TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 35

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 3️⃣5️⃣


_______

🥀🥀🥀

Tun Asubha daya tashe ta salla ya fita kuma bae dawo bh har bayan ƙarfe tara, akan dinning table Safeerah tayi zaune tana yin breakfast. Ƙarar shigowarsa cikin gidan yasa ta ɗaga kanta, sanye da sweatpants da riga mara hannu ta gansa kuma duk a jiƙe yake da zufa, cikin basarwa Safeerah tace, "Ina kwana.." kai kawai ya ɗaga mata ya juya ya haye upstairs, tana cikin tattara plate ɗin da tayi amfani dashi Abideen ya sauke downstairs sanye da khaki, dinning ɗin ya ƙaraso inda tayi serving ɗinsa ta koma kitchen.


Idanu ya bita dashi ganin yanda black shaddar jikinta ɗinkin bubu mae zubin red ya karɓi jikinta ya fitar da shape ɗinta, sauke idanunsa yyi ya fara bawa cikinsa abinci. Bae ƙarasa ba ta taho ta zauna a gefensa tace, "Ina so naje gida, Umman Safna bata da lafiya.." kallonta kawai yyi ya cigaba da cin abincinsa, sae da ya gama tsaf ya barta da kallonsa a tsanake yace, "Ki shirya. I'll drop you off!" Cikin farin ciki ta miƙe ta wuce ɗakinta ɗauko veil da jaka, a mota ta tarar dashi inda tana shiga suka fice daga gidan, ta lura yanzu ko kulata sojojin gidan sun dena yi kuma ta rasa dalilin hakan, ko tayi musu magana sae suyi mata shiru su sauke kai ƙasa kamar marasa gaskiya. 


A ƙofar gate ɗin gidansu Safna ya sauke ta, har zata fita ya fusgota ta faɗa kan ƙirjinsa, fararen idanunsa ta tsaya kallo bata lura ba ya kamo lips ɗinta ya fara kissing, luff tayi jikinsa tana jin yanda harshensa ke exploring bakinta. Sakinta yyi yana maida numfashi a hankali, tana gyara zamanta yace, "I'll text you idan na gama.." kai ta ɗaga masa, by mistake idanunta suka sauka akan bulge ɗinsa, idanunta ya bi ya kalli inda take kallo, basarwa yyi ya ɗauke kansa ko a jikinsa. Sauka tayi daga motar tayi shigewarta cikin gidan, sai da ya tabbatar ta shiga gidan yyi ajiyar zuciya ya gyara zaman wandonsa yana mayar da numfashi, agogon hannunsa ya kalla yaga ya ɓata lokaci sosai hakan yasa yyi reverse ya bar anguwan.


Akan gado ta tarar da Umman Safna, gaisawa sukayi taga ma harta samu ɗan sauƙi, ɗakin Safna ta wuce ta ganta tana kwance har kusan 11 na safe amma tana kwance. Zama tayi gefen gadon tace, "Safna.." a hankali ta zame blanket ɗin data rufe fuskarta dashi ta kalli Safeerah, cikin mamaki ta miƙe ta zauna tana goge idanunta. Kallonta Safeerah tayi tace, "Kar ki mun magana sae kinyi brush.." dariya suka kwashe dashi nan Safna ta zame daga gadon ta wuce bathroom, ta ɗan ɗauki time kafin ta fito ɗaure da towel.


Tana gama shiri cikin dogon riga ta dawo gefen Safeerah ta zauna tace, "Naga kin rame ne fuskarki ma ta kumbura, kinyi rashin lafiya ne?" Girgiza mata kai tayi nan Safna ta fita daga ɗakin, bata jima ba ta dawo ɗauke da tray, duk yanda Safeerah ta ƙi cin abincin nan sae da Safna tayi mata dole har suka ci suka gama Safna ta fitar da kayan ta dawo ta zauna. 


Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ciro littafin tace, "Ban samu zuwa ba amma kin kawo kanki.." dariya Safeerah tayi tace, "Dama kece baki ga daman zuwa ba.." dariya suka sake yi nan Safeerah ta karɓa littafi ta fara karantashi, bata gama ba ta ajiye littafin, kallonta Safna tayi tace, "Ya dai..?" Taɓe baki Safeerah tayi tace, "Toh ai littafin yana da yawa sae dae naje gida na karanta.." kallonta Safna tayi cikin mamaki tace, "Yoh na manta matar aure ce" dariya Safna tayi amma taga Safeerah ko gezau bata yi ba, hannunta Safna cikin lallashi tace, "Safeerah meya faru?"


Kallonta Safeerah tayi tace, "Safna Yaya Abideen ne, wallahi ban san me yake damunsa ba ko nace me ya shiga kansa. Kwata-kwata ya koma yin abu kamar bashi ba, kinga last week yyi wa wani friend ɗina duka yyi masa jina jina. Shi a lallai bazan kula ko wani namiji ba dan Allah haka ake rayuwa kuma ya kama harda punish..." shiru tayi jin ta saki layi agaban Safna, kallonta Safna tayi alamar taji mae tace toh ta cigaba, ajiyar zuciya tayi tace, "Har da punishing ɗina yake.." ko da Safna taji haka sae ta tsorota tace, "How??" Kanta a ƙasa tace, "Spanking ɗina yyi.." dariya Safna tayi tace, "Ke dalla toh ai wasu na yin haka.." ganin Safeerah tayi shiru yasa Safna yin ajiyar zuciya Safna tunda da sauƙi amma ta tausayawa Safeerah sosai tunda duk bata san abubuwan nan ba, "Ki karanta littafin nan har ƙarshe, ni ma zan karanta idan na gama exams. Baby yace zai turo..." ihu suka sake tare na murna da jin daɗi, sosai Safeerah ta taya Safna murna inda nan Safna ta gyara zama ta shiga bawa Safeerah shawarwari suna ɗan ƙus ƙus har lokacin sallar Azahar tayi. 


...

Abideen na zaune a office ɗinsa yana aiki cikin computer, message ya shigo ta email ɗinsa. Yana dubawa yaga wani Mission za'a tura sa a wani sashen Kenya ɗin da suka ƙi amicewa da masalaha da aka yi tsakanin ƙasashe biyun. Office ɗin LTC ya wuce ya nuna masa nan ya sanar masa daga higher-ups saƙon yazo kuma idan yana aikin soja dole ne ya bi command ɗin na sama dashi amma an tabbatar da ƙara masa matsayi idan ya dawo daga Mission ɗinsa lafiya. 


Cikin ya yarda tund ba yanda ta iya amma harga Allah bae so tafiyar ba tunda so yake ya ƙara kusanci da matarsa, cikin takaici ya shige cikin motarsa ya nufi hanyar gidansu Safna, a hanya kuma ya tsaya ya siya basket ɗin fruits da akayi wrapping, har ya kusa ya tsaya ya tura mata message sannan ya ƙarasa gidan. Tana zaune a parlour ita da Safna suna hira bayan sallar Laasar message ɗin Abideen ya shigo wayarta, har kyarma jikinta yake ta duba saboda bata manta da punishment ɗinta ba. 😅


💬Ki shirya, I'm on my way.


Tana ganin haka ta fara shiri inda Safna ta bi ta da ido tana ganin yanda jikinta har rawa yake yi, ba'a jima ba kiransa ya shigo wayar, ko numfashi mae kyau bata iyayi ba tayi saurin picking kiran, "Ina waje.." yana faɗin haka ya kashe wayarsa yana murmushin mugunta jin tana ringing ta ɗauka. 😅


Fitowa tayi ta zagaya ta gurin windown sa tace, "Baza ka duba Umman Safnan ba?" Cikin tattaushi tayi tambayar tana yi tana murza yatsun hannunta, sa'a taci kuwa dama yyi niyyar shiga sae taga ya fito daga motar ya buɗe boot ya ciro basket ɗin, nan tayi masa jagora suka shiga cikin gidan. A parlour suka tarar da Umman Safna nan suka gaisa yyi mata sannu da jiki ya  ajiye mata basket ɗin sannan yyi musu sallama ya fice, a tsatsaye Safeerah tayi musu sallama sannan tayi wa Safna alamar za su yi waya ta fice. 


A mota ta tarar dashi fuskarsa cikin rashin walwala, tunda ta kallesa sau ɗaya bata ƙara yunƙurin su haɗa ido ba ma bare wani abu ya haɗa su, can suna tafiya inda idanunta suka waje tana kallon jamaa kamar daga sama sama taji muryarsa yace, "Zan tafi mission.." da sauri ta juyo ta kalle shi saboda ita duk idan aka faɗi abubuwan nan duk tunaninta kan mutuwa yake komawa, a tsorace ta kalleshi tana tunanin me ya kamata taji, daɗin tafiyar da zai yi ko kewarsa da zatayi, ɗauke kanta tayi bata sake ce masa komai ba.


Kallo ya bita dashi ganin ko nuna ta damu bata yi ba, sosai ya ji ba daɗi a ransa yana ganin kamar kusancinsu ya ragu ko kuma bata sonsa har yanzu, ajiyar zuciya ya sauke ya ɗauke kansa daga gareta. 


Yana cikin driving wayarta ta ɗau ƙara, cirowa tayi daga jakanta bata kai ga ganin waye ya kira ba sae ji tayi Abideen ya fusge wayar, a gigice ta juya tana kallonsa, sunan caller ɗin ya tsaya yana gani har wayar ta katse. Wurgar mata da wayar yyi ta faɗa kan cinyarta, cikin mamaki da tsoro ta ke kallonsa ganin idanunsa sun fara yin ja gashi ya ɗaure fuska, a fusace ya juya yana ɗage mata kira yace, "Waye shi? Sabon saurayi kika yi bayan Habeeb?"


Ido ta zare tana kallonsa ga girarta da ta haɗe cikin rashin fahimta, tana buɗe baki tace, "Ya Abideen meye haka..." bata ƙarasa ba yasa ɗayan hannunsa ya kamo bakinta ya matse, cikin jin zafi yasa ta ɗaga hannayenta tana ƙoƙarin cire hannunsa daga bakinta amma kamar ba ƙoƙarin ture hannunsa take ba dan ƙara ƙarfinsa yyi wa riƙon bakin. Mitsi mitsi yyi da idanu yace, "Wato har kina da bakin musa man huh? Da aurena akanki kike neman maza??." Cikin kaɗuwa ta ɗaga kanta tana kallonsa amma ba damar magana tunda ya matse bakin, hawaye ne suka fara zuba daga idanunta jin ɗacin kalaman da Ya Abideen ɗin yake jifarta dasu, anya Ya Abideen ɗin da ta sani ne ko chanza shi akayi ne...


Don't forget to like and comment!🦋✨️

Facebook #Fatee Mah

Wattpad #_khanoum_


©️ Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments