TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 95-96

 _TUNATARWA_:


 *QARYA DA ILLOLIN TA*



_Qarya ita ce tushen laifuka kuma jagoran manyan kaba’irorin da d’an adam ke aikatawa_.



_Qarya ita ke santa mutum yaci amanar d’an uwan sa ko abokin sa_.



_Qarya ita ce tambarin dukkan munafukai domin it ace sinadarin da suke amfani da ita wajen had’a dukkan sharruka da qulle-qullen su_.



_Qarya babu abin da yafi ta saurin zubar da mutunci da qimar mutum da zai aikata_.



_Qarya tana nesanta baewa daga rahamar mahaliccin sa sannan ta kusanta shi zuwa ga gidan azaba_.



_Ya Allah ka kiyaye mu daga yin Qarya ko yin furuci mara tushe, ka nuna mana hanyar gaskiya ka nisanta mu da yin Qarya_.







95 & 96



Washe gari bayan mun yi breakfast ne na je na wanke kayan da muka yi amfani dasu kana na zo na gyara falon.



Bayan na gama ne na koma d’akin na ci gaba da zama na.



Ji nake yi kamar in kira Anisa ko na samu sauk’in damuwar da nake yi.



Kiran da ya shigo ne ya katse min zancen zucin da nake yi.



Ga mamaki na Anisan ce ke kira na.



A raina na ce kamar tasan ita nake tunanin kira.



Da sauri nayi picking d’in call d’in ta.



Bayan mun gaisa ne Anisa ta ce "Fatima ashe abin da ya faru kenan, Allah ya canza miki da mafi alkhairi".



"Amin Anisa" na amsa mata.



Anisa ce taci gaba da cewa "yaya Khalil ya ce min kina gidan yaya Faruk ko? gani nan zuwa".



"Sai kin zo, ki gaishe min da Amatur-Rahman" na fad’a.



"Za ta ji" ta Amsa min kana ta katse wayar.



Ba a fi awa d’aya da rabi ba sai ga Anisa ta zo gidan yaya Faruk d’in.



Maganar ta naji a falo suna gaisawa da yaya Faruk da Nana.



Hakan yasa na fito falon na zauna kusa da Anisan.



D’aukar Amatur-rahaman dake hannun ta nayi na fara mata wasa.



Nana ce ta ce "Fatima sai yanzu muke ganin ki, ina jin da ba ki ji maganar Anisa ba baza ki fito ba".



Murmushi kawai na yi ba tare da na ce komai ba.



A raina nace "yaushe zan fito ba na samun sakewar fuska a gurin yaya Faruk, magana ba had’a ni take yi dashi ba in ba ta kama ba, in ban da gaisuwa ta da yake amsawa in na gaishe shi, sannan ga soyayyar da ya ke yi miki a gaba na wanda dole in haramta ma kaina zaman falon, ni gani na ke yi yaya Faruk kamar ma da gayya yake yin haka a gaba na".



Tashi nayi daga falon na kalli Anisa na ce "In kin gama hirar ki same ni a d’aki".



Ina gama fad’ar haka na wuce d’akin na ci gaba da yi ma Amatur-Rahman wasa.



Jin yarinyar na ke yi har cikin zuciya ta, ba tunanin da ya fad’o min a lokacin shi ne yaushe nima zan ga d’an kaina?



Wannan tunanin da nayi ne yasa hawaye ya tarun min a ido.



Anisa ce ta shigo d’akin da sallama tana kallo na.



Amsa mata sallamar nayi da murmushi a fuska ta.



Kusa dani tazo ta zauna muka sake gaisawa kana na tambaye ta yaya Khalil ta ce yana gaishe ni.



Anisa ce ta ce "Fatima ban ji dad’in abin da ya faru ba, nasan ko wane bawa ba ya guje ma k’addarar sa, kar ki sa abin a rai har ya dinga damun ki, nasan mutuwar aure akwai ciwo, shi destiny ba wanda ya isa ya kauce mishi, fata na Allah ya daidaita ku ki koma d’akin ki".



Murmushin takaici nayi kana na ce "Anisa nasan duk abin da ya same ni k’addara ce, amma wani abin har da laifi na da ban d’auki shawarar ku ba a lokacin da kuke ba ni shawarar, Anisa ke shaida ce a irin son da na nuna ma Dr amma shi bai duba haka ba, sai yayi amfani da wannan damar yake min abin da ya gadama, Anisa kin sha fad’a min illar makauniyar soyayyar da nake nuna ma Dr da irin abin da zai haifar min nan gaba amma sai a lokacin na d’auka kamar a lokacin ba kya son tarayya ta da Dr d’in ne, sai gashi a yanzu na yarda da maganar da kuke fad’a min".



Kuka na fashe dashi mai ratsa zuciyar mai saurare na ci gaba da magana cikin kuka na ce "Anisa wai ni Dr ya saka akan zai k’ara aure, yana fad’a min cewa shi zai yi ma Momin shi biyayya akan auren da take so yayi, har yana goranta min da cewa bai so yayi kuskuren da nayi na k’in bin maganar su Abbu, ina ma naji maganar ku a lokacin da kuke fad’a min gaskiya, Anisa nayi nadamar kuskure nah…" na k’arasa maganar da k’ara sautin kuka na.



Ita ma Anisa hawaye ne ya zubo mata na tausayi na.



Cikin sanyin murya Anisa ta ce "Fatima ki daina kuka, komai da kika ga ya same ki rubutacce ne, dama can Allah ya k’addara cewa Dr mijin ki ne, kuskuren da kika yi Fatima shine rashin bin maganar mutane da suka dinga baki, a lokacin idon ki ya rufe kika nuna ke sai Dr, a lokacin maimakon ki nemi zab’in Allah sai ki ka bi zab’in zuciyar ki".



"Ni ma nayi nadama Anisa, a yanzu na gano cewa zab’in Allah shi yafi ba wai soyayya ba".



Haka Anisa ta ci gaba da kwantar min da hankali.



Yaya Khalil ne ya kira Anisa ya sanar da ita ya zo gidan yana falo, tare muka fito falon da ita.



Samun su muka yi da yaya Faruk da Nana suna hira.



Tun da na shigo falon yaya Khalil ke bi na da kallo.



Gaishe shi nayi nayi ba tare na k’ara cewa komai ba.



Hira aka ci gaba dayi ba tare da na saka baki na ba, duk hirar da suke yi ina sauraron su.



Bai wani jima ba ya musu sallama ya fita.



Anisa ce ta bi shi ta dawo ta sanar dani yaya Khalili na kira na.



A harabar gidan na same shi yana jingine jikin motar shi.



Jiki a sanyaye na k’arasa kusa dashi.

Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kana na kau da shirun da cewa "yaya Khalil ya su Abbu da Ummu".



"suna nan lafiya kau" yaya Khalil ya amsa min.



Yaya Khalil ne ya ce "Fatima ashe abin da ya faru kenan, san da Ummu ta fad’a min sakin da Dr ya miki ba k’aramin tashin hankali na shiga ba, ban ji dad’in abin da ya faru ba, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a tsakanin ku, idan kuma da rabon ki koma sai Allah ya daidaita ku ki koma d’akin ki".



Yaya Khalil ne ya ci gaba da cewa "Amma Fatima me kika mishi ya sake ki?" ya k’arasa maganar yana kallo na.



Sunkuyar da kaina na yi yayin da hawaye ya tarun min a ido na ce "yaya Khalil baa bin da na mishi, kawai dai mun sami misunderstanding da shi ne akan auren da yake son k’arawa wanda a dalilin haka yasa muka rabu".



"Fatima saboda zai k’ara aure ne yasa ki ka d’aga hankalin ki har ta kai kun sami matsala dashi ya sake ki, me yasa ba ki yi hak’uri ba tun da wanda zai aura ba akan ki zai ajiye ta ba, kin san kuma namiji mijin mace hud’u ne, why Sis" cewar yaya Khalil.



"Yaya Khalil ba akan shi kad’ai muka samu matsala ba, Momin shi ce ke son yayi auren, dan na mishi magana shine ya ce min wai zai yi ma Momin shi biyayya, ba zai yi irin mistake d’in da nayi ba da ban ji maganar su Abbu ba…" na k’arasa maganar da fashewa da kuka.



Cikin kukan na ci gaba da cewa "yaya Khalil su Abbu na fushi dani ko? nasan tafiyar nan da za ayi dani Abuja Abbu bai yarda in dawo gida ba ne, yaya Khalil I have ralised my mistake, ina so in nemi yafiyar su Abbu da Ummu, I have learnt a lesson".



Tun da na fara maganar yaya Khalil yake kallo na, da gani yana ji tausayi na ne.



Hannu na ya rik’e yana girgiza min kai.



Jikin shi na fad’a na ci gaba da kukan, bai hana ni yin kukan ba dan yasan a hali da nake ciki a yanzu ina buk’atar yin kukan.



Sai da ya ga nayi shiru ya d’ago ni da ga jikin shi.



Cikin lallashi ya ce "Anisa komi da ya sami bawa rubutacce ne a gurin ubangiji, sai dai kamar yanda kika ce Dr ya ce miki shi zai yi ma Momin shi biyayya ba zai yi mistake d’in da kika yi ba kin ga anan darasi ne babba a gurin ki da ya kamata ki d’auki izinah, Fatima ko da su Abbu suka amince aka yi auren ki da Dr kin san wanda suke so ki aura amma saboda son da ya rufe miki ido yasa ba ki duba hakan ba, akan ki yarda da k’udurin sun a auran yaya Faruk shi yasa Abbu ya sa miki wannan sharad’in amma duk da haka Fatima sai ki ka amince da wannan sharad’in, Fatima ni da yaya Aminu sau nawa muka miki magana akan ki bi abin da su Abbu kike so but you reduce, sau nawa na nuna miki b’acin raina na kuma zaunar dake na miki fad’a akan abin da kike niyyar yi is not wright but still Fatima you did’nt take my advice, yanzu mai gari ya waya tun da shi wanda kika yi domin shi gashi shi yake miki gorin abin da kika yi at the end kuma ya sake  ki sannan kuma zai bi umarnin Momi d’in shi ya auri wacce take so yau aura, kin ga ba ki yi gaining d’in komai ba".



 Cikin shashshek’ar kuka na ce "yaya Faruk I want to see Abbu & Ummu, ina so su yafe min, ba na so su ci gaba da fushi dani, I miss them".



Yaya Khalil ne ya ce "Ki daina kuka Fatima, Abbu da Ummu ba fushi suke yi da ke ba, sai dai a yanzu dole su shiga damuwa jin abin da ya same ki, Fatima ko wani iyaye dole ya shiga damuwa idan aka yi divorcing d’in y’ar shi, Abbu yana cikin b’acin rai ne, nasan idan ya sauka zai ma yaya Faruk magana ya dawo dake, kar ki damu su Abbu za su yafe miki, ki daina sa ma kan ki damuwa Fatima, komai zai wuce, ban ji dad’in ganin ki haka ba, kowa ya kalle ki yasan ki na cikin damuwa, stop worrying your self kin ji my sis".



"Toh yaya Khalil zan kiyaye" na fad’a cikin sanyin murya.



Murmushi yayi yaya Khalil yayi kana ya ce "that is my Sister, so smile for me".



Ban san lokacin da murmushi ya sakar min a fuska ta ba.



Fuskar yaya Khalil ce ta k’ar yalwatuwa da murmushi ganin na yi murmushi.



Kallon wrist watch d’in shi da ke hannun shi yayi kana ya ce min "Fatima zan koma gurin aiki, excuse na nema na fito, ki kira min Anisa sai in sauke ta a gida".



"yaya Khalil ka gaishe min da su Ummu da Abbu da yaya Aminu da su Anty Jidderh" na fad’a a hankali.



"Za su ji" yaya Khalil ya amsa min.


Falon na koma na sanar da Anisa yaya Khalil na jiran ta.



Sallama ta ma su Nana kana muka jera tana ci gaba da kwantar min da hankali.



Sai da na ga sun shiga motar sun fara tafiya na musu waving d’in hannu na, su ma waving d’in su ka min.



Koma wa nayi cikin d’akin ban sake fito wa ba.



Wajen la’asar yaya Faruk ne ya shigo d’aki na.



Yau ma kamar kullum fuskar nan tashi a d’aure take ya tsaya a gefe.



Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin ya kau da shirun da cewa "Fatima za mu koma Abuja yanzu, ina so in ji saki nawa ya miki saboda akwai sakin da in aka yi shi in har ba kin gama iddah ba kina matsayin matar shi ce in dai ya maida ke a lokacin, za mu tafi dake Abuja ne na d’an wani lokaci.



Ji nayi jiki na yayi wani irin sanyi, nasan tun da yaya Faruk ya ce zan bi su Abuja hakan na nufin cewa Abbu bai hak’ura ba da sharad’in da ya sa min, ji na ke yi kamar in ce ma yaya Faruk ba zan bi su ba, ko a nan d’in ma a takure nake saboda rashin sakewar fuskar yaya Faruk da kuma yanda wani lokacin suke gudanar da soyayya su a gaba na ba tare da jin kunya ba, Nana ce ma wani lokacin take nuna jin kunyar ta idan yaya Faruk yayi mata wani abin a gaba na.



Sai dai nasan ba ni da mafita da ta wuce bin su d’in tun da nasan Abbu bai yarda da dawowa na gida ba tun da har na ji yaya Faruk bai fad’a min yadda suka yi da Abbu ba.



Cikin sanyin jiki na ce "Saki d’aya ya min".



"Kin ga kenan kina matsayin matar shi tun da ba ki gama iddah ba in har yace ya dawo dake, ki shirya kayanki".



Yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin.


Jiki a sanyaye na had’a kayana na zauna jiran su.



San da za mu tafi Abujan ne Nana ta shigo ta min magana in fito mu tafi.



Trolik d’ina na d’auka muka shiga mota muka nufi Abujan.


Wajen magrib muka isa Abuja.



Nana ce ta nuna min d’akin da zan zauna.



Ina shiga d’aki na shiga band’aki na watsa ruwa.



Kaya mara sa nauyi na sa ka.



Ban fito d’akin ba sai da Nana ta zo ta min magana in zo mu ci abinci.



Bayan mun gama cin abincin ne na koma d’akin da aka sauke ni.



Ban jima da shiga d’akin ba na ji waya ta tana kuwwa.



Ganin sunan Ummu da na yi ne yasa jiki na ya k’ara sanyi.


Cikin sanyin murya na d’auka kana na gaishe ta.



Amsa min tayi kana ta d’aura da cewa "Fatima kuna Abujan ne".



"Eh Ummu" na amsa mata.



Ummu ce ta ce "Fatima tun san da Faruk ya zo ya fad’a min mummunan labarin abin da ya same ki hankali na ya gaza kwanciya, na so a ce kina kusa dani a yanzu sai dai ba ni da halin yin haka a dalilin zafin da Abbun ku ya d’auka kuma ba kowa ya jawo hakan ba fa ce ke Fatima da kika yarda da sharad’in shi, yanzu ga avin da kika yi ya jawo miki, ke yanzu abin farin cikin ki ne a ce wannan mummunan k’addarar ta same ki amma ba kya gaban iyayen ki, abin da yasa hankali na ya kwanta shi ne nasan Faruk zai kula dake amma duk da haka ina so ki yi taka tsantsan saboda ba ki gama iddah ba, yanzu saki nawa shi Sadik d’in ya miki" Ummu ta k’arasa maganar da tambaya.



"Saki d’aya ya min" na amsa mata.



"Allah yasa hakan shi yafi miki alkhairi, in kuma da rabon ki koma gidan Dr Allah ya daidaita ku, ki kula Fatima, kin ga har yanzu ba ki fita iddar ki ba, yanzu shi Dr d’in yana cewa ya maida ki kin maidu, sannan ki zauna da Nana lafiya nasan ba ta da matsala, insha Allah ba wani dad’e wa za ki yi a Abujan ba, nasan Dadin ku zai mishi magana, yanzu ma dan yana kan k’udurin shi ne shi yasa bai yadda kin dawo gida ba, ki yi hak’uri kin ji Auta".



Wani irin tausayin kaina da na Ummu ne ya kama ni a lokacin.



Nasan Ummu ma na cikin damuwa akan sakin da Dr ya min, a maganar da ta min na fahimci haka.


Ban san lokacin da na fashe da kuka ba.



Ummu ce ta katse ni cikin tashin hankali ta ce "Yanzu mi ye abin kuka daga magana".



Cikin kuka na ce "Ummu ku yi hak’uri ku yafe min, ki neman min yafiya a gurin Abbu akan laifin da na muka a baya".



"Ki daina kuka Fatima, na yafe miki, idan kika dawo Kadunan za mu yi magana, Abbun ki ma zai yafe miki".



Cikin shashshek’ar kuka na ce "Na… gode…Ummu".



"Ki gaida su Khadijan" Ummu na gama fad’ar haka ta katse wayar.



Kuka na naci gaba wanda ni kaina ban san dalilin yin kuka na ba.






Yau muna zaune a falo ni da Nana kasancewar ta je lectures ta dawo da wuri, yaya Faruk na wajen aiki.



Anty Maryam ce ta shigo rik’e da hannun Asim.



Gaisawa muka yi kana na tashi na d’akko mata drinks da snacks na ajiye mata na rik’e hannun Asim muka wuce d’aki na.



Bayan tafiya ta ne su Nana suka ci gaba da hirar su.



A cikin hirar ne Anty Maryam ta ce "Nana bak’uwa kuka yi ne, kin san tun da kuka dawo Kadunan ban samu shigowa ba, san da kuka shigo gurin mu kuma ba ku shigo da ita ba".



"Fatima ce k’anwar yaya Faruk" na amsa mata.



Da sauri Anty Maryam ta ce "Wai wace Fatiman kike magana?".



Nana ce ta ce "Fatima dai da kika sani y’ar uwar yaya Faruk".



"Tare kuka tawo da ita kenan?" Anty Maryam ta sake watso mata tambaya.



"Eh tare muka tawo da ita" Nana ta fad’a.



"Ina fatan lafiya dai kuka tawo da ita" Anty Maryam ta sake tambayar Nana.



Nana ce ta ce "Sun rabu da mijin ta ne, shine yaya Faruk ya ce Dadin shi ya ce ya tawo da ita".



"Kina nufin nan za taci gaba da zama kenan" cewar Anty Maryam.



"yaya Faruk ya ce ba dad’ewa za tayi ba" Nana ta fad’a.



Nana ta ci gaba da cewa cikin marairaicewa "Anty Maryam tun da yaya Faruk ya ce zai tawo da Fatima na rasa peace of mind d’ina duk ya tabbatar min da yanzu ba wata alak’a ta soyayya da zai k’ara shiga tsakanin su da ita amma hankali na gaza kwanciya, nasan in har yaya Faruk suna zama a guri d’aya da Fatima wataran dole ya ji son ta ya dawo mishi a cikin zuciyar shi ya ji yana sha’awar auren ta, Anty Maryam ke kan ki shaida ce a irin son da yaya Faruk ya ma Fatima, nasan har yanzu ba yanda za ayi ya ce ya rabu da son Fatiman a zuciyar shi, sai dai yana dannewa ne dana bin da ta mishi, kin ga in har yaya Faruk ya dawo da Fatima rayuwar shi ban san yanda zan yi ba in hakan ta kasance" ta k’arasa maganar cikin rawar murya.



Anty Maryam tsura matai do tana kallon ta, ganin hawayen da ya tarun ma Nana a ido yasa tai tausayin ta ya kama ta, tasan Nana tana da hak’uri da kau da kai, tun da ta fito tayi magana abin na damun ta ne.



Cikin lallashi Anty Maryam ta ce "ki yi hak’uri Nana kar ki sa damuwa a ranki, nasan dole hankalin ki ya tashi akan tawowa da Fatima da kuka yi, shawarar da zan baki shine kar ki sa ma  zuciyar ki wani tunani daban tsakanin Fatima da Faruk, ina so ki ci gaba da zama da ita Fatiman lafiya, ina so ki yarda da maganar da shi Bregadier ya fad’a miki cewa ba wata alak’a da za ta had’a shi da Fatima, nasan tun da ya fad’a miki wannan maganar to hakan take a ranshi, ki ci gaba da hak’urin da na san ki dashi, kar ki bari shaid’an ya fara sa mi ki wani tunani na daban a ranki, duk abin da kika ga ya samu bawa to rubutacce ne daga wajen ubangiji".



"Na gode Anty Maryam, insha Allah zan yi amfani da shawarar da ki ka ba ni" Nana ta fad’a cikin cool voice d’in ta.



Murmushi Anty Maryam tayi kana ta ce "yawwa Nana, Allah ya k’ara ba ku zaman lafiya da Faruk d’in".



Cikin fara’a ta amsa da "Amin Anty Maryam".



Da haka suka canza hirar da suke yi, sai da Anty Maryam za ta tafi ne sannan Nana ta shigo d’akin da na ke ta amshi Asim a hannu na.



Fitowa nayi muka yi sallama da ita.




Post a Comment

0 Comments