    "Wai ke ba ji abin da na ce da ke ba ne? Shi ya sa fa na ce mu dawo ta nan mu ji daɗin zancen. Tsohuwar mace ce fa! Bari ganin ta da ɗan jiki ki ruɗe da yabo, to 'yarta ta farin za ta kai shekara sha takwas. Ke idan aka ce ma an kusa auren ta kada ki ce a'a."


    Shiru na ji kafin na ji mai maganar ta sake cewa,

     "Wai ke mamaki kike yi ne? To bari mu je a nuna mana 'ya'yan nata mu gan su da idonmu. Amma wallahi ba yarinya ba ce! Jikinta ne a haka shi ya sa ta yaudare shi ya aure ta. Domin idan aka ce tsinin hancinta ne da ƙirjinta suka ɗebe shi ma ba a musu. Don na san zai sha ɗan banzan bala'i da Fatima a kanta, musamman da ya kora ta gidan Ammi sanadin auren ta! Hu'umm! Akwai gwarama wallahi, saboda ta ci alwashin..." 


    "Zo, zo, mu je! Ga su can za su tafi su bar mu!"


 Shirun da na ji tsawon mintuna ya sa na fahimci sun bar  jikin tagar, tsam na miƙe na nufi bakin ɗakin kamar zan fita. Babu shiri muka yi ido biyu da wasu mata biyu, tun daga kallon da suke yi mini zuciyata ta ba ni cewa su ne suke gulma ta. Abin mamaki ɗaya daga cikinsu ta nufo ni tana faɗin,

    "Amarya zo mu yi hoto, idan mun je mu nuna wa Angonki!"


    Wani kallo na bi ta da shi, kafin na wayance murmushi ɗauke a kan fuskata na sassauta murya na ce, "Ki dai kai wa Maman Nu'aim! Amma shi tun ɗazu ya matsa mini sai da na tura masa ya gani."


    "Oh Allah! Ki ce ya riga mu gani! Ba za mu samu tukuici a wurinsa ba? Zuhura zo a yi hoton da ke mu samu tubarrakin amarya!"


   Wacce ta kira Zuhura yaƙe kawai ta yi sannan ta ce, "Ki dai yi sauri mu je Zee, kada ki janyo a bar mu! Kin ga har sun fice mu kaɗai aka bari."


     Abin da ta faɗa kenan tana ɓata fuska tare da gyara zaman jakar da ke rataye saman kafaɗarta. Ummu Salma na hango cikin sauri na kira ta, har wacce aka kira Zee za ta bar wurin na ce da ita,


   "Ga 'yata ta farin fa, a yi mana hoton da ita!"


   Ina hankalce da kalar kallon da Zuhura ta yi mana ni da Ummu Salma. Zee ta dawo inda nake tana yaƙe ta ce,


    "Ahhh! Ki ce da na yi laifi ban yi wa 'yata hoto ba!"

     

    Ina ɗan murmushi muka saita ni da Ummu Salma ta raɓa kusa da ita ta yi mana selfie. Sannan ta bar wurin gudu-gudu sauri-sauri tana faɗin,


  "Baby mene ne sunanki?"


Ummu Salma tana murmushi ta faɗa mata, sannan suka fice tana yi mata bye-bye.


    Ajiyar zuciya na sauke bayan fitar su muka haɗa ido da Inna Kulu, tana yi mini kallon ƙarin bayani da ido. Na yi murmushi kawai zan juya, na ji muryar wata tsohuwa mai kawo wa Inna daddawa tana guɗa. Rawar da take yi ta saka ni dariya na tsaya ina kallon ta. Kayan ta fara buɗawa tana faɗin,


   "Um-um! Yanzu waɗannan kayan duka na Zaitu ne?" 


    Amina da ke mayar da wasu kayan akwati ta ce,  "Nata ne duka Inna, ko kina so ke ma a ce da Angon ya haɗo miki naki?"


    Innar ta riƙe haɓa tana jinjina kai tsawon mintuna sannan ta ce, 


    "Ikon Allah! Ashe mu dukanmu an ci mu a banza!"






     🤭😂🏃🏻‍♀️








D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*TALATIN DA BIYU.*


       Gabaɗaya wurin dariya aka fashe da ita, ni kaina ba ƙaramar dariya ta ba ni ba. Hakan ya sa na kasa komawa ɗakin na samu wuri na zauna, mutane sai Allah ya sanya alheri suke ta yi mini ina ƙoƙarin amsawa cike da kunya. Aka shiga zuzuta kyawun ɗinkin da aka yi wa manyan atamfofi da lessukan da ke cikin lefen. Kayan cosmetics birjik kala-kala, bayan takalmi da jakunkunansu iri daban-daban. Ɓangaren sarƙoƙi ma ma sha Allah, saboda duk wacce na ga an ɗaga sai na ji ta burge ni.

       Kasancewar magrib ta kawo jiki, Amina da su Sajida da 'ya'yan Inna suka mayar da kayan tsaf cikin akwatunan kamar yadda aka kawo su. Sannan aka shiga bitar zancen kirkin dattijan da suka rako kayan, da Zee da Zuhura sarakunan gulma masu muƙamin lamba ɗaya. Firdausi tana 'yar dariya ta ce,


    "Ita fa wannan mara jikin; ban da harare-harare babu abin da take yi. Ina hankalce da ita lokacin da ta ce a fito da amarya har wani mere ta yi tana yi wa wata ƙusƙus. Sai ga shi ido ya raina fata a lokacin da suka ga na fito da Zaituna suka koma kallon juna cike da mamaki."


     "Bar 'yan jakar uba! Daga ganin su ba daga cikin dangin Aliyun suka fito ba! Idan kuma har cikinsu suke; to su tasu kala daban take da mutanen gari. Saboda dattijan kam, ban da sa albarka da yabo babu abin da suke yi har suka bar gidan suna addu'ar Allah ya ba da zaman lafiya."


    Cewar Inna Kulu tana kawar da turminta zuwa mazaukinsa. Wanda alamu ya nuna wata ta janyo shi ta zauna cikin masu tarbon lefen ko masu kawowa. Kiran sallar magrib ya sa aka tsayar da hirar aka fara shirin sallah. 

     Ni ma na miƙe zuciyata cike da tsantsar farinciki na bi layin buta, jira ya zo kaina na yi arwala na koma ɗakin Umma domin na yi sallah. Bayan mun gama sallah muka baje ɗakin muna cin abinci ana ta hira, kowa sai sambarka yake yi daga kan kayan har zuwa gwarzon gwaraza, Aliyuna, kuma Angon Zaituna.

      Firdausi, Amina, da Sajida. Tare da wasu daga cikin 'yan'uwanmu suka saka ni gaba da shawarwarin zaman aure iri-iri. Sai godiya nake yi musu cike da jin daɗin bajintar da kowa yake ƙoƙarin nunawa domin ya faranta mini. Firdausi a gaban kowa ta janyo buhun da ta zo da shi gidan ta jingine ɗakin Umma. Har ina yi mata tsarguwar kada ta ce talla ta zo yi mana a gidan. Kuloli ne masu kyau saiti biyar, haka ta dinga fito da su tana ajiyewa gabanmu, kowace a kwalinta ko buɗe su ba a yi ba. Mutanen da ke ɗakin suna ta taya ni godiya, Sajida ma kuɗi ta fito da su daga jikinta tana lissafi aka fara ihu. Naira ɗaiɗaya har dubu ashirin haka ta miƙa wa Inna Kulu su ta ce tata gudunmuwa ce. Inna ta shiga godiya, ina ƙoƙarin yin magana wayar da ke hannuna na ji ta yi ƙara alamun shigowar saƙo. Cike da mamaki na ɗago kaina bayan na gama dubawa, idona na kafe a kan fuskar Amina na buga mata wata kalar harara, saboda gabaɗaya ta kashe mini jiki da kalar tata bajinta. Saboda dubu talatin cas na gani a account ɗina, wanda kai tsaye credit alert ya shigo mini ɗauke da sunan Amina Muhammad Sani. Baki har kunne na ce da ita,


 "Hajiya kanki ɗaya kuwa?" 


     Ta fara ƙoƙarin miƙewa tana saɓa jakarta ta ce, 

     "To ni bari na tafi, kada ki ɗora mini jakar tsaba, kaji su caccake ni!" 


   Mayafinta na riƙe tana ƙoƙarin ficewa na ce da su Inna Kulu, "Inna kun ga haukar da Amina ta yi kuwa? Kuɗi ta turo mini har naira dubu talatin fa! Kuma wallahi sun yi yawa, dole ne ma sai ta rage ko na fasa karɓa duka!" 


     Amina ta yi hanzarin faɗin, "Wallahi Inna ko ficika ba zan rage ba! Allah dai ya ba da zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba!"


    Gabaɗaya ɗakin ya ɗauki faɗin "Amin!" Cikin muryoyi mabambanta. Bin ta na yi baya su Inna suna mata godiya tana tafiya, har bakin ƙofar gida na  raka ta, da niyyar mu je titi sai ta samu abin hawa na dawo. Amma gargaɗin da MD yake yi mini a kan fita; ya sa na ja na tsaya a ƙofar gidan, na shiga yi mata godiya cike da jin sabuwar ƙaunarta cikin raina. Saboda ina jin ta a zuciyata tamkar wata 'yar'uwata, wacce muka haɗa jini da ita a cikin ahalina. 


     Fatan sauka lafiya na yi mata sannan na juyo, Iman da muka fito tare ta riƙe hannuna tana cewa, 


    "Wai da gaske barin gidan nan za ki yi ki bar mu mu kaɗai?"


   Ƙirjina na ji ya buga, saboda damuwar da na gani kwance a kan fuskarta. Dakalin ƙofar gidan na nemi wuri na zauna babu shiri. Zaunar da ita na yi kusa da ni sannan na rungumo ta jikina na ce,


    "Duk inda na je ai muna tare da ku Iman! Kuma ma babu inda zan je na bar ku muna tare har abada sai na ga auren ku da yardar Allah!"


   Murmushi ta dinga yi tana goge mini hawayen da ban lura da fitowarsu daga kwarmin idona ba. Ni ma hannu na saka na share mata nata hawayen sannan na ce,


    "Ba kin ce mini ya ce a gidansa za ku zauna ba?"


  Ta yi hanzarin ɗaga mini kai. Na ce "Yawwa! To kin ga muna tare ba za mu taɓa rabuwa ba!" 


      Da haka na shawo kanta da hira har aka aiko wani yaro kira na, na riƙa ta muka yi cikin gidan. Zuciyata cike da tunanin Haidar, da kuma ƙiyasin in da yana nan; da ya fi kowa murna da zumuɗin kayan da aka kawo. Saboda ya sha faɗin, idan ya girma ya zama babba, zai cika mini akwatuna da kaya, ya saka ni motarsa mu yi ta yawo cikin gari muna shan iska. 


    Guntuwar ƙwalla na goge da gefen mayafin da ke jikina, idona a kan Sajida da na ga ta gama shirin tafiya tsaf. 


    "Ba dai tafiyar za ki yi ba ke ma?" 


   "To Aunty me muke jira? Abin da ya kawo mu an yi, Allah dai ya nuna mana ranar mu dawo mu raka ki gidan Angon..."


    Kallon da na yi mata ya sa ta yi saurin rufe bakinta tana faɗin, "Ba fa zan bari ba Aunty!"


    Kafin na yi magana Firdausi ta fito da nata shirin. Tare na raka su ƙofar gidan, inda mazajensu suka jeru kowa da abin hawansa ya zo ɗaukar matarsa. Godiya na ƙara yi musu cike da ƙaunarsu cikin raina, har suka bar ƙofar gidan ban daina ɗaga musu hannu ba. Ina ƙoƙarin juyawa na koma hasken mota ta dallare mini fuska, hannu na saka da sauri na kare fuskata daga kashe mini idon da ake ta yi tsawon mintuna ba a janye ba. Hakan da na gani nan take jikina ya ba ni MD ne ya zo. 


     'Oh Allah! Ko me ya kawo shi yanzu kuma?"


    Tambayar da na yi wa kaina kenan, saboda dakan luguden da ƙirjina yake yi. Da sauri na juya da nufin shigewa gidan, odar da ya biyo ni da ɗiiiii ita ce ta sa na juyo babu shiri. 

     A hankali na dawo, ina wani irin taku a cikin hasken, ba tare da na san inda nake jefa ƙafafuwana ba. Damƙa ta na ji an yi, cikin sauri na zabura har ina ƙoƙarin ƙwalla ihu, hannuna ya ja ba tare da ya ce da ni komai ba ya buɗe gaban motar ya saka ni. 

     Ban tantance ba, sai jin na yi ya tayar da motar. Ido na zaro cike da tashin hankali da mamakin inda za mu je a wannan lokacin. Titi ya hau babu shiri na haɗiye wani yawu muƙut bakina yana rawa na ce,


     "Ina za mu je cikin dare haka? Ga shi ko Kawu ban faɗa wa zan fito ba! Don Allah ka tsaya kada mu je ko'ina Baba zai yi mini faɗa!"


    Abin da na faɗa kenan,   cikin muryar tashin hankali amma ko kallon gefena bai yi ba, ballantana ya ba ni amsa ko ya juya mu koma kamar yadda na nema. Juyowa na yi idona a kansa na haɗa hannu wuri ɗaya cikin marairaita na ce,


    "Please! Kada ka je da ni ko ina don Allah!"


   "Ok! Na bar ki mazan duniya suna kalle ki kenan ko? To kin gama zama gidan daga yau! Daman bikin tariyar ba dole ba ne! Ballantana zaman jiran lokacin ya sa ki dinga yin abin da kike so saboda kin ga ba na kusa. Wai ko tsoron Allah ba kya ji kike fitowa son ranki gaban wasu maza ba tare da kin nemi izinina ba!" 


    Kallon mamaki na bi shi da shi kafin na ce, "Yanzu daga cikin gidan zuwa waje ne zan tambaye ka don zan fito? Ƙawayena ne fa na rako, kuma mazajensu ne ba wasu maza ba! To mene aibu a cikin hakan? Sanin kanka ne ko ban da aure, girman alaƙata da su; za ta haramta mini mazajensu!"


     Ƙanzil bai ce da ni ba, sai ma karatun Alkur'anin da ya saka yana ta sharara gudunsa tamkar zai tashi sama. Muƙut na haɗiye wani yawu mai ɗaci, saboda tsabar tsoro da firgicin da nake ciki, ga kuma ɓacin ran da na ji sanadin mulkin da yake ƙoƙarin nuna mini. 


    "Ka tausaya mini don Allah! Kada ka sa a tuhumi inda na je ba tare da na sanar a gida ba!"


    Na ƙare maganar cikin rauni, muryata tamkar na yi kuka, amma bai bi ta kaina ba. Wani sabon tashin hankali bai sake dirar mini ba sai da na gan mu a bakin ƙofar gidansa. Babu shiri na zaro ido a ruɗe na ce, 


    "Don Allah ka yi mini rai tun kafin mutane su zage ni!"


     "Gara zagin, da abin da kike ƙoƙarin aikata mini!"


    Oda ya yi maigadi ya buɗe masa ya shiga da motar. Wuri ya samu a harabar gidan ya yi parking, sannan ya buɗe mini ƙofa ya riƙo hannuna. Kukan da nake yi bai hana ni bin shi ba, upstairs muka fara hawa bayan mun shiga cikin gidan. Takanas ya ɗauke ni irin ɗaukar da ake yi wa Indiyawa yana taku da ni ina rera masa kuka.  Ƙofar wani ɗaki ya dire ni, domin tun zuwana gidan a farko na na fahimci nanne ɗakinsa. 

     Key ya zura jikin ƙofar ya buɗe. Tare da jan hannuna ba tare da ya damu da kukan da ya ga ina yi ba. Rufe ɗakin ya sake yi sannan ya zare makullin, kai-tsaye sip ya buɗe, ya ciro wani sabon towel ya jefo mini a jiki. Cike da shan ƙamshi ya ce,


 "Tashi ki yi wanka. Ki cire wannan shigar tun da bayan ni da matan da suka zo gidan; akwai waɗanda kika gwada wa kwalliyar suka gani!"


     Ko motsi ban yi ba, illa kallon da nake bin shi da shi cike zallar mamakin asalin halin MD da na sani ya dawo. Saɓanin Aliyuna mai tausasa mini harshe da zafafan kalamai masu saka zuciyata natsuwa. Nan take tsoron shi ya kama ni, da ido na dinga aika masa kallon tsabar mamakin da ya ba ni. Sai hawayena da nake ta sharewa jefi-jefi ina zuƙar majinar kuka.


     "Ko ki tashi ki yi abin da na ce! Ko kuma na tuɓe ki da kaina na yi miki wankan."


     "Don Allah! Don girman Allah ka tausaya mini ka mayar da ni gida! Wannan wane irin abu ne hak...?"


Abin kunyar da yake son saka ni aikawa, ya sa na duƙe ina ta gunjin kuka tamkar wacce aka daka. Sannan na ƙara da cewa,

      "Idan dai fitowar da na yi ita ce matsalar ake ƙoƙarin yi muni irin wannan punishment ɗin;  to wallahi daga yau ko ƙofar gidan ba zan sake leƙowa ba har sai an fito da ni da nufin kawo ni wurinka." 


    Dariyar gefen baki na ga ya yi kafin ya zauna kusa da ni, mayafina ya fara ja na yi hanzarin riƙewa tare da ƙanƙame jikina. Bakinsa ya kai cikin wuyana ya ɗan laso fatar wuyan kaɗan, na yi hanzarin zabura na miƙe tsaye ina faɗin,


     "Don Allah ka tausaya mini ka mayar da ni, kada ka sa a yi ta nema na ba a gan ni ba hankulan mutane ya tashi!"


    "Idan kina son komawa da gaske, to mu taimaki juna kawai! Ki ba ni to, ni kuma sai na mayar da ke!"


    Bakina yana rawa na ce, "Me zan ba ka?"


   Kallon da ya aiko mini ya sa na fara ja da baya, ina ta faman girgiza kai tamkar wata ƙadangaruwa. Sai da na ji bayana ya jingine da bango sannan na zuƙe majinar kuka na ce,


    "Ka rufa mini asiri kada ka janyo mini surutun mutane! Wannan abin kunya har ina?"


     Dariya na ji ya fara yi tamkar ba shi ne yake mini muzurai da zarar ido ba. Haushi ya sa na kawar da kai saboda ganin kamar tashin hankalin da nake ciki bai dame shi ba. Bakin ƙofar na nufa gadan-gadan duk da na san ba za ta buɗe ba ballantana na samu ƙofar guduwa. 

     Nufo ni ya yi da wani siririn murmushi a kan fuskarsa ya tsaya bayana. Ƙoƙarin buɗe ƙofar nake ta ƙarfi amma ko gezau ba ta yi ba, shirunsa da na ji na ɗan lokaci; ya sa na waigo tare da ɗora idanuwana a kan fuskarsa. Wata jar harara na wurga masa, saboda wani irin kallon da yake yi mini. Hannunsa ɗaya a aljuhu, ɗaya yana shafar gemunsa da shi, da wani kalar murmushi a kan fuskarsa. Juyawa na yi bayan wurga masa wata kalar harara a ƙufule na yi ta murzar handle ɗin ƙofar ina jijjiga cike da gayya. 


    Numfashinsa da na ji a bayana bai sa na fasa murɗar ƙofar ba. Gemunsa na ji a dokin wuyana, babu shiri na zabura, ina ƙoƙarin barin wurin ya janyo cikin zafin nama ya haɗa ni da jikinsa. Wuyansa a kafaɗa ta ya zuro hannuwansa duka saman ƙirjina, duka na fara kai wa hannuwan nasa amma bai fasa murza ƙirjina ba yana sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya. 

     Kokawar ƙwatar kaina na shiga amma yi na kasa, mintuna kaɗan jikina ya fara rawa. Saboda saƙonnin da ya fara aika mini cikin dabara da salo irin nasa, dole na fara bi ina sauke numfashi saboda tsikar jikina da tashi gabaɗaya. 


    "Innalillahi!"  Shi ne sautin da na furta cikin rawar baki saboda tallabar da ya yi mini ya ɗora a tsakiyar gadon. Ƙarshen gadon na isa cikin zafin nama ina haɗa hannuwana wuri ɗaya cike da masifar tsoron da ya shige ni na ce,


    "Ka yi wa Allah! Ka yi mini rai kada ka janyo mini abin kunya da surutun mutane!"








To fa😊









D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*TALATIN DA UKU.*


     Tsawon mintuna ya ɗauka tsaye yana kallona riƙe da ƙugu, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Kafin ya bar jikin gadon ya nufi hanyar fita ɗakin kai-tsaye. Jikina yana rawa na zabura hantar cikina tana kaɗawa. Ga mamakina, hannunsa na ga ya saka a aljihu ya ciro key yana ƙoƙarin buɗe ɗakin, ni ma na diro daga kan gadon.  Yana buɗe ɗakin ya fice a ɗari na rufa masa baya, ina goge hawayen da ke kan fuskata. Yana gaba ina bin sa a har muka fito gidan. Motarsa kawai ya buɗe ya shiga ya zauna, tare da dafe kansa. 

     Ban jira umurninsa ba ni ma na buɗe seat ɗin gaba na shiga na zauna, mayafin da ke jikina na saka ina ƙoƙarin goge hawayen da ya jiƙa mini fuska. Sannan na jingina bayana da seat ɗin kujerar ina sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Shiru ya ratsa tsakani tsawon mintuna kafin ya tayar da motar, a hankali ya ja ta muka nufi bakin gate. Maigadi ya wangale masa ƙofar gate muka fice gidan yana masa a dawo lafiya.

       Babu shiri na sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, saboda tsabar farincikin ganin zai mayar da ni gida. A gefe ɗaya kuma zuciyata cike da tunanin amsar da zan bai wa su Inna, idan suka tambaye ni abin da ya fitar da mu cikin daren. Wani kallo ya yi mini kafin ya ɗauke kansa yana cizon haƙorinsa, raina na ƙara haɗewa saboda ko kaɗan ba na farinciki da abin da zai ɓata masa rai. Cikin siririyar murya da ɗari-ɗari na ce da shi,


     "Ka yi haƙuri! Allah ya gani ban yi da niyyar ɓata maka rai ba. Kawai ina tsoron surutun da mutane za su yi a kan haka, matuƙar suka ji labarin na kawo kaina da kaina."  


     "Ok tom! Yana da kyau ki bi ta mutane ki saɓa wa mijinki!"


    Shiru na yi masa na ɗan lokaci, kafin na sake cewa da shi, "Shi kenan kawai sai a yi mini kallon wata mara kunya! Babu sanin kowa na kwaso jiki na biyo ka kamar wacce aka ce da ita 'je ki kya gani' haka kawai mutane su yi mini kallon wata 'yar iska ko a buga mini tambarin harija. Ina zaman zamana ka sa a shiga da ni bakin duniya!"


     Murmushi na gani a kan gefen bakinsa kafin ya furzar da iska mai sauti daga bakin nasa ya ce,

     "Da yake zina zan yi da ke ba sunnar ma'aiki ba! To su mutanen da kike gudun surutunsu; ba za ki taɓa iya musu ba. Kuma su saboda ke; ba za su iya bijirewa mijinsu ba, a kan abin da yake so kuma yake ƙulafuci kansa. Da kin san halin da nake ciki da ke da kanki kin nemi mu yi zamanmu kada ki koma gidan, matuƙar dai kina tausayina. Amma babu komai, duk wayon amarya watarana sai an sha manta. Ki gama gudun da tsalle-tsallen ki dawo hanyar gaskiya, a lokacin ni ma zan yi abin da ba zan ji kuka, ko magiyar da duk za a yi mini ba."


    Wani hargitsattsen kallo na yi masa ƙirjina yana bugawa, shi ma kallo na ya yi yana wani kalar murmushi tare da shafa gemunsa. Idona a kansa na yi hanzarin faɗin,

     "Tsoron ka ya fara kama ni fa! Domin zuciyata ta fara rawa a kan tambayar da ke ta mini kai-da-komo cikin rai. Wacce ta tsaya mini a ƙahon zuci ta kasa fita, kuma ta kasa faɗawa ciki na samu sukuni. Don Allah ka sanar da ni gaskiya, shin ni kake so ko jikina?"

      Tsawon ɗan lokaci yana dariya mara sauti, kafin ya damƙo hannuna ya rintse da ƙarfi har sai da na yi 'yar ƙara. Sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce,

     "Da jikinki kaɗai nake so; da tuni na gama mallakarsa! Da jikinki kaɗai nake muradi; da tuni kin gama zama akalata, domin na sarrafa ta ta yadda na ga dama. Saboda ina da dubarun kama zuciya ko da kangararriya ce, ballantana irin taki mai rauni da saurin rusuna. Ba zan ɓoye miki ba! Da ni ɗan iska ne, da tuni ni da ke ba irin wannan turbar da muke kai muke zaune kanta ba. Zan hure miki kunne da yawa, zan buɗe miki idanuwana sosai, kuma zan goge miki hadda, ta yadda ba za ki yi shayin idon kowa ba, matuƙar na neme ki; dole ki kawo ƙafafuwanki a duk inda nake. Amma tabbas yanzu da igiyar aure ta ƙulle wuri ɗaya mu ni da ke; ina kwaɗayin shiga kogo ko don na samu mafaka daga daga kurayen da suke ƙoƙarin kai mini cafka! Sannan na kauce wa abin da ba halina ba, wanda kuke ƙoƙarin jefa ni a ciki ta ƙarfi duk da yadda nake ƙoƙarin katange kaina kansa." 


    Shiru ya yi na ɗan lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ku mata har kullum tunaninku iri ɗaya ne! Da kun ga ana bin ku da wannan sabgar, ko kuma an fito muku da zahirin komai a yadda yake; sai ku yi tunanin kamar don wannan abin kaɗai ake son ku. To ni ba na cikin maza masu rufi, duk wata shaƙuwata; ina nemar mata ruwa mai sanyi na sha, irin wanda na san zai ladaftar da ita, sai dai idan an hana ni na haƙura na sha lemun tsami. Amma ina tsoron watarana ku janyo na cika gidana da mata huɗu, domin ba zan zauna ana gara ni kamar ƙwallo ba. Saboda gudun surutun mutane, sai kuma ni a cutar da ni, haka kawai don kina gudun a kira ki da sunan harija, shin haka ne ko?"


     Wani kallo ya yi mini yana murmushin gefen baki, tare da kafe ni da ido ƙur, ko tsoron tuƙin da ke gabansa ba ya yi. Harara na aika masa tare da turo bakina, saboda haushin da ya cika mini zuciya. Tagumi na yi da hannuna ɗaya idona a kansa na ce,


      "Su kurayen da suke ƙoƙarin kai maka cafka; ba su san kana da mata ba ne?" 


     Raina yana ƙuna na furta maganar, domin tun lokacin da ya yi zancen; na ji zuciyata tana suya. Har na dinga hango matan da yake zancen suna ƙoƙarin janyo ra'ayinsa domin ya kasance su cikin idona. Rintse idona na yi cikin sauri hawaye ya dinga tsalle daga kwarmin idanuwana zuwa hannuna, kafin ya ɓalle ya fara bin hannun nawa yana sauka saman jikina.  Wata 'yar dariya ya yi mai sauti kafin ya ce,


     "Tun da ku kun kasa; ai sai a kula muku da ni ta can ɓangaren yadda ya dace!"


     "E, a je a kula da kai ɗin! Auren mata duka huɗu ka je ka yi kada ka fas..."


   Da ƙyar na hattama maganar saboda kukan da ya turnuƙe ni. Tsabar takaicinsa, da mugun kishinsa da ke cizon zuciyata; ya sa na nemi  fita daga motar a lokacin da na so buɗe ƙofar ta ƙarfi duk da bala'in gudun da yake shararawa. Allah ya tsare duka ya sa ƙofofin a lock, da na yi mugun ganganci domin ya gano tsananin ɓacin ran da na shiga a kan furutansa, waɗanda ke ƙoƙarin jingina shi da wasu mata bayan ni da matarsa. 


     Kansa ya shafa cike da nishaɗi a kan fuskarsa ya ce, "Gida huɗu maganin gobara! Idan dama ta ƙi sai a koma hagu. Tun da gudun surutun mutane zai iya sa a ƙi sauƙe nauyin da Allah ya ɗora! Har ana ƙoƙarin jingina ni da wani bahagon tunanin da babu komai a cikinsa sai sharrin shaiɗan la'ananne! Amma idan ana so na tsayar da kaina wuri ɗaya a ba ni kawai idan na roƙa! Saɓanin haka kuma mu je ganin gari!"


      Kuka na fashe da shi wiwi, saboda zuciyata ta kasa shanye bala'in dukan da maganganunsa suka yi mini a ƙirji. A fusace na ce da shi, "Wallahi duk macen da ka raɓa sai na soke ta da wuƙa ta mutu! Don duk abin da take da shi ni ma ina da! Kuma zan iya yi maka abin da ba ta isa ta yi maka ba!" 

     "Ai za mu gani, don inda babu ƙasa a nan ake gardamar kokawa. Zan tura miki kuɗi ki gyara kanki, ta yadda zan gano ke da su akwai bambancin da kike faɗa! Saɓanin haka kuma kada a zarge ni a kan duk abin da na aikata!"


     Ƙanzil ban ce da shi ba har ya yi parking Shazam suya ya fita ya dawo da ledodi a hannunsa. Kawar da kaina kawai na yi saboda dariyar da na ga yana yi a duk lokacin da ya kalle ni. Har muka kai ƙofar gidan ban bi ta kansa ba, shi ma bai ce da ni komai ba. Illa 'yan waƙa-waƙensa da yake yi alamun yana cikin farinciki. Parking ya yi ƙofar gidan, amma ya ƙi ba ni damar fita. Ni kuma a lokacin na zo wuya, tare da cin alwashin ko sau dubu zai neme ni ba zan taɓa nuna masa gajiyata ba, ballantana ya hango kasawar da zai nemi rakito mini abin da zai sa na ƙone garin Sokoto gabaɗaya ƙurmus.  

       Zulo jikinsa ya yi kusa da ni ya rungumo ni, na yi hanzarin ƙwace jikina ina ture shi da hannuwana. Saboda murmushin da yake yi mini ya ƙara kai ni bango, duk da na san yana yi ne kawai don ya ƙara tura mini haushi tun da na ƙi amince wa buƙatarsa. Ganin da gaske na kai wuya; ya daina ƙoƙarin haɗa jikinsa da nawa, ya yi hanzarin riƙo hannuna fuskarsa a haɗe ya ce, 


     "Plss! Ki daina kukan nan ya isa haka nan! Saboda ba shi ne zai ƙwace ki ba, matuƙar ba ki fanshi kanki da kanki ba!"


    Hannuna na zare daga cikin nasa saboda hango Kawu ya fito cikin gidan, sannan na zuƙe majinar kuka na ce da shi, 


"Buɗe mini ƙofa!" 


   Babu musu ya buɗe mini, kusan tare muka fita ni da shi, ya durƙusa har ƙasa ya gaishe da Kawu, kansa a ƙasa kamar ba shi ne ya gama zaro zance ba. Majinar kuka na zuƙe ina ƙoƙarin raɓa wa ta gefen Kawun na wuce; ya yi hanzarin faɗin,


     "Kukan me kike yi ke kuma?"


    Kafin na yi magana MD ya riga ni da cewa, "Tun da muka bar gidan nan take kuka Kawu, wai ba ta so ka gano mun fita ka yi mata faɗa!"


    Da sauri na kai kallona kan fuskarsa, duk da babu wadataccen haske a wurin; sai da na yi masa hararar gefen ido a lokacin da muka haɗa ido Sannan na kawar da kaina ina murguɗa baki kamar wata ƙaramar yarinya.

     "To mene ne abin kuka a ciki? Ba mijinki ba ne? Kuma ai ya sanar da ni za ku fita tun kafin ku tafi! To kuma kukan na mene ne, idan ba sakarci irin naki ba?"


     Mayafina na saka ina goge fuskata da ke jiƙe taf da hawaye, sannan cikin muryar kuka na ce da shi,


 "To ai Kawu ni ban faɗa muku ba!"


    "Kin ci gidanku Zaituna! Shi tasa faɗar ba ta yi ba har sai kin yi taki kenan? Zo ki wuce kada na kai miki faka ban sani ba!"


    Sum-sum na bar wurin, zuciyata cike da tunanin lokacin da ya sanar da shi ban sani ba. Ko da na shiga gidan ɗakin Umma na yi wa tsinke, ina tura ƙofar ɗakin na yi tozali da akwatunan lefen da aka kawo, a jere reras gwanin burgewa. Bakin gadon Umma na zauna ina goge fuskata raina yana suya, cikin sanyin jiki na baje kan gadon ina mayar da numfashi tamkar wacce ta sha gudu. Iskan fankar da ke ta kaɗawa ya dinga bugun fuskata na yi hanzarin lumshe idona. 


      Tsawon mintuna na ɗauka a kwancen ko motsin kirki na kasa yi. Muryar Inna na jiyo a bakin ƙofar ɗakin tana faɗin,


     "Ashe kin dawo?"


Daga kwancen na ce mata, "E, Inna! Daman ban yi niyyar bin sa ba shi ne ya matsa mini. Kuma a tsaitsaye na sa muka juyo gudun a yi ta nema na ba a gan ni ba!" 


    Ɗakin ta shigo, ta tsayu a kaina tana faɗin, "Me ya faru? Na ji muryarki kamar kin yi kuka?"

     Babu shiri na ji wani sabon kuka ya zo mini na fara rera abina wiwi, Inna Kulu ta fara salati cikin tashin hankali tare da tambayar me aka yi mini, kafin na yi magana na ji Kawu ya nufo ɗakin yana faɗin,

     "Aikin shirme fa! Idan ban da tana son wahalar da kanta mene ne abin kuka don mijinta ya fita da ita? Ko da bai faɗa mana ba ballantana ya sanar da ni tun kafin su fita! Amma ta zauna tana  aikin kuka haka kawai ta janyo wa kanta ciwon kai a banza!"


    Inna Kulu ta fara tafa hannu, sannan ta riƙe baki tana 'yar dariya ta ce, "Yanzu a kan haka kike ta wannan uban kukan Zaituna?"


   Shiru na yi musu ban ce ƙanzil ba, ya ajiye mini ledar da ya shigo da ita yana sanar da ni in ji mijina. Har suka gama bi da zancen shirmena da suke faɗa ya fice ban motsa ba. Inna ma wayata ta miƙo mini tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin ta ce,


     "To ko yaranki dai salun alun suka yi barci, tun da suka neme ki na ce da su kun fita ba su sake ɗaga zancen ba! Don haka don Allah ki daina kukan banzan da ya dace a ce ke kike hana wani yi!" 


    Bayan fitar ta da ɗan lokaci na ji shigowar saƙonni har sau biyu a cikin wayata. Ko da na duba na ga alert ne daga MD, na zunzurutun kuɗi har dubu ɗari lakadan. Sannan ɗayan saƙon da yake jajjadada mini abin da zan yi da kuɗin, tare da sanar da ni tun lokacin da yake kashe mini ido da hasken motarsa; ya kira Kawu a waya ya sanar da shi zai fita da ni. Don haka na daina damun kaina shi ma ba ya fatan na saɓa musu saboda shi.

     Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na furzar da iska mai zafi daga bakina. Agogon da ke manne jikin bangon ɗakin na ji ya buga, alamun ƙarfe goma dam na dare. Firdausi ta faɗo mini a rai, amma ganin dare ya yi ya sa na ƙi kiran ta, data na kunna aka yi dace na hango ta online. Nan take na yi mata voice a kan ina so ta kai ni wurin masu gyaran jiki, saboda ina so na nuna masa ko gaba da gabanta.

     Babu ɓata lokaci ta duba saƙon, ta ce da ni gobe za ta zo mu je gidan ƙamshi na Humkam. Cike da jin daɗi na sauka online, saboda na daɗe da jin labarin matar, ta shahara sosai wurin gyara amare, 'yanmata, har ma da tsofaffin auren da ke buƙatar zama sabon zubi, tamkar a lokacin aka kawo su gidan miji.


    Wayar na ajiye kasancewar ban yi Isha ba, na sauko daga kan gadon idanuwana suka ci karo da ledodin da Kawu ya kawo, kuma ya ce in ji mijina. Buɗe ledodin na yi tare da zaro ido waje, saboda duk da tare muka je ya siyo kayansa; amma ban san mene ne ya saya ba. Yawu na haɗiye muƙut! Saboda ganin danƙara-danƙaran kaji guda biyu cikin leda kowace ta sha kayan haɗi sai ƙamshi ke tashi. Ɗayar ledar kuma drinks ne sabon zubin da wayewata ba ta kai na sha irinsu su ba, sai Hollandia guda biyu raɓa ta kama jikinsu. 

     Kaza ɗaya na ciro da sauran kayan jiƙa maƙoshin na saka a leda na fito ɗakin. Kaina yana sara mini na shiga ɗakin Inna da sallama na ajiye mata ledar. Ganin ba ta cikin ɗakin; zuciyata ta ba ni cewa tana wurin Kawu, kai-tsaye na fito ina ƙoƙarin zuba ruwa a buta ta fito daga ɗakin Kawu tana faɗin,


     "Idan kina ƙara abincin akwai shi kitchen!"


    Ɗan murmushi na yi mata sannan na ce, "Saƙo na can ɗakinki na kai miki ke da Kawu. Ba sai kin ajiye wa su Iman ba, nasu yana hannuna da safe zan ba su!"


    "To" kawai ta faɗa, sannan ta shige ɗakin, na gama alwala na koma ɗakin Umma. Ina ƙoƙarin tayar da sallah ta shigo da ledar a hannunta tana faɗin,


     "Ke da aka siyo wa abu don ki ci jikinki ya ƙara ƙwari; shi ne za ki kwashe ki ba mu? To ki rage, don ya yi mana yawa daga ni sai Sale!"


     "Don Allah Inna ki bar shi ki je ku ci abinku!"


     "Ba za ta saɓu ba, kura da shan bugu gardi da kwasar kuɗi!"


    Bakina na rufe cikin sauri saboda fahimtar inda ta dosa, ga shi kuma daman abin da na yi gudu kenan tun farko.


 "Wallahi Inna, billahillazi babu abin da ya shiga tsakanina da shi! Shi ya ga dama don kansa ya siyo, amma ba don wani abu ya faru tsakanina da shi ba!"


     Abin da na faɗa kenan ina ƙumshe dariyata, ita ma dariyar ta fara yi sannan ta ce, "Ni dai ba bincike na miki ba! Ko ma ya yi ai halalinsa ce ke, idan ma kika hana shi za ki kwasar wa kanki zunubi ne a banza! Don biki ba dole ba ne, ɗaurin aure ne mai muhimmanci."


    "Allah dai ya yafe to!"


Iya abin da na faɗa kenan, sannan na tayar da sallah cikin sauri. Ita ma ta fice tana mitar ba za su cinye su kaɗai ba, dole ta ajiye wa su Ummu Salma nasu kaso.


      Bayan na gama sallah na ɗaga hannu, na dinga jero addu'o'i iri-iri. Kuma duka a kan Allah ya hana wa MD ganin kyawun wasu mata ballantana su shiga ransa. Allah ya sa duka matan duniya, fuskokinsu su koma na jakuna a cikin idanuwansa. Tun ina addu'ar cikin ƙumaji, har na koma yi wa kaina dariya, saboda zaƙewar da nake yi wurin toshe wa sauran mata daraja duk don kada ya ga wata ya ce yana so a cikinsu bayan ni. 


      Sannan na gyara zamana da kyau na ci kazata, ina ci ina lumshe ido, na kora da Hollandia na baje ƙasan sallayar ina mayar da numfashin ƙoshi. Mintuna a tsakani barci ya yi awon gaba da ni cikin yanayi mai daɗi. Saboda mafarkansa da na dinga yi kala-kala kuma dukansu muna ta faranta wa juna. Da safe na tashi cikin kuzarina, a raina na ce,


 'Kaza duniya ce!'


 Su Ummu Salma ma, bayan Inna ta ba su na ƙara musu. Sannan na saka sauran drinks a firij, na fara gyara gidan. Saboda Firdausi ta ce tun da safe za mu je don a yi komai da wuri a gama mu dawo cikin lokaci. 

       Ƙarfe goma da rabi a ƙofar gidan HUMKAM GIDAN ƘAMSHI ta yi mana. Macen da ko a gidan masu gyaran mata kayanta sun fita daban da na kowa. Tarba ta mutunci muka samu a wurinta, cikin sakin fuska tamkar mun saba da juna. Don ita ma Firdausi ta ce mini labarinta ta ji a bakin wata maƙociyarta, ta ci burin zuwa Allah bai nufa ba, sai ga dalilina ya sa mun zo, saboda ko adireshinta wurin maƙociyar tata ta samu. Sai ga shi mun same ta fiye da yadda muka yi tsammani.  

     Ɗakin gyaran amare ta kai mu, babu ɓata lokaci ta fara aikinta cikin a kaina ƙwarewa, don mun yi sa'a ba mu taras da jira sosai ba. Ita da kanta ta gyara ni na dawo tamkar wata tarwaɗa don kyau, domin fatar jikina har wani santsi take yi tare da sheƙi. Kuma Haskena ya ƙara fitowa, fuskata ta yi luwai, ni kaina da na kalli kaina a madubi sai da jinjina wa HUMKAM GIDAN ƘAMSHI. Firdausi da sauran wasu matan da ke gidan sai zuzuta ni suke yi, nan take na fara jin kaina yana kumbura, a raina na ce,


     'MD ka shiga uku! Sai ka san ni kake yi wa gori!'


     Hotuna Firdausi ta yi mini, sannan ta ce da Humkam ta haɗa mini kayan mata. Babu ɓata lokaci ta ja mu zuwa wani ɗaki, wanda babu komai a cikinsa face kayan gyaran mata kala-kala kowane a muhallinsa cikin kwalbensu. Mai ɗauke da tambarin sunanta da abubuwan da ke ciki, har ma da lambar wayarta a jiki kamar haka +234 813 250 6044.

    Sosai abin ya burge ni, kuma jikina ya ba ni tabbas na zo gidan ƙare kukanki bora a wurin miji. Domin kaya ne original, irin waɗanda ko a fuska za a tabbatar da qualitynsu. Zama muka yi tana fito da su ɗaya bayan ɗaya tana yi mana bayani dalla-dalla, ta yadda za mu yi saurin haddacewa kuma mu yi yadda ake buƙata.


    "Kun ga wannan, sunansa HARBI GADO! Babban daka ne, yana matuƙar taimakon ma'aurata, ana shan shi da magriba a tsaye, kuma da madara mai sanyi ake sha. Kuɗinsa @2300.  Sai murmushin amarya, daka mai saurin saukar da ni'ima a jikin mace. Kuɗinsa 2k. Ga kuma dakan 'yar gata, ƙorama, green emergency. Dukansu daka ne masu kyau da suke gyara mace ciki da waje. Zan siyar muku da kowane 1k idan kun saya duka ukun za su kama 2600.  ƁATA GABAN KISHIYA, ɗanɗano ne da babu kama hannun yaro, kuɗinsa 1500 kacal. SA BUZU KUWA VIP mix..wannan dakan gaske ne, duk wani muzurai da murza gashin baki sai namiji ya dara. Waton da gaske shi buzun sai ya yi kuwwa. VIP @2300."


    Kallon juna muka yi da Firdausi muka yi dariya, sannan Humkam ta ci gaba da kora mana bayani, 

     "Akwai kuma sa buzu kuwa normal, idan kuka samu madara mai ɗimi, kika zuba cokali ɗaya, tare da zuma mai cizo. Shi kenan kin gama haɗa kanki da kanki farashinsa 1700. TABAJE ma yana matuƙar tayar da sha'awa, kuma ya saukar da ni'ima. Yana maganin sanyi maza da mata suna sha, domin tabajenmu ya sha bamban da wanda kuka sani. Ana bayar da kowace roba 1700. TSUMIN MAGARYA, yana wanke mara ya saukar da ni'ima. Kuɗin jarka 3k amma zan iya ba ku shi a 2500. ZUMA MAI CIZO, haɗaɗɗiyar zuma kenan, zan bar muku ita a free dakan 'yargata. A kan prize 2100."

MUMMUNA DA AIKI, wannan haɗin magani ne mai matuƙar ƙarfi. Saboda ƙarfinsa sai dai a sha cokali ɗaya da madara rabin gwangwani. Zan bar muku shi a 2200."


    Firdausi ta fara tsallen murna sannan ta ce, "Ma sha Allah Humkam! To yanzu ki haɗa mana kowane, sannan ki daɗa mana bayani gudun mantuwa. Sai dai kuma ina so ki yi mana ƙarin bayani a kan shan magungunan gari don na ji wasu suna faɗar yana toshe hanji."


    Humkam tana murmushi sannan ta ce, Amfanin shan maganin daka, yana saukar da ni'ima sosai, kuma yana daɗewa yana aiki a jikin mace. Sannan babu wata matsala matuƙar maganin da za ki sha kin bi shi a kan tsari. Kuma akwai CCCIƁI, idan kuna so zan ba ku, don yana haka yana wuta. Sosai yake ciko mace, ya matse ta gam-gam ta yadda komai nata zai haɗe. Duk roba ɗaya 2300.  Sai zakaran maƙale mata da gaigai, zan ba ku shi a bononza 6k idan kuna buƙata."


    "Ma sha Allah! To a haɗa mana duka, sannan a yi total ɗin kuɗin mu ji nawa za su kama. Saboda ina so ƙawata ta haukatar da oganta, ta yadda duk ya motsa sai ya kira sunanta."  Duka na kai mata muka saka dariya gabaɗaya, sannan na yi tagumi zuciyata cike da tunanin sunan wani da na ji ta ambata; ƁATA GABAN KISHIYA. Saboda har ga Allah ba na fatar na cutar da matarsa, hakan ya sa na sauke ajiyar zuciya na ce da ita. 


     "Amm! Wannan maganin da na ji kin ce ɓata gaban kishiya, kada a saka shi. Saboda ba na son na yi abin da Allah zai tambaye ni."


     Dariya ta yi mai sauti sannan ta ce, 

"Ai kamar yadda kike shan maganin gyaran jikinki; haka shi ma yake. Kawai dai sunansa ne a haka, saboda matuƙar kika yi amfani da shi ba zai taɓa jin ki daidai da kowa ba. Kuma abu ne a zahiri, macen da ke gyaran jikinta ba a haɗa ta da 'yar ba ruwana a karɓi abin da aka samu. Amma idan har zuciyarki ba ta aminta da shi ba ki bar shi kaw..."


     "Don Allah share ta! Saka mana kawai duk muna so!"


   Harara Firdausi ta aiko mini bayan ta gama faɗar maganar. A leda aka saka mana kayan, sannan aka yi total, kuɗi suka kama dubu hamsin da bakwai 57k har na gyaran jiki, ta yafe mana canjin da ke sama. Sannan ta haɗo mana da turaren wutarta mai shegen daɗi, wanda tun da muka shiga gidan ƙamshinsa ya kwanta mini a rai. A gabanmu ta zuba cicciɓin a robobi, wanda ta saukar a lokacin da zafinsa har tiririn ƙamshi yake yi.

    Godiya muka yi mata, bayan ta kawo mana abinci muka ci. Sannan muka yi sallama da ita, da ƙudurin idan muka ji daɗin kayan, kuma suka yi aiki yadda ake so za mu dawo. Liƙabi na saka, saboda kare wa rigimammen angona mutuncin aurensa. Domin ni kaina ina ji masa haushin wani ya ga yadda na ƙara zama, tun da har na san ba ya so. 

       Misalin  ƙarfe biyar da kwata na yammaci muka koma gida. Tare da tsarabar kayana a leda, Firdausi ta baje wa Inna kayan duka, tana yi mata bayanin yadda suke filla-filla. Inna sai jinjina kai take yi, cike da jin daɗi ta yi ta zuba wa Firdausi godiya da sa albarka. Ita ko ta samu abin da take so, har da zaƙewar cewa, Inna ta saka mini ido na yi komai a yadda aka ce, har da roƙon don Allah kada ta ɗaga mini ƙafa sai na yi komai yadda ake so.

     Ajiyar zuciya na sauke, bayan tafiyarta, saboda wani sabon tunanin baya da ya zo mini. A lokacin da Maman Taufiƙ take ta hidimar ire-iren kayan matan, ni kuma ina mata kallon marar abin yi. Saboda ganin ni babu ruwana da irin wannan sabgar, saboda halin Mukhtar. Amma ga shi yanzu tun kafin na shiga daga ciki na fara zama 'yar mai ganye.


     "Allah Sarki Maman Taufiƙ!"



 








 Hmmm!








D. AUTA CE



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*TALATIN DA HUƊU.*


      Abin da na faɗa kenan cikin karyayyiyar muryar da babu ɓata lokaci hawaye ya cika mini ido. Saboda tsabar tausayin ƙaddarar da ta ruguje mata farincikin gidan aure. A raina, na ci alwashin nemo ta, duk da ban san ta ina zan dosa ba balle na gwada sa'ata ko za a dace.


    Daren ranar muna chat da Firdausi ta ce da ni, Humkam ta kira ta a waya ta ce mu zo ga BACK TO VIRGIN idan muna so. Ta manta da shi ne tun farko da ta haɗa mana da shi a cikin kayanmu. A cewarta yana dawo da budurcin budurwar da ƙaddara ta sa ta rasa budurcinta. Haka ma matar aure yana mayar da ita tamkar sabuwar budurwa muddin ta yi amfani da shi.

  Shiru na yi mata kafin na mata reply da cewa, "Ni fa kada ku je ku janyo a kashe ni fa! Na fara jin tsoron waɗannan kaya da kuke ƙoƙarin ɗura mini a halaka ni a banza!"

     Dariya Firdausi ta dinga turo mini emoji da stickers tamkar wata zautacciya, sannan ta ba ni amsa da cewa,


 'Lafiyarki muke nemar miki Hajiya!' 


   "Ohh! Yanzu ban da lafiya kenan?"


   'Ina kika gan ta kuwa? Shekara huɗu babu miji a hannu!'


   "Abin na gori ne?"


'E, idan kin ji haushi ki rama ke ma!"


    Daga haka muka ci gaba kwasar juna, kafin MD ya kira ni a waya na kashe datar na gyara kwanciyata. Hira muka sha da shi sosai, har yana cewa na ɗaukar masa hotona a yadda nake na turo masa. Amma ƙememe na ƙi saboda ba na so ya gan ni sai ranar da za a kai masa ni. Gudun ya ƙara janyo rigimar da za mu hau sama da shi mu faɗo ƙasa, a kan alwashin da na ci, na sai an kai ni ko zan bari ya same ni a yadda yake so.


    ***

Bayan kwana biyu hidima sai kankama take yi, domin ya hana a yi kowane irin taro a bikin sai na ranar tariya. Ni ma ban tsara kowane biki ba ko da bai hana ba ni ma ban da niyyar yin komai. 

     Ana sauran kwana uku, Kawu Sale ya darzo mini kayan ɗaki na ji da kwatance. Domin tsofaffin kayana aka siyar, aka haɗa kuɗin da waɗanda Baba Ali ya turo aka yi mini kayan fitar kunya. Kasancewar ranar Juma'a ne tariyar, ranar Laraba aka je aka mini jere gidan MD, ɓangaren da ya keɓe mini ni kaɗai ba tare da matarsa ba. Daman can gidan sashe biyu ne, kowane yana da sama yana da ƙasa. Hakan ya sa sashenta daban nawa daban, kuma a cikin kowane sashe akwai ɗakinsa a ciki. 

    Lokacin da su Firdausi suka dawo, suka sanar da ni sun taras da matar MD a gidan. Ita da ƙawayenta sai habaici suke sakar musu a lokacin da suka je su gaisa da su. Saboda tsabar sun raina mutane waƙoƙin habaici suka dinga saki cikin speaker mai ƙara, gabaɗaya suka cika gidan da kiɗa suna ta rawa da ihu tamkar ana wani ɗan ƙaramin fati. A ƙoƙarinsu na son nuna abin bai dame su ba, wasu daga cikin 'yan'uwana sun so su tanka su; Inna Kulu ta hana su da abin ya zamo fitina a tsakaninsu.  

    

   'Alhamdulillah!'


Kalmar da na faɗa kenan a raina, saboda ni kaina ba na so a biye su, mu taru da su mu zama ɗaya. Saboda na san zafin kishi da kishiya, duk da ba na tare da Mukhtar irin tarayyar miji da mata; amma na ji ciwo sosai a lokacin da zai auri Barira. Don haka dole ne na yi wa Fatima uzuri, saboda kishi masifa ne, kuma bala'i ne mai zaman kansa, matuƙar ba a saka dutse aka danne zuciya ba. 

     Daren ranar na sha kuka ba kaɗan ba, saboda ganin da gaske Umma ba za ta dawo a yi komai da ita ba. Na kira ta a waya aka dace ta ɗauka, ina kuka na ce da ita ta don Allah ta yafe mini duk abin da na yi mata. Amma ƙanzil ba ta ce da ni ba, da na matsa mata da kukan ma katse kiran ta yi ta bar ni da waya riƙe a hannu ina ta kukan. 

     Har raina, a lokacin  ba na farinciki da barin gidan Kawu, matuƙar ba ta yafe mini ta saka wa aurena albarka ba. Ga shi shi kuma ya rantse ko bai sani ba idan na je wurinta bai yafe mini ba. Na ci kuka kamar zan shiɗe, saboda ba na so na kunyata shi na je wurin Umma, gudun ya zargi kamar bai isa da ni ba. Kuma zai ga kamar na watsa masa ƙasa a ido na nuna masa uwata ta fi shi.

      Lallena da aka yi wuni sukutum ana yin sa na kalla, ya yi ja sosai saboda ya sha muhallabiyya. Sannan zanen baƙin lallen da aka zana mini ya ƙara ƙawata adon lallen sosai. Kukan da nake yi ya ƙaru, saboda ganin da gaske ni amarya ce, amma zan tafi gidan miji ba da son zuciyar Ummata ba. Domin ko kitson da ke kaina ya yi kyau ma sha Allah! Duk da da gashina aka yi kitson, amma ya sauko mini har gadon bayana. Ga shi ritsi-ritsi tamkar an yi tsaga da allura, ban son kitson ya yi tsirit, amma Firdausi ta ce dole shi za a yi mini, ko ina so ko ba na so.


    Cikin sanyin jiki na sulale kan gadon na kwanta ina zuƙe majinar kukana. Wayata da ke saman ruwan cikina ta fara ƙara, ƙirjina na ji ya buga dam! Saboda zaton ko Ummata ce ta biyo ni. Sai ga sunan MD na gani, cikin sauri na ɗauka tare da saita muryata gudun ya gano kukan da nake yi. Bai jira cewata ba ya fara magana da cewa,


    'Ga ni kan gadon amaryata! Sai juyi nake yi ina ta ƙiyasin yadda zan mori aurena a kansa!" 


   Murmushin yaƙe kawai na yi kamar yana gani na,  sannan na ce, "Ina taya ka murna ango mijin amarya!"


    'Please! Me ya taɓa muryarki ne? Na ji ta sauya gabadsy kamar kin yi kuka!'


  "Kaina yake ciwo!" Abin da na faɗa kenan ina rintse idona, tare da dafe kan nawa da hannuna.


"Wannan punishment ya yi yawa fa! An kama ƙafarki an yi miki lalle! Kuma kanki ma ba a bar shi ba sai da aka tsuke shi da kitso, ni ma aka hana ni wayatayawa tsawon wuni zir. Sannan kuma ke ma ga shi an saka mini ciwon kai! Ke ni fa ko a ƙwalkwabo kika zo mini zan karɓa, domin ba lalle da kitson na gani na ƙyasa ba! A kan me za ki wahalar da kanki a kansu?'


    Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi kafin na ce, "Amarya ba ta cika sai da kitso da lalle fa! So kake na zo a yadda nake tsufan da nake da shi ya ƙara fitowa?"


   'Tsufa?' 


  Tambayar da ya yi mini kenan cikin wata murya, ni ma na amsa masa kai-tsaye da,


 "E, ko kai ba ka hango shi ba?"


   "Cabɗijam! To ko jaririya sabuwar haihuwa ba za ta fi ki yarinta a wurina ba! Kuma ki ɗauka ko da kin fi Sarauniyar Ingila tsufa, a haka nake son ki, kuma a haka zan yi ta miki kallon ƙwaila sabuwar ƙyanƙyasa. Saboda ke ɗin dai ke nake so! Tsufanki da yarintarki duka ba su ne a gabana ba. Zaitunar dai da kika sani, ita ɗin dai nake so ba daɗi ba ƙari! Don haka idan ciwon kan ya matsa miki; ki sa a since kitson ki zo mini da gashin a haka ni zan miki irin wanda ba zai saka ki ciwo ba!'


    "Ohhh! Daman ka iya kitso shi ne ban sani ba?" 


  Na ƙare maganar ina ƙumshe dariya, cikin sigar barkwanci ya ce, 'Yo kitson ai ba wani wuya ne da shi ba, da an tsaga sai a sarƙe gashin wuri ɗaya a murɗe su haɗe da juna. Shi kenan fa an kammala, to mene ne a ciki da ba zan iya kalmashe miki gashin ba?'


   "Uhumm! Ni dai ba na son kitson ɗan koyo!"


        Daga haka muka ci gaba da hira cikin raha, tun ina haɗe rai har zuciyata ta washe na saki jiki muka sha hirarmu. Ya saka ni sai da na tura masa hoton lallen da kitson ya gani. Na lalubo a wayata na tura masa hotunan da aka yi mini a lokacin da aka gama mini. Shi mai faɗin a zo masa haka nan, ya dawo yabawa har da santin bai taɓa ganin kitso da lallen  da suka yi kyau irin nawa ba. Cikin nishaɗi na yi barci, saɓanin damuwar da nake ciki, wacce ke damun zuciyata.


     Ranar Alhamis gida ya cika da danginmu na Birnin Kebbi. Tsakanin matan Baba Ali, surukansa mata, 'ya'ya da jikokin gidan, tare da wasu daga cikin gidajen da muka fito zuri'a ɗaya da su. Gida ya runtume da dafe-dafe idan an sauke wannan tukunya a ɗora waccan. Domin Baba Ali da buhun shinkafa biyu ya turo su bayan kuɗin cefane, gudun a ɗora wa Kawu lalura shi kaɗai. Saboda har fente gidan ya yi da sabon fenti lungu da saƙo har ƙofar gida. Ɗakin Umma ma sai da aka fente shi da fenti mai two color, gida ya dawo sabo ma sha Allah. Don daman can kullum cikin gyaran shi yake yi, abu kaɗan zai lalace ya nemo masu gyara a gyara, hakan ya sa koyaushe yake komawa gidan zamani, saɓanin sanin da aka yi wa gidan a wasu shekaru baya.


    Ranar Juma'a, tun da safe gidan Kawu ya fara ɗaukar baƙin 'yan'uwa na nesa da na kusa. Mutane sai sambarka suke yi da ganin yadda na murje na yi kyawu. Takanas aka nemo mai kwalliya ta fente mini fuska, sannan ta shirya ni shiri irin na budare masu sabon aure, tamkar ba ni Zaituna uwar su Ummu Salma, Iman da marigayin yarona Haidar ba. Saboda kyawun da na yi, da kalar jikina tsantsan, domin ga wanda bai san ni ba kai-tsaye zai rantse da Allah ni ɗin budurwa ce ba tsohon hannu ba. Saboda kayan matan da na yi amfani da su, sun ƙara ciko ƙirjina ya yi ɓulɓul. Daman ƙirjin fulani ne da ni a tsaye ƙyam, irin wanda ake kira da girkin tasa, a cike suke tantsan, kuma har lokacin ba su durƙusa ba ballantana su kwanta tamkar aljihun gaba.

     Hotuna Sajida ta dinga yi mini tare da video'n da ake yi wa amare, wanda ake ɗauko su tun daga kan ƙafafuwa har zuwa saman fuska. Sai murmushi nake yi, fuskata a washe saboda tsokanar da wasu abokan wasata suke yi mini. 


     Wunin bikin ya ƙayatar sosai, duk da Kawu ya hana a ɗauko masu DJ. Kiɗan ƙwarya kaɗai aka yi, inda aka baje tsakar gidan mutane suna ta cashewa da rawa, ɗaya bayan ɗaya gwanin burgewa. Ni ma aka saka ni tsakiyar filin ina ɗan rausayawa ana mini liƙin kuɗi, masu hotuna da video suna ta aikinsu, saboda mai hoto MD ya turo mana takanas duk juyin da na yi sai na ga hasken flasher a kan fuskata. 

     Dangi, 'yan'uwa da abokan arziƙi, suna ta ɗokin a yi musu hoto tare da ni. Saboda tsabar farin jinin jikina irin na amarya, ballantana ni da na zamo tamkar wata a cikin taurari. Don ko kaya na sauya ya kai sau huɗu zuwa biyar, duk da ba na son sauye-sauyen; amma Firdausi da Sajida sai sun takura ni na canza. Amina dai dariya ce tata, saboda ita akwai ɗan nauyi tsakanina da ita, duk da ina jin ta wani ɓangare a cikin ahalina. 

    'Yan wurin aikinmu ma da suka zo, ita ce ta yi ta hidimarsu har aka watse taron. Gida ya koma daga mu sai tsirarun da suka nace sai an kai ni da su. Ni dai iyakacina kallon kowa da murmushi, saboda duk wata bajinta da karamci; babu irin wacce ba a nuna mini ba a lokaci bikin. Tsakanina da kowa sai godiya da fatan alherin gamawa da duniya lafiya. 


    Ƙarfe takwas da rabi na dare 8:30pm. Motocin ɗaukar amarya suka yi layi a ƙofar gidan Kawu Sale. Domin a yadda na ji labari; mota ta kai ashirin jere da juna, wata bayan wata har zuwa bakin titin da za a saki hanya a shigo kwanar gidan Kawu.

    Ni kuma a lokacin Firdausi ta saka ni yin wani sabon wanka, duk kwalliyar da aka yi mini na wanke ta tas. Na fito a asalin Zaitunata ba mai aron fuskar fentin hoda ba. Na yi sabuwar shiga cikin wani rantsattsen lesi fari ƙar da shi ya ci adon golden color. Ɗinkin riga bubu ne da zani single, na soke rigar cikiz na dora zani a saman rigar na tsuke shafaffen cikina. 

     Turare Sajida ta bi ni da shi, ta ko'ina sai da aka feshe ni da turaruka masu sanyin ƙamshi. Sannan Inna Kulu ta saka ni ɗakin Kawu ta ba ni wani haɗi a kwalba ta ce na ɗiba na matsa a jikina. Na yi kamar yadda ta umurce ni, sannan ta ce na adana shi wuri mai kyau, saboda ba ƙaramin muhimmanci gare shi ba.  'Yar dariya na yi mata sannan na yi godiya muka fito, zuciyata cike da tunanin kayan matan da na loda wa kaina. Waɗanda ni da kaina sun fara damuna a jiki, saboda a cikin kwanakin duka sun saka ni yawan tsarki lokaci bayan lokaci.


     Wata Gwaggona, a cikin danginmu na Birnin Kebbi ce ta riƙa ni muka fito ƙofar gida. Bayan an gama yi mini nasiha kamar yadda ake yi wa sauran amare a al'adance. Wata tsadaddiyar mota aka saka ni, Firdausi a mazaunin gaba, Inna Kulu da Gwaggon tawa suka saka ni tsakiya a mazaunin baya.  A hankali aka fara tafiya har aka fito kwanar su Kawu, sannan aka hau kan titin Bafarawa Estate bi-da-bi ana tafiya slow motion, kafin a kama manyan tituna a dinga sharara gudu ana ta oda ɗiiii irin ta 'yan ɗauko amarya. 


     Tafiya tiryan-tiryan, sai ga mu a Yawuri flat. A hankali aka gangara kan wani dogon titin da zai kai mutum har ƙofar gidan MD. Jiniyar da ake yi tun da muka doshi gidan, ta sa na ji jikina ya fara rawa. Haka kawai na tsinci kaina da faɗuwar gaban da ban san ko na mene ne ba. Amma tabbas tsoron haɗuwata da MD ya yi tasirin saka ni bugun zuciya. Domin ƙarshen tika-tika-tik ne, yau babu mai ƙwata ta a hannunsa sai dai Allah. Nan take na ji kuka ya zo mini, wanda na yi namijin ƙoƙarin shanyewa kafin mu fito gidan. 

     Guɗa aka fara yi 'Ayyururui!' Wata bayan wata har aka fito da ni daga motar muka nufi bakin gate ɗin gidan da aka wangale mana duka, wanda tunanina ya ba ni don mu ji daɗin ɗuruwa cikin harabar gidan ne, ba tare da an yi turereniya ba. 

     Sautin kiɗan da muka fara jin yana tashi, tun lokacin da muka doshi hanyar shiga cikin gidan, ya sa na ji zuciyata ta tsinke da yawa. Domin labarin da Firdausi ta ba ni na tuna, wanda ta ce sun cika gida da kiɗa har an so a yi faɗa Inna ta hana. 


   'Allah ga mu gare ka!'


Abin da na furta kenan muna ci gaba da tafiya, saboda jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau. Zuciyata ta shiga tunanin ta yadda zan hana kowa nawa zuwa inda suke, gudun rigima ta tashi, ko wani tashin hankali ya ɓarke a sanadin hakan. Cikin azama na yi hanzarin riƙo hannun Inna Kulu, magana na fara yi mata ƙasa-ƙasa ina cewa,

     "Don Allah Inna ki hana a kai ni wurinta, saboda ba na so garin gyaran doro a kare wuya. Kuma ki ce don Allah a daina guɗar nan da ake yi!" 


   Cikin sauri ta ɗaga kanta alamun gamsuwa. Ta janyo mayafin Gwaggona ta sanar da ita kada a kai ni wurin Uwargidana abin ya janyo wata fitina. Babu musu ta amince, kuma ta buɗa murya cikin sauti ta ce don Allah masu guɗa su daina. 

     Sai da aka yi tsit, sannan muka shiga babban falon gidan. Inda muka hango Ƙawayen Fatima suna ta casu a tsakar falon. Ta gefen falon aka raɓa da ni muka haye sama ba tare da an yi abin da ake yi a al'ada ba, waton ba da amanar amarya ga uwargidanta.


      Har raina, na yi farinciki da hakan, domin da muguwar rawa ƙara ƙin tashi. Saboda ni kaina, da a lokacin da aka kawo mini Barira an tambayi ra'ayina; da na ce a wuce da ita ɗakinta kawai saboda zafi da raɗaɗin da na ji, tun daga  lokacin da ake guɗa za a shigo da ita, har zuwa lokacin da na yi mata kyautar kuɗi na kai ta ɗakinta da kaina. Saboda kishi gaskiya ne, kuma wajibi ne ya fito komai aka yi ƙoƙarin ɓoye shi.


    Da sallama na shiga Falona, kamar yadda Inna Kulu ta ce na yi, kuma na shiga da ƙafar dama. Wani sanyi da ƙamshi mai daɗi ya daki hancina, tare da wani siririn daɗin da ya ziyarci zuciyata.

     Ba a tsayar da ni falon ba, ƙuryar ɗakina aka kai ni bakina ɗauke da addu'o'in tsari da na kariya iri-iri. Sannan na zauna bakin gadona da bisimillah cikin zuciyata. Inna Kulu da Gwaggona, suka saka ni gaba da nasihohin da jikina ya ƙara mutuwa. Zuciyata ta karye na shiga sharɓen kuka Firdausi tana ta rarrashina. 

     Mutane suna ta shigowa ɗakin suna mini addu'ar zaman lafiya ina ta amsawa da kan leɓunan bakina. Saboda ba zan iya magana mai ƙarfi ba a lokacin, domin abu uku ya riƙe mini zuciya. Fitar su Inna gidan ba tare da an yi faɗa ba, da tunanin fushin da Ummata take yi da ni har na zo gidan miji ba ta yafe mini ba, sannan da kalar baje kolin da MD zai yi saman kaina a daren ranar. 

     










   Ni na yi nan🏃🏻‍♀️







D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*TALATIN DA BIYAR.*


      "Inna Kulu." Na kira sunanta cikin wata raunanniyar murya, ta iso kusa da ni ta zauna tana faɗin,


      "Me ya faru kuma?"


 Hawayen da ke cikin kwarmin idona na share, sannan na ce da ita, "Don Allah kada ki bari kowa ya kula mutanen can. Saboda yanayinsu ya nuna ba zaman lafiya suke so a yi ba. Idan aka biye su komai zai iya faruwa, kuma ni har ga Allah ba na fatar a ce wani abu ya shiga tsakaninmu da su." 


    "In Sha Allahu babu wanda zai kula su ballantana a samu wata matsala. Saboda ni kaina tun da muka zo jere na gano take-takensu na neman rigima. Amma ba za su samu yadda suke so ba da yardar Allah!"


   Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce da ita, 

"Ki ƙara roƙar mini Umma don Allah ta yafe mini."


   Shiru na ɗan lokaci ta yi sannan ta ce, 

"Ki daina damar da kanki a kan matsalar Habi! Saboda ko ga Allah ba ki da laifi don kin auri wanda kike so kin bar zaɓinta. Kuma idan za ta yi miki adalci ai ta san ke ma ba ki san da auren ba a sama kika tsinta. To fushi na mene ne? Haka kawai ka koma yin jayayya da ƙaddarar Allah!"


    Ta ƙare maganar fuskarta a cure, wanda alamu ya nuna ita ma ta zo wuya da abin da Umma ta aikata. Ta miƙe  tana faɗin,

     "To mu dai za mu tafi, kada mu tsayar da masu komawa da mu gida ba mu san uzurinsu ba! Amma ki cire damuwar kowa a ranki ki kula da mijinki. Iya shawarar da zan ba ki kenan yanzu, Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba." 


    Ganin suna ficewa ni ma na miƙe hawaye yana zirara a kan fuskata. Bayan kowa ya fice ɗakin Firdausi ta zo kunnena tana cewa,


    "Ki saki jikinki da kyau idan ya zo, ban da raki, kuma don Allah ki  ɗaga masa ƙafa har sili."


      Duka na kai mata,  sannan muka saka dariya tare, muka fito falon ina musu Allah ya kiyaye har bakin step inda ake sauka a yi ƙasa. Ga mamakina na ji gidan tsit sai hayaniyar mutane, kiɗan da ya cika gidan ma an daina yi, ballantana masu rawar duka babu kowa main falon, sai wasu da nake kyautata zaton dangin MD ne.

     A gabana su Inna suka fice gidan salun alun babu wani tarnaƙi ko tashin hankali. Sannan na juyo zuciyata babu daɗi, na koma falon na zauna, mutanen da ke nan su ma suka shiga yi mini addu'ar zaman lafiya. Da ɗaiɗaya suka fara mini sallama suna ta ficewa. Har aka bar ni, daga ni sai wasu mata biyu, ɗaya daga cikinsu ta matso inda nake tana cewa,


     "Saƙo Ammin ta ba ni gare ki, shi ya sa na bari mutane suka rage, saboda abin magana ba ya kaɗan. Ta ce na sanar da ke, don Allah ki yi haƙuri da duk abin da Fatima za ta zo miki da shi. Saboda ba ta so ki biye ta ku koma yin abin da bai dace ba. Don dukanmu babu wanda bai san halinta ba, amma sanadin zuwanki muke fatar gidan Aliyu ya gyaru. Don haka don Allah kada ki biye sabgoginta, saboda muddin kika biye ta ba za a taɓa zama lafiya ba. Kuma mu ba ma fatar a ce kun zama iri ɗaya ke da ita kullum a dinga jin kanku. Ubangiji Allah ya ba ku zaman lafiya da fahimtar juna, Allah ya kaɓe fitinar da za ta taso kowace iri ce ya daƙile ta!"

     "Amin!" Muka haɗa baki ni da ɗayar da ke zaune tana sauraro. Miƙewa ta yi daga kan kujerar da take kai, ta dawo inda nake ta zauna. Murmushi a kan fuskarta ta ce da ni,


    "Sunana A'isha, ni ƙanwar Aliyu ce uwa ɗaya uba ɗaya! Tun da an gama isar da saƙon Ammi ni ma zan miƙa nawa! Amma ni amanar Yayana zan ba ki, saboda ina so ya san ya yi aure yanzu. Kada ki bari idon kowa ya hana ki tarairayar mijinki, ki saki jikinki da kyau ki kula da abinki don ita ya fi buƙata yanzu fiye da komai. Domin Allah ya gani, duk da ban san ki ba, amma tun daga ranar da na ga hotonki na ji ina ɗokin ki zamo matar Yayana. Kuma ina miki albishir za ki same shi fiye da yadda  kika tsammata,  ko waccan halinta ne ya janyo ta kasa gane kansa har yanzu. Don haka ke ki kwantar da kai ki yi abin da ta kasa yi.."


    "Idan kin gama faɗar saƙon tashi mu je! Tun da kin fara aikin da kika saba!"


    "Sorry Aunty Umaima, amma sai na faɗa mata gaskiya. Don ni ba na cikin kayan haushi da takaici, mace kamar 'yar club, ta tara wa mutane matan banza a gida suna ta rawa sai ka ce gidan gala!"


   Ta ƙare maganar a fusace, zahirin fuskarta ya nuna tsabar haushin abin da Fatima da ƙawayenta suka aikata. 


  "Yanzu dai tashi mu je! Allah ya ba su zaman lafiya! Shi ne da gidansa, idan ya zo shi zai tsara komai tun da mu mun yi iya namu."


   Cewar wacce na ji A'isha ta kira da Aunty Umaima kenan. A'isha ta miƙe fuskarta a haɗe ta ce, "Mu za mu tafi! Amma kamar yadda na ce da ke, ki tsayu da kyau ki kama Yaya Aliyu tsaf ki bar shashasha da haukar da ta saba!"


    Ba ta jira komai ba ta fice falon cikin sauri, Aunty Umaima ma ta yi mini sallama ta fice, suka bar ni da juya maganganunsu a ma'aunin hankali. Kai-tsaye na fahimci A'isha ba ta cikin Fatima, Ammi kuma ta yi hakan ne kawai don kada na biye Fatimar mu hana kanmu zama lafya da mijinmu gabaɗaya. 


    'Idan haka ne, in Sha Allah ba zan taɓa biye ta ba!'


    Zancen da na yi kenan a raina, sannan na sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, a hankali na fara ƙare wa falon kallo.  Ta ko'ina sai wurga idanuwana nake yi, ina sambarka cikin raina da godiya ga Ubangijina.  Saboda komai ya ji tamkar ɗakin sabuwar budurwa, kuma ɗiyar wani mai hannu da maiƙo ba ni marainiya Zaituna ba. 

     Jingina bayana na yi da jikin kujerar, kaina a sama ina sauke ajiyar zuciya wata bayan wata. Kafin kalmar "Alhmdulillah!" Ta dinga fitowa daga bakina wata bayan wata. 

     Shiru ya ratsa na ɗan lokaci, nan take ƙirjina ya buga saboda takun tafiyar da na fara ji. Dum-dum! Shi ne sautin bugun da da ƙirjina yake yi. Duk da jikina bai ba ni MD ne ba, amma tabbas ƙirjina bai daina dakan luguden tara-tara ba har zuwa lokacin da aka turo ƙofar falon aka shigo. 


    Kallon-kallo muka dinga yi wa juna ni da ita, kafin ta fara takowa a hankali har zuwa gabana ta ja ta tsaya riƙe da ƙugu. Wani kallon uku kwabo ta dinga bi na da shi sannan ta yi wata shewa, tana girgizar jiki ta nuna ni da hannu ta ce,


     "Ke amarya ko? To babban albishir na zo miki da shi! Kin yi nasarar auren mijina! Amma ki sani kin kawo kanki ƙabarinki da kanki! Domin kuwa, ni ce nan ajalinki! Ni zan kashe ki da hannuna! Ta yadda ba ki isa ki sake cin amanar kowa ba! Saboda fansar karayar da kuka yi mini ita ce kawai na yi miki kisan gillah! Sai dai idan na kashe ki ni ma a kashe ni!"


    Cikin zafin nama na kauce daga muguwar sukar da ta kawo mini da wata sharɓeɓiyar wuƙar da ta zaro daga jikinta. Idona a zare na fara ja da baya, saboda wani matsanancin tsoron da ya kama ni a lokacin. Ta biyo ni tana wata irin mahaukaciyar dariya tana faɗin,


    "Ni ce ajalinki! Kuma sai na kashe ki! Domin ba ki isa ki kwanta da mijina ba! Na fi son mutuwata da ganin iri wannan rana! Ihhuuuuu!"


     Ihun da ta yi ya kiɗima ni matuƙa, cikin zafin nama na fice ɗakin ta rufa mini baya tana ci gaba da kururuwar faɗin sai ta kashe ni. Gudun ceton rai ya sa na shiga tsallake matakalar benen bibbiyu uku-uku, har na zo gaf da sauka tsananin tsoro ya sa ƙafata ta zame na yi zarto ƙasa. Babu zato na ji ni jikin mutum kafin mu faɗi ƙasa tare, ƙamshin jikinsa ya sa na gano shi ne ya cece ni. Da ko ban mutun ba kamar yadda take so; sai na kakkarye ga irin muguwar faɗowar da na yi. 

    Domin duk da haka sai da na ƙwala hannuna da ƙasan tyles, babu shiri na fasa ƙara. Wacce ta yi daidai da isowar Fatima kanmu wuƙa a sama tana ƙoƙarin caka mini ita a sautin fuskata. 


    Ƙafa MD ya saka mata ta faɗi ruf da ciki. Wuƙar ta yi tsalle ta faɗi gefe, ta yunƙura cikin zafin nama za ta isa wurin wuƙar ya yi hanzarin sakina ya take mata hannun da ta zura tana ƙoƙarin sake ɗauko wuƙar. Ihun da ta saki ya sa ni ma na zabura riƙe da hannuna da ya ƙwalu jikina yana ta rawa ina ƙare mata kallo. 


     Kafin ka ce me, ta karɓi mari a wurin shi ya kai kala biyar. Sannan ya ja ta ƙiii ya jefa a wani ɗakin ƙasa ya rufe ta da makulli. Da sauri ya dawo inda nake cikin matsanancin tashin hankali  yake dudduba jikina. Hannuna da ya taɓa na yi hanzarin fasa ƙara saboda wani irin zugin da ya ratsa ni. Jikinsa yana rawa ya ce da ni,

    "Tsaya mu ga hannun, mahaukaciyar banza, za ta janyo mini asara!"


     Da ƙyar na bari ya taɓa hannun, ganin ƙashin ba daidai ba ya yi hanzarin riƙa hannuna mai lafiya muka fito harabar gidan. Cikin zafin nama ya fito da motarsa cikin rumfa ya ce na shigo, jikina yana rawa na faɗa riƙe da hannun ina ta cije baki saboda zafin da nake ji ya wuce misali. 

      Uduth muka nufa kai-tsaye,  cikin sa'a muka ga likitan da ya dace mu gani. Aka yi 'yan cike-cike da sa hannu, ya biya kuɗi ƙasa sannan aka gyara mini hannuna. Wanda aka ce gocewa ce na yi ban samu karaya ba, sun so riƙe ni ya roƙi alfarmar mu dawo gida gobe mu koma. Aka haɗo ni da magunguna muka juyo, tuƙi yake ransa a ɓace sai faman tsaki yake yi. 

     Ni dai shiru kawai na yi ko motsin kirki na kasa yi, saboda tsananin mamaki da takaicin wauta irin ta Fatima. Haka kawai ta nemi kashe mutum a kan baƙin kishi, har da iƙirarin ita ma ta fi so a kashe ta idan ta kashe ni. 


    "Allah ya kyauta!"


Iya abin da na faɗa kenan bayan na sauke ajiyar zuciya, kallo na ya yi na ɗan lokaci sannan ya fesar da iska a bakinsa ya ce da ni,


     "Na fi ki takaicin wannan al'amari! Domin gabaɗaya ta ɓata mini darena!" 


     "Hmmm! Ka yi haƙuri!"


Iya abin da na furta kenan, saboda tsantsar imanin da ya kama ni. Domin sai tuna kalar sukar da ta kawo mini a farko nake yi, wacce ban da Allah ya tsare da tuni aikin gama ya gama.


     Gidan muka koma, ya yi parking cikin rumfar da ya ɗauko motar, sannan muka fito ya riƙa ni muka yi cikin gidan. Inda tun kafin mu isa muka dinga jiyo ƙarar dukan ƙofa tamkar za a ɓalla ta. Wasu ledodin da ke ƙasa zube ya duƙa ya ɗauki ɗaya ya nufi ɗakin da ya saka ta ciki. Buɗe ɗakin ya yi ya shiga tsawon mintuna bai fito ba, haushi ya sa na haye sama, cikin ƙunar zuciya na yi ƙuryar ɗakina, kan gadona na kwanta tare da fashewa da wani irin kuka har muryata tana shaƙewa. Na ɗauki minti goma a hakan, kafin na jiyo muryarsa a falo yana cewa, 


   "Ammi sai da na ce a bar ta can gidan kika ce ta dawo! To ai ga shi nan ta kusa jaza mana bala'i! Domin ta so caka wa Zaituna wuƙa, Allah ya tsare. Amma yanzu haka garin gudun ceton kanta ta goce a hannu. Ni na gaji Ammi! Saboda Fatima ba za ta canza ba!"


     Daga haka ban sake jin me ya faɗa ba, ballantana abin da Ammin ta ce, sai sautin takunsa da na ji zai shigo ɗakin. Shiru kawai na yi har ya zauna bakin gadon ya janyo ni jikinsa yana cewa,


    "Ki yi haƙuri, in Sha Allah ta yi na farko kuma na ƙarshe. Domin hakan ba za ta sake faruwa ba!"


    Rintse idanuwana na yi sannan na buɗe tare da sauke ajiyar zuciya na ce, 

   "Komai ya wuce! Ka ɗauka kamar komai bai faru ba!"


     "Ta ya ya zan ɗauki komai bai faru ba! Ga shi ko'ina ba a zo ba rashin hankalinta ya janyo mini asara!"


    "Asara kuma!"


 "E mana, don yanzu duk zalamata dole na sassauta miki. Saboda ba zan haiƙe miki da rauni a hannu ba!"


   Murmushin gefen baki na yi masa sannan na ce da shi,  "Kada ka damu am ok fa!"


    Wani kallo ya yi mini sannan ya miƙe ya fara rage babbar rigar da ke jikinsa. Hular kansa ya ajiye, yana ƙoƙarin cire clips na yi hanzarin miƙewa ina taimaka masa da hannuna ɗaya mai lafiya. Jikinsa yana rawa ya haɗa ni da jikinsa duka ya rungume, sai ajiyar zuciya yake ta saukewa wata bayan wata. Mun ɗauki minti uku a haka, kafin ya ɗago ya ja ni bakin gadon ya zaunar da ni. Sannan ya duƙa gabana tare da riƙe hannuna gam-gam ya ce, 


     "Cike nake da ƙisarki Zaituna, ga wannan abu da ya zo ya faru. Ba na so na ƙara miki nauyi, idan kin ga zan takura ki kawai ki sanar da ni.  Kada ki cuci kanki don kawai kina so ki faranta mini."


     Gefen fuskarsa na kai hannuna na shafo sajensa ina cewa, "Ko da gaɓɓan jikina duka suka kakkarye; ba na jin zan iya takura don kawai na faranta wa mijina! Ka yi komai a yadda kake so, in Sha zan zamo mai juriya!" 


     Hannuna ya kai bakinsa yana sakar mini kisses mai sauti 'Tsuuuuit' sannan ya ɗora kansa saman cibiyoyina yana cewa,


     "Allah ka gani ina son matata, saboda kyawawan halayenta abin koyi ga sauran wasu mata. Ubangiji ka ba ni ikon kyautata mata daidai iyawata."


    Hannuna na ɗora saman kansa, na shiga shafa gashinsa ina faɗin,

     "Amin mijina! Ni ma ya ba ni ƙarfin gwiwar shanye duk wata gwagwarmaya a dalilinka."


    Ya miƙe fuskarsa cike da annuri ya zauna bakin gadon, tare da saka ni jikinsa ya shiga shinshinar ƙamshina yana lumshe ido. Cikin wata siririyar murya ya ce,

    "Komai naki ya yi mini, Allah ya bar mini ke iya rayuwa. Kuma ya ba ki ikon ɗauke ɗawainiyata babu gajiya." 


     "Amin mijina."


Mayafin jikina ya zare, sannan ya fara cire mini 'yan kunne da sarƙar da ke wuyana. Awarwaro da agogon da ke hannua duka ya cire ya ɗora a saman bed side. Sannan ya miƙar da ni muka nufi ɗakinsa ya ja nawa ya rufe. Jikinsa na shige muna taku a hankali har muka isa ɗakinsa, ko zama bai bari na yi ba muka nufi toilet. Arwala ya taimaka mini na yi, sannan ya fito da ni na zauna bakin gadonsa. Ya kwashi tsawon minti goma a toilet ɗin, sannan ya fito da towel ɗaure a ƙugunsa alamun wanka ya yi.

      Cikin sauri na koma kallon lallen da ke hannuna saboda ba na so mu haɗa ido a yanayin da yake, domin gabaɗaya jikina ya ɗauki rawa. Murmushin da ya yi mai sauti ya nuna alamun ya gano ni, gabana ya tsaya da towel ɗin yana faɗin,


    "Mene ne abin kunya kuma? Bayan komai naki ne, kuma ya dace ki ga irin baiwar da Allah ya yi miki."


    Fuska na ɓata tare da turo baki, yana 'yar dariya ya nufi ma'adanar kayansa yana cewa,

     "Oya tashi mu gode wa Allah, sannan mu nemi albarkar wannan dare namu mai tarihi, tare da wasu dararen da za mu ribata a cikin sauran rayuwarmu."


    Babu musu na miƙe, ya miƙo mini sabuwar carpet na shimfiɗa mana. Sannan ya ba ni dogon hijabi sabo na saka, shi ma ya saka doguwar jallabiyarsa, ya kashe wutar ɗakin ya kunna dum light. Ɗakin ya yi duhu nan take ya fara ja mana sallah. 


     Ya ɗauki lokaci dafe da kaina yana jera mini addu'o'i, sannan ya dawo yi mana na zaman lafiya ya kawar mana da shaiɗan a tsakani. Shiru kawai na yi amma a zuciyata ina ta amsawa da 'Amin' saboda jikina ya gama mutuwa gabaɗaya da irin zafafan addu'o'in da yake yi mini tare da aurenmu gabaɗaya.

     Bayan ya ƙare ya saka ni jikinsa ya rungume, hannuna mai gociya kuma ya fara hura masa iskan bakinsa yana tofe shi da addu'o'in da ba na jin me yake faɗa. Ƙarshen addu'ar da ya yi a fili ce ta saka ni dariya babu shiri, domin kuwa cikin wata murya ya ce,


     "Allah ka tsare hannun nan kada na ji masa ciwo a lokacin da ba na hayyacina!" 


      Ledodin da ya shigo da su ya ɗauko, ya baje mana kazar amarcin da fresh milk kala-kala. Da kansa ya ciyar da ni har na ƙoshi, wani lokaci idan ya saka mini naman a baki sai ya kai bakinsa cikin nawa mun ci tare. Wani zubin kuma da hannuna nake ba shi, sai ya gama tsotse hannun tas sannan ya koma lasar bakina. A haka muka ƙoshi ya mayar da sauran kayan a firij ɗin da ke Kitchen ya dawo.


        Babu zato na ji ya fara mini tafiyar tsutsa a wuya, na yi hanzarin gantsarewa. A hankali ya kai bakinsa nawa, cikin ɗan lokaci ya fara mini wani kalar tsotson da ban taɓa sani da irin shi a duniyar aure ba. Nan take jikina ya hau tsima, tsawon mintuna yana bai wa bakina haƙƙinsa. Sannan ya koma lasar wuyana, ganin kamar rigar da ke jikina tana takura shi ya yi dabarar raba ta da jikina. Na langaɓe a jikinsa domin har bra ta ya cire ya cillar, wata kalar tsutso ya shiga yi wa ƙirjina yana nishin da ya ƙara susuce ni. 

     Na shiga miƙa ina sauke numfashi a hankali ina ƙara banƙaro masa ƙirjina. Tsawon mintuna muna haka sannan ya miƙar da ni tsaye muka koma kan gado, bayan ya raba ni da komai a jikina ina noƙe jiki amma bai ji ko ɗar wurin yi mini uryanan ba. 


      Jallabiyar da ke jikinsa ya cire, sannan ya kwantar da ni a hankali, hannuna mai ciwo ya ɗora shi a kan wani lallausan bargo. Sannan ya fara yamutsa ni cikin ƙwarewa, tare da kaffa-kaffa da hannuna gudun ya fama mini ciwo. 

       Ya shiga lasar jikina tamkar wanda ya samu zuma, ni ko sai nishi nake yi kamar wacce ta sha gudu. Ya ɗauki tsawon lokaci yana tsotse-tsotsensa, sannan ya koma babbar hedkwata. Tun da ya shafo wurin ya fara murmushi tare da faɗin, 


    "Woww!" 


Saboda yadda ɗan ƙaramin kududdufi ya haɗu a wurin cikin ɗan lokaci. Kansa ya saka daidai wurin ya dinga yi mini wani abun da ban san da me zan kwatanta shi ba. Na shiga ihu da kururuwar daɗi har na nemi shiɗewa tare da ƙugin da ban san na iya shi ba. 

     Sai da ya tabbatar da na yi laushi sosai sannan ya fara addu'ar saduwa.


 "Allahumma jannibnish shaiɗana, wa jannabish shaiɗana ma razaƙatana!"


    Ina ji, ina sauraro ya fara ƙoƙarin kutsawa cikin jikina. Nan take na fara wata ƙarar da babu shiri ya zare jijiyarsa yana ba ni haƙuri. Kuka na shiga yi masa ina roƙon don Allah ya yi mini a hankali kada na mutu, kamar yadda na ce haka ya dinga yi a hankali ya fara kutsawa yana cije da leɓensa tare da girgiza kai har ya shige gabaɗaya. Dam-dam! Na ji ya cike ni  tamkar mayen ƙarfe, duk yadda ya so ya yi motsin kirki; amma wurin ya kasa ba shi haɗin kai. Dole ya kwanta samana jikinsa ya ɗauki rawar da har sai da na dinga shafa bayan shi da hannuna ɗaya alamun ya yi haƙuri. Tsawon mintuna muna haka kafin ya yi jarumtar shiga da fice cikin jikina yana wani irin ƙugi. Ni ma abin da nake ji har kwanyata, ya sa na shiga ihun daɗi saboda ko'ina na jikina karɓar saƙonsa yake yi.

     Tsawon minti arba'in yana safa da marwa a jikina har ya koma sassarfa da sauri da sauri. Na ƙara wa sautina ƙara ina ihun ya yi haƙuri, amma hakan bai sa ya daina ba balle ya rage ƙarfin gugar guron da yake yi. Domin shi kansa ihun yake yi yana jijjiga kansa tare da faɗin,

  

    "Ohhh shitttt!"


Ni kuma ban da ambaliya, da feshin ruwa babu abin da nake yi. Sai ihun da na cika ɗaki da shi ina kururuwar ya yi haƙuri. Babu zato muka ji ƙarar bugun falon sashena tamkar za a ɓalle ƙofar, kasancewar ɗakinsa shi ne farko idan an shigo falon. 






    To fa!🤭









D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*TALATIN DA SHIDA.*


        Shi kam, ko a jikinsa, duk ina kyautata zaton ya ji dukan ƙofar kamar yadda ni ma na jiyo. Shirun dole na yi ba don ina so ba, amma abin da nake ji ko babu shiri sai na fasa ihu da kuruwawar haƙurin da nake ba shi kamar wani kurma. Tsawon lokaci yana ta kwasar ganimarsa, har aka gaji da dukan ƙofar aka daina. Amma fuskarsa kaɗai ta nuna zallar ɓacin ran da yake ciki a lokacin. Hakan ya ba shi damar sarrafa ni ta yadda yake so yana ta ihunsa kamar wanda ke shirin zaucewa, tausayina ma da yake yi saboda ciwon da ke hannuna ya daina.

     Tun ina jarumtar nuna masa ƙwazona; har na koma magiya da kukan da nake so ya tausaya mini ta sanadinsa ya bar ni na huta. Wani sabon dukan ƙofar na sake ji kamar da guduma ake yi, har sai da na zabura, hakan ya sa na riƙe hannuna da ke ta mini zogi na fashe da kuka wiwi. Saboda ganin da gaske yake yi ba zai bar ni ba balle ya bi ta kan bala'in dukan da ake yi wa ƙofar sashena.


     Jikinsa ya zare a ƙufule ya kwanta gefena yana ta mayar da numfashi ɗaiɗaya. Kafin ya zabura ya mayar da jallabiyarsa ya buɗe ɗakin a fusace ya fice. Shiru kawai na yi ina ɗan kukana ƙasa-ƙasa, saboda zuciyata ta ba ni cewa matarsa ce ta zo da wata sabuwar haukar. Motsin da na dinga ji kamar ana kokawa ya sa na zabura, jikina yana rawa na ɗaura zani sannan na ja dogon hijabin da ke kan sallayar da muka yi sallah na saka. Cikin sauri na fice ɗakin da sassarfa duk da zogin azabtar da nake ji ƙasana da hannuna.  A dalilin sautin doke-doken da nake ji yana tashi a cikin falona, wanda fitata ta yi daidai da jin muryar Fatima, wacce ta fasa wata uwar ƙara tare da faɗin,


     "Sai na kashe ku daga kai har ita 'yan iska jarabbu! Tsinannun Allah waɗanda suka gama tanbaɗewa tun a kan titi!"


    Jikina ya ɗauki kyarma, saboda hango MD a tsaye a kan Fatima da ke yashe ƙasa. Hannunsa riƙe da extension waya yana huci alamu ya nuna kamar ma dukanta ya gama yi. Nufo shi na yi cikin sauri da niyyar karɓe wayar gudun ya sake taɓa lafiyarta; babu zato na ji ta yo kaina tamkar wata zakanya da nufin kai mini cafka. Bayansa na koma cikin zafin nama, domin tun kafin na isa bayan nasa ya sha gabanta tare da riƙe ta gam-gam, gudun ta taɓa ni. Ƙoƙarin fitar da ita falon ya fara yi tana fasa ihu tare da tirjiyar sai ta kashe mu dukanmu tun da la'anannu ne mu haihuwar bariki.


    Duk da ƙarfi irin na maza; amma da ƙyar MD ya fitar da ita daga falon, saboda tirjiyar da take yi tamkar mahaukaciya sabon kamu. Domin jikinta babu komai sai wata 'yar fingilar riga mai kama da bra, da wando 3quater iya cinya tamkar wata 'yar dambe.


    Biyo su na yi a baya ina ta ba shi haƙurin don Allah ya ƙyale ta, amma bai fasa tisa ƙeyarta gaba ba har suka sauka ƙasa. Bakin bolcony na tsaya ina kallon su, har ya hau da ita sashenta ba ta daina tirjiyar da kwashe mana albarka ba. Ajiyar zuciya na sauke, sannan na juya kaina yana sarawa kai-tsaye na koma ɗakina. Toilet na faɗa duk da nake jin ba zan iya wanka da hannun ba, amma a haka na ƙoƙarta na gasa kaina da ruwan zafi. Saboda raɗaɗin da nake jin jikina yana yi tamkar an yanka ni wurin,  sannan na tsarkake kaina cikin daraba na fito.


      Hango shi bakin gadon dafe da kansa alamun kashi ya game masa. Motsin fitowata da ya ji ya yi hanzarin ɗago kansa ya ƙura mini kallo har na iso na zauna gefen shi. Kansa ya karkato yana mini wani kallo ƙurin kafin ya samu kuzarin magantuwa ya ce,


    "Ban san da wace irin kalma zan yi amfani da ita wurin ba ki haƙuri ba! Saboda ni kaina ina jin matuƙar kunyar kaina dangane da abin Fatima ta aikata. Don haka ki yi haƙuri, kuma ki ba ni lokaci zan yi hukunci daidai da abin da ta yi mana!"


    "Wane kalar hukunci za ka yanke?"


    Tambayar da na jefo masa kenan, cikin wata hargitsattsiyar murya. Sumar kansa ya shafo sannan ya fesar da iska mai sauti daga cikin bakinsa ya ce,

     "Ba zan iya kallon ire-iren wannan tozarcin da cin kashi daga wurinta ba! Na yanke hukuncin zan kai ta har gidansu idan Allah ya kai mu safiya. Sannan zan ba ta takardar sallamarta a hannunta domin na huta da mugayen halayenta!"


     Fuskata na haɗe, kafin na yi hanzarin faɗin, "Za ka ɓata goma biyar ba ta gyaru ba kuwa! Ai babu babban sakacin da namiji zai yi a rayuwa; irin ya saki matarsa a kan zazzafan kishin da take yi a kansa!"


    "Me ya sa kika ce haka? Bayan a gaban idanuwanki ni kaina ban tsira da cin zarafinta ba! Kishi hauka ne? Ko a kanta aka fara kishiya duniya?"


    Ya ƙare maganar a fusace cikin ɗaga murya. Hannunsa na yi hanzarin kamawa na rintse cikin nawa hannun, sannan na ɗora kaina saman kafaɗarsa. Cikin wata sanyayyiyar murya na ce da shi,

    "Ka yi haƙuri mijina! Amma ka san kishi halas ne ko a musulunci ko? Kuma abin da ake so shi ake yi wa kishi. Don haka don Allah kada ka yi gaggawar yanke hukunci cikin fushi, idan da hali ma kada ka kai ta gidan. Saboda mutane za su zargi a kan ka yi sabon aure ne ka kore ta, ko kuma ka sake ta."


    "Ba na shayin duk abin da za a faɗa a kan hakan, domin ita nata kishin ya wuce na Musulunci! Sannan ci gaba da zama da ita tana wannan haukar; ba ƙaramin haɗari ba ne da barazana ga rayuwarmu duka! Saboda komai za ta iya aikatawa matuƙar ta samu sararin hakan."


     "Dole ta ji haushi fa! Ko ni ce zan yi kishinka fiye da zafin da take ji a ranta!"


   Na ƙare maganar raina a haɗe, saboda ina so ya fahimce ni ya gamsu da bayanina ya janye mummunan ƙudurin sakin matarsa. Saboda iya abin da ya faru ga Maman Taufiƙ ya zame mini baƙin tarihin da ba zan taɓa mantawa da shi ba. Ballantana na saki damar da nake da ita, har a sake kwata faruwar hakan a gabana. 


     "Ke ma za ki iya iƙirarin za ki kashe ta kenan? Ko kuma ni ki nemi illata ni a kan kishi?"


     "E, zan iya!"


 "Za ki iya kika ce fa?" 


"Matuƙar ina da zazzafan fushi irin nata, tunani irin nata, haukar kishi irin nata; to ni ma sanadin zafin da ke cizon zuciyata a kan matsanancin kishin mijina zan iya kisa!"


    Wani kallo ya bi ni da shi kafin ya ce, "Kina hayyacinki kuwa?"


     "A yanzu da nake wannan maganar ba na hayyacina tabbas! Saboda zafin kishinka ya sa na manta makomata a lahira, da abin gorin da zan bari a nan duniya bayan an ƙaddamar mini da haddi kisa kamar yadda na aikata! To kwatankwacin haka Fatima ta tsinci kanta, don haka ka yi nazarin haɗarin  da ta sadaukar da kanta da rayuwarta a kanka.  Kuma a sanadin son da take yi maka da tsananin kishinka! Me ya sa za ka rufe ido ka saka mata da irin wannan ɗanyen hukuncin da bai dace ya rataya kanta ba? Kai a ganin ka ya dace masoyi ya zama abin ƙyama a lokacin da yake ƙoƙarin nuna kishinsa ga abin da yake so?" 


   Kallon da ya yi mini; ya tabbatar mini da magangunana sun shiga jikinsa. Kai na fara girgizawa sannan wani hawaye mai zafi ya shiga ambaliya a kan fuskata. Gabansa na koma na durƙusa gwiwa bibbiyu ina cewa,

    

      "Ka tausayawa Fatima! Kada rayuwarta ta lalace a sanadin haka! Ka tuna lokacin da ka aure ta tana son ka, duk wani zafin kishin da ka ga ta nuna a yanzu; tsananin son ka ne ya ja mata komai! Da a ce ba ta son ka; ba za ta taɓa adawa da aurenka ba ballantana wacce ka auro! Sannan ka sani kishi halitta ne, kowane mutum da kalar yadda ya ɗauke shi, kuma duk jarumtar mutum sai ya ci galabarsa a wasu lokutan. Saboda haka ka ɗauka ita ɗin a yanzu ba ta cikin masu cikakken hankali. Duk abin da ta aikata yana da kyau a yi mata uzuri a matsayin mara lafiyar da kishi ya taɓa ƙwaƙwalwarta. Maimakon a biye ta; yana da kyau a tattausa mata harshe, ko don a tseratar da ita daga kangarar da zuciya take saka ta a sanadin haka. Saboda nata kalar kishin kenan, kuma muddin aka ƙara tunzura ta za ta halaka kanta mu ma ta jefa mu  a masifa. Amma sannu a hankali idan abin ya bi jikinta yau da gobe za ta rage haukar kishin ta samu lafiya, ko da ba ta warke duka ba. Amma idan aka yi dace ita da kanta za ta gano rashin alfanunsa ta yi wa kanta faɗa, har ta yi  wani idan ta kama!"


    Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya ce, "Kin kashe mini jiki gabaɗaya! Domin maganganunki sun yi matuƙar tasiri a zuciyata. Kuma in Sha Allah zan yi aiki da su duk da ina ji a raina ba za ta saduda ba!"

      "Za ta saduda! Matuƙar aka rage mata nauyin kishin da ke saka ta 'yar ƙaramar hauka!"


     Abin da na yi hanzarin faɗa kenan, saboda farincikin samun kansa. Kafin shi ma ya jefo mini wata tambayar da cewa,


"Ta wace hanya?"


     "Ta hanyar rage abubuwan da ke janyo ta yi kishin!"


    "Kamar me da me?"


 Cikin ƙumaji na fara amsa masa fuskata cike da annuri, saboda jin daɗin sauƙin kan da ya nuna mini a lokacin. 


      "Na farko, ka dinga ɓoye son da kake yi mini a gabanta, gudun ta zargi kamar ka fi so na da ita, gudun haukar kishin nata ya motsa ta mana aika-aika! Na biyu ka yi ƙoƙarin kwatanta adalci a tsakaninmu, duk abin da ka yi mini ita ma ka yi mata ko da tana da shi ka sabunta mata. Sannan na uku, wannan ihun da ka yi ka daina shi daga yau!"


    Na ƙare maganar ina haɗe fuska, baki sake ya dinga bi na da kallo yana wata siririyar dariya kafin ya ce,

      "Ohh! Ta nan kika zo? To idan na yi alƙawarin komai ban da wannan! Saboda ni kaina ba na sani zan yi sai dai na ji ina yi. Kuma a yadda kike da zuma a jikinki ko na yi alƙawarin zan daina sai na saɓa. Saboda ni kaɗai na san me na ji yau, kuma ba na fatar na zamo kurman da zan kasa yaba abin da nake so kuma Matata ta ba ni shi fiye da zaton da na yi wa ɗanɗanonsa!"


     "Yanzu dai a taƙaice ba za ka daina ba ko?"


    "E, babu wannan a cikin dokokin, amma na karɓi sauran idan da wasu ma ki ƙaro duka zan yi ƙoƙarin kauce musu!"


     Fuskata a haɗe na tashi daga durƙushen da nake, saboda ƙafafuwana har sun yi sanyi. Kallo ya bi ni da shi har na cire towel na sauya da rigar barci, kan gadon na bi ta bayansa na kwanta har lokacin yana kallo na. Shi ma gyarawa kawai ya yi ya kwanta kusa da ni tare da janyo ni jikinsa yana sauke numfashi. Ban hana shi ba ballantana na zare jikina daga nasa, amma na saka wa raina ba zan sake ba shi kaina ba; har sai ya yi mini alƙawarin ba zai yi kuwwar da zai janyo matarsa ta watsa mana fetur ta ƙone mu ba. Kamar yadda Maman Taufiƙ ta yi wa su Sajida, duk da ba gida ɗaya ya haɗa su ba. Ballantana mu da muke a haɗe, lokacin da za ta aikata ma ba mu sani ba, ko ceton mu za a yi sai mun kusa zama gawayi za a gane mun ci wuta.


      Yamutsa ni ya fara yi yana ƙoƙarin dawo da mu ruwa, amma na dake, tare da ƙanƙame jikina, idona a rufe, kuma fuskata a haɗe. Ganin da gaske sabon zubi yake son yi; na yunƙura na tashi zaune tare da turo baki ina faɗin, 


    "Ka ƙyale ni!"


"Ke ma kin san ba zan iya ƙyale ki ba! Ko a baya ballantana yanzu da na san amfanin gishiri da Maggi cikin abinci!"


     Kamar wata sokuwa, haka na fara shesshekar kuka ina jan majina har da ɓare baki kamar ƙaramar yarinya. "Yiiiii!" ina wani kalar kuka irin na shagwaɓaɓɓu. Janyo ni ya yi na faɗa jikinsa yana lalubar ƙirjina ya ce,


     "Wannan kukan ma ina son irin shi! Amma ki bari har na samu abin da nake so sai ki yi ta yi ina rarrashi!"


     Duk yadda na so share shi sai da ya sa na biye shi muka sake raya daren. A lokacin ƙarfe biyun dare, babu motsin komai sai na ƙarar A.c da na sa ya ƙara mana sauti, gudun Fatima ta ji mu shiga uku. 

    Barci mai daɗi muka yi maƙale da juna, bayan ya gama goge mana duk wata tsohuwar tsatsar da ke jikinmu. Cikin sa'a kuma bai yi ihun da nake tunanin zai ci gaba da yi ba, domin ko da ya fara da ƙarfi sai ya dawo rage sautinsa.  Tun da muka yi sallar asuba ba mu sake tashi ba sai ƙarfe takwas na safiya, shi ma da ƙyar na motsa jikina na miƙe jiri yana kwasa ta. Saboda gabaɗaya ko'ina ciwo yake yi mini, ga wani sabon zazzaɓin da nake ji sanyi yana huda jikina. Saboda daren ranar sau uku na yi wanka kafin mu ga safiya. Domin wankan da Firdausi ta saka ni, bai hana ni wankan tsarkake jikina ba a lokacin haɗuwarmu ta farko. Sai na uku da muka tashi sallar asuba, dole na sake wani wankan tun da MD ya lalata wanda na yi gaggawar yi.

     Abin break Ammi ta sa aka kawo mana mai rai da motsi. Amma yanayin jikina ya sa ban iya cin komai ba sai tea da na sha na koma na kwanta. Shi ko ban da aikin sannu da shiga jikina babu abin da yake yi, a cewarsa ta hakan zan samu zazzaɓin ya sauka na samu ƙarfin komawa asibiti. Cikin ikon Allah wani barci mai nauyi ya sake yin awon gaba da ni bayan na sha magunguna. 


     Ƙarfe ɗaya na rana da minti takwas, na farka jikina sakayau tamkar an sauke mini nauyin wani ƙaton dutsu. Har wani sabon kuzari na ji a lokacin, ta yadda na yi hanzarin wanka a gurguje na fito na shirya cikin shiga ta alfarma. Sai baza ƙamshi nake yi a duk lokacin da na motsa, falo na fito, saboda ƙwanƙwasar da ake yi mini a ƙofar falon ƙirjina yana bugawa cike da fargaban buɗewa. A'isha na gani fuskarta a washe, tare da wasu 'yanmata da kulolin abinci a hannunsu. 


    Tarbon su na yi cike da mayalwacin murmushin a kan fuskata,


      "Aunty Amarya kin yi kyau!"


      Abin da A'ishar ta faɗa kenan tana ƙoƙarin zama. Fuskata a washe na ce da ita "Na gode ƙanwata A'isha mai kyawu!"


       "Ohh kin rama kenan?"


     "Babu ramuwa! Ai ƙanwata mai kyau ce!"


   Na ƙare maganar ina 'yar dariya. "Ammi ta ce a kawo miki abinci! Amma don Allah Aunty matar Yaya; ki zuba masa abincin ya ci ya ƙoshi kafin ki fara dafa masa da kanki! Saboda ina son Yayana ya saba da abincin gidansa daga yanzu, ko don ya daina kai wa restaurants kuɗinsa a banza!"


    "Ba ki da matsala! In dai abinci ne har ɗure sai na yi masa!" 


    Na ƙare maganar ina 'yar dariya, zuciyata cike da tunanin dalilin da ya sa A'isha ta yi wannan magana. A take na gama fahimtar inda zancenta ya dosa, waton ma'anarta dai Fatima ba ta masa girki, shi ya sa yake yawon gidan abinci yana saya.


      'Oh Allah!'


Abin da na faɗa kenan a raina, kafin A'isha ta ce, "Matar Yaya mai kike tunani?"


    Murmushin yaƙe na yi mata sannan na ce, "Babu komai! Amma na so na je gaishe da Ammi yau, idan ya dawo in Sha Allah zan je mu gaisa!" 


     "Ke da ba ki da lafiya! Ki yi zamanki kawai Ammi ba ta da matsala! Tun da ta san raunin da aka yi miki a hannu ita da kanta ma za ta zo duba ki!"


     Ta ƙare maganar fuskarta a haɗe sannan ta ƙara da cewa, "Kin ga ma ko sannu ban miki ba ina ta surutu, saboda tsabar takaicin Fatima ya hana zuciyata sukuni! Mace har mace amma zuciyar dabbobi ne da ita! saboda ita komai sai ta yi rashin hankali a kansa kamar gare ta farau kishiya? To wallahi ni gaskiya zan faɗa miki ko da ta dawo gidan nan; kada ki sake bari ta ga fuskarki ma ballantana ta nemi taɓa lafiyarki ta cuce ki a banza!" 


      Ta ƙare maganar tana ƙwafa, tare da jijjiga ƙafar da ta ɗora a kan ɗaya ƙafar tana cizon yatsa. Murmushi na yi mai sauti sannan na ce da ita,


     "Fatima fa ba ta da laifi A'isha! Kishi halas ne, kuma wajibi ne ga kowa! Sai dai hanyar da za ta bi da shi ne kawai ta kasa fahimta! Amma ni ban ga laifinta ba don ta yi kishin mijinta!"


     







     Bariki🤔😂🤗🏃🏻‍♀️











D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*TALATIN DA BAKWAI.*


       Wani kallo na ga ta yi mini bakinta a sake har da riƙe ƙugu daga zaunen, sai da ta fesar da wani iska mai zafi a bakinta sannan ta ce,


     "Ahh! Lalle! Yayana ya auro mace mai imani! Yanzu duk wannan rashin hankalin da ta tafka ke ba ki ga laifinta ba? Cabɗijam! To an gode wa Allah da ya kaɗa ƙeyarta zuwa gidansu gyaran hali, da sai dai watarana a zo a taras da gawarku duka ta cinna muku wuta, daga ku har gidan ta ƙone ku ƙurmus tun da ba kya ganin laifinta! Ni kin ma ɓata mini rai, ku ku tashi mu je matar Yaya ta ɓata mana hira!"


     Murmushi a kan fuskata na dinga bin ta da kallo kafin na magantu, tana ƙoƙarin gyara gylalenta da zummar tafiya na yi hanzarin faɗin,


    "Yanzu ke saboda Allah, idan aka miki kishiya ba za ki ji ciwo ba?"

     Shiru ta yi na ɗan lokaci sannan ta karya kai ta ce, "Zan ji ciwo tabbas! Amma ba zan yi irin wannan kishin halaka irin na Fatima ba!"


     "To ki ɗauka kowa da kalar nasa kishin, da kuma kalar yadda yake tafiyar da shi! Saboda ni kaina da kika ji ina kare ta; a ce ni ce a matsayin ita, ba ƙaramin kishi zan yi a kan Yayanki ba! Saboda abin da kake so wajibi ne sai ka yi kishinsa. Sai dai ba zan yi irin wanda duniya za ta fahimci tsananin kishina a zahiri ba, don ko da kin bayyana kishin; ƙalilan ne za su tausaya miki, sannan ba za a yi miki uzuri ba. Saboda wani  lokaci mutane da kansu suke zunguro kishin uwargida da bakin wuta, musamman irinku dangin miji, a ƙoƙarin yi mata wasa a kan ƙarin auren; sai ta ƙara zaburewa gabaɗaya. Idan ma tana ɓoye kishin gudun a zage ta; sai ta fara bayyanawa a ƙoƙarin ta na son shigar wa kanta faɗa da kanta, domin za ta yi tunanin an juya mata baya ba a son ta. Sai ta koma tunanin kamar ita kasawarta ce ta sa za a mata kishiya, ko kuma an daina yayinta wata ake so ba ita ba."

     Ajiyar zuciyar da ta sauke, wacce ta sa na ɗan tsahirta, ganin ta koma ta zauna a kujerar da tashi; hakan ya sa na yi murmushi mai sauti.  Tagumi kawai ta yi tana kallo na ko ƙyftawa babu, ni ko na ƙara gyara zamana na sake cewa.


      "Sau da yawa maza da makusantansa, su suke tunzura uwargida ta yi abin da bai dace ba. Saboda a lokacin komai aka yi mata ko da ba a yi da niyyar ɓacin rai ba; sai  ta ji ranta ya sosu. Domin ko fari a baƙi za ta kalle shi, saboda komai zai cakuɗe mata ta yadda za ta koma jin haushin kowa da komai, matuƙar za a faɗi wani abin yabo ga auren da amaryar duka, in dai har ba taya ta kishin za a yi a zahiri ta gani da idonta ba. Domin shi kansa mijin duk abin da zai yi mata na kyautatawa ko da ta nuna masa jin daɗinta a fuska, sai ta ji haushin shi a ranta matuƙa gaya. Saboda tunanin don wata ya yi mata ba don Allah ba, kuma hakan zai bayyana mata zumuɗin auren da yake yi cikin idonta. To ballantana ya koma cusguna mata don taƙamar zai yi aure! Saboda Allah ta ya za ta ji daɗi? Ina za ta saka kanta? Irin shi ne ake samun ɓaragurbin abokai su koya mace bin bokaye ko da ba ta iya ba, musamman idan aka kwaɗaita mata amaryar za ta koma ba a bakin komai ba a wurin mijin. Ita kuma za a ɗaukaka darajarta wurinsa ta fi baya, ta yadda zai koma ɗokinta fiye da sabuwar amaryar da ya auro. Wata mai sauƙin tunani; a take za ta amince, saboda wanda ya faɗa ruwa ko tsinin takobi aka miƙa masa da sunan ceto zai kama. Shi ya sa mata da yawa suka zamo matsafa a dalilin kishiya, mata da yawa sun lashi takobin babu su babu kishiya har abada. Mata da yawa sun koma mazinata a dalilin bin bokaye, saboda a yadda na ji wani asirin mallakar miji ba zai yiwu ba har sai an kwanta da mace. Kin ga garin neman gira an rasa ido, kuma ba kowa ya janyo hakan ba face mijin da danginsa matuƙar suka fito da farincikinsu a kan sabon auren har ta gani da idonta. Domin shi a matsayin maci amana za ta dinga kallonsa, su kuma danginsa su koma manyan maƙiyanta. Muddin suka nuna jin daɗinsu a kan auren, ko kuma idan amaryar ta zo  su koma wurinta ko da ba su yi zancenta ba; kullum ganin take yi zaginta ake yi. Haka ma za ta yi kallon zuga ce ake yi wa amarya don ta ci zarafinta ko ta karɓe mijin a hannunta ta mayar da ita bola a cikin gidan."


     "Ai kuwa dai ni tuni ba ma shiri da ita matar Yaya, saboda abubuwan da take yi ina faɗa mata gaskiya ba ta ji. Yanzu ma a sanadin goyon bayan auren ki da na yi; ta kulle da ni ko magana ba ta mini. Saboda rashin son gaskiya irin nata, domin lokacin da nake nusar da ita ai ba ta ji ba, ni kuma duk inda hankalin Yayana zai kwanta a can nake wallahi. Ƙiyayya kuma ta je ta yi ta yi, don ba ni na sa ta yi sakacin da za a yi mata kishiyar ba!" 


    Ta ƙare maganar tana ɗaga kafaɗa, alamun ko a jikinta. Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Sakaci da rashinsa ba su suke sa a yi wa mace kishiya ba, duk da a wasu lokutan ana ƙarin aure ne idan ba a ji daɗin na farko ba! Amma wani lokaci; ko an ji daɗin ana ƙari saboda a ƙara jin wani daɗin. Sannan ki mata uzuri a matsayinki na mace, ki tausaya mata ki daina ci mata fuska a kan auren Yayanki! Saboda ciwon mace na 'ya mace ne, kishiya ko 'yar tsana ce aka nuna ta aka ce kun zama ɗaya ke da ita a wurin miji dole ki ji haushinta, ballantana ɗan mutum!"


      "Ummmmh! Matar Yaya a bar zancen nan kawai! Don na fahimci kusan halinku ɗaya da Ammi. Ita kullum zancenta a yi wa Fatima uzuri, amma duk yadda take goyon bayanta yanzu ta fita cikinta. Saboda wannan aikin haukar da ta aikata muku, don ita da kanta ta ce a miƙa ta gidansu don ba a wasa da rai ballantana a bar ta ta halaka ku a banza! Ni zan tafi, amma kada ki manta a bai wa Yayana abinci da yawa ya yi ƙaton ciki!"


    Ta miƙe cikin sauri ta fice, yaran da suka zo tare ma; suka mara mata baya. Na bi su ina musu Allah ya tsare, bayan sun tafi na nufi ɗakin MD na gyara shi tas, bayan na canza masa zanin gado na feshe ɗakin ko'ina da airfreshner mai daɗi. Sannan dawo falon na zauna ina sauke ajiyar zuciya. Saboda zantukan A'isha sun sa na gano Fatima ba ta gidan, kuma har a raina ban ji daɗin haka ba. Domin babu wanda zai kalli abin a yadda yake, illa ma wasu su jingina mini asiri na zamani mata da shi, wanda ya yi aiki kwana ɗaya tal na sa aka kore ta a gidan.

      Bayana na jingina da kujerar ina nazarin abin, da tattauna shi daga ni sai zuciyata. A take tunanin Umma ya faɗo mini a rai, saboda fahimtar abin da take gudar mini ne ya fara faruwa kaina bayan ko'ina ba a je ba. Hannuna na kalla, wanda ɗaurin da aka yi masa har ya fara saki. Kamar haɗin baki na ji ya fara mini zogi, na riƙe shi ina masa addu'o'i tare tofa masa fatiha ƙafa bakwai. Sannan na kwanta riƙe da shi idona a rufe ina jin zogin yana ratsa jikina.


     Mintuna a tsakani na ji taku alamun za a shigo, amma na kasa motsi ballantana na yi wani abin kirki. Murɗa ƙofar falon aka yi tare da sallama, hakan ya sa na yi hanzarin rufe idanuwana kamar mai barci. Saboda muryarsa ta sa na ji ƙirjina ya buga dam, motsinsa da na ji gaf da ni ya sa na ja numfashi tamkar mai barcin gaske.

       Gabana na ji ya tsaya, babu zato na ji kiss a saman goshina, kafin na dawo daidai na ƙara jin wani a kumatuna. Ya koma bakina ya fara tsotso a hankali yana hura mini iska a fatar idona, 'yar miƙa na yi tare da riƙe hannuna na ce,


    "Wash!"


Cikin sauri ya tayar da ni zaune ya saka ni jikinsa a ruɗe yana cye, "Hannun ko? Shi ya dawo da ni daman, kin ci abincin da Ammi ta aiko miki?"

   

    Bakina na turo alamun shagwaɓa sannan na ce, "Kenan ban da hannu ba za ka dawo yanzu ba?"


     "Wa ya faɗa miki? Ai wannan zuƙeƙiyar amarya tawa ba zai taɓa yiyuwa na bar ta ita kaɗai a gida ba! Ko babu komai zan tsotsi zumar da ke jikinta na more."


    "Zuma kuma?"


"Idan ma akwai abin da ya fi zuma zaƙi ke ce matata! Don da na san haka kike; da ban bari na yi haƙurin da na yi ba."


    Wata 'yar harara na yi masa ina zunɓuro baki tare da faɗin, "Ni dai ka bari."

 

      "Ai kuwa dai ba zan bari ba, bari na ki abincin ki ci mu koma asibitin. Don na ga kamar hannun ya ƙara kumburewa." 


    Shagwaɓe fuska na yi sannan na ce, "Dole ya kumbure, tun da an kasa tattalinsa bayan azabar da aka gama gana masa uhumm uhumm!" 

       

     "Laaa la laaa! Abin har da sharri matata? A gaban idanuwanki fa na yi masa addu'a, kuma aka yi dace ban yi masa komai ba. Don da na bi ta kan abin da na ji a jikinki har wata sabuwar  karaya sai ya samu. Ba ni hannun na tambaye shi da kaina ai zai faɗi gaskiya. Yanzu kai hannu tsakaninka da Allah da gaske ban tausaya maka ba wai?"

     Babu shiri dariya ta suɓuce mini, saboda yadda ya riƙe hannun yana nuna shi da yatsa bayan ya ƙura masa kallo har da haɗe fuska, tamkar da mutum yake magana.

      "Tun da ba zai amsa ni ba, bari ki ci abinci na sake kai shi a ƙara hora shi! Idan ban da rashin adalci ma duk kauciyar da na yi masa gudun na taɓo shi sai da ya kumbure, don kawai ya haɗa ni da matata! To ko ka warke da wuri na ji daɗin cin amarcina da kyau, ko kuma ni da kai a ga wanda zai yi nasara."


    Baki na dinga rufewa ina toshe dariyata amma sai da ta fito, ya miƙe da kansa ya zubo mini abincin. Zaman dirsham ya yi a tsakiyar falon ya ce na sauko ɗure zai yi mini idan na ƙi ci ta lalama. Kusa da shi na zauna ina shagwaɓe fuska na ce,


 "Ni fa ba na jin yunwa!"


      Bai ce da ni ƙanzil ba, ya dinga ciko spoon yana ta aika mini a baki, idan ma na nemi kawar da kaina ya gatsa mini wata harara, dole nake buɗe baki ya juye mini shi, ina tauna ina kumbure fuska. Da haka har na yi ƙat sannan ya ɗauko magungunana ya ba ni, sannan na kora abin jiƙa maƙoshi ina sauke ajiyar zuciya. Da kansa ya kwashe kayan ya kai kitchen duk da na hana shi ya ƙi hanuwa, a cewarsa sai hannuna ya warke ko da zan yi aikin da ba iya nasa ba.

     Sai da muka yi sallar Asr, sannan ya sa na cire shigar da ke jikina. Ya ba ni wata doguwar riga na saka tare da dogon hijab har da niƙaf da safar ƙafa. Mamaki ya kama ni, lokacin da yake ɗaura mini liƙabin a fuska na ce,


     "Wai duk wannan rufe-rufen na mene ne?


    Miƙar da ni ya yi tsaye yana ƙara gyara zaman liƙabin a fuskata sannan ya ce, 


      "Allah ya isa ɗari ga wanda ya kalle mini fuskar matata!"

     

    Kafin na yi magana ya ɗaga liƙabin ya kai bakinsa kan nawa ya tsotso leɓunana yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya sake cewa, "Tsinuwa dubu ga wanda ya ga kyawun zubin matata ya yaba a cikin zuciyarsa!"


    "Ita tsinuwar da Allah ya isa duk me ya kawo su?"


    "Kishin matata! Ko kin ga laifina?"


    "A'a, ba ka da laifi mijina! Mu je, kada ni ma na gan ta na yaba; a ce na yi ba daidai ba, sai ka ce matarka ta fi ta kowa."


    Na ƙare maganar ina haɗe rai tare da aika masa harara cikin liƙaf ɗin, ya rungumo ni jikinsa muka fito ɗakin yana faɗin, "Ke ma kin san kaf matan duniya babu kamar matata!"


    Na yi hanzarin rufe baki ina faɗin, "Ka daina mijina, kada ka yi saɓo tun da akwai Ammi da A'isha a cikin duniyar!"


    "Ɓangarensu daban naki daban, domin a jera mata miliyan ba a za a samu irinki goma ba."


    Saman kafaɗata ya ɗora kansa muna sauka ƙasa yana cewa, "Ni na yi sa'a, da na samu ɗaya tamkar da hamsin, domin matata ta fi ta kowa!"


     "Uhumm! Idan ka gama sambatun ka same ni!"


    Na yi maganar tare da zame jikina na yi gaba ina masa dariya. Ya biyo ni yana rera mini waƙar da ta sa dole na ja na tsaya ina kallonsa tare da ƙumshe dariyata.


"Yar budurwa 'yar yarinya.

Sonki raina na ɗau niyya.

Mu yi wa soyayya biyayya.

Don mu san daɗin duniyaaaaa!"











🤔🤭🤣🏃🏻‍♀️









D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA TAKWAS.*


        Ya ja baitin ƙarshe tare da isowa inda nake da wata 'yar rawa ya fisgo ni na faɗa jikinsa. Ture shi na shiga yi ina faɗin, "Ka daina mijina, za ka sake fama mini hannun fa!" 

    Nanuke ni ya yi kamar bai ji me na ce ba, a haka muka dinga tafiya yana ci gaba rero wata sabuwa yana cewa, 


    "Soyayya in za ka so ɗan'uwanki; 

     So shi tsakaninka da mai sama Allah ko Rasulullah!"


    Haɗe rai na yi cikin liƙabin har muka isa bakin motar ina kumbura fuska, da kansa ya buɗe mini motar na shiga. Sannan shi ma ya shiga ya tayar da ita muka nufi bakin gate, maigadin gidan ya rusuna yana ta gaishe ni,


    "Sannu Hajiya! Allah ya dawo da ku lafiya!"


    Ta cikin liƙabin na amsa tare da ɗaga masa hannu, babu shiri na ji ya saukar da hannun nawa yana faɗin,


      "Nuna hannun kuma na mene ne?"


   Kallon shi kawai na yi ba tare da na ce da shi komai ba, mun ɗan fara tafiya, idonsa a kan titi ya ce da ni,

     "Sai fa an yi haƙuri da ni, don ba komai zan gani na ƙyale ba!"

     Nan ma ban ce da shi komai ba, babu zato na ji ya kwanto ni kamar zai zuge gilashin gefen da nake, kawai na ji ya damƙo hannuna mai ciwo. Ihu na saki saboda wani zugin da na ji ya ziyarci ƙwaƙwalwata. Cike da mugunta ya shafa kansa yana faɗin,


    "Oh! Ashe kina magana."


    Kukan shagwaɓa na saka masa ina ɗan gunjin mai ɗauke da sautin, 'Ummmmm!' shi ma ya ɗauko wata sabuwar waƙa yana nuna ni tare da shafo gefen fuskata duk da ina ƙoƙarin kaucewa.


 "Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciyata.

Komai ruwa da iska a kanki ba za ni daina kewa ba.

Idan na samu zarrar samunki ba za na tanka kowa ba.

Ni ban ga mai harara ba balle na waiwaya."


      Mamaki fal raina, saboda ganin da gaske barkwanci kawai yake ji da shi, a raina na ce, 'Ashe daman yana da sauƙin kai? Amma shi ne yake haɗe wa mutane fuska a baya tamkar bai san wani abu dariya ba ballantana wasa.'


    Tun ina masa fuska har na saki rai ina masa dariya, saboda yadda ya nace dole sai ya saka ni dariya da kalolin waƙoƙinsa. Ni ma na shiga mayar masa da tawa ina kwance cikin seat saboda shauƙin son shi da ya fisge ni. Dalilin ganin ya yi daidai da irin mijin da nake yi wa kaina fatan samu a duk lokacin da Mukhtar ya shuka mini wani rashin mutunci. A lokacin na yi ta jin ina ma ina da ikon zaɓo wa kaina irin mijin da zai yi daidai da tsarina, halina da rayuwata gabaɗaya. Lumshe ido na yi cike da tsantsar farincikin Allah ya karɓi addu'o'ina a kan sauyin miji mafi alherin da ya fi Mukhtar komai a rayuwa.


"Kai nake tunani dare ko da safiya.

Kyauta ta so ka ba ni ka sa ni dariya.

Har muna kamanni a fili da zuciya,

Halinmu ma guda ne mu za a kwaikwaya.

Ko Hassan Husaini ba za su yi kamarmu ba.

Masoya na zamani ba sa bar salonmu ba.

Allah da zamani, amma ba za a kai mu ba.

Ya yarje mana mun samo farinciki."


   Baitikan da na rero kenan cikin zubar hawayen tsimin son mijina da ya ratsa zuciyata, waɗanda yayin furzar da su nake jin wani sabon shauƙin son shi yana ɗiba ta. Ajiyar zuciya kawai na ji ya sauke kafin ya yi magana cikin wata sanyayyiyar murya ya ce, 


    "Kalaman da kika yi amfani da su a waƙarki sun shige ni da yawa matata. Kuma duk abin da kika faɗa haka ne, ta ko'ina mun dace da juna, ke ce irin matar da nake yi wa kaina fatan samu tun kafin na yi aure. Sai ga shi a dare ɗaya Allah ya cika mini burina, ya mallaka mini mace har da rabin wasu mata."


    Ya ƙare maganar tare da riƙo hannuna mai lafiya ya rintse a cikin nasa yana fesar da iska a cikin bakinsa. Kafin ya dawo faɗin,


    "Alhmdulillah!"


Tsiyayar ruwan hawayen da nake yi cikin liƙabin bai bar ni cewa komai ba har muka isa asibitin. Saboda tunanin Ummata da ya tsaya mini a zuciya, wacce nake ji ina ma na yi tsuntsuwa na gan ni gabanta. Sai dai ba na so ya san abin da ke nan da na masa magiya ya kai ni wurinta. Dole na haƙurƙurewa zuciyata son ganin ta na bi shi sawu da ƙafa har muka isa ofishin Likitan. 


     Ba a yi wani dogon turanci ba aka duba mini hannun, sannan aka kwance ɗaurin aka sake naɗa mini wani sabo. Sai sharɓen kukana nake yi a jikinsa yana ta faman rarrashi, tare da hura wa hannun iskan bakinsa yana tofe shi da addu'o'in da ba na jin me yake faɗa.

     Riƙe da hannuna mai lafiya muka fito ofishin Likitan, yana ta jera mini sannu har muka kai inda ya ajiye motarsa. Sai da ya saka ni na zauna, sannan ya zagaya ya zauna a mazauninsa idonsa a kaina yakr ta faɗar,


    "Sorry! Sannu! Akwai zafi ko?"


Kaina kawai na girgiza masa, sannan muka fito asibitin. Ba mu wuce gida ba, kai-tsaye gidansu muka wuce, waton wurin Ammi, a lokacin marece sakaliya gari har ya fara duhu. Tun daga shigar mu na hango fuskarta ta bayyana tsantsar farincikin gani na da ta yi, nan take  aka cika gabana da abinci tare da kayan maƙulashe irin na tarbar baƙi. Ni ko sai faman washe baki nake yi, bayan na durƙusa har ƙasa na gaishe ta cikin ladabi da kwantar da murya. Ta dinga jera mini sannu da zuwa da ya jiki cike da kulawa. Ban so taɓa komai daga cikin abin da aka kawo mini ba, amma sai da ta matsa na ɗan ci meat five na kora da lemu rabin kofi. Saboda kunyarta gabaɗaya ta rufe ni, musamman da MD yake ta tsokana ta gabanta ina noƙewa alamun ba na so, tana ta mana dariya. 

     Kiran sallar magrib ya fitar da shi gidan da zummar yin sallah ya dawo. Ni ma A'isha ta ja ni ɗakin Ammin daga ni har ita a can muka yi sallah tare da Ammin.  Bayan na gama shafa addu'a na miƙe cikin sum-sum da kai na isa inda take zaune kan sallaya da carbi a hannunta tana ja. Gabanta na durƙusa na yi mata barka da dare, ina ƙoƙarin tashi ta dakatar da ni na koma na tanƙwashe ƙafafuwana na yi zaman dirsham. 

     Sai da ta gyara zamanta sannan ta kira sunana cikin kamilar muryarta ta dattijan arziƙi. Ta fara magana cikin taushi ta ce,


     "Ki yi haƙuri da abin da ya faru, kuma don Allah ki yafe wa Fatima kada ki ƙullace ta a ranki, dalilin wannan rashin hankalin da ta aikata miki. In Sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba da yardar Allah ta yi ɗan farin ta yi auta. Sannan ki ƙara kwantar da hankalinki ki kula da mijinki, matsalar Ummarki kuma; ki ƙara juriya, akwai alamun nasara cikin lamarin. Ina ji a raina; za ta sauko, domin da kanta za ta gano alheri aka ƙulla ba sharri ba. Kuma hakan da ta yi shi ne daidai, domin kowace uwa tana fatan 'yarta ta je inda hankalinta zai kwanta. Don da a ce tun farko ta san amanarki aka bai wa Aliyu; da duk abin da ya faru bai faru ba. Domin ba za ta yi irin zargin da take yi masa a yanzu ba, amma duk da hakan; babu abin da ya fi ƙarfin Allah. Mun sanar da shi, kuma a hankali ya fara sauya tsanani zuwa sauƙi. Idan kika ƙara kwanaki zan ce da Aliyu ya kai ki ku ƙara ba ta haƙuri, zuwa lokacin ta ƙarasa sauka daga dokin naƙin da ta haye."


    Shiru kawai na yi ko motsin kirki na kasa yi, saboda ban taɓa tunanin MD zai gano abin da kenan ba. Ballantana har a ce mahaifiyarsa ma ta san borin da Umma ta yi a kan rashin son auren. Saboda bai taɓa nuna mini wata alamar da zan gano ya san wainar da ake toyawa ba.


    'Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!'


   Kalmar da na ambata a zuciyata kenan, wacce ta zo tamkar amsa ga maganganun da Ammi ta faɗa. Saboda sharɓen kukan da na fara yi; ya hana ni cewa da ita komai. Haƙuri ta dinga ba ni cikin rarrashi har na daina kukan ina zuƙar majina tare da ajiyar zuciyar kuka wata bayan wata. A haka MD ya tarar da mu, kusa da ni ya zauna idonsa a kaina yana faɗin,


 "Ammi me aka yi wa 'yar taki take kuka kuma?"


     Ajiyar zuciya ta fara saukewa sannan ta ce, "Zancen Ummarta ne muka gama, idan an kwana biyu ka kai ta ta ƙara ba ta haƙuri da kanta. Saboda fushin uwa babbar masifa ne a rayuwar ɗa, ko da an fi ta gaskiya; yana da kyau a bi ta sau da ƙafa ko don a rabauta da abin da fushin nata kan iya janyowa."


    "In Sha Allah, Ammi zan kai ta."


    "Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, kuma ya saka wa aurenku albarka ya ba ku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba."


    "Amin." 


Ya amsa a fili cikin wata sanyayyiyar murya, ni ma na amsa cikin zuciyata. Saboda gabaɗaya kunyarsu ta rufe ni ruf, domin na tsargu sosai, kuma ban ji daɗin da suka san da zancen ba. Hakan ya sa har muka baro gidan ban saki jikina ba, duk da cewa alamun Ammin ya nuna ba ta ji haushin Umma ba, amma dai ban so suka san da zancen ba. 

    A mota ma sai tsokanata yake yi na masa banza, saboda haushin bai taɓa nuna mini ya san abin da ke faruwa ba. Amma kuma cikin zantukan Ammi na gano shi yana zuwa wurin Umma yana ba ta haƙuri, ni ce ya bari a duhu ba tare da na sani ba.

     Siyayya ya tsaya ya yi mana, sannan muka wuce gida, a lokacin ƙarfe tara saura na dare. Ban jira shi ba, yana parking na yi gaba abuna, kai-tsaye ɗakina na zarce zuciyata babu daɗi. Ina jin motsinsa a falo na yi hanzarin faɗawa toilet na datse, wanka na yi bayan na ƙulle hanuna da leda. Sannan na cire ledar na yi arwalar barci na fito ina tsane jikina da towel, turare na goga wa jikina sannan na saka rigar barci na kwanta, tare da yin addu'a na tofe jikina da kuma ɗakin kowace kusurwa.

     Mintuna a tsakani na ji motsin buɗe ɗakin ya shigo, bakin gadon ya zauna tare da faɗin, "Ba dai kin yi barci ba? Ga magungunanki ma ba ki sha ba."

      Sharɓen kukan da na fara yi ya tabbatar masa ba barcin nake yi ba. Kusa da ni ya kwanta tare da shigewa jikina kansa saman fuskata yana faɗin,

      "Shi kuma kukan me ya kawo shi? Ni wannan shagwaɓa taki duk da nake son ta ba na son kukan nan gaskiya."


    "Dole na yi kuka, tun da ka ɓoye mini kamar ba ka san abin da Umma ta aikata ba."


    "To mene ne abin kuka a ciki? Ko kuma ni ba ta haife ni ba ke kaɗai ta haifa? Shi ya sa zan sanar da ke na san meke faruwa! To ni ban ga laifin Umma ba, asali ma burge ni ta yi, don hakan ya ƙara tabbabar mini matata ta samu tarbiyya mai kyau a hannun jarumar uwa managarciya. Ki gode wa Allah, sanadin tsananin da kike ganin tana yi miki; ya taka muhimmiyar rawar da a yanzu muka zamo abu ɗaya ni da ke. Domin ta hana ki abubuwan da ni na so ki aikata ko don na jaraba ki, cikin sa'a kika tsallake tarkon da na haɗa miki ba tare da kin sani ba."


    Na yi hanzarin tashi zaune cike da mamaki na ce, "Tarko kuma? Kamar me da me?"


     "Kamar hana ki shiga motata da ta yi a lokacin da kike idda. Kamar hana ki sakewa da ni, a lokacin da nake neman haƙƙina ido rufe."


    "Ban gane ba! Me kake nufi?"


"Yanzu ba lokacin magana ba ne, zo ki kwanta idan kika yi barci na je na yi wanka."

      

    Wani kallo na yi masa, yana wani kalar  murmushi ya ce, "E, a yi haƙuri na ce! Gobe tana nan, kuma babu inda zan je. Duk abin da kike son sani ki tambaye ni zan sanar da ke komai."


   Ban musa masa ba, na gyara kwanciyata da kyau na juya masa baya. Ya yi hanzarin ɗago ni tare da juyo da Ni muna fuskantar juna. Idon cikin ido muka dinga kallon juna kafin na rufe nawa idon tare da sauke ajiyar zuciya. Wasa da jelar gashina ya fara yi, tun ina sauraron shi har zuwa lokacin da barci ya ɗauke ni. Asubar farin bayan mun gama sallah ya nemi haƙƙinsa, babu musu na amince ya sha bidirinsa son ransa yana ta faman sambatun kala-kala, amma ni zuciyata cike take da tunanin maganganunsa da suka saka ni kwanar da na kasa fita kai-tsaye tun kafin na ji ta bakinsa. 


    


   


🤭


D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA TARA.*


      Ko da ƙarfe goma na safiya ta yi na yi wanka, na ƙara gyara sashena lungu da saƙo. Amma har lokacin zuciyata cike take da tunanin hirarmu da shi. Ƙasa na sauko saboda barcinsa yake yi sharkaf a lokacin, shi ya sa na fito da tsintsiya a hannuna, da niyyar gyara inda ke buƙatar gyara a babban falon gidan. 

     Sai da na kakkaɓe kujerun tas, sannan na share shi fes na goge tyles, tare da ƙamsashe shi da turaren wutar Humkam nan take gidan ya ɗauki ƙamshi. Zama na yi kan ɗaya daga cikin kujerun falon ina mayar da numfashi.

     Takun tafiyarsa da na ji; hakan ya sa na yi hanzarin kai kallona inda yake. Da sassarfa yake saukowa idonsa a kaina hannunsa ɗauke da Laptop, yana mini wani shu'umin murmushin da na kasa fassara ma'anarsa kai-tsaye. Kusa da ni ya zauna tare da ajiye Laptop ɗin gefensa ya kwanta saman kafaɗata, sannan ya zagaya hannuwansa jikina ya rungume yana sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya yana cewa,


    "Matata ta fi ta kowa. Ƙamshinta ma na daban ne."

 

   Ɗan murmushi na yi masa sannan na lumshe idona cike da jin daɗin yabonsa gare ni na ce,

     "Mijina ma na daban ne ko a cikin jerin mazajen duniya!"


    Kansa ya ɗago tare da kai wa gefen kumatuna kiss sannan ya ce, "Ƙamshinki ya yi mini jagoran da na gano inda kike bayan na gama bulayin nemanki a sama. Amma wa ya ce ki wahalar da kanki bayan kin san kina fama da ciwo a hannu?"


   Ɗan murmushi na yi tare da kwantawa jikinsa na ce, "Ba na son zama kurum ne, ga shi kana ramuwar barci kuma ba na so na takura ka."


     "E kam, kin yi tunani mai kyau, amma kin san me? Akwai mai aiki a gidan nan, wacce duk ire-iren waɗannan ayukan ita ce take yi. Barin Fatima gidan ya sa na ce ita ma ta je gida ta huta kafin na neme ta. Amma tun da akwai amfanin da za ta yi mana zan ce ta dawo bakin aikinta kawai."


    "Idan har ka fi natsuwa da ta je hutun; to ka bar ta kawai sai zuwa lokacin da kake so ta dawo. Domin ni aiki ba ya ba ni wahala, abu ɗaya ne ba na so wanke-wanke. Shi ma tun da ba wasu kaya ne da yawa ba zan iya yi da kaina babu wata takura."


    "Ai kuma tun da ba kya son shi; matata ba za ta yi shi a cikin gidana ba. Oya sanar da ni sai me da me kuma don na nemo mai yin su tun da wuri? Saboda aikina kika zo yi da aikin haifar mini 'ya'ya, amma ba na son duk wani aikin da zai jigatar mini da matata."


    Ƙara shigewa na yi cikin jikinsa cike da jin daɗi na ce, "Allah Sarki mijina! Amma ka san me? Iya mai wanke-wanken ma ya wadatar, don ko wanki ma zan iya yi mana har da guga, ballantana shara da girkin da na fi son su fiye da kowane aiki."  

     "Ai kuwa yau-yau ɗin nan zan kira ta a waya ta dawo, duk da kuma ba na son ganin ta ya sa a tauye mini haƙƙina uhumm'uhumm!"


    Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa tare da ɗan kuka irin na shagwaɓaɓɓu. Dariya na yi masa sannan na ce, "Babu abin da zai hana ni kula da mijina, ko a gaban waye ba na shayin ririta abina, amma zan ji nauyin idon matarka gudun ta zargi da gangan na yi don na ɓata mata." 


    Daga haka bai ce da ni komai ba tsawon mintuna, illa ajiyar zuciyar da ya sauke kafin ya magantu da cewa, "Da a ce duka sauran mata haka suke kamar ke; da an rage tashin hankulan da ke faruwa a tsakanin kishiyoyi. Saboda ɗan zaman da muka yi na kwana biyun nan; na fahimci duk abin da zai ɓata ran Fatima ba kya son shi. A'isha ma ta yi mini ƙorafi a kan hakan, kuma na yi farinciki sosai da samun macen da ta san kanta. Ko babu komai za ki dawo da ni a kan hanya duk lokacin da na nemi zamewa, cikin rashin sa'a ko akasinsa. Allah ya yi miki albarka matata, kuma ya albarkaci zamanmu, ya dauwamar mana da farinciki."


    "Amin mijina."


Na amsa cike da tsantsar farincikin da ya gama kama mini zuciya. "Uhumm na ce ba!"


    "Kika ce me?"


"Zancen jiya don Allah ka sanar da ni komai. Saboda na kasa fahimtar da ka nufa ballantana na hasko ma'anarsa."


   Kallonsa ya kai wurin Laptop ɗin da ke ajiye gefensa sannan ya ɗauko ta ya fara buɗewa yana murmushi. Na tashi daga jikinsa ni ma na zuba wa Laptop ɗin ido har ta gama daidaita ya shiga danne-danne, idan ya shiga nan ya fita can. Wasu jerin videos ya shiga ya fara kamo mini na farko, tare da ɗora mini ita a cinya ya ranƙwafo jikina ya ƙara volume.

     Mamaki ya so kashe ni a lokacin da na hango ni cikin vedion, ina zaune ofishina Amina zaune a kan kujera ina magana. Tiryan-tiryan na shiga kallon duk hirar da muka yi da Amina, a lokacin da nake ba ta labarin zamana da Mukhtar. Kaina na ji ya sara, a lokacin da na ji maganar rashin gamsar da ni da ba ya yi. Hanzarin rufe bakina na yi , jikina ya hau rawa a ruɗe na shiga faɗin,


    "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


    "Cool down!" 


Abin da ya faɗa kenan yana matse ni jikinsa tare da shafa hannuna da ya rungumo ta gefen. Kasa kunne na yi ina sauraron hirar tamu tiryan-tiryan inda nake cewa,

     _Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kullum abin yana damuna a zuciya, ga shi ina jin kunyar sanar da shi meke damuna balle na yi masa bayanin abin da yake yi mini ba na jin daɗin shi. Saboda kunya da kuma nauyin ta yadda zan fito masa da abin da ke zuciyata, amma a raina kullum muka haɗa shimfiɗa sai na ji kamar na kuwata don haushi da takaici. Saboda ko kaɗan bai damu da nemar mini gamsuwa ba, da ya tsiyayar da ruwansa cikin minti biyu, uku zuwa biyar ya gama. Kuma babu wata wasar kirki da yake yi mini balle na ɗan rage zafin abin da ke damuna, ga shi da yawan buƙatuwa a lokacin kai-da-kai yake nema na kuma da buƙatarsa ta biya shi kenan._

     

     Cikin sauri na rintse idanuwana, saboda tsabar kunyar da ta lulluɓe ni tamkar ƙasa ta buɗe na shige. Sai tsagwaron takaicin da ya cika mini zuciya tamkar na ture Laptop ɗin daga jikina ta faɗi ta fashe. Fuskarsa ya haɗa da gefen fuskata ya shiga goga mini sajensa yana faɗin, 


     "Sorry matata!" 


Ture shi na so yu a jikina da nufin na tashi na bar wurin, ya yi hanzarin riƙe ni ƙam-ƙam yana cewa,

     "Daman na san duk lokacin da kika ga video's ɗin nan za ki ji nauyi tare da jin haushin me ya sa na ji hirarku. To amma yadda abin yake; tun farko na sa an saka CCTV camera a ɓoye cikin ofishin tun lokacin Basiru kafin ki zo. Saboda fahimtar ruf da cikin da yake yi da kuɗin ma'aikata, bayan sama da faɗin da yake yi  a rasa ina suka maƙale. Ta hanyar CCTV camera na gano duk abin da yake shiryawa shi kaɗai ba tare kowa ya sani ba. Haka ma da kika zo; da ita na karanci halayyarki mai kyau, bayan jarabawar da na yi miki ta hanyar ajiye kuɗi ofishina ko naki da gangan domin na gwada ki. Cikin ikon Allah kika tsallake siraɗin da ba ki san ma an yi shi ba. A dalilin haka na dinga bin komai naki cikin cameras ɗin har zuwa lokacin da kika fara zancen rayuwarki da Amina. Bari ki gani.."


    Wani vedion ya sake kamowa, wanda nake murmushi kafin na fara safa da marwa a tsakiyar ofishin ina furzar iska daga bakina. Hawayen yana gangara a kan fuskata na share da gefen hannuna, sannan na ce da Amina da ke durƙushe tana gunjin kuka ƙasa-ƙasa.


 "Kin taɓa kama mijinki yana hulɗa da matar aure?"

 "Mijinki ya taɓa faɗa wa duniya kin ce sai kin kashe shi?"

"Mijinki ya taɓa damfarar Iyayenki?"

"Mijinki ya taɓa yi wa 'yar aikinki ciki?"

 "Mijinki ya taɓa neman auren ƙawayenki na ƙud-da-ƙud waɗanda kuka tashi tun kuna ƙurciya?"

"Mijinki ya taɓa bai wa ɗanki matsayin da ya yi kamanceceniya da zama kishiyarki?"

 "Mijinki ya taɓa sayar miki da kayan ɗaki? Ko ya taɓa satar miki kuɗi ko wani abin amfani?"

 "Mijinki ya taɓa fallasa ki a bisa ƙazafi cikin dangin shi da naki bayan 'yan'uwa da abokan arziƙi masu ganin girmanki?"

"Mijinki ya taɓa zuwa wurin mutanen da kike jin kunya aron kuɗi ko roƙo?"

 "Mijinki ya taɓa yi miki ƙazafin kina tare da wasu mazan waje a gaban 'ya'yanki?"

 "Kin taɓa neman haƙƙinki wurin mijinki bai sauke ba?"

 "Kin taɓa shekara huɗu ba tare da mijinki ya kasance ki ba...?"


     Salati na fara yi kafin na koma dafe goshina saboda tsabar kiɗimewar da na yi, a lokacin da na gama sauraron abin da nake faɗa. 


    "Sorry matata! Ki yi haƙuri kuma ki yafe mini jin abin da bai kamata na ji ba. Duk da labarinki da na ji a bakinki; ya taka muhimmiyar rawar sargafo ni da kika yi ta ƙarfi zuwa gare ki. Domin waɗannan jerin tambayoyin da kika yi wa Amina; su suka ƙara mini ƙaimin bibiyar duk wani abin da ya shafe ki. Musamman ɗokin jin komai daki-daki kamar yadda kika feso su ɗaya bayan ɗaya. Dalilin da ya sa na dinga bin komai sau da ƙafa kenan saboda tsabar tausayin rayuwarki, sannan kuma kina ƙara wani matsayi a cikin zuciyata. Sannu a hankali ƙaunarki ta dinga shiga jikina lungu da saƙo, ta yadda idan abin ya motsa mini ina ji kamar na yi ihu ko da za ki jiyo ni ki kawo mini agaji."


    Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce, "Da na san da Camera a ofishin; da na kifar da ita a duk lokacin da zan bai wa Amina labarina. Babban abin haushin ma; da komai nawa ka gani har da wanda ba na so a ce wani ya gani. Yanzu don Allah kana nufin duk abin da na yi a cikin ofishin kaf ka gani?"

     Na ƙare maganar cikin raunin murya, yana murmushin gefen baki ya ce da ni,

     "E, na ga komai, har turaren da ake gogawa a jiki idan za a je ofishina don kawai a sargafo ni ta ƙarfi, duk da na yi warning a daina amma aka sake kwatawa saboda a kai ni bango a jingine."

    

    Idanuwana na yi saurin rufewa cike da jin kunya, ya yi hanzarin janye Laptop ɗin daga kan cinyata. Hakan ya sa na samu sararin dunƙulewa cikin cibiyoyinsa ina faɗin,


 "Innalillahi!"


Dariya ya yi ta mini yana shinshina jikina sannan ya ce, "Yanzu ba ga shi ina shaƙar halalina ba?"


   Sai da na gama zuƙe kunyata sannan na tashi ina faɗin, "Yanzu dai tun da ka gama kalle ni a biya ni kuɗin saka Camera ta ɗauke ni ba tare da izinina ba."


     "Ok tom mu yi tsada, faɗi farashin nawa kike so a biya ki?"


    Hararar gefen ido na yi masa sannan na ce, "Ni na ma fasa son biyan, amma ka goge videos ɗin duka, shi ne hukuncinka."


     "Daman ke nake yi wa ajiya, bari ki ga wani ma..."


    Ya kamo wani da iya murya ce kawai babu hoto, cikin sauri na zaro ido waje. Bakina yana rawa na dinga nuna Laptop ɗin ina so na yi magana amma na kasa, saboda tsabar mamakin da ya kama zuciyata ya sa na kasa furta komai sai aikin nuna shi tare da Laptop ɗin da nake yi. Saboda jin hirar da muka yi da Amina alokacin da na je gidansu. 

     Ajiye Laptop ɗin ya yi gefensa sannan ya haɗa hannu wuri ɗaya yana wani kalae murmushi ya ce, "Allah ya huci ran matata ta yafe mini ko da zan samu natsuwa. Don haka tun kafin ki yi magana, zan sanar da ke yadda aka yi na same shi don ba na so ki zargi abin da ba shi kenan ba!" 


   Bakina na yi hanzarin rufewa tare da haɗe fuskata, saboda tunanin da ya shigo kaina kai-tsaye a kan Amina ce ta naɗar masa hirar a waya ba tare da na sani ba. Janyo ni ya yi na kwanta jikinsa yana shafa bayana ya fara magana.


    "Idan za ki tuna ranar da kika je gidan su Amina na haɗu da ke asibiti. Aka yi dace na kawo Fatima duba wata 'yar'uwarsu da ta haihu, na yi amfani da damata a lokacin da kika bar ni da Iman, saboda ta sanar da ni inda za ku je. Babu jinkiri na damƙa mata wata recorder a hannunta, sannan na ce duk inda ta ga kun zauna ta yi dabarar ajiye ta kusa da ku kada ta bari ku gan ta. Kuma idan za ku bar gidan, ta ɗauko ta kawo mini a siyasance domin zan dawo ɗaukarku. Sai ga shi kin ƙi shiga motata, amma cikin nasara ta damƙa wa yaron Amina recorder'r bayan wucewarku. Domin ba na tunanin ko Amina ta san me ya kawo shi a lokacin, saboda da gudunsa ya zo inda motata ya wurga mini camerar a jiki ya juya da gudu. Kin ji ta yadda aka yi na samu labarin ƙawarki Hafsa da kalolin artabun da kika sha da su. Amma abu ɗaya da na ji cikin hirar taku ya fi taɓa mini rai da komai. Waton abin da ya yi miki a lokacin da kike naƙuda, don na ɗauki kwanaki ina jin ƙunar abin a cikin raina tamkar a lokacin abin ya faru. Amma duk da haka ina fatan Allah ya yafe masa ke ma ki yafe masa kafin ya bar duniya. Domin akwai hisabi mai girma a tsakaninku matuƙar ba ki yafe masa laifun da ya yi miki ba."


Hawaye na ji yana gudana a fuskata, saboda tuno wasu abubuwan da suka faru a baya. Cikinsu kuwa har da Haidar, da lokacin da na samu cikinsa cikin tsananin wahala har zuwa lokacin da na haife shi cikin azaba. Babu shiri na fashe da kukan da nake jin ƙunar zuciya a cikinsa, tamkar a lokacin na rasa Haidar ɗina. 


      😿🤦🏻‍♀️


D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*LAMBA ARBA'IN*


       "Subhanallah! Don Allah ki daina ba na son kukan nan naki, amma ke na ga abin burge ki yake yi. Please ki daina na ce, ko kuma a jingine hirar kawai tun da tuna bayan ne yake janyo kukan."


    Abin da ya faɗa kenan, a ruɗe, saboda kukan da nake yi cikin ɗaga murya. Da ƙyar na bi rarrashin da yake yi mini na yi shiru, amma ban daina zuƙar majinar kuka da shessheka ba. Saboda tuno wasu shuɗaɗɗun abubuwan da suka faru a lokacin haihuwar Haidai da zamanin rainon cikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya yi magana cikin sanyin murya ya ce, 


    "Ni ne na saka ki kukan ko?"


   Na yi hanzarin girgiza masa kai, tare da zuƙe majinar kukan da nake, na goge hawayen da ya jiƙa mini fuskata. Sannan na samu kuzarin yin magana cikin raunanniyar murya na ce,


    "Haidar!"


Ido ya zaro tare da faɗin, 


   "Me kuma Haidar ɗin ya yi?"


    "Shi na tuna, da abubuwan da suka faru a lokacin haihuwarsa, sanadin maganar Abbansa da ka yi a kan idan ban yafe masa ba. Saboda ya cutar da ni da yawa, kuma ya ci amanar haƙƙin da ya rataya kansa. Domin ko kaɗan ba na manta abubuwan da ya yi mini a lokacin."


    "Ki yi haƙuri matata, duk da ba na son kukanki; amma ni kaina ina son na ji labarin abin da kike yi wa kuka, ko babu komai zan kiyaye kuma na yi ƙoƙarin kauce musu gudun na aikata miki a rashin sani. Saboda ina fatar rayuwar auren da za ki yi yanzu ta sha bamban da ta baya, ina so ki yi farinciki da dariya, saɓanin ƙunci da kukan da kika yi a baya. Don haka ki sanar da ni komai, amma ba na son kukan nan kwata-kwata, idan kuma kin san za ki yi; abar hirar a jingine komai mu janyo wata sabgar daban."


    Nisawa na yi cikin sauti sannan na ce, "Ina da jarumta a duk lokacin da na tuno abubuwan da suka faru ba na kuka. Amma rashin Haidar; ya sa duk na tuno da lokacin haihuwarsa sai na ji hawaye ba tare da na sani ba. Kuma tun da ba ka son kukan ba zan yi ba in sha Allah!" 


    Kansa ya ɗaga tare da lumshe idonsa ya buɗe, alamun gamsuwa da jin daɗin furucina. Jikinsa ya saka ni ya rungumo ni ta yadda zan ji daɗin zaman kuma na ji daɗin bayar da labarin. 


    _"A lokacin da na samu cikin Haidar; rayuwa ta sauya mana sosai, domin sauyin wurin aikin da ya samu mai ƙwari; ya sa mutane da yawa suna yi mana murnar waraka ta zo mana. Amma ni a lokacin aka buɗe mini wani sabon shafin wahalar rayuwa, bayan zaman haƙurin da nake yi da shi. Domin ko cikin Haidar da na samu a lokacin; mutane suna ta faɗar ciki ya zo mana da alheri. Sai ga shi tun a tashin farko ya fara nuna mana iyakarmu, daga ni har cikin da yaransa gabaɗaya. Kasancewar boɗinga ne aka tura shi, ya zaɓi kwana can sai ranar Juma'a ya dawo mana week end. Sanadin haka, ƙofofin wahala suke buɗe mini, saboda wani lokaci ko da zai bar garin ficika ba ya bar mini, sai dai ya ce zai aiko mini kafin ya bar garin. Amma shiru zan ji babu shi babu alamun ɗan aike, kuma wani lokacin ma ƙwarar shinkafa babu a gidan ballantana a je ga abin karin safiya. Haka zan yi  ta fafutuka da kaina da yarana, saboda sana'ar saƙar kayan sanyin da na koya ƙarfi da yaji. Amma kasancewar ba koyaushe kasuwar saƙa ke ci ba; wani lokaci sai na sha da ƙyar nake samar mana abin da za mu ci. Ga shi a lokacin mahaifiyarsa ta rasu, kuma ban saba buɗe matsalar gidan aurena ga kowa ba. Shi ya sa ko Ummata ba ta san a wane hali nake ciki ba, saboda tunanin da nake yi; idan na faɗa mata zan zubar masa da ƙima a wurinta._

      _Haka nake fafutukar rayuwar faɗi tashin nemar wa yarana abin da za su ci. Sannan ga ciki,, wanda ko ba na so dole na ci abinci ko don abin da ke jikina. Da haka na koma cin bashi a wurin 'yan unguwar da muke mutunci, hatta wani mai shagon sayar da kayan masarufin da ke unguwar ya san da ni. Saboda tun da na gwada sau ɗaya na ga yana ba ni bashi; duk lokacin da na buga ban samu abin bai wa yarana shi nake yi wa guntuwar takarda, na zayyano duk abin nake so na bai wa Ummu Salma ta kai masa. Cikin ikon Allah haka zai zubo mini kayan a leda ya ba ta ta kawo mini. Sannan na samun walwala da kuzarin dafa musu abincin mu ci ba tare da sun mini kukan yunwa ba. Ni kuma duk lokacin da na samu kuɗinsa jikina har rawa yake yi na biya shi na huta, saboda ina so gobe idan na dawo ya sake ba ni. Duk da ban iya roƙo ba, domin a rayuwata na tsani kalmar roƙon kanta ballantana aikatawa; amma haka nake ɗaga waya na kira Baba Ali na roƙe shi kuɗi. Cikin sa'a kuma ya ɗauko ya ba ni har fiye da abin da na roƙa, ta hanyar kuɗin nake rufa wa kaina asiri da yarana. Saboda shi da ya ɗaga ƙafa ya bar gidan; ba zan sake jin ɗuriyarsa ba sai idan ya dawo garin. Domin ko a waya na kira shi ba na samun shi, saboda kashe wayarsa yake yi, sai idan ya so jin mu da kansa ya kira mu gaisa. Kuma ko na faɗa masa matsalolin da muke ciki da abin da muke buƙata; cewa yake yi na yi haƙuri na ranta kafin ya dawo. Kuma ko na yi rancen kuɗin idan ya dawo ba duka yake biya ba, wani lokaci ma barina yake yi da bashin a kaina ya yi ta mini hanya-hanya har ya tsallake ya bar ni, dole na san yadda zan yi da masu kuɗin don kariyar mutuncina. Matuƙar ina son mutuncin da suke gani na da shi ya ɗore, saboda sanin zubar da girman da rashin biyan bashi yake haifar wa masu cin shi. Babban abin haushin; idan ya dawo na rufe shi da masifar Allah bai bar mu wulaƙance ba kamar yadda  yake son ganin mu, sai ya ce ai yana can yana mana addu'ar Allah ya ba mu.Tun da kuma na ga mun samu; to addu'arsa ce Allah ya karɓa._


      _Ba na manta wataranar da na buga ko'ina ban samu yadda nake so ba; na ɗaga waya na kira shi aka yi dace ta shiga ya ɗauka. Kai-tsaye na koka masa halin da muke ciki ni da yara, domin har kukan yunwar da suke yi duka ya ji a cikin wayar; amma sai cewa ya yi mu ƙara haƙuri har ya dawo. Ko kuma idan na ga akwai inda zan samu bashi na je na nemo idan ya dawo zai biya. Da haka ya kulle mini baki muka yi sallama ina tunanin inda zan samu bashin, bayan wanda na ci ma ko biya ban yi ba. Saboda damuwar haka barci ma rabi da rabi na yi, asubar farin na miƙe ina tunanin ta ina zan fara. Tausayin yarana ya sa ina sallah ina kukan yadda zan yi na nemo musu abin kari tun kafin su fara mini kukan yunwa. Dole ta sa na ɗaga waya tun da uwar safiya na kira Ummata ina sanar da ita su Ummu Salma za su zo gidan su yi musu kwana biyu. Ta tambaye ni sun yi hutun makaranta ne, na ce da ita karatun dai ne ba a yi a makarantarsu, malamai ba su cika zuwa ba. Kuma yaran sun matsa can suke son zuwa su ɗan kwana biyu.

    _Da haka na shirya su, da kaina na nemo abin hawan da na sani na saka su. Kuma na ce idan sun je gidan Kawu Sale Umma ta biya musu kuɗin adaidaitasahun. Sannan na dawo zuciyata cike da farincikin na sauke rabin matsalata. Saboda idan ta ƙuƙe mini har wurin maƙotan da muke shiri nake tura su roƙon abinci. Duk da na san zubar da ƙimata nake yi, amma sanin ban da wata mafita sai ita; dole nake yi ba don ina so ba. Sannan na saka auduga na toshe kunnuwana daga surutun mutane, kuma na shanye duk wata baƙar maganar da danginsa suke buga mini a kan roƙon abincin da nake yi. A cewarsu ina yi wa ɗan'uwansu tereren bankaɗa, duk yawan abin da yake bar mini ba na godiya sai na yi roƙo don kawai na ja masa zagi. Saboda suna zaton wata uwar duniya yake bar mini kafin ya tafi, duba da albashinsa ya yi ƙarfin da gidansa aka fi ƙarfin abinci da wasu buƙatun rayuwa, ballantana a koma roƙo._


    _Ajiyar zuciya na sauke bayan na dawo daga rakiyar yaran, kwance na yi saman doguwar  kujerar. Na yi shiru ina sauraron wutsi-wutsil ɗin da tayin cikina yake mini a ciki, saboda ni kaina yunwar ce take addaba ta. Don ko da dare abincin da na roƙo mana loma biyu na yi na bar musu saura suka cinye. Sannan ita kanta lomar na yi ta ne don abin da ke cikina ya lafa mini da yawan motsin da nake ji._ 

     _Cikin sanyin jiki na miƙe ina gyara ɗakin, ganin babu wani aikin da zan yi a gidan; na tsiro kwalemar ƙarfi da yaji. Na dinga ɗaga abubuwa ina sharo ƙarƙashi har na zo kan katifar da ke gadona na ɗage ta da zummar sharo ƙarƙashin gadon. Babu zato ko tsammani na ci karo da kuɗi zube a kan tabarmar da na shimfiɗa saman hanjin gadon, gudun katifata ta yi saurin lalacewa. Jikina yana rawa na sauke katifar, na rarumo kuɗi na haɗa musu kai na shiga lissafi.  Nan take na gama lissafin kuɗin dubu ashirin da huɗu har da ɗari biyu sama. Mamaki fal raina na zauna ƙasa daɓas tamkar an zare mini laka. Saboda sanin ajiyarsa ce, amma ya san da su kuma ya zaɓi barinmu cikin wahala, a kan ya sanar da ni inda kuɗin suke na ɗiba mu ci abinci. Nan take wani sabon kuka ya zo mini ban shirya ba, wanda na ɗauki lokaci ina rera abina har na gaji don kaina na bari, saboda babu mai rarrashina ballantana na ji sanyi._ 


     _Zuciyata ta shiga saƙe-saƙen abin da zan yi da kuɗin, saboda na ci alwashin ba zan faɗa masa na gan su ba. Saɓanin baya da idan na ga kuɗinsa nake tattara su na ba shi ko sun kai dubu talatin da 'yan kai. Ba na jin haushin miƙa masa kayansa yadda na gansu, amma kuma da ƙyar yake ba ni dubu ɗaya a ciki, ko shi sai na yi masa tsaye a kan sai ya ba ni ladar tsintuwa. Da na gano haka na koma ba shi kaso takwas cikin goma idan na gani, amma daga baya ina sanar da shi ya yafe mini na ɗauki nawa kason tsintuwa. Ya yi fushinsa na ɗan lokaci ya saki, saboda duk inda ya samu zubar da abu yake yi babu ruwansa. Dalilin haka mai masa wanki yake ta zaryar zuwa karɓar kayan wankinsa, sai daga baya na gano dalilin da ya sa yake ɗokin wankin nasa. Saboda ya saka ni wanke masa kalarsa biyu, ban san akwai kuɗi ba sai da na gama wankin na zo juya riga na shanya na ga kuɗi sun zubo. Kuma abin haushi duk na wanke su sun yi fari fes, wasu har sun duƙunƙune sun cure wuri ɗaya. Tun daga lokacin na tsiri duba aljihunsa kafin na miƙa wa mai wanki kayan, idan na gani ba na ɗauka ba shi abinsa nake yi. Amma tun da na fahimci mugunta ce sana'arsa; sai na koma yagar rabona duk da ban iya ƙeta da yawa ba, don idan dubu goma ce dubu ɗaya nake ɗauka, idan sun haura kuma na ɗauki dubu biyu na ajiye masa saura._

      _Amma ranar tsabar haushin abin da ya yi mana ya sa na ci alwashin ba zan ba shi ko ficika ba. Na zabura bayan na gama kukan na ja hijabina na fice, ko aikin da nake ban bi ta kansa na. Duk wanda na san na ci bashin shi sai da na rage masa kaso biyu cikin uku, sannan na auno mana shinkafa kwano biyu da rabi, tare da ɗan ƙaramin cefanen kayan haɗin abinci. Kuma na siyo wa kaina burodi da ƙwai uku na yi karina mai ƙwari. Sannan na samu kaina na koma sauke numfashi, saboda jiganiyar da na yi ta saukar mini da ciwon gaɓɓai. Nan take barci ya kwashe ni a wurin, saboda shi kansa barcin na ci bashinsa da yawa. Duk da lalura irin ta mai ciki wani lokaci a yi ta barci; amma ni ko na kwanta kukan yunwar da yarana suke yi; yake sa dole na tashi ko babu shiri._

      _Cikin 'yan kwanakin hankalina kwance nake dafa abinci na ci, daga ni sai ni, saboda sai ranar Jumu'a suka dawo gidan, kuma a ranar ce yake dawowa shi ma. Sauran shinkafar da ta rage na dafe ta duka na yi mana tuwo da ita, saboda mu samu mu ci har ɗimame da safe. Aka yi dace Umma ta haɗo su da gero da masara tare da dangin manja, man ƙuli, daddawa, Maggi da sauran tarkace har da sugar mu sha kunu._

      _Tun da na ga wani yaro ya shigo da jakarsa na haɗe rai, tare da girgizar ƙafa don na san dole ne mu kwashi 'yan kallo ni da shi sanadin kuɗin. Ai kuwa yana shigowa ko ta kaina bai bi ya shiga ɗage katifa, ganin babu kuɗin cikin tashin hankali ya dinga ƙwala wa su Ummu Salma kira. Da gudu suka shigo ɗakin suka isa inda yake, sauke katifar ya yi tare da riƙe ƙugu ya ce,_ 


     "Wa ya ɗauki kuɗin da na ajiye ƙarƙashin katifar nan?"


    _Kallon juna suka shiga yi tare da girgiza kai a lokaci ɗaya suka ce ba su ɗauka ba, kuma ba su ma san akwai kuɗin ba. Ni ya wurgo wa wani mugun kallo a hargitse cikin ɗaga murya ya ce,_


     "Idan ma ke kika ɗauke su; to ki yi gaggawar fito da su saboda ba nawa ba ne! Na wani abokin aikina ne ya ba ni ajiya, na manta shaf da zan tafiya ban ɗaukar masa kayansa ba! Saboda haka ki ba ni kuɗin mutane yanzu na tura masa kayansa kamar yadda muka yi da shi kafin na baro Boɗinga."


     _Ni ma mugun kallon na yi masa sannan na yi mere na ce,_

     

     "Sai ka tambayi ƙarƙashin katifar da ka bai wa ajiya, wataƙila ta san wanda ya ɗauki kuɗin?" 


    "Me kike nufi? To wallahi ko da tsiya ko da arziƙi sai kin fito da kuɗin nan tun da ba nawa ba ne!"


     "Ka ba ni ajiya ne? Ko ka ba ni gadin kuɗin da za ka hayayyaƙo mini da masifa a kansu? To tun da tsiyar kake ji; buɗe kunnuwanka da kyau ka ji ni na ɗauki kuɗin na ci abinci da yarana. Sannan na rage bashin da kake saka ni ci da sunan za ka biya!" 


      "Na rantse da Allah sai kin biya kuɗin nan ko kuma na ɗauki mummunan mataki a kanki!"


      "Ka kashe ni idan za ka iya! Amma kuɗi sun tafi kenan ba za su dawo ba! Don ban san rashin imaninka ya kai haka ba sai yanzu! Wai na ɗaga waya na sanar da kai halin da muke ciki, amma ka yi biris da zancen kuma ka san akwai kuɗi cikin ɗakin nan. To na ga kuɗin kuma na ɗauka! Ka mayar da gabana gabas ka yanka saboda su!"


    _Na ƙare maganar ina haki, babu shiri na isa kujera na zauna, saboda ruwan masifar da ke kwarara a jikina ban san lokacin da na isa gabansa ba ina masifa. A daburce ya yi saurin faɗin,_


     "Abin da ba nawa ba ta ya zan ce ki ɗauka?"


    "A hakan za ka iya ranta a ciki ka ba mu ai, tun da har ya yi imanin ba ka ajiyar kuɗin ya san za ka biya shi idan ka ara! Don haka yanzu sai ka san yadda za ka yi da shi, saboda ban da dubu ɗaya da ɗari biyar babu komai da ya rage a cikin kuɗin!"


    _Na ƙare maganar ina aika masa da harara, shi ma kallo na yake yi idon cikin ido tsawon mintuna kafin ya yi ƙwafa ya ce,_


    "Ba ni dubu ɗaya da ɗari biyar ɗin! Amma wallahi kika sake yi mini irin haka sai kin yaba wa aya zaƙinta."


     "Oho dai! Ko gobe na gani kuma aka hana mana sai na ɗauka! Sai dai idan ban yi ido biyu da su ba. Saboda tsabar rashin imani ka bar ni da yara na yi ta fama kuma ka san akwai kuɗin da za mu amfana da su, amma ka yi ƙarfin halin ɓoyewa don taƙamar an ba ka ajiya. To waɗannan kam mun ci su, sai a mayar da ni ƙuliƙuli kafin zuwan wasu gudun na taɓa!"


    _Ina surutan na ɗauko masa kuɗin na wurga gabansa na koma na zauna ina hurar hanci. Tare da hakin da ya ziyarto ni sanadin masifar da nake yi. Ya duƙa ya ɗauki kuɗinsa ya fice fuu tamkar zai tashi sama. Na bi shi da harara tare da ɗan ƙaramin tsakin da iyalacinsa kan leɓena._ 


    "Ikon Allah! Gaskiya matata kin ga rayuwa, amma kin san me?"


    "Sai ka faɗa mijina!"


   "Babban kuskuren da kika yi a lokacin; rashin faɗa wa manya halin da kike ciki. Domin hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin ɗorewar matsalolin daga wannan sai wannan."


    "Ni kaina daga baya na gano ni na  yi wa kaina illar da kaina, don ko Umma duk ta tashi faɗanta tana faɗar ni na janyo abin ya yi yawan da ba za iya magance matsalolin duka ba.  Hmmmm! Don ma ba ka ji lokacin da ya je Lagos ba, a lokacin cikin Haidar yana wata takwas. Yadda na koma abin tausayi ko mara imani ya gan ni a lokacin sai na ba shi tausayi. Saboda cikin ya janye ni na yi muguwar rama, babu komai a jikina face tsinin cikin da karan hancina, sai idanuwana da suka yi zuru-zuru tamkar mai kamun yunwa."


     Tagumin da ya yi ya ba ni damar ƙara nutsawa cikin labarin, inda na ƙara gyara zamana da kyau a jikinsa na ce,

      








     Mu tara a next page🤗







Gaisuwa ga mutanen MASARAUTAR D. AUTA Allah ya hutar da gajiya.😊







     D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*


*TAKU NA BIYU*


*HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA; DAUGHTER ANUP*



*ARBA'IN DA ƊAYA.*


      _A ranar da zai yi tafiyar; ɗari biyar ya bar mini, sanann ya ce wasu za su kawo mini dubu biyu na haɗa. A cewarsa kwana biyu kacal zai yi ya dawo. Babu musu na karɓi ɗari biyar ɗin muka yi sallama ya tafi muna yi masa addu'ar Allah ya tsare._

     _Bayan tafiyarsa da ɗan lokaci; sai ga wasu matasa su biyu sun yi sallama. Na tura Ummu Salma ta je ta duba, ko da ta dawo ta sanar da ni wurina suka zo, kuma ni suke son gani. Na ja hijabina na yi bakin soron gidan na tsaya, bayan mun gaisa suka yi mini bayanin kuɗin da ya sa su samo mini ba su samu ba. Na ce musu babu komai muka yi sallama a mutunce suka tafi, na dawo gida raina a ɓace saboda mugun haushin zubar mana da girman da yake yi a wurin mutane. Don daman can yana da ɗabi'ar cin bashi, kuma idan ya ci wani lokaci ba ya biya da wuri a yi ta ɗan banzan rikici da shi. Na sha yi masa nasiha a kan ya daina, tamkar ina ƙara ingiza shi. Mun yi faɗa ya fi a ƙirga a kan hakan, amma kasancewar hali zanen dutsi ne ya kasa dainawa._


       _Ɗari biyar ɗin da ya bar mini tun a ranar muka cinye ta, saboda muna da sauran shinkafa a lokacin. Da ita na yi cefanen abin da babu muka dafe shinkafar muka cinye. Haka na yi ta gurgura rayuwarmu har zuwa kwana biyun da ya ce zai dawo. Sai ga shi tun da safe wani ya yi mana sallama a ƙofar gida,  Ummu Salma ta je, mintuna a tsakani ta dawo da dubu biyu ta ce wani mutumi ya ce a kawo mini. Farinciki fal raina, saboda tunanin shi ne ya aiko mana da kuɗin a yi girki tun da a ranar ya ce zai dawo. Nan take na auno mana rabin kwanon shinkafa, har da su kayan miya, dangin su tumaturi, attarugu da albasa. Raina fes ina ƙoƙarin ɗora girki matasan suka rafka mana sallama. Na ja hijabina na isa bakin soron muka gaisa da su a mutumce, sannan ɗaya ya ce da ni,_


     "Aunty kuɗin nan da aka kawo za ki ba mu, saboda Babanmu ne ya kawo su. Kuma shi muka fara zuwa neman masa kuɗin a wurinsa ya ce zai ba mu. Ganin ya matsa da son kuɗin muka je wani wuri muka nemo masa muka ba shi, sannan ya ce mu sake nemo masa wasu dubu biyu mu kawo miki. To yanzu wacce muka aro kuɗin a wurinta ta matsa mana mu ba ta abinta. Daman niyyarmu idan Babanmu ya bayar sai mu biya ta, to sai ga shi yanzu ya sanar da mu har ya kawo miki kuɗin. Saboda mun yi masa bayanin ke za a kawowa kuɗin idan ya ba mu."


      _Shiru na yi na ɗan lokaci ina tunanin yadda zan yi da su, tun da  har na taɓa kuɗin. Na yi jarumtar faɗin su jira ni na zo, na dawo cikin gida raina a ɓace na ce da Ummu Salma ta je gidan wata maƙociyata ta nemo mini aron dubu ɗaya. Jim kaɗan ta dawo da kuɗin ta ba ni, na haɗa musu kuɗinsu dubu biyu cif na koma soron zan miƙa musu; sai ɗaya daga cikinsu ya ce,_


     "Aunty ki bar kuɗin, bari kawai mu je mu bai wa matar haƙuri har ya dawo." 


     "A'a, ku karɓi kuɗin kawai ku kai mata, tun da tana buƙatar kayanta."


     _Suka nuna ba za su karɓa ba, sai dai na cire ko ɗari biyar a ciki idan suka je su nemo su haɗa mata. Fahimtar tausayina ne ya sa suka canza shawara; na matsa sai da suka karɓi kuɗinsu, tare da sanar da su su je kawai babu komai ina da abin da zan riƙa kaina har zuwa lokacin da zai dawo. Jiki a sanyaye suka karɓi kuɗin suna ta godiya cikin girmamawa suka tafi. Na dawo tsakar gidan kan tabarma na zauna numfashina yana sama da ƙasa. Saboda tsabar ɓacin rai da hakin da ya taso mini cikin ɗan lokaci._

     _Tsawon mintuna ina sauke numfashi a wahale kafin na samu numfashin ya daidaita. Don daman can da na je awo likita ta tabbatar mini da jinina ya yi sama, a kan haka suka ɗirko mini maganin hawan jinin da ya so janyo mini wata sabuwar matsala. Saboda ba asalin ciwon gare ni ba, sanadin cikin ne aka gano jinin nawa ya hau, ba kamar yadda ake son ya tsaya ba._

       _Duk da takaicin da ya ba ni, kuma cike nake da ya dawo mu sake kaftawa; haka na taƙarƙare na yi mana shinkafa da biya, da zummar tarbonsa idan ya dawo. Daga ni har yara muna ta zuba idon ganin ya dawo har ƙarfe goma da rabi na dare, a lokacin yaran duka sun yi barci. Ni ma sai gyangyaɗi nake yi, sai na tafi luu na dawo na gyagije, saboda ba na son ya dawo ya yi ta bugun gida ban ji shi ba. Don mun sha ya yi tafiya ya dawo ya yi ta bugun gida ban san yana yi ba. A ƙarshe sai ya bi ta cikin gidansu ya tsallako katangar gidan rijiya sannan ya shigo gidan. Saboda daga baya ya rufe ƙofar da suke shigowa ɗibar ruwa, domin rijiyar ta bar ruwa babu komai sai danshi._


      _Bai tashi kira na a waya ba sai sha biyun dare saura, a lokacin yake sanar da ni babu mota ba zai dawo ba sai washegarin ranar. Ƙanzil ban ce da shi ba na kashe wayar zuciyata tana ƙuna, ranar barci rabi da rabi na yi saboda tsabar haushinsa da ya cika mini ciki. Domin tun da marecen ranar ya ce da ni ya kawo wuri kaza, duk da na san ɗabi'arsa ce ko bai taso ba ya ce yana kan hanya. Na yi ta zuba ido daga baya ya ce na yi haƙuri ba zai dawo ba sai ranar kaza._


     _Da safe yara suka dame ni da tambayar Babansu bai dawo ba, haushi ya sa da ya kira waya na bar shi da su na ƙi karɓar wayar. Duk da fushin da na yi bai yi amfanin komai ba, don sai da ya ƙara kwana huɗu bayan biyun da ya ce mini zai yi. A lokacin mun gama jigatuwa, duk wani kuzarina ya ƙare, saboda duk inda ake ba ni bashi na karɓa kuma ina jin nauyin komawa._


     _Ranar da ya tabbatar minu zai dawo, tun da yammacin ranar na yi ta dubon shi, saboda na san ya san halin babun da muke ciki ni da yaransa. Domin tun karin safiya da na ci waina bashi muka karya ba mu ci komai ba sai da marecen. Da na ga duhun magriba ya fara, na tura su neman abinci wurin wata da muke mutunci. Kaɗan suka samo, saboda alamunta ya nuna kamar ta fara gajiya da taimakon da take yi mana. A take suka lamushe abincin na ce su kora da ruwa yana gaf da isowa garin. Da haka na taushe su suka haƙura, amma har aka gama Isha bai dawo ba. Zuwa lokacin; ba su ba, ni kaina yunwa ta gama galabaitar da ni, ta yadda na koma hannuna ma wuyar motsa shi nake yi. Saboda babu laka a jikina ko kaɗan, bayan  dishi-dishin da nake gani gari ya koma juya mini, jiri yana kwasa ta a duk lokacin da na nemi miƙewa tsaye.  Domin tun karin safiya babu komai a cikina har zuwa lokacin._


     _Na koma lissafin lokaci, bini-bini sai na duba agogon da ke jikin bangon falona. Har na samu yaran suka yi barci bayan sun gama kukan cikinsu ke ciwo, don ita Iman har da amai ta yi saboda tsabar yunwar da ke ƙwaƙular hanjinta, ni ma ban san lokacin da barci ya kwashe ni ba.  Cikin dare na ji bugun katangar ɗakina, don daman ita ya dawo bugawa da dutsi a duk lokacin da ya yi dare, saboda na fi jin sautin na tashi fiye da dukan ƙofar gida idan ya yi. Na zabura a firgice na buɗe ɗakina, ina layi  kamar wata 'yar maye na buɗe masa gidan na juyo. Ƙanzil ban ce da shi ba na koma kan doguwar kujerar da nake kwana na kwanta ina mayar da numfashi._


      _Shi ma bai ce da ni komai ba, ya gama sabgoginsa ya nemi wuri ya kwanta, mintuna a tsakani na fara jin minsharin shi alamun ya yi barci. Ni ko na kasa rintsawa saboda wata azababbiyar yunwar da ke kartar cikina. Abin ka ga mai tsohon ciki, fitsarin da ya cika mini mara dole na miƙe jiri yana ɗiba ta na nufi hanyar toilet. Babu zato na ji na yi taga-taga na tafi luu na faɗa kan gado ruf da ciki._


" Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


    Ita ce kalmar da na faɗa cikin ɗaga murya da tsananin tashin hankali, wacce  ta sa ya zabura yana faɗin lafiya. Ban samu damar sake faɗar wata maganar ba, ballantana na samu kuzarin yi masa bayanin halin da nake ciki. Dafe da cikin na sulale a hankali na yi ƙasa, bajewa na yi bakin gadon ina nishi ɗaya bayan ɗaya. Uffan bai ce da ni ba har na samu kaina numfashina ya daidaita. Na ɗauki lokaci a wurin kwance ina jin kaina yana mini wani irin sara tamkar zan mutu, ga ciwon marar da ya taso mini gadan-gadan, saboda cikin ya cure wuri ɗaya gabaɗaya ya daina motsi. Daman tun rana na ji ya rage motsin da yake yi, wanda na jingina hakan da abincin da ban jefa masa ba._

     _Minsharinsa da na ji ya fara tashi ya ƙara tabbabar mini da wani barci ya koma. Zuciyata tana suya, na yunƙura da ƙyar da dafe-dafe na dinga bin bango har na isa toilet a tsaye na ziraro fitsarin. Saboda azabar da nake ji a marata ba zan iya duƙawa ba, a tsayen na yi tsarki tare da wanke inda fitsarin ya taɓa a jikina, sannan na fito kamar yadda na shiga da dafe-dafe na koma kan doguwar kujerar na kwanta. Shiru na yi ina jin hawaye yana ta zirara a gefe da gefen fuskata ba tare da na shirya zuwansu ba._

      _Yadda na ga dare; haka na ga safiya, domin damuwa da ƙuncin zuciya sun hana ni barci. Don ita marar ta daina mini mugun ciwo, amma ina jin zafinta kaɗan-kaɗan. Asubar farin Iman ta fara kuka, wanda na tabbatar da yunwa ce take ji, amma da yake iya kukan take yi ba ta ambaci abinci kl yunwar ba; har dukanta ya so yi a kan ta yi masa shiru. A ƙarshe ya fice ɗakin a ƙufule yana mitar mun takura shi mun hana shi barci._


      _Bai dawo gidan ba sai da rana ta yi shaa! A lokacin ƙarfe takwas da rabi na safiya har ta gota, ko shi saboda ganin wata da muke mutunci ta shigo gidan duba yanayin jikina kamar yadda take yi lokacin bayan lokaci. Hakan ya sa kai-tsaye zuciyata ta ba ni ya zaci ƙararsa na kai mata, shi ya sa jikinsa yana rawa ya kwaso ledodin biredi ya ajiye gabana. Sannan ya fita jim kaɗan ya dawo da madarar leda guda uku ya ajiye mini har da ƙwai da sikari yana cewa,_


     "Ki daure ki tashi ki nema muku abin kari rana ta fara yi!"


    _Wani kallo na yi masa cike da mamakin kissa da kisisina irin nasa, sannan nan take na ji wani sabon kuka ya zo mini. Na shiga rero shi wiwi tamkar wacce aka yi wa mutuwa, saboda tsabar baƙincikin rainin hankalin da yake yi mini. Matar ta shiga salati tare da yi mini nasihar na daina kuka saboda su Ummu Salma ma kukan suke yi. Wa'azi ta dinga mini a kan na taimaki kaina na daina saka wa zuciyata damuwa ko don abin da ke cikina. Jikina yana rawa na miƙe na ja hijabina tare da tasa ƙeyar yarana da nafin bar masa gidansa. Matar ta riƙe ni, tare da ba ni bakin na yi haƙuri kada na je ko'ina a halin da nake ciki. Buɗar bakinsa ya ce,_


    "Idan ma za ta je ban hana ta ba! Amma ta bar mini yarana! Domin babu inda za ta je da su matuƙar ni ne ubansu!"


     _Matar ta dinga rarrashinsa amma sai ƙara zaburewa yake yi, domin gabaɗaya idonsa ya rufe ya dinga feso magana cikin ɗaga murya tamkar ya kai mini duka yana cewa,


    "Ni fa ba zan hana ta tafiya ba! Amma ta sani ko ƙofar takashi ba za ta je da yarana ba! Tun da na gano rayuwata da mutuwata duk ɗaya a wurinta. Domin duk wanda ya san hanyar Lagos ya san ba ƙaramin haɗari gare ta ba! Amma a haka na yi ta kiran ta ina kan hanya ta ƙi ɗauka, sannan na dawo gidan ma sai ta nuna mini iyakata sannu da zuwan banza ban samu a wurinta ba. Ballantana tarbon arziƙin da zai nuna mini ta ji daɗin na dawo gida lafiya!"


      "Ko mutuwa ka yi ai ba kanka farau ba!"


      _Abin da na faɗa kenan a ƙufule, saboda ya gama kai ni bango ya jingine. Don tsabar laifi ya zama tudu ka take naka ka hango na wani; ni yake ganin laifina, amma ya manta da wanda ya aikata._


     "Kin ji ko? Fatar mutuwa ma take yi mini! To ta Allah ba taki ba wallahi! Don sai kin riga ni mutuwa ko kina so ko ba kya so!"


      "An yi maka fatar mutuwar! Ka sake ni!  Idan har cikakken ɗan halas ne kai ka tsinke igiyoyin aurenka duka!"




Post a Comment

0 Comments