TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Da Na Kowa neh page 80-85

 

              *BY BEBEELO*




~SADAUKARWA~ <GA> *UMMI A'SHA**😘*

[22/12 7:39 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿

*D'A NA KOWA NE*

            🌿🌿


      *©BEBEELO*


                 *80~85*

                  ********


~ Tana komawa ciki, ta rubuta yan abubuwanda take bukata ba wani masu yawa ba, ta mikawa Mukh ya kai mashi, lokacin iya sukuwa ya suku yadda ta barshi yana jira.

Sallama yayi da Umma ya fice yana mai nazarin irin zamanda zasuyi shida Ummi.

                    ** ** **

Shagali ya kam kama sosai, gidansu Ummi ba zakace shine ba irin yadda aka gyara ahi,

harda su fenti, yan uwa ancika gidan, da wanda aka gayyata da wanda na baa gayyata ba sunzo dan ganin kwakwaf.

Ma tayi rawar gani sosai har Umar M Shareef ta gayyota domin ya masu waka, tabb je kaga mutane yadda aka taru ranar.

Abinci kala kala da lemu ake fitowa dasu, ga naman kaji dana rago kai harda talotalo.

Ranar daurin aure 12 na rana aka daura auren *Ummi A'isha*da angonta *Barrister Umar*Aurenda ya samu hallattar manyan mutane, daga mutanenmu bakar fata har fararen fatar.

Bayan an dawo daga daurin auren, aka shirya amarya cikin code less arsh color sai head dinta red da net dinda ta rufe jikinta shima red, sarkarta ta gold da sauransu, tayi kyau har ta gaji.

Take kaji ana rangada guda, aka kira amarya da ango dan daukar hoto da yan uwa.

Ma itace ta jawo amarya takaita inda angon yake zaune kan wata kayatacciyar kujera, mai ado.

Yasha dinkin kaftani shaddar fara sol taji kwado red, hula da takalma duka red shima.

Fuskar shi ba yabo ba fallasa, zaunarda Ummi akayi take kaga sun haska gurin kamar wasu taurari,

ga kalan kayan nasu, ita kanta Ummi tayi mamakin haka, tasan bazai wuce aikin Ma ba.

Barr sai satar kallon Ummi yake yadda yaga tayi bala'in kyau, bama zakace wai tayi ko shekara ashirin ba balle talatin.

Hannunta yabi da kallo yadda aka tsantsara mata kunshi, mai dauke da baki da ja,

yayi kyau sosai, a ranshi ya fadi haka amma baisan hakan ya fito fili ba, saida tadan saci kallon shi,

ta sake juyawa kai gefe, ba laifi ta fada a ranta,nan mai hoto yace su gyara a dauke su.

Kallon juna sukayi suna dubin to wane gyarawa zasuyi bayan wanan, mai hoton bayarbe ne shi da kanshi yaje kusa dasu ya nuna masu yadda zasuyi.

Kallon juna suka sakeyi, sanan ko wannensu yayi shuru ganin Ma da Umma sun kura masu ido yasa,

Umar yayi karfin halin yanyo ta jikin shi din kamar yadd mai hoton yace suyi.

Aikuwa su duka wani irin shock sukaji, daurewa kawai Barr yayi amma wani irin hali ya shiga haka itama Ummi.

Dariya wayayyun mutanenda ke wurin suka saka inda yan kauyen suka fara suruce suracen babu kunya.

Bayan an gama d'aukarsu su kadai,Mukh ya arto ya fada jikin su ya hade fuskokinsu guri daya har suna juyo nunfashin juna, take k'wak'walwar Barr ta fara dif.dif.

Sumba Mukh ya kaiwa Ummi a kunce, tana dariya aka dauki hoton sunyi masifar kyau kamar su suka haifi yaron.

Bayan an gama Umma tayiwa yarta nasiha mai ratsa zuciya da kukanta shabe shabe,

nan aka wuce da ita dakinta, babu rakiyar ko mutum d'aya dama Ummi batada kawa, sadai taje can zan hadata kwance da Chuchu, ga Meena dan Musa, gasu Benazir, tabb inaga na hadata da Ummu samha, waiiwaihh na manta da Jabo, shawara kuwa sai na hadata da anty Ybk.😘


                      ** ** **

Ankai Ummi dakinta lafiya, a nan Abuja, bayan Ma da mutanenta su, watse ne, Barr Ahmad suna tafe a mota shida Barr Umar, sai surutu Barr Ahmad keyi,

amma Barr ya k'yaleshi.

Dariya Barr Ahmad yayi yace"wanan shan kamshin na meye kuma?

D'an murmusawa Barr yayi yace"bansan meyasa Ma ta auramin wanan bagidajiyar ba wlhy.

A fusace Barr Ahmad ya kalle shi yace"komai dai mecece ita yanzu ta zama matarka,

kuma wlhy ka daina irin haka ba kyau.

Shima a fusace ya kalli Barr Ahmad yace"idan na fada sai ka mutu, nifa bana sonta,

wlhy sanan kaima kasan ba ajina ba ce, nafison karamar yarinya wacce zamu more yarantarmu,

amma wanan me ma zan sama a jikinta, tunda budurcin ma ya zube a hanya mstwwww ya fada,

dai dai sun shigo gidan ya fito.

kallo kawai Barr Ahmad ke binshi dashi, tabbas yasan wani gefen abokin shi nada gaskiya,

cox Ummi sa'arshi ce, irin yadda sukeji kuwa ance idan mace ta jima batayi aure ba,

budurcinta tafiya ya ke😳

da haka shima ya shiga gidan, falo ya sami she ya zube, murmushi yayi yace"ka tashi na kaika har dakin matarka.

Tsuki yaja yace"ban tashi ba ka tafi kawai, badai ka kawoni gida ba?

"saifa ka tashi, ganin ya takura shi yasa ya mike ya shige room din shi yabar Barr Ahmad nan,

shima fusata yayi yabar gidan.Yana shiga yayi wanka ya saka kayan baccin shi,ya zube kan gadon,

yana tunanin irin rayuwarda zasuyi shida Ummi, da haka har bacci yayi gaba da shi.

                        ** ** **

Ummi bata kwanta ba, saida tayi wankanta tayiwa Mukh ta shirya su cikin kayan bacci suna kamshi, ta cika karamin galss cup da fresh milk ta bawa Mukh yasha itama ta cika tasha, sanan ta kashe masu wuta taja masu balnket take bacci ya kwashe su dama sun gaji.


      *Washe gari*

Tunda asuba tayi sallah, ta sake komawa bacci, Mukh kam tashi yayi yana buga game din shi,

Daurewa Barr yayi ya shigo dakin acewar shi saboda Mukh ya shigo,Mukh na ganin shi ya sheka,

ya rungume shi, shima yana shafar kanshi yace"My Mkukh ka tashi lafiy.......bai idar ba sanadiyar abinda ya hango.

Ummi ce tayi dai dai kan gado, da yar karamar rigan baccinta pink, mai shara shara hatta pant din ciki kana hangowa,

gashi zaninda ta dora yayi gefe akan nauyin bacci, wani yawu Barr Umar ya hadiye, kamin ya saita kanshi.

Da saurin shi ya nufi gurin ya d'auki filo yana dukanta dashi, yana fad'a, ke boyar Allah, ai sai ki tashi haka an samu gado mai taushi ko?

haka ya dinga kiranta, a hankali ta bude idonta, ta mike tana mika tareda salati, aikuwa da sauri Barr yabar d'akin,

saboda ashe botirin rigar ya balle, gashi ta buga uban mika,na fulaninta a fili, gasu tsaye cak, tsuki taja ta mike ta shige ban d'aki.

Barr kuwa har wani duhu yake gani kamin ya isa falo ya zube, tabbb meke shirin faruwa dashi? abinda yake tambayr kanshi kenan.

ohh boy Brr na luv ohhhh😉




               ** ** **

Ina farin ciki masoyana, akan irin yadda kuka nuna damuwarku,akan ciwonda nayi.

Nagode maku kuma Addu'arku a gareni ta karbu, cox naji sauki sosai. Allah ya sakamaku da khairan Allah kuma ya barmu tare

*Bebeelonku*😘




Post a Comment

0 Comments