TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 7

 D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


 *SAƘON GODIYA! Zanyi amfani da wannan dama, domin na miƙa saƙon godiya ta musamman, a wurin mutane na musamman masu gwaggwaɓan matsayi a wurina. Ina godiya sosai a kan ƙoƙarinku da jajircewar ku ta yaɗa wannan littafi kusufa-kusufa lungu da saƙo. Alherin Allah ya baibaye rayuwarku ta yau da ta gobe. Ina yin ku abadan da'iman ina alfakhari da ku koyaushe.*

*1. YARGATA (MAMAN SULATAN).*

*2. MARIYAM JUMARE.*

*3. KHADIJA MUHAMMAD (MRS BASAKKWACE).*

*4. HALIMA BABY (LEEMAS MANDI KITCHEN).*

*5. MUHAMMAD KARIM (MK).*



 *LAMBA TA BAKWAI.*


        Ganin da gaske bacci ya ƙi kawo mini ziyara, na miƙe na fito tsakar gida na ɗoro arwala. Carpet na shimfiɗa ina ta jera salloli har sai da gaɓɓan jikina suka yi sanyi. Sannan na zauna ina yi wa Allah kirari, tare da kai masa kukana domin ya kawo mini mafita ta alheri a cikin rayuwata. 

       Na ɗauki lokaci ina ta addu'o'in tsari a kan yarana, kafin bacci ɓarawo ya sace ni. Zuciyata wasai na tashi da safe bayan wani sabon kuzarin da nake ji. A gurguje na gama ayukan da na ɗora wa kaina kullum safiya. Sannan na shirya a cikin sauri muka fice. Zuciyata cike da tunanin yadda zan kwashe da MD yau idan na je.

       Aka yi dace ina shiga ma'aikatar yana doso kan motarsa cikin gate. Ƙirjina da ke dakan luguden uku-uku, ya hana ni kataɓus na dinga tafiya ƙafafuwana suna harɗewa.

       Da sassarfa na shige doguwar barandar da ke ɗauke da ofishoshinmu. Na buɗe nawa cikin sauri na shige don ba na so ya riske ni. Sai dai shiga ta babu daɗewa ya turo ƙofar tare da sallama. Kaina da ke duƙe ina nazarin wata takarda na ɗago, sannan na watsa masa idanuwana duka a kan fuskarsa. Cike da son karantarsa da yanayin shi.

      Sai dai ƙamshin turarensa ya so raunata ɗan kuzarina, bayan kallon da yake yi mini rungume da hannunsa a ƙirji, fuskarsa babu yabo balle fallasa.

    Kaina na sunkuyar bayan na janye idanuwana da ke kan shi, saboda na kasa jure jarumtar haɗa idonmu wuri ɗaya da shi. Cikin wata kalar murya ya yi magana, wadda ta so fallasa asirin da ke ƙumshe cikin zuciyarsa.


     "Me ya sa ba ki da tausayi? Yanzu saƙon ma idan na yi miki ba za ki mini reply ta yadda ya dace ba?"


    Kallo na bi shi da shi kafin na ce, 

      "Sir! Ka duba wayarka da kyau na ba ka haƙuri!"


     "Haƙuri! Haƙuri fa!? To wallahi ba zan taɓa haƙurin ba!"


 "Mene ne laifin haƙurin? Duk da ni ban san na yi komai ba!"

      Na ƙare maganar cikin sanyin murya da jan zarena da kyau domin na ƙara karantarsa. 


     "Hmmmm! Ke a wurinki haƙurin ne kawai za ki iya furtawa a bakinki?"


     "E! Saboda ban san laifina ba."


    "Ok tom! Ki yi yadda kike so!"


Yana ƙare faɗar hakan ya juya ya fice ofishin, cikin tashin hankali na bi bayansa da kallo. Zuciyata sai bugawa take yi da sauri da sauri, sannan tana ta ingiza ni a kan na bi shi na rarrashe shi. 


      'A kan wane dalili to?'


'Babu!'


     'Idan har babu dalilin a zahiri, zancen bin sa ki rarrashe ma bai taso ba.'


     Zantukan da zuciyata take yi kenan cikin ɗan lokacin da bai gaza mintuna biyu ba. Na tsayu a kan maganar ƙarshe saboda ban san me zan ce da shi ba, tun da shi kansa bai fito fili ya sanar da ni laifina ba.

     Tsawon lokaci na ɗauka ina ta zancen zuci, kafin na ji alamun shigowar saƙo a wayata. Cikin sauri na fiddo wayar na duba, babu shiri na miƙe saboda saƙon nemana da na hango. Sai da na shiga natsuwata da kyau na daidaita numfashina, sannan na tura ƙofarsa na shiga da maƙalalliyar sallama a bakina.

      Sai dai yanayin fuskarsa da na hango, ya sa na sha jinin jikina babu shiri. Waya yake yi cikin faɗa-faɗa kafin ya sauke ya yi mini nuni wurin wasu file's da wayar. Hakan da na gani na fahimci ɗauka yake so na yi maganar ce yake rowa.

     Na zura hannu zan ɗauka ya yi saurin ɗora hannunsa saman files ɗin yana girgiza kai. Hannuna na janye da sauri ƙirjina yana ta bugawa, sannan na ɗan matsa baya kaɗan ina masa kallon me kake nufi.  Rufe idonsa ya yi yana jijjiga kansa kafin ya ce da ni,


     "Go!"


Babu shiri na juya saboda jirin da nake ji ya fara ɗiba ta, har riƙe handle ɗin ƙofar zan fice ya dakatar da ni, ta hanyar faɗin,


     "Wait!"


Na ja na tsaya tamkar an dasa ni wurin, fuskata a haɗe nake kallon gefe saboda raina ya fara ɓaci. 

       "Yanzu idan na ce ki je kuma sai ki tafi?"


    Wata kalar muryar da ya yi amfani da ita wurin faɗin maganar, ya sa na kai kallona saman fuskarsa a ɗarare na ce,

       "A kodayaushe ni mai biyayya ce a wurinka Sir! Idan ka ce na je tafiya zan yi saboda na san akwai dalilin da ya sa kake so na tafi. Haka ma idan ka ce na tsaya zan tsaya a inda kake so, saboda ina da cikakken tabbacin ba za ka tsayar da ni babu dalili ba."


     "Good! Zo ki ɗauki files ɗin ki tafi. Sannan wannan shigar gyalen da kike yi don Allah ki daina."


      "In Sha Allah na daina daga yanzu. Amma idan zan zo aiki kawai, ko shi saboda ba ka so!"


     Idonsa ya rufe bayan ya duƙar da kansa yana shafa fatar idon nasa, wanda na hango gumi yana ta tsattsafowa a saman goshin shi. Hankacif ya yi amfani da shi wurin goge gumin, kafin ya yi mini nuni da hannunsa a kan na ɗauki files ɗin na tafi.

     Babu jinkiri na dawo na ɗauka na fice tare da rufo masa ƙofa a hankali. Cikin mutuwar jiki na isa ofishina na zauna ina mayar da numfashi, tamkar wacce ta yi gasar tserarrar gudu. Na ɗauki lokaci ban dawo natsuwata ba ina ta jujjuya zantukansa cikin raina. 

       Ina tsaka da wannan yanayin Amina ta turo ƙofa ta shigo, kalar tarbar da na yi mata ya sa ta zauna idonta a kaina.

      "Hajiya na gan ki a jirkice! Me ke faruwa ne?"


    Ajiyar zuciya na sauke sannan na yi mata nuni da zuciyata na ce,


      "Ƙirjina zafi yake yi!"


"Ke ma kin san ulcer ce, kawai ki sha magani."


     Shirun da ta ga na yi idona a rufe ya sa ta fiddo Tagmen a jakarta tare da gorar ruwa ta miƙo mini tana faɗin, 

     "Ki sha ɗaya, in sha Allah za ki ji daɗinsa sosai!"

        Gudun ta gano ni ya sa na ɓalli maganin na sha. Sannan na ja files ɗin da ke gabana ina faɗin,

       "Ina su Hajiya da Yusuf? Fatan kowa lafiya?"

       "Yusuf lafiya lau, Hajiyar ce kawai jikinta ya motsa."

      "Ubangiji ya ba ta lafiya, don Allah ki mata ya jiki kafin na zo!"


     Wani kallo ta yi mini sannan ta ce,

       "Kamar gaske zuwan za ki yi?"

  "Zan ba ki mamaki a wannan karon, ke dai ki jira ganin Asabar. In Sha Allah zan zo na gaishe ta, kuma na yi mata ya jiki."


    Cike da jin daɗi Amina ta cika fuskarta da murmushi tana cewa, "Wallahi da kin yi mutuncin da ba ki taɓa yi ba. Don tun da nake da ke ko gidan da ake ara mini ina zama ba ki taɓa zuwa ba, balle ki san muhallina."


     "Waton ma ara miki ake yi?" 


     "E kam, ba ga shi yanzu an koro ni ba!"


"Hmmm! Allah dai ya kyauta. Amma yana da kyau a zauna tsakaninku domin a samu maslaha."


       "Ni kaina abin da na ce kenan, Babanmu ya ce a zuba mata ido a ga ƙarshen gudun ruwanta."


      "Wannan ba ya kawo mafita gaskiya. Zaman dai shi ya fi alheri, domin a ɗinke inda ɓarakar take kowa ya gyara."


      "Ke Ni wallahi har na fi farinciki da zaman gidanmu. Saboda tun da na zo ba a nuna mini ɗan yatsa ba balle a hantare ni. Amma da can ne ɓacin ran da zan shiga sai ya riɓa kwanakin da  na yi gidanmu sau dubu. Ke ni da ma za a bar ni a haka, ya je ya yi ta riƙon auren daga shi har ita su ƙarata da halinsu."


      "Sasancin dai shi ya fi alheri."


"To Allah ya kawo sauƙi"


     "Amin."


Ina ta aikina muna hira da ita har na kammala, ta ɗauki ledar da na ga ta shigo da ita ta miƙo mini. Hannu na sa na karɓa ina jinjina kular da ke ciki na ce,


      "Wannan fa?"


 "Buɗa ki gani, takanas na yi ta domin ke!"


     Kular na ajiye saman teburin bayan na ture files ɗin gefe. Ƙamshin ƙulin da ya dake ni; ya sa na yi hanzarin zuƙe  numfashi.


     "Wowww! Wannan garar duka ni kaɗai?"


     Tana 'yar dariya ta ce, "Kin tuna jiya da muka fita mun ga mai tallar gurasa ya wuce ta gabanmu?" 


     "Tabbas! An yi hakan."


"To Sanin kina son ta da yawa, na ci alwashin zan zo miki da ita yau."


     "Allah Sarki! Ki ce na ɗora miki aiki!"


   "To Hajiyar Makka ni ce na saka kaina ai!"


     "Ubangiji ya saka miki da alheri."


 "Amin" Ta ce tana murmushi. Mayar da murfin kular na yi sannan na ajiye ta gefena ina duba agogo. Ganin an kusa tashi na miƙe ina faɗin,

      "Bari na miƙa wa MD file's ɗin nan na dawo."


     "Ok"


Ta ba ni amsa tana dannar wayarta, na fice cikin sauri na nufi ofishin. Murɗa ƙofar na yi tare da guntuwar sallamata. Ɗan jim na yi ina jiran ya amsa kafin na shiga, shirun da na ji na ɗan lokaci. Da muryarsa da na jiyo nesa ya sa na gano yana toilet, cikin sauri na faɗa na ajiye takardun zan juya. Kamar da gayya iska ya kwaso mini abin da yake faɗa a cikin kunnuwana.


     "Kwantar da hankalinki aure zan yi a cikin satin nan! Don haka ki je ki cigaba da duk abin da kike yi. Allah ya kusa ba ni wacce take daidai da ra'ayina. Ko ma wace ce mene ne damuwarki? E, na ji komai za ki ce ki faɗa kawai, zan yi auren ne a bisa son raina kuma da niyya. Ok tom you will see!"

      Fitt na fice offis ɗin, saboda motsin takunsa da na ji zai fito daga toilet. Gumi ya fara tsattsafo mini tun daga saman kaina har zuwa tafin ƙafata. Saboda zancen auren da na ji zai yi kuma sati ɗaya kacal ya razana ni.

      'Daman can yana son wata shi ne yake nuna kamar yana so na? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wannan wane irin mugun albishir ne na jiyo wa kaina?'


     Babu shiri na ja na tsaya a hargitse, na kasa gaba na kasa baya. Sai da Baba Masinja ya hango ni ya taso yana faɗin,


      "Hajiya lafiya?"


"La..fi...ya lau Baba!" 


Na furta maganar da ƙyar saboda ji nake yi tamkar na kurma ihu. Ko da zan rage jin abin da nake ji a lokacin. Baban ya ƙure ni da kallo yana faɗin,

     "Fatan dai ba jikin ne zai tashi ba!?


     "Lafiyata lau Baba! Cikina ne kawai yake riƙewa. Amma yanzu ya saki"


      "To Allah ya ƙara sauƙi..."


     Ƙarar buɗe ofinshin MD ya sa na yi hanzarin barin wurin cikin sassarfa na shige ofishina. Kafin na shige ina jin Baban yana yi masa bayanin ban da lafiya.

      Kiran da na ga ya shigo wayata tun kafin na zauna, ya sa jikina ya ba ni shi ne. 

     

       "Ki fito mu je asibiti a duba ki"


    "Ahh'aaa! Ba sai mun je ba! Na ji sauƙi na ware"


      "Ina jiran ki a mota"


Zancen da ya faɗa kenan a gadarance sannan ya katse kiran, jiki babu kuzari na sauke wayar ina haɗe rai na ce,


     "Ni fa lafiyata lau!"


Amina ta ɗago kai tana kallona cike son ƙarin bayani a cikin ƙwayar idonta. Na yarfar da hannuna cikin basarwa na ce,

      "Asibiti MD ya ce zai kai ni. Kuma na ji sauƙi tun da na sha maganin da kika ba ni"


     "To ki sanar da shi mana!"


     "Ba zai yarda ba, don Allah ki yi masa bayani zai fi gamsuwa."


     "Ke me ya sa ba ki yi masa bayanin ba!"


 "Ganin zai yi ba na son ganin likitan ne. Kuma da gaske ba na so na je a binciko mini wani ciwon da ban san ina da shi ba. Saboda damuwar da ta yi mini yawa tsaf za a ce ina da hawan jini."


      "Allah dai ya tsare..."


Kiran da ya sake shigowa ne ya sa na yi saurin faɗin,

      "Mu je ki masa bayani don Allah!"


    Tare muka fice ƙirjina yana zafi saboda ƙunar da zuciyata ke yi. Bakin motarsa muka tsaya Amina ta rasuna cikin girmamawa ta ce,


      "Na ba ta magani ta sha, kuma an yi sa'a ciwon ma ya lafa."


     "Oya ta shigo mu je kawai sauri nake yi."


    Kallon juna muka yi ni da Amina tana mini maganar ido alamun babu nasara. Raina ya ɓaci na ƙara harɗe fuska tamkar ban taɓa dariya ba. Motar na buɗe na shiga, Amina ma ta zagaya ta shiga muka hakimce baya. Mintuna a tsakani bai yi dogon motsi ba balle ya tayar da motar mu tafi. Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya ajiye wayar da yake danna, sannan ya tayar da motar muka fice Ma'aikatar.

     Jugum-jugum babu wanda ya yi magana har muka hau babban titi. Kai-tsaye Uduth muka nufa zuciyata a cunkushe ina kallon gefen titi. Ƙira'ar Sudais ya saka har muka shiga Asibitin, a bisa tsautsayi ina ƙoƙarin fita motar bayan ya yi parking, karaf! Muka haɗa ido da shi.

     Cikin sauri na janye nawa na fice daga motar. A.c'n da ya sanyaya jikinmu ya sa ina fita na ji wani zafi ya daki fuskata.  Yana gaba muna bin shi a baya har Consultancy, inda Ofishin wani likitan da ya taɓa duba ni lokacin da na some a ofis.


      Jira muka yi sai da ya shiga mintuna a tsakani ya fito, sannan ya yafito Ni na bi shi baya.




Post a Comment

0 Comments