TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 3

 D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



  *LAMBA TA UKU.*


         Tafiya na dinga yi cikin sauri ƙafafuwana suna harɗewa, ban samu natsuwar zuciya ba har sai da na shiga doguwar rumfar; da ke ɗauke da ofis-ofis ɗinmu. Waɗanda ke jere reras daga wannan sai wannan. Makulli na zura a jikin ƙofar nawa ofishin da ke kusa da na farko. 

      Da sallama na shiga kamar yadda na saba duk da babu kowa a ciki. Amma sanin akwai Mala'ikun da ke amsawa; hakan ya sa abin ya zame mini jiki ba na iyawa sai na yi sallamar koyaushe. Tun kafin na isa inda kujerata, na ji ƙwanƙwasa ƙofa tare da sallamar Inna Taru mai mana shara. 

       Cikin ladabi ta gaishe ni na amsa mata cikin sakin fuska cike da kulawa. Idonta a kaina ta ce, 

      "Maigida ne yake neman ki?" 


      Babu shiri ƙirjina ya buga dam-dam, kai-tsaye na amsa mata da "To" bakina yana rawa, saboda har raina ba na son duk wani abu da zai sa; ya ƙara mini wani lodin damuwa a cikin zuciyata. Haka kawai na tsinci ƙirjina yana bugawa, cikin sauri na fito fuskata a haɗe na doshi ofishinsa. 

       Sai da na ƙwanƙwasa ya ce

 "Come in."

       Sannan na tura ƙofar a hankali na shiga kaina a duƙe fuskata a cure. Tsayuwar minti biyu na yi a gaban teburin shi, yana ta rubuce-rubuce sannan ya ba ni umurnin zama, a kan kujerar da ke fuskantar shi ba tare da ya ɗago fuskarsa ba. A nan ma sai da ya ja lokaci yana tattara wasu file ɗin da ke gabansa tare da gyara musu zama. Sannan ya cire gilashin da ke fuskarsa ya yi tagumi da hannunsa biyu. Ido ya zuba mini ƙurin na ɗan lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya ya magantu.

       "Ban san me ya sauya ki cikin ɗan lokaci ba! Haka ma ban san me na miki ba gabaɗaya kika tsane ni?"

       

      'Ikon Allah'

      

Ita ce kalmar da na faɗa a zuciyata tun kafin na yi magana. Duk da ba na son haɗa ido da shi saboda kwarjininsa da ke fisgata. Amma sai da na yi jarumtar jefa ƙwayar idona cikin nasa kafin na sauke idona ƙasa, bayan na duƙar da kaina ina wasa da yatsun hannuna na ce,


       "Ban tsane ka ba!"


Abin da na iya faɗa kenan saboda girmansa da ya cika mini ido, sannan ƙirjina har lokacin yana dakan luguden da ban san me ya janyo shi ba. Duk da kai-tsaye zan iya alaƙanta hakan da kallon da yake yi mini ko ƙyaftawa babu. 


     "Ban ji daɗin yadda kike ƙoƙarin yin wasa da aikinki ba. Ranar Jumu'a kin zo har aka tashi ba ki neme ni ba, balle ki ji in da aiki ki karɓa. A yadda kika zo haka kika koma ba tare da kin damu da aikin ba. Don haka a shawarce idan irin wannan zaman kawai yake kawo ki; to ki yi zamanki a gida ba sai kin fito aikin ba!"


     Dirim-dim! Shi ne ƙaƙƙarfan bugun da zuciyata ta yi, saboda ƙarshen maganarsa ta na yi zamana ba sai na fito ba. Nan take raina ya ɓace na miƙe, ba tare da na ce da shi komai ba na nufi hanyar fita. Cikin saurin murya ya ce da ni,


     "Ban ba ki umurnin tafiya ba!"


    Cak! Na tsaya ina ƙoƙarin goge hawayen da suka cika idona, wanɗanda suke neman gangarewa a kan dandamalin fuskata. Cike da mamaki na tsinkayo muryarsa tana yawo a cikin kunnuwana, wacce ta kashe mini jiki ta so luguiguitar da zuciyata. Saboda yanayin da ya yi maganar da kalaman da ke fitowa a bakinsa sun tsuma ni.


     "Ban san me ya sa kike murna da hana zuciyata sukuni ba! Ban san me na miki kike ƙoƙarin sai kin cusa mini damuwa ba! Amma ki je ki yi duk abin da kike so, na daina takura ki daga yau ba zan sake yi miki zancen abin da ya shafi aikin ba! Ki je! Ki tafi na ce! Ba na son sake ganin ki a cikin ofishina daga yau! Idan akwai abin da za ki karɓa ko ki kawo mini; to ki bai wa Baba Masinja kawai ya kawo ko ya karɓar miki a hannuna."


     Ban iya ce masa uffan ba, kawai na buɗe ƙofar na fice zuciyata tana tiririn baƙinciki na koma ofishina. 


      "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun"


      Ita ce kalmar da na yi ta maimaitawa a cikin bakina. Saboda ban san me na masa da zafi har haka ba. Ban san wani mummunan aikin da na aikata ba, balle ya yi mini wannan tsattauran kashedin. Da sassarfa na isa kan kujerata na zauna tare da jingina bayana a jiki na kwanta. Ruf na rufe idona ina ta nanata kalmar a bakina a hankali tamkar mai raɗa. Saboda amsa-kuwar da zantukansa suke yi mini a cikin kunnuwa, tamkar a lokacin yake furta su. 


     Na ɗauki tsawon lokaci a haka, kafin na ji sallamar wadda ban yi zato balle tsammanin ganin ta a lokacin ba. 

       

      'Amina!'


Zancen da na yi kenan a cikin zuciyata kafin na buɗe idanuwana na sauke su a kanta. Murmushin da na gani shimfiɗe a kan fuskarta, ya sa na ƙarfafa kaina, na daidaita zamana. Da murmushin yaƙe na tarbe ta cike da mamakin ganin ta a kan fuskata. Zama ta yi tana 'yar dariya ta ce,


      "Daɗa sai ga mu tsidik! Kamar an jefo mu."


    Ta ƙare maganar tana dariya, ni ma na faɗaɗa fuskata da murmushi na ce,


      "Wannan ba zata haka?"


     Jakarta ta ajiye gefe sannan ta gyara zamanta ta ce,

      "Allah ya nufa shi ya sa kika gan ni. Saboda har na cire rai da zan sake zuwa aiki, sai ga shi an 'yanta ni na dawo tun kafin a yi mini salalan tsiya."


       "Ban gane ba!"


Zancen da ya fito bakina kenan a hargitse, saboda ni kaina ba a natsen nake ba tun a kan fuskata. Amina ta yi ɗan murmushi mai sauti sannan ta ce,


      "Allah ya nufa na dawo bakin aikina. Wanda Mama ta so salwantar mini da shi, kuma ta so na yi asarar shi..."


     "A taƙaice dai yanzu ta haƙura ta bar ki ki ci gaba da aikin kenan?"


     Wani kallo ta yi mini, wanda na fassara da,

'Ba ki san dawan garin ba'

      Sai ga shi ta tabbatar mini da hasashen da na yi da cewa,

       "Har yanzu tana kan bakanta ba ta saduda ba. Asali ma ba na gidan, saboda ta kore ni a kan na koma gidan ubana ɗanta ya gama zama da ni..."


      "Subhanallah! Me ya yi zafi?"


      "Hmmmmm!" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sake cewa,

      "Tun daga ranar da ta karɓe wayata, kuma ta ce ba zan sake zuwa aikin ba; ban bi ta kanta ba balle na roƙe ta ta ba ni wayata ko ta yi haƙuri na dawo ba. Ganin hakan bai dame ni ba ya sa ta tsiro da zancen sai na bar gidan, shi kuma ya ce da ni kada na je ko'ina. Dokarsa ita ce ta hana ni guje wa matsin lambar da Mama take yi mini. Kullum ina ɗaki kamar garar kunya, ban da miji a hannu balle abin da ya kawo a raba da ni."


"Ikon Allah! Ita ko Mama ina za ta kai haƙƙinki?"


    "Amma fa aikin gidan kaf da ni ake yin sa, matuƙar ina son na samu abin da zan saka wa bakina. Duk ranar da na ƙi fita aikin kuma ranar gabaɗaya babu kwanon abincina, Yusuf ma ɗan kaɗan ake ba shi don kada na ci. Shi ma ban damu ba na dinga ba shi kuɗi a ɓoye yana siyo mini abin da nake so, ko kuma Baban shi da dare ya shigo da abu a ɓoye ya wurgo mini ɗaki a ɗarare. 

        Sai dai kuma tun da ta ƙyalla ido ta gani, komai ya tsaya kamar ba a taɓa yi ba. Domin a daren ranar har tsine masa ta so yi, a kan ya siyo mini dafaffiyar Indomie a cikin takeaway. Haka ma Yusuf ranar da ta kama shi ya siyo mini awara a ya saka a aljihunsa; dukan da ta yi masa duk sai da ta farfasa masa jiki da tabon bulala. Bayan zagin da ya sha da kiran shi munafiki ya fi cikon kwando. Na sha kuka ranar kamar zan shiɗe, na kira Babana a waya na sanar da shi ya ce na yi haƙuri, shi ma ya bar ta da Allah da ƙarfin zumunci, domin a tambaye ta tun a nan duniya."


    Shiru ta yi tana goge hawayen da ke ta ambaliya a kan fuskarta. Imani ya sa na kasa furta komai har ta ɗora maganarta a inda ta tsaya.

       "Ranar da ta kore ni kuma, ina kwance ɗakina da dare, har bacci ya fara ɗiba ta na ji bambaminta cikin ɗaga murya tana ihun ɓarawo. Cikin sauri na fito na nufi ɗakinta da sassarfa, cike da zummar na kai mata agaji domin kada ɓarawon ya yi mata illa. Turus na yi babu shiri saboda hango Yusuf cakume a hannunta tana buga masa kula. Sannan tana ihun ɓarawo a kawo mata agaji ya zo yi mata sata. Jikina yana rawa na isa inda suke na fara jan Yusuf raina a ɓace, cike da tsautsayi na ture ta ta faɗi garin karɓar shi daga irin mugun riƙon da ta yi masa a wuya. Ai kuwa ta fasa ihu da kururuwar na karya ta, na nufe ta da nufin tallafa mata ta miƙe ta kai mini mugun bugu na kauce. Sai ga ɗanta ya shigo gidan cikin tashin hankali yana tambayar abin da ya faru. Babu tsoron Allah da haɗuwar ta da shi ta ce; Yusuf ya yi mata sata don ta kama shi na hau ta da duka. Shiru kawai ya yi bai ce da ni komai ba illa kama ta da ya yi ta miƙe tsaye tana faɗin. Wallahi sai na bar gidan nan a lokacin, ko kuma ita ta bar mana gidan gabaɗaya. Haushi ya sa ina kuka na ja hannun Yusuf muka koma ɗaki, saboda ban san lokacin da ya fita ba kuma ban san abin da ya kai shi ɗakinta ba. Sai da ya fito mini da wayata a aljihunsa ya miƙa mini, sannan na gano abin da ya kai shi ɗakinta a daidai lokacin da take bacci."


      "A gaskiya abin da Mama take yi ko kaɗan ba ta kyautawa. Kuma wai a cikin familynku babu wanda take jin maganarsa a sanar da shi? Ko da za ta rage wannan ɗaukar kayan ita ma ta rage wa kanta nauyin da ke kanta."


    Abin da na faɗa kenan cike jin haushin halin Mamar. Murmushin yaƙe Amina ta yi sannan ta ce,

       "An sha zama a kan matsalar amma kullum ƙara tuɓurewa take yi. Kuma shi ma ɗan nata ba ya nuna mata abin da take yi babu kyau, duk abin da ta ce ya yi shi yake yi ko da ya san ba daidai ba ne. Domin ko ranar haka ta saka shi gaba a kan dole sai mun bar gidan daga ni har Yusuf. Sai ce mini ya yi na yi haƙuri na je gidan kamar yadda ta ce, shi zai shawo kanta idan ta huce sai mu dawo. A cikin daren ya raka mu har ƙofar gidanmu ya ajiye mu muka yi sallama ya tafi, bayan ya yi ta bai wa Babana haƙurin da ya fi dacewa da Mama a kan kada ta kore mu. Amma ni da Babanmu ya juye wa shi ya bar mu da tunanin yaushe matsalar za ta zo ƙarshe. Yanzu haka kwanana biyu a gidanmu, kuma shi ne ya ba ni umurnin zuwa aikina har zuwa lokacin da zai shawo kanta."


       "Kai jama'a! Wannan lamari yana buƙatar dogon bincike gaskiya. Amma haka kawai Mama ba za ta yi miki irin wannan ƙiyayyar ba. Bayan zumuncin da ke tsakaninta da mahaifinki ba na wasa ba. Ai uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa ba, ko wani ta ga yana miki hakan ita mai hanawa ce balle a ce ita ke yi. Hmmmmm! Allah ya kyauta, kuma ya kawo sauƙi cikin lamarin."


    "To Amin!"


Amsar da ta ba ni kenan, kafin mu yi shiru jugum-jugum kowa da tunanin da yake yi. Domin yanayinta ya nuna a fili ta lula duniyar tunani. 

       Mun ɗauki lokaci babu wanda ya yi magana, sai da Baba masinja ya ƙwaƙwasa ƙofa sannan muka dawo natsuwarmu. Umurnin shigowa na ba shi ya shigo cikin ladabi ya ce da ni,

      "Ranki ya daɗe kina da baƙi a waje ke suke jira." 

       "Ok tom su shigo Baba ai da sauran lokaci."

      Zancen da na yi kenan bayan na duba agogon da ke hannuna. Amina ta miƙe tana faɗin sai na fito ta fice, na bi ta da kallon tausayi har ta fice, mutumin na farko ya fara shigowa. 

       Natsuwar dole na gayyato sannan na ciro gilashina na saka. Karɓar kuɗin harajin na dinga yi ɗaya bayan ɗaya ina rubuta sunansu a jikin takarda, tare da ba su uzurin su yi haƙuri gobe su dawo su saka hannu shaidar sun biya. Saboda babu files ɗin su a hannuna kuma na saka wa raina ba zan ce da MD ya ba ni ba. Tun da ya san da zuwansu kuma bai ce da ni komai ba.

        

     Ƙarfe biyu saura minti shida na kammala da su na fito. Takardar sunayensu da na ɗauka na bai wa Baba Masinja, sannan na damƙa masa ruwan kuɗin tare da saƙon ya miƙa wa MD. Kai-tsaye na fice Ma'aikatar. Ko Amina ban tsaya nema ba na tari adaidaitasahu na yi gida. Zuciyata cike da tunanin Haidar, a gefe ɗaya kuma mugun halin da Mama take gwada wa Amina.

       Tunanin kiran Najib ya faɗo mini a rai, cikin sauri na ciro wayata na cire ta a Airplane mode ɗin da na saka ta. Saboda ba na son MD ya neme ni duk da jikina ya ba ni ba zai neme ni ba har a tashi. 

      Kira na danna masa ringing ɗaya biyu ya ɗauka, gaishe ni ya fara yi sannan ya ce, 

       "Aunty tun ɗazu na kira ki ba ta shiga. Ki kwantar da hankalinki na gano Makarantar da aka canza masa. Saboda na gan shi a kan hanya lokacin da aka tashi, na ɗauke shi tare da abokan tafiyar shi na ajiye su cikin unguwar na juya. Gobe idan Allah ya kai mu za mu je makarantar mu jira shi."


        "Ok tom!"


Abin da na iya faɗa kenan na kashe wayar, saboda kukan da nake ƙoƙarin dannewa ya ƙi ba ni haɗin kai. Ganin da gaske Mukhtar neman makasata yake yi ta kowace fuska.

      'Mene ne amfanin canza masa makaranta kuma, idan ba baƙinciki ba?'


    Zancen da na yi a zuciyata kenan bayan na goge hawayen fuskata. Har aka ajiye ni ƙofar gidan Kawu Sale ban san an kai ba, saboda tunanin ƙetar da Mukhtar yake nuna mini. Wacce babu komai a cikinta face baƙƙan ciki da ɓacin rai, bayan takaicin da yake cusa mini ta ƙarfi ko ba na son kulawa.







Sai haƙuri Zaituhabba😢




Post a Comment

0 Comments