TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 17

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____17💎



 Daidai k'ofar gidansu mom yayi parking motar Batool tafito aguje tana kiran mom, mom dake zaune bisa d'aya daga cikin kujerun dake falon mahaifinta ta d'ora kanta bisa kan kujerar idanuwanta arufe azahiri zaka d'auka bacci takeyi amma idanunta biyu kawai tashiga duniyar tunanin hanyar da zata d'auki fansar wannan zaman da  Ummi tajawo tanayi agidansu, muryar 'yar tata da tajiyo yasata saurin bud'e idanuwanta ahankali tace


"Batool" tare da dubon k'ofar da tajiyo sautin muryar ta, hangota tayi aguje Mahmud na biye da ita hannayensa rik'e da Bassam da Bilal yana dariyar gudun da Batool keyi, tana isowa inda take suka rungume juna tamkar sun dad'e basu had'uba cikin farinciki mom ta d'ago ta tana kallon yanda ta canza, Batool na dariya ta sake rungumeta


"Nice mom, nayi matuk'ar kewarki da yawa" wasu hawayen dad'ine suka zubowa mom tace


"Nima haka 'yatah, ina auntynki ne?" Ganin Bassam yasa bata jira amsar da Batool zata bata ba tasa hannu ta  d'aukesa had'e da cillasa sama tana fad'in


"Oyoyo autana" shafa kansa tayi tana dariya"Auta bakayi missing mom d'inka ba gaskiya, dubi yanda ka canza lallai aunty Basmah tana kula mani daku yanda ya kamata ko Yaya Mahmud zance?"


"A'a mom Ummi ce ba yayya Basmah ba ko Yaya Mahmud?" Yak'arasa maganar yana kallon gefen da suke tsaye shida Bilal, d'ago kan da mom tayi sukayi ido biyu da Bilal dake gefen Mahmud yayi saurin b'uya a bayansa, kallonta Mahmud yayi sannan ya jawo hannun Bilal dake bayansa ya durk'usa daidai tsawonsa tare da d'ora hannuwansa akan kafad'unsa,


"Bilal! kai bazakaje kayiwa mom oyoyo bane?, dubi yanda Bassam yaje yayi mata ta d'aukesa kai baka so ne ta d'aukeka?" kad'a masa kai yayi ahankali yaje saitin kunnensa yace


"Yaya inajin tsorone"


"Karkaji wani tsoro, ka saki jikinki ba abunda zatayi maka saboda haka yimaza kaje kajiko?" juyowar da Bilal yayi yaga yanda mom ke dariya saboda farincikin ganin 'ya'yanta datayi yasa shima sai ya samu courage d'in rugawa ya rungumeta kamar yanda Mahmud ya umurcesa da yayi, yana kaiwa mom tasa hannuwa biyu biyu zata ingijesa cikin tsorata yayi saurin rintse idanuwansa zuciyarsa nabugawa, sai ga papi nafitowa daga bedroom d'insa, mom na ganinsa saita waskewa ta d'aga Bilal sama tana fad'in


"Oyoyo autan dady kana lpy?" zuciyarta na rad'ad'i don bahaka tasoba gudun cin mutuncin da papi zai yimata idan yaga abunda tayi niyar aikatawa yasa tayi hakan, wata irin muguwar harara ta watsawa Mahmud dake dariya har kyawawan hak'oransa na bayyana da sauri ya juyar da kansa gefe had'e da shafa k'eyar kansa yana mai gintse dariyar dake neman sake fito masa da gudu su Batool suka nupi inda papi ya zauna akan kujera suna gaishesa shi kuma Mahmud ya k'araso inda mom yana Sosa k'eyar kansa


"Mom ina wuni" batare data amsa gaisuwar tasa ba tace "ina 'yatah Basmah?" Cikin rashin damuwa akan amsar da zai bata yace "tana kan hanya nan da minti ashirin nasan zata k'araso" zaro idanuwa wajenta awaje tayi sannan tace "kamar ya? Halama ita wa zai kawota ne?"


"Haba mom kowa kinyi masa tarba mai kyau hatta d'an autanmu Bilal yasamu kyakkyawar tarba daga wajenki saini ne zaki tarbeni ta hanyar wud'annan da tambayoyi"


"Ka amsamun abunda natambayeka yanzun nan koka fuskanci fushina"


"Ehh to ita dai zata kawo kanta da k'afafunta don nasan girman kanta bazai barta tahau napep ba" ya k'arasa maganar yana d'an sosa bayan kunnensa, suna had'a idanuwa da mom baisan lokacin da yafara yimata bayanin abunda yafaru ba shine shikuma da ransa ya b'aci yace tafitar masa a mota, 


"What? Kana nufin atiti kabaromun yarinya? Wlh minti biyar nabaka ka koma ka d'aukota" hak'uri yabata sannan ya nufi wajen papi dake rungume da Bilal agefensa na dama yayinda ya tokare sandarsa da hannunsa na hagu, cikin girmamawa tare da tsokana Mahmud ya karb'i sandar tare da ajiyeta gefe yana fad'in


"Yallab'ai yo ai sai ka ajiye wannan sandar tunda kazauna, irin wannan abu haka sai kace tsohon daya fara rud'ewa " saida papi yayi dariya sannan yace


"Uwarka gatacan ita tafara rud'ewar da takasa banbance gaskiya da kuma rud'in zuciya"


Ya k'arasa maganar had'e da nuna mom dake can gefe zaune, don tun ranar da tazo yakira dady yaji abunda yafaru tsakaninsu yake fushi da ita kuma baya shiga alamurranta dashi har hajiya kaka wato mahai fiyarta,


"Allah yabaka hak'uri papi abun baikai haka ba" gaishesa Mahmud yayi tare da tambayar ina hajiya kaka, ai kuwa da sauri papi ya d'ora yatsansa akan baki yana kallonsu Bassam dake wasa suna d'aga murya


"Shiiiiii.....kuyi shiru karku tadamun da masoyiya bacci" kafin yarufe baki Batool da Bilal da suka fahimci tana bedroom d'insa suka rugo aguje shima Bilal yabi bayansu suka shige d'akin suna fad'in


"Hajiya kakaaaa.."


Sandar papi dake gefe ya d'auko yana kwalar Mahmud da ita wai duk shi yaja zasuje sutayar da ita, dariya Mahmud ya kwashe da ita had'e da tashi zaibar wajen papi ya rik'e masa riga 


"Ba inda zakaje sai kafito mani da ja'iran k'annen can naka masu zubi da aku" ba Mahmud kad'ai ba hatta mom dake cika tana batsewa saboda abunda Mahmud yayi saida tayi dariya, aranta tanaji inama ace itama ita kad'ai take ga dadynsu Bassam yayi mata irin son da papi keyiwa hajia kaka ya bata kula kamar yanda papinta ke bawa hajia kaka.  Muryar Basmah ce tafito da ita duniyar tunanin data lula da sauri ta iso inda take tana dudubata.


"Sannu Basmah ashe haka yaron nan yayi maki? Kibarni dashi sai yagane kurensa, injin k'afafunki basa yimaki ciwo" 


Batare da Basmah ta lura da papi dake falon ba tace


"Wallahi Allah mom Yaya mugune, badon Allah yasa inada wani guy dake da motaba nakirasa yazo ya d'aukeni da saidai ink'araso gidannan ak'afa, kinga ma ice cream yabiya dani ta ten 'o seven ya siyamun" ta d'ago ledar tana nunawa mom


 "Allah sarki yaron kirki, dubi yanda yayi maki abunda yayanki ya kasa yimaki, Allah dai yayi masa albarka"


Mom narufe baki taji saukar sandar papi ajikin Basmah jikinsa har cira yakeyi yanata doka mata ita a duk inda yasamu, duk da yake bawani k'arfine da papi ba sosai take jin zafin dukan da yake yimata hakan yasata b'uya a bayan mom da yake idanunsa sunrufe ya had'a harda mom d'in yana dukansu, hakan yasa mom taja Basmah suka bar falon shikuma papi Mahmud yarik'asa ya zaunar dashi akan kujera yana faman nishi d'aya bayan d'aya kamar wanda yayi wani ja aiki, tafa hannuwa Mahmud yashigayi yana fad'in 


"Sannu papi, gud job" da sauri papi ya d'aga sandarsa shima ya doka masa a k'afa har saida yayi d'an tsalle "washh papi ni kuma meye laifina"


"Tirr...... ai wannan duka laifin kane da baka tsawatar mata tunda kaine babba agidan, nasan shi dadyn naka yafiye sanyin hali da yawa ba lallaine taji tsoron saba ita kuma mahaifiyar taku shashashace ko kanta batayiwa fad'aba balle tayiwa 'yarta, kai yakamata ace kasa ido akan k'annenka amma dubi yanda tsabar rashin kunya yanda take fad'ar wani namiji ya d'aukota hadda biyawa wani wajen da ita, ita kuma sakaryar harda wani samasa albarka allah ya tsare bata damu da sanin koshi ya dad'e da samun albarka 'yar tataba"


"A'a papi kadena fad'an haka wlh muna iya k'ok'arin mu Basmah ce tacika rawar...." Sandar papi yasake d'agawa kafin ya iyar da maganar sa da nufin sake doka masa yana fad'in


"Maza fice kabani wuri kafin kalma na nuna maka naka kuskuren"


Aguje Mahmud yanufi wajen hajiya kaka yana dariyar yanda papi baya shakkar dokawa kowa sandarsa, yana shiga ya tarar dasu Batool gaba d'aya akan gadon sun tada ita suna faman yimata surutu amma dayake baccin bai ishetaba sai faman gyan gyad'i takeyi sukuma suna yimata dariya...




Post a Comment

0 Comments