TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 47

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 4️⃣7️⃣

________

Ya Jamilah tasan cewa Abideen yana waje amma ya ƙi ya shigo saboda kunyar haɗa ido da Safeerah bayan aika aikan da yyi mata, a waje kuwa Ya Jamilah ta tarar dashi ya saka hannayensa ya dafe kansa. Wani tausayinsa ne ya kamata sosai, zama tayi gefensa tareda kamo hannunsa, juyowa yyi ya kalleta da idanunsa da suka faɗa suka ƙanƙance kamar ya kwana yana kuka ga yanda ya sake ramewa yyi ƴar wuya sae murɗaɗɗen jiki amma fuska duk a rame, kallonsa Ya Jamilah tayi tace, "Ka ci abinci?" Shiru yyi mata kafin ya girgiza mata kai, hannunsa ta koma da niyyar ya tashe su shiga cikin ɗakin yaci abinci, da kyar ya bita kawai. 


Suna shiga ya tarar da Safeerah a shimfiɗe tana bacci, kyakkyawar fuskarta ya bi da kallo kafin ya ɗauke kansa cikin jin kunyar kansa, a kujera ya zauna nan Ya Jamilah ta jawo table ɗin ɗakin ta ajiye masa breakfast akan table ɗin, da kyar ya fara ci amma ji yake kamar ƙasa yake ci amma ganin Ya Jamilah ta zuba masa ido yasa ya ɗan ci ba laifi. 


Wani juyi Safeerah tayi wanda yasa duka ƙirjinta motsawa sae, turo baki tayi cikin shagwaɓa tace, "Way..yoo ..Allah..na.." tana faɗin haka sae tayi shiru tana juyin neman ta yadda kwanciyar zae yi mata daɗi, can dae ta kwanta ta gefen damanta tareda turo ƙirjinta gaba, Abideen da idanunsa ke kanta ji yyi mararsa ta fara ɗaurewa, shi kansa takaicin kansa yaji hakan yasa ya miƙe zae fice daga ɗakin, Ya Jamilah ta so ta tsayar dashi amma bbu faidar yin haka sae ta barshi ya fice abunsa. Cikin motarsa ya koma ya shiga yana jin kamar kansa zae fashe saboda ya ma rasa tunanin me zaeyi, wani juyi yaji kansa yana yi masa kamar ana murɗe masa kwakwalwa, ta ke veins ɗin kansa suka fiffito suka yi ruɗa ruɗe dasu, iska mae zafi ya furzar ya taka motarsa sae asibitin Na'ima, mask ya ciro ya saka ya shige cikin asibitin. 


Yana shiga ya tarar da ita tana breakfast, agogon jikin bangon Office ɗin ya kalla, 11:02 ajiyar zuciya yyi ya samu guri ya zauna, daga yanda ta kalleshi tasan ba ƙalau yake ba hakan yasa ta ture breakfast ɗinta ta koma ta zauna a opposite ɗinsa tana sake yi masa kallon ƙurilla. Idanunsa da suka ƙanƙance ya kalleta dasu kafin yace, "Na'ima, ki bani drugs ɗin na duba sauran pharmacy amma duk basu da shi.." kallonsa tayi tareda yin ƴar dariya tace, "Ba'a shiyarwa sae a asibiti, asibitin ma sae likitan dayake duba mutum kuma ya tabbatar ya kamata a bashi.." runtse idanu Abideen yyi yace, "Na'ima please, kai na zai iya exploding any moment from now, dan Allah.." kai Na'ima ta ɗauke tace, "Aah Zayn" dafe kansa yyi da hannayensa yace, "Ki bar Antipsychotics ɗin, ki bani ko da Mood stabilisers ɗin ne.." ajiyar zuciya Na'ima ta sauke tace, "You can work this out Abideen, get support from your wife and it's.." bata ƙarasa ba ya daka wani tsawa ya ce, "Oh shut it Na'ima.." kallonta ya sake yi yana ɗage mata gira sannan ya cigaba, "What fucking support when my wife is in the hospital and ni ne reason ɗin da take a asibitin???" Yana cikin bayanin yakai hannu ya bugi table ɗin glass ɗin Office ɗinta ta ke ya tsatstsage sosai amma bae fashe ba tunda yana da ƙarfi sosai, yanzu da ya sake yin masifah sae jijiyoyin kan nasa da goshi su ka sake yin manya ga idanunsa da suka yi ja sosai.


 Runtse idanunsa yyi yace, "I'm so damn confused and I feel like my head is gonna explode!!!" Na'ima dae mutuwar zaune tayi dan duk cikin patients ɗinta bbu wanda ya taɓa yin outburst a gabanta, ajiyar zuciya ya sauke ta baki dan baze fita ta hanci ba dan baya cikin natsuwa, komawa yyi ya lafe jikin kujera yace, "I'm so tired literally.." ganin ya lafe jikin kujerarta yasa ta miƙe ta wuce safe ɗin office ɗinta ta ciro pills guda shida a hannunta ta rufe sannan ta tunkari inda yake, tana ƙarasowa ya buɗe ido tareda miƙa mata hannunsa alamun ta zuba masa, tun kafin ta miƙa masa ruwa ya watsa a baki ya haɗiye sae daga baya ya karɓa ruwan ya shanye tas. 


Zama Na'ima tayi ta gyara zamanta tace, "Me ya faru da Safeerahn?" ajiyar zuciya ya sauke tareda ɗauke kansa yace, "Well, I.. I took her last night.." kallonsa Dr Na'ima tayi tace, "Were you that rough on her??" Kallon banza ya watsa mata yace, "I admit that I have wild sexual desires amma a hankali na bita sosai wallahi.." kallonsa Na'ima tayi tana jin dariya na neman zuwa mata ganin babban soja kamar Zayn yazo yana mata rantse rantse, rolling eyes ɗinsa yyi yace, "Kema baki yarda ba ko, ko baki yarda ba ni dae Allah Ya san a hankali na bi ta, I was so damn careful with her.." ajiyar zuciya Na'ima ta sauke tace, "Just take it easy on her.." sosa ƙeya Abideen yyi yace, "Doctor ta ce mun she's an SVT patient.." hannu ta kai ta rufe bakinta kafin tace, "Subhanallah, patients ɗin zuciyar su is very weak, abu kaɗan sae ta fara bugawa da sauri and in severe cases kuma ko su suma ko tarin jini ko ta hanci.." kai Abideen ya ɗaga mata nan tace, "Take it easy on her.." kai Abideen ya ɗaga mata kafin ya kai dubansa ga agogo yaga har 11:38, murmushi yyi mata ya miƙe tsaye yyi mata sallama, toh dama ya samu magani mae zae tsaya jira. Yana fita ya mayar da mask ɗinsa ya koma gidansa, ɗakin Safeerah ya koma yyi laundry ya gyara ɗakin. (Husband material)😂🤭


Yana gama ɗan gyare gyarensa zuwa lokacin an tada sallar Azahar, sallah yyi yana idarwa a shimfiɗe a parlour yana maida numfashi, a haka wankin ma a washing machine yyi sae ɗakinta kawai da ya gyara kuma ba gyaran azo a gani ba amma sae sauke ajiyar zuciya yake yi sae a lokacin yyi tunanin lalle mata na ƙoƙari a haka take yin gyaran duka gidan tayi girki sannan ta tafi school. 


...

Can Safeerah ta farka daga bacci around 4:20, tana buɗe idanunta ta tarar da Safna a gefenta tana danna waya, wani murmushi Safna ta sake mata kafin tace, "Sannu, ya jiki?.." numfashi tayi kafin tace, "Da sauƙi.." ajiye wayar Safna tayi tace, "Mu je kiyi sallah.." taimaka mata tayi ta sauka daga gadon da kyar har suka wuce bathroom, tana cikin alwala ta ɗaga kanta ta kalli Safna tace, "Ya Abideen ya zo?" Girgiza kai Safna tayi tace, "Tun ɗaya Aunty Jamilah ta kira ni amma ban ganshi ba tun da na zo.." taɓe baki Safeerah tayi sannan ta cigaba da alwalan ta. Bayan ta idar da sallar ta zauna tana cin abincin da Safna ta kawo daga gida, tana gama ci tasha drugs ɗinta da taimakon Safna ta koma kan gadon ta kwanta, can ta kalli Safna tace, "Ina Aunty Jamilahn?" Kafin Safna ta amsa kuwa Ya Jamilah ta shigo ɗakin ta samu tayi crashing a wani kujera tace, "Ya Allah! Toh zuwa anjima za'a sallame ki mu koma gida.." nan fa zuciyar Safeerah ta tsinke ta fara bugawa, ƙiri ƙiri tsoro ya bayyana a fuskarta wanda kowa ya lura dashi amma basu yi magana ba, basu jima ba sosai aka yi knocking ɗakin...😁😁



*Knock, knock! Who's there? 😂💔



Murɗa ƙofar ɗakin yyi ya shigo cikin ɗakin da sallama a bakinsa, riƙe yake da wasu bags a hannunsa, yana ƙarasawa cikin ɗakin ya ajiye ledojin kansa a ƙasa. Safeerah tana jin muryarsa tayi saurin runtse idanunta, Safna ce ta amsa sallamar tareda gaishesa, amsa mata yyi amma yaƙi yarda su haɗa ido da Safeerah, da kyar ta buɗe ido ta kalleshi jin yanda ƙamshin turarensa ya cika ɗakin yana shiga mata hanci, suna zaunen nan yana ta faman taɓa ƙeya Ya Jamilah ta fito daga toilet tace, "Ka dawo?" Kai ya ɗaga mata dan neman muryarsa yyi ya rasa, jakan ta buɗe taga abinci ne ya siyo nan dae ta rufe tunda sun ci abinci, "Kai ka ci abincin ne?" Tambayar Ya Jamilah ya tsinke shi daga duniyar tunanin da ya tafi, tsintar kansa da kasa yin ƙarya yyi sae kansa daya kama juyawa, "Me ya sa baka ci ba jiba duk yanda ka rame rana ɗaya?!" Kallon Yayar tasa kawai yyi ganin yanda ta damu dashi sosai. (*Hearts for you Ya Jamilah..😁😘❤️*)


"Na ƙoshi.." kallonsa Ya Jamilah tayi dan ko da safen ma ai kaɗan yaci nan tace, "Tun safe bbu abunda kaci shine zaka ce ka ƙoshi.." tarrr Safeerah ta buɗe idanunta jin ance mijinta bae ci abinci ba tun safe..🤣🤣🤣🤭


....

©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments