TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 47-86

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Gaisuwa tare dafatar alkhairin Allah da rahamarsa sulullub'e rayuwarki data gidan auren ki my dear sister in-low *MARYAM HAMZA* (Mr's Manir katuka), bakina bazai iya fad'ar farincikin dana tsinci kaina acikiba lokacin danayi karo da dad'ad'an kalamanki dkuma shawarwari agareni, hak'ik'a inajin dad'in yanda kike bibiyar wannan littafi daki daki, fatana Allah yatabbatar da soyayyarki azuciyar yayana tahar abada kuma ya albarkaci 'ya'yanah yasa suzamo abun alfahari agaremu duniya da lahira,  LUV U SO MUCH MY IN-LOW🥰❤_


💎Page_____47💎



    Suna fita hajia kaka ta kalli papi tace 


"Bai kamata ka tirsasa yaron nan ba tunda har akwai wacce yakeso aransa, katuna bamuda wani cikakken Iko akansa kasancewarsa jikane nawajen 'ya mace inda ace mahaifinsa muka haifa to zamu iyayi masa tilas, yanzu idan kuma shi mahaifin nasa ya nuna rashin amincewarsa yazamuyi?" Cikin basarwa papi dake rik'e da 'yar sandarsa yana k'ok'arin mik'ewa yace "karki damu baby nafad'a masa hakanne don natabbatar zaije, idan kuma har baijeba shikenan nasamu amsar da zan dogara da ita wajen bawa aminina hak'uri da fad'a masa cewa yaron yanada wacce yake so, kinga rashin zuwan nasa zai tabbatar masa da haka kuma zai fahimceni"


"To idan kuma yajefa?" Itama tafad'a tare da mik'ewa tabi bayansa, dakatawa yayi da tafiyar daya farayi tare da juyowa yana murmushi


"Shikenan dama hakan nafi buk'ata, sai ahad'a masa duka biyun ya aura" cikin tsokana hajia kaka tak'araso gabansa tana fad'in "idan aka aura masa mata biyu ni kumafa? Ina zai kaini" hannunsa ya d'ora akan kafad'arta ya rungumota ajikinsa yana dariya " sai yabarki wajen mijinki dama can fashine yayimun" da haka suka shiga d'aki abunsu tana addu'ar Allah yazab'awa jikin nata mace mafi inganci daga cikin 'yan matan.


Suna isowa kai tsaye suka wuce part din mom, Basmah na zaune Batool na tsefe mata kai afalo, da sallama suka shigo palourn kan Mahmud pilot na sunkuye ak'asa, Basmah najin muryarsa gabanta yayi wani irin fad'uwa da sauri ta k'wace kanta dake hannun Batool tashige d'akinsu, duk yanda take son ciresa aranta takasa, kullum soyayyar sa ruruwa takeyi acikin zuciyarta, tunowa da kalamansa nad'azu tayi batasan lokacinda hawaye suka zubo mata ba tafara kuka, Batool kuwa saida tagaishesu sannan tabi bayan 'yar uwarta sautin shesh-shekar kukanta da taji yana tashi tun abakin k'ofa yasa tayi saurin K'arasawa wajenta "Yayya Basmah ya da kuka haka?, meyake damunkine? Yanzufa muka gama fira lafiya dake shikenan sai nasameki kina kuka, meyake faruwa da kene?"  tak'arasa maganar had'e da tallafo kanta, 


"Nashiga uku Batool nakasa dena son yaya Mahmud, muryarsa kad'ai idan naji wata irin wutar sonsa kesake ruruwa acikin zuciyata" juyar da kai gefe Batool tayi kafin tace


"To shine me yayya Basmah, kije kifad'a masa, ke 'yar uwar sace kuma natabbata bazai k'ikiba, idan kuma bazaki iya fad'a masa ba nibari inje infad'a masa" kanta ta ajiye akan katifa had'e da mik'ewa tarik'o hannunta da sauri,


"Don Allah kada kiyi haka 'yar uwata, zan k'ara tirsasa zuciyata akan tahak'ura dashi amma bazan iya yafewa zuciyata ba idan tabari kika aikata haka"


"What? Mekike fad'a, so kike kiyiwa kanki illa akan abunda kike da tabbaci akan samunsa, to tukunama don me bazaki fad'a masa ba kuma bazaki bari afad'a masa ba, haba 'yar uwa bazan iya jurar ganinki haka ba" hannunta tarik'o sannan ta d'ora d'ayan hannunta akai tace


"Saboda bani yake soba, yanada nashi zab'in ransa"


"And so what? Ko kin manta shi mijin mace hud'une zai iya had'a zabinsa dake ya aura"


"Bazai yuyuba!, kuma bazai tab'a yuyuwa ba Batool domin zab'insa jininace da Allah ya haramta masa aurenmu mubiyun kuma alokaci d'aya"


"Mekike nufi yayya, kwata kwata kinsani aduhu ban fahimcekiba" kallonta tayi idanuwanta na tsiya yar da hawaye tace


"Ina nufin 'yar uwarmu Billy itace zab'in yaya Mahmud, da kunnena naji yana fad'awa yaya cewa ita yakeso kuma zai iya rasa rayuwarsa akanta, kinga kuwa matuk'ar zai aureta bazai yuyu ya aureni ba, narasa sa kenan har abada" tasake fashewa da wani kukan, mutuwar tsaye Batool tayi tana furta innalillahi wa inna ilaihirraji'un,


"Amma yayya naga ko shiri bayayi da twiny kuma natabbata shi kad'ai ke kid'ansa ita bata sani ba, mezai hana kisanar dashi kafin yafad'a mata"


"Bazan iyaba, idan nayi haka naso kaina da yawa, karki mantafa nasan yana son k'anwata taya zancutar dashi tahanyar hanasa samun burin ransa, shin ni idan aka yimun haka zanji dad'i?" Cikin tausayawa da kalaman dake fita bakin 'yar uwarta tace


"Shikenan ni zanje nasanar da Billy duk halin da akeciki" zabura Basmah tayi had'e da mik'ewa tarufo k'ofar d'akin sannan tadawo gabanta ta durk'usa tare da had'a hannuwanta waje d'aya tace


"Narok'eki Batool ko mom kada kibari tasan da soyayyar da nakeyiwa yaya Mahmud balle Billy, inaso kiyimun alk'awari komai rintsi komai wuya zaki rufemun sirrina hakan kad'ai zaisa nasan kina k'aunata kinji 'yar uwata" ganin yanda take kuka tana rok'onta yasa tayi saurin saukowa akan gefen gadon da take zaune ta rungumeta " shikenan yayya Basmah bazan fad'aba matuk'ar hakan zaisa kiyi farinciki nayi maki alk'awarin zan b'oye sirrinki har iya k'arshen rayuwata, amma pls kidena wannan kukan zai iya haifar maki da matsala kinji ko?"


"Shikenan nadena bazan komaba, kin ganima nashare hawayen?" Basmah tafad'a tana goge hawayen da suka zubo mata a idanuwa.....



_pls kuyi manage, inabaran addu'arku zuwa ga yayata data haihu yau, kuma Allah ya sauketa lafiya tasamu baby girl nasamu takwarata (Bilkisu) amma allah yayi ba rayayya bace takoma😭😭😭😭, kusata cikin adduarku Allah yabata lafiya kuma yabata juriya da hak'urin raahinta,_"😰👏🏻





 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____49💎


 

    A b'angaren yaya Mahmud kuwa kallon mamaki yabi Basmah dashi lokacin daya ga tabar palourn aguje sai kuma yabasar a tunaninsa k'ilan tayi hakan ne saboda bata so ya rik'eta ayanayin da  take ciki, mere baki yayi aransa yana cewa ai anriga angama inji mai kashi gado.


Suna zaunawa saiga mom tafita daga bedroom d'inta zata shiga kitchen, ganinsu yasa tawuce cikin palourn kai tsaye tana murmushi, 


"My son da kuma my son again, yaushe kuka shigo yaran basuzo suka fad'a mani ba" tajuya tana kallon inda tabar su Basmah azaune  suna tsifar kai,


"Ai yanzun nan muka shigo mom, barka da marece anwuni lpy?" Yaya mahmud pilot yafad'a yana sissinne kai k'asa


"Lafiya klw Mahmud ina kabaro junior sarkin rigima da ummanku duk lpy suke"


"Lafiya klw mom, gashican shida su Bassam suna buga Ball aharabar gida" nan shima yaya Mahmud yaga ida mom ta amsa tana fad'in


"My son meyake damunka nagaka ahaka" murmushin yak'e yayi masa kafin yace


"Farinciki da akasinsa mom" alokaci guda yana kallon Mahmud pilot


"To afad'amun farincikin akasinsa kuwa anemi sauk'insa ga Allah" murmushi pilot yayi had'e da cewa "k'yalesa mom duka farincikine saidai inbayaso kijine kawai" harararsa yayi kafin yace "haka kace ko? shikenan Allah yayi maka yanda yayimun"


"Ba amin ba, kaifa..." Mom na dariya tace a'a to ya abun yakene Mahmud kace duka farincikine amma ya rok'amaka kace ba amin ba, afad'amun naji ko meye tak'are maganar tana kallon yaya Mahmud, kamar su had'a baki atare suka mik'owa  mom makullan motar da dady ya siya masu suna fad'in "surprise from our dad, motocine guda biyu ya siya mana yanzu haka suna cikin gidan nan munzo dasu" cike da farincikin dake k'unshe da mamaki tace


"Wow.. masha Allah yaran dady, congrat, gaskiya dady ya iya surprise, irin wannan kyauta haka? to Allah yasa ku kashe da kanku kuma yakarawa dady arzik'i" su duka suka amsa mata da amin, mik'a masu makullan tayi tana fad'in to saura d'ayan farincikin shi kuma ina saurarenku, Allah yasa shi kuma makullan gidajene aka baku" dariya Mahmud pilot yayi sannan yace


"A'a mom ai wannan kyautar tamusammance, d'an uwana kad'ai akayiwa ita" kallonsa yayi sannan yaci gaba da cewa "mom masu zaman gidan aka fara bashi kafin gidan yazo" murmushi mom tayi had'e da dafa kafad'ar yaya Mahmud "my son wannan kake kira akasin farinciki, baka son nima inga 'yan jikokina ne halan" "mommmm" yafad'a tare da rik'o hannuwanta kamar zaiyi kuka, "Ba wannan ne matsalar ba, mata uku fa mom!?"


Tashi Mahmud pilot yayi yana dariya yace "d'an uwa nidai bari naje don nagaji dajin wannan irin raki naka haka, kasameni a part d'in Ummi, mom sai anjima"sannan ya ficewarsa, kallonsa yaya Mahmud yayi batare daya amasa masa ba tare da kallon mom, hannunta tasa a gefen fuskarsa had'e da cewa,


"Kamarya mata uku my son, da wasa kakeyi ko kuma mafarki"


"Taya zanyi wasa da mahaifiyata ga abun da nasan itama zan iya sakata cikin damuwa, da gaske nakeyi mom, inada wacce nakeso arayuwata kuma nayi mata alk'awarin zan aureta, sai ga dady kuma yasanar dani cewa sun yanke shawarar had'ani aure da 'yar gidan amininsa alhaji usman, ina cikin jimamin maganar dady kuma sai ga papi ya kirawoni wai shima yasamar mun mata 'yar wajen abokinsa, mom taya zan iya rik'e mata uku acikin wud'annan shekaru nawa" ya k'arasa maganar kamar zaiyi kuka, shiru mom tayi tana nazarin maganganun yaronta kafin tace


"Ka kwantar da hankalinka babu wanda zai aura maka har mata uku alokaci d'aya dole ko hakan zai faru ya zamana a maban banta lokutan, kai dai abunda nakeso dakai kamar yanda papi ya umurceka katafi wajen wacce ya zab'o maka to katafi, shi kuma dadynka kajira amsar da zidawo maka da ita, ya sunan ita yarinyar da kake sone?"


"Faraaha"


"To kaje nidai babu abunda zan iya yi acikin wannan alamarin banda shawarar dana baka" duk da yaya Mahmud nacikin damuwa saida yayi mamakin mahaifiyarsa domin ko kad'an banyi tsammanin zata amshi wannan magana da sauk'i haka ba, tabbas d'an Adam d'an tara ne, duk yanda kake kallonsa da hawaye marasa kyau to akwai lokutan da idan annatsu za'aga yana da wasu kyawawan halaye daban, yau ga mom d'insa tana magana irin yanda Ummi keyi cike da fahimta da kuma natsuwa, tabbas soyayyar uwa awurin d'anta daban take, murmushi ya sakar mata tare da rungumeta "mom nagode da shawararki, kuma nasamu natsuwa sosai fiye da lokacin dana shigo, in sha Allah zanyi kamar yanda kikace, ubangiji Allah ya zab'a mana mafi k'ololuwar alkhairin sa"


"Amin my son" bari naje na d'ora abunda za'aci naji har ankira sallar magrib, bai bar part d'in mom d'in saba saida yayo arwala yana fitowa ya wuce masallaci kai tsaye yanajin wata 'yar k'aramar natsuwa na ziyartar zuciyarsa.


Izuwa yanzu zuciyar Batool tagama yarda da soyayyar Dr Ahmad d'ari bisa d'ari domin duk bayan mintota sai kalamansa sun dawomata ga kunne, lokaci guda kuma idan ta tuno da kyakkyawar fuskarsa da zati dayake dashi saita tsinci kanta cikin murmushin da batasan lokacin dayake fitowa ba, idan kuma tatuno da yanda yaraza lokacin data sakar masa ihu har ya k'wale kansa saitayita dariya, yama zaune take tana tunaninsa tana dariya saiga Billy ta iso wajen rik'e da hannun junior, kallo d'aya tayi mata takauda kai had'e da samun wuri can gefe da ita kad'an ta zauna, juyowa Basmah tayi tare tsagaita dariyar da takeyi "twiny ya da haka naga kin wani ja tunga gefe?"


"Ai dole inyi haka kafin kishak'o wuyana, wannan irin dariya haka ko control babu" muryar yayya Basmah sukajiyo abayansu tana fad'in


"Kema kyafad'a sister, d'abi'ar data sameta kenan yanzu kullum cikin tunani da faman dariya take, inajin tsoron inba wata cutarce takamata ba" d'ago kai Billy tayi tana murmushi "Yayya Basmah ina wuni barka da marece"


"Yawwa my sisto ykk!?" Hannun junior tarik'o had'e da cewa


"Junior how far? Give me five" hannunsa yabata suka kashe tare da zaunawa tana kallon Batool


"Kai yayya Basmah wannan irin kallo haka, twiny matso kusa nabaku labarin abunda kesakani dariya" tasowa Billy tayi ta dawo gefen Basmah tare da aza kanta akafad'arta "yawwa to muna saurarenki 'yar gidan mom koba hakaba yayya" murmushi kad'ai ta iya yimata batare data amsa ba tana wasa da hannuwan junior. Cikin shauk'i Batool take kallon k'afar data jimu tana murmushi sannan tace


"Kuna tuna ranar da aka kaini asibiti gyaran k'afata, zaku iya tunawa da labarin dana baku akan abun da yafaru tsakanina da dr. n?"


"Eh.eh.sai akayi me?" Billy tafad'a cike da zak'uwar son jin abunda zata fad'a masu, murmushi Batool tasakeyi sannan taci gaba da cewa "shine ranar yakira yaya mahmud da lambar aunty faraaha aka bani shine yace wai soma yake" murmushi Basmah tayi don dama tasan anan labarin zaya dire, ita kuwa Billy kwaro idanuwa waje tayi tace "and ke kuma sai kikace me?" Had'e da dawowa gefenta tana dariya


"Ban bashi amsaba, amma dai nima na fola" dariya suka saka gaba d'ayansu hadda Basmah


"Shikenan yaya Mahmud yasamu 'yar uwar folawa ko yayya Basmah?" Billy tafad'a had'e da mik'a mata hannu suka tafe,


"Kwarai kuwa sisto, yaya Mahmud ya fola, Batool ta fola, yaya Mahmud pilot ma ya fola" tsalle Billy tayi cike da jin dad'i tana fad'in "dagaske yayya Basmah? kice so soon zamusha buki, sauran kema ki fola duka muhad'a mukaiku d'akunanku muhutawarmu ko junior?"  Tafad'a tana jamasa kumatu, duk abunda kefaruwa Mahmud pilot yana tsaye jikin tagar d'akin yaya Mahmud yana kallonsu amma baya jin abunda suke fad'a,wani farinciki ne ya mamaye masa zuciya ganin yanda Billynsa ke cikin jin dad'i da walwala, baisan lokacin daya shafo sumar kansaba tare da sakin wani k'ayataccen murmushin daya bayyanar masa da gaba d'a hak'oransa, ahankali yafurta "I luv u so much Billy nah!" Aransa kuma yatabbatar wa kansa da cewa komai zaifaru yau sai ya gabatar da soyayyarsa agareta, Billy kuwa bata fahimci komai ba cikin maganganun da Basmah tayi ba kuma itama ta fahimci hakan, 


d'ago kai Basmah tayi daniyar yin wata magana ta hangosa a tsaye aji tagar d'akinsu hangosa a tsaye daidai lokacin da yake shafa kansa yana murmushi, kallon Billy da batasan abunda kefaruba tayi tasake maida kallonta agaresa ta tabbatar ita yake kallo,  wasu zafafan hawayene suka zubo mata agefen ido tayi saurin gogewa, "junior taso muje mu gaida su Ummi duk yau sau d'aya naje gunsu" tafad'a tana k'ok'arin danne damuwarta. "Bye sisters sai kun shiga"


"Ok yayya gamunan zuwa" nan tabarsu tawuce part d'in Ummi, tana shiga yaya Mahmud nafitowa, kallo d'aya yayi mata ya tabbatar tana cikin damuwa, hannunta ya jawo suka rab'e gefen d'aki ya d'ago kai yana kallonta sannan yace


"Basmah kirage sa damuwa aranki, kisa azuciyarki duk abunda zai zamo naka Allah yariga daya rubutashi acikin k'undin littafinka kuma komai rintsi komai wuya sai yazamo mallakinka kinji ko?" 


"Eh yaya" tafad'a atak'aice don idan tace zatayi wata doguwar magana to tabbas kuka zaici k'arfinta kuma bata buk'atar haka ayanzu, wucewa yayi itama ta k'arasa shiga palourn Ummi, tare ta taddasu ita da Umma zaune suna firar kyawon motocin da dady ya basu tare da Allah yasanya alkhairi kuma yak'aro bud'i, gaishesu tayi cikin natsuwa sannan tanufi d'akin Billy, Bayan sun amsa Umma tayi mata nuni da tazo ta zauna a inda suke, wani irin nauyi tajiya don bata sama zama cikin manya ba idan suna zaune, cike dajin kunya tak'araso wajen Umma tarik'o hannunta tana fad'in


"Oh ni hafsatu wai 'yatah ina zakije da wannan kunyar, kisaki jikinki nima mahaifiyar kice kinjiko? Haka zani kaiki d'a kinki kina b'oyon fuska Basmah" 


"kinga kibarta haka ake son 'ya mace takasance da kunya ko agidan mijinta domin adoce ga duk 'ya macen da tasan kanta" ummi tafad'a tana kallon fuskarta cike da alamar tambaya don taga Basmah d'in ta canja cikin kwana biyu hadda d'an fad'awa tayi. "Basmah meke damunkine?


Shiru tayi kafin tace


"Babu komai Ummi"


"Anya Basmah?"


"Allah kuwa babu komai" shikenan Allah yasa haka d'inne. Basmah bata jima da barin wajen ba itama Batool tanufi part d'insu rik'e da ciki tana cewa Billy


"Twiny my stomach ina zuwa?" Ita dai Billy zaunenta tayi saboda bata son bin Batool mom tab'ato mata rai, haka kuma ganin Ummi da Umma a falo zaune suna fira yasa takasa walwala a part din nasu, shiru tayi tana faman karanta wasik'ar jaki kawai taji an rik'o hannunta, d'aga kai tayi da niyar magana amma yakasa bata damar yin hakan, jan hannunta da yayi yasata mik'ewa tabishi bud'e da baki tana binsa da kallo, can gefe bayan part d'in dady daba kowa ke iya ganin suba ya nufa da ita, dama tuntuni wannan damarce da zaiganta ita kad'ai yake jira shiyasa yana samu bai tsaya wata wata ba yanufi wajenta, suna isa yasaki hannunta sannan yayi folding hannuwansa akan k'irjinsa yakafeta da idanuwa yana kallon fuskarta data matse alamun b'acin rai, k'asa tayi da kanta tanajin haushin rik'o hannunta da yayi don ita tunda take babu wanda yatab'a rik'e hannunta inba yayan taba, jin yayi shiru baice komai ba yasa tajuya zatabar wajen, da sauri yasha gabanta cikin wata iriyar kasalalliyar murya yace


"Ina kuma zakije?" Tsayawa tayi batare data amsa masa ba, amma zuciyarta nabuga mata da sauri da sauri saboda tsananin b'acin rai, jitake yau daba d'an uwanta bane yaya Mahmud data shayar dashi mamaki, ahankali yafara magana cikin taushin muryar da bazaka tab'a cewa yaya Mahmud pilot bane...







*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____50💎



Bilkisu! Shiru tayi batare data amsa masa, "Bilkisu" yasake fad'a yana mai kallon fuskarta dake kallon k'asa, d'ago kai tayi rai ab'ace ba tare da tace masa komai itama tana kallonsa.


"Wai meye na wannan ciccije fuska da kikeyi?, nidai nasan ba kalar tarbiyar da Ummi da daddy suka baki kenan ba ta wulak'anta d'an adam, d'an adam d'in ma kuma d'an uwanki" wasu yawu tahad'iye cike da takaici kafin itama tamayar masa amsa da


"Nima natabbata kaima ba irin tarbiyar dasu Umma suka baka kenan ba!, taya za'ayi ka kai hannunka katab'ani bayan kasan cewa yin hakan kuskurene kuma haramun bai halatta ba a addininmu" yanda take maganar ne ya tabbatar masa da cewa ranta ab'ace yake saboda rik'o hannunta da yayi hakan yasa ya rik'e kunnuwansa yana fad'in 



"kiyi hak'uri tabbas nayi kuskure kuma hakan bazai sake faruwa ba" had'e da kallon idanuwanta, tajima batace komai ba kafin nan ta amsa masa da "Shikenan, ammafa ka kula yaya baniba da nake 'yar uwarka ko wace irin mace yin hakan agareta laifine kuma zunubine matuk'ar ba muharramar kabace" murmushi yayi had'e da cewa "insha Allah malama Billy, amma zanso inyi maki wata tambaya idan kin bani dama" nisawa tayi sannan tace to mukoma a guarding yaya don wlh bazan iya jurewa tsayuwa anan ba"  bai so hakanba saboda wani dalili amma dole yabita suka koma can don bayada zab'in daya wuce yimata biyayya, zaunawa sukayi akan d'aya daga cikin kujerun dake wurin sannan tace


"Ina sauraren ka yaya Mahmud, Allah yasa nasani"


"Meyasa kwana biyu kika dinga wasan b'uya tsakaninmu?, meyasa kika canza ga yanda muke dake ada?, meyasa kika yanke shak'uwar dake tsakanina dake?, me yasa kikasa shamaki acikin kulawar da mukeba juna ada?" Dariya tayi had'e da cewa


"Tabd'i jam yaya! Wai duk kana nufin wud'annan tambayoyin dake kama da laifuka ni zan amsa su?"


"Sosai kuwa, tunda gashi da kanki kin fahimci cewa laifukane, kinga kuwa yazama dole ki amsa saboda ban san meyasa zaki aikata hakan gareni acikin lokaci d'ayaba"


"Saboda tsangwama, mugunta da kuma takurawar da katsiri yimani a wannan karon, shiyasa naga yadace inyi nesa dakai don kauce masu" tafad'a kai tsaye batare da shayi ko wani tsoro arantaba, hakan datayi yasa yaji yak'ara k'aunarta, d'ago kai yayi yana kallonta cikin wani irin so da k'auna yace


"Amma yakamata ace kin fahimceni dalilina nayin hakan, duk wannan abun da nakeyi ina yinsane saboda so da k'aunar da nake yimaki" 'yan k'ananan idanuwanta ta fiddo waje tana fad'in "kai yaya! Wane irin so da k'auna zasusa ka dinga yiwa k'anwarka haka? Gaskiya akwai alamar tambaya a wannan maganar taka?"


"Ofcourse Bilkisu, wannan tambayar ce nakeso nabaki amsarta tun kafin kitambaya, Bilkisu tun kina 'yar k'ank'anuwarki ni kuma ban mallaki hankalina ba nake jin sonki araina kema sheda ce akan hakan don zakiji Umma nafad'i banida zancen dayafi naki agida kuma idan mukazo babu wacce nake kulawa sama dake acikin gidan nan duk dako kasancewar kinada 'yan uwa bake kad'ai kike ba, gaba d'aya zuciyata tagama amincewa da ki zamo mallakina kuma uwar 'ya'yana, haka kuma gangar jikina da ruhina keta zab'amun amatsayin abokiyar rayuwata, dukkanin wani tanadi da buri nawa aduniya inayinsane wake kad'ai, kiyarda dani don Allah Bilkisu hakan ne tabbacin wanzuwar farincikina nahar abada, natabbata ubangijina ya halicceni ne da sonki daga cikin jinin 'yan uwantakar dake tsakanina dake kinkoga babu yanda za'ayi sonki ya iya ficewa cikin zuciyata sai inhar jininki dake yawo acikin jinina da kuma jikina zai iya fita, ki amince dani zan d'aukaka darajarki acikin 'yan uwanki mata kuma zantabbatar dacewa duk inda kika shiga sai an hango tsantsar soyayya da kulawar da nake baki atare dake, Bilkisu inayi maki so mai tsanani tunkafin insan koni waye, yanzu kuma dana sani inajin soyayyarki na shiga sau dubu acikin kowane lumfashi d'aya na rayuwata da zanyi aduniya" tunda yafara magana take kallonsa cike da mamakin wai anya wicked yaya d'in nanne nata kuwa?, anya yaya mahmud d'in data sanine kefitar da wud'annan kalamai masu tsananin nauyi agareta batare da gittawar kowane irin shamaki atsakanin suba kodai mafarki takeyi? Lumshe idanuwanta tayi had'e da bud'esu akan nasa tana kallonsa "Yes Bilkisu! I mean all dis for u, ba mafarki kikeyi ba, dagaske ne ina sonki sosai kuma bazan tab'a iya rayuwa ba idan babu ke, bazan tab'a komawa cikakken mutum ba face har sai wannan awazar da aka cira daga jikina tadawo mazauninta, kuma natabbata kece wannan awazar aka halitta mani amatsayin mata wacce kasancewar ta atare dani zai tabbatar da zamowata cikakken mutum rayayye, jarumta da kuma kamalata bazasu cikaba har sai kin yarje mani nazamo zaka ran gwajin dabin da zai iyayin yak'i acikin zuciyarki, wlh Bilkisu matuk'ar kika barni zansha wuya koma inrasa rayuwata gaba d'aya, ban tab'a son wata mace azuciyata ba inba ummanah ba kuma inada yak'ini akan kece tak'arshe insha Allah" speechless tazama don gaba d'aya ya d'ad'd'aureta da kalamansa, babu wata k'ofa da bai k'onk'osaba acikin zuciyarta kuma tabbas idan taci gaba da saurarensa gaba d'ayansu bud'ewa zasuyi, mik'ewa tayi da zimmar barin wajen kafin yayi galaba akanta yayi saurin zube gwuiwowinsa agabanta kamar zaiyi kuka,


"Kar kiyimun haka Bilkisu, kar kisa raina k'una da kuma cikin tunani don Allah kicemun wani abu kada kitafi kibarni da ciwo cikin raina"


"Meye haka kakeyi yaya? Shin baka gudun wani yazo ya ganka ahaka, don Allah karufan asiri katashi"


"Bilkisu, bazan tab'a tashi anan gurinba har sai kinsanar dani makomar soyayyata, bazan damu da duk wanda zai riskeni a hakaba koda kuwa Iyayen mune don Allah kikarb'i tayin soyayyata Bilkisu kada in rasa raina" lokaci d'aya taji wani irin tausayinsa ya mamaye mata zuciya, har ga Allah idan tace bata son yaya Mahmud tayi k'arya domin itama tun tana k'arama take dakon soyayyarsa saboda irin kulawar da yake bata, amma kuma wane irin tabbaci take dashi akan maganganun daya fad'a balle tayi saurin nuna masa tata soyayyar ba har sai tagwadashi ta tabbatar da shima yana sonta, kallonsa tayi tace


"Bazan b'oye makaba yaya Mahmud, nima gaskiya akwai wanda zuciyata keso tun ina k'an k'anuwa kuma shima yana sona, don haka kayi hak'uri muci gaba da zumuncinmu yanda muka saba" wani irin juyawa yaji kansa yayi hawaye suka zubo masa a idanuwa,


"Taya hakan zata faru bacin koda yaushe ina saka idanuwa akanki kuma natabbata babu wani dayake zuwa wajenki, kada kiyi wasa da rayuwata Billy don yanzu haka zuciyata gab take da bugawa" d'aure fuska tayi had'e da cewa


"Koma meye dai nafad'a maka, kawai kayi hak'uri ni inada wanda nake so"  da sauri tabar wajen ganin yanda hawaye kezubar masa gudun kada yayi nasarar karya mata zuciya,


Tana kaiwa bakin k'ofar shiga part d'insu taci karo da Basmah dake tsaye tund'azu da tazo fitowa tahango yanda wanda takeso ke durk'ushe agaban k'aunarta yana baran soyayya, hakan yasa takoma da baya tayi tsaye saboda bazata iya komawa cikiba tasha kukanta sosai, tana niyar fitowa wajenne sukaci karo da Billy. Murmushi tayi mata had'e da kauda fuskarta saboda kada taga halin da take ciki, "yayya Basmah su Ummi na palour"  tafad'a had'e da waigawa tana kallon inda yake duk'e har lokacin bai tashiba"


"A'a sun shiga kitchen" ta amsa mata atak'aice tare da barin wajen tana sharar k'walla.


Kwance take tana waya da all i have d'inta taji muryar jaddi na k'walo mata kira, "faraaha, faraaha.. Wai kina inane nake faman kiranki kikayimun shiru" yafad'a yana turo k'ofar d'akinta, da sauri ta b'oye wayar tana fik'ifik'i da idanuwa, jin anyi shiru yasa shi kuma tab'an garen sa yafara kiran


"Hello, hello" danne wayar tayi sosai har saida ta mutu gaba d'aya tare da mik'ewa zaune tana kallon jaddi dake k'ok'arin zaunawa agefen katifar "malamar asibiti, me kikeyi haka da kika kasa amsa kirana"


"Bakomai jaddi ina d'an duba wani abune to banjiba saida kishigo" zamansa ya gyara daidai yana kallonta yace


"Faraaha, ina ranar nace dake ina son yin magana dake idan kindawo wajen aiki amma shine da kika dawo baki tuntub'eni ba, gashi har yau anyi kwanaki da yin maganar" dafe goshi tayi da tafin hannunta had'e da cewa


"Yaa salam, wlh na shafa'a gaba d'aya, kwatakwata namanta da wannan maganar, kayi hak'uri jaddi banyi hakan da ganganba kodon in b'ata rankaba, amma yanzu gani gaka, kafad'i duk maganar da kake son fad'a mani ina saurarenka mijina" shafa kanta yayi yanajin tausayin jikanyar tasa data taso cikin hali na maraicin uwa da uba, ahankali yabud'e baki yana fad'in


"Kimanta da wannan tsohon mijin naki dake gab da shigewa kuahewarsa kiyi tunanin samun wani mijin mai nagarta da kuma kamala wanda zaiyi maki soyayya fiye da wacce nayi maki, yabaki kulawa fiye da wacce nabaki kinji jikata" rik'o hannunsa tayi tana d'an murzawa ahankali tace


"Jaddi baza'a tab'a samun wannan mutum ba aduniya domin kaine uwa da ubana, kamaye gurbin duhuna da haske alokacin da narasa mahaifana, kabani kulawar da tahanani zubar da hawaye taya kake tunanin akwai wanda zaifika awurina, don Allah kadena fad'ar haka jaddi karkasa nakasa yafewa kaina" murmushi jaddi yayi sannan yace


"Idan kina tunanin baza'a samuba to kibani dama ingabatar maki da zab'in danayo maki natabbata zaki fahimci akwai wanda zai yimaki wud'annan abubuwan daidai da yanda nayi maki koma fiye da hakan"


"Jaddi ni bana buk'atar hakan domin inada wanda nake tunanin zai kwatanta bani irin kular da kabani koda d'aya bisa goma ne" sosai yaji badad'i aransa amma sai yace


"Faraaha nariga nayi magana da aminina akan d'an wurinsa zaizo kuga juna, amma tunda bakya buk'atar hakan mezai hana ki amince yazo ku gaisa kinga daga nan zansan abunda zanfad'awa aminin nawa"


"Jaddi kayimun uzuri amma da zaku dakatar da zuwansa zanfi jin dad'i"


"Yin hakan tamkar watsawa aminina k'asa a idanuwane bayan nina buk'aci hakan amma tunda bakya buk'ata shikenan zance masa ya dakatar dashi har sai naje munyi magana" hakan datayi kuma sai taji badad'i aranta, aranta kuma jitake tamkar tacutar da masoyinta idan takeb'anta dawani amatsayin wai yana sonta, kuka tafashe dashi tare da fad'awa jikin jaddi dake k'ok'arin mik'ewa jikinsa duk ba k'wari tace


"Kayi hak'uri jaddi ina son mahmud sosai kuma nayi masa alk'awarin zan auresa amma idan kana buk'atar in saurari zab'in ka zanyi hakan don faranta maka......







 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____51💎



      Karki damu, nafahimceki, zanje inyiwa alhaji bayani, kiyi shiru bana son kukanki kinji ko?


"Don Allah jaddi kayafemun idan nab'ata maka rai, na amince da zab'inka agareni koda hakan na nufin zanrabu da nawa zab'in har abada" d'ago kanta yayi daga jikinsa yace


"Had'uwarki dashi bayana nufin zaki auresa bane har sai inkun daidaita tsakaninku, saboda haka ki kwantar da hankalinki ni farincikin ki nake so, matuk'ar nagartar wanda kikeso takai ina tabbatar maki da bazaki rasashiba da yardar Allah" hakan daya fad'a sai yakwantar mata da hankali sosai tarungumesa tare dasa hannuwa tana goge hawayen dake kwance akan fuskarta, "nagode jaddi, Allah ya tsawaita mani rayuwarka, ina matuk'ar sonka sosai"


"Nima ina sonki jikata Allah yajik'an mahaifanki ya gafarta masu"


"Amin" ta amsa masa dashi tana k'ara kwantar da kanta ajikinsa.


A b'angaren Mahmud kuwa sau kusan goma yana sake kiran numberta but switch up sai yayi tunanin matsalar chajine don haka ya tashi ya fad'a toilet, wanka yayi ya d'auro arwalar bacci ya koma kan gado ya kwanta zuciyarsa cike da kewar abun k'aunarsa har bacci ya d'aukesa, can cikin dare misalin k'arfe uku da kwata nishin d'an uwansa ya farkar dashi, zazzab'ine sosai ajikinsa sai rawar sanyi yakeyi ga jikinsa yayi zafi sosai, cikin hanzari yaya Mahmud yatashi zaune yana dafa goshinsa,


"'Dan uwa meyake damunka bakada lpy ne?"   Tsananin yanda zazzabin yayi masa zafi yasa yakasa amsa masa, rik'o hannunsa yai yanaso yayi masa magana amma yakasa sai hawaye ke gangarowa daga cikin idanuwansa, ganin rawar sanyin da yakeyi tayi yawa yasa yaya Mahmud ya yaye bargon dake lullub'e ajikinsa yak'ara rufa masa ajiki, sauka kan gadon yayi yabud'e wardrobe d'in kayansa yaciro first aid box aciki, yamutsa box d'in ya shigayi yaciro pcm (paracetamol) cikin magungunan dake zube aciki sannan ya maida first aid d'in, fridge ya bud'e ya d'auka gorar ruwa marar sanyi sosai yadawo gefen gadon wajen kansa ya zauna ya kwand'aro maganin ahannunsa. Tallafo kansa yayi har lokacin jikinsa na rawar sanyi ya tura masa maganin abak'i, k'in karb'a yai yazame kansa zai koma ya kwanta yaya Mahmud yace


"Haba d'an uwa kadaure kayi taken pcm d'innan before asuba tunda yana treating fever, jikinka yayi zafi sosai da alama itace takamaka" bai jira cewarsa ba ya sake d'ago kansa saida yayi dagaske sannan yasamu ya tura masa maganin cikin baki saboda yanda hak'oransa ke bugun junansu, da sauri ya d'auko ruwan gorar yabud'e batare daya tsaya zubawa a cup ba ya d'ora masa bakin gorar, saida yaga yasha ruwan sosai sannan ya d'auke gorar abakinsa, maishesa yayi kwance tare da hanasa bargon zuwa wuyansa sannan yakoma inda yake kwance, kasa komawa baccin yayi saboda yanayin da yaga d'an uwan nasa keciki, hakan yasa ya d'auro arwala yafara nafilfili kafin asuba tayi,


Ab'angaren Billy ma hakance tafaru don kalaman Mahmud sun hanata bacci sai juye juye takeyi, duk yanda taso kauda tunanin agabanta saboda tasamu baccin ya d'auke ta hakan yacutara, tausayinsane ya kamata tuna yanayin data barshi d'azu aciki, ahankali ta shiga kunna bedside lamp d'in dake gefenta tana kashewa "Am so sorry yaya mahmud nima ina matuk'ar sonka fiye da tunaninka amma bazai yuyu in bayyana hakan agareka ba har sai natabbatar da k'arfin soyayyar da kake yimun, a wannan lokacinne zannuna maka irin girma da darajar da soyayyarka take dashi acikin zuciyata, kuma awannan lokacinne zan nuna maka so fiye da yanda kake tsammani" ganin baccin baida niyar d'aukarta yasa tamik'e had'e da shiga toilet ta d'auro arwala, salloli tafara tare da addu'ar Allah yazab'a masu alkhairi acikin soyayyar da suke yiwa junansu, tana a haka aka kira sallar asuba, saida tayi sallah had'e dayin azkar sannan takoma tad'an kwanta kafin hasken safiya yafito.



Yaya Mahmud kuwa ana gama sallar asuba ya taimakawa Mahmud pilot shima yayi sallah dayake balaifi jikin nasa yad'an saki duk da shi kad'ai yasan pain d'in da zuciyarsa keyi, komawa yayi zai kwanta yace


"'Dan uwa tashi ka canza kaya muje asibiti"


"Noo..thank you broth amma bana buk'atar asibiti tunda nasamu sauk'i"


"Are you serious?" Ya tambayesa yana kallon yanda yad'an fad'a kad'an saboda gaba d'aya jiya bai samu yin bacci ba.


"Ofcourse Alhmdllh nasamu sauk'i" jin hakan yasa yaya Mahmud ya shaye kan gado saboda baccin da yakeji a idanuwansa yana fad'in 


"Allah yak'ara sauk'i" ya kwanta abunsa tare dajan bargon dake gefensa ya lullub'e


Kallonsa yayi yana mamakin yanda yasamu soyayyar sa cikin sauk'i abun nurse d'insa amma shikuma bugun farko soyayyar wacce yake k'auna nashirin hallaka rayuwarsa" Runtse idanuwansa yayi yafara tunano kalaman da Billynsa tafurta masa nan take yaji wani irin abu nataso masa azuciya, da sauri yabud'e idanuwansa yana fad'in "no...." da k'arfi wanda saida yasa yaya Mahmud da bacci yafara d'aukar sa ya zabura, kallonsa yayi yace


"Anya lafiya kake d'an uwa? Kodai intaso muje asibitin" yana k'ok'arin saukowa daga kan gadon, hannu ya d'aga masa yana dakatar dashi,


"A'a d'an uwa koma abunka ka kwanta, babu wata matsala in sha Allah, dole yaya Mahmud yahak'ura amma kasa komawa baccin yayi yadawo inda yake ya zauna yana tambayarsa abunda kedamunsa, babu yanda baiyi dashiba amma yak'i fad'amasa saboda bayason yaga yagaza wajen nemo soyayyarsa da kansa, haka yagaji da tambayarsa ya k'yalesa yana furta Allah yasawak'e, yana zaunene yaji kiran faraaharsa a waya yashigo domin kobai dubaba yasan kalar ringing d'in daya samata daban dana saura, tashi yayi yaje ya d'auko wayar tare da zaunawa gefen gadon yace


"Hello golden heart! Kintashi lafiya"


"Lafiya klw all i have" tafad'a cikin sanyin muryar da zata tabbatar maka da yanayin damuwar dake tattare da ita, tsaye yamik'e cikin tashin hankali yace


"My faraah! Meyake damunki naji muryarki haka, fad'amun meke faruwa dakene my golden heart"


"Pls ka kwantar da hankalinka babu komai, kawai ina son ganin kane, natashi da wata irin matsananciyar k'aunarka da kuma kewarka sosai" ajiyar zuciya ya sauke wacce har tanajiyo fitar askanta akunnuwanta, ahankali ya furta mata


"Alhamdulillah Allah nagode maka daka tayar da masoyiyata cikin aminci da kwanciyar hankali, karki samu matsala indai wannanne nesa takusa zuwa kusa domin very soon zanturo iyayena sunemamun aurenki agun jaddi, kinga daga lokacin no more missing me kuma kullum muna tare da juna nahar abada" jin kalamansa yasa damuwar da take k'ok'arin b'oye masa ta haifar mata da fashemasa da kuka" tana cewa 


"Kayafemun all i have, zan bawa wani damar zuwa ya ganeni da sunan maganar aure tsakaninmu bisa ra'ayi da kuma umurnin jaddi, bazan iya yimasa musuba amma natabbatar masa da cewa kaine zab'ina kuma wanda nake burin na aura" tak'arashe maganar tana sheshshekar kuka, wani irin juyi kan Mahmud ya fara yimasa da sauri yakoma ya koma bakin gadon ya zauna ya dafe kansa da hannu d'aya yanaji tamkar zuciyarsa zata b'alle ta fito saboda tsananin kishi, ya kusan minti uku a haka baice komai ba kafin can yace


"Hello kinaji" 


"Eh ina jinka"


"Faraah! Kidena kuka duk abunda Allah ya tsaroga bawa sai yafaru to tabbas zai farud'in komai dubararsa da kuma wayonsa, rashin son b'ata maki rai da sakaki cikin damuwa shiya haifar da b'oye maki makamancin irin wannan damuwar da kike ciki, amma da yake ban isa canza duk abun da Allah yatsaro zai faru akaina ko akankiba sai yajuya  samuwar b'acin ran agareki ta sanadin jaddi, kwana biyu da suka wuce dady yakirani ya sanar dani ya nemamun auren 'yar abokinsa, ana haka kuma saiga papi shimadai d'in abunda yafad'amun kenan!, naso nakiraki na sanar dake amma nakasa saboda gudun b'acin ranki" faraaha dake kwance tana kuka bata san lokacin data tashi zaune ba tana sharar hawayen dake zubowa daga idanuwant ba had'e da cewa "wai mekace!?, har mata biyu aka nema maka aurensu? Wannan wane irin sonkai ne haka, sufa sauran mazan ya ake so suyi daza'a tashi abaka har mata, kai kuma mekace masu papi" tak'arashe maganar cike da tsiwa abakinta, duk da yana cikin damuwa hakan bai hanasa yin dariyar da seda taji sautinta akunnen taba, cikin b'acin rai tace


"Au dariya ma kakeyi, wato kaji dad'i anbaka auren har mata biyu, ni kuma nakoma marar amfani awajenka ko,shikenan ngd" sanin cewa kishi ne yamotsa mata kuma yaji haushin abunda tafad'a masa shima yana so yarama ya sashi cewa


"Haba faraah! Meye abun damuwa da b'acin rai aciki, nariga nafad'awa papi da kuma dady ke nake so kuma sun amince da zab'ina kina shikenan kece uwar gidana ta gaban goshina ko kuwa" rintse idanuwanta tayi tanajin d'acin maganar da yayi azuciyarta, jin bazata iya jurar cigaba da waya da shiba yasa takashe wayar had'e da fashewa da kuka, aranta kuwa cewa take lallai ashe har akwai ranar da mahmud d'inta zai iya furta mata kalaman da zasu iya tarwatsa mata zuciya, kenan ita ke haukan kishin sa amma shi bayayin nata ko kad'an, kiransane yasake shigowa awayar tayi banza dashi har ta tsinke, dariya yayi kafin nan yasake kiranta amma tak'i d'agawa, saida ya kirata sau wajen takwas sannan ta d'auka had'e da cewa


"Mezai hana kakira sauran matan naka tunda uwar gida tak'i d'agawa?, ni nafarka daga baccin da nakeyi duk da banida mahaifin da zai samomin wani mijin da zan aura amatsayin zab'insa bayan nawa, zanyiwa jaddi magana yasake nemamun wasu mazan da yake tunanin sun dace dani duka suzo mu maganta har zuwa lokacin da zansamu daidaini kai kuma kaje ka k'arata da matan da aka zab'a maka" tak'arashe maganar tana k'ara sautin kukan da takeyi...sosai yaci mamakin maganganun ta masu cike da yarinta ga dariya na neman kucce masa amma ba halin yayi gudun kar ya b'allowa kansa ruwan da zasu had'iyeshe, gyaran murya yayi tare da danna dariyar dake nema taci k'arfinsa yace


"Relax my golden heart, ba hakan nake nufi ba....bayani yaci gaba dayi mata dalla dalla akan yanda sukayi da dady da kuma papi, amma duk da hakan baisa tadaina jin zafin wannan had'in da ake nema ayi masaba, rarrashinta ya dingayi yana bata hak'uri, amma sai riga take sake yimasa, dak'yar yasamu ya shawo kanta tare d tabbatar mata da cewa komai rintsi kuma komai wuya shi natane kuma itama tasace,


"kayi alk'awari" tafad'a cikin sigar shagwab'a


"Eh nayi alk'awari in sha ALLAH" yatabbatar mata da hakan cike da yak'ini sannan suka ajiye wayar, shiru tayi tana tunanin makomarta idan har su papi suka aurawa masoyinta mata biyu.


Yau kimanin kwana uku kenan Mahmud pilot na fama da zazzab'in rashin masoyiyarsa sosai yarame saboda rashin cin abinci da tunaninta da yakeyi, tun ranar yadena fitowa kuma baya zuwa ko ina hatta su Umma da dady saidai yakirasu awaya, sunyi tambayarsa ko lafiya basa ganinsa sai yace masu wai idanuwansane keciwo bayason haske, yaya Mahmud kuwa yayi yayi dashi suje asibiti yace shi lafiyansa kalaw babu inda zaije duk dako yana ganin yanda bacci ke gagararsa acikin 'yan akwanakinnan ga zazzab'in da yake fama dashi kuma yarok'esa akan don Allah kada yasanar da ummansa domin hankalinta zai iya tashi, yaukam abun ya gagari yaya Mahmud domin halin da yaga d'an uwan nasa yatayar masa da hankali sosai, zazzab'ine mai tsananin zafi yarufesa kamar zai rasa ransa, hakan yasa yaya Mahmud yaje ya sanar da dady halin da yake ciki da sauri ya nufi d'akin yana yimasa fad'an don me zai bari hakan tafaru dashi batare daya sanar dashi ba sai yanzu da abu yayi tsamari, suna shigowa suka tarar dashi asume ko motsi bayayi, jijjigasa dady yashigayi yana kiran sunansa amma ina ko motsawa baiyiba, hakan yasa dady yace Mahmud yaje yacewa Nazir driver yafiddo mota akaishi asibiti, dady da kansa ya tadashi zaune ya mahmud na dawowa ya rik'a masashi suka nufi wajen mota dashi, Billy da tadena ganinsa kwana uku d'innan da suka wuce tashiga damuwa tawani b'angaren kuma tunani tayi k'ilan yayi fushine akan abunda tafad'a masa shiyasa yadena barin suhad'u ko akan hanyane, taso taje d'akin yaya Mahmud tadubosa amma sai wata zuciyarta tanuna mata yin hakan tamkar tanuna gazawar tane bisa abunda ita tasa kanta da kanta, tana zaune a guarding tak'urawa tagar d'insu idanuwa tana jiran taga koda wulgawar inuwarsace ajikin labulen kawai saita hango su dady da yaya Mahmud sun tattalabosa, gabanta ne yayi wata irin muguwar fad'uwa ganin masoyinta acikin wannan halin da gudu tanufi wajensu tana fad'in


"Dady me yasamu yaya Mahmud, meke faruwa dashi?" Ganin sunci gaba da tafiya dashi da sauri da sauri batare da sun bata amsaba yasa takoma gefen yaya mahmud tana goge hawayen idanuwanta "yaya Mahmud meyasa mesa, don Allah kufad'amun" Dai dai nan suka iso gaban motar da tun d'azu nazir yabud'eta yana jiran isowarsu, kama masu yayi akasashi cikin motar dady yashiga sannan yaya Mahmud yakoma gaba ya zauna Nazir driver yaja motar aguje yabar gidan dady nafad'in 


"Maza kataka motar nazir! Lumfashin yarona kad'ai nake gani amma baya motsi, kad'an kad'an nake iya ganin bugun zuciyarsa"


Ita kuwa Billy naganin haka ta aza hannu akai tana fad'in "nashiga uku, nice silar faruwar haka ga d'an uwana, pls yaya mahmud am so sorry ina sonka, ina matuk'ar sonka sosai wlh dawasa nake yimaka kada kamutu kabarni" tafashe da kuka


Basmah dake tsaye abayanta mutuwa kad'ai yarage tayi jin kalaman'yar uwarta, kenan itama 'yar uwarta na sonsa kamar yanda take sonsa, shikenan babu sauran wani hope tsakaninta dashi, kuka ne yazo mata da sauri tatoshe bakinta had'e da komawa da baya da baya tabar wajen aguje, itama Billyn aguje tabar wajen tana kuka tana kiran Ummi Umma...








*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻_* 


 

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____52💎



    Ke lafiya ummi dake fitowa itada umman barno jin yanda da take faman k'wallamasu kira suka tambayeta arud'e, kasa magana tayi sai faman nuna masu get takeyi, kafad'unta Ummi tarik'e had'e da girgizata tana fad'in "wai meke faruwa dakene Bilkisu, bud'e baki kiyi muna magana mana ko so kikeyi sai hankalinmu yagama tashi" had'iye wasu yawu da suka zomata tare da hawaye tayi tana kallon ummi.


"Yaya ne ummi!" Tafad'a hawayen nasake ziraro mata a idanuwa, Matsowa umman borno tayi itama tana fad'in "yaya ne yayi me Bilkisu? Kinatsu mana kifad'a mana abunda kefaruwa kinji ko?" Ganin zata b'ata masu lokaci sai kuku take gashi hankulansu suntashi yasa ummi tasaketa tanufi d'akinsu, wayar ummace dake hannun ummi tayi k'ara, ganin lambar dady ce yasa ummi dake gab da shiga d'akin nasu tad'aga,


"Hello Hafsatu, kusamemu a asibiti Mahmud ba lafiya gamunan nan akan hanyar zuwa asibiti" dady yafad'a yana kallon fuskar Mahmud pilot da tayi wani irin duhu, sai alokacin ma yalura da yanda duk yayi bak'i kuma yarame, muryar Ummi yaji tana fad'in "subhanallahi dadyn yara meyasa meshine?"


"Bamu saniba sai inmun isa asibitin tukuna, amma dai yanzu haka ko motsi bayayi, yanzu ina ita maman tashi" 


"Gatacan wajen Bilkisu" "meyasameta ita kuma" yafad'a cikin damuwa, "babu komai tad'an rud'ene tana faman kuka ganin halin da d'an uwan nasu keciki!"


"Allah ya sawak'e, kada kisanar da Ummansa komai kinsan tanada matsalar hawan jini, kawai kisan mezaki fad'a mata sai kuzo" 


"In sha Allah, Allah yabashi lafiya, gamunan zuwa yanzunnan, awace asibiti kenan zamu sameku"


"Jidda specialist hospital" yafad'a atak'aice


Juyawa Ummi tayi had'e da nufar inda suke tsaye Billy nafad'awa Umma cewa yaya Mahmud ne ba shida lafiya anyi asibiti dashi, dai dai lokacinne ta iso wajen had'e da jawo hannun Umma dake k'ok'arin tambayar wane yaya Mahmud daga cikinsu.


"Bar wannan maganar kizo muje asibitin muganewa idonmu, ke kuma kije kifad'awa mom d'inku" sannan suka wuce jiki babu k'wari.


Daga can gaban mota yaya mahmud yace


"Dady meyasa kace suzo? Ai indai sukazo asibitin to tabbas komai na iya faruwa ganin halin da yake ciki tunda ita umman tanada matsala to zaifi dacewa su zauna har sai munga yanda jikin nasa yayi tukuna sai suzo ko kuwa?"


"Eh hakane son nrud'ene gaba d'aya, call her kace nace sujira basai sun zoba" daidai lokacin suka shigo asibitin, sunayin parking Mahmud yafita dasauri yakira nurses sukazo da d'an gadon da ake aza marasa lafiya aka shiga dashi emergency aguje, kasancewar yaya Mahmud yakira dr. jamal tun akan hanyarsu ta zuwa yasa nan da nan aka bud'e masa file, suna isowa aka fara basa taimakon gaggawa, dady kuwa komawa cikin mota yayi yayi zaune yana tunanin ko meye yasamu d'and'an 'yar uwarsa, waya Mahmud yaciro yakira Ummi dake k'ok'arin fitowa ita da mom yafad'a mata cewa dady yace suyi zamansu tunda babu wanda zai kawosu, nazir driver ma yana nan tare dasu sannan ya kashe wayar yana safa da marwa abakin k'ofar da aka shiga da Mahmud pilot.


Basmah kuwa tunda tashiga d'akinsu ta shige cikin toilet tanata rasgar kuka, wanda ko baka tambayaba kasan damuwar ce takasan mata biyu shiya haifar mata da tsanantar kukan nata, ga dai masoyinta kwance ba lafiya rai a hannun Allah wanda takeji tamkar tamaido ciwon atare da ita sannan tawani b'angaren ga tabbatuwar rashinsa da zatayi tunda wacce yakeso kuma yake k'auna itama tana son sa sosai wannan dalilin yasa ya zamemata dole ta koka kobata buk'atar yin kukan duk wata magiya da rarrashi Batool tayi mata akan tabud'e k'ofar ta sanar da ita abunda kefaruwa amma tak'i saima kukan nata dake tsananta, hakan yasa taje tafad'owa mom, da sauri mom tashigo d'akin tana bubbuga k'ofar toilet d'in da k'arfi.


"Basmah..Basmah, kibud'e k'ofannan kinaji na ko?, bazaki bud'e bane sai nakira malam habu yazo ya b'allamun ita? Kibud'e k'ofa kina jina ko?" Da sauri Basmah ta tsaida kukan nata don har ga Allah batason mom d'insu tasan halin da take ciki, wanke fuskarta tayi ga fanfon dake jikin toilet d'in sannan tazo ta zare makullin tabud'e k'ofar, mom da tuni ranta yagama b'aci tsaye tayi tana kallon Basmahr data noce kai k'asa tana k'ok'arin wucewa ta gefenta.


"Basmah, me yafaru?, naga fuskarki ta kumbura? fad'amun meke damunki" tafad'a cikin rud'ewa tana kamo hannunta suka zauna gefen gadon, hannu tasa ta d'ago fuskarta tana kallon yanda manyan manyan fararen idanuwanta suka koma jawur saboda tsananin kukan da tayi, ad'an tsorace tace "Basmah kifad'a mani abunda kedamunki, meyasa ki kuka haka" rasa k'aryar da zatayi mata tayi, saita dunk'ule tana fad'in "mom marata take yimun ciwo"


"Shine zaki zauna kina kuka hadda rufe kanki cikin bayi? Ko gudu bakyayi ki k'ara kwasarwa kanki wata cuta?, sannu Allah ya sawak'e, Batool zo karb'o mata declofenac tasha kuma kibar kukan haka zata dena ciwo kinji ko?"ta dafata had'e da mik'ewa zatabar d'akin, Billy ce tashigo tare da fad'in 


"Mom yaya Mahmud bayada lafiya su dady sunyi asibiti dashi" batare data kalli inda takeba tace


"Allah yabashi lafiya" sannan tawuce abunta duk da zuciyarta cike take da fargabar wane Mahmud d'inne daga cikinsu, saida tabud'e bedside drower ta d'auko magani taba Batool data biyo bayanta tace kibata biyu tasha saita kwanta Allah yakara sauki, ta amsa da amin tafice sannan ta d'auko wayarta, lambar yaya Mahmud takira bugu d'aya ana biyu ya d'aga 


"Hello mom" ajiyar zuciya tayi sannan tace


"My son kana lafiya?"


"Lafiya klw mom tun d'azu nake so nakiraki infad'a maki d'an uwana ba lafiya munanan asibiti karkiga ban shigo nagaisheki ba hankalina ne ya d'auku"


"Ayya babu komai son, Allah yabashi lafiya hop da sauk'i?"


"Eh da sauk'i mom amma har yanzu likitan bai fitoba"


"Shikenan Allah ya sawak'e" tafad'a tare da kashe wayar.


Tunda Basmah taji muryar Billy tashigo taji tsananin bugun zuciyarta yak'aru, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tadinga maimatawa acikin zuciyarta har saida taji natsuwa tazo mata, tashi zaune tayi tana kallon Billy dake zaune itama agefen gadon ta rabka uban tagumi hawaye nabin kuncinta da alama tunanin halin da masoyinta yake ciki takeyi, matsawa tayi akusa da ita tarik'o hannunta, ahankali tafara motsa bakinta tana yimata magana da muryarta dako fita batayi sosai saboda kukan da tayi,


"My sister, tunanin me kikeyi kina kuka" d'ago kai Billy tayi had'e da cewa


"Nice sila yayya Basmah, inada tabbacin wannan ciwon na yaya Mahmud nice silarsa, ya zanyi ingyara wannan kuskuren danayi" daidai lokacin Batool ta turo k'ofar d'akin hannunta rik'e da magani da kuma gorar ruwa, mik'awa Basmah tayi "ungo yayya ga maganin kisha" karb'a tayi ta ajiye akan stool d'in dake gefenta tace


"Anjima zansha idan na karya" shiru Batool tayi tana kallonta don dama ita tasan cewa babu wani ciwo da mararta keyi kawai tsananin soyayyar da takeyiwa yaya Mahmud kejefata cikin wannan halin, dama kwana biyu tana lura da ita duk dare bata bacci saidai tazauna tana kuka da sabbatun soyayyar da takeyi masa, tana k'yaletane saboda batasan irin yanda takeji arantaba shiyasa batason takurata. Wannan kallonfa?  Basmah tafad'a tana hararar Batool kafin tajuyo akan Billy tace


"Tone sisto mekike yimasa da kike tunanin kece silar wannan ciwon da yake ciki?"


Juyowa tayi tana kallonta sannan tarik'o hannun Batool ta zaunar da ita a gefenta, labarin abunda yafaru tsakaninta dashi shekaranjiya tabasu had'e da abunda tafad'a masa na cewa ita tanada wanda take so bacin yatabbatar mata da cewa bazai iya rayuwaba idan babu ita, da kuma dalilin ta na d'aukar wannan matakin da tayi, goge hawayenta tayi had'e da cewa


"Wlh yayya babu wanda nake so duk duniya idan bashi ba, tun ina k'arama nima nake sonsa kamar yanda yake sona, amma sai gashi da kaina na d'auki matakin dazan ruguza rayuwata da kuma tasa, ku 'YAN UWANA NE, bazan iya b'oye maku komai ba, wlh nima zan iya rasa rayuwata idan babu shi saboda ina sonsa sosai, kubani shawarar abunda zanyi don gyara kuskuren dana tafka" mutuwar zaune Batool tayi jin kalaman dake fitowa daga bakin 'yar uwarta alokaci guda kuma tana kallon Basmah da idanuwanta suka cika da k'walla, tausayin sune gaba d'aya yarufeta nason mutumen da bazai tab'a yuyuwa su auresa ba su duka. Yatsa Basmah tasa ta goge hawayen da suka zubo mata sannan tarik'o hannuwan Billy tace


"Tabbas kinyi kuskure sister da kika nemi shek'e farincikin ki, don me zaki b'oye masa son da kike yimasa alokacin dashi kuma ya bayyanar maki da soyayyar da yakeyi maki? Inaso kisani babu abunda yakai kaso asoka dad'i, haka kuma babu abunda keda d'aci irin ke b'oye soyayyarka ga wanda kasan kana so har akai matakin da zaka rasata gaba d'aya agaresa, ak'alla koda bazaki soshi fiye da yanda yanuna yana sonki Batool kimayar masa da soyayyarki daidai kwatankwacin daya yimaki? duk abunda zai faru yariga daya faru saidai muyi fatar Allah yabashi lafiya, amma inaso kisani don gyara kuskuren da kikayi dolene awannan karon kema kinuna masa soyayyar da kike yimasa kinji ko?" Tak'are maganar had'e da d'an jamata kumatu kad'an ita kuma tana cije bakinta saboda zugin dataji zuciyarta nayi sannan tasa hannu tashare mata hawayen da suka jik'a mata fuska "kije kiyi masa addu'a kinji ko baya buk'atar kukanki" murmushi Billy tayi had'e da rungumeta sosai tana fad'in 


"You are d best sister in d world nagode sosai da shawararki" sannan tamik'e zata fita, har tarik'e handle d'in k'ofar Basmah takirata juyowa tayi fuskarta cikin fara'a tace "na'am yayya" kamar sun had'a baki ita da Batool sukace


"Billy ta fola" suna dariya dawowa tayi itama tana dariya tace


"Yes nayi given up twiny tunda nayi falling wa yaya Mahmud sosai" rungume juna sukayi gaba d'aya sunajin k'aunar 'YAN UWANSU arai, sunjima ahaka kafin suyi breaking hug d'in Billy tawuce part dinsu, duk wannan abun dake faruwa mom nafalo kuma tajiya da Billy zata fita tarakata da harara kafin tace


"Hmmm kyaji dashi indai d'a namijine, dama can ke kikafi dacewa dashi don nikam neman tsarin Allah nakeyi da abunda zai had'a 'ya'yana da jinin hajia hafsat tunda bata sona kuma bata k'aunata, amma yanzu alhamdulillah da Allah yasa baifad'a soyayyar d'ai daga cikin yarana ba"


Tana fita Basmah tayi kwance tana dafe zuciyarta dake tsananin yimata ciwo, kan gadon Batool tahau ta zauna, d'ago kanta tayi ta d'ora asaman cinyoyinta tana goge mata hawayen da suka gangaro mata a fuska,


"Yayya Basmah meyasa zakiyi haka bayan kinsan kema kina sonsa?"


"Yazanyi Batool? Kina ganifa cike da hope 'yar uwata ke neman taimakonmu akan soyayyarta cike da yak'inin cewa zamu samamata mafita, don me bazan yimata hakan ba don tabbatar mata da cewa mud'in 'yan uwan tane dake shirye subata kowane irin farincike aduniya koda hakan na nufin zamu samu tawayar namu farincikin, kuma hakan danayi bayana nufin banason yaya Mahmud bane yanzu, a'a ina matuk'ar sonsa, yanzu haka zuciyata rad'ad'i da ciwo takemun saboda sanin da nayi cewa yayimun nisa sosai" hannunta tajawo tad'ora asaitin zuciyarta tace


"Inama zaki iya jin zafi da rad'ad'in da takeyimun, natabbata bazaki bar hannunki awurin ba daidai da minti d'aya don zata iya k'onaki"


"Amma yayya kinsan da haka kuma kike yunk'urin tirsasata abunda bazata iyaba, to yanzu meye makomar soyayyarki idan kinyi hakan?, don Allah kibarni nafad'awa twiny halin da kike ciki natabbata zata barmaki yaya Mahmud ki aura" 

 

Tashi zaune tayi tana kallonta "karki yi kuskuren aikata haka sister bayan kin d'aukar mun alk'awari, domin a k'ok'arin ceto soyayyata zaki iya rasa gaba d'aya rayuwar 'yanuwanki, ni ina sonsa sosai, itama tana sonsa sosai shin kina tunanin idan tahak'ura da soyayyarsa tabarmunshi ita bazata fad'a makamancin halin da nake cikiba koma fiye da hakan sannan nikuma kina tunanin damuwata zata gushene don nasameshi amatsayin miji alhalin baya sona? Dafata tayi sannan taci gaba da cewa Batool kicire sonkai a wannan alamarin domin nice yadace nahak'ura da soyayyata inbarwa k'anwata shi tunda nice babba kuma ita yake so" 


"Shikenan yayya narok'i Allah yazab'a maku dukkanin abunda yafi zama alkhairi 'YAN UWANA!"


"Amin" Basmah tafad'a tana murmushin k'arfin hali sannan takoma ta kwanta akan cinyoyinta tana shafa mata kai ahankali cikin tausayawa rayuwarta.


Dr Jamal ne yafito daga d'an d'akin da aka shiga da Mahmud pilot yana cire hand gloves a hannunsa, iskoshi yaya Mahmud yayi yana fad'in 


"Dr. Yajikin d'an uwana?"


"Alhamdulillah da sauk'i don munyi nasarar farfad'owarsa daga doguwar sumar da yayi, kuma babu wani abun dake damun sa yanzu don har munsamu anyi masa allurai yayi bacci, but ina alhaji yake?"


"Yana cikin mota, bari inkira sa" 


"Ok kusameni a office d'ina" yafad'a tare da barin wajen, bayan kamar minti biyar saiga dady yashigo office d'in Mahmud nabiye dashi... Da sauri dr. Jamil ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya mik'awa dady hannu suka gaisa cikin girmamawa, bayan sun gaisa ya nunawa dady kujera ya zauna, 


"Alhaji barka da safiya ya iyali?"


"To alhmdllh dr. Yaya jikin yaron nawa?"


"To alhmdllh da sauk'i ya farfad'o daga doguwar sumar da yayi har yasamu yin bacci, amma am sorry to say tunanin me yakeyi daya haifar masa da damuwa haka har yakaishi ga shiga cikin wannan hali?, abu na biyu kuma malaria takamashi sosai don haka dole zamu d'an rik'eta na kwana d'aya saboda nasamu ayi treating d'inta don kada tayi masa illa, insha Allah ko zuwa gobene za'a iya sallamarsa amma yakamata tun yanzu ad'au matakin hanasa yawan tunanin da yakeyi don gudun fad'awarsa babbar matsala anan gaba ina nufin damuwar zata iya zame masa ciwon zuciya nan gaba, Allah yakare...







*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____53💎



    Da sauri dady ya d'ago kai yana kallon dr jamil.


"Mekace dr! Ciwon zuciya fa kace?" 


"Sosai kuwa matuk'ar bai dena yawan tunane tunane ba kuma yacire damuwa aransa to tabbas hakanne zai iya faruwa!"


"Noo..Allah ya tsare amma hakan bazai faru ba in sha ALLAH" dady yafad'a zuciyarsa cike da tambayoyin dalilin daya haifar da faruwar haka, takardar da za'aje pharmacy abiya kud'in magungunan da yake buk'ata ya mik'awa dady sannan sukayi sallama, har zasu fita dady ya juyo had'e da cewa "zamu iya shiga wajensa yanzu?


"up course! Zaku iya shiga babu wata matsala" godiya yayi masa sannan yafice shida yaya Mahmud, suna fitowa dady ya mik'a masa takardar yace yaje ya biya kud'in shi kuma yashiga d'akin da aka kwantar da Mahmud, kujerar dake gefen gadon yaja ya zauna had'e da rik'o hannunsa yana kallon fuskarsa,


Ba'a jimaba yana nan zaune saiga yaya Mahmud yadawo hannunsa d'auke da maganukkan daya anso, anan saman side loka d'in gadonsa ya ajiye sannan yace


"Dady kaje Nazir driver ya saukeka gida daga nan sai ya d'auko su Umma" motsin da Mahmud pilot ne yayi ya hana dady bashi amsa, tasowa yayi had'e da dafa goshinsa yana jera masa sannu,  amsawa yayi had'e da cije baki yana kallon yaya Mahmud, ahankali ya mik'a masa hannu had'e da cewa "d'an uwa" da muryarsa da bata fita sosai, matsowa yayi yarik'e hannun nasa "sannu d'an uwa, ya jikin" "da sauk'i" yafad'a had'e da juyowa yana kallon dady "yaronah mekake so?, me yake damun Kane?" dady ya tambayesa cikin  sigar rarrashi, "Bakomai dady" yabasa amsa had'e da kauda kansa gefe hawaye na zubo masa, gudun kada yatakurasa masa yasa dady ya cewa yaya Mahmud


"Kakula dashi, bari naje gida sai su umminku su taho, sorry son Allah yak'ara sauki" sannan yafice daga d'akin, kamar jira yake dady yafita ya rumk'e hannun yaya Mahmud sosai idanuwansa na hawaye yace


"Bata sona d'an uwa, Bilkisu bata sona tafad'a mun tanada wanda take so itama, meyasa baku barni na mutuba?, matuk'ar narasata to tabbas mutuwa zanyi koba yanzu ba" dama yaya Mahmud ya dad'e da noticing haka amma saboda k'infad'a masa da yayi tunfarko shiyasa baiyi wani abu akai ba yafita batun sa. Zagayowa yayi tagefensa yajawo kujerar da dady ya tashi akai ya zauna, sannan yace


"Shine zaka nemi saka kanka cikin wannan mawuyacin hali, kar ka manta ba ita kad'ai keda buk'atar kaba, umma damu duka muna buk'atarka, ita kanta tafad'i hakanne kawai amma inada yak'ini akan tana sonka, ko kamanta da irin shak'uwar dake tsakaninku ne na tsawon shekaru? Yayana za'ayi tace bata sonka, ka zauna duk girmanka ace k'ank'anuwar yarinya tayi wasa da zuciyarka amma ka kasa gane haka har kana neman hallaka kanka" yunk'urin tasowa yayi jin abunda yafad'a aransa yana cewa shin wai da gaskene Billynsa na sonsa wasa take yimasa da zuciya. Saurin dakatar dashi yayi tare da gyara masa kwancinsa sannan yaci gaba da cewa


"A gaskiya banki dad'in abunda ka aikatawa kankaba, babu yanda banyi da kaiba akan kafad'amun matsalarka amma kak'i da tuni haka bata faruba, dubeka duk halittarka ta canza saboda taurin kai irin naka, gashi har kana neman kajawowa kanka ciwon zuciya"


"Sorry d'an uwa, narasa yazanyine, banaso natakurata ko kuma nasanar atilasta matani shiyasa amma kayi hak'uri hakan bazai sake faruwa ba"


"Is better kam, dole kajure ka k'wato soyayyarka ko kuma wlh infad'awa dady ya aura maka meamah" Murmushi Mahmud pilot yayi yana jin soyayyar d'an uwan nasa har cikin ransa tare da kuskuren da yayi na b'oye masa duk da yasan tsakaninsu babu abunda suke b'oye wa juna kallonsa yayi kafin yace


"Hop dai batasan halin da nake cikiba ko?" Dariya yaya Mahmud yayi tare da gyara zamansa akan kujerar da yake zaune yace,


"Tab..ai you fail guy!, itace tafarko data fara ganin halin da kake ciki bayan ni da dady lokacin da muka tallaboka, but thank God hakan ya taimaka maka don bakaga yanda tarud'e ba tana tambayarmu me yasameka da alama tadamu" 


"Hmm how do u know bayan da bakinta tafad'a mani akwai wanda takeso" yafad'a yana kauda kansa.


"I know my sister fa, kuma ai cemaka tayi akwai wanda take so batace bata sonka ba, kayi tunani mana, anya bala'i d'in bane tunda nidai bntab'a jin tayi zancen wani ba kuma ban tab'a ganin ta tare da wani ba,ina tunani gwadaka tayine kaikuma ka kasa ganewa" sai alokacin Mahmud pilot yafara tunano lokacin da take fad'a masa maganar tabbas babu damuwa atattare da ita ko kad'an idan kuwa da gaskene dolene sai tad'an shiga wani yanayin da zai tabbatar masa da haka, tafin hannunsa ya buga ga goshinsa yace "kash...I think hakane fa d'an uwa" Dariya yaya Mahmud yayi tayi masa yana tsokanarsa, sai gashi cikin mintota kad'an yadawo a Mahmud pilot d'insa tamkar bashine d'azun aka kwaso asheme ba rai a hannun Allah, suna hakan saiga sister faraaha tashigo d'akin, sallama tayi sannan tak'araso ciki tana jifar yaya Mahmud da wani irin kallon k'auna, saiti zuciyarsa ya dafe yana fad'in


"Kai baby irin wannan albarushi haka ai sai kisa ya shek'eni" dariya tayi had'e da gaida Mahmud pilot da shima dariyar yakeyi tana yimasa ya jiki? Kallon yaya mahmud yayi bayan ya amsa tare da kallonta kafin yace 


"Da alama kece wadda yamak'alewa kullum kuke rura mani wuta azuciyata saboda soyayyar da kukeyi" 


Dariya tayi batare data tankaba tana kallon gorar drip d'in dake shiga jikinsa, shikuwa gogan naka kafeta yayi da idanuwa kasancewar yau acikin kayan gida ya ganeta ba ba uniform ba tunda ba aiki tafito ba, kiran dayayi matane yasanar da ita yana asibiti d'an uwansa ba lafiya yasa tashigo don ta duba jikinsa.


Tashi yaya Mahmud yayi ya nuna mata kujera ta zauna, girgiza masa kai tayi had'e da gyara tsayuwarta alamun kar yadamu a tsayenma yayi mata, hakan yasa shima yakasa komawa kan kujerar, shiru wajen yayi na tsawon mintota kafin can yaya Mahmud yadawo kusa gareta yana fad'in 


"Kinga patient d'inmu ko da my sister ta rikita yakoma raggo har takaishi ga rashin lafiya" gaban faraaha ne yayi saurin fad'uwa ta d'ago kai tana kallonsa had'e da cewa "wace sister d'in taka aciki?, kaddai kace kutse yayiwa dr.Ahmad acikin gonarsa" "mayar da wuk'ar my golden heart" yafad'a yana cigaba da cewa


"Ai d'an uwana sai 'yar uwata Billy koba haka ba d'an uwa?" Yak'arasa maganar yana kallonsa. 


"Thank God" faraaha tafad'a tana juya idanuwanta, kafin tace wani abu sai ga Dr. Jamil  yaturo k'ofar d'akin had'e da shigowa, gaishesa sister faraaha tayi ya amsa cikin sakin fuska yana tambayarta ko itace on duty tace masa a'a tazone duba patient d'in sa, kallonta yayi da alamar tambaya abakinsa sannan yaci gaba da dudduba Mahmud pilot, maganukkan da aka siyo yadudduba tare da injection d'in sannan yayi masa duka abunda yakamata, kai dubansa ga Mahmud yayi yace


"Alhamdulillah nagama jikin nasa ya k'ara samun sauk'i sosai k'ila zuwa anjima ayi discharging nasa in sha Allah" sanan ya bar d'akin yana yimasa godiya. Kallon yanda suke soyayarsu Mahmud keyi cike da burgewa yanaji inama ace shima Billynsa zata bashi had'in kai haka da  soyayyarsu tazama abun kwatance aduniya.


Dady kuwa yana komawa part d'in mom yanufa da yake ita keda girki, yana shiga yasameta zaune afalo tana kallon maimaicin wata drama da akeyi SAPNE SUHANE, kallo d'aya tayi masa takauda kai batare da tace masa komai ba, kusa da ita yasamu ya zauna agajiye yana fad'in


"Am sorry kinjini shiru, Mahmud ne ba lafiya, yanzu haka yana asibiti"


"Eh naji ga 'yarka tund'azu, tunda ni banida daraja da kima awurin ka  zaka kirani kafad'amun" dafa goshi yayi kafin yace


"Ayya sorry ba haka bane, hankalina ne atashe shiyasa, ummansa kad'ai nakira wayarta"


"Oh ka kirasu kafad'a masu amma ni tunda ka maisheni daniyar ware shine ka kasa kira kafad'amun, Allah dai nasane da duk namijin dake banbanci tsakanin matansa" baki tabud'e dady ke kallon mom, meyayi anan na rashin adalci? Shifa 'yar uwarsa yakira sai akayi sa'ar wayar na a hannun ummi ta d'aga, shikenan sai yafasa yin maganar da zaiyi da ita don ba girkin tabane, saboda bayaso maganar tayi tsauri yasa yace da ita


"Kiyi hak'uri nayi kuskure, in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba, shikenan ko" yak'are maganar yana kallon fuskarta, da yake Allah yayiwa mom son girma nan take tasaki, breakfast tashiga kitchen tahad'o masa, bayan yaci yace tagyara zaije ya watso ruwa sai suje asibitin shima yaya Mahmud yadawo gida yayi breakfast. Basmah dake kwance zazzab'i ya rufeta ya k'walawa kira, jin muryar mahaifinta yasa ta tattaro sauran d'an k'arfin da take dashi tamik'e taje inda yake kiranta, batare da yakula da yanayin da take cikiba yace


"Kije kifad'awa 'yan uwanki kushirya Nazir driver ya ajiyeku asibiti kugano yayanku kafin muzo" ta amsa masa da "to dady" jikinta na rawar sanyi, Batool ta tura tafad'owa Billy sak'on dady sannan ta dawo ta taimaka mata itama ta shirya sannan suka nufi wajen Nazir driver ya ajiyesu asibitin, ita kuwa ummi koda yaya Mahmud yakirata yafad'a mata dady yace suyi zamansu kitchen tashiga ta had'a abincin daza suje dashi asibiti bayan ta sanar da Umma zancen rashin lafiyar Mahmud cikin hikima tayanda hankalinta bazai tashi ba, kuma Alhmdllh tafahimta cikin sauk'i tare da fatar Allah yabashi lafiya, suna zaune saiga dady yashigo da sauri suka taso suna tambayar yajikin Mahmud ya tabbatar masu daya samu sauk'i sosai don har ya farka kuma yana magana,


"Alhmdllh" suka fad'a atare had'e da fatar Allah yak'ara masa lafiya, cemasu yayi su zama cikin shiri inya fito zasuje asibiti sai sudubosa.


Tun acikin mota Billy kefaman jerowa Nazir driver tambayoyi wai ya jikin yaya mahmud? Yaji sauk'i?, ya farka, yana magana? Ko k'ak'a, murmushi yayi had'e da kallonta yace


"Kai 'yar gidan Ummi, wud'annan tambayoyin anya basuyimun yawa ba, to wace zanfara  amsawa aciki?"


"Duka" tafad'a atak'aice cikin d'auki da zak'uwar ganinsa, 


"To 'yar gidan dady alhamdulillah yaji sauk'i sosai" Basmah kuwa tunda tashiga motar ta jingina ajikin kujerar baya ta rufe idanuwanta batace uffan ba har suka iso asibitin, duk da Billy na d'okin ganin masoyinta hakan bai hana tajira fitowa 'yan uwanta daga cikin motar ba jiri ke d'ibar Basmah Batool na k'ok'arin rik'eta amma don kar a fahimci tana cikin wani yanayi ta dinga tureta tana k'wace jikinta, dole tak'yaleta takoma gefenta tana kallon yanda take takawa cikin k'arfin hali itama Billy ta tsaya ad'ayan gefennata suka san yata tsakiya har suka iso d'akin da aka kwantar dashi da taimakon Nazir driver shida yasan wajen.


 Suna shiga suka nufi wajen gadon duk su uku  suna yimasa sannu ba tare da sun lura da faraaha dake can gefe tare da yaya Mahmud suna soyewa. 


Tunda suka shigo idanuwansa na akan masoyiyarsa abur k'aunarsa wato Billy, ganin haka yasa Basmah tamatse hannun Batool dake rik'e da ita sosai alamun sud'an basu wuri, suna juyawa itama Billy tabiyosu, muryarsa suka jiyo yana fad'in


"Kin.ji.." Cikin i'ina kamar an matso maganar dole, gaba d'ayansu suka tsaya cak had'e da juyowa suna kallonsa in banda Basmah data runtse idanuwanta taci gaba da tafiya.


"Sorry Batool da Bilkisu nake" yafad'a idanuwansa na akanta..



 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Some are celebrating, dancing, singing, happy, drunk, their head is almost vibrate on their birthday date with out knowing dt they are just close to their graves, hope u will not be among them, u will be among those one's who said "ALHAMDULILLAH ya rabh, forgive my sin's and make ur holy home jannatul Firdausi be my final abode👏🏻" *Happy birthday to you MRS. QUDIEDIE* may Allah forgive ur fast years and bless ur up coming years, wish u more qudie qudie in ur bank accaunt🥰😍😘_


💎Page_____54💎



   Wucewa Batool tayi ita kuma Billy tadawo inda yake kanta ak'asa zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, "Bilkisu!"


"Na'am" ta amsa kanta na daga k'asa,


"'Dago kanki ki kalleni" yafad'a, d'agowa tayi cike da jin kunyarsa amma takasa kallon k'wayar idanuwansa, "kinga yanda nakoma, meyasa zakiyi wasa da rayuwata, kina tsammanin kalaman duk dana yimaki bana gaskiya bane don in yaudare kine?, meye ribar Mahmud idan ya yaudari 'yar uwarsa kuma jininsa da yake matuk'ar k'auna, shin ko da gaske kikeyi bakya sona har cikin zuciyarki?" Kallon gefen dasu yaya Mahmud zuke zaune tayi ashe su har sun dad'e da ficewa daga d'akin don dama kunyarsuce tasa takasa tanka masa.


Girgiza kanta tayi sannan tace "Ko kad'an yaya niban furta bana sonka ba, amma tabbas zuciyata akwai wanda takeso kuma take k'auna tun ina 'yar k'ank'anuwata kuma bakowa bane wannan face kai," tak'are maganar had'e da d'agowa tana kallon cikin idanuwansa, lumshe idanun yayi had'e da cewa "Dagaske kikeyi Billynah kina sona?" Jinjina masa kai tayi itama had'e da lumshe idanuwanta,


"Why? Meyasa kika bani wahala baccin kinsan da kema kina k'aunata, ko bakya tsoron zaki iya rasani" dariya tayi sannan tace "saboda ingano daraja da girman son da kake yimun ne yasa nayi haka kuma nasan bazani tab'a rasa kaba insha Allah"


"Tabbas hakane! Domin indai ina raye ke mallakina ce kuma nima mallakinkine har abada"


"Amma shine kayi k'ok'arin jefani cikin halin ni 'yaso wajen illata kanka"


"Soyayyarki tajawo hakan, amma tunda naci gari hakan bazai sake faruwa ba" 


Turo gambun k'ofar da akayi yasa gaba d'aya suka d'ago kanso don ganin ko waye, dadyne ya shigo mom nabiye dashi abaya dasu Ummi, Billy na ganin haka tabar wajen cike dajin kunyar Allah yasa basuji abunda tafad'a ba, kallo dady yabita dashi kafin ya maido kallonsa ga Mahmud cike da alamar tambaya. Sosa kansa yayi sannan ya gaishesu yana kallon ummansa dake fad'in.


"My soldier yajikin naka?" Dayake da haka take kiransa wasu lokutan "Alhamdulillah Umma naji sauk'i sosai hop dai baki tashi hankalinki ba ko?"


"Ko d'aya, ai nasan shi ciwo ba mutuwa neba, amma kuma nashiga damuwa akan abunda likita yafad'a" d'an zaro idanuwa yayi "Umma me likita yace akaina?" Sai alokacin hawayen da takasayi tun lokacin da dady keyi masu bayani cikin mota akan abunda likita yace suka samu damar zubo mata cikin kuka tace "yanzu kai yaron nan meka rasa arayuwarka da zaka zauna kayita tunanetunane har ciwon zuciya na neman kamaka, kuma kasan bazan juri rashinkaba amma kake nema ka hallaka kanka" jawota ummi tayi ajiki tana rarrashi tare da yiwa Mahmud d'in fad'a akan yadena yin hakan idan wani abun yakeso k'ara yafad'a daya zauna da damuwa cikin ransa, "ya isa haka koma meye abari yasamu lpy in munje gida naji komeye kedamunsa, son koma ka kwanta, Allah yak'ara sauk'i" dady yafad'a tare da mik'ewa, murmushi mom tayi azuciyarta tana watsawa Ummi wani kallo "kyasan abunda yake so lokacin da yafurta yana son 'yarki tilo da kike tunk'aho da ita aka aura masa yabar garin da ita" azahiri kuma cewa tayi


"Sannu Mahmud Allah yak'ara sauk'i amma ka bayyana kome kake buk'ata gidan kune kuma za'a baka kaji ko" d'aga mata kai yayi tare da kallon ummansa "kiyi hak'uri ummanah kiyafemun, in sha Allah bazan sake ba" d'an bubbuga kafad'arsa dady yai had'e da cewa "Good dt's my son, ni zanwuce office sai nadawo, ku kuma inkun gama sai Mahmud ya ajiyeku gida tunda ga k'annensa nan" yana gama fad'ar haka yanufi k'ofar fita, Bayansa mom tabi ba kunya ba tsoron Allah tana fad'in "ni yanzu zankoma muje ka sai ka ajiyeni kawuce ko?, tsayawa yayi had'e da juyowa yana kallonta "Banida wannan lokaci saboda nariga da nayi latti" yafad'a tare da ficewarsa, nan take taji duk ta muzanta da abunda yayi mata, juyowa tayi tana kallon gefensu amma sai taga gaba d'aya hankalinsu baya kanta ta Mahmud sukai, duk da ko suna jin abunda yafaru amma sai basu kula kantaba, hakan yasa takasa komawa wajen adole tafice tabar d'akin tana fita tahango su Basmah zaune ita da Batool da kuma Billy, wajen tanufa tana tambayarsu ina Nazir driver yayi ya maidata gida suka fad'a mata cewa tare suka fita da dady shi kuma yaya Mahmud baya wajen yana can yana soyewarsa da faraaharsa don ko isowarsu bai gani ba, a dole yasa takoma cikin d'akin taja kujera can gefe dasu ta zauna tana lallatsar wayarta saboda tacire mata kewa, kallonta Umma tayi ta mere baki cike da jin haushinta yayinda Ummi ko gefen da take bata kula dashi ba balle ita,


Mom na barin wajen sai gasu yaya Mahmud sun dawo saboda faraaha nason tawuce geda, murmushi tayi masu tare da cewa


"Sister's am going" Batool tayi saurin cewa


"Laa aunty faraaha gasu mom can sunzo fa,  bazakije ku gaisaba"


"Kai wlh kunya nakeji Batool, amma zanzo har gida in gaishesu"


"Ai kuwa baki isaba, dole kije ku gaisa" Mahmud yafad'a lokacin da yake k'ok'arin shafa kansa yana kallonta,


"Pls All I have wlh kunya nakeji, don Allah kabari zanzo har gida ingaishesu kaji my luv?" Tafad'a had'e da marairaice masa fuska, wayar tace tashiga ruru ta d'auko had'e da duba mai kiran taga ashe dr.Ahmad ne, har zata mayar da wayar aljihu saboda a 'yan kwanakkin nan ya matsamata da kira waishi gaskiya yagaji da zaman jiran amsar fatima yanaso tabashi address d'in gidansu yaje suyita ido da ido don ba k'aramar wahala yake shaba sai taga yaya mahmud ya k'ureta da idanuwa, saboda ta fidda kanta daga tuhumar da yake k'ok'arin yimata yasa tayi saurin maido wayar had'e da d'agawa, "Hello dr. Good morning" jin muryarta yasa dr. Ahmad ya mik'awa mamy wayar yana fad'in "mamynah amsa kirok'amun ita ta had'ani da fatima tunda ni nayi k'ank'anta da tayimun wannan alfarmar" zaro idanuwa waje faraaha tayi don tanajin duk abunda yake fad'a cike da mamakin yanda taji ya shagwab'ewa mamyn tasa murya yana magana, muryar mamynce ta katse mata tunani lokacin data daki dodon kunnenta "Assalamu alaikum 'yatah" mamy tafad'a cikin dariyar wannan rigima da Ahmad ya azamata yau akan fatimarsa.


"Wa'alaikissalam mamy ina kwana" tafad'a kamar yanda taji yakira mahaifiya tasa, "Lafiya klw 'yata ya aiki?"


"Alhmdllh mamy ya gida kowa lafiya?" Kallonsa mamy tayi yanda ya k'ura mata idanuwa yana son jin mezata fad'a tayi dariya sannan tace


"Alhamdulillah duk lafiya klw muke, yaron Abba daine yatashi da rigimar son ganin fatimarsa, nace 'yatah koda akwai wata matsalane da tasa kika hanasa addreahin gidansu yarinya" babu wata matsala mamy tunda yayan yarinyar ke sonta itama" suka jiyo muryar dr.Ahmad yana fad'a, sosai faraaha tayi dariya kafin tace


"Mamy sannu da k'ok'ari, dama haka dr. Yake?"


"Hmmm ai yafi haka 'yatah, kad'an ma kikaji, don Allah indai babu damuwa kitaimaka masa da address d'innan ko ma huta dani har ke"


"Shikenan mamy dama don kada nayi katsalandan ga alamarin yasa nabari har saina nema masa izinin yin haka awajen yayanta amma tunda yamatsa mamy bashi wayar muyi magana ko kyahuta da rigimarsa"


"To nagode 'yatah Allah yayi maki albarka kuma yajik'an mahaifa kinji" 


"To mamynmu ngd ssai" wayar mamy tamik'a masa had'e da mik'ewa tanaci gaba da gyaran d'akin da takeyi, yana karb'a yace


"Hmm ai kinga yanzu kodon albarkacin mamy kyafad'amun, wato da'in bakisan zafin so ba shiyasa kike jamun rai haka amma bakomai nagd"


"Tuba nakeyi dr ayimun afuwa, tunda dai azarb'ab'inka na nema yayi yawa to kamaza ka hanzarta kazo inanan cikin asibiti tare da fatimarka ankawo wani yayanta ba lafiya" tafad'a tana kallon Batool, gaban batool ne yafad'i don ko shakka babu tasan dr Ahmad ne d'an muskutawa tayi daga zaunen da take tana kyakkyafta idanuwa kamar marar gaskiya, shikuwa yana jin haka yayi wani irin dirowa daga kan gadon cike da farinciki yana fad'in.


"Are you serious sister faraaha?" 


Dariya tayi masa had'e da cewa ofcourse, kayi sauri don wucewa zanyi yanzu "nooo..pls bani minti goma ganinan isowa" bai jira me zataceba ya kashe wayar had'e da rungume mamy yana dariya sannan ya saketa yanufi wajen kayansa dake tsare cikin 'yar k'aramar wardrobe d'in da mamy tagama gyarawa yanzu yana fad'in mamy zo kizab'amun kayan da zansa inje in had'u da fatimatah,


"A'a da wuri haka? Ahmadidinah"


"Eh mamy tana asibiti yanzu haka yayantane ba lafiya"


"Ashsha Allah yabashi lafiya" mamy tafad'a had'e da matsowa inda yake tsaye duk ya rud'e yarasa kayan da zai zab'a yasa, d'ai d'ai yadinga ciro kayan yana watsowa kan gado mamy na tsaye tana kallonsa har saida ya kwashe kayan gaba d'aya. Dariya mamy tayi sannan tazo ta d'ago wata sky blue d'in shadda data sha aikin blue d'in zare amma mai light tayi kyau sosai tamik'a masa had'e da cewa 


"Karb'i wannan kaje kasa" karb'a yayi don dama bai dad'e da fitowa wankaba ya shiga toilet ya sanyo, yana fitowa mamy tamik'a masa wata hula mai k'ube kalar blue gaba d'aya sai d'an touch na sky blue aciki kad'an, karb'a yayi ya daidaita zamanta akansa yana kallon madubi "eyyeee ashe dai mamynah nason 'yar nan tata tak'yasa idan taga yaronta" turare mai k'amshin gaske na kamfanin oud ya d'auka ya feshe jikinsa, sannan ya sagala agogon hannunsa, d'an k'aramin glass d'insa da yake amfani dashi ya d'auko zai sawa mamy ta karb'a "kaje mata amatsayin ka na Ahmad batare da wani k'yale k'yaleba da zai d'aukar mata hankali sai yafi" black cover shoe's d'insa ya jawo tare da kakkab'esu duk da basa da wata datti yana sake gogewa da wani d'an k'aramin towel dake ajiye akan madubin sannan yasaka, kiran faraahane ya sake shigowa a wayarsa daidai lokacin daya d'ago daga sa takalumman nasa, d'auka yayi da sauri had'e da rungume mamy yana fad'in "mamynah natafi" sannan yace da faraaha "am sorry sister on my way" yafice mamy nasaka masa albarka had'e da fatar nasarar samo zuciyar fatimarsa...



 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____55💎



    Tsaye yake abakin titi yana jiran abun hawa saiga wani abokinsa khalid yana k'ok'arin karyo kan motarsa zuwa gidansu, yana hangosa tsaye ya juyar da kan motar kamar zai bugesa, da sauri yad'an ja baya had'e da d'ago hannu cikin b'acin rai, ganin motar Khalid abokinsa yasashi ajiye hannun tare da nufar wajensa, dariyar shak'iyanci Khalid yashiga yimasa had'e da yin parking gefe yafito cikin motar yana mik'a masa hannu suka tafe "dr.dr wannan irin kwalliya haka kamar wani sabon ango, sai ina" uffan dr. Ahmad baice masa ba baya ga gaisawar da sukayi, motar yanufa kawai yabud'e gidan gaba yazauna yana duba agogon hannunsa, ganin haka yasa Khalid shima ya koma ciki ya tayar da motar, sai da suka hau ka titi ya kallesa.


"Dr wai ina zuwane inata magana ka k'yaleni?" Saida ya sake duba agogon hannunsa kafin yace


"Pls kataka motarnan don Allah" 


"Intaka mota zuwa ina? Kaifa wani lokacin d'an walak'ancine!"


"Naji dai komai zakace nayarda, asibiti zaka ajiyeni emergency ake jirana!"


"Mtssss.." Khalid yayi tsaki had'e da k'ara speed d'in motar, cikin minti biyar sai gashi sun iso asibitin, kallonsa dr Ahmad yayi had'e da cewa.


"Thank you Khalid, zaka jiranine don naga alamar da akwai magana a bakinka?" harararsa yai tare da tada motar yana fad'in "Ai kuma baka isaba tunda ba drivern ka nakeba" dariya ya sakar masa har kyawawan hak'oransa na bayyana sannan yace


"Ok, muyi waya anjima" baice masa komai ba yajuyar dakan motar yabar asibitin cike da mamakin halin abokin nasa, duk dako tun suna yara suke tare ba sabon bane a wajensa.


 

Wayarsa yaciro yakira sister faraaha, bugun d'aya ta d'auka tana fad'in "Allah ka kuru, yanzun nake cewa bari natafi abuna sai nabaka lambar all I hv idan kashigo sai kuyi waya"


"To tunda gani nashigo yanzu ina zannufa don ganinki"


"Ina kallonka tun lokacin da kuka shigo, gamunan emergency" d'aga kansa yayi ya hangota tsaye ita da Mahmud. Sai wasu 'yan mata su uku agefe wanda yake kyautata zaton fatimarsa nacikinsu, tsinke wayar yayi sannan ya nufi inda suke fuskarsa cike da annuri, gabansa ne yafad'i lokacin daya kusa k'arasowa wajen ganin 'yan matan su biyu kamar su d'aya hasken fata kawai ya d'an banban tasu, kasa gano wacece fatimarsa daga ciki yayi kasancewar gani d'aya yayi mata, kuma bai wani tantanceta sosai ba, ita kanta Batool tana ganinsa taji gabanta yafad'i don tabbas ta gane dr. Ahmad d'in,


Ganin d'ayar zaune agefe kamar bata motsi da yai ita kuma sai faman nonnoce kai da mutsumutsu takeyi tana neman yanda za'ayi tasamu tabar wajen yasa zuciyarsa cinko masa ita amatsayin fatimarsa saboda yanda kunya da tsoron abunda ya had'ata dashi ranar suka hanata natsuwa, murmushi yayi lokacin daya iso idanuwansa na akanta sannan ya mik'awa yaya Mahmud hannu suka gaisa cikin girmamawa, kallon Mahmud faraaha tayi bayan sun sake gaisawa da dr. Ahmad had'e da cewa,


"All I have wannan shine dr Ahmad d'in da kaji muna waya dashi, anan asibitin yake aiki ab'an garen k'ashi, sunansa dr. Ahmad Bashar, k'wararren likitane da yasan aikinsa sosai kuma shine nayi maka bayani akan yaga sister Batool ranar da kuka kawota batada lafiya yace yana sonta" juyowa tayi ga dr. Ahmad shima tace


"Dr. Here is my luv, husband to be in sha Allah, sunansa Mahmud kuma yayan fatimar da kake so" hannu ya mik'a masa fuskarsa d'auke da farinciki yace "Nice to meet you yaya Mahmud, ya mai jiki?"


"Me too dr. Ahmad" shima yafad'a fuskarsa d'auke da murmushi "mai jiki Alhmdllh yaji sauk'i, ya aiki?"


"Alhamdulillah, ko zan iya ganinsa?"


"Sosai kuwa muje mana, my golden hope kin bani permission?" Yafad'a yana kallon cikin idanuwanta, dole kunya tasa faraaha bin bayansu itama saboda tagaida su ummi da akace sunzo duk da bata so hakan ba, tambayarta da yayi ne yasa tafahimci hakan, suna wucewa Billy ta k'yafaci Batool tana nuna su da idanuwa "ke twiny wancan shine dr Ahmad d'inki ko?" Murmushi tayi mata had'e da kad'a mata kai cikin jin kunya, rungume Basmah Billy tayi wacce tuni ta lula duniyar tunani har saida ta d'an tsorata tana fad'in "Yayya kinga dr. twiny d'ina gaskiya he's so cute" tana dariya, murmushi Basmah tayi had'e da cewa "is he cute more than yaya Mahmud d'inki?"


"Inaa yayya! Akwai banbanci sosai don yayan mu is damn cute fiye dashi ko?" Dariya tayi mata batare da tace komai ba sannan ta maida kanta ga jikin k'arfen rumfar da suke ciki zaune, ita kuma Batool cewa tayi "tab da baki fad'a don za'a rubuta maki zunubin wannan sab'on, da wud'annan k'ananan idanuwa irin na Japanese zaifi dr kyau?" Turo baki tayi had'e da b'ata fuska "Yayya kinji twiny ko?"


"Manta da ita my sister fad'a kawai takeyi, amma tasan shid'in na daban ne" dad'i Billy taji harda yiwa Batool gwalo ita kuma takafeta da idanuwa tanajin tausayinta sosai aranta, tasani duk abunda takeyi k'arfin haline kawai take don farincikin 'yar uwarta.


Cike da kunya Ahmad yashiga d'akin saboda ganin su Ummi aciki wanda ko ba'a fad'a ba yasan sune iyayensu, cikin girmamawa ya gaidasu shida faraaha sannan yadawo ga Mahmud pilot ya mik'a masa hannu suka gaisa yana yimasa ya jiki, kallonsa yaya Mahmud yayi cikin zolaya yace


"To idan angirma asan angirma don kada afara ciwo iri d'aya da 'yan k'anne, wannan sunansa dr Ahmad" kallonsu ummi yayi da hankalinsu kecen suna maganarsu sannan ya matsa ga kunnensa yace "d'an uwa wannan fa surukin kane, shine keson Batool kuma anan asibitin yake aiki" kallon gefen da mom take zaune tana dannar waya Mahmud pilot yayi shima ya rad'a masa akunne


"Kai bakaga mom zaune bane hakan, kaida ita idan tajika" juyowa yayi yana kallon mom d'in tasa don har ga Allah yazata tare da dady suka koma saboda yanda yasan halinta basa shan innuwa d'aya dasu ummi, wajenta yanufa tare da cewa mom, d'ago kai tayi tana fad'in "aw sai yanzu ka ganni" don dama tund'azu da suka shigo tacika tayi fam ganin ko kallon gefen da take dashi har bak'in daya shigo dasu basuyi ba sai faman dudduk'e kai sukeyi suna gaidasu Ummi, nan take taji duk haushinsu ya mamaye zuciyarta, bata jira mezai ceba tamik'e tana hurar hanta, "kazo ka sauke ni gida don zaman ya ishe ni haka" kallon Mahmud tayi tare da yimasa Allah yak'ara sauk'i tana juyowa idanuwanta sukaci karo da faraaha dake tsaye suna fira da Ummi da take tambaya inasu Bilal da Bassam sarakunan rigima tana fad'amata rigimar da sukayi mata kafin su fito tana dariya, saboda ta shak'u dasu sosai lokacin da Ummi tayi jinyar Bilkisu, nan take mom taji tsanarta ta dirar mata azuciya wani irin mugun kallo tabita dashi wanda saida cikin yaya Mahmud ya murd'a, sosai jikinsa yayi sanyi yadawo wajen dr Ahmad yace "dr here is our mom kaje kugaisa" yana nuna mom dake k'ok'arin ficewa cike da tsanar yarinyar da bata tab'a  ganiba akan taso wacce tafi tsana acikin zuciyarta wato Ummi. Da sauri dr Ahmad ya matsa wajen mom yana fad'in.."sannu mom ina wuni ya maijiki?" Ko tsayawa kallonsa batayi ba balle ta amsa gaisuwarta taci gaba da tafiyarta. 


Shiru yayi yana tunanin ita kuma wannan meye matsayinta a family d'in duk da yaji suna kiranta da mom, ga alama dai ga iyayensu Batool can wud'anda ya gaisa dasu daga farko, to ita wannan wacece?


Shikuwa yaya Mahmud bin bayanta yayi don bayada zab'in da yawuce yin hakan, kai tsaye bakin mota tawuce, tana isa shima ya iso wajen, hannu yasa a aljihu yaciro keys d'in motar yabud'e had'e da zagayawa ya bud'e mata gambun baya ta shiga batare da tace uffan ba sannan shima yabud'e gefen driver ya shiga had'e da tada motar yaja sukabar asibitin, tunda suka fara tafiya babu wanda yace k'anzil sai da suka hau titi daidai, gyaran murya yayi kafin yace


"Tuba nakeyi mamynah bisa b'ata ranki da nayi har ga Allah bansan da zuwanku ba, kuma lokacin da nagasu Ummi zaune nazata tare kuka wuce da dad ko kad'an ban lura dake awajen ba, natuba kiyafemun kinji momynah?"


"Shikenan, dama ni ba dakai nake wannan fushin ba, da waccan figaggiyar yarinya mara d'a'a nakeyi, kina 'ya mace kiyi tsaye gaban maza kina dariya kuma cikin tsofaffin mata don rashin tarbiya, mtssss gaskiya wanda zai aureta yana cikin takaici, gaba d'aya tsarinta keyimun ba ko kad'an" tsabar razanar da yaya Mahmud yayi da jin kalaman mom d'in tasa baisan lokacin daya taka burki ba, juyowa yayi yana kallon yanda mom ta b'ata rai sai fad'a takeyi wata irin ajiyar zuciya yayi had'e da cewa 


"Mom ai yanayin aikintane haka, itama nurse ce a asibitin dole ta sakarwa marasa lafiya tare da 'yan uwansa fuska hakan shi zai taimaka mata tayi achieving acikin aikinta"


"Koma meye hakan baiyiba gaba d'aya ni haushinta nakeji." Juyawa yayi yaci gaba da driving yana tunanin ganin faraaha da mom tayi tare da Ummi shi yayi causing wannan matsalar, "ya ilahiee" yafad'a had'e da dukan starring motar batare da yasan yayi hakan ba, muryar mom yaji tana fad'in "wai meye haka son, tukunama meyasa d'azu ka tsayar da motar nan"


"Bkomai mom kawai nayi mamakin abunda kika fad'a ne?"


"Kadena mamaki don har azuciya nakejin haushin abunnan, nidai bazan tab'a yarda ace d'ana ya auro mun irin waccan yarinyar ba!" Daga haka baice komai ba har yakai mom gida ya juyo ba abunda yake sai tunanin maganganun mom wud'anda ya tabbata basuda tushe inba zallar kishin ganinta da Ummi datayi ba.


Ita kuwa faraaha gaba d'aya ta shaga da labrin da ummi ke bata, don ma takasa sakin jiki sosai da ummin saboda atunaninta Umman borno itace mahaifiyarsu yaya Mahmud, ko kad'an batasan da zaman mom ad'akin ba sai lokacin da zata fita, anan ne taga fitarta. Taso ta tambayi ko wacece sai kuma tabari har sai Mahmud d'in da taga yabi bayanta yadawo duk da jikinta yagama bata cewa itace mom d'insa da taji yana fad'a kuma gashi taji Mahmud yakira wacce tayi tsammanin itace da Umma, nan take jikinta yayi sanyi, kallonta ta maido ga Ahmad da shima hakan take awurinsa tace


"Dr. Ni zan wuce, yaya Mahmud Allah ya k'ara sauk'i, ummi sai anjima ina gaida su Bilal"


"Faraaha har zaku wuce? To nagode sosai agaida gida"


"Zasuji in aha Allah" N5000 Ahmad yaciro ya ajiye a gefen pillown da Mahmud pilot ke kwance yayi masa Allah yak'ara sauk'i, duk suka amsa da amin, tare da yimasu godiya suna Allah shiyi masu albarka.


Suna fitowa Dr Ahmad ya kalli faraaha yace


"Sister wai waye wannan mom d'in data fita yanzu itama cikin family naau take" shiru faraaha tayi kafin tace


"Mom sunan da all I have da Batool ke kiran mahaifiyarsu, tunda har kaji all i have yakirata da mom to inada yak'ini akan itace d'ince" shiru shima d'in yayi kafin yace


"Muje inga fatima in wuce don gaba d'aya kaina yad'an kwance" murmushi tayi suka nufi inda suke zaune takirawota acan gefe, tasowa Batool tayi cikin natsuwa ta gaida dr. Ahmad kafin nan faraaha dake kallonsu tana dariya tace "to Batool yau dai gaki ga dr. Ahmad nan agabanki yazo da kansa ba aikeba, ni zan wuce sai anjima, Allah yak'ara sauk'i" batare data d'ago kanta dake duk'e ak'asa ba tace "Amin aunty faraaha Allah ya kiyaye" dr Ahmad kuwa yana jin muryarta ya nemi dukkanin damuwar da ya shiga da fargaba yarasa, murmushi ne kwance fal afuskarsa yanajinsa yau yafi kowane namiji duniya sa'a tunda gashi ga abut k'aunarsa...






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Hi you guzs, am sorry for hearing me quiet, afuwan afuwan, nakai ziyara to my family and relatives so i was so busy shiyasa bana samun damar yin typing, so kuyi hak'uri zan dinga manage ina yimaku kad'an kad'an before inkoma gida, thanks for those who message and given me a call don suji ko lafiya nake, jaxakumullahu bijannatul Firdausi, wud'an da ma basu samu damar yin haka ba amma ina ransu ngd sosai, luv all am so proud of you_💋😍💃🏼


💎Page_____56💎



    Shiru sukayi na kusan mintota kafin ya d'ago kansa yace


"Fatima ykk, ya mai jiki?"


"Alhamdulillah" tafad'a atak'aice, yayi murmushi don ganin yake kamar tafiye yanga da yawa, kuma hakan naburgesa, "ranki shidad'e gani agabanki da k'ok'on barana kitaimaka kijefomun abunda zan dogara dashi wajen ceto rayuwata, gaba d'aya kwanakinnan da kika d'auka wajen yin tunanin amsar da zaki bani a daddafe nayisu cikin shan wahala k'iris ya rage kiganni akan titi ina neman ta inda zanganki, don Allah kifad'amun matsayina domin komawa da kyakkyawan albishir awajen mamynah". Dago kai tayi tana murmushi idanuwansa akanta kafin tace


"idan har dr. zai samu ganin marar lafiyar da yake kula da ita cikin farinciki da walwala had'i da k'oshin lafiya ya kamata yasan cewa tabbas yayi nasara acikin aikinsa kuma yayi achieving goal d'insa, don haka zanyi farinciki idan har kaima kagano amsa da matsayin soyayyar ka agareni da kanka kuma shi zai tabbatarmun da cewa nawan na musamman ne" tana gama fad'ar haka tabar wajen da sauri tana dariya, dunk'ule hannu dr yayi yace "yes alhamdulillah" takowa yayi zuwa inda tadawo wajen 'yan uwansa cikin farinciki yayi nailing down agabanta batare da yaji kunyar Billy da Batool dake gefen saba yace


"Godiya nake fatima bisa karamcinki agareni, tabbas nasamu amsarki tun daga irin tarbar dana samu agareki, ina alfaharin zamowa namijin da yau yafi kowane namiji sa'a acikin wanna safiyar, gani agabanki zuciyata, rouhina da kuma gangar jikina duka nakine na mallaka makisu har iya k'arshen rayuwata amatsayin tukuicin amsar dana samu batare da shan wahala ba." Gefe gefenta ta kalla had'e da turo idanuwa tana ware hannuwanta tace


"Me kakeyi haka dr. U get what u want, so meye nayin wannan abun, baka jin kunyane halan aganeka haka, look at my siblings! they are all watching you, abeg wakeup kaji" tashi yayi yana dariya yana juyi yace


"Thank you fatima, i luv you so much" yafad'i i luv you d'in da k'arfi tayanda wad'an suma dake nesa dasu zasu iya jiyowa, kunya ce tarufeta da sauri ta tashi tanufi wajensa cikin wani shauk'i dake d'ibarta ta tace


"Pls dr..." Katseta yayi ta hanyar matsowa kusa da ita sosai had'e da kallon fuskarta yana fad'in "yes my fatima i do luv you so much, bana shakku ko haufi akan kowa yaji domin ina yimaki soyayyar da zan iya baki rayuwata tunda kema kina sona don haka kibarni inshedawa duniya cewa ni d'in nakine batare da shayi komai ba"


"Ya isa haka dr. Kanasa inajin kunya sosai, nayarda da kai d'ari bisa d'ari kuma nagamsu da soyayyarka nima ina sonka ina k'aunarka!"


"Are you serious?" Yafad'a yanaji tamkar ya rungumeta tsabar farinciki, jinjina masa kai tayi tana tabbatar masa had'e da cewa "kaga bari inje wajen 'yan uwana nabarsu su kad'ai, ina fatar kasamu kyakkyawan albiahir d'in da zakajewa mamynmu dashi kamar yanda kake buk'ata?"


Cike da soyayya yake kallonta yanaji kamar ace yau tagama zama mallakinsa ta har abada kafin yace


"A'a kada kitafi kibarni fatima, bangaji da kallon ki ba, ai nima 'YAN UWANA NE, natabbata zasu yimun uzuri subarni insamu natsuwata tare dake kona minti biyar ne, hak'ik'a kin k'ara samun matsayi azuciyata yanda naji kin ambaci mamynah a matsayin mamynki kema, darajarki da martabarki sunk'ara girma acikin zuciyata, ina sonki fatima ina sonki sosai" ganin yana nema yafara yimata sabbatu yasa tace


"Nima haka dr. Ina sonka, sai anjima ka gaida mamy" tajuya tana dariyar yanda wicked dr d'in da take tunani yakoma tamkar wani susu akan sonta, kafeta da idanuwa yayi har tabar wajen yanajin k'aunarta na ratsa dukkanin sassan jikinta. Juyawa yayi tare da ciro wayarsa yana lalabar lambar Khalid abokinsa ita kuma tanufi wajensu Billy zuciyarta cike da farincikin samun irin wannan soyayya daga wajen dr, wani shu'umin kallo Billy tabita dashi ganin yanda sai faman murmushi takeyi,


"Batool gaskiya ki rik'e gayen nan sosai domin ba k'aramin sonki yake ba, dubi yanda yake yimaki wani irin mahaukacin so, congrat sister kekam kinyi sa'ar soyayya" Basmah tafad'a itama tana kallonta, da sauri Billy tace "fad'amata yayya wlh ni har mamaki yabani, irin wannan so ko a littafin soyayya da finafinai ban tab'a ganiba ballantana a tarihin Wasu tsofaffin masoya" dariya Batool tayi kafin tace " ittaqillaha my twiny ai duk soyayya tabiyo bayan ta yaya Mahmud pilot, dubifa yanda tsabar so yasa yanemi rasa ransa, kawai kice salon sane ya burgeki don bak'arya nima ya burgeni sosai" gaba d'ayansu sukasa dariya tare da mik'ewa suka nufi d'akin da yaya Mahmud pilot yake.


Faraaha nafitowa bakin get sukaci karo da yaya Mahmud yadawo yana k'ok'arin kunno kan motar tasa zuwa cikin asibitin ransa adagule, yana ganinta ya fasa shigowa yayi reverse da motar ya daidaita parking d'insa yafito, wajenta yanufa had'e da karb'ar hand bag d'in hannunta batare da yace mata komai ba yakoma wajen motar, gidan gaba nacan gefen ya bud'e had'e da ajiye jikkar sannan yayi tsaye yana kallonta dafe da marfin gambun motar, ganin yana jiran isowarta yasa taga batada zab'in da yawuce itama tabiyo bayansa tashiga motar, matsawa kad'an yayi yak'ara bud'e mata gambun motar tashiga ta zauna sannan yarufe ya zagaya yashiga cikin motar shima had'e da tadawa sukabar wajen, atsanake yake tuk'in maganganun mom d'insa nadawo masa akai, cikin siririyar muryarta datafi  tafiya da zuciyarsa tace


"All I have lafiya kuwa?"


"Lafiya klw my golden heart" yabata amsa had'e da kallon fuskarta yana murmushi, murmushin ta mayar masa itama sannan tace


"Akwai alamun damuwa a fuskarki amma tunda bakaso nasani, ko meye ma Allah ya yaye makashi"


"Amin babynah, ina sonki"


"Nima haka sweetheart" Harararta ya d'anyi "banason wannan sweet d'in abarni a all i have d'ina, yanzu ina muka nufa?"


"Eh to da gidan qawata shamsiya naso inje" b'ata rai yayi had'e da cewa "bazakije ba, nifa banason kina zuwa ko ina inba asibiti ba koshi don yana taimakon alummahne babu yanda zaniyi saboda kada ayimun sakiyar da babu ruwa beside yau so nakeyi nafara zuwa gidanku na gaida jaddi"


"Pls.." Kafin tace wani abu kiran papi yashigo a wayarsa, yana dubawa yaga sunansa gabansa ya fad'i, kallon fuskarta yayi kafin ya d'aga wayar ita kuma tayi kamar batasan da abunda yakeyi ba, cikin girmamawa yace


"Hello papi ina wuni?" Cikin b'acin rai papi yace


"Lpy, wai mahmud yau kwana nawa da maganar mu amma har yanzu najika tsit, idan baka buk'atar zab'ina ai saika fad'amun amma ka barni cikin duhu haka, kodon banine nahaifeka ba?"


"Subhanallahi papi mekake fad'a haka,  ko kamanta annabi cewa yayi matsayin kakanni awurin jika shima iyayena? Don Allah kayi hak'uri dama d'an uwanane ba lafiya yanzu haka muna asibiti an basa gado amma insha Allah gobe zanzo sai kabani address inje, shikenan hakan yayi maka" murmushi papi yayi had'e da cewa


"Eh yayi Allah yayi maka albarka, kagaida mana da Mahmud d'in Allah yabashi lafiya, in sha Allah anjima zamuzo nida baby mudubasa" da haka suka katse wayar ita kuma faraaha da tanajin duk maganganun da sukeyi kuma tagama fahimtar akan maganar yarinyar da papi keson had'asa da itane kuma har yace gobe zaije yasa takauda kanta tana kallon gefen titi ta glass had'e da goge wasu zafafan hawaye da suka zubo mata"


"My golden.." Tayi saurin katsesa cikin muryar data tabbatar masa da hawaye kezuba daga cikin idanuwanta tace "Pls kawai kakaini gidansu shamsiya nace, basai kaje gaida jaddi ba idan nakoma zanfad'a masa kana gaishesa" da sauri ya taka burkin motar yana k'ok'arin kallon fuskarta data juyar acan gefe...


 

 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____57💎



  Faraaha! Me kikeyi? badai kuka kikeyi ba akan wannan matsalar da tun safe muma riga muka kai k'arshenta, kinsan damuwar da nake ciki kuwa akan wud'annan matsalolin duk don insamu inga cewa kud'in kin zamo tawa?, kinsan irin abunda nakeji idan naga b'acin ranki da har kike k'ok'arin sake jefani cikin damuwa?, don Allah kiyimun afuwa kitanada wud'annan tsadaddin hawayen naki har lokacin da abu mai muhimmanci zai ziyarto rayuwarmu, zuwa gano zab'in da papi yayi mani bashine amincewata ba, wlh duk duniya babu wata mace da nakeso da aure idan ba keba don haka ki kwantar da hankalinki, ina tabbatar maki da cewa ni Mahmud Bashar mai furnitures mallakin faraaha ibrahim ne har abada saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji all I have?" Wani irin sanyi taji azuciyarta dayasa nan take taji damuwa da kishin da takeji ya gusar mata, juyowa tayi tana kallonsa hawaye kwance a fuskarta yaciro handcachif fari a aljihunsa ya mik'a mata "Pls my faraah! Kigoge hawayen nan dake da matuk'ar tsada kafin kisa hannayena suyi kuskuren isa ga fuskarki don goge makisu" karb'a tayi tana murmushi had'e da cewa


"Duk tsadarsu, bazai hana kwaranyar suba idan sukaga wata katangar na neman shiga tsakanina dakai, all I have bana tunanin zuciyata zata iya jurewa rashinka domin kai haskene dake jagorantar rayuwata izuwa mafificiyar sabuwar duniyar daban tab'a shiga ba"


"Indai akan wannan ne kid'auka hasken nan yana tare dake har izuwa k'arshen rayuwarki don tare zaku rayu kuma tare zaku mutu" saurin tada motar yayi had'e da cewa "bari na ajiyeki wajen shamsiyar amma idan kika tashi komawa gida ki kirani in saukeki, don yau inaso inga jaddi shima ya ganni kafin yaturo zab'in nasa" yi tayi tamkar batasan meyake fad'a ba don tatsani maganar gaba d'aya. Sai da sukayi nisa sannan tafara kwatanta masa inda anguwarsu shamsiya take, yana ajiyeta ya juya yakoma asibiti,


Misalin karfe biyar da rabi aka sallami Mahmud pilot suka wuce gida, idan kagansa bazaka tab'a cewa shine aka d'auko da safe asheme ba, motsi kad'an idanuwansa na akan Billynsa itakuma da sun had'a ido saita sakar masa murmushi, yanzu kam gaba d'ayansu aahirye suke dasu bayyanar da soyayyarsu wajunansu kuma agaban kowa don zukatansu sun gama amincewa da surayu a inuwa d'aya, haka ta b'angaren Basmah itama yak'i takeyi da zuciyarta sosai don ganin ta manta da Mahmud pilot gaba d'aya arayuwarta kuma amatsayin masoyi tana k'ok'ari matuk'a wajen gusar da tunaninsa da soyayyarsa atare da ita.


Kusan kira uku dr.Ahmad yayiwa Khalid bai d'aga wayar saba hakan yasa ya tari okada ya hau yakaishi gida, Allah Allah yakeyi ya biyasa kud'insa yashiga gidan don yiwa mamynsa albishir, yana shiga yasamu mamy na sallar azahar, safa da marwa yashigayi kafin ta sallame fuskarsa d'auke da farinciki, tana sallamewa bai tsaya yin komai ba ya rungumeta yana fad'in "mamy albishirinki?" Tari tayimasa alamar bata gama abunda takeyi ba don ko azkar d'in da akeyi bayan salloli bai bari tayi ba, hakan yasa yayi zaune agabanta had'e da lank'washe k'afafuwansa ya zuba mata idanuwa, sosai yakusa sata dariya ganin yanda ya zubo mata idanuwa, gajarce addu'o'in da takeyi tayi had'e da tofawa a hannuwa tashafe a fuskarta, kamar yanda tayi shima yayi yana fad'in "amin mamynah Allah ya karb'a" hannuwanta yarik'o tana dariya "mamy addu'ar ki takarb'u fatima ta amsa tana sona"


"Kai masha Allah nayi farinciki, Allah yayi mata albarka kuma yasa ka dace"


"Amin mamynah, kinsan me?..." Nan ya shiga bata labarin yanda takasance tsakaninsa da Batool yana dariya hadda kwatanta mata yanda ta furta cewa tana sonsa cikin kwaikwayon muryarta tare da fad'a mata cewa tace tana gaisheta, dariya mamy tayi sosai kafin tace


"Allah sarki 'yata, ai ni yakamata nagaisheta data iya d'auke rigima irin ta d'ana" tak'arasa maganar had'e da mik'ewa ta nufi kitchen,  bayanta yabi yana cigaba da bata labrin Batool da irin tsari da natsuwar da Allah yayi mata, kai tun mamy na dariyarsa har saida tace


"Anya amadidi fatimar nan taka zaku daidaita da ita, irin wannan uban surutu haka daka tsirarwa kanka ai idan kayi matashi sai kasa kanta ciwo kuma kasan bazan lamunci hakan ga 'yata ba" hannunsa tarik'o kafin yace wani abu tadawo falo d'ayan hannun nata narik'e da warmer da plate d'in abinci, zaunar dashi tayi akan kujera tare da ajiye masa kular agabansa.


"Kadaure kaci abinci kada kasa yunwa tabiyo bayan wannan farinciki naka ta tarwatsashi" tafad'a had'e da bud'e kular ta zubo masa jalof d'in shinkafa da waken datayi da tasha bak'in busashshen kifi irin gasasshen nan, dr Ahmad da gaba d'aya yunwa ta b'ace masa yakarb'a tare da k'ok'arin sake yin magana mamy ta dakatar dashi had'e da d'aure fuska,


"Ahmad bana son wasa, maza kaci abinci, inyaso idan ka k'oshi kaci gaba da bani labarin 'yar TWA kaji ko?" Ganin yanda tayiwa fuskarta yasa yaci gaba dacin abincin yana faman murmushi, girgiza kai mamy tayi had'e da mik'ewa don takawo masa ruwa.


A b'an garen Umma da ummi kuwa tuni sunfara d'ago wani sabon al-amari tsakanin 'ya'yan nasu guda biyu wanda anan take Batool tazo tafasa k'wan gaba d'aya tana dariya, murmushi Ummi tayi don har cikin zuciyarta taji dad'in wannan alak'ar sosai haka itama Umma harda gud'a tayi tsabar tafarinciki tana fad'in



"Shikenan tuwona maina, mai abu maganin akwatsesa, Allah yakaimu lokacin buki musha shagali" tsananin kunya tasa Billy mik'ewa tabar wajen tana jifar Batool da harara ita kuma tana dariya, 


"Ina zakije 'yatah dawo kizauna abunki, babu wata kunya atsakanina dake, ni mahaifiyar kice kuma gwaggonki kar kisake kid'aukeni amatsayin suruka, don nikam nayi murna Allah yatabbatar mana da alkhairinsa"..



 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Uwa ko kuma ince mahaifiya ab'ace mai daraja dake zama ginshik'i ga 'ya'yanta idan tana raye harma da bata raye, kasancewarta itace cikakken jigon rayuwa dake d'auke da mafificiyar soyayyarta acikin zukatan dukkanin mutane aduniya yasa bazan iya wuce wannan shafiba har sai na mik'a gaisuwa ta tamusamman tare da fatan alkhairin Allah ya tabbata agareki mahaifiyata da d'auka cin tak'warorinki dake duniya wud'an da nasani da wud'anda ban saniba, matuk'ar kina d'aya daga cikin wud'anda suka albarkatu da wannan suna mafi daraja agareni wato *HAFSAT* to gaisuwar takice don kun cancanci hakan agareni dukkaninku ina yimaku, fatan Allah ya albarkaci rayuwarku yakareku aduk inda kuke, *UR DOTA LUVS YOU SO MUCH*💋❤_


💎Page_____58💎



  Bayanta Batool tabi tana dariya had'e da cewa


"Iyyee my twiny kin zama 'yar gata, mijinki yayan ki, surukarki gwaggonki, babanki kawunki, kekam wayafiki sa'ar aure? Gaskiya ba k'aramar sa'a kika taka aduniya ba" tak'arasa fad'ar haka daidai lokacin da suka shigo d'akin Billy, da sauri Billy tajawo hannun ta tamaida gambun k'ofar d'akin tarufe tana harararta had'e da cewa


"Don Allah twiny meyasa kika fad'iwa su Umma wannan maganar, yanzu ya kike so inzauna cikin gidannan dasu? Allah kinb'atamun tsari don bahaka naso ba, naso har Umma sukoma batasan da wannan zancen ba, amma gashi tsabar surutu irin naki kinsa sunsan da komai" zaro idanuwa Batool tayi had'e da rik'e baki cikin mamaki tace


"Saboda me?, to idan har basu sani yanzuba ai ko yaushene sani zasuyi, beside ai wannan abun farincikine da yakamata ace kowa yasan dashi"


"Eh hakane twiny amma ai sai nake gani kamar yayi sauri idan maganar takai kunnensu yanzu, ko yayana babu yanda baiyi dani akan cewa zai sanar da dady nace masa yabari bayanzu ba"


"Lallai to kitsaya kallon ruwa wlh su ciki don ko yaushe dady na iya had'asa da wata, ranar inaji suna firar wai dady ya had'a 'yar gidan amininsa aunty fareeda da yaya mahmud d'inmu kuma kinsan yanda suke son juna shida aunty faraaha sosai, yanzu haka yana nan abun nadamunsa, kinsan meya jamasa? To wlh nauyin bakin da tayine wajen sanar da dady yanada wacce yakeso" 


"Allah twiny?"


"Hmmm to kitambayi yaya Mahmud d'in kiji, nidai nafad'a maki gaskiya sauran ya rage naki" tana gama fad'ar haka tafice abunta ita kuma shiru tayi had'e da zaunawa agefen gado tana nazarin kalaman 'yar uwar tata.


Koda faraaha tafito gidansu shamsiya k'in kiran yaya Mahmud tayi gudun karta takurasa, rakota shamsiya tayi har bakin titi ta tarar mata adaidaita sahu tashiga tawuce gida, tana isa ta samu jaddi abakin k'ofar gidana zaune yana tilawar alqur'ani, duk'awa tayi har k'asa tagaishesa ya amsa had'e da cewa


"Malamar asibiti har adawo?"


"Eh jaddi barka da gida"


"Yawwa ya maijikin?" "Da sauk'i jaddi"


"To masha Allah, Allah yak'ara sauk'i"


"Amin" tafad'a had'i da mik'ewa, har tabar wajen tana batun shiga cikin gida jaddi yakirata, dawowa tayi ta zuk'una had'e da cewa "Gani jaddi, Allah sa dai rud'un tsufa bai fara d'ibarmun kai ba" murmushi yayo kafin yace


"Kedai kika sani, dama ina sone infad'a maki cikin satinnan yaronnan zaizo don haka kizama cikin shiri, bayan haka ina so kifad'awa shi saurayin naki da kike so yazo ina nemansa idan har da gaske yakeyi" turo baki tayi cikin jin haushin nacewar da jaddi yayi ta adole saidai zab'in nasa yazo yace


"Wai jaddi har yamzu kana akan bakanka"


"Habawa faraaha karku maidomun da hannun ago baya mana, ina kekikace kin amince yazo ko?"


"Eh jaddi, shine akansa kake cewa wai saurayina yazo inda gaske yakeyi?, yo aima duka laifinane yai babu yanda beyi dani akan yanaso yazo ya gaisheka ba nace a'a" tayi maganar cikin sigar shagwab'a har tana b'ata rai, baki abud'e jaddi ke kallonta kafin yace


"To nikuma meye nawa dakike yimun wannan sangarcin, ai da yaso tuntuni yakamata ace yasan k'ofar gidanku amma dayake da wasa yad'auki abun ai kinga bai zoba, shikenan kuma sai don nafad'i hakan yazama laifi" raurau tafarayi da idanuwa tana son tayi kuka yayi saurin cewa "to sakin rigima shikenan basai munkai ga haka ba, jeki kindaiji menace maki ko?" Mik'ewa tayi tawuce jaddi yabita da kallo zuciyarsa cike da tausayinta tunawa da yayi tataso hannunsa shida matarsa baba wacce yanzu watanta goma kenan da rasuwa cikin maraici na rashin uwa da uba, shiyasa yayi sha'awar had'ata da d'an gidan papi saboda yanda ya yarda da tarbiya da mutuncin gidansa yasan zasu rik'e masa ita amana ko bayan ransa, amma gashi ita gabad'aya takasa samun natsuwa da gamsuwa akan zab'in da yayi mata, girgiza kai yayi had'e da cewa "ya Allah kazamema wannan 'yar marainiyar yarinya gata"


Arayuwa ita zuciya batada k'ashi duk yanda mutum yakai mak'ura wajen tsananta hak'uri da juriya dole wata rana zuciyarsa tagaza takasa shanye masa wata damuwar, to kamar hakane ab'an garen Basmah koda yaushe tana kauda kai tare da b'oye damuwarta akan soyayyar da takeyiwa Mahmud pilot duk da takan fuskanci barazana sosai awajen zuciyarta saboda yanda Mahmud ke gudanar da soyayyarsa shida Billy cikin kwanciyar hankali batare da shayin kowaba don yanzu babu wanda baisan da zancen soyayyarsu ba agidan hatta dady yasan da hakan saboda lokacin daya kirasa don yabincikesa meye silar damuwarsa data sakashi cikin halin daya kaisa ga kwanciya asibiti kai tsaye yafad'a masa cewa akan Bilkisu ne, yana sonta kuma ita yakeson a aura masa, sosai dady yayi masa fad'an jefa kansa cikin damuwa da yayi sannan yayi farinciki sosai tare da tabbatar masa da cewa yabashi Bilkisu don haka yakwantar da hankalinsa, daga k'arshe dady ya had'a meeting gaba d'aya gidan kowa da kowa ya sanar dasu burin Mahmud pilot kuma ya tabbatar masu da cewa ya amince da qudurinsa don k'ara dank'on zumunci duk dako bai tuntub'i ta bakin Billy ba yaji tana sonsa ko bata sonsa nan take ya amince da hakan d'ari bisa d'ari, kowa yayi farinciki da murna da jin wannan labari, baranma masoyan guda biyu dakeji tamkar suzama tsuntsaye sutashi sama tsabar farinciki hatta ita kanta Basmah lokacin tanuna farinciki da jindad'inta har cikin zuciya tare dayi masu fatan d'orewa cikin k'auna da soyayyar junansu har abada, sosai yaya Mahmud da Batool suka tausayawa 'yar uwarsu saboda ganin yanda tatirsasawa zuciyarta hak'ura da abunda takeso aduniya don d'orewar farincikin 'yan uwanta, misalin k'arfe biyu na dare wabi irin matsanancin ciwon zuciya yatada Basmah cikin bacci saboda yanda take matsawa zuciyarta akan saita hak'ura da abunda Allah yariga yad'ora mata sonsa, tun tana hak'uri har kuka yafara cin k'arfinta hakanne yayi sanadiyar farkawar Batool daga nannauyan baccin daya dad'e da d'ibarta a firgice ta tashi jin yanda 'yar uwar tata ke kuka, rungumota tayi cikin tashin hankali tace " yayya Basmah lafiya kuwa?" Saiti zuciyarta tashiga nuna mata cikin kuka tana cewa "zan matu sister, wani irin ciwo nakeji azuciyata" tasake fashewa da kukan, 


"Innalillahi wa inna ilaihirrajiuun yayya Basmah don Allah kidena fad'ar haka, bazan iya jurewa ba yazama dole infad'awa dady matsalarki asan yanda za'a maganceta, nagaji da kallon bak'in k'arfin halin da kikeyi kina cutar da kanki bayan inada masaniyar inda za'a samo maganinta" rumk'e hannunta tayi sosai kafin cikin k'arfin hali yace


"Batool wlh babu abunda kedamuna, ciwone kad'ai Allah yajarabceni dashi kada tunaninki yakaiki ga abunda bashine ba.." Shiru tayi sakamakon tarin daya tirnik'eta tana kuka cikin lokaci guda saboda yanda ciwon zuciyar ya tsanan tarmata, kuka Batool tafashe dashi tare da ficewa tanufi d'akinsu yaya Mahmud saboda mom na part d'in dady. Nocking biyu tayi saiga yaya mahmud yazo yabud'e mata k'ofar bayan yatambayi kowaye tafad'a masa itace,


"Yaya kazo yayya Basmah batada lafiya kuma mom na part d'in dady" bai tsaya wata wataba yafito tare da bin bayanta cikin tashin hankali, suna shiga d'akin suka isko Basmah asheme, jijjigata mahmud ya shigayi amma yaga bata motsa ba da sauri yaje ya d'auko ruwa a fridge ya yayyafa mata afuska, saida yayi hakan kusan sau uku sannan tafarfad'o daga sumar datayi tana ganinsa tarungumesa.


"Yaya zanmutu, kuyafemun duk abunda nayi maku" tanarike da saiti zuciyarta dake yimata wani irin azababben ciwo, agogo yakalla yaga dare yayi sosai balle ya kaita asibiti, wayarsa yasa Batool taje takarb'o masa wajen yaya mahmud pilot saboda Haba d'ayansu basuyi bacci ba zaune suje suna firar bankwana saboda gobe zasu koma borno shida Umma, tana zuwa karb'o wayar yake tambayarta ko lafiya nan tasanar dashi yayya Basmah ce batajin dad'i  hakan yasa shima yabiyo bayanta suka dawo tare kuka takeyi sosai yana rarrashinta gaba d'aya yarud'e yarasa ta ina zaifara da wannan matsalar don dagashi sai Batool suka san halin da Basmah keciki akan soyayyar d'ana uwansu da baisanma tanayi ba, suna shigowa yakarb'i wayarsa yakira faraaha saida tayi ringing sau kusan biyar ta tsinke saboda baccin da takeyi kafin can yasake kiranta.


Cikin magagin bacci ta d'auki wayar had'e da sawa akunnenta, yanajin muryar all I have d'inta kuma da alama cikin tashin hankali yake tamik'e zaune da sauri a tsakiyar gadon. "All I have lafiya?"


"Lafiya klw faraaha don Allah kitaimaka kiyo mun text d'in magungunan ciwon zuciya masu kyau yanzunnan Basmah ce balafiya yace zuciyarta keciwo gashi dare yayi ballantana nakaita asibiti"


"Subhanallahi ita kuwa meyajawo mata wannan matsalar da k'ananun ahekaraunta?"


"Abeg faraaha wannan balokacin yin tambaya neba da amsarta ina jiranki yanzun kituromun"


"Ok" tafad'a tare da tsinke wayar tarubuta masa magunan da sauri ta tura masa, message na shigowa ya rik'o hannun Batool yamik'e tsaye tare da zaunar da ita inda ya tashi ya d'ora mata Basmah ajikinta yace


"Batool kikula da ita kina tofa mata addu'o'i bari naje nasamo mata wud'annan maganukkan" ficewa yayi pilot nabiye dashi suka nufi bakin gate, 


"Dan uwa inazakaje awannan tsohon daren" mahmud pilot yafad'a yana kallonsa, 


"Baka ganin 'yar uwata batada lafiya ne, kome tsananin dare aidole nafita nanemo mata magani"


"To mezai hana mu d'auki mota mukaita asibiti ai ina ganin zaifi ko?" Jiyowa yayi ya kallesa kafin yace


"Babu buk'atar haka d'an uwa domin banaso su dady susan abunda kefaruwa har sutashi daga bacci, kaga muntayar masu da hankali akan matsalar da zamu iya solving d'inta, idanu zaka iya fita acan bakin titi zanje akwai wani chemist anan innemo mata magani" ganin mahmud naneman jefo masa wata tambayar lokacinsa nak'ara b'aci yasa tayiwa maigadi knocking yace yabud'e masa k'ofa zai fita....



 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


.👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_ 



💎Page_____59💎



  Da sauri malam habu yataso yabud'e k'ofar d'akinsa don dama ba bacci yake yiba zaune yake yana jiran kota kwana, yana ganinsa yace


"Ranka ya dad'e ko lafiya?"

 

"Lpy klw malam habu bud'e mun k'ofa" yaya mahmud yafada yana k'ok'arin maido kallonsa ga mahmud pilot daya d'oro hannunsa akan kafad'ar sa, e


"'Dan uwa kada kafita, kabari mud'auko mota mukaita asibiti i think dis is the solution"


"Noo..k'ara tasamu  taimakon gaggawa tunda abunda sauk'i inyaso idan baiyiba da safe sai muje asibitin" yana gama fad'ar haka malan habu nabud'e k'ofa, bai jira yaji amsar da zai basa ba yabar wajen, hakan yasa shima yabi bayansa duk dako ba hakan yasoba amma bayada zab'in daya wuce yabi bayan nasa. Malan habu yaso bin bayansu shima amma mahmud ya  dakatar dashi akan yazauna bakin aikinsa tunda yaga su biyune in sha Allah babu abunda zai samesu har suje su dawo, dole Mlm habu ya hakura bakinsa d'auke da adduar Allah yakaresu zuciyarsa nayaba k'ok'arin yaya mahmud akan kulawa da soyayya da yake yiwa 'yan uwansa, komai yataso akansu zakaji yana fad'in 'YAN UWANA NE cike da shauk'i da soyayyayaw da zai tabbataar maka da muhimmancin da suke dashi aransa,


Tafiya sukayi sosai kafin sukai babban titin da acanne suka sami wata babbar chemist kuma da alama akwai mutun aciki duk daba abud'e takeba, d'an k'wank'wasawa sukayi kusan sau uku kafin can suji muryar wani inyamuri yace


"Pls waye anan wurin"


"Am srry sir munzo sayen magani ne" abunka da inyamuri da son kud'i bai tsaya wata wata ba yabud'e, sunan maganin ya fad'a masa had'e da mik'a masa kud'in yakarb'a, maganin ya d'auko yamik'a masa yana fad'in


"Thank you sir" karb'a sukayi suka nufi gida cikin sauri suna shiga malam habu yamaida k'ofar ya kulle kamar yanda take, suna shiga part d'in kai tsaye suka shiga d'akin tananan kamar yanda suka barta har Batool d'in natayata kuka, maganin yayi shaking saboda na ruwane, sannan yabud'e yasa Batool ta d'agowa masa kanta yabata tasha dama har bayanin yanda za'a shasa Faraaha ta turo masa, bayan tasha Batool ta ajiyeta akan gado tashiga toilet shikuma yadawo gefen gadon wajen kanta yana shafawa ahankali tare da yimata sannu, Mahmud pilot dake tsaye bakin k'ofa shima k'arasowa yayi cikin d'akin yana jero mata sannu, da kai ta amsa masa had'e da rufe idanuwanta har ya gaji da tsayi yakoma parlour ya zauna shikuma yaya Mahmud nan yayi zaunensa har saida yaga bacci ya d'auketa sannan yamik'e yana kallon Batool dake can gefenta zaune idanuwanta sunyi jawur hadda d'an kumburowa sunyi kad'an saboda kukan datayi yace


"Kinemi wuri kikwanta kema kafin akira sallar asuba tunda itama baccin ya d'auketa kinji ko?"


Ahankali tad'an mirgina kad'an daga inda take zaune ta kwanta saiti kan Basmah fuskarta na kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tayi, da k'yar take fitar da lumfashinta don bakad'an taji jikiba, kallo yabita dashi yanajin wani irin tausayinta aransa, yanaji badon ita da Billy duka 'yan uwansa bane da yabayyana matsalar dake damunta ga iyayensu ko tadena shan wannan wahalar haka amma idan yayi hakan bak'aramin sonkai ya aikata ba, furzar da iskan yayi ahankali ta bakinsa had'e da cewa "Allahumma yassir wala ta'assir" sannan yafice daga d'akin, shima palourn yadawo yanemi waje ya zauna yana tunanin matsalar dake bibiyar rayuwarsa shida 'yar uwarsa ta b'angaren soyayya, kallon Mahmud yayi dake zaune ya dafa kafad'arsa had'e da cewa


"'Dan uwa kaje ka kwanta, tasamu sauk'i don har bacci ya d'auketa" sai da safe sukayi yawuce shikuma yayi kwancensa nan palourn batare da yadamu da komawa d'akin saba.


Kasancewar bai samu yin bacci sosai ba yasa da baccin ya d'aukesa har aka gama sallar asuba bai farkaba, sosai dady yayi makin rashin ganinsa masallaci shiyasa lokacin da suke dawowa ya tambayi yaya Mahmud pilot ina d'an uwansa yake abbai ganesa masallaci ba, nan yake sanar dashi abunda yafaru jiya k'ilan shiyasa baccin yayi masa nauyin shima badon dadyn yayi masa knocking ba kafin yatafi da bai samu sallar ba, "Ashsha" dady yafad'a tare da nufar part d'in yana fad'an meyasa basu taddo shiba. Suna shiga suka samesa palour yana sallah, ganin haka yasa dady yawuce d'akinsu Basmah shikuma Mahmud pilot yayi zamansa parlour wajen yaya Mahmud, koda yashiga yasamu Batool har ta sallame sallah da alama ita d'inma tamakara ita kuma Basmah na kwance kan gado, zauna wa dady yayi tare da shafa fuskarta ahankali yana tambayar Batool meke damunta, nan ta sanar dashi cewa ita dai bata saniba kawai dai taga tarik'e zuciyarta tana kuka tace ciwo take yimata, ajiyar zuciya dady dake kallonta ya sauke yana fad'in


"Ciwon zuciya kuma?, Allah ya sawak'e dole idan safiya ta ida wayewa muje asibiti kenan!" Basmah da alokacin tafarko tana bud'e idanuwa a hankali taji abunda yafad'a ta tattaro k'arfinta gaba d'aya tamik'e zaune tana fad'in "a'a dady basai munjeba nasha magani kuma naji sauk'i sosai" k'ura mata idanuwa yayi tare da mik'a hannunsa ya d'auko maganin da yaya mahmud yasawo jiya dake ajiye akan bedside wardrobe yana duba sunannsa, d'ago kai yayi yana kallonta kafin yace


"Basmah meye dalilin wannan ciwon nak?, a wud'annan shekarun da kike dasu bai kamata ace kinada ciwon zuciya ba"


"Dady daga Allah ne shike jarabtar bawa da ciwo aduk sadda yaso komai girman sa ko k'ank'antarsa kuma batare da yana da damuwar komai ba, dady kamanta shi ciwon zuciya hatta jarirai akwai wud'anda ake samunsu dashi lokacin da aka haifesu?" Shiru yayi yana nazarin kalamanta kafin yarik'o hannunta yace


"To meyasa bakyason kije asibitine" yayi maganar cikin damuwa da nuna kulawa sosai ganin haka yasa tak'ak'aro murmushi a fuskarta sannan tace


"Saboda alhamdulillah dady naji sauk'i sosai da taimakon yaya mahmud" rik'e hannunsa tayi tana dariya sannan taci gaba da cewa "dady kayiwa Allah godiya daya baka yaya Mahmud amatsayin d'a kuma magaji natabbata zai kula damu acikin kowane hali batare da yabari kashiga damuwaba"  duk wud'annan abubuwan da takeyi cikin Mugun k'arfin haline don kada hankalin kowa ya tashi kuma batason aje asibiti har likita yanemi fayyace sirrin da take b'oyewa tarusa farincikin 'yan uwanta amma ita kad'ai tasan yanda takeji da kuma halin da take ciki sai Allahnta. Hannunsa yasa yajawo kanta ya d'ora asaman kafad'arsa yana fad'in


"Tabbas nasan Allah ke kawo ciwo gabawansa kuma nayi imani da hakan amma idan akwai abunda yake damunki kifad'amun ko dukiyata zata k'are duka matuk'ar bazaki cutu ko wani ya cutuba akansa nayi maki alk'awarin zaniyi makiahi kinji ko?" Wasu zafafan hawayene suka zubomata a fuska tayi saurin gogewa had'e da cewa 


"Dady kayi mana komai aduniya baka barmu da matsalar kome ba, hatta yayan da zai iya kula damu kamar yanda kake yimana kabamu, to meye zai kuma dameni aduniya?, addu'arka kad'ai nake buk'ata nida 'yan uwana akan Allah yabamu ikon yimaka biyayya da kuma faranta maka kamar yanda kayimana har iya k'arshen rayuwarmu"


"Nasani Basmah ko bana duniya yayan ku zai kula daku fiyema da yanda nakeyi, addua kuma akoda yaushe ina yimaku, amma ina tsoron ko akwai wani sakaci danayi har wata damuwa tayi kuskuren isowa acikin rayuwarki shiyasa nafad'i haka amma tunda babu matsala alhamdulillah Allah yak'ara maki lafiya"


"Amin dady bari inje inyi sallah" tamik'e da k'yar har tana shirin fad'uwa wajen saukowa daga kan gadon, Batool ce tayi saurin rik'eta had'e da cewa


"Kiyi ahankali yayya kinsan jikinki baiyi k'wari ba" rik'ata tayi ta sauko kan gadon tarakata har toilet shikuma dady yana kallonsu cike dajin dad'in yanda suke ba 'yan uwansu kulawa, saida yaga fitowarsu sannan yabar d'akin ya koma parlour inda su yaya mahmud ke zaune, zaunawa yayi akan kujera mai zaman mutun d'aya yaya mahmud yataso a inda yake zaune yana gaida dadyn, sun jima suna tattaunawa akan matsalar ciwon Basmah tare da tunanin abunda yajawo matashi amma ko kad'an yaya Mahmud bai bari yabada wata alama da zata nuna cewa wai don tana son Mahmud pilot bane daga k'arshe dai dady yayarda cewa ciwon Basmah daga Allah ne kuma yana fatar Allah yabata lpy.


Part d'in Ummi yanufa yasanar masu da halin da Basmah keciki, sun matuk'ar tausaya mata sannan ya fice zuwa nasa part d'in, Billy kuwa tun kafin yagama fad'a masu tabar wajen tanufi part d'in mom cikin sauri fuskarta d'auke da damuwa, tuna abunda yafaru ranar da taje ganinta ita da mom da basa da lafiya yasa Ummi datayi saurin mik'ewa da zimmar zuwa ganota takoma tazauna, kallon Umma tayi dake tsaye itama don da atare suka mik'e zasu tafi idanuwanta nahawaye don har ga allah ta tausayawa Basmah sosai tace


"Ummansu kigaishemun da Basmaty Allah yabata lpy kuma ya yaye mata wannan lalurar"


Dady kuwa na isa part d'insa ya kalli mom dake cire bedsheet d'in dake kan gado tana shimfid'a wani ya kira sunanta had'e da mik'a mata hannu alamar tazo, murmushi tayi masa tare da ida gyara gadon sannan tazo inda yake tazauna tare da gaishesa, rik'o hannunta yayi yana d'an murzawa ahankali yana kallon fuskarta kafin yace


"Kintashi lafiya Momyn mahmud?"


"Lpy klw" tafad'a tana duk'ar da kanta k'asa don baitab'a kiranta da wannan sunanba sai yasa taji kunyarsa


"madallah amaryar dady kar dai kice kunyar wannan suna kikeji?" dariya tayi batare data amsa masa ba don indai salon soyayyane dady yakai k'arshe awajen bazata iya ja dashi ba, muryarsa tajiyo yaci gaba da cewa


"To ki ajiye kunyarnan agefe kije ki dubomun 'yatah Basmah batajin dad'i, ashe jiya da daddare gaba d'aya basuyi bacci ita da 'yan uwanta muna nan bamu san abunda kefaruwa ba, a gaskiya ina tunanin zanfara biyar kowacenku part d'inta saboda kula da yaranmu domin wannan nisanta kanmu da mukayi dasu don inganta tarbiyarsu zai iya cutar mana dasu, don ma Allah yasa yayan nasu na kusa aida muntarar da abunda bama so yau da safe" gaban mom ne yayi saurin fad'uwa jin 'yar tata ba lafiya had'e da mik'ewa cikin firgita, saurin rik'o hannunta yayi yace


"Relax ai yayanta natare da ita kuma alhamdulillah tasamu sauk'i, kitafi ahankali karkije idanuwanki surufe kijiwa kanki wajen sauka k'asa kinji ko?" d'aga masa kai tayi tanaji kamar ta k'wace hannunta daga rik'on daya yimata saboda yanda tamatsu taje taga halin da 'yar tata keciki, yana sakin hannunta tabar d'akin, da sauri da sauri take saukowa daga upstairs d'in sannan tanufi part d'inta, tana kawowa zata shiga part d'inta sukaci karo da Billy, wata uwar harara ta zabga mata itako Billy yi tayi tamkar bata ganeta ba tashige abunta, d'akin 'yan uwanta tanufa kai tsaye mom nabiye abayanta tana shiga tayi kan Basmah dake kwance kamar zatayi kuka "Yayya Basmah yajiki? Ashe bakyada lafiya, wayyo yayyatah sannu kinji" tafad'a tana d'ora hannunta akan fuskarta, itama Basmah hannunta ta d'ora akan nata tana murmushi "my sister naji sauk'i wannan irin rud'ewa haka da kikayi har ina, ni kwantar da hankalinki am ok kinji ko?, inasu Ummi lafiya suke"


"Lafiya klw, yayya dole in rud'e mana 'yar uwata balafiya tun jiya banjiba sai yanzu, bana son ganinku cikin halin ciwo ko damuwa wlh sai inji tamkar in maidosu akaina, ina sonku 'YAN UWANA NE ku dabanida tamkarku aduniya ina..." ai kafin tarufe baki taji andamk'o hannunta had'e da fizgota lokaci d'aya anjayeta daga kan gadon, tana d'agowa sukayi ido biyu da mom ta b'alla mata harara, "wannan wace irin takura ce yarinya ba lafiya kinzo kintasata agaba sai surutu kike yimata sai kace aku...mtsss dalla jaye kibani waje ai wannan dak'ik'anci ne" jayewa gefe tayi ita kuma ta zauna gefen gadon ta d'ago Basmah tarungume ajikinta tana yimata sannu, daga Batool har Basmah saida ransu yab'aci akan abunda mom tayiwa 'yar uwarsu, hawayene suka zubowa Basmah lokacin dataga Billy nak'ok'arin fita idanuwanta cike da k'walla ta kalli mom tace


"Meyasa mom?" 


"Srry dota yajikin naki?"


"Naji sauk'i tafad'a" tare da kauda kanta gefe ita kuma Batool da sauri tarik'o hannun Billy tana dariya "laa kinga halin mom idan yayya Basmah batada lafiya duk sai tabi tarud'e tayita fad'a da mutane tamkar mu muka azo mata ciwon, shiyasa nake k'orafi kullum akan tafi son yayya Basmah dani, zo muhau tacan gefe karta had'a mana da duka" tajata suka hau kan gadon acan gefe dayake k'aton gadone irin family d'innan, murmushi Billy tayi tana goge hawayen da suka zubo mata don ba kad'an irin wannan wayon da twiny d'inta tayiba yabata dariya wai duk don tafaranta mata tahanata jin haushin abunda mom tayi mata ba, hakan yasa itama tadanne zuciyarta don tayi masu yanda sukeso wato gusar da damuwarta tace


"Ayya mom Kiyi hak'uri in sha Allah yayya zata warke, nida twiny kuma zamukai k'ara wajen dady tunda aka fifita yayya akan my twiny ko twiny?" Tak'are maganar tana kallon Batool, "k'warai kuwa my twiny haka za'ayi dole mom ta amsa quarry a wajen dady" gaba d'ayansu dariya sukayi hadda Basmah dake rungume ajikinta tace


"Kinjisu ko mom, ashe tare nake da 'yan partyn adawa ban saniba?" Rungume ta tayi sosai taci gaba da cewa "Momynah ink'ara sona sosai kinji?" Mom data b'ata rai bata san lokacin da dariya ta kucce mataba, wato ita zasu linkewa don farincikin 'yar uwarsu, murmushi tayi tare da hugging back d'in Basmah tace


"Zan kuwa soki sosai akan kowa tunda ke nafara gani", d'ago kai tayi had'e da cewa


"Mom shifa yaya mahmud d'inka?" Saida ta d'aure fuska sannan tace "nabarwa dadynku da matarsa" ko kad'an wannan dasu har Billy bai tab'a ransuba saima cewa da sukayi kamar sun had'a baki  "aikuwa sun gode" suna dariya sallamar Umma da suka jiyo a parlour tasasu tsagaita dariyar tare da amsawa tana shigowa cikin d'akin mom tajanye Basmah daga jikinta tamik'e tabar d'akin batare da takalli ko inda Umma takeba, takowa bakin gadon tayi tana kallon Basmah da gaba d'aya tad'an zurma yace "'yatah sannu ya jikin naki?" Saida ta gaisheta sannan ta amsa mata da cewa jiki da sauk'i, bakin gadon Umma tazauna tana kallonsu Batool dake gaisheta tace "lafiya klw 'yan tagwayen Ummi, kuna nan kuna jinyar auntynku ko?" 


"Eh Umma" 


"To masha Allah, Allah yayi maku albarka, kurik'e junanku sosai kuma kowannenku yaso d'an uwansa fiye da yanda yake son kansa hakan zai k'ara maku dank'on zumunci kunji ko?" Haka ta dinga yimasu nasiha sosai don tana matuk'ar k'aunar 'ya'yan d'an uwan nata aranta, tajima d'akin kafin tayi masu sallama don zuwa anjima zasu wuce borno idan maigidanta dubai amince da suk'ara kwana biyu ba, saboda tayi tunanin barin tafiyar sai jibi saboda wani dalili tana jiran feedback daga wajensa.


Alhamdulillah jikin Basmah yayi sauk'i sosai don tana samun kulawa takowane b'angare hatta Billy yau yini tayi ad'akin nasu duk da yanda mom ked'an takurata hakan baisa tayi zuciyar tafiyarta ba, haka babu yanda Mahmud pilot baiyi da itaba akan yanaso sud'an keb'e yayi missing d'inta amma fir tak'i amincewa daga k'arshema kwancenta tayi takwana anan, iya jin haushi Mahmud yaji haushinta don shikam da gaske he badly missing her, haka yakwana yanata faman tsuki duk da yaji dad'i da alhajinsa ya amince suk'ara kwana biyu amma bakad'an yasamu damuwar rashin keb'ewa da masoyiyar tasa ba, yayi maya takai sau tara part d'in da sunan ganin Basmah amma azahiri Billynsa yake zuwa gani da sun had'a ido yayi mata alama tazo saita mak'e masa kafad'a tana dariya har yagaji ya hak'ura don kansa, 


Da safe haka yadinga ciccin magani waishi alatilas fushi yakeyi akan abunda tayi masa ko wanka yakasa tashi yayi, shikuwa yaya mahmud yana fitowa wanka ya kallesa had'e da cewa "d'an uwa pls don Allah kataimaka karakani wajen papi inkarb'o address d'in zab'innan tasa ko nasamu nahuta da wannan naci nasa haka" tsaki yayi masa had'e da cewa


"God forbid babu inda zanje, kaje kai kad'ai, k'asan halin danake ciki kuwa zakazo kadameni?" Idanuwa yaya mahmud ya zuba masa cike da mamaki don tunjiya yalura da garasan da k'anwarsa keyi, murmushi yayi had'e da cewa


"Allah yabaka hak'uri, kumburi ga doki sakkiya ga jaki? Kada kaje d'in ai yau gareka gobe ga d'an uwa" yana gama fad'an haka ya gyarawarsa tsaf batare daya sake kallon inda yakeba, motarsa ya d'auka yaje gidan papi yakarb'o address d'in gidan jaddi sannan yadawo gida, yadad'e zaune yana tunanin mummunar shigar da zaiyi yaje gidan jaddi don ganin yarinyar saboda tace bata sonsa. Murmushi yayi saboda wata mafitar daya samu cikin sauk'i nan take yaji hankalinsa ya kwanta, wayarsa yaciro yakira faraaharsa da bata dad's da gama kumbure fuskaba saboda fad'a mata da jaddi yayi tagyara yau zuwa la'asar bak'on daya fad'a mata zaizo cikin satinnan to zaizo yau, firarsu suka sha ta soyayya suka faranta zukatan junansu batare da kowanenau ya bayyana halin da yake cikiba, suna kammala wayar faraaha tayi kwance akan katifar dake d'akinta tarufe idanuwa tana tunanin mafita akan had'uwarta da zab'in jaddi, wata irin dariya ta kwashe da ita had'e da cewa "yes" sannan tamik'e zuwa tsakar gida taci gaba da aikace aikacenta tana rera 'yan wak'ok'inta hankali kwance don ita kad'ai tasan muguntar data shiryayi anjima,..


 



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____60💎



      Cike da mamaki jaddi ke kallonta saboda bata dad'e da barin wajenba tana kumbure kumbure akan yayi mata maganar zuwan bak'on nata, amma abun mamaki cikin mintota kad'an sai gashi tadawo masa cikin fara'a da jin dad'i, tunanin dalilinta nayin haka yafarayi ganin bayada amsa yasa yaci gaba dayin abunda ke gabansa batare daya damu da hakan ba, 


Mahmud pilot kuwa yana fitowa daga d'akinsu yanufi part d'in Ummi cike da damuwa, Billy ya hango tana tahowa daga part d'in mom yayi saurin b'oyewa gefen k'ofar shiga palourn yana jiran isowarta, tana zuwa ya tare bakin k'ofar had'e da kafeta da idanuwa, murmushi tayi tarab'a ta gefensa zata wuce yasake tareta, dariya tayi had'e da folding hannuwanta akan k'irji ta jingina ajikin bangon dake rik'e da k'ofar tana kallonsa, shima hakan yayi ad'ayan b'angaren bangon yana faman ciccije fuska, sunfi k'arfin minti biyar ahaka batare da kowanensu yace uffan ba, ganin haka yasa tasake yunk'urawa da zimmar shigewarta yayi saurin nufowa inda take, ja tadingayi da baya shikuma yana matsowa har saida takoma jikin bangon, hannuwansa yasa ajikin bangon yayi mata rumfa yana binta da kallo kafin yace


"Meyasa!?.meyasa kikayi haka? Billynah halama Bakya tausayina ne? Shin ko kinsan gaba d'aya jiya ban samu bacci ya d'auke niba ko kad'an saboda d'ai rashin jin zazzak'ar muryar nan taki?, shin kinsan kuwa irin halin da nashiga adaren jiya saboda rashin abincin zuciyata da kika saba bata amma kika hanata? Haba qanwata kinsanfa dad'ad'an kalamanki sune ke qarawa zuciyata nagartabda k'arfin iya rik'e gangar jikina, k'iris kad'an yarage jiya kisa inyi dying saboda kinbar zuciyata da yunwa har tayi raunin da bazata iya rik'eni ba, badon idanuwa da suka taimaka mataba wajen kusanto mata da wannan kyakkyawar fuskar takiba da bansan makoma taba adaren jiya" tunda yafara magana take kallon cikin idanuwansa har ya dasa aya, lumshe idanuwanta tayi had'e da cewa


"Dagaske kake?" K'ara matsowa yayi a kusa da ita sosai tayanda zata iya jiyo sautin bugawar zuciyarsa shima d'in yana kallon cikin idanuwanta yace "baki yarda bane 'yan mata?" Yanda tagansa very close da ita yasa gabanta yashiga bugawa da sauri da sauri, zillewa tayi ta gefensa a k'ark'ashin hannunsa tashige palourn da sauri, juyowa tayi tana murmushi tare da kad'a kanta tace.


"Sosai nayarda don nima hakanne tab'angarena, karka damu domin nid kai tagwayen junane, kasa aranka tare zamu rayu kuma tare zamu mutu in sha Allah" d'ago kai tayi takallesa daga can cikin palourn tayi dariya sannan tawuce zuciyarta cike da k'aunar yayan nata


Nan take Mahmud yaji wani irin farinciki marar misaltuwa yarufesa, aransa yanaji babu abunda zai rabasa da Billynsa inba mutuwa ba domin tagama tabbatarwa da zuciyarsa itama tana sonsa tana k'aunarsa kamar yanda shima yakeyi, Nan take yayanke shawarar suna komawa borno zai sanarda alhajinsa azo atsaida magana tare dasa rana don bazai koma wajen aikin saba har sai yagama mallakarta amatsayin matarsa.


Bayanta yabi shima ya shigo palourn ya tadda Bilal da Bassam suna homework da aka basu a makaranta da taimakon Ummi dake zaune tana nunnunamasu shikuma junior yana gefensu shima sai gwalaje yakeyi awani extra buk daya tsira rigima Ummi tabashi saboda tasamu yabarsu suyi home work d'in cikin kwanciyar hankali, bakinsa d'auke da sallama ya k'araso cikin palourn fuskarsa ba yabo ba fallasa ya gaida ita cikin natsuwa yana kallon k'annen nasa dake faman gaishesa suma, amsawa tayi had'e da tashi tabar wajen don itakam kunyarsa takeji yanzu abunka ga fulani, dariya Umma dake fitowa daga kitchen tayi tana tsokanarta "dama kindena jin wannan kunya don andad'e da dena yayin haka banda abunki ai Mahmud d'an d'an kine tunda ahannunki aka haifesa kuma ke kikayi yayensa fitsarinsa da kashinsa babu wanda bakiciba, to meye najin kunyarsa yanzu? Zaifi maki sauk'i ki ajiye sarakutar agefe kibarshi amatsayinsa na d'anki" murmushi d'ai Ummi tayi batare data tanka mata ba tawuce d'aki abunta ita kuma tana tayimata dariya, shikansa dariyar yakeyi jin yanda tabud'ewa Ummi wuta yace "Kai ummanah"


"Eh mana, nifa ba wata kunya kaida Bilkisu duka kallon 'ya'yana nake yimaku don kasani baka fitaba awajena" 


Game girarsa ta sama data k'asa yayi yana kallon k'ofar d'akin Billy da itama tana can tana dariyar maganganun Umma yace


"Ummanah don Allah kidena fad'a kada taji tarenani" basar dashi tayi ta mik'awa su Bassam goldenmon da madarar  data had'o masu a kofuna, saida tazauna sannan tarik'e hannunsa "Meya kawo maganar raini Mahmud indai ba tsanani tsakaninku, ai tausayawa da kulawa da juna cikin rayuwar auratayya ita kesa mata girmama mijinta, bawai girmansa ko d'aure fuskarsa ba ko fifikon matsayi ko kuma cutawa ba" hannunsa yasa ya rumk'e na Umma had'e da cewa "Ummana da wasa nakeyi taya zan iya nuna duk wud'annan abubuwan ga 'yar uwata, jinina kuma wacce nafiso akan duk abunda zai iya zamowa mallakina aduniya, ai kisa aranki soyayyar da nake yiwa 'yarki bazata bari natab'a cutar maki da itaba, wannan alk'awarina ne" murmushi Umma tayi tare da shafa gefen fuskarsa "Mahmud matuk'ar ka aikata haka kuwa zanyi alfahari da samunka amatsayin d'ana har iya k'arshen rayuwata, kuma zanzamo mai saka maka albarka fiye da albarkar da kowace uwa kesawa d'anta aduniya" rungumeta yayi yana fad'in 


"Allah yabani iko ummanah, ina sonki sosai"


Yajima a part d'in Ummin kafin yatashi ya nufi part d'in mom don dubo jikin Basmah, yana fitowa ya d'auki motarsa yafice daga gidan, saida yabiya banki ya ciro kud'i sanna ya tsaya daidai wata arniyar plaza da taji komai na buk'atar rayuwa, gefen cosmetic da turarukka yanufa ya kwaso masu yawa da k'amshi sosai adadin yawan da mutun uku zasu iya amfani dasu, har zai wucewa sai ya zagaya tagefen da 'yan kunne da sark'ok'i da zobbuna da agogayye kejere, ahankali yafara duba zobban dake wajen don ya siyawa Billynsa amma har yakai k'arshe bai samu ba, har zai wuce ya hango wani cikin jerin azurfofin dake wajen, ruwan azurfane zallarsu fari k'al sai zanen capital B da aka fidda shape d'inta atsakiya da wani salon rubutu daba kowa ke iya ganewaba don yayi kamar wani salon zanen fulawane amma azahiri idan ka k'ura ido zakaga B ce arubuce, nan take yaji zoben ya burgesa, d'aukowa yayi yana imagining zoben ahannunta yayi murmushi yana zuwa akayimasa totallyn kud'in da zai biya ya biya sannan ya ajiye masu zoben shima aka fad'a masa kud'insa yabiya, kallon zoben yayi saboda tsadarsa ya tabbatarwa zuciyarsa cewa da ita d'in yafi dacewa don dama Billyn tasa tafi tsada tsada, rik'o masa kayan akayi tare da kai masa mota shikuma yakad'a zoben a aljihunsa bayan an saka masashi acikin wata 'yar jikka, yana jan motarsa bai tsaya ko inaba sai _Bebeji plaza_ wajen da ake saida nau'o'an wayoyin hannu kala kala, techno phantom 8 ya siya k'waya biyu tare Samsung galaxy S8+ saida aka yimasa testing d'in kowace sannan aka maidasu cikin kwalayensu bayan an sanya masa aleda yabiya kud'in sannan yad'auko, yana fitowa yanufi mtn office ya sayi layukka guda biyu masu registered sannan yasayi wani k'waya d'aya da ba'ayiwa register ba ya zauna yabada duka information d'insa nan take akayiwa layin register dasu, yana fitowa ya mik'i hanyar gida lokacin ana kiraye kirayen sallar la'asar hakan yasa yana isa kai tsaye yanufi d'akinsu yafad'a toilet yayo wanka bayan yatada yaya Mahmud da ya isko yana bacci, shima wankan yayo yasamu har Mahmud pilot ya shirya cikin k'ananan kayansa da suka karb'i jikinsa sosai kamar bashiba, jeans ne yasa brown colour sai shirt d'in data d'an kama jikinsa kad'an itama brown da ratsin layi fari a gefen hannunsa nadama daga can sama kayan sunyi matukar yimasa kyau sosai, kallonsa yayi yace


"Pls d'an uwa don Allah karakani tun d'azu nake begging d'inka amma ka wofantar dani" murmushi yayi kafin yace


"Shikenan bari mudawo sallah, ai kai d'inne kab'atan rai d'azu kana ganin mutun cikin damuwa bakayi masa solving d'inta ba ka wani d'auko masa zancen rakiya wajen budurwa" mahmud dai bai cemasa komai ba yaci gaba da shirya warsa cikin wata shadda black colour,  saida ya kimtsa tsaf sannan ya kallesa yace "d'an uwa kasha kyaufa, yau kace zaka rud'amun k'anwa"


"Nagd d'an uwa, amma kaikam ko shakka banida akan zaka firgita 'yar mutane don gaba d'aya kayannan basuyi maka kyauba, haba d'an uwa irin wannan shiga haka sai kace ba akanka d'aya ba" baki yaya mahmud ya washe tare da mik'a masa hannu yana fad'in


"Alhamdulillah, da gaske kakeyi d'an uwa? Gaskiya naji dad'i sosai don dama hakan nake so, wlh dolece zata sakani zuwa wajen yarinyar nan, Allah yasa tace banyi mata ba"


"Kai amma dai kai mugune, don d'ai haka zakayi mata wannan shigar, duk da shigar batada illa kayanne dai basu zauna ajikinka ba duk sunyi wani oversize dasu haka ballema ayi batun suyi maka kyau..mtss Allah yasama tace taji tagani ahaka tanayi" cikin b'acin rai Mahmud yace


"Kaima Allah yasa tace kai takeso tunda kaine kayi shigar da tayi kyau" yaya mahmud yafad'a tare da ficewa cikin fushi, jin anazancen tada sallah yasa shima yabi bayansa bayan yafeshe jikinsa da turare suka nufi masallaci, suna fitowa sai ga kiran papi yashigo, saida yaya Mahmud yad'an bubbuga k'afarsa ak'asa sai kace yaro sannan ya d'aga wayar har lokacin fuskarsa babu walwala, dariya mahmud pilot yadinga yimasa hadda rik'e ciki ya galla masa harara lokacin da yake cewa papi bayan sun gaisa,


"Eh papi yanzu can zamu tafi nida d'an uwan in sha Allah, eh papi, babu matsala zantafi karka damu" suna gama wayar yacewa Mahmud pilot "ka k'addara kaci bashi d'an uwa ko yaushene zan rama wannan dariyar da ka keyimun"


"Sorry d'an uwa nadena ainikam anriga angama tunda nafad'i zab'ina kafin azab'omun banyi nauyin baki irin naka ba" k'yalesa yayi yawuce abunsa don kar wani yaga shigar da yayi ya tilastasa yasa suna shiga cikin gida yabud'e motarsa ya shige had'e da kallon Mahmud pilot yace "muje ko"


"Baza kasa kod'an turare bane?"


"Bazan saba! Aitunda kasa ya wadatar" yabashi amsa atak'aice


"Shikenan ammafa ni yunwa nakeji ko zamuyi lunch kafin muwuce?"


"Noo.. bana buk'ata jeka kai kayo zan jiraka" kad'a kai Mahmud pilot yayi sannan yawuce abunsa, harara kawai yabisa da ita fuskarsa ba walwala, yana shire rufe idanuwansa ya hango Billy rik'e da warmer tanufi part d'in mom aikuwa Mahmud pilot na ganinta yanufi wajen yana murmushi, "my noor" yace yana k'ok'arin k'arasowa inda take, juyowa tayi suna had'a idanuwa suka sakarwa juna murmushi, shigar datayi sak irin tasace kamar sun had'a baki, doguwar rigar shaddace ajikinta shape d'inta yazauna aciki tayi kyau sosai, bawani aikine aka yiwa shaddarba, shape kad'aine aka fitar mata, giznah ce data karb'i sunanta Brown colour sai k'yalli takeyi light make up ce afuskarata tasaka takalmi brown suma masu d'an tudu da suka k'ara mata tsawo duk da cewa itama tanada nata tsawon ba gutuwa bace, yatsunta biyu tahad'e ta kad'a kai ahankali tace "na'am yayana kayi kyau sosai"


"Allah my noor?" Yace yana fiddo wayarsa daga cikin aljihu, murmushi tayi had'e da jinjina masa kai alamar sosai kuwa, warmer d'in ya karb'a a hannunta ya ajiye gefe yana fad'in


"Ai ga tsantsar kyaunan awurinki, gaskiya da nayi missing kwalliyarnan dana tabka babbar asara" rufe baki tayi tana yimasa dariya kawai taji yana d'aukarta hotuna, duk motsin da tayi wajen yunk'urin hanasa sai yad'auketa hoto yana dariya, tun tana hanasa har tagaji ta k'yalesa yayi iyayinsa sannan yadena,


"Weldone sun isheka haka?" Tafad'a cikin shagwab'a tana d'an harararsa,


"No..one more pls" kafin tace wani abu yadawo gefenta had'e da maida phone camera d'in front ya saitasu, kallonsa tayi had'e da d'an turo baki irin na shagwab'a d'in nan zatayi magana aikuwa ya d'aukesu hoto, "smile my nooor.." Yace ta sigar da dole yasata dariya, tanayin dariyar yasake d'aukarsu har kusan so uku sannan ya tura wayar a aljihu yaduk'a yad'au warmer d'in yawuce gaba ta bisa tana fad'in


"Pls nidai kabani bance ka d'aukar munba" "ai bake kika sakani ba ni naga dacewar haka tunda ina wajen, kinmanta da nayi maki alk'awarin zan bauta maki akoda yaushe?" Bubbuga k'afa tashigayi tare da cin gabansa ta karb'i warmer d'in hannunsa a daidai lokacin da yake k'ok'arin shigewa part d'in da ita. "Thank u here is enough ma kaje kaji ko?"


Dariya yaya Mahmud dake cikin mota yana kallonsu cike da Sha'awa da burgewa yayi had'e da bugun stearing motar


Shikuwa Mahmud pilot kallonta yayi tare da cewa


"Shikenan tunda korata kikeyi natafi, i luv u" yawuce had'e da jefo mata kiss da hannu, cafkewa tayi da sauri ta aza saiti zuciyarta tana dariya tace luv u too yayana" zagayawa yayi yabud'e motar ya shiga tare da cewa "muje d'an uwa nafasa cin abinci now sai mundawo"


Mere baki yaya Mahmud yayi had'e da cewa "dama can bawani abinci zakaciba kai dai kawai kace qanwata kake son kaje ka gani, kuma kaganta, jarababbe kawai"


"Eh naji d'in bakomai, infitsari Banza ne kaza tayi mugani"


Batare daya kula saba yaja motar habu mai gadi yabud'e masu gate suka fita, tafe yake yana tuk'i amma gaba d'aya cikin damuwa yake da qunci, sai da suka kai bakin wani gida dake kan titi yayi parking motar had'e da kallon gefen da Mahmud pilot yake zaune sai faman kallon pics d'in da sukayi da Billynsa yakeyi yace


"'Dan uwa minti biyu don Allah ina zuwa, zan d'an anshi wani abu wajen abokina" bai d'ago  kansaba daga kallon da yakeyiwa hotunan kan wayarsa yace "badamuwa sai kadawo"


Bayan kamar minti biyar sai gashi yadawo hannunsa rik'e da wani abu yayi saurin kad'awa aljihu kafin ya iso gaban motar, a hankali yaci gaba da  tuk'a motar suka nufi anguwar su faraaha tamkar bayason su isa , baisan cewa sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba'a kaiba, da haka suka isa anguwar tambaya d'aya sukayi aka nuna masu gidan kuma akaci sa'a jaddi na zaune a k'ofar gida, parkin d'in motar yayi agaban gidan sannan suka fito cikin girmamawa suka gaida jaddi da fuskarsa tacika fam da farincikin ganinsu, umurni yabasu dasu shigo cikin gida har zaure shi kuma ya wuce ciki, d'akin faraaha yanufa daya iskota har tayo wanka tasanya kayanta masu kyau kasancewar tasan da maganar, sosai yaji dad'in ganin yanda tagyara yafad'a mata cewa ta samu bak'in azaure sun iso sannan yajuya tare da basu hak'uri ya sanar dasu cewa gatanan zuwa yana fita mahmud yaji kamar ya fashe da kuka, juya bayansa yayi don shikam ko fuskarta baya son gani balle yaji yana sonta ko akasin haka, ita kuwa faraaha jaddi nafita tayi irin kwalliyarnan ta k'auyawa sannan tanemi bak'in kwalli tacike gaba d'aya bakinta da gefensa dashi, sannan tane concealer tayi 'yar gira da ita, brown pencil tasa k'asan idanuwanta amatsayin kwalli sannan tanemi jan bakinta 24hrs ja tasama haurunta guda biyu na gaba, ita kanta data dubi madubi taga yanda takoma saida ta tsorata dariya tayi sosai kafin ta d'auko jikkarta ta lak'ame a hamutta, fitowa tayi tare da d'aure fuska tanufi zauren har zata shiga sai kuma ta tsaya, tsaki tayi kafin ta botsare had'e da d'ora hannunta akan cinya tafara tafiyar guragu dama tun jiya da daddare yayita koyon yanda akeyi,  kanta na kallon k'asa ta shiga zauren batare datayi sallama ba, shi kuma yaya Mahmud dama yana juyawa baya yaciro haurun robarsa daya aro wajen abokinsa irin masu fitowar nan agaba guda biyu sunyi jajaja da bak'i bak'i ya saka, tunda tadoso wajen Mahmud yafara ja da baya yana tab'in mahmud pilot amma yak'i juyowa, hakan yasa ya daure yace mata "sannu 'yan mata, ya kike?, wannan bazata haka ko sallama babu" wata irin harara ta d'ago kai ta zabga masa da sauri yaja baya saboda yanda yaga fuskarta, yaso yatuna ina yataba ganin irin fuskar amma waccan kyakkyawace kuma ba gurguwa bace, maida kanta tayi k'asa da sauri dariya na neman kucce mata ganin yanda yafirgita, hakan yaba Mahmud pilot damar cewa "'yan mata maida wuk'ar irin wannan uwar harara haka? to banine saurayin naki ba ni d'an rakiyane" tab'o yaya Mahmud yayi yana fad'in


"Dan uwa kajuyo mana kaga masoyiyar ka tunda tak'i magana, kila idan taga fuskarka tayi" cikin b'acin rai yaya Mahmud yace


"Kada Allah yasa tayi maganar, dama hakan bai dameni ba, idan batada abun cewa sai intafi abuna don dama dole aka sani badon ina soba, kuma idanma kinsa rai akaina to kifiddo donni inada wacce nake so" yak'are maganar had'e da juyowa, tunda yafara magana taji kamar muryar all I have d'inta amma saboda baijuyo fuskarsa ba yasa tad'an jira har sai tatabbatar shid'inne sannan tayi magana, yana juyowa suka had'a ido takalli haurun da suka fito agaban bakinsa shima yakalli fuskarta da kyau ya tabbatar wannan faraahar sace, nunata yayi da hannu yana fad'in "My golden" had'e da cire haurun roban da yasa abakinsa, ai faraaha bata san lokacin data nufi cikin gida agujeba har lokacin tana tsingila k'afa saboda yanda tarud'e takasa barin tafiyar gurgurtan, zaune yaya Mahmud da pilot sukayi akan d'an teburin dake cikin zauren suna faman dariya hadda rik'e ciki ita kuwa da gudu tafad'a toilet ta wanko fuskarta sosai ta sako hijabinta, zauren tadawo tana kallon yanda suke dariya itama sai takwashe da dariya tuna yanda taga all I have d'inta da hak'ora biyu zagozago agaban baki kamar zai cijeta..





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Sincerely i will not past dis page with out sending my big greeting and gratitude to you *ZAINAB PINKI🌸💕* you are such a big and adorable fans dt am always proud of her, thank you fd luv sister, thank u for encouraging me and thanks for always been with my write step by step😍 I pray for a wanderful, handsome, and charming husband to u my dear, jaxakillahu bikhair wa'arju anyaj'alallahu min ahlil jannah👏🏻 *much luv fillah❤*_


💎Page_____61💎



  K'arasowa tayi cikin zauren tayi folding hannayenta akan k'irji tana kallon yanda yake dariya sai taga ya k'ara mata kyau fiye da kullum, d'ago kansa yayi yana k'ok'arin tasaida dariyar tasa yace,


"My golden wai dagaskene kedince agabana kuma a matsayin zab'in papinah? I can't believe!" Yafad'a  had'e da d'ora hannunsa akan cinyarsa yana mamakin yanda ikon Allah ya kawosa har cikin gidansu masoyiyarsa amatsayin saurayin had'i, lumshe idonta tayi tana murmushi itama abun yabata mamaki sosai wanda hakanne ya haifar da ita zama speechless, mik'ewa Mahmud pilot da har yau dariyar acting d'in da masoya biyu sukayi yakeyi, hannuwansa yashiga tafawa yana fad'in "finally finally d game is over tunda dara taci gida, gaskiya kud'innan kuncancanci award na mugwayen duk duniya" nuna yaya mahmud yayi da hannu sannan yaci gaba da cewa "kai da hauru zarozaro agaban baki ga wata muguwar bak'ar shadda oversize daka saka ita kuma tafito tana tsingila k'afa alatilas ita gurguwace ga fuska databi ta b'ata tamkar horanya taya za'ayi idan harku d'in ba masoya bane da kuka san juna har kuso junanku? Wlh Allah danaga fuskarki kad'an yarage inruga balle wannan shikuma k'iris yarage nayi fitsari a wando" ya k'arasa maganar yana kallonta tana faman murmushi"


Gefen yaya mahmud taje tazauna had'e da cewa


"Wannan ai kad'an kagani indai tsakanin faraaha da mahmud ne, zasu iya yin fiye da hakan akan duk abunda yanemi rabasu, kuma wannan itace soyayyar gaskiya da ake kira mutu karaba ko all i have"


"Sosai kuwa my faraah kuma ina alfaharin samunka a matsayin rabin raina domin natabbata zaki rik'eni amana" murmushi tayi tare da mik'ewa tsaye taje takawo tabarma ta shimfid'a masu sannan takawo masu ruwa da kunun aya masu sanyi sosai had'e da kofuna ta ajiye masu,


"Pls all i have, kusha wannan kafin nadawo, kubani just 5mnt i will be back in sha Allah" tafad'a tana k'ok'arin ficewa daga palourn, binta yayi da kallo har tafice, shikuwa yaya Mahmud ya shiga tsarguwarsa, bai tankasa ba illama fiddo wayarsa da yayi ya kira papi, yana d'agawa cikin farinciki yace


"Nagode papi da kazamo silar tabbatuwar farincikina, nayarda da zab'inka kuma na amince dashi ubangiji Allah ya tsawaita rayuwarka cikin amincinsa kuma yasaka maka da alkhairi"


Speechless papi ya zama ya juya yana kallon hajia kaka dake gefensa fuskarsa d'auke da murmushi yace


"Baby kinji abunda mommodunki kefad'a? Wai ya amince da zab'ina!" Yafad'a cikin mamaki, muryar yaya mahmud yajiyo cikin wayar yana cewa


"Papi ba wai bane kuma kadena mamaki don tabbas na amince kawai kutsaida ranar shagali" yana gama fad'ar haka yakatse wayar yana kallon mahmud pilot da yarik'e baki yana kallonsa, basarwa yayi tare da d'aukar gorar ruwan dake gabansa ya tsiyaya a cup yana sha.


Hello, hello, papi ya dinga fad'a yana k'ok'arin jefa masa tambaya amma sai yaji yakashe, wata sanyayyar ajiyar zuciya yayi sannan yajawo babynsa ajiki yayi mata kiss a goshi had'e da cewa


"Alhamdulillah, baby yaronnan ya gamamun komai aduniya, duk da jikina nabani cewa akwai dalilin da yasashi saurin amincewa nayi farinciki sosai" d'ago kai tajiya kaka tayi tana kallon fuskarsa sannan tace


"Gaskiya kam akwai alamar tambaya, amma koma meye, alhamdulillah Allah yatabbatar mana da alkhairin sa" kiss yasake yimata tare da cewa


"Amin babynah" ya rungume abussa,


Cikin mintuna da basu wuce goma ba saiga faraaha tadawo hannunta d'auke da kuloli guda biyu babba da k'arama akan tray da kuma plates da spoon ta ajiye agabansu, cikin natsuwa tafara zuzzuba masu kuskus d'in data dafa yanzu tare da miyar k'wai da yake da electric stop tayi girkin kuma bamai wahala bane shiyasa tayi saurin gamawa, iya tsarguwa da sheri yau sunshata awajen mahmud pilot, sukuma sai dariya suke suna cewa ai duk cikin sone,


Sunci sunsha  sosai tare da firarsu cikin so da k'auna batare da sunyi la'akari da Mahmud pilot dake wajen ba, duk da yana ganin abun nasu yafi k'arfin hankalinsa barmasu shimfid'ar yayi yakoma saman tebur d'in dake can gefe yana lallatsar wayarsa, basu baro anguwar ba sai gab da magrib bayan sunyi sallama da jaddi daya dad'e yana mamakin yanda suka samu fuska awajen faraaha har suka samu damar iya dad'ewa haka, suna wucewa ya shiga cikin gidan fuskarsa cike da mamaki, bai sake shiga cikin mamakiba sai daya ga faraaha tarugo da gudu ta rungumesa tana fad'in


"Nagode jaddi da zab'in da kayimun kuma na amince zan auresa, tabbas dana bijere wajen yarda da ganin zab'inka dana tabka babban rashi" d'agota yayi daga jikinsa had'e da rik'o fuskarta yace


"Me kike nufi faraaha?, kenan kin amince da zab'in da nayi maki?" Girgiza kai tayi da sauri tana hawaye tace "Eh jaddi na amince da zab'inka domin shine zab'in nawa shima" farincikin dake kwance afuskar jaddine ya k'ara bayyana yace "da gaske kikeyi shine saurayin naki?, kai alhamdulillah Allah daka sauk'ak'amun burina yazamo zai cika cikin sauk'i batare da k'untatawa wannan 'yar marainiyar Allah ba" rungumesa tayi sosai shima haka tace


"Ina sonka jaddi sosai, Allah ya karb'i iyayena amma yabani wani uba kuma kaka da bazai tab'a bari na wofanta ba, ya Allah kada ka karb'i raina har saika bani ikon faranta zuciyar wannan bawa naka"


"Amin" jaddi yafad'a yana goge 'yan hawayen da suka zubo masa...


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____62💎



  Driving yakeyi yana shiga da fita akan titi zuciyarsa cike da tunanin faraaharsa da suka rabu yanzu, hannu Mahmud pilot yakai akan stearing motar yana jifarsa da harara  "d'an uwa wai mekake yine haka, ina dai yanzu karabu da ita to meye kuma na tunaninta? Kaga idan yawo zaka dingayi damu saman titin nan toyi parking a gefe na sauka, haba! Wannan abu sai kace Romeo kana neman kashemu akan titi!"


"Sorry d'an uwa am enjoying the mood shiyasa" harara yasake balla masa kana yace


"Don kana enjoying mood d'inka sai kuma ka kashemu! Pls ajiyeni intari napep kaje can kaida mood d'in naka ku k'arasa" dariya yaya Mahmud yayi sosai sannan ya daidaita tafiyar motar akan titi.


Billy kuwa tana shiga ta tadda Basmah nak'ok'arin mik'ewa akan gadon ita kuma Batool na sallah, da sauri ta ajiye warmer d'in dake hannunta ta isa wajen had'e da rungumota gaba d'aya ajiki "haba yayya so kikeyi ne kafad'i baccin kinsan bakida k'warin jiki, zauna annan kifad'amun mekike so inkawo maki" kallonta tayi tana murmushi tace


"Sister u look so beautiful, Allah yasa yayanmu yaga wannan kwalliyar"


"Kai yayya manta da wannan, mekike sone" sake murmusawa tayi kafin tace


"Ke nake so 'yar uwata"


"Naji, nima ina sonki sosai fiye da kankaina"


"Da gaske?"


"Sosai kuwa yayya" 


"Ngd sister dama toilet nake son shiga nayo arwala kozaki taimkamun"


"Ofcouse, tashi muje" har toilet Billy takaita sannan tajira tagama arwala tasake rik'ota suka fito, suma fitowa Batool tamik'e daga kan sallayar ita kuma tahau tafara sallah, hugging d'in Billy Batool tayi had'e da jujjuyata tace


"So cute twiny masha Allah, gaskiya kayannan sunfi d'agoki akanmu, may be don kind'an fimu k'iba, kinga yanda kika had'u kuwa? Gaskiya da akwai waya ahannuna da kinsha pics nak'in k'ari" saida Billy tayi murmushi sannan tace


"Thank you twiny,kin riga yayanki fad'a amma yarigaki aikatawa"


"Wow da gaske twiny? Can't wait to see d pics, nasan sunyi maseefar kyannan" dariya Billy tayi had'e da jawo warmer d'in data shigo da ita ta ajiye agaban Basmah data idar da sallah yanzu "yaya here's ur fav food Ummi tahad'o maki kuma tace tana gaisheki da jiki sosai"


"Allah sarki Ummi nayi missing d'inta kwana biyu" bud'e warmer d'in tayi had'e da cewa  "awwwn..yummy, luv it much, Batool d'okomun plate naci kafin yawuna su tsinke" faten tsakin masara ne da yasha tarugu da alayyahu da kuma wake sai k'amshi ke tashi.


Dariya suka aza mata ganin yanda take sauri sauri wajen cire hijab d'in data gama sallah tajawo kular agabanta tana nema tasaka hannu, mik'ewa Batool tayi tana fad'in "kai yayya yihak'uri inkawo maki spoon da plate kada ki k'ona kanki, wannan irin zumud'i da kikeyi har ina!" Ganin zata b'ata mata lokaci ta mik'e da k'yar taje kitchen ta d'auko plate tadawo tad'ibi mai yawa sosai ta tasa agaba tafara sha tanayi tana lumshe idanuwa tana murmushi. Kallon Billy Batool tayi sannan tace


"My twiny kinga wani sonkai, ko tayi yayya takasa yimun"


"Hmm bari kawai twiny bansan wane irin so yayya keyiwa fate-fate ba, sanin soyayyar da take yimasa ne yasa Ummi tazauna da kanta tahad'a mata" saida Basmah tacika baki sannan ta d'ago kai tace


"Allah yabar mun Umminah shiyasa nake matuk'ar sonta araina" kallon juna sukayi suka kwashe da dariya suna mamakin yanda take tsananin son fate-fate aranta.


Sai bayan magrib Mahmud pilot yaje wajen motarsa yabud'e ya kwaso sayayyar da yayo d'azu kai tsaye falon Ummi ya wuce yazube kayan acan saman dining table yana tambayar Umma wai ina Billynsa, harararsa tayi had'e da cewa


"Yaronnan nalura rashin kunyarka na nema ya wuce wuri, ni kake kallo ka tambayeni wai ina Billynka take?" Kafin yayi magana Umma tajiyo muryar Ummi tana dariya tare da cewa


"Ai shine daidai uwar zamani sai d'an zamani, meye laifinsa tunda ke kikace a ajiye kunya agefe ke mai 'yah, babu wata rashin kunya tambayar inda k'anwarsa take yayi" 


Murmushi Mahmud yasaki had'e da juyawa yana sosa kansa don maganar takoma tsakaninsu, yana shirin fita sai gasu sun turo gambun k'ofar had'e da shigowa, kasancewar Basmah ce agaba don itace tamatsa masu akan suzo tana so taga Ummi kuma tayi mata godiya, kawai saiji sukayi sunyi karo da juna, baya baya Basmah tayi zata fad'i yayi saurin rik'o hannunta, wani irin yarr taji ajikinta, soke kanta tayi k'asa alokacin da taga hannunsa rik'e da nata lumshe idanuwanta tayi tanajin wani sabon yanayin nashigarta, sanin cewa batada cikakkiyar lafiya yasa yak'i sakin hannunta saima jawota da yayi suka shiga daga ciki yanufi wajen dining table d'in da ita yana fad'in


"Sorry sister banlura daku bane da kinsa na ida gawar da batawa ba, sannu kinji? Hop jikin naki da sauk'i" gaba d'aya Basmah da Batool kallo suka bisa dashi ita kuwa Billy dama indai su Ummi na awuri yitakeyi tamkar bata san da shiba, kai tsaye tana shigowa wajensu tanufa tana basu labarin shan fatefaten yayya Basmah tana dariya, 


Ganin haka yasa Basmah tayi saurin zare hannunta daga rik'on da yayi mata cikin i'ina tana fad'in "alhamdulillah yaya naji sauk'i" baro dining area d'in tayi tayo cikin falon tanaji zuciyarta na halba mata da sauri da sauri har k'afafuwanta na neman kasa d'aukar gangar jikinta, rik'on da Batool tayi matane yasa tasamu courage d'in k'arasawa tana gaisheda su Ummi, sosai Ummi taji dad'in ganinta tare da yimata ya jiki, Bini bini Billy ke d'ago idanuwanta suna had'uwa da na mahmud pilot dake can zaune yabuga uban tagumi had'e da tsareta da idanuwa, dasun had'a ido sai ya sakar mata murmushi itama saita mayar masa tare duk'ar da kanta k'asa, "Batool zonan keda yayya Basmah muyi firar bankwana kinji" yafad'a yana bud'e ledojin dake gabanshi, tashi su Umma sukayi suka shige d'aki abunsu ita kuma Billy ta nufi kitchen. Ko kad'an Basmah Bataso zuwa wajenba saboda yanayin da take jin kanta amma saboda kar wani tunani yazo masu arai yasa tarik'o hannun Batool data mik'e tana batun iskosa tasamu itama tamik'e tsaye, tare suka isa wajen kowacensu tajawo kujera ta zauna, juyawa Batool tayi tana k'walawa twiny d'inta kira, ita kuma Basmah ta noce kai k'asa tanaji tamkar zuciyarta zata fito saboda tsananin soyayyarsa dake fizgarta, wani irin ciwo zuciyar tafara yimata amma saita daure tace


"Yaya kozaka bari sister ta wakilceni tunda banida lpy" d'ago kai yayi yana kallon Billy data nufo wajen saboda kiran da taji twiny d'inta tayi mata rik'e da apple tanaci, murmushi yayi sannan yace


"Karki damu yanzun nan zamu gama, dukkaninku 'YAN UWANA NE, don haka kowace tanada matsayin da babu wacce ke iya wakiltarta acikinku" hannun Billy Batool tarik'o da niyar zaunar da ita akan kujerar dake kusa da ita tace


"Twiny ina zuwa akwai aikin da zan k'arasawa ummi a kitchen, so kusha firarku ta 'yan uwa kafin in dawo" tana gama fad'ar haka takoma kitchen abunta shi kuma ya fiddo wayoyi da layoyan daya siyo guda uku ya janje kwalin Samsung galaxy agefe had'e da layin da akayi wa register da sunansa, phantom d'in guda biyu ya mik'awa Basmah d'aya sannan yaba Batool d'aya had'e da layoyan yace "ga tsarabarku dana manta ban kawo maku ba da mukazo" sannan ya ajiye qatuwar ledar kayan cosmetic d'in daya sawo masu itama yace "ga wannan ku k'ara da ita kuda twiny d'inki, yaya is srry fd let tsaraba" yafad'a yana kallon Batool, cikeda farinciki suka bud'e baki suna yimasa godiya especially Batool da bata tab'a rik'a wayaba, don dady cewa yayi basu isa rik'a taba, Basmah ma dake da ita ada ab'oye mom tasaya mata ita wai saboda abokananta nayi mata dariya wai batada waya,




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____63💎



   Kallonsu kawai yakeyi yana dariyar yanda suke nuna jin dad'i da tsantsar farincikinsu akan kyautar da yayi masu, d'ago kai Basmah tayi had'e da cewa


"Yaya anya hidimar nan batayi yawa ba?" "Dame kuma Basmah?" yafad'a yana kallonta


Sadda kanta k'asa tayi tace "Mungode sosai yaya Allah yabar zumunci kuma yakareku da dukkanin abink'i" saida ya lumshe idanuwansa fuskarsa d'auke da murmushi sannan yace 


"Shiiii...kidena godiya ku 'YAN UWANA NE, don na kyautata maku basai kun godemun, fatana Allah ya kawo maku miji nagari da zai kula daku yanda yakamata koda yake naga rawar kan Batool tayi yawan da bazata bari sai auntynta ta tsaida miji ba sannan ita ta tsayar da alama aure takeso" yafad'a cikin zolaya yana kallon Batool, dariya tayi kafin tabashi amsa dace


"Kaji yaya da wata magana ai duk rawar kaina bankaina k'anwataba ita data kawo mana miji har cikin gida suna tsula soyayya ko kunyar iyaye basaji" zaro idanuwa yayi kafin ya jefeta da simpack d'in dake hannunsa yana fad'in "iyyeee ya tabbata yarinyar nan aure kike so, yayan kike ga yawa magana haka?" Kaucewa tayi tare da d'aukar kwalin wayarta tamik'e tabar wajen tana dariya, karo tayi da yaya Mahmud zai shigowa wayarsa lak'e akunne suna waya da faraaharsa, kallo d'aya yayi mata ya had'e girar sama data k'asa sannan yaciro wayar yamik'a mata yana fad'in


"Ke nifa gayennan naki yafara takurani, always feel a little jealous idan naji muryarsa acikin wayar matata" karb'a tayi had'e da barin palourn tana nuna masa kwalin wayar da mahmud pilot ya siyamata tana nuna masa yabud'a yagani irin nima nayi tawa d'innan, mere baki yayi tare da jujjuya kwalin wayar sannan yanufi inda su Basmah da Mahmud pilot kezaune yana fad'in


"Zaki gane yarinya" kujerar dake gefensa yaja ya zauna had'e da cewa


"Sannun ku d'an uwa, Basmah yajikin?" 'Dago kanta da tund'azu yake ak'asa tayi tana kallon yaya Mahmud tace


"Naji sauk'i yaya, barka da shigowa"


"Yawwa, kije mom naki ranki" yafad'a ganin yanda take zaune awajen takure da alama tana cikin damuwa, sosai taji dad'in hakan da yace tayi saurin mik'ewa zatabar wajen taji muryar Mahmud pilot nafad'in


"Basmah dawo kizauna dama akwai maganar da naso nayi da d'an uwa akanki kafin muwuce gobe don banajin dad'in yanayin da kike ciki yanzu, gaba d'aya kin canza daga Basmar dana sani agidannan zuwa wata Basmar daban, so tunda dai gaki gamu ina so kisaki jiki mu 'yan uwanki ne najini kifad'a mana meyake damunki"  gabanta ne yayi rass rass jin kalaman dake fitowa daga bakin wanda take tunanin kamar bai damu da halin da take cikiba kafin tajuyo da k'arfi tana kallonsa,


"Yes akwai abunda kedamunki 'yar uwa, koda kin b'oye hakan to yanayin walwalarki shizai bayyana halin da kike ciki koba haka ba d'an uwa" kallon yaya Mahmud da damuwarsa tabayyana k'arara afili tayi sannan ta kallesa tace


"Ni babu abunda yake damuna, duk wannan yanayin da nake ciki jarabtuwa da ciwone ya jawomun haka amma ina warkewa zan koma normal" wata maganar Mahmud pilot ya yunk'ura zaiyi yaya Mahmud ya dafa kafad'arsa had'e da girgiza masa kai,


"Haba d'an uwa to meye zumuncin idan bazamu iya fuskantar damuwar 'yan uwanmu mumagance taba, let her answer d question natabbata tanada damuwa, idan tafad'a sai muyi mata maganinta idan kuma tafi k'arfin mu saimu fad'awa iyayenmu su magance mata ita, haba kadubi yanda takoma sai kace ba Basmah ba" cike da takaici Basmah ke kallon idanuwansa yanda yake zabgar fad'a da kuwa ace zata fad'a masa damuwarta ta tabbata shikansa zai shiga damuwar da zata rusa gaba d'aya farincikinsu, fashewa tayi da kuka tabar wajen aguje, binta yayi da kallo yayi har tafita kana ya kalli yaya Mahmud yace


"Kaga niko, kaga abunda nake fad'a maka ko? Idan har babu damuwa aranta taya za'ayi daga tambaya tafita tana kuka"


"Relax d'an uwa bazamu iya fahimtar matsalarta yanzu ba saboda situation d'in da take ciki,  mubita a sannu zata fad'a, kuma i promised  koma meyake damunta zanyi settling d'insa in sha Allah, karka damu kajiko!" Yaya Mahmud yafad'a tasigar rarrashinsa saboda ganin yanda yanuna damuwarsa k'irik'iri, ji yake inama ace bainuna soyayyar da yake yiwa qanwarsu Billy afiliba, tabbas da dakansa zai zauna ya fayyace masa damuwar 'yar uwarsa, amma yanzu dole sanin matsalar Basmah taga gari kunnuwansa, bubbuga kafad'arsa yayi sannan yamik'e yabar palourn yana fita ya tarar da Batool lak'e ajikin corridor sai zuba soyayyarsu sukeyi ita da dr Allah awaya. Harara ya 'balla mata sannan yawuce part d'in mom cike da damuwa afuskarsa, kai tsaye d'akin au Basmah yashiga ya taradda ita kwance tana kuka, jin tayi andafa kafad'arta tare da zaunawa gefen gadon, k'amshin turarensa ya tabbatar mata da cewa yayanta ne, hakan yasa tad'ago da sauri tafad'a jikinsa tanaci gaba da kukan,


"Nashiga uku yaya don Allah kad'aukeni daga gidan nan kada zuciya ta tunzurani na aikata abunda zai cuci rayuwata data 'yan uwana, ahalin yanzu kowane lokaci raunina da gazawata zasu bayyana batare da sanina ba, pls yaya..."


"Meye haka kike fad'a Basmah, shin ashe bazaki zamo cikin bayi masu yadda da qaddarar da Allah ya tsaro akansuba, bazaki so ki cinye wannan jarabawar da Allah yayi makiba acikin sauk'i sai kin fitini rayuwarki da yawa, haba Basmah kefa musulmace da kikayi ik'irarin zakiyi imani da kowace irin qaddara mai kyau da marar kyau, ki k'arfafa zuciyarki sosai nasan zaki iya, bana son ganin wannan kukan naki yana sakani jin nazamo mafi raunin yaya ga qannensa"


'Dago fuskarta tayi tasa hannuwa tana goge hawayen idanuwanta tace "kayi hak'uri yaya nadena kukan, nayi imani da wannan qaddarar da ubangijina ya jarabceni da ita, daga yau zan aro k'uwwa nasaka azuciyata, kuma zance gaba da addu'o'i da nafilfili kamar yanda nasaba akan Allah yasamu juriya da hak'urin da zancanye jarabawata, in sha Allah bazani koma zudda hawayena akan soyayyar yaya Mahmud pilot koda hakan na nufin zamowar ajalinane" rik'e fuskarta yayi yana kallonta yace


"Kinyi alk'awari?" Hawaye nazubo mata had'e da dariya duk cikin lokaci guda ta jinjina kai tace


"K'warai kuwa yaya kodon farincikinka" had'e goshinsa yayi da nata shima hawaye nazubo masa,


"Allah yayi maki musanya da wanda yafisa zama alkhairi sister, wlh ina matuk'ar jin tausayinki, so dafine kuma yanada zafi sosai, banida yanda zanyine domin ke da Billy duka 'YAN UWANA NE shiyasa kikaga nazubawa sarautar Allah idanuwa"


"Nasani yaya, nasani karka damu nima nabarwa Allah ya zartar da duk tsarin da shine mafi k'ololuwar alkhairi akanmu"


A b'angaren Batool kuwa Soyayya kam yau sun shata kamar ba gobe don sai da yaya Mahmud yagaji yaje ya anshi wayarsa yana jininin baisan mesuke fad'aba acikin waya fiye da mintuna arba'in, cike da kunya Batool tabasa hak'uri tare da barin wajen tana jin wani fresh air nashigarta ahankali. 'D'akinsa ya wuce ita kuma ta koma part d'in Ummi, zaune ta isko Mahmud pilot shikad'ai yana latsar wayarsa, murmushi tayimasa had'e da cewa 


"Sannu da hutawa yaya" batare da yad'ago kansa ba yace


"Yawwa Batool sannu kema da soyewa" hannunta tamik'a takwashi kwalayen wayoyin daya siyo masu tare da ledar cosmetic d'in tanufi bedroom d'in Ummi, har takusan shigewa ya d'ago kansa yace


"Batool kituromun Bilkisu pls" kad'a kai kawai tayi sannan ta shige abunta, kayan tashiga nunnunawa su Ummi cikin jindad'i da yaba kyautar suka dinga sanya masa albarka suna masu yimasu addu'a da  fatar Allah yabar masu zumuncinsu har abada. Kayan ta d'auka had'e da kallon Billy da shigowarta kenan takawowa su Umma fruitslad d'in data gama had'owa mai sanyi tace


"Twiny wai kije yaya Mahmud nakiranki" sannan tajuya zata fita, d'ago kai Billy tayi daga duk'en da take tace "twiny wanne daga cikinsu" murmushi tasakar mata had'e da cewa "pilot" kana tafice tana kaiwa bakin k'ofar fita tace masa "yaya tana zuwa"


"Thanks" yafad'a atak'aice ita kuma tawuce abunta.Billy kuwa saida tagyara kitchen d'in tsaf sannan tad'ebo had'in fruitslad d'in da tayi a bowl tanufo wajensa bakinta d'auke da sallama, can k'asan mak'oshi ya amsa sallamar yaci gaba da latsar wayarta batare daya kalli inda takeba, tafi minti biyu atsaye ita bata zaunaba kuma bata tafiba sannan yad'ago kansa yana fad'in "ai saiki zauna ko" saboda yanda ranta yab'aci tajawo kujera da k'arfi ta zauna had'e da d'aure fuska tana wasa da d'an yatsanta bayan ta ajiye bowl d'in da spoon agabansa, sanin halinta da yayi don yasan taji haushi yasa ya had'e hannuwansa yana fad'in


"Am sorry my noor" kauda kanta gefe tayi shikuma sai yarik'e kunnuwansa yana cewa 


"Pls noori yaya is so sorry" juyowa tayi taturo baki cikin shagwab'a tace


"Shikenan, amma kada akoma domin zuciyar Billy bata son  walak'anci"


"Angama ranki shidad'e baza'a sakeba, me kuma kika kawowa mijin naki?" Yafad'a yana bud'e bowl d'in data ajiye masa agabansa, d'an harararsa tayi kafin tace "abunda matar tasan mijin nata naso ne" ahankali yafara sha yana lumsar idanuwa saboda ba k'arya tabbas shi d'in masoyin fruitslad d'inne sosai, saida ya shanye tas sannan yature bowl d'in gefe yace


"Alhamdulillah matar gaskiya nagode, Allah yayi maki albarka"


"Amin yaya, ya shire shiren tafiya? Gobe kuma sai borno state ko?"


"Eh idan Allah ya yarda kuma ina zuwa da sayi d'aya su alhaji zasu zo nemamun aurenki da duk abunda yakamata, in the next 3month wannan had'in fruit d'in saidai kiyimunshi agidana"


"Hmm, kadaiji yaya nifa bazanyi aure ba har sai anyiwa yayuna don sune manya" d'aure fuska yayi had'e da k'walalo idanuwa awaje yace


"What? Ai baki isaba, idanma mafarki kikeyi kifarka don wlh bazan koma wajen aikiba saida matata" dariya tadinga yimasa tana fad'in "kai yaya wannan rawar k'afa kuma har ina gaskiya wannan tsarin beyi ba"


"Haka kikace" yafad'a cikin b'ata rai, da sauri tace "a'a yallab'ai wasa nakeyi" dariya yayi sannan ya d'auko wayar daya siyo mata ya saka mata layi had'e da mik'a mata sannan yace


"Ungo wannan Kiyi chaji sosai kuma don Allah inaso takasance tare dake akoda yaushe" kallonsa tayi cike da mamakin tsadar wayar daya mik'omata amatsayin tata, zatayi magana kenan yace


"Shiiii...bana son jin komai daga bakinki koda kuwa godiya ce" speechless tazama kafin tace


"Shikenan amma ayimun izinin bada tukuici idan an amince" "bana buk'atar tukuici matuk'ar bana harafi hud'u bane ko takwas"


"Shikenan kayiwa kanka, dama cewa zanyi ina k'aunarka amatsayin tukuicinka, kuma kagashi haruffa sha d'ayane amma ba matsala tunda kahutar dani" dariya yayi tare da cewa


"A haka ma ai nagode tunda anfad'a duk dako ba'a matsayin tukuici bane"




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Gaisuwar yau tamusammance zuwa gareku Auntynah da kuma takwarata *BILKN JML AND ZAINAB MUHAMMAD🌹* ina mai yimaku fatan alkhairin Allah yakai agareku a duk inda kuke bisa soyayya da k'aunarku ga wannan littafi na 'YAN UWANA NE, maganar gaskiya kud'in na dabanne kuma bazantab'a mantawa da kyawawan addu'o'inku agareni ba, ngd ngd ngd sosai, Allah ya albarkaci rayuwarki data dukkanin ahalinku kuma yasanya aljannah itace tabbataccen wajen zama agareku, I do really appreciate ur always care, LUVS U FILLAH_😘


💎Page_____64💎


 

   To shikenan tunda haka kace "narok'i Allah daya k'aro maka tarin arzik'i mai yawa da kwanciyar hankali acikin dukkanin al'amurranka,


"Amin ya Allah matar" tashi yayi ya zagayo har inda take zaune yai neildown agabanta yana kallon cikin idanuwanta yace


"Bilkisu har ga Allah bana son intafi nabarki, gani nakeyi tamkar zaki bawa wani k'ofar da zai iya fuskantarki yace yana sonki, kuma idan hakan yafaru tabbas zan iya rasa raina, Bilkisu inajin sonki ako wane fitar lumfashina ba adadi, tayanda bazan iya cigaba da rayuwaba idan babushi azuciyata, dena sonki atare dani tamkar tsayawar lumfashina ne, kiyarda dani kuma ki amince mani kikula mani da kanki idan natafi, nabaki amanar ajiyar zuciyarki da ruhinki dkm gangar jikinki, don Allah kikula mani dasu har ranar da zandawo gareki" yak'arasa maganar idonsa cike tab da k'walla, gefen d'akin dasu Ummi ke ciki sannan tajuyo takalla da sauri tana fad'in "wai meye haka kakeyi yaya tafiyafa ba mutuwaba, kuma natabbata maki cewa duk duniya banida burin rayuwa da kowane d'a namiji amatsayin miji inba kaiba, to meye nayin wud'annan maganganu haka agabana ko baka yarda dani bane" girgiza mata kai yayi hawayen da suka cika masa idanuwa nak'ok'arin fitowa yace "Nayarda dake Bilkisu amma tsoro nakeji kada wanda yafini iya dubarar sace zuciya yayi ido dake yanemi raba soyayyarmu, wlh bazan iya jurar hakan ba ko kad'an" jitayi tamkar tarungumesa saboda yanda yabata tausayi, dama haka yake matuk'ar sonta da yawa shiyasa baya iya hurar b'acin ranta, tabbas tayarda shid'in masoyine na musamman kuma tayi alk'awarin rik'e masa kanta shikad'ai batare data bari ya jigata akan sonta ba, itama hawayenne suka zubo mata tana kallonsa cike da k'auna tace "ka kwantar da hankalinka ni d'in takace kuma mallakinka domin kaf aduniyarnan kai kad'aine Allah yayiwa baiwa da dubarun da zasu iya sace zuciyata, kasa aranka ni takace kuma kai nawane  da yardar Allah, ko kamanta akullum ina fad'a maka cewa tare zamu rayu kuma tare zamu mutu kuma a k'ark'ashin inuwa d'aya"


Hannunsa yasa yagoge hawayen da suka zubo masa had'e da cewa "Dagaske kikeyi?" Saida tayi murmushi sannan ta d'aga masa kai had'e da cewa "sosai kuwa"


"Kinyi alk'awari?" Yafad'a yana nunata da d'an yatsa yana murmushi


"Tabbas insha Allah" tafad'a tana dariya hawaye kwance a fuskarta, zoben yaciro daga aljihunsa yabud'e 'ya jikkar da yake ciki ya ciro k'onk'on tare da bud'ewa yaciro zoben, d'ago kansa yayi yana kallon fuskarta yace "idan kin tabbatar da haka, to kikarb'i wannan zoben amatsayin shedar alk'awarin da mukayi tsakanin ni dake" had'e da mik'o mata zoben dake hannunsa, kallon zoben tayi dake walk'iya a hannunsa saboda hasken k'wan lantarkin daya bugesa tace


"What a nice...really luv it yayanah" hannunta tamik'a masa yasaka mata tana dariya, cike da farinciki yaturo zoben zuwa d'an yatsanta nakusa da k'arami da sauri tajuya hannun zoben yafad'a a tsakiyar tafin hannunta, d'auka tayi tasaka a yatsanta tana kallon hannun nata, sosai zoben yayi mata cicciccif kuma yama hannun nata kyau, d'ago kai tayi tana kallonsa had'e da d'an murza zoben ahankali tace


"Thank you yayanah it was so amazing and excited, luv you so much" tare da kissing zoben, rufe idanuwansa yayi yana murmushi tare da bubbuga saiti zuciyarsa yace "luv you uncountable my Noor"


"To ataimaka mun atashi kar Ummi tafito ta d'auka punishment ne nasa yaronta, kajamun rigima" dariya yayi sannan ya mik'e tare da jawo kujerar dake kusa gareta yajuyo da ita tana facing d'inta sannan yazauna.  Sunjima suna firar bankwana da jimamin rabuwa da juna tamkar karsu rabu, haka itama Umma da Ummi firar sukeyi ta bankwana, d'aga kai Ummi tayi takalli agogo taga past 12:00 sannan taci gaba da firar amma hankalinta gaba d'aya nakan 'yarta hakan yasa tamik'e tanufi kitchen da zimmar d'auko ruwa a fridge, bayan ta d'auko takashe wutar kitchen sannan ta kuma kashe tafalon yarage saura tagefen dining area inda suke zaune sannan tashige d'akin, hakan ya ankarar da Billy abunda mahaifiyarta kenufi tamik'e da sauri tana cemasa


"Gudnigth yayanah my milkheart" d'aga mata hannu yayi shima yana fad'in


"Sweet dream nourii!"


Kai tsaye d'akinta tawuce don kunya bazata barta taje wajensu Ummi taba, tana shiga tayi arwala tayi sallar isha'i sannan tayi azkar d'in bacci takwanta, kwanciyarta tagyara tana kallon silin had'e da d'ago hannunta tana kallon zoben daya bata, kissing d'in zoben tayi tanajin wata irin zunzurutun k'aunar yayanta nabin dukkanin sassan jikinta izuwa yanzu tagama tabbatarwa kanta da zuciyarta itama bazata tab'a rayuwa idan babushi ba, juya kwancin nata tayi zuwa gefen hannunta nadama sannan tarufe idanuwanta ahankali tana tunano irin yanda yake nuna mata masifaffen son da yake yimata, da wannan tunanin tasamu  bacci b'arawo yayi gaba da ita.


Bayan kamar minti biyar Ummi tamik'e saboda hankalinta baida natsuwa tanufi falon don ba tarbiyar mahmud pilot take tsoroba sharrin shaid'an daba ruwansa  da tsakanin wa da k'anwa balle d'an uwa d'an uwa, ajiyar zuciya tayi ganin basu falon sannan tanufi d'akinta, globe d'in d'akin takunna ta hangota kwance akan gado lokacin bata dad'e da kwantawa ba, shigowa tayi tabud'e toilet tarufe sannan tasake tofe d'akin da addua takashe fitilar tarufe sannan takoma d'akinsu, murmushi Umma tayi don har ga Allah taji dad'in hakan da Ummi tayi kuma yasake tabbatar mata da tarbiyar data bawa 'yarta tare da alfaharin cewa itama zata tarbiyantar mata da nata jikokin idan Allah yanufa.


Da sassafe kowa yatashi da sanin komawarsu Umma yau don haka da sukayi sallar asuba babu wanda yakoma bacci, gaba d'aya dady umurni yayi masu dasu had'u part d'insa bayan kowa ya hallara dady yafara bud'e taron da addua sannan ya yimasu nasiha sosai akan girman zumunci kuma suyi koyi da k'anwarsa 'yar uwarsa dake biye dashi akoda yaushe don d'abbak'a zumuncinsu duk da cewa ba ita kad'aice 'yar uwarsa ba amma tarik'e sa hannu biyu. Yana kawowa nan yafashe da kuka tunawa da sauran 'yan uwansa da yayi kuma suna raye amma gaba sun gujesa bisa wani banzan dalili nasu amma ita tarik'esa hannu biyu, godiya yadinga yimata yana rok'on Allah yafarant zuciyarta kamar yanda ta faranta tasa, gaba d'aya yaran kallonsa sukeyi cike da mamaki jin cewa dadyn nasu nada wasu 'yan uwan bayan umma inbanda Ummi da mom da kuma umma da suka san da wannan matsalar tuntuni, ita kanta Umma kuka takeyi sosai tunawa da abubuwan da suka faru can baya bayan haihuwar yaya Mahmud wanda shine yazamo silar rabuwarsu da 'yan uwansu,daga k'arshe dady ya tsagaita kukansa sannan yakalli Mahmud yace


"7:00am tayi yakamata ace kun kama hanya saboda bana son tafiyar dare sai katashi ku hanzarta ko?" Godiya Umma itama tashiga yimasa akan alkhairin da yayi masu da kuma kyautar motar da yayiwa Mahmud pilot sannan tasanar dashi bayan sati d'aya idan sun koma iyayensa maza zasuzo zancen nema masa aurenki Bilkisu, yaso ya gardanta hakan saboda yafiso sai suma 'yan uwanta sun tsaida nasu mazan sai yahad'asu tare yayi masu aure amma don ya sanyata farinciki kamar yanda take sakashi yasa yayi murmushi had'e da cewa "Shikenan hafsatu ai kema 'yarkice duk yanda kikayi daidaine, ubangiji Allah yakaimu kuma ya sanya alkhairi" duk suka amsa da amin sannan aka watse taron,


kasancewar Umma tasanarda alhajinta cewa yayanta ya yima Mahmud kyautar mota yasa tunjiya yaturo drivernsa ta motar haya don yaja d'ayar motar da sukazo da ita, sunyi bankwana da kowa cikin so da k'auna sannan suka d'auki hanyar komawa borno cikin jimamin rabuwa da 'yan uwansu wanda Billy saida tashige d'aki tayi kukar rabuwa da milkheart d'inta.


Mom kuwa tunda taji anfara zancen batun turowa auren Bilkisu gabanta yafad'i ganin cewa ganata yaran nan har guda biyu agabanta babu mashinshini kasancewar bata san da zance soyayyar dr Ahmad da Batool keyiba, sai taji wata irin damuwa da bak'in ciki sun rufeta lokaci d'aya har zazzabi na neman saukar mata, yau dai gida yayi tsit, tsakanin Billy da yaya Mahmud anrasa wanda yafi jin kewar Mahmud pilot atattare dashi haka itama Ummi yini tayi sukutum da kewar ami niyar tata wato Umma, hatta Bilal da Bassam sunyi kewar junior sosai don bini bini sai kaji suna cewa junior kaza junior kaza.


Dady kuwa yini yayi ad'aki yana rafkar kuka domin ahalin yanzu bayaji zai iya k'arsa rayuwarsa batare da 'yan uwansaba ahankali cikin kuka yake fad'in "why? Sufa 'YAN UWANA NE!, meyasa suka zab'in haka  atsakaninmu, meyasa zasu gujemu akan abunda yashafi rayuwata nikad'ai, tabbas ku 'YAN UWANA NE! kuma ina matuk'ar sonku, duk da kunbarni kunnesanta kanku dani amma ina bibiye da dukkanin alamurranku kuma zanci gaba da bibiyarku bazan tab'a rabuwa da kuba.


Yau kwanansu Umma uku da komawa kuma yaune dr. Ahmad yaci alwashin gabatar da kansa awajen dady don sun gama magana da Batool akan zaizo ya gaida dady kuma yagabatar da kansa kasancewar tkullum yana mak'ale da ita awaya don tuni yaya Mahmud ya turawa faraaha lambar Batool yace tatura masa don yadena damunsu.


Haka tab'angaren Billy kullum cikin waya take da Mahmud pilot suna raya soyayyarsu tare da ingantata, Basmah ma tuni ta dangana da soyayyar Mahmud pilot duk da har yanzu abun nacin zuciyarta amma ko kad'an bata bari kowa yasan halin da take ciki, hatta Batool da yaya Mahmud tadena bari sufahimci tana cikin damuwa ita kad'ai ke shanye abutta idanma ciwonne yatasar mata bata bari kowa yagane part d'in dady take zuwa acan gefen corridor dake can saman upstairs taci kukanta har tagaji sannan idan yalafa mata tadawo, tana k'ok'arin sakin jikinta dayin walwala kamar yanda tasaba.


Dr. Ahmad yasamu nasarar ganin dady kuma ya gabatar masa da kansa amatsayin wanda ke neman izinin zuwa wajen 'yarsa da sunan aure idan ya amince, sosai dady yayi farinciki kuma yatarbesa hannu biyu, yatambayiesa ko waye mahaifinsa kuma yabashi lbr a-z akansa batare daya b'oye masa ba daga k'arshe dady yabashi izinin cigaba da neman auren Batool kuma ya amince daya turo iyayensa don ga bayanin daya yimasa akan kowaye mahaifinsa yasanshi kuma yasan mutumen kirkin shiyasa yayi saurin amince masa. Dr mahmud yaji dad'i sosai da karamci irin na dady don kasa hak'uri yayi har sai yakoma gida yaba mamy labari yakirata awaya lokacin daya baro wajen dady yana labarta masa irin karb'uwar daya samu daga wajen mahaifin Batool, taji dad'i sosai itama harda 'yan k'wallanta a idanuwa tanata yiwa Allah godiya dayasa surikin d'an nata bai zamo d'aya daga cikin masu kud'in dake walak'anta talaka bane kamar alhaji Tukur.


Bayan yagama waya da ita yakira Batool yasanar da ita yanda sukayi da dady cikin farinciki tana tayi masa dariya yace tafito gashi aharaba zaiwuce. Kaisa tafarayi yagaida Ummi kafin yawuce sannan bayan sunfito tace yazo suje yagaisa da mom...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____65💎



     A parlour tayi masa mazaunin sannan tawuce bedroom ta iske mom kwance duk abun duniya yasha mata kai, babu abunda yanzu ya dameta kuma ya tsaya mata arai irin yanda ace wai Bilkisu k'anwar k'anwar 'ya'yanta ake zancen tsayarwa da miji bayan ansan yayyunta nanan zaune kuma su ba'a tsayar masu da mijin auren ba, abakin k'ofar d'akin tatsaya had'e da cewa


"Mom" sau kusan takira sunanta kafin tajuyo ta amsa mata tana kallonta "Batool lafiya?" 


"Lafiya klw mom, dama bak'one akayi yana palour zaune dadyne yaturo sa"


"Ok kije ina zuwa" juyowa tayi tadawo parloun tana kallonsa tare da yimasa murmushi shima yamayar mata yana kallon k'wayar cikin idanuwanta had'e da murza hannayensa waje d'aya, mom nashirin saukowa daga kan gadon saiga kiran dady yashigo awayarta, tana d'agawa tagaishesa cikin girmamawa, bayan ya amsa sund'an tab'a firar soyayya kamarta minti biyu yake sanar da ita zancen dr.Ahmad da abunda yakawoshi na neman auren 'yarsu, daga k'arshe yace tafara zuwa sugaisa da yaron saita iskoshi part d'insa su tattauna maganar, sosai mom taji dad'i aranta sukayi sallama da dady sannan ta ajiye wayar cike da fatan Allah yasa yaron d'an babban gidane wanda yad'ara Mahmud pilot komai.


Ita kuma Batool kitchen tashiga ta d'auko ruwa da lemon exotic ta azo akan tray had'e da d'oro glass cup akai tayo cikin parloun, a gabansa ta ajiye tabud'e gorar ruwan ta tsiyaya a cup ta mik'a masa tana fad'in "Bisimillah dr." Murmushi ya sakar mata sannan yamik'o hannu yakarb'i cup d'in hannunta "Nagode gimbiyata, Allah ya nuna mun ranar da nine zanyi maki haka" yana rufe baki saiga mom tashigo parloun fuskata ba yabo ba fallasa, da sauri ya ajiye cup d'in ita kuma tanemi kujera tazauna tana kallon mom k'asa k'asa cike da fargaba, saida tazauna sannan ya d'an zamikke akan kujera had'e da duk'awa yana gaisheda ita, tunda ta shigo takallesa ta tuno da fuskarsa ranar da yaje asibiti ganin Mahmud pilot, kallonsa tayi daga sama har k'asa kafin tace


"Daga ina?" Saboda gaba d'aya tun ranar data fara ganinsa bai yimata kuma ace wai shine keson 'yarta, Batool najin wannan tambayar da mom tajefo masa amadadin ta amsa gaisuwar da yayi mata gabanta yafad'i, muryar Basmah da fitowarta kenan taji abunda mom d'insu keshirinyi tace


"Laaa..dr Ahmad yau kaine agidanmu? Sannunda zuwa" tak'araso cikin parloun tana yimasa murmushi, duk'ar da kansa yayi don dama har ga Allah baisan ta ina zaifara bawa mom amsartaba, zaunawa gefen mom tayi tana dariya tare da rik'o hannunta tace "Mom wannan shine dr. Ahmad cikakken likita kuma k'wararre a 'b'angaren gyaran k'ashi wato orthopedic doctor, shine yakula da Batool ranar da k'afarta naciwo muka kaita asibiti" dakatar da ita mom tayi cikin b'acin rai tahanyar d'aga mata hannun had'e da cewa


"Kibarshi yayi bayani da kansa mana ko bayada bakine?" Cikin i'iniyar  muryar da baisan yanada itaba yace


"Ayi hak'uri mom, kamar yanda dai tayi bayani ni sunanan.." Shima katsesa tayi tahanyar cewa "Bana buk'atar jin wannan yanzu "fad'amun waye mahaifinka kuma meye sana'arsa a wannan garin" rik'o hannun Basmah Batool tayi kamar zatayi kuka jin abunda mom keahirinyi, girgiza mata kai tayi alamun tayi hak'uri, bud'e baki dr.Ahmad yayi zaiyi magana saiga yaya Mahmud yashigo parloun, gaida mom yafarayi sannan yajuyo ya mik'a masa hannu suka gaisa,


"Abokina idan kungama gaisawa da mom ana jiranka awaje, i think emergency call ne daga hospital" yatsa Batool tasa tagoge hawayen da suka zobo a idanuwa had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya, duk'ar dakai dr. Ahmad yayi sannan ya d'ago yana kallon mom yace


"Sunana Ahmad Bashar mai fulawa kuma ni cikakken haifaffen wannan jaharne, nai karatuna na boko dana arabiya daidai gwargwado kuma yanzu haka ni jami'in lafiyane a asibitin Jidda specialist hospital, muna zaunene a anguwar g.r.a nida mahaifiyata, mahaifina kuma bakowa bane face k'aramin d'an kasuwa mai matsakaicin k'arfi dabai rasa rufin asirin ciyarda iyalansa ba kuma Allah yayi masa rasuwa kimanin watanni biyar da suka wuce, bamuda kud'i amma munada d'inbin soyayya wacce da ita nazo nan don neman amincewarku na auri 'yarku, ina son fatima kuma ina son na aureta, natabbata koban bata komai ba aduniya zan bata soyayya da farinciki nahar abada" yana gama fad'ar haka yamik'e tsaye tare da cewa


"Kiyi hak'uri mom idan nab'ata maki rai acikin amsar tambayar dana baki da kika yimun, nizan tafi" sannan yajuya yabar wajen zuciyarsa cunkushe da damuwa, tashi Batool tayi zatabi bayansa mom ta dakatar da ita 


"Karki kuskura kibar palourn nan idan ba b'acin rai kike so yabiyo bayanki ba, kimanta dashi don keba sa'ar sabace ni bazan bari 'yata ta auri mai jinin mai saida fulawa ba wanda yamutu a sanadiyar bashi, tsaye cak dr. Ahmad daya kai bakin k'ofar fita yayi tare da juyowa yakalli mom sannan ya kalli Batool dake hawaye yayi murmushi tare da ficewarsa, fad'a mom tadinga yiwa Batool sosai akan wai taje tayo mata kwashe kwashen d'an gidan maifulawa da mahaifinsa bai barmasa gadon komai ba saina bashi tabuga mata warning akan karta kuru tasake kulasa saboda tadad'e da jin tarihin mahaifinsa agari bazata yarda tahad'a jininta da matsiyaci kamar saba bedroom d'inta tashige tanaci gaba da banbami da kumfar baki, tana shigewa da sauri tafice tabi bayansa ita kuma Batool tazube k'asa tana kuka had'e da maimaita "innalillahi wa inna ilaihirraji'un"


Yana k'ok'arin ficewa daga gate ne bayan yaya Mahmud yayita bashi hak'uri Basmah ta cimmasa "docter" tafad'a tana k'ok'arin dai daita tsayuwarsa, juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ba walwala, duk'ar da kanta tayi k'asa kafin tad'ago kanta tace


"Don Allah kayi hak'uri da abunda mom tayi maka nida 'yan uwana duka bamuji dad'in hakan ba ko kad'an" "babu komai yayya Basmah dama haka rayuwa tagada wani lokacin farinciki wani lokacin bak'in ciki wani lokacinma atare suke zomaka da farinciki da kuma bak'in ciki kamar dai yanda suka zomun yanzu atare, karku damu kinji"


"Kayi hak'uri don Allah kar hakan tashafi soyayyar da 'yar uwata keyimaka domin natabbata bazata juri rasakaba saboda tana matuk'ar sonka sosai" tsayuwarsa yagyara yana murmushin da saida hak'oransa suka bayyana yace


"Haba yayya kima dena wannan tunanin domin ni wannan abun bazai sa naja da bayaba, fatimafa itace rouhina, zuciyata da kuma gangar jikina taya za'ayi narabu da ita akan wannan d'an k'an k'ananen abun, ashirye nake dana bada dukkanin farincikin rayuwata matuk'ar hakan zaisa na mallaki fatimatah" dariya Basmah tayi jin yanda ya ajiye kalmar sunan fatimah saika rantse yafi kowa iya fad'ar sunan sannan tace


"Shikenan dr. Nagode Allah yatabbatar maku da alkhairinsa"


"Amin yayya yanaga kina dariya don nace fatimatah ko bazaki bani qanwar takiba ne"


"Rufamun asiri dr.karka jamun naje asibiti ak'i dubani, ai indai Batool ce nabaka gaba d'aya gangar jikinta da rouhinta kai kad'ai nake jira kazo ka d'auki aburka" murmushi yayi sannan yace


"Shikenan yayya godiya nake sai anjima ni zanwuce"


"To agaida mana da mamynmu sosai" farincikine yarufe dr. Don yana mugun son duniya yaji ana karrama mamynsa da girmata "in aha Allah zataji" yafad'a tare da ficewarsa aransa yanaji komai rintsi komai wuya bazai tab'a rabuwa da Batool d'insaba...



_Manage  pls kutarbene anjima in sha Allah_





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Ina kuke iyayen K'warai iyayen kirki, kumatso kusa domin gaisuwar yau takuce ku kad'ai, nagaisheku durum durum tare da fatar alkhairi agareku manya iyayen yaran gobe *Mmn Sss, Mmn Adnan, Mmn muhad, Mmn hanan, Mmn taufiq, Mmn Usman, Maman fatima and Ummi, Maman Ahmad and fatima da kuma oum Imaan* ina matuk'ar jin dad'in yanda kuke bibiyar wannan littafi, ngd ngd ngd sosai ubangiji Allah yabaku aljannah da rahamarsa kuma ya albarkaci yaranku👏🏻 ina so kusani ni Billy s fari ina alfahari daku akoda yaushe_😍


💎Page_____66💎


 

    Koda ya isa gida bai sanar da mamynsa labarin matsalar daya samu awajen mahaifiyar Batool ba illama dad'a bata labarin karamci da halacci da mahaifinta ke dashi, sosai mamy tanuna masa farincikinta saidai idan yalura da ita kamar akwai abunda kedamunta.


Kusa da ita yadawo had'e da rik'o hannunta yace "Mamynah meyake damunki naga bahaka natafi nabarki ba kuma koda mukayi waya banji alamun kina cikin wannan damuwar da nake gani atattare dake ba?" Fashewa da kuka tayi tace "Yau antunomun da rasuwar mahaifin kane, naso yana raye yagani kuma yaji abunda ya dad'e yana addu'a taganin ansamu zaman soyayya da lafiya tsakanina da 'yan uwansa amma abun yacutara, sai gashi yau da baya raye Allah yakarb'i addu'arsa kuma hakan tafaru" hannu tasa ta d'ago hab'arsa tana goge hawayen idanuwanta taci gaba da cewa "Yau baffanka wato yayan mahaifinka sunzo harcikin gidannan lokacin bandad'e da gama waya d'a kaiba suna kuka tare da nadamar abunda suka yimana nida mahaifinka, sun zubar da hawaye sosai suna rok'ona dana yafe masu abubuwan da sukayimun suntuba sunyarda da kuskurensu, kuma dama canni banrik'esu araina ba nace duka nayafe masu abunda na sani dama wanda bansani ba, sunjima suna jiran dawowarka kaima surok'eka kayafe masu, anan nake sanar dasu cewa kana wajen nemo auren surukarsu, sunji dad'i sosai kafin sutafi akan cewa jibi zasu dawo saboda kiran da akayi masu daga gida ana bid'arsu da gaggawa, wannan abun shiya janyomun tunawa da mahaifinka har yasa damuwar ta taushe farincikin wannan labari dana so yimaka albishir dashi", Rungumeta yayi sosai shima yana hawaye yace


"Alhamdulillah mamy naji dad'i sosai nima zan shiga cikin 'yan uwana, ubangiji Allah yajik'an Abba yagafarta masa"


"Amin ya Allah, ya kabaro 'yatah lafiya take?"


"Lpy klw sunce agaisheki sosai da ita da yayarta"


"Allah sarki ina amsawa, ashe tanada yaya?"


"Eh mamy inkika ganta kamarsu d'aya da 'yarki d'an haske kawai ne ya banban tasu don kina ganinsu zaki zata sud'in 'yan biyune"


"Ikon Allah! To Allah ya albarkaci rayuwarsu"


"Amin mamynah ni kad'ai, dadyn tama yace inturo iyayena idan har da gaske nakeyi, to da nayi tunanin inje infad'owa su baba bala da liman suje tare da kayan nagani inaso amma yanzu nabar shawara ahannunki duk yanda kikace kuma kika ga yadace sai ayi" 


"Karka damu idanma sud'in zasuje duk d'ayane sai asanar dasu tunda wuri amma da zaka iya hak'uri har zuwa jibi idan baffan naka yazo tunda yasan da maganar sai akira shi liman d'in sutafi tare kai kuma saika tanadi abubuwan daya kamata aje dasu kafin ranar tayi" Shiru yayi na d'an mintota kafin can yace "Shikenan mamy babu damuwa Allah yakai ranmu"


"Amin yaron Abba" tafad'a had'e da mik'ewa tabar d'akin, tana fita yacire safunan dake lak'e a k'afafuwansa tare da rigar jikinsa ya lak'e ajikin hanger yarage dagashi sai dogon wandon shaddar daya cire da singlet ya haye akan gadon tare da rufe idanuwansa ahankali yana tunano maganganun da mom tayi masa, duk dayaji zafinsu azuciyarsa hakan baisashi tsanartaba saboda kima da daraja da take da ita a idanuwansa koba komai takasance mahaifiya awurin yarinyar da yakeji tamkar jinin jikinsa don haka dole yamanta da abunda tayi masa, beside duk maganganun data fad'a gaskiyane babu k'age balle sharri aciki saidai ita cinfuska da walak'anci da rena arzik'in mutum ba abubane mai kyau kuma ko a musulunce Allah da manzonsa duka sunyi hani da hakan, yana cikin wannan dogon tunaninne yaji rurin k'arar wayarsa dake neman agaji acan cikin aljihun gaban rigarsa dake rataye, tashi yayi ya d'auko wayar ya d'aga kiran had'e da karawa akunnensa yana murmushi,


"Hello rabin raina ya kike" yafad'a tare da sake komawa kan gadon yakwanta fuskarsa na kallon silin, cikin muryarta maikama da tasha kuka sosai tace


"Lpy klw my angel hop ka isa gida lafiya?"


"Sosai kuwa swthrt gani kwance yanzu nagama tunanin mom d'inmu, pls don Allah kibata hak'uri bisa abunda yafaru d'azu, bana son wannan abun yashafi soyayyarmu ko kad'an"


"Insha Allah zanbata my angel, amma kaima kayi hak'uri bisa zafafan kalaman datayi agareka, ko kad'an banji dad'in faruwar haka kuma banzaci hakan zai faruba, am so srry for dt my angel" tafad'a hawaye nagangarowa daga gefen idanuwanta,


"commonnn..swthrt kar wannan abun ya dameki, ai ita uwa tanada matuk'ar muhimmancin da duk abunda tayi ga d'anta daidaine kuma tayine don tana sonsa, saidai awasu lokutan soyayyar kejawo asamu akasin da zaisa a aikata kuskure aciki bawai don a k'untata rayuwar 'ya'yaba, dani dake duka d'ayane don haka dole muyi hak'uri da duk wani kuskuren mom d'inmu kinji ko?"


"Eh my angel nagode sosai daka zamo mai yiwa mahaifiyata uzuri da kuma fahimtarta, don Allah kak'ara hak'uri nasan da sannu zata fahimceka"


"Karkiji komai nafad'a maki ko kin manta matsayinkine awajena?" Murmushi tayi sannan tace


"Bazan mantaba saboda nasan my angel namusamman ne"


"Dagaske kikeyi hayaty ni d'in na musamman ne?" Yafad'a tare da mirginawa yajawo pillown dake ajiye can gefe ya rungume yana murmushi


"Sosai kuwa my angel, saboda arayuwata bantab'a ganin mutumen da Allah yayiwa baiwa mai tarin yawa kamarka ba" lumshe idanuwansa yayi had'e da cewa 


"Kifad'amun wace irin baiwa nake da ita wacce tasani zamowa namusamman awurinki nikuwa nayi maki alk'awari zanbaki tukuici mafi soyuwa azuciyarki" 


"Shikenan bari nafad'a kodon wannan feeling da kake dashi yasake samun gurbin zama fiye da yanda kake dashi don nasan hakan zaisa 'yanmata suk'ara nisanta kansu dakai" 


"Ki hanzarta fad'a kada kisa inyi azarb'ab'in baki tukuici tunkafin naji abunda kikeson fad'a, 'yar dariya tayi kafin ta juya kwanciyarta zuwa kife hab'arta na akan pillow sannan tace


"Ahmad! Suna mai matuk'ar daraja da Allah ya ambata acikin alqur'ani, kasantuwar wannan suna atare dakai yasa Allah yayi maka ni'ima da baiwar hak'uri, fad'ar gaskiya, kwarjini, cikakkiyar siga, fikrah tare da iya magana, kyakkyawar zuciya, sanyayyan murmushi, girmama iyaye, tarin ilimi,  sanin yakamata sannan abu mafi girma da yasa nake matuk'ar k'aunarka shine rama kyakkywa da mummuna" 


"Kai.ka.kai..hayatie kaffa kisa nafad'o akan gadon tsabar farinciki, mamy ta'aza mani dariya" 


"Kasan Allah nama manta wasu my angel, amma duk wud'annan abubuwan suna cikin baiwar da Allah yayi maka"


"Hayatie mezan baki amatsayin tukuici domin wanda natanadar maki nida kaina na tabbatar yayi kad'an, amma inaso kisani ina yimaki so irin wanda romeo beyiwa Juliet ba haka kuma majnunnin laila baiyiwa kaima shiba"


"My angel kenan! Ai nadad'e da sanin hakan domin soyayyar ka agareni fili take azahiri ba b'oyayyiyaba abunda kawai nakeso shine, duk lokacin daka fita wata takalleka to kace mata ni nace antsayarmun dakai amatsayin mijin da zan aura sannan katsole mata idanuwa tayanda bazata sake iya kallonkaba" tak'arasa maganar tana dariya, k'walo idanuwa yayi awaje kamar zasu fad'o k'asa shima d'in yana dariya


"Ki rufan asiri hayaty kada kisa akirani da mijin makafi don natabbata hukunci da iyayensu zasuyi mun baiwuce na saina auresu" da haka sukaci gaba da firarsu cikin so da k'auna tamkar babu wani abun daya faru d'azun.


Yaya Mahmud kuwa tuni ya sanarwa da papi cewa zab'insa itace zab'in daya yimasa don haka jaddi da papi sukayita murna tare dasa albarka koda maganar taje kunnen dady cewa yayi babu matsala don dama ita fareeda d'iyar amininsa tuni mahaifina yasanar dashi cewa mahaifiyar yarinyar da yarinyar duka basu yarda da zancen cewa ahad'asu su biyu ya auraba wanda jin hakan bak'aramin dad'i yayiwa yaya Mahmud ba, nan take dady da amininsa sukaje suka nemowa yaya Mahmud auren faraaha wajen jaddi da k'annen mahaifinta bisa jagorancin papi, kuma alhamdulillah ankarb'esu cikin mutunci da girmamawa tare da karramawa, sosai dady yaji dad'in samun sarakanai nak'warai da yaronsa yayi wanda saida farincikin da yake ciki ya bayyana k'arara afuskarsa.


Yau sati d'aya da komawarsu Mahmud pilot borno kuma yaune mahaifinsa da k'annensa suka sanar da zuwansu, hakan yasa gidan suka tashi da shire shiren tarbar bak'i na musamman, wata hotel dady yasa akayo odar kalolin abinci da namomi kala kala, ga lemunan kwali dana goruna da aka tanada suma banda snacks da fresh lemons da suma akayo oda awajen k'wararrun Baker's kai abun sai wanda yagani, kiran dr.Ahmad daya shigo wayar dady yanzu yasa aka sake yowar wani sabon had'i na musamman duk don tarbar sarakanan nashi don dama tun kwana biyu da suka wuce dr.Ahmad yaje har office d'in dady ya sanar masa da zancen zuwan iyayensa amma sai ya dakatar dashi akan yayi hak'uri yabari sai bayan wasu kwana biyun auzo kenan ranar da iyayen Mahmud pilot suma zasu zo, yayi hakanne saboda abun yazo masu cikin sauk'i to shine dr. Ahmad d'in yakirasa akan zuwa bayan azahar iyayen nasa nanan isowa. Yaufa idan kaga fuskar dady da Ummi zaka d'auka ranar auren yaran nasune tazo sab'anin mom dahar yanzu tak'i sauka akan dokinta nabata son auren Batool da dr.Ahmad, duk nasiha da lurarwar daya kamata dady da yaya Mahmud da Basmah sunyi mata amma fir tak'i tasauko itadai kawai bata sonsa, dady kuwa da ransa yab'aci kai tsaye yace mata kotana so ko bataso sai ya aurawa 'yarsa wanda takeso donshi natsuwa da hankalin yaron sunyi masa, 


Yaya Mahmud ma cike yake da farinciki yau za'azo neman auren k'annensa wanda shi dady ya wakilta a matsayin wakeelin 'yan uwansa, mahmud ikon allah yaro kenan mai hankalin manya da kuma dattako, farinciki sosai yakeyi duk da ak'asan zuciyarsa tausayin k'anwarsa Basmah ke kwance aciki, jiyake inama ace duka su akunne haka zai faru agaresu da yafi kowa farinciki, ita kuwa hankalinta kwance tariga ta dangana tabarwa Allah komai saidai idan ciwon yatasar mata tashige toilet ko can part d'in dady tayita fama har Allah ya kwantar mata dashi, izuwa yanzu ciwon yayi mata tsanani don bata bari kowa yasan halin da take ciki balle akaita asibiti ashawo kanta duk data d'an rame babu wanda yakula da hakan kasancewar dama can batada wani jiki sosai shiyasa aka kasa fahimtar hakan saidai duhu da tayi kuma shima ba sosai ba.


Alhamdulillah duka family's d'in biyu sun iso lafiya tsayawa fad'ar yanda abu yakasance b'ata lokacinne, domin takowa ne b'angare suntaka rawar gani da kuma ban mamaki wajen kayan nagani ina so da suka kawo especially dr Ahmad da mom keyiwa kallon matsiyaci d'an mai saida fulawa sai gashi yayi abunda ko wani maikud'in bazai iya ba.













 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Bazai yuyu na manta da d'inbin soyayya da k'aunar da kuke yiwa wannan littafi, hakan yasa nake mik'o gaisuwata tare da fatan alkhairin Allah yakai agareku aduk inda kuke my sisters *Haifa💋, Jidda alk'ali, Ni'ima barhama, Asma'ul husnah💏, Kubrah, Shamma halliru, Oum Suhaima, Ummeeteey, Sara2zamfara, Balqias, Hawwabilyer, Chamsiya, Salmah shafi'u salis, Hauwa isa Ibrahim, Maman ummi, Sumaya sifawa, Jamila abdullahi garba, khadija  tukur* a gaskiya kunada matuk'ar yawan da idan nace zan tsaya lissafoku gaba d'aya page d'innan bazai isheniba, amma ina masoya wannan littafi na 'yan uwana ne, wud'anda na ambata dama wud'anda ban ambaci sunan suba su sani cewa kune hasken fitilar dake yadamun acikin rubutuna kuma ina alfahari daku a duk inda kuke, ina rok'on Allah yafaranta dukkanin zuciyoyinku kuma yabaku aljannah firdausi da rahamarsa👏🏻, ngd ngd ngd sosai da zallar k'aunarku Allah yabar zumunci_🤝🏻


💎Page_____67💎



  Sanadiyar maganganun da mom tayi masa yasa yaci burin nuna mata cewa ba tarin dukiyane arzik'i ba, kyakkyawar zuciyar iyayi dakai shine arzik'i, don kuwa shima yaya taka rawar ganin dta zarce fiye da wacce iyayen Mahmud pilot sukayi sosai, kwalayen lemun exotic katam  biyar sai kuma na hollandia suma katam biyar sai biscuit shima kala kala har kwali goma masu matuk'ar tsada ga kwalayen cingums da mintuna kowane kwali goma ga chaculate chaculate kwali biyar, ga dabino kusan tiya goma had'e da k'aton kwali da aka zubo sabulayye da turarukka masu kyau da tsada. Ba dady kad'ai ba hatta yaya Mahmud yayi mamakin kayan da dr Ahmad yakawo, duk da itama Billy Mahmud yazubo kaya sosai saidai gaba d'aya tsari da had'uwa da burgewar kayan dr. Ahmad sun tsallake tunani godiya su dady sukayi sosai tare da d'inbin alkhairin tukuici da yayima kowane ahalin iri d'aya batare da banbantawa ba bayan ya gabatar da kowannensu da matsayinsu, suma d'unki dad'i K'warai dagaske inda anan iyayen Mahmud pilot suka bijiro da suna son ayanka masu sadaki zasu biya had'e dasa rana saboda yanda Mahmud pilot yatsare mahaifinsa da rigimar shi bazai koma wajen aikiba saida matarsa, dady yaga gaggawar hakan sosai amma saboda karamci 'yar uwarsa agaresa yasa yaji bazai iya girgiza masu ba don haka yaba yaya Mahmud dama daya yanka masu sadaki, Shiru yaya Mahmud yayi don shima d'in baiso hakanba yaso abari har nan dawani lokaci zuwa sannan itama 'yar uwarsu Basmah tatsayar da miji sai ayi masu komai atare,


"My son kai muke sauraro kabar mutane azaune, mekake tunanin?" Sai alokacin yabud'e baki yace


"Dady idan sun amince kowace sadakinta za'a biya naira dubu hamsin" kallon dady qanen mahaifin Mahmud pilot yayi had'e dayin murmushi yaciro dubu d'ari biyu yace 


"Ga wannan dubi d'ari biyune amatsayin sadakin 'yarmu domin tafi k'arfin hamsin awajen mu" sudai iyayen dr.Ahmad dama basuzo da shirin biyan sadakiba don haka baffansa yafita waje ya kirasa awaya yasheda masa cewa tofah har sadaki anyanka kuma gashi su basuzo da wannan shirinba amma ita 'yar uwar tata har iyayenta sun amince kuma sunbiya dama su suka d'auko maganar, wani irin farincikine ya lullub'e dr lokacin yana duba wata marar lafiya yamik'e tsaye had'e da cewa  


"Baffa kuma ku amince ko nawane zanbiya, saiku sheda masu cewa zaku sake dawo ku kawo sadakin daga baya saboda yanzu ba'a shirya kukeba, ni kuma dama k'arshen watannan nakeso naciro kud'in da nake tariya a account saboda wata lalura dake gabana sai acira akai masu"  


"To shikenan ahmadu kayi hak'uri ni yakamata nayi maka wannan amma gashi saboda alfahari da sonzuciyata yasa arzik'in nawa da nake tink'aho dashi yak'are banida hanyar da zan iya yimaka d'ana abunda zaisa yayi alfahari dani amatsayin wan mahaifinsa" baffa yafad'a yana kuka.


"Haba baffa miye haka kakeyi, aikoda kana dashi nafi farinciki ace ni nabiya sadakin matata dakaina akan abiyamun, kuma koyanzu baffa ina mai alfahari dakai cewa a matsayinka na wan mahaifina kaje kanemomun aure da kanka, kadena wannan tunanin kajiko baffa"


Saida yagoge hawayensa da hannu sannan yace "shikenan Ahmadu Allah yayi maka albarka"


Acan cikin d'aki kuwa yaya Mahmud cewa yayi bazasu karb'i dubu d'ari biyuba amatsayin sadakin Billy saboda idan kud'i zasu saka to tabbas sadakin nata sai yafi dubu d'ari biyu amma albarkar abu tafi yawansa kuma albarkar Allah suke nema aciki don haka subada dubu hamsin d'in sun isa, dady dake gefe zaune abunsa yayi murmushi tare da godewa Allah daya yimasa ni'imar d'a kamar Mahmud har ya iya zaunawa yayi wakilcin auren k'annensa da yakamata ace 'yan uwansane sukayi, bud'e baki k'anen mahaifin mahmud pilot yayi zaiyi magana dady ya dakatar dashi tahanyar murmushi yana fad'in 


"A'a alhaji mubarshi ahaka, ai yagama magana tunda yace albarkar Allah ake nema kawai muyi fatan Allah yanuna mana lokaci kuma yasanya masu albarka"


Adole auka cire dubu hamsin d'in suka mik'owa yaya mahmud yakarb'a suna fad'in


"To alhamdulillah Mungode sosai Allah yatabbatar mana da alkhairinsa." Kowa ya amsa da "amin" 


Shikuma baffa tab'angaren sa bayani yayi masu kamar yanda dr.Ahmad yace yayi kuma sun amince da hakan, nandai shima dady yarok'esu dasuyi hankuri zancen sarana har sai yayi shawara da iyayen yaran mata da kuma 'yan uwansa in sha Allah zai nemesu ya sanar dasu a duk lokacin da suka kai k'arshe,


Bahaka suka soba amma tilas sukayi hak'uri saboda duba da irin shima karamcin da yayi masu daga nan baffa ya jagoranci taron yayi masu addu'ar watse taro sannan kowanensu yakama hanya da kyakkyawan labari zuwa ga ahalinsa bisa karamci irin na Allah Bashar mai furnitures. 


Bayan sun wucene dady yasa yaya mahmud yakira masa Ummi da mom, kusan atare suka shigo mom sai faman wani d'ad'd'aure fuska takeyi ita kuma ummi fuskarta d'auke da farinciki taje kusa dashi ta zauna tana fad'in "mun amsa kira ranka ya dad'e Baban amare harma da angwaye duka anya wannan rana bazamu rubutata a qundin tarihiba irin wannan k'yalli da annurin da fuskarka kefitarwa, yau sainaga siga da kamalar da Allah yayi maka tak'ara bayyana ka k'ara kwarjini sosai fiye da ko yaushe" tak'arasa maganar cike da tsokana, dariya yaya Mahmud yayi shikuma dady yashiga gyaggyara babbar rigarsa yana d'aga allon kafad'unsa wanda hakan yasa mom data nemi waje can nesa dasu tazauna batasan lokacin da murmushi ya kucce mataba, tabbas yau ba k'arya suma maigidan nasu yayi  matuk'ar kyau sosai masha Allah, kallon Ummi yayi sannan ya juya yana kallon mom itama irin kallon nan da ake cewa ya kuka ganni, kauda kai gefe tayi duk dako tasan ya wanku sosai amma saboda takaici dake cinta naganin kayan nagani inason yaransu wasu sunfi wasu yawa yasa takasa yaba masa don aranta ta tabbatar marar yawan sune na 'yarta, murmushi yayi had'e da kallon kayan da yaga tak'afe da idanuwa ya girgiza kansa, muryar Ummi yaji tana fad'in gaskiya yau babu inda zakaje abu Mahmud irin wannan kyau haka duk watarbon sarakanai kad'ai?. Kashe mata ido d'aya yayi had'e da cewa 


"Anfad'a maki sarakuta wasace nifa yanzu nazama cikakken dattijo saboda haka girma da matsayi sunk'aru"


"Aikuwa naga alama yallab'ai to Allah yatabbatar mana da alkhairi" duk suka amsa da amin inbanda mom datayi kamar batasan dasu awajen ba, sake juyowa dady yayi yana kallonta had'e da mik'a mata hannu yace


"Zonan kizauna amaryata kifad'amun waya tab'aki haka kike d'addaure fuska keda yakamata kiyi farinciki?" Kallonsa tayi taga yanda Ummi kezaune kusa dashi sosai tana murmushi saita kauda kai,


"Yau sarautar tamotsa kenan,! To bari injuya ga uwargidana ta taimaka tayoman biko tunda baza'a kulaniba" yak'arasa maganar yana kallon Ummi, murmushi tayi duk da tad'anji kishi aranta amma saita danne tace


"A'a yallab'ai rufani kasayani, ai wannan tsakaninku ne don kafi kusa da ita" 


"Au haka zakice, lalle tunda abun naku hakane bara nafita abuna kozan samo 'yar bazawarar da zata kulani"


"Dadai kayi hak'uri kasasanta dana ciki kaga sai inbaka wuri har kagama lallashin k'anwar tawa don kam nasan ita kad'aice zata iya kula dakai fiye da duk wata bazawarar da zakayi d'okin d'aukowa" ba dady ba hatta yaya Mahmud saida Ummi taburgeshi dariya yayi sannan yace


"Dady nibari inwuce don naga alamar yau tunawa da baya iyayen nawa keyi, haddai mom irin d'an feeling d'innan da in budurwa taje fira takeyiwa saurayi to shine tatuno dashi don haka dole dady sai kayi da gaske" yaya mahmud yafad'a yana dariya, ai kafin yarufe baki yaga mom tanufo wajensa rik'e da throw pillow tana dariya


"Kabarni inkamaka nan zaka gane sai kayi dagaske, ja'irin yaro kawai" dayan gefen dady yakomo yana fad'in


"Afuwan mom aigaskiya nafad'a kuma ga dadyna nan atambayeshi idan ba haka bane" wajen tanufo dama haka yakeso tana zuwa da sauri yamik'e yabar wajen yana dariya yakoma k'ofar d'akin yayi tsaye had'e da folding hannayensa akan k'irji yana kallon yanda dady yarik'e hannun mom yanaso yazaunar da ita ai kuwa cikin sa'a yasamu tazauna amma fuskarnan a d'aure, ajiyar zuciya yaya Mahmud yayi tare da jindad'i aransa don yana matuk'ar son yaga iyayen nasa zaune waje d'aya cikin kwanciyar hankali, wayarsa yaciro cikin aljihun gefen rigarsa ya d'aukesu hoto suna dariya su duka saboda dady da yace "kinga ranar haihuwa cikin sauk'i da wayau d'ana yasa kin kawo kanki da kanki harnan nayi maki damk'ar kukun kaza, hakan daya fad'a shiyasa su dariya don sai alokacin suka gano cewa dubarace Mahmud yayi wajen canza mata wajen zama da inda mahaifinsa keso, 

 

Kallon hoton yayi yaga yanda yayi kyau sosai sannan ya kalli iyayen nasa yak'ara d'aukarsu har sau uku kowane kala daban daban, sunjima dady najansu da fira cikin so da k'auna kafin ya bijiro masu da dalilin kiran daya yimasu, sosai mom tasha mamaki lokacin da dady yayi masu bayanin cewa kayan da sukafi yawa sune na Batool, juyowa tayi tace 


"dadyn yara anya yaronnan shiya kawo kayannan, ina yaga halin iyayinsu shida naji ana fad'ar cewa mahaifinsa bai barmasa komai ba sai gadon bashi, mukam da zakabi tatawa wlh amayar masa da abunsa kar azo muna zaman zamanmu yaje yajawo mana fitina, yo wannan indai ba sa...." Ai kafin tarufe baki dady ya katsa mata tsawa cikin b'acin rai da qunar zuciya yace


"Tir da wud'annan miyagun maganganu naki waike har yau bazaki daina cin zarafin yaronnan ba, meyasa bakyada tunani? Kinmanta yaronnan babban likitane hakan da kike tuhumar inda yasamo kud'in yin wannan hidima, to idanke bazaki d'auki kayanba kisanya albarka kuma kiba duk wanda yakamata to kibarmun ni inaso kuma wallhi matuk'ar ina raye Batool batada mijin daya wuce dr Ahmad tunda tana sonsa koda kuwa bayada ko 'yar biyar kuma zaicigaba da biyan gadon bashin mahaifinsa da kike ik'irarin anbar masa har iya k'arshen rayuwarsa to saina aura matashi" hannu yasa a aljihu ya ciro kud'i ya k'irga dubu hamsin ya ajiye saman jikinta yace "ga wannan sadakin 'yarkine kuma nan da wata uku za'a d'aura aurensu, idan kinga dama kizagaye duniya kina aibantashi, yanzu haka yana amatsayin mijin 'yarkine" sannan yafice daga palourn ransa ab'ace,


Maseefa tadinga zubawa akan wai dama tasan baya sonta ita da yaranta shiyasa ya walak'antata kuma yake neman had'a 'yarta da matsiyaci bayan ga 'yar uwarta nan yanema mata d'an 'yar uwarsa da yake da arzik'i don tsabar munafucci ma ga yayarsu agida zaune ba'ayi zancen auren taba sai nak'annenta don d'ai mugunta, haka tadinga fad'in maganganu da habaice habaice kala kala don Ummi ta tanka, amma Ummi najin haka ta tattara inata inata tabar palourn yarage daga ita sai yaya Mahmud daketa faman bata hak'uri yana rarrashinta amma ina kamar yana turawa fetur wuta, daga k'arshema d'aukar kud'in tayi tawatsa masa afuska


"Wllahi indai ni nahaifeka maza kad'auki kud'in nan tare da kayansu kaje kakai masu, narantse 'yata bazata auresaba abun kunya ya isheni acikin gari" tana kaiwa nan tafice abunta tana faman banbami, sororo yaya Mahmud yayi tsaye yana kallon mom d'insa cike da mamaki, to taya zaije yamaida kaya bayan ankarb'a ankuma basu yarinya tare da yanka masu sadaki, "innalillahi wa inna ilaihirraji'un" yafad'a had'e da duk'awa yana tattara kud'in aransa kuwa cewa yakeyi "Allahumahdi ummi, Allahumahdi ummi (Ya Allah kashiryar da mahaifiyata, ya Allah ka shiryar da mahaifiyata) idan kuwa hakane to tabbas bazai bari faraaharsa tazo gidannan ba, kuma bazai tab'a bari mom tasanta ba harsai bayan aurensu, sai kuma gawaya idan sun gaisa, gaskiya 'yan uwansa dashi kansa suna cikin jarabawa sosai" 


Bayan yagama tattara kud'in yanufi sama can bayan d'akin dady inda yatabbatar yanzu yana can saboda yasa duk sadda damuwa tayi masa yawa acan yake zuwa ya zauna, yafi minti biyar atsaye yana kallon dady dake zaune bisa kujerarnan takwance mai d'an tsawo yarufe idanuwansa yana shak'ar wata daddad'an fresh air dake fitowa daga saman wajen, takowa yayi ahankali har wajen kansa had'e da duk'owa yace


"Dady" juyowa yayi yana kallonsa da idanuwansa da sukayi jawur yace


"Son am tired of ur mom, duka wud'annan abubuwan da nakeyi inayin sune saboda ku, hak'uri nakeyi da mom d'inka sosai saboda banaso akaro nabiyu ku kalleni amatsayin wanda bayason zamansa da mahaifiyar ku, yanzu meye aibun yaronnan? He's trying all his possibilities just to show how much care and love he have for our dota amma kadubi yanda take jifansa da kalamai marasa dad'i laifinsa d'aya shine don yace yana son 'yarmu, yanzu idan kaine aka yiwa haka mekake tunani, shin ni zanji dad'i ko ita kanta zataji dad'in haka?, to don me zata yiwa d'an mutane haka don yace yana son 'yarta"


"Kayi hak'uri dady mom bata kyautaba kuma zanyi mata magana, nasan kana hak'uri and we do appreciated amma don Allah kak'ara dady da sannu komai zai wuce" mik'a masa kud'in yayi yace ga wannan tace amayar masu da abunsu, murmushi dady yayi kafin yace "ka ajiyewa Batool a hannunka sadakin tane nabiya masa"

Jinjina kai yaya Mahmud yayi aransa yace tabbas dady nason dr. aransa kuma yatabbata babu abunda zai hana ya aura matasa Batool koda ita d'ince tadawo da kanta tace bata sonsa..






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


[10/10, 18:13] BILLY S FARI💎: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Zumunci abune mai k'arfi wanda yakai matsayin da Allah ya ratayoshi daga k'asan al-arshinsa, haka 'yan uwanta ka tushene da iyaye ke haifar da ita a tsakanin 'ya'yayensu tayanda zasu saka masu soyayyar junansu azuciya da bazata tab'a gushewa ba har abada kuma komai rintsi komai wuya wannan soyayyar za'aci gaba da wanzuwa a tsakaninsu tayanda zakaga suna farinciki aduk lokacin da suka had'u tare da alfaharin kasancewarsu 'yan uwan juna, to kamar hakane nima yau nake alfaharin mik'a sakon gaisuwata mai d'inbin yawa agareku 'yan uwana rabin jikina kuma gaba d'aya rouhin rayuwata, *ASMA'U SANI FARI❤, MURJANATU SANI FARI💚, ZAINAB SANI FARI💖, AISHA SANI, JUWAIRIYYA SANI FARI💝, FATIMA SANI FARI💘, KHADIJA SANI FARI💞 AND ÃMINATU SANI FARI💞* ku d'in *'YAN UWANA NE* da nake matuk'ar k'auna acikin zuciyata, fatana Allah yaraya maku zuri'arku kuma ya albarkaceta, Allah kajik'an mahaifinmu ya gafarta masa😭😭😭sukuma iyayenmu Allah ya tsawaita mana rayuwarsu cikin amincinsa ya karemusu rayuwarmu kuma yahad'e masu kawunanmu ya kauda fitina atsakaninmu da dukkanin musulmi baki d'aya_ 😭👏🏻 *INA SONKU SOSAI HAR IZUWA LUMFASHINA NA K'ARASHE❤😍🥰*


💎Page_____68💎



  Shikenan dady amma don Allah kada narik'e wannan damuwar aranka,


"Karka damu son komai yawuce Allah yaganar damu baki d'aya"


"To amin dady amma batun aurenfa da naji kace nan da 3month fa? Sai nake gani kamar yayi kusa ko?"


"Eh to!, bari abari sai anje anjiyo ranar da iyayen taka matar sukasa sannan natuntub'i shi dr. Ahmad idan yanada hali lokacin saboda banaso ak'ulesa, naga shi mahmud iyayensa kamar ashirye suke to idan shima lokacin yaahirya bamatsala sai ahad'e gaba d'aya" cike da kunya ya sosa k'eyar kansa yana fad'in


"Ai dady da anbari anfarayin nasu, inyaso sai nawa yabiyo baya"


"A'a son nafiso nahad'a gaba d'aya ku ukun idanma lokacin Allah ya kawowa Basmah nata sai inhad'e ku hud'un insallameku kubarni da 'yan autana, jekama ka kirawomunsu sud'eben kewa" da to ya amsa masa had'e da mik'ewa ya sauko yana tunanin makomar aurensa idan mom tayi ido hud'u da faraaharsa amatsayin matarsa kuma aurukarta, yana fitowa ya hangosu guading suna wasar k'asa kira ya k'walamasu


"Bassam,Bilal kuzo nan" da gudu suka nufo wajensa suna rigaggen wanda zai fara isowa, Bassam ne yafara isowa kafinnan Bilal shima ya iso yana fad'in


"Yaya ai he's cheated ko don yaga yafini girma, ai watarana nima zanrama" dariya yayi had'e da  shafa kansa yace


"A'a Bilal u're wrong, ai babu cheating anan, kawai yafika cin abincine shiyasa ya wuceka, kalmar cheating is not gud ga 'yan uwa kaji ko" kad'a kansa yayi yana kallon Bassam had'e da cewa "Srry yaya Bassam, bazan k'ara fad'an maka haka ba" hannuwa yabasu suka tafe su duka sannan yace "kuyi maza dady nacan sama wajen shan iskansa yana neman ku" zasu ruga dagudu ya katsa masu tsawa yana ce


"Kuje ahankali mana kada kuji ciwo, ku kullum bakowa gajiya da gudune wai?" Sannan ya mik'e yanufi part d'in mom, yana shiga ya samu ta tasa Batool agaba sai ruwan masifa takeyimata akan dole saita hak'ura da soyayyar dr.Ahmad in kuma ba haka ba, bata ba ita, kuka Batool keyi sosai tana rok'onta don Allah tayi hak'uri ita shine zab'inta amma ina mom tayi kunnen uwar shegu da ita. Ana hakane yashigo palourn ya isko 'yar uwar tasa duk'e ak'asa tana kuka yasa hannuwa biyu ya d'agota tare da gogemata hawayen idonta yace


"Jeki wanko fuskarki kidawo" fuskarkarsa kamar zaiyi kuka yajuyo yana kallon mom dake zaune bisan kujera yazube a k'asa daidai inda yatada 'yar uwarsa yace 


"Mom wai wane laifi ko zunubi muka aikata agareki da muka kasa samun damar faranta ranki da kuma sanyaki cikin farinciki da muke fuskanta damuwa arayuwarmu, don Allah koma meye kiyi hak'uri kiyafe mana wud'annan matsaloli surabu da rayuwarmu, kece kika haifemu kuma kika renemu har muka girma natabbata bazaki tab'a so kiga rayuwarmu na salwanta acikin duniya ba sanadiyar munkasa sakaki cikin farinciki, kifad'i  duk abunda kike muyi maki amma don Allah wannan maganar kiyi hakuri kibarta tawuce" yafad'a had'e da game hannayensa waje d'aya, kafin mom tace wani abu saiga Batool tafito tana fad'in "yaya" tare da nuna k'ofar d'akinsu takasa magana, dak'yar idanuwanta nakawo hawaye taci gaba dacewa "Yayya Basmah bata mots.." aikafin tarufe baki dashi da mom har 'yar rigangan sukeyi wajen shiga d'akin da gudu, suna shiga suka sameta ak'asa kwance idanuwanta sun kakkafe sama, da sauri mom ta duk'a tarungumota ajiki tana jijjigata tana kiran sunanta, Mahmud daya dafe kai duk yarud'e yarasa mezaiyi iyayi nan yayi can, yaji kansa yayi wani irin mugun sarawar dayasa da kad'an yafad'i yayi saurin dafe wardrobe d'in, hannu ya d'agawa Batool da k'yar yana fad'in "jeki kawo ruwa" cikin kuka tanufi palour ta d'auko gorar swan a fridge cikin kitchen takawo masa, bud'ewa yayi ya yayyafawa Basmah sannan yafad'i zaune k'asa kansa najuyawa yana kallon fuskarta da yanda lumfashinta yadawo tana k'ok'arin bud'e idanuwanta.


Ganinta ajikin mom yasa tafashe da kuka tare da game hannayenta tana fad'in "Don Allah mom kibar Batool ta auri wanda takeso, zuciyata batada k'warin jurewa ganin damuwar 'yar uwata, nida nake kwana da ita kuma natashi da ita ni kad'ai nasan irin son da take yimasa, wlh matuk'ar kika rabata dashi tamkar kina neman rasa duka 'ya'yankine" mom da jikinta duk yayi sanyi itama tafad'i azaune hawaye nazubo mata a idanuwa cike da tausayinsu, karo nafarko kenan da zuciyarta tafara k'araya akan abubuwan da takeyi, kallon yaya Mahmud daya jingina kansa dake tsananin sara masa ajikin wardrobe tayi tatuna da abunda likita yafad'a masu alokacin baya akan adena barinsa yana shiga damuwar da zata haifar masa da taahin ciwon kansa domin akwai matsala inhar hakan nafaruwa, da sauri tad'aga Basmah ajikinta ta ajiye k'asa takoma kansa tana fad'in "a'a my son kada kayi hakan, don Allah kada kabari ciwon kannan naka yatashi pls k'asan abunda likita yace narok'eka kadena kaji ko"


Jin haka yasa Batool itama tatuna da irin yanayin da yayan nasu ke kasancewa idan yaga tashin hankali yayi yawa, wani irin kuka tafashe dashi da k'arfi tace


"Mom kifita, kifita d'akin nan shikenan zanbi umurninki, naji na'amince zanrabu da dr, amma kitafi kibar mun 'yan uwana zankula dasu, kije abunki kiyi farinciki yanda kike so, mu zamu zauna anan duka mumutu tunda bakya son mu kifitaa" tasake fad'a da k'arfi, tashi mom tayi tana kuka zata fita don tagama fahimtar koma meye ita tajanyowa kanta, gani tayi yaya Mahmud yamik'e had'e da d'auke Batool zafafan marora har guda biyu yana fad'in


"Tir dake Batool, tir, tir mahaifiyar tamu kike fad'awa haka har kike yiwa tsawa? ko kinmanta me alk'ur'ani yace akan iyaye _walatak'ullahuma uffin wala tanharhuma waqullahuma k'aulan kareema_ kada kace dasu ko uf ne balle har kayi masu tsawa kagaya masu zance cikin girmamawa amma shine kike d'aga muryar akanta haka kin k'ok'arin jefa kanki a halaka ki kai kanki awuta akan matsalar da zata iya wucewa idan mukayi hak'uri, ni ina zaton k'annena basada matsalar tarbiya ashe har yanzu da saura, to taya zaki iya zama agidan miji idan har zaki iya yiwa mahaifiyarki haka natabbata shikuma zaki iya dukansa wataran" yafad'a cikin sanin murya had'e da zaunawa gefen gadon rashi nasuya,


Agaban mom Batool tafad'i akan guiwowinta tana fitar da wani irin sautin kuka maicin rai tare da nadama tace "Mom natuba kiyafemun don Allah, tsoron kada inrasa 'yan uwana ganin halin da suke ciki saboda damuwa yasa nahalakar da kaina haka, kiyi hak'uri mom kigafartamun ko rahamar Allah zata kasance tare dani, kiyimun duk hukuncin daya dace dani bisa wannan laifin dana aikata wanda yanzu haka nasan ubangijina yana fushi dani kuma bazai denaba har sai lokacin da kika yafemun, wlh mom daga yau nahak'ura da dr bazan koma kulasaba nabarsa har abada matuk'ar mahaifiyata zatayi farinciki" tak'are maganar had'e da rik'e k'afafuwan ta gam tana kuka kamar ranta zai fita, itama kanta mom kukan takeyi ga Basmah da yaya Mahmud suma kukan sukeyi na wannan wace irin jarabawace ke bibiyar rayuwarsu d'aya bayan d'aya kowanensu da tasa kalar damuwa da ake jarabtarsa da ita. Ganin mom tak'i motsawa daga inda take tsaye kuma batayi maganaba yasa Basmah ta taso itama tana tayata ba mom hak'uri,










 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

[10/10, 21:09] BILLY S FARI💎: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Zumunci abune mai k'arfi wanda yakai matsayin da Allah ya ratayoshi daga k'asan al-arshinsa, haka 'yan uwanta ka tushene da iyaye ke haifar da ita a tsakanin 'ya'yayensu tayanda zasu saka masu soyayyar junansu azuciya da bazata tab'a gushewa ba har abada kuma komai rintsi komai wuya wannan soyayyar za'aci gaba da wanzuwa a tsakaninsu tayanda zakaga suna farinciki aduk lokacin da suka had'u tare da alfaharin kasancewarsu 'yan uwan juna, to kamar hakane nima yau nake alfaharin mik'a sakon gaisuwata mai d'inbin yawa agareku 'yan uwana rabin jikina kuma gaba d'aya rouhin rayuwata, *ASMA'U SANI FARI❤, MURJANATU SANI FARI💚, ZAINAB SANI FARI💖, AISHA SANI, JUWAIRIYYA SANI FARI💝, FATIMA SANI FARI💘, KHADIJA SANI FARI💞 AND ÃMINATU SANI FARI💞* ku d'in *'YAN UWANA NE* da nake matuk'ar k'auna acikin zuciyata, fatana Allah yaraya maku zuri'arku kuma ya albarkaceta, Allah kajik'an mahaifinmu ya gafarta masa😭😭😭sukuma iyayenmu Allah ya tsawaita mana rayuwarsu cikin amincinsa ya karemusu rayuwarmu kuma yahad'e masu kawunanmu ya kauda fitina atsakaninmu da dukkanin musulmi baki d'aya_ 😭👏🏻 *INA SONKU SOSAI HAR IZUWA LUMFASHINA NA K'ARASHE❤😍🥰*


💎Page_____68💎



  Shikenan dady amma don Allah kada narik'e wannan damuwar aranka,


"Karka damu son komai yawuce Allah yaganar damu baki d'aya"


"To amin dady amma batun aurenfa da naji kace nan da 3month fa? Sai nake gani kamar yayi kusa ko?"


"Eh to!, bari abari sai anje anjiyo ranar da iyayen taka matar sukasa sannan natuntub'i shi dr. Ahmad idan yanada hali lokacin saboda banaso ak'ulesa, naga shi mahmud iyayensa kamar ashirye suke to idan shima lokacin yaahirya bamatsala sai ahad'e gaba d'aya" cike da kunya ya sosa k'eyar kansa yana fad'in


"Ai dady da anbari anfarayin nasu, inyaso sai nawa yabiyo baya"


"A'a son nafiso nahad'a gaba d'aya ku ukun idanma lokacin Allah ya kawowa Basmah nata sai inhad'e ku hud'un insallameku kubarni da 'yan autana, jekama ka kirawomunsu sud'eben kewa" da to ya amsa masa had'e da mik'ewa ya sauko yana tunanin makomar aurensa idan mom tayi ido hud'u da faraaharsa amatsayin matarsa kuma aurukarta, yana fitowa ya hangosu guading suna wasar k'asa kira ya k'walamasu


"Bassam,Bilal kuzo nan" da gudu suka nufo wajensa suna rigaggen wanda zai fara isowa, Bassam ne yafara isowa kafinnan Bilal shima ya iso yana fad'in


"Yaya ai he's cheated ko don yaga yafini girma, ai watarana nima zanrama" dariya yayi had'e da  shafa kansa yace


"A'a Bilal u're wrong, ai babu cheating anan, kawai yafika cin abincine shiyasa ya wuceka, kalmar cheating is not gud ga 'yan uwa kaji ko" kad'a kansa yayi yana kallon Bassam had'e da cewa "Srry yaya Bassam, bazan k'ara fad'an maka haka ba" hannuwa yabasu suka tafe su duka sannan yace "kuyi maza dady nacan sama wajen shan iskansa yana neman ku" zasu ruga dagudu ya katsa masu tsawa yana ce


"Kuje ahankali mana kada kuji ciwo, ku kullum bakowa gajiya da gudune wai?" Sannan ya mik'e yanufi part d'in mom, yana shiga ya samu ta tasa Batool agaba sai ruwan masifa takeyimata akan dole saita hak'ura da soyayyar dr.Ahmad in kuma ba haka ba, bata ba ita, kuka Batool keyi sosai tana rok'onta don Allah tayi hak'uri ita shine zab'inta amma ina mom tayi kunnen uwar shegu da ita. Ana hakane yashigo palourn ya isko 'yar uwar tasa duk'e ak'asa tana kuka yasa hannuwa biyu ya d'agota tare da gogemata hawayen idonta yace


"Jeki wanko fuskarki kidawo" fuskarkarsa kamar zaiyi kuka yajuyo yana kallon mom dake zaune bisan kujera yazube a k'asa daidai inda yatada 'yar uwarsa yace 


"Mom wai wane laifi ko zunubi muka aikata agareki da muka kasa samun damar faranta ranki da kuma sanyaki cikin farinciki da muke fuskanta damuwa arayuwarmu, don Allah koma meye kiyi hak'uri kiyafe mana wud'annan matsaloli surabu da rayuwarmu, kece kika haifemu kuma kika renemu har muka girma natabbata bazaki tab'a so kiga rayuwarmu na salwanta acikin duniya ba sanadiyar munkasa sakaki cikin farinciki, kifad'i  duk abunda kike muyi maki amma don Allah wannan maganar kiyi hakuri kibarta tawuce" yafad'a had'e da game hannayensa waje d'aya, kafin mom tace wani abu saiga Batool tafito tana fad'in "yaya" tare da nuna k'ofar d'akinsu takasa magana, dak'yar idanuwanta nakawo hawaye taci gaba dacewa "Yayya Basmah bata mots.." aikafin tarufe baki dashi da mom har 'yar rigangan sukeyi wajen shiga d'akin da gudu, suna shiga suka sameta ak'asa kwance idanuwanta sun kakkafe sama, da sauri mom ta duk'a tarungumota ajiki tana jijjigata tana kiran sunanta, Mahmud daya dafe kai duk yarud'e yarasa mezaiyi iyayi nan yayi can, yaji kansa yayi wani irin mugun sarawar dayasa da kad'an yafad'i yayi saurin dafe wardrobe d'in, hannu ya d'agawa Batool da k'yar yana fad'in "jeki kawo ruwa" cikin kuka tanufi palour ta d'auko gorar swan a fridge cikin kitchen takawo masa, bud'ewa yayi ya yayyafawa Basmah sannan yafad'i zaune k'asa kansa najuyawa yana kallon fuskarta da yanda lumfashinta yadawo tana k'ok'arin bud'e idanuwanta.


Ganinta ajikin mom yasa tafashe da kuka tare da game hannayenta tana fad'in "Don Allah mom kibar Batool ta auri wanda takeso, zuciyata batada k'warin jurewa ganin damuwar 'yar uwata, nida nake kwana da ita kuma natashi da ita ni kad'ai nasan irin son da take yimasa, wlh matuk'ar kika rabata dashi tamkar kina neman rasa duka 'ya'yankine" mom da jikinta duk yayi sanyi itama tafad'i azaune hawaye nazubo mata a idanuwa cike da tausayinsu, karo nafarko kenan da zuciyarta tafara k'araya akan abubuwan da takeyi, kallon yaya Mahmud daya jingina kansa dake tsananin sara masa ajikin wardrobe tayi tatuna da abunda likita yafad'a masu alokacin baya akan adena barinsa yana shiga damuwar da zata haifar masa da taahin ciwon kansa domin akwai matsala inhar hakan nafaruwa, da sauri tad'aga Basmah ajikinta ta ajiye k'asa takoma kansa tana fad'in "a'a my son kada kayi hakan, don Allah kada kabari ciwon kannan naka yatashi pls k'asan abunda likita yace narok'eka kadena kaji ko"


Jin haka yasa Batool itama tatuna da irin yanayin da yayan nasu ke kasancewa idan yaga tashin hankali yayi yawa, wani irin kuka tafashe dashi da k'arfi tace


"Mom kifita, kifita d'akin nan shikenan zanbi umurninki, naji na'amince zanrabu da dr, amma kitafi kibar mun 'yan uwana zankula dasu, kije abunki kiyi farinciki yanda kike so, mu zamu zauna anan duka mumutu tunda bakya son mu kifitaa" tasake fad'a da k'arfi, tashi mom tayi tana kuka zata fita don tagama fahimtar koma meye ita tajanyowa kanta, gani tayi yaya Mahmud yamik'e had'e da d'auke Batool zafafan marora har guda biyu yana fad'in


"Tir dake Batool, tir, tir mahaifiyar tamu kike fad'awa haka har kike yiwa tsawa? ko kinmanta me alk'ur'ani yace akan iyaye _walatak'ullahuma uffin wala tanharhuma waqullahuma k'aulan kareema_ kada kace dasu ko uf ne balle har kayi masu tsawa kagaya masu zance cikin girmamawa amma shine kike d'aga muryar akanta haka kin k'ok'arin jefa kanki a halaka ki kai kanki awuta akan matsalar da zata iya wucewa idan mukayi hak'uri, ni ina zaton k'annena basada matsalar tarbiya ashe har yanzu da saura, to taya zaki iya zama agidan miji idan har zaki iya yiwa mahaifiyarki haka natabbata shikuma zaki iya dukansa wataran" yafad'a cikin sanin murya had'e da zaunawa gefen gadon rashi nasuya,


Agaban mom Batool tafad'i akan guiwowinta tana fitar da wani irin sautin kuka maicin rai tare da nadama tace "Mom natuba kiyafemun don Allah, tsoron kada inrasa 'yan uwana ganin halin da suke ciki saboda damuwa yasa nahalakar da kaina haka, kiyi hak'uri mom kigafartamun ko rahamar Allah zata kasance tare dani, kiyimun duk hukuncin daya dace dani bisa wannan laifin dana aikata wanda yanzu haka nasan ubangijina yana fushi dani kuma bazai denaba har sai lokacin da kika yafemun, wlh mom daga yau nahak'ura da dr bazan koma kulasaba nabarsa har abada matuk'ar mahaifiyata zatayi farinciki" tak'are maganar had'e da rik'e k'afafuwan ta gam tana kuka kamar ranta zai fita, itama kanta mom kukan takeyi ga Basmah da yaya Mahmud suma kukan sukeyi na wannan wace irin jarabawace ke bibiyar rayuwarsu d'aya bayan d'aya kowanensu da tasa kalar damuwa da ake jarabtarsa da ita. Ganin mom tak'i motsawa daga inda take tsaye kuma batayi maganaba yasa Basmah ta taso itama tana tayata ba mom hak'uri, hannu mom tasa tad'agosu tarungumesu har lokacin hawaye na zubowa daga idanuwanta tace


"Ya isa haka, kuskuren nawane kuma nayafe maki Batool, nayafe maki duk wani abu da kika tab'a yimun dake har 'yan uwanki" sakinsu tayi ta koma gefen da yaya Mahmud kezaune akan gado tana sharar k'walla tace


"Ayau nagano kuskuren da nake aikatawa bakowa yake cutarwa ba face ni kaina da kuma 'ya'yanah, gaba d'aya idanuwana sunrufe wajen son kaina nakasa magance matsalata da kuma ta 'ya'yana saboda wani dalili dake cikin zuciyata, amma ina so kuyafemun daga yau bazan koma yin abunda zaisa kushiga damuwa ba, zanbaku kula da kowace uwa ke baiwa 'ya'yanta , zanzamo uwa tagari kamar yanda mahaifana ke buk'ata, zanyi k'ok'ari inmanta da wasu abubuwan koda ba duka bane, amma inaso kusani kowace irin k'iyayya nada asali haka kuma kowace sosayya itama tanada nata asali, Na amince kowanenku ya auri wanda yakeso bazan koma hanaku muradin zuciyoyin kuba kuma ina maraba da wud'anda kuke so nima ina son su har cikin ziciyata,


Tana gama fad'ar haka tamik'e tawuce d'akinta cike da nadama da dana sani.


Fad'a sosai yaya Mahmud yayiwa Batool da nasihohi akan abunda tayiwa mahaifiyarsu ya nuna mata kuskuren data aikata da kuma fushin Allah da tajefa kanta aciki dabata rok'i mom tayafe mata ba, har d'aki tasake bin mom tana k'ara bata hak'uri da neman yafiyarta, shi kuma yaya Mahmud ya kalli Basmah yanda tayi duhu da rama yace


"Basmah ciwon nan yana matsamaki don haka dole yau muje asibiti, nagaji da ganinki cikin wannan yanayin duk da nasan kina k'ok'arin cire komai aranki dolene yau sai munje kinga likita koda asirrancene"


"Don Allah yaya kadena batun zuwa asibitin nan har sai bayan aurenku, banaso wani abu da zai kawo cikas awannan lokacin, kana gani dai yanzu muka gama shawo kan wata matsala kar kuma mujawo wata dazata iya watse farincikin da mom tagama tabbatar mana da samunshi daga wajenta, alhamdulillah ina samun sauk'i sosai, d'a zuma dana shiga wannan yanayin saboda nakasa jurewa ganin yanda 'yar uwata ke kuka akan tasamu amincewa akan abunda takeso awajen mom, to sai nayi tunanin kada tafad'a irin tawa matsalar ga abunda takeso akusa da ita har shima yana sonta amma takasa samunsa, to ina wannan tunanin ne kuma daga nan bankoma sanin abunda yafaruba saida nabud'e ido naganni ajikin mom, damuwa da tunani sune kesa ciwon na tasarmun amma tunda yanzu zasu k'auracewa rayuwarmu natabbata in sha Allah itama zata dena ciwon, amma kaima ya kamata kaje asibiti kaga likita" harararta ya d'anyi kafin yace


"Babu inda zanje nima ko kin manta inada tawa likitar agida" dariya tayi kafin tace


"Point of correction yaya kana dai da malamar jinya agida amma kam ba likita ba" rank'washi yakai hannu zaiyi mata akai da sauri tayi baya takwanta ajikin kan gado tana dariya, ita kuma mom don d'ai tacirewa Batool damuwar dataga tashiga akan abunda tayimata kuma ta tabbatar ta yafe mata yasa tace taje tabud'e bedside wardrobe ta d'auko reza tayi mata yankan k'umba, haka ta tashi cikin sanyin jiki ta tashi taje ta d'auko rezar tadawo gefenta ta zauna kanta ak'asa tanaji duk ta tsargu, murmushi mom tayi data fahimci hakan tadinga jawo mata fira kala kala har saida taga tasaki jikinta sannan tamik'a mata hannu tafara yimata yankan k'unban sunayi suna labari...


NOTE


_A wannan gab'ar 'yan uwa yakamata mufahimci cewa ita uwa duk mugun halinta da shed'ancinta baya halatta ga d'a yamunana mata ko yacutar da ita da halshenta, yin hakan babban kuskurene a musulunce da kuma aladance matuk'ar d'an nagarine mai neman yagama lafiya da duniya, sannan mufahimci cewa ba'a yanke tsammanin shiriyar bawa akowane lokaci duk mugun halinsa ta sanadiyar wani abu daban, kamar dai yanda yau bazato ba tsammani mom tacanza halinta ta sanadiyar yaranta, badon sun kasance masu girmamata da bata hak'k'inta na uwaba da hakan bazai tab'a faruwa ba_




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____69💎



  Izuwa yanzu abubuwa sun sauya sosai agidan dady domin mom ta ajiye komai agefe tarungumi mijinta da 'ya'yanta tana basu kula yanda yakamata wanda hakan bak'aramin sauya rayuwarsu yayi ba ta b'angaren dady kuwa duk da canjin da yagani daga wajenta da irin kulawa da biyayyar da takeyi masa hakan baisa yadena fushi da itaba, saboda yanda yasan halinta idan ya amince mata yasaki jiki da ita zata iya sake b'ullo da wata matsalar daban, tunda mom take bai tab'a fushi da ita haka ba, gaba d'aya yadena cin abincinta, maganama sai idan takama dole yake amsa mata shima baya wuce um ko a'a, yadena sakar mata fuska, ranar girkinta kuwa yana k'asa palour abunsa ita kuma tana sama ita kad'ai tayi basa hak'uri har tagaji amma yak'i hak'ura kullum sai tsaurara fushinsa yakeyi akanta, ya matuk'ar juya mata baya fiye da tunaninta wanda duk yayi hakanne don hukuntata bisa kuskuren da tadad'e tanayi yana samata ido, amma aransa kwata kwata bayajin dad'in hakan da yake yimata, ita kuma ganin hakan yasa tadena zuwa part d'insa aranakun girkinta, amma takan shirya abincinsa kowane lokaci tasa akai masa, yanda akakai na safe haka za'a d'aukoshi idan anje kai narana batare daya tab'a ba haka kuma nadare idan ankai haka za'a d'auko naranar baiciba kullum haka yakeyi har tafita girki kuma hakan baisa tadena dafa masa ba, idan kuwa yafita baruwansa daya kira wayarta har yadawo, hakama idan yadawo kawai zai shiga part d'inne don yaduba lpyrta data yaransa amma ko kallon inda takeyi bayayi balle har tasaran yayi mata magana, inkuma tayi masa ciki ciki yake tanka mata kuma batare daya kalli inda takeba, tun abun baya damunta yanzu har yafara damunta, fiye da wata d'aya kenan yanzu kullum cikin kuka take da nadamar abubuwan datayi, tasani cewa iya so da k'auna ya nuna mata arayuwarta, bai tab'a cimata fuska ko mutunci ba agaban abokiyar zamantaba, yana iya k'ok'arinsa wajen kyautata alak'a da zamantakewarsu ita da matarsa amma tarufe idanuwa tanata cuzgunawa rayuwarsu akan wani d'an k'ank'anen laifi daya aikata mata wanda yakamata ace tuni tamanata da hakan, gashi yanzu tajawa kanta tsanar da batasan makomartaba awajensa, 


Gaba d'aya yaranta sun fahimci halin da take ciki amma saboda suma suna son canzawar mahaifiyar tasu yasa suka kauda idanuwansu ga abunda ke faruwa, amma suna iya k'ok'arinsu wajen ganin sunrage mata damuwa sosai, duk abunda zaisa tayi farinciki shi suke yimata, kuma alhamdulillah tana cire damuwa idan tana tare dasu zasu zauna suyita firarsu irin ta uwa da d'a wani zubin sai taji cewa ba kad'an tamatuk'ar cutar da kantaba abaya data kasa samar da irin wud'annan lokuttan farinciki tsakaninta da 'ya'yanta sai yanzu da take gab da rabuwa dasu kowace zataje gidan mijinta, hatta Billy da Bilal yanzu dinga canji awajen mom saboda tadena takura masu idan sunje wajen 'yan uwansu duk da koyanzu acikin ranta bata son ummi dasu kansu amma kuma babu ruwanta dasu, gaba d'aya ta shafe cewa akwai wata Ummi da yaranta agidan cikin ranta, rayuwarta kawai takeyi da 'ya'yantah batabi takansu balle har ranta yab'aci.


Yauma dai kamar kullum zaune take a guiding abubuwa duk sun isheta, gashi su Basmah basunan sunje gidan papi yimasa weekend shikuma yaya Mahmud yana wajen faraaha Ummi kuma tun safe taje anguwa yau ita kad'aice a gidan sai maigadi, gashi har magrib takusababu wani da zai d'ebe mata kewa, mik'ewa tayi da niyar komawa part d'inta sai ga motar dady tahango tana shigowa, tsaye tayi tana jiran fitowarsa har yagama parking d'in motarsa yafito don yau kwananta biyu bata sashi a idoba, wata irin soyayyarsa da k'aunarsa ke fizgarta wanda shine dalilin daya sata tsayawa tagansa ko rad'ad'in dake damunta azuciya zairagu, zagayawa taga yayi ta d'ayan gefen yabud'e murfin mota Ummi tafito tana dariya, nuni yayi mata da hannu alamar ta shige gaba suje, rausayar da kai tayi had'e da mak'e kafad'arta wai saidai shi yafara wucewa gaba, dariya yayi had'e da d'ago kansa karaf sukayi ido hud'u da mom dake tsaye tana kallonsu, d'aure fuska yayi tare da tura murfin motar ya rufe sannan yarik'o hannun Ummi suka nufi part d'inta yana murmushi, saida ya kalli mom sannan yakai hannunsa ga fuskar Ummi yana d'an goge mata k'asan idonta.  


'Dago idanuwa Ummi tayi tana kallonsa had'e da cewa "meye haka abu Bilal karfa ka tsolemun ido" 


"Ni na isa intsole icon rabba'atul bait d'ina, wani abune na kakkab'e maki" yafad'a yana k'ara kallon gefen da mom take idanuwanta Sunci ka tafe da k'walla, da gudu tabar wajen tanufi part d'inta hayen na ziraro mata afuska, wani irin kishi da tsanar Ummi na sake taso mata acikin zuciya, a tunaninta da sanin ummi kuma da amincewarta duk dady keyimata wud'annan abubuwan, tabbas idan hakane bazata tab'a sonta aranta ba sai dai kawai tazauna da ita zaman lafiya don  samun farincikin 'ya'yanta dana mijinta, ita kuma Ummi gaba d'aya bata san abunda kefaruwa tsakanin mom da dady ba hatta abubuwan da dady keyi yanzu batasan inda yanufa ba, tunaninta d'aya shine soyayyar tashice ta motsa don haka tashige abunta jikinsa tana fad'in "dadyn yara kullum kai baka tsufa akowane lokaci sake sabunta salon soyayyarka kakeyi"


"Allah ko rabba'atul bait?"


"Sosai kuwa, shiyasa nake ganin munfi duka matan duniya dacewa da masoyin namiji daya sangartamu, natabbata arayuwata babu wani namiji dazai iya tasiri acikinta face kai kad'ai, madalla da ni'imar da Allah yayi mana tasamunka amatsayin miji agaremu" murmushi yayi had'e da yimata kiss agoshi sannan suka k'arasa daga ciki wani gefe nazuciyarsa cike da damuwa, kawai yana jurewa kansa yiwa mom wasu abubuwane don koya mata darasi amma badon yanajin dad'iba.


Sosai mom ke kuka tana fad'in, "Allah natuba kayafemun bisa kurakuran danayi agareka da kuma mijina dake matuk'ar sona, ya Allah ka maidomun da hankalinsa agareni, nayi alk'awarin zan zauna dashi bisa kyautatawa da kuma biyayyar aure har iya k'arshen rayuwata, zanjure dukkanin abunda nakeji inbasa farinciki da kwanciyar hankalin daya rasa awurina" ganin kukan bazai yimataba yasa tashiga toilet tayo arwala ta tada sallah tana hawaye batare da tasan metake karantawa acikiba, Allah sarki rayuwa kenan, shi namiji haka yake duk yanda yakai k'ololuwa a soyayyarka bazai hana ya shayar dakai ruwan mad'aciba wani lokacinma ruwan guba, duk ko yanda kake yimasa biyayya balle ga wacce batayi irin mom, sai gashi yau tayi sake hak'urin da yatayi da ita can baya ya koma mata bak'in ciki, b'acin rai da kuma damuwa.


Kasancewar yau zata karb'i aiki da daddare yasa bayan anyi sallar isha'i tafad'a kitchen ta d'ora sanwar tuwon alkama dama tanada miyar shuwaka datayi yau da safe tayi warming d'inta, cikin mintuna ashirin ta kammala sannan takoma d'aki tawatso ruwa, har zatayi makeup saita tuna da cewa wanda zatayi donshi ai yanzu bata gabanshi kawai tafasa, doguwar rigarta tasa tare da lullub'e jikinta da mayafi sannan tanufi kitchen ta d'auki kulolin abincin data d'ora akan tray tanufi part d'insa saboda yaran basunan dako zuwa bazatayiba don tasan baci zaiyiba, da sallama tashiga parloun tanufi dining area shikuma yana zaune akan kujera 3sitter ya d'ora k'afarsa d'aya akan d'aya yana karatun jarida, ciki ciki ya amsa mata had'e da bin bayanta da kallo sannan yamaida kansa ga jaridar da yake karatu, tad'an jima tsaye bayan ta ajiye abincin kafin tajuya tanufo inda yake kanta aduk'e tace


"Barka da dare, ga abincinka nan nakawo maka" d'ago kansa yayi had'e da cewa "ok" yaci gaba da karatun jaridarsa, duk da batada tabbacin cewa zaici abincin hakan daya fad'a tad'anji sanyi aranta, taso ta sake bashi hak'uri a lokacin amma yanayin da taga fuskarsa a d'aure tamkar bashine d'azu yagama kwasar dariya da matar saba yasa tajuya tafice abunta ranta cike da k'una, aranar kwana tayi tana salloli akan Allah yakarkato da hankalin mijinta agareta ya yafe mata laifukan datayi masa abaya, yanzu tagano cewa, makirci, fitina, mugunta, k'azafi, tashin hankali da sauran abubuwan zalinci aduniya basu isa susa ka iya mallakar zuciyar mijin kaba har sai inka koma ga Allah, wanda hakan yasa tazubar da komai aranta takoma ga Allah saboda bakad'an mijin nata yajuya mata baya ba.


Har aka saka ranar auren faraaha da Mahmud dady bedena fushi da itaba yadai d'an canza kad'an tawajen cin abincinta da kuma yimata magana idan takama amma zancen sakin fuska da walwala tsakaninshi da ita haryau babu, ansa ranar auren yaya Mahmud nan da wata biyu wanda hakan yasa yau dady yakirasu Ummi ita da mom yayi masu bayani da ganan kuma ya shawarcesu akan cewa idan sun amince yanaso yahad'a da auren su Batool da Bilkisu ayi arana d'aya, dukkaninsu sun amince da hakan tare da fatar Allah yasanya alkhairi kuma yasa ayi cikin nasara, ba dady ba hatta Ummi tayi mamakin amincewar mom alokaci d'aya amma sai tabar abun azuciyarta.


Iyayen dr Ahmad sun kawo kud'in sadakinsu dubu hamsin kamar yanda aka yanka masu amma da yake dady bayanan yaya Mahmud kad'aine sai yakarb'a hannu biyu bayan yayi masu iso ababban falon dady nak'asa sannan yayi masu bayanin cewa ga ranar da akasa d'aurin auren saisu sanar da d'ansu idan lokacin yanada hali, sun jinjina maganar sosai saboda tunanin kamar ank'uresa nan da wata biyu amma abun mamaki koda suka koma suka sanar dashi nan take ya amsa da cewa ya amince kuma ashirye yake cikin farinciki da murna kamar zai taka kan jariri ya rungume mamy yana sanar da ita.


  



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____70💎




  Wata 'yar madaidaiciyar jikka yad'auko cikin wardrobe d'in Ummi ya ajiye agabanta yana fad'in mamynah zoki gani.


Jid'owa mamy tayi da kan gadon tadawo k'asa inda yake tazauna tanabin jikkar da yake k'ok'arin zuge zip d'inta da kallo cike da mamaki, zabura tayi da sauri had'e daja baya tana kallon kud'in da yake cirowa daga cikin jikkar, "innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ahmadi ina kasamo wud'annan kud'ad'e haka? Kadafa kace kafara...Allah dai ya tsare""


Murmushi yayi tare da zazzage kud'in agabatanta wud'anda gaba d'aya d'aurin 'yan dubu dubune, ajiye jikkar yayi gefe sannan yagyara zamansa yana kallon kud'in yana murmushi yace "Kud'i masu gidan rana"


"Kai kafad'amun a inda kasamo kud'ad'en Ahmadu, gaba d'aya a tsorace nake nan inba zuwa kayi kad'aukomun abunda yafi k'arfina ba" rik'o hannunta yayi kafin yace "mamynah ki kwantar da hankalinki, bazantab'a yin abunda zaijawo maki b'acin raiba, nayi alk'awari ga Allah insha Allah bazantab'a ciyar dake ko fatimata haramunba don haka kidena kokonta akan yaronki wud'annan kud'ad'en da kike gani mallakina ne kuma halak malak" shafo sumar kansa tayi tana kallonsa kafin tace 


"Banida kokonto ko kad'an anan tarbiyar da muka gina maka nida mahaifinka amma wannan duniyarce dake cike da rud'i da abun mamakice banida tabbas da akanta shiyasa kaji ina tambayarka, amma tunda kace haka shikenan fad'amun a ina kasamesu"


"Mamy kinsan yau kimanin watana shida kenan da fara aiki kuma duk kwanan wata ina d'aukar albashina dubu d'ari uku da hamsinne a matsayina na consultant, to sune duk lokacin dana kwasa baya wuce muyi amfani da dubu 20 zuwa 30 ga wata sauran kuma sai na dinga tarasu acikin account saboda in samu inbiya alhaji Tukur kud'insa sannan in sake bud'e shagon Abba tunda da dad'ewa na karb'esai hannun wanda yabawa jinginarsa tundana biyasa kud'insa sai inzuba flaour nima infara sayarwa, ina so inyo gadon wannan sana'ar da Abba yaci damu ya shadamu kuma yatufatantar damu da ita tayanda lak'anin sunan bazai tsaya akansaba kad'ai har d'iyan d'iyansa sai sunyi gadonsa da izinin Allah" idanuwan Ummi nahawaye tarik'o fuskarsa tare da kissing forehead d'insa tace


"Ubangiji Allah yayi maka albarka, Allah yajik'an mahaifinka kuma ya gafartamasa, naji dad'i sosai da wannan shawarar daka yanke amma mezai hana kamanta da zancen bud'e shagon mahaifinka har sai nan gaba tunda ga zancen aurennan naka yataso kuma kaga bakada wani muhalli gashi ka amsa masu da cewa ka amince da ranar da suka sa inyaso sai inkoma gidan liman tunda akwai d'akuna nasan bazai hanani d'a yaba sai kayi k'ok'ari ka gyara nan d'in kafin lokaci yayi"


"Shikenan mamy duk yanda kikace ayi haka za'ayi, amma agaskiya banyarda daki koma gidan liman ba, duk inda zaki to dolene ina tare dake domin kece hasken rayuwata, to idankika tafiyarki can aikinga kinbarni acikin duhu dani har matar tawa dazan kawo, meye amfanin gidannan idan babuke aciki mamy?"


"A'a Ahmad taya wannan gidan zai ishemu, don Allah kada ka takura kanka, kayi hak'uri inkoma can har Allah yahore maka inda zamu zauna awadace, kuma ai kaga da nan da gidan liman babu wani nisa kullum zaka iya zuwa kaduboni koba haka baj" fir dr.Ahmad yak'i yadda da hakan daga k'arshema yashiga lissafa mata abunda yakamata afarayi da kud'in don bayason zancen, kud'in alhaji Tukur yafara cirewa dubu d'ari uku da hamsin sannan yamaida sauran acikin yace


"Mamy ga wannan ki ajiye, gaba d'aya kud'in milayan d'ayane da dubu d'ari da ashirin ancire wud'annan dubu d'ari uku da hamsin zanje inkaiwa alhaji Tukur abunsa yarage saura dubu d'ari Bakwai da saba'in daga can zanzo da masu gyaran gida sai suduba sugani nawa gidan zai buk'ata" 


Juyawa mamy tayi tana kallon gabas tayi sujudush shukur ga Allah daya nuna mata wannan rana da yaronta ya sauke hakk'in da mahaifinsa yabar masa yabiya na mutane wanda ta tabbata yau rouhin mijinta zai samu salama saboda wannan nauyin da aka sauke mata tajima kafin ta d'ago kanta tana sake sanyawa d'an nata albarka sannan yafice zuwa gidan alhaji Tukur, Allah Akbar tabbas alk'awarin Allah baya tashi duk abunda kayi sai anyima, abunda dr.Ahmad yagani lokacinda mai mashin ya ajiyesa a k'ofar gidan alhaji Tukur ya matuk'ar bashi mamaki da ban alajibi, sosai ya sake gaakata alamarin Allah tare da imani dashi, Wasu mutane ya hango s biyar a k'ofar gidan cikin kayansu riga da wando bak'ak'e sai rigar ciki light blue wuyansu d'aure da necktie sunsha bak'ak'en takalma cover shoes da alama ma'aikatan bankine suna k'ok'arin rufe gidan alhaji Tukur duk'e agabansu yana magiya da basu hak'uri ga matansa uku da yaransa kusan goma aha d'aya a zagaye dashi suna kuka d'ayar matarma d'auke take da ciki wanda gadukkan alama yatsufa sosai, k'arasowa yayi wajen yana kallon ikon Allah da kuma tarihi dake maimaita kansa, nan take yatuno da mahaifinsa yanda ranar yake durk'ushe agaban alhaji Tukur yana basa hakuri da neman yayi masa alfarma amma yawofantar dasu har yayi silar rasa rayuwarsa sai gashi yau shima yana raye ya gansa durk'ushe agaban wasu yana neman alfarma ikon Allah kenan wato duk abunda kashuka to tabbas shizaka girba, goge hawayen idonsa yayi daidai lokacin da wani d'aya daga cikin jami'an bankin da bayama jin hausa sosai kecewa alhaji Tukur 


"alhaji, alhaji, kinga gida wenan bizaki doki komai acikiba har sekinbiya kud'in banki da kika cinye, zamuyi gonjonsha ga maisho nan da kwana uku iden baki kawo kudinba yarage ruwanci" 


Cikin kuka da magiya alhaji Tukur yace "Yallabai don Allah kuyimun afuwa zuwa nan da wani d'an lokaci zan kawo, kutaimaka kubud'emun gidannan gani da mata ga yara da yawa ina kukeso naje dasu"  

"Kitambeye kenki.mudai aiki akeshamu kuma mungama, to baruwana da danki kece kika haifeshu don haka  shekisan yanda jakiyi dashu" mutumen yafad'a tare da juyawa yabarsa nan wajen a duk'e yana kuka, ga yaransa suma suna tayasa, duk'awa dr. Ahmad yayi yasa hannu ya d'agota daga durk'ushen da yake yana goge masa hawaye, d'ago kai alhaji Tukur yayi yana kallon dr.Ahmad nan take yatuna da abubuwan da suka faru watanni bakwai da suka wuce, cike da kunya yamaida kansa k'asa yana fad'in


"Ahmad kaga yanda Allah ke ikonsa ko?, kaga yanda hak'k'in mahaifinka kebibiyata, wlh tun ranar nayi dana sani da nadamar abunda na aikata masa har ya zamo silar barinsa duniya amma duk da haka kadubi yanda  hak'k'insa yayi dani"


Goge hawayensa yayi sannan yace "karka damu alhaji dama lokacin Abba yariga da yayi ranar koda hakan bata faru tsakaninkuba natabbata tabbas dole zaibar duniya aranar don haka kadena wannan tunanin, yanzu kamata yayi ka k'arfafa zuciyarka kadena wannan kukan haka agaban iyalanka insha Allah komai zai dai daita"


"Ahmad kenan taya zakace haka bayan kimanin dubu d'ari bakwai banki kebiyata kuma banida halin biyansu, ga shagona dake kasuwa nayi gobara komai yak'one k'urumus taya abubuwa zasu dai daita agareni"


"Kayi imani mana alhaji kuma karok'i Allah natabbata zai kawo maka d'auki" k'arar matar alhaji dake tsaye tana sharar k'walla saboda azaba data zamemata kashe biyu tun d'azu ta bak'incikin halin da suke ciki data yaron cikinta dake nemanan hanyar fitowa suka jiyo, da sauri alhaji yajuyo yaganeta k'asa asheme jini nazuba ta k'asan k'afa fuwanta ga abokanan zamanta su biyu sun zagayeta suna kiran sunan, fad'uwa zaune yayi had'e da d'ora hannuwa akai yana fad'in


"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun nashiga uku wayyoni Allah na"


"Haba alhaji meye haka, bakaga halin da matarka take ciki bane?, jini ke zubar matafa!, idan har baka hanzarta kaita asibiti ba zaka iya rasa rayuwarta da ita har abunda ke cikinta"


"Ahmad taya zankaita asibita bayan banida ko sisi a aljihuna, ubangiji Allah dai ya tausaya mata ya saukete lapy," nuna matansa yayi yace kutallabeta kushiga mak'wabta har muga yanda Allah zaiyi da ikonsa" gidan wani mak'wabcinsu suka nifa da ita da sauri Ahmad ya dakatar dasu yace 


"Kudawo, wannan haihuwar akwai matsala bata buk'atar azauna gida dole sai an dangana da asibiti, kujirani anan ina zuwa" da sauri yanufi titi yataro mai keke napep, rik'ota yasa suyi amma takasa tafiya hakan yasa yajuya ga alhaji daya buga uban tagumi yace


"Don Allah alhaji katashi karik'ota sanyin jikifa ba naka bane" mik'ewa alhaji yayi jiki bak'wari ya nufi inda take zube akwance ya cirata amma yakasa ga jinin sai zuba yake sakeyi sosai, tsufa da rashin kuzarin da yake ciki yasa yakasa d'aukarta gashi dama tak'ara nauyi saboda cikin dake jikinta daya girma, tsoron kada arasa rayuwarta kota yaron yasa dr Ahmad k'arasowa wajen yace dashi


"Zan iya taimakonka?" Kad'a masa kai alhaji yayi nan take dr Ahmad yaciccib'i matar batare daya damu da jinin dake zubo jikinta ba, a napep d'in yasata sannan yace alhaji ya shiga ya rik'eta, kallon mai napep d'in yayi yace


"Kayi sauri ka kaisu specialist hospital, ganinan biyowa bayanku"


Kallon iyalin alhajin yayi yace "kushigar da yaran mak'wabta sai kuzo mutafi ko?" To suka amsa masa dashi shikuma yanufi titi ya taro mashin da wata keke napep, suna fitowa yace su shiga shikuma ya hau mashin d'in yacewa mai napep d'in yabiyo bayansa.


Suna zuwa asibitin suma suna isowa nan take yabiya masu napep d'in kud'insu sannan da sauri nurses sukazo aka dauki matar bisa d'an gadon d'aukar mararsa lpy aka gungurata zuwa emergency, kasancewar ansan dr Ahmad yasa ba'a tsaya wata wataba aka shiga tearter room da ita bayan anba alhaji Tukur wata takarda yasa hannu, saboda tazubar da jini sosai yasa akace tearter za'ayi mata don bazata iya haihuwar da kantaba gashi d'an d'an ya gicce mata aciki, gorar jini uku aka buk'ata wanda da k'yar aka samu d'iyar gora d'aya ajikin babban d'and'an alhaji Tukur, duk inda yakamata asamu cikon gora biyu asaye dr yasa anema amma saboda jininta mai wuyar samune wato blood 0- ba'a samuba, hakan yasa dr Ahmad yaje yakwanta aka d'ebi gora biyu ajikinsa saboda irin jininne agaresa, sosai faraaha tadinga zolayarsa akan jini yayi masa yawa ko yanzu za'a iya d'ibar wata gora biyun ajikinsa don dama da ita ake zirga zirgar komai tunda suka shigo yakirata awaya akan tazo yana neman taimakonta, shidai murmushi kawai yayi sannan yamik'e bayan tafasa masa madara peak data bayar aka sawo masa a canteen dake can gefen asibiti yasha,


Shidai alhaji tukur zaune d'ai yayi jugum wasu hawaye nabiyar wasu cike da kunya da nadama ganin wanda ya cutar yau shine ke taimakonsa, shikuwa dr Ahmad wajen biyan kud'i yanufa yasayi  duk abubuwan da yakamata ya biya sannan yaje yabiya kud'in tearter dubu talatin tare da kud'in gadon jinyar da za'a bata na kwana biyar dubu goma sha biyar ganin yanda ake kallonsa duk inda yabi yasa yashiga dubon kayan dake jikinsa yaga ashe gaba d'aya duk sun b'aci da jini, kasance warsa mutum mai tsananin tsanda nan take sai yaji duk ya tsargu, wajen alhaji yanufa ya mik'a masa takardun receipts d'in kud'ad'en daya biya sannan yace 


"Alhaji bari naje gida nacanzo kayana, naga ashe duk sun lalace, ga wannan idan anfito da ita aka tambayeku takardar shedar biyan kud'in aikin saika basu, insha Allah bazan jimaba zandawo" fashewa da kuka alhaji yayi kamar ransa zai fita yana rok'on dr. Ahmad ya yafe masa bisa zamowarsa na sanadiyar rasa mahaifinsa har yana rik'e k'afafuwansa, ja dabaya yayi had'e da sa hannuwansa ya d'agosa yana fad'in "haba alhaji sau nawa zance maka komai yawuce babu komai kamanta"


"Wlh bazan iya tsaida kaina daga rok'onka ba saboda kunyar alkhairin daka ramamani da sharrin da nayimaka, don Allah kayafe mani Ahmad"


"Shikenan alhaji naji kuma nayafe maka, kaje kamatsa kusa kaida iyalinka kafin afiddo maku da jaririn kuma karok'i Allah yasa ayi nasarar ceton uwar da abunda ke cikinta"


"To Ahmad nagode nagode Allah yajik'an mahaifinka kuma ya gafarta masa"


"Amin alhaji bari naje nadawo"


Yana fitowa asibiti saiga kiran Batool yashigo awayarsa, rejecting yayi sannan yayi calling nata back daidai lokacin daya tare maimashin yahau sannan yace


"Hell my amarya to be"


"Na'am my dr. Ya kake ya k'ok'ari?"


"Alhamdulillah hop kina lafiya?"


"Sosai kuwa don gani a asibiti nakawo wata mata zata haihu har nabata jinina gora biyu amatsayin jahadi, kaga kuwa ina lafiya klw my dr." Murmushi yayi don yatabbata sister faraahace takirata tafad'a mata abunda yafaru sannan yace


"Faraaha ko?" Saida tayi dariyar da sautinta yadakar masa zuciya sannan tace


"A'a aunty faraaha dai, Weldone my ango gaskiya kaid'in namusammanne kamar yanda nafad'a maka, naji dad'i sosai da kazamo mai taimako natabbata kaida ahalinka bazamu tab'a tozarta ba aduniya in sha Allah, dama just call u to appreciate and telling I love u so much my man, always proud of you my ango and lucky to have you milkheart" tana gama fad'ar haka takatse wayar cike dajin kunya tana dariya, ciro wayar yayi akunnensa yana kallon screen d'inta yayi murmushi tare da cewa "I luv you too my fatima, ked'in tamusammance kema"


Muryar maimashin d'in yaji yana cewa "Ranka yadad'e halan sabon aurene kayi kuma budurwa ko, nima cikin shekarar nan nakeso nasamo 'yar yarinya ko ak'auyene tadinga suburbud'omun kalamai irin haka inyita nishad'i abuna" duk da miskilancin dr.Ahmad da rashin son maganarsa saida abun yabashi dariya, kafad'un mai mashin d'in yad'aga had'e da cewa


"Kai malam k'asimu, bana son munafucci da sauraren abunda ba'a kasa da kaiba, maza nik'a kaini anguwar g.r.a nasamu nafita wannan shigar"


"Hhhh ai yallab'ai balane sunana ba k'asimu ba"


"What ever dai sunanka karik'e matarka gam inaga zaifi maka"


Dr Ahmad baijima da fitowa ba sai gashi anfitowa da alhaji Tukur da jariri anan nad'e cikin d'an kwalin matar anmik'a masu da sauri alhaji yakarb'a yana kallon jaririn yace "masha Allah dr. ansauka ko?" Cikin damuwa dr yace


"Alhamdulillah anyi nasarar ciro yaron d'and'ane amma saidai kuyi hak'uri ita uwar Allah yakarb'i abussa" baya baya alhaji yayi da kad'an yafad'i yana fad'in "innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, Allah sarki jamila shikenan kitafi kinbarmu , duk k'ok'arin da yaronnan yayi don ganin rayuwarki tatsira dake da jaririnnan ashe Allah yayi ke bazaki tashiba," rik'osa matansa sukayi suka zaunar dashi suma suna kuka tare da fad'in alkhairinta suna cewa sun yafemata, sosai alhaji yarik'e jaririn yana kallonsa jawur dashi amma ba uwa tatafi tabarshi, matsowa dr yayi had'e da bubbuga kafad'arsa yace


"Sorry yanzu kushirya zuwa anjima za'a baku gawar"


Dr Ahmad kuwa yana zuwa gida yafad'a toilet yayo wanka sosai sannan yafito yana labartawa mamy abunda kefaruwa da alhaji Tukur wanda garin taimakon matarsa ne yab'ato kayansa da jini, sosai mamy ta tausaya masa tare da fatar Allah yasa ayi nasarar wajen aikin, kud'in hannunta yace tabashi ya ida cikashe kud'in alhaji daya tab'a akayiwa matarsa aiki sannan yaci abincin agurguje, yana gamawa yayiwa mamy sallama sannan yakoma asibitin, yana shigowa yaci karo da sister faraaha zata fita idanuwanta jawur da alamar tayi kuka, nan take sanar dashi rasuwar matar alhaji Tukur cikin tausayi da shaida masa tabar jariri yana can ahannunsu rungume gwanin ban tausayi, sosai dr Ahmad ya girgiza da rasuwar matar duk da bai santaba had'e da nema mata ga farar Allah, sallama sukayi da faraaha sannan ya k'arasa wajen alhajin, tasowa yayi tare da mik'a masa jaririn yana kuka yace


"Ahmad kaga ikon Allah ko? Yakarb'i ajiyar daya bamu ya sake bamu kyautar wata ya Allah kaba wannan yaro dangana"


Tunda dr Ahmad ya d'ora idanuwansa afuskar jaririn yaji k'aunar yaron tashiga ransa sosai kuma yaji tausayin maraicin uwa da zaiyi arayuwarsa.


Cikin k'ank'anen lokaci aka basu gawar suka tafi da ita akayimata wanka aka suturceta tare da kaita gidanta na gaskiya duk tare da dr Ahmad,  bayan kwana uku dr.Ahmad yakawo mamy tayiwa alhaji Tukur gaisuwa sannan ya d'auko kud'insa da yake biyar mahaifinshi dubu d'ari uku da hamsin yabashi tare da cewa 


"Alhaji ga kud'in da kake biyar Abbanah don Allah  kayi hak'urin rashin samunsu da bakayi ba akan lokaci, ubangiji Allah yajik'ansu duka kuma ya gafarta masu, kuku alhaji Tukur yafashe dashi had'e da cewa 


"Don Allah Ahmad kuyafemun, bazan karb'i kud'innan ba ko kad'an duba da halacci da kuma taimakon da kayimun, haba Ahmad ai da nazama butulu"


"A'a alhaji ai hak'k'in kane kuma wlh duk taimakon danayi maka nayine don Allah badon komai ba saboda haka kakarb'i abunka nasan bazaka rasa abunyi dasu ba" k'in karb'a alhaji yayi saida mak'wabcinsa daya bashi aron wani d'aki agidansa shida iyalansa yasa baki sannan yakarb'a koshi saidai dr.Ahmad ya ajiye masa kud'in ak'asa gabansa, kan alhaji duk'e ak'asa yana kuka yadinga yiwa mamy godiya tare dasawa dr Ahmad albarka sosai sannan sukayi maau sallama suka wuce batare daya d'ago kai sunk'ara had'a ido da mamy ba saboda kunya, har sunkai k'ofar fita ya dakatar dasu tahanyar cewa


"Ahmad don Allah kujirani ina zuwa" cikin gida yashiga jaririn na hannun uwar gidansa ya karb'esa, wajensu mamy yanufo tare da durk'usawa agabanta ya mik'a mata jaririn.


"Wannan d'ankine na bakishi duniya da lahira, Allah da mala'ikunsa sune sheda akan haka sai kuma wud'annan bayin Allah dake zagaye dani, banaso kirenesa amatsayin kyautar da nabaku, ina so kirenesane a matsayin d'anki dake kika haifi abunki ina fatar wannan zai zamo kyautatawar da zan iya yimaku aduniya bisa rabaku da farincikinku da nayi, sannan tun ranar da aka haifesa narad'a masa suna Bashar, amma idan kunso zaku iya canza masa da wanda kuke so"  karbar yaron mamy tayi jikinta har yana tsima saboda soyayya da wata irin k'aunarsa da taji tana ratsata, idanunta nahawaye takalli alhaji Tukur tace...









 *_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____71💎



  Alhaji taya zakayi tunanin bamu d'an d'anka alhalin kana cike da alhini da rad'ad'in rashin mahaifiyarsa, sai nake tunanin idan kayi hakan kewar zata zame maka biyu, karik'e yaronka mu azuciyarmu babu komai har ga Allah munyafe maka duk abunda yafaru koba komai muma Allah zai iya dubonmu da idanuwan rahama ya yafemana wasu laifukan da muka aikata masa.


"K'warai kuwa alhaji kabarshi ya zauna cikin 'yan uwansa kada kasa muje dashi yayi rayuwa cikin kad'aicin daba wa balle k'ane" dr Ahmad yafad'a yana kallon jaririn daya dad'e da shiga ransa, wasu hawayenne suka sake zubowa alhaji Tukur a idanuwa yace


"Bazan tilas taku karb'ar saba, amma Allah shine sheda akan da zuciya d'aya nabakushi kuma inda son samu kada ku tab'a nuna masa cewa shi ba d'an gidanku bane, kada kutab'a fad'a masa cewa nine mahaifinsa don zuwa gobe zanyi nesa daku zan koma k'auye da iyalina na nemi wata sana'ar da zata iya rik'emu don natabbata dole banki su zauni gidana amatsayin bashin kud'insu dana karb'a koda zan tsira da wani abun acikin gidan bazai wuce suturunmu ba, don haka don Allah da girmansa ku karb'i yaronnan nabakushi duniya da lahira" mamy zatace wani abu Dr Ahmad ya hanata ya kalli alhaji Tukur yace


"Shikenan alhaji Mungode da wannan kyautar kuma bazamu tab'a mantawa da wannan alkhairin daka yimana ba, akaro nafarko kenan da wani ya saka mamynah zamowa uwa bayan tahaifeni kuma a lokacin da take da tabbacin cewa har iya k'arshen rayuwarta bazata koma samun d'a aduniya ba bacin ni da Allah yabata sai gashi kabata wani d'an da zata kalla taji sanyi, nikuma kabani k'ane wanda zan iya bugun k'irji innunawa duniya cewa nima inada d'an uwa, gashi kayiwa mahaifina takwara wanda hak'ik'a hakan bakad'an ya sakamu farincikiba mungode mungode sosai Allah yaraya shi kuma ya sanya mashi albarka" dariya alhaji yayi mai had'e da kuka sannan ya rungumesa yana fad'in


"Nagode ahmad da wannan karamci naka ina rok'on Allah daya yimaka albarka kuma yakare rayuwarka aduk inda kake"


"Amin ya Allah alhaji, kace dai Allah yayi mana albarka kuma yakare rayumarmu aduk inda muke ko kamanta cewa yanzu bani kad'ai nake ba inada d'an uwa" yak'are maganar had'e da d'ora hannunsa bisa kan jaririn, murmushi alhaji yayi tare da goge hawayen idonsa yana kallon mamy da itama hawayen takeyi tsabar farinciki daya lullub'eta na samun damar zamowa uwa akaro nabiyu, rungume jaririn tayi ajikinta sosai tare da had'e hannayenta waje d'aya tana yimasa godiya, duk wanda ke wurin ya jinjina alamarin tare da yabawa abunda alhaji yayi koba komai anaso musulmi ya kasance yanabin mummunan aikin da yayi da kyakkyawa. 


Wasu 'Yan uwan alhaji da mutanen gari kuwa sunyita yin k'orafi akan wai alhaji ya sayar da d'an sane saboda halin da yake ciki wasu kuma suce bazai iya kula da 'ya'yan bane sunyi masa yawa tunda ya tsiyace yanzu shiyasa yabayar da kyautar d'ansa, kai maganganu dai iri iri amma yayi kamar baisan ana yiba ya toshe kunnuwansa saboda shi yasan don Allah yayi da kuma kyautatawa ga mutanen da sukayi masa ramakon alkhairi da sharrin da yayi masu, kwana biyu da faruwar haka aka saida gidan alhaji da abun duk dake ciki a daidai farashin kud'in daya ranta, k'arin dubu saba'in kawai ne aka samu akai, nan banki tacire kud'inta dana dillalan da suka had'o mutane wajen yi  gwanjon gidan sannan aka mik'a masa dubu arba'in amatsayin canjinsa daya rage, hannu biyu yasa yakarb'a yana hawaye tare da tattaro kayansu nasawa shida iyalinsa sukayi sallama da mutanen anguwa sannan suka kama hanyar komawa k'auye, ko kad'an baiyi tunanin neman dr Ahmad ba balle yaje gidan saboda acewarsa iya abubuwan alkhairin daya yimasa sun isa hakanan, bayaso yaje yimasa bankwana kuma yanemi k'ara had'asa da wani alkhairin da zai sashi cigaba da zubar da hawaye da danasanin abunda yayi masa har abada, Shikuwa dr Ahmad ko daya sake komawa anguwar yatarar har alhaji Tukur yawuce, gashi bayada nombarsa kuma baisan k'auyen daya koma ba kuma daya tambayi dattijan anguwar suma cemasa sukayi bai sanar dasu ko a wane k'auyenne zai jeba, ko kad'an hakan bai yimasa dad'i araiba amma dole tasa ya hak'ura cike da fatar allah yasake had'a fuskokinsu da alkhairi,


Mamy kuwa tuni taci gaba da renon yaronta Bashar da sukayiwa lak'ani da MUHIB wato abunso cikin tsantsar kulawa da soyayya, sosai taso tashayar dashi amma sai dr.Ahmad ya hanata, acewarsa tsutsa nada matuk'ar wahalarwa arayuwa kuma shi duk abunda zaisa tawahala baya sonsa ko kad'an, sannan ba'asan tsarin da Allah zaiyo tsakaninsu da shiba nan gaba don haka tayi hak'uri a d'ora daci gaba da bashi madarar insha Allah babu abunda zai samesa sai adinga had'a masa da ruwan zamzam da yardar Allah zai samu cikakkiyar lafiya da kuzari, dole haka mamy tahak'ura tabi shawarar d'an nata badon ranta yasoba.


A b'angaren Mahmud  pilot kuwa saida su Umma da alhajinsa sukayi da gaske sannan yakoma abakin aikinsa don bazai yuyu ya zauna masu cikin gidaba har nan da wata biyu kafin aurensu, kullum cikin mita yake yiwa Billy akan wai da had'in bakinta aka kai auren har nan da wata biyu don bata sonsa ita kuma saidai tayita yimasa dariya tana fad'in babu ruwanta tsarinsu dadyne, ranar da kuwa yaji labarin cewa ai iyayen faraaha suka saka ranar auren nan da wata biyu shiyasa dady yasaka nasu suma ahaka saboda yanaso a had'e auren gaba d'aya lokaci guda, musamman yakira yaya Mahmud yata yimasa jininin wai sun cutar dashi don basu san meye cutar so ba da zafinta shiyasa akai fixing aurensu nan da 2mnth gashi yanzu sunja masa, haka dai shima yata yimasa fitina sai kace shine farahar ko iyayenta, shimadai d'in dariya yayi masa yace ka kwantar da hankali d'an uwa nan da 2month ai kamar gobene, tsabar takaicin yace masa wai nan da 2month kamar gobene yasa yakashe masa wayar yana cigaba da mita, Umma ko data shigo d'akin tund'azu tana sauraren fitinar da yakeyi zata kwashe kayan da yayi breakfast dasu dariya tayi cike da mamakin yanda duk kunyar d'an nata da yake da ita tacire akan soyayyar Bilkisu, mudai Allah ya nuna mana wannan rana koma huta da rigimarka son, tafad'a tare da ficewarta


Lambar Billy yakira bugu biyu ana ukun tad'aga had'e da cewa


"Hello mijin"


"Na'am matar ya kk, kina lafiya?"


"Lafiya klw yayana kaifa?"


"Not fine at all"


"A'a'a'ahh.... assha to fad'amun waya tab'a mun kai da safiyarnan"


"Waye banda yayanki, shine yab'atamun rai shida damammiyar waccan malamar asibitin tasa" saida tayi murmushi sannan tace


"Ayya d'an uwan naka da kansa yatab'amun kai?"


"Eh mana, shiyasa nakiraki ki sanyayamun zuciyata"


"To shikenan mijin kayi hak'uri, kaga dai acikinku babu wanda zan shigar wa don dukanku 'YAN UWANA NE, amma rufe idanuwanka kabud'e kunnuwanka sosai inturo maka da wani sak'on na musamman da zai dad'ad'a maka rai kaji yayana"


A hankali yarufe idanuwansa ya sake manna wayar akunnensa sosai had'e da cewa "to ina saurarenki matar" 


Wayar takara abakinta tare da jan wani irin dogon kiss ta jefe masa direct acikin kunnensa had'e da cewa "I luv you yayanah" takashe wayar tana dariya.


Murmushi yayi tare da manna wayar saiti zuciyarsa yakoma kan gadon yayi kwance yana fad'in


"Yarinyar nan kasheni zatayi da salon soyayyarta, innayi wasa lumfashina gagarar fita zaiyi aduk lokacin dana tunata" d'ago wayar yayi ya k'urawa hotonsu dake a fuskar wayar suna dariya yayi kissing d'inta tare da fad'in "I love u too my noor"


Basmah dake kwance gefenta tayi dariyar k'arfin hali tace


"Allah Billy kinzare yanzu ko kunyata bakyaji ko?"


Rufe idanuwanta tayi da tafin hannuwanta tare da cewa "kai yayya to ai laifin yayankine shine ya b'atani" murmushi Basmah tayi sannan tace


"A'a sister baruwan yayanmu kedai ke neman b'atasa da soyayya" juyowa batool dake lunkar kaya tayi had'e da cewa "hmmm yayya kenan kawi bakisan halin yayannan namu bane, mugun d'an soyayyane kamar shahrukan, wlh duk shi ya lalata my twiny da wannan soyayyar har tazama lamba d'aya itama" tak'arasa maganar tana zungure Billy ga kai, da haka sukayita firarsu Basmah na zolayarta tanata faman dariya ita kuma Batool nashigar mata, soyayyace mai tsananin gaske tsakanin wud'annan 'yan uwa guda uku da basa k'aunar ganin b'acin ran junansu, akoda yaushe bakin kowane d'aya daga cikinsu baya gajiya da fad'in cewa 'YAN UWANA NE!


A 'yan kwanakin nan gaba d'aya Basmah tadena jin dad'in jikinta, kullum cikin ciwon kai da jiri take ga ciwon zuciyar na yawan tasar mata akai akai gashi bukin 'yan uwan nata sai k'aratowa yakeyi don yanzu saura sati biyar, iya k'ok'ari da juriya tanayi wajen b'oye halin da take ciki wanda hakan yajawo hankalin mom akanta, yau tana kwance saiga mom tashigo d'akin, kallo d'aya tayi mata tashiga tashin hankali da sauri tak'arasa wajen tare da rik'e hannuwanta cikin damuwa tace


"Basmah injin bajikinne ya tasar maki ba" cije baki Basmah tayi tana k'ok'arin tashi mom tadakatar da ita "Aa Basmah koma ki kwanta, amma don Allah kifad'amun meyake damunki, kullum kece cikin ciwon kai da jiri ga wannan ciwon zuciyar naki yak'i kwantawa kuma idan akace aje asibiti kice bakya zuwa to wai menene hakan kedamunki"


"Mom babu komai, kawai ciwone kad'ai keda muna kuma zansamu sauk'i in sha Allah kiyimun addua zanwarke da yardar Allah mom"


"Haba Basmah to idan ciwone donme da bazaki bari aje asibiti ba"


"Mom banaso muje akwantar dani, gashi bukin 'yan uwana namatsowa inaso ayi komai dani shiyasa"


"Amma Basmah nifa mahaifiyar kice bai kamata kib'oyemun komai narayuwarki ba, don Allah kifad'amun idan da akwai wani abun da bansani ba" duk'owa tayi kusa da fuskarta had'e da dafa goshinta tana shafa gefen fuskarta "Basmah kodai tunani kike akan 'yan uwanki zasuyi aure subarki a gida" "A'a mom" tafad'a had'e da girgiza kanta lokaci guda hawaye nazubo mata,


"To meye Basmah?"


"Babu komai mom, kicire wannan tunanin aranki aishi aure lokacine dashi kuma nayi imani cewa duk lokacin da nawa yazo zanyi, kuma don 'yan uwana zasuyi aure su barni mezaisa nadamar da kaina bacin nasan Allah yana zab'a wa kowane bawa abunda yafi zama alkhairine akansa, kawai kiyarda dani ciwona jarabawa ce daga Allah kuma kiyimun addua Allah ya yaye manishi"


"Shikenan Basmah tunda haka kika fad'a Allah yazab'a maki kema miji nagari kuma yabaki lafiya"


"Amin mom" Basmah tafad'a had'e da juyar da kanta gefe hawaye nazubar mata, akoda yaushe Batool na lure da halinda 'yar uwar tata keciki kuma tana zaunawa tayita lurar da ita illar b'oyon damuwar da take ciki, takan rok'eta akan don Allah tabari suje asibiti adubata abata maganin daya dace tasha amma tsabar k'arfin halin Basmah saita nuna mata itafa babu abunda kedamunta ciwonma yadena tasar mata gaba d'aya, shikuma yaya Mahmud yanzu baya zama tunda akasa ranar bikinsu cikin zirganiya yake yau baya nan gobe baya can wajen ganin ya had'a lefensa balle yasan halin da 'yar uwar tasa ke ciki, Ummi ma da kanta tazauna tayita bincikar Basmah meke damunta amma tak'i fad'a mata, maganarta dai d'ayace ciwone kawai Allah ya jarabceta dashi amma babu damuwar da take ranta, daga k'arshe dai kowa ya ta'allak'a abunda k'ilan kewa da damuwar  d'auke 'yan uwanta da za'ayi abartane kesata wannan ciwon, ita kuma Basmah ba abunda ke hanata son zuwa asibiti illah kada likita yafayyace masu gaskiya matsalarta wanda tatabbata dole dady yanemi sanin dalili kuma hakanne bata fata don kozaka mutu bazata tab'a bayyana sirrin zuciyar taba kodon farincikin 'yan uwanta,


A lokacin da labarin halin da Basmah ke ciki yakai akunnen dady sa yayi aka kirawo masa ita, sosai ya canza mata fuska ganin yanda takoma don d'ai kawai tafad'a masa meke damunta amma tak'i fad'a sai cemasa takeyi ciwon zuciyane kad'ai da take fama dashi amma babu abunda kedamunta. Hakan yasa ran dady ya matuk'ar b'aci had'e da yimata fad'a donme zata d'auki ciwon da wasa haka bayan gashi yana nuna illar da yake yimata atare da ita kuma har tace wai bata son zuwa asibiti akan wani banzar dalilinta, to meta d'auki lafiyartane wato bukin 'yan uwanta kenan yafi lafiyarta,


Kuka take sosai kamar ranta zai fita saboda fad'an da dady keyimata tasan inda zai ajesa daga k'arshe, shikuwa ganin haka yasa yayi lowering voice d'insa cikin ransa yana tausaya mata naganin gashi itace babba amma za'a d'auraye k'annenta akai gidan miji wanda ko wannan kad'ai ya isa yazame mata damuwar da zata iya jefata cikin wannan halin, cike da tausayawa yashiga yimata nasiha dake nuni da tayi hak'uri shi aure lokacine insha Allah itama yana fatar nan kusa lokacin nata yazo, kallonta yayi tare da mik'a mata hannu alamar tazo, rik'a hannunsa tayi takoma k'asan kujerar da yake zaune kusa da k'afafuwansa ta zauna tare da d'ora kanta akan cinyoyinsa, shafa kanta yashigayi alamar rarrashi sannan yace


"Kiyi hak'uri Basmah Allah yazab'a maki kema miji nak'wari, yanzu kije ki kwanta gobe da safe in Allah yakai ranmu kafin nawuce wajen aiki saiki shirya muje asibiti kinji ko?" Gabanta ne yafad'i da sauri ta d'aga masa kai don batada zab'in daya wuce amsa masa saboda maimaitawar daya yimata, mik'ewa tayi had'e da cewa


"Saida safe dady"


"Allah yatashemu lafiya Basmah kuma Allah yayi maki albarka" ta amsa da amin tana k'ok'arin barin d'akin, da k'yar takawo d'akinsu kanta nawani irin mugun juya mata tashige toilet dama Batool na part d'in ummi wajen Billy, tana shiga ta fashe da kuka had'e da duk'ewa tatura kanta a tsakankanin cinainanta jitake tamkar ranta zaya bar jikinta saboda tsananin ciwon da takeji, zuciyarta cike da fargaba zancen zuwan asibiti da dady yace zasuyi gobe don ko kad'an bata buk'atar haka, jin tayi ana bubbuga gambun toilet d'in da k'arfi, mom ce tashigo saboda tana zaune afalo taga shigowarta amma ko lura da ita batayi ba balle tayi mata magana ta wuce abunta, ganin haka yasa ita kuma tabiyo bayanta don ganin ko lafiya, sake bubbuga gambun k'ofar tayi had'e da cewa


"Basmah, Basmah maza kibud'e gambunnan kinajina ko?" Jin muryar mom d'inta yasa ta d'ago kanta tana goge hawayen da suka mik'e mata fuska don kar tagane halin da take ciki, hannunta takai ga hancinta jin wani abu nafitowa daga ciki mai sanyi tana duba hannunta taga jini da sauri tanufi wajen madubin dake saman sink d'in dake cikin toilet d'in taga ashe tabbas jinine ke zubowa daga hancinta... 



 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭



👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____82💎



    Bai tsaya jiran dawo warsa ba yad'au wayarsa yakirasa, dady naganin kiran nasa yayi rejecting sai yakirasa da kansa.


"Bashar wannan wace irin hidimace haka, bayan duk abubuwan da suka faru tsakaninmu yanzu kuma kana jifarmu da tarin alkhairai haka, kai da kake da hidimar aurar da 'ya'ya agabanka" alhaji kabiru yafad'a cikin raunin murya,


"Yaya kabar wannan maganar mana, ai komai yariga daya wuce, kufa 'YAN UWANA NE idan banyi makuba to wazanyiwa?"


"Duk da haka hidimar tayi maka yawa akai da bari kayi har sai bayan bukin yarannan tukuna" murmushi dady yayi don yafahimci meyake nufi, kuma shi Alhamdulillah cikin arzik'in da Allah yayi masa ko d'aya bisa kashi gomai bai kasheba tundaga hidimar 'ya'yansa har wannan, muryar alhaji kabiru yajiyo yana fad'in


"Mungode Allah yabar zumunci kuma ya albarkaci zuri'armu baki d'aya"


"Amin yaya, sai anjima idan nashigo, sai kuzama cikin shiri don yau ake dinner da daddare"


"To! Kuma dinner hardamu iyaye aciki?" Dariya dady yayi sannan yace


"Eh mana, baku kad'ai ba hadda manyan mutane daban daban insha Allah, yara k'anana kad'ai bazasu ba, amma daga 'yan shekara sha takwas abunda yayi sama are all invited"


"To masha Allah Allah yakaimu"


"Amin yaya sai anjima" suna gamawa yakira wayar baba k'arami yace yaje yafad'awa iyalansu yaya zasu iya komawa sashensu yanzu ya mallaka maau duk abubuwan da sukaga ansaka acikin d'akunansu halak malak, kayansu kuma zasu iyaba duk wanda suke so 


Misalin k'arfe biyar da rabi na yamma yaya Mahmud yayi parking motarsa bakin k'ofar shagon maman abulkhair, yana zuwa ba b'ata lokaci duk suka fito don dama tuni tagama gyaresu tsaf from head to toe, a tsammaninta ma gaba d'ayansu amarene har Basmah da Zainab shiyasa tafara da faraaha tana gama mata sai kawai tace Basmah ta shiga, wani irin mahaukacin gyaran jiki tayi mata wanda nan take yasa haskenta fitowa dama gata fara abun ba'a magana ita dai Basmah sai binta takeyi da kallo dama tuni Billy da Batool tasa k'wararrin yaranta suma sunfara gyarasu yanda idan kagani baka tab'a banbancewa da ita tayi saboda ita ta koyarwar dasu, atare tagama gyara Basmah dasu lokacin ana zanawa faraaha bijin, nan takirawo wata daga cikin yaranta tace tazauna tazanawa Basmah siffar saboda yanda tayarda da k'warewarta, sukuma su Batool wasu suka cigaba da yimasu suma sun matuk'ar k'warewa sosai, Zainab kuwa cewa tayi ita bataso gaba d'aya gobe zataje itada 'yar uwarta Amina wajen wata mata ayimasu lallen daga nan sai suje wajen saloon, babu yanda basuyi da itaba amma tak'i yarda sai da maman abulkhair tafito takalleta had'e da cewa "pls kizo agyaraki mana, zakiyi kyau sosai"


"A'a madam nagode, akwai 'yar uwata da zamuyi tare"


"Ha'a keba amarya bace?" Mmn abulkhair tafad'a tana yimata kallon mamaki, dariya Zainab tayi had'e da cewa


"A'a madam, ai wud'annan ne amare nida yayya Basmah 'yan rakiyane kawai" tak'are maganar tana nuna su faraaha dake jeri su uku waje guda"


"What of dis one" tanuna Basmah


"Banda ita"


"Mts. Ba gaskiya ba, look at her she's totally resemble with amare fa" d'ago kai Basmah tayi had'e da cewa


"Gaskiya nefa ai nafad'a maki tun can ciki kika k'yaleni"


"Ha! Banjiba, namanta gaba d'aya nayiwa yayanku totalin kud'in gyaranku da price d'in amare" guntun tsaki taja had'e da ba Basmah hak'uri sannan tarok'i Zainab data bari ayi mata ko gyaran kaine da lalle, saida faraaha tasa baki sannan ta amince aka yimata. Wani irin kallo yaya Mahmud yabisu dashi saboda yanda sukayi kyau sai yakasa tsakaninsu wa zai cewa yayi kyau, kallon Mman abulkhair dake murmushi yayi yace


"Thank you madam, they all look excellence" fad'a d'a murmushinta tayi tana maijin dad'in yabon daya yimata sannan taciro kud'in daya bata d'azu taki'rga daidai nata tabashi sauran had'e da cewa


"Here is ur balance, nazata duka amarene to ashe mutum uku kad'aine amaren, so gashi nacire kud'ina na mutum uku wannan chanjin kane"


"Oh madam amma naga kowanensu yayi kyau sosai especially my big sis kinsa takoma har tafi amaren ma" yafad'a tare da jan hancin Basmah yana dariya


"Bakomai sir let take it volunteer"


"Wow..madam we do really appreciate it gaskiya kibarsu kema Mungode sosai, muje ko sisters" yafad'a tare da juyawa yafice, godiya suma sukayi mata don gaskiya sun yaba da gwanewarta da kuma karamcinta har Batool nafad'an itakam tasamu wajen zuwa bayan tayi aure, hadda karb'ar no tayi, har bakin titi maman abulkhair tarakosu ita da yaranta tana fad'in "thank you, thank you sir for the patronage, Allah yabada zaman lafiya" saida taga sun wuce sannan takoma cikin shagonta tana mai farinciki da jin dad'in zuwansu don ba k'ananan kud'i tasamu ba"


Kai tsaye yawuce dasu shagon Hindu _Him's touch_ wajen kwalliya don dama yakirata yace tazauna abunta basai tazo nan gida ba saboda lokaci yak'ure idan ya d'aukosu zai kawosu nan shagonta sai tayi masu makeup d'in.


Kasancewar ankira sallar magrib yasa suna shiga tace sushiga toilet suyo arwala suyi sallah kafin afara kwalliyar, haka kuwa akayi suna kammalawa tahau yimasu kwalliyar cikin gwanewa nan take cikin awa d'aya sai gashi tak'are masu duka su ukun, dama tuni yaya Mahmud yaje gida ya d'auko masu kayan da zasu saka wud'an da jiya suka fitar had'e da sakaau cikin akwati sannan yabiya yakarb'o na faraaha, yana kawowa ya juya yakoma gida don shima yayi shirinsa nazuwa wajen dinner. Yauma light make up Basmah tace Hindu tayi mata amma takafe kai da fata saida tasa tatsaya ta cancara mata kwalliya taji da fad'i wacce ko batafi amare ba sai dai suzo d'aya., sallar isha'i sukayi ta kawo masu abinci sukaci sannan tahau shiryasu cikin wasu arnayen dogayen riguna dasu kasha d'ige d'igen rose flowers ajiki suna ja har k'asa, gaba d'ayansu su uku komai iri d'ayane har zuwa takalmi kala kad'aice ta banbanta.


Faraaha aka fara shirya wa cikin rigarta pink colour flowers d'in dake jikinta da head sky blue, sai kuma Batool red colour d'in riga flowers and head ash colour sannan ita kuma Billy rigarta royal blue flowers da head kuma golden colour, nan take Hindu tafara watsa masu hotuna saboda yanda sukayi masifar kyau badai kamar Billy da zakaji kamar ka sace ta saboda d'an jikin dake gareta sai yazamana rigar tafi zaunawa ajikinta sosai,


Yayya Basmah kuwa street gown ce popul da  tasa ajikinta wacce adaidai bayanta inda yakamata ayi tsaguwa sai telan ya zuba wata tattara dake ja har k'asa itama Hindu ta Nad'an mata head cilver saidai bayayi bud'ewar na amaren ba amma yayi maseefar yimata kyau abun sai wanda yagani, murmushi Basmah tayi ganin yanda itama tayi kyau, sai taji inama ace itama auren zatayi, fad'a d'a murmushinta tasakeyi had'e da fad'in "Alhamdulillah"


Saida suka kammala gyarawa da kusan minti ashirin saiga kiran yaya Mahmud ya shigo awayar Hindu, tana d'agawa ba abunda yace face


"Ya 'yan uwana hope dai dukansu kowa ya shirya" 


"Eh angon faraaha ku kad'ai suke jira" tafad'a tana kallon faraaha dake faman kashe selfie da sister inlows d'inta, katse wayar yayi had'e da k'arasa saka agogon hannunsa yana kallon kansa amadibi, sosai yayi matuk'ar kyau cikin shaddarsa giznah da tasha d'unkin babbar riga sai wani maik'o maik'o da k'yalk'yali takeyi, feshe jikinsa yayi da turare sannan yanufi part d'in mom yanajin wani nisha d'i naratsa zuciyarsa, kallo d'aya mom tayi masa had'e da sakin murmushin da bata san lokacin daya kucce mataba tace


"Masha Allah my son kayi kyau sosai, to ina sauran 'ya'yan nawa banganesu ba" 


"Yanzu zanje in d'aukosu Hindu tace sungyara"


"To masha Allah, Allah yasanya alkhairi kuma yasa ayi lafiya awatse lafiya ya amsa da "amin mom" sannan yafice, 


Daidai shiga part d'in Ummi yaci karo da Mahmud pilot shima yafito cikin shirinsa na d'unkin babbar riga golden sai wani shek'i yakeyi saboda yanda kayan sukayi masa kyau abunka ga farar fata sai shida kayan suka kusa sadewa, murmushi yayi tare da kallonsa yace


"'Dan uwa kafayi kyau masha Allah, anya yau k'anwata zata ganeka kuwa?"


"Haba ai wlh nasan yanda tayi kyau rena wannan kwalliyar tawa zanyi idan naganta, abeg dady fa yakira yace kowa ya hallara wajen shigowar mu kad'ai ake jira"


"Ok to kodai muwuce gaba d'aya tacan idan mun d'aukesu"


"Eh ina ganin zaifi don dare yafarayi, nafi nakira dr inji idan ya shirya" yana rufe baki sai gashi yakirasa da kansa, d'auka yayi had'e da cewa


"Hello dr. Kana inane?"


"Gani bakin gate ko har kun wuce ne?"


"Haba yanzunnan muka gama shiryawa gamunan fitowa" ok dr Ahmad yafad'a tare da kashe wayar yana kallon Khalid abokinsa daya tuk'osa, madubin dake lak'e a saman motar yad'an gyarawa zama yana kallon fuskarsa ciki, sosai shima yayi kyau cikin shaddarsa gizna  itama d'unkin babbar riga ash colour data matuk'ar karb'ar jikinsa, zaman hular kansa ya gyara tare da ciro d'an siririn glass d'in idonsa agaban aljihun motar ya saka, 


Kallonsa Khalid yayi had'e dayin d'an guntun tsaki sannan yace "wai kai don Allah yanzu har wajen dinner ma sai kasaka glass d'innan? Ko gajiya bakayi kullum abu mak'ale afuskarka?"    Murmushi dr yayi batare da yace masa komai ba saima fiddo wayarsa da yayi yana daddagalawa, 


Ganin yayi banza dashi yasa shima ya sharesa har su yaya Mahmud suka iso wajen, fita sukayi sukaba juna hannuwa suka gaisa Mahmud pilot nata tsarguwar dr. Yana fad'in 


"Kai ashe dr ba wankan k'ananan kaya kad'ai ka iyaba, ka kuwaga yanda kayi kyau cikin manyan kayannan, masha Allah ba'a magana dole yau kasa sister tarud'e" murmushi kawai dr yayi don shikam yana d'an jin nauyin yaya Mahmud shiyasa baifiye biye masaba idan yana wajen, abokanan yaya Mahmud ne suka k'araso wajen cikin wasu manyan motoci masu d'an karen kyau guda biyu da bak'a da kuma wata golden gaba d'ayansu k'irar marcadis, kallon dr yaya Mahmud yayi had'e da cewa


"Am srry dr. Zaku iya biyo bayanmu domin muje d'auko amaren daga can sai muwuce don dady yace mukad'ai ake jira"


"Badamu, Khalid tada mota ko?" Yafad'a yana kallonsa


Suna isa bakin k'ofar him's touch yaya Mahmud ya shiga ciki, ba'ayi minti biyu ba sai gashi ya fito amaren sun biyosa abaya, cikin bak'ar motar daya fito suka shiga gaba d'ayansu su uku, sannan yabud'ewa Basmah gaba tashiga, yace da sauri sadiq abokinsa dake tuk'a motar yashiga gaba amma yayi tafiya ahankali, cikin hanzari yace Zainab tabiyo bayansa suka nufi motar da dr keciki, ya kalli Khalid had'e da cewa


"Khalid zaka bamu angonnan sai kawuce mana da sister d'inmu pls.."


Haka kuwa akayi dr yafito Zainab tashiga azuciyata tana mijin haushin rashin amincewar da tayi suzo tare da Amina, gashi yanzu duk taji ta tsargu duk da babu wani wariya da aka nuna mata amma wannan mutumen da zata shiga motarsa ko kad'an baiyi mata ba saboda yanda taga khalid ya tsuret da idanuwa yana kallonta, adole dai tashiga tunda ba yanda zatayi shi kuma dr ahmad da yaya Mahmud suka shiga d'ayar motar dake bayan wacce amaren keciki dama Mahmud pilot shima yana cikinta nan take faruq abokin yaya mahmud da shine zai driving d'insu yayiwa sadeeq horn yatashi sannan yabi bayansa shima suna tafiya slowly shima Khalid daya d'auko Zainab yana biye dasu har suka isa babban hall d'in da yasha gyara tun daga waje, suna isa wasu securities d'in da aka zuba wajen tare da sojoji 'yan sanda da sauran wasu masu kaki da aka zuba wajen saboda tsaro ga manya manyan k'ososhin gwamnati da 'yan kasuwa dake wajen suka rufo had'e da bud'e masu gambunan motar, yaya Mahmud ne yafara fitowa daga cikin motarsu ya nufi inda aka bud'e gambun motar amaren yaba faraaha hannu tafito, sannan dr Ahmad shima yafito yaje shima yamik'awa Batool hannu tarik'o itama tafito, sannan Mahmud pilot shima yafito yaje yamik'awa Billy hannu itama tafito tare da yimasa kallo d'aya ta noce kai k'asa,


Bilal, Bassam da junior na hango cikin suit riga da wando iri d'aya milk colour sai rigar can ciki popul da necktie shima milk, takalminsu halfcover sun fito tare da nufo wajen, suna zuwa suka shiga gaba tare da gyara tsayuwarsu, sauti DJ yasaki dake nuna alamun cewa tabbas ga amare da angwayensu nan sun iso nan take kowa ya zubawa k'ofa ido yana jiran shigowarsu.


Ahankali su Bassam suka fara shigowa sannan yaya mahmud da faraaha nabiye dasu Batool da dr.Ahmad suma suka biyo baya sannan su Billy da yaya Mahmud pilot suka shigo, wow mutanen wajen suka fad'a saboda ganin yanda tsarin nasu yayi kyau, gashi sai taku sukeyi d'ai bayan d'aya tamkar suna bin sautin kad'an, Basmah kuwa suka shigo tare da sadeeq abokin yaya Mahmud da sai faman manne mata yakeyi ita kuma tana basarwa kamar bata fahimta ba, ga kuma Khalid abokin dr. Ahmad da shima sai shisshige ma Zainab yakeyi ita kuma tana jin haushin sa, bayan duk sun zauna akujerun da aka tanadar masu kowa da matarsa mc yashiga kwararo dad'a d'an kalamai da zasu sanyaya zuciyar angwaye da amare cikin raha da nishad'i yayin da duk lokacin da ya d'auko kalmah ya ajiye sai hall d'in and'auki dariya, saida mc ya tabbatar ya gama saka kowa nisha d'i sannan akaci gaba da gudanar da shagalgulan bukin yanda ya kamata, mc ne yafara magana cikin barkwanci irin nasu yace


"So iyaye, yanne, k'anne so dama sauran mutanen dake wurinnan irinsu k'awayee, abokanai kai harma da 'yan uwa da abokanan arzik'i muna so gaba d'aya amik'e tare da tafawa don karrama angwaye da amare saboda nuna tsantsar farin cikinmu agaresu, but kafin nan zanso d'aya daga cikin wud'an da ke wajennan yafito don bada tak'aitaccen tarihin  wud'annan ma'auratan" kasancewar babu wanda yasan ta inda zai fara bada tarihin ma'auratan yasa har aka kwashe fiye da minti biyar mc namagana amma babu wanda yafito, sai murya dake tashi k'asa k'asa mutane cike da mamakin taya hakan zai faru"


"To angwaye idan harfa aka kasa samu dolene zaku bamu amarenku don subamu tarihin kansu da kanku, ko kuma tarar dubu hamsin ga kowane ango, so DJ let have a count to five" kowacensu kallon angwonta tayi kamar zatayi kuka saboda bazasu iya tsayuwa agaban iyaye su wani bada tarihinsu da nasu ba, can mc yafara k'irga tare da taimakon DJ na tamashi "5.4..3...2...." Kafin su ida five sai ga Basmah tafito tsakiyar wajen cike da kunya ta duk'ar da kanta k'asa, nan waje ya d'au ihu tare da mik'ewa tsaye harda angwaye da amare ana tafi, kallon juna sukayi tare da sauke ajiyar zuciya kafin can suji muryar mc natashi


"Hello" duk aka amsa da hy, hall d'in yayi tsit kallon Basmah yayi had'e da cewa "what is ur name" ya karamata microphone abaki cikin lallausar muryarta tace "Basmah" had'e da folding hannayenta akan k'irji.


"Basmah ko zamu san meye alak'arki da wud'annan amaren har ma da angwaye" yasake karamata microphone din abaki, juyowa tayi takallesu had'e da yin murmushi sannan tace


"They are my relatives"


"Da hausa kenan 'yan mata?" takarb'i lasifikar tana dariya tace


"'YAN UWANA NE!" tare da duk'ar da kai k'asa tana kallon yanda hasken wajen ke jijjuyawa ajikin tays d'in dake k'asan wajen


"'Yan uwanane!, nice relation, shin ko zaki iya bamu tak'aitaccen tarihinsu.


"Yes comfirm" nan tafara bada tarihin yaya Mahmud dasu Batool tana d'an had'awa da barkwanci ana dariya daga k'arshe tace


"Both dr Ahmad and sister faraaha are very kind and very nice person dt have a good moral behavior of helping people in our society, so i  think no need for their history because is always upon to the most of our people in the society, thank you all" tana gama fad'ar haka tabar wajen don gudun kada mc yak'ureta saboda batada wani tarihi da zata iya bayarwa akan dr. da kuma faraaha, sosai mc yayi appreciating d'inta, gaba d'aya wajen aka d'au tafi don ba k'aramin burge mutane Basmah tayi ba, nan aka sakarwa amare sauti suka fito suka d'an tattaka masoyansu da masoyan dady sukayita fitowa suna yimasu lik'i da ruwan kud'i can na hango maku sis 'yartulluwa andija anyi ture kaga tsiya sai faman lik'i takeyi da rafar naira goma goma hankalinta kwance batare da tadamu da 'yan dubu dubu da taga sunata yawo awajen kamar ruwa ba, tsabar gudun kar arena mata wayau tasake turo d'an kwalinta gaba tana taunar cingum fuskarta d'auke da wani makeken glass da ake kira no respect, murmushi nayi tare da d'aga mata baban d'an yatsan hannuna alamar jinjina mata da k'ok'arin da tayi na samun damar shigowa wajen batare da an hanataba, 


Nan mc ya gabatar dasu teburin yanka kek wanda  nan ma abun gwanin ban sha'awa akayi komai sannan aka wuce wajen jerin abintayyen da aka tanada kala kala da ake kira serve ur self, angwayene agaba sai sauran mutane suka biyo layi abayansu, sai da kowa ya kammala d'ibar abunda yakeso saiga 'yan home of novel da 'yan Asy khalil novels suma sun biyo layi sai d'ibar ganima sukeyi sukuwa 'yan group din hajjace novel da zauren sainah tuni na hangosu can gefen amare kowace na ruguguwar kashe salfie dasu hatatta 'yan group d'in khairat up suma sun samu damar halartar wannan dinner don bak'aramin mamaki nashaba lokacin dana gansu,sara2zamfara ce ta ahedamun ai wajen Ummi sukaje tanemi masu izini aka basu damar shiga, maganar gaskiya anci an chashe sosai awajen bukinnan dady kuwa banda wasar baki babu abunda yakeyi tebur tebur yabi yana yiwa mutanen dake cikin hall d'in sannu da kuma godiya, juyowar da zanyi nahango 'yan rano online auna lek'e ta window suda 'yan Billy s fari novels, aunty fareeda ce nafara ganewa tana yafitoni da hannu, juyawa nayi ina kallon mutanen hall d'in kowa na harkar gabansa sannan nak'arasa wajenta, dariya nayi tare da cewa


Aunty fareeda ya haka? Ina kika baro Ummie da oum imaan dasu Hijjah yaks ga naman kaji dana raguna nan na yawo ta ko ina"


Kibarni kawai wud'an can tsinannun securities d'inne suka hanamu shigowa kinganmu nan haddasu zee kitchen's da oum aslam dasu baby leemah duk anhanamu shiga, pls ungo ledata don Allah zubomun naman kaji, ji nayi an wafce ledar ahannun aunty fareeda kafin inkarb'a ashe meamah ce tace


"Tab wlh baza'a zubobah haka kurum kusa gp d'inmu yayi down" tana watsawa aunty fareeda harara, kamar zatayi kuka tace


"Meamah ni zakiyiwa haka, ashe dama bakida m"


"Eh naji amma baza'ayi wannan abun kunyar ba" nan taja hannuna muka wuce aunty fareeda nafad'in "meamah..meamah.."


Muna barin wajen mukaci karo da haifa ita da Zainab pinki sunrik'o Bilal da Bassam, kallonsu meamah tayi tundaga sama har k'asa tace


"Oh iyayen shisshigi wato ku har iyayinku ya kaiku nan" basu ce mata k'ala ba suka nufi wajen mom dasu, kallonsu Basmah tayi had'e da yin murmushi tace


"Sannun ku sisters" ai kamar jira sukeyi da sauri suka amsa da yawwa had'e da mik'a mata hannu auna rige rigen fad'in sunansu Zainab pinki tace 


"Sannu Yayya Basmah agaskiya mu masoyankine muna matuk'ar sonki saboda yanda kike son 'yan uwanki da kuma irin role d'in da kike takawa wajen nuna jajircewa akan hak'uri" haifa taci gaba da cewa "hakane gaskiya yayya saidai ni inaso ki k'ara koyamun yanda kika had'a ferfesun kifinnan naki da ranar wajen breakfast da yaya mahmud yasaki" tak'arasa maganar cikin sigar zolaya da dariya,


Dariya Basmah tayi had'e da cewa "it's pass sweetheart, let take a pics" tafiddo wayarta tare da shiga tsakiyarsu suka d'au hoto, nan suma suka cicciro nasu wayoyin da yake ba k'arya suka d'auka tare da yimata godiya, duk k'wak'war meamah akan sai tayi hoto da dr.Ahmad hakan ya faskara don Batool takasa ta tsare ko nan da can bata bari yaje ganin haka yasa tamik'o mani wayarta had'e da cewa zataje wajensu tayi kamar zata d'auki gorar ruwa don Allah in d'aukesu hoto, aikuwa ashe Batool na kalle da duk wani motsi nata tana zuwa wajen tasa mata k'afa sai ga meamah ak'asa tafad'i daidai lokacin nikuma na d'auki hoton, ganin Batool ta wurgomin idanuwanta yasa nab'oye wayar had'e da juyawa nabar wajen don kada nima tasamu k'etar da zata yimun, can na hango maku meamah ansa mayafi had'e da rufe gefen fuskarta wanda da alama ya kumbure tayo inda nake, ashe duk abunda kefaruwa aunty fareeda tahango ta taga nan ta azamata dariyar k'eta harda hawaye had'e da cewa


"Ala gui meamah, dama duk wanda yahana tukunyar wani tafasa to tasa ko zafi bazatayi ba".


Nan dai aka kammala dinner cikin farinciki da walwala Ummi tasa aka kwaso souveneirs masu uban yawa tace abawa su aunty fareeda tare da naman kaji ak'aton tray anyi raping dinsa da takardar nan mai k'yalk'yali sunata murna tare da cewa Allah yabar masu Umminsu agidan dady....


_oum imaan k'orafinki yakarb'u asha karatu lafiya_




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____83💎



   Dady baibar wajenba saida ya tabbata angama kwashe kowa wud'anda suka samu hallara wajen bukin sannan shima yashiga motarsa ya wuce gida, yana isa tuni Ummi tahad'a masa ruwan zafi masu zafin gaske saboda kaida kawon da taga yasha, kallonta yayi had'e da cewa


"Sannu rabba'atul bait, ngd Allah yayi maki albarka, amma ataimaka a ida ladar mana ko kuwa?" saboda ta fahimci meyake nufi yasa har zata fita tadawo tacire hijab d'inta ta ajiye akan gado sannan ta rakasa har cikin bayin ta taimaka masa ya watso ruwan sannan suka fito atare, kasan cewar yariga yayi sallar sa ta isha'i da kuma shafa'i da wuturi yasa yana gama tsane jikinsa yajawo Ummi had'e da hayewa kan gado yaja masu blanket, ahankali ummi tafurta masa akunne "Dadyn yara akwaifa gajiya, kuma gashi Bilkisu kad'ai nabaro a part d'in sai 'yan buki, Bilal kuma na wajen Bassam can zai kwana saboda d'akinsa na saukar  da bak'i, kaga da kunya subud'e idanuwansu suga bana nan" cikin wata kasa lalliyar murya dady yace


"To mehakan zai canza rabba'atul bait, ai sunsandai wajen mijinki kika tafi, ko bakyason nasama maki wata abokiyar fira tunda Bilkisu guduwa zatayi tabarki?" Lumshe idanuwa Ummi tayi tana karb'ar sak'onnin da yake aika mata dasu kafin can taji yamik'a hannu ya d'auko wayarsa, lambar Bilkisu yakira lokacin tana gyarawa Ummi d'akinta saboda yanda 'yan buki suka b'ata mata shi duk da bawata taruwa akayiba sai zuwa gobe atashi safiyar d'aurin auren, tana d'agawa dady yace


"Bilkisu ki kulle part d'in naku idan kowa ya kwanta kuma kitabbatar kinyi addu'a kafin kirufe kinji ko?"


"Eh dady saida safe" tafad'a, yana kashe wayar ya kalli Ummi had'e da cewa


"Ina shikenan ko?, kinji 'yar taki ko nemanki batayi ba don tasan dadynta nabuk'atar kulawarki" murmushi tayi tare da rufe idanuwanta shikuma ya kashe masu wutar d'akin dake gefen bedside wardrobe, nan take suka tsunduma duniyar masoya tamkar wasu sababbin ma'aurata.


Billy kuwa tana gama waya da dady taci gaba da gyaran gadon da takeyi, acan gefen gado tana shara saiga tissue tasharo mai uban yawa da jini ajikinta wanda hakan ba k'aramin tsoratata yayiba, mamaki tashigayi son tasan ummi ba ad'akin ta kwana jiya ba yayya Basmah ce takwana ciki to idan hakane kenan ita tatara wud'annan abubuwan kuma da alama mantawa tayi bata zubar ba, shin to inhar hakane wannan jinin meye ajikin tissue d'in? 


Ganin batada wanda zai bata amsar wud'annan tambayoyin nata yasa taci gaba da shararta, bayan ta kammala tafeshe ko ina da room freshener sannan tajawo d'akin ta koma nata, ganin ita kad'aice kwance aciki don Zainab daga wajen dinner tabi baba k'arami akan cewa zata jene ta d'auko kayanta sai tadawo gobe yasa Billy ta tashi had'e da d'aukar hijab d'inta ta saka, wajen wata cousin d'in Ummi taje tace "momy jidda don allah kitaso kirufe k'ofarnan ni wajen 'yan uwana zanje inkwanta"


"Ke Billy sai kibarmu nan mukad'ai kitafi can to mezai k'araki dashi idan kika kwana can da nan d'in bazai k'araki dashi ba?" 


'Bata rai Billy tayi had'e da cewa "Momy jiddah nifa bana son haka, kamarya mezai k'arani dashi? 'YAN UWANA NE fa, gaskiya kada kikoma yimun hakan banaso" tana gama fad'ar hakan tajuya tabar falon tare da cewa


"Saida safe kuma kiyi addu'a idan zaki rufe"


"Hain shashasha wacce batasan abunda takeyi ba, mace bata sonku kuda uwarku amma sai shsshige mata kikeyi ita da 'ya'yanta samnar banza samnar wofi" mom Jidda tafad'a cikin jin haushin Billyn


"Eh koma meye naji d'in" Billy tafad'a itama lokacin data ida ficewa daga cikin falon tanufi part d'in mom


Ab'angaren mom kuwa tunda suka dawo bayan ta watso ruwa takoma d'akinsu Batool dake zaune ita da yayya Basmah suna fira, zaunawa itama tayi cikinsu sukaci gaba da firar abun gwanin ban sha'awa uwa tare da 'ya'yanta, wayar Basmah ce dake cikin jikka tayi k'ara Batool tajawo jikkar had'e da ciro wayar tamik'a mata, karb'a tayi tanabin special no d'in data gani arubuce ankirata da ita da ido kafin can ta d'aga,


"Hello, assalamu alaikum" taji anfad'a 


"Wa'alaikassalam" itama tamayar masa da amsa ta b'angarenta,


"Kina magana da sadeeq ne abokin yayanki"


"Oh Allah sarki yaya sadeeq, bakaji gajiya ba?"


"No..indai akanki ne babu wata gajiya da zata iya hanani kira don inji muryarki" murmushi basmah tayi duk da dai harga Allah bataji tana sonsa ko kad'an ba, amma zatayi accepting d'insa tagani kozai iya cire mata tunanin da k'aunar Mahmud pilot kuma yamaye mata gurbinsa, muryarshi ta tsinkayo akunnenta yana fad'in


"Kinyi Shiru Basmah kona takurakine?" Mik'ewa tayi tabar d'akin takoma falo takwanta akan kujera tree seater sannan tace


"No!.ko kad'an just dat ina jin baccine" 


"Ayya ina tuba, dama zuciyatace ta tirsasani kiranki akan sai taji zazzak'ar muryarnan taki zata samu natsuwar da zata bani damar yin bacci kuma.." Ai kafin yarufe baki Basmah taji wani irin ciwo da bazata iya kwatantasaba ya taso mata,


"innalillahi wa inna ilaihirraji'un" tafad'a da k'arfi had'e da mik'ewa tsaye tanufi d'aki har suna neman karawa da mom dake k'ok'arin fitowa daga cikin d'akin zata shiga nata


"Ke lafiya?" Mom tafad'a tana kallonta, k'ok'arin danne yanayin da takejin kanta ciki tayi tare da d'an sosa k'eyar kanta sannan tace


"Fitsarine ya matseni mom"


"Mts..Basmah yaushe kika tsiri wannan d'abi'a kuma?, maza kije kiye mana kintsareni da wud'annan idanuwa naki, ai wannan d'abi'a ba mai kyau ceba ko kad'an inma zaki dena kidena" sannan tawuce bedroom d'inta tanaci gaba da fad'an,


Hayewa tayi kan gado had'e da lumshe idanuwa tana fitar da lumfashi ahankali, kiran sadeeq ne yasake shigowa awayarta, saida takusa tsinkewa sannan tad'aga har lokacin idanuwanta na arufe


"Hello" tafad'a batare da tasan cewa shine yasake kira ba, wata ajiyar zuciya yasauke jin muryarta da yayi had'e da cewa


"Basmah are you ok"


"Yeah! Yaya sadeeq am ok tafad'a had'e da cewa sorry kaji natsinke maka waya ko?"


"Ayya badamuwa, tunda dai lafiya kike"


Yanayin da take jin kanta aciki daurewa kawai takeyi tana wayar dashi don kada yaga tayi masa walak'anci bawai don tana buk'atar hakan ba, haka taci gaba da amsa wayarsa har saida ya gaji don kansa yayi mata sai da safe, saboda tund'azu shikad'ai ke surutunsa, batayi minti biyar da gama waya dashiba kawai taji wani irin azababben ciwon kai yataso mata, rik'e kan tayi tana k'ok'arin yiwa Batool dake zaune kan gadon tana tofa addu'ar bacci zata kwanta magana kawai taji kamar an cinna mata wuta acikin zuciya, nan take ta tuna da cewa gaba d'aya yau Batasha maganin taba saboda baau wuni agida ba gashi kuma hankalinta ya d'auki da suka dawo balle tasha sai yanzu da taji ciwon yataso mata, ai kafin tasake yunk'urin yin wani abu saiga jini nafita ta hancinta, hannunta tad'a ya sauka saman kafad'ar Batool yasata juyowa,


 Arud'e take kallonta cikin tashin hankali ganin jinin dake fitowa ta hancin ta, don tunda Basmah tafara bleading tahanci daidai da rana d'aya bata tab'a bari wani yagani ba, afirgice batool tace


"Yayya, meyake faruwa, jinifa kefitowa daga hancinki?" Cikin k'arfin hali tasa hannu tagoge jinin dake neman gangarowa cikin bakinta had'e da cewa 


"Batool bud'e wardrobe maganina na nan saman kaya kid'aukomun, gaba d'aya yau namanta bansha ba" 


Batool da gaba d'aya tagama rud'ewa saukowa tayi kan gadon batare da tabi takan maganin da tace ta d'auko mata ba tafice d'akin aguje, wannan karon d'akin mom tafara shiga tasanar da ita halin da 'yar uwarta keciki sannan tanufi d'akin yaya Mahmud shima tafad'o masa, tsabar firgicewa yaya dagashi sai boxer da bes yafito har suna rice rigen isowa d'akin shida Batool dat fashe da kuka, yana zuwa ya tadda mom rik'e da ita itama tana kukan, kallonta yayi tana k'ok'arin goge jinin da tissue d'in da mom tad'auko tare da cewa 


"Is over Basmah, wlh wannan karon duk abunda zai faru saidai ya faru, amma dole kowa yasan halin da kike ciki, taya za'ayi muzuba ido kirasa rayuwarki saboda farincikin 'yar uwarki, to koda za'a fasa d'aura auren mune gaba d'aya banda gobe saidai afasa, amma sai nafad'i dalilin wannan ciwon nakai, haba Basmah dubi yanda k'arfin halinki kenema ya salwantar maki da rayuwa to bazan juri hakan ba ko kad'an nayi iya abunda zan iya amatsayina na d'an uwanku dake sonku gaba d'aya"  kallon mom yayi sannan yace "mom kidena kuka dole yau kisan abunda muka dad'e muna b'oyewa akan wanna ciwon da Basmah keciki"


"Pls yaya don girman Allah kada kafad'a, kada kafad'i abunda zai rusa farincikinmu don Allah, mom karki tab'a yarda da yaya" Basmah tafad'a daidai lokacin da Billy ta kawo bakin k'ofar d'akin, har zata shiga sai taji Batool namagana cikin kuka kamar haka


"Yayya dolenefa mom tasan komai don ita mahaifiyar muce sannan yanda muke son Billy kema haka muke sonki, natabbata itama Billy bazata so ganinki acikin wannan yanayin ba don itama tana sonki, har sau nawa zaki hak'ura da farincikinki, har zuwa wane lokaci zakuci gaba da sadaukar da rayuwarki akan soyayyar 'yar uwarki, duk da bamuda yak'ini akan yaya Mahmud zai soki irin soyayyar da kike yimasa tun baki mallaki hankalinki ba yakamata ace ansan da wannan matsalar taki in akwai yanda za'ayi a maganceta sai ayi amma dole kidena azabtuwa haka dole kidena shanwahala akan soyayyar d'an uwanki da zaki iya mallakarsa amatsayin mijinki, mom yayya tadad'e tana son yaya Mahmud d'in borno kuma koda sukazo garinnan ashirye take data nuna masa haka, amma duk yadda tayita k'ok'arin nuna masa soyayyar da take yimasa yakasa fahimtar hakan daga k'arshe ma saita fahimci cewa gaba d'aya hankalinsa baya kanta yana wajen  'yar uwarta, tundaga lokacin da taji yafurtawa Billy soyayya kuma tafahimci itama tana sonsa tad'auki d'a marar yak'i da zuciyarta akan tahak'ura dashi wanda gaba d'ayanmu nida yaya muka goya mata baya akan haka saboda soyayyar da muke yiwa 'yar uwarmu bayan munsan cewa tana k'aunarsa fiye da tunani" share hawaye Batool tayi cikin kuka tace nagaji da ganinki kina shan wahala haka bayan gaba d'aya keda Billy duka 'YAN UWANA NE kuma ina sonku, 


"Haba Batool yanzu mekikayi haka, ashe alk'awarin kenan da kika d'aukarmun? Ashe akwai ranar da zaki iya bud'e baki kitona wannan sirri da muka riga muka binne tsakanina daku, shin atafi ina son yaya mahmud to ai itama Billy atana sonsa fiyema da yanda ni nake sonsa kuma shi ai ita yace yana so bani ba, kada kuzamo masu aon kai yaya, wlh natabbata son da suke yiwa junansu zai iya jefasu mummunan halin da yafi nawa idan akayi yunk'urin raba tsakaninsu, shin yanzu meye amfanin yasan da soyayyar dani nake yimashi, shin kunyarda cewa kurasa 'yan uwa biyu aduniya akan kurasa 'yar uwa d'aya? a gaskiya baku kyautamun ba ko kad'an idan kuka yimun haka kuma kun karya zuciyata akan yardar da nake da ita akanku" wani irin tarine ya sark'eta tad'ago kai tana kallon mom dake faman sa tissue tana tare jinin dake fitowa cikin hancinta sannan da k'yar taci gaba da cewa


"Mom nasan ke uwace da zata iya rufewa 'yarta asiri, don Allah kada kibari maganarnan tafita, koda hakan na nufin zan rasa rayuwata, kada kitab'a basu damar aikata wannan kuskuren har sai farincikin 'yan uwana da burinsu ya cika " kallon mahmud mom tayi dake tsaye hawaye naziraro mata a idanuwa tace 


"Son jeka kafiddo mota muje asibiti da ita tukun" da sauri Basmah ta k'ank'ameta tare da fashewa da kuka tana fad'in


"Pls mom don Allah kada kukaini asibiti, narok'eku daku barni agida akwai maganin da likitana yabani ina sha," kallon Batool tayi tace "Batool d'auko maganin dana cemaki in sha, zansa mu sauk'i sosai, zan samu relief kafin gobe, mom nayi maki alk'awari gobe da kaina zanje inga likitan dake dubani kafin afara walima dama dalilin tashin ciwon saboda mantawa danayi yau bansha maganin ba gaba d'aya shiyasa" jin cewa akwai maganin da zai taimaka mata da gaggawa yasa mom tace Batool ta d'auka abata tasha amma idan ciwon bai kwantaba dole suje asibiti komai dare, 


Wani irin kukane ya kuccewa Billy dake lab'e tana saurarensu tayi saurin sa hannu ta toshe bakinta had'e da ficewa part d'in aguje...





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


U👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Bless upon you people who says bad word to me, thank you so much, amma ina so kusani babu abunda zai canza gayanda nad'auko labarin nan insha Allah, I feel so bad ga yanda kuke k'orafi da nuna anajan littafi ko ana jamaku rai after all am here trying all my possibilities wajen ganin nakammala littafinnan dis week, Basmah zata mutu ko bazata mutuba, zata auri Mahmud ko bazata auraba is all about of her destiny, ciwon Basmah is so worst or not, duka fiyema da hakan nafaruwa kuma azahiri ana samun hakan acikin rayuwar al'ummarmu, ni akoda yaushe fatana asamu darasin da za'ayi koyi dashi daga ciki, bawai inbi ra'ayin kaina kona fan's ba, wlh mutum d'aya idan yak'aru da wannan littafin Alhamdulillah kwalliya tabiya kud'in sabulu, so for those who says anything they want on me,  pls keeps it up, am always free heart bazan tab'a rik'eku araina ba_😍 

💎Page_____84💎



  Dagudu ta isa part d'insu lokacin mom Jidda nashirin rufe k'ofa don bayan tafiyarta ba rufe ba saboda saida suka gama fira ta watso ruwa sannan tazo zata rufe k'ofar saiga Billy tagani tataho aguje tana kuka da kad'an tabingijeta, da sauri mom Jidda tajaye had'e da bin bayanta da kallo har tashige d'akinta, mere baki mom Jidda tayi had'e da cewa


"Ikon Allah" sannan tarufe k'ofar had'e dayin bisimillah don neman tsari daga shed'anun aljanu, bayan tarufe kuma ta tottofa addu''o'i ajikin k'ofar sannan tawuce d'akin Billy, ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita yasa tak'arasa daga cikin d'akin had'e da zaunawa gefen gadon da take kwance takifa kanta akan pillow, dafata tayi sannan tace


"Ke Billy lafiyarki kuwa? Mekuma yadawo dake bayan kince wajen 'yan uwanki zaki kwana?" Shiru tayi mata batare data tankataba taci gaba da kukanta kamar ranta zaifita,


"Au shine kikayi kunnen uwar shegu dani sai kace nina b'ata maki rai, ina ai saida nace kiyi kwancinki nan amma kikak'iji waike mai 'yan uwa harda wani cemun 'YAN UWANA NE, yanzu kuma da kikaje aka shuko maki rashin mutunci aka yimaki walak'anci shine zakizo ki ishemu da kuka har ina yimaki magana kina k'yaleni, to ai shikenan ke kika sani" tamik'e tare da ficewa abunta tana fad'in "yarinya can gasu gada....waya aikeki?"

 

Ita kuwa Basmah bayan tasha magani, mom takalleta had'e da cewa "duk da nakasance mai matuk'ar son kanta, da goyawa 'ya'yanah baya akan abunda sukaso to wannan karon dolene in kauda kaina domin duka abunda yafaru akanku nice sila tunda nakasa kula daku lokacin daya kamata sai yanzu da lokaci yak'ure, Basmah kinyi kuskure sosai wajen tirsasa zuciyarki dena son abunda kika sancewa bazata tab'a iya hak'ura dashi ba, don haka dolene kiyi hak'uri har Allah yayi maki wani zab'in mafi k'ololuwar alkhairi akanki, matuk'ar kinsamu sauk'i nayi alk'awarin bazan tab'a bayyana sittin zuciyarki ba da kuma halin da kike ciki har zuwa lokacin da za'a kammala bukinnan, amma idan wannan ciwon yak'i kwanta maki har zuwa lokacin to tabbas da kaina zanje insanar da dadynku kuma zan nuna wannan sonkan nawa tahanyar durk'usawa koda agaban 'yar uwar kune data hak'ura tabarmaki Mahmud don bazan iya jurewa in rasaki ba" tak'are maganar cikin kukan dake nuna irin tsantsar soyayya da tausayin 'yar tata da takeji. 


Ko kad'an yaya Mahmud da Batool basuyi na'am da shawarar da mom tayanke ba, wanda hakan yasa yaya Mahmud cewa


"Mom wannan fa bashine mafitaba kawai.." Katsesa mom tayi tahanyar d'aga masa hannu tare da d'ago kai tana kallonsu tace


"Indai nice mahaifiyarku banyafe kuje kufad'i wannan maganarba ga kowa saboda yin hakan tamkar kun muzanta 'yar uwar kune" murmushi Basmah tayi jin abunda mom tafad'a tare da qudurtawa aranta dayardar Allah har akanmala bukin bazata koma yarda tabayyanawa kowa halinda take ciki ba koda sud'in ne, nan take tarufe idanuwanta kamar tayi bacci mom na shafa gashin kanta ahankali,


Tsabar yanda ransu tab'aci akan abunda mom tafad'a yasa daga yaya Mahmud d'in har Batool suka fice daga cikin d'akin, kallonsa Batool tayi had'e da cewa


"Yaya kaji dai abunda mom tafad'a yanzu meye shawara?"


"Babu!, kawai abunda yafi mubita da addu'a Allah yasawak'e kuma yarabata da wahala"


Gaba d'aya Basmah da Batool da Billy da kuma yaya Mahmud daren basuyi bacci ba, it dai Basmah ciwon da take cikine ya hanata, Billy kuma rad'ad'i da zafin hukunci data yankewa kanta ne ya hanata sukuma su Batool tunanin makomar 'yar uwarsu akan halin da take cikine yahanasu bacci. 


Soboda kukan da Billy keyi har saida ya sakar mata zazzab'i tashi tayi tajawo first aid d'in dake cikin wardrobe tab'allo PCM tasha sannan tashiga toilet tayo arwala, sallah takeyi amma har lokacin hawaye basudena saukowa daga cikin idanuwan taba har aka kusan kiran sallar asuba, addu'a tayi sosai mai tsayi tare da fawwalawa Allah dukkanin al'amurranta, har aka kira sallar asuba tananan  zaune akan abun sallah, tashi tayi tayi raka'atanil fijir sannan taci gaba da addu'o'inta kafin atayar da sallah, tana gama sallar asuba tad'auko azkar d'inta taci gaba da karantawa har rana tafito, toilet tashiga tayo wanka sannan tafito tayi tsaye gaban madubi tana kallon yanda idanuwanta suka kumbura, gaba d'aya ko iya bud'esu batayi sosai, wasu hawayene suka ziraro mata a fuska ta koma gefen gado tazauna tare dasa hannuwanta tadafe kanta tanaci gaba da kukan, wata zuciya ce tace mata,


"To yanzu meye abun kuka tunda ke kika zab'awa kanki rabuwa da farincikinki, yazama dole kema kiyiwa 'yar uwarki sadaukarwa da halaccin da tayi maki wajen danne soyayyarta, wanda badon kunnuwanki sunji komai ba da tak'wammacewa tarasa ranta saboda kisamu farinciki" nan take ta tuna da jinin data sharo jiya ad'akin ummi ajikin tissue, tabbas yanzu tasamu amsar cewa wannan jinin na Basmah ne don ita takwana ad'akin kuma tasamu dalilin fitar jinin atare da ita.


Hannu tasa tagoge hawayen ahankali tafurta


"Ya hayyu ya qayyum birahmatika astagisu, aslihli sha'ani kulluhu wala takilni ila nafsi d'ar fata ain,laa'ilaaha illa antassubhanka inni kunta minazzalimin, Allah ina tawassali da girman zumunci da kuma kyakkyawar manufar dake cikin zuciyata, ya Allah Kabani hak'uri da juriya rashin yaya mahmud, Allah ka sanya alkhairi acikin kasantuwarsa shida 'yar uwata, Allah Kabani dangana kuma ka tausayawa 'yar uwata mahaifinmu ya amince mata tasamu farincikinta" kuka maik'arfine ya sake kuccemata tafad'a akan gado tana auruttai masu kama da sabbatu "kayafe mun yayana, ina matuk'ar sonka, ina sonka sosai sonda bazan koma yiwa wani d'a namiji shiba aduniya, amma dole nahakura dakai domin ina son 'yar uwata fiye da soyayyar da nakeyiwa ni kaina, zan barkane kawai don ceto rayuwarta, badon hakaba da tare zamu rayu kuma atare zamu mutu", 


A hakane har bacci mai nauyi yasoma d'aukarta saboda rashin baccin da bata samu tayiba jiya, cikin baccin ne tayi mafarkin wai gata zaune cikin taron mutane d'auke da wani abu ahannunta da batasan ko meyeba tanata kuka, nan taga ana k'ok'arin fitowa da makara d'auke da gawa, tasowa tayi tana son taje taga ko gawar waye sai aka rik'eta aka hanata zuwa wajen, kuka takeyi sosai lokacin da mutane ke k'ok'arin fita da gawar tana don Allah abarta taje amma aka hanata, wani iskane mai k'arfi yataso had'e da d'age tabarmar da aka rufe gawar da mayafi, kawai sai taga fuskar 'yar uwarta yayya Basmah aciki kwance tana murmushi, fad'uwar da tayi zaune ne tare da k'ank'ame abunda ke hannunta tasaki wani irin kuka mai sauti yasata farkowa daga baccin da takeyi afirgice wanda yayi daidai da shigowar Ummi ad'akin, da gudu ta taso had'e da rungumeta tana kuka "Ummi ni bazanyi aurennan ba nafasa, don Allah Ummi kifad'awa dady bazan auri yaya Mahmud ba" murmushi Ummi tayi da fitowarta kenan daga part d'in dady bayan tafito wanka yanata tsokanarta akan Billy zata tafi gidan mijinta tabarta shikuma zata samo masa wacce zata cire mata kewarta, atunaninta duk jimamin barinta da zatayine yasa take wud'annan maganganun amma saitaji yanayin rik'on da tayi mata da kukan da takeyi yafi k'arfin ace kawai narabuwa da itane, d'agota tayi da sauri had'e da kallon fuskarta data kumbura tashiga bubbuga kumatunta cikin tacin hankali tana fad'in


"Bilkisu, Bilkisu, lafiyarki kuwa? Ke wai meyake damunkine, bazaki bud'e baki kiyimun maganar da zan fahimta bane?" Cikin shesshekar kuka tace


"Ummi bana son aurennan, don Allah kada ad'auramunshi, bana buk'ata Ummi" wani irin jirine ummi taji ya d'ibeta ganin da gaske da gaske billy ke wannan maganar wanda yasa nan take ta d'auketa da zafafan maroran da saida tafad'i k'asa, cikin b'acin rai Ummi takalleta had'e da cewa "idan mafarkine kikeyi Bilkisu to maza kifarka kafin ranki yab'aci kamar yanda kika b'atamun nawa" sannan tajuya cike da b'acin rai zata bar d'akin, da sauri Billy tarik'o k'afafuwanta had'e da cewa


"Wayyo Ummi nah wlh ba mafarki nakeyi ba, afarke nake Ummi kuma da gaske nakeyi bana son aurennan, saboda koda anyimunshi bazan tab'a samun farinciki ba"


Juyowa tayi tana kallonta had'e da cewa "innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Bilkisu anya ko ba aljanu suka shigeki ba, taya za'ayi ace gobe aurenki wai kice kin fasa, to kibari idan aka d'aura auren aka kaiki kimutu kinji ko? Shashashar yarinya kawai" tafice abunta cike da jin haushin 'yar tata.


Basmah kuwa duk da tanajin jiki haka tatashi tazage suka fara shire shiren walimar da za'ayi yau, ko kad'an bata bari gazawarta tabayyana afili don d'ai kar mom tafahimta harta aiwatar da abunda tace, Batool ma gaba d'aya yau babu walwala atattare da ita saboda rashin sanin madafar 'yar uwarta akan sharad'in mom, don duk b'oyon da Basmah keyi tana kalle da ita da kuma yanayin da take ciki, 


Ganin kuka bazai amfana mata komai ba dole tayi abunda keyuyuwa don gaba d'aya mafarkin da tayi yaga tsoratata akan cewa tabbas Basmah zata iya rasa rayuwarta idan har tayi saken da igiyar aure tashiga tsakaninta da yayanta gobe, tashi tayi tasaka kayanta don dama towel kad'aine d'aure ajikinta tare da nufar part d'in dady tana maijin kowane hali da matsala zata fuskanta bazata tab'a auren yaya Mahmud ba bacin 'yar uwarta tafita buk'atarsa.


Da sallama tashiga parloun fuskarta ba yabo ba fallasa duk da kana kallonta zaka gane cewa tayi kuka kuma ba d'an kad'anba saboda yanda idanuwanta da fuskarta suka kukkumbura, cikin sa'a tasamu dady yana k'asa ya sauko don bai dad'e da gama breakfast ba yana waya da Mahmud pilot akan yazo yana son ganinsa akan zai tambayesa idan an d'aura aure gobe asabar zasu wuce da amaryarau ko sai banda gobe safiyar lahadi, shigowa tayi ta zauna gabansa wani b'angare na zuciyarta cike da tsoron rashin sanin abunda dady zai yimata idan tafad'a masa abunda ketafe da ita, yana gama wayar yakalleta fuskarsa d'auke da murmushi yace 


"Auntyn Bilal injin dai ko lafiya naga fuskarki takumbura haka, Kaddai ince har kinfara kukan rabuwa da ummin taki tun yau" Shiru tayi kanta na duk'e ak'asa kafin tad'ago tana kallonsa idanuwanta na hawaye tace


"Dady kayafemun don Allah" tak'arasa maganar tare da had'a hannuwanta wuri d'aya, shima jiyayi hawayen sun cika masa idanuwa saboda tausayinta don shi atunaninsa saboda rabuwar da zatayi dasu ne, gashi za'a d'auketa tayi nisa dasu sosai, hannuwanta yarik'e had'e da cewa 


"Aini baki tab'a sab'amun ba duk iya zamanki dani tun kina k'aramarki don haka kidena neman yafuwata saboda keda 'yan uwanki nadad'e da yafe maku duk wani abu da ku kayimun" cikin kuka tace


"Nasani dady shiyasa yau nake rok'on ka saboda akaro nafarko zansab'a maka da girmana, dady don Allah ina neman alfarma agareka amatsayina na k'aramar 'yarka daka tausayamun ka amshi k'orafin da nazo dashi agareka zuciyata cike da sarai da kuma yak'ini akan cewa zaka amsa mun" jikin dadyne yayi sanyi tare da d'an matsowa gaba daga zaunen da yake akan kujerar yace


"Bilkisu meke faruwane?, kin sanyani aduhu, maza ki gaggauta fad'amun k'orafinki ashirye nake dana karb'a makishi matuk'ar zakiyi farinciki"


"Kayimun alk'awari dady" tafad'a tare da mik'o masa hannu, cikin mamaki yabita da idanuwa yana kallo cike da tunanin wannan wane irin k'orafine da har saita nemi yayi mata alk'awarin cewa zai karb'ar matashi yamik'a hannunsa had'e da d'ora sa akan nata yace


"Nayi maki Bilkisu, ina fatar Allah yasa incika maki wannan alk'awarin matuk'ar baifi k'arfina ba" murmushi tayi tare da goge hawayenta sannan tace


"Don Allah dady afasa d'aura aurena da yaya Mahmud, bana son in auresa ko kad'an bana buk'atar yin aure yanzu dady don Allah kataimaka mun kada ad'aura wanna aur..." Ai kafin tarufe baki taji saukar zafafan marora da batasan ta ina suke fitowa ba, da gudu Mahmud pilot daya dad'e a tsaye bakin k'ofar yana k'ok'arin shigowa saboda kiran da dady yayi masa sai yatarar da mummunar maganar data nemi tasakasa suma yak'araso cikin falon jin saukar maroran da dady kesakar mata yana nema ya rufeta da duka ya rik'esa tare da shiga tsakaninsu.


Jikin dady naciccira yake fad'in


"Dama ke shashashace ban sani ba? Nizaki zowa da wannan mummunar maganar da zatasa inzama mutumen banza? to wlh baki isaba, idan tarok'i akayi to k'aryarku tasha k'arya inkuma Wasu jinnune suka hau kanki to zanyi maki maganinsu, mutuniyar banza da wofi baki isa ki watsemun zumunci ba nida 'yar uwata data nuna mun soyayya fiye da kowa aduniya, wallahi da inb'ta ran 'yar uwata k'ara natabbata cikin k'unci da damuwa nahar abada akan rashin yimaki abunda kike so" kalmar k'arshe da yayi tak'arasa Billy k'warin guiwa akan cewa idan har dady yana tsoron b'atawa 'yar uwarsa rai haka to ita yafi cancanta ace taji tsoron rasa 'yar uwarta, tabbas zata jurewa kowane hukunci dady zai yimata kuma tad'au alk'awari bazata tab'a bayyana sirrin zuciyar 'yar uwar taba saboda hakan shizai sa Mahmud ya aminta da aurenta batare daya musguna mata ba bisa da ace yasan cewa itace silar da tasa tak'i amincewa data auresa.


Dak'yar Mahmud pilot ya zaunar dady had'e da d'auko ruwa a fridge yabashi yasha, sanan shi kuma yajuya inda Billy ke zauna tahad'a kai da guiwarta tanaci gaba da kuka, gabanta ya duk'usa cikin sanyin murya dake nuna yanayin damuwar da yake ciki yace


"Billytah" d'ago kai tayi da niyar kallon fuskarsa amma sai taji bazata iyaba "Billytah d'ago kai kifad'amun menayi maki kikace kinfasa aurena? narok'eki kifad'amun komeye ashirye nake dana rok'eki kiyafemun, Bilkisu kiyimun magana mana" yafad'a ijiyarsa d'aya nafidda k'walla, jin tak'i cewa komai sai kuka da takeyi yasa yaci gaba da cewa "karki manta ba sau d'aya ba ba sau biyu ba da bakinki kinsha fad'amun cewa atare zamu rayu kuma atare zamu mutu, har alk'awari kika d'aukar mun cewa tabbas zamu rayu tare dake kuma ak'ark'ashin inuwa d'aya, to meyasa yanzu kuma zaki karya" yafad'a cikin tsawa tare da jawo hannunta yana k'ok'arin cire zoben daya bata ranar da zasu koma barno.   


Da sauri tak'wace hannunta tare da cewa


"Saboda bazan tab'a samun farinciki ba idan na aureka, pls don Allah kabarni bana son auren nan yanzu ko kad'an" matsowa yayi dafa da ita kamar zai rungumota sannan yakama kunnuwansa idonsa na hawaye, zuciyarsa nayi masa wani irin k'una da rad'ad'i


"Pls Billy kiyi hak'uri, idan wani abu nayi maki na amince kiyimun hukunci amma don Allah kada kibarni, ko kad'an bana son wannan kalmar rabuwa da kike furtawa atsakaninmu, kiyi hak'uri billy kituna da cewa munyiwa juna alk'awari akan tare zamu rayu tar..." ganin zai iya cin galabar zuciyarta har ya sauya mata quduri yasa tayi saurin katsesa tare da turesa da k'arfi tana fad'in 


"Bazai yuyuba yaya don ahalin yanzu bazan iya auren kaba, don Allah kayi hak'uri ka d'auki wanna kalmar atare zamu rayu kuma atare zamu mutu amatsayinmu na 'yan uwa kawai amma bada aure ba"


Dady da tund'azu yake saurarensu yanaji tamkar  yakamo Mahmud d'in dake faman rarrashinta da ita dake bashi haushi yayita duka yanufo wajen da sauri cikin fushi da b'acin rai zai rufeta da duka saboda yanda yaji ta katsawa Mahmud d'in tsawa tare da turesa, 


Da sauri Mahmud pilot ya dakatar dashi had'e da cewa


"A'a dady kabarta, nahak'ura bazan aure taba tunda har tanaji cewa bazata samu farinciki dani ba, na amince murayu amatsayin 'yan uwa ni da ita" juyowa yayi tare dasa hannu yagoge hawayen da suka zubo masa a idanuwa yana kallonta sannan cikin sanyin murya yace


"Zanbarki Billy, zanbarki kiyi farinciki akaro nabiyu kin sake wasa da zuciyata, karki damu nafahimci duka laifina ne dana tirsasaki akan soyayyata, amma ina so kifad'amun da bakinki cewa bakya sona kuma kin tsaneni hakan zai tabbatar mun da cewa da gaske kikeyi bazaki iya aurena ba" 


Wani irin kuka mai tsima rai takeyi wanda duk wanda yasan meye soyayya da yanda akeji akanta zai iya fahimtar cewa ko kad'an babu komai azuciyarta face tsantsar soyayyar yayanta kafin tad'ago kanta idanuwanta acikin nasa tace


"Wlh yaya dagaske nakeyi bazan iya auren kaba, kawai ka hak'ura dani" ai kafin Mahmud yace wani abu yaga dady yaciro wayar socket yafara bugun Billy da ita yana fad'in "wlh baki isaba sai kin auresa idanko ba hakaba sai dai kibarmun gida, su alhaji kabiru ne shida 'yan uwansa da shigowarsu kenan suka isa wajen da sauri suka rik'esa shi kuma baba k'arami ya d'auketa k'asa ransa ab'ace don duk yafisu zuciya yace


"Yaya wannan wane irin muzgunawane zaka jima yarinyarka ana gobe d'aurin aure kuma agaban mijin da zai aureta"


"Muzammil don Allah kubarni inkoya wa yarinyar nan hankali, agabana take wulak'antamun d'a, take fad'a masa kalaman da zasu cutar dashi sai kace ita kad'aice mace aduniya" nan dai suka zazzauna suka rarrashi dady tare da bin ba'asin abunda kefaruwa, take dady yazayyane maau komai a-z har yanda sukayi da Mahmud d'in agabansa, iya girgiza sunyita jin abunda dady yafad'a cike da mamaki suna faman jinjina kai, ita kuma inbanda addu'a da fatar Allah yasa sugoyi bayanta babu abunda takeyi duk kuwa da tsamin da jikinta keyi, alhaji bukarne yayi k'arfin halin kirawota ya zaunar da ita a k'asa tsakankanin k'afafuwansa dana baba k'arami sannan yace Mahmud yaje ya zauna tsakanin dady da alhaji kabiru saiti da ita. Cikin natsuwa yadafa kanta had'e da cewa 


"Bilkisu karkiji komai ni mahaifin kine, kuma zanyi maki adalci matuk'ar kinada hujja mai k'arfi akan cewa bazaki auri d'an uwanki Mahmud ba, don haka saki jikinki kifad'amun meye dalilinki. 


Shiru tayi tare da d'ago idanuwanta tana kallon Mahmud da shima ya tsureta da idanuwa kafin tace


"Baffa tun ranar da Mahmud yace yana sona nafad'a masa gaskiya inada wanda nake so, bayan haka tunda yasanar da dady yana sona zai aureni ba'a tab'a kirana akaji shin nima na amince ina sonsa zan auresa a matsayina na 'ya, sannan kafin infurta cewa bazan auresa ba saida narok'i dady akan inada k'orafi kuma da kansa yayimun alk'awarin zai karb'a sai abu nak'arshe na amincene  zan auresa saboda ceto rayuwarsa lokacin da likitoci sukace yakusa kamuwa da ciwon zuciya matuk'ar ba'ayi masa abunda yake soba, sanin haka yasa danaje asibiti yarok'eni nayi sauri amincewa don kada yafad'a cikin wani hali amatsayinsa na d'an uwana yanzu kuma baffa nafahimci bazan samu farinciki ba idan na auresa shiyasa nazo da k'ok'on barana da tunda yanzu yasamu lafiya kawai yahak'ura" runtse idanuwa Mahmud yayi hawaye suka ziraro masa afuska don yasan duka gaskiya tafad'a amma shiyasan tana matuk'ar sonsa sosai don koyanzu yaga haka cikin idanuwanta dole akwai abunda yasa tace bazata auresa ba, dole sai indai shiga tsakaninsu akayi amma haka kurum ya tabbata Billynsa bazata k'isaba duk da cewa tayi masa abubuwan daya kamata idan har shi yanada zuciya yahak'ura da ita.


Ajiyar zuciya alhaji bukar yayi had'e da cewa "to kunji hujjojinta da dalilanta duk da Wasu basuda amfani amma akwai wud'anda dolene aduba mata koba hakaba yaya" yafad'a yana kallon alhaji kabiru da gaba d'aya kansa ya kwance, nan yatambayi both dady da yaya Mahmud cewa shin abunda tafad'a gaskiyane haka yake, duk suka tabbatar masa da eh, hakane, amma dady yace shi wud'annan hujjojin bazasu sa yajanye zancen aurnba saidai idan ankaita ta mutu, ganin rigima ta kabre tsakaninsu baba k'arami da dady sunce baza'a fasa aurenba shikuma alhaji kabiru da bukar sunce dole ahak'ura don gudun lalacewar zumuncin su tunda bataso yasa   Mahmud yace


"Dady, baffa don Allah abari wannan rigima haka, tunda batason auren shikenan, Allah yayi mana zab'in dukkanin abunda yafi zama alkhairi"


Sosai ya burgesu kuma dama shi dady tuni wata shawara tazo masa saboda baya son suci gaba da musu da yayunsa har azo wani sab'anin yasake rabashi dasu kamar yanda na mahaifiyarta yasa suka rabu na tsawo lokaci, bayan duk sunyi shiru  dady yakalli 'yan uwansa had'e da cewa


"Shikenan na amince, amma baza'a fasa d'aura aure da Mahmud gobe ba, Alhamdulillah da Allah yasa ba Bilkisu kad'ai nahaifa aduniya ba, ina so amatsayinku na 'yan uwana kusheda cewa naba d'ana auren 'yarku Basmah wato babbar 'yatah kuma ina fatar b'acin rai bazaisa Mahmud kawatsamun k'asa a idanuwaba kamar yanda 'yar uwarka tayi" Alhamdulillah wannan abu yayi sukace gaba d'aya tare da kallon Mahmud, "kaji abunda mahaifinka yafad'a, shin mekace?"


Har ga Allah yaso yamanta da zancen aure nan kusa gaba d'aya arayuwarsa amma bazai iya musawa dady ba, kuma dole yanunawa Bilkisu cewa ba ita kad'aice mace ba aduniya kuma don yarasata bazai mutuba, kuma bazai fasa son wataba azuciyars duk dako ba haka bane yasa yace


"Dady, baffa, Basmah da Bilkisu duka 'YAN UWANA NE, kuma duka ina sonsu ina k'aunarau tunda jininane, don haka na amince zan auri Basmah ina fatar Allah yasanya alkhairi tsakanin nida ita, dama wani baya tab'a auren matar wani" yak'are maganar had'e da mik'ewa yabar d'akin idonsa nazubar da hawaye, runtse idanuwanta tayi itama hawayen suka zubomata tayi murmushi mai had'e da kuka tare da cewa amin sannan tabi bayansa, gaba d'aya iyayen nasu nata saka mashi albarka, 


Nan su alhaji bukar suka sake ba dady hak'uri tare da mik'a masa kud'i dubu hamsin da biyar da suka had'a masa amatsayin gudun mawarasu agaresa duk da cewa sunsan yafi k'arfinsu wanda dama shiya kawosu gidan suka isko wannan bak'on alamari da Allah yasa aka warwaresa cikin sauk'i, kud'in baba k'arami yabashi tare da cewa


"Yaya ga wannan tsayawa bak'i ruwa gobe, kayi hak'uri dasu kasan yanayin yanda yake"


Karb'a dady yayi cikin jin dad'i da farinciki duk da yana cikin damuwa don nunawa 'yan uwansa cewa lallai suma suntaimaka masa duk dako yasan cewa yanada d'unkin ba lunkin wud'annan kud'in, godiya yadinga yimasu sosai  sannan yaciro wayarsa tare da cemasu  yakamata akira Umman borno don asanar da ita halin da ake ciki nafasa auren Mahmud da Bilkisu wanda gobe za'ayi sa da mahmud da Basmah, nan take suka amince da hakan bayan sun sheda masa itama suntura mata da dubu ashirin da biyar ta account taba bak'i ruwa amatsayin tasu gudun mawa..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Thanks for your beautiful comment, am so happy yanda naga kuna comment saboda yanda page d'in jiya yatab'aku, u people surprise me harda wud'anda bana tsammanin suna karanta littafinnan yau naga comment d'insu😅 thanks to my takwara Billy yau kin zak'ulomun ghost reader's d'ina💃🏼🤣, I luv you so much guzs jazakumullahu bikhairan🤝🏻Allah yak'aramaku k'arfin idanuwa da sabbin wayoyi na kamfanin iPhone🍏 *STAY BLESS FOR EVER MY FAN'S*_


💎Page_____85💎



     Nan take duk suka amince dady yakira Umma bugu d'aya tad'auka cikin yanayin da zai tabbatar maka da irin tsantsar farincikin da take ciki had'e da cewa,


"Assalamu alaikum yayana ina kwana?, barka da wuni"


"Lapiya klw hafsatu nah kina lafiya"


"Alhamdulillah ya hidama da taron bak'i"


"Masha Allah muma nan komai Alhamdulillah, gamu zaune tare da 'yan uwana"


"To kagaida mani dasu, naga sak'o nagode sosai Allah yasaka da alkhairi kuma yabar zumuncinmu"


"Amin ya Allah" dady yafad'a tare da yin shiru, hak'ik'anin gaskiya wani irin nauyi yakeji tayanda zai fuskanci 'yar uwarsa da wannan maganar kuma ko kad'an baya son taji zancen abakin kowa inba shiba, don gudun kada tayiwa abun mummunar fahimata, gaba d'aya 'yan uwansa zuba masa idanuwa sukayi suna jiran suji yanda zata kaya tsakaninsa da 'yar uwar tasu.


"Hello yaya yanaji ka kirani kuma kayi shiru, injin dai ko lafiya ko?" yaji Umma tafad'a cike da zak'uwar jin dalilin da yasa ya kirata, 


"Eh lafiya klaw saidai wata 'yar matsalace nake nema kibani shawara akanta"


"To yaya Allah ya azamu akan daidai" ajiyar zuciya yayi tare da fitar da wani irin iska mai zafi ga bakinsa da kuma hancinta sannan yace


"Hafsatu tsakanin Bilkisu da Basmah wa kikafi so aranki" dariya tayi kafin tace 


"Kai yaya wannan wace iriyar tambaya ce kayimun? Ai ina da Basmah da Bilkisu duka 'ya'yan kane kai ka haifesu ni kuma kai d'an uwanane don haka gaba d'ayansu ina sonsu kuma so maitsanani tunda jinina ne!"


"Kintabbata?" 


"Sosai kuwa yaya wai meye na wannan tambaya, nifa kasani aduhu?" Saida dady ya runtse idanuwansa, sannan yafara kwararowa Umma bayanin abunda ke faruwa da kuma hukuncin daya yanke namayewa mahmud pilot gurbin auren Bilkisu da Basmah sosai Umma taji maganar tamkar saukar Aradu cikin kanta, cikin rud'ewa tafara tambayar halin da d'anta keciki saboda irin son da tasan yana yiwa 'yar uwar tasa Bilkisu,


"Ki kwantar da hankalinki, lafiyarsa klw, karki tab'a tunanin cewa Bilkisu shi tacutar, wlh koka d'an bata cutar dashiba kamar yanda tacutar dani domin har inmutu bazan manta da wannan abun da yarinyar nan tayimun ba, kiyi hak'uri hafsatu banyi hakan bane don b'ata ransa ba nayine saboda kada ayi auren matsalolinta sutaba mana zumuncinmmu" danne rad'ad'i da zafin da takeji azuciyarta tayi had'e da cewa


"Shikenan yaya bakomai ai dukansu 'ya'yana ne, ubangiji Allah yasa hakan shiyafi zama alkhairi"


"Amin hafsatu ngd" bai kashe wayar ba duk saida yaba 'yan uwansa wayar suka tayasa bata hak'uri tare da nuna mata cewa matar mutum kabarinsa don haka kada wannan abun yasa taji badad'i har 'yan buki sufahimci damuwarta. Cikin ikon Allah kuma taji duk b'acin ranta fiye da rabi yakau saidai d'an kad'an da yazama dole tajisa aranta, sallama sukayi tare da kashe wayar sannan takira yaya Mahmud dake tsaye Billy nak'ara basa hak'uri cikin dakewa duk da yanda takejin tausayin kansu amma tacije tanuna masa cewa k'addarace tarabasu amma badon bata sonsa bane, murmushi yayi had'e da kallonta yana k'ok'arin jawo wayarsa dake ruri yace


"You are so funny Bilkisu, kina sona, amma bazaki iya aure naba? to meye wannan"


"Jarabawa yaya, kawai kayarda cewa dama Allah ya tsaro zamuyi soyayyane ak'ark'ashin jarabawarmu amma bazamuyi aure ba"


"Ko?, to ai shikenan" yafad'a tare da kara wayarsa akunne yabar wajen yana fad'in "hello ummanah" ajiyar zuciya tasauke jin yanda muryarsa tafito awayar tamkar baya cikin damuwa wanda har saida tayi tunanin kodai wasa yayanta keyi mata, don gayanda tasan son d'inta na k'aunar Billy bata tunanin rabuwarsa da ita tazamo abu mai sauk'i awurin sa, muryar sace da taji yasake cewa


"Ummanah are you there" tasa da sauri itama ta amsa masa da cewa


"Yes my son, ya kk? Kana lafiya? shin da gaskene abunda dadynku yakirani yana fad'amun yanzu?" Ta jefo masa wud'annan tambayoyin ajere cikin lokaci d'aya kamar zatayi kuka, murmushin da baikai ciki ba yayi tare da kallon gefen da Billy ketsaye a inda yabarta har lokacin ko motsawa batayi ba balle tabar wajen sannan yad'an d'aga muryarsa tayanda zata iya jiyosa yace


"Eh ummanah lafiya klw nake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah gobe ana gama d'aurin aure zamu kamo hanya nida amaryata, kiyi farinciki sosai domin dady mutumen kirkine, yayimun gata da babbar 'yarsa alokacin da k'aramar 'yar tasa taso ta tozartar da rayuwata" sosai Billy taji d'acin kalaman da taji kunnuwana najiyo mata daga bakinsa amma sai tabasar tare da barin wajen tana nanata kalmar _hazbunallaha wani'imala wakeel_,


Gaba d'aya duk abunda kefaruwa daga yaya Mahmud harsu Basmah da Batool da kuma au mom babu wanda ya sani kuma dady sunbar maganar atsakaninsu akan cewa sai gobe tayi idan and'aura auren kowa zai san da maganar, 


Yinin ranar kuma gaba d'aya Ummi fushi tadingayi da Billy akan maganar da tayi mata d'azu batare datasan cewa tuni mafarkin da tace idan shi Billy keyi ya kusa zama gaskiya.


Shikuwa yaya Mahmud yana can wajen faraaha da kullum cikin k'orafi take yimasa akan baya attending programs d'in duk da tayi on time don haka tana son ganinsa kafin lokacin waima yayi don atare za'ayita da tasu Batool, hakan yasa yaje don ya nuna mata cewa tabbas shid'in natane kuma zai iya bata lokacinsa aduk sanda ta buk'ata.


K'arfe 5:00pm na marece aka gabatar da waleema cikin kwanciyar hankali wacce Billy da kanta taje taciro wata abaya acikin kayan lefen da yaya mahmud yakawo mata bayan sun shirya za'a wuce takaiwa yayya Basmah had'e da cewa


"Yayya ga wannan kisa gaskiya yau shiga kala d'aya zamuyi dake mungaji da warewar da kikeyi acikinmu bayan mudake 'yan uwane" murmushi basma tayi had'e da cewa


"Ikon Allah, kufa amarene ku akeyiwa walima to mezai kaini yin shiga d'aya daku?"


"Pls yayya don Allah kikarb'a daga yaufa shikenan gobe rabuwa zamuyi" 


"Eyyeee lallai sisto na fahimci kinyi nisa a so, har kin matsu murabu  kiganki agidan yaya Mahmud ko?" Basmah tafad'a tare da lak'amo hannunta wajen wuyan Billy tana dariya saboda yanda taga tab'ata rai tad'an turo baki, hakan yasa Basmah takarb'i abayar bayan tagama shiryawa tsaf ta aza asama, jitayi nan take gabanta yafara fad'uwa wanda bata san meye dalilin hakan ba, cikin wannan yanayin sukaje wajen walimar da tasamu hallarar manya manyan malamai mata awajen, inda malama Jidda alk'ali tagabatar da nasiharta mai taken YARDA DA QADDARA itace tabbatuwar imanin musulmin k'warai, tana gamawa itama malama Afrah tagabatar da tata mai cike da nuna muhimmanci akan rik'o da zumunta acikin al'ummah sannan malama tak'arshe malama Asma'ul husnah itama takarb'a tayi masu nasiha akan biyayyar aure agidan miji bisa tarbar hak'uri da juriya, sosai amaren ke kuka wanda nan take itama Basmah ganin kukan da sukeyi yasa itama ta tayasu wanda kowanensu akwai dalilin daya sashi kuka akan nasihohin, bayan ankammala cikin natsuwa akabi duk wud'anda suka samu damar halartar walimar da wata k'atuwar leda da aka rubutawa _JAZAKUMULLAHU BIKHAIR FOR ATTENDING OUR MARRIAGE WALIMAT_ dake d'auke da alk'ur'ani hizib sittin dardumar sallah, tazbaha, hisnil Muslim, kaskon turare  da kuma turaren wuta acikin wata kwalba mai kyau, kasancewar akwai alk'ur'ani acikin ledar yasa ba'ayi wata hayaniya ba wajen rabawa kuma manya kad'ai aka bawa, sannan kowa yatafi gida jiki duk yayi sanyi saboda nasihohin da suka karb'a awajen k'wararrin malaman daban daban, 


Aranar kam Billy tayi kuka kukan da ita kad'ai tasan dalilinsa sai kuma mahaifinta da kuma Mahmud pilot, duk wanda yaga yanda take kuka lokacin da aka taso wajen walimar saida ya tausaya mata, shikanshi yaya Mahmud pilot yayi kuka kamar ba gobe, ji yakeyi tamkar kada safiyar gobe tawaye saboda itace ranar da zata haramta masa Billynsa har abada matuk'ar 'yar uwarta na agidansa kuma amatsayin matarsa daga k'arshe ya d'auro arwala tare da rok'on Allah yabashi hakurin rashin Billy kuma ya bashi ikon rik'e Basmah bisa gaskiya da amana batare da soyayyar Billy tayi tasirin da zatasa ya taushe mata hak'k'ok'anta dake kansa ba, Umma kuwa tuni ta shedawa alhaji mahaifin Mahmoud abunda kefaruwa Wanda nan danan ya kira dady yasake tambayarsa ko meye gaskiyar al'amarin, sosai yaji badad'i cikin zuciyarsa kuma ransa yab'aci sosai amma daga baya da yaji yanda dady kebasa hak'uri cike da nuna damuwa sai shima yayi fatan Allah yasa hakan shiyafi zama alkhairi, tun safe har dare Umma bata minti goma bata kira Mahmoud ba don taji ko yana lafiya, ta kirasa babu adadi wanda daga k'arshe yafahimci cewa ya amshi k'addararsa ayanda tazo masa kuma ya hak'ura da ita.


Basmah kuwa yanda tayi bacci a wahalce jiya kuma ta wuni a wahalce tana b'oye ciwon hakama daren yau ta kwana awahalce, amma duk da haka bata bari kowa yafahimci yanayin da take cikiba.


Da shire shire yau aka tashi sosai agidajen ahalin guda hud'u, gidan dady, garin borno gidansu Mahmud, gidansu faraaha da kuma gidansu dr. Ahmad don gudanar da shagulgulan bikin d'aurin auren nasu yanda yakamata, sosai yau mamy kecikin farinciki ganin yanda 'yan uwan mijinta da abokanan arzik'i suka taru agidan don taya d'anta tilo farinciki da murnar aurensa, Dr Ahmad kuwa baki yakasa rufuwa yau za'a kawo masa fatimarsa agidan sa kuma amatsayin matarsa, kallon Muhib sake faman tsula kula ahannun wata mak'wabciyarsu da mamy taba tashi tarik'e masa yace


"Shiii..Muhib today is a happiest day, bai kamata ace kana kuka ba saboda ur in-law is coming to dis house in d next few hour's" yana yimasa wasa da glass d'in hannunsa daya ciro daga  idanunsa.


Shiru Muhib yayi yana kallon yanda yake jujjuya glass d'in a fuskarsa tamkar yana jin abunda yake cewa.


Yau dai bakin alk'alami ya bushe domin da misalin k'arfe 1:00pm aka d'aura auren yaya Mahmud da amaryarsa faraah bisa zunzurutun kud'i har naira dubu d'ari, lak'adan ba ajalan ba d'aurin auren daya samu halartar manya manyan 'yan kasuwa daga k'asashen duniya daban daban abokanan kasuwancin dady, dattijai da sarakuna, manya manyan k'usoshi acikin gwamnati duk sun samu hallara wannan bukin, wanda alhaji kabiru da kansa ya ansarwa d'an d'an d'an uwansa auren faraha, murmushi dady yayi mai had'e da kuka tare da d'aga idanuwansa sama lokacin da aka gama d'aurin auren yana godewa Allah daya nuna masa wannan rana daya samu kusanci da soyayyar da d'an uwansa yayiwa d'ansa waliccin aure. 


Ana gamawa kuma aka nufi anguwar nasarawa family house d'insu dady inda kusan sama ga kashi tara bisa goma da suka halarci d'aurin auren faraaha suka sake garzayawa can harda iyayen nata don shedar aurensu dr Ahmad, kasancewar dama k'arfe biyu daidai za'a d'aura auren nasu yasa ana isa ba'awani tsaya b'ata lokaciba aka shiga sigar d'aurin aure tsakanin alhaji bukar da kuma iyayen Mahmoud filot da suka samu isowa tun k'arfe sha biyu narana kusan mota biyar, inda dama tuni sun dad'e da amsar k'addarar data kutso cikin auren, nan take suka fara nemawa d'insu Mahmoud auren Basmah ahannun alhaji bukar kuma yabasu bisa yanda addini yatanadar kowanensu farinciki na kwance afuskarsa, hatta Mahmoud pilot ya danne damuwarsa yayin da mutane suka fara kallon kallo da tambayar kansu taya hakan tafaru, yaya mahmud kuwa kusan mutuwar zaune yayi yana  tambayar kansa shin da gaskene abunda yaji ko kuma mafarki yakeyi, kai hardai aka kammala d'aurin auren Batool da dr.Ahmad kawunan mutane na ad'aure munkasa fahimtar wannan sark'ak'iya da akayi, ana kammala d'aurin auren aka fara fir fitowa mutane da take away na abinci da ferfesun nama dasu drinks, garar swan water ana rarrabawa da yake wasu irin manya manya rumfunane au alhaji kabiru sukasa aka kakkafa abakin k'ofar gidan yayinda dama antanadi securities d'in da zasu kula da tsarin auren har zuwa lokacin daza akammalawa, 


Kasa hak'uri yaya Mahmoud dake sanye cikin babbar riga farar shadda yayi har awatse taron saida yaje yajawo hannun Mahmoud pilot dake can gefen da aka tanadarwa iyayensa da abokanan sa da sukazo tundaga borno d'aurin auren, cikin rud'ewa yana d'aga hannun Babar rigarsa ya aza akan kafad'a yace


"'Dan uwa anya kaji wajen d'aurin aurennan sunan wacce aka ambata kuwa, wai kodai su dady sun mantane?" Cikin halin rashin damuwa da ko inkula da abun Mahmud pilot yace


"Eh mana najiya, ba nida 'yar uwata Basmah aka d'aura ba?"


"Wai mekake fad'i kana nufin da saninka kenan akayi? Bilkisu fa?" Saida Mahmud pilot yayi wani irin murmushin da yafi kuka ciwo sannan yace


"Ba ita bace Allah yatsaro zan aura, kasan matar mutum kabarinsa, to Allah baiyi cewa Bilkisu zata zamo matata ba saidai Basmah" cike da damuwa yaya Mahmud ya shafo  hancinta zuwa bakinsa yayinda idanuwansa suka kad'a sukayi jawur yace


"Look amma aikai Bilkisu kake so, daidai da rana d'aya baka tab'a cewa kana son Basmah ba, donme za'ayi maka haka?" B'ata rai Mahmoud pilot yayi yana kallonsa had'e da cewa


"Kai yaushe nafad'a maka cewa bana son Basmah, dukansu 'YAN UWANA NE kuma ina sonsu ina k'aunarsu kuma rashin auren Bilkisu bazai canza komai tsakanina dasu ba don haka Allah yatsaro cewa Basmah itace matata saboda haka kacire wannan mugun tunanin aranka kaje kakula da bak'in ka kaji ko" yak'are maganar had'e da d'aga hannu yana nunasa, Wasu hawayene suka zubo a idanuwansa lokaci d'aya ya rungume Mahmoud pilot yace


"Tabbas kai d'an uwane na K'warai, wlh inajin rad'ad'i da zafin faruwar wannan abun don nasan jurewa kawai kakeyi amma bak'aramin abubane ka hak'ura da soyayyar Billy don kana sonta sosai, kawai bayanda zakayine don anfi k'arfin kane" sai alokacin Mahmoud pilot yasamu damar zubar da hawayen nasa da tun d'azu yake k'ok'arin dannewa zuwansu, hugging d'insa shima yayi sosai kamar zai tsaga jikinsa yashige tanaci gaba da kukan, ahankali yaya Mahmud da shima hawayen yakeyi yadinga bubbuga bayansa alamun rarrashi har saida yayi ku kansa mai isarsa sannan yad'ago daga jikin d'an uwan nasa had'e da cewa


"Tabbas naso Billy arayuwata tayanda nake tunanin idan narasata bazan sake moruwa aduniyaba, ahiyasa Allahn daya bani rayuwar yajarabceni da kanta tace bazata aurenba saboda bazata samu farinciki agidana ba, kaga kuwa dole duk son da nakeyi mata inbarta kuma in amshi sauyin da Allah yayimun da hannu biyu, koba komai abunda yayi Billy shiyayi Basmah don haka nayi imani da wannan qaddarar so da Allah yayimun kuma Alhamdulillah" yana gama fad'ar haka yayi murmushi tare da barin wajen.


Har ga Allah kokad'an yaya Mahmoud baiji dad'in fasa auren Billy da Mahmoud pilot ba, amma shiwaye da bazai amshi wannan qaddarar ba tunda har wanda akayita akansa ya amince da ita, tunaninsa d'aya shine meyasa Billy ta aikata haka, meyasa Billy tarusa farincikinta da kanta?, shin kodai mom d'in sace taje tafad'i halin da Basmah keciki?, haka yadinga jerowa kansa tambayoyin da bayada mai bashi amsarsu awannan lokacin, ganin haka yasa jiki bak'wari yaje aka k'arasa tarbon bak'i dashi, ancire Ansha tare da fatar Allah yazaunar da wud'annan amare da angwaye lafiya kuma yabasu zuri'a masu albarka, multicolours d'in shaddodi masu tsada da agogayyen hannu dady yadinga rabawa duk wud'anda zasu tafi bayan kammala d'aurin auren har zuwa lokacin da taron yawatse.


Bayan ankammala taron d'aurin auren su dady sun dawo gida Basmah da duk tad'an fad'a tana zaune itada su Billy sunsha kwalliyar yinin buki sai k'arfin hali take famanyi tana tsokanarsu tana cewa


"Yau dai kunzama, kun zama d'auko hula, kun zama d'auko riga, kun zama d'auko wand.." Kafin ta iyar sukaji irin masu kirarinnan acan k'ofar gida suna fad'in


"Ina kike uwar amarya Basmah uwar amarya Batool yau kifito ranar murna ce da farinciki and'aura auren 'ya'yanki, kifito kiyi mana alkhairi yau kike uwar ango Mahmudu farin d'a mai farar aniya yayan amarya Basmah da Batool, ubangiji Allah yazaunar lafiya yabada zuria masu albarka, gaban Billy ne yayi wata irin muguwar fad'uwa da sauri ta rintse idanuwanta had'e da karanto " hazbunallaha wani'imal wakeel" shikenan yau shikenan tafaru tak'are duk wani mafarkinta da burinta akan yayan nata yak'are, kallonta Basmah tayi tana dariya had'e da cewa


"Kai sister tsofaffincan sunrud'e, kinji abunda suke cewa kuwa?" Tak'are maganar had'e da dafa Batool tana kallonta, murmushi itama tayi don gaba d'aya jikinta yamutu yana bata kamar akwai wani abun, mik'ewa Basmah tayi cikin k'arfin hali jin basu dena kiran sunanta amatsayin amarya ba tad'auki hijab d'inta tare da d'aukar rafar 'yan naira ashirin ashirin tanufi wajen masu ik'irarin dake cikin harabar gate, tana zuwa tamik'a masu had'e da cewa 


"Batool da Bilkisu ne amaren ba Basmah ba don haka kugyara" tana rufe baki motar su  Mahmoud pilot da yaya Mahmoud tashigo, bayansu kuma motocin mutanen borno ne da suka d'aurin aure sukazo  su d'auki amaryarsu anjima kad'an suwuce" da sauri yaya Mahmoud yafito cikin motar had'e da jan hannunta da k'arfi suka wuce cikin gida, yayinda sukuma masumasu kirarin ganin tajik'esu da rafar kud'i yasa suka koma kirarinsu yanda tafad'a, fitowa Mahmoud pilot dake zaune tunda suka shigo yana kallonta har zuwa lokacinda yaya Mahmoud yaja hannunta suka shige yayi tare da dafa wanda kefaman bushes bushe suna kirari yace


"Malan auren Basmah da Mahmoud, Batool da dr Ahmad zakace ba Bilkisu ba kaji ko?" Kallon kallon suka shiga yima junansu cikin rashin fahimta suna kallonsa kafin suce


"Amma yanzu kuma wata tafito tace ba Basmah ba Bilkisu ce sunan d'ayar amarya"


"A'a itace Basmah amaryar nikuma nine angon ko baku ji yanda aka fad'a wajen d'aurin auren bane" yafad'a tare da shigewarsa...


 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____86💎



    Suna shiga cikin gida yaya Mahmoud ya d'aga hannu kamar zai mareta had'e da nunata da hannun yace


"Meke damunki? Meya kaiki fitowa awannan lokacin?" 


"Ya kyauta naje yimasu, kuma bakaji shiren da sukeyi ba wai Basmah amarya" tak'are maganar tare da turo baki, tsaki yaja sannan yajuya tare da sake juyowa yana kallonta yace


"Ofcouse ba waibane, ke yanzu amarya ce domin dake aka d'aura auren"


"Kaji yaya da wani zance, sai kace shi auren wasar k'asace da za'a tsaroshi da wanda za'ayi daga k'arshe kuma ace amfasa"


"Keep joke aside Basmah, Billy tace bazata auri Mahmoud ba shiyasa dady yace a d'aura auren dake, believe me Basmah ba wasa nakeyi ba, keyanzu matar aurece bai halarta kije wajen waniba har saida izinin mijinki" yafad'a tare da rik'e mata kafad'u ganin yanda take yimasa wani kallo tanaja da baya, 


"Bazai yuyu ba yaya wlh Billy nasonsa, kada kuayarda da zancenta domin nida kaina natabbatar da irin soyayyar da takeyi masa" itama tafad'a tanaja da baya da baya, 


"What ever dai Basmah anriga da angama yanzu kece matarsa" wani irin kuka tafashe dashi don tatabbatar da cewa yayan nata bawasa yakeyiba lura da yanda marok'an tun farko suka shigo auna kiran sunanta amatsayin amarya, toshe baki tayi hawaye na tsiyaya a idanuwanta tace


"No.." Tare da barin wajen aguje, k'ok'arin rik'ota yayi sanin batada cikakkiyar lafiya yaji andafo kafad'arsa, juyowa da zaiyi yaga dady tsaye abayansa fuskarsa ba walwala yace


"Barta, amma wayasa kafad'a mata?, tun d'azu saurin da nakeyi kenan in dawo gida inkirata insanarda ita komai tayanda zata fahimceni, yanzu kaga shikenan inba Allah yaso ba birkice mana zatayi tunda batada isashshiyar lafiya"


"Afuwan dady nakasa controlling kaina saboda yanda abun yazo abazata shiyasa nafad'a mata, farko ma nazata da saninta komai yafaru, amma dady meyasa zakayi haka wlh Billy tana son Mahmud sosai, kawai k'ilan wata 'yar matsalace tafaru tsakaninsu shiyasa fushin zuciya yasa ta aikata haka amma..." Saurin dakatar dashi dady yayi tahanyar d'aga masa hannu kawai sannan yabar wajen, dafe kai Mahmoud yayi tare da cewa


"Meyasa kika aikata haka my sister, tabbas nasan bazakiyi hakaba sai kinada wani babban dalili, ya Allah kazamo mata gata kuma majib'incin al'amurranta, Allah kada kawofantar da ita bisa wannan abu da tayi" hango Mahmud yayi zaune a guiding yayi tagumi babu abunda yake tunawa sai irin rayuwar soyayyar da sukayi awurin tare da yanayin murmushin da take yimasa da dariya idan suna wajen, d'aga kansa yayi sama had'e da cewa


"Qadarallahu wama sha'a fa'ala" sannan yasauko da kansa had'e da furzar da wata iska mai zafi abakinsa idanuwansa na tsiyayar da hawaye, jiyayi ansa hannu anagoge masa k'walla, d'ago idonsa da zaiyi yaga yaya Mahmoud tsaye agabansa shima hawayen tausayin 'yan uwan nasa gaba d'ayansu yakeyi,


"Kayi hak'uri d'an uwana, kuma kada ka k'ullaci my sister arai, wlh natabbata tanada babban dalilin da yasa ta aikata hakan, tana matuk'ar k'aunarka Allah ne yashiryo haka atsakaninku saboda wani dalili nasa da bamu saniba, pls d'an uwana don Allah kayi mata uzuri kuma kayafe mata" yak'are maganar tare da had'e hannuwansa waje d'aya har yana zancen duk'awa agabansa, da sauri Mahmud pilot ya d'agosa had'e da kallonsa sannan ya rungumesa.


"Karka damu d'an uwa duk da naji zafin abunda tayimun hakan baisa narik'eta araiba, ina mai yimata fatar Allah yabata wanda takeso itama kuma yabasa ikon kula da ita kamar yanda nayi buri, sannan yasota fiye da yanda nake sonta"


Lokacin da labari yakai kunnen Ummi cewa bada Billy aka d'aura auren ba fad'uwa tayi asume  saida akayita yayyafa mata ruwa sannan tafarfad'o saboda tsabar yanda hankalinta yatashi, "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, allahumma ajirni fi musibati wa'ahlifni khairan minha" tadinga nanatawa afili sannan taci gaba da cewa "Shikenan Bilkisu burin ki yacika, gaba d'aya wannan kuskuren nawane da nad'auki cewa maganarki da wasa kuma amatsayin mafarki, har kikaje kika aikata wannan babban kuskure batare dana hanaki ba, amma ina rok'on Allah da yasa hakan shiyafi zama alkhairi tsakanin ke dashi" 


Anan wata tazo masu da zancen cewa ai da 'yar uwarta Basmah aka d'aura auren don tsabar munafucci, duk abunda annan momyce ta aikatashi don ganin 'yar tata batada mashinshini shine tasan yawa Billy tsanar d'an uwanta don d'ai ya auri 'yarta, nan dai aka dinga gulmace gulmace da tsogumukka ana zagin mom,


"Alhamdulillah, Allah nagode maka daka sanya cewa alhaji yanada wata 'yar da zata share masa hawaye batare da muntozarta a idanun duniyaba, Basmah Allah yayi maki albarka kuma yazaunar dake lafiya agidan ki yabaki 'ya'yan da zasu yimaki biyayya kamar yanda kika yiwa mahaifinki" sukaji Ummi nafad'a cikin farinciki duk da tanajin wani irin mugun rad'ad'i azuciyarta nafasa auren 'yarta amma saita samu quwwar data iya dannesa saboda sunan Allah data ambata had'e da mik'ewa tsaye tajuyo tana kallon matar data kawo gulmar har 'yan uwanta suka biye mata ana zagin mom tace


"Ke kuma kiji tsoron Allah, kuma kije kinemi gafarar hajiya hussaina don kinyi mata k'azafi kuma Allah zai tambayeki kuma yabi mata hakk'inta" sannan tajuya ga 'yan uwanta da sukayi tsurutsuru da idanuwa suna kallonta cike da mamakin anya ko ita tahaifi Bilkisu da har aureta zaifasu tadalilin makircin kiahiyarta kuma tayi tsaye tana yimaka Allah godiya akan haka tare da musa zagin nasu tace


"Ku 'YAN UWANA NE bai kamata ace kuzaku had'a wutar da zata ruru agidana ba harta tarwatsamun farincikina, kusa tutar babu tacimmin gani cikin damuwar abunda yafaru ga 'yatah sannan ga bak'ar fitina da gaba da bak'in ciki da zai dinga ruruwa acikin zuciyata, nuna mom Jidda tayi sannan taci gaba da cewa ke shedace akan fad'an da kikaji inayi jiya da safe har kikazo kina tambayata nace maki da 'yarki Bilkisu nakeyi kika cemun Allah yasawak'e, to ba'akan komai bane illa akan wannan matsalar Allah shine sheda sai kuma ni da iyayenta maza dana tabbatar sutajewa da wannan maganar suka goya mata baya da kanta tace batason auren nan, idan akayi matashi bazata tab'a samun farinciki agidan saba wanda bansan meye dalilinta na aikata hakanba amma zaku kama kuyita zagin wud'anda basuji suka ganiba akan wannan maganar, gaskiya banji dad'iba kuma kunyi kuskure, nan gaba yakamata kudinga tantance magana kafin kuhau yin sharhi akanta" tana gama fad'ar haka tabar wajen had'e da maimaita hazbunallaha wani'imal wakeel saboda tasamu sauk'in rad'ad'in da zuciyarta keyimata,


Sukuma gaba d'aya nan rake kunya takamasu, jikinsu yayi sanyi tare da fad'in "to Allah kayafe mana"


Yayinda mom dake k'ok'arin shigowa palourn wajen kiran Ummi da dady yakirata awaya yace tayi lokacin daya taso zaizo gida akan suhad'u a parlounsa don fayyace masu abunda kefaruwa, wanda kawai tazone bisa umurninsa badon ranta yasoba, sai gashi tajiyewa kunnuwanta abunda idan wanine yafad'a mata nan take zata k'aryatasa, tayi sauri juyawa da sauri tabar wajen idonta cike da k'walla tare da nadamar abubuwan da tayiwa Ummin abaya jin yanda take k'ok'arin wanketa akan zargin da ake yimata, tabbas yau tayarda Ummi tafita ako ina kuma tad'arata aduk inda za'a shiga, ko kad'an bata tab'a tsammanin cewa kyawawan halayenta sunkai haka ba, yanzune tafahimci dalilin dayasa tayi mata zarra kuma take tsallake duk wani makirci da tuggu da take k'ulla mata saboda kyakkyawar zuciyartane, part d'inta takoma duk jikinta amace sannan tatura Batool taje tafad'o mata sak'on dady, 


Ana hakanne saiga Basmah tashigo aguje tana kuka tashiga d'akinsu tare da fad'awa kan gado, wanda nan take taji zuciyarta nabuga mata da sauri da sauri, bayanta mom tabiyo hankalinta atashe tana fad'in


"Basmah, Basmah lafiya kike kuwa" tare da shigowa d'akin ta d'agota daga kwance da take "Basmah nikuma yafaru haka kike kuka bayan kinsan halin da kike ciki" cikin kuka tace "Nashiga uku mom abunda nake gudu shiya faru, mom wai don me matsaloli ke bibiyar rayuwarmu nida 'yan uwana?"


"Basmah kinsani aduhu, kiyimun bayani mekuma yake faruwa ayanzu"


"Mom an..d'au..ra aurena da wanda k'anwata ke matuk'ar k'auna aranta, taya zan iya rayuwa dashi bayan ita yake so? Innalillahi wa inna'ilaihirrajiun wannan wane irin son kaine nayi haka, naci amanar 'yar uwata da kaina natabbata bazan tab'a yafewa kaina ba"


"Yishiru mana Basmah wai duk wannan bayani ina yanufa ne?"


"Mom and'aura aurena da yaya mah.mu.." ai kafin ta iyar kawai tasome, Billy dake tsaye jikin k'ofar itama tabiyosu lokacin da taga 'yar uwar tata tashigo tana kuka tayi saurin juyawa zatabar wajen saboda tausayinta akan kalaman da taji suna fitowa daga bakinta sai ga dady ya shigo, saurin shigewa d'akin mom tayi har saida yashige d'akin nasu Batool sannan tafita tanufi part d'insu cike da tsarguwar kanta saboda 'yan buki da suka zubomata idanuwa suna kallo wasu har da nunata ana suruttai.


Daidai lokacin da tasumà mom na jijjigata ne dady yashiga d'akin, a firgice ya k'arasa wajen had'e da d'an bubbuga kuncinta yana kiran sunanta wanda anan take yagane cewa suma tayi, tura mom yayi takawo masa ruwa ya yayyafa mata wanda saida tayi kusan minti biyar yana shafa mata ruwa afuska sannan shed'arta tadawo, ahankali tabud'e idanuwanta suka sauka akan fuskar mahaifin nata tayi saurin fad'awa ajikinsa tana kuka.


Shafa kanta yadingayi cikin sigar lallashi yake yimata magana


"Kiyi hak'uri Basmah, nasan ba'a kyauta makiba ganin cewa and'aura maki aure bada sanin kiba kuma da wanda kike tunanin zai zama miji ga 'yar uwarki, amma amatsayina na mahaifinki da kike da hak'k'i akaina nayi hakanne don inada tabbaci akan zakiyi mun biyayya kuma zakibi zab'in da nayi maki don bazan tab'a cutar da keba, Basmah yazanyi daidai lokacin dana tara duniya nace suzo au sheda auren 'ya'yana guda uku idan har aka samu akasin haka alokacin da suka hallara, shin kina tunanin akwai sauran kima da darajata a idanuwan wud'anda nayiwa alk'awarin basu auren 'yata, nakarb'ar maau sadaki da lefe kuma nace nafasa, shin ashe girma da mutuncina basu zube ba a idanuwansu dama duniya? tsoron hakan yasa lokacin da 'yar uwarki tafad'amun cewa bata son aurenta da d'an d'an 'yar uwata bisa wani dalili nata da take ganin kamar na tauye mata hak'k'inta nayi tunanin musanya masa ke da ita, cike da yak'inin cewa bazaki tab'a bani kunya ba ko kuma watsamun k'asa a idanuwa ba, amma idan har kina ganin kema natauye maki hak'k'i shikenan sai inje inrok'esa ya sawwak'e maki tun kafin ranar nadamar yin hakan tazomun" da tuni jikinta yayi sanyi jin kalaman mahaifinta ta d'ago kai had'e da kallonsa har lokacin idonta na hawaye tace


"Dady amma 'yar uwata fa?, nasani tana matuk'ar son yaya Mahmud kamar yanda yake sonta"


"Kenan ke bakya buk'atar kasancewa dashi amatsayin matarsa tunda 'yar uwarki yake so? Shikenan nafahimta, zance ya sawwake maki inyaso zanje insamo masa matar da zata sosa tunda duka 'yan uwansa basa buk'atar kasancewar su atare dashi"


"Ba haka nake nufi ba dady, kawai ina tausayin 'YAN UWANA NE akan halin da zasu shiga saboda yanda suke son junansu, amma dady idan wannan zab'in da kayimun yayi maka zanzauna dashi duk da cewa har inmutu bazan tab'a dena kallon kaina amatsayin wacce ta cutar da 'yar uwarta ba kuma ta ruguza farincikinta"


Jayeta yayi daga jikinsa cikin b'acin rai jin kalaman dake fitowa daga bakinta, da sauri ta sake rungumesa tana kuka tace


"Na amince dady kayi hak'uri kayafe mun idan nab'ata maka amma ina rok'on alfarma akan gada kayi fushi da 'yar uwata kada ka hukunta zuciyarta alokacin da tayi nisa da 'yan uwanta domin hakan zaisa nakasa samun salama da kuma ikon gudanar da ibadar auren da akayimun matuk'ar tana cikin k'unci, dady kayafe mana dukkanin damuwar da muka haifar maka arayuwa domin muyi rayuwa cikin farinciki" ajiyar zuciya dady ya sauke tare da d'agota yana goge mata hawaye yace "nagode Basmah, Allah yayi maki albarka, Allah yasanya alkhairi mai yawa acikin rayuwar aurenki keda 'yar uwarki" "amin dady, 'yar uwarmu fa"


"Hadda ita Basmah" yafad'a tare da mik'ewa tsaye yabar d'akin cikin jindad'i, cewa yayi mom tabiyo bayansa suka nufi part d'insa gab da sushiga saiga Ummi itama tadoso wajen, kallo d'aya dady yayi mata yakauda kansa don shi fushi yakeyi da ita, atunaninsa duk abunda yafaru dasa hannunta aciki, yayinda ita kuma mom tana ganinta taji tayi mata wani irin kwarjini alokaci d'aya kuma kunyarta tarufeta,  


Bayan sun shiga sun zauna sun gaishesa ya amsa ciki ciki sannan yashiga yimasu bayanin duk abunda yafaru da kuma hukunci da yayanke don rufar asirinsu gaba d'aya daga k'arshe kuma yace suje au kimtsawa Basmah ana gama sallar la'asar zasu wucewa sannan ya sallamesu, nan mom tamik'e tabar wajen yayinda tana fita Ummi tazube ak'asa tana basa hak'uri saboda ganin yanda ransa yab'aci amma ko kallon gefen da take beyiba balle ya amsa, hakan yasa tayi masa murnar auren 'ya'yan nasa tare da fatar alkhairi duk da tasan bazai tankata ba sannan tabar wajen zuciyarta a cunkushe, part d'inta takoma tazauna kan gado cikin damuwa tare da zuba tagumi, ganin wannan bazai fiddata cikin yanayin da take cika yasa tashiga toilet tayo arwala, raka'a biyu tayi tanemi Allah yakawo mata sauk'i da d'auki acikin wannan yanayin da take ciki, 


Batool ma da labarin yaje kunnenta gaba d'aya mantawa tayi da cewa ai da kanta tayi yunk'urin neman abunda zai kawowa 'yar uwarta mafita akan soyayyar da takeyiwa d'an uwan nata tashiga rera kuka kamar ba gobe, gaba d'aya duniyar jitake tayi mata zafi duk wani d'okin zuwan wannan ranar da takeyi ya gushe mata, ba abunda ke cikin zuciyarta illa tausayin 'yar uwarta kuma twiny d'inta, iskota tayi d'aki akwance idanuwanta arufe, kwantowa tayi daidai fuskarta had'e da cewa "My twiny meyasa kikayi haka" 


"Saboda Allah yatsaro tun can cewa niba matarsa bace don haka duk yanda muke son juna bazai tab'a zamowa mijina ba" tabata amsa tare da rungumota ajiki, kalamanta susuka kashewa Batool baki wanda takasa cewa komai sai kukan da taci gaba dayi.


Basmah ce tashigo d'akin jikinta narawar sanyi itama takwanta tacen d'ayan gefen Billy fuskarta nakallon tata har lokacin idanuwanta na arufe ahankali cikin rawar baki tace


"Sis..to, meyasa, me yaya Mahmoud yayi maki kika nemi rabuwa dashi, kin manta akoda yaushe kina cemun kina matuk'ar sonsa kuma bakya tsammanin zaki iya rayuwa idan bada shiba?" Hawayene suka zubo mata tace


"Yayya wannan maganar kuskurece nayi kuma shiga hurumin Allah ne nayi domin shi yake da rayuwa, ban rabu dashi wai don haka kurumba amma inada yak'inin cewa bazan iya rayuwar farinciki agidansa ba wanda hakan yasa nayankewa kaina bazan auresa ba, kiyi hak'uri nazamo silar tauye maki farincikin aka d'aura maki aure alokacin da bakya buk'atar hakan, kiyafemun Yayya tah" tak'arasa maganar had'e da rungumeta, sunjima ahaka suna kukan rabuwa da juna cike da maganganun dake nuna rashin jin dad'in faruwar aurenta wanda ko kad'an bata nuna maau cewa tasan zancen matsalar Basmah ba balle tanuna shiyasa tayimata sadaukarwa, ita kuma Basmah tuni tafahimci ta dalilinta tayi hakan amma nuna tasani bayada wani amfani yanzu wanda hakan yasa kukanta da damuwarta suka tsananta, 


Duk wasu shire shire da Ummi tayiwa Bilkisu tasa 'yan uwanta sund'auka sunkaiwa mom amatsayin tata gudun mawar wanda hakan yasake jefa mom cikin kunya da dana sani, sosai jikin Basmah ya rikice mata har saida aka kira dady, yaso abarta har sai taji sauk'i amma Mahmoud pilot yace "A'a shidai abashi matarsa suwuce, kome dare suna isa zai kaita asibiti, saida mom tabata magunanta tasha sannan tamik'awa Mahmoud pilot sauran maganukkan tace lallai yatabbata ana sallar isha'i tashasu, bawani shiri aka yimata ba, dady yasa aka fito da ita lokacin zasu tafi tanata kuka duk wanda ke wurin shima saida yayi hawaye baranma Batool da yaya mahmud, Billy kuwa kasa fitowa tayi saidai tad'age labule window d'akinta tana hangensu, kuka takeyi sosai don Ummi tace dole da ita za'aje takai 'yarta har d'akinta, tayi hakanne don tasamu taba aminiyarta hak'uri saboda tayita kiranta awaya amma tak'i d'agawa, yaya mahmud dady ya aikawa Ummi akan baza'aje da itaba don kada tasa rai, duk da ranta yab'aci dole tahak'ura akaje da matar alhaji kabiru da matar baba k'arami, 


Har za'asa Basmah mota tadinga waiwaye waiwaye tana dibon inda zataga 'yar uwarta amma ina koka d'an bata ganeta awurinba, ture mutanen wurin tadingayi tare da kukkutsawa cikinsu amma babu alamarta, hakan yasa dady yaje yakamo hannunta had'e da cewa


"Basmah ke kad'aifa ake jira marece nayi" kallonsa tayi tace


"Dady banga 'yar uwataba, don Allah kubarni inje ingata" sakin hannunta dady yayi tare da juyawa idonsa na hawaye, itakuma tanufi part d'in Ummi tana tafiya ahankali saboda yanda jikinta bayada k'wari mahmud pilot nabiye da ita abaya, wasu motocinne dady yace sufara fita kafin afito da amaryar wanda jin k'ararsu yasa Billy fitowa aguje don itama tanaso taga tafiyar 'yar uwarta, fitowar da zatayi kawai taci karo dasu tafe, dagudu tak'arasa wajen tare da rungumeta tace


"Ina sonku 'yan uwana kuma zanyi matuk'ar kewarku sosai" horn aka dinga yimasu amma babu alamar zasu saki junansu, mahmud pilot yaja hannun Basmah har yagaji amma tak'i sakin Billy saida yatattaro gaba d'aya k'arfinsa batare da yaji kunyar Billy ba da mutanen da zaibi tawajensu ya d'aukikke Basmah ahannunsa, dagudu Billy takoma d'aki tana kuka shikuma dama da gayya yayi mata hakan yawuce abunsa duk da yanajin kukan nata har cikin tsakiyar zuciyarsa,


Da haka yasakata mota sannan suka sake gaisawa da yaya mahmud da dady suka yimasu Allah ya kiyaye sannan yashiga motar driver yaja suka d'auki hanyar borno da amaryar sa Basmah daketa faman rera kuka.


Suna wucewa yaya mahmud yanufi part d'in Ummi wajen Billy zuciyarsa cunkushe da damuwa... 




Post a Comment

0 Comments