TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 87-101

 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____87💎



 Koda yashiga d'akin ya iskota zaune tahad'a kai da bango tana cigaba da rusar kukanta, maganar gaskiya tanajin zafi da rad'ad'in rabuwa da Mahmoud d'inta amma babu yanda zatayi sai fatan Allah yazaunar dasu lafiya, yajima tsaye abakin k'ofar d'akin yana kallonta kafin ya k'arasa wajen had'e da duk'awa agabanta yasa hannu ya d'ago kanta.


Kallonsa tayi da idanuwanta da sukayi jawur kuma suka kumbura kafin tasake maida kanta cikin cinainanta tana kuka,


Ahankali yafurta cewa "my sister, meyasa kika aikatawa rayuwarki haka bayan kinsan cewa bazaki iya jure rabuwa dashi ba?, duk da bansan ko meyasa kika aikata hakaba amma ni inaga kamar kinyi kuskure, shi so da kike gani sa'ane kuma sannan alkhairine, idan kasamu mai sonka da gaskiya rik'esa kakeyi hannu biyu batare da kaguje masaba sai inbisa ga wani babban dalili!" 'Dago kanta tasakeyi had'e dasa hannuwa tagoge hawayen idanuwanta sannan tace


"Ya zanyi yaya da qaddarar da Allah ya tsaromun arayuwata, ni kaina nasan natabka babban kuskure amma nakanji dad'i idan Natuba cewa zai zamemun alkhairi, mu manta abunda yafaru mu fuskanci rayuwarmu ta gaba"


"Bilkisu naji kuma nayarda da haka amma inaso kidubi girman Allah kifad'amun dalilin dayasa kika aikata haka matuk'ar kinyarda cewa ni d'an uwanki ne, saboda wannan abun da kikayi akwai d'aure kai aciki, haka kurum ace cikin lokaci d'aya kice bazaki auri d'an uwana ba dole sai in akwai wani babban dalili"


"To yaya koma meyefa anriga da angama, to meye amfanin saninsa yanzu? Just pray for Allah yasa hakan shiyafi zama alkhairi" Shiru yayi yana nazarin kalamanta kafin yace


"To tunda kinsan hakane mekuma yasa kika zauna kina kuka?"


"Broth kenan ai kukan is under most but insha Allah da sannu komai zai daidaita" 


"Ok to shikenan idan hakane yanzu kitashi kije ki wanko fuskarki kije wajen 'yar uwarki, kafin zuwa lokacin da za'a kaita, sannan kuma kiyi ready tare za'aje dake wajen d'auko auntynki hope dai zaki iya ko?"


"Gaskiya a'a broth kayi hak'uri ni twiny d'ita zan raka har d'akinta" tana rufe baki saiga Batool tashigo d'akin fuskarta a kumbure saboda kukan da tayi, da sauri Billy tamik'e had'e da rik'o kafad'unta tana fad'in


"Kai.kai..kai fuskar amarya ce ahaka? Tab gaskiya da sake my twiny, yaya ka kirawo hindu kasan akwai cikon makeup d'in da zata yimana yau tagyare mana my twiny kada dr.Ahmad ya tsorata idan ya ganta ahaka" tsaye yayi yana kallonta cike da mamakin yanda take k'ok'arin danne komai aranta kafin yace


"Idan nakirata zaki yarda ayi maki kema"


"Noo..ai no use for that broth, just help and call her pls." tafad'a kamar zatayi kuka.


"Shikenan is ok zan kirata" yafad'a tare da sawa azuciyarsa bazai cigaba da kallonta hakanba har sai yagano dalilin dayasa ta aikata haka don ya wanketa daga fushin da yaga kamar dady nayi da ita, da haka yabar d'akin ita kuma Batool ta rungumeta sosai sannan tace


"Twiny ke tadabance, dukkanmu muna alfahari da samunki a matsayin 'yar uwa, ko kad'an bana haufi akan cewa munfi kowa samun nagartacciyar 'yar uwa tagari, ina sonki twiny, ina matuk'ar sonki"


"Nima haka my twiny, nima bana haufi ko shakka aduk inda nashiga inbugi k'irji ince ku 'YAN UWANA NE da nake matuk'ar alfahari daku, fatana Allah yarik'e mana zumuncin mu har a aljannah"


"Amin ya Allah, amma twiny don Allah meyasa kika fasa auren yaya Mahmoud" Batool tafad'a tana kafeta da idanuwa, dafe goahinta tayi had'e da cewa


"Oh my God, twiny sau nawa zanfad'a maki cewa saboda bazanyi farinciki agidan saba shiyasa" 


"To taya akayi kika san cewa bazakiyi farinciki agidan saba?, Billy bari infad'a maki gaskiya idan kin b'oyemun dalilinki nida yaya Ahmad da yayya to kada wannan kuskuren ya sake jamaki aikata wani kuskuren na sanarda dady da Ummi, wlh duka fushi sukeyi dake kuma kinsan illar haka arayuwarki, ada nayi tsammanin babu wanda yakai yayya taurin kai da kuma zurfin ciki, amma yanzu sai nafahimci cewa ke kinfita, don haka amatsayina na 'yar uwarki nake baki wannan shawarar don wlh koni naji zafin abunda kikayi ballesu dady, duk wani b'oye b'oye yak'are tunda anyi maki yanda kike so, shikuma ya auri wata, so idanma sab'anine yahad'aku har kikayi fushi ko kuma wani abun yayi maki da bai kamataba ranki yab'aci kikaji bazaki iya aurensa ba to kifito fili kifad'a masu don kaucewa saukar fushinsu akanta" goge 'yan k'illen hawayen da suka zubo mata tayi kafin tace


"Twiny nariga nafad'a masu dalilina tun farko, to yanzu mezan koma ince masu, kinsan halin both dady da Ummi idan ransu yab'aci, basa saurarar kowa har sai lokacin da suka huce, amma duk da haka zanje inyita basu hak'uri har zuwa lokacin da suka sauka" dafa kafad'arta Batool tayi had'e da cewa 


"Shikenan, ubangiji Allah yayi mana dukkanin mashiga da mafita ta alkhairi"


"Amin twiny, muje intayaki ki k'arasa kimtsawa"


Kasan cewar za'aje d'auko faraaha da misalin k'arfe bakwai da rabi bayan sallar magrib ita kuma Batool za'a kaita k'arfe tara bayan sallar isha'i yasa ana gama kiran sallar magrib yaya Mahmoud ya iskosu d'aki ita da Billy yace 


"Batool tund'azu nakira Hindu tace tananan tafe tayi maki make-up d'in, har yajuya zai fita kuma yadawo had'e da kallon Billy ya duk'o daidai fuskart yace


"My sister baza kije a d'auko auntynki tare dake ba" b'ata fuska tayi had'e da cewa


"Yaya..." Da sauri yamik'e tare da bud'e hannuwansa yace


"Shikenan sister, nahak'ura tunda dai bakya buk'ata" ganin yafita cikin rashin jin dad'i yasa tayi saurin cewa


"Ok, ok, zanje broth" amma da sharad'in tare zamuje da 'yar uwata, duk da dai ita amarya ce bansani ba kozata iya tafiya, muryar Batool taji tana fad'in "zanje mana amma kada kubarni dady yasani tunda akwai sauran lokaci"


"Yes" yaya mahmud yafad'a cikin jin dad'i da farinciki, agogon hannunsa ya duba bakwai saura minti goma yace 


"To kuyi maza kufito muje don motoci nawaje suna jira, ammafa karku cewa kowa tare mukaje don bazan bari Abokina suganeni ba, ku kad'ai zankai kuma zanjiraku har afito da amarya idan ankaita kuka gaisa da ita sai kuyi sauri kufito indawo daku kafin a ankara" dariya Billy tayi had'e da cewa


"Ikon Allah, ango zaije wajen d'auko amaryarsa tare dashi" naji d'in nidai so nake kununamun cewa ku 'YAN UWANA NE, nasan da Basmah nanan babu buk'atar in tsaya 'yan b'oye b'oye itace agaba wajen nuna cewa inada 'yan uwa, fuskar Billy yaga tad'an sauya tare da duk'ar da kanta tana wasa da yatsunta kafin tace


"So sorry broth" jiyayi duk bai kyauta mataba, hakan yasa yace


"Am sorry u too my sister" sannan yafice daga d'akin cike da nadamar maganar da yayi, 


Yanda suka tsara haka sukayi, koda Hindu tazo wajen yiwa Batool makeup ta isko batanan, kiransa tayi tafad'a masa cewa yayi don Allah tayi hak'uri tad'an jira nan da minti goma zasu dawo, Allah sarki faraaha duk da tana cikin farincikin yau za'akaita d'akinta wajen masoyinta hakan bai hanata zubar da k'wallaba sosai, tayi kuka kamar ranta zai fita tunawa da iyayenta da kuma rabuwa da jaddinta da zatayi wanda dak'yar aka samu aka b'anb'arota ajikinsa, shi kansa saida yayi hawayen yanata kwararo mata addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali agidan ta tare da yiwa iyayenta da suka rasu addu'ar Allah yajik'ansu kuma yayi masu rahama, nan aka fito da ita zuwa cikin motar da za'a d'auketa, da sauri Billy da Batool sukaje suka rik'o gefen kafad'unta suka shigar da ita cikin motar tare da zaunar da ita, rik'e hannuwansu tayi tare da cewa "don Allah kushigo nan kuzauna"


"Lahh rufamana asiri gasu yakumbo nusaiba can nahango sai faman harararmu sukeyi, ai wannan aikin nasune ba namuba" cewa da matan k'annen mahaifinta da sukayi kane kane suna jiran subasu wuri sushiga tare da 'yar "muma ga yaya can yana jiran mu shi yakawomu" suka fad'a had'e da fito da kawunansu daga cikin motar,


Jansu yaya Mahmud yayi dake can gefe ya rakub'e da mota don kada agansa dama gashi akwai d'an duhu a anguwar ba haske sai hasken fitillun motoci da aka kunna. Gidansa yanufa dasu wanda yaji kyau har yagaji ko ina sai k'amshin sabuntar kayan d'aki da fenti ketashi, suna suka fara isa don ita amarya saida aka tsaya biyawa da ita wajen iyayen mijinta, yayinda dama tun ranar dinner mom taganta ta tuna da ranar da tacewa Mahmud bata sonta sai gashi yau ankawo mata ita amatsayin suruka, murmushi tayi had'e da cewa "ikon Allah kenan" acikin zuciyarta, sosai tayi mata nasiha dama ita Ummi da ita akaje d'auko faraaha wanda ana basu amarya sukayi godiya sannan suka koma cikin motocinsu suna jiran gwaggonninta sufito da ita wanda hakanne yasa bata lura dasu Billy awajen ba, nan aka wuce da ita wajensu dady yayi mata hud'uba sosai shima sannan aka d'auketa zuwa gidanta, nanfa kukan faraaha yak'aru tanaji kamar bazata iya rabuwa da Iyayen nata da 'yan uwantaba, ana shiga da ita d'akinta au Billy ne suka fara tarbarta had'e da rungumeta suna cewa


"Welcome to our family aunty faraaha, we wish you happy matrimonial home" har bisa gado suka kaita itako kukan da takeyima yasa tagagara amsa masu, kusan minti biyar auna zaune tare da ita auna rarrashinta tare da gwarza yayan naau akan tayi hak'uri zataji dad'in zama dashi, saboda mutumne mai tausayi da kulawa zai kula da ita yanada ya kamata,


Muryar Ummi suka jiyo data shigo yanzu tana sallalami hango Batool amarya da tayi anan bayan itama anacan ana shire shiren kaita, sai da safe tayiwa mutanen wajen tare da jan hannun Batool tafice da ita daga gidan tana yimata fad'a wai itama so takeyi tab'atawa mahaifinta rai da zata biyewa marasa gudun zuciyar iyayensu batare da ko kallon gefen da Billy take zaune tayi ba,


"Ummi don allah jira 'yar uwata tazo mutafi tare, tare mukazo har da yaya mahmud shima yakawomu yana can cikin mota yana jiranmu, kobi takan suruttanta Ummi batayiba ta turata cikin motar data kawosu tare da cewa faruq abokin yaya mahmud yawuce suje gida, don shi ke driven motar, itako Batool harda kukanta saboda haushin abun da Ummi tayiwa 'yar uwarta


 Murmushin k'arfin hali Billy tayi lokacin da ummi taja Batool suka fita don tasan duk maganganun da tayi da ita take, tare da cewa faraaha


"Aunty saida safe, Allah yabada zaman lafiya" hannunta tarik'e kafin tace 


"Amin sister am so sorry for what happened Allah yasa haka shiyafi zama alkhairi"


"Amin aunty nagode" tafad'a tare da fitowa tanajin wani d'aci aranta saboda abunda Ummi tayi mata, hazbunallahu wani'imal wakeel tadinga nanatawa har ta iso jikin motar yaya mahmud dake tsaye yajingina da ita suna waya da sadeeq da takaicin rashin Basmah yahanasa zuwa wajen d'auko masa amaryarsa, dariya yaya mahmud yayi sannan yace


"What ever dai kayi hak'uri haka Allah yatsaro, amma kasani wlh kaci bashi duk randa kazo gidanmu bazan barka kaganemun amarya taba" tare da kashe wayar yana dariya, yanayin da yaga Billyn yasa da sauri yamatso inda take yace


"My sister lafiya?" K'ak'aro murmushi tayi sannan tace


"Lafiya klw yaya, yau dai gaya can mun kaima amaryarka, Allah yabaku zaman lafiya" sinne kai yayi wai irin yaji kunyarnan had'e da cewa


"Amin my sister ina Batool d'inne?"


"Ummi tawuce da ita" tafad'a tare da bud'e gambun motar tashige, sosai mahmud yaji ransa bai yimasa dad'i ba don yatabbata wani abun tayi daya b'ata mata rai, shiga cikin motar yayi tare da tayarwa suka nufi hanyar zuwa gida yanata bata hak'uri.


Iya kyau Batool yau tayisa duk da simple make up ce Hindu tayi mata, zaune suke ita da Billy dake faman yaba kwalliyar tata lokacin har tara tawuce da minti biyu ana jiran isowar iyayen Mahmud suzo biko, tsayawar motoci suka jiyo wanda hakan ya tabbatar maau da cewa 'yan bikone suka iso, 


Wajen dady aka kaita ummi narik'e da hannunta takasa ta tsare don batason ganin Billy tarab'o wajen ko kad'an, nasiha yayi mata akan tagirmama mahaifiyar mijinta tare da tausaya mata kuma tayiwa mijinta ladabi da biyayya sannan yasa mata albarka tare da fatar samun zuri'a tagari, 


Lokacinda aka kaita wajen mom kasa cewa komai tayi sai "Allah yayi maku albarka gabaki d'ayanku kuma yakareku daga sharrin duk abunk'i" tare da fashewa da kuka, duk da bawata shak'uwace sosai tsakaninta da yarantaba inba d'an lokacinnan da abubuwa suka canzaba taji matuk'ar kewarsu aranta. 


Ganin haka yasa nan take itama Batool tarungumeta had'e da fashewa da wani irin kuka maiban tausayi tana nemanta gafara, Ummi dake tsaye gefe itama hawayenne suka zomata da sauri tafita tabar d'akin, dak'yar aka rabi jikinta da nata yayinda matar alhaji bukar da hajiya kilishi suka rik'ota aka fito da ita Ummi nabiye dasu abaya tana goge hawaye, dama tuni Billy na cikin motar yaya mahmud agaba ana fitowa da ita za'a kaita cikin motar da angonta yaturo a d'auketa da ita yayi saurin bud'e bayan motarsa had'e da cewa


"Gwaggo kushigo nan yayane da k'anwa zasu d'auki 'yar uwarsu da kansu sukaita d'akinta" hakan yasa suka shiga da ita baya, ummi da matar alhaji bukar suka zauna da ita ita kuma hajiya kilishi tanemi wata motar tashiga,


Wajen mamy aka fara shiga da ita, cikin so da k'auna suna shiga mamy tarungumeta tare da zaunar da ita kan kujera tana jero mata addu'a, duk wanda ke wurin saida yayi mamakin irin son da wannan sarakuwar tanunawa surukarta tare da yiwa Batool sambarka, nasiha tayi mata maicike da alamun rarrashi tare da kulawa sannan aka hau da ita sama inda d'akinta yake, duk da gidan ba girma mutane sun matuk'ar yabawa k'ok'arin tsarin da dr. Ahmad yayi tare da kayan da mahaifinta yazuba mata.


Har bisa kan gadonta yaya mahmud da Billy suka kaita tare da rarrashinta kafin suwuce saboda har lokacin kuka takeyi bata daina ba, saida Billy tarad'a mata wata magana akunne sannan tayi shiru, sukayi dariya atare, wata irin muguwar harara ummi tabi billy da ita shikuwa yaya mahmud nagani yaje yajawo hannunta had'e da cewa


"Muje 'yar uwa kafin idon ummi sufad'o k'asa" murmushi ummi tayi jin abunda yafad'a tare da cewa


"Lalle kam daya fimaku, kafin abu yasha maku kai"




 



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____88💎



  Suna fita yace tajirasa a mota, dube dube yafarayi, yana neman inda zai hango su zainab da Amina 'ya'yan baffansu bukar, can ya hangosu suna fitowa daga cikin gidan da sauri yak'arasa wajensu, 


"Yawwa Alhamdulillah, Zainab Amina dama kunake nema tun d'azu, kuzo muje" yafad'a yana kallonsu


"Ina wuni yaya mahmud" suka fad'a tare dayi masa ya gajiyar biki,


"Lafiya klw sister, buki ai ya watse Alhamdulillah, ku muje Billy nacan cikin mota so nake don Allah yau kuje can gida ku kwana" kallon Amina da kanta ke noce tayi saboda ita haka Allah yayita da muguwar kunya, bazaka tab'a cewa ga ranar data had'a idanuwa dakai ba duk k'wak'warka tace


"Yaya amma bumu fad'awa su baba zamu kwanaba, yanzu haka baba k'arami nacan yana jiran mudawo yakaimu gida"


"Karku damu zan fad'a masu kunji ko?" Wucewa yayi gaba sukabi bayansa har zuwa inda motarsa take Billy na zaune duk abun duniya yadameta,


Bud'e masu gambun motar nabaya yayi suka shiga sannan ya zagaya ta gidan driver yazauna had'e da tada motar,  wayarsa yaciro daga gaban aljihu tare da yin scrolling agefen contacts d'insa ya kira lambar baba k'arami, bugu d'aya ana biyu ya d'auka, cikin girmamawa ya gaishesa sannan yace


"Baffa dama su Zainab ne nad'auko daga gidan Batool, gamunan tare dasu da Bilkisu, shine nace bari nakiraka in sanar dakai idan ka amince zan wuce dasu can gida sai su kwana wajen Bilkisu"


"Af to ai shikenan ba komai k'ara daka kira kasanar dani gani tund'azu zaune ak'ofar gida sun barni ina faman  jiransu, to ni bari in wuce saida safe ko?"


"To baffa nagode, Allah yatsare hanya kuma yatashemu lafiya" 


"Amin ya Allah" baffa yafad'a tare da kashe wayar


A saman starring mota ya ajiye wayarsa had'e da d'an k'ara gudun motarsa yana fad'in 


"Zainab shikenan ko?"


"Eh" tafad'a tana murmushi


Yana isa yasamu abokanan sa duk na tsaye a k'ofar gida suna jiransa yadawo sukaishi wajen amaryarsa, yanayin parking yafito ya gaggaisa dasu sannan yace sud'an jirasa, bayan Billy yabi tare da tsaida ita yadinga bata hak'uri akan dole duk abunda Ummi tayimata tahak'ura dashi tunda ita tab'ata mata rai kuma kada tasa damuwar hakan aranta har wani ciwo yakamata. 


Murmushi tayi masa had'e da cewa "in sha Allah broth" har zai wucewa tace


"Yaya!" Tsayawa yayi ta rungumesa tana fad'in zanyi kewarku sosai 'yan uwana" ta matuk'ar bashi tausayi sosai ganin yanda suke tare sai gashi yau sun rabu da juna, gaba d'ayansu kowane na gidansa sunbarta ita kad'ai agida tabbas wannan alamarin daya faru jarabtawace maigirma agaresu domin kamar hakane duk soyayyar da suke yiwa junansu watarana zasu mutu subar wasu daga cikinsu duniya araye.


Sakinsa tayi tace "saida safe" sannan tawuce idanuwanta nafidda k'walla.



 Ab'angaren su Basmah kuwa tafiyace sukeyi mai tsananin cinrai saboda bak'aramin nisa bane tsakanin kaduna da borno tun tana kuka yana lallashinta har yagaji yasa mata ido tayi mai isarta, da haka bacci ya soma d'aukarta har kanta na bugun glass d'in gambun motar, kasancewar dagashi sai itane abayan motar yasa yasake matsawa can jikin d'ayan gambun motar had'e da kai hannu yarik'o kafad'unta ya kwantar da kanta ajikin cinyarsa shi kuma yayi baya da jikinsa ya jingina a jikin kujerar da yake zaune, ahankali ya rufe idanuwansa yayinda tunanin Billynsa da irin soyayyar da suka nunawa junansu yafara ziyarto k'wak'walwarsa, wani irin k'unci da rad'ad'i suka taso masa a zuciya, hawaye masu zafi suka dinga kwaranya a fuskarsa, ahankali yafurta "why Billy?.. Meyasa kika yimun haka?" 


Jin abunda yace yas basmah kuwa da tuni tafarka daga baccin daya d'auketa saboda hawayensa da suka d'igomata a fuska, tayi saurin sake runtse idanuwanta tana fad'a aranta cewa "Kayafemun yaya duk laifina ne yajanyo haka" har suka isa garin borno misalin k'arfe 10:30pm nadare babu wanda yakoma cewa komai, gaba d'aya kowanensu da abunda yake kitsawa cikin ransa da kuma zuciyarsa dan gane da auren nasu, wanda za'a kira da auren qaddara ko kuma auren d'ibar fushi, kai tsaye yaya Mahmud pilot yacewa wanda ketuk'asu ya wuce dasu asibiti, yayinda yakira dadynsa yace su zasu iya wucewa gida shizai tsaya asibiti aduba 'yar uwarsa.


"To shikenan my son Allah ya sawak'e, sai kun iso" gaba d'aya alhajinsa yaba sauran motocin umurni suwuce can gida kai tsaye kafin su iso, don shima binsu zaiyi zuwa asibitin, 


A wata 'yar madaidaiciyar asibiti da aka rubutawa _HAIFA SPECIALIST HOSPITAL_ wacce take mallakin garince a k'ark'ashin gwamnatin jahar suka shiga motar dady na biye dasu abaya, sunayin parking yad'an bubbuga gefen fuskarta kad'an da yake tuni takoma baccin nata dake cike da damuwa, ahankali tabud'e idanuwanta sannan tamik'e daga ka cinyarsa da take kwance cike da jin kunya,


"Sorry yaya nagajiyar dakai ko?" Tafad'a kanta ak'asa, 


"Bakomai" yafad'a had'e da bud'e gambun motar yafito ya zagaya tabaya ya bud'e mata gambun gefenta had'e da mik'a mata hannu, kallon ginin wajen tafarayi d'aya bayan d'aya saboda yanda taga tsarin irn na asibitotane yasa tab'ata fuska kamar zatayi kuka,


"Fito mana" taji yana fad'a tare da sake mik'o mata hannunsa, hannunta tamik'a masa yarik'o sannan tafiddo da k'afafuwanta daga cikin motar da suka d'an kumburo saboda yanayin zaman da tasha, ahankali take takawa yana rik'e da hannunta, rufe gambun motar yayi sannan suka shiga daga ciki, nan take suka samu tarba tamusamman daga wajen nurses d'in dake wajen tare da tanadar masu inda zasu zauna kafin agama had'a folder d'inta a sadasu da babban likitan da zai dubata.



Suna zaune kiran Ummansa yashigo awayarsa, agajiye ya d'aga wayar had'e da cewa


"Hello ummanah"


"My son kun iso kuwa?"  hannu yasa yana d'an mummurza goshinsa a hankali kafin yace


"Afuwan Ummanah, mantawa nayi ban kirakiba nasanar dake, bamu dad'e da isowa ba, halan bak'inku basu iso ba" muryar mutanen da yajiyo acan cikin wayar suna sallama yatabbatar masa da yanzu suka isa. Cikin farinciki Umma dake amsa sallamarsu tace


"Alhamdulillah gasunan sun iso yanzu kai kana ina danaji kace bak'ina basu iso ba?"


"Ina nan asibiti nida dady za'a duba Basmah don koda muka taso batada lafiya"


"Allah sarki ai dole yarinya tayi ciwo ace cikin rana d'aya and'aura mata aure bada sanin taba kuma aurenma da wanda k'anwarta zata aura"


"Umma mubar wannan zance koma meye Allah yakyauta, ana gama dubata zamu iso gida insha Allah"


"To shikenan Allah yak'ara mana lafiya, ka gaisheta" 


"zataji in sha Allahyafad'a had'e da kashe wayar yana kallon fuskarta data jingina kanta idanuwanta arufe, gaba d'aya ta canza daga Basmahr da yasani takumbure saboda kukan da tayi"


Sosai tabashi tausayi don yasan biyayya kawai tayi ta auresa badon yana zab'in rantaba, hannunta yakamo yarik'e yana mai rayawa azuciyarsa cewa duk daba ita yake soba kuma babu k'aunarta aransa yayi alk'awarin zai bata kulawa tare da sauke duka hak'k'ok'anta dasuka rataya akansa amatsayinta na k'anwarsa kuma 'yar uwarsa.


Bayan kamar minti biyar aka kira sunanta ya rik'ata suka shiga cikin office d'in tayiwa dr bayanin yanda takeji da abunda ke damunta wanda anan take yafahimci matsalarta, magunguna ya rubuta mata yace tasha na tsawon sati d'aya amma gobe tadawo akwai gwaje gwajen da za'ayi mata don yafahimci kamar akwai matsala, godiya Mahmoud pilot da dadynsa suka yimasa sannan suka nufi hanyar gida, 


Cikin so da k'auna family d'insu Mahmoud suka tarbeta, soyayyar da har saida tabata mamaki, hawaye suka zubo mata a idanuwa tunawa da batasan ko wane hali 'yar uwarta Billy da itace yakamata ace ta tsinci kanta cikin wannan ahali mai matuk'ar karamci da soyaya take cikiba.


Jawota Umma tayi ajikinta tana fad'in "'yar gidan dady kisaki jikinki mana, meye abun takura kanki keda gidansu gaki ga Ummanki keyi" kallon Mahmoud tayi daya zube kan kujera saboda tsananin gajiyar da yayi tace


"Son sannu da hanya ko?, ya jikin Basmah d'in injin da sauk'i"


"Eh Umma amma doctor yace gobe mukoma akwai wasu 'yan gwaje gwaje da za'ayi mata" yafad'a had'e da tashi zaune yana kallon mom data wani sanya Basmah ajikinta, imagining yayi inama ace Billyn sace da tuni shima yaje ya nanik'eta, murmushi yayi yana murza tafunan hannunsa kafin yace 


"Umma bari inje in watso ruwa, inajin gajiya sosai"


"Ai kuwa gajiya dole son, kaje kafito zuwa lokacin itama tad'an watso sai kuci abinci tasha magani ko? tafad'a had'e dasa hannu ta d'ago fuskar Basmah, dakanta tarik'a Basmah takaita cikin d'akinta sannan tashiga toilet tahad'o mata ruwan wanka masu zafi tace ta shiga tawatso,


'Dakin alhaji tashiga kafin tafito tayi masa sannu da zuwa, sannan shima tahad'o masa ruwan wanka, bayan yafito yana kimtsawa tace


"Alhaji dama nace ko zakayi magana da yaronnanne yabar Basmah hannunmu har nan da kwana biyu idan tasamu sauk'i naga har yanzu kamar tanajin jiki, kasan halin yaran zamani ba'a iya masu kada inyi masa magana yaga kamar wani abun ko yak'iyamun amma idan kaine kayi masa magana natabbata zai barta"


"A'a hajiya wannan ba huruminmu bane, shiya ke da iko da matarsa don haka don Allah ki kauda idanuwanki akansu kibashi matarsa sutafi" yafad'a yana zura doguwar jalabiyarsa ajiki, 


Haka kuwa akayi misalin k'arfe sha d'aya da rabi bayan sun kammala cin abinci duk da kad'an Basmah ta tsakura, alhaji da Umma suka d'auketa cikin mota da kansu suka kaita har cikin gidanta tare da yimata addu'ar Allah yazaunar dasu lafiya kuma yabasu zuria mai albarka sannan suka fito suka koma gida, daidai lokacin sukaci karo da mahmud yafito yana kullikke d'akinsa dake nan cikin gidan alhaji yakirawosa had'e da cewa "Son kayi maza kaje gidanka iyalin ka nacan munbaro ita kad'ai, ubangiji Allah ya albarkaceku"


"Amin alhaji" yafad'a tare dayi masu saida safe sannan yad'auko motarsa yabar gidan, wajen masu kaji ya tsaya yasai k'waya biyu tare da gorar fresh lemon da gorar swan water sannan yak'arasa gidansa,


Saida ya kukkulle ko ina bakinsa d'auke da addu'a sannan yashigo cikin d'akin tana kwance ya ajiye ledojin akan bedside, wardrobe ya bud'e yaciro sallaya ya shimfid'a tare da cewa


"Basmah kije kiyo arwala kinji ko?" Ahankali tabud'e baki tace inada arwala, rik'ata yayi ta tashi sukayi sallah raka'a biyu sau biyu sannan ya sallame, addu'o'i yayi masu sosai masu tsayi tare da rok'on Allah yabasu ikon sauke hakkokan juna dake tsakaninsu, bayan sun kammala yajawo ledojin yabud'e naman tare da tura mata agabanta yace taci, girgiza masa kai tayi alamun tak'oshi yace


"A'a Basmah kada kihad'a yunwa da k'arya waje d'aya don naga kocan bawani abinci kika ciba, kinsha maganinki ko?"


"Eh Umma tabani nasha"


"Yawwa kici wannan ko kad'anne kinji ko? Yaya baya son kafuwa" tare da d'ebo naman yakai mata abakinta, dole haka tadaure tadinga ci yana bata har saida takauda kanta sannan yamik'a mata gorar fresh lemon d'in tasha kad'an, gorar ruwa ya sake bata takarb'a suma takurb'a 'yan kad'an abakinta sannan ta ajiya. Kan gado takoma takwanta shikuma yakwashe sauran naman da lemunan yakai kitchen sannan yashiga toilet yayo arwala, yana fitowa yaja mata bargo ya lullub'eta sannan shima yahau gadon ya kwanta yana karanto addu'o'in bacci dana neman tsari daga shed'anun aljannu, saboda yanda yagaji kafin kaceme tuni bacci ya d'aukesa yayinda ita kuma inbanda tunanin 'yar uwarta tana hawaye babu abunda takeyi, tashi tayi taje tad'auko wayarta cikin jikkarta tahannu takoma parlour takira Billy dake zaune tana fira dasu Zainab, bugu uku tayi ba'a d'agaba saiga na hud'u sannan Billy talura da wayarta dake haake  tad'aga had'e da cewa


"Hello Yayya lafiya bakiyi bacci ba" murmushi Basmah tayi kafin tace


"Taya zan iya bacci bayan k'anwarta batayi ba"


"Laa fira nakeyi dasu Zainab da Amina gamunan atare, ya gajiyar tafiya kun isa lafiya"


"Lafiya klw sisto"


"Masha Allah, ya k'arfin jiki? Gaskiya yayya akwai gajiya kije ki kwanta dare nayi nima yanzu zamu kwanta kinji?"


"Bilkisu" Basmah tafad'a cikin rawar murya, Billy dake sauraronta taji gabanta yafad'i don a iya tarihin rayuwarta bazata iya cewa ga ranar da ta tab'ajin takira sunanta kai tsayeba sai yau, ahankali tafurta "Na'am yayya lafiya?" had'e da mik'ewa itama tabar inda take zaune ita dasu Zainab takoma can palour wajen dining area tazauna.


"Kiyi hak'uri 'yar uwa bisa rushe farin cikinki da nasa kikayi don kisakani cikin farinciki, Nashiga damuwa sosai akan hakan da kika aikata, naji kunya dana kasa zamowa nice wacce zanyi sadaukarwar da kikayimun akaina, narasa gane wane irin sonkai nayi wajen tauye zuciyarki bacin nasan cewa tawa batada wani dogon amfani da zatayi aduniya, don Allah kiyafemun 'yar uwata ina matuk'ar jin zafin haka araina"


"Mekike fad'a haka 'yar uwa nifa..."


"Shiiii...kidena b'oye mun haka 'yar uwata, natabbata cewa ranar duk kinji abunda kefaruwa, kuma nasan cewa kinga tissues masu jini dana manta nabasu ad'akin Ummi shiyasa kika aikata haka, nayi dana sanin faruwar haka don nazamo silar rushe farincikinki" Billy dake murmushi hawaye nafitar mata a idanuwa tace


"Shikenan yayya tunda kinriga kin san komai, ni nayi hakanne don bazan iya juriyar rasaki akan abunda nasan cewa idan nabar maki zaki iya cigaba da rayuwa ba, wlh ko kad'an tun farko bansan da soyayyar da kike yiwa yaya ba daban so shiba har nasakashi azuciyata ba, amma ko yanzu alhamdulillah tunda kin mallakesa amatsayin miji da ace sai bayan na auresa ne nasan da haka da bazan tab'a yafewa kaina ba, kimanta da komai yayya kuma kibar wannan magana atsakaninmu in sha Allah komai zai dai daita kedai kiyi farin ciki kinji ko 'yar uwatah" Shiru Basmah tayi tana mamakin yanda k'anwarta ta iya jure son yaya Mahmoud haka azuciyata har take da k'arfin halin iya furta irin wud'annan kalaman, amma ita takasa jurewa haka har tayi saken daya illatata kafin tace


"Dukkanin farincikin da ni'imar Allah sutabbata agareki, hak'ik'a kinyi abunda bakowa ke iyayinsaba aduniya, madallah da samun 'yar uwa irinki, ina rok'on Allah daya yalwata akhairansa agareki kuma ya haskaka maki dukkanin al'amurranki, kitayani addu'a kada Allah ya amshi rayuwata har sai nayi maki abunda zai sakaki farinciki har iya k'arshen rayuwarki"


"Karki damu yayya, saida safe ngd sosai" billy tafad'a tare da kashe wayar, zama tayi wajen na tsawon minti biyar tana tunane tunane aranta kafin tamik'e takoma d'akinta, inda ta tarar harsu Zainab sunyi bacci, 


Ita kuwa Basmah tana gama waya da ita saiga kiran Batool yashigo, cikin sanyin murya ta d'aga tace "hello Batool"


"Na'am yayya ina wuni?, ya jiki?, kun isa lafiya"


"Lafiya klw sister, jiki Alhamdulillah da sauk'i"


"Masha Allah dama tun d'azu nake son nakiraki to bansamu time ba sai yanzu da aka watse"


"Ayya 'yar uwa to inashi dr.ne da kika iya bud'e baki haka ba kunya kina waya?" 


"Yaje yarakki abokansa , shinefa nace bari inkiraki inji ya jikinki?"


"To naji sauk'i, kije ki kwanta saida safe kinji ko"


"To yayya ina kewarki sosai"


"Nima haka my sister" sannan takashe had'e da rungume wayar tana hawaye har bacci b'arawo yayi nasarar saceta.


Lambar Billy tayi k'ok'arin kira sai gashi tajiyo takun step d'in dr. Ahmad yana hawowa sama, da sauri ta maida wayar a jikkar dake gefenta sannan taja mayafi tarufe fuskarta, saida yayi kusan minti biyar tsaye abakin k'ofa yana kallonta sannan yak'araso ciki bakinsa d'auke da sallama, kan gadon ya hau tare da yaye mayafin daya rufe mata fuska yana fad'in


"Tsarki da dukkanin yabi sutabbata ga Allah daya mallaka mani fatimatah amatsayin matata, batare da k'arfina ko kuma dubarata ba, arrzik'ina ko kuma kyawona, ya Allah ina godiya akan haka"


Murmushi tayi kanta na duk'e ak'asa had'e da cewa


"Alhamdulillah Allah daka fiddani tamusamman acikin 'yan uwana mata kuma ka azurtani da samun miji wanda shima yake na musamman acikin dukkanin fad'in mazajen dake duniya, Allah nagode maka kuma ina alfahari da hakan da kamun acikin rayuwata" cike da farincikin jin dad'in kalamanta yasa hannu ya tallabo hab'arta yana kallon fuskarta yace 


"Fatima nine yafi dacewa nayi irin wannan godiya ga Allah kafin ke amma saboda yanda ubangijina ya suranta mani ke yasa daga kallo d'aya danayi maki na manta da wannan, ina sonki fatima so mai tsanani kitayani addu'a Allah yabani ikon kiyaye dukkanin hak'k'ok'anki akaina kuma yabamu ikon zaunawa lafiya da farantawa juna"


"Ka kwantar da hankalinka mijina in sha Allah zanyi maka biyayya iya k'arfina, kuma nayita alk'awarin zan faranta ranka tamkar yanda farin wata ke haska duniya amaren sha biyar gawata, zan kula dakai tamkar yanda uwa ke kula da d'anta sannan zan kasance mabiyi maka hidima fiye da yanda bawa keyiwa uban gidansa, fatana ka kasance mai afuwa, rangwame, yafuwa da kuma yimani uzuri aduk lokacin da nayi maka kuskure kona sab'a maka" murmushi yayi yana maijin sanyin kalamanta acikin zuciyarsa kafin yace


"In sha Allahu zaki sameni ayanda kike so koma fiye da haka, kitashi muyo arwala mu mik'a godiyarmu ga Allah daya cika mana burin ganin wannan ranar da muka dad'e muna fatar zuwanta"


Ba musu tajuyo tare da sauko da k'afafuwanta daga kan gadon ya mik'a mata hannu tarik'o had'e da sau kowa, mayafin dake kanta yacire mata sannan suka shiga toilet d'in atare sukayo arwala, suna fitowa ya shimfid'a masu sallaya suka gabatar da sallah raka'a biyu tare da yiwa Allah godiya daya nuna masu wannan rana, suna idarwa ya d'auko ledojin da abokanansa suka shigo masa dasu yabud'e leda yaciro gasashahen naman rago da yasha had'i mai kyau tare da k'atuwar gorar yoghurt, a hankali yafara ciyar da ita itama tana cidashi har suka k'oshi sannan yaje ya d'auko cup k'waya d'aya ya tsiyaya yoghurt d'in yabata tasha sosai har saida takusa shanye cikin cup d'in sannan tajaye kanta shi kuma ya shanye sauran daya rage, d'aukar sauran yayi ya saka a fridge sannan yashiga toilet ita kuma takoma kan gado takwanta abunta, kasancewar akwai gajiya atare da ita yasa kafin yafito tuni bacci yasoma d'aukarta, yana fitowa yad'an feshe jikinsa da turare sannan yahau gadon had'e da kashe fitilar d'akin, tanaji yanda yake k'ok'arin rage mata kayan dake jikinta amma duk da tsoron dake tare da ita haka takasa hanasa, cikin sigar rarrashi da kuma lallab'awa yaci nasarar maida Batool d'insa cikakkiyar macce, sosai ya jinjinawa Batool irin k'ok'ari da k'arfin hali da kuma juriyar da take dashi, wanda hakan bak'aramin k'aramai sonta da k'aunarta yayi ba azuciya, yanajin yanda taki fidda nishi ahankali tana hawaye dake nuna irin rad'ad'in da takeji, cikin dubara ya lallab'ata ya kimtsa mata jikinta sannan suka watso ruwa suka koma abunsu suka kwanta, jawota yayi ajiki ya rungumeta sosai yace


"Alhamdulillah, fatima ina sonki ina k'aunarki sosai, ubangiji Allah yayi maki albarka Allah ya d'aga daranarki tun anan duniya har izuwa aljannah" ahankali tafurta "amin" 


"Kinsan me?" Tura kanta tayi acikin k'irjinsa batare da tace komai ba tana shak'ar k'amshin sabulun da sukayo wanka dashi mai matuk'ar k'amshin gaske, janyota ya sakeyi ajikinsa tare da yimata kiss a goshinta yana 'yar dariya mai sauti kafin yace


"Ana cewa sai idan miji ya d'agewa matarsa tafin k'afarsa sannan zata shiga aljannah, to ni ba tafin k'afata kad'ai nad'age makiba har da k'afar tawa da duka gangar jikina, ina mai rok'on Allah da yabaki aljannah da rahamarsa, nagode nagode maki sosai da kika faranta zuciyata da baki d'aya duka raina, nanma "amin" kad'ai ta iya amsa masa dashi, haka yadinga yimata addu'o'i kala kala har saida yaji bacci ya d'auketa sannan yagyara mata kwanciyarta ajikinsa yaja masu bargo.


Kusan motoci biyar suka isa k'ofar gidan yaya mahmud duka abokanan sane aciki da suka rakosa, suna isowa k'ofar shiga gidan ya dakatar dasu tare da karb'ar ledar dake hannunsu yace 


"To friends gudnigth don gaskiya babu wanda zai shigarmun gida ya kallemun kwalliyar amarya, ko banzama namakara kuma idan kuka shiga sake b'ata mani lokaci saboda haka you guzs da bakwada aure saida safe, don Allah yafidda Mahmud acikinku"


Gaba d'aya dariya sukayi had'e da rik'e baki kafin suce 


"Dakyau ango, ai indai amaryace muna zaune zamu ganta kuma watarana zata koro mana kai musake jonewa, kawai jeka malam munyi maka uzuri" da haka suka cigaba da dariya had'e da mimmik'a masa hannu sukayi sallama suka wuce sannan yarufe gidansa, 


Wata irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya shigo palourn, kai tsaye ya wuce bedroom d'in daya tabbatar tana ciki, yana shiga yasameta kwance ta lullub'e fuskarta don tagaji da jiransa har bacci ya soma d'aukarta, ledojin dake hannunsa ya ajiye kan bedside tare da hawa kan gadon rungumota tabaya, saboda bataji lokacin daya shigoba yasa ta tashi fasa ihu da sauri yasa bakinsa acikin nata ya toshe, ganin shine yasa tayi saurin jaye bakinta tare da juya masa baya alamun tayi fushi, aikuwa yaya Mahmoud saida yayi da gaske sannan yasamu ya shawo kanta, hardasu  rik'e kunnuwa wajen ban hak'uri sannan ta hak'ura, sun ciyar da juna cikin so da k'auna kafinnansu gabatar da duk abubuwan da musulunci ya tanada a tsabtace kuma a ilmance. 


Tsayawa fad'ar irin farincikin da wud'annan ma'aurata suka shiga a wannan daren b'ata lokacine domin sun ahayar da juna zumar da bazasu tab'a mantawa ba, albarka kuwa ranar faraaha tashata babu adadi, 


Wanda hakan yasa faraaha tayiwa Allah godiya sosai daya bata ikon kai mutuncinta agidan mijinta har yayi alfahari da hakan tare da sanya mata albarka....



_KUYIMUN AFUWA JINA SHIRU DA KUKAYI, BANAJIN DA'DINE, AMMA YANZU ALHAMDULILLAH NASAMU SAUKI, *LUV U ALL FILLAH💋❤*_





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎


  

Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Kai Alhamdulillah gaskiya masoyi dad'i garesa, nagode sosai da kulawarku agareni my fan's, hak'ik'a dukkanin addu'o'inku sun iso agareni kuma sunyi matuk'ar tasiri akaina domin Alhamdulillah nasamu sauk'i fiye da tsammaninku, godiya agareku mai yawa wud'anda suka kirani awaya da wud'anda suka turo mun text messages da masu biyoni private kai dama wud'anda suka turo addu'o'insu ta group tare da yimani ya jiki duka nagode sosai Allah yabar tare🤝🏻, you guzs are always made proud💃🏼💃🏼 thanks and jaxakumullahu bikhair👏🏻_



💎Page_____89💎


   Tunda sassafe mom ta tashi tahad'a breakfast d'inta mai rai da lafiya sannan tashiga toilet tawatso ruwa, shiryawa tayi cikin wata atamfarta mai golden doguwar riga d'unkin buba, rigar tayi matuk'ar yimata kyau sosai, sannan tawuce kitchen tad'oko wanda tashirya cikin wani madaidaicin kwando tanufo part d'in Ummi dashi, har zata shiga sai kuma taji wata irin kunya takamata, tunda take rayuwarta bata tab'a zuwa part d'in Ummi inbanda ranar da dady ya aikota, kuma koshi bata shiga ba abakin k'ofa tatsaya saboda maganganun da taji sunayi, koda kuwa rashin lafiyane Ummin keyi ko ita ko 'ya'yanta daidai da rana d'aya bata tab'a zuwa lek'osuba balle taje gaiaheta, amma shine yau saboda tana buk'atar taimakon wanda zata aika gidan d'anta shine hadda wani bugo uban sakko haka, girgiza kai tayi tare da juyawa zata koma don gaskiya kunya bazata barta ta iya zuwa ba, ji tayi Bilal da har ya shiryo cikin shirin kayansa na islamiya zaije wajen Bassam zasuje tahfiz yarik'o hannunta had'e da cewa


"Laah mom, kawo in rik'a maki kwandon, yeee Ummi, Ummi, fito ga mom tazo part d'inmu," ya k'arasa maganar yana tsalle had'e da k'ok'arin karb'ar kwandon saboda jin dad'i, yau yaga abunda bai tab'a gani ba koda wasa a gidan, 


K'ok'arin rufe masa baki tayi had'e da jansa zasu wuce saiga ummi tafito itama taci adonta cikin wani lace mai k'yalli riga da sket, cike da mamaki tace


"Am Bilal lafiya kake k'wallamun kira haka?, kai da waye atare da kai" cike da farinciki yafara k'ok'arin jawo hannun mom yana so tajuyo don tuni yasamu fuskar da yafara sabawa da ita kuma tana kulawa dashi tamkar yanda take yiwa bassam shiyasa yasamu k'arfin halin yimata haka 


"Ummi zo kiba mom yaya Bassam ce tazo kuma zata koma" yafad'a yana k'arasowa wajen rik'e da hannunta ita kuma tana biye dashi kanta duk'e ak'asa har suka iso wajen da Ummi ketsaye sake da baki kamar ruwa yacita tsabar mamaki, 


Ahankali Ummi tace


"Bilal cikata mana haka akacema anayiwa manya idan safiya tawaye"


Da sauri ya sake hannun mom tare da noce kansa k'asa "yace mom good morning" sannan yabar wajen aguje yana tsallen jin dad'i da farinciki wai yau mom ce a part d'insu, 


Cikin wata iriyar kunya da mom tarasa yanda zatayi da ita tace


"Yaya ina kwana?" Tsabar mamaki saida ummi taji wani irin jiri ya soma d'ibarta don atarihin rayuwarta in aka cire ranar da taje ganinta bazata iya tuna waau ranakun da magana ta tab'a had'ata da mom ba balle gaisuwa har takirata da yaya, Allah dai yasa lafiya, dakewa tayi kafin can tace


"La.fi.ya klw momyn yara, injin dai lafiya ko? bawani abun yaron nan yaje yayi maki ba, nasan halin Bilal da raahin ji sosai"


Girgiza kai mom tayi had'e da cewa "ko zan iya shigowa ciki?" Wannan karon kam ummi danne mamakinta tayi had'e da cewa


"Why not, Bisimillah" tare da bata hili tawuce tamkar kwai yafashe mata aciki, kwandon data baro can ajiye Ummi ta d'auko had'e da shigowa dashi ta ajiye a can saman floor d'in dining area sannan tadawo paloun ta zauna akan kujerar dake passing d'in wadda mom tazauna, nan dai kowanensu yayi shiru zuciyarsa nasak'a masa abubuwa, fitowar Billy dasu Zainab ce takatse shirun saboda gaishesu da sukayi, wanda su Zainab kad'ai Ummi ta amsawa amma banda Billy mom kad'ai ta amsa mata sannan suka fice zuwa part d'in dady don su gaishesa idanuwanta cike da k'walla. duk abunda kefaruwa tsakanin Billy da iyayen nata mom nalure dashi tun jiya kuma tasan duka akan abunda tayine wanda mom najin cewa tayine don 'yar uwarta amma saboda rashin hujjar da zata iya fuskantar iyayen nata da ita yasa tazuba ido tana jira tagani ko zata iya samun wani abun da zai tabbatar mata da zarginta sannan taje ta warware matsalar da kanta, 


Bayan sunfita, mom takalli Ummi had'e da cewa


"Bansan ta ina zanfarawa da baki hak'uri bisa abubuwan da suka faru abaya tsakanina dake, amma ina so kidubi girman Allah da manzonsa yaya kiyafemun, nafahimci cewa ni kad'aice ke haukata akanki na ganinan cewa kota kowane hali saina cusgunawa rayuwarki, na b'ata maki rai kuma na cutar dake keda yaranki amma ke ba haka kike rik'e dani azuciya ba, wanda ayanzu ne nagano cewa matuk'ar ban rok'eki yafiya ba bisa wud'annan abubuwa dana yimaki ba hakkinki bazai tab'a bari in gama da duniya lafiya ba, ada babu sunan dana tsana kamar naki, ina matuk'ar jin haushinki keda yaranki amma ayanzu Allah shine sheda nabi d'i duk wud'annan abubuwan narasa azuciyata saboda kad'ai kyakkyawar zuciya da halacci da kike dasu, wanda ada son kaina da sharrin zuciya dana shaid'an suka hanani fahimtar haka, hak'ik'a nagano cewa ke alkhairice atare dani kuma kece hasken wannan gida, nagano hakanne saboda irin hak'urinki da juriya da kuma kauda kai uwa ubama maida alkhairi da cutarwar da aka yimaki" mom dake zaune kan kujera idanuwanta cike da k'walla tana faman mummurza tafin  hannayenta waje d'aya ta d'ago kai tana kallon Ummi da duk jikinta yayi sanyi sannan taci gaba da cewa


"Wlh yaya nayi nadama don Allah kiyafemun, kuma kiyarda dani don na dad'e dayin tubar da babu kome acikinta, zan so ki amince dani kibani dama cikin sauran tafiyar damuke da ita tsakanin nida ke idan rayuwa tabarmu inyi k'ok'arin kamanta kyautata maki tare da gyara halayyata koda so d'ayane, watak'il zan samu ingoge mikin dana dad'e ina yimaki acikin zuciya koda kashi d'aya ne acikin d'ari, don inada tabbaci akan cewa ubangiji ya d'aukaki akaina tunda kika kasance cikin bayinsa masu hak'uri" 


Tasowa Ummi tayi had'e da dawowa kusa ga kujerar da take zaune tarik'o hannuwan mom tare da cewa


"Daga yau babu wani zargi tsakanina dake nayafe maki dukkanin abunda kika yimun, ina rok'on shima ubangiji daya yafe maki gaba d'aya laifukanki damu baki d'aya" nan mom tasake cika da al'ajabin wace irin rayuwa ce Ummi keda ita, ace ta shekara kusan ashirin da wani abu tana cutar da ita amma cikin mintuna da basu fiye biyar ba gaba d'aya tayafe mata, gaskiya tayi kuskure tare da tabka asarar moruwar rayuwa farinciki acikin wud'annan shekarun da suka gabata,


Rungume Ummi tayi tana hawaye tare da cewa


"Nagode Ummin yara, ubangiji Allah ya jik'an iyaye kuma ya gafarta masu, ayau nasake tabbatar da maganar papi dake cewa ke baiwar Allah ce kuma kinfini ilimi da hankali, nida kaina yau nayarda cewa ke tadabance kuma ba hankali da ilimi kad'ai kika finiba gaba d'aya kinfini komai" wani irin farincikine yaratsa zuciyar Ummi tare da yiwa Allah godiya daya nuna mata wannan ranar da zataci d'ibar hak'urin da tayi sannan cikin zolaya tana dariya tace


"Kenan kinyarda har awajen alhajinki nafiki" tayi hakanne saboda tana son ta auna abunda mom kefad'a shin har acikin zuciyar tane don tasanta da mugun kishi n da zai iya tayarda da nadamarta akoda yaushe, ai kuwa abunda yabata mamaki shine yanda taji mom tace


"Nayarda mana tunda ke rabba'atul bait d'in sace, nikuma mom d'in yara kad'ai" dariya sukayi atare don kowace ta wanke zuciyarta daga abunda takeji ga 'yar uwarta kafin can Ummi tace


"Kiyi hak'uri 'yar uwa nima kiyafemun don baza arasa abubuwan dana yimaki ba, wud'anda suka b'ata maki rai, kimanta da duk wani abun muyafi juna sannan mufara tsara gina rayuwar da zamuyi anan gaba cikin yiwa juna uzuri bisa kuskure idan anyi had'e da kauda kai don farantawa maigidanmu"


Murmushi mom tayi itama tarik'e hannun Ummi tana dariya tace 


"Insha Allah komai yawuce rabba'atul bait, zan biyo bayanki in d'auki darussa don mu faranta zuciyar mijinmu kona samu nima yakirani da koda miftahul qalbin sace" nan suka sake sa dariya tamkar babu abunda yatab'a faruwa tsakaninsu abun gwanin ban sha'awa, kallon kwan don da mom tazo dashi Ummi tayi cikin tsokana irin tasu ta manya tace


"A'a Momyn yara meye kika tanadarwa 'yata haka acikin basket, lallai da alama kinaji da 'yar nan tawa babu batun sarakuta dama haka yaran zamani keso" iya kunya mom tajita don bakin rai girkine tahad'a akaiwa su yaya Mahmud, mik'ewa tayi da sauri tanufi inda basket d'in yake ajiye tana fad'in


"Ai kuwa dama taimakone nayi amma nafasa, indai surakace dama batawa bace takice don haka kararma nafasayi kiji da abukki ke kad'ai nikam nawa nazuwa idan bassami na da Bilal sun girma" had'e da d'aukar basket d'in tabar palourn Ummi nayi mata dariya.


A b'angaren Basmah kuwa koda aka kira sallar asuba mahmud yatashi bai gantaba mik'ewa yayi had'e da bud'e toilet yana tunanin kozai hanta amma ga mamakinsa sai yaga bata ciki, palour ya wuce kai tsaye ya hangota a k'asan tile's d'in kwance tana bacci, da sauri ya k'arasa wajen yana bubbuga k'afarta yana kiran sunanta "Basmah, Basmah" bud'e idanuwanta tayi ahankali suka sauka akan nasa sannan tasake rufewa, 


"Oh my God Basmah, meyake dawo dake nan har kika kwanta a sanyin tile's bacin kinsan bakida cikakkiyar lafiya" yafad'a tare da tayar da ita zaune, ganin yanda baccin yayi mata nauyi yasa ya d'auketa cak bai ajiyeta ko inaba sai cikin toilet, fanfo ya kunan had'e da taro ruwan a hannunsa ya watsa mata afuska, nan da nan tasaki wata 'yar k'ara tare da sakin ajiyar zuciya tana goge fuskar tata da hannu, tsaki tad'anji tagefen baki yace


"Kibud'e idanuwanki mana kiyi arwala yanzu za'a tada sallah masallaci" yana gama fad'a yafara arwalarsa yana gamawa yabata waje itama tayi sannan suka fito atare, 


"Kifara yin raka'atanil fijir kafin atayar da sallah ni zan wuce masallaci" yafad'a yana k'ok'arin saka babbar rigarsa dake ajiye acan gefen bedside, seda yatabbatar ta tada sallar sannan yafice zuwa masallacin, 


Bai dawo gidanba saida rana tafito yabiya tacan gidansu ya gaida iyayensa tare da karb'o masu abun karyawa sannan yadawo gidan, koda yadawo ya iskota kwance ta k'udundune kanta cikin zanen gadon dake shimfid'e akan gadon, girgiza kai yayi tare da zuwa yafara yaye zanen yana fad'in 


"Wai dama ke trouble maker ce Basmah, komai naki yasha banban dana mutane, don Allah dube yanda kikabi duk kika nad'id'iye kanki cikin zanen gado, agaskiya in hakane kina wahalda Batool sosai ita dake kwana dake" yanayin daya gatane ya tayar masa da hankali domin gaba d'aya bata motsi kamar babu rai ajikinta, cikin rud'ewa yadinga kiran sunanta, makullan motarsa ya d'auka tare da d'aukarta ya kaita cikin mota, saida yaje yabud'e gate sannan yazo yafiddo motar tare da komawa yarufo k'ofar gidan had'e da gate d'in, aguje yaja motar zuwa asibitin da suka yada zango jiya da suka iso, suna zuwa emergency nurses d'in dake ward d'in suka rugo tare da d'an gadon da ake tura marasa lafiya suka kama masa aka shiga ita, cikin sa'a kuwa suka samu dr daya dubata jiya bai wuce ba, nan take yakarb'i case d'inta suka shiga bata taimakon gaggawa, sun matuk'ar aha wahala kafin su samu suceto rayuwarta, 


Kamar yanda likita yayiwa Basmah bayanin halin da take ciki haka shima wannan likitan yayiwa Mahmoud pilot bayanin halinda take ciki, kuma yatabbatar masa da cewa ahalin yanzu matuk'ar wata damuwa mai girma tasake gittawa rayuwarta to tabbas za'a iya rasa rayuwarta don ko yanzu Allah yanufa tanada kwana gaba amma koshi d'in bazatayi walwala ba yanda yakamata kamar yanda sauran mutane keyi saboda raunin da jijiyoyin  zuciyarta sukayi gaba d'aya wajen halbawa sassan jikinta jini yanda yakamata, don haka dolene akiyaye shan maganinta akan lokaci duk wani abu da zaisa agajiyar da ita har ya haifar da bugun zuciyarta da sauri da sauri kada abari tayisa ko kuma zama cikin damuwa, dolene abata kulawa yanda yakamata don gudun kada hakan tasake faruwa, 


Ba Mahmoud ba hatta alhajinsa da Umma saida suka tausaya mata tare da zubar mata da k'walla, tabbas Mahmud da Umma sunsan da wannan ciwon nata amma basu tab'a tsammanin yayi mata tsauri hakan ba,


Satinta d'aya kwance a asibiti kafin tasamu lafiya sosai, Umma namatuk'ar kulawa da ita yanda yakamata tamkar mahaifiyarta hakama Mahmud ya maye mata gurbin yaya Mahmud d'inta, don kuwa yana iya k'ok'arinsa amatsayinsa na mijinta wajen nuna mata kulawa da duk abunda yakamata batare da nuna gazawar saba, amma kowane lfitar lumfashinsa mak'ale yake da soyayyar Billy acikin zuciyarta, ganin ba'a dad'e da gama hidimar bikiba yasa mahaifinsa yace tunda dama ansan batada lafiya to kada asanar dasu kwanciyarta asibiti har sai anga yada jikin nata yayi su kuma wud'anda suka kawota dama tunda asussubar fari suka d'auki hanya saboda su isa dawuri shiyasa basusan da cewa ranar aka kwantar da ita asibiti, haka kuma bawanda yasan tana asibiti acan wajensu dady iyaka dai insun kira wani lokacin ace tana bacci wani lokacin kuma takan d'anyi k'ok'arin yin magana dasu, ranar da taji sauk'i sosai aka sallamesu suka dawo gida, wayarta tad'auka had'e da komawa can bayan kitchen lokacin Mahmud yaje wajen sallar azahar, lambar mom takira bugu d'aya ta d'auka, bayan sun gaisa tace 


"Mom ina 'yar uwata Billy take ina fatar dai tana lafiya kuma cikin walwala"


"Sosai kuwa Basmah babu abunda kedamunta, yanzu nida umminku muna cikin zaman lafiya da k'aunar juna, babu wata damuwa ko tashin hankali atsakaninmu, wlh Basmah sai yanzu nakeji kunyar abubuwan da nayiwa baiwar Allah nan da wud'anda nasa kuka tayi mata, Umminku macece mai sauk'in kai da kuma kyakkyawar zuciya, wlh dana yarda namutu da hakkinta da bansan makomata ba" murmushi Basmah tayi don ita dama tadad'e da sanin hakan kafin tace


"Mom itafa 'yar uwata dana tambayeki? Kinata fad'ar kyakkyawar zuciya irin ta mahaifiyarta amma kinkasa fahimtar ita wace iriyar zuciya ce da ita har kina fad'in babu abunda kedamunta, tabbas ummi macece tagari don ita tasauyawa 'ya'yanki rayuwa alokacin da suka nemi lalacewa kuma ta canza wannan rayuwar taki da zuciyarki dake cike da tsantsar tsana ta sauya da cikakkiyar soyayya, mom har ila yau dai bisa taimakon tarbiyar da tabawa 'yarta ne yasa 'yarki keci gaba da rayuwa agidan wanda takeso kuma take k'auna" jingina wa Basmah tayi ajikin k'ofar kitchen d'in tana goge hawayen da suka mik'a mata fuska taci gaba da cewa


"Mom kifad'amun shin Billy nacikin farinciki kuwa bayan ta sadaukar mani da soyayyarta da masoyinta don d'ai kawai ta ceto rayuwata, abunda ni nakasayi amatsayina na yayarta" rufe baki mom tayi don yanzune ta tabbatar da abunda take zargi azuciyarta kafin tace


"Gaskiya nake fad'a maki Basmah, babu abunda kedamun 'yar uwarki saboda tanada matuk'ar juriya da hak'uri, abu d'ayane nafuskanta shine har yanzu dadynku da umminku fushi sukeyi da ita akan abunda ta aikata kuma takasa zuwa tafad'a masu gaskiya, amma shikenan nida kaina zanje infad'a masu saboda su fahimceta kuma suyi mata adalci" 


"Don Allah mom kigaggauta yin hakan don fiddota cikin wannan damuwar, natabbata bazata tab'a iya bud'e baki tafad'i cewa saboda ina son yaya Mahmoud tahak'ura da auren saba, ina matuk'ar bak'in cikin da Billy tasan cewa ciwon da nake fama dashi ta silar soyayyar da nake yiwa yaya Mahmoud ce har yakai gata aikatawa rayuwarsu haka, tarusawa kansu farinciki donta ceto rayuwata, taraba kanta da masoyinta gudun kada narasa rayuwata, tafuskanci fushin iyaye had'e da damuwa duk don inyi farinciki, mom kifad'amun wannan wace irin 'yar uwace nake da ita da take sona fiye da yanda take son kanta, shin ashe batayo gadon kyakkyawar zuciyaba fiye data umminta? Da'ace haka 'yan uwa kenunawa 'yan uwansu soyayya da kuma k'auna aduniya da baza'a tab'a samun lalacewar zumunci ba, shin kinsan maganar Billy akoda yaushe idan za'afad'i wani abu akanmu tun tana k'arama? Cike da so yayyarmu take furtawa kowaye cewa su 'YAN UWANA NE!, don haka mom kije ki daidaita abubuwa ko kuma nida kaina zan kirasu infad'a masu komai akan cewa su yafewa 'yar uwata domin batada laifi"


"Shikenan Basmah hakan zanyi don shikad'aine zai wanke Bilkisu a idanuwan iyayenta" mom nahawaye takashe wayar kafin itama Basmah tajuyo zata dawowa cikin palourn kawai taci karo da Mahmoud...






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____90💎



 Da sauri Mahmud ya saita kansa daga rud'ewar da yayi ta sanadiyar jin maganganun da yaji Basmah nayi awaya yace


Basmah dama kina anan? nadawo inata faman kira ban jikiba, keda waye abayan yak'arasa maganar had'e da lek'awa ta bayan kitchen d'in, irin yanzu yazo baisan tana wurinba, juyowa yayi had'e da kallonta yana d'an turo idanuwansa awaje ganin tana k'ok'arin goge hawayen da suka zubo mata a idanuwa yace


"Basmah kuka kikeyi?shiyasa kikazo nan kika b'uya don kar ingani?" 


Girgiza masa kai tare da rugawa da gudu tabar wajen, don gaba d'aya jitake shikenan yaji komai duk wani mutuncinta da kimarta da yake gani zasu zube tunda yagano itace silar rabuwarsa da wacce yake matuk'ar k'auna fiye da komai aduniya, bayanta yabi yana kiran sunanta saboda tsoron abunda likita yafad'a masa akanta, bisa gado ya isketa tanaci gaba da kukan yayi tsaye yana kallonta cike da tausayi duk da ransa cewa yakeyi    Basmah bake yakamata kiyi kuka ba, nine wanda yakamata na koka, kokad'an banajin soyayyarki araina amma k'arfin jinin 'yan uwantaka bazai bani damar nuna maki hakaba, keda Billy duka 'YAN UWANA NE amma Allah shine sheda itace mafi soyuwa araina akanki, duk wani tanadin rayuwata da ita natsarashi amma dole narungumi qaddarata tunda ke Allah yazab'amun, soyayyar da kikayimun har tajefaki cikin wannan halin itace zata tirsasa zuciyata yimaki adalci tare da danne duk abunda nakeji akan 'yar uwarki saboda kisamu farinciki, kuma tukuicin soyayyarki agareni shine bazan tab'a nuna maki cewa nasan tadalilin kine aurena yafasu da farincikin zuciyata, Ina son Billy sosai kuma bazan tab'a iya dena son taba balle har na iya cireta azuciyata badon haka ba da kema na sama maki gurbi aciki kodon narama maki soyayyar da kike yimun.


Ahankali yafara takowa zuwa inda take kwance abakin gado ya duk'a bisa guiwowinsa saiti fuskarta had'e da cewa


"Don Allah Basmah kidena kukan nan, meyasa amatsayina na d'an uwanki baza kiyi hak'uri da tsarin da Allah yayi atsakaninmu ba kizauna dani? nasani cewa no bazab'inki bane biyayya kikayiwa iyayenmu amma tunda hakane ai sai kiyi hak'uri kidena damuwa da kuma wannan kukan haka kinsan abunda likita yafad'a maki koso kike kirasa ranki don bakya sona"


Shiru tayi tana sauraren kalamansa wud'anda kenuni da gaba d'aya baisan halin da ake ciki ba, gaba d'aya a tsammaninsa tana kuka da damuwane don an aura matashi bata sonsa, kenan baiji wayar da takeyi d'azu ba? tana wannan tunanin taji yace 


"Basmah dake nake magana amma kika k'yaleni" shiru tayi har lokacin don batasan mema zata cemasa ba, mik'ewa yayi had'e da cewa


"Shikenan Basmah tunda bazaki denaba zanje insanar da umma idan so kikeyi na sawwk'e maki to zan rungumi k'addara na sawwak'e maki don amatsayinki na 'yar uwara bazan zauna inzuba idanuwa Ina tare dake har ki ollata kanki kikai ga rasa rayuwarki baccin nasan cewa zan iya hana faruwar haka tunda aurena ne bakya buk'ata.


Da sauri ta d'ago kanta had'e da mik'e tsaye tana goge hawayenta tace


"A'a yaya kada kayi haka, zan zauna dakai mana kawai Ina tunanin.." sanin abunda zata fad'a yasa yayi saurin juyowa ya rungumeta don baya buk'atar jin haka, mutuwar tsaye Basmah takusayi had'e da rufe idanuwanta ta bud'e, shin wai mafarkine takeyi ko kuwa, yau itace ajikin yayanta wanda take matuk'ar so da k'auna itace jikinta ke gugan jikin masoyinta da bata tab'a mafalkin zata mallakesa ba, ahankali tarufe idanuwanta hawaye nazubo mata takwantar da kanta bisa kafad'arsa tare da tura hannuwanta tabayansa itama ta rungumesa cikin zuciyarata tana cewa alhamdulilah ya Allah ko yau namutu nasan banida asarar dakon soyayyar da nayi, shikuwa da nan take yaji wata irin kunya da k'aunar Billynsa sun cika zuciya yayi saurin sakinta had'e da rik'o kafad'unta ya zauar da ita akan gadon ya durk'usa agabanta tare da cewa  


"Pls Basmah don Allah kidena shiga damuwa, ni d'an uwankine kuma mijinki zan kula dake iya k'arfina, zan baki farinciki iya gwargwado kuma zan sauke maki dukkanin hak'k'ok'anki dake kaina, kiyi hak'uri muyi rayuwar aurenmu da Allah ya tsaro mana batare da sanin junanmu ba kodon mubarranta daga wajen ubangijinmu"


Girgiza masa kanta tayi dake sunkuye ak'asa alamun eh taji, hannunsa yasa akan hab'ar bakinta ya d'ago fuskarta yana kallon manya manyan idanuwanta da farinsu yad'an sauya zuwa ja kad'an ga hawaye duk sun jik'e mata lashes d'insu sannan yace


"Kin tabbata?" Nanma kai ta sake kad'a masa, hannu ya mik'a mata yace "promise me" Saida takalli k'wayar idanuwansa ya sakar mata murmushi sannan itama ta d'ago hannunta ahankali ta d'ora akan nasa tace "in sha Allah"


Kiss yayi mata a hannun had'e da cewa "yawwa koke fa, Allah yayi maki albarka"


"Amin yaya" tafad'a tana k'ok'arin jaye hannun ya rik'e yana kallon fuskarata tare da cewa


"Baza'a taimaka ayiwa yayan nan dariya ba ko kad'anne" murmushi tayi ya lakuto hancinta tare mik'ewa tsaye Yana fad'in 


"Yawwa 'yar gaban goshin mom kokefa, bari naje gida ummah tace naje nakarb'o maki sak'o, nikam gaba d'aya naga ummah tadwna kulani sai ke, Allah yasa ba kwacemun ita zakiyi ba" yak'arasa maganar cike da tsokana yana shagwab'e fuska, dariyar da saidahak'oranta auka bayyana yabata had'e dasa tamik'e tashige toilet tanajin wani sabon sauyin yanayi atare da ita.


Mom nagama waya tanufi part d'in Ummi, tana shiga Ummi na zaune tagama had'in doughnut tana fidda shape d'insa, gaisheta tayi had'e da zaunawa takarb'i abun tana tayata fitarwa ita kuma tana ciro mata had'in tana aza mata, sun jima ahaka kafin can Ummi ta kalli yanayin da mom keciki tace


"mom Bassam lafiya kuwa?" 


"Me kika gani halan yaya?" Mom tafad'a tanaci gaba da abunda takeyi


"Nagaki kamar yanda nasaba ganinki ba" 


"Eh yaya babu komai"


"Anya kuwa"


"Eh mana, kawai gaskiya bana jin dad'in yanda kike yiwa Bilkisu ne!" Murmushi Ummi tayi had'e da jaye tray d'in da mom tagama a'aza shape d'in data fitar na doughnut tana fad'in,


"Mtss indai akan wannan ne kidena damar da kanki, taya za'ayi yaro yayi badaidai ba kuma asa mashi idanuwa, yanzu abunda tayi kid'auka ita kad'ai mahaifinta yake da ita, shikenan ta tozartashi kenan a idanuwan d'inbin mutanen daya taro, kuma shikenan sai akasa nuna mata tayi kuskure, shin kinga haka yakamata?"


"A'a yaya ba haka nake nufiba, ina so kifahimta cewa fushin da kikeyi da ita yin hakan kuskurene, duk da sanin tsakanin d'a da mahaifi sai Allah ina tsammanin tunda abunnan yafaru baki tab'a bata fuskar da zata fuskanceki tayi maki bayanin dalilin aikata haka ba ko kuma ke kitambayeta?"


"Hmmm! mom Bassam kenan yarinyar nan kibarta kawai, babu wani dalili da take dashi in bacin rashin mutunci, ita da kantafa ta iya dubin k'wayar idanuwana tafad'amun cewa wai bata son aurennan, saboda ko anyisa bazata samu farinciki ba, haba momynsu kijifa!, yanzu don Allah wannan wace irin hujja zata bani da har zan gamsu da ita? Ai gaba d'aya ma tagama raina ni wlh"


"Assha Ummansu, ai Bilkisu ita takeda hujja da kuma dalilin abunda ta aikata" mom tafad'a tare da rik'awa ummi gyara wajen da sukayi aikin tanaci gaba da cewa


"Kiyarda dani yaya, ko kad'an Bilkisu batada laifi, garin taimakon 'yar uwarta dake neman rasa rayuwarta tayi wannan kuskuren, wanda rashin tsayawa tayi maku bayani shi kad'ine inda tayi laifi, ranar da aka dawo dinner ciwon Basmah yatashi inda ina d'aki Batool taje takirani aguje tana kuka wai ga Basmah can jini nayi mata tsiyaya ahanci...." Bayani mom tadinga yiwa ummi dalla dalla akan abunda yafaru ranar tundaga farko har k'arshe bata b'oye mata komai ba hatta maganar da yaya mahmud da Batool suka fad'a mata akan soyayyar da Basmah keyiwa Mahmud pilot saida tafad'a mata, wanda daga k'arshe tace "kiyi tunani yaya idan har keda kike mahaifiya ga Bilkisu kina tunanin yafewa wacce tacutar dake na tsawo shekara kusan ashirin da wani abu cikin lokaci d'aya taya za'ayi Bilkisu da take jininin kuma tarbiyarki takasa samun zuciyar da zata iya sadaukar da wani abu ga 'yar uwarta da suke matuk'ar son juna, gaba d'aya wannan abun data aikata koyarwarki ce wacce ni dana gaza yiwa 'yata ita gashi raunin data samu yana nema ya kaita ga rasa rayuwarta wanda wannan shine dalilin da yasa lokacin da Bilkisu taga yanayin da 'yar uwarta keciki kuma taji ta aikata hakan bisa kuskure da yarinta don d'ai kawai ta tsiratar da rayuwarta"


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" suka ji dady dake tsaye k'ofar palourn tun d'azu yana sauraren abunda mom kefad'awa ummi yafad'a yana k'ok'arin shigowa tare da cire hular dake kansa, a firgice suka juyo tare da nufowa inda yake suna fad'in "alhaji lafiya kuwa?"


Shiru yayi na wasu 'yqn mintota kafin ya d'ago kansa idanuwansa cike tab da k'walla yace


"Dr dake kula da Basmah ne yakirani yanzu yana fad'amun cewa, wai inbinciki 'yata Basmah inji halin da take ciki akan rashin lafiyarta, shine nake fad'a masa cewa ai tayi aure tun last week yafad'a mun inji in wani abune yafaru da ita idan babu matsala, nan yake fad'amun cewa condition d'in rashin tafiyarta yayi tsauri da yawa wanda yakaiga idan ba'a fitar da ita wajeba zata iya rasa rayuwarta don gaba d'aya k'arfin bugawar zuciyarta yaragu da kaso sittin da biyar bisa d'ari wanda hakan shine nuna kusan fiyema da rabin jijiyoyin dake aiki ga zuciyar tata sunyi rauni, kuma tun sati d'aya daya wuce yaso sanar dani hakan amma tarok'esa akan kada yafad'a har sai bayan bukin 'yan uwanta, wanda hakan yasa yarubuta mata magungunan da zata rik'a sha har zuwa wannan lokaci sai tadawo kak'ara dubata sannan asanar damu amma bayan lokacin yayita jiran ganinta bai gantaba, wanda hakanne ya tayar masa da hankali ya ciro no dake jikin file d'inta har yasanar dani don gudun faruwar wani abun gareta ya haifar masa da matsala wajen aikinsa, to shine nikuma naje can part d'inki hankalina atashe don nasanar dake nasamu bakican sai nayo nan, maganar da naji kunayi itace ta dakatar dani ga shigowa har nasamu tabbacin abunda dr yace acikinta, abu nabiyu kuma shine yanda na wofantar da alamarin 'yata alokacin da take buk'atar kulawar mu saboda tarage rad'ad'in dake cikin zuciyarta na rabuwa da masoyinta, Allah sarki najima ina rok'on Allah ya had'e mun kan 'ya'yana su so junansu, sai gashi yabasu abunda yafi k'arfin akirasa da had'in kai ko soyayya sai dai ace masa sadaukarwa, domin aduk inda aka samu sadaukarwa kasan ba k'aramar soyayya ce da kuma had'in kai a wurinba, Bilkisu kenan baiwar Allah, bacin juriya da hak'uri da Allah yabata sai kuma ya had'a mata da k'ana'ar iya rik'e sirrin 'yar uwarta da mutuncinta, itace k'arama acikinsu amma babba mai hangen nesa, tayarda tafuskanci damuwa da bak'in ciki matuk'ar kowa zaiyi farinciki" Shiru dady yayi cike da tausayin 'yarsa da nadamar marora da bugun daya yimata dad'in dad'awama harda fushi yayi da ita amma tsabar son 'yar uwarta hakan baisa ta iya bud'e bakinta tafad'i gaskiyar dalilinta ba, Ummi kuwa tuni jikinta yagama yin sanyi duk dazai har ga Allah duk abunda take yimata bawai fushine takeyi sa'a itaba don tasan illar da fushin ta zaiyi mata, kawai tana yimatane don taji haushi kamar yanda itama shiriyar da mijinta keyimata kesata jin haushi, wata irin jiwace taji tad'ibeta tana neman kada ita daga tsayen da take, da sauri mom tarik'ota tare da zaunar da ita akan kujera tana fad'in "Ummin yara lafiya?"


'Dan cije baki tayi tana cije gefen bakinta had'e da cewa


"Kawai mamakine da al'ajabin yanda fari  yakasa fahimtar cewa asalin fari d'an uwansa bazai tab'a canzawa ba da kuma yanda son zuciya ya rufewa shuwagabanni biyu idanuwa suka kasa fahimtar damuwar wanda suke mulka balle har suyi tunanin sama masa mafita alokacin da farincikinsa ya kucce masa har yafad'a cikin damuwa, wannan dalilin shine yahaifarmun da sarawar kai dajin jiri nad'ibana"


Sosai dady ya fahimci cewa dashi take saboda fushin da yakeyi da ita akan zargin tanada alak'a da laifin da 'yarta ta aikata da kuma yanda dashi har ita suke fushi da Billy tare da kasa bata kula saboda jin d'acin abunda tayi azuciyarsu balle suyi tunanin faranta mata, ita kuwa mom dafarko bata fahimci abunda Ummi tace ba saiga maganarta tabiyu tafahimceta, cikin jin nauyi tace


"Gaskiya abun ba dad'i amma duk laifin Aina Basmah ne data kasa jurewa qaddararta saida ta cinna 'yar uwarta aciki, gashi taja mata rabuwa da masoyinta kuma kuntsiri fushi da ita, alhaji da rabba'atul bait don Allah da girmansa narok'eku amadadin 'yatah Bilkisu kuyi hak'uri kuyafe mata b'acin ran da kuka samu awannan abu da yafaru, kufahimceta kuma ku jawota ajiki koda tasamu rangwame azuciyarta, haba yakamata ku yabawa jarumtarta don da Basmah ce da yanzu ba ita kad'aiba kowama da yaji ajikinsa saboda yanda matsalarta zata addabi kowa da zuwa asibiti" 


Tak'asan idanuwa dady ke kallon Ummi data jingina kanta ajikin kujera tana suraron mom, cikin jin kunya yana d'an sosa k'eyar kansa yace


"Koma meye tunda maigama tagama ai sai ayafi juna koba haka ba hajiya hussaina" 'yar dariya mom tayi kafin tadafa kafad'ar Ummi tace


"Yaya Allah ya sawak'e kuma ya k'ara shirya mana 'ya'yanmu yaci gaba da had'e mana kawunanmu, pls don Allah aduba al'amarin nan yaya wanda yayi abun k'awarai tayimasa afuwa amanta da komai wanda kuma ya aikata laifi to inaga shikam maganar dashi kuskuren sa amma nidai 'yata nakeji tunda ansan gaskiya ayafe mata" tana gama fad'ar haka tazagaya tabayan kujeru don tun d'azu tana kalle da yanda dady ke aiko mata da harara shiyasa tafasa bi tagabansa ta zagaya tabar part d'in tana dariyar k'eta k'asa k'asa...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____91💎


  

   Kallon Ummi dady yayi yanaji gaba d'aya bai kyautaba abunda yayi mata, nan take yaji ya tsinci kansa cikin wata irin kunya da dana sani, tasowa yayi yadawo inda take yazauna kusa da ita dayake kujerar 3seater ce take zaune akai, hannu yasa da niyar tab'ata yana fad'in 


"Rabba'atul bait ya ciwon kan da sauk'i dai ko?" Mik'ewa tsaye tayi had'e da kallonsa tace


"Wannan zafin ciwon kan da nakeji bai kai rad'ad'in  zafin ciwon fushin da kayi dani ba har natsawon kwanaki takwas ba, don haka idan har ka iya jurewa ganina cikin wancan zafin ciwon ai bai kamata ace wannan d'an zafin ciwon kan yasa kakula niba" tana gama fad'ar haka tawuce bedroom d'inta hawaye na zubar mata a idanuwa,


Zaune dady yayi wajen tare da buga tagumi yace "Tirk'ashi! yaufa nataro ruwa, saida meamah dasu Ummie  suka yita bani shawara akan bekamata na d'auka da zafiba amma nak'iji, ai yau ga irinta nan, wannan fushin da tayi nasan babu mai bata hak'uri taji idan ba mutanen rano online ba" haka yazauna shikad'ai yana faman suruttansa yakasa zuwa ya fuskanceta saboda tsabar nauyin abunda yayi mata balle yasamu yabata hak'uri ta hak'ura, gyara zamansa yayi tare da jawo wayarsa yana lallatsawa  har aka kusa kiran magrib saiga su Bassam da Bilal da kuma Billy sun dawo daga gidan yaya Mahmoud da shima yake biye dasu abaya, da gudu sukaje suka haye jikin dady suna yimasa oyoyo, cikin fara'a dady ke shafa kanunsu yana fad'in "oyoyo yaran dady andawo?"


"Eh dady aunty faraaha mai mutunci dady ta siya mana chaculate da sweet hadda Ball" Bilal yafad'a tare da rik'o wuyan dady yana dariya


"Iyeee gayu, to injin dai lafiya kuka baro auntyn taku?"


"Eh dady kuma tayi mana abinci mai dad'i mukaci kuma taba aunty Billy wani abu aleda" Bassam yafad'a shima yana lak'ame ajikin dady, murmushin jin dad'in hakan dady yayi kafin yace


"Iyyeee lallai agaida aunty faraaha Allah yayi mata albarka gaba d'aya suka amsa da "amin"


Juyowa yayi yana kallon Billy da sai yanzu suka iso ita da yaya mahmud tare da amsa sallamarsu cikin girmamawa suka k'arasa cikin parloun had'e da gaishesa, bayan ya amsa Billy tamik'e zata wuce d'akinta dady yayi saurin cewa


"Bilkisu" wani irin fad'uwa gabanta yayi tare da juyowa tace "na'am dady"


"Zonan mana" yafad'a cikin sigar rarrashi da alamar sakkowa daga fushin da yakeyi da ita, dawowa tayi cikin palourn tazauna kanta na duk'e ak'asa, alama yayi mata data dawo kusa dashi ta zauna sannan yacewa su Bassam suje su d'auro arwala ankusa kiran sallah, bayan sun fita dady yafara k'warara masu labarin abunda dr yafad'a masa akan 'yar uwarsu da kuma abunda ya isko mom nafad'awa Ummi sannan yajuyo yana kallon Billy yace


"Hak'ik'a ke 'yace tagari da zanyi alfahari da ita duniya da lahira, kinnuna mun cewa kobana duniya zakibi 'yan uwanki kuma kisoau fiye da yanda nake buk'ata, kiyi hak'uri bisa abubuwan dana yimaki, yanzune nafahimci dalilinki na cewa bazaki samu farincikiba idan kika auresa, duk da dai cewa kinyi laifi wajen rashin sanar mani da gaskiyar hak'ik'anin dalilin da yasa kikace bazaki auri d'an uwanki ba hakan bazai hana inrok'eki yafuwar hukunci dana yimaki bisa rashin fahimtar ki, kiyafemun Billy ubangiji Allah yayi maki albarka kuma kema yabaki 'ya'yayen da zakiyi alfahari dasu kamar yanda nima nake alfahari dake, yanzu kije kiyi tunani idan kina buk'atar cigaba da karatu sai inda ayimaki replacement da takardar gurbin karatun da aka nemowa Basmah kinji ko?"


"Eh dady, ngd Allah yak'ara girma" tafad'a hawaye nazuba a idanuwanta, abu biyu ya sakata kuka, nafarko halin da taji 'yar uwarta keciki, na biyu kuma yanda Allah yakawo mata k'arshen fushin da dady keyi da ita, ahankali ta d'ago kanta tana kallonsa tace


"Dady kakira yayya kaji tana lafiya kuwa?, wlh bana tunanin koda akwai matsalar dake damunta zata fad'a don tanada matuk'ar zurfin ciki"


Mahmud da gaba d'aya jikinsa ya mutu jin abunda dady yafad'a yana kallon irin jarumta da sadaukarwar da Billy tayiwa 'yar uwarsu baisan lokacinda tafurta cewa


"Billy bana tantama cewa insha Allah ke 'yar aljanna ce, bantab'a ganin wanda zaiyi irin sadaukarwar da kikayi ba kuma yakama bakinsa yarufe duk da matsalolin da yaketa fuskanta da damuwa ba sai ke, Allah narok'eka kada kisake bani damar yin rayuwa aduniya idan babuke 'yar uwata" idonsa na kawowa cike da k'walla tunawa da yanayin da tashiga cikin lokacin don ko yanzuka kalleta zakaga yanda tafad'a, duk da tab'angarenta ita batada wata damuwa irin sosai d'innan don ta dad'e da fawwalawa Allah dukkanin al'amurranta kewar 'yan uwanta kad'ai kedamunta.


Mik'ewa tayi jin ankira sallah tawuce d'akinta sukuma sukayi arwala tare da wucewa masallaci.


Tana gama sallah tanufi d'akin Ummi, zaune ta iskota saman sallaya tagama sallah, gefenta tazauna tana mummurza zoben hannunta kafin tad'ago kai tace


"Ina wuni Ummi" juyowa Ummi tayi had'e da cewa


"Lpy klw, agaisheki mai gayya mai aiki, yau naji duk abubuwan da kikayi wud'anda amatsayina na mahaifiyarki ban cancanci ace najisu daga wajenki ba"


"Don Allah Ummi kiyi hak'uri nayi kuskure, tutuni nayi tir da halina na rashin sanar dake abunda kefaruwa har najawowa kaina shiga cikin fushin ki" tashi tayi tadawo gabanta tare da durk'usawa akan guiwowinta tace


"Umminah kiyimun duk hukunci daya dace dani bisa b'acin rai da bak'in cikin danasa kika shiga a idanun mutane matuk'ar hakan zaisa kidena fushi dani kuma kiyafemun, Ummi nayi hakanne saboda a kullum ke kike fad'a mana muso 'yan uwanmu, kuma muso masu duk abunda muke so fiye da muke sonsa, sannan kika horemu akan kame baki ga yawan fad'ar alkhairin da kayi domin zai iya tafiyar da ladarmu, shiyasa saboda son da nake yiwa 'yar uwata nabar mata wanda zan aura kuma bak'i fad'ar haka saboda kada kimanta ta tab'a ko kuma in rasa k'afar yin hakan" cike da tausayi Ummi ta rungumeta had'e da cewa


"Hakane Bilkisu amma ita uwa abokiyar shawarace bai kamata kib'oyemun ba, kinsan bazan tab'a cewa a'a ba don nima Basmah 'yata ce amma zan d'ora ki hanyoyi mafi sauk'i da zakabi ki sadaukarwa da 'yar uwarki Mahmud batare da kin wahala ba, kuma kinsa mun fuskanci damuwa dani har ke, kidena fad'ar kin sani cikin bak'inciki a gaban mutane Bilkisu,  domin farinciki da alfaharin zamowarki 'yatah kawai kika sani, kawai naji badad'i ne ganin har laifinki ya shafeni, shiyasa nake shareki don kiji irin d'acin da nakeji akan shiriyar da dadynki keyimun amma ko kad'an bafushi nakeyi dake ba"


"Ummi natuba kiyi hak'uri  kiyafemun hakan bazata koma faruwa ba"


"Shikenan Bilkisu Allah yayi maki albarka, kije kitchen doughnut nanan dana had'a kifara soyawa kafin in ida azkar d'ina, ina fatar kema kinyi ko?"


"Eh Umminah" Billy tafad'a cikin wani courage dajin dad'in ganin yau she's free from any sorrow and annoyed


Bayanta Ummi tabi cike da mamakin yanda gaba d'aya wannan abun bai dami zuciyarta ba balle har ya illatata, godiya tayiwa Allah da wannan baiwa da ni'ima daya yimata nasamu 'yar da tasan daraja da kimar 'yan uwanta da kuma rayuwa sannan taci gaba da azkar d'inta zuciyarta cike da farinciki marar misaltuwa.


Batool kam yanzu anriga da anzama jerin matan aure kuma 'yan gida domin kullum cikin samun kulawa da riritawa take awajen mamy, haka shima dr Ahmad don har yau bai koma wajen aikinsa ba, duk yanda zatayi tayi akan yakoma amma yace ina ba inda zaije sai anyi sati biyu, gashi indai yana cikin gidan babu abunda yafi buk'ata irin yagansa tare da fatimarsa yana tayata aikace aikace shima yana aikinsa ajikinta na 'yan....., zallar shagwab'a take yimasa son rai shikuma yana biye mata, ita kuwa mamy intun safe har zuwa magrib zai kai babu abunda yadameta tana d'aki ita da yaronta Muhib da yayi matuk'ar wayo, sosai Batool ke girmamata tare da bata kulawa don tana gama had'in breakfast d'inta da taimakon dr.Ahmad zata silalikkewarta k'asa tabarosa sama tazo ta gyarawa mamy bedroom d'inta da palour sannan ta karb'ar mata Muhib ta hau sama dashi tayo masa wanka tagyarosa tsaf yana k'amshi sosai sannan takawowa mamy shi, 


Yauma kamar haka tana yiwa Muhib wanka taga dr. Sai faman cika yakeyi yana batsewa, yana jejjefa kayans nawasa da tazo masa dasu abakin k'ofar toilet d'in, juyowa tayi takallesa tana murmushi had'e da cewa


"My angel meye haka kakeyi?, kana faman yimasa jifa da kaya, koda yake kaine saya idan ka lalata kasiya masa wasu" irin 'yar k'aramar Ball d'innan ya d'auko ya d'an  jefeta da ita adaidai waist d'inta had'e da cewa


"Wato ke tama kayan wayarsa kikeyi ko? to Allah bazan yarda da wannan wayon da Muhib keyimun ba nima yau bazan yarda ba sai kinyimun wanka, ido ta k'walalo waje tubarkallah daidai lokacin tafito rik'e da Muhib tak'are masa wankan tana neman towel d'in da zata nad'esa dashi don ta tsane masa jiki tana dariya tace


"Tab wai wayaga bursili, ina ni ina yimaka wanka dubeka fa?"


"Aww haka kikace?, wato nima ne bursili ko?" Wajen yanufo tare da tad'ar d'uwawun Muhib da take gogewa jiki yanda bazai ji zafiba, ai kuwa Muhib yazata abun wasane ya b'angale masa da dariya sannan ita kuma yace mata


"Ki maimaita abunda kikace ko kema ki karb'i naki hukuncin" sanin abunda zai iya biyo bayanta yasa tace


"Haba my Angel, ai da wasa nakeyi, bari nakaiwa mamy yaron nan sai kaima inyi maka naka kaji ko?" tak'are maganar had'e da yin kiss a 'yan yatsunta ta d'ora masa akan lips d'insa, shima hakan yayi mata tare da cewa ina sonki milkheart d'ita. 


Hmmm tsabar rigimar dr. Sai dai da tagama gyare Muhib tsaf sannan ya karb'esa ya kaiwa mamy yadawo suka farantawa juna sosai tare da samun nishad'i, kamar yanda ya buk'ata haka tayi masa tanata nishi yanata yimata dariya saboda yanda tagaji, taimaka mata yayi itama tayo wankan sannan suka fito tana mitar gaba d'aya jikinta ciwo yakeyi, bayan sun shirya tsaf cikin k'ananan kayansu suka dawo palour ya zauna akan 3seater ita kuma takwanta tare dayin matashi da cinyoyinta, soyayya sukeyiwa juna mai cike da tsafta da yarda da kuma kulawa duk da dai hakan bai hana wataran sud'an sab'awa juna wanda nan take kowanensu zai fahimci kuskurensa kuma sai yagyara don gudun sake faruwar hakan"


Mom kuwa tunda tafita takoma part d'inta take kukan jin yanayin da akace 'yarta na ciki, gashi tayi kiran wayarta har tagaji amma bata d'aga ba, lokacin ita kuma Basmah tashiga kitchen don tace yau ita zata d'ora masu abinci da kanta saboda tahutar da Ummansu da kullum saita aiko masu da abincin da zasuci, hakama dady yayita kiran wayar Basmah amma bai samu. 


Ana hakane yaya Mahmoud yashigo ya iske mom cikin wannan damuwar, lallaahinta yayi tayi har saida yaga tasaki sannan yake tambayarta cewa "mom ya akayi kika gano cewa saboda Basmah Billy tak'i auren d'an uwa wanda gaba d'aya wlh ni mom tunanina bai tab'a bani haka ba"


"Nima ban saniba son, Basmah ce da kanta tasanar dani haka d'azu da mukayi waya"


"Allah sarki Bilkisu, duk inda d'an uwa ke kaiwa takai, wani zubin har mamakin irin firar da Allah yayi mata nakeyi, yanda tayi wannan sadaukarwar don farincikin 'yar uwarta itama Allah yakawo mata wanda zai sanyata farinciki, kingani mom abunda nake nuna maki ada idan nace 'YAN UWANA NE sai kice a'a ba 'yan uwanmu bane su, yanzu don Allah idan ba d'an uwaba kuma nagartacce wazai iyayin hakan? Akoda yaushe kamata yayi ace idanau iyaye sunada matsala atsakaninsu to kada susa 'ya'ya aciki domin su 'YAN UWANE dabai kamata ace sun sanya masu gaba da tsanar junansu azuciya ba, wlh mom badon kyakkyawar zuciyar Ummi ba da take nunawa 'ya'yanta damu dasu duk abu d'ayane kada sutab'a bari wani abu yarabasu damu da natabbata saidai Basmah ta mutu Billy bazata tab'a barmata d'an uwaba don itama tana sonsa"


"Hakane son ai nagano kuskurene tunkan insan da faruwar haka kuma nayi nadama, kuci gaba da k'aunar junanku ubangiji Allah yatsare mana ku"


"Amin mom bari inje ingaida Ummi sai in wuce, saida safe"



"To masha Allah ya iyalin naka lafiya take ko?"


"Eh mom tacema in gaisheki sosai, kinga namanta"


"Ina amsawa, Allah yayi maku albarka, inkaje ka gaiahemun da ita sosai"


"Zataji insha Allah" yana fita yanufi part d'in Ummi, yasamu tana yiwa Billy tsifar kai.


"A'a'ah Ummi yau tsifar dare kukeyi kuma?" Yafad'a tare da kamo tsoron Billy d'aya yana cigaba da cewa "Ummi najifa kamar anacewa bakyau rage gashi takeyi, Billy idan bak'yason gashin bari nayi cutting d'insa daga nan sai inkaiwa auntynki tak'ara dama gata guidus"


"Tab..aikuwa kamar kayi akunnenta don saina fad'a mata" dariya Ummi tayi had'e da cewa


"To kanwa uwar gami, dako kinyi abun kunya kai gulmar yayanki ga auntynki" sannan takallesa had'e da cewa


"Sannu da zuwa babana ya 'yatah take tana lafiya?"


"Lafiya klw Ummi tana gaisheku"


"Muna amsawa, yau tasha rigimammin bak'i duk sun wahalar mani da ita, ga kuma abun arzik'i data had'osu dashi, Allah dai yayi maku albarka yasa agama lafiya"


"Amin mom, ya akaji da abubuwan da suka faru?"


"To Babanah aikomai yawuce, Allah dai yaba 'yar uwarku lafiya"


"Ai yanzu naje muke maganar da mom tana k'ara yimun bayanin ashe Basmah takirata d'azu tana kuka tayi mata bayanin komai saboda taji ance har yanzu bakudena fushi da my sister ba, shine hankalinta yatashi tace mom tazo tafad'a maku ko kuma ita tazo da kanta tafad'a kowama yaji"


"Allah sarki, ni yanzu condition d'in da take ciki shiyafi damuna babana, wlh jinake kamar inje indubo halin da take ciki"


"To Ummi muyi mata addu'a in sha Allah zata samu lafiya, ai tunda matsalar tunani da damuwa ke haifar da ita natabbata yanzu zata samu sauk'i koda kashi sittin bisa d'ari ne"


"Allah yasa haka?"


"Amin ya Allah, ummi ni zan wuce saida safe, my sister Allah kidena tsifar dare ko kema ki koma gui.." bai k'yar ba ummi tace


"Kama bakinka babana tunda kana da redio maijini akusa da kai, haka kurum tafitineni da marecennan wai gobe gidan Batool zataje tanaso tayo mata kitso, to kannata ne da d'an banzar yawa shiyasa nafara tun yanzu kafin gobe da safe don kada yahanamu aiki"


"To Ummi, saida safe"


"Agaida mani da 'yata inkaje, kafad'a mata nace sannunta da k'ok'ari angode"


"Yaya gudnigth" Billy tafad'a tare da rakasa zuwa bakin k'ofa 


"Yawwa our mighty baby sweet dream kinji" sannan ya buga motarsa yayi gida, yana isa yatarar da faraaharsa zaune agaban wasu littafanta tana 'yan dube dube aciki, saye da wani d'an k'aramin mini skirt pitch colour sai wata armless shirt brown tad'an bud'e k'asa kad'an ajikinta, baki k'ofa ya tsaya yana kallon yanda tayi kyau abinta kafin yace


"My faraah am backkk..." Faraaha da batasan dashi awurin tsayeba tad'ago kai tana kallonsa had'e da tasowa cikin murna tana bud'e hannuwa tana fad'in  "oyoyo all I have, you are wlcm sweet me" dariya yayi tare da bud'e hannuwa shima yana jiran isowarta sai ji yayi an sakar masa kiss akumatu saboda yanda ya shafa'a da kallonta har ta iso wajen tamaida hannuwanta baya sannan tayi masa kiss bai sani ba, dariya tayi masa had'e da juyawa tana k'ok'arin barin wajen yayi saurin d'auketa ta baya yana fad'in "lallaima yarinyar nan ni kika shammata haka ko?, tab zaki gane kuwa don bazan yarda da wannan wayon ba" bai direta ko inaba sai kan gado tanata faman wutsil wutsil da k'afafuwa tana dariya, ganin haka yasa yafara yimata cakulkuli yana fad'in "zaki k'ara?" Dak'yar tasamu cikin dariyar tace 


"A'a" tashi yayi zaune tare da duk'awa akan guiwowinsa saman gadon yasake bud'e hannuwansa kamar yanda yayi d'azu yana fad'in "so am waiting for my welcoming hug" cikeda gajiyar da tayi itama tayi kamar yanda yayi sannan tayi hugging nasa had'e da yimasa romancing kiss, wanda nan take yafara jin yana neman fita hayyacinsa, hannu yakai da niyar jawota ajikinsa sosai tayi saurin jabaya had'e da fad'awa kwance saman gadon fuskarta na kallon ceiling tana dariya, shima hakanan yayi kamar yanda take kwance agefenta tare da juyowa fuskokinsu na kallon juna yace


"Ina sonki my faraah!"


"Nima ina sonka fiyema da sonda kake yimun mijina" nandai kalamai suka antayar dasu duniyar da tazamo sabuwar shiga a tsakaninsu har suke tunanin cewa babu wasu taurari da suka fisu haskawa aciki, 


Bayan sun fito wanka suna shan 'yan ruwan tea yaya Mahmud ya kalleta had'e da cewa


"My faraah wai wud'ancan littafan dana isko kintara kinsa agabanki namiye?"


Dafa hannunsa tayi had'e da cewa "sweet me dis week fa zankoma wajen aiki, kuma coliques d'ina nawajen aiki sun kirani sunce akwai seminar d'in da zamuyi nan cikin asibiti don k'arawa  juna sani, shine nake d'an biyar littafaina, kasan aikinmu dole sai mutum yanayi yana sake dudduba karatun daya yo a school don gudun wasu abubuwan su kucce masa"


"Ok ..gud matata Allah yakaimu kuma ya taimaka"


"Amin mijina" tafad'a sannan taci gaba da kurb'ar tea d'in dake gabanta, ganin tayi yaya Mahmoud yafara dariya sosai har yana rik'e ciki, tabishi da kallo sake da baki kafin can ya tsaya da dariyar sa yace


"My faraah don Allah kitashi kiyimun tafiyar nan da kikayi ta guragu ranar da muka had'u amatsayin zab'insu jaddi, 'yar harararsa tayi itama tana dariya tare da shafo hancinta da yayi zufa tace


"ita kake so nayi?"


"Eh"


"Shikenan anything for you my husband ni matarka ce babu wata kunya da zanji" mik'ewa tayi ta jefa k'afarta sai kuma ta kwashe da dariya yana tanata kafin ya juya yamaza ya d'auko wani abu acikin wardrobe yana fad'in


"Pls my faraah kiyimun ita nake sha'awar gani yau saboda gobe tafiya nake son yi, inba haka ba kuwa idan naje na gano wata 'yar gurguwa acan Allah sai in aurikketa tayita yimun ina gani, juyowa tayi tab'alla masa harara, shikuma ya d'aga mata kafad'i had'e da mere baki alamar I don care d'innan. 


'Bata fuska tayi tare da botsewa tana jefa k'afar tana danne dariyar dake taho mata har ta isa bakin gado yana biye da ita shima yana dariya, tana juyowa tagan haurun da shima yasaka aranar abakinsa yana faman dariya, gaba d'aya suka fad'a kan gadon atare yajawota ajikinsa bayan yacire haurun ya ajiye akan bedside locker yace


"Thank you my faraah, haka nake son mu kasance happy family akoda yaushe har lokacin da muka tara 'ya'yan mu, ina so bisa taimakonki mu gina gidanmu a matsayin Happy home kinji ko?" Ya k'are maganar tare da kissing forehead d'inta sannan ya kashe masu wutar d'akin had'e da cewa "I luv you"itama tace


"I luv you too".


Tunda sassafe faraaha tatashi bayan tayi sallar asuba tahad'a masa breakfast yaci sannan tayi had'a masa lunch shima a lunch box tare da kayansa kala biyu ajikka saboda yafad'a mata yau zaije borno yadubo Basmah da jiki, tana kammalawa suka shiga wanka atare bayan sun fito tana 'yan kukanta akan saita bisa yace


"my faraah kiyi hak'uri in sha Allah nafad'a maki gobe zan dawo kinji ko, ina so indubo 'yar uwata insan halin da take ciki shiyasa amma badon haka ba nida nake ango mezai kaini tafiya wani waje, zance naturo maki Billy ta tagaji kwana idan tsoro kikaji, ko kuma kitafiyarki gidansu papi kafin indawo gobe" dak'yar yasamu yashawo kanta tayarda zataje gidan papi don basuda nisa had'e da cewa


"Shikenan ubangiji Allah ya tsare hanya kuma ya saukeka lafiya, yakareka daga dukkanin sharrin k'arfe dana mugun mutum da aljan kuma yadawo mani dakai lpy"



"Yawwa my faraah amin ya Allah matata, ngde maki sosai da wannan addu'ar Allah yayi maki albarka" k'arfe takwashe nayi ya d'auri niyar kama hanyar zuwa borno tare da shiga motarsa tana maiyi masa bye bye tare da cewa ya gaida mata da Basmah sosai bayan tahad'a mata wani sak'o ga leda tace yakai mata sannan yawuce....

 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭

_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____92💎



   Kai tsaye asibiti yafara biyawa kafin ya wuce wajen family dr d'insu ya rok'esa akan ya had'asa da likitan dake kula da rashin lafiyar Basmah duk da dai ya sanshi amma saboda yana sauri yasan idan shi yaje ya had'asu zaifi saurarensa cikin lokaci, haka kuwa akayi har office dr jamil yaje yayi masa magana yabashi dama suka shiga, nan yaya Mahmud yasake gabatar masa da kansa sannan ya rok'esa daya sake yimasa bayanin da yayiwa dady akan rashin lafiyar Basmah, kasancewar ya wayesa kuma ga dr. Jamil atare daahi yasa yayi masa bayani dalla dalla yanda zai iya fahimta, nan yayi masa godiya sosai tare da fad'a masa dalilin ciwon na Basmah kuma ya sheda masa cewa yanzu haka wanda ta aura shid'in ne wanda takeso, murmushi dr yayi kafin yace


"I think yanzu everything will be right, tunda dama rashin samun sane ya haifar mata da damuwa har tashiga cikin matsala amma yanzu kuwa tunda gata ga wanda take so ina tsammanin za'a d'an samu sauyi ko kad'anne don bazance zata warke ba saboda yanda ciwon yayi mata tsanani, amma muna fatar zata samu sauk'i koda ba gaba d'aya bane in sha Allah matuk'ar za'ayi k'ok'arin kula da Shan maganunnukkanta bisa k'a'ida tare da yawaita zuwa wurin likita ana duba lafiyarta akai akai"


Godiya yaya Mahmud yayi masa sosai sannan sukayi sallama bayan sunyi musayar lambobin wayoyinsu, 


Yana fitowa assibiti yakama hanyar zuwa garin maiduguri lokacin har tara tayi na safe, 


Kusan awa biyar yayi akan titi yana faman tafiya kafin ya isa, faraaha kuwa tayi kiran wayoyinsa har tagaji amma bata samuba saboda gaba d'aya kashesu yayi don gudun kada su d'aukar masa hankali yana driven, hakan yasa dole tahak'ura tafara tattara abunda zatayi amfani dashi ta tafiyarta gidan papi tana kumbure kumbure ita ala tilas taji haushi,


Ab'angarensa kuwa yana isa kai tsaye gidansu ummah yafara wucewa, bakinsa d'auke da sallama ya shiga cikin cikin palourn lokacin ummah tafito nafitowa daga kitchen rik'e da plate d'in abinci tana k'walawa junior kira.


"Ah lale marhaban da baban bak'o, Mahmud kaine yanzu atafe?" K'arasowa cikin palourn yayi yana murmushi had'e da cewa


"Eh Ummah mun sameku lafiya?"


"Lafiya klw, saukar yaushe haka yaronah"


"Yanzunnan ummah" Yana rufe baki yaji anfad'o masa ajiki ana fad'in "oyoyo yayan kd" 


"A'a junior daga ina kafito haka banga shigowar kaba saidai naganka anan" yaya Mahmud yafad'a tare da mik'a masa hannu suka gaisa yana kallon ummah dake faman harararsa sannan yace


"Ina nan bayan kujera nab'uya ummanah zata yimun d'ure, yaya don Allah kace kada tabani bana sonci nak'oshi"


"Au! dama ashe kana jina inata faman kiranka shine ka k'yaleni?, Maza zonan kazauna kaci abinci kafin yanzunnan in sab'a maka, jimun yaro so kakene yunwa tayi maka illa" umma tafad'a tana mik'o masa plate d'in abinci dake hannunta. Kallon yaya Mahmud yayi ya tab'e baki zaiyi kuka yayi saurin cewa


"A'ah yaron dady, idan kayi kuka bazan baka abunda nazo maka dashi ba kaji ko?"


Abincin yakarb'a hannun Ummah tare da d'orasa saman cinyarsa yasa spoon yana basa abincin abaki, da wayo da wayo yayita tura masashi har saida ya canye plate d'in tas sannan ya zuge zip d'in jikkarsa daya zo da ita yaciro masa jirgin wasa da k'atuwar ledar chocolate ya mik'a masa yana fad'in


"Kadinga cin abinci sosai ni kuma zandinga kawo maka irin wud'annan aduk lokacin da zanzo kaji ko" cike da jin dad'i junior ke tsalle Yana fad'in "Thank you yaya, Ummah kinga kayana kuma bazan sammaki ba, 


"Dallah ja can, kazo ka wahalshemun da yaro daga isowarsa, fad'amun yanzu waya cinye abincin tunda kace bazaka ciba kak'oshi" wucewa yayi abunsa yana b'allar ledar chocolate d'in takalli yaya Mahmud sannan taci gaba da cewa


"Duk kai ke sangarta k'annen nan naka shiyasa sukuma sukeyita wahalsheka"


"Ummah meye abun wahalshewa anan? To idan banyi masuba ummah wazanyiwa? 'YAN UWANA NE fa.." bata tsaya jiran tajira ya ida fad'aba don tasan ta tsuniyar gitso bata wuce k'ok'i taje tad'auko ruwa masu sanyi a fridge tare da cup takawo masa agabansa ta aje tana cewa


"Sannu da hanya ga ruwa kasha ka kwaso rana, gashi baka fad'awa ummar taka zuwanka ba balle tayi maka tarba ta musamman" gorar ruwan yad'auka yana murmushi ya aza abaki saboda k'ishirwar da yakeji da zafin ranar dake bugunsa bai sauke taba saida ya shanyesu tas sannan ya ajiye gorar had'e da cewa,


"Afuwa ummanmu, wlh babu wanda yasan da zancen tafiyar nan inba 'yarki ba, yanzu nake cewa bari inkira dady infad'a masa cewa gani nan tare dake nazo gaisheku"


"Anya Mahmud wannan tafiyar tawace kuwa?" Sosa 'yar k'eyar kansa yayi kafin yace


"Sosai kuwa ummah ai duk tafiyar da zatasa ind'auko k'afafuwa inzo har garin borno to don kine za'ayi saboda kece dalili" 


"To ai shikenan tunda kace haka, yanzu kaje kawatso ruwa saika fito kaci abinci kahuta, bari naje nakawo maka makullan d'akin d'an uwan naka" 


"Ummah d'akin dai junior, aishi mun yayesa" 


"Rufamun asiri kada yajika, ai yace shikam bai yarda da hakaba, yanzu haka d'akinnanan kamar yanda kasanshi, hatta kayansa na sawa da wasu abubuwa duk sunanan, shiyasa duk bayan kwana biyu dole sai nasa anje angyaro masa d'akin, gudun kada datti yataru aciki" dariya yaya Mahmud yayi had'e da cewa


"d'an uwa kenan, badai rigima ba" d'aki tashiga ta d'auko makullin takawo masa yakarb'a tare da wucewa, da gudu junior yabi bayansa yana fad'in"


"Yayan kd wai inasu ya Bassam da Bilal,? Nayi missing d'insu da funny joke d'in da mukeyi dasu"


"Kai junior kaji tsoron Allah yau duka duka kwananku nawa da rabuwa da zakace haka?" B'ata rai yayi tare da cewa


"Ai yaya 'YAN UWANA NE shiyasa nake missing d'insu kullum" juyowa yayi tare da duk'owa daidai tsawonsa yace


"Am sorry nasan 'yan uwan kane malam junior, suna can gida nabaro lafiya klw suke suma sunyi missing d'inka sosai" yak'are maganar tare da d'an bubbuga kafad'arsa sannan yawuce abunsa, wajen Ummah shima yanufa ya aza mata rigima wai sai ankaisa wajen su Bilal,


Saida ya gama watso ruwa ya shirya sannan yakira faraaharsa data aza masa mita da rigimar yakashe wayoyinsa yanata faman rarrashi sannan ta hak'ura, seda suka sha firar soyayyarsu sannan yakira Mahmud pilot yasanar dashi Yana garin borno yanzuma haka Yana cikin gida kuma a d'akinsa sannan yafito yaci abinci, Yana kammalawa suka shiga firar yaushe rabo da ummah tana tambayarsa ya yayanta yake da can wajensu mom da batool da kuma iyalin nasa, jin bata ambaci ummi da 'yar uwar saba yasa yace


"Ummah ba dai kema fushi kike da ummi da kuma 'yar uwata ba?" Kauda kanta gefe tayi batare data amsa masa ba cike da takaicin tunawa da abunda yafaru, 


"Ummah kenan, agaskiya indai hakane baki yiwa ummi adalciba, taya zakiyi tunanin cewa inhar abunda Billy tayi kuskurene zuciyarki ta aminta da cewa dasa hannun Ummi aciki, wlh yanda kikasan halin Ummi ko wani bazata tab'a iyasa 'yarta tayi masa haka ba balle ke, bai kamata ace kinkasa fahimtar taba" juyowa ummah tayi tana kallonsa tace


"Amma kasan duk wani abu da 'ya'ya keyi Saida goyon bayan iyayensu? Data nuna mata cewa bata isaba tunda ba ita tahaifikanta ba wlh dole Bilkisu tahak'ura amma saita zuba mata ido tunda taga d'ana Yana sonta kamar ransa tayi wasa da zuciyarsa, to alhamdulillah allah daya saka masa sonta kuma yabashi hak'urin rashinta tunda gashi raye bai mutu ba"


"Ashsha Ummah, ai awannan zamanin 'ya'yan sun dena saka iyyensu acikin al'amurransu sai lokacin data kwab'e masu, amma duk da haka komai yana son fahimta"


"Hmmm Mahmud kenan, kadena wahalda kanka, don bazan iya fahimtar komaiba wanda yawuce hajia aisha tanuna cewa duk abunda 'yarta keso shi za'ayi mata koda hakan nanufin wani ko waau zaau cutu acikin al amarin"


"Ba haka bane Ummah don Allah kibani dama inyi maki bayani nasan zaki fahimceni sosai, wannan zargin da zuciyarki keyi akan Ummi zaya wanke gaba d'aya pls Ummah don Allah kisaurareni"


"Shikenan ina jinka" tafad'a ranta ab'ace, cikin natsuwa yafara bata labarin duk abubuwan dake faruwa tun daga farko har k'arshe, halin da Basmah tajefa kanta aciki naganin cewa saita hak'ura da soyayyar da takeyiwa Mahmud da kuma sadaukarwa da Billy tayi mata da b'acin rai da fushin data fuskanta wajen dady da ita har umminta babu abunda yab'oye mata, daga k'arshe yace


"Mahmud, Basmah, Bilkisu duka 'YAN UWANA NE, babu wanda zan d'auka inbar wani saboda infaranta ma wani cikinsu, amma inaso kiyar da dani wlh ummah dukkanmu babu wanda yasan dalilin Bilkisu nayin haka sai jiya da Basmah takira mom tana kuka tasanar da ita saboda tafad'awa dady da Ummi sudena fushi da  ita, shin Ummah kifad'a mun har yanzu Ummi mai son kantane da 'yarta, Bilkisu k'aramar yarinyace shiyasa ta iya jure wannan matsalar ita kad'ai don farantawa 'yar uwarta duba da yanda Basmah data girmeta takasa jurewa zuciyarta haka har takai ga fad'awa cikin irin wannan mugun yanayi" gaba d'aya ummah jikinta ne yayi sanyi idanuwanta cike da k'walla tace


"Allah sarki Bilkisu garin faranta zuciyar 'yar uwarta tajawo nayi abun da nasani ga tawa 'yar uwar kuma aminiyata, Mahmud nayarda da zancenka kuma natabbatar da haka don tun washe garin da aka kawo Basmah aka kwantar da ita asibiti, sai jiya aka sallamomu, kuma likita ya tabbatar mana da irin matsalar daka fad'a akan Basmah yanzu, wanda har yace tana stage d'in k'arshe yanzu da dole sai ankula da ita sosai da kuma kiyaye wasu al'amurranta amma alhamdulillah taji sauk'i yanzu sosai, tabbas duk wanda ya yanke hukunci cikin fushi yana tare da nadama ni yanzu da wud'anne idanuwa zan kalli hajiya Aisha bisa abubuwan da nayi mata"


"Shiyasa nace bai kamata alokacin kiyi fushi da itaba, tsayawa ya kamata ace kinyi kin fahimceta, amma koyanzu nasan Ummi batada matsala matuk'ar ke kinyi hak'uri to shikenan komai ya wuce" cikin kuka tace


"E'em Allah mai iko, wlh gaba d'aya yaran nan Basmah da Bilkisu duka tausayinsu nakeji, Allah yayaye masu dukkanin damuwa"


"Ameen umma damu baki d'aya" wayarsa yaciro yakira dady lokacin yana zaune palourn Ummi don tun jiya daya fita yadawo bayada wajen zama sai nan don ranakun girkin tane, ita kuma ko kallon inda yake batayi balle yasa ran zata tanka masa, abincima idan tagama akan dining take aje masa ta tura su Bilal sufad'a masa gashican ta kaimasa, haka zai tashi yaje can ya wani cika plates ya cinye hadda k'ari suk don tagani taji dad'i amma tayi kamar bata san yanayi ba, bugu d'aya ya d'auka had'e da cewa


"Assalamualaikum, my son"


"Na'am dady barka da rana, an wuni lafiya?"


"Lpy klw my son, yau Ina kashige ban ganeka ba da safe, kuma nayita kiran wayoyinka ba'a samu?"


"Afuwan dady ina borno naje gaidasu ummah Dan nan indubo maka 'yarka da jiki" wani irin farincikine ya lullub'e dady da Allah yabashi d'an dake iya wakiltarsa har acikin zuciya, domin tun jiya yakwana da tunanin Basmah aransa duk dako sunyi waya yajita lafiya klw amma sai yayi sha'awar inama zai samu damar zuwa koya aika adubo masa ita tunda ba'a wani dad'e da kaitaba balle yace yaje, yana kallon kamar yin haka akwai kunya aciki, sai gashi kamar ya shiga zuciyarsa har ya aikata hakan, 


"Masha Allah my son, Allah yayi maka albarka, to yakasamu 'yar uwar tawa da kuma taka" yafad'a cikin wani irin shauk'i dake nuna Yana cikin farinciki


"Lafiya klw dady gama Umman ku gaisa" nan yamik'a mata waya suka gaisa tare da sake biya abunda kefaruwa, nan dady yake sanar da Umma abunda yayiwa Ummi tare da rok'onta akan don Allah yana so ta lallasarmashi ita kozata hak'ura.


"Tirk'ashi ai yaya duk kanwar ja ce, wlh nima yanzu haka cike nake da dana sanin abunda nayi mata, bansan ta Inama zanfara bata hak'uri kaidai kasan yanda zaka lallab'a abukka tahak'ura" da haka auka gama wayar Mahmud yakarb'a tare da cewa


"Dady idan kana tare dasu mom ko Ummi kabanisu" ai kamar jira dady yakeyi yace


"Ina zuwa my son jira in kirawo maka ummin" hanu yasa ya dad'e speaker wayarsa yana faman kiran Ummi,


"Oum Bilqis yo sauri mana, d'anki keson yin magana dake" har taso tak'yalesa sai kuma taje takarb'i wayar a hannunsa, binta yayi da wani irin shu'umin kallo yana murmushi ita kuma tabasar tayi kamar bata ganesa ba.


"Hell" tafad'a lokacin data kara wayar akunne,


"Hello Ummi ina wuni?" Fad'ad'a murmushinta tayi kamar ba itaba sannan ta amsa masa da 


"Lafiya klw babana, ya gida ya 'yatah take? Injin dai duk kuna lafiya ko?"


"Lafiya klw Ummi ina borno fa?"


"Haba Allah sarki, ya ka isko umman taku da Basmah suma suna lfiya ko?"


"Lafiya lau Ummi"


"Masha Allah, babana wannan tafiyako sanarwa babu gaahi inada sak'on da zaka jewa Basmah dashi ai daka kaimata"


"Wlh Ummi kawai naji bari dai inzo in dubasu, amma ayi hak'uri tunda anriga angama"


"To shikenan, kagaishe mana dasu, suk da dai laifin 'yar uwarka ya ahafeni ummanku fushi take dani"


"To Ummi ai gani kusa da ita sai kugaisa"


"A'a babana kabasshi don nasan da k'yar idan zata amsa" muryar umma taji tana cewa


"Mezai hana in amsa qawata indai har zaki iya tsayawa ki saurareni, kiyi hak'uri bansan yanda abun take ba sai yanzu da Mahmud yayimun bayani, wlh gaba d'aya nazata cewa da son ranki ta aikata haka kuma kika k'yaleta shiyasa raina yab'aci" ji Ummi tayi batama San amsar da zata bataba kenan da ace bisa ra''ayin Bilkisu tafasa auren da bazatayi mata uzuri ba zataci gaba da zarginta akan ita ta aikata haka, cijewa tayi sannan tace


"Karki damu, ai duk abunda yafaru ga balbela farin tane yajawo mata" hakan da Ummi tafad'a ya tabbatarwa da Ummah cewa lallai ranta ab'ace yake kuma duk abunda tayi dagaskiyarta, dole Ummah tashiga bata hak'uri har saida ta tabbatar tahak'ura sannan takashe wayar tana ajiyar zuciya, karb'ar wayar yaya Mahmud yayi yana daria kafin yace


"Dama mai hak'uri idan aka k'uresa bai iya ba haddai ga wanda yake tsammanin bai dace ace yayi masa abu"


"Hmmm! Ai nagani, tunda muke bantab'a ganin b'acin rantaba ko zafin zuciya wlh sai yau, kai Allah dai yakaremu da sharrin shaid'an da kuma na zuciya"


"Amin ya Allah Ummah" wayar mom yakira itama yabata suka gaisa sosai mom cike da kunyar abubuwan da suka faru abaya tsakaninta da ita tace


"Don Allah hajia hafsatu muyi hak'uri da abubuwan da suka faru abaya mu manta da komai"


"Bakomai hussaina nidama banwani rik'eki araiba, kawai halinnan nakine yasa banfiye son mu'amala dake ba, kinsanni da zuciya in raina yab'aci ban iyaba, to gudun kar inb'atawa yayana rai kasa kota kanki banabi amma kema kiyi hak'uri kinji matar yaya" yak'are maganar cike da zolaya, murmushi mom tayi had'e da cewa


"Aikam dai wancan halin da kika sani gaba d'aya aminiyarki tazamo silar sauyawarsa don haka Ina fatar muyafi juna duk"


"To Allah ya yafemu baki d'aya" nan dai suka d'an tab'a fira kad'an sannan suka katse wayar abun gwanin ban sha'awa, duniya kenan babu abunda hak'uri yabari,kuma duk abunda yayi farko zaiyi k'arshe, sanadiyar shiruwar mitum d'aya acikin family kan iya samar da farin ciki mai d'orewa don haka mukasan ce masu hak'uri da 'yan uwanmu hakan zaisa duk wasu dake da raunin zuciya acikinmu rana d'aya sucanza saboda albarkar wannan hak'urin da mukayi da juna ubangiji Allah yasa mudace kuma yabarmu da 'yan uwanmu.


Godiya sosai ummah yayiwa yaya Mahmud bisa wannan k'ok'ari da yayi na daidaita tsakaninta da iyayen nasa wanda hakan ba k'aramin farinciki yasataba, ana haka saiga Mahmud pilot yashigo cikin palourn da hanzari yana fad'in Ummanah Ina d'an uwa yace yana nan ya gida ya iso, Yana rufe baki idonsa na sauka akansa, murmushinsa ya fad'ad'a had'e da qarasawa wajen yabasa hannu suka gaisa Yana fad'in


"Ango, ango, ango kasha k'amshi" murmushi yayi had'e da rungumesa sannan ya rad'a masa akunne "angwaye dai" sabod kunyar Umma da yakeji bazaya iya ramawa a fili tana jin saba, murmushin shima yayi don yafahimci hakan tare da juyawa yana gaisheda Umma dake k'ok'arin barin wajen, amsawa tayi had'e da tambayarsa ya 'yarta da jiki yace lpy klw take tana gaisheta sannan tabar wajen.


Tsokanar yaya Mahmud yafarayi wai yafara zama d'an lukuti, ashe malamar asibiti ta iya kula da miji, ai yazata majinyata da allurai da sirinjai kad'ai ta iya kula dasu ashe abun ba haka bane, mere baki yaya Mahmud yayi kafin yace


"Zauna nan, aini matata expert ce komai ta iya, inma bakabi hankali ba so soon zanzama baba inbarka nan kaga dole inzama nine yaya kai kuma ka koma k'ane"


"Eyye lallai d'an uwa bakada dama, naji bakomai ai dama tuni nazama k'anenka tunda kabani auren k'anwarka"


"Aw k'anwata bada kaiba?"


"Ina aini saidai inkirata k'anwata matata, mubar wannan zancen yasu dady, Ummi, mom da kowa ma, duk lafiya suke?"


"Lpy klw, bazaka tambayi k'anwarka takaba?"


"Wakenan?, Kasan k'annena yawa kedasu kuma babu wacce na ambata aciki balle kace nayi wariya"


"Amma ai ita ta musammance ya kamata ace katambayeta maganar gaskiya"


"To mai 'yar uwa, ya Billy dasu Batool suke? ina sunanan cikin farinciki dai ko?"


"Yes ofcourse" yabashi amsa atak'aice,


Nan suka shiga firarsu ta 'yan uwantaka dake cike da tsokana har suka gangaro akan firar rashin lafiyar Basmah, wacce yanda yaga Mahmud yanuna masa damuwarsa akan haka bak'aramin dad'i yajiba, yasan koda 'yar uwarsa bata warke duka ba zata samu farinciki sosai bisa kulawar da yake bata, daga k'arshema kai tsaye suka wuce HAIFA SPECIALIST, Suka samu tattaunawa da likitan dake kula da ita, inda yaya Mahmud yayi k'ok'arin had'asa da dr inta nagida yayi masa bayanin komai dake cikin folder d'inta tare da magungunan da take sha don ya taimaka masa wajen cigaba da kula da ita har zuwa lokacin da zata samu sauk'i sannan suka kashe wayoyin, kamar dai yanda wancan dr. Ya tabbatarwa da yaya Mahmud zata samu sauk'i tunda tasamu abunda take so zata dena shiga damuwa kuma haka zai taimaka mata sosai wajen samun lafiya matuk'ar aka kula da ita yanda yakamata kuma kuma tatsare shan magunukkanta cikin lokaci,.


Sosai yaya Mahmud yayi masa godiya sannan suka baro asibitin, gidansasuka nufa dama tuni Mahmud yakira Basmah awaya yace tashirya zai kawo mata wani surprised don dama bata san da zuwan yaya Mahmud ba, ai kuwa tayi wanka tayi 'yar simple makeup tana jiran dawowarsa, haka kurum taji ta tsinci kanta cikin farincikin da sharabonta tayishi har ta manta, 


Tanajin tsayawar mota tamik'e had'e da b'uya bayan labule tana jiran isowarsa taga surprised d'in da zai bata, ai kuwa tana nan alab'e tajiyo murya har ta mutun biyu ana sallama alamun kamar bashi kad'ai yake ba, ahankali tad'aga labulen don taga shida waye kawai tahango yayanta atsaye rik'e da key d'in mota yana murmushi don yanda yaga Mahmud yanufi uwar d'akin yana tafiya ahankali kamar wanda zai kama wani abun saboda yazata tana ciki sai yarufo idanuwanta suzo taga surprise d'in daya cemata, har ya aza k'afarsa zai shiga yaji anyi ihu tabayansa tare da fitowa inda tab'uya aguje ta lak'ame yaya Mahmud tana fad'in "oyoyo yaya sannu da zuwa"


Juyowa yayi yad'an b'ata fuska tare da nufo wajen yada'an zungure mata kai yna fad'in


"Wayace kifito shikenan kin b'atamun tsari" yak'are maganar yana harararta, daga yaya Mahmud har ita dariya suka saka masa tana yimasa gwalo had'e da cewa


"To sorry yaya ai kaine bakace kada infito ba ko?"


"Basmah wai sai yaushe zaki girmane, wannan irin shagwab'a da kike yi har Ina?" Yaya Mahmud yafad'a yana tsokanarta ganin yanada tawani nanik'e masa ajiki,


Rufe ido tayi had'e da mik'ewa tanufi kitchen don kawo masa ruwa da abincin da zaici, sosai yanayin daya gata tabashi tausayi don ta rame sosai ga wani duhu da tayi saboda ciwon da tayi,


Ita kuwa tsabar farinciki yasa tadinga jido drinks da abinci tajere masa agabansa,


Dariya yayi tare da cewa "ke Basmah duk ina zankai wud'annan abubuwan" tare da karb'ar ruwan data tsiyayo masa acup ta mik'o masa,


"Kacinye duka yaya, Ina Billy da Batool suke"


"Wato su zaki fara tambaya bazaki tambayi su mom da dady ba?"


"Kai yaya zan tambayesu mana sufa 'YAN UWANA NE shiyasa wlh kullum sai nayi mafarkinsu" 


"To ai yayi, innaje zan fad'amasu suma dena damun kansu akanki ke baki damu daauba sai dai 'yan uwanki" 


"A'a yaya ayimun hak'uri yasu dady da Ummi da mom da aunty faraaha dasu Bassam duk suna lafiya?" 


"Kowa lafiya klw Basmah ya k'arfin jiki" sinne kai tayi k'asa had'e da cewa


"Alhamdulillah naji sauk'i Ummah nakula dania sosai" 


"Kai Basmah kiji tsoron Allah nifa, bana kula dake? Mahmud pilot yafad'a yana kallonta, kallonsa itama tayi tak'asan idanuwa had'e da kad'a kai tace


"Kaima kanayi sosai ma" 


"Bana so tunda ummanki kad'ai kika sani" yafad'a tare da komawarsa gefe yasha toka, ala tilas yayi fushi


Ido yaya Mahmud ya zuba masa cike da tsoron Allah yana kallon abunda yakeyi kafin yaji Basmah nafad'in


"To kayi hak'uri bazan k'araba, ko yayanah" yak'are maganar tana kallon yaya Mahmud, kad'a kai Mahmud yayi tare da cewa


"To babban kobo ai sai ahak'ura tunda yaya da k'anwarsa sun bada hak'uri" dariya sukasa gaba d'aya sannan aukaci gaba da fira har lokacin Basmah na zaune kusa da yayanta kamar bataso surabu.


Kwaninsa d'aya yajuya ya koma gida cikin farincikin yanda yabaro 'yar uwarsa, yatabbata cewa yanzu tasamu natsuwa da kulawar da duk wata damuwarta zata kau, Basmah kuwa da zaitafi tasha kuka sosai haka yatafi yabar Mahmud yanata faman lallashi, dole tahak'ura amma gaba d'aya ranar yini tayi kamar batada lafiya.


Dady kuwa kullum cikin 'yan dubaru da kame kame yake amma fir Ummi tak'i saukowa saida akayi adadin kwana takwas d'in da yayi yana fushi da ita sannan tabashi fuskar da zai iya tunkararta, har takwanta da daddare sai gashi ya iskota har cikin bedroom d'inta d'auke da bargo da pillow, tana ganinsa tayi saurin rufe idanuwanta don dama tun ranar da abun yafaru ta k'auracewa part d'insa saboda fushin da yakeyi da ita gashi duk da yadena kuma yau kimanin kwana takwas ko girkinta ya zagayo bata zuwa kwancenta takeyi apart d'inta, saboda yagaji da sharesan da takeyi yasa yace yau duk fushinta anan zai kwana shiyasa ya d'auko bargonsa da pillownsa koda tace bazata kwana gado d'aya dashiba, 


Sosai ya bata dariya amma saita fuske tayi kamar bacci takeyi, k'arasowa yayi ciki tare da ajiye kayan gefe sannan ya zauna bisa gadon yana kiran sunanta, 


"Oum Bilkis" tak'yalesa "rabba'atul bait" nanma sharesa tayi had'e da juyar da kanta gefe,

 

Rasa yanda zaiyi da ita yayi kawai sai yafad'a kanta had'e da lalubo bakinta yafara kissing d'inta, k'yalesa tayi har sai da yayi abunsa yagaji don kansa sannan yatashi had'e dayin niledown agabanta yana fad'in "haba rabba'atul bait wai mekike so inyine,  gaba d'aya kinsa zuciyata cikin damuwa kin dabai bayeta kin hanata sukuni, don Allah kiyi hak'uri nayi kuskure amma bazan iya cigaba da jurewa wannan fushin da kikeyi dani ba, idan kuma kikace a'a to tabbas zuciyata TNA gab da bugawa kirasani gaba d'aya tunda kindena sona"


Tashi tayi had'e da gyara rigar jikinta tana kallonsa tace


"Meye don nashareka kai da kake da mata biyu, kaje mom d'in yara yafaranta maka mana, meye abun tada hankali haka harda zancen zuciya zata buga, don Allah rufan asiri katashi kaje ka kwanta abinka nima bacci nakeji"


Hannunta yarik'o tare da d'orawa saiti zuciyarsa ta kauda kanta gefe yace


"Rabba'atul bait saurari yanayin da zuciyata keciki, zafi take kamar zata k'one don Allah kiyi hak'uri kinji, gaba d'aya fushinki yasa babu wani hasken da nake gani acikin gidannan har ma da rayuwata gaba d'aya, kiyi hak'uri kiyafemun kamar yanda kema Allah keyafe maki" juyowa tayi tana kallon k'wayar idanuwansa had'e da son gasgata abunda yake fad'i sannan ta rungumesa tace


"Irin wannan yanayin da kaji nima irinsane naji lokacin da kake fushi dani wannan zafi da k'unar da zuciyarka keyi naji fiye da haka acikin zuciyata, ni nasamu k'warin guiwar jurewane saboda inada gaskiya kai kuma kakasa ne saboda rashin adalcin da kayimun, ba lallaine ace duk wani laifin d'a za'a maida hak'k'in yinsa ga mahaifiyarsa ba, idan kuma hakane don me bazaka zargi kanka ba tunda dani har kai matsayi d'aya muke dashi awurin ka, abu Bilal komai nason bincike da kuma afuwa koda ace kabincika katabbatar dasa hannuna bai kamata kayi fushi dani ba, afuwa yakamata kayimun saboda watakil kuskure yasa na aikata haka amma kahau fushi dani tamkar wacce baka so" tafashe da kukan da sai yau tasamu damar yinsa


"Kiyi hak'uri in sha Allah hakan bazata sake faruwaba, kiyar da dani ina sonki sosai kuma kema sheda ce akan haka, kawai sharrin shed'an ne da kuma fushin zuciya" yak'are maganar shima had'e da rungumeta yana jin cewa bazai tab'a iya rayuwa ba idan baya tare da ita...


_Wash duk nagaji, pls afuwan wlh jiya nayi typing garin inyi copying da pasting inturo yagoge gaba d'aya nikuma danaji haushi nak'iyin wani sai yau, kuci gaba da hak'uri muna gab da kammala sa insha Allah komai yazo k'arshe_





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____93💎



 Komai ya dai daita tsakanin ummi da dady yanda yakamata, sun manta da komai sun koma bawa junansu kulawa fiyema da yanda sukeyi ada, dama ance fushin masoya hutune, haka tab'an garen zaman gidan dady komai ya dai daita kamar yanda ya dad'e yana buk'ata tsakanin mom da ummi, zamane mai cike da girmamawa da kuma tsafta sukeyi, sun ajiyar kalmar kishi agefe sun amince zasu zauna a inuwa d'aya cike da kyautatawa da kuma mutunta juna, ko wace batada burin da yafi tafaranta zuciyar mijinta, tare da yiwa 'yar uwarta uzuri da kuma kauda kai ga abubuwan da suka san cewa tabbas Allama yasan bazai iyayin adalci ba a tsakaninsu, wani irin amintaccen zamane da babu cuta acikinsa balle cutarwa, duk wanda ya shiga gidan bazai tab'a cewa zaman kiahiyoyine akeyi aciki ba, daidai gwargwado kowace na kamantawa 'yar uwarta kuma suna b'oyon hankula sosai don samun wanzuwar tabbataccen zaman lafiya, ta b'angaren dady ma yana iya k'ok'arin sa wajen kamanta yimasu adalci tare da k'ara kyautata masu bisa kwanciyar hankali da kulawar da suke bashi,


Hakama su alhaji kabiru takanas ta kano suka zauna sukayiwa kansu fad'a tare da tunanin gyara kuskuren da suka aikata abaya na cutar da matar d'an uwansu, bayan buki sukaje har gida suka nemi dady yakira masu Ummi, wanda anan gabansa suka nemeta yafuwar abunda suka yimata ashekarun baya, baranma muzammil da duk yafisu jin kunya saboda kiran da yayi mata awaya lokacin tana jinyar Billy asibiti ya zazzageta tare da cimata mutunci akan wai tarabasu da d'an uwansu ta asircesa tayanda yazab'i yayi rayuwarsa batare dasu ba, wanda hakan ba kad'an ya matuk'ar tayar mata da hankaliba amma duk da haka batace masa komaiba har yagama zazzage zazagensa yakashe wayar, sosai lokacin ranta yab'aci amma saita danne abun aranta bata tab'a fad'awa kowa ba hatta dady kuwa, cike da kunya baba ka'rami ya kalli inda take had'e da cewa


"Hajiya Aisha ina rok'on kiyi hak'uri akan zagin dana kiraki awaya nayi maki alokutan baya, nayi matuk'ar nadamar yin hakan"


Sosai dady yasha mamaki jin cewa wai muzammil d'an uwansa kefad'a da bakinsa cewa yakira matarsa awaya ya zazzageta amma daidai da rana d'aya bata tab'a fad'a masaba, juyowa yayi yana kallonta yayinda ita kuma ta d'ago kai tana kallon baba k'arami had'e da cewa


"Hak'ik'a nasha mamaki kuma naji badad'i alokacin amma inaso kasani ko kad'an ba zagin da kayimun yab'atamun raiba, shirkar da akoda yaushe kuke jifata da ita cewa na mallake maku d'an uwa na asircesa ita tafi komai k'onamun rai, akoda yaushe burina baifi infarantawa d'an uwanku raiba, banida burin da yafi inyi masa sakayya da alkhairin da zaiyi alfahari dani agobe k'iyama, amma ku gani kuke Ina cutar maku dashi, Allah shine sheda akan bantab'a had'asa da kowaba don in mallaki mijina amma nasan Ina rok'onsa daya mallakamun zuciyarsa kuma yabani hak'uri da juriyar zama dashi har iya k'arshen rayuwata, shin taya za'ace yin hakan zai zamo laifi agareni bayan Allah da kansa yace murok'esa zai amsa mana domin babu abunda yafi k'arfinsa, gashinan zaune agabanku kutambayesa shin akwai abunda narik'a wajen k'ok'arin mallake zuciyarsa face ubangijina? Idan har kun musunta haka daga wajensa narantse da ubangijina shine shedar babu wanda nake kaiwa kukana face shi amma ku kunjefeni da kalma mafi muni arayuwa wacce aduk lokacin dana tuna sai nazubar da hawaye, shin meye ribar da zanci idan na asirce maku d'an uwa bayan ba cinsa akeyiba ko sha ko kuma sutura da zan tanadawa kaina don inburge aduniya, wlh inhar sai nayi hakan zn mallakesa nafiso inmutu amatsayin baiwa cikin gidansa matuk'ar zan mutu da imanina, karku manta ku kuke da d'an uwanku, zai iya rabuwa danina har abada amma ku kuma bazai iya rabuwa da kuba" 


Basu ba hatta dady Saida yaji kalamanta sun kashe masa jiki, tasowa yayi ya zauna kusa gareta tare da rik'o hannuwanta yace


"Tabbas ba'a kyauta maki ba Aisha, kuma 'yan uwana sunyi ba daidai ba, matuk'ar jin zafin abubuwan da suka faru batare da sanina ba kuma sunyimun d'aci azuciya amma ya zanyi? Karki manta su 'YAN UWANA NE da banida tamkarsu aduniya, dolene nayi hak'uri akan haka duk dako rashin jin dad'in da nayi, ba kuma wai don bana son kiba zanyi haka, A matsayina na mijinki kuma amadadin 'yan uwana, ina rok'onki akan don Allah da girmansa kiyi hak'uri kiyafe masu, sosai muzammil yayi kuskure kuma bai kyautaba, amma kiyi hak'uri bisa wannan cutarwar da akayi maki" sannan yajuyo yana kallon baba k'arami yace


"'Dan uwa maganar gaskiya baka kyauta ba, kusan kafi kowa aikata kuskure anan wajen, taya za'ace a matsayinka na k'anena kakira matata awaya ka zazzageta bisa wani dalili da baka da tabbas akansa, meyasa zaka aikata haka, ai kamata yayi ace koba komai taci albarkacin ina yayanka awajena, amma duk da haka karuntse idanuwa kaci mutuncinta,  hak'ik'a da wani mutumne awaje ya aikatawa iyalina haka to tabbas sai nayi shari'a dashi, yanzu kuwa dole inyi hak'uri kasancewar kai d'an uwana ne, amma kafinn nan Ina shawartarka da kada kasake aikata haka domin cin zarafine da cutarwa ga bayin Allah, kumashi Allah kasan baya yafe hakk'in wani tun aduniya balle lahira, Aisha da kake gani macece mai matuk'ar hak'uri da juriya, kullum batada burin da yafi ta sakani cikin farinciki tare da kwantarmun da hankali, duk abunda nake so shi takeyi, wanda kuma bana so baza tab'a yin shiba taya kake tunanin irin wannan mace zanso a muzantata ko awalak'antata agabana kuma inyarda, shin ashe irin wannan mace bata cancanci ace angujewa damuwar taba?  Ina son matata kamar yanda nake sonku sosai shiyasa bana tunanin zan iya rabuwa da ita komai rintsi komai wuya, nadad'a maku gaskiyar kowaye ita don Allah kucire tunanin cewa ta asirceni domin yin hakan kuskurene" alhaji bukar ne yadafa kafad'arsa alamun ban hak'uri kafin baba k'arami yace


"Don Allah yaya kayi hak'uri, kema hajia Aisha kiyi hak'uri, tabbas bai kyutaba abunda na aikata wanda nadamar haka takawoni wajenki don innemi yafiyarki, koma meye yariga yafaru kuma nayarda nayi kuskure don Allah muyafi juna" kanta na duk'e ak'asa tace


"Babu komai kuma komi yawuce, koba komai kuma tamkar 'YAN UWANA NE tunda na auri d'an uwanku don haka nayafemaku kuma kuyafemun, Allah yabamu ikon hak'uri da junanmu" gaba d'aya suka amsa da amin cike da kunyarta, dady kuwa jiyayi k'aunarta na sake lillinkuwa acikin zuciyarsa yana jin kansa amatsayin wanda yafi kowa sa'ar mata aduniya, lumahe idanuwansa yayi Yana kallonta tare da sauke wata irin ajiyar zuciya kafin yace


"Nagode maki sosai da kika d'auki 'yan uwana amatsayin auma 'yan uwanki kuma kika yafe masu, ubangiji Allah yayi maki albarka" amsawa tayi ciki ciki had'e da mik'ewa tabar wajen tana murmushi, part d'inta tanufa tanaji gaba d'aya zuciyarta tayi fresh batada wata sauran damuwa aranta tunda Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta, abokiyar zamanta, dangin mijinta, 'ya'yan mijinta yanzu batada wata matsala.


Abangaren dady ma tana fita suka yanke shawarar za'a maye gurbin da Basmah tasamu nakaratu da sunan Bilkisu dama tuni itama zainab 'yar gidan alhaji bukar dady yasa itama ansamo mata admission zasu fara zuwa tare next week, Billy kam gaba d'aya yanzu tazama 'yar gatan kowa mafi yawancin lokutama apart d'in mom take kwana shi kuma Bassam da Bilal awajen Ummi har mom nayimata sherida tazama uwar maza, 


Hakama Basmah duk da mahmud nayawan jin soyayyar Billy na motsa masa azuciya hakan bai hana yabata kula sosai ba, tasamu sauk'i k'warai da gaske gashi koda yaushe sai k'ara murmurewa takeyi tana fresh saboda yanda tasaki jiki sosai, hakan yasa yau yaya Mahmud ya quduri aniyar karb'ar hakkinsa amatsayin matarsa, Yana dawowa daga gidansu yabiya ya sawo kazar amarcinsa guda biyu tare da madarar hollandian yabiyo dasu, kwance ya iskota tana kallon wani tsohon season film my lover my wife, tanajin shigowarsa tamik'e tare da tarbosa tana fad'in 


"Sannu da dawowa yaya"


"Yawwa 'yar gidan Ummatah" turo baki tayi had'e da cewa "Ummanka dai ko Ummatah"


"Ummanki Ummatah, shikenan?"


Ledojin ya mik'a mata tare da wucewa kitchen ya d'auko tray da cups yazube masu aciki, hannunta ya rik'o bayan ya zauna k'asa tare da d'orata akan cinyarsa, duk da yasaba yimata irin wud'annan abubuwan sai taji yau abun yasha banban dana kullum, ahankali yadinga yagar naman Yana bata abaki har saida taci tak'oshi sannan shima yaci, ita dai gaba d'aya hankalinta na akan film d'in da take kallo batasa komai aranta ba, kwashe kayan yayi yakai kitchen sannan yadawo ya zauna kusa gareta tare da jawota ajikinsa yana fad'in  


"'yar gidan Ummah meye sunan wannan film d'in da naga tunjiya kike faman kallonsa" ahankali ta motsa bakinta har lokacin idanuwanta na akan tv tace


"My lover, my wife" shiru yayi Yana tunanin kalmar wai my lover, my wife, ya maimaita azuciyarsa sai yaji tamkar don shi akayi kalmar. Murmushi yayi tare da cewa


"K'adarallahu wama sha'a fa'ala"


Ganin gaba d'aya hankalinta na akan tv yasa ya tashi yaje yakashe tvn sannanya kashe wutar palourn, bubbuga k'afa tafarayi tana kukan shagwab'a had'e da cewa


"Kai yaya, kai yaya! Pls don Allah ka kunna mun abuna in kallah" cikin wata irin kasalalliyar murya yace


"Basmah darefa nayi kizo muje mukwanta gobekya iyar kinjiko" k'yalesa tayi tana turo baki duk da cikin duhune amma hakan bai hana yagani ba saboda d'an hasken wutar bedroom d'in daya zo nan"


Ta gefenta yabi zai wuce tasake bubbuga k'afafuwanta kamar zatayi kuka, dawowa yayi tabaya yana kallonta sannan ya d'auketa chak ya shige da ita ciki yana bata hak'uri, tare suka shiga toilet sukayo brush sannan suka dawo suka kwanta abunsu bayan ya kashe masu wuta had'e daja masu bargo, ahankali yafara matsowa kusa gareta yana shasshafa jikinta, ai nan take jikin Basmah yad'au rawa saboda sai yanzu tafahimci cewa suk wanda yaci ladar kuturu to dole zaiyi masa aski, tsorone yakamata sosai inda take tunanin kamar bazata iya bashi kan taba amma awani gefen zuciyarta bataso tayi masa haka don iya adalci yayi matashi, kimanin wata d'aya kenan da aurensu suna kwana agida d'aya, d'aki d'aya, kuma a gado d'aya amma saboda yanayin da take ciki bai tab'a neman hakkin saba awajenta sai yau don me zata hanasa, runtse idanuwa tayi tanajin yanda yake aika mata da sak'wanninsa masu wahalar karb'a awajenta, ai batasan lokacin data tafashe masa da kukaba, duk da yayi nisa bayajin kira hakan bai hana yasaurara mata ba yana tambayarta idan bata buk'atar hakan zaiyi hak'uri, jin tayi shiru yasa yaci gaba da abubuwansa cikin natsuwa da kwanciyar hankali saboda tunawa da abunda likita yace tare da lallab'ata, Ina ganin haka nikam nace


_Sai da safe k'awata Basmah Allah ya sanya alkhairi, yasa pilot yayi sa'ar jefa k'wallo aragartayanda yakamata😃🙈_




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Gaisuwa tare da fatar alkhairi agareki MY NOURI *UMMU MEENAL* 💋❤, bak'ina bazai iya fad'ar iya adadin alfahari da kuma farincikin da nakeyi ba, saboda samunki acikin rayuwata, mutane kance soyayya had'uwar jini ce amma tamu ta shallake haka saidai nace had'uwar ruhikan muce, domin kulawarki da soyayyarki agareni is always beyond my expectation, ba abunda zance dake illa Allah ya saukeki lafiya kuma yabamu healthy babies rayayyu masu albarka, haka kuma ina yimaki fatan Allah yasoki soyayya mai tsanani fiye da lullunkawar wacce kike yimun kuma yabaki aljannah da rahamarsa👏🏻 *HAPPY JUM@T TO U, LUV U SO MUCH*_



💎Page_____94💎


  

   Cike wani irin salo mai rikitarwa da wuyar d'auka Mahmud ya dinga sarrafa Basmah cikin kulawa da kuma tausayawa har yasamu cimma burinsa, duk da yatsinci kansa awani yanayi na daban dabai tab'a tsintar kansa acikiba hakan bai hanasa yin komai cikin natsuwa ba, har ya samu gamsuwa batare daya cutar da itaba,


Basmah kam taci kuka kamar ba gobe wanda yasa har saida zazzab'i yasoma rufeta, tashi yayi had'e da shiga toilet ya tsarkake jikinsa sannan yadawo ya jawota ajikinsa yana rarrashi, addua yayi mata sosai cikin ransa tare da tawassali da albarkacin darajarta data kawo masa har gida, Allah yabata lafiya kuma ya yaye mata wannan ciwo dake damunta, Sosai yaji wata irin kima da darajarta sun k'aru azuciyarsa, duk da ko har yanzu baya jin soyayyarta acikin zuciyarsa amma yabata wani matsayi namusamman aciki.


Koda aka kira sallar asuba tashi yayi yasake tsarkakikke jikinsa sannan ya sauya kayansa, yana k'ok'arin tayar da ita yaji antada sallah a masallaci don dama sun makara, hakan yasa yaga bari yabarta har sai yadawo masallaci sai ya taimaka mata tagyaro jikinta tayi sallah


Yana fita ta tashi tana faman cije baki saboda yanayi da rad'ad'in zafi da take jinta aciki, samu tayi ta mik'e ta lallab'a tashiga bayi, ruwa masu zafin gaske dake cikin flaks ta surka a bahon wanka sannan tashiga ciki, duk da tanajin yanda suke d'an qunarta haka ta daure tajima sosai aciki tana gasa jikinta, cikin mintuna da basu wuce biyar ba bacci ya sake d'auketa tana cikin bahon wankan saboda dad'in ruwan da takeji suna ratsata ajikinta,


Shi kuma ana sallame sallah ko addua'a bai tsaya yiba saboda hankalinsa nawajenta yabaro masallacin, yana shigowa yaga bata bisa gadon da sauri ya bud'e toilet d'in ya hangota cikin bahon wankan, hakan yasa ya rufo mata k'ofar yadawo yacire bedsheet d'in ya aza wani sannan yaciro mata wata doguwar riga marar nauyi da hijab ya d'ora mata akan gadon, zaman jiran fitowarta yayi har nakusan minti biyar amma yaji shiru, hakan yasa yakoma tashi yatura gambun k'ofar toilet d'in, hangota yayi cikin bahon wankan bacci ya d'auketa wanda sai alokacin ne yalura da haka, tsaye yayi yana k'are mata kallo kafin ya cire jalabiyar jikinsa ya ajiye gefe sannan yasa hannu ya danna inda ruwan zasu zuk'e sufita tacan k'asa don har sun soma hucewa, hakan da yayi yasa tafarka daga daddad'an baccin daya d'auketa tana ganinsa a a gabanta cikin sauri da jin kunya tashiga kakkare jikinta idanuwanta na k'ok'arin kawo k'walla, basar da ita yayi yasake had'a mata wasu ruwan masu d'umi sannan ya taimaka mata tayi wankan tare da tsarkake jikinta sannan yaciro mata towel d'in dake sagale ya d'aura mata, 


Rik'ota yayi tana takowa ahankali har suka fito ya zaunar da ita bakin gado sannan ya shimfid'a mata abun sallah, rigar yafara samata sannan yasa mata hijab had'e da cewa


"Basmah kidaure kiyi sallah saiki koma ki kwanta kinji" d'aga masa kanta dake k'asa tayi sannan yarik'ata ta tashi tsaye yana fad'in "ko azaune zakiyi bazaki iyaba atsaye" tare da k'ok'arin zaunar da ita, girgiza masa kai tayi ta tada sallar sannan shi kuma ya wuce kitchen ya kunna gas ya d'ora ruwan zafi akai, cikin minti uku sukayi daidai zafin da yake buk'ata ya sauke tare da juyewa cikin cup bayan ya kashe gas d'in ya had'a mata tea mai kabrin gaske, koda ya shiga har ta dad'e da gama sallar ta kwantar da kanta abakin gado, lallab'ata yayi yasamu tashanye ruwan tea n tsaf sannan yad'ibo PCM dake cikin bedside wardrobe  yabata tasha saboda yanda yaji jikinta nata yayi zafi, rik'ota yayi takoma saman gadon takwanta sanan shima ya zagayo tabayanta ya kwanta tare da rungumeta sosai ajikinsa yaja masu bargo,


Billy kam tuni sun fara wuce makaranta A.B.U zaria ita da Zainab yayinda take karatunta fannin medicine ita kuma Zainab faculty of science, sosai take samun kulawar 'yan uwa takowa ne gefe saboda yanda ta zame masu zakaran gwajin dabi, kowa na son Billy saboda hakurinta da kaifin hankalinta, hakama kafin tawuce makaranta saida tarok'i dady daya barta taje borno wajen Umma daga nan kuma tagano 'yar uwarta, ganin idan ya hanata bazata ji dad'i ba yasa ranar Saturday yace da ita dasu mom duk su shirya aje borno kwana d'aya adubo Basmah da jiki wanda hakan ba k'aramin dad'i yayi masu ba, nan suka hau shiri mom ko kunya babu tana shire shire zataje dubo 'yar gaban goshinta Ummi nata yimata tsiya har sukaje lafiya kuma suka dawo lafiya, fad'ar irin dad'in da Basmah taji naganin iyayenta da 'yan uwanta ba'a magana, hakama Mahmud ganin Billynsa bakad'an ya tado masa da cutar soyayyarta da akoda yaushe ke mak'ale azuciyar saba, wanda hakan yasa tunda suka had'u so guda bai koma bari suka sake had'uwa ba har suka tafi, Basmah tafahimci hakan amma tabasar saboda tasan illar so kuma tasan dole haka zata faru, 


Ummi kuwa tunda Billy tawuce makaranta zazzab'i ya soma rufeta, gaba d'aya bata iya aikin komai ga yawan bacci da rashin kuzari duk sunbi sun adda beta, da farko dai dady yayi tsammani  kewar rashin Bilkisu atare da itace ta tab'ata, lura da ko sau d'aya bata tab'a rabuwa da itaba kamar irin wannan lokacin, ganin abun yak'i ci yak'i canyewa yau kimanin sati uku kenan yasa mom tarakata sukaje asibiti, tashin farko likita ya tabbatar ummi na d'auke da juna biyu na tsawon sati uku da kwana biyar, iya kunya ranar Ummi tajita duk da dai tana sha'awar haihuwar amma sai take ganin kamar yanzu tayi tsufa da yinta, sosai mom ta taya dady farinciki da murnar jin wannan labari har tana fad'in "Allah ya kawowa uwar maza 'yammace kota huta da tsokanar da nake yimata" dariya dady yayi had'e da rungume mom yace "Amin momyn yara tare dake" k'wace jikinta tayi taje inda Ummi ke kwance cike tarufe fuskarta tace


"Yaya Allah ya inganta kuma ya tsayar gareki da alkhairi, ai nikam daga Bassam d'an autana babu k'ari in sha Allah, haihuwa fa shidda alhaji! Ina laifi aiko ahaka Allah yatsayarmun alhamdulillah"


Bayan sun dawo gida kuwa haka Ummi tayita yiwa mom magiya akan don Allah kada tafad'awa kowa koda yaya Mahmud ne, wai ita ina zata da wannan abun kunya idan sukaji,


"Ikon Allah, Aikam dama kindena rok'ona, ai wannan abun farinciki ne koban fad'awa kowa ba dole su papi suji" mom tafad'a tana dariya, harararta Ummi tayi kafin tace


"Ai shikenan gaki ga waje, Allah ya mak'awa jaki k'ofo"


"A'a ba amin ba, Allah yabarshi ayanda yake, meye abun kunya ko tada hankali aciki, tunda ni nagama nawa tone d'in, yanzu ke nakine, iya naki d'aukar ciki da haihuwa indai renone bakida matsala kinada wacce zatayi maki"


"Hmmm ai renon ne da wahala yanzu saboda tarbiyar da zaka zaman d'ora yaro akai, kuma awannan zamani wazai zauna zaman yimaka reno tsakani da Allah bisa ingantacciyar tarbiya" murmushi mom tayi kafin tace


"Gani zanyi maki reno mana iya naki kiyita haifarwa nikuma ina tayaki reno kinga shikenan bakida wani tunanin mai reno agabanka"


"Hmm kedai kad'an ma mai albarka idan Allah yabani ina godiya, fatnmu dai Allah yaraya manasu kuma ya albarkacesu"


"Amin ya Allah umminsu kuma da zancenki gaskiya"


Tun tafiyarsu Ummi borno abubuwa gaba d'aya suka dawowa Mahmud sabbi, banda tunanin Billy da kallon fotunansu babu abunda yakeyi, hatta 'yar kulawar da yakeba Basmah tad'an ja baya wanda hakan yasa yakasa fahimtar yawan zazzab'in da take kwana dashi, tana sane da halin da yake ciki kuma ko kad'an bataji zafi ba ko ganin laifinsa, balle ta tayar da hankalinta, kullum addu'ar ta shine Allah yarage masa rad'ad'in da yakeji azuciya narabuwa da masoyiyarsa, yauma zaune suke yayi matashi da cinyoyinta suna kallo amma shi latsar wayarsa kawai yakeyi, gaba d'aya ya manta da Basmah na wajen ya dinga jawo hotunansa na buki da Billy yana kallo, tana kalle dashi amma sai tayi kamar bata san yanayi ba, 


Ganin tayi gaba d'aya yayi marking d'insu zai goge tayi saurin rik'e masa hannu, 


"Haba yaya meyasa zaka gogesu?" Sai alokacin yatuna cewa ashe tana wajan, jiyayi kunya tarufesa kuma gaba d'aya bai kyautaba da yayi hakan, 


"Basmah! Ya salam, don Allah kiyi hak'uri, bansan lokacin da hakan yazomun ba, amma ina so kisani ko kad'an wlh banyi don in b'ata maki raiba, don Allah.." Kafin ya k'yar ta toshe masa baki tana murmushi had'e da cewa


"Babu buk'atar kayi mani rantsuwa mijina, nayarda dakai, bazan tab'a zarginka ko tuhumarka acikin zuciya taba, dolene kaji ba dad'i aranka don haka kada kasamu akan wai don kayi haka raina zai b'aci, ko kad'an banajin haka domin da kai da Billy duka 'YAN UWANA NE don haka ko soyayya bata tab'a gittawa tsakaninku ba, bazanji haushiba tunda nasan 'yan uwan juna kuke, kabar pics d'inku mana kuma ka kallesu aduk lokacin daka buk'ata matuk'ar hakan zaisa kaji sanyi azuciyarka, takaicina d'aya shine yanda nazama katangar da tahanaka kasancewa da abunda kake so, amma wlh ko d'aya bana d'aukar wannan abun da wata fuska, kuma kasa aranka akoda yaushe inyimaka kyakkyawan zato" tak'arasa maganar tana shafa kansa tare da yimasa kiss agoshi sannan yamaida hankalinta ga kallon da takeyi,


Jikinsa asan yaye yatashi had'e da juyo da fuskarta suna kallon juna yace 


"Basmah infad'a maki wata magana?" Murmushi tayi had'e da kad'a masa kai yace


"Kinada wani girma da kima azuciyata da zan iya cewa ked'in tamusammance" 


"Dagaske yaya?" Tafad'a tana k'ara fad'ad'a murmushin ta da har saida hak'oranta suka bayyana, hannuwa yasa yarik'o fuskarta sannan yace


"Ofcouse Basmah har cikin zuciyata ked'in ta musammance.." Rufe bakinsa keda wuya yakai hannunsa ga wuyanta yana tattab'awa saboda zafin da yaji jikinta yayi had'e da cewa


"Basmah lafiya kike kuwa?" 


"Lpy klw amma kusan sati d'aya kenan inajin zazzab'i" tunawa da yayi tun bayan sati d'aya da kusantarta yalura da kamar tana fama da rashin kuzari kuma duk walwalarta taragu shiyasa duk yanda yakejin buk'atar ta yake hak'ura don bayason matsamata har ciwonta yatashi,


"Tashi tashi d'auko mayafinki muje asibiti!" yafad'a hankalinsa atashe,


"Kai yaya bawata matsala cefa ke damuna, ni lafiyata klw babu inda zanje, muna zuwa yanzune zasu sossokewa mutum jiki da alluran nan nasu, gaskiya nidai bazan jeba yaya" sake tab'a jikinta yayi tare da cewa


"Ai baki isaba, kina wasa da lafiyarki ko?, maza kije kid'auko hijab d'inki kafin nakira d'an uwa insanar dashi abunda kikace"


Turo baki tayi sannan taje tad'auko hijab d'inta tafito rik'e dashi ga hannu tana tuk'uburi, karb'e hijab d'in yayi ahannunta yana samata had'e da cewaf


"U're not serious Basmah, kin manta da abunda likita yafad'a makine har kike tunanin bazaki jeba" yana gama fad'ar haka ya d'auki makullan motarsa tare da kashe kayan kallon sannan yarik'o hannunta yajata suka tafi,


Tun akan hanya yakira dr dake dubata yasanar dashi gasunan tafe don Allah yayi maza yazo inbaya asibiti, cikin sa'a kuwa yace "sai sunzo yana nan" yana kashe wayar yajuyo yana kallonta ya dafe kansa tare da dukanta starring motar yace


"Kinga yanda ma kika kumbure ga wani haske kinyi? Mtsss Alla yasa ba jinine bakida ba" sake turo d'an bakinta tayi had'e da cewa


"Nifa nagaya maka lafiyata klw, kadena yimun jaye jayen ciyo"


Har zasu wuce tahango mai guiva tace


"Laa yaya hango guiva acan, don Allah ka tsaya kasiyamun zansha" harararta yayi don shi gaba d'aya hankalinsa yagama tashi inba wajen aikinsa yaje yajawowa yarinyar nan tashin ciwonta ba, tunda likita yace kada yabari tayi abunda zata wahala yasa har zuciyarta tadinga harbawa da sauri da sauri, nunata yayi da hannu kafin yace


"Ke ko?, wato inata lafiyarki amma ke tawani guiva kikeyi, to bazan siyaba" kad'a starring yadingayi da hannunsa yana fad'in "oh my God, ammafa komai ahankali naje dashi how come"


Ita kam da haushin rashin siya mata guiva yakamata fita batunsa tayi tajuyar da kanta gefe tana kallon titi harda 'yar k'wallarta a idanuwa,


Suna isa kallo d'aya dr. Yayi mata yace


"Ah..alhamdulillah, lallai madam tasamu sauk'i sosai, we have seen alot of progress"


"Haba dr kamarya, tafi sati biyufa tace tana fama da zazzab'i duk daren Allah, kuma dubi kaga yanda tayi wani haske kamar marar jini gashi duk ta kumbura, pls dr don Allah kayi mata checkup akan matsalarta kagani ko lafiya take, wlh inajin tsoro sosai"


Murmushi dr yayi kafin yayi mata 'yan tambayoyi tana bashi amsa sannan yakira wata nurse yace suje a d'ibi jininta da fitsari, kuma akawo masa result yanzu yanzu"


"Ok" tafad'a tare da cewa Basmah "muje ko?" Sannan tamik'e suka fita.


Kallon Mahmud yayi da duk yabi yatada hankalinsa yace


"Calm down my friend! your wife is ok in sha Allah, ba kumburine tayi ba kuma tanada jini don haka ka kwantar da hankalinka"


Bayan kamar minti ashirin sai gasu sun dawo nurse d'in biye da ita abaya, dr tamik'awa result d'in sannan tajuya tafita, d'ago kai dr yayi bayan yagama karanta takardar ya kalli Basmah had'e da tabbatar da zagin da yakeyi akanta sannan yaba Mahmud hannu suka gaisa yace


"Congrat malam Mahmud, ur wife is pregnant har na tsawon wata d'aya da kwana uku" wani dmmm yaya Mahmud yaji had'e da cewa dr


"Are you serious?"


"Yes confirmed" yamik'a masa takardar, karb'a yayi yana karantawa tare da yiwa Allah godiya, ita kuwa gaba d'aya farincikin dake kwance a fuskarta yabayyana, azuciyarta kuwa girmama ikon Allah takeyi daya yimata wannan baiwa da ni'ima alokaci d'aya, shikanshi Mahmud mamaki yakeyi ace sau d'aya abu har ciki ya shiga tabbas Allah shiyake tsara komai ayanda yaso, dama wannan rabonne dake tsakaninsu ya haifar da fasuwar aurensa da Billynsa? Godiya yayiwa likita sosai bayan yabasu 'yan shawarwari akan yanda zai kula da ita, da kuma yanda zasuyi renon cikin, Sannan suka bar asibitin kowa da abunda take sak'awa azuciyar.


Wajen mai guiva da tace yasiya mata d'azu ya tsaya ya saye gaba d'aya kwandon sannan suka nufi hanyar gida, tun amota yakira yaya Mahmud yayi masa albishir 'yar uwarsa na d'auke da ciki har na tsawon wata d'aya da kwana ukku, 


"Allahu akbar, Allah sarki wato wannan dalilin shine yajawo rabuwarku da my sister" abunda yaya Mahmud yafad'a kenan kafin yafara taya d'an uwan nasa murna, sosai yayi farinciki da yimasu addu'a sannan yace yaba Basmah wayar,  juyowa yayi yana kallon yanda ta daddage sai famin cin guivar ta takeyi hankali kwance yayi murmushi had'e da girgiza kai kafin yace masa


"Sorry d'an uwa she's too busy, yaron naku har yafara sanyata 'yan ciye ciye anjima mayi waya" yana gama fad'a masa ya katsiye wayar, murmushi yaya Mahmud yayi yana kallon screen d'in wayar kafin yafara kiran 'yan uwa da abokan arzik'i yana sanar masu da zancen, Bilkisu kad'ai yaji bayada courage d'in fad'awa wannan maganar  don haka kawai ya tsinci kansa cikin jin kunyar tunkararta da ita,


Ummice da kanta takirata take sanar da ita zancen wanda tana zaune batasan lokacin data mik'e tsaye ba, ada tana kallon duk abunda yafaru amatsayin mafarki amma yanzu ta tabbatar da cewa gaskiyane, runtse idanunta tayi hawaye suka zubo mata a idanuwa kafin tashiga yiwa 'yar uwarta fatar alkhairi da kuma Allah ya sauketa lafiya, yau dai duk k'arfin zuciyar Ummi da kuma basar da al'amarin da takeyi saida ta tausayawa 'yarta don ta tabbatar da cewa kuka takeyi, rarrashinta tashigayi tare da cewa bai kamata ace tana bari shed'an na bijiro mata da wata dangantaka data tab'a faruwa tsakaninta da mijin 'yar uwar taba har yasa tana shiga damuwa tunda ita ta yankewa kanta wannan hukuncin da kanta, tayi hak'uri in sha Allah Allah zai dubi zuciyarta ya zab'a mata abunda yafi zama alkhairi agareta don haka ta manta da komai ta fuskanci karatunta.


Haka kuwa akayi nan take Billy taji komai yakwanta mata azuciya, kiran Basmah tayi da Mahmud pilot ta tayasu murna tare da fatar Allah ya inganta ya sauketa lafiya, gaba d'ayansu duk saida sukaji ba dad'i alokacin yayinda ita kuma cikin farinciki tare da jin dad'i ta tayasu murna badon wani abuba,


Duk wanda yaji labrin cikin Basmah cewa yake ashe rabone yahana aurensa da Bilkisu Wanda dama haka yake rabon wani na danne wani koma yasa arasa gaba d'aya.


Mahmud kuwa tuni ya lullunka kulawar da yakeba Basmah ada saboda samun cikakkiyar lafiyarta da ita har baby, ga Ummah da ko yaushe take tsaye wajen nemawa Basmah duk wani abun k'walame k'walame da zata nema, ko kad'an babu wata damuwa atare da ita tana samun kulawa takowane b'angare sosai kuma yanda yakamata, yaya Mahmud ma da Batoo da Billyl kusan kullum suna yimata kira fiye da uku don d'ai suji ya lafiyarta da kuma ta unborn d'insu,

 

Ita kuwa Billy ta tattara komai ta ajiye gefe amatsayin tarihin da bata son tunawa ta maida hankali ga karatunta duk da har yanzu ak'asan zuciyarta akwai zazzafar k'aunar yayanta aciki, tafe  take tafito lecture itada k'awarta husnah kawai sukaga anyi parking da mota ta gabansu,


"Ke zo nan" sukaji wanda kecikin motar yafad'a, kallon kallo suka yiwa juna kafin Billy tayi yunk'urin rab'awa tagefen motar zata wucewa, da sauri husnah tarik'o hannunta had'e da cewa


"Don Allah Billy kirufa mana asiri, malam jika ne, kuma kinsan halinsa wlh mugune bayada mutunci, pls tunda kinga ya nace maki yana nema yahanaki shaqat acikin makarantar nan to kisauraresa kiji abunda zaice don Allah kinji?"


Juya idanuwanta gefe tayi had'e da cewa, "husnah wlh bana son kula kowa ayanzu, zuciyata tana buqatar hutu fiye da tunaninki, idan natsaya na sauraresa tamkar na cutar da kaina ne, wlh ahima yafiye nacin tsiyane, ace kimanin watana uku da shigowa makarantar nan mutum na bibiyata ya kasa k'yaleni"


"To yazakiyi!? shifa babban malamine, narok'eki don Allah da kitsaya ki sauraresa, bari inje canteen injiraki" husnah tawuce tana waigenta.


Ganin ta tsaya ba tare data motsa daga inda takeba yasa malam jika yafito cikin motar, mutumne mai matuk'ar kamala a idanuwa duk dako d'alibai nayi masa kallon mugu marar mutunci, kallonta yayi tun daga sama har k'asa kafin yace


"Bilkisu Bashar maifulawa ko?" D'ago kanta tayi itama ta kallesa kamar yanda yayi mata kafin tace


"Yes my name"


"Kin burgeni gaskiya, Ina son mace marar tsoro"


"Ni kuma ko kad'an baka yimunba don natsani namiji mai naci"


"Da gaske?"


"Da dawasa?" Murmushi yayi don shikam gaba d'aya son yarinyar yakeyi da gaske kuma a shirye yake yayi komai akanta


"Bilkisu, sunana alhaji lawan amma amfi kirana da malam jika, ni malamine anan makarantar, bana d'agawa kowane d'alibi dake wasa da karatunsa, kuma Ina quntatawa d'aliban da duk suke nuna su wata tsiyane acikin wannan makarantar, wannan dalilinne yasa sukayi mani lak'ani da mugu kuma macuci, inada mata d'aya da yara uku, tun ranar da kikazo makarantar nan naji Ina sonki kuma nayaba da hankalinki, sosai nayi sha'awar aurenki a matsayin matata tabiyu idan kin amince nayi alk'awarin zan kula dake har iya k'arshen rayuwata, wannan dalilin kawai yasa nake bibiyarki amma kikak'i saurarona"


"Kayi hak'uri, nafahimceka kuma nagode da soyayyar ka, amma zuciyata bata muradin wani atare da ita, tana buk'atar hutu sosai don haka kayi hak'uri" tana gama fad'ar haka tarab'a ta gefensa tawuce abunta.

 

Yajima wajen atsaye cike da mamakinta kafin yace "Hmm! Muje zuwa in sha Allah sai na mallake ki amatsayin matata"...

 






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Gaisuwa tare da fatar alkhairi agareku *Nana Hauwa'u, Aisha abubakar* and also once agains to you *Jaanatusanikaka* a gaskiya inajin dad'in yanda kuke comment littafinnan cikin fahimta tare da fad'in ra'ayoyinku akai abun nak'ara mani k'warin guiwa sosai especially you jaanatu sai nakeji tamakar debating ne mukeyi akan abu d'aya da ke kike supporting ni kuma nake opposing, nakanji nishad'i sosai akan hakan, ngd sosai ina fatar Allah yakai amincinsa agareku aduk inda kuke kuma yabarmu tare🤝🏻_


💎Page_____95💎


   

 Gaba d'aya wunin ranar yini Billy tayi ranta ab'ace, koda suka koma hostel haka zainab tasata agaba tana tambayarta ko lafiya taga gaba d'aya yau bata cikin walwala,


"Babu komai 'yar uwa am just borring da wancan malamin kenema ya takurawa rayuwata, yasani tunowa da memories d'in da nake neman shafewa arayuwata?"


"Wa kenan 'yar uwa?" Zainab tafad'a tana k'ok'arin d'ora tukunyarta saman d'an k'aramin gas d'in dake can gefen d'akin nasu, tsaki Billy tayi kafin tace


"Wa kuwa Inba malam jika ba, wai harda wani yana son in zama matarsa ta biyu, kijifa!, Ashe yana da mata yake zaman b'ata lokacinsa wajen bibiyata instead of yaje ya bata kulawa" dariya zainab tayi had'e da cewa


"Maza kenan, ai indai sune sunfi da haka, kedai kawai kiyi addu'a kuma kiyi abunda yakawoki dt's all"


Tsaye take ta rakosa abakin bakin mota tana hawaye, kallonta yayi bayan yabud'e motar ya shiga had'e da cewa


"Basmah don Allah kidena kukan nan haka!, Bana son kina shiga damuwa ko kad'an, pls badon niba ko don albarkacin abunda ke cikinnan naki kiyi hak'uri, in kin lura na shanye hutun dana d'auka wajen aiki amma saboda rashin lafiyarki na sake komawa na d'auki excuse wajen kuma aka bani, yau gashi almost one week fa kenan da k'arewarsa ban koma ba, ko kinfiso akoreni indawo gida in zauna" Saida tagoge hawayen idonta sannan tace


"No..no at all" 


"Yawwa to kokefa, kinga kiyi zamanki wajen Ummah nasan zata kula dake fiyema da yanda zanyi kinji"


"Shikenan yaya, Allah yatsare hanya kuma ya saukeka lpy, nida little d'inka zamuyi kewarka sosai" tafad'a tana shafa d'an tummy plat d'inta da har yanzu bai fara fitowa ba,


"Nima zanyi kewarku, pls ki kula mana da little d'inmu kuma kidinga cin abinci sosai kinji ko?"


"In sha Allah yaya" fitowa yayi had'e da jawota ajikinsa, da sauri tafara k'ok'arin jaye jikinta daga rik'on da yayi mata tare da duba gefe gefen da suke tsaye tana fad'in


"Pls yaya cikani kada Ummah ko alhaji sufito su ganmu ahaka"


"Kibarni mana ko d'iminki dana little inji kafin natafi, kin fiye raki da yawa Basmah, badon haka ba dana d'aukeki mun koma gida," zaro idanuwa tayi kafin tace


"Gida kuma yaya? Mezamuyi acan kai dake kan hanya?"


"Basmah kema kinsani dole inada buk'atarki, tausayin halin da kike ciki kesa bana son damunki, shiyasa kikaga tun ranar har yanzu ban sake kusantar kiba, don Allah kibani dama Basmah ko sau d'aya ne?" Sosai tausayinsa ya kamata, ita kanta tasan yanada matuk'ar hak'uri, kimanin watansu biyu kenan da aure amma sau d'aya suka tab'a had'a shimfid'a har aka samu abunda ke cikinta kuma duk yana hak'urine saboda rashin lafiyarta, amma ya zatayi ita kanta idan tace bata buqatarsa tayi k'arya kawai tana daurewane don ita kad'ai tasan yanayin da ranar tashiga tana tsoron sake faruwar haka shiyasa itama take nesa nesa dashi, jin tayi shiru yasa ya rik'o hannunta yana murmushi yace 


"Kada kidamu kinji, dama da wasa nake yimaki, amma promise me ranar dana dawo zaki bari ingaisa da my little?" Rufe  fuskarta tayi had'e da cewa


"Am sorry yaya, in sha Allah yanda duk kake so hakan za'ayi, Allah dai ya dawo dakai lpy"


"Amin ya Allah Basmah" yafad'a tare da kissing d'in goshinta sannan ya koma cikin motar ya tayar ya wuce yana yimata bye bye horn,


Tuni itama faraaha da dr Ahmad sunjima da komawa bakin aikinsu tun bayan aurensu da sati biyu, inda faraaha itama ke d'auke da cikinta d'an kimanin wata biyu da sati uku, a b'an garen Batool kuwa har yanzu batada komai, kuma hakan bai dameta ba da ita har Ahmad d'inta, soyayyace mai k'arfi da k'aunar junansu da kuma kulawa ta musamman suke yiwa juna, ga muhib d'in mamy shima yak'ara wayau da girma sosai kamar bashiba don ba kad'an madarar da yake sha takarb'esa ba, kamarsa kuwa da mahaifiyarsa sai dad'a fitowa takeyi, watansa hud'u kenan amma har ya iya zama yana koyon rarrafe,


Jaddi kam hankalinsa ya kwanta, kullum cikin farinciki da jin dad'in yanayin kwanciyar da jikanyarsa keciki yake, wasu lokuta da dama idan yazo wajen papi yakan biya yadubo lafiyarta wanda hakanne ya tabbatar masa da tana cikin kwanciyar hankali, gashi tayi kyau sosai kuma tayi k'iba saboda yaron cikin dake jikinta, ko kad'an bata wani shan wahala wajen renon cikin don wataran har mantawa take dashi ajikinta saboda lafiyarsa, ga kula da tausayawa da take samu wajen yaya Mahmud abun ko magana ba'ayi,


Yaya Mahmud ne tafe cikin motarsa ya d'auko faraaha wajen aiki kawai saiga wasu macce da namiji aguje anbiyo ana jifarsu sun fad'o masa agaban mota wanda badon yayi k'ok'arin tada burki da sauriba da gaba d'ayansu ya bugesu, da sauri ya fito cikin motar yana ba mutanen da suka biyosu hak'uri duk sun jejjefesu sun jimasu ajiki, cikin girmamawa yaya Mahmud ya kalli wasu dattijai maza guda biyu yace


"Baba don Allah ina rok'onku a matsayina na d'a agareku da kuyi hak'uri kuyafe masu, duk da bansan laifin da suka aikata maku ba amma ina rok'onku da kuyi masu afuwa, watak'il hakan zaisa sugyara kuskurensu nan gaba" cikin b'acin rai d'aya daga tsofaffin yace


"Yaro kabarmu  mu illata wud'annan karnukkan, sunjima suna shigowa anguwar nan suna d'ibar mana yara 'yan mata suna b'ata su da shaye shaye da sauran fasik'anci da sunan abota, don haka muka yanke shawarar cimaau mutunci da kuma kai k'arshen iakancinsu a anguwar nan" Shiru yaya Mahmoud yayi tunawa da yanda rayuwar k'awaye shima taso b'ata masa rayuwar 'yar uwa kafin yajuyo zai yima wud'an da aka biyo suma fad'a da nasiha, mezai gani qawar Basmace Suby da kuma saura yinta Babs, suna ganinsa suma jikinsu ya hau rawa don lokacin babu bid'ar da baiyi masu ba akan abunda suka yiwa 'yar uwarsa,


"Suby, Babs..dama har yanzu kuna cikin garinnan?" Cikin jin haushinsu da tsanarsu ya juyo yana kallon tsofaffin yace 


"Shikenan baba duk abunda kukaga ya dace dasu zaku iya yimasu Allah yasawak'e" yakoma warsa cikin motarsa ya tayar ransa ab'ace, kallonsa faraaha tayi don duk abunda akeyi tanaji kafin tace


"All I have meyasa ka kasa taimakonsu bayan nasa zaka iya haka"


"My faraah wato nadad'e ina neman wud'ancan mutanen saboda su sukaso b'atawa Basmah rayuwa ada, badon Allah yakareba da tuni rayuwarta ta muzanta tasanadiyarsu, waccan da kika gani k'awartace, shikuma d'ayan saura yinta, wlh da alokacinne nahad'u dasu yanzu babu abunda zai hana inkakkaryasu kuma Inaa akullesu, don banga amfanin abunda suke aikatawa ba" duk wannan bayanin da yake yimata yna kallon yanda ake dukansu ta madubin motarsa, reverse yayi daidai lokacin da Basmah ta gama cemasa


"Kayi hak'uri mijina, tunda gashi kaga k'arshensu Allah yanuna maka, kabi alkhairi da mummuna don Allah kataimakesu kada kabarsu a hannun mutanen can don zasu iya kashesu lura da yanda duk jikinsu yayi jinajina amma sukak'i k'yalesu, kataimakesu hakan zaisa suma sugyara halayyarsu" dama tuni shima yaji tausayinsu kawai b'acin Raine ya rufe masa ido, saida yakai dazai wajen sannan ya sake tsaida motarsa yafito, hak'uri yayita ba mutanen kafin yasamu da k'yar su hak'ura su k'yalesu, bayan sun buga masu warning akan kada su sake ganinsu cikin anguwar basu ba yaransu, faraaha ce tafito ta rik'a suby shikuma yarik'a Babs suka sakasu cikin mota suka kaisu general hospital, kud'i yaya Mahmud yaciro ya mik'awa Babs dake jin jiki yace


"Ga wannan kubiya kud'in magani, ubangiji Allah ya shiryeku" cikin kuka suka dinga yimasa godiya, Suby tace "yaya Mahmud Mungode, daga yau bazamu sake aikata maka mancin wannan kuskuren ba, don Allah Kabani lambar Basmah in rok'eta itama tayafe mun" kwalo idanuwa waje yaya mahmud yayi kafin yace


"What? Lambar Basmah?, u're not serious, kije tayafe maki amma keda lambarta har abada, kuma ni don Allah nataimake ku don haka basai kinyimun godiya ba, kud'i canza rayuwarku don ita duniya batada tabbas" murmushi faraaha tayi domin komai na rayuwar mijin nata daban yake acikin mutane, hannunta yarik'o suna tafe tana kallonsa, ahankali tafurta masa "I luv you so much mijina"


Juyowa yayi tare da rufe idanuwansa yabud'e sannan yace


"I luv you too"


Kai tsaye gidan papi suka sauka yana zaune shida babynsa a palour suka shigo bakunan su d'auke da sallama, har k'asa faraaha ta duk'a ta gaishesu kafin tawuce ta zauna saiti k'asan k'afafuwan hajia kaka, shi kuma yaya Mahmud hannu ya mik'awa papi suka gaisa sannan yagaida hajia kaka ya wuce kitchen yana fad'in "Babyn papi me kika dafa yau in samoma tawa babyn don da alama yunwa takeji"


"Kai dallah ja can no nagaji da faman yimaku girki inkaji haushi ka auro wata tunda wannan aiki takeyi?" Hajia kaka tafad'a cikin raha da ban dariya


"Oh'oh hajia kaka rufamun asiri, duka duka ni nawane da zaki kiramun ink'aro aure, naga dai wasuma sarakunane amma mata d'aya kedasu balle ni" 


Dariya papi yayi kafin yace "bakayi k'arya ba, amma nima can inada wata matar, rud'in duniya ya d'ibeta, tagujeni tunda na ajiye masu sarautarsu, badon haka ba ai nida kake gani nan saidai ka kirani mijin mace hud'u harda k'wark'wara" ita dai faraaha kanta naduk'e ak'asa ta kasa cewa komai Saida hajia kaka ta dafa kanta tace "'yar tsohuwa uwar d'and'ana mezakici akawo maki, don wancan mijin naki d'an banzar surutunsa bazai bari yaje ya kawo maki abunda zakici ba" d'ago kai faraaha tayi tana murmushi had'e da cewa.


"Indai tsufane nabar maki hajia kaka, saboda nalura so kikeyi da k'arfi da yaji sai kinsa mijina ya dena yayina kamar yanda ya dena naki"


"Aw..haka kikace?, Shikenan gamu gani indai mommodu ne" daidai lokacin yaya Mahmud ya iso wajen hannunsa d'auke da plate da dambun masara yasha zogale aciki ya zauna gabanta had'e da cewa


"Baby zaki iya cin wannan?" Faraaha da har yawunta sun tsinke da sauri ta d'aga masa kai tare da karb'ar plate d'in a hannunsa tafara ci, 


Ko kad'an bata takura kanta agabansu domin sun bata fuskar da zata iya kallonsu suma amatsayin jaddi d'inta.


Tasowa Mahmud yayi had'e da zaunawa tsakanin papi da babynsa  sannan yace


"Papi na tambayeka?"


"Allah yasa nasani malam mahmudu"


"Wai ya akayi kadawo nan garin da zama bacin mom tafad'a mun cewa ku 'yan asalin garin kanone a wata k'aramar hukuma da kaike sarautar garin"


"Tab ai wannan labarine mai tsawo amma bari nabaka kad'an daga ciki, sarautar da kaji mom d'inka tace nayi, sarau tace mai had'ari wacce na gajeta awajen mahaifina shi kuma ya gada awajen nashi mahaifin, kasancewar munada yawa awajen mahaifinmu yasa sai kujerar tazama abun rigima atsakaninmu wacce daga k'arshe ni Allah ya mallakawa ita, rigingimu da fitintinun da sukayi yawa ga tsaface tsaface da surk'ulle da akeyi duk akan kujerar ana neman salwantar mun da rayuwata data iyalina yasa bayan waau ahekaru da naga abun yayi yawa nayanke shawarar ajiye mulkin sarautar don gaba d'aya 'yan uwana sun kasa yimun mubaya'a, babu abunda ke gabansu irin sukauda rayuwata adoron duniya don su samu su mallaki wannan kujerar, Wanda adalilin hakan matata ta biyu tace ita bazata iya da abun kunya ba indai saina ajiye sarautar nan dole inbata takardarta, ni kuma alokacin babu abunda ke gabana illa inceci rayuwata data iyalina saboda matsaloli da jefe jefen da akeyomun, don ma Allah ya taimaka ina kula da ibadodina yanda ya kamata tare da addu'o'in tsari shiyasa basuyi nasara akaina ba, nan take narubuta takarda zuwa ga babbar masarauta cewa na ajiye mulkina bisa wasu dalilai nadaban don haka abama wani, ita kuma dama Allah bai bamu k'aruwa a tsakaninmu ba saboda yanda ta fitineni sai na sawwak'e mata sannan da taimakon aminina wato mahaifin dadynka wanda shine silar had'a dadyn naku tare da mom d'inku nadawo nan garin nayi zamana nida babynah wannan shine tak'aitaccen dalili da kuma tarihin ajiye sarautata, bana son fitina kuma bana son inyi duk wani abu da zaisa inyi shirka da Allah shiyasa nayi haka, kuma alhamdulillah wannan rayuwar da nake ciki tafimun rayuwar mulkin sarautar da nayi"


Jinjina kai yaya Mahmud yayi had'e da cewa "Allah kasa ingadoka papi wajen gujewa rud'in duniya da kuma taka tsantsan da rayuwar cikinta, kuma Allah yasa in gado ka da wannan halin na rik'o da addininka papi"


"Mahmud ai kayo gado fiye ma dani, Allah dai yayi maku albarka" gaba d'aya suka amsa da amin har da hajia kaka da wannan labarin yasata tunowa da wasu abubuwa da suka faru ta share k'wallan da suka zubo mata ga idanuwa, Basu bar gidan ba har sai bayan sallar magrib sannan suka tafi cike da shauk'in k'aunar kakannin nasu, ba komai kesa yaya Mahmud son zuwa gidan nasu papi ba tare da faraaha illa don su koyi wasu abubuwa masu ma'ana akan zamantakewar rayuwar auratayya domin suma suyi koyi dasu har zuwa k'arshen rayuwarsu


"Bilkisu, Bilkisu!" Billy taji ana faman kiran sunanta a bayanta, lokacin tana k'ok'arin shiga lecture 10am-12am, sanin ko muryar waye yasa tabasar tare da cigaba da tafiyarta, da sauri malam jika yaci gabanta yana fad'in


"Haba Bilkisu tah! Don me zaki wofantar danibayan kinsan ni d'in mai k'aunar kine" sanin idan ta tsaya yimasa musu zai iya jawo mata asarar wannan lecture yasa tace


"Kayi hak'uri mlam yanzu inada lecture, idan nafito sai muyi magana" bata jira mezai ceba da sauri tana had'awa da d'an gudu gudu tabar wajen.


Shikuwa Mahmud pilot tunda yakoma bakin aiki bayada aikin daya wuce tunanin Billy, wani zubin sai ya gama zai koma jin hauahin kansa tuna cewa ita bata damu dashi ba tunda har ta iya rabuwa dashi batare da tunanin komai ba, don haka dole shima ya manta da ita ya rungumi wacce Allah yabashi amatsayin mata, Yana yawan kira akai akai  don yaji lafiyar Basmah da kuma little d'insa haka kuma Ummah nakula da ita yanda ya kamata, yau kimanin watansa hud'u kenan da tafiya amma ko sau d'aya baiyi tunanin dawowa ba, gashi har cikin Basmah yamik'a wata shida, sosai cikin yayi mata kyau kuma babu wata matsala da taka facing akansa, ummah ce da kanta kekaita asibiti a ranakun awo kuma sudawo tare, babu abunda ke damunta don tana samun kulawa yanda ya kamata kuma tanajin muryar masoyinta fiye da sau uku arana don haka hankalinta ke kwance kuma tanata renon cikinta.


Ranar da cikin Basmah ya  cika wata bakwai aranar kamfanin da yake aiki suka turasa a branch d'insu dake k'asar India kuma sai yayo wata biyu kafin yadawo, ko kad'an baiso haka ba, don yaso ace yakoma gaban iyalinsa ya taimaka mata wajen renon cikin amma duk hanyar da zaibi koda kwana biyu abarsa yaje yayi sunk'i bari, sosai ransa yab'aci har saida su Ummah da alhajinsa suka yita rarrashinsa akan yayi hak'uri yaje sannan ya amince koshi Saida Basmah ta tabbatar masa da yaje babu wata matsala in sha Allah don motsi kad'an idan tayi su umma nakula da ita kuma bayan haka ai watan da zai dawo shine watan haihuwarta don haka ya kwantar da hankalinta zai iskota lafiya ita da little d'insa, sai alokacin yasamu natsuwar yin tafiyar amma yasa aransa bazai cike wata biyu acan ba zai dawowarsa don yafiso Basmah tahaihu Yana nan.


Yana gama waya da ita sai yaji kawai yanada sha'awar Kiran Bilkisu, bai jira me zuciyarsa zata fad'a masa ba kawai ya dannawa lambar wayarta kira lokacin tana kwance tana tunanin bawa malam jika dama saboda yanda yabi yatakura rayuwarta kota samu tahuta. Ko kad'an batayi niyar taahi ta d'aga wayar ba saboda yanda take enjoying kwancin da tayi amma kamar antsikareta tamik'e tare da d'auko wayar dake jikin socket tana charji, ganin lambar wanda ke kiranta yasa gabanta fad'uwa, amma hakan bai hanata d'aga kiran cikin sauri ba kafin ya tsinke hannunta narawa ta kara akunne had'e da cewa..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____96💎



  "H..he.hello" yanda yaji tafad'i hello d'in cikin i'ina shiya bashi dariya yace


"Hello 'yar uwa" ajiyar zuciya ta sauke kafin tace


"Yaya Ina wuni?"


"Lpy klw, Bilkisu kina lafiya?"


"Alhamdulillah, yaya ya yayyatah lfiya take"


"Lafiya klw, ya karatu?"


"Alhamdulillah, ya aiki?"


"To gashi babu dad'i, yau insha Allah zanbar k'asarnan sunturani a d'ayan branch d'insu dake k'asar India"


"Allah sarki to yayya fa?" 


"Tana wajen Umma kafin nadawo"


"Allah yatsare kuma ya dawo mata da kai lafiya" murmushi yayi Yana mamakin yanda akoda yaushe k'arfin halinta da courage d'inta akansa ke k'aruwa, jin yayi shiru yasa tace


"Sai anjima yaya"


"Aw korar yayan akeyi?, Dama kwana biyu nace k'anwa ta manta da yayanta bari nakira tunda har ga tafiya ta gitto mugaisa kuma muyi bankwana"


"Ayya nagode yaya, stress d'in karatune sukayi mani yawa shiyasa, be side nasan yaya nafad'a maka cewa nace Ina gaisheka idan mukayi waya"


"Yes ofcourse, ana Kiran yayya amma banda yaya, abun banbancine kenan!"


"Noo. Bahaka ba, ai babu banbanci tsakaninku domin gaba d'anku 'YAN UWANA NE, so just keep dt word aside, just dt su su biyune kai kuma kai d'ayane, kaga at least akwai buk'atar kulawa dasu duk yanda strees yayi yawa, amma tunda nayi laifi kayi hak'uri" 'ya dariya yayi kafin yace


"Shikenan 'yar uwa, aikin kashe bakin maganar, ngd ssai sai anjima" dariyar itama tayi had'e da cewa


"Ehem, ngd yaya Allah yatsare hanya" sannan suka kashe wayoyinsu, itakam Billy har ga Allah babu wani abu da taji aranta sab'anin Mahmud da yaji wani irin farinciki, duk da dai bawani abu da yake tunani atare da ita ahalin yanzu, wayar yaya Mahmud yakira shima suka gaisa sannan yakira ta Batool, sosai yadinga tsokanarta wai taji tsoron Allah amarcin ya isa haka ta samo masu baby, tayita dariya tana fad'in sai sun gama shan bukin sunan yayya tukuna,


Ummi ma ciki ya mik'a don itama cikin wata na bakwai yake, babu inda take zuwa saboda kada aganeta da ciki, Batool kuwa randa tazo gida ta isko Ummi da ciki tsalle da ihu tayi tayi na farinciki Wanda nan take takirasu Basmah da Billy ta sanar dasu, suma can sunata farinciki da murna sunaji tamkar suyo tsuntsuwa sutaho gida, zungureta Ummi tayi had'e da cewa


"Allah ya shiryaki Batool, shikenan kinfad'a hankalinki ya kwanta ko?" Mom dake gefe tana tuyar wainar fulawa saboda da kwad'anta Ummi ta tashi yau tace


"Ah dama ai k'yaleki kad'ai nayi ban fad'a masu ba don nasan mai fayyace abun natafe ko yaushene, kinga wata bakwai Ina k'umshe da bakina amma cikin minti bakwai ta fayyace komai" hararar mom Ummi tayi had'e da cewa


"Waya sani halin d'a da mahaifi ko dama can kin b'ulguta mata zancen"


"To ai 'yar kice, idanma hakane sai inke kika shige d'aka kika fad'a mata"


"Wa? Allah yasatari buk'ui, aini Basmah ce 'yatah indai wannan ce mai guru gurun idanuwa kamar k'waruru nabar maki abukki kiyita fama, Ina zan iya da wannan iyayin na Fatima"


"To ai shikenan tunda haka kikace, kyaga mai kula maki da 'yar taki idan tadawo, muna kallonku uwa kwance d'iya kwance" mom tafad'a tana dariya, ita dai Batool sai kallonsu takeyi cike da sha'awar yanda rayuwar zamansu ta kasance gwanin ban sha'awa.


Ayanzu kam Mahmud pilot ya gama yarda cewa Basmah itace qaddararsa kuma zab'in da Allah yayi masa don ya gada imaninsa, don haka yayi imani da haka saboda tuni ya samama Basmah wani gurbi acikin zuciyarsa wanda bai tab'a tsammani ba, tsaye take tana faman har had'a wasu 'ya kayayyakinta tare da 'yan kakkab'e kakkab'e saboda yau cikinta ya shigo wata na tara kwasam saiga kiransa ya shigo awayarta dake kan madubi ajiye, murmushi tayi kafin ta d'aga had'e da cewa


"Ranka ya dad'e Abban little, barka da rana?" Shima ta tasa b'angaren cewa yayi


"Tare dake oum little naki ya dad'e har yayi k'arko, ya kike da my little d'ina?"


"Lafiya klw yaya, gashinan duk ya isheni ya shamun kai da rashin ji tun cikin ciki, gaskiya wannan babynta kwata kwata bakai ya gadoba, kuma basu yaya da sister naba, don rashin zamansa kurum yayi yawa, inaga duk Batool ce zai gado da rashin ji" 


 "Kai Basmah da gaske kikeyi?"


"Sosai kuwa yaya, baranma idan baci abinci da wuri ba, zo kaga yanda yake faman halbina yana shure shure sai kace jetli, koda yake no wander yanada iyaye Japanese amma dai ni sisternah batada irin wannan karauniyar" dariya yayi kafin yace


"Basmah kinsan wani abu kuwa?"


"A'a yaya sai kafad'a" tace had'e da k'ok'arin zaunawa gefen gado tana fad'in


"Awwshh" da sauri ya mik'e daga kwancen da yake yana fad'in


"Basmah lpy kuwa?" lumshe idanuwanta tayi tare da d'an sakin murmushi kafin tace


"Kai yaya meye kuma abu razana anan? Lafiya klw fa nake, kawai girman cikinne yayi yawa shinefa zan zauna kaji nace haka" wata irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace


"Alhamdulillah, Basmah bana son abunda zai sameki ko kad'an keda little d'ina"


"Saboda me? Ai bawa baya wuce qaddara da kuma tsarin da Allah yayo masa"


"Nasan haka Basmah, amma inajin soyayyarku araina fiye da tunaninki, babban burina aduniya baifi inga Allah ya saukeki lafiya ba"


 Karka damu yaya, in sha Allah lafiya klw zan haihu, kawai dai munyi missing d'inka sosai nida little"


"Iyyeee dama ashe k'anwa zatayi missing d'in yayanta hakan?" Murmushi tayi had'e da cewa


"Sosai kuwa Abban little munyi kewarka"


"To shikenan kuyi hak'uri very soon zandawo gareku in sha Allah,"


"Hop so yaya!"


"Yawwa Basmaty to me aka tanadarwa yaya kafin yazo?" Saida tayi daria kafin tace


"Babu komai face ni kaina, gangar jikina, zuciyata da kuma rouhina gaba d'aya" 


"Ashe dai anaji da yayan nan"


"Sosai ma kuwa kawai yakasa ganewa ne, amma k'anwarsa na matuk'ar sonsa sosai, I luv you so much" tana gama fad'ar haka takashe wayar da sauri don tunda take bata tab'a furta masa makamanciyar irin wannan kalmar ba sai yau, shiyasa nauyi da kunyarsa sukasa ta kashe wayar. Hakan daya ji yasa ya ciro wayar a kunnensa tare da kallon screen d'in wayar ahankali yace


"Nasani Basmah ko baki fad'aba, amma fad'ar da kikayi ya tabbatar mun da cewa ked'in masoyiya tace da zanyi alfahari da ita" sake kiran wayarta yayi har sau biyu bata d'aga ba hakan yasa yayi dariya tare da cije leb'ensa na k'asa sannan ya shiga text messages d'insa a waya ya rubuta .


_I LUV YOU TOO BASMATY, OUM LITTLE_  yatura mata.


Koda message d'in ya shigo wayarta tana k'wance akan gado idanuwanta arufe, hannunta tasa tana lalubo wayar had'e da d'aukowa tabud'e idonta, duk da kwance take haka bai hanata jinwani irin jiri ya d'ibeta ba d'akin nayi mata yawo, tunani tafarayi shin anya wannan ba mafarkine takeyi ba, maessage d'in tashiga karantawa tanayi tana maimaitawa fiye da sau goma kafinnan ta gasgata abunda tagani, cikin farinciki dajin dad'i tamik'e da ky'ar tare da maida gabanta gabas tayi sujudush shukur tana yiwa Allah godiya d'aya nuna mata wannan rana da mijinta zai furta mata wannan kalmar batare da  tsammanin taba, tabbas ta aminta cewa duk wanda yayi hak'uri to kome daren dad'ewa kuma duk rintsi duk wuya sai yaci ribarsa, rufe idanuwanta tayi hawayen farincikin dake lak'ame aciki suka fito sannan tace


"Ya Allah kaine mai sassaura abubuwa kuma kai kace arok'eka, Allah Ina tawassali da dukkanin ayukana na alkhairi Allah kabawa 'yar uwatafarinciki kamar yanda tabani kuma kazab'a mata miji nagari wanda zai kula da rayuwarta fiye da tunani albarkacin sadaukarwa da tayiagareni,


"Amin" taji umma dake k'ok'arin k'arasowa wajen tafad'a saboda ganin tajima ad'aki bataga fitowarta ba shine tashigo tagani shin kolafiya?


Kallonta tayi had'e da cewa


"Basmah injin lafiya najiki shiru?"


"Lafiya klw Umma alhamdulillah, ya k'ok'ari?"


"Alhamdulillah, Basmah keda wa naji kinata faman zubo addu'o'i haka?" Cike da jin kunya kanta na ak'asa tace


"Ba komai" kafin Umma tace wani abun saiga kira yashigo awayarta, girman Umma da take gani yasa takasa d'aga wayar, mik'ewa Umma tayi tafice tare da cewa "ki d'aga wayar mana kafin ta tsinke amma da zaran kin gama ki sameni a palour Ina jiranki", tanafita da sauri Basmah ta d'aga wayar, muryar Batool ce taji tana ihu cikin farinciki tace


"Yayya albishirinki aunty faraaha ta haihu gamunan a asibiti" 


"Don Allah my sister da gaske kikeyi?"


"Wlh Allah yayya dagaske  tasamu baby boy baki ganesa ba tamkar ke kika haifesa" wani irin farincikine yarufe Basmah tamik'e da k'yar tanufi palour tana fad'in 


"Allah sarki aunty faraaha, tahuta wlh Allah yaraya mana baby"


"Amin yayya karki damu saura kema in sha Allah lafiya klw zaki haihu"


"Allah yasa my sister, Ina aunty faraahar bani ita"


"An kaita d'akin hutawa kuma ba'a bari aganeta sai nan da zuwa anjima" tana isa palourn tasamu itama Umma ashe anyita kiranta awaya bata kusa saida tafito sannan tagani, tana kiran dady nan yake sanar da ita cewa matar d'anta ta haihu, nanfa farinciki ya rufesu sunaji tamkar suyi tsuntsuwa sugansu agarin kd.


Yaya Mahmud kuwa abun ba magana don bakinsa kasa rufuwa yayi sai kiraye kirayen waya yakeyi yana sanar da 'yan uwa da abokan arzik'i ni'ima da baiwar da Allah yayi masa tasamun kyautar d'ah aukutum da guda, 


Faraaha kam sai baccin gajiya takeyi saboda ba kad'an ta wahala ba kafin tahaihu saboda girman yaron don har ansa hannu akan za'a yimata tiyata sai gashi Allah gafururrahim ya sauketa lafiya, mom da dady gaba d'aya mantawa sukayi da zancen sarakkuta sai murna da farinciki sukeyi, su papi da jaddi kuwa ba'a magana don jaddi harda k'wallan farinciki yayi wai yau shine Allah yayiwa tsawon ran da yaga jinin 'yar marainiyar Allah da aka bar masa amana tun tana 'yar shekara d'aya da rabi tabbas ya gaskata cewa Allah shine maiyi kuma mai komai,


Ummi kam d'aka ta hana wuri magana, tana son ta sakata tawala yau babanta ya sama mata k'ane ta bakinta, amma ina itama cikinta da watansa takwas kenan ya hanata, duk da dai haka tata yakice kunya gefe amatsayinta na uwar d'a tana gudanar da abubun da ake buk'ata don tayiwa  mom kara, sosai faraaha taso takoma gida wajen jaddi amma sai yace tayi hak'uri ta zaunawarta gidan mijinta tunda ga hajia kaka na kulada ita yanda yakamata, dole yasa ta hak'ura don koda takoma daga ita sai jaddine agida sai kuma wata matar k'anen mahaifinta dake gidan wacce kad'anne shekarunta zasu girmi nata,


Ana gobe suna Mahmud pilot ya tattaro inasa inasa yabaro India duk da cewa da sauran lokacin da kamfani suka d'ibar masa amma haka ya tahowarsa don gaba d'aya yanzu tunaninsa na akan Basmah, wacce dama sati ukune kacal da kwanaki tsakaninta da faraaha shiyasa yaya Mahmud nafad'a masa cewa faraaha ta haihu yaji hankalinsa yakoma akan matarsa, Saida yayi dagaske kafin su amince da dawowarsa bayan sun tabbatar masa da cewa hutun sati biyu kacal suka bashi, 


Basmah kuwa rigima ta dingayi wai saitaje suna, seda dady ya kirata awaya yanata lallashinta akan tayi hak'uri har sai bayan ta haihu tunda dama bazata koma gida haihuwa ba saboda nisa ga kuma gwaggonta atare da ita sai in har Allah ya sauketa lafiya, in yaso sai akoma da ita can ayi suna" dole tahak'urabadon ranta yasoba, tana zaune tana faman tuk'uburine sai ga Mahmud yadiro palourn ba zato ba tsammani dama yace Surprise zaiyi mata, shiyasa yak'i sanar da ita zancen isowarsa, 


Tsaye yayi bakin k'ofa Yana kallon yanda tayi wani fresh tayi haske sosai kamar ba itaba gashi cikin yafito ajikinta yak'ara mata kyau, rufe idanuwansa yayi had'e da bud'ewa yana admearring  irin kyawon data yimasa kafin ya d'anyi tari tayanda hankalinta zai dawo akansa don duk ranta ab'ace yake akan rashin zuwanta suna, gashi tunda sassafe Umma tawuce abunta bayan ta tabbatar mata da cewa zata turo wadda zaici gaba da kula da ita kafin tadawo, ashe dama tuni yasanar da ita cewa yau zai dawo amma kada ta sanar da ita, shiyasa tasamu k'warin guiwar zuwa don sharabonta dataje garin tun zuwansu kafin aurensu. Koda zata wuce wata k'anwar  makwabciyarta takira tace tazauna mata kafin zuwa marece maigidanta ya iso.


Jin tarin da Basmah tayi yasa ta d'ago kai don ganin ko waye, cikin azama da k'arfin hali tamik'e fuskarta cike da farinciki tanufi inda yake shima ya nufota yana dariya had'e da bud'e mata hannuwa, da sauri suka k'arasa had'e da rungume juna yana fad'in


"Iyyee Basmaty kece kika koma haka?" tare da d'agata sama yana juyawa da ita ahankali ko nauyinta da abunda kecikin cikinta bayaji" tana dariya tadinga nuna masa k'asa da yatsanta alamun ya sauketa tagaji,  ajiyeta yayi ya duk'a yayi kissing d'in tulelen cikinta  sannan yad'ago yana kallon fuskarta, fad'awa tayi ajikinsa cikin farinciki had'e da cewa..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_*ROUHI* Kalma ce mai tsada daba kowane abu ke karb'ar sunan ba saboda sunanan abune mai matuk'ar muhimmanci acikin rayuwar kowace irin halitta, hakan yasa nakiraki da wannan suna saboda girma da kima da kuma muhimmancin da kike dashi awajena, *FATIMA TAMBARY* (BATOOL), Gaisuwa mai yawa tare da fatar alkhairi agareki k'awata, hak'ik'a ke mutunce da bazan tab'a mantawa dake ba, saboda girman soyayya da alkhairanki agareni, fatana Allah yakareni aduk inda kike kuma yabaki miji nagari wanda zakiyi alfahari dashi arayuwarki, ur *ALBIE* is always luv you so much *ROUHI*_❤💋🙈


💎Page_____97💎


   "Oyoyo abu little d'insa i missed you so much"


Hab'arsa ya aza akanta had'e da cewa "missed you too 'yar gidan ummanta" rik'ota yayi ahankali tana tattakawa har suka dawo cikin palourn ya zaunar da ita akan kujera yana kallonta,  d'an turo bakinta tayi kafin tace 


"Yaya wannan kallon fa? Shine zaka dawo ko fad'amun bazakayi ba?" Rik'e kunnuwansa yayi had'e da cewa


"Sorry oum my little, just want to surprise you"  k'afa fuwanta yashiga mammatsawa yana cigaba da cewa "Basmah halama bakya fita motsa jiki naga suk k'afafuwanki aun kumbura haka"


"Ina fita acan cikin harabar gate ind'an zazzagaya, Umma kecewa wai bazan fitaba saboda matsalar ciwona ba'a son inyi abunda zai wahalar dani har zuciyata tadinga bugawa da sauri da sauri, kumafa wlh ni naji sauk'i don har namanta yau sharabon ciwonnan daya tasammani yanzu, kaga ba wannan ba, yanzu dai katashi muje in had'a maka ruwa kawatsa kaci abinci sai kahuta" tana gama fad'ar haka tamik'e tsaye tare da d'aukar jikkar dake hannunsa, da sauri ya amsa sannan ya mik'a mata d'ayan hannunsa tarik'e yanufi hanyar zuwa d'akinsa da ita tana takawa ahankali, suna tafe suna hira tana dariya har suka isa d'akin, key d'in motarsa ya ciro da yake akwai na d'akinsa ajiki ya bud'e suka shiga, da kanta ta taimaka masa yarage kayan jikinsa sannan tashiga toilet tahad'a masa ruwan wanka don dama kullum d'akin a gyare yake don ita dakanta wataran kezuwa tana gyara masa ko ummah tatura a gyara masashi duk dako ansan baya ciki, 


Bayan tahad'a masa ruwan tafito ya kalleta had'e da cewa "ke bazakiyi ba?"  


"A'a nayi nawa tun d'azu" 


Murmushi yayi sannanya shiga yayo wankan, koda yafito ya tarar har taciro masa kayan da zaya sawa tabar d'akin, cikin mintota yagama shiryawa sannan ya nufi palon, a kitchen ya hangota tana k'ok'arin had'a masa abunda zayaci mai sauk'i tunda batasan da isowarsa ba sai d'ai tagane, kitchen d'in yashiga had'e da rungumota tabaya tare da turo kansa ta wuyanta yana fad'in


"Sannu matar yaya, me ake girkamuna" d'ago kai tayi tana kallonsa had'e da yin murmushi sannan tace


"Abunda mijin oum little yafi so" nan dai ya kama mata girkin tanayi tana bashi labarin yanda hanata zuwa bikin yaron yaya Mahmud yayi mata zafi arai, cikin tsokana ahima yace


"Nima gobe tunda safe zan wuce anma jirgi zanbi, kinga sai Ummi takira maki matar da na isko d'azu ta tayaki kwana kafin indawo duk da dai inatunanin da k'yar idan zan kwana, saboda ke"


Turo idanuwanta tayi kamar zatayi kuka tare da b'ata fuska tace


"Wai kenan ana nufin ni kad'aice bazan samu halartar bikinnan ba gaskiya ni wannan little d'in ya takurani" tak'arasa maganar cikin shagwab'a tana d'an bubbuga k'afafuwanta a k'asa,


Da sauri ya rik'eta yace "tsaya mana Basmaty kada kijiwa kanki ciwo da wasa nakeyi fa? Babu inda zanje inbar matata a wannan yanayin in sha Allah Ina tare dake akoda yaushe har zuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya" 


"Da gaske yaya"


"Eh mana, saboda haka kisaki fuskarnan taki, mureni babynmu kafin yazo, sukuma suje susha shagalin sunansu"


Haka dai sukaci gaba da soyayyasu har suka kammala girkin, da kansa ya d'auko plate ya zuba masu yakai palour ya ajiyikke ak'asa, sannan yadawo ya bud'e fridge ya d'auko gorar ruwa guda biyu, da cups sai lemon exotic k'waya d'aya, sannan yarik'ota suka dawo palourn atare. Da kansa yayita bata abaki har saida ta k'oshi sannn ya jawo sauran ya cinye, suna gamawa yaje d'akin daya san nanne mazauninta ya d'auko mata silifas a toilet tare da mayafi, rik'ata yayi ta mik'e tsaye sannan ya yafa mata gyalen tare da duk'awa ya d'aga k'afafuwanta d'aya bayan d'aya da taimakonta ya sanya mata silifas d'in tana fad'in "yaya wak ina zamuje haka"


Saida ya mik'a mata hannu tarik'o sannan suka fita ya kalleta yace


"Motsa jiki zamuje oum little, kinga yanada matuk'ar amfani gareki da kuma lafiyar abunda ke cikinki don haka ko bakyaso daurewa zakiyi muje"


Da yake saida akayi sallar la'asar zuwa k'arfe biyar suka fita, suna tattakawa ahankali yanda baza tayi saurin gajiya ba mutane sai faman kallonsu sukeyi, tafe suke suna fira har suka dawo gida,



Billy ko ranar da ake suna aranar zasu k'are zana 2nd semester exam d'insu, don haka taketa Allah Allah sugama koda da marecene tayo gida don ayi taron suna da ita, haka kuwa suna fitowa exam dama tayo shirinta ko hostel bazata komaba don tun safe tayiwa dady waya yaturo mata naziru driver ya d'auketa wanda tunda zasu shiga exam taga tahowarsa, shiyasa tana fitowa ta nufi wajen motar, har zata shiga taji ance


"Ranki ya dad'e Bilkisu tafiya zakiyine ko notice babu?" Sanin ko waye yasa tajuyo tana murmushi tace


"Sorry malam, da yakeina saurine shiyasa" cikin jin haushi da takaicin naziru daya gani yana k'ok'arin shiga gaban motar yace


"To amma shi wannan waye?" Ya nuna naziru daya gani cikin k'ananan kayansa yafito d'an gaye dashi, rausayar da kai tayi gefe kafin tace


"Drivern dadyna ne, ko akwai wata matsalane?"


"Gaskiya Bilkisu bai kamata ace kamarki driver zai saukeki gida ba,  mezai hana kizo in kaiki amotata, nan da k.d ai bawani distance bane" yatsina fuska Billy tayi ta kallesa tundaga sama har k'asa sannan takalli motarsa had'e da cewa


"Unfair" sannan tashige mota abunta tare da cewa naziru daya jima cikin motar


"Muje ko naziru"


Basmah kam tasamu yanda take so awajen Mahmoud hakan yasa daren jiya duk da nauyin cikinta tacika masa alkawari tabarahi yayi duk yanda yake so da ita, duk tausayin da yakeyimata ranar kam mantawa yayi dashi har saida yasamu natsuwa, sosai yadinga saka mata albarka yanda tajure kuma tayi k'ok'ari batare da tayi yunk'urin nuna gajiyawarta ko kad'anba har sai daya samu natsuwa.


Tunda safe yatashi ya had'a mata breakfast mai kyau wacce ta dace da ita, bayan ta kammalaya taimaka mata tayo wanka ta gyara tsaf cikin wata doguwar riga dark purple yayi mata rolling kanta da white d'in mayafi sannan shima yashiga yayo wanka yasa k'ananan kayansa riga purple da wando jeans fari sunyi matuk'ar kyau, sannan ya d'auko mata 'yan plat shoes marassa nauyi suma farare ya duk'a ya samata sannan yarik'ota suka fito, sai daya bud'emata gaban mota tashiga sannan yakoma ya kukkulle ko Ina yadawo ya tayar da motar suka fita, wani k'ayataccen wajen hutawa ya nufa suka yada zango acan, tunda k'arfe goma har zuwa magrib acan suka wuni kuma sukaci abincin su sunayi suna hotuna,  


Maijego faraaha kuwa tuni yaya Mahmud da dady suka bud'e bakin aljiffansu suka narka mata kaya ita da jinjiri naji da fad'i, hatta mom da Ummi ma ba'a barsu abaya don suma sun nuna cewa sunyi sabon maigida, Billy na dirowa kai tsaye gidan Batool dake cantana jiranta tace a sauketa, dama tuni d'unkunan da zasu saka and'unke masu, tana zuwa wanka kad'ai tayitasa kayanta suka nufi gidan yaya Mahmud, acan suke iske Hindu him's touch tazo yiwa farahaa kwalliya ana gama mata suma akayimasu nan take suka amshi jaririnsu da aka rad'awa sunan mahaifin faraaha daya rasu wato Ibrahim amma ana kiransa da MU 'AZZAM, Suka fara kashe selfie suna turawa Basmah ta WhatsApp, lokacin suna zaune ita da Mahmud can wajen wasu flowers yana nunnu na matasu da hannu yana fad'a mata sunayensu ita kuma ta d'ora kanta a saman kafad'arta.


Kallonsa tayi had'e da cewa "yaya idan Allah ya saukeni lpy kuma nasamu baby girl wane suna zaka saka mata" hannunsa yasa ya shafo fuskarta had'e da cewa


"Wannan zab'in kine"


"Kenan duk sunan da nakeso zaka sanya mani shi?"


"Ofcourse, ammafa idan namijine wannan yarage zab'ina kin amince?"


"Meyasa kace haka?, Mace da namiji duka ba d'aya bane?" Dariya yayi kafin yace


"Duka d'ayane amma naga ke kika tsaya selecting idan macece kike son kisaka mata suna, shiyasa nikuma nace nizan saka suna idan namijine, da ace kinbarsa akan kome aka haifa da nace kisa duk sunan da kikaga yadace ga abunda Allah yabamu"


Wayar tace dake cikin aljihunsa tafara rurin neman taimako, cirowa yayi had'e da duba lambar da aka kira, _My sister_ yaga anrubuta, hakan yasa yagane cewa Batool ce, d'aga wayar yayi yakara akunnensa had'e da cewa


"'yan buki mashaya gara, lafiya ake kiramun matata, ko don arikitamun itane don bata zoba?"


"Hmmm ai wlh yaya, baby mu'azzam yayi fushi, ace gudan mmansa batazo ba kuma kaima baka zoba, ai hark'ara yayya ana yimata uzuri ko don saboda unborn d'inmu amma kai kam..hmmm!"


"Nikam me Batool?, Kinaso inzone inbar yayyad'inku ita kad'ai bacin Umma ta tsere tunda tasamu maigida tabar mun matata ita kad'ai?"


"Afuwan nidai yaya ba yayya wayar muyi magana kafin kud'ina suk'are" kara mata wayar yayi har lokacin kanatana saman kafad'arsa tace


"Hello my sister" cikin fara'a da jin dad'in muryarta da taji tace


"Na'am yayya, ya kike ya unborn d'inmu?"


"Lfy klw, gashinan ya gadoki da mugun rashin ji, sai faman shurina yakeyi aciki"


"Ayya sorry ko? Kema soon kinkusa bamu abunmu ahannu sai kihuta"


"Aikuwa dai ba wani srry idan ya damini nima ramawa nakeyi, to da yaji nabugesa sai kiji ya natsu, ya shagalin buki"


"Alhamdulillah, not sweet with out you yayya, baki ganmu ba nida my twiny we have being so lonely"


"Ayya, Ina sisto d'in take?"


Gatacan tana gyarawa baby mu'azzam, da sauri ta mik'e had'e da kaiwa Billy dake sauyawa mu'azzam kaya zuwa masu d'an nauyi saboda sanyin marece daya fara sauka,


"Ungo twiny ga yayya"


"Hello yayya barka da marece, ya kke ya unborn?" Billy tafad'a tare da aza baby mu'azzam akafad'arta tana murmushi


"Lafiya klw my sisto just missing you, kunata shagalinku bani" dariya tayi sannan tace


"Sorry yayya situation d'inne yazo a haka, muma munyi missing d'inki here"


"Ya karatu ko ince exam"


"Alhamdulillah yayya ba dad'i wlh, ai munk'are exam yau"


"Kice kunyi hutu, pls sisto don Allah kizomun kizauna har inhaihu sai mudawo tare gida kinji" turo idanuwa Billy tayi awaje had'e da cewa


"Yayya rufamun asiri continue semester ce, zuwa jibi zan koma in sha Allah"


"Kai sisto"


"Allah da gaske nakeyi, kibari aini zan tayaki renon baby idan zaki koma bayan kin haihu don wajen Umma zamuyi hutu nida zee"


"Shikenan Allah yakaimu"


"Amin yayya, Allah yasaukeki lpy kuma yabamu healthy baby mai kama dake?"  Dariya Basmah tayi had'e da kallon fuskar yaya Mahmud dake latsar wayarta tace


"Sedai mai kama dake da yayanki, nikam abari sai nayi wata nan gaba abani mai kama dani" juyowa yayi yana kallonta yanamurmu shi kafin yace


"Meye laifin idan Babyn yayi kama dak"


"Babu ko d'aya, amma nafiso team d'insu baba k'arami suk'ara yawa don sune jefi jefi acikin family" dariya Billy dake jinta tayi had'e da cewa


"Yayi kyau ai kamar kinyi a kunnensa saina fad'a masa"  itama 'yar dariyar tayi kafin tace "menayi ai gaskiya nafad'a"


"Shikenan ai kowa yayi zagi akasuwa yasan da wanda yake, idan ma Babyn yayi kama damu babu komai rayayye dai muka fata mai albarka" nan tamik'awa Batool wayar tare da mik'ewa takai mu'azzam wajen wasu bak'i da suka shigo barka tun d'azu ana jira, 


"Hello yayya kihau WhatsApp kigani naturo maki pics d'in suna," Batool tafad'a tare da lak'amo wuyan Billy dake neman fita d'akin.


"Ok shikenan, bari naduba, kugaidamun da aunty faraaha nasan by now she's too busy"


"Zataji yayya bye"


Suna gama wayar Batool tarik'o hannun Billy suka koma cikin bedroom d'in aunty faraaha, ta zaunar da ita kan gado itama ta zauna gefenta had'e da cewa


"Wai my twiny meye labari?"


"Dame twiny" d'an duka takai mata agefen kafad'a had'e da cewa


"Abeg twiny keep joke aside, Allah nasan duk kingano menake nufi, wlh namatsu kema naga anyi bukinki munkaiki d'akinki" shafa wajen data d'an duketa tayi kafin tace


"Sai kuma akace saikin dokeni zan gane, Allah zanma fasa baki labarin"


"Haba 'yar uwata srry fad'amun insha" yak'are zancen had'e da rungumota ajiki...d'an harararta tayi kafin yafara bata labarin malam jika from a-z da kuma decision d'in data yanke akansa na tsayawa ta sauraresa.


"Nashiga uku ni Fatima, twiny kikace waye sunansa? Lawan malam jika?, Tab wlh Allah karma ki soma, kiji mutum harda mata da yara uku, kike kikai kanki da quruciyarki a hallaka ki, nifa Allah tsoron masu matarnan nakeyi bakiga yanda mukasha wahala ba kafin asamu daidaita tsakanin mom da Ummi?, Gaskiya kima Dena zancensa nibai yimun ba gaba d'aya , we will wait for our right man in sha Allah, ai ba gajiya mukayi dake ba da zaki wani kwasowa kanki wai malam jika, a'a ba kaka ba" dariya Billy ta azamata ganin yanda ta rufe ido sai faman zabga maseefa takeyi, 


Masha Allah taro kam yayi taro maijego anyi ado anyi kyau ita da babynta, anci ansha anraba kayan buki naji da gani sannan kuma anwatse taro lafiya,


Batool bata bar gidan ba sai da goma tawuce nadare, bayan sun gyaggyarawa aunty faraaha ko ina ita da Billy da wasu 'yan uwanta sannan Dr Ahmad yazo d'aukarta suka wuce gida, ita kuma Billy anan tayi kwancenta don tace bazata koma gida ba saboda taron mutane, 


A b'angaren gidan dady ma anyi buki an watse lafiya, hajiya kilishi kad'aice tanemi had'a fitina tsakanin mom da Ummi amma sai akaci nasara wannan karon mom bata biye mata ba saima fad'a da sukayi kaca kaca akan kada takoma shiga harkar gidanta don Allah tabarta ta zauna lafiya da abokiyar zamanta don batada wata matsala, to shine ran hajia kilishi yab'aci wai mom taci mata mutunci cikin taron jama'a don haka tunkafin taro ya watse ta harhad'a inata inata kunya kunya ta tafiyarta, sosai mom bataji dad'in hakaba lokacin da taga zata tafiyrta, tayita bata hak'uri amma tak'i hak'ura, ita kuwa mom duk abunda yanzu zai koma tarwatsa farincikin gidan aurenta bata sonshi shiyasa da tak'i hak'ura tabarta ta tafiyarta.


Yaya Mahmud kuwa basu koma gida ba sai bayan magrib, Basmah nata yimasa santin hotunan da suka turo mata na suna tana fad'in da yanzu itama tana ciki,


Kwana biyu da suna Umma ta tattara inata inata takoma borno tana yiwa Ummi sherin wai sai sundawo suna idan d'iyar bata riga uwar haihuwa ba, Ummi dai inbanda dariya ba abunda tace mata, momce tace


"Aikuwa dai, in kuma sunyi tare kinga mun huta abunmu sai musha shagalin zuwan baba da d'ansa aduniya" harararta Ummi tayi, Umma nadariya itama tace


"Ai bari zakiyi kema inda akuyar gaba tasha ruwa to tabayan tama acan zata sha, maida k'aimi zance yayana yayi har sai yaga kema kin samawa Bassam k'ane ko k'anwa, kinga lokacin idan Allah yaba Batool sai kuma ayi uwa kwance d'iya kwance" gaba d'aya sukasa dariya mom nafad'in "Allah dai ya kiyaye, kidai rok'awa 'yar taki itama Allah yakawo mata nata kamar yanda yaba 'yan uwanta, amma Ina zanji wannan muguwar fata da kike yimun" da haka dai suka rabu cikin farinciki da nishad'i da kuma aon juna.


Koda Umma ta isa ba k'aramin farinciki tayiba ganin yanda Mahmud d'in keba Basmah kulawa, don har wani fresh taga tak'ara mata, duk wata kulawa da tarairaya tare da soyayya yaya Mahmud na nunawa Basmah, d'ari bisa d'ari ya yarda cewa yanzu yanajin soyayyarta awani b'angare na musamman acikin zuciyar sa, kuma itama tagamsu da hakan, hatta abinci da wanka shi yake yimata da kansa duk wani abu da zaisa tawahala baya bari tayishi gashi duk marece sai yafita da ita sund'an motso jiki abun gwanin ban sha'awa, hakan yasa itama Basmah ta jajirce wajen ganin tafaranta masa nauyin da cikin yayi mata bai hanata bawa Mahmud hak'k'in saba yanda ya kamata batare data k'osa ko gaji yawa ba, wanda hakanne ya k'aramata kima da daraja a idanuwansa kuma har tasamu soyayyarsa da bata tab'a tunani ba, iya more rayuwa da soyayya sunyita ad'an wannan lokacin don kusan ma dashi Mahmud yasamu damar gwangwaje amar cinsa.


Yau sati biyu kenan cikin na uku da sunan yaron su yaya Mahmud, zaune suke cikin palourn Basmah nacin popcorn ta aza k'afafuwanta da suka d'an kumbura a saman cinyoyin Mahmud yana d'an mammatsa mata ahankali,  cike da jin dad'i take cin popcorn d'in shima tana bashi abaki yana ci, har ya kusa k'arewa sannan ta dena bashi tasa sauran agefen pillow d'in kujera, harararta yayi had'e da cewa


"Kai oum little, wa kika ajiyewa wancan da naga kin b'oye"


"Na Ummana ne, idan tadawo anguwa zan bat.." Ai kafin tarufe baki taji kamar an tsikara mata allura abaya, d'an runtse idanuwanta tayi had'e da cije baki sannan tayi baya baya ta kwanta akan kujerar har lokacin idanuwanta na arufe


"Basmaty lafiya?"


"Eh" kawai ta iya fad'a tare da gyara kwancinta, tun Basmah nak'ok'arin danne zafi da wani irin juyi da mararta keyi har takasa, jin bayanta ya amsa mata kamar zai karye yasa tace 


"Wash yaya" arud'e ya ajiye k'afafuwanta nata akan kujera yayi wajen fuskarta yana fad'in


"Basmah lafiya? ko haihuwarce?" Cikin qarfin hali tace


"Ina tunanin haka" tare da sakin wata 'yar k'ara da tasa Mahmud rud'ewa,


Da sauri ya ciro wayarsa a aljihu yakira Umma yana fad'in Umma kiyo sauri Basmah haihuwar zatayi, yana gama fad'ar haka saiga alhajinsu ya dawo daga wajen aiki nan take yaya Mahmud ya sanar dashi halin da Basmah ke ciki, 


"Maza ka d'aukota muje asibiti, bari in fidda motar dama banyi parking d'inta daidai ba" da sauri ya koma cikin d'akinsa ya sauyo kayan dake jikinsa sannan yasa hannu biyu biyu ya d'aukota yana kallon yanda gaba d'aya nan take ta sauya kamar ba Basmah saba sai faman cije baki takeyi tana furta.


_laa'ilaha illa antassubhanaka inni kunya minazzalimeyn_ can kuma sai kaji tace wash yaya,


"Kiyi hak'uri in sha Allah ba abunda zai sameki kinji ko?" Yafad'a daidai lokacin daya fita da ita, yana kaiwa bakin mota saiga Umma tashigo hankalinta atashe don dama ba wani nisa tayi ba tana cikin anguwar, kama masa ita tayi suka sata cikin mota, sannan yakoma gaba yashiga, ita kuma Umma ta tsaya baya tana rik'e da ita tana yimata sannu, da gudu alhajinsa yabar gidan har suka iso haifa specialist hospital, ko kad'an Mahmud bai jira nurses suka iso wajen ba yad'auki Basmah ya shiga da ita maternity yna kiran nurses, da sauri suka k'araso wajen tare da rik'ata suka k'arasa ciki da ita, sosai Basmah nada dauriya domin inba addu'a da wash d'in da take fad'a idan yazo babu abunda takeyi, cizon baki daine tayishi yafi ak'irga kuma take kan yinsa,


Wayarsa yaciro ya kira dr dake kula da ita ya sanar dashi suna asibiti Basmah ce zata haihu, nan take likitan yace yajirasa ga yanan zuwa, ba'afi minti uku ba saiga likitan ya iso dama da yake yana kusa da ward d'in, kota kan Mahmud baibi ba yawuce d'akin da yaga ankai Basmah hankalinsa atashe don yasan akwai matsala idan aka bari ta haihu da kanta, yana shiga yafara duddubata yaga haihuwarce gadan fad'an don har takai 3cm, nan take yasa aka cike mata file akan za'a shiga da ita emergency theater yanzu yanzu sannan yafita indasu Mahmud suke tsaye shida alhaji da Umma,


   A gurguje yayi masu bayanin cewa due to problem d'in da take dashi na cardiac disorder  bazai yuyu abari ta haihu da kanta ba domin zuciyarta batada k'arfin da zata iya k'arfafa mata wajen nak'uda, idan kuma akace abarta tahaihu da kanta tofah komai zai iya faruwa da ita, don haka dole zasu yimata theatre don ceto rayuwarta da kuma abunda ke cikin cikinta, file d'in ya mik'awa yaya Mahmud had'e da cewa


"We need you sign here" ya nuna masa wani d'an layi inda zaisa hannu dake jikin takardar, jikin yaya mahmud narawa yasa hannu sannan likitan yakoma cikin d'akin, gaba d'aya jikin Umma da alhaji sunyi sanyi jin abunda likitan ya fad'a baran Mahmud da sai faman safa da marwa yakeyi yana addu'ar Allah ya sauketa lafiya, likitan ne sukaga yafito da sauri saiga Basmah wasu nurses sun biyo bayansa da ita bisa wani d'an gado da ake turawa, da sauri Mahmud yanufi wajensu tare da rik'o fuskarta yana fad'in


"Ki kwantar da hankalinki Basmah, insha Allah babu abunda zai faru dake" manyan yatsunsa yasa yana goge mata hawayen da suka zubo mata tare da yimata kiss agoshi yace


"Ina sonki Basmah.."  Bai rufe baki ba yaji nurses d'in sunja d'an gadon da sauri ganin yana shirin b'ata masu lokaci, ji yayi tarik'o hannunsa cikin juriya tace "nagode yayana" sannan aka wuce da ita yana biye dasu, sai faman fad'a mata takwantar da hankalinta lafiya klw zata haihu in sha Allah yake.


Sosai yaba alhaji tausayi ganin yanda duk yabi yarud'e yaje yarik'o hannunsa had'e da cewa


"Ka kwantar da hankalinka kaima kuma dukanmu muyi mata addu'a tare da fatar Allah ya sauketa lafiya..


 


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Awasu lokutan nuna zallar farincikinka ga masoyi bisa kulawa da farantawa da yakeyi maka kad'ai bazai wadatar ba har sai baki da zuciya sunyi gamayya wajen furtawa abayyane, Gaisuwa tare da fatan alkhairin Allah agareku *SHA'AWANATU ABUBAKAR* (MAMAN QUEEN) DA *SHAFIHA M SAMBO* tabbas ku aminaine da keda matuk'ar muhimmanci atare dani domin kun zamemun hannayena na dama da hagu wajen bani kulawa da kariya, nagode sosai da soyayyarku ubangiji Allah yabar qauna atsakaninmu, maman queen Allah ya albarkaci zuria, aunty Shapy ke kuma Allah yakawo miji nagari mai albarka ranar aunty billy ta girgiza kwankwaso_🤭🙈💃🏼


💎Page_____98💎



  Maganganu masu dad'i iyayen nasa suka shiga bashi ganin yanda hankalinsa yatashi kafin su samu yanatsu, ciro wayarsa yaciro ya Kira lambar yaya Mahmud, bugu d'aya ya d'aga, yanda yaji muryarsa ya tabbatar masa da akwai damuwa hakan yasa nan take shima hankalinsa ya tashi, 


"'Dan uwa gamu asibiti Basmah zata haihu amma ance tiyata za'a yimata, pls kuyimata addu'a" duk inda hankalin yaya Mahmud yake saida yatashi, amma saboda kada ya karyar da zuciyar d'an uwansa yasa yace


"Karka damu d'an uwa zamuyi mata addu'a, kaima kayi addu'a sosai don ita tafi buk'ata, wannan ba lokacin damuwa bane kaji" d'aga kansa yayi kamar Yana gabansa kafin ya kashe wayar, 


Suna gama waya yaya Mahmud yakira mom ya sanar da ita halin da Basmah keci amma sai yab'oye mata zancin tiyata za'ayi mata don ta tashi hankalinta ko zancen haihuwar yafad'a matane saboda sanin muhimmanci da tasirin addu'ar uwa ga d'anta don tayi mata, badon haka ba da bari zaiyi sai anhaihu sannan suji komai, Allah sarki uwa da d'a mom natsaye ba tasan lokacin data fad'i zaune akan kujera ba, addu'a tadinga jerowa 'yar tata tare da fatar Allah ya sauketa lafiya, sannan ta tashi tafad'a toilet tayo arwala tafara nafilfili tanaci gaba da rok'awa 'yar tata sauk'i wajen Allah, ji take inama zata iya zuwa takarb'ar mata wannan zafin nak'udar da akeji, tabbas ko acikin 'ya'ya Allah yasanya fifikon soyayyar wani d'a akan wani, gaba d'aya cikin yaranta babu wanda tafiso kamar  Basmah, kuma hakan yasamo asaline tun tana k'arama saboda tausayinta daya zauna aranta narashin shan isasshen nonon da batayi ba saboda cikin Batool daya haifar dayin rurrutsa atsakaninsu,


Gaba d'aya bakin k'ofar d'akin suka koma shida su umma sun kasa zaune sun kasa tsaye kowane bakinsa d'auke da addu'a tare da fatar Allah ya yassare mata kuma yasa ayi aikin cikin sa'a.


Jin irin nishin da Basmah keyi yasa suka k'arasa shiga da ita d'akin tiyatar aguje, suna shiga nan take aka sauya mata kaya dama tuni angama shire-shiren kayan aikin da za'a yimata tiyata dasu, cikin gaggawa aka d'orata bisa gadon likitocin suka rufa mata, ai kamar jira takeyi ana k'ok'arin yankata sukaji tafara wani irin nishi mai k'arfi dake nuna cewa haihuwa tariga tazo, kafin suk'ara wani yunk'urin ana dubata sai dai sukaga kan jariri yafara b'ullowa, dole yasa gaba d'aya nurses da doctors d'in suka dakata suna kallon sarautar Allah, banda juye juye da cizon baki da addu'a cikin rai ba abunda Basmah keyi, cikin ikon Allah taji wani irin nishi yazo mata da k'arfi da yasa duk juriyarta saida tasaki wata irin k'ara alokaci saiga kan jariri yafito gaba d'aya, da sauri likitan yazo ya ida taimaka mata aka ida ciro jaririn da uwa akaba nurses d'in da zasu gyrashi, kanta likitocin suka koma ganin gaba d'ya bata motsi ga saitin bugun zuciyarta baya tashi, lumfashinta ma yayi k'asa gaba da'ya nan take suka jawo oxygen suna bata taimkon gaggawa, sunfi minti ashirin akanta suna k'ok'arin ceto rayuwarta kafin su samu lumfashinta yafara daidaita da taimakon oxygen, zaune babban likitan yafad'i lokacin data ga lumfashinta ya dawo don gaba d'aya sun gama  katsewa akan ba tada rayuwa domin abunda akayi gudu shi yafaru amma cikin ikon Allah saiga lumfashinta yadawo fiyema da yanda suka tsammani, "wannan wani sabon miracle me daga Allah" sukaji wani d'aya daga cikin doctors d'in da kristcher ne yafad'a yana kallon na'urar dake nuna adadin lumfashi da daidai tuwar bugawar zuciyar mutum keye,


Mahmud kuwa da gudu yanufi k'ofar d'akin tiyatar yana jijjigawa lokacin daya jiyo k'arar da Basmah tayi, securities d'in dake tsaye abakin k'ofarne suka rik'esa alhaji yazo ya jayesa yana fad'in "meye haka zakayi Mahmud?" 


Nuna k'ofar d'akin yayi tare da cewa


"Alhaji baji sautin k'arar Basmah ba?, don Allah kubarni nashiga naga halin da take ciki, nasani tanada buk'atar kasancewata awajen, natabbata zata samu k'warin guiwa sosai idan taganeni, bana son wani abu yasameta ko kad'an har sai ta tabbatar birinta yacika akaina, alhaji Basmah tamatuk'ar shan wahala akaina bana so kuma ace ta sanadina yanzu zata rasa rayuwarta" yak'arasa fad'a hawaye nazubo masa ga idanuwa, itama kanta Umma kuka takeyi saboda tausayin yarinyar, tabbas duk abunda Mahmud yafad'a gaskiyane, akwai buk'atar Basmah tasamu tabbacin soyayyarta awajensa.


Rungumesa alhaji yayi tare da cigaba da rarrashinsa yana bashi magana,


Saida likitocin suka tabbatar komai ya daidaita angyara baby cikin wasu kaya overall blue colour da asibitin ta tanada ga kowane jariri da aka haifa asibitin a matsayin welcoming don taya murna da farincikinsu na zuwan yaron duniya kuma a hannunsa, sannan suka fito d'aya bayan d'aya jiki a sanyaye, aka baro sauran da zasuci gaba da duba lafiyarta.


Da gudu Mahmud yak'araso wajen babban likitan da dashi zai yimata tiyatar yana tsaye da likitan dake dubata suna tattaunawa akan matsalar da Basmah tasamu na collapse d'in jijiyoyin zuciyarta, wanda basa tunanin k'arfin d'aya rage masu zai iya sa tarayu fiye da kwana goma aduniya, cikin tashin hankali Mahmud yace


"Dr Ina matata?, awane hali take yanzu?" Yana rufe baki yaji wata nurse tafito daga cikin d'akin tana fad'in "Ina mutanen Basmah?" Ai bai jira amsar da doctor zai bashiba yanufi wajen nurse d'in har suna rige rige tsakaninsa dasu Umma wajen fad'in 


"Gamu"


"Yawwa ga wannan kuje akawo yanxu yanxu, Ta sauka lafiya, ansamu baby girl" tamik'a masu takardar wasu magunguna da oxygen d'in da zasuje sukawo sannan tajuya zata koma ciki,


"Don Allah nurse ya mahaifiyar take?"


"Alhamdulillah itama tana lafiya, kuje ku kawo abubuwan da ake buk'ata" tafad'a had'e da juyawa tabar wajen,


"Alhamdulillah" duk sukace ammashi jikinsa nabashi kamar akwai matsala, komawa wajen likitan dake kula da ita yayi amma sai ya samu gaba d'aya basa wajen, dole yadawo shida alhaji sukaje sawo kayan da ake buk'ata,


Bayan sun dawone Umma takira dady ta sanar dashi Basmah tahaihu ansamu baby girl, amma har yanzu da ita har Babyn ba'a basu damar ganinsu ba amma antabbatar masu da duk suna cikin k'oshin lafiya, 


Sosai dady yayi farin ciki tare da adduar Allah yaraya ita kuma yamayar mata da lafiyarta, 


Batool dake zaune palour tarafka uban tagumi saboda safiyar yau gaba d'aya koda ta tashi haka kurum ta tsinci kanta cikin wani yanayi marar dad'i gaba d'aya tarasa meke damunta, tayita Kiran lambar Bilkisu da itama ab'an garen nata batajin dad'i ko lecture bata fitaba shiyasa tasa wayarta silent amma bata d'aga ba, tana zaune saiga mamy tahawo saman rik'e da muhib saboda gaba d'aya yau bata ganeta ba shiyasa tahawo saman don ta dubata tagani ko lafiya, tana ganin mamy ta zame akan kujera had'e da karb'ar muhib tana gaida mamyn, murmushi mamy dake k'ok'arin zama akan kujera tayi tana fad'in


"Fatima lafiya kike?, naga duk yau banganki ba?"


"Lafiya klw mamy yau jikina ne baya yimun dad'i"


"Ayya to ubangiji Allah ya sanya alkhairi kuma ya sauk'ak'a duk abunda ya tsananta, amma ai ba zama zakiyiba kiyi tagumi, idan zaki iya kije kiyo arwala kiyi koda raka'a biyu ne, ko kuma ki karanta alqur'aninki kinji ko? Ina tunanin komeye Allah zai yaye maki, kada kiyarda kiba damuwa muhalli acikin zuciyarki domin zatayi nasarar tarwatsa maki farinciki wanda ni bana fatar haka gareki" 


Kanta na ak'asa duk'e tana wasa da hannun muhib tace "insha Allah mamy"


"Yawwa 'yatah ko kefa, Allah yayi maki albarka, kinga kawo wannan yaron, kada ya k'ara maki gajiya"


"Amin mamy nagode" tace sannan mamy takarb'i Muhib d'in da sai faman wangalewa Batool baki yakeyi sabo yasan itace mai yimasa wasa da kuma k'ilbasa, tana fita ta tashi tayi kamar yanda mamy tace mata, tana cikin karatun ne kiran mom ya shigo wayarta, da sauri ta d'aga tare da cewa "hello mom ina wuni"


"Lpy klw Batool, ya kike ya mamyn taku da Muhib"


"Duk lafiya klw mom"


"Masha Allah, to 'yar uwarki ta sauka ansa baby girl, yanzu haka tana asibiti kuyi mata addu'a kinji.."


Ai mom bata k'arasa fad'aba Batool tasauka k'asa tana fad'in "Yeeee mamynah 'yar uwata Basmah tahaihu" da sauri mamy tafito itama cikin farinciki tana fad'in 


"Alhamdulillah ya Allah, ubangiji Mungode maka, Allah yaraya mana ita, ashe halin da 'yar uwarki keciki yasa kema kika jiki cikin wannan yanayin, Allah sarki, 'yan uwantaka kenan amusulunci ya kasance duk abunda yasamu d'an uwanka kaima zakaji tamkar yasa meka wannan shine k'auna" manta sukayita murnar haihuwar tata, mamy kuwa na addu'a cikin ranta itama Allah yaba fatima da d'an nata rabi mai albarka kusa kusa, don bata so tayi afili yarinyar taji damuwar haka,


Lambar Billy ta sake gwada kira acikin sa'a tasameta itama lokacin suka gama waya da mom ta sanar mata da zancen yayya Basmah d'insu tahaihu, cike da farinciki suke rige rigen taya junansu murna da fatar Allah ya mayarwa yayyarsu da lafiyarta, nan Billy ke sanar da ita yau da zazzabi itama ta tashi tun safe take ko lecture bata samu ta tafiba, ashe yayya take tamawa nak'uda sunata dariya.


Kafin kace me, tuni labarin haihuwar Basmah ya zagaya ko ina tsakanin 'yan uwa da abokanan arzik'i, Ummi kuwa jitayi inama ace itama ta haihun saboda nauyin da cikinta yayi mata haihuwa ko yau ko gobe.


Murna kuwa awajen yaya Mahmud ba'a magana, nan take yafara shire shiren tafiya don dubo halin da 'yar uwarsa keciki, saboda matsuwa da d'okin ganin ya isa da wuri kai tsaye kud'in jirgi yabiya ya saukesa garin na maiduguri, babu yanda faraaha batayi dashi suje tare ba amma yace a'a tayi hak'uri tunda ko arba'in batayi ba, kuma ai nan za'a dawo da ita ayi suna.


Sai bayan awa 7bakwai da haihuwar Basmah sannan aka basu damar shiga wajenta don ko jari riyar ba'a kawo masu ba sai lokacin da suka shiga suka ganeta, kallo d'aya zaka yiwa Basmah nafahimci irin tsanin ciwon da take ciki ga oxygen ga bakinta da aka samata na biyu don nafarko yak'are tuntuni , gaba d'aya tausayintane yarufe yaya Mahmud da tun d'azu ya iso baisan lokacin da hawaye suka zubo masa a idanuwa ba, 


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" yadinga fad'a amma ina kasa tsayawa yayi wajen yabar d'akin yana kuka, shikuwa Mahmoud kota kan babynta bebi ba yarik'e hannunta ahankalin yana kiran sunanta "Basmah, Basmah, don Allah kada kitafi kibar little d'inmu, bud'e idanuwanki kaga kyautar da Allah yayi mana, kitashi kigani Basmah gaba d'aya Allah yacika maki burinki yanda kike son babynmu tazo ahaka tazo don Allah kibud'e idanuwanki kinji Basmaty" ganin ko motsawa batayi ba sai lumfashinta kawai da suke gani yana fita da sauka ahankali yasa Mahmud yafashe da wani irin kuka mai ban tausayi, dafasa alhaji yayi had'e da cewa


"Be strong my son" d'ago kai yayi yana kallon mahaifinsa kafin yace


"It's all my fault, nine silar shigarta cikin wannan halin Abba taya za'ayi bazanyi kuka ba"


"What ever dai, hak'uri zakayi, muci gaba da yimata addu'a Allah yatashi kafad'unta, k'ananun kukan da jari riyar dake hannun Umma tafarayine ya maido hankalin Mahmud gareta, hannu ya mik'awa Umma ta azomashi ita yana binta da kallo, gaba d'aya yarinyar dashi take kama, babu ta inda tabarosa, gata babba tubar kallah kamar ba yau aka haifeta ba, cike da soyayya yabita da kallo ya karata daidai saiti fuskar Basmah had'e da cewa


"kitashi Basmah ga little d'inmu, ki samata duk sunan da kike buqata, wannan alk'awarina ne"


"My son yakamata kayi hakuri hakanan, katashi kaje kunemowa yarinyar nan abunda zataci kafin mahaifiyarta ta farfad'o don da alama tafara jin yunwa" Umma tafad'a had'e da karb'ar yarinyar a hannusa.


Dai dai lokacin yaya Mahmud yadawo cikin d'akin idanuwansa jawur saboda kukan da yayi, nan Umma tahad'asu tayita basu hak'uri kafin tace


"Kubiya gida akwai kaya na nan acikin wani pink trolley bag cikin wardrobe a d'akina ku d'auko sannan kabud'e loka d'in mirror akwai dabino da ruwan zam zam kahad'o dasu inyaso idan zaku dawo saiku biyo da fida da kuma zuma sai afara bata mugani"


Tare suka fita kowa ransa babu dad'i, shima alhajin suna fita ya fita don ankira sallar isha'i, saida yayi sallah sannan ya wuce siyo masu abunda zasuci dama tun k'arfe d'aya da suka kawota babu wanda ya koma cin abinci, yarage Umma kad'aice zaune awajen tana kallon yanda jaririyar gaba d'aya ta kwashikke d'anta da d'an uwanta baba k'arami, lallai Allah da iko yake, duk wanda yaga babyn aka tambayesa waye mahaifiyarta zai iya rantsewa yace Bilkisu saboda yanda kamarta tafi fitowa dasu akan mahaifiyarta,


Ana haka suka dawo tare da kayan da suka d'auko, yaya Mahmud ya karb'i baby ita kuma Umma ta anshi fida da ruwan zam zam d'in da sukazo dasu, Mahmud tabawa dabinon tace ya tattauna har sai yayi laushi sai yaba yarinyar abaki, ita kuma ta had'a ruwan da zuma acikin fida, 


Bayan ya tattauna dabinon kamar yanda Umma tace yayi yaya Mahmud ya mik'a masa ita, 


Ahankali ya aza harshensa dake lak'e da dabinon abakin jaririyar idanuwansa na akan Basmah yana kallon fuskarta, aikuwa da sauri babynta tafara tsutsar dabinon da harshensa tamkar tasamu nono, rufe idanuwansa yayi cike da tausayin yarinyar yanajin soyayyarta na ratsa kowane lungu da sak'o dake cikin zuciyarsa. Saida ta tsotse dabinon tas sannan ya zare harshensa, aikuwa tanajin haka tsanyara ihu, 


Gaba d'aya murmushin k'arfin hali sukayi kafin Umma ta karb'eta da sauri tasa mata fidar abaki, sosai tayi tashan had'in ruwan zamzam d'in da zuma har saida takusan shanye rabin fidar sannan Umma ta jaye mata, ba'afi minti biyar ba bacci ya d'auketa Umma ta maisheta cikin d'an gadon jarirran dake gefen gadon mahaifiyarta sannan tafita taje tayi sallah tadawo cikin d'akin taci abincin da alhaji yakawo masu sannan yayi masu seda safe yawuce gida, tafi minti biyar tana amsa wayoyin da aketa faman kiranta ana tambayar yaya jikin Basmah kafin tagama, gaba tasa mahmud shida yaya Mahmud saida sukaci abinci sannan tace suje gida su kwana ita zata kwana anan" 


Gaba d'ayansu k'in yarda sukayi sukoma gidan sai dai sukace nan suma zasu kwana tare da ita koda za'a buk'aci wani abun, haka kuwa akayi daren ranar babu wanda yayi bacci acikinsu har safiya tawaye, 


Misalin k'arfe tara na safe likitoci sukazo duba Basmah, dubata sukayi sukaga  komai ya daida ita yanda ake buk'ata, waccan matsalar d'ai ce da basusan taya zasu iya fuskantarsu da itaba, tsakanin jiya da yau saida aka saka mata oxygen har sau biyar yana k'warewa amma har yanzu bata farkaba,


Suna cikin tattauna matsalarta tsakaninsu Basmah tafarko amma maganganun da taji sunayi su sukasa takasa bud'e idanuwanta, sosai taji fargaba da tsoron abunda taji suna fad'a amma sai taji cewa babu wanda ke mutuwa sai lokacinsa da Allah yad'ebo masa yayi don haka duk tsarin da Allah yayi mata alhamdulillah.


Suna fita tabud'e idanuwanta ahankali sannan tajuyar da kanta gefe tana kallon jaririyarta da Allah ya bata, wacce takasa banbance tsakanin 'yar uwarta da kuma mijinta dawa babyn tayi kama, murmushi tayi hawaye nazirarowa ta gefen idanuwanta cike da tausayin yarinyarta da take tunanin bazasu rayu tare da itaba kafin tace 


"Alhamdulillah, Allah nagode maka daka cika mani burina, kabani farinciki da soyayya awajen mijina kuma kahad'a mani da kyautar 'ya wacce nake burin faranta zuciyar 'yar uwata da ita bisa sadaukarwa da soyayyar data nuna mani, ya Allah karaya mana Bilkisu bisa turba ta islama kuma kasa tayo gadon takwararta, tabbas zatayi rashin mahaifiya idan ta Allah tazo gareni amma inada tabbaci akan bazata tab'a kukan rashin uwa aduniyaba matuk'ar tana a hannunki 'yar uwata"..



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


*_Akwai kuskure da kuma raunin imani ga duk bawan da baya tunanin mutuwa arayuwarsa, laifine bawa yadinga tunanin cewa bai dace wata rayuwa ta mutuba saboda rayuwar ba'a hannunsa take ba, Allah yana karb'ar rayuwar bawa aduk lokacin da yaso kuma alokacin da yaga dacewar haka agaresa, yarda tare da yak'ini akan zuwan mutuwa akowane lokaci shikesa bawa barranta daga sab'on Allah, tunani da kuma sakankancewa akan cewa ai bai kamata wane ya mutuba saboda wani dalili shine shiga hurumin Allah, muyarda da ikon Allah da kuma tsarinsa akoda yaushe saimu samu barranta daga garesa, Allah baya barin wani don wani domin da kansa yacewa jabrilu ya fad'awa annabinmu cewa " INNAKA MAYYITUN WA ANTUM MAYYITUUN"_*😭



💎Page_____99💎


 

   Kwanan Basmah uku asibiti ta samu sauk'i sosai tunda dama ba yankata akayiba aka sallamesu, bayan doctor yayiwa Mahmud bayanin halin da take ciki amma bai fad'a masa cewa ga kwanakin da zata iyayi aduniya ba, ya dai fad'a masa cewa due to cardiac disorder da take fama dashi kuma anyi k'ok'arin ganin anyi mata operation kafin faruwar wani abun amma da yake haka Allah ya tsaro kafin sukai ga fasata tahaihu da kanta, sanadiyar haka veins d'in jijiyoyinta sunyi damaged da bazasu iya aikinsu yanda yakamata ba, saboda haka aci gaba da bata kulawa yanda yakamata kuma ta tsare shan magungunanta, inyaso sauran abarwa Allah don shi yake da rayuwa kuma shi yakeda mutuwa. 


Iya tsorata Mahmud yayi don ga yanda yaga likitan nayi masa bayani yasan akwai matsala, amma abu guda yasa aransa shine, mutuwa wajibi ce ga kowace rayuwa sannan duk mumuni yasan akoda yaushe tana tare dashi ko yanada lafiya ko bayada lafiya kuma babu wanda ke mutuwa har sai lokacinsa yayi, Allah yaga damar ya d'auki ransa ahida yake da lafiya yabar Basmah da akw tunin mutuwarta akoda yaushe kuma akowane lokaci, wannnan ikon sane don haka yabarwa Allah daya wanzar da duk tsarin da yayo akansa.


 Bayan kwana biyu da sallamoau asibiti alhaji da kansa shida Umma da yaya Mahmud suka hau shire-shiren maido Basmah gida, dama ana sallamota asibiti yaya Mahmud yakoma, dady kuwa duk da yana son ganin 'yar tasa hakan bai hanasa yima 'yar uwarsa kawaicin cewa abarta acan har sai bayan suna sannan adawo da ita amma Umma tace tunda dai tasamu sauk'i sosai kuma ba tiyata akayi mata ba yabari amaidota cikin 'yan uwanta kamar yanda akeyi a al'adance, hakan yasa dady ya tura mata kud'i masu yawa yace subiyo jirgi zaifi sauk'i akan tafiyar mota.


Zaune take gefen gado bayan tagama shiryawa cikin wani had'ad'd'en less pink da touch na white tanaba baby nono kafin sutashi tafiya shi kuma yafito wanka d'aure da k'ugu a kunkurunsa, kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai tana gyarawa baby nonon abakinta, murmushi yayi had'e da zaunawa gefenta Yana kallon fuskar jaririyar tace


"Yaya ba kunya!" Zaro idanuwa yayi awaje tare da cewa


"Ikon Allah, danayi me oum little?"


"Agabana kake k'urawa yarinyar nan idanuwa haka kaman zaka cinyeta" rik'e hab'ar bakinsa yayi da hannunsa  yana kallonta idonuwansa cikin nata kafin yace


"Tab..yanzu Basmaty ni da ke wayafi zama marar kunya keda kika kware nono agabana kina bata"


"To ai wannan dolene yaya so kake nabarta da yunwa?"


"A'a ranki ya dad'e ni kuma so kike incuci kaina  tunda yau guduwa zakuyi kubarni, ai dole nakalli 'yata son raina, wai bama wannan ba, wane suna kika zab'a mata?" Yafad'a tare da mik'ewa yana k'ok'arin gyara kanshi don shi kad'aine ake jira duk su umma sun gama shiryawa, a hankali ta zarewa nonon abakinta saboda tasmu yin bacci sannan ta ajiyeta akan gadon tare da gyara rigarta tanufi inda yake,


Karb'ar d'an k'aramin towel d'in dake hannunsa yana tsane jiki tayi taci gaba da goggoge masa ruwan ajikinsa, sannan tajawo mai tana shafa masa, idanuwa ya bita dasu ganin yanda ta sauya masa gaba d'aya, ga wani kyau da 'yar k'iba da tayi kamar ba Basmatyn daya sani ba, d'ago kai tayi tana kallon idanuwansa tare da d'aga masa gira tana dariya tace 


"Abban little wannan kallon haka fa?"


"Kinyi kyau oum little"


"Nifa kadena kirawa yarinyata little ba hakane sunanta ba" hannunsa yasa ya d'agota da duk'en da take tana shafa masa mai ak'afafuwansa shi kuma yana zaune abakin gado ya zaunar da ita akan cinyarsa sannn yace


"Ranki ya dad'e fad'amun sunan mana tun muna asibiti nake tambaya aketa faman jamun rai, ataimaka afad'a mani koma bar 'yatah a little d'inta"


"Afuwan yaya, sunanne na musamman kuma da tsada sai anbiya, idan kana so kaji to kabiyani nikuma yanzun nan zan fad'a maka.." kafin ta ida rufe baki kawai taji bakinsa cikin nata yana yimata wani irin passionate kiss da yasa jikinta mutuwa nan take, saida ya shanye gaba d'aya lipstick d'in data shafa a lab'b'anta sannan ya d'ago idanuwansa arine yace 


"Gashi nabiya afad'amun"  wata irin kunyace tarufeta da tasata yunk'urin mik'ewa daga kan cinyarsa da take zaune yayi saurin rik'eta, kanta naduk'e tace


"Bilkisu" a hankali ya saki hannunta, zuciyarsa nabugawa jin sunan data anbata, shiru yayi na mintota kafin ya d'ago kansa ya kalleta 


"Shi kike so? Kuma ya yimaki?" Kad'a kanta tayi had'e da cewa


"Eh"


"Shikenan Allah ya albarkaci rayuwarta kuma yaraya mana ita"


"Amin ya Allah" tafad'a tare da bud'e wardrobe taciro masa wata shadda sabuwa dark pink sai k'yalli takeyi, taimaka masa tayi yasa sannan ta d'auko masa takalminsa da hula mai k'ube ta daidaita zamanta akansa, agogonsa na rolex dake kan madubi ta d'auko ta saka masa sannan ta d'auko turare ta feshe masa jikinsa dashi, hannunsa tarik'a ta kaishi agaban madubi tana murmushi, kallon kansa yayi yaga yanda yayi matuk'ar kyau, juyowa yayi shima yana murmushin tare da rungumota ajikinsa sosai yayi kissing d'inta a forehead yace


"Nagode sosai oum little, Allah yayi maki albarka"


"Amin yaya" tafad'a tana d'an turo bakinta gaba kafin tace "Ai dai ba sunan 'yata little ba" 


Dariya yayi had'e da jamata hanci kad'an sannan yace


"Basmaty ba kunya, agabana kike cewa 'yarki?"


"Eh mana zan iya fad'ama agaban kowa, yanda nake sonta ko kaina banaso haka infact dia baby is my everything, she mean alot to me and I proudly to have her in my life" Saida tayi murmushi sannnan taci gaba da cewa "Bilkisu kenan baiwar Allah, my sister my dota" tak'arasa maganar had'e da d'okarta tayi kissing d'inta, bata ankara ba sai dai ganin hasken camera tayi ya d'aukesu, d'ago kai tayi da niyar yimasa magana ya sake d'aukarsu wani sannan yadawo kusa da ita ya maido camerar agaba ya d'aukesu gaba d'aya fiye da sau biyar, karb'ar babyn yayi ya ajiye gefe sannan ya jawota ajikinsa yayi masu wani su biyu kad'ai, wani murmushine yabayyana a fuskarta wanda zai iya fassara maka irin farincikin dake tattare da ita.


Sallamar da suka jiyo a palour tasa yayi saurin kad'a wayarsa a aljihu, ya d'auki little yafito, harararsa Umma tayi tana fad'in,


"Ai nazata baka shirya bane in sab'a maka don nasan 'yata batada matsala" karb'ar little tayi a hannunsa sannan tawuce tana fad'in 


"Ku ake jira kufito rana tasoma yi"


Tsaye ya iskota tana juye tsakiyar d'akin tana kuka, tanajin muryarsa tayi saurin goge hawayenta tare da yafo mayafinta akai, 


"Basmaty fito muje ko? Umma tace mukad'ai ake jira" sannan yajuya tana biye dashi, har takai bakin k'ofa tadawo da sauri tare da bud'e wardrobe ta hankad'a tsakiyar kayansa ta ajiye wani abu sannan tayi saurin ficewa d'akin tana goge hawayen idanuwanta.


A garin k.d kuwa shirye shirye akeyi sosai na isowarsu, musamman dady yasa aka sake gyra asalin d'akinau ita da Basmah aka chanza sababbin kayan d'aki akasa wasu ga d'an gadon jarirai da sauran kayan kula da yara abun gwanin ban sha'awa, gida yacika da 'yan uwa da abokanan arzik'i sosai gasu aunty faraaha da Batool duk sun iso, ga family d'insu alhaji bukar da kabiru dasu baba k'arami duk sun iso tarbonsu kai kace ranar ake suna, saboda tunda tayi aure kusan shekara bata samu tazo ganin gidaba, shiyasa kowa yake mararin ganinta, 


Basu iso ba sai misalin k'arfe sha d'aya na rana saboda matsalar da aka samu acan filin jirgin kafin su taso amma alhamdulillah sun iso lafiya, 


Murna kam ba'a magana awajen mom haka Batool da Billy kamar zasu canye little da tunda suka iso suka kamata suka rik'e, Batool ce ta kalli Billy tace


"Twiny Allah yarinyar nan duk dake take kama" murmushi Billy tayi had'e da cewa


"a'a twiny aikam dai da abbanta take kama ba niba", 


Shi kuma dady da yaga yarinyar cewa yayi da baba k'arami take kama, ai kuwa duk akasa dariya a palourn, kallon babyn baba k'arami yayi had'e karb'arta yace


"wannan yarinya duk wanda yasan bababnta, yana ganinta yasan dashi take kama bani ba, indai kamfen ne kukeyi mata to kuma dena don bazanyi da mai fuskar 'yan china ba" sake kwashewa da dariya akayi kafin alhaji bukar da Umma suce


"To ai jiya iyau, duk abunda yayi ka shi yayi Mahmud kuma shi yayi Bilkisu, don haka dai kaga zancen duk d'ayane angulu ta koma komawa gidanta na tsamiya"


"Ahh to indai hakane jinina mai k'arfine gashi har yafara kaiwa ga jikoki"


Nan dai akayita farinciki da murnar sake had'uwarsu akaro na biyu bayan aurensu, kuma kowa yayi farinciki jin sunan da suka rad'awa 'yarsu, Billy kam harda kukan dad'i tayi jin cewa ita 'yar uwarta tayiwa takwara,


Kasancewar yau su Umma zasu koma yasa dady yanemi keb'ewa da alhaji mahaifin Mahmud da kuma 'yar uwarsa yayi masu godiya sosai bisa kulawa da suka bawa Basmah cikin so da qauna, ga kayan da sukazo dasu har akwatuna set biyu na baby guda na Basmah guda, sai yaga kamar hidimar tayi yawa, nan suma suka nuna masa cewa ai komai sukayiwa Basmah 'yar suce kuma hidima dole suyi tunda suna farinciki da kyautar da Allah yayiwa d'an nasu,


Ahaka dai suka rabu kowa cikin farinciki da k'aunar juna.


Ana gobe suna 'yan uwan Mahmud nawajen mahaifinsa suka iso garin tare dashi, tarba ta musamman akayi masu bayan angyara masu part d'in da yaya Mahmud yabari, duk wani abun da zasu buk'ata antanadar masu, 


Bukine na musamman aka had'a don har hall aka kama musamman don gabatar da walima, tunda sassafe aka fara shire shiren suna,tsayawa fad'ar irin kyawon da Basmah tayi ita da baby b'annar lokacine, sunsha kyau sosai kamar ba gobe, Batool ma tunda sassafe ta iso ita da aunty faraaha da mu'azzam d'inta da yayi wayau sosai, 


Mamy ma ta iso da ita su mom ke duk hidimar daya kamata, papi da Hajia kaka ma suma sun iso sai hidima ake guda narwa,


Duk irin yanayin da Ummi kejin kanta aciki haka tadaure akayita 'yan aikace aikace da ita, mom na tsokanarta wai taje ta huta karta haihu abakin murhu, itadai Ummi dariya tayi kafin tace


"Ba ruwanki ko baisan murhu zai haihu, biki namu nida 'yatah dole ingwadi uwar d'iya nake"


"Ai kuwa mungani amma dai ai aje ahuta" dariya Ummi tayi had'e da cewa


"Aifa sai kiyi, badai so kike ace ganican kwance ba? Kice anyi uwa kwance d'iya kwance? To da yardar Allah hakanne bazaki gani ba"


Gaba d'aya dariya akasa wajen kowa fuskarsa d'auke da farinciki da sha'awar su mom yanda suke zaunensu lafiya.


Ana gama sallar azahar aka kwasa sai wajen walimar da dady ya shirya masu, saida kowa ya hallara sannan maijego Basmah da Mahmud suka shigo,


Sanye take cikin wata rantsattsiyar shadda mai tsananin kyau da tsada royal blue anyi mata aiki pink da gyalenta shima pink shima sai takalmi, shi kuma gaba d'aya royal blue ce don banko sukayi hular kansa kad'aice pink irin wacce ake lank'wasawar nan gefe (yoruba style) sunyi matuk'ar kyau sosai bayansu kuma Batool da Billy ne sun takikke masu baya cikin ado na musamman da burgewa, billy ce tarik'o little itama tasha doguwar rigarta ta 'yan kanti pink colour ansa mata baby band akai royal blue abun gwanin ban sha'awa,


Cikin farinciki da natsuwa akayi walimar har aka k'are, kyautukka kuwa maijego da 'yarta sunsha wajen abokanan dady babu adadi, 


Kallo d'aya Billy tayi masu ta d'auke kai saboda yanda sukayi matuk'ar kyau sai taji wani abun nason motsa mata azuciya, murmushi n qarfin hali tayi tare da korar shed'an tana fad'in "qadarallahu wama sha'a fa'ala" sannan tabar wajen tanufi wajen tarbon bak'i dake isowa, anci ansha antaya little Billy murnar isowarta duniya, hotuna kuwa duk inda kajuya camerorine ana vedioting da d'aukar hoto, tsabar farinci both Basmah da Mahmoud bakinsu kasa rufuwa yayi, 


Dr Ahmad ma da abokinsa Khalid sun samu hallarar walimar inda yayi bud'i tare da fatar Allah ya nuna masa shima da teemarsa sun rik'a babynsu ahannu,


Zuwa k'arfe hud'u aka kammala waleemar bayan anraba kayan buki masu d'auke da hoton baby da aka rubutawa THANKS FOR ENJOYING WITH US IN OUR BABY NAMING CEREMONY BILKISU MAHMUD (little Billy), sannan kowa ya watse ya nufi gida.


Agajiye Basmah da baby suka isa gida saboda hayaniya da zirga zirgar da suka sha fama da ita. 


Da daddare bayan tayo wanka itama little anyi mata wanka tahaye kan gado saiga yaya Mahmoud ya shigo


"Sannu amaryar jego, yau kunsha hidima" yafad'a yana k'ok'arin zama kan gadon, murmushi tayi masa tana daga kwance, kafin tace "Yawwa angon k'arni, ai hidimar tamuce duka, ya gajiya?"


"Alhamdulillah ya k'arfin jikinki?"


"Naji sauk'i sosai ko dambe zan iyayi" 


"Ah lallai kice komai normal, to bari inzo infad'a maki wata magana" yafad'a tare da hayewa kan gadon yayi mata rumfa, juyawa tayi yanda fuskarta na kallon tasa had'e da jawosa tayi kissing d'in lips d'insa sannan tace


"Go ahead in abun kunya zakayi a gidan sarakai ni am not afraid of anything"


"Haba! Meyasa?"


"Saboda nasan mutuwa zanyi" da sauri ya d'agata had'e da fad'awa gefenta cikin tashin hankali yace 


"Meye kike fad'a haka Basmah, kina so kishiga hurumin Allah ne? Sanin lokacin mutuwar mutum a hannun Allah yake kuma gaibine don me zaki ce haka?"


Ganin yanda hankalinsa ya tashi yasa ta jiyo kwancinta suna fiskantar juna sannan tace


"Am sorry abban bilqees kuma yayan bilqees, kasan dolene duk wata rayuwa ta d'and'ana mutuwa, shiyasa kaji nafad'i haka amma i beg of you koda namutu kada kutab'a mantawa dani acikin zuciyarka kuma kayafemun duk abunda nayi maka, ka kula da 'yarmu, ka kawo 'yar uwata tamaye mata gurbina sannan kada soyayyar da kake yimata tarufe maka idanuwa tasa kayi rauni wajen barin momynta yimata tarbiya"


Tashi yayi zaune yana kallonta had'e da cewa


"Wai meye kike fad'a haka, don Allah kidena wannan tunanin, inada tabbaci akan insha Allah zamu rayu tare da 'yarmu kuma muyi mata tarbiya atare har zuwa girmanta, kada ki aminta akan cewa ciwo mutuwane, hakan ba gaskiya bane"


Murmushi tayi had'e da aza hannunta agefen fuskarsa tana d'an shafawa ahankali shima ya d'ora hannun nasa akan nata yace


"Basmah! Believe me cuta ba mutuwa bace, sau nawa Allah yakarb'i lafiyayye yabar marar lafiya? Kiyarda cewa sai lokacin bawa yayi yake mutuwa tsananin ciwo bayasa mutuwa saidai awahala"


"Yaya i do believed, amma akwai kuskure da kuma raunin imani ga duk bawan da baya tunanin mutuwa arayuwarsa, laifine bawa yadinga tunanin cewa bai dace wata rayuwa ta mutuba saboda rayuwar ba'a hannunsa take ba, Allah yana karb'ar rayuwar bawa aduk lokacin da yaso kuma alokacin da yaga dacewar haka agaresa, yarda tare da yak'ini akan zuwan mutuwa akowane lokaci shikesa bawa barranta daga sab'on Allah, tunani da kuma sakankancewa akan cewa ai bai kamata wane ya mutuba saboda wani dalili shine shiga hurumin Allah, muyarda da ikon Allah da kuma tsarinsa akoda yaushe saimu samu barranta daga garesa, Allah baya barin wani don wani domin da kansa yacewa jabrilu ya fad'awa annabinmu cewa " _INNAKA MAYYITUM WA ANTUM MAYYITUUN_"


Duk inda ilahirin jikin Mahmud yake saida yayi sanyi jin kalaman dake fitowa abakin Basmah,


Jawota yayi ajikinsa ya rungumeta sosai yana fad'in "karki damu insha Allah bazaki mutu yanzu ba Basmaty"


Baibar d'akin ba sai wucewar k'arfe sha biyu nadare sannan sukayi sallama, bai jima da fitaba saiga Billy tashigo don dama tund'azu tazo part d'in, muryarsa da taji yasata komawa wajen mom suna fira kafin ya wuce, dama tun ranar da Basmah tadawo gida tare suke kwana, kwance ta iskota ta aza Billy saman cikinta, fad'awa tayi akan gadan tana fad'in


"Yayya barka da soyewa, gaskiya yau yaya yashiga hak'k'ina, tund'azu nakeji bacci yazo ya takurani" 


"Kai sisto yayan naki? da bakinki kike fad'ar haka ko?, insha Allah saina fad'a masa" dariya Billy tayi tare da jawo d'an net d'in da akesa little Billy aciki ta ajiye a tsakiyarsu tagyara shimfid'ar ciki sannan tamik'a hannu zata d'auketa, k'ok'arin mik'ewa zaune da taga Basmah nayi yasa tafasa tare da jawo pillow zata kwanta don tazata nono zata bata sai taji takira sunanta,


"Na'am yayya" tafad'a had'e da tasowa tana kallonta, murmushi tayi mata had'e da d'ora mata little dake bacci saman jikinta sannan tace


"Sisto ki d'auka kece kika haifi little da cikinki, shin wace irin rayuwa zaki gina mata tun tasowarta har zuwa lokacin data girma"


"Kai yayya wannan wace irin tambayace haka a wannan tsohon dare?"


Rik'o hannunta tayi cikin hikima tace "ina so inkoya wani abu daga gareki nasan zan amfana, just answer me pls."


Shiru Billy tayi kafin tace


"Zan gina mata rayuwa bisa turbar tsoron Allah da sanin hakk'ok'ansa akanta domin hakan zaisa nima tasan hakkokana da suke akanta, zanyi hak'uri da kurakuranta kafin tagirma amma zanyimata hukunci bisa isgilancinta idan tagirma, zan bata kulawa kuma najata ajinina shixaisa tasan muhimmancina sannan zanyi mata tarbiya ingantacciya tayanda zata zamo mai alfahari dani da kuma yimani addu'a idan bana raye daga k'arshe kuma zan nuna mata so bisa horo da turbar hak'uri da juriya acikin al'amurranta"


"Alhamdulillah" Basmah tafad'a tare da cewa


"Bilkisu ina so kisaka aranki cewa little 'yarki ce ta duniya da lahira, kuma kinada iko akanta ko ina araye ko bana raye nabaki amanarta kuma ina fatar  zaki kula da ita bisa wud'ancan tsari da buruka da kike dasu"


Billy kam ko kad'an bata kawo komai arantaba tace


"Yayya kenan ai indai baso kike kiraba d'aya biyu ba, babu batun kibani amanarta domin kuwa zan iya kula da ita fiye da tsammaninki, tunda nima 'yatah ce koba haka ba?"


"Hakane sistonah afuwan kinji Billy uwar Billy" dariya tayi tare da sanya little cikin net d'inta sannan takoma ta kwanta abunta. Basmah kuwa daren kwana tayi zaune tana kallon little cike da tausayinta saboda tanajinta awani yanayi da bazata iya fassara shiba, ba abunda takeji azuciyarta irin maraicin uwa da little zata tashi dashi amma awani b'angare na zuciyarta idan tatuna cewa 'yar uwarta zata kula mata da ita kuma zata tashi a hannun nagartaccin mutane irin family d'insu sai taji ta samu natsuwa sosai, ana haka misalin biyu da rabi na dare little ta tashi tafara k'ananun kuka, k'ok'arin bata nono tayi amma tak'i karb'a sai kuka takeyi, tun tanayi ahankali har tafara d'aga murya, tashi tayi tagoyata tana jijjigata amma tak'iyin shiru, momce tashigo dai dailokacin da Billy itama tafarka saboda kukan yarinyar daya tadasu, karb'arta tayi tana jijjigata tare da cewa Basmah


"Kin bata nono"


"Eh amma tak'i karb'a" jijjigata akayitayi amma tak'iyin shiru, wani irin kuka Basmah tafashe dashi tare da duk'ewa gaban mom tana fad'in


"Mom dama haka kikasha wahalar renonmu tare da kula da rayuwarmu har muka girma bayan wahalar d'aukar ciki data haihuwa da kika sha amma duk kika jure rana d'aya baki tab'a nuna gazawa damu ba kullum burinki musamu farinciki da ingantacciyar rayuwa? Mom da wane abu zamu saka maki dashi? a gaskiya na jinjina maki kuma Ina alfaharin zamowarki mahaifiya agareni, mom don Allah kiyafemun duk wata wahala da kika sha tawa da kuma b'acin ran dana saki arayuwa"


Haka kurum mom taji jikinta yayi sanyi, wani b'angaren zuciyarta ne yabata ai saboda fitinar da little keyimata da 'yan matsalolin reno data fara fuskanta yasata furta wud'annan kalaman, kallonta tayi cikin yanayin bacci dake fuskarta bai saketa ba tanaci gaba da girgiza little tace


"Basmah kenan ai indai renone haka yake sai ka kai zuciya nesa, ai yarinyar nanma batada wata rigima don tunda kukazo bantab'a jin kukan taba, yauma dai inaga da akwai abunda kedamunta" baki ta'aza  saiti saman cibiyarta ta busa cikin da d'an k'arfi ko cikin natane ke ciwo amma taji kukan bai canza ba, ya tsunta biyu tasa tana daddanna mata kunnenta amma shima taji kukan nata ya gagara canzawa,


Billy ce ta matso takarb'eta hannun mom tare da d'orata saman kafad'arta tana d'an jijjigata ahankali sai gashi tayi shiru, inda Basmah take zaune k'asan k'afafuwan mom tajeta aza mata ita ahankali had'e da cewa


"Yayya karbeta kibata nono kigani ko zata karb'a" cikin sa'a kuwa tana bata takarb'a tanasha har bacci ya sake d'aukarta.


"Ja'ira kin koma baccin bacinmu kin hanamu ko?" Mom tafad'a tana zungureta tare da tashi ta koma d'akinta, murmushi sukayi kafin Billy ta karb'eta had'e da cewa 


"Yayya da alama bakiyi bacci ba tun d'azu,kawota  kije kikwanta bari nagoyata" tashi Basmah tayi cikin rashin k'warin jiki ta'azawa Billy ita abaya sannan taje tayo arwalar bacci tahaye gado abinta ta kwanta, addu'o'in bacci tayi sannan tarufe idanuwanta.


Tunda asuba yaya Mahmud ya shigo part d'in saboda kukan little da yakeji, rashin baccin da basuyi ba jiya yasa baccin nasu yayi nauyi sosai suka kasa jin kukan little, a bakin k'ofa ya tsaya yayi knocking had'e da cewa


"Basmah, Basmah kitashi  ki kama yarinyar nantana kuka, wannan wane irin nauyin baccine haka?" Yana gama fad'ar haka yajuya ya wuce masallaci, knocking d'in da yayi yasa Billy ta tashi taga little rungume ajikin Basmah sai kuka takeyi fuskarta tayi jajir da alama tajima tana kukan, d'aukarta tayi sannan ta shiga bubbuga hannun Basmah tana fad'in "yayya, yayya kitashi tun d'azu little sai faman kuka takeyi kibata nono" ganin tayi ko kad'an Basmah bata motsaba balle ta tashi, hakan yasa tayi tunanin k'ila saboda bata samu tayi bacci sosai bane shiyasa takasa farkawa, fita tayi da little dake hannunta tana kuka tayi d'akin mom da ita, koda tashiga ta tarar tana sallah don itama bubbuga k'ofar da Mahmud yayine ya tayar da ita, jijjigata taci gaba dayi kafin tagama sallar, tana gamawa tamik'a mata ita had'e da cewa "mom karb'e insamu inyi sallah, nayi tada yayya bata tashiba may be baccin yayi mata nauyi don jiya batayi bacci da wuriba"


"A'a to kuma shine saiki k'yaleta yarinya nafaman kuka bazaki tasheta tabata nono ba" mom tafad'a tare da karb'ar little tana cigaba da cewa


"Bilkisu Allah dai yasa lafiya kike wannan kuka haka da kike faman yi tunjiya" had'e da mik'ewa tabar d'akin d'auke da ita a hannu, dady ne ya shigo shida Mahmud dasu Bassam dawowarsu masallaci kenan saboda kukan da takeyi yasa sukayo part d'in, 


"Ke amaryata lafiya yau kika tashemu tunda asuba da kuka, inaita Basmah d'in take data barta tanata faman wannan kukan" dady yafad'a yana k'ok'arin karb'arta ahannun mom, shidai Mahmud ji yake kamar yaje yajawo Basmah saboda kukan da yarinyar keyi amma kunya bazata barshiba, d'akin mom tawuce tare da nufar inda Basmah take kwance, tada ita tayitayi amma taga bata motsaba, cikin tsoro da yanayin da taga Basmar keciki tad'aga hannunta gabanta nafad'uwa, ganin hannun tayi yayi luuu.k'asa ya koma, cikin firgita tace


"Alhaji, alhaji" da k'arfi" da sauri alhaji ya shiga cikin d'akin rik'e da little Mahmud na biye dashi Yana fad'in "lafiya momyn yara?" cikin rikicewa mom tace "Alhaji Basmah bata motsi.." ai kamar karta rufe baki Mahmud ya hau gadon tare da rungumota ajikinsa yana fad'in "Basmah, Basmah, oum little, Basmaty" Yana d'an bubbuga fuskarta amma ina.. Billy ce data shigo d'akin lokacin bayan ta ida kammala sallarta a d'akin mom dady ya mik'a mata little sannan shima yamatsa wajen gadon jikinsa amace, hannunsa ya kara a hancinta, ya aza yatsunsa biyu a jijiyar hannunta, sannan ya sake aza yatsunsa akan jijiyar wuyanta,


"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun," yafad'a har sau uku kafin yace


"Allah yayi mata rasuwa" daidai lokacin Ummi itama tashigo tana takawa da k'yar don dama jiya tanajin kukan yarinyar saboda itama batayi baccin ba a zaune takwana,  wata irin k'ara Mahmud yayi tare da k'ank'ame Basmah ajikinsa yana kuka Yana fad'in 


"No..kada kitafi kibarni Basmah, kin sani tare zamu rayu mukula da 'yarmu don allah kada kitafi kibarni"


Mom kuwa mutuwar tsaye tayi tana hawayen itama innalillahi wa inna ilaihirrajiun kawai take maimaitawa, 


Cikin k'arfin hali dady ya mik'e zai fita kawai yaga Billy dake rik'e da little tayi suuuuu.. tafad'i k'asa asume, da sauri Ummi tarik'o little d'in tana cije baki tayi k'asa zaune rungume da ita idanuwanta na tsiyayar da hawaye, shikuma dady kan Billy yayi tare da bud'e fridge ya d'auko ruwa ya yayyafa mata sannan tafarfad'o, kuka takeyi sosai tare da nufar gadon tana fad'in.


"Yayya kada kitafi kibarmu, ni Batool da kuma yaya duk munada buk'atarki ga little itama tanada buk'atarki sosai, yaya don Allah kace yayya ta tashi" haka Billy tayita sabbatu tana kuka hakama shima Mahmud Saida dady yayi da gaske sannan ya b'anb'are gawarta ajikinsa, ya kwantar da ita had'e da lullub'eta sannan yafita dashi,


Yaya Mahmud dady yakira sannan ya papi da Dr. Ahmad ya sanar dasu halin da ake ciki, gaba d'ayansu babu wanda yafad'awa matarsa halin da akeciki kawai cewa sukayi su shirya zasuje wani waje, 


Nan take kafin safe mutuwar Basmah ta mamaye ko ina, duk wanda yaji sai jikinsa ya mutu tare da shiga tashin hankali, sosai jimamin mutuwarta ya ratsa zukatan mutane da yawa tunawa da ganinta da sukayi jiya.


Batool kam kasa k'arasawa tayi da k'afafuwanta lokacin da suka wucikke k'ofar gidan cike da mutane ana yimata gaisuwa saida Dr Ahmad yarik'ota k'afuwanta narawa, dagudu ta kwace hannunta tafad'a cikin d'akinsu, kwance tahango gawar Basmah anlullub'eta ga Billy zaune sai sabbatu takeyi, k'arasowa tayi jiri na d'ibarta tabud'e Basmah dake kwance fuskarta sai  annuri take fitarwa zaka d'auka murmushi takeyi, da sauri taja baya tana k'ok'arin fad'uwa yaya Mahmud ya tarota, d'ago kai tayi takallesa tqna nuna gawar Basmah had'e da cewa


"Yaya bata mutuba, don Allah katasheta" tana kuka sosai, rungumeta yayi shima yana kuka yakasa cewa komai.


Ummi kuwa tsabar firgita yasa tuni labari ya canza mata a inda take zaune rik'e da little saidai mom tajiyo tana wani irin nishi dake kama da naquda tana cije baki, da sauri  mom tamik'e ta karb'i little hannunta tamik'awa Billy da itama yanayin da sukaji ummin ta shiga ya maido da hankalinsu wajen sannan tarik'ata ta wuce d'akinta da ita,


Kafin agama shirya gawar Basmah Ummi ta haifo 'yarta k'atuwa tubarkallah  amma saboda yanayin da ake ciki babu wani annuri balle farinciki a fuskokinsu hatta Ummi, "Alhamdulillah" kad'ai tafurta bayan ta haihu saboda jimamin yanayin da take ciki,


Kan kace me, tuni rasuwar Basmah da haihuwar Ummi tawatsu agarin inda da misalin k'arfe shabiyu aka fita da gawar Basmah don a sallaceta zuwa gidanta na gaskiya, ana d'auko gawar Billy ta taso rik'e da little tana kuka, ana rirrik'eta nan ta sake fad'uwa asume akayi kanta aka shiga da ita cikin d'aki, Batool ma tamkar mutum mutum takoma ba um balle a'a, mom kuwa Allah yasa mata juriya da dangana banda addu'a da takeyi tana fad'in "Basmah nayafe maki, ubangiji Allah yakarb'i bak'uncinki, Allah ya albarkaci 'yarki ya yafe maki dukan zunubbanki"


"Har aka kai Basmah gidanta na gaskiya Billy bata farfad'o ba, hatta wud'anda sukazo jana'izar Basmah sun tausayawa Mahmoud da yaya mahmud, baranma da suka shigo cikin gida wajen gaisuwa duk wanda ya shigo sai yafita da hawaye saboda tausayin halin da wud'annan 'yan uwa suka shiga na rashin 'yar uwarsu,


Dady ma duk da yawan mutanen da sukazo wajen gaisuwa hakan bai hanasa shigewa d'akinsa ba yayi kuka sosai yana mai rok'a mata gafarar Allah tare da Allah yaraya mata abunda tabari, yana zaune Umman borno tashigo d'auke da jaririyar da Ummi ta haifa, gaisuwa suka yiwa juna sannan tamik'a masa jaririyar tana fad'in 


"Yaya ga kyautar da Allah yayi maka, muyi hak'uri mu ajiye kuka gefe mugodewa Allah daya bamu kuma yakarb'a, kai 'ya'ya shida gareka aka karb'e maka d'aya, adaidai wannan lokacin akwai wanda d'aya ke garesa kuma aka karb'e masa shin ashe kai bazaka zamo cikin bayin Allah masu godiya ba?"


Karb'ar jaririyar yayi da gaba d'aya fuskarta tamkar ta Basmah lokacin da aka haifeta, murmushi yayi dake nuna iyakarsa bakin leb'ensa sannan yace


"Allah Akbar, Allahu Akbar, Allah kaine keda ikonka kaine mai jujjuya al'amurranka yanda kake so, nagode maka daka karb'ar mun 'ya kuma kabani wata adaidai lokacin, ya Allah ba wayona bane ni'imar kace da kuma baiwarka" kallon Umma yayi had'e da cewa


"Hafsatu dubi ikon Allah, gaba d'aya yarinyar nan da Basmah take kama" had'e da nuna mata fuskarta, goge hawaye Umma tayi da gefen mayafinta kafin tace


"Nagani yaya, rabon sai wannan tazo aduniya yasa waccan tatafi, ya Allah kayafewa Basmah" tak'are maganar tare da fashewa da kuka.


Hud'uba dady yayiwa jaririyar had'e da yimata hud'uba da sunan Basmah sannan ya mik'awa Umma ita


"Hafsatu afad'a masu cewa taci sunan yayarta Basmah" dady yafad'a yana goge hawayen idonsa.


"Allahu Akbar, Basmah ta tafi Basmah tadawo, ubangiji Allah ya rayata " Umma tafad'a tare da ficewa takoma cikin gida, mik'ewa dady yayi shima ya wanko fuskarsa sannan yakoma waje wajen amsar gaisuwa...





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


_Bazan manta dake ba Aunty nah *AISHA MATAZU* gaisuwa mai yawa da fatar alkhairi agareki bisa yanda kike bibiyar wannan littafi d'aya bayan d'aya, ngd sosai Allah yabar tare, am really appreciate it🤝❤_


_*INNAKA MAYYITUNN WA ANTUNN MAYYITUN*_❌✖


_*INNAKA MAYYITUNN WA INNAHUM MAYYITUN*_ ✔💯

_Apage d'in d'aya gabata hannuna yayi kuskuren rubuta wannan aya👆dake sama, don haka nafarkon kuskurene na biyun shine daidai Ina fatar Allah kayafe mana kurakuranm kabamu ikon gyarawa_


💎Page_____100💎


  

Ba family d'in alhaji Bashar mai furniture d'ai ba mutuwar Basmah ta tab'a hatta ilahirin al'ummar dake duniyar  da suke ciki mutuwarta ta girgiza, kasancewar dady mutumne mai kyakkywar mu'amala da kowa yasa tako ina mutane tururuwa sukeyi wajen gaisuwar 'yar tasa, iya rashi kam sunyisa amma gaba d'aya sun tattara sun barwa Allah daya basu ita  sun bita da dad'ad'an addu'o'i domin sune tsantsar soyayyar da zasu nuna agareta.


Sosai sunanta da aka mayarwa jaririyar da ummi tahaifa ya tab'awa kowa zuciya, baran ma Ummi da gaba d'aya sai abun yadawo mata sabo tunawa da shekarun baya da Basmah tayi zama hannunta lokacin da aka samu cikin Batool kafin ayayeta sai aka barmata sukuma mom da dady suka bar k'asar, gaba d'aya kamannin babyn sak ita alokacin haka sunan ma d'aya, ai nan take kukanta ya tsananta tanaji inama Allah zai sake bata damar rayuwa mai tsayi tare da wannan Basmah d'in har zuwa girmanta da gaba d'aya ta tarbiyantar da ita a yanda tsarin rayuwar Basmah take saboda ta dinga d'ebe masu kewar d'abiunta.


Ko kad'an dady bayada sha'awar zaman makokin da akeyi, shiyasa yana fitowa bayan angaggaisa wud'an da basu samu damar yin jana'iza ba sukayi masa gaisuwa sannan ya mik'e yayi godiya sosai bisa kulawa da lamurransa da 'yan uwa musulmi sukayi daga k'arshe yace


"Allah shine yabamu wannan 'ya kuma yakarb'i abussa, zaman da zamuyi anan bazai dawo mana da itaba, don haka kowa zai iya tafiya wajen al'amurransa, koba komai yin haka a shari'ance kuskurene, saboda haka babu amfani ga wannan zaman illa muyi mata addu'a Allah yajik'anta kuma ya gafarta mata, Mungode Mungode Allah yabar tare, yajik'an wud'anda suka rigamu gidan gaskiya" duk mutanen dake wajen suka amsa da "amin" tare da mik'ewa suna saka takalummansu d'aya bayan d'aya suna mik'a masa hannu sannan duk suka watse, wajen ya rage daga dady sai 'yan uwansa da Mahmud da mahaifinsa sai kuma yaya Mahmud da dr Ahmad, suma cewa dady yayi kowa yaje ga harkar gabansa saboda zaman bayada alkhairi wani zubinma tak'urawa ne, haka kuwa akayi kowa ya tafiyarsa dady da Mahmud da kuma yaya Mahmud kad'ai yarage suma d'in saida aka nuna masa cewa bai kamata wajen yazama ba kowaba saboda masu zuwa gaisuwa sannan ya amince suka zauna amma shi shigewarsa yayi cikin gida duk wanda yazo sai yasa ashiga dashi su gaisa yafito yatafiyarsa, hakama cikin gida yasa Umma ta sallami duk matan da sukazo gida ya rage daga su mom sai ita dasu Batool., 


Basmah kam tayi mutane sosai don har akayi sati mutane nashiga wajen gaisuwa kuma hakan bai hana satin na zagayowa ba dady ya yankawa little Basmah dabbar sunanta tare dasa akayimata aski kamar yanda musulunci ya tanada, saidai babu wani taro ko shagali da akayi saboda yanayi da alhinin da suke ciki, hatta naman acan family house d'insu dady aka aika dashi matan yannensa suka gyara, little Billy kuwa tuni akayi shawarar had'awa Ummi ita tashayar dasu su biyu wato little Billy da little Basmah, sosai suke samun kula wajenta duk da kasancewar bawata cikakkiyar lafiya ke gareta ba hakan baisa tarasa ruwan mono sosai ba, wani zubin har isarta yakeyi sai tayi masu da gaske sukesha saboda sun k'oshi,


Mahmud gaba d'aya ya susunce kamar wani marar amfani, sosai yaji mutuwar matarsa duk dako bawani dogon zama da ahak'uwa sukayi da itaba, yaso ace ambari Umma taje masa da 'yarsa sai adinga bata madara kodon yadinga ganinta yanajin sanyi amma anriga da anfi k'arfinsa dole yahak'ura, ranar da zai koma borno kuwa haka mutuwarta ta koma masa sabuwa, kuka yayi sosai little na ahannunsa sannan yayi mata addu'a tare da fatar Allah yajik'an mahaifiyarta, Batool kuwa har asibiti saida takwanta daga k'arshe dai anata yimata addu'o'i sannan aka samu takoma Batool d'inta ta da, amma gaba d'aya kuzarinta da walwalarta yaragu ba kamar da ba.


Koda Mahmud ya koma gida kasa zama yayi cikin gidansu ya tattara inasa inasa yakoma gida gaba d'aya, tabbas rashin mata ko miji wata fitinace arayuwa koda kuwa basa son juna balle shida bazaice baya son Basmah aransa ba, yanayin zaman da yayi da ita da irin hak'uri da kulawar da take basa uwa uba soyayyar da takeyi masa su suka taru waje d'aya sukayi tasiri azuciyarsa har yafara k'aunarta, abinci ma wannan sai Umma tayi dagaske da kuma rarrashi da ban magana yakeci,


Bayan rasuwarta da wata d'aya wajen aikinsa suka buk'aci daya tattaro masu inasu inasu idan bazai iya aikin ba yabasu sun sallameshi, hakan yasa yagyara yatafi yabasu hak'uri sannan yak'uduri watsar da komai aransa ya amshi rubutaccen al'amarin da Allah ya wanzar akansa yaci gaba da aikinsa acan reshen kamfaninsu na India da suka turasa wanda dama dak'yar yasamu ya kuccike lokacin daya dawo har Yana zancen zai rok'esu da suyi masa transfer, amma faruwar haka yasa yaji gaba d'aya baya buk'atar yaci gaba da zama annan shiyasa ya amince da komawarsa.


Bayan sati d'aya ya gama shire-shiren komawarsa yaje har k.d yagano little d'insa da tad'anyi wayau sosai gashi tayi k'iba saboda yanda nonon Ummi yakarb'eta. Hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba kuma yasamu natsuwa sosai aransa, rik'eta yayi ga hannu yasata agaba yanata faman yimata suruttan daba fahimta take yiba har yagaji sannan yamaida ita wajen Ummi yayi masu bankwana yawuce, saida yabiya ta mak'abartar da aka rufe Basmah yayi tsaye yana kallo, jiyake kamar Basmahrsa zata dawo, addu'a yayi mata sannan yabar wajen yana hawaye, Billy ma tuni takoma makaranta yayinda ko sau d'aya tunani da kewar 'yan uwanta basu tab'a barin taba, kullum cikin waya take da Batool idan bata kirata ba to ita zata kirata, akoda yaushe jisukeyi tamakar suma mutuwar zata rabasu shiyasa basa iyayin fiye da awa uku batare da sunji muryoyin junan suba.


A b'angaren malam jika kuwa ya kasa ya tsare yasa Billy agaba har saida tafara saurarensa duk dako ba sonsa takeyi ba,


Babu ranar da zatazo ta shud'e batare da yaya Mahmud yayiwa Basmah sadaka ba da niyar Allah yakai ladan agareta, hakama Batool duk ranakun alhamis da juma'a cikin yimata sadaka take, musamman dady ya gina rijiya da sunanta matsayin sadaqatujjariya agareta, a gaskiya tsayawar fad'ar yanda wannan family suke k'aunar junansu b'ata lokacine domin azahirine Basmah tarasu amma abad'ini ita rayyayyace atare dasu don akoda yaushe addu'o'insu da sadakokinsu natare da ita.


Mahmud kuwa tunda yakoma India kimanin shekara d'aya kenan bai dawoba saidai tawaya, sau da yawa idan yanaso yaga little d'insa saidai ya kira Mom ko Ummi ta vedio call anuna masa ita don da ita har little Basmah sun wayau sosai sun iya tafiya, idan kagansu zakayi tunanin cewa tagwayene, wanda da duk yasan tashin Basmah da Billy lokacin da suna k'anana babu abunda ya banban tasu dasu little. Mom kuwa bazaka iya tantancewa tsakanin little Billy da little Basmah kowa tafi so, kowace jinta takeyi har tsakiyar ranta ga wata soyayya mai tsanani da shak'uwa a tsakaninta dasu, duk wata kicaniyarsu da renonsu ita keyi,  inka ganesu wajen Ummi to tabbas vaccine zasuyi ko kuma zasu sha nono ne, haka ma Umma takan d'an zo can baka rasaba taduba jikanyar tata sannan takoma wani lokaci ma tare suke zuwa da alhaji shima ya dubata,


Ganin gaba d'aya Mahmud baya maganar aure gabansa gashi har ana shirin yaye little Billy yasa Umma takira dady awaya, bayan sun gaisa tace


"Dama yaya maganar d'an kace, kaga tunda Allah yakarb'i Basmah har yanzu ya kasa samun natsuwar da zai komayin batun wani auren, gashi yanzu ana batun yaye su little kaga akwai buk'atar ace yasamu wacce zata kular masa da ita, bawai don bani iya rik'eta a hannuna ba amma nafi sha'awar ace tana hannun ubanta ko ita yadinga kallah yaji sanyi aransa, shine nace idan Bilkisu bata tsayar da miji ba, mezai hana amayar da wannan alak'a da zumuncin da tun farko akaso yi da ita, tunda dama tana sonsa kuma shima yana sonta rabon wannan yarinyar da aka haifa ya hana aurensu"


Shiru dady yayi yana nazarin maganarta kafin yace


"Hakane maganarki hafsatu amma wani hanzari ba gudu ba, shin munada tabbaci akan cewa har yanzu suna k'aunar junansu? Kada azo ayi maganar auren kuma d'aya daga cikinsu ya bijiro da wani abu daban sannan kinga ita Bilkisu yanzu haka tana makaranta kinsan karatu takeyi na medicine kuma shekara bakwaine zatayi kafin tak'are gashi sai yanzu suka shiga shekara tabiyu, kina ganin anya zasu dai daita  kuwa don kinga idan akace ak'ire mata karatu inaga kamar ba'a yimata adalciba indai ba ita tabuk'aci haka ba" 


"Gaskiyane yaya, ni banida haufi ko shakku akan har yanzu suna k'aunar junansu kuma bana tantama akan cewa a wannan karon wata matsala zata iya bijirowa, maganar karatunta kuma  yaya tunda batayi nisa ba idan ta amince zata iya hak'ura suyi aurensu inyaso sai yasama mata gurbin karatu acan india tunda shekara biyar zaiyo kaga yayi d'aya yanzu saura hud'u, kafin sudawo natabbata takammala karatunta acan ko kuwa?"


"To bantari lumfashin kiba koma meye yanzu mufara tuntub'arsu muji ra'ayinsu, idan sun amince kinga babu wata matsala kome annan zasu kai k'arshe tsakaninsu"


"Shikenan yaya Allah yatabbatar mana da abunda yafi zama alkhairi kuma yagafartama Basmah da kulluhin musulmi baki d'aya" murmushi dady yayi saboda yanda tafahimcesa kafin yace


"Amin ya Allah hafsatu manga shiyasa nake jinki araina, kinada fahimta sosai, na tabbata da kece gurbin muzammil fushi zakiyi kiga kamar bani so ink'ara had'a jini dake don narasa Basmah"


"Haba yaya ai babu wannan tunani araina kwata kwata, koda Bilkisu tasake k'in amincewa da auren Mahmud akaro na biyu babu abunda zaisa nayi fushi don nasan babu mai auren matar daba tasaba, balle ina fatar Allah yasa ta amince don nasan shi har yanzu yana k'aunarta, kuma kaga ita kad'aice zata auresa munsamu natsuwa da kwanciyar hankali akan tabbacin tarbiyar little da kuma kula da ita, shiyasa nayi kwad'ayin hakan"


"Hakane hafsatu Allah yasa mudace"


"Amin ya Allah yaya sai anjima" 


Suna gama waya da dady takira lambar Mahmud, lokacin yana kwance yana tunanin yanda gaba d'aya Billy tasharesa tafita lamarinsa ko tunawa dashi batayi balle yasamu kira daga wajenta, watakilma tuntuni tasamu wani wanda yashafe mata soyayyarsa azuciya sai ga kiran Ummansa yashigo,  hannu yamik'a ya d'auko wayar tare dayin rejecting call d'in sannan shi yayi calling d'inta back saboda anfi sauk'in cin kud'i.


"Hello Ummana, barka da safiya?" Cike dajin dad'in muryarsa da taji tace


"Yawwa my son, kana lafiya?"


"Lafiya klw Umma yasu little?"


"Aikuwa lafiya lau take itama shekaranjiya nadawo dubata na isko har ana batun yayeta"


"Kai Ummi yanzu harsu little sun isa yaye? don Allah Umma kice Ummi tabarsu ko shekara d'aya su k'ara" zaro idanuwa Ummi tayi waje had'e da cewa


"Sannunka shugaban 'yan wauta, yanzufa ana maganar shekararsu d'aya da wata shida aduniya kake zancen ak'ara shekara ko don bakai ake tsutsa ba, kuma banda shirme irin naka waya fad'a maka cewa anayin fiye da shekara biyu ana shayar da yaro?" d'an yatsina fuska yayi had'e da sosa k'eyar kansa kafin yace 


"To Umma don Allah abarsu ko shekara biyunne suyi, wlh tausayin little nakeji sosai"


"To shugaban 'yan iyayi, ni rufemun baki ba wannan ne yasa nakirawo kaba, to waye baya tausayin nata inba dai rashin kunya irin taku ta 'ya'yan zamani ba" murmushi yayi had'e da jinkunya yana d'an shafa kansa kamar yana gabanta yaji tace


"Wai kai har yanzu tunanin naka bai baka kafiddo da matar da zaka auraba?, gashi kasan dole ana yaye yarinyar nan maidota hannunsu ya kamata ayi tunda munada buk'atarta"


"Umma wazan aura tunda Bilkisu nasan yanzu bata sona, kuma ni agaskiya bazan iya jurar auro wataba tazo tana cutarmun da yarinya, inda ace Bilkisu zata amince ta aureni da nayi auren don ni har yanzu ina matuk'ar sonta sosai fiyema da wanda nakeyi mata ada, amma tayama zanyi tunanin haka bayan tashareni azuciyarta ko tunanina batayi balle takirani, koda yake ma taya za'ayi ta aureni yanzu wacce tun farkoma tak'i aurenba balle yanzu da zataga har inada 'ya" sosai Umma taji dad'in kalamansa kuma tasamu amsar tambayar da tayi niyar yimasa, amma saita sa aranta bari ayi masa bazata, don haka sai tak'i sanar dashi komai tace


"Allah yasawak'e, amma bazamu zauna dakai ba aure ba don tak'amar cewa Bilkisu bazata iya aurenki yanzuba wannan yarage naka, nagaji da kullum ina yimaka zance d'aya amma kak'i kayi abunda ya kamata, to nida kaina zan samo maka mata awannan karon wacce zata iya kula mani da kai da kuma 'yarka, bazan zauna zaman jiranka ba nafad'a maka" Umma tafad'a da d'an fad'a fad'a,


"Umma kiyi hak'uri amma wlh ni babu wacce zuciyata ke k'auna idan ba Billy ba, don Allah kada ki auro mun kowace yarinya don bazata samu kulawa awajena ba"


"Aw ni kake gayawa haka, to shikenan kabari idan na auro maka ita ka kasheta kaji ko?" Umma tafad'a tare da kashe wayarta alamun kamar tayi fushi, jefa wayar yayi bisa gado kafin yasa hannuwansa yarik'e kansa dasu, wasu hawayene suka ziraro masa a idanuwa kafin yace


"Shikenan ni rayuwata ahaka zata k'are burina bazai tab'a cikiba?, to wlh duk wacce tayi k'ok'arin shigowa rayuwata sai tayi nadama itama arayuwarta, idan nayi biyayya na kyautata awancan auren to awannan akasin haka za'a gani don wancanma saboda 'yar uwatace shiyasa na rungumi qaddarata har tayi nasara akaina, amma wannan karon zan yak'i qaddaratane har sai nayi nasara akanta" jawo wayarsa daya jefa kan gado yayi zuciyarsa nak'una ya lalubo lambar Billy batare da wani shayiba ya danna mata kira, sau uku tana ringing amma bata d'agaba lokacin tana class suna lecture, jiyayi kamar yafasa ihu zuciyarsa natafarfasa tare da sak'a masa cewa da gangan tak'i d'agawa saboda ta dena sonsa, lambar alhajinsa yakira kamar zaiyi kuka, ringing d'aya tayi ya d'aga had'e da cewa,


"Hello my son kagama fushin dani?"


"Am sorry alhaji, ai bazan iya fushi da kaiba, kawai nad'an shiga damuwa ne"


"Mahmud wannan wace irin rayuwace, kai kace da zaran anyi maka maganar aure saika shiga damuwa ko kayita faman fushi, shin haka kakeso ka k'are rayuwarka ba aure don matarka tarasu?, Allah fa yabaka ita, don me da bazaka hak'ura ba" haba ina ruwan zafi Mahmud yafad'a tunda Alhaji yatayar masa da maganar da sukayi  shekaran jiya bayan shi so yakeyi ya taimaka masa yasa Umma tajaye qudurin da tayi na auro masa matar da bai sani ba kuma baya so, cikin damuwa yace


"Alhaji ayi hak'uri in sha Allah ina dawowa komai zaizo k'arshe amma don Allah karok'amun Umma kada ta auro mun wacce bana so don Allah alhaji"


"Aw ashe shiyasa kakirani? Madallah da wannan hukunci data yanke aini yakamata tuntuni inyi wannan tunanin had'aka da wata amma koyanzu takwana gidan sauk'i, zan iya hana Ummanka ta hanu duk da zamanta kaifi d'aya amma bazanyi haka ba saboda hukunci data yanke yayi mun daidai, kuma wlh kaji na rantse maka nan da wata d'aya kadawo ko kuma in sab'a maka"


"Alhaji, alhaji.." Mahmud kefad'a amma yaji har ya kashe wayars, jefar da tasa yayi ak'asa cikin b'acin rai tayi d'ai d'ai kota kanta bebi ba ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa idanuwansa arufe yanajin kamar zuciyarsa zata fito.


Suna gama lecture da sauri Billy tafito, husnah nabiye da ita abaya tana tambayarta ko lafiya, k'ok'arin fiddo wayarta tayi daga cikin jakarta cikin fara'a da jin dad'i saboda tuntuni taci alwashin cewa matuk'ar Mahmud bai kirataba ko soyayyarsa zata kasheta bazata kirasa ba balle har tanuna masa cewa babu abunda ya canza azuciyarta game da k'aunar da takeyi masa ada kodon takula da d'iyar 'yar uwarta data bata amana, sai gashi yau yakirata har sau uku saboda malami dake cikin class ta kasa d'agawa, kallon husnah tayi bayan taciro wayar tana murmushi tace


"Husnah yayanah ne da nake baki labari yakirani my love is back to me again" batajira me husnah data bita da kallo tana dariya zatace ba tayi calling nasa back, amma kash har sau uku itama tana kira lambarsa akashe saboda yanda tayi d'aya d'aya ak'asa daya bugata, cike da damuwa tajuyo tana kallon husnah kafin tace 


"Kinji kuma wayar tasa akashe, kodai soyayyarsa tasa yafara yimun gizo har awaya husnah" tak'are maganar had'e da mik'a mata wayar, karb'a tayi tareda duba jerin missed calls d'in dake cikin wayar sannan tad'ago kai tace


"Billy ba gizo bane, wlh shine yakira har sau uku, koba shi kika sakawa *Abban my baby*"


"Eh shine.." tafad'a tare da mik'a hannu zata karb'i wayar, ai kafin tarufe baki sai ganin mutum tayi yaci gabanta, cikin k'ufulewa da b'acin rai dake cikin zuciyarta ta d'ago kanta, malam jika tagane tsaye yana faman sakar mata murmushi, juyar da kanta gefe tayi tare da rab'asa zata wuce don bataso ta jid'ar masa damuwar da take ciki akansa, sake tare gabanta yayi yana fad'in


"Haba gimbiyata, ya zaki rab'ani kiwuce bayan kinsan kin fara saba mani da soyayyarki da kuma kulawa" wani iska billy taja a hancinta sannan tafurzsa awaje tare dasa hannu d'aya ta dafe k'ugunta dashi, husnah naganin haka tabar wajen aranta tace


"Tab..yau qawata zatayi tsiyar, malam jika yau kam zaka ji zafafan kalamai" ai bata gama tunanin da takeyi ba taji cikin b'acin rai Billy nafad'in 


"Wait malam jika kake ko waye? lemme end it here, i don't bloody care who ever are you! don Allah kak'yaleni, kabarni haka kanajina ko? Haba! Kai wane irin mutumne fisabillillahi da bazaka fahimta ba? duk hanyar da zanbi inga cewa mun rabu lafiya batare dana cutar da kaiba nabi don karabu dani cikin sauk'i amma kak'i fahimta, kasan komeye dalili kuwa, saboda nasan zafin so da kuma illarsa, nasan yanayin da zuciya keshiga idan tana son abu takasa samunsa, bari nafad'a maka gaskiya wannan zuciyar tawa mutum d'aya na tanadawa ita aduniya," tak'arsa maganar tana nuna saiti zuciyarta sannan taci gaba da cewa "duk da ada inada tabbaci akan bazan tab'a samun saba saboda nisan da yayimun hakan baisa daidai da point d'aya na k'aunarsa yafita acikin zuciya taba shin kana tunanin cewa yanzu da nake da tabbacin zan samesa in Allah ya yarda sai kuma nacire k'aunarsa acikin zuciyata nasaka taka?, Malam jika zanfad'a maka gaskiya koka yarda ko karka yarda shi nake so kuma shine farincikina sai in kuma idan Allah yaso ya sake jarabtata akaro nabiyu shi zaisa naso wani bayan shi, kuma koshi inda tabbacin kawai gangar jikinace zata sosa idan har hakan tayuyu amma zuciyar Billy bazata tab'a son saba" ko kad'an bata damu da mutanen dake gefe gefensu sun zubo masu idanuwaba taduk'a gabansa tare da cewa


"Narok'eka da kayi hak'uri kabarni, kayi hak'uri ka gwada amsar wannan jarabawar da Allah yayi maka kamar yanda nima nayi, natabbata Allah zaiyi maka musanya da wacce tafini zama alkhairi"


Cikin b'acin rai malam jika yace


"Shikenan kitafi nabarki Billy, yazan da raina, da nad'auka kece rabin jikina, amma yanzu nayarda cewa yaudarata zuciyata keyi, duk da haka bazan manta dake ba dare ko da rana, Amma Ina rok'on Allah daya musanya mani da wata Bilkisu wacce tamallaki dukkanin halaye da kyawon sura irin taki, ngd da gaskiyar da kika fad'amun, Allah yacika maki burinki"


Mik'ewa tayi had'e da cewa "Amin ya Allah nima ngd" sannan tajuya tanufi inda husnah take can gefe atsaye suka wuce, shikuma yafi k'arfin minti biyar atsaye wajen kafin yajuya ransa a dagule ya shige motarsa yabar makarantar aguje ransa na suya, baki husnah tasaki tana kallon Billy da har yanzu fuskarta babu annuri ita kuma tayi kamar bata gane taba, yini ranar Billy tayi tana trying no Mahmud amma bata samesa ba, jitayi gaba d'aya ranar haushin kowa da komai ya isheta, komai baya yimata dad'i hakan yasa tahad'a kanta da guiwoyinta tanata kukan da batada merarrashinta akai,


Jin k'arar wayarta yasa tayi saurin d'ago kanta tare da jawo wayar dake saman pillow tad'aga batare data tsaya duba sunaba cike da fatar Allah yasa Mahmud d'inta ne, muryar dady tajiyo tadaki dodon kunnenta yana fad'in


"Bilkisu" da suri tasa hannu tagoge hawayen idonta tare da daidaita muryarta tace


"Na'am dady inawuni? Barka da marece, anwuni lafiya?"


"Yawwa Bilkisu lafiya klw, ya kike ya karatu?"


"Alhamdulillah dady, yasu little da su mom kowa lafiya?"


"Lafiya lau, Allah ya taimaka, akwai wata matsalane?"


"A'a dady babu ko kad'an?" Ta aje maganar tana k'ok'arin danne damuwarta


"Shikenan kiduba za'ayi maki aleart naturo maku duba arba'in keda 'yar uwarki zainab koda kunada wata matsalar kinji ko?"


"To dady mungode Allah yak'ara bud'i da d'aukaka kuma ya tsawaita mana rayuwarka cikin amincinsa" lumshe idanuwa yayi don yanajin dad'in wannan addu'ar da  takeyi masa kafin yace


"Amin ya Allah bikisu Allah yayi maki albarka"  ta amsa da "Amin" har zai kashe wayar da sauri tace


"Dady yasu Umma da yaya Mahmud? Kuna waya kuwa?" Murmushi yayi had'e da cewa


"Lafiya klw, yawwa dama nace yakamata idan kinsamu wanda kikeso kiturosa atsayar maki, saboda bazai yuyu nace sai kin kammala karatunki ba, shekara bakwai ba wasa ba, kuma nasan dak'yar idan zaki amince ki auri zab'in da kika kawo farko tunda da bakinki kikace bazaki samu farinciki idan kika auresa ba saboda bakya sonsa balle nasaran zaki mayewa takwararki gurbin yayarki, shiyasa ma nayi saurin da katar dashi daya nemi kawomun maganar?" Wani irin farincikine ya lullub'e Billy, kenan yayanta har yanzu shima yana sonta?, kenan wannan maganar tasa yakirata suyi d'azu shine har dady kenema ya maida hannun agogo baya, turo d'an bakinta tayi kafin tace


"Nifa dady babu wani wanda nake so, kuma da bakina ban tab'a furta cewa bana son d'an uwana ba, kawai dai nace.." sai kuma tayi shiru takasa k'arasawa, dariya dady yayi had'e da kashe wayarsa don yasamu amsarsa cikin tak'aitaccin lafuzzan da tayi k'wara biyu "Allah sarki, haka shi son gaskiya yake, baya tunanin komai kuma  baya b'oyuwa aduk lokacin daya motsa, tana son sa amma bazata iya furtawa ba, zata auresa amma bazata fad'aba, tsarin da Allah yayo na sake had'uwarsu a inuwa d'aya yasa ya Allah ya amshi ran 'yar uwarsu, ikon Allah kenan babu yanda bayayi" dady yafad'a yana jinjina al'amarin,


Dariyar itama tayi had'e da rungume wayar, saiga zainab da bata jima da fitaba tabarta zaune wajen tana kuka tashigo, binta tayi da kallo had'e da cewa


"Tofah! Mai kuka kuma takoma dariya, fad'amun insha Aunty Billy" pillow Billy ta d'auko tajefeta dashi tana dariya had'e da saukowa kan gadon tace


"Kan munafiki baya gashi, wato d'azu baki tambayi meyasa nake kuka ba kika tafi kod'an rarrashinnan babu sai yanzu kiwani tsuromun idanuwa kina tambayar meyasani dariya to koma meye baza kijiba" tamitsile mata ciki tare da juyawa tafice tanufi d'akinsu husnah tan tsallen farinciki, b'ata rai zainab tayi tare da shafa inda tamitsile mata ciki kafin tace


"Yo waya kaini tambayar dalilin kukanki balle har nima kisakani kukan, kada Allah yasa kifad'i koma meye intayi tsami maji" sannan ta kakkab'e gadonta tahaye tare da jawo wayarta takira masoyinta Khalid abokin Dr.ahmad don tuni suma sun jone.


Bayan kwana biyu Umma takira dady tasanar masa yanda tayi da Mahmud, dariya yayi sosai kafin yace


"Yara kenan?, Ai kinji kinji yanda nayi da 'yar taki itama" nan ya labarta masa shima yanda sukayi da Billy sunata dariya daga k'arshe dai taba Alhaji mijinta waya sukayi magana da dady inda nan take suka tsaida maganar aurensu nan da wata d'aya idan Allah ya kaimu kenan lokacin da zai dawo, cikin sati biyu iyayensa suka sake dawowa Suka nema masa auren Billy wajensu Alhaji kabiru tare da sadaki, Mahmud kuwa nacan har zazzab'i yayi, bai koma bi takan wayarba shiyasa baisan abunda ake shiryawa ba,  Batool da yaya Mahmud kuwa ba k'aramin farin ciki sukayi ba lokacin da sukaji wannan maganar, dangi da 'yan uwa kowa sai sama Billy albarka akeyi data amince zata auri Mahmud, Umma da alhaji ko sunyi nemansa har sungaji wayarsa akashe wanda daga k'arshe haushi da takaicin yarufesu a tunaninsu fushi yakeyi dasu don sun nema masa aure, baccin gata suka yimasa, 


Tuni Billy tayi bankwana da 'yan makarantarsu zainab har da kukanta haka ma husnah randa zata wuce yini tayi tana kuka, oh Billy ba kunya kowata wahala dady baisha da itaba wajen zancen ajiye karatunta ta amince cikin sauk'i abun nema yasamu, Wanda hakanne yasake tabbatarwa da dady irin soyayya da k'aunar da takeyiwa d'an uwanta wanda sai yanzu yafahimci cewa ko lokacin da tahak'ura da aurensa k'arfin soyayyar 'yar uwarta ce data rinjayi tasa yasa ta iya jurewa da hak'urewa bawai don bata sonsa.


Saboda yanda Umma taji haushin kashe masu wayar da yayi yasa takira Billy tace kada ta tab'a nunawa Mahmud cewa shizata aura koya kirata, kawai tafita batunsa inya iso yaga kowaye amaryarsa, ko kad'an itaka kam Billy wannan plan beyi mata ba, amma saboda Umma dole tayi hak'uri dama itama yabata haushi kiransa da kullum take famanyi baya d'aga waya, nan take ta amince da abunda Umma tace.


Mom kuwa ita tashige gaba wajen hidimar bikin dama Ummi nacan na fama da nonuwanta dake ciwo saboda yayen da tayi don haka takoma gefe tana kallonsu iya nata abunda yazama dole tayi amatsayinta na uwar d'iya, duk da mom gaba d'aya hidimar ta tuno mata da abubuwan da suka faru da dama alokacin bukinsu yaya Mahmud amma haka tajure ta manta da komai tayi imani da Allah yabata Basmah kuma shiya karb'i abissa.


Ana saura sati d'aya d'aurin aure Mahmud yaje yasiyo sabuwar waya yasaka layinsa aciki don har 'yar rama sai da yayi  saboda tunanin auren da ummanshi ke son yimasa daga k'arshe ya yanke shawarar zai lallab'a Umma tayi hak'uri idan yaje hutu daga nan sai ya d'aukikke 'yarsa sudawowarsu kuma bazai komaba sai sadda yasan anbuk'aci ganinsa, to alokacin yasan babu wanda zai takurasa da zancen auren, wannan dalili yasa yayi tunanin sayen wata wayar yabud'e layinsa.


Kamar da wasa umma na zaune sun gama waya da alhaji akan ya canzawa Mahmud gida saboda yanda taga gaba d'aya wancan yafita ransa saboda rashin matarsa tace bari tagwada kiransa taji ko zata shiga, ai kuwa cikin sa'a bugu biyu tayi taji tafara ringing,  Mahmud da gama searching d'in wayar kenan yaga Kiran Umma yashigo, gabansa ne yafad'i yayi saurin tsinke kiran yana faman jero addu'o'i kafin yakirata.


Saida takusa tsinkewa sannan tad'aga tare da cewa


"Agaisheka my son, ubangiji Allah dai yayi maka albarka kuma yarabaka da wahala, yanzu Mahmud mukake kashewa waya don muntirsasaka kayi aure? Wai shine har zaka d'auki fushi damu?" Jikinsa ne yayi sanyi cikin girmamawa yace


"Kuyi hak'uri Umma nayi kuskure, kuma lalacewa wayata tayi wlh ba kasheta nayiba, Umma dole inyi maki biyayya amma kibari har sai nadawo sai muyi magana, idanma so kikeyi inje har gidansu wacce kika zab'amun da kaina innemo aurenta duk da nasan bana sonta wlh zanje"


"Dalla rufemun baki wani zakayiwa dad'in baki, ai tunda abunnaka yazama tsiya munriga mungama yin komai idan kaga dama kada kadawo, wlh kahad'u da b'acin raina, satinnan maizuwa za'a kawo maka mata don haka yarage naka, ita wacce ma kake zancen aure zatayi itama satinnan da wanda ranta keso yanzu kaga kai saika tabbata a gauronka tunda bakasan ciwon kankaba " sannan takashe wayarta.


"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Billy aure zatayi dama shiyasa tak'i d'aga wayarsa? Tabbas idan hakane taci amanar k'auna kuma sai Allah yakamata, amma taya zai yuyu yabari wani ya aure masa farincikinsa bayan ya d'aukarwa Basmah alk'awarin zai kawota amatsayin matarsa kuam burin ransa da zata iya kula masu da 'yarsu" yafad'a tare da lalubo lambarta awayarsa,


Billy dake zaune ita da Batool tana tuyar wainar fulawa ita kuma Batool tana kallon pics a wayarta taji wayar tana ruri, ABBAN MY BABY..da tagani arubuce jikin screen d'in nayawo yasa tamik'awa Billy wayar tana fad'in


"Allah sarki yaya Mahmud, walh tausayi yake bani" k'in d'aga wayar da Billy tayi har ta tsinke yasa Batool taci gaba da cewa


"Allah twiny bakida kirki, ai wannan ma mugunta ne, ita kuma Umma Allah tafiye tayarwa da rayuwa hankali, ko tsoro batayi yashiga wani halin" zataci gaba da maganar Billy ta aza yatsanta abaki alamar tayi shiru saboda kiran sa daya sake shigowa, cike da farincikin dake tabbatarwa Mahmud da cewa hankalinta kwance yake bata cikin damuwa kamarsa tace


"Hello yaya Ina wuni?"


Rufe idanuwa yayi cike da takaici kafin yace 


"Menene gaskiyar abunda naji ana fad'a" cikin b'acin rai, zaro idanuwa Billy tayi kafin ta had'iye wasu yawu da k'yar tace


"Name fa?" Jin yayi tazo masa da tambayar cikin rene, yana wani irin huci yamik'e cikin b'acin rai da k'arfi yace 


"Karki maidani sakarai Bilkisu, kada kisa nakasa controlling kaina bisa renin hankali irin naki, nizaki yaudara, nizaki ciwa amana saboda bakida tausayi, gaba d'aya baki damu daniba saboda tsananin sonkai irin naki kin manta da soyayya da k'aunar da nake yimaki gaba d'aya, koda yaushe burinki insha wahalar rayuwa bayan kinsan cewa my life is incomplete with out you" lowering voice d'insa yayi sannan yaci gaba da cewa "Bilkisu kesani Ina sonki sosai, qaddarace tashiga tsakanina dake har muka nisanta da juna amma shine kuma qaddara tasake bamu dama zakije ki auri wani bayanni, kuma har kina farinciki da hakan"


Amaimakon ranta yab'aci da kalaman da yake yimata saima murmushi take famanyi jin yanda har yanzu wannan soyayyar da yake yimata bata canzaba, ahankali cikin muryar da duk abunsa dole ta tank'wasa b'acin ransa tace


"Haba yaya, meye abun b'acin rai anan bayan kaima auren zakayi, ni inaga kamar lokaci yayi daya dace muhutar da kanmu musama zukatanmu natsuwa tunda kowanenmu aure zai yi, pls kai yayanane kamanta da komai karik'eni ababban matsayi na 'yar uwarka domin yafi muhimmanci akan wancan matsayin, zaka rabu dani wataran idan Ina matarka amma amatsayin k'aunarka bazamu tab"a rabuwaba har abada zamu rayu nahar abada amatsayin 'yan uwa batare da munrabeba..." Tsabar takaicin kalamanta baisan lokacinda ya kashe wayarba tare da blocking d'in no. Zaune yayi yana tunanin inda kalamanta suka sama gaba, wato inya fahimta dai da gaskene auren zatayi, kuma taciresa aransa bata sonsa, fad'awa yayi kan gadon fuskarsa na kallon cielyn idanuwansa arufe yace


"Am sorry Basmah, bazan iya cika maki burinki ba saboda 'yar uwarki tadena sona"


Itakam dariya tayi tare daci gaba da tuyar wainar fulawarta duk da k'asan zuciyarta bataji dad'in haka ba, duka Batool ta kaimata abaya tare da cewa


"Wlh Allah bakyau abunda kikayi, banda Umma ce tatsara hakan Allah dasaina fad'a masa gaskiya"


"Hh ai Umma tace surprise me take son yimasa"


"Jacan don Allah surprise ko suffering, Allah yasa yaya Mahmud yakirasa yafad'a masa"


"Ba Amin ba wlh, ai k'ara yasan ba'a samun mai gadon zinari cikin sauk'i" haka dai sukaci gaba da firarsu har dare Batool nak'ara enlighten d'inta akan rayuwar aure,


Da daddare suka kaita gida itada Dr Ahmad saboda yanzu arzik'i yafara bud'uwa har yasai mota kuma gininsa na k'aton gidan da yakeyi  nacan yafara azawa a anguwar maitama,


Shawarar da Umma taba Alhaji ita yabi don wani d'aya daga cikin gidansa dake opposite dasu yasa aka gyarawa Mahmud, dady kuwa bai dubi kayan Basmah dake can ba yasa aka zubawa Billy nata wasu kala daban sabon design kamar yanda yayiwa 'yan uwanta, kodasu baba k'arami suka nuna masa cewa kamata yayi ace tunda na Basmah basuyi komaiba abarmatasu tazaunesu cewa yayi a'a ai hakan bai halattaba domin kayanta hak'k'in magadan tane, sannan itama Billy tanada hakki dashi don haka kamar yanda yayiwa 'yan uwanta itama dole yayi mata,


  Billy dai cewa tayi babu wani program da zatayi inba walima ba, haka akai ko ranar juma'a akayi walima taji da gani, sosai Billy tayi kuka ita da Batool tunawa da 'yar uwarsu Basmah saboda kusan malaman da sukayi wa'azi a waccan walimar aurensu na farko sune suka sakeyi a wannan, bayan an kammala aka raba manya manyan jikkuna da aka rubutawa HAPPY MARRIEGE LIFE BILKISU AND MAHMUD PILOT, wacce ak'asawa cutecy Little's Billy & Basmah, babu komai aciki illa kayan motsa baki kala kala da drinks da naman kaji dasu snacks ga take away d'insu friedrice da tasha kayan lambu kai komaidai Masha Allah Masha Allah


Musamman dady yayi booking d'in jirgin da zaikai amarya da wud'anda sukazo d'aukarta da masu kaita don tak'aita nisan tafiya da Basu wuce mutum takwas ba, had'i da ita da mom goma, 'yan uwan Ummi uku dana dady uku, sai faraaha da Batool sannan mom da amarya wanda idan aka qidanya kud'in jirgin da dady zai biya bakomai bane acikin dukiyar da Allah yayi masa, 


Da misalin k'arfe 1:00pm aka d'aura auren Mahmud pilot da Bilkisu Bashar maifunitures bisa sadaki dubu d'ari lak'adan ba ajalanba, indaana gama d'aurin aure yaya Mahmud ya damk'a matasu a hannunta. Tuni yaya Mahmud yabi 'ya d'aurin aure suka wuce don yace shi bazaibi mataba kuma dole dashi za'aje kai 'yar uwarsa rabin ransa wanda hakan yasa yabi 'yan d'aurin are saboda jirgin da za'a shiga kai Billy bazai tashi ba sai k'arfe 5:00pm namarece, 


Billy kam yau idanu sun raina fata, duk d'oki da farincikin da takeyi zata auri masoyinta saida yakau saboda kukan data sharb'a, momce da kanta tarik'ata takaita wajensu dady da yannensa dake part d'insa lokacin da za'atafi suka yimata nasiha sosai tare da adduar Allah ya tamata rik'on 'yar 'yaruwarta data barmata amana sannan aka wuce da ita part d'in Ummi dake zaune tare da wasu 'yan uwanta tana rungume dasu little, nan suma suka yimata nasiha mai ratsa jiki wacce tasa kukan nata yak'ara tsananta, hannunta Ummi tarik'o sannan ta damk'a mata little Billy a hannunta tace


"Bilkisu ga amanar marainiyar Allah nan a hannunki, kece uwarta yanzu kuma gatanta, shin amatsayina na mahaifiyarki wane irin tabbaci zaki bani bisa tarbiyar dana yimaki akanta" cikin shesshekar kuka Billy tace


"Ummi zankula da ita bisa gaskiya da amana kuma zan bata tarbiya bisa tsoron Allah batare dana cutar da itaba har izuwa k'arshen rayuwata." kukane yaci k'arfin Billy takasa cigaba da magana, ita kanta Ummi hawaye takeyi kafin tayi k'arfin halin cewa


"Alhamdulillah, ya isa haka, ahaka kad'ai kika tsaya kuma kika tabbatar da abunda kika fad'a natabbata Bilkisu zatayi rayuwa maikyau kuma 'yar uwarki zatayi alfahari dake kuma nima zaki sani farinciki, tashi kuje cikin amincin Allah, ubangiji Allah yayi maki albarka kuma yabaki ikon rik'e wannan amana, yabaki zuri'a masu albarka" tana rufe baki ta tashi tashige d'aki tana kukan rabuwa da 'yar tata, duk wud'anda ke d'akin suma saida suka zubar da hawaye saboda tausayi, mom ma tayi kuka sosai kaman ba gobe sannan aka fita da ita zuwa gidan mijinta, dama tuni yaya Mahmud yawuce da kayan little Billy don haka Batool ta d'aukota yayin da faraaha ta d'auko little Basmah don gida tabar mu'azzam wajen Ummi da take shima anjima da yayesa tun yanada shekara d'aya da wata hud'u saboda shigar cikin da faraaha yasamu na biyu.


Mahmud kuwa bai baro India ba sai ranar d'aurin aure tunda asuba, shima d'in saboda Alhaji ne daya kirasa yayi masa fad'a sosai tare da nuna masa b'acin ransa sannan yabaro k'asar don data tashi za'a biyewa bazai dawoba sai wani sati, 


Kai taye jirginsu na isa gidan Umma Suka nufa da ita, inda farinciki yasa tarasa Ina zatasa kanta, murna da farinciki tayi sosai harda 'yan hawayenta kafin tayimata nasiha da samata albarka, tare da ita aka kai Billy har cikin gidanta dake kallon nasu, mom nata tsokanarta tace


Ita kam babu wata sarakkuta tsakaninta dasu, ita gwaggoce kuma uwar d'iya don haka bawata kunya da zataji,


Sai misalin k'arfe 8:30pm nadare Mahmud ya iso gida tare da rakiyar wani abokinsa daya sauka wajensa tunk'arfe hud'u na marece amma yak'i shigowa garin sai yanzu, lokacin yaya Mahmud yafita shida faraaharsa da little Basmah zagaya gari, ita kuma Batool tana can tareda Billy don cewa tayi tsoro takeji bazata iya zama ita kad'aiba, kasancewar bak'i na part d'in da aka saukesu yasa Mahmud wucewa kai tsaye d'akin mahaifinsa don tun amota sukayi waya, koda yashiga Umma naciki taje kaimasa abinci fuskarnan tasa ko walwala babu, cikin farinciki Suka tarbesa tare da yimasa sannu da zuwa, ganin fuskarsa babu walwala yasa Suka zaunar dashi sunata bashi hak'uri da lallashinsa, Umma da kanta ta dinga bashi abinci abaki tana bashi magana har saida taga ya saki ransa sannan tace yaje ya watso ruwa sai yazo yagaida bak'i, 


Haka kuwa akayi d'akinsa ya wuce ya watso ruwa, sannan yaje ya gaida bak'in da akace lokacin mom tashiga toilet 'yan uwan dady kuwa dama yasansu baiyi mamakin ganinsu ba tuda 'yan uwane yazata bukin nasa sukazo, na Ummi kuma bai wayesu ba, abokinsa yabi suka sake fita inda yanata yimasa Sheri wai ango ango, suna tashi su yaya Mahmud nadawowa, koda yasamu labarin cewa d'an uwansa ya iso cewa yayi a k'yalesa gone zasu had'u kafin suwuce don yagaji bacci yakeji,


Batool na ganin goma tayi ta tattara inata inata tayi wajen mom gida yarage Billy kad'aice aciki, 


Saida goma da rabi tawuce Billy taji motsin shigowarsa shida abokinsa da sauri taja mayafin fuskarta tarufe, tsaye yayi bakin k'ofa tare da mere baki yana kallonta kafin shureim yayi k'ok'arin shigowa dashi da k'arfi, muryar Junior suka jiyo a palour hannunsa d'auke da wani tray daya sha soyayyin kaji da sukasha source anyi rapin d'insu da wata leda mai kyalkyali sai had'ad'd'en fruithsalad mai sanyin gaske daya sha madara da zuma acikin wani bowl Umma da taji tsayawar motarsu tace yakawo, shureim ne yaje yakarb'o yakawo ya ajiye masu saman madubi sannan yayi masu saida safe, guntun tsaki yaja tare da bin bayansa ya rufo gidan, har zai shiga yaji ankira wayarsa Yana dubawa yaga ashe Batool ce,


Cike da gajiya ya d'aga had'e da cewa


"Hello sister" murya k'asa k'asa tace


"Na'am yaya Mahmud, andawo lpy?"


"Lpy klw, Ina mijinkine yabarki yin waya a wannan tsohon daren"


"Yaya don Allah ba wannan ba, kashiga d'aki surprise nanan anyi maka believe me, yanzu haka muna nan.." ai bata rufe baki ba yayi saurin shiga cikin bedroom d'in yana tunanin wani abu da zuciyarsa ke raya masa, bakin gadon ya isa had'e da yaye mayafin fuskar Billy, wa zai gani a cikin gidansa, a d'akinsa kuma amatsayin amaryarsa inba Billy ba, kenan hasashen da yakeyi yazama gaskiya? Tirk'ashi yafad'a abayyane tare da murza idanuwansa Yana kallonta, wani irin murmushi ta sakar masa da yasa yaji da zai iya mutuwa alokacin d'aya mutu, tuna kalaman data yimasa yasa sai kuma yabasar tare da kauda kai  yana fad'in


"Meyasa kika aureni bayan kince bakya Sona"


"Bantab'a cewa bana sonka ba saidai ince bazanyi farinciki idanna aureka ba kuma shima sab.." dakatar da ita yayi ta hanyanr d'aga mata hannu don bayason jin dalilinta tunda ya dad'e da saninsa, 


"Meyasa kika aureni yanzu?"


"Saboda kai kad'aine na mallakawa zuciyata, kuma kaine farincikina kuma hasken dake yimun jagora acikin tafiya aduniyar soyayya"


"Meyasa kika b'oyemun cewa ni zaki aura kikasa zuciyata takusa tarwatsewa"


"Saboda intabbatar maka da cewa komai rintsi komai wuya atare zamu rayu kuma atare zamu mutu, intabbatar maka da cewa kai kad'aine kake da mallakina da kuma duk abunda ketare dani"


"Bilkisu kin tabbata har yanzu kina Sona kuwa"


"Karok'i Allah yabamu aron lokaci da aryuwa da kanka zaka tabbatar da hakan"


Juyowa yayi yana kallonta had'e da cewa "akoda yaushe kece mai yin nasara akaina saboda hakurinki da juriyarki, kiyafemun bisa kausasan kalaman danayi agareki, tsantsar b'acin rai da kishin jin cewa wani zai mallakeki yasa na aikata haka"


"Konice iya abunda zanyi maka kenan koma fiye da haka, bazan iya auren waniba ba bacin soyayyarka da k'aunarka na cikin zuciyata idanko nayi hakan to natabbata kowaye gangar jikina kawai ya aura amma zuciya da rouhina gaba d'aya na wajenka" wata irin runguma ya kaimata had'e da cewa


"Ina sonki Bilkisu, Ina sonki sosai fiye da wandakike yimun"


Wayarsa yaciro ya yiwa Batool transfer d'in naira dubu hamsin sannan ya tura mata message kamar haka.


_Thank you sister ga goron albishir d'inki nan kici da hak'uri tabbas badon keba da zuciya ta d'ebeni daren yau natabka babbar asara wajen yiwa Allah godiya da wannan ni'imar daya yimun_ 


Karb'e wayar tayi ahanunsa da sauri tana karanta message d'in da taga yatura ga contact d'in Batool data gani aeubuce, murmushi tayi aranta tace Allah sarki my twiny kindai yi nasarar  bayyana sirrin kafin yagani da kansa ahankali ta furta Ina sonku 'yan uwana, shima murmushin yayi tare da juyawa yayi sujudush shukur sannan ya d'ago ya kalleta yace


"Nima Ina sonki sosai 'yar uwata kuma matata"...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_* 


👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


             🔚 _*END*_🔚


💎Page_____101💎



    Lumshe idanuwanta tayi had'e da bud'ewa itama tace


"Nima Ina sonka yayana mijina" nan take yaji kamar ank'ara masa wani kuzari akan wanda yake dashi duk kuwa da gajiyar doguwar tafiyar da yayo,


Mik'ewa yayi yacire mata mayafin sannan yarik'o hannunta suka shiga toilet, da kansa ya kunna fanfo ya dinga d'ebo ruwan a hannunsa yana zuba mata tayi arwala saida ta kammala sannan shima yayi tasa suka fito suna yiwa junansu kallon so da k'auna, ganin yanda gaba d'aya yacanza alokaci d'aya yasa Billy ta noce kanta k'asa tana murmushi, tabbas arayuwa babu abunda yakai hak'uri dad'i, lokacin yinsane kawai keda wahala har mutum yaji tamkar kamar bazai tab'a fita cikin qunci da damuwa ba, yau gata ga masoyinta da farko tayi tsammanin cewa ya haramta gareta kenan har abada sai gashi Allah ya halasta matashi akaro na biyu, tana cikin wannan tunaninne taji yarik'o hannunta lokacin harya shimfid'a masu abun sallah, 


"Me kike tunani kuma bayan Allah yariga daya mallaka makini gaba d'aya, kizo mumik'a godiyarmu agaresa saboda yacika mana burinmu nazamowa ma'aurata a k'ark'ashin inuwa d'aya" yafad'a tare da shiga gaba ya kabbarta sallah, raka'a biyu yayi masu a daddafe ya sallame sannan yajuyo had'e da d'auko chicken source d'in da Umma ta aiko masu dashi tare da fruithsalad, yage ledar yayi sanna ya jawota ajikinsa ya dinga bata tanaci itama tana basa, saida suka cikawa juna ciki sannan yaje kitchen ya d'auko spoon d'aya yana bata fruithsalad d'in abaki tanasha har saida tak'oshi 


Kusan atare suka kwashe kayan kafin ta koma shiga toilet ta wanko bakinta, tana fitowa taga fitilar bedroom d'in akashe, gaban tane ya fad'i kafin jikinta ya soma rawa jin mahmud yarik'o hannunta, runtse idanuwa tayi yayinda shikuma ya d'auketa cak yadireta akan gado, wani irin shauk'i da k'aunarta yaji suna fizgarsa alokaci d'aya wanda nan take yafara aika mata da sak'wanni masu wuyar fassarawa, jin haka yasa kukan da tund'azu take k'ok'arin danne wa ya kucce mata, k'ok'arin yanda zata tsere masa tafarayi amma ina tuni yayi mata damk'ar da bazata iyaba, kuka takeyi sosai tun kafin komai ya kankama saboda yanda tasa tsoron abun aranta, ahankali taji ya rad'a mata akunnuwa,


"Pls noorul hayat" had'e da sakar mata kiss acikin kunnen, jikinta narawa yayi nasarar rabata da kayan jikinta yana faman fitar da wani nishi kamar zaki, jin yafara karanto addu'ar saduwa yasa Billy tayi saurin rintse idanuwanta, ai bata karasa rufewaba tasaki wata irin k'ara da tasa yayi saurin had'e bakinsa da nata, 


Yau kam Mahmud yagano sirrin dake cikin auren so da kuma k'auna, don badon Billy ta nuna raggwanci da rakiba  zai iya cewa har safiya tawaye yanada zarrar da zai iyaci gaba da kashe arna, gaba d'aya ji yake wata irin sabuwar yunwantar na taso masa duk kuwa da jimawar da yayi yana d'ebe k'ishirwar da yadad'e tana taso masa akanta, Billy kuwa suma kad'aine batayiba amma tasha matuk'ar wahala, tayi nadamar soyayya ba adadi idan haka take, tuncikin dare yake rarrashinta har asuba tayi tana kuka, bata bar kukan ba har saida taji ya sauka kan gadon ruwa masu zafi ya had'o had'e da zuwa ya ciccib'eta tana faman wutsil wutsil da k'afafuwa bai direta ko inaba sai bayin, taimaka mata yayi tagasa jikinta sannan ya dawo da ita, bud'e idanuwanta da suka kumbura tayi tare da turo baki cikin 'yar dasasshiyar muryarta da bata fita saboda kukan da tayi tace


"Ni ka ajiyeni into wanka" yanaji ana kiran sallah amma ina yakasa hak'ura   har saida angulu ta komawa gidanta na tsamiya, duk da dai zafin yanzu bai kai nafarko ba haka bai hana Billy ta narke masaba tanata kuka, yayi rarrashi har ya gaji amma tak'iyin shiru, harara kuwa yashata babu adadi, wankan sa yaje yayo sannan ya fice zuwa masallaci, lokacin kuwa har angama dalla mutane sunwatse cikin masallaci sai d'aid'aiku, ai yana fita dak'yar Billy tasamu ta lallab'a tasama k'ofar key sannan tashiga toilet tagasa jikinta da sai faman rad'ad'i yake yimata sosai tayo wanka, bayan tafito ta jaye bedsheet d'in ta d'auko wani ta shimfid'a, sallah tayi had'e da karanta azkar sannan tahaye saman gado takwanta tana faman ajiyar zuciya, koda ya dawo yamurd'a k'ofar yajita da key, dariya ta bashi sosai aransa yace


"Tab lallai ashe akwai aiki gabana" sannan ya juya yakoma warsa parlour saman 3seater yayi kwancensa aransa yana fad'in tabbas kowace mace da yanayin da Allah yayi mata, kuma tanada baiwar da Allah yayi mata daba kowace mace 'yar uwarta keda itaba, Billynsa kam tamusammance, amma tafiye raki, inda kenan Basmah tad'arata, don Basmah kam nada hak'uri da juriya da duk tsawon lokacin da zai d'auka bazata tab'a nuna masa gazawar taba, da haka bacci yayi awon gaba dashi, 


Dashi har ita basu farkaba sai misalin k'arfe goma nasafe koshi muryar junior ce ta tadashi daya shigo falon rik'e da hannun little, da gudu ta k'araso wajensa cikin muryar gwarancinta tana fad'in


"Abba" murmushi yayi bayan yatashi zaune tare da d'aukarta ya aza saman cinyarsa yana fad'in


"Oyoyo my little, kintashi lafiya?" Hannunta tad'aga tana nuna junior d'ayan hannun na abaki tace


"Uncle" 


"Me uncle yayi maki?" yafad'a yana kallonsa,


"A'a Yaya ummace tace muzo mugani idan kuntashi za'a kawo maku breakfast" junior yafad'a cikin inda inda,


"Ok jeka kayiwa auntynka nocking tabud'e" yana wucewa little ta fashe da kuka tana fad'in 


"Ni janje, Abba"


Sauketa yayi da gudu tanufi k'ofar d'akin tana bubbugawa cikin sautin da ko junior dake kusa da ita ba lallaine yaji sosai ba, idan kuma ya bubbuga saita fashe da kuka, hakan yasa Mahmud yace yazo yawuce ya k'yaleta, ita kuma Billy dama tun d'azu tatashi tashiga toilet tayo wanka sannan tayi simple make up d'inta cikin wani material peach colour, tana jin surutunsu natashi sama sama amma saboda tsoro takasa bud'ewa saida taji irin rigimar da little keyi da junior sannan tataso tana takawa ahankali tabud'e k'ofar.


Little na ganinta taruga ta d'auketa tana fad'in "yayya" yanda taji su Bassam nafad'a


Rungumeta billy tayi ajikinta sosai tare da cewa


"Iyyeee little d'in Ummi ina kika tafi jiya kika barni?" Kissing d'in kumatunta billy tayi had'e da cewa "ur yayya missed you so much" 


Dariya tayi tana wasa da d'an kunnen dake lak'e da kunnen nata, parloun Billy tanufa kanta sunkuye a k'asa ta zauna kujerar dake facing d'insa har lokacin kanta na k'asa aduk'e cikin jin kunya tace


"Ina kwana yaya?" 


"Bazan amsaba don wannan gaisuwar batakai cikiba har sai kindawo nan akusa dani" duk da tanajin tsoro hakan bai hanata mik'ewaba taje kusa dashi ta zauna" hannu yasa yajawota ajikinsa tare da cewa 


"Lafiya klw my fearfear noorul hayat" 


Kallon Billy da har lokacin bata d'ago kanta ba little tayi sannan takalli abbanta tare da k'ok'arin turemasa hannu tana fad'in 


"Bayyi tafamun yayya" d'ago kai Billy tayi ta kalli little sannan ta kallesa tabushe da dariya, dariya itama little tayi had'e da bud'e hannuwa tarungume Billy tana kallonsa cikin yarinta tace


"Yayya tace" mahmud daya zama speechless jin abunda little tafad'a yana ganin haka sai shima ya rungumo Billy ajikinsa tare da had'e girarsa yace 


"Yayya tace"


"O'oh Abba yayya tace" tafad'a tana kukan shagwab'a dariya sukayi gaba d'aya ya mik'a hannu zai d'auketa ta lak'alk'ame wuyanta,


"Shikenan naji takice amma daga yau kada inkoma ji kinkirata da Yayya, sunanta mommah kinji ko, idan ko ba haka ba zata zama yayyata ba taki ba" yak'are maganar yan nunata da yatsa irin tabbatarwa da mutum abu,



Yanda take kallon sane ya tabbatar masa da cewa tafahimci meyake nufi don haka sai yace


"Fad'a naji ya sunanta?"


Aza kanta tayi asaman k'irjin Billy tana kallonsa sannan tace


"Mommah" tana murmushi


"Yawwa gud girl, Allah yayi maki albarka" cike da sha'awarsu Billy ta amsa da amin.


Bayan sun kammala karyawa yashiga ya watso ruwa da misalin k'arfe sha biyu na rana sai gasu yaya Mahmud sun shigo zasuyi masu bankwana, kallo d'aya Batool tayiwa Billy takauda kanta gefe tare da rufe baki tana 'yar dariya saboda yanda taga idanuwanta sun kumbura, gaggaisawa sukayi mom taja Billy cikin bedroom had'e da bud'e side mirror wardrobe d'inta tagwada mata kayayyakin gyaran jiki dana sirrukanmu mata ta gwada mata yanda zatayi amfani dasu, itadai Billy tsaye tayi tana sauraren mom kamar ruwa suncita, 'yar nasiha ta sake yimata sannan tafito dama mahmud nacan waje shida yaya mahmud suna d'an firar bankwana, 


Suna fitowa Billy tajawo hannun Batool suka shige k'uryar d'akinta tab'ata rai kamar zatayi kuka tace 


"Amma dai ke twiny muguwa ce dama kinsan wahalar da zanfuskanta shine harda wani kiransa kisanar dashi, wlh Allah dana san haka soyayyar take da bazanyi ba, kinga yanda jiya ya..." Da sauri Batool tad'ora yatsanta bisa bakin Billy tana girgiza matakai


"Karki sake kifara 'yar uwa, haramunne bayyana shimfid'ar mijinki duk kusancinki da mutum, kiyi k'ok'arin boye sirrin kwanciyar ki da mijinki ga kowa hakan zaisa kimarki da darajarki suk'aru awajensa, laifine kuma haramunne kad'a'an mace taje tana fad'ar yanda mijinta ya takata, yin hakan zai kad'aki cikin fushin ubangiji da tsinuwarsa don haka bani ba komai kusancinki da mutum kada ki kuskura kibayyana masa sirrin aurenki kinji 'yar uwa?, yanda kikaji haka kowace matar aure taji don haka kijure ko meye kuma kazamo mai hak'uri da juriyar iya d'aukar buk'atar mijinki hakan zaisa yak'ara sonki azuciyarsa idan kuma kika zama mai k'orafi da taushe masa hak'k'i to da sannu zaki koya masa yanda zai tsaneki azuciyarsa don haka ki kula kinji" tak'are maganar had'e da dafa kafad'arta, rungumeta Billy tayi tana hawaye tace


"Ina alfahari daku 'yan uwana bisa kulawa da soyayyar da kuke bani, ina rok'on Allah kamar yanda yaba yayya da yaya 'ya'ya kema Allah yabaki naki rayayyu masu albarka" Batool dake d'an bubbuga bayanta ahankali tace  


"Amin my twiny tare dake"


Da haka sukayi bankwana Billy rik'eda little tarik'e yaya mahmud tanata kuka, saida Mahmud yayi da gaske sannan yasamu ya rarrasheta takoma cikin gida shi kuma yarakasu har filin jirgi,


Koda ya dawo kai tsaye gidansu Umma ya sameta zaune da wasu cousin's d'insa sunata yimasa sheri wai "yau ba zama maye yayi sabuwar amarya" 


Ko kallonsu baiyi ba yanufi inda mom take zaune shima ya zauna tare da d'ora kansa bisa kafad'arta ahankali yake yimata magana


"Umma ina alhaji?, yana ciki?"


"A'a kam yafita yace zaije dubo abokinsa ne dake asibiti injin dai ko lafiya, ina ba matarce zakace bata yimaka ba" d'an sosa k'eyar kansa yayi had'e da cewa


"Umma wa mutum inji mutuwa, dama godiya zanyi maku fa nasama mun farincikina da kukayi" baki bud'e Umma take kallonsa kafin takai masa duka agefen hannu tana fad'in


"Oh ni hafsatu 'ya'yan zamani, d'age kabani waje kafin in mammakeka, marar kunyar yaro, godiyar gidanku, ja'iri" Mahmud yabar palourn yana dariya don dama yasan za'a rina.


Ganin aurensu yanzu almost 3years kenan har yanzu ko b'atan wata Batool batayi ba yasa dr Ahmad yafara kai Batool asibiti ana dubata agani koda akwai matsala haka shima yana k'ok'arin ganin likita saboda ayi investigating d'in lafiyarsa duk gwaje gwajin daya kamata ace su dukansu sunyi sunyi, amma maganar d'aya itace lafiya klw suke, Batool kam tunda taji haka takwantar da hankalinta taci gaba da addu'ar idan alkhairi ce agareta Allah yabata idan kuma babu alkhairi Allah yabata hak'uri da juriya cinye jarabawarta.


Hatta dady da mom rashin haihuwar Batool tana damunsu baranma mom da wani lokacin har hawayen tausayin 'yar tata takeyi, duk da bawani jimawa tayiba bata haihun ba.


Sai yanzune mom ke dana sani da kuma jin haushin abubuwan data tayiwa Ummi lokacin da bata haihu ba, tabbas yanzu tafahimci rad'ad'i da damuwar da mutum keshiga idan Allah ya jarabcesa da rashin haihuwa, wanda gata ita 'yarta ce ma bata haihuba amma duk tashiga damuwa balle ace ita kanta ce aka jarabta kamar yanda akayiwa Ummi, komawa tayi ga Allah tanata istigfari bisa isgilanci da tayiwa abukiyar zamanta wanda yau sai gashi anjarabceta da haka tahanyar 'yarta.


Ummi kuwa duk lokacin data kwatanta takanje wajen Batool tayita bata magana tana buga mata misalai da wud'anda Allah ya jarabta da irin matsalarta amma sukayi hak'uri kuma daga baya sai Allah yabasu, kuma tana lak'anta mata addu'o'in neman haihuwa wud'anda suka inganta daga alk'ur'ani, irinsu


_*RABBI LAA TAZARNI FARDAN WA 'ANTA KHAIRUL WARISIYN, *RABBI HABLI MINLA DUNKA ZURRIYATAN 'DAYYIBA INNAKA SAMI'UDDU'AH, *RABBHI HABLI MINASSWALIHIEYN_ Da dai sauransu, haka kuma tace ta yawaita istigfari da fad'ar _*YAA HAYYU YAA QAYYUM_ insha Allah komai zai wuce kamar ba'ayi ba, sosai kuwa Batool ta maida hankali tare da tsananta addu'o'in cike da imani da kuma yak'inin cewa Allah zai karb'ar mata,

kowa ma dai yana tausayawa Batool ganin cewa tad'an jima bata samu k'aruwa ba don haka tako ina ake tayata addu'ar Allah yabata nata zuriar.


Mahmud kuwa tuni ya bud'e sabuwar rayuwa da shafin soyayya shida Billynsa, wata irin kulawa da soyayya mai k'arfi yake yimata wacce gaba d'aya tasa ta sanar cemasa, matuk'ar suna zaune atare Billy batada wajen zama idan ba a jikinsa ba, wani lokacin haka zaauyita rigimar haye jikin mahmud ita da little yayita yimasu dariya, yauma zaune yake yana kallo ya hangosu aguje suna tsere tseren iskosa, da sauri yabud'ewa little hannuwa tana gab da kawowa ya juyar da hannuwansa zuwa inda Billy tafad'a ya rungumeta sunata yiwa little dariya, dukanta dady tafarayi tana k'ok'arin sai ya sake Billy, tashi Billy tayi had'e da cewa 


"Oya musake tunda baki yarda ba" komawa baya sukayi suka sake rugowa ya bud'e hannuwansa har Billy takusa kaiwa yayi saurin juya hannuwansa little tafad'a tanata dariya har da suyiwa mommah Billy dariya.


Fridge ya bud'e ya ciro ruwa yabawa Billy tasha saboda hakin da yaji  tanayi, bayan tasha tab'a little itama tasha sannan duk suka zube k'asa suna faman nishi ahankali, ganin wasa naneman canzawa yasa Mahmud ya d'auki little yakai wajen Umma sannan yadawo sukaci gaba da farantawa juna.


Satin mahmud biyu hutun daya d'auka yak'are don haka yafara shire shiren komawa, nan su Umma da alhaji suka sanar dashi yanda akayi akan zancen karatun Billy wanda gaba d'aya shi yama manta da tanayi balle ya tambayeta. 


Nan take ya d'aga tafiyar bayan yaroki alfarmar da akara masa sati d'aya wajen aikinsa bisa wani dalili kuma suka amince masa don basa son surasashi saboda ba k'aramin cigaba yake kawowa a kamfanin nasu ba, cikin satin yayi cukucukun had'a bizar Billy data little don yace bazai barta ba da ita zasu wuce.


Ana saura kwan biyu jirginsu ya tashi sukaje kd  gaida su dady, yanda Ummi taga 'yarta yatabbatar mata da tana samun farinciki sosai, hakan yasa tak'ara samun natsuwa azuciyarta, gaba d'aya sun canza da ita har little, da suka tashi tafiya mom tasake had'a mata kaya masu kyau sannan suka rakasu da dad'ad'an addu'o'i masu kyau amatsayinsu na iyaye, gidan yaya Mahmud sukaje sannan suka biya gidan papi, Basu wani jima ba suka nufi gidan Batool inda tsabar farinciki kasa hak'uri Billy tayi har su isa da d'an gudu gudu tahaye saman tana kiran my twiny, itama da gudun tafito suka rungume juna, duk da yanda Mahmud baiso sujima ba dole yayi hak'uri sukasha firarsu ta 'yan uwa sunaji tamkar karsu rabu, suna fita sukayi gidansu baba k'arami suma suka gaishesu bayan Mahmud yayi masu alkhairi sannan sukayi masu bankwana suka koma gida safiya na wayewa suka kama hanyar borno saboda gobe tunda safe jirginsu zai tashi,


Muhib ma yayi wayau sosai don har ansashi makaranta, yauma kamar kullum yaya Ahmad yaje d'aukosa yasamu wani abokinsa nata dukansa amma yak'yalesa sai faman kuka yakeyi, tsabar takaici Dr Ahmad kasa cewa komai yayi saida ya d'aukosa yasashi cikin mota, fad'a yayi masa sosai tare da cewa karya sake yakoma zuwa d'aukosa ya isko ana dukansa yana kuka, indai bai iya hak'uri to dolene yarama yagaji da sanyin halinsa.


Har zai wuce ya hango wani mutum cikin motar kanta yatsaya shan mai awani gidan mai kamar Alhaji tukur wato mahaifin muhib, parking yayi agefe yashiga gidan man yana regen fuskarsa  aikuwa suna had'a ido alhaji tukur ya washe baki tare da mik'a masa hannu suka gaisa yana tambayarsa ya mamynsa take, tsabar kawaici har suka gama gaisawa bai tambayesa labarin Muhib ba Saida dr.ahmadda kansa yaje yafito dashi cikin motar yakawo masashi, Allah sarki d'a da mahaifi sai Allah, Alhaji tukur na ganinsa ya  d'aukesa cike da so, sak fuskar mahaifiyarsa yagani atattare dashi wanda hakan yasa yatuno masa da ita, acan gefen gidan man suka samu waje suka zauna suna tattaunawa inda daga k'arshe dr.ahmadya karb'i address d'insa tare da lambar wayarsa bayan ya nuna masa irin rashin jindad'in da baiyi ba natafiyarsa da yayi wancan karon batare da aun had'uba, kallon Alhaji tukur Muhib yayi had'e da cewa


"Yaya waye wannan?" Rik'osa Dr Ahmad yayi had'e da cewa


"Muhib wannan shine mahaifinka ni kuma yayanka" sannan ya juya ga alhaji tukur yace "kaji abunda ake gudu ace d'anka na cikinka bai sanka ba, ai abun akwai kunya" nan dai sukaci gaba da zantawa har yake basa labarin yayi aure, kafin su d'unguma suje gida tare bayan Alhaji tukur ya bada ajiyar motarsa kafin yadawo, sosai mamy tasha mamakin ganinsa  nan aka kira Batool tare da gabatar masa dashi  amatsayin mahaifin Muhib. Nan dai yayi masu sallama tare da alk'awarin zai dinga kira kuma idan yashigo zai samu lokaci yadinga  kawo masu ziyara 

Sannan ya wuce bayan Dr. Ahmad yayi masa alkhairi


Tuni jirginsu Billy ya isa a delhi birnin India tun kwana uku da suka wuce, inda suna isa da sati d'aya batare da b'ata lokaciba ya nemawa Billy gurbin karatu a wata makaranta mai suna _priya higher institution_ haka ma little ya sama mata makaranta daidai k'arfinsa batare daya k'ure kansa ba tunda yanayin tsarin karatunsu ba d'aya yake dana k'asarmu ba, cikin wata d'aya suka fara zuwa makaranta kuma ba laifi suna ganewa sosai, matsalar kawai yaren sune da Basu wani ji, Wanda saida suka d'ansha wuya kafin sufara iyawa, musamman  Mahmud yasama masu wanda zai dinga koyar dasu harshen nasu saboda su samu sauk'in mu'amala da mutane, haka kuma duk ranakun da baya zuwa aiki sukazo kuma aka dace da suma basa zuwa school to zai d'auke sune suyita zaga gari cikin farinciki da soyayyar juna, tsabar kamar da little keyi dasu kuwa duk inda suka shiga sai sun burgeka don bazaka tab'a yarda ace maka wai ba Billy ce mahaifiyar taba.


 *_After nine (9) years_*


Abubuwa da dama sunfaru acikin rayuwar wannan family, ciki kuwa hadda komawar family na farinciki da kuma akasin haka, yaya Mahmud tuni girma yazo don yanzu yaransa biyar, mu'azzam sai Bashar wanda sukeyiwa lak'abi da abie, sai Fatima, da kuma Aisha (mami), tuni yaya Mahmud shima ya koma makaranta tyahad'o Masters d'insa under business administration, wanda saboda kwarewa da sanin harkar kasuwanci yasa arzik'in mahaifinsa yasake bunk'asa har shima sunansa yafara fitowa saboda wani katafaren kamfaninsa na kansa daya bud'e mai suna *M.BASH FURNITURES*


Ummi ma Allah yasake arzuttata da wata haihuwa bayan little Basmah tasamu Salim da Abdurrazaq sai kuma Amatullah tun tanajin kunya idan tasamu ciki har tahak'ura gaba d'aya tabarwa Allah don shine yayi mata ni'imar data kwashe tsawon shekaru tana bid'a bata samuba sai awannan lokacin don ya nuna ikonsa da kuma iyawarsa akanta.


Mom kuwa tuni tasake tsorata da kuma gano kuskurenta, gadai wacce tayita quntatawa arayuwa saboda ganin ita takeda 'ya'ya alokacin baya yanzu sai Allah mudabbirul amru, dake jujjuya al'amurransa takoma ita takeda 'ya'ya agidan yanzu, tunda ita nata duk sunriga da sun girma sunyi aure, ga Bassam ma da Bilal suma sun zama kyawawan samari dake jida kansu, kasancewar yanzu sune manya acikin gidan babu abunda dady baya yimasu sai wanda baiyi daidai da tarbiyar musulunci ba, yanzu haka suna youganda wajen had'o degree d'insu yayinda little Basmah itama tagirma don yanzu haka tana cikin shekara ta goma sha biyu kuma ashekarar nan zataje j.s.s one, gaba d'aya kamarta sak da Basmah tafad'a fitowa babu abunda ya banban tasu illa 'yar k'iba kad'an da little Basmah ta d'ara waccan Basmah d'in.

 

Jaddi ma Allah yayi masa rasuwa faraaha tayi kuka sosai har tana kallon kanta amatsayin marainiyar da tarasa gata, amma cikin qanqanin lokaci Mahmud yashafe mata wannan tunani aranta don kuwa duk wata kulawa da gata da macce kenema ita da 'ya'yanta agidan mijinta yabata kuma ita da kanta tasan Allah ya d'aukaka darajarta acikin sauran mata 'yan uwanta shiyasa akoda yaushe take alfahari da Allah ya mallaka matashi amatsayin miji kuma uban 'ya'yanta.


Tuni Billy itama tashiga sahun manyan mata dake amsa sunansu, don tun shekara hud'u da suka wuce bayan Billy tayi nasarar kammala karatunsu a fannin likitanci inda tayi specialising akan harkar kula da matsalolin mata wato "gynecology" nan suka tattaro inasu inasu suka baro India suka dawo mahaifarsu, duk tsawon wud'annan shekarun da suka kwashe haihuwarta biyu mace da namiji,saboda yanayin karatun nata dake buk'atar kulawa da kuma maida hankali,   first born d'inta mace sunanta hafsat suna kiranta da (ilham) sai kuma namijin shi kuma mahmud  suna kiransa (Abbaty), little Billy kuwa angirma sosai don idan kaganta zaka d'auka girmanta yafi k'arfin shekarun da take dasu, yarinya mai natsuwa tare hankali, gaba d'aya kamannin mahifinta da take dasu tun tana yarinya babu abunda yacanza saima sake bayyana da sukayi, gashi Allah yabata basira da hazak'a, batada hayani shiyasa bata cika son shiga mutaneba kullum tana gida tare da mommah d'inta, hakan yasa duk lokacin da sukaje k.d su amatullah dasu salim ke kama kansu har saita baro garin don sunsan hukunci da zai biyo bayansu idan suka cikata da hayaniya, ko kad'an ba'a b'oye mata rasuwar mahaifiyar taba don tun tanada shekara uku aduniya suka tarbiyantar da ita akan muhimmanci mahaifiya, wannan dalilinne yasa lokacin da tasan cewa tata mahaifiyar bata raye kullum take yimata addu'a Allah yajik'anta da rahama kuma ya gafarta mata, hatta Billy bata mantawa da ita cikin addau'arta tana rik'on Allah ya tsawaita mata rayuwarta bisa kulawa da soyayya da kuma tarbiyar da take bata. 


Tunda su Billy suka dawo tamaida hankali wajen taimakon 'yar uwarta wajen aika mata da magungunan dake taimakawa k'wayak'wayin haihuwar ta suk'ara k'arfi tare da magunan dake k'ara vitamin ajiki duk dako tasan cewa batada wata matsala kamar yanda bin cike ya nuna, amma kasancewar batada babban buri daya wuce taga itama 'yar uwarta Allah yabata haihuwa kamar yanda kowanensu keda ita, kimanin shekara hud'u kenan ana abu d'aya amma billy bata gazaba haka itama Batool bata gaki da shan magungunan ba had'e da yin addu'a har Allah itama yabata nata rabon, farinciki awajen dr Ahmad mamy da mom baya fad'uwa balle Billy dako da yaushe bakinta baya gajiya da addu'ar Allah yaba 'yar uwarta haihuwa, nan take family yad'au murna da farinciki don dama burinsu kenan suga jinin Batool aduniya, haka tab'angaren dady shima yayi farinciki tare da fatar Allah ya inganta kuma ya sauketa lafiya, cikin Batool ya zama d'an gata kuma d'an lele tako wane b'angare baranma daya fara girma akayo scanning akace 'yan biyune, wata irin tarairaya da lici take sha awurin a dr Ahmad, motsi kad'an zatayi saiya binciki lafiyarta har zuwa lokacin da cikin yakai wata tara, zama da k'yar tashi da k'yar haka Batool kefama gashi k'afafuwanta duk sun kumbura saboda nauyi da girman da cikin yayi mata sosai, yana neman fitowa ako wane lokaci, yau ana gama sallar asuba tatashi cikin wani matsanancin ciwon mara ga amai da taketa famanyi abun gwanin ban tausayi, hakan yasa dr.Ahmad yanufi part d'in daya k'ank'arawa mamynsa acikin gidan don tuni dama sunkoma sabon gidan daya gina masu naji da gani, yana shiga ya sanar da ita halin da Batool d'in keciki lokacin tana jan tarbaha, da sauri ta tashi cikin rud'ewa tace "subhanallahi wuce muje" tafad'a tana bin bayansa.


Suna isa mamy tace "assha sannu fatima ai gawar bakace takeyi da alama yau insha Allah komeye keciki zai fito" dr najin haka yace "mamy kina nufin haihuwa ce?"


"Eh mana, ai wannan aman da takeyi fawar bakice ko yaushe haihuwa na kusa" ai yanajin haka hankalinsa yatashi don tuni Billy tafad'a masa cewa kada abari tayi yunk'urin haihuwa da kanta tunda haihuwar farice kuma tajima batayiba komai zai iya faruwa,


Nan take shida mamy suka d'auketa suka kai cikin mota sukayi asibiti da ita, suna isa yasa hannu aka shiga tiyata da ita, bayan mintota da basu haura sama da talatinba sai gashi anfito mata da jariranta guda biyu namiji da mace manya manya dasu tubarkallah sai faman tsala kuka sukeyi alamun sunada cikakkiyar lafiya.


Tsayawa fad'ar irin farincikin da dr da mamy suka shiga b'ata lokacine don mamy bakinta kasa rufuwa yayi saboda murna yau gata ga jikokinta har biyu da Allah yayi mata ni'ima dasu lokaci d'aya.


Nan take dr yakira dady da yaya Mahmud yasanar dasu, cikin d'an k'ank'anen lokaci family ya d'au murna Batool tahaifi 'yan biyu, Allah kenan dama dukkanin mahak'urci mawadaci ne, kimanin shekara goma sha biyu kenan da aurensu bata tab'a b'atan wata ba, sai gashi yau hakurinta da tawakkali ga ubangijinta yajawo mata Allah yayi mata ni'ima da kyautar 'ya'ya biyu alokaci d'aya.


Kafin kace me tuni asibiti tacika da 'yan uwa da abokanan arzik'i wajen tayasu murnar wannan kyauta da Allah yayi masu.


Billy kuwa tsabar farinciki jitayi kamar ta take kan jariri, jitake inama zata iya tsuntsuwa taganta agarin k.d da yau babu abunda zai hanata kwana tare da 'yar uwarta, gaba d'aya ita da yaranta sun rud'e gidan da murnar haihuwar dama tuni suka matsu ahaihu don suje kd wajen grannys d'insu abbansu nacewa suyi hak'uri har sai anyi hutu idan mommah Batool tahaihu, shiyasa yau da ita dasu baka iya banbance wayafi farinciki da murna, jitayi Mahmud yajawo hannunta yayi wajen corridor d'in da zai sadaka da bedroom had'e da matseta ajikin bango yana kallon k'wayar idanuwanta d'aya bayan d'aya saboda mamakin yanda yaga tagame ita da yaran sai wasar baki takeyi gaba d'aya ta manta dashi ad'aki kafin yace


"Wai kina nufin duk wannan murnar da kukeyi wa haihuwar Batool ne shiyasa har kika manta dani ad'aki?" Rik'o kwalar rigarsa tayi tana kashesa da wani irin mayen kallo da yasa yaji duk jikinsa ya mace sannan itama tafara turasa izuwa d'ayan bangon tana kallonsa kamar yanda yayi mata tace


"Fad'amun are we not deserve to be happy" tana k'ok'arin aza bakinta akan lab'b'ansa, kamar wani sakarai yasaki baki yana kallonta had'e da rufe idanuwansa yabud'e sannan yatura hannunsa ta bayanta asaman kunkurunta yajawota da k'arfi yahad'e da jikinsa, yanda yaga tana k'yafk'yaf da idanuwa shiya bashi dariya had'e da cewa


"Matsoraciya! Wish ace nima nasamama twins d'in Batool k'anne acikin plat tummy d'innan naki" ya k'arasa maganar yana shafa k'asan cikinta, murmushi tayi kafin tace 


"Badai za'aji mutuwar sarki abakina ba, amma kabari idan tayi wari kaji" tana gama fad'ar haka tajuya zatabar wajen tana dariya da sauri yarik'o hannunta don idan har hasashensa yayi daidai da kalamanta kenan tanada ciki, ahankali cikin son ta gasgatasa yace


"K'anwata kina nufin akwai ajiyata atare dake?" Batare data juyoba ta kad'a masa kai, wani irin farincikine ya dira azuciyarsa saikace wannan shine karo nafarko yajawota tafad'a masa ajiki yad'ago fuskarta had'e da cewa


"Da gaske kikeyi noorul hayat?"


Kwace jikinta tayi tare da sake kad'a masa kai sannan tabar wajen tana murmushi tare dajin dad'i akan yanda akoda yaushe yake nuna mata zallar soyuwarsa da kwad'aituwarsa akan abunda zata haifa idan tasamu ciki,


Murmushin shima yayi tare da furta "Alhamdulillah Allah bisa wannan kyauta daka k'ara yimun, ya Allah kasauketa lafiya kuma kabamu ikon tarbiyantar da zuriar daka bamu, ka albarkaci rayuwarsu data dukkanin 'ya'yan musulmi baki d'ai" jitayi an amsa da "amin" ta bayansa juyowar da zaiyi yaga ashe Ilham da abbaty ne da tund'azu suke tsaye suna sauraronsa suka amsa masa suna dariya, saida shima yayi dariyar sannan yayi kamar zai biyosu ya dukesu da gudu sukabar wajen had'e da tserewa suka nufi gidan Umma,


Kitchen yanufa inda ya hango Billy tare da little suna k'ok'arin had'a dinner, yana shiga ya dafa kan little tare da cewa


"Little baba, me ake dafamun?" 'Dago kanta tayi tana kallonsa tare dayin murmushi, kafin tajuya ta wanke hannunta tare dasa kitchen towel d'in dake lak'e ajikin kusa tagoge sannan tace


"Mommah d'in little ke girki Abba bani ba, ni koyo nakeyi tare da rik'a mata 'yan wasu abubuwa" murmushi yasakar mata had'e da bubbuga kafad'arta yace


"Gud girl, Allah yayi maki albarka, haka akeson 'ya'yan K'warai" 


"Amin Abba" tafad'a sannan tajuya tare da kallon Billy tace


"Mommanah natafi wajen Umma"


"To kigaishe mani da ita sosai kafin inshigo" Billy ta amsa mata sannan tafice abunta, ai kamar jira yakeyi tafita yazo ya rungomo Billy tabayanta had'e da kurd'o kansa ta wuyanta yace 


"K'anwata baki fad'amun ko wata nawa bane ko saina biya?" Yana maganar yana kissing gefen wuyanta, motsa stew d'inta taci gaba dayi batare data d'agoba had'e da cewa


"Ka k'idanya mana kagani adadin yaranka shine watannin babynka including him" cike da farinciki ya d'agata yana jujjuyata ahankali yana fad'in 


"Iyyeee..you mean 4month kenan! Wow this baby is a miracle baby, gaba d'aya nakasa fahimtar cewa kinada juna biyu saboda lafiyarsa sai yanzu da kika fad'a, kai Alhamdulillah no wahala, no amai, no any malaises, zamuyi renon abunmu in a peace" Shiru yayi had'e da tunowa da takardar daya tsinta cikin kayansa da Basmah ta ajiye lokacin da zasu maidata gida.


_salam yaya, don Allah idan namutu kada ka auri kowace mace face Bilkisu tabbas zakayi farinciki da ita har iya k'arshen rayuwarka, ina fatar zaka cikamun wannan alk'awarin  bayan raina_


Sosai yasake rungumeta ajikinsa aransa yana cewa "kinyi gaskiya Basmah ubangiji Allah yajik'anki ya gafarta maki" ji yayi billy ta amsa da "amin" ashe har maganar zucin da yayi tafito fili.


Turo baki tayi cikin shagwab'a had'e da cewa


"To ka saukeni mana kada garin wannan farinciki naka yasa stew d'ina tak'one" ahankali ya sauketa ta motsa miyar sannan ya juyo da ita ya rik'o fuskarta yana yimata kissing d'inta tako ina har saida yagaji don kansa sannan yace


"You have been the first and will be the only one ever to touch my heart. Ever since the day i met you, my heart stopped beating for me. It beats for you alwas saying i love you with every beat, ina sonki sosai mommah little, ubangiji Allah yayi maki albarka, kuma ya saukeki lafiya" rufe idanuwanta tayi sannan ta bud'e cike da jin dad'in kalamansa da suka daki zuciyarta tace


"Nima ina sonka sosai abban little" rungume junansu sukayi alokaci d'aya kowa najin shine mafi sa'ar abokin rayuwa aduniya.


Bayan kwana uku da yiwa Batool CS aka sallameta, don taji sauk'i sosai, kasancewar tiyatar tayanzu ansamu cigaba bakamar daba, mamy na kimtsar kayansu najinya ita da faraaha saiga dr Ahmad yashigo, ba kunya yaje gefen gadon da Batool kezaune rik'e da hassan tana bashi nono, kallo d'aya tayi masa takauda kai don itakam bata son yanayi mata hakan agaban mamy, shikam dako ajikinsa ya d'auko hussainar dake kwance bisa d'an gadonsu na jarirai yace


"Kinba momynmu tasha kuwa?" Banza tayi dashi yay murmushi yana shafa fuskar babyn don kar yafahimci metake yiwa, faraahace ta d'ago kai tana kallonsa had'e da cewa


"Oh ni dr! Gaskiya rawar kannan naka yayi yawa, kai daya kamata ka tausayawa qanwata amma kai saita d'iyanka kakeyi ko kunyar mamy baka ji?" Saida yaduba gefe gefen d'akin yaga ashe mamy tafita sannan yace


"Kunyar mezanji sister nida 'ya'yanah?, kawai wanda bazai iya gani ba ya kauda kai?" Turo idanuwa faraaha tayi tana dariya had'e da cewa


"Ahhh...lallai abunka azimunne dr, koda yake da gaskiyarka, 'ya'ya rahamane"


"Yawwa sister zaki iya tuna ranar da kika had'ani da fatima awaya, ranar da nagabatar mata da kaina nace maki kici tukuici awajena zaki iya tunawa?"


Shiru tayi kafin can ta d'aga masa kai had'e da cewa 


"Yes natuna meyafaru yanzu?"


"Babu komai, dama nasa araina idan Batool tahaifamun 'ya mace zanyi maki takwara Inaa mata faraaha amatsayin goron tukuicinki to sai gashi sunzo su biyu, amma duk da kasancewarsu su biyu bazan karya wannan alk'awari danayi ba, tun ranar da aka haifesu nayi masu hud'uba da sunan FARHAAN DA FARAAHA koba komai macen sunan mom gareta da nauyi mudinga kiranta da sunan shiyasa nayi masu kinaya da wud'an nan sunayen, ina fatar Allah yayi masu albarka" speechless faraaha tazama jin tasamu takwara, kasa bayyana zallar farincikinta tayi saidai ta anshi babyn tare da zuwa kusa ga Batool dake kallonta tana dariya ta rungomota ajiki tace


"Thnk you sister da kika haifa mun takwarata, ngd sosai Allah yak'ara maki lafiya kuma yaraya mana farhaan da faraaha" 


Kallon dr tayi shima tayi masa godiya sosai da karamcin daya yimata, 


Mahmud kuwa bai bari Billy tazo ba sai ana gobe suna, tayi tunzure tunzurenta da fushi har tagaji tahak'ura tadena,


Dr Ahmad kam anyi hidima sosai kuma ya nuna bajintarsa da godiya akan ni'imar da Allah yayi masa, yayi masu kayan barka masu kyau da tsada sannan ranar suna aka yanka raguna manya manya guda biyu da sa, musamman faraaha tahad'owa twince da mamansu akwati biyu don nuna yabawarta ga takwarar da akayi mata, 


Ranar suna maijego da yaranta sunsha kyau sosai kamar basu ba, haka kuma dr yasa aka had'a walima ta musamman da marece sannan kowa ya watse ana yiwa babys addu'a tare da fatar alkhairi, Billy na hango tsaye da aunty fareeda tana bata hak'urin rashin gayyatarta aureta da batayi ba ita kuma tana cewa


"Ai wlh abun yayimun zafi, ace bikinki ko gayyata babu, ainazata saboda bakya son in more shiyasa"


Dariya Billy tayi kafin tace "haba tuba nakeyi, yanzu haka kinga nakusa juye maku na ukku insha Allah zan kiraki, kodon ki kula mani da naman suna kada su aunty meamah da zainab pinki dasu Nana hauwa'u su wawushe" tsalle aunty fareeda tayi tare da gyara jikkarta dake d'an k'are da naman sunan twince sannan tace


"Kai Allah dai yabarki da pilot d'inki, ai wlh shiyasa nake mugun sonki, Allahu Akbar Allah yajik'an 'yar uwarki yayya Basmah" muryar little Basmah dake sak data yayya Basmah aunty fareeda tajuyo abayanta tana fad'in 


"Laa banfa mutu ba aunty fareeda kidena yimun fatar mutuwa mana" arazane aunty fareeda tajuyo had'e da cewa


"Nashiga uku ni fareeda daga addu'a?"


Both Ummie da kubra dake tsaye gefe suna jiranta da Billy suka kwashe da dariya, dafa kafad'ar aunty fareeda Billy tayi da sauri tajuyo idanuwanta awaje Billy tace 


"Kai aunty fareeda kwantar da hankalinki, little Basmah ce, kinsa gaba d'aya babu ta inda tabaro yayya, wannan kuma 'yatace little Billy" tak'are maganar tare da jawo hannun Billy dake tsaye tana kallonta fuskarta d'auke da murmushi,


"Eh nagani itama sak babu ta inda tabaroki, to nikam sai da safe Allah yaraya maku yaranku kuma yashirya maku su" aunty fareeda tafad'a tare da wucewa tanayi tana wawayen Basmah da take ganin kamar yayya Basmah ce data dawo.


Da safe Billy na zaune rungume da farhaan ita kuma Batool rungume da faraaha ta k'walawa Basmah kira, fitowa tayi aguje Ummi nashigowa tazo duba ya 'yan biyu suka tashi da kad'an ta bugeta, 


Kallonta Ummi tayi had'e da cewa


"Oh ni Basmah Allah ya shirya mani ke, baza dai kidena wannan gujegujenba ko? Bari Bilal yazo shine maganinki zansa yakoya maki hankali"


"Kai Ummi aunty Billy cefa takirani shine nayo sauri kisan maau ciki da saurin hasala"


"Mtss Dallah rufamun baki jeki"


Kusan tare suka isa wajen Billy nadaria tace


"Wlh little Basmah bakida dama, ke kuma ahaka halinki yazo, mudai yayyammu ba haka takeba Allah yajik'an rai"


"Amin ummi tafad'a tare da amsar farhaan ahannun Billy tana fad'in "morning my fresh sweetheart" duk suka kwashe da dariya, ita kuma Basmah data b'ata rai don ance bahaka yayya take ba cikin k'unk'uni tace


"Amma dai ai komai bamu d'ayane harma da muryarmu"


"Eh naji, don Allah jeki ki toyamun wainar fulawa" Billy tafad'a tana dariya


Haka little Basmah tashige kitchen tana k'unk'uni gashi dai bata wani iya wainar fulawa ba saboda ummi bata sonta shiyasa bata tab'a gada yintaba balle takoya, ganin yanzu aka gama yimata sheri yasa takasa fad'ar bata iyaba don haka tayi tsaye tana tunanin ta ina zata fara, tunowa tayi da taga sauran wainar da akayi jiya tabuki data rage mom tasa a fridge don tanaso yau taci,


Da sauri ta kunan gas nad'ora faranfam awuta ta zuba mai aciki sannan ta bud'e fridge d'in taciro k'waya uku har tana fad'in wannan "wainar zata isheta tunda manya ce, bari na raba biyu" nan ta d'auko fulawa ta tankad'a sanan ta d'ebo ruwa ta ajiye agefenta, tana fad'in "banda abun aunty Billy wai wainar fulawa taya za'ayi ta toyu ba'a saka wainar aruwaba kafin asamu fulawar tazauna ajikin wainar" tsunbula duk yankan wainar data d'oko ta dingayi sannan tasaka cikin fulawar ta birkideta saita jefa cikin ruwan mai, haka ta dingayi har saida tak'arar da yankan wainar, little Billy ce tashigo kitchen d'in had'e da cewa 


"Momcy" don haka take kiranta, mekike soya mana haka!" tare da d'okar yankan wainar da ya soyu da fulawar tana jujjuyawa


"Bari kawai doty aunty Billy ce tace in toya mata wainar fulawa da sanyin safiyarnan, don ma Allah yataimaka mom ta ajiye sauran tajiya a fridge ai data wahalar dani" zaro idanuwa little Billy tayi had'e da cewa "what momcy? Wainar fulawa ahaka?" Kafin takwashe da dariya tanufi inda suke tana cigaba da dariya had'e da rike ciki tana fadin "mommah..mommah" takasa iyarwa saboda dariyar dataci k'arfinta, 


Little Basmah kuwa ko ajikinta ta d'auko plate d'in tanufo falo dashi, mik'awa Billy tana fad'in 


"Gashi Aunty Billy" ta nad'awa little Billy da har yanzu takasa dena dariya duka abaya "kekam kinshiga uku da muguwar dariya.


Ai kafin tarufe baki taji Billy data tsurawa plate d'in ido sannan takalli Batool itama ta kalleta suma sun fashe da dariya.


Saida sukayi mai isarsu sannan sukace atare " yayya Basmah delious returned" saboda tunowa da ferfesun kaifin da yayya Basmah tayi tare da kunun gid'a.


Cikin dariya Batool tace "kai gaskiya Basmah kin biyani yanzu twiny zata fahimci cewa dake da yayya Basmah abu d'ayane babu banbanci"


Ummi kuwa kunya ce tarufeta, tafahimci cewa tayi kuskure, bai kamata ace don uwa batacin abuba tace bazata koyawa 'yarta shiba saboda batasan wataran inda rana zata fad'iba.


Kallon Billy little Basmah tayi data kasa tayarda dariyarta kafin tace


"Kufa 'YAN UWANA NE..amma kuka azamun wannan dariyar, shikenan dama ai nasan bakwa sona yaya mahmud da yaya Bassam kad'ai ke sona idan suka dawo zanfad'a masu" tamik'e zatabar palourn da sauri Billy tarik'ota had'e da jawota ta zaunar da ita tsakiyarta da Batool suka rungumeta atare sannan sukace


"Sorry Basmah muma muna sonki sosai fiye da tunaninki"


_ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ANAN NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA *'YAN UWANA NE*,  INA GODIYA GA ALLAH DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA, INA FATAR DANI DAKU ALLAH YA YAFE MANA KURAKURAN DA MUKA AIKATA KUMA YASA MUYI CU'DANYA ACIKIN LADAR DA MUKA SAMU ACIKI YABAMU IKON AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKI, INA GAISUWA TARE DA FATAN ALKHAIRIN ALLAH GA DUKKANIN MASOYANA BISA HAK'URI, JURIYA DA KUMA JAJIRCEWARSU HAR ZUWA WANNAN LOKACI DA MUKA KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA, NAGODE DA ADDU'O'INKU DA KUKEYI AGARENI DA KUMA MAHAIFINA, YA ALLAH KAJIK'AN ABBIENA DA KULLUHIM MUSULMI BAKI 'DAYA, ALLAH YA HASKAKA ROUHINKA YA YALWATA KABARINKA,😭 MASOYANA KU *'YAN UWANA NE* A MUSULUNCE  KUMA INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE DOMIN DUK WATA NASARAR DANA SAMU ARAYUWA TA DALILIN KUNE, KUMA INA ROK'ON WANDA DUK NA 'BATA MASA RAI YAYIN RUBUTA WANNAN LITTAFI DAYA YAFEMUN SABODA HALIN RAYUWA, NAGODE SOSAI 'YAN UWA SAI KUNJINI  A SABON LITTAFINAN  A SHEKARAR 2020 MAI SUNA........😜😇IN SHA ALLAH 🤝 *MISSED U AND LUV YO ALL FILLAH*❤💞💋_


_Comment d'inku shizai tabbatar mun da kun nishad'antu, kun ilmantu, kuma kun amfana da darussan dake cikin wannan littafi, hakan kuma zai bani k'warin guiwar cigaba da rubuta maku sabon littafina mai suna........😉_ asha


 *karatu laafiyaaa*




Post a Comment

0 Comments