TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Hauwah kulu book 1

       ‘YAR CIKIN BADALA

    (HAUWA-KULU)


              (Paid Book)

SUMAYYAH ABDULKADIR

                       07030137870

    (whtsp only)

     

                      babbangoro2015@yahoo.com

      takorikabara@gmail.com







WANNAN KARON SADAUKARWAR KACOKAM TA KANAWA CE, A DUK INDA KUKE, LITTAFIN YAR CIKIN BADALA SADAUKARWA NE GA DUKKAN MAKARANTA NA ‘YAN ASALIN KANON DABO

    





                      SHIMFIDA


NIGERIAN BAR ASSOCIATION

         (CONFERENCE HALL)

 

W

ani irin cika dakin taron yayi, da manya da kananan lauyoyi wasu sun zo ne tareda iyalansu, wasu sun halarta babu iyali, a can gefe kuma a muhallin baki na musamman wakilan kungiyoyi ne masu zaman kansu (International NGOs) masu kare hakkin masu nakasa da tabbatar da ‘Equal Rights, Inclusion and Opportunities ga mutane masu bukata ta musamman.


    Duk da cewa dakin taron bai cika girma ba, amma ya hadiye mutane da yawa da suka halarta. Wasu da yawa ba don taya ta murnar mukamin da aka bata yau suka zo ba, sun zo ne musamman don son ganinta ido da ido (don debe haso da kore shakku), na son tabbatar da jita-jitar da suke yawan ji akan cikar lafiyarta, a matsayin ta na ‘celebrity’ din Najeriya ga duniyar masu nakasa, wadda sunanta ya watsu, ya fantsama a kafafen yada labarai da soshiyal midiya. Haka muryarta ta dade da zamowa familiar (sananniya) ga kowa akan kwato hakkin nakasassu da kare martabar su (physically-challenged people) a arewacin Najeriya.

    Wasu kuwa sun zo taron ne kawai ta hanyar ganin sakon gayyata a kafafen sadarwa wato sun zo ne don farin jininta shiyasa kawai suke son ganinta. Kwarai ita din mai farin jini ce ga kowa.

    Kungiyoyin kare hakkin masu bukata ta musamman, su suka hada mata wannan taron na gani da ido (meet and greet), domin taya ta murnar karbar shugabancin kungiyar gamayyar lauyoyin kasa da aka fi sani da suna Nigerian Bar Association.      

    Wadannan kungiyoyin sun tsaya mata ne a dalilin tsayuwar ta tsayin daka wajen kare hakkin nakasassun arewa, da tsayawa cigabansu da ilminsu dana 'ya'yansu, karkashin hadin guiwarta da Sustainable Development Goals da kuma aikin da ta zaba na zama lauyar marassa 'yanci da physically-challenged persons. 


    Bayan kasancewarta SDG ADVOCATE har ila yau, lauya ce ita mai zaman kanta, wadda aikinta yafi karkata ga tsayawa less-privileged da wadanda basu da halin daukar lauya ko akaci zarafinsu adalilin nakasa ko aka take hakkinsu na 'yan kasa a dalilin nakasa, itace kan gaba wajen kare hakkin nakasassu a duk fadin arewa. 


    Lokacin data durkako dakin taron, wato (ta doso) cikin shiga ta kamala da kwarjini, hannunta yana makale cikin nasa, suna taku a hankali zuwa inda aka tanadar musu don tsayuwa tare. Sai aka mike don nuna girmamawa a gareta, da yawa yau da suka samu ganinta a zahiri sun ce a zukatansu "hakika *HAUWA* ganin ki ya fi jin ki!"

    Duk da cewa wannan karon ma da bakin gilashin nata a idanunta. Hakan bai boye zahirin cikar zatinta da cikar kamalarta da iya adonta ba.

    Bayan an zauna an nutsu, ta karbi lasifika ta fara da rero godiya ga duk mahalarta taron, da sauran zaqaquran lauyoyi 'yan uwanta, da kungiyoyin da suka hada mata wannan muhimmin taron gani da ido da gaisawa, kungiyoyin ne masu tabbatar da cewa, mutane masu bukata ta musamman sun samu rabauta daga duk wani matsatsi na rayuwa karkashin  tallafin Sustainable Development Goals  da take yi wa aiki partially, ta sake godewa kungiyoyin nan da suka roki ta fito yau, duniya ta ganta, a wannan ranar mai muhimmanci a gareta, kasancewar muryarta kadai aka sani a kafafan sadarwa, sun roki ta baiwa al'umma labarin ta, maiyuwuwa ya  zamo inspiration ga al'ummar da suka samu kansu cikin kwatankwacin irin situation dinta. 

    Kungiyoyin sun hada da manyan kungiyoyin kare yancin masu nakasa da tabbatar da cigabansu wato kungiyar 'AGILE', da kungiyar 'Sight-Savers', sannan kungiyar 'Action Against Hunger' da 'PERL (Partnership to engage, Reform and Learn) '.

    Ta kuma godewa manema labarai daga gidan rediyon BBC, karkashin jagorancin wakilin yada labarai na BBC a Kano, da gidan rediyon VOA karkashin jagorancin wakilinsu HAMZA MUSTAPHA MAWONMASE.

    

    Sama da kowa, above all, and above all, tace tana godewa Uban ‘ya'yanta, wanda ta kira da suna My PACE-SETTER....". 


    Zazzakar muryarta ta cigaba da karade dakin taron ta cikin bututun lasifika, wadda murya ce da dama take familiar (sananna) ga kowa tun kafin bayyanar fuskarta a zahiri a ranar yau, a daidai sanda take cewa;


    Kamar yadda kowa ya sani sunana na yanka Hauwa-Kulu. Hauwa shine sunan da aka yankamin rago dashi. Sau-tari idan na bushi iska musamman a lokutan nishadi na da son baiwa kaina farin ciki na kan bugi kirji in gayawa kaina da kaina,

     babu wanda ya kaini samun yin kuruciya mai dadi! 

    Na kan yi tunanin ai nafi duk tsararrakina jin dadin dabdalar kuruciya, dalilina na fadar haka shine nayi kuruciyata ne a zamanin da hankulan kasarmu da jihohin arewa bakidaya suke a kwance, sannan kuma dukkan iyayena Uwa da Uba suke a raye tare, ina jingine jikin su musamman Innata, ina rabar ni'imar dake tattare da kulawar Uwa da ta Uba a tare, cikin rayuwar rufin asiri irin ta kowanne talakkan Bakano. 

  Nayi yarintata a sa'ilin da muke cikin shekarar nan mai tarin abubuwan bada labari a kasarmu ta Najeriya, zamanin da sojoji suka kwace mulki daga hannun sibiliyan koko in ce musu (farar hula) cikin shekarun (late 80s), wanda lokacin da wayona mulkin Najeriya ya koma hannun mulkin soja, bayan mulkin (Alhaji Shehu Shagari)”.


    Hauwa ta cigaba da cewa a lokacin ana gudanar da wata irin rayuwa ne mai matukar sauki da hadin kai a tsakanin alummar jihar Kano, har ma da daukacin kasar Najeriya gabadaya irin wanda yayi karanci ko kuma ace babu shi sam! A halin da muke ciki a yanzu.

    Ni Hauwa-Kulu nayi 'yammatancina a zamanin mulkin Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

    A wancan lokacin da muke zance, kwanciyar hankali shine babban arzikin da al'umma suka mallaka, suka Kuma wadatu da shi ba tarin dukiya ta yaki-halak yaki-haram ba.

    Koko ince a lokacin Ubangiji yayi mana ludufin arzikin kwanciyar hankali da wadatar zuciya sama dana komai, wanda yafi tarin dukiyar yanzu alfanu ga dan adam alhalin babu kwanciyar hankali, godiyar Ubangiji ya wadaci zukatan al'ummar BADALAR Kano da kewayenta, saboda kowanne talakkan birni a zamanin, in kayi duba na tsanaki zaka ga cewa ya iyawa talaucin sa, dai-dai gwargwado kuma daidai misali jama'a basa cikin halin wahala da kaka-ni-kayi; tunda kowa yafi karfin hatsi, wato duk tsananin talauci ba zai sa a kwana da yunwa ba, saboda ba'a damu da cewa lallai sai an ci mai dadi ba, ko sai an sha koko da sukari, ko sai an ci abinci mai maiko da nama, ko sai an sha shayi da madara, gidan talakka da gidan mai kudi kusan duk irin rayuwa daya ake yi babu banbanci, abinci iri daya ake ci, babu yi wa juna rowa, haka suttura kusan iri daya ake daurawa tsakanin matayen cikin badala duka, daga na masu kudi har na talakkawa.


    Sanin kowa ne a lokacin babu ta'addancin 'yan kasa da zaluncin shuwagabanni sosai, shiyasa ake cikin kwanciyar hankali da koshin ciki, wato babu masifar talauci da yunwar da har zata tunzura matasa sana'ar nan ta satar mutane da yin garkuwa dasu, sannan babu hadama da gasar rayuwa tsakanin mazauna badalolin Kano, kamar gasar motocin hawa, dana dogayen gine-gine, ko gasar sanya suttura mai tsada a tsakanin matan badala. Wannan a takaice shine misalin irin zamanin da ni Hauwa na taso a cikin sa, wato zamanin da duniya take a kwance lumui.

    Babban kwanciyar hankalin da ake ciki a lokacin shine; al'ummar 70s da 80s basa cin bashin bankuna don su rayu, irin yadda ake ci a zamanin yanzu kamar yadda ake cin dussa, wai don biyan bukatun yau da kullum wadanda ba masu karewa bane.

     Ga daukar zunubin kudin ruwa.

    Shiyasa zaka ga duk tsananin talauci a lokacin iyayenmu basa cikin fargaba da zullumi, irin wanda tunanin bashi ke haddasawa magidantan yanzu, mai haifar da cututtukan kwakwalwa irin na damuwa da akeyi a zamanin yanzu wanda yake yiwa magidanta illa. 


    Hakan ya faru ne sakamakon cewa kowa yana da abin yi daga (sana'ar data karbe shi), ta kuma ishe shi rufawa kansa asiri, da biyan bukatun sa na yau da kullum batare da ya ci bashi ba. Kuma ba tareda yayi rayuwar dage ba.

    Kusan kowanne mutum a cikin Badalar birnin Kano da kewaye (kauyuka da kananan hukumomi) yana rayuwa ne daidai shi kuma cikin farin ciki, yalwa da wadatar zucci, domin kullum cikin sa a koshe yake da *Gurasa* Tuwo, Dumame, Kunu, da Koko da Kosai (manyan abincin Kanawa).

    A takaice, ko da a ce kai ne beran masallaci sabida talauci a zamanin can da nake yarintata a gaban Innata da Babana, zuwa balagata (‘yammatancina) nayi rantsuwa bazaka rasa abincin da zaka ci sau uku a rana ba. 

    A kullum ranar Allah tunanin Babana wanda anan unguwarmu ake kira "Baban Hauwa, dama na kowanne magidanci kamarsa na jama'ar dake zaune cikin kwaryar gidajen Badala da ganuwoyin garin Kano, shine; na yadda gobe idan garin Allah ya waye, karfe nawa zai yi sammako ya fita kasuwa ko wajen sana’ar sa??

    Ba kuma don komai ba sai don samowa cikinsa dana iyalinsa abincin da zasu ci a yinin ranar. 

    Kowa ya san a lokacin fiye da rabin Kanawa yan kasuwar saye da sayarwa ne. Wannan ne yasa ba'a kwana ana jin yunwa, sannan za'a wuni a koshe. Kuma ba'a tara komai a banki ba, sannan hakan baisa sai an ci bashin kowa ba. Duk da hakan kuma ana zaune lafiya cikin farin ciki. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ake yi a gidanmu.

    Ina farawa da baku labarina ni HAUWA_KULU tun daga tushena, ta hanyar dora shi akan katangar zamantakewar gidajenmu na Kanawa, wadanda aka fi sani da 'yan kwaryar BADALA, yanayin rayuwar iyayenmu na cikin Badala wata irin rayuwa ce irin mai ban sha'awa ga wanda ba Bakano ba.

    Rayuwa ce wadda bako zai tafi gaba ya bada labara, tunda an ce wai Allah daya gari bambam. 

****               ****                    ****

    

  GIDAN MALAM BILYAMINU 

T

sakar gidanmu mai fadi da yalwa ne sosai, irin ginin nan ne tun na 70s wato ginin Kanawan zamanin da, Gidan namu yana nan a bayan tsohuwar Badalar nan mai tsohon tarihi daga cikin Badalolin Kano, wato bayan Badalar Kofar Naisa, a lokacin nan ni Hauwa-Kulu, zan kimanta shekaru na da cewa ina yar shekaru goma.

    Yalwataccen gidan namu duk da cewa a can cikin surkukin lungu yake, wanda ainahi mahaifina Malam Bilyaminu ya gaje shi ne shida dan uwan sa Malam Zakari, daga baya rigima ta hada shi da Zakari a kan gidan, wadda har ta kaisu gun mai unguwar kofar Naisa, aka ce zaaje kotu, inda mai unguwa ya hana, ta hanyar kawo shawarar bai kamata su je kotu alhalin sun fito gida daya ba akan abin duniya kararre, duk da ya san cewa Zakari ne mara gaskiya, don so yake ya gaje gidan shikadai, mai unguwa ya kawo shawarar daya ya sayarwa daya gidan, don a samu maslaha a tsakanin su. Don ya gaji da rabon fada tsakanin Bilyaminu da Zakari akan gidan gadon sunnan. 

    Don haka Zakari ya sayar masa da gidan, don a lokacin babu ta yi masa yawa yana neman abinda zai ja jari ne, kudin yafi bukata ba wai gidan ba shiyasa yakeso a sayar. Don haka gidan ya zama mallakin Malam Bilyaminu shi kadai bisa shaidar mai unguwa da makwabtansa, bayan ya biya shi kudaden da ya yanka masa da kansa, ko kusa bai zaci Bilyaminu zai iya biyansa wadannan kudin ba, don haka yana karba ya bar masa unguwar, ya koma kofar Dan agundi da zama, inda ya sayi karamin gida a can da rabin kudin, ya cigaba da sanaar sa ta wankin hula. Malam Bilyaminu kuwa saboda kaunarsa da gidan sai ya kara gyare shi daidai bukatar kowanne talakkan badala.

  Gidanmu, gida ne na kasa da turbaya (gidan da aka gina da Laka), wanda aka bi aka sumunce shi tsaf da suminti, aka kuma shafe shi tas da farar kasa yayi haske gwanin shaawa. Tsafta da iskar shaqa sun wadace shi, kamar yadda tsaftar zuciya ta wadaci jamaar wannan gidan bakidayan su, wato Mallam Bilyaminu da matarsa Inna Safiya. 

    A kowanne wayewar gari ko yammaci, zaka samu iska mai dadi da shiga jiki na kadawa a tsakar gidanmu, musaman a lokacin hunturu, wannan ya samo asali daga manyan bishiyoyin da ke girke a tsakar gidan tun ginashi, na darbejiya dana itacen umbrella, zaka ga reshen bishiyoyin dake tsakiyar gidanmu na rangaji, idan iska na kada su, busassun ganyaryaki na zuba a kas. 

    Amma bazaka gansu sun bata tsakar gidan sosai ba, saidaima ka ga zanen tsintsiya da ya bi nan take ya share su, wanda ke nuna matar gidan, wato Inna (Safiya) wadda kowa ke kiranta da (Innar Hauwa), bata da kyuyar yin shara, abin nufi Innata jaruma ce wurin yawan kauda datti, koina ka shiga a gidanta zaka gan shi tsaf-tsaf gwanin ban kaye da dadin zama, kamar ba gidan dake cikin surkukin lungunan bayan Badala ba.

     La-shakka ko lomar tuwon ka ce ta fadi kasa a gidanmu, za ka sunkuya ka dau kayar ka, ka jefa a baka ka ci, ba tare da kyankyamin komai ba, duk da rashin sukunin aljihu na jamaar gidanmu wato iyayena tofa suna da wannan dabiar ta cikar Imani wato nazafah. Irin tsaftar da har ake cewa masu ita, ko suna da aljanun tsafta, ba Innar kadai ba, ba Malam din kadai ba har ni dake tasowa sun min wannan horon, kowannenmu ya rike tsafta irin ta malam bahaushe kai har ta zama symbol din gidanmu, bazaka ce ana kiwon dabbobi iri-iri a gidan ba, sabida yadda Innar Hauwa bata gajiya da share shi duk safiya da marece. 

    Innata na kiwon dabbobin gida, tun daga raguna har awaki da tumaki, a can wani bangare na gidanmu da aka zagaye da langa-langa. Da zarar awakin sun fito daga garke sun sakar mata shi a tsakar gida ko a can garken nasu zaka ga tabi ta share.

    Sau tari zaka samu yayan bishiyar nan ta Umbrella yellow sharr dasu sun zubo a tsakar gidan mu, don haka yaran unguwa da yawansu da sassafe kafin su tafi makarantar boko suna yawan shigowa rokon Inna Innar Hauwa Umbrella ta fado? 

    Nan zaka ga Innar Hauwa ta debo wankakkun yayan umbrella ta babbasu, su yi godiya su tafi suna ci da murna da farin ciki fal a fuskokin su.

     Yayan bishiyar (umbrella fruit) sunada farin jini a wurin yaran cikin Badala sabida zakin dandanon su.

    Yadda bishiyoyin suka yiwa gidanmu rumfa da manyan ganyaryakinsu zai matukar baka shaawa, domin ya koma tamkar wani dan karamin lambu, bishiyoyin sun samarwa mamallakan gidan wadattacciyar inuwar hutawa musamman a lokuta na zafi, ko cikin watan azumin ramadana da kuma lokacin da rana ta take sosai, to kuwa tsakar gidanmu zai zame maka muhallin hutawa sabida inuwa da duhuwar bishiyoyin.

    Gidanmu ya kunshi dakunan kwana guda uku kacal, daya a gefe na Babane, biyu na kallon sa, wanda daya ya zama na Inna ne, dayan kuma dakina ne nikadai a kusa da shi. Sai madafinmu mai rufin kwano da akayi da langa-langa, sai bayan gida daga gefe na gargajiya.

     Duk shaanonin cikin gida na Innar Hauwa a karkashin bishiyun nan take yin su, kamar su daka, gyaran kayan miya, surfe, wankin kayanmu, kai har da yin kuli-kuli da man gyada, don sau tari Inna da kanta take yi wa kanta mankuli, don wani lokacin na sayarwa sai ta ce an yi kazanta mai yawa a cikin sa, haka ta kan yi duk wasu abubuwan da hannunta kan iya sarrafawa da kanta ne don amfanin ta na gida. Hatta markaden kayan miya ita take nika abunta da dutsen nika. Inna bata da ganda (kiwa) ko kadan, akwai kuzari da koshin lafiya irin na matan da, da kashinsu yayi kwari daga shan surfe da dakau da tukin tuwo, sakamakon hakan kasusuwansu suka yi karfi sosai, gashi bata wasa da shan magungunan gargajiya masu kara koshin lafiya da cire kananan cututtuka irin su shawara (jante) dasu basir. 

    Girman tsakar gidan zai isa a gina wani dakin guda, ba tare da daya ya gogi sauran dakunan ba, amma mahaifina wato Malam Bilyaminu ya barwa iyalin sa filin su yi amfani da shi don hidimar gida ta yau da kullum da hutawar su, don ya fahimci yadda rayuwar mu tafi bada karfi a zaman tsakar gidan. 

    Kowa ya san yadda babu wanda ya kai mutanen dake cikin gari da badalolin nan na jihar Kano jin dadin alfarmar dake tattare cikin zaman kwaryar birnin Kano, da kuma jin dadin rayuwar birni gabadayanta. Mutanen cikin Badala, na da rayuwa ta tsaro ga junan su, da hadin kai, da taimakekeniya a tsakani, don suna kaunar juna ne kamar jini guda suka fito, ga kula da hakkin makwabtaka.

     A irin wadannan unguwannin na cikin Kano, a tsakanin 1970s, 1980s da 1990s zaki samu akwai saukin rayuwa na ban mamaki, misali arhar kayan masarufi dana abinci, makwabci baya iya cin abinci shi kadai a gidan sa ba tare da ya zuba an kaiwa makwabcin sa ba, ko ya fito da shi majalisa ayi ciyayya don inganta hakkin makwabtaka da zaman tare, da karfafa taimakon juna da zumuncin Allah. 

    To a unguwarmu ma, wato Kofar Naisa, irin rayuwar da su Babanmu ke yi kenan kullum, shi da makwabcinsa Malam Isa, kullum bayan sallahr ishaI kowa zai fito da abincin gidan sa su shimfida katuwar tabarmar kaba a kofar gidan Malam Bilyaminu, su sallaci magriba da isha tare, sannan su zauna zaman cin abincin a kwano guda, da hannayen su dana kawo musu ruwa suka wanke. 

    Akwai wadatar shaguna na kayan masarufi da abubuwan bukatar yau da kullum a kowanne lungu da kowanne kwana na unguwannin Badala, babu abinda baa sayarwa.

    Iyaye na dorawa yaran su talla ba tare da fargabar wani abu ba, akwai abincin sayarwa iri-iri kuma mai arha mai tsabta da a ke yi a gidaje, ga rijiyoyin burtsatse a koina da rijiyoyin amfani a cikin gidaje, don haka babu batun wahalar ruwa a lokacin, kai duk iya talaucin ka zaka rayu ne cikin jin dadi ba tare da ka sayi ruwan amfani ba a unguwannin cikin Badala.

    A hakikanin gaskiya sai kana zaune a irin gidajen nan namu dake cikin Kofofi da Badalolin Kano, shine kadai kake samun duka wadannan alfarmomin masu tarin yawa, kuma shine zai sa a kira ka da cikakken Ba-Kano, ko ka kira kanka da Bakano, ba dan wajen gari ba ko bakon haure a Kano.

           ****      ****      ****

    

         KANAWAN DABO

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                             

A

lummar Kano su akewa kirari da laqabi da KANAWAN DABO. Ni Hauwa-Kulu ina alfahari da kasancewata (yar asalin cikin BADALAr Kano), don haka ne na dauko muku labari na tun daga tushe, wato na fara da baku shimfidar labarina daga inda na taso, kuma inda aka haifeni, wato cikin kwaryar BADALA. 

    Garin Kano gari ne da ake ma kirari da Ta-Dabo Tumbin Giwa (Yaro ko da me ka zo an fi ka). 

    Mun samo wannan lakabin ne daga masarautar Kano (Dabon Kano) ta Sarki Abdullahi Bayero, Kano garin Sarki Ado, Kano mai Mata mai Mota, mai Ganuwoyi da Badaloli da wasu irin kofofi wuri-wuri lungu-lungu na tarihi, suna nan birjik bila adadin zagaye damu. 

    A takaice tarihin birnin Kano tarihi ne mai dogon zango kuma mai zaman kansa, wanda in aka ce zaa bada shi saidai a dauko shi tun daga tushe, wato tun daga lokacin zuwan Habe, har zuwa shigowar Turawan mulkin mallaka, da rayuwar Mai-Tatsine a Kano, data sarakunan Kano da suka gabata.

     Don haka ba zai takaitu a shafi guda na gabatarwar/shimfidar littafi ba, sai dai I can boldly say; Kano ta zarta kowacce jiha a arewa kyakkyawan tarihi na sarauta, da ilmin addini dana boko da rike kasuwanci da muhimmanci.

    Abinda kowa ya sani ne Ba-kanon mutum bai yarda da zaman banza ko zaman kashe wando ba. Haka kuma bai yarda da zama cikin jahilci ba komai yawan shekarunsa; wato dai Gemu baya hana Ba-Kano neman ilmi.

    Saboda zaka ga daga yara har manya a Kano kowa dalibi ne, matan aure ma a wancan zamanin duka da suna dakin miji dalibai ne a gidan auren su, da zarar an yi sallahr isha, zaka ga suna firfitowa daga gidajen su cikin lullubi da shigar mutunci don tafiya makarantar dare ta matan aure, haka da safe akwai masu halartar makarantun manya (adult education schools) irin su Gidan Galadima, ko makarantar Gidan Makama, don haka akasari a Kano maza da mata bakidaya kusan kowa yana da abin yinsa daga neman ilmi zuwa sanaar da ta karbe shi, ko kuma wadda ya gada daga iyayensa. 

    Zauna gari banza ga Bakanon mutum mace ko namiji sai mu ce sai dai abinda bazaa rasa ba, don hatta maaikatan gwamnati baka raba su da kodago a kasuwar kantin Kwari, ko Bata (Sabon gari), ko kofar Wambai, kasuwar Singa, ko kasuwar Kurmi, manyan kasuwannin birnin Kano kenan. 

    Mafi yawan jamaar Kanon kuma da kasuwancin kacokam suka dogara, basu damu da aikin gwamnati ba, koda sun dan yi karatun zamani kuwa, balle wadanda basu samu yin mai zurfi ba, kamar mahaifina, wanda akafi sani da suna “Malam Bilyaminu dan Kofar Naisa”.

    Sanaar Babana Malam Bilyaminu itace sayar da kayan yara na gwanjo a kasuwar kofar Wambai. Da wannan sanaa muke rayuwa kuma da ita ya dogara, sannan kuma ta rufa masa asiri ya rike iyalin sa daidai gwargwado da kulawa irin ta Bakanon mutum, mai zucciyar kula da iyali, wato Mallam mutum ne har mutum wanda ya san ciwon iyalinsa. 

    Malam Bilyamin ya taba yin sakandire ya kuma yi aikin masinja a wata maaikata daga baya ya bari ya kama kasuwar gwanjo sadidan.

     Duk wanda ya san Malam Bilyaminu, (kafin a neme shi a rasa rana daya), ya san cewa mutum ne da ya dogara da sanaar sa ta gwanjo, ya kuma bata muhimmanci sosai, sannan kuma shi din mai kula da iyali ne fiyeda kima da duk abinda Allah ya hore masa a lokacin da yake tare damu, bai yarda ya tara komai ba, in dai iyalin sa bazasu nemi komai su rasa ba. 

    Kafin ni Hauwa, Innarmu Safiya da Babanmu Malam Bilyaminu sun haifi Yayana Zulkifilu, wanda ya jima da rasuwa tun yana saurayi dan shekaru sha biyar da haihuwa, ya rasu ne a sanadin wankan cikin rafi (wankan kogi) na samari irinsa marassa ji da fitina, sai ni kanwar sa Hauwau, Hauwa – Kulu, ko kuma ace Kuluwa” duk babu wanda bana amsawa sai Kuluwa. 

    Mahaifiyar mu wato Inna ita kadai take kirana “Hauwa” ko ta ce Kulu”. In kuma ta bushi iska ko in ta so ganin zumburo bakina, sai ta ce Kuluwa din.

    Malam Bilyaminu Ya kasance mutum mai kyakkyawar muamala da makwabta da abokan sanaarsa a kasuwa, kai dama duk wadanda suka zauna tare da shi a unguwar Kofar Naisa da Wambai sun yi masa kyakkyawar shaida. 

Shiyasa alamarin bacewarsa rana daya ya girgiza duk wanda ya san shi.

    Ni kadai ce yar sa a raye a duniya yanzu, a yayan da ya Haifa wajen guda biyar, wasu sun mutu a ciki, wato wasu an haifesu stillbirth, daga kaina kuma ni Hauwa-Kulu, ko batan wata Innata bata sake yi ba, ni nasan Inna tana matukar so na, watakila don ni kenan guda da Allah ya bar mata.

     Tun daga wata fitar Babana kasuwa bai dawo gida ba, babu inda Inna bata je neman sa ba, haka ba inda bata turani ba data san yana zuwa. Har gidan kanin sa Zakari ta je neman sa, duk da ta san ba wajen zuwan sa bane, masu iya magana suka ce “in abinka ya bata, duba har inda baka tsammanin shigar sa”.

     Wannan ne dalilin ta na zuwa Dan agundi gidan Baba Zakari cigiyar mijin ta Malam Bilyaminu.

     Baba Zakari da ya fito sai ya gyara tsayuwar sa a kofar gidan sa yana gyatsa, sannan ya dubi Innar Hauwa da wani kallo a tsiyace, irin na kashi wannan ya fi ku daraja a ido na, yace cikin gatse, 

    “Halan kin yi batan kai ne? To yana inda kika bani ajiyar sa a kuryar daki na ko, in banda neman jidali yaushe rabo na da matsiyacin mijin ki da bai san hakkin zumunci ba, yo banda neman magana irin naku na mata me zai zo yayi min? Ko ya gaya miki akwai wata sauran kadara tsakanina da shi ne bayan ta yan ubancin da ke tsakaninmu?

    Don haka sawun ta a likkafa ta bar kofar gidan Zakari. Bayan ya caccaba mata bakaken maganganun da gobe koda sadaka aka hadata bazata yarda ta sake tako kafafun ta kofar gidan sa ba. 

    Tun ana maganar batan nasa kadan-kadan, har Innar Hauwa ta tabbatar mijin ta wani abu mara dadi da bazata ce ko meye ba watakila ya same shi, ko daga irin muggan mafarkan data ke yi a kan sa, ko dai ya bata, ko ya mutu a wani wuri inda baa san shi ba, don bai taba kwana a wani waje tun sanin ta da shi da ba a gidan sa cikin iyalin sa ba.

    Batan mahaifina ya faru ne tun ina yar shekaru goma, wannan alamari ya sanya mu cikin wani hali na damuwa da dimuwa mai tsanani, wanda ya kusa haukata Innar Hauwa, kasancewar mahaifiyata wato Innar Hauwa, irin matan nan ne da miji ya gatanta ta hanyar dauke musu nauyin komai na rayuwar yau da gobe, don haka bata sanaar komai sai kiwon dabbobin ta, duk abinda zasu ci shi yake kawowa, hatta omon wanki da sabulun wanka Malam Bilyaminu ya daukewa iyalin sa.

    Don haka batan sa ran daya ya daga hankalin ta dana duk wani mai kaunar mu kamar Malam Isa, kada tilon yar sa wato ni Hauwa in ji labari, domin na saba da shi kusan har fiye da yadda na saba da Inna don shi kam Baba ba kwaba ne ba hantara ba kamar Innata ba.

    Daga baya da watanni suka mika baa gan shi ba, kuma babu labarin sa, sai aka tattaro duka kayan sayarwarsa na gwanjo da ke rumfar da yake ajiyewa a kasuwa aka kawo mana gida.

    Daga wannan lokacin rayuwa ta sauya mana nida Innata, takalihun rayuwata ni Hauwa ya koma kan Innata kacokam, kasancewar bamu da tabbacin Malam na raye ko mutuwa yayi ya fi komai daga mana hankula, sannan a wancan lokacin baa satar mutane balle a yi tunanin ko an yi garkuwa da shi ne mu jira kira. 

    Daga baya daga ni har Innar Hauwa muka ga babu mafita banda addua agare shi, sai Inna ta maida komai ga Allah ta kuma saka nima na koma yi masa addua kan Allah yasa a koina yake ya fada a hannu nagari, hannun da ba zai taba cutar dashi ba. 

    A duk sallahr farillar Inna tana rokon Allah idan Baban Hauwa yana raye, Allah ya bayyana mana shi cikin koshin lafiya, idan mutuwa ya yi, Allah ya bayyanar da hakan a gare mu hankalin mu ya kwanta, ta maida hankalin ta kacokam! Kan kula da rayuwar tilon yar ta wato ni (Hauwa-Kulu). 

    Ganin cewa yanzu bamu da mai taimaka mana ta fuskar ciyarwa sai Allah sai makwabta da muka saba ciyar da junan mu, musamman gidan malam Isa, komai na gidan da Malam ya ajiye mana a rumbun abinci a hankali ya kare tas, sai hakan ya sa Innar Hauwa ta fara tunanin sanaar yi, daga karshe ta tsayar da sanaar da ta fi yawa ga matan cikin Badala wato sanaar dafa abincin sayarwa a cikin gida don nemar mana na batarwa dana cefane da bukatun yau da kullum. 

    A kullu yaumin Inna ta kan dafa shinkafa da wake tiya daya, dahuwa mai kyau, ta soya mankulin ta da albasa, ta daka yajin maggi, bata dora min talla a dalilin tana cikin masu adawa da tallan yara mata, ta fi yarda da in je makaranta fiye da in nemar mata kudi, don haka tun Baba yana nan ina zuwa makarantar boko da safe, da ta allo da yamma. A rashinsa kuma ban fasa zuwa ba.

    Da aka gane tsaftar abincin ta a hankali har gida ake zuwa a saya, kuma akwai wani yaro anan makwabtanmu wai shi Saleleh, yaron ya saba da Inna ya shiga jikinta don shi yake zamarwa Babana a shago in zashi wani wuri, bayan batan sa ya cigaba da shigowa gun Inna tana bashi abinci da haka har suka saba don haka shi ta roka yake zuwa ya fitar mata da abincin makarantar bokon da nake zuwa, wato makarantar firamare ta gwamnati ta Kofar Naisa, wadda bata da nisa da gidanmu. Ita kuma tana bashi abincin data dafa da naira goma daga cikin cinikin kullum ya dawo. 

    Kafin sha biyun rana Saleleh zai dawo da kudin ta a kulle a leda cif. An sayar da wake da shinkafan, har ana neman kari, sabida dadi da tsaftar abincin Innar Hauwa.

     Sai mu yi cefanen abincin gobe kuma, mu kuma yi amfani da ribar da muka samu. Idan shekara ta zagayo Innar Hauwa na fitar da ragunan data kiwata ta sayar a kasuwar Raguna duk sallar layya, sai ta sayi wasu kanana ta kara kiwatawa zuwa shekara ta gaba.

     Da wadannan sanaoin guda biyu ni Hauwa da Inna ta muke rayuwa har tsayin shekaru biyu da batan Malam, muna cikin alhinin rashinsa. 

    Duk da cewa ni Hauwa ba wata kyakkyawa bace acan-acan, gani nan dai kalar Kanawan usli, wankan tarwada kuma makimanciya ga kyau, banda idanuna farare manya dasu masu kama da zagayen kwan zabo, ba abinda zaka ce mai bayyannnen kyau ne a halitta ta.

    Na farko bani da tsayi, kuma bani da rama, amma bazaka kira ni mai kiba ba, gani nan dai yar duma-duma haka, lubu-lubu mai jiki (luscious) tubus-tubus kamar na kulba, na kasance yarinya mai zafin nama tun ina karama da kwazon taya Inna aiki, sannan da tsananin son Uwa-mahaifiya da tausaya mata, musamman dana wayi gari babu Baba tare da ita, na fahimci ita kadai take buga-buga da kulle-kulle don ganin ban rasa komai ba. 

    Hakika na saka son Inna ta da yawa a raina, da tausayinta tun ina kankanuwa mai cikar lafiya, ga Inna da kujuba-kujuba a cikin gida tayi wannna ta koma ta yi wancan, shiyasa nima bana kyuya wajen taya Innata aikin abinci da ayyukan cikin gida tunda na soma kawo karfi, ni dai bar ni da shiru-shiruna na rashin son magana da rashin son hayaniya, sai manyan idanuwa tubarkallah masu yiwa wanda duk na harara barazana, farare kal dasu, masu haske da sheki da wani kwantaccen ruwa a kasan su, inna juya ido sai ka ga kamar hawaye ya kwanta.

     A kaina akwai tarin sumar hausawa baka mai karfi irin cunkus dinnan, wadda bata taba ganin man shamfo ba (relaxer) ko na Danjangabo da ake amfani da shi a lokacin domin motsa gashi. Ni Hauwa tun ina kwailata akwai son wanka da yawan shafa turaren ‘Binta-Sudan’ ko ‘Dan Duala’ wanda na Inna ta ne da take yawan siya don amfaninta, kullum tayi wanka su take shafawa, sai nima na ara na yafa.

    Lokaci-lokaci Inna kan sai min maina na shafawa na musamman (Dela-Maigurguwa), can gaba da zamani ya kara sabuntawa wato ‘cream’ ya shigo, sai ta koma saya min ‘TonyMontana’ don nima in jera da yammata, a lokacin a shekaru goma sha biyun da nake dasu sune matakin farko na fara zama budurci, duk da ko kirgen dangi ban fara ba. Komai nawa dai-dai misali ne na asalin hausawa gaba da baya, kuma na halitta wanda babu kirkirarre. Zaku iya kiran ni Hauwa  Kulu da (natural black African beauty) ta zamanin da na taso.

    A wannan shekarar da aka shiga na samu kammala makarantar firamare, na zana jarrabawar kwamen intarans, watakila don na fara karatun da wuri ne na gama firamare da wuri, inda ba da jimawa ba sakamako ya fito, Hauwa sarkin himma (ta bakin Inna), na ci makarantar yammata ta gwamnati ta jeka ka dawo wai ita Shekara (GGSS Shekara).

     Asalin iyayena kanawa ne na usul, wadanda ake kira Kanawan cikin Badala.

     Wane tudu wande gangare duk aka bi za a fahimci daga Inna har Malam yan asalin cikin kofofin Kano ne, basu da wani kauye da zaa ce daga can suka fito ban da kwaryar cikin birnin Kanon. 

    Inna iyayen ta sun jima da kwantawa dama yan cikin Kofar Kansakali ne, kusan yanzu ita kadai ta rage a raye cikin jamaar gidan su babu wanda zata kira nata da ya saura, ta haifeni a shekaru na girma tana da kusan shekaru arbain sanda ta haife ni, shi yasa wasu ke dauka Kaka ta ce, babu wanda Inna zata kira nata a halin yanzu duk sun gushe, banda makwabta da abokan arziki da suke rayuwa a lungu guda.

    Shi kuwa Malam Bilyaminu yana da dan uwan sa na jini Zakari mai wankin hula, yana nan a raye da nasa iyalin a unguwar kofar Dan agundi wadda ke daura da kofar Naisa.

     Sabanin Malam Bilyaminu shi Zakari Allah ya bashi haihuwa da yawa maza da mata sun kai goma, sabida yana da yawan aure-aure, mata biyar ya aura, uku ne a gidan yanzu, don haka yayan iyaye daban daban suka haife su, sai dai ka samu biyu a daki daya ko uku a daki daya, amma kowa ya san babu jituwa ko kankani tsakanin Malam Bilyaminu da kanin sa malam Zakari sai yan ubanci na gani kashe ni, wanda a kan sa suka rayu tun suna kanana har gashi sun cimma furfurar su basu daina ba. 

    Bayan batan Malam, Inna na yawan korafi gareni, “tun batan dan uwan sa bai taba zuwa ya ga halin da muke ciki ba, bai kuma taba tuna wai dan uwan nasa ya bar diya mace guda daya, yayi tunanin kula da lafiyarmu ko da bai taimaka mana da komai ba”. 

    Sai in ce Inna kenan. Ai bai ma kamata ki damu ba Inna, don dama kin kwana da sanin ba batan sa ba damuwar sa bane, da kin yi shawara da ni ma bazaki je cigiyar Baba gidan sa ba Inna. 

    Amma a cewar Innar Hauwa, lalurar batan mutum ta wuce komai, don gara a ce mutuwa yayi a kan ta, a ganin ta sun cancanci kulawar sa ko yaya ne a bayan ido dan uwan nasa. Wannan shine cikar zumunci.

    Wani abun mamaki shine bai fi shekaru biyu da batan Malam Bilyaminu ba, aka wayi gari aka ga Baba Zakari ya kudance, ya rushe gidan sa ya zabga ginin katon gida mai dakali biyu irin na masu kudin da, anan kofar dan agundi, ya sayi motar yayi ta zamani da ake kira Marsandi, ya kuma bude katon shagon sayar da atamfofi a Singa. Sunansa ma ya koma Zakari mai atamfa.

    Ba irin maganganun da mutane basa yi akan arzikin Zakari na rana daya, wanda babu wanda ya san inda ya samo shi. Shikuwa ya kame bakin sa daga tambayoyin jamaa da an yi magana Baba Zakari zai ce DARE DAYA Allah kan yi Bature.  

    Wannan ba shi ne a gaban Innar Hauwa da ni kaina Hauwan ba, sai shirin fara karatuna a makarantar yammata ta Shekara, abinda Zakari bai yarda yaran sa maza da mata ko daya cikin su ya yi ba hana rantsuwa in ka dauke babban cikin su da ya saki uwarsa ta fita dashi shikadai yake yi a boye, wato Jamil Zakari, da kannen sa ke kira “Yaya Jamilu”. 

         ****         ****            ****     


       APOLO”

W

ani ciwon ido ne na yayi (eye flu) da aka yi annobar sa a wasu shekarun can baya. Wanda daukacin yara da manya dai-dai ne suka tsallake shi. 

    A wani wata na Junairu da muka shiga, bazan manta ba aka wayi gari da annobar cutar ciwon ido na apolo a garin Kano, yaya aka yi yaya aka yi? Ko wane tudu wane gangare aka bi aka samo? Sai gani nima Hauwa na samo nawa rabon na apolo, daga makarantar bokonmu ta Shekara. Amma Inna ta gagara dauka sabida karfin jinin ta da shaye-shayen magungunan gargajiyanta yana bata immunity iri- iri.

    Da farko Innar Hauwa bata dauki abun nawa da muhimmanci sosai ba, don haka bata damu ba, duk da idon yayi jajawur ya kuma kankance kamar gauta, abinda yasa bata damu ba shine kusan kowanne yaro ya samu rabon sa na apolo a wancan lokacin, kai har manya ma, don in yaro daya ya samo duk gidan su sai sun raba (dauka). Amma in aka kwana biyu ko uku da kan sa sai kaga yana washewa. Daga nan kuma sai labari ko ba a saka masa maganin komai ba.

    Don haka babu wani mataki da Innar Hauwa ta dauka baya ga tunanin cewa in an kwana biyu idon zai washe dan kan sa, kamar yadda yake yiwa 'ya'yan kowa.

Ciwon idon ya ritsa dani Hauwa-Kulu ina yar shekaru goma sha biyu da haihuwa. Aji biyu na karamar sakandire a GGSS Shekara.

    Wasa-wasa abin da ake zaton kwana biyu ko uku zai washe sai gashi ya dauki wata biyu ba abinda ya canza, sai ma idon ya koma ya cabalbale da kwantsa ba kyawun gani, ko buduwa baya yi idan gari ya waye wato na tashi daga barci, in kai mai kyankyami ne kaga idona a lokacin bazaka iya cin abinci ba, kullum kuma ciwon karuwa yake ta yi kamar ana rura shi maimakon ya ragu ko yayi sauki, na kan cewa Innata idan na yi sujjadah ji take kamar kwayan idon zata zazzago (fado kasa).

     Daga baya idon ya koma tsiyayar da ruwa da hawaye ko buduwa ya daina yi sosai, yayi jawur yayi luhu-luhu gwanin ban tausayi. 

    Innata, wato Innar Hauwa na daga cikin mutanennan yan gargajiya da a rayuwar su basu bada yarda da maganin asibiti ba, kai ita ko sunan likita ta ji an ambata sai ta yi tsaki, don haka kullum saidai ta gasa min idon da ruwan zafi da dan gishiri, ta rambade min shi da farin kwalli, in yi ta kuka don azaba, wanda hakan yasa ciwon idon kullum sai karuwa da cigaba da taazzara yake ta kara yi.

     Watanni uku da fara ciwon, idon ya rikide ya koma min wata kebantacciyar cutar idanu da ake kira hakiya’ (cataract) ta fito ta kwanta tayi babakere a tsakiyar duka idanun guda biyu.


Lokacin ne hankalin Innata ya fara tashi, ganin wadannan Hakiya cikin kwayar idona sun fara girma, kowa ya ganni sai yayi fadan don me Inna ta ki kai ni asibiti? Meyasa ta bar idon ya zama haka? Ayi ta mata fada kamar a ari baki. A kuma gaya mata ai Innar Hauwa hakiya baa wasa da ita fa”. 


    Amma Inna tayi funfurus. Sai da ta kai na daina fita don zuwa makaranta don fadan da malamai ke yi akan a kaini asibiti amma Inna ta ki ji, sai cewa take ai tana saka min farin kwalli shine babban maganin ciwon ido, a hankali zai tsotse hakiyar gabadaya, amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Har sai da ta kai ta kawo idanuwan nawa gabadaya sun yi fari tas, sabida yadda hakiya ta mamaye su.

    Yau muna tsakar gida ina zaune bisa tabarma da littafin makaranta a hannuna, ba tun yau ba na fahimci na daina ganin abubuwa da kyau, yadda suke a zahirin kamanninsu, amma duk da haka na dage ni a dole karatu zan yi wanda ya wuce ni a makaranta, duk da idanuna dake neman zagwanyewa yau don zafi, amma me? 

    Ko da na bude cikin shafukan takardar sai na ga bana banbance duk wani rubutu dake cikin littafin sai hasken takardar kadai. Sai wasu taurari suna gilmawa ta gaban idona. Wannan ya tabbatar min, kodai ganina ya tafi, ko yana gab da tafiya ya barni. 

    Cikin tsorata da alamarin na kwalawa Innata dake madafi tana kwashe tuwo kira, nace, Inna ki zo, watakila fa Inna NA MAKANCE!!!

     Inna na daina ganin komai a cikin littafi na komai ma bana ganewa. 


    Mummunar faduwar gaban da ta samu Innar Hauwa a wannan lokacin bata taba jin irin ta a rayuwar ta ba, ko lokacin data gane batan Baban Hauwa, da sanda aka shigo mata da gawar Zulkiflu daga rafi. Watakila sabida son da take wa Hauwa ne, ko kuma don ta saka buri mai girma a kan Hauwa a ran ta??? 

    Burin ta na Hauwa ta yi maza ta girma ta aurar da ita, burinta na HAUWA ta zamo mai zurfin ilmi a rayuwa, irin wanda basu samu damar yi ba su, itada Malam, kuma basu da wasu yayan da zasu yi shi bayan ita, burin ta na Hauwa ta samu kwakkwaran abun yi da zai rike su a tsufanta nan bada jimawa ba, koda ta zama malamar makaranta ne. Ta kuma yi aure ta hayayyafa, yayan ta su maye mata gurbin yaya masu yawa da Allah bai bata ba a rayuwar ta? Ko kuwa don ita kadai ta rage mata matsayin sanyin idaniya a halin yanzu, amma ace yau idanun ta babu? Ba karamin fadar da gabanta hakan yayi ba.

    Sai Inna ta bar abinda take yi, ta taso zani na kwancewa ya kusa faduwa ya barta, ta yo kan Hauwa da gudu, tana ambaton "bana son fatan tsiya HAUWA. INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIOUN.

    ****     ****          ****


    

    

    

    

    Wannan shine labarin da Barr. Hauwa Bilyaminu ta bayar a safiyar yau a dakin taron da aka hada mata na 'meet and greet,' tsakanin ta da kungiyoyin da take da alaqa dasu, kungiyoyi ne da suka tsayawa rayuwarta har ta kawo wannan matsayin, da sauran masoyanta mutanen arewa wato masu nakasa iri daban daban maza da mata wanda yau yayi quenching curiousity da jita-jitar kowa cewa HAUWA BILYAMINU IS A PHYSICALLY CHALLENGED PERSON. Kuma a ranar ne Hauwa take murnar cika shekaru hamsin da haihuwa, sannan a ranar ne ta karbi jagorancin Nigerian Bar Association. Wanda yayi daidai da ranar anniversary din aurenta da "HER PACE-SETTER..." shekaru dai-dai har talatin da daya. 

    

    Barr. Hauwa Bilyaminu Kofar Naisa, ta bamu labarin asalinta da tushenta ne a wannan muhimmiyar ranar mai tarin achievements a gareta daga hakikanin bakinta, da asalin lalurar ta. Daga nan na kasa hakura da jin me ya faru da sauran rayuwar HAUWA-KULU? Ni Sumayyah Abdulkadir (Takori) na bibiyi labarin Barr. Bilyaminu bayan taron nan, zan kuma labartawa Takorites labarin HAUWA-KULU daga ranar data rasa abu mafi muhimmanci ga rayuwar bil adama har zuwa yau da take bikin murnar zagayowar cikar shekarun haihuwarta hamsin a duniya.


     ****              *****            *****



M

afarin makancewar Hauwa-Kulu kenan. Makanta mai sunan hakiya da akafi sani da (cataract blindness), ko a ce makanta mai lasisi, tunda kuwa Innar ta ce ta sayo mata da kudin ta.

     Don da farko Inna ta dauka Hauwa wasa take yi, amma cikin kwana biyun da Hauwa ta koma lalube da tsakar rana ko da daddare ta fahimci cewa Hauwa da gaske take, tana gab da daina gani, amma dai tana ganin haske da inuwar mutum in ya tsaya a kan ta, dan ko daki sai da lalube take kai kan ta, ko Innar ta kama hannunta ta kai ta don kada ta buge goshi. 

    Saboda haka ne wannan karon Innar ta tsorata. Dole kanwar na ki, ta tambayi inda zata kai Hauwa aka ce mata ta kaita bangaren ido a Murtala (Murtala Mohammed Specialists Hospital), washe gari tasa ta a gaba sai asibitin Murtala.

    Da tambaya suka isa bangaren ido, a kafa suka tako suka taho tun daga kofar Naisa har zuwa bakin asibitin Murtala. Kusan wannan shine karon Inna na uku da zuwa asibiti a rayuwar ta, sauran biyun duk dubiya ta zo, don ita ba mai yawan ciwuwwuka bace sabida yadda ta tsaya da shan magungunan gargajiya da jike-jiken saiwoyi akai-akai bata yarda tayi wasa da su, don ko haihuwar Hauwa data marigayin Yayan ta bata yarda an kaita asibiti ba, don haka hatta yanda ake karbar kati basu sani ba, saida taimakon wata mata da itama ta kawo yar ta ganin likita, suka samu suka karbi kati suka hau dogon layin ganin likitan ido. Don kuwa a makare suka iso.

     Suka kuma gamu da dogon layi don ranar ganin likitan ido ce wato Alhamis.

    Sune kusan na karshe a kan layin, suka zauna a kan bencin da aka tanadar wa marassa lafiya masu bin layin ganin likita bayan sun mika katin su, maaikatan jinya da yake akwai marassa kirki cikin su, idan suka juya suka kalli idanun Hauwa sai suyi tsaki, su hau maganganu na gugar zana cikin zagin jahilcin mutanen kauye wajen sakaci da zuwa asibiti, sai ciwo ya ci ya cinye a kwaso jiki hajaran majaran wai an zo asibiti, sun dauka daga kauye suke don sun fi musu kama da kauyawa. 

    Inna na jin su, ta yi shiru ta sadda kai, bata tanka musu ba.

     Wata metron zaqaqura a cikin su, ta kasa gugar zanar ma, sai da ta fito fili ta dubi tsakiyar idon Inna ta ce.

     To yanzu saboda Allah baiwar Allah me likita zai iya muku a wadannan matattun-rubabbun idanun da hakiya ta riga ta cinye? 

    Allah wadaran bakauyen mutum wajen wasa da lafiyar sa!.

    Da sauri Inna ta dago ta dube ta, kafin ta rufe baki dayar ta amshe. 

    “Taya ni gani, tun dazu nake kus-kus din hakan a raina kika riga ni furtawa, saboda Allah dubi yarinyar nan sai da Hakiya ta gama cinye idon tas, sannan zasu wani dauko kafa budu-budu dasu su zo asibiti, yo wannan ai ta gama makancewa da lasisi, ko me likita zai iya musu a wannan lokacin ina ce aikin banza ne?. 

    Inna dai na jin su, amma bata tankawa, duk da ta yarda basu da mutunci kuma basu girmama furfura, amma ita da kanta ta yarda har da sakacin ta wajen lalacewar idon Hauwa-Kulu.

    Ta sunkuyar da kai kasa sosai, hawaye fal idon ta, amma bata bar su sun zubo ba. Ta dago ta dube su, su duka basu fi a kira su yayan cikin ta ba amma suke mata wannan tanadin. Kodayake kowa ya san yadda maaikatan jinya na gwamnati suke, daidaiku ne masu jin kai da kirki ga marar lafiya, musamman ga mutanen kauye da talakawan da suka raina wa ajawali kamar yadda suka raina Inna din, don sun ganta da kodaddiyar atamfa mai barewa, kuma tayi abunda a wurin su jahilci ne da gidadanci. 

    Sanin halin malaman asibiti da sau tari ake bata labari tuntuni, yau da suka gwada mata sai bata yi mamaki ba kuma bata ji zafi sosai ba, shiyasa ta daure taki damuwa da su, fatan ta kawai su mika katin su ko sa samu ganin likita.

     In ya so shima ko me zai ce mata yace mata a shirye take da daukan laifin ta. Fada ne dai ta san zata sha shi har a wurin likitan shima, to in dai a karshe zai baiwa Hauwa magani, ganin ta ya gyaru, ta rabu da wannan hakiya, to babu komai, shima zata jure nasa.

    Ba abinda malaman jinya basu ce mata ba na raini da wulakanci, da suka tambaye ta ko tun yaushe Hauwa ta fara hakiya? Ta ce an fi wata uku, suka ce to tun yaushe suke ganin likita? Nan kuma ta sunkuyar da kai ta ce basu taba zuwa ba sai yau. 

    Sai wata maaikaciyar jinyar mara kunyar gaske tayi kamar ta doke ta, yadda ta rufe Innar da fada duk da ta girme ta, ta ce to ba zata mika katin nata ga likita ba, su tattara su tashi su tafi, in yaso su je su karata da farin kwallin da take rambada mata kamar idanun kwatami. 

    Inna ta kauda kai ta rabu da su. Amma bata yarda ta tafi ba, duk da sun kore ta. sun kuma tabbatar mata bazasu mika katin nata ba. Sai suka rabu da ita suka koma hirar da ta shafe su, suka manta da su a wurin. Lokaci lokaci suna kiran sunan marasa lafiya suna shiga ofishin likita amma basu kara bi ta kan su Hauwa ba, don a wurin su sun gama da babin su.

Hirarrakin da suke yi duk a kan matashin likitan su ne, wanda aka kawo musu ya maye gurbin kwararren tsohon likitan ido wato Dr. Barde Abba, wanda shi kowa ya san kwararre ne. Inna na ganin hirar tasu a matsayin cin naman abokin aikin su. 

    Don a cikin hirar tasu ta ji suna fadin.

    “Ai tsautsayi ne kadai zai sa mutum ya fada hannun sa, da sunan wai yayi masa aikin fidar ido, yayi yarinta kwarai da gaske da zama likitan ido, a ganin su baa taba yin yaron likita a tsangayar ido mai kananan shekaru, kuma mai jarumtar hali da karfin hali kamar sa ba, a dai tarihin asibitin Murtala bakidaya da suka jima da sani, don sun dade suna aiki anan.

     Dayar tace ai hatta sauran likitocin duka asibitocin da ke cikin kwaryar birnin Kano a yanzu, bata jin akwai karamin yaro kamar wannan da kwalin likitanci, bama na MBBS kadai ba, wai har consultancy ya gama, wanda bai wuce ace masa saurayi dan tashen balaga ba, watakila dai zuqen karatu aka yi tayi masa, saboda yana da uwa a gindin murhu, tunda Baban sa wato mahaifin sa Farfesa ne (Prof.) na tsangayar likitancin ido, a jami’ar koyarwa ta Abdullahi Bayero.

  Gulma tayi dadi sosai a tsakanin su. Daya daga cikin su kuma ta ce,

    aah fah, ku daina Magana akan abinda baku da tabbas, ai an ce baa jamiar Bayero yayi karatun likitancin nasa ba, a can Jeddah ne, ta kasar Saudi-Arabia.

     Wato alumnae ne na Jamiar Sarki Abdulaziz. Can kuma kun san baa dadewa ana karatun likitanci kamar yadda ake dadewa a nan Kano da sauran garuruwan Arewacin Najeriya, idan muka auna a hankali, a bisa maauni na adalci, zamu ga cewa in har ya bar sakandire a shekaru goma sha shidda, ya shiga jamia a shekarar da ya bar sakandire zai iya yin MBBS na tsahon shekaru biyar acan, ya kuma dora da consultancy shima na shekaru biyar zuwa shidda, zaku ga cewa babu zuke cikin ilmin sa har kuwa da hidimar kasa”, inji mai dan hankalin cikin su. 

     Ta kare zancen ta da cewa.

  Don haka ba abun mamaki bane don ya zama likitan fidar ido a shekaru ashirin da bakwai zuwa da takwas da haihuwa, in dai har da gaske ya fara karatun da wuri, ya kuma gama karatun sakandire a shekaru akalla 16-17, kuma dai yana da gatan sa a fannin karatun nan kowa ya sani”.

    “Sai shegen iyayi da uban tsayi kamar karan raken takanda, dan sirit da shi kamar ka bushe shi ya fadi amma sai iyayi, ga dan banzan manyance kamar gyambo a kafa.

     Karambanin irin su ya wuce shekarun su, don ko ni nan na tabbata na girme mishi wallahi”.

    In ji wadda ta fi sauran rashin ta ido wai ita Nos Saratu. Duk suka sa dariyar maganar tata, Nos Maria har da kyalkyalawa da sukuyawa da rike ciki, irin ta wadanda dariyar gulma tayiwa dadi.


    Zaka yi mamaki in ka ji cewa kusan duk wannan gulmar tasa da zunden nasa da suke yi, wato shi sabon likitan nasu, yana sauka ne reras, kuma tiryan-tiryan a cikin kunnen sa kamar an kunna radio yana sauraren su. Bai san sanda ya ajiye biron hannun sa ba don ya kasa cigaba da rubutun, ba wai haushi yaji ba don sun aibata halittar sa, aah, kawai abin ya bashi tsoro, cin naman mutum haka a kan kunnen sa da tsakar rana babu ko shakka, ya fiddo ido warwaje ya kuma kara sakin kunnuwa yana sauraren su da alajabi da mamaki. Mata sun kware da gulma ya sani, amma ta wadannan ta bashi mamaki kasancewar su Nosis ne dake karkashin sa.

     Shima ya yarda kamar yadda mahaifiyar sa ke yawan fada wato shi “SARHAM” mutum ne mai karfin JI. Wato jin sa yana da karfi, kamar yadda ganin sa yake da karfi yadda baa zato. Kusan komai na halittar sa ma mai karfi ne Ubangiji ya yi masa, idanun sa basa bukatar madubin kara karfin gani (medicated glass) da yawancin likitoci ke amfani da shi. 

    Sarham hatta takun tafiyar sa wato (gait) din sa shima mai karfin gaske ne, gab-gab-gab… haka zaka ji takunsa in ya dumfaro ko ya durkako inda kake. Kafin ya iso sautin takunsa zai gaya maka isowar sa. Baban sa kan ce, shi din, wato Sarham, “DAN BAIWA NE KUMA NA MUSAMMAN A CIKIN DUKA YAYAN SA.

    Komai nisan zance in dai yana gefe aka yi shi, to kuwa tabbas Sarham zai jiyo shi tsaf. Wannan wata baiwa ce da Ubangiji ya yi masa da ba kowa yake yiwa ba, wadda a kullum yake gode masa a kanta, wato baiwar kyakkyawan ji da gamsashshen gani, da suka banbanta dana sauran mutane da yawa, shiyasa a kullum kunnuwan sa suke zuko masa abinda baa zaci ya ji ba.

    Ga shi dai da gaske siriri din ne shi, kuma dogon mutum a halitta, kamar dai yadda suka gulmanta, shima ya san hakan, don har wasu na yawan fadin wai yana dieting ne saboda sirantar sa mai yawa ce a matsayin sa na namiji, amma kuma a zahiri kakkarfa ne ta cikin kasusuwansa, zaka gane hakan ko daga fadin kirjin sa da kaurin kwanjin sa, wanda ke nuna duk safiya yana motsa jikin shi da kyau da hanyoyin motsa jiki irin na bature, ko daga kaurin tsokar damatsan hannun sa. 

    Kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham ka fahimci yana matukar kula da lafiyar sa kwarai da gaske, ta hanyar kula da abinda yake ci, da motsa jini (exercise) bada wasa ba a duk safiyar Ubangiji. Shi yasa yake dan shafal da shi mai dogon hanci.

    Sannan tsayin sa bai wuce kima ba kamar yadda Nosis dinsa suka kintata shi a gulmar tasu, kuma kaurin jikin sa ya wuce ace masa kamar na karan-raken takanda, kai shi bai taba jin wani ya kushe halittar sa ba banda wadannan magulmatan matan, iyakaci ana cewa yana ‘dieting’ baya cin abinci saboda kwalisa, amma shima ya san shi dogon ne saidai ba kamar karan-rake kamar yadda yaji suna cin naman sa ba. 

    Don haka ba tantama in aka yi laakari da kalaman bakinsu, da bayanin da mai dan hankalin cikin nasu tayi a kan karatun sa, zaa fahimci tabbas sun yi masa farin sani ba kirkirowa suka yi suka fada ba, har da abinda ya bashi mamaki cikin zunden nasu, wai a Baban sa Farfesa ne na tsangayar ido, kasancewar bai dade da zuwa Murtala ba, kuma shi dai ya san bai taba abota da kowa a asibitin nan ba, balle su maaikatan jinya mata wadanda a karkashin sa suke.

     Sai yayi dan murmushi kawai wanda ya motsa gefen kuncin sa na dama, ya cigaba da rubuce-rubucen da yake yi a cikin wani fayal na mara lafiyar da ya kammala dubawa ya fita, yace a ran sa.

    

     A zauna a kafa tebur saboda kai, ana rage maka zunubi haka ai ka isa ne, wanda bai isa ba ko kallon sa ba mai tada kai yayi.

    

     Yana cigaba da rubutu yana murmushi cikin mamakin gulma ta rashin aikin yi irin na mata musamman maaikatan jinya.

    

    Dr. Sarham Abbas Shanono kenan. Siririn wankan tarwadan matashin likitan da bai fi ace a bana ya gama makarantar sakandire ba, sabida duka-duka bai fi shekaru ashirin da takwas ba. 


    Hayaniyar Malaman jinyar sa, da ta dattijuwa Innar Hauwa data dage bazata tafi ba sai yar ta Hauwau ta ga likita, koda kuwa dukan ta zasu yi karewar rashin kunya, tace ban haife ku ba? ta kuma ce ai asibitin ba nasu bane na gwabnati ne, don haka basu isa ba da zasu hana ta ganin likita, inji dattijuwar, don sun kure hakurin ta, wannan hayaniyar ta hana shi fuskantar rubutun ma da yake yi yadda ya kamata. Gashi kuma a kofar ofishin sa ake ta wannan taqaddamar. 

    Su Nosis din sun dage da rashin mutuncin tunda ta bari sai da ido ya rube zata zo asibiti, to ta je ta nemi sandar yi wa yar ta jagora zuwa bara. Amma bazata batawa likita lokaci ba, a lokacin da ba abunda zai iya tabukawa wadannan idanun da hakiya ta gama canyewa murus.

     Innar Hauwa har da kukan ta, don taga alamar fada ba zai bi da su ba, tana rokon su da muryar ban tausayi su bar yar ta ta gan shi kada ta makance, ta yarda ta yi laifi amma a taimaka musu su ga likita don Allah, ta tuba. Kuskure ne ta riga ta yi. Nan gaba zata kiyaye. Amma maaikaciyar jinyar nan ko a jikin ta, ta dora kafa daya kan daya akan kujera tana karkadawa ta hana su shiga ta yi rantsuwa da Jesus din ta, ba zata bari su batawa likita lokaci a kan idonnan da sun riga sun kashe shi a banza ba.

     Me ke faruwa haka? Hayaniyar me kuke yi mata haka? Ke Maria, meye haka kike yi? Wannan ya dace da maaikacin jinya? Sister Saratu wannan matar bata girme ku ba?”

    Dakusassar muryar DR. SARHAM, irin ta mai fama da sabuwar mura, ta karade wurin, yana maganar yana furzar da dan tari, don sosai yake fama da mura daga jiya zuwa yau da ya dan sha ruwan sanyi, jikin sa baya son sanyi ko kadan.

    Muryar tasa ta dira a kunnen su da sigar tambaya daga inda yake tsaye a jikin kofar ofishin sa, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun bakar Jacket din sa, yana dan yamutsa fuska cikin gajiya da alamun jin yunwa, don tun safe yake aikin duba marassa lafiya har zuwa yanzu da agogo ya buga karfe biyun rana, wato lokacin cin abincin ranar sa kenan da zuwa yin sallahr azuhur, lokacin tafiyar sa gida yayi kenan. Don haka ya fito ne don tafiya gida.

     Yana sanye da bakaken ‘suit’ da ya zanzare kugun sa a cikin su, ya dora bakar jacket a kan su, wadda ta sauko har zuwa gwiwar sa, ta bada suurar cikakken dan gayun likita kuma dan kwalisa dashi na wancan zamanin, masu yawan yin zanzaro da belt.

     Bafullatanin Shanono mai kakkaifar murya, amma a halin yanzu ta dushe, ta dakushe da alama yana fama da ‘Catarrh’. 

    Yanayinsa na Kanawan usli ne, amma yanayin zubin jikin sa na Fulani ne, sabida sirantar sa da ta zabge masa cika ido kai bazaka ce yayi shekaru ashirin da takwas din da yake da su bama.

    Sister Saratu ta hau raba ido tsakanin Innar Hauwa da Likita Sarham, ta ki cewa komai, don a dan zamansa da su na dan gajeren lokacin da bai wuce sati biyu ba da aka yi masa transfer daga asibitin Abdullahi Wase (Nassarawa hospital) zuwa nan wajen su, sun fahimci halinsa na kirki yayi yawa a kan marassa lafiyan sa, (hes very compassionate and caring to his patients), shi yasa a halin rashin mutunci irin nasu suke cewa ya fiya iyayi da kidifiri.

     Ilai kuwa ya fahimci komai tun ma kafin su bashi amsa, don ya san ba yau suka fara ba, wulakanta marassa lafiyan da suka rainawa ajawali halin maaikatan su ne, daga zuwan sa zuwa yanzu ya gama shaidar hakan, kuma yana cikin sahun likitocin da suka san darajar dan adam, basa yarda da hakan, sai dai in an yi ne a bayan idon su. 

    A fusace ya soma fadin wato Metron Maria, Sister Saratu, Nos Mairo ba zaku daina wulakanta bayin Allah ba ko? Shin anya kun san aikin ku? Wannan ba shine halin da aka san maaikacin jinya na hakika da shi ba, hakan cin amanar aiki ne babba, kuma tozarta dan adam ne.

     Ina humanity din ku da aka hore ku da shi matsayin ku na maaikatan jinya, dana kiwon lafiya?

    A gaskiya na gaji da halin ku, ko jiya na raba ku fada da patient. Idan baku yi hankali kun yi aikin da ya kawo ku yadda ya kamata ba wallahi duk sai na yi reporting din ku.

     Ya dubi Innar Hauwa data sunkuyar da kai kasa tana tsane ido, yace.

     Baiwar Allah me ya faru? Waye babu lafiyan? 

    Innar Hauwa ta ji dan kwarin guiwa ya shige ta, saboda a cikin muryar sa mai dushewa da rashin karsashi saboda mura, akwai (caring) wato kulawa da darajja dan Adam, ta rausayar da kai gefe ta ce,

     dama yarinya ce na kawo tana ciwon ido, to sun ce ban zo da wuri bane shiyasa bazan ga likita ba, shine dalilin da nake ta basu hakuri”.

     Tausayin matar ya kama shi, ya dubi yarinyar da take rike da hannun ta, yadda hakiya ta cinye rabin idon sai da tsigar jikin sa ta tashi, zuciyar sa ta tashi, ga kwantsa babu kyawun gani, da sauri ya dauke idon sa daga kallon yarinyar, ga kafafun su futu-futu da kura tabbacin sun sha tafiyar kasa mai nisa kafin su iso asibiti, sai ya karbi katin su daga hannun maaikaciyar jinyar da katin ke hannun ta wato Nos Maria, ya kuma yiwa Inna umarnin su biyo shi a baya zuwa cikin ofis din. 

    Sai lokacin Inna ta gane shine likitan da ake musu rowar gani. 

    “Iya yaya aka yi aka bar idon yaci hakiya sosai har haka? 

    Dr. Sarham ya tambayi Innar Hauwa, yana haska cikin idanun Hauwa da yar tocilan din sa mai tsananin haske, yana magana cikin tsantsar damuwar da ta kasa boyuwa a muryar sa, yana cigaba da haska cikin idanun bayan ya gwale su sosai, Inna bata iya ta ce komai ba amma guilt ya bayyana akan dattijiyar fuskar ta ainun. 

    Dr. Sarham ya gama duba idon Hauwa da tocilan din sa, ya kuma gama nazarin sa gabadaya duk cikin dan lokaci, sai ya koma ya zauna a bakar kujerar sa mai juyawa, itama yace ta zauna a kan kujerar zaman maras lafiya da ke fuskantar sa, ya bude mata fayil a take don ya gama gano Hauwa na bukatar aikin ido na gaggawa kawai, don a cire hakiyar. Ya sunkuyar da kai yana rubuce-rubuce a cikin fayil din ta, kafin ya gama ya dago ya dubi Inna.

     A hankali kuma cikin tsanaki, Dr. Sarham Abbas Shanono, ya shiga yiwa Innar Hauwa bayanin amfanin zuwa asibiti da wuri, da zarar an ga alamun ciwo, ba sai ciwo ya ci ya cinye ba, cikin tausasawa da lallashi da fasahar harshe irin nasa yake mata magana, ya gaya mata yanzu ba abinda zaa iya yiwa Hauwa a ceci idanun ta illa cataract surgery watau (fida don cire hakiya) ta gaggawa. 

    Likitan ya saka musu ranar aiki jibi-jibin nan, ya kuma fada musu kudin aikin. Duk da Innar Hauwa ta tsorata da yawan kudaden bata nuna ba ko a fuska. Duk da ta san kuwa bata da su a ajiye.

    Da suka koma gida Inna ta shiga cikin matsananciyar damuwa, na farko bata da kudin da likita ya bukata a yanzu, ko jarin wake da shinkafar ta ba zai yi kwatan su ba, abu na biyu tana ganin bazata iya bari a farkawa Hauwan ta ido ba haka kawai. A je garin neman gira a rasa ido. Ko a jangwalo wani abun da yafi karfin su. 

    Amma Hauwa ta dagewa Inna ita dai tana so ayi mata aikin nan. Inna ta gaya mata abinda take tsoro da kuma rashin kudin aikin a hannu, nan Hauwa ta dinga magiya har da kuka, tana rokon Inna ta amince in yaso ko dan taure daya ne cikin dabbobin ta a sayar a biya. Komai ya faru daga Allah ne. 

    Haka kan dole Inna ta amince da shawarar ta, don bata son kukan Hauwa ko bacin ranta. Ta fidda Akuya budurwa aka sayarwa mahauci. Washegari, wato ranar da aka basu, da sassafe suka koma asibitin Murtala.

Likita da abokan shiga tiyatar sa suka gama shirin yi wa Hauwa aiki, aka nemi Inna da ta saka hannu, Inna ta saka hannu amma da ganin ta zaka fahimci a matukar firgice take, gani take kamar aka shiga da Hauwa tiyatar nan bazata fito a raye ba, Inna ta soma hawaye tana sharewa da habar zanin ta, tana kankame da hannayen Hauwa. 

    Ganin haka Dr. Sarham ya shiga yi wa Innar Hauwa maganganu na kwantar da rai yana cewa kada ki damu Innar mu, lafiya zan maido miki ita, da iznin Ubangiji, da kiyayewar sa, da albarkar sa zaa yi aikin nan lafiya a fito lafiya, in sha Allahu. 

    Idanun Hauwau su koma tangaras, kamar yadda suke a baya su rabu da hakiyar da ke cikin su, hakiya musiba ce ga ido, kin ji ko Inna?. 

    Ta daga masa kai, ba don ta gamsu ba, amma bata fasa zub da hawayen ba. 

    A haka aka shiga da Hauwa dakin tiyata. Ko kafin masu allura su yi mata allurar tafi-da-ran ka wato (anaesthesia) fuskar Dr. Sarham Hauwa ta kurawa ido tana cewa a ranta inama tana ganin sa tar-tar, domin ta ji dadin abinda ya cewa Inna.

    Haka ta cigaba da kallon saitin fuskarsa kamar tana ganin sa sosai, alhalin inuwar sa da karshen tsayin sa kawai take iya gani, bata san me yasa take son sanin yaya kamannin sa na halitta suke ba, ko don tausasan kalaman bakin sa ne da yadda yake lallaba mata rikitacciyar Innar ta, domin a lokacin bata ganin komai dadai ama dai tana ganin haske cikin idanun ta. 

    Murmushin da Dr. Sarham yayi mata a lokacin kamar ya san me take ciki da zuciyarta ne, taji sautin murmushinsa a kunnen ta, ji tayi kamar ya fahimci ba abinda take son gani a lokacin sai hakikanin kamannin fuskar sa, ba don komai ba sai don ta kwatanta su da kyawun kalaman bakin sa.

     Ta kasa manta sautin murmushin nasa. Haka kalaman karfafawa marar lafiya zuciya cikin mutumtawa wadanda Dr. Sarham ya yi mata a lokacin, bata jin har abada zata manta su. Ya bata hope na cewa zata rayu, kuma zata warke cikin yarda da amincewar Ubangiji; wanda ya saukar da cuta kowacce iri tare da maganin ta.

    Tsananin tsoron da Dr. Sarham ya gani cikin idanun Hauwa-Kulu, da karkarwar da jikin ta ya fara lokacin da zaa yi mata allurar anaesthesia, ita ta saka shi dakatawa daga abinda yake yi wato saka safar hannu, ya sake matsowa daidai kanta har tana iya jin kamshin balaraben turaren sa, cikin taushin murya da lallashi Dr. Sarham yake cewa,

     Relax Hauwau. Zamu yi aikin nan lafiya da iznin Ubangiji kinji, kuma zaki samu lafiya Insha Allahu, zaki warke, saki ranki kin ji ko Hauwau?

     Daga haka aka soka mata allurar ‘tafi-da-ran ka wanda hakan yasa Hauwa runtse idanun ta, kuma ta tafi cikin barcin ne da mafarkan kamannin LIKITA SARHAM! Da fatan ko a lahira Allah ya hada fuskokinsu. 

    Don gani take kamar ta tafi kenan, duk kuwa da hope din da ya bata, har abada ba zata farka ba. 

    Wato dai Hauwa ta tafi barcin ne da kintacen fuskar Likita Sarham a zuciya da kwakwalwar ta, na wani irin kintace, da dakace, da kuma hasashen ko shin yaya kamannin sa na zahiri suke?

     Idan aka yi laakari da irin kyawawan furucinsa/kalaman sa???

    

    Dr. Sarham na iya ganin yadda Hauwa ta runtse marassa lafiyan idanun ta masu cike da ciwon hakiya a kan saitin fuskar sa… (with utmost curiosity) na son ganin hakikanin kamannin sa..

     Lokacin da ya dora hannnu akan idanun Hauwa-Kulu domin fara aikinsa da bisimillah dauke a bakin sa, sai ya ji wani sako na kwakwalwar sa kamar yana yi masa amsa kuwwa akan kada yayi, yana janye shi daga yi wa Hauwa aikin ido, yana ce masa kada yayi wannan aikin, don 10% ne tsammanin waraka wato nasarar wannan aikin kashi goma ne cikin dari. Amma aka ce kaddara ta riga fata!!! 

    

    Ya ci gaba da aikin sa cike da fargaba don ji yake tamkar wani dabaibayi ya zo ya dabaibaye hannayen sa ya rikita shi, ya hanashi yin komai daidai, don wannan itace tiyatar hakiyar ido (cataract surgery) ta farko da zai yi a rayuwar likitacinsa. Amma wannan bai isa ya zama dalilin kwacewar azancinsa da kwarewarsa ba ai. 

    Lokacin da yayi nisa da yi mata aikin, sai ya ji hannun sa da jikinsa sun karasa rikice masa da karkarwa gabadaya, zazzabi na shigarsa, zuciyar sa ta hau raurawa, ilmi da fasaha da training din abun duk suka kwace daga kwakwalwarsa ga wani gumi da ya hau yanko masa ta koina, zazzabin da wani irin ciwon kai na kara karfi, ji yayi ya koma tamkar wani dan koyo anan take, ya nemi iyawarsa da jajircewar sa a aikin tiyata da jaruntar sa wajen yin ta duk ya rasa. 

    A karshe ma Sarham ji yayi ya koma dalibin ajin farko da ko sakandire bai gama ba, exactly dai yadda maaikatan jinyar nan masu gulmar sa su Nos Saratu suka suffanta shi, har daya daga cikin su ta ce tsautsayi kadai zai sa ta bashi idon ta.

     Watakila kwacewar azancin da ya same shi a take, yana da nasaba da gulmar su Nos Saratu dasu Metron Maria, da ya saka a ran sa ya dameshi tun ranar, da suka saka shi cikin wani hali na rashin yarda da kansa. 

    Gulmar tasu ta dade tana yawo a cikin kwanyar sa, domin a zahiri sun ci fuskar sa, sun kuma raina matsayin iyawarsa da darajar kwalayen sa kamar yadda suka raina shekarunsa. 

    Bai san ta ina zancen nasu mara dadi ya samu halartowa cikin kwanyar kan sa ya hargitsa shi irin haka ba, musamman a daidai yanzu yayin gudanar da aikin nasa da ya kamata ya samu nutsuwa fiyeda kowanne lokaci, ya ji ya koma tamkar lokacin da yake cikin ajin sakandire a Science College Dawakin Tofa, ko kuwa sanda yake dan koyo na matakin farko a MBBS, inda ya koyo aikin likita a jamiar Sarki Abdul Aziz.

             ****          ****       ****


         HAUWA _ KULU

A

n yi aikin Hauwa lafiya an basu gado domin su yi jinyar idon kafin lokacin da likita zai kwance mata shi, a duba nasarar aikin ko akasin ta.

Makwabtan su Inna da yawa sun zo har asibitin domin duba Hauwa. Tun ranar da ya yiwa Hauwa aikin nan Dr. Sarham bai dawo asibitin ba yana gida ya killace kan sa a dakin sa yana fama da zazzabi da masassara da ciwon kai na damuwa da zullumi, domin kaso 80% na zuciyarsa na gaya masa cewa yayi kuskure a cikin aikin tiyatar da ya yi wa Hauwa.

Ilai kuwa ranar kwance idanun Hauwa ta zo, sai ranar ne Dr. Sarham ya shigo asibitin Murtala Muhammed. Bayan ya gama abinda zai yi a ofishin sa cikin rashin fara da rashin walwala kamar da (wanda ba halin sa ba kasancewar shi mutum ne mai yawan sakin fuska ga maaikata, mai fara da faram-faram da mutane musamman marassa lafiyan da suka zo gare shi) amma yau bai tsaya ganin kowa ba yana gama abinda zai yi a ofishin sa sai ya nufi dakin kwantar da mata domin ya duba aikin da ya yiwa Hauwa Bilyaminu.

Tun daga bakin kofa marassa lafiya da masu jinyar su ke gaisar da Dr. Sarham A. Shanono, shi Sarham, an yarda likitan kowa ne, sannan marasa lafiya na son shi saboda kirkin sa da farar sa, yana dakatawa a gaban kowanne gado yana amsawa cikin mutuntawa da tambayar kufan jiki, saidai fuskar nan ba murmushi kamar na kullum, murmushin nan da baya rabo da kyakkyawar fuskar sa ta fulanin Shanono yau babu shi. Haka yayi ta bin su daya bayan daya yana jin lafiyar su. Kusan kowa ya gane cewa shi din mutum ne mai mutunta jamaa ba Innar Hauwa kadai ba. 

    Har ya iso ga gadon Hauwa, wadda itace a gadon karshen dakin, suka gaisa da Inna da ke zaune a gefen gadon kan Hauwa bisa cinyar ta, ya tambaye ta ko yaya jikin na Hauwa, ta ce tun jiya take min korafin ciwon kai, amma Nos dinnan ta zo ta bata magani. Ta nuna daga cikin Nosis din da ke bayan sa, wadanda suke take masa baya su biyu suna gatsine mata fuska na kin zama ba yadda zamuyi dake.

    Bai kula da zancen Inna ba don hankalin sa kusan baya jikin sa. Bakidaya ya tafi ga son sanin aikin sa yayi nasara ko aah. Ya dauki file din Hauwa ya duba yayi rubutu a ciki sannan ya karasa gaban gadonta, yace cikin murmushin fatar baki wanda bai je koina ba. 

    Kululu-Kuluwa, Kuluwa yar gidan Innarta, yau zaa kwance ido, ina fatan kin shirya? Daga kwance ta amsa na shirya mana Dr, yau sati guda ban ga hasken rana ba, ka bi ka kunshemin ido da bandeji.

    Ta bashi dariya amma sabida yana cikin fargaba murmushi kawai yayi, ya fara kuncewa. Da adduoI a bakin sa. Nos din da ke bayan sa ce ta taimaka masa, suka soma warware bandejin da aka nannade idanun Hauwa da shi da dan almakashin da ke hannun su.

Aka warware bandejin tsaf. Sai ga kyawawan idanun Hauwa tsaf da su garai-garai dasu kamar a wanke babu hakiya, aiki yayi kyau kenan. Amma me?

    Dr. Sarham ya tambayi Hauwa su nawa ne a tsaye a gaban ta? Hauwa ta shafa idanun ta ta kyafta su, ta sake kyaftawa kafin ta girgiza kai tace,

     LIKITA AI BANA GANIN KOMAI A GABANA SAI DUHU!


In kin ji faduwar gaba da tashin hankali a wurin su su duka dake wurin abin baa cewa komai. Amma shi Dr. Sarham ba faduwa kawai gaban sa ya yi ba, yankowa yayi daga zuciyar sa ya tsinko daga kirjin sa ya fado kasa yana majaujawa a dandaryar kasa..

Ko dama ya dade cikin wannan zullumin tun ranar da ya yi wa Hauwa aikin. Jikin say a gama bashi bai yi nasara ba. Ya tabbata yayi kuskure a cikin aikin domin a lokacin da yake mata aikin ya samu kansa cikin wani bakon yanayi na rashin yarda da kai, wanda zai iya cewa ya gusar da consciousness din sa (hayyacin sa) na dan wani lokaci. 

    Yanayi ne da bai taba samun sa ba a yayin ‘surgery’, ya sha yin aikin da yafi wannan hatsari na glaucoma amma bai taba sarewa ba sai a kan wannan, yafi danganta abinda ya same shi a lokacin da fargaba da tsoron rashin yin nasara sakamakon abinda ya tsinkaya ana cewa a kan sa, wanda ya jefa shi a halin rashin yarda da kwarewar sa akan karan kansa, amma ba don bai iya ba din, dadin dadawa bai taba yin aikin hakiya ba sai wannan karon akan idon Hauwa, ya kuma ga yadda hakiyar tayi zurfi sosai taci idanun ta lalata maganan ta, wannan ya jefa shi a fargaba mai yawa ta aikin bazai yi nasara ba wadda bai kamata ta zo masa a lokacin ba a matsayin sa na likita.

    Tunda ya koma gida kuma da wannan tunanin ya kasa dawowa asibiti, don ya tabbatar bai yi aikin yadda ya kamata ba, ko yace yayi kuskure a aikin da ya yiwa Hauwa, ko yace kamar hakiyar da ragowa a ciki bai cireta duka ba, a sakamakon gushewar hayyaci da ya samu na dan wani lokaci (at the said moment).


A karshe ya tabbata garesu dai bakidayan su babu ko tantama Hauwa ta makance a dalilin aikin da Dr. Sarham Abbas Shanono yayi mata ba daidai ba, iyakar maganar kenan. Gulmar su ta tabbata aka bai iya di ba. Ga idanun nan tarr a bude, amma Hauwa bata iya ganin ko dan yatsan ta balle inuwar mutum ko hasken rana da take iya gani kafin ayi aikin.  

 ****                 ****                  *****

               

                 GULMA AJALI

A

 wannan yammacin a Nurses station na sashen ido a asibitin Murtala baa komai sai gulamammaki masu lasisi, na abinda ya faru a kan aikin da sabon likitan ya yiwa maras lafiyar tasa. Su Nos Saratu da Metron Maria an samu abinda ake so, aka maida abin topic of discussion na wannan ranar. 

    Ko aikin su na ranar sun kasa yi yau, tsabar saboda yadda gulmar Sarham ke cin su.      

  Metron Maria wadda ita ta halarci aikin warware idanun Hauwa tare da likitan, ta ce hey! In baku labari dai, kunnen ku nawa? 

    Suka hada baki (in chorused) wajen cewa kunnen mu biyu, to ku kara biyu ku sha labari. 

    Dr. Sarham dai ya karasa makantar da yarinyar nan mai hakiya da yake mana balbali akan su, aikin da yayi mata was not successful at all.

     Kuma ya kama bakin sa salin-alin bai ce komai akai ba ya bar asibiti, ba tareda kowa ya san taasar da yayi ba, ya ja bakinsa ya tsuke ko sum utu ko suyi rai oho musu.

Nos Gambo tace ki bari don Allah?

    Saratu ta yi rantsuwa ta labarta musu abinda ya faru, ta ce yo dama idon ya gama rubewa fa, maganin su kenan suma, da sun lallaba sun tafi da muka kore su da ta ci gaba da morar dan wani abun a idon, aa su ga sarakan naci dambun kuturu, ni dama na san idon kiris yake jira a taba shi, shikuma karambanin sa kenan, an ce musu sawun su a likkafa su koma gida su cigaba da barbada farin kwallin su da suke barbadawa suka ki ji, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho, yanzu da ya maidata totally blind ai sa hakura. 

    Ni ai dama na fada muku tsautsayi ne kadai zai saka ni baiwa wannnan yaron idanuna ya saka musu wuka, har yaushe ya bar sakandire ko ince ya bar shan nono a cinyar uwar sa? Da zan bari ya fede min ido? Ai yafi kama da Romeo (Uban soyayya) fiyeda consultatant.

    Ban da ilmi a Najeriya ya zama sabatta-juyatta, ya zama abinda ya zama wajen tabarbarewa, ban taba ganin inda dan kasa da shekaru talatin ya zama surgeon ba” wata bakuwa a cikin su mai hankali ta ce,

    ku kuwa ku daina abinda kuke yi bai kamata ba, shi aikin fida ai haka ya gada, ko ayi nasara, ko akasin ta, kafin ayi aikin mara lafiya ya san da haka saboda haka nema ake saka hannu bisa yarjejeniyar amincewar iyaye da makusan ta, so ko mutuwa ta yi bashi da alhakin hakan. Yayi iya kokarin sa Allah ne bai yi ba.

    Idan fitsari banza ne kaza ta yi mana? Kuna ta zagin sa da kushe shi alhalin bai ci muku ba bai sha muku ba, ku ku je kuyi karatun fidar idon mana? Shin wai kyawun Dr. Sarham da gayunsa ne ya koma masa abin hassada a bakunan ku ko me?.

Da wannan ta kashe bakin su murus, bayan sun musa da cewa ina abin yake da zasuyiwa hassada abu tsololo kamar karan raken takanda. Wata kuma mara kunya a cikinsu ta kada baki tace ai irinsa sun fi dadin shaani a gado, baa dakin tiyatar ido ba. suka kwashe da dariya. Har suka tashi aikin ranar basu bar wadannan zantukan ba na shegantaka har daya na cewa ya kamata a kwace licence din sa na aikin likitanci tunda daga zuwa ya fara da makantar da yayan mutane, saboda rashin iya aiki. (Ni kuma nace gulma-ajali mai yin ki kadai zaki kashe).

    *****      *****              *****


      DESTINY TORMENTS.”


(DA KARFE SHIDDA NA YAMMA A GIDAN PROF. ABBAS SHANONO) 


M

awakin ya sake cewa Destiny torments my heart… cikin baitin wata waka ne da Dr. Sarham yake saurare daga kwancen da yake a yammacin ranar, bayan komawarsa gida daga kwace idon Hauwa.

    Yana kwance har kusan magriba a rigingine a tsakiyar matsakaicin gadon dakin sa. Sai ya ji shahararren mawakin zamanin wato R-Kelly kamar dashi yake. Don zuciyar sa duk ta takura. Ya shiga kunci na babu gaira babu dalili. Ya yarda abinda ya faru dashi a kan aikin da ya yiwa Hauwa Bilyaminu kaddara ne, wadda ta rigayi fata, ba don haka ba ai yaji ‘warning alarm’ a cikin kansa, mai cewa ya bari kada yayi aikin nan babu nasara a cikin sa sam, don haka tunanin sa yafi karkata ga cewa sakacin sa ne ko gangancinsa. 

    Amma kuma da aikin kaddara ai, altogether.

     Allah ya riga ya rubuta Hauwa Bilyaminu zata makance a hannun sa. But this written destiny really touched and tormented his heart.

Ace ka zama sanadin nakasar idanun wani dan adam kwata-kwata, duk da cewa dai aikin likita irin wannan (a mutu ko a rayu) ne, sannan ba zaa tuhume shi ba, tunda ya tafiyar da komai a kan kaidar aikin sa ne, amma IDO fa ake zance, wannan kwayar tsokar guda biyu mafi amfani da muhimmanci ga halittar dan adam, sannaan in har kana da zuciyar yan adamtaka a cikin kirjin ka da humanity a tare da kai, dole zuciyar ka ta tabu, da ganin yadda fuskar Innar Hauwa ta shiga tashin hankali a lokacin da Hauwa tace,

     bata ganin komai a gabanta sai duhu.

     Wanda tayi ta kokarin danne tashin hankalin data shiga din saboda shi. To shi tashi zuciyar ba tabuwa kawai ta yi ba da tausayin su da disappointment akan aikinsa, ta kekkece ne, sannan ta tsatstsage ta yayyage ta yagalgale (into pieces at the same time). Ta yadda a gaban Innar Hauwa duk dauriyar da yake yi sa sai da idonsa ya kada, kwalla ta cika idonnasa, a fakaice ya yi kokari maida kwallar, ta hanyar juya musu baya ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihu yana maida kwallar sa, bai san Innar ta gane halin da yake ciki ba.

     Hakan ya faru ne lokacin da ya ji Hauwa tana cewa.


Shike nan yanzu Inna sunana Makauniya? Ba zan sake ganin fuskar ki data Baban mu ranar da ya dawo gare mu ba? Kema na daina ganin ki kenan daga yanzu?”  

Yana iya tuno kalaman Innar Hauwa gare shi, da ta ga yasa hankici yana tsane kwallar da yake ta hadidiyewa cikin idanun sa a wayance, yanzu kam tafi karfin sa, ta baiwa kanta yanci ta digo, a lokacin yana rubutu cikin fayil din Hauwa sai hawaye ya diga a kai, wannan ya faru a kan idon Innar Hauwa.

    Sai Innar Hauwa ta bagarar da tasirin maganganun Hauwa suka yi mata a ranta, ta maida kulawarta a kan shi inda ta dube shi cikin lallashi tace Haba likita? Kaida zaka bata karfin guiwa? Shi Dan adam ai baya tsallake kaddarar sa. Ita Hauwa-Kulu kaddarar ta kenan.

     Abin yi a yanzu gaba dayanmu shine mu yi mata fatan Allah yasa makanta ta zamo kaffara a gare ta. Idan makantar nan jarrabawarta ce ta dan wani lokaci Allah ya yaye mata ya bata ikon cinye wannan babbar jarrabawa, idan kuma ta har abada ce Allah yasa ta zamo silar shigarta aljannah. Nakasa ai ibadah ce ga wasu kebabbub bayin Allah!.


Amma duk da tawakkali irin wannan wanda Innar Hauwa ta nuna, Dr. Sarham ji yake yana blaming kan sa, kamar rashin kwarewar sa ce ta saka Hauwa a wannan halin na rasa abinda yafi komai dadi ga rayuwar mutum, wato idanun ta. 

    Zai fi yarda idan aka ce sakacin sa ne, laifin sa ne, rashin kwarewar sa ko iyawarsa ce. To ko dai gaskiyar mutane ne da suke cewa yayi kankanta da zama mai ceton rayuwar idanun alummah? 

    Yaushe tasirin maganganun jahilan matan nan magulmata zai bar ransa ya sake ne? meyasa ma kunnen sa sarkin ji, ya zuko masa abinda ba alkhairi bane a gareshi kuma wanda zai dame shi?

Don haka koda ya baro su a asibitin ya dawo gidan su a ranar, wato gidan mahaifin sa, da matsanancin duhun zuciya ya shigo, mahaifiyarsa kanta ta fahimci cikin matsananciyar damuwa Lelen Abba yake. Tun daga bakin kofa kanwar sa Sumayya ta soma tarar sa da zance yadda suka saba saboda shim aba laifi akwai hira musamman da kannen sa, Sumayya tana gaya masa ta yi (passing exams) din ta, kawai ya zo ya bata kyautar da yayi mata alkawari bata son a bata lokaci har kyautar tabi ruwa tunda shi yayi alkawari. Amma ga mamakin Sumayya yau Lelen na Abba ko kulata bai yi ba, yayi fuska kamar ba shi ba, don ko kallon ta bai tsaya ya yi ba, balle ya bata lokaci wajen taya ta murna yadda ya saba in taci na daya a kowanne zangon karatu, balle har ya ce su fita kingsway ta zabi ‘gift’ din da ya yi mata alkawarin.

     Kawai sai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa abinsa, yana cewa a ransa baki da matsala, ko sannu da gida yau bai iya ya yi mata ba itada sauran jamaar gidan bakidaya.

Sumayyah bata daddara ba, ta sake kwasar faranti data shake da abinci ta biyo shi da abincin rana har dakin sa. Da yake ta gan shi cikin damuwa sai tayi tunanin yi masa abincin da ta san ya fi so, wanda dole zai kula yayi godiya, wato tuwon alkama miyar kubewa busassa. Miyar ta ji busashshen kifin banda da cryfish, ga lafiyayyen farfesun kayan ciki ta hado masa da shi da yaji kayan kamshi da attarugu, komai zai ci sai ansa tarugu da tafarnuwa, sune abinda ke sawa yaci abinci sosai ta sani, duk ta jera a kan tray ta biyo shi da shi har daki. 

    Sai ta samu kofar tasa ma a kulle da mukulli, wato ya kulle kan sa, don baya son kowa ya dame shi. Musamman ita Sumayya sarkin naci da zuba zance, ya san saita biyo shi, saboda da shi kadai take shiri ta kuma fi sabawa cikin gidan, bata iya zama idan ba kusa da shi ba. 

    Wannan kulle kan sa da yayi a daki tun dawowar sa gida da hantsi har bayan laasar ya dami mahaifiyar sa Barr. Mai shariah Haj. Maimuna (Mama inji yaranta). Har bayan laasar suna zuba idon ganin fitowar sa shiru suke ji, ta tambayi Sumayyah ko ya ci abincin ranar data kai masa? Nan take gaya mata cikin tata damuwar, 

    ai Mama ko bude dakin bai yi ya dauka ba, dazu na kara dubawa na ga abincin yana nan a bakin kofa inda na ajiye masa”.

A lokacin Yayar Sumayyah mai bin Dr. Sarham a haihuwa wato Aunty Surayyah ta dawo gidan, daga gidan Kakar su Hajiya Kulu. Ba jimawa mahaifin su ma ya dawo daga cikin makaranta inda yake koyarwa wato Prof. Abbas Shanono, nan gidan ya idasa cika ya zama full-house yadda yake a kowanne yammaci in sun dawo daga sabgogin su.

     Prof. Abbas ya tadda su jigum  jigum a falo wato dai damuwar Lelen Abba (Sarhamu) ta taba kowa. Don an yi bugun duniya bai bude ba, da Sumayyah ta dame shi da nacin rokon ya bude kofa ya dau abinci, a fusace yace mata in bata bar masa bakin kofar dakinsa ba zai fito ya yi kasa-kasa da ita a wurinnan.

Yau ban ga Sarham a masallaci ba ko bai dawo bane? In ji Abba Prof. ya fada yana nazarin yayan nasa mata guda biyu da mahaifiyar su wadanda duk suke cikin damuwar abinda ke faruwa da babban Yaya. 

    A kaidar Abba Prof. idan ya dawo gida daga cikin Jamia kullum, kasancewar suna zaune ne a cikin rukunin gidajen manyan malamai na sabuwar Jamiar Bayero, kafin ya shiga gida masallaci yake fara zarcewa wanda ke kofar gidan sa, mafi yawancin lokuta a can zai tadda Sarham ya riga shi isa, sabida baya wasa da bin jamI, kuma sautari ya kan riga shi dawowa, zasu hadu a can, su bi jami tare, ba zasu shigo gida ba sai bayan laasar.

     Amma sabanin kullum yau har aka idar da sallah bai ga Sarham ba. Wannan abu ya dugunzuma shi, don ya jima rabon da yaga ranar da yana gida bai je masallaci haka kawai ba. Mama ta gaya masa yau sun rasa gane kan sa, ya shigo cikin damuwa daga wajen aiki, ya kulle kan sa tun dazu, har ya kusa dukan Sumayya da ta dame shi sai ya bude ya dauki abinci.

Bata kai ga rufe bakin ta ba sai ga Dr. Sarham ya fito daga dakin sa da saurin sa da hanzari, da mukullin motar sa a hannun sa, tun kayan dazun ne a jikin sa bai canza su ba, (which was unlike him) ya wuni da kayan da ya je asibiti dasu, idanun sa duk sun tasa kamar na wanda ya yi kuka ko ya kwana ido biyu da nannauyan barci. 

    Ya gaida Daddy da Mama cikin sauri zai wuce, sannan kafin a yi masa kowacce tambaya Sarham ya kama hanyar fita, sai da ya kai bakin kofa sannan yace musu zai koma asibiti ya dawo yayi mantuwa ne ba jimawa zai yi ba. Ya kara da cewa kada su damu ba wani abu ne ya same shi ba, lafiyar sa kalau. Ya dubi Sumayyah yace ki je ki dauke farantin da kika tokaremin kofa da shi. Daga haka ya fice. Duk suka bishi da ido har ya fice daga main falon, sun kasa dakatar da shi.

Yana tafe cikin yar karamar motar sa Honda Prelude ta yayin samari yan gata mai kofa daya, wadda Abba Prof. yayi masa kyautar ta, bayan kammala karatun sa da dawowar sa gida daga kasa mai tsarki matsayin cikakken likitan ido (at a very young age), yana tafe yana tunanin makasudin sake fitowar sa daga gida yanzu menene?

     Tunani kawai ya yi bai kamata ya bar Hauwa da Innar ta su tafi gida ba su ko yi sallama ba, don haka ya baro su a asibitin dazu (absent-minded) ya tafi gida don ya samu nutsuwar ran sa, bayan sallamar da asibiti yayi musu a yau (wato discharge). Son samu ma ya tambayi inda suke, don watan watarana. 

    A fahimtar sa dai, idanun Hauwa ya gama tafiya kuma ta sanadin sa. Wannan tunanin kadai yana matukar daga hankalin Dr. Sarham kamar ba likita ba, yana kuma azabtar da zuciyar sa, kasancewar bai taba aikin da bai yi nasara ba sai wannnan karon kan na Hauwa, shi ko kiyashi baya so ya ji rauni a hannun sa, watakila don wannan ne karo na farko da yayi aikin cataract ya kuma fara da rashin nasara.

     Har ya iso asibitin Murtala yana share zufa daga kan goshin sa da farin hankacin sa, da zara-zaran yatsunsa. 

    Ya karya kan motar zai shiga asibitin kenan sai ya hango Innar Hauwa dauke da dan kunshin kayansu a kan ta, ta kamo hannun Hauwa suna fitowa daga cikin asibitin.

     Don haka da hanzari Sarham ya juya kan motar sa zuwa inda ya hange su, yayi gaba da su kadan ya tsaya, sannan ya fito daga motar ya nufe su.

     Inna har kun fito ne? Sarham ya fada da karyayyar muryar data idasa karyewa a wannan lokacin, idanun sa fal kulawa da damuwa, bayan ya fito daga motar sa, ya maida kofar ya rufe ya tako a hankali zuwa inda suke a bakin titi suna jiran motar haya. 

    Da fara Inna ta amsa Mun fito likita, zamu taka zuwa gida, gashi har ka je gida ka dawo bamu tafi ba muna kailula don tun dazun anka sallame mu.

     Kulu ce ta ce in bari ta kara jin karfin jikin ta bazata iya doguwar tafiya a dazun ba. 

    Idanun Sarham fal damuwa, ya daga ido ya dubi Hauwan, ga idanu tar a bude, manya dasu, masu haske kamar an wanke su an kuma kara musu lafiya, unfortunately sun koma gululu, kuma ta sanadin aikin hannun sa, sai jujjuyawa kawai suke a kan titi. 

    Shin ta yaya zai yi ya daina damuwa a kan aikin nan da yayi ba nasara? Naturally shi mutum ne mai phobia na gudun zuciyar mutanen da yasan ya batawa, yawan tausayi ga marassa lafiya da masu karamin karfi, balle ga mata da kuma kananan yara. Shiyasa kannen sa mata biyu ke tsananin jin dadin sa da kaunar sa, saboda kulawar sa garesu. 

    Sai ya saka hannu ya karbi kullin kayan su da ke kan Innar Hauwa, ya ce ku yi min alfarma Inna in raka ku zuwa gida, ko don in ga wuri. Ni dan ki ne, wace unguwa kuke?

     Inna ta ce cikin mamaki anya dan nan ma saka ka wahala haka? Can muke da dan nisa, a can bayan Badalar kofar Naisa. Tuni kafin ta gama fada Sarham ya isa ga motarsa ya saka kayan nasu a bayan motar, ya budewa Inna da Hauwa kofar gidan baya.

Babu komai Inna, don Allah ku shigo in kai ku. Inna bata da zabi ban da kama hannun Hauwa ta shigar da ita bayan motar, don ta kasa tankwabe tasirin da kirkin sa da kamalar sa da jin kan sa yayi a ranta.

Dr. Sarham ya shigo ya tada motar ya juya ta suka fita daga asibitin Murtala gabadaya. Ba jimawa suka hau titin da zai sada su da Kofar Naisa. Suna tafe a hanya Inna na nuna masa inda zai bi da su, lokacin da suka shiga cikin Ganuwa.

     Hauwa dai bata cewa ko uffan, abinda ya dameta ya dameta, tana dai jin su jefe-jefi suna hira shi da Inna a kan ta. A surutu irinna Inna har tana gaya masa wai Hauwa yar makaranta ce, tana aji biyu na sakandire a GGSS Shekara, ta yi jarrabawar shiga aji na uku yanzu, suna zaman jiran fitowar ta (jarrabawar) Hauwa ta fara apolo. 

Can kuma ta nisa tace, umh! Yanzu kuwa Hauwa-Kulu ai sai zaman gida ko? Tunda dai idanu sun tafi?.

Ta yi maganar cikin wata irin murya kamar mai neman amsa daga gare shi, a lokacin da bawa ya rasa abinda ya kamata yayi akan wata babbar masala data tunkaro shi ba shiri. Dr. Sarham yayi shiru, yana cigaba da tukin mota, bai ce komai ba don duk wani blame na makancewar Hauwa ya rasa me yasa ya daukeshi bakidaya ya dora shi a kan sa, bayan kuma ba haka aikin likita ya gada ba. 

    A kaidar aikin sa bashi da laifi. Amma a humanity da dattaku irin nasa ji yake shine sila, shine cause kuma shine at fault.

Daidai lokacin suka iso lokon gidan su Hauwa. Daga inda mota bazata iya shiga ba, Inna ta nuna masa inda zai iya aje motar ta ce sun gode zasu karasa da kan su a kafa daga nan, don gidan na su can cikin loko ne mota bata kaiwa.

“Inna ai har gida zan kai ku, bani kayan in rike miki, zan so ganin gidan naku don watarana in dinga gaishe ki, ina ganin lafiyar idon kanwata. Inna ta ce to likita muna godiya kwarai, kamar ka san bata da dan uwa. Allah ya yi albarka ya baka masu yi maka kai ma.

Daga haka Inna ta wuce gaba Dr. Sarham ya bi bayan ta zuwa cikin lokon su tana rike da Hannun Hauwau yana dauke da kunshin kayan su.

Sarham yayi ta mamakin sanayyar jamaar unguwar da Innar Hauwa yadda duk inda suka bulla jamaar unguwar ke gaida Innar Hauwa cikin girmamawa suna kuma tambayar ta yaya Hauwa da ido?

     Inna sai ta ce sauki na wajen Allah tunda yanzu Hauwa ido babu! Kamar yaya ido babu? Anan kam saidai tayi murmushi ta sa kai ta wuce su tana mai cewa “da sauki dai”. Ta kasa bayani don kada ta karasa Sarham a blame. Sosai kowa ya kasa ganewa haka dai ake ta jajantawa ana wucewa har suka shiga gidan su.

Dabbobin Inna duk sun bata gidan da kashin su da fitsarin su yayi daka-daka, kasancewar ta kwana biyu bata nan ba wanda ke sharewa, duk sun cakalkala gidan, ga ganyayyaki sun zubo a kaina irin busassun ganyen bishiyoyin su na darbejiya da umbrella duk gidan ya yi kaca-kaca.

Inna ta shiga dakin ta ta dauko ma Sarham kujera yar tsugunno tana cewa cikin takaicin yadda ya tadda gidan nasu daka-daka,

     kayi hakuri Likita, gidan namu yayi datti, tumaki sun bata shi kwana biyu da bama nan, sun yi abunda suka ga dama a tsakar gidan nan. Ka ga nan shine gidan namu, ana cewa gidan gidan Malam Bilyaminu Kofar Naisa”, ko da nan gaba ka zo ka bata ko ka kasa ganewa, haka zaka ce, ko gidan su Hauwa-Kulu.

Sarham yayi murmushi yana jinjina surutu irin na Inna, duk surutun sa ya samu Inna ta fi shi iyawa, don haka da alama tasu zata zo daya kamar Kakar sa Haj. Kulu yake jin maganganun nata, ya zauna a kujerar da Inna ta aje masa yana walainiya da kayatattun idanun sa a gidan, sosai yake shaawar rayuwa irin ta cikin Badala irin wannan, don suma da can a bayan Badalar suke ta kofar Gadon kaya, amma tun sanda aka bude sabuwar Jamiar Bayero aka maida mahaifin sa gidajen malamai na ‘New Site’, kasancewar a lokacin yana daya daga daidakun tsafaffin malamai masu matsayin Farfesa a tsangayar magani (medicine).

    A can baya kafin a gina ‘New Site’ din iyayensa suna zauna ne a unguwar Kofar Gadon Kaya.

Suka sake sosai a tsakar gida suna cafkar hira shi da Inna, (they are all talkatives) kamar wasu yara. Hauwa na daga can cikin dakinta a kwance, kan siririyar katifar audugar ta, tana jin su da rabin hankalin ta, amma rabi baya tare da su sam. Ita kadai ta san me take (going through) wato me take fama da shi a zuciyar ta, wadda ke cike taf da rauni da karaya da rayuwa, idan ta shafa idanun ta taga duhu didim! Idan ta kyafta su taga babu komai a gabanta sai duhu! Shin wai shikenan haka zata dauwama har abada cikin duhun idanuwa bazata kara ganin fuskar kowa da komai ba, har kuwa fuskar Innar ta? 

    Har kuma tata fuskar a mudubi idan ta kalla bazata gani ba? Ko kuwa rashin ganin nata na dan lokaci ne watarana zai dawo? Ko kuwa tafiyar idon kenan? Duka wadannan tambayoyin da take yiwa kanta bata da amsar ko daya. Allah shine masani, amma hakika tana cikin matsanancin tashin hankali da dimuwa da wannan jarrabawa, wanda sai wanda ya taba rasa wata gaba ko wani sashe na jikin sa ne kawai zai iya relating.

     Imanin ta yau ya karu akan mutane masu nakasar ido (visual impairment) da ta dade tana ganin su a hanya ko suna bara. Yau ta yarda makanta ba abu ne mai sauki ba. Tana jin yadda hira tayi dadi tsakanin Sarham da Inna, kamar su kam ba abinda ya dame su da abinda ya same ta. 

    Sai labarin halin baban ta wato Malam Bilyaminu da Yayan ta Zulkifl Inna take bashi a sanda suke tare dasu, da irin rashin jin Zulkifilu a sanda yake yarintarsa, tace kullum sai yayo tsokana ya dauko mata Magana shi haka Allah yayi shi ba kamar Hauwa ba da ko naman jikin ta zaka yanka sai ta ga dama zata daga ido ta dube ka.

     Can ajima sai kaji Inna ta gangaro kanta ita Hauwan, tana gaya masa irin halin ta na kirki da yasa take tausaya mata wannan lalura data sameta yanzu, yadda Hauwa ke taimaka mata da ayyukan gida bata da kiwa (bata da ganda), ga son karatu kamar tsuntsun alhuda-huda. 

    Inna ta ce cikin mutuwar jiki da yanke tsammani, babbar damuwar ta a yanzu da makancewar Hauwa-Kulun ta, ba makantar bane ba kai tsaye, ko kiranta makauniya da mutane zaa ke yi, damuwar tata shine; ta yaya Hauwa zata yi ta cigaba da karatu?

Wannan magana da Inna ta yi, ba Hauwa kadai ta saka a tunani da damuwa ba har da shi kan sa Dr. Sarham.  Kamar wani assignment na lissafi (mathematics) mai wuya yaji Innar Hauwa ta bashi shima. Wanda zai tafi gida dashi domin yayi solving ta hanyar tunani. Don haka koda suka yi sallama da Inna jikin sa duk a sanyaye yake shima, ya fito lokon ya shiga motar sa ya tayar, amma sai ya kasa tafiya, sai ya kifa kansa a kan sityarin motar na tsayin lokaci yana tunanin ta inda zai iya taimaka musu da rage musu.

    Ya shiga cikin tunanin ta wace hanya zai bi ya taimaki rayuwar wadannan bayin Allah da yarinyar su tilo, ta nakasa a hannun sa? Yo a hannun sa mana! Da yayi aikin nan da kula yadda ya dace da Hauwa bata makance ba (a tunanin sa). 

    Iyaka tunanin sa bai ga da me zai iya taimaka musu ba banda a kan shaanin karatun Hauwa din, don haka ya yanke shawarar baiwa Abban sa labarin su, da neman shawarar sa da karin haske akan ilmin da bai sani ba wato special education. Kasancewar Abban sa mutum mai hangen nesa da yalwar ilmi a bangare daban-daban fiye da shi, ya san a nan ma bazai rasa sani ba.

Shi da Abban sa (are more than father and Son, they are very close and best friends) na junan su tun yana karami. Haka kanwar sa Sumayyah ita ce babbar abokiyar sa a rayuwa, Sumayyah is nice and easy going sannan (talkative like her Bhaiya) yadda take kiran sa kenan, shiyasa tasu ta zo matukar daya, su yi hira suyi dariya kasancewar sa very jovial likita abokin kowa, ba kamar sakuwarsa ba wato Surayyah, wadda ta dauki rayuwar sababbin yan jamia (JJC) mai tsauri ta sanyawa kanta.

     Duk da kasancewar Sumayyah mai karancin shekaru to fa ya shaida ta fi Surayya hankali da hangen nesa, kai dai bar Surayya wajen iya ado, da iya daukar wanka da kuma son kyale-kyalen da zaa ce tafi kowa cikin tsararrakin ta aji.  Halayen da ke hadata fada da Bhaiya din kenan a matsayin ta na sakuwarsa a haihuwa, kusan kullum sai an ji kansu, don shi ta rage wuni a gidan su sai gidan Hajiya Kulu kakar su.

      Dr. Sarham, in ka cire abokan karatun sa da har gobe in an hadu akan gaisa, bashi da wani shaqiqin aboki da zaa kira aminin sa, duk da surutun sa da sakin fuskar sa to fa ya san a inda yake yin su, baida abokai sam saboda training din da mahaifin sa yayi masa kenan na ya zamo shine babban abokin sa (Abban), saboda gudun kada abokai su bata masa shi. Abba Prof. akwai saka ido akan tarbiyyar yaransa kamar baida wani aiki a duniya sai kula da su, sai ko abokanan aikinsa a Murtala, wadanda yanayin aiki kan hada su akan dole. 

    Maman sa kan ce he is very anti-social, yet a parrot”, bashi da saurin yarda da sakin jiki da kowa, sai ko autar su Sumayyah, ko ita kan ta Maman ba komai yake iya gaya mata ba, da ya shafi sirrikan shi, amma tsaf zai iya gayawa kanwar sa Sumayyah komai su kashe su rufe ba tare da iyayensu sun sani ba.

Babu shakuwa mai yawa tsakanin Barr. Maimuna da daukacin yaranta, wannan ya faru kasancewar gabadaya rayuwarta ta sadaukar da ita ga aikin ta na Lauya da zurfafa karatu, don haka su Sarham sun taso kusan a gaban Kakar su ne Hajiya Kulu. Sun fi shakuwa da Hajiyar Gadon Kaya fiye da Maman su, wadda a can baya a gidan su take zaune.

     Lokacin da aka maido Prof. cikin gidajen malamai na sabuwar jamiar Bayero sai Hajiyar Gadon Kaya tace ba zata biyo su ba, domin bazata iya zaman wajen gari ba, a cewar ta a cikin Badala aka haifeta don haka a kwaryar badala take so ta mutu a binneta, don haka Prof. ya samar mata mai aiki mai suna Gambo, ta zame mata abokiyar zama suke zaune tare a gidan sa na Gadon Kaya wanda mallakin sa ne da ya gina da gumin sa. Lokaci-lokaci yana sabunta shi zuwa ginin zamani irin na wancan lokacin daidai da yawan iyalin sa. 

    Har yanzu Hajiyar gadon kaya na can amma ta tsufa ainun, sun yi sun yi ta dawo ta zauna tare da su ta ki, don haka kusan koyaushe kafar su bata rabo da gidan Hajiya musamman Surayyah, saboda yadda Hajiya ta shagwaba ta, kuma tafi jan ta a jiki duk cikin su.

    Wannan ya samo asali ne daga sanda aka haife ta bada jimawa ba Mama tayi wani dogon rashin lafiya mai tsanani na lokaci mai tsaho wanda yasa dole aka dauke Surayyah a nono ba tare da ta isa yaye ba, Hajiya ce ta cigaba da rainon ta a dakin ta da madarar yara har ta yaye ta, sai ta cigaba da zama a wurin ta har bayan da Maman ta samu sauki, aka zo aka haifi auta Sumayyah, amma Hajiya ta rike Surayyah, bata kara bari ta dawo wajen Maman su ba, saidai ta zo da yawo har girma. 

    Ita kuma Sumayya dalilin shakuwar su itada Sarham ya samo asali da cewa kusan Sarham shi yayi rainon ta, domin akwai rata ta kusan shekaru goma sha biyu a tsakanin su. 

    In Mama na wajen aiki shi yake kula da Sumayya su tafi makarantar islamiyyar sa tare, har zuwa sanda itama ta isa shiga makaranta, malamai na hanawa azo da kananan yara amma Sarham ba ya jin Magana, gobe sai ya dawo tare da kanwar sa, in har ba za’a bar shi ya shiga aji da Sumayyah ba tofa zai koma bayan tagar ajin su ne shi da ita su make su yi ta leke, korar duniya malamai zasu yi masa ba zai tafi ba, har suka gaji suka kyale shi yake zuwa aji tare da ita, don Mama bata da lokacin kula da ita. 

    Inda Mama ta zama akasin Prof. Kenan, shi kam yanada lokacin yaran sa no matter what, yana jan yaran uku a jiki, daga yamma zuwa lokacin barci idan ya dawo daga cikin makaranta suma suka dawo makarantar islamiyya zai kasance tare da su.

     Ita Mama zaka samu ko ta dawo aiki zata ce ta dawo da muhimmin (case) a hannunta zata yi nazari, tace su zauna a falo kada su dame ta. A haka Sarham da kannen sa biyu mata suka rayu tsakanin yan bokon iyayen su. Sai ya zama cewa a girman su ma Surayya ta fi shakuwa da Kakar su, itada Sarham basa ga maciji, sai fadan sako da sakuwa, yayin da Sumayyah kuma tafi shakuwa da shiri da shi fiyeda Mama.


    Ya iso gida wajen karfe tara na dare. Jamaar gidan su dama ga aladar su karfe tara na dare na yi sun baje daga falo kowa ya nufi makwancin sa. Amma Abba na nan bai tashi ba, yana nan zaune a kujerar da yake zama a falon yana jiran ganin dawowar sa, yana sauraron labaran kasa da ake yi a gidan talbijin na NTA yana kuma duba tangamemen agogon dake like a bango.

Sarham yayi sallama a babban falon mahaifin sa, inda Abba Prof. ya amsa masa, ya shigo ya zauna daga kasan kafafun Abban, ya ce Abba sannu da gida Abba yace yawwa, kai kuma sannu da yawon dare, daga ina kake haka? Ka bar yan kannen ka cikin damuwa, ka birkice musu wuni guda, me ke faruwa da kai yau?

    Sarham ya yi ajiyar zuciya ya ce Abba ina kofar Naisa, wata marainiyar yarinya na yi wa aikin ido, Abba cikin rashin saa zan ce ko kaddara ko tsautsayi ko gangancina ne ban sani ba, ta makance gabadaya, maimakon a samu lafiyar da ake nema.

     Muryar Sarham kamar zai fashe da kuka don damuwa, zaka iya karantar tsantsar karaya da sarewar da yake ciki a cikin sautin nasa.

    Prof. Abbas Shanono, ya dubi babban dan nasa Sarham cikin kulawa, yace haba Muhammad Sarhamu! Be a man mana! Sai kace ba likita ba? Da haka zaka cigaba da aikin likita kana karaya akan rashin nasarar aiki irin haka? Ai dama aikin likita ba a hannun ku yake ba, a hannun Allah yake, sai abinda ya hukunta ga marar lafiya. 

    Never blame yourself a kan duk wani unsuccessful surgery. Ka sa a ranka ka yi iya yin ka, sauran, wato samun lafiya ko akasin ta, yana hannun Ubangijin halitta.

Maganar mahaifin nasa ta dan kwantar masa da hankali, at least shi bai ce masa bai iya ba, bai ce don shekarunsa ba masu yawa bane, bai kuma ce laifin sa bane this is soothing, a hankali Sarham ya ce.

     Abba kuma shikenan idan yaro ya makance wato ya samu nakasar ido ba zai yi karatu ba sai ‘bara?’ 

    Abba Prof. yace in ji wa? Ai akwai cigaba yanzu sosai akan ilmin masu nakasar ido, akwai makarantu na musamman da gwamnati ta bude domin koyar da su kyauta (public special schools) can ya kamata iyayen ta su kai ta, har anan Kano akwai special school dominyara mau nakasa daban-daban. 

    Sai Sarham ya ji tamkar Abban sa ya bashi amsar ‘assignment’ din da ya baiwa kansa, ko yace Inna ta bashi, na yaya zai yi Hauwa tayi karatu, sannan kuma Abba ya bashi mafita akan damuwar sa kan matsalar Hauwa, at least zai iya taimaka musu da wannan wato ya tsaya a kan karatun ta, nan take ya yi wani kuduri mai girma ga zuciyar sa shi kadai; na daukan nauyi da takalihun alhakin ilmin Hauwa Blyaminu na sakandire har sai ta kammala in har yana raye, in dai da gaske makafi suna iya yin karatu da rubutu su samu ilmi kamar kowa, da yardar Allah zai tsayawa Hauwa, tunda shi ya samu yayi har gashi ya tsaya da kafafun sa yana kuma da albashin sa, to zai tsaya ya ga cewa Hauwa bata tagayyara a fannin ilmin sakandire sanadin makantarta ba.

     Wannan wani alkawari ne da Dr. Sarham ya yi wa kan sa a zuciyar sa, da yake fatan Allah ya bashi iko da tsawon ran cika shi.

Sai washegari wajen karin kumallon su akan dining suka hadu da Maman sa da sauran kannen sa biyu wato Sumayyah da Surayyah. Bayan ya gaida iyayen nasu shikuma kannen sun gaishe shi yadda suka saba ya ja kujerar sa ta dindindin a dining din ya zauna. Mama ta tambaye shi me ya faru da shi ne jiya? 

    Nan yake gaya mata labarin aikin da yayiwa Hauwa da yadda yake blaming kansa kamar yadda ya gayawa Abban sa. 

    Barr Mama. itama kamar Abban nasa cewa ta yi ba laifin sa bane. Ta kuma kara da cewa kada ya kara sakawa kansa damuwa irin wannan kan aikin sa in har yana son cimma nasara a gaba, don hakan zai iya sawa ya tsani ‘profession’ din nasa da ya tashi da burin sa. Surayya ta gatsine baki ta ce, 

    dadi na da mutum daurawa kai damuwar wasu, damuwar da Allah bai dora masa ba, to sai me zai faru don aiki bai yi nasara ba da zaka bi ka wuni cikin damuwa har da kulle kofa da yiwa kai horon yunwa ta hanyar kin cin abinci wuni guda haka Yaya Doctor, ina dalili ina dan mafari? 

    Sarham ya jefe ta da harara, Mama ta ce ke bana son rashin kunya, wa ya saka ki a maganar mu?

    Dagagefen sa inda take zaune Sumayya ta ce cikin jimami.

     Bhaiya, kayi wa Allah ka kai ni in duba ta, haka kawai naji tausayin ta ya kama ni nima, makancewa fa totally, a hannun ka, ai da tausayi da sanya damuwa, dole ka shiga phobia dinka, dama dai a ce a hannun wani liktan ne ba kai ba bazaka damu har haka ba, Allah sarki Bhaiya na!.

    Yace I know you always pity me Summy, and you are with me especially in such a bad situation (nasan koyaushe kina tausayamin Summy, kuma kina tare dani musammman a lokaci mara dadi). Madallah da wannan kanwa tawa. Karamar su-babbarsu!.

Haka suka karya kumallon suka tashi, masu zuwa aiki wato Sarham da iyayen su suka shiga motocin su daban daban suka wuce wajen aikin su, Surayya ta wuce cikin makaranta inda take karatu anan cikin jamiar Bayero, tana aji daya na digiri a tsangayar ilmin lissafi (mathematics).    

Sumayya na aji biyu na babbar Sakandire a makarantar Musa Iliyasu College, dake nan daura da sabuwar jamiar Bayeron, suna fitowa ne kullum tare da Yayan ta Dr. Sarham tun bayan fara aikin sa, sai ya sauke ta sannan zai mika zuwa asibitin Murtala inda bai jima da fara aiki ba, bayan yayi aiki na dan lokaci da asibitin Abdullahi Wase da aka fi sani da asibitin Nasarawa, suka maida shi can don an fi bukatar kwararru a asibitin Murtala fiye da kowanne asibitin gwamnati a Kano. 

    Wannan ya faru ne jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Saudi-Arabia da kadan, inda ya karanci fannin likitancin ido a jamiar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah. 

     ****              ****            ****


    Bayan ya sauke Sumayyah ta daga masa hannu, ya ja motar sa zuwa asibiti. Koda ya zo ward round na wannan ranar sai idanun sa suka hango masa gadon da “Hauwa-Kulu” ta kwanta jinya. Nan da nan ya tuno su, wadanda dama da su ya kwana ya kuma tashi a ran sa. 

    Sai ya ji yana son sake zuwa ya duba su, ya ga lafiyar su itada Innar ta. 

    Haka kawai yake jin Innar Hauwa a ran sa, jinta yake kamar uwa a gare shi, sabida halin kirkin ta da dattaku, da kuma tawakkalin data nuna akan abinda ya samu yar ta a hannun su.

Don haka da ya fito daga asibiti sai ya samu kansa da juya sitiyarin motar sa zuwa unguwar su Inna, da ya isa bayan Badalar kofar Naisa kasa gane gidan yayi, da tambaya ya isa har kofar gidan su Hauwa don ya kasa ganewa da farko, kansa ma juyewa yayi ya rasa direction abode gidan yayi cikin lungu sosai, amma da yake ya rike sunan maigidan da Inna ta gaya masa kamar ta san zai bata din sai baa sha wahalar kai shi har kofar gidan ba. 

    Dr. Sarham yayi sallama a kofar gidan Mal. Bilyaminu, Inna dake duke tana share tsakar gidan ta amsa sannan ta leko, koda dau taso daukar muryar dama mai kaifi kamar an fike ta anyi sharpening fitar ta gently daga makogaron sa, bakin ta ya koma har kunne da ganin Dr. Sarham, ta dau wankan ta tsaf ta sha wankakkiyar atampa, kodayake dama ta dauki muryar sa, Inna ta bashi iznin shigowa ya sa kai ya rage dogon wuyan sa ya shigo da sallama.

     Inna ta amsa cike da faraa ta shiga lale marhabin da shi, sannan ta dauki tabarmar karauninta ta shimfida masa.

     Sarham ya tsuguna har kasa ya sake gaishe da Inna, ya kuma tambayi jikin Hauwa. Inna ta ce cikin damuwa, 

    ai tun bayan tafiyar ka jiya zazzabi ya rufe Kuluwa, ko tashi bata iya yi, sallah ma sai na taimaka mata take iya yi daga zaune, ta dauki damuwar duniya ta dorawa kanta a banza akan abinda Allah ya kaddara mata. Dr. Sarham ya ce,

     ashsha! Kakata jiki bai yi dadi ba ashe, ki barta Inna, dole ne ta damu, amma a hankali damuwar zata bi jikin ta in sha Allah, bari to in koma in samo mata magani. 

    Har ya mike zai saka takalmin sa sai ya dubi Hauwa dake zaune a kan tabarma daga gefe, ta jingina da filo, ga idanuwan tarr a bude kal dasu, amma shi a iya dan ilmin likitancin ido da Allah ya bashi, da abinda ya karanta, ya san wadannan idanun na Hauwa’u in ba wani babban kudurar Allah ba sun tafi kenan, wato sun tashi aiki sai ko wani ikon Allah, wanda ya fi gaban ilminsu su likitocin fidar idon. 

    Ya matsa gaban tabarmar ya russuna yace sannu Kakus, ina yake miki ciwo? Don in san irin maganin da zan karbo? Ko allura kike so?” Hauwa ta bata rai sosai saboda sunan da ya kira ta da shi kamar wata tsohuwa, haka mafa a asibiti yace mata Kululu bata ce masa don me ba, yanzu kuma yace mata kuskus, ta dan fiddo manyan idanun kamar tana ganin sa irin warning look dinnan, ta yi fuska sosai ta ce masa, sunana Hauwau Bilyaminu ba kuskus sunana ba, kuma ni ai bana tsoron allura inda a hannu za’a yimin, ba sai na kwaye zani ba”, Inna ta ce an ce miki Kuskus din, ke da baki san wasa ba. Yayi murmushi ya sake cewa.

     Kakus, idan na ce miki sunan Kakata gare ki, wadda ta haifi mahaifina zaki yarda? I mean you have my Grandmas name, Hajiya Kulu Shanono”. 

    Anan kuma sai tayi shiru, don ta san ba karya yake ba, ba kuma zolaya a maganar sa ta yanzu, ta zuba masa gululun idanunta kawai kamar tana ganin sa, yace to sunan ki daya da Kakata Hajiya Kulu (Hajiyar Gadon kaya), ni kuma Kakus nake kiran ta, idan ban kira ki Kakata ba bazan iya cewa Hauwa ba, don in ta ji na fadi sunan ta haka gatsau, ba sakayawa, sai tayi kuli-kulin kubra da ni. 

    Hauwa bata san sanda ta yi dan murmushi ba, sabida yadda Sarham ya fadi kuli-kulin kuburar ya bata dariya matuka. 

    Ya ce daga yau ni da kaina zan saka miki sunan da ya dace da kyakkyawar diyar Inna kamar ki, kin ga daga Hauwa, har Hauwau, har Kulu, zuwa Kuluwa duk na tsofaffi ne Inna ta lika miki, don haka ki lamunce min daga yau in kira ki da MAIJIDDAH!.

    Ai kuwa nan da nan Hauwa ta washe baki, fararen hakoranta suka bayyana, batun yau take so a kirata da Maijidda ba amma ba mai kiranta da hakan. Dr. Sarham ya ce, amma bisa yarjejeniyar banni arawa kowa sunan nan, nawa ne nikadai, ni na saka miki, don haka nikadai zan kira ki da shi, ke ko wani kika ji ya kira ki da shi ki gaya masa ba nasa bane nawa ne, ban yarda ko Inna ta kwaikwayar mun ba.

     Inna tayi dariya tana cin goro ta ji Sarham ya kara burgeta, ko ba komai yau ya saka Hauwa murmushi don ta manta rabon Hauwa’u da murmushi (ear to ear) irin haka, watakila tun kafin ta fara ciwon idon yayi na apolo.

Yadda Sarham yayi ta yi musu hira sai da zazzabin Hauwa ya sauka a take, ba tare da sun san lokacin da ya sauka ba, ko dama damuwa ce ta sanya a ranta ta hanata sukuni har ta saukar mata da zafin jiki, amma duk da haka Sarham bai kyale ta ba saida ya fita chemist din Lamco ya samo mata magunguna da first aid kala-kala ya dawo, har da gorar locozade da daurin gasassar kaza da biredi. Ga kayan shayi ya sayo musu makil, tun daga kan sukari, milo da madara har da lipton. 

    Lokacin da ya dawo ya tsugunna gaban Inna yana nuna mata komai kasa magana ta yi ta ce dan nan ya da wahala haka? Ya murmusa yace kada ki damu Inna, na neman albarka ne.

Inna ko ta shiga shi masa albarka kwando  kwando sannan shi da kan sa ya dau kunshin naman ya isa gaban Hauwa, ya bude ya tura mata gabanta, kamshin kazar nan wadda taji kayan kamshi na gargajiya har cikin kwakwalwar Hauwa wadda rabon ta da abinci dama tun kokon safe da ta dan kurba, don ta rasa ‘appetite’ dinta gabadaya, yace kanwata ci nama ko zazzabi ya idasa tafiya sosai yana ganin yadda ta hadiye miyau, mukut, a makoshin ta, amma don karfin hali da ki-fadi irin na Hauwa sai tayi fuska, ta ce ita ta koshi, sai ya ce “to in ni ne baki so in ga lomar ki, bari in tafi, Inna zan wuce gida sai an kwana biyu, kin san na zama dan ki yanzu, zuwa gidan mu sai kin gaji kin kore ni. 

    Inna tace wane mutum ya kori mai kaunar sa, likita Allah ya jikan mahaifan ka, idan suna raye kuma Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana mai albarka.

Wannan addua tafi komai dadi da ga Sarham, da sauri Dr. Sarham yake amsawa da Amin-amin ya rabbi Inna, Abba da Mama duk suna lafiya, cikin koshin lafiya. Allah ya karawa kanwata Maijidda lafiya, da Yakanar karbar kaddarar ta.

    Tun daga wannan ranar gidan su Hauwa ya zama wajen zuwan Dr. Sarham hira, wato tsakar ginan Inna ma tsafta da wadatar iska ya zama dakalin hirar sa, kusan kullum ya taso aiki sai ya je, su yi hira su yi dariya shi da Inna, hirar duniya iri-iri haka suke yini yin ta suna nishadantuwa da daukewa kai damuwar duniya. Inna tayi girkin ta mai dadi ta zubo masa, tuwo ne, dambu ne ko danwake ko dafadukan alkama da ire-iren su, ko gudun kurna da miyar taushe, sai ka ga Dr. Sarham ya mike kafa a kofar dakin Inna ya nade hannun riga ko yayi loosing tie din suit din jikin sa yana kwasar girkin Inna na gargajiya irin wanda baya ci sam a gidan su koda sadaka zaa hadashi, musamman da ya fahimci irin tsaftar Inna, har yan gidan su saida suka gane ya daina cin abincin ranar sa yanzu a dining. Ballde ya zana ya ci abinci tare dasu. In sun yi magana ya ce ya ci wajen wata Innarsa ne. Ga Inna da jin radio komai ta ji a radio sai ta kwashe ta gayawa likita Sarham, shikuma da yake ba maabocin sauraron radion bane sosai yake jin dadin labaran duniya daga radio mai jini wato Inna, sam Hauwa bata iya saka musu baki don ta fahimci daga Innar har Sarham maganannu ne na karshe (talkatives), ita kuma Allah bai halicce ta da yawan magana ba, ciwon kai take saka ta, don haka sau tari haushi sosai suke bata.

A wani hutun karshen mako wato ranar wata lahadi Sarham ya zo gidan, Hauwa na duke gindin famfo wai wankin kayanta take yi, ba yadda Inna bata yi da ita ba kan ta bar su zata saka Salele ya wanke mata in ya shigo, Hauwa ta ki, wai wankin Salele baya fita, Inna ta ce cikin subul da baka,

     “da wanne idon zaki ga wankin har ki san ya fita ko bai fita ba? 

    Ai kuwa Hauwa ta fashe da kuka sosai, wai Inna ta yi mata gorin ido. Ta tattara kayan wankinta ta yi bakin famfo tana ta dirzar su kamar Allah ya aiko ta tana kuka wurjanjan. A haka Dr. Sarham yayi sallama a gidan.

Inna ta amsa daga dakin ta, ya shigo har dakin nata don yanzu ba bakon sa bane, dardumar Sallahr ta ta shimfida masa tace Lale Maraba da Da na Sarhamu yayi dariya yana kokarin zama ya ce Inna kema sunan bakin Abban mu zaki koyi lika min, don a ce ni din wani tsoho ne ko? Bayan ko talatin ban rufa ba, ina cikin twentieth dina? Inna ta ce kai da Kuluwa ban san waya fi wani son yarinta da gudun tsufa ba, ita ta hana a kira ta Kulu, kai ma kace Sarhamu tsoho ne, bayan ainahin sunayen kenan kuke bata maanar su da zamananci. Sarham yace by calling Hauwau da Maijiddah, ai baa bata maanar sunan ba Inna, tunda inkiyarta ce ta hakika. Inna ta ce “hakane kuma, duk inda Hauwa take, Jidda ce. 

    Sai ya dubi inda Hauwa ke wanki bata kula shi ba yau, duk da dama ba wai kula shi ta ke sosai idan ya zo ba, amma akalla ta kan ce masa sannu da zuwa, tacigaba da sabgar gabanta ta manta dasu, ta hanyar kame bakin ta, amma yau kam ko uffan bata ce masa ba, bata kuma kai hankalin ta kan su ba, sai wanki take dirka lokaci zuwa lokaci ta na tsane ido da habar zanin ta.

Inna me ya samu autar ki haka? Wa ya taba miki Maijiddah? Kamar kuka haikan naga tana yi? Inna tace “ai tana jin ka, tambaye ta mana. Waka a bakin mai ita tafi dadi. 

    Wai daga cewa ta bar wakinnan Salele yayi mata, shikenan ta maida abun tashin hankali. 

    Sarham ya ji wani iri, ganin kukan Hauwa’u ya karu da maganar da Inna tayi, kamar ta kara kunna ta, amma duk da haka bata fasa wankin da take faman yi ba kamar na dole, har da kara karfin sheshshekar kukan ta, Sarham ya mike daga kan dardumar da yake zaune ya matsa har inda Hauwa take wankin a gindin famfo ya russunna a gaban ta yace.

     Maijidda yaya haka zaki tadawa Inna hankali? Kinsan bata son kukan ki.

     Hauwa tayi sharbe, hannu a bayan ido, ta ce bayan gorin ido tayi min?! 

    Gorin ido kamar yaya? 

    Ta fashe da kuka ta ce cewa fa tayi wai da wanne ido zan san kaya na sun fita ko basu fita ba, menene wannan in ba gorin ido ba? 

    Sarham yayi kokarin danne dariyar sa ya ce easy Maijidda, ko kowa zai miki gorin ido, ai banda Inna. Ke dai kin fassara maganar ta ba daidai ba sabida dama akan tsini kike, amma ba haka Inna take nufi ba, kin ji?

Ta gyada kai tana share hawaye. Ya ce to tashi ki bar wankin haka, in ya zo sai ya karasa ai har na gama dauraya nake yi, sai shanya. Yace to dinga daurayewa kina bani ina shanya miki Hauwa ta zaro ido ta ce. Lah! Likita da kai, zan saka ka shanya ka jika jikin ka? Sarham ya ce likita bazai taimaki kanwar sa ba? Shi dama ai mai taimakon alumma ne tun asalin sa da haka ta yarda, ta ke dauraye su daya bayan daya tana miko masa, yana karba yana shanyawa akan igiyar shanyar su, nan da nan suka gama. 

    Dr. Sarham ya ce da Inna zai tafi gida, ba zai jima ba yau, dama ya leko ne kawai ya gansu ya wuce saboda Mama ta aike shi Dakata. Suka yi sallama shi da Inna.

    Har ya kai bakin kofa ya tuna abinda ya kawo shi yau, kukan Hauwa yasa ya manta, sai ya dawo ya ce “Inna kiyi wa Maijidda shirin tafiya makaranta gobe, amma ba tata ta da zata koma ba.

     Na nema mata makaranta wadda tayi daidai da masu irin lalurar ta (special school), yadda zaa yi ta dinga zuwa tana dawowa kullum shine ban sani ba, inata tunani a kai har yanzu. 

    Inna taji idon ta har kwalla ta taru, wato shi Da nagari wanda ya samu tarbiyyar iyayen kwarai daban yake, ba sai wanda ka haifa ne kawai zai iya zame maka Da ba, da gaske akwai yayan mutane yan albarka fal a duniya wadanda baku hada kowacce irin alaqa ta jini ba, don dama damuwar ta kenan tun bayan makancewar Hauwa cewa itada karatun sakandire yaya zasu karke?

Gashi tun ba’aje koina ba likita Sarhamu yayi musu maganin wannnan damuwar. Ya share musu wannan hawayen. Me zata yiwa wannan bawan Allah banda duk sallahr farillar ta ta roka masa rahmar Ubangiji da gafara ga iyayen sa ba don sun mutu ba? da gamawa dasu lafiya.

Godiya sosai Inna tayi masa, ta shi masa albarka iyaka, sannan tace kai ta da daukota wannan ba damuwa bane Salele zata yiwa magana ya dinga kaita kullum yana zuwa ya dawo da ita in sun tashi”. Sarham ya ce shi kuma ya saka masa albashin hakan, don kada yau da gobe ya gaji.

    A yammacin ranar Sarham ya kawowa Hauwa uniform na Special School ta Kano, littafai, jakar makaranta da takalmi sau ciki da socks. Ita da kanta Hauwa saida ta rasa ta inda zata godewa Dr. Sarham.

Mafarin fara karatun Hauwa Bilyaminu a special school kenan, tare da sauran yaran Kano da zagayen ta masu visual impairment’ (lalurar gani.) Dr. Sarham yayiwa Hauwa photochromic glass baki saboda ta dinga sakaya kwayar idanunta cikin hasken rana kada (sun exposure) yayi ma kwayar idon ta lahani wadanda kyawun su mai matukar ban mamaki ne, kamar bayan makancewar tasu an kara musu wani (added beauty) a cikin su, da haske mai daukar idon duk mai kallon ta.

    Washegari litinin tun kafin ya tafi asibiti ya zo gidan don kai Hauwa makaranta da kansa, ya kuma ce da Inna da Salele duk su tafi tare don su ga makarantar ya kuma gabatar da su ga malaman makarantar. Hakan kuwa a ka yi.

****          ****                            ****


Hauwa-Kulu ta soma zuwa makaranta kullum tare da Saleleh da yake yi mata jagora, in lokacin tashi yayi ya je ya taho da ita. Hauwa ta soma karatu tare da sauran yara irin ta ta hanyar ‘Braille reading and writing’. Wanda ake koya musu tun a mataki na farko a matsayin hanyar rubutu da karatun su. 

Hauwa’u an zama daliba, karatun data ke yi kullum ya dauke mata damuwar rashin idon ta manta da komai, kafin shekara ta zagayo a yi canjin aji na gaba Hauwa tayi na daya har sau uku a kowane zango, ta iya rubutu da braille sosai ta kuma iya karatu da braille din tiryan-tiryan. Sabida har a gida karatun take yi bata hutawa yasa Inna ta dauke mata tayata da ayyukan gida, ko tayi kokarin karba don ta taya ta Inna cewa take koma daki kiyi karatu kin ji Kulu na yafe miki, ba nakasashshe sai kasahshe, nakasa ba kasawa ba, kiyi ta karatu da nakasa domin kubuta daga bara da tozarta, aikin gida ba naki bane. Nawa ne, nida Allah ya baiwa lafiya.

Sarham ba sosai yake zuwa gidan su Inna yanzu ba, saboda yanayin ayyukan nasa sun koma safe da yamma. Don haka sai karshen mako yake samun leko su Inna ya ji lafiyar su, ya kawo musu sayayyar da yakan yi musu ta kayan masarufi idan ya dauki albashin sa, yana matukar farin ciki da cigaban Hauwa ta fuskar karatu, da kokarin da take yi a ajin su kullum. Don yakan je wajen malamanta ba tare da su Inna sun sani bama, don bincikar progress din ta, ana kuma tabbatar masa da irin kokarin Hauwa bana wasa bane, gifted ce.

     Don hatta lissafi (mathematics) da yake baiwa makafi wahala a braille ita Hauwa tsaf take ganewa abinta.


    A karshen shekarar har kyauta aka bata wato ranar hutun karshen shekara prize giving day kasancewar a shekarar gabadaya ita ke daukar na daya, kuma tafi kowa zuwa makaranta akan lokaci da kasancewa cikin tsaftar jiki data kayan makaranta. 

    Hakan yasa Sarham da kan sa kawowa Hauwa tasa kyautar ta musamman don kara mata karfin gwiwa inda ya dauki Sumayya a motar sa suka je Levintis suka yo mata sayayyar kayan kamun azumi rankatakaf. Kayan dadi na kwali dana gongoni iri-iri. 

    Wannan ne karon Sumayyah na farko da zuwa gidan su Hauwa, tunda jimawa Bhaiyan ta Sarham ke bata labarin su, amma bai taba yarda ta biyo shi ba sai yau, yau din ma don ta taya shi sayayya ne don ta iya provision na kayan kwalama, ta kuma taya shi da daukar kayan zuwa cikin lungun.


Suka yi sallama Hauwa na gindin famfo tana alwalah Inna na daga kitchen, Inna ta amsa musu don ta dau muryar Sarham tun daga madafi, amma Hauwa a cikin cikinta ta amsa, zaka ga dai yadda bakin ta ya motsa alamar ta amsa, Sumayya ta tsaya daga nesa ta saka ma Hauwa ido don jikin ta ya gama bata itace Maijiddan, Hauwa Kulun Badalar kofar Naisa da Yayanta yake yawan bata labari kullum, wadda yake cewa ya makantar daga kuskuren aikin ido. A kunnen sa yaji Sumayyah ta rada masa cewa.

     Tabarakallah-masha Allah, Subhanallah Ahsanal Khaliqeen da wadannan idanuwa na Hauwau. Bhaiya, ashe dai Hauwa-Jidda beauty ce, irin kalar dana ke so na koma (kasancewar Sumayyah fara ce tas). 

    Sarham ya juya ya galla mata harara don ya ji ta sarai. Yace wallahi zaki koma yanzunnan in baki yi min shiru ba”. Inna ta leko jin maganganun su tana maraba da bakuwa, nan da nan ta saki fara tace Sumayyatu ce ko? 

    Sumayyah ta washe baki jin farad daya Inna ta kama sunan ta, ko da wannan ta san tana da matsayi mai girma a gun Bhaiya, tunda har wadanda yake muamala da su sun san da zaman ta. 

    Ta ce ni ce Inna ina wuni? 

    Inna ta bata shimfidar karaunin ta ta zauna, inda Hauwa ta tashi, a lokacin ta gama alwalarta ta juyo tana tafe zuwa inda suke kanta tsaye babu ko lalube, tsabar ta dade da sanin kowanne lungu da kowanne sako na gidan su. Sumayyah ta kamo hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita, cikin girmamawa Hauwa tace da Sarham Ina wuni likita, yaya aiki? Ya dan dubeta kadan kafin yace an gode Allah Maijidda, ga Yayarki Sumayyah na kawo miki Sumayyah ta saka hannunta cikin na Hauwa, sai Hauwata rike hannayen nata sosai a cikin nata tana murmushi tace sannu da zuwa.

    Basu jima suna hira ba Inna ta kammala girkin ta na dambun shinkafa da yaji zogale da soyayyen mangyada ta zubo musu a kwano guda, sannan ta zubawa Sarham yadda ta saba zuba masa a kwanon sa da ta ware masa na samira wanda sabida shi ta dauko shi daga cikin samirunta, shikadai take zubawa abinci a ciki. Ga yaji da yaji tafarnuwa a gefen abincin. Kamar ta san shi da son tafarnuwa, Sumayya ta hadiyi miyau tun kan ta kai loma abincin ya gama yi mata, sannan tsaftar masu gidan ta gamshe ta.

     Hauwa kasa cin abincin tayi da Inna ta hada musu itada Sumayyah don bata sakewa da baki amma Sumayyah sosai take kai loma, nan da nan ta tashi da dambunnan. Shima Sarham tuni ya tada nasa sai kwanuka aka direwa Inna.

     A ranta Sumayya ta ce eh, wato dole Bhaiya yayiwa abincin gidan su kaura, yana nan an gargajiyantar da shi da wannan girki mai motsa kunnuwa. Basu jima ba sosai don zasu gidan Hajiya Kulu, Sumayya ta baiwa Hauwa sayayyar a hannun ta inda ta saka mata ledojin a cikin hannun ta ta ce,

     ga nan gift dinki ne inji Bhaiya, ki cigaba da dauko na daya kin ji Hauwan Inna, shi kuma yayi ta kawo additional gift, duk karshen shekara. 

    Murmushi Hauwa tayi, tana shafa kayan da ledojin, murmushin na karuwa a fuskar ta, kanta a kasa ta ce kice masa nagode, Allah ya saka da alkhairi, kema na gode da ziyara Anti Sumayyah.

    Bayan fitar su da kadan itada Inna shiru suka yi. Hauwa tace Inna ni bazan taba komai ba, don bana son abinda zaa zo ace muna kwadayi. Inna tace to ban ki ta taki ba Kulu, amma shima ya san bamu kwadayin komai nasa tunda baki roke shi ba kuma ba yau ya fara ba, saidai na yau nima ya tsorata ni, don kayan sun ci kudi da yawa da alama. “To Inna ki ajiye ni dai bazan taba ba Inna tace “tsahon shekara guda kenan muna tare da yaron nan, in da wata manufa a tare da shi ko da wani hali nasa mara kyau zuwa yanzu ya kamata in sani, to ban taba gani ba sai tarin alkhairi da nagarta a tare da shi. 

    Alheri da kyauta wannan na lura halin sa ne na halitta kawai. Don haka ni mahaifiyar ki Safiya na ce ko bayan raina duk abinda Sarhamu ya dauka ya baki da hannun sa ki karba da godiya, ki kuma yi amfani da shi da zuciya daya, wannan yaron bashi da wata manufa akan mu sai zumuncin Allah da ya saka kansa tsakanin sa da mu, don bazan ce wani ne ya saka shi ba ko don neman wani abu daga gare mu”.

****                          ****                         ****


A cikin mota suna kan hanyar zuwa gadon kaya, Sumayyah ta kasa shiru, abubuwa da yawa sun tsaya mata a rai game da muamalar Sarham da gidan su Hauwa, babu tudu me ya kawo gangare? Ta saci kallon Bhaiya, wanda ke tukinsa hankalin sa a kwance, ta ce,

     Bhaiya, ina da tambaya, if you permit, may I ask? Tsakani da Allah son Hauwa kake yi?

    Wani irin wawan burki da Sarham ya ci da motar, saida dukkan su suka wuntsulo gaba, suka kusa ci da baka a gaban motar. Saura kadan ya kwadawa Sumayyah mari, domin ji yayi kamar ta yi sabo, amma ya daure ya rike hannun sa yana cewa ba zai taba dukan mace a rayuwar sa ba in sha Allah, balle Sumayyah, da yafi so duk gidan su, kowacce irin katobara zata yi masa kuwa, ba shiri Sarham yayi parking motar a gefen titi.

Cikin matsanancin mamaki da fushin da yake so ya danne yake kallon kanwarsa, yace da Sumayyah ke kuwa me ya kaiki wannan tunanin mai kama da sabo? Sumayya sakewa ta dake har ta kai da ki raina ni irin haka? 

    A duniya mutum bazai yi wata kyakkyawar alakar mutunci da zumunci da mutanen da ya san darajar su, suma suka san tasa ba, kuma yayi sanadin janyo musu lalurar da basu da yadda zasu yi da ita sabida raunin su, da rashin namiji tsayayye a cikin rayuwar su, mutum bazai yi tunanin taimaka musu da faranta musu domin Allah ba sai don wannan shirmen?

     Sumayyah idon ta ya raina fata da ganin bacin ran Sarham karara, ta ce kayi hakuri Bhaiya, ba raini bane hasashe na ne dana kasa dannewa a rai na, na yi laakari ne da maganar Hausawa da suka ce in kaga kare yana sunsunar takalmi… dauka zai yi.”.

      Da sauri Sarham yace amma kuwa Allah wadaran wannan bahaushen da a wajen sa babu kowacce alaqa ta mutunci da taimako a tsakanin alumma sai da manufa, babu kyautatawa mara galihu sai a dalilin wani shirmen banza wai SO!”. Yana fadi yana tada motar, da gaske a gareshi so shirme ne, don baiga ranar da so yayi masa ba.

    Yana tukin yana maida numfashi, fuskar MADINAH ATTAHIRU na gilmawa a idanun sa. Itace silar bacin ran sa ba maganar Sumayyah ba, ita tayi fami ne akan gyambon da aka samu yayi healing ba tare da ta sani ba. 

    Sumayyah jikin ta har rawa yake ganin yadda jikinsa har tsuma yake, ta ce don Allah don Annabi kayi hakuri Bhaiya, ni tambaya kawai nayi bansan ranka zai baci haka ba, kayi hakuri bazan sake shiga abinda ba ruwa na ba.

    Sai kawai ya fizgi motar ba tare da ya kara ce mata komai ba, amma ya fasa kaita gidan Hajiyar Gadon kaya, kofar gida ya maida ita wato can gidan su, New Site.

    Tun bai gama tsayawa ba da motar yace, fice min daga mota malama, daga yau bazan kara fita da ke koina daya shafeni baba, uwar kaudi uwar tsugudidi, fadi baa tambaye ki ba. 

    Jikin ta nata bari ta bude kofar motar ta fita daga gaban motar, hawaye ya tsirgo mata, zata cigaba da bashi hakuri ya fizgi motar sa ya bar harabar gidan su.

Sumayya ta dade tsaye a wurin, tana nadamar shegen surutun ta, da bata iya gani tayi biris, daga karshe ta share hawayenta ta shiga gida. 

    Yinin ranar zungur, Sumayyah ta kasa sukuni idan ta tuna Bhaiya na fushi da ita, Aunty Surayya na tambayar ta me aka yi mata take kulubi da hade rai? Sai ta ce a fusace ina ruwanki dani? Ko ina shiga harkar ki? Mama tace ke ko! Ina laifin Yayan da ya damu da kai? Nifa rashin kunyar ki ce take hada ni da ke Sumayyah ta tashi fuuu! Tayi dakinta ta bar musu falon. Surayyah na fadin kyaleta Mama ta yi da yar halak.

     Shikuma tunda ya sauketa asibitin Murtala ya koma. Ya shige ofishin sa ya kulle kan sa a ciki. 

    Maganar da Sumayyah tayi kuskuren furtawa ta tuna masa da shekaru biyar a baya, abinda ya dade da mantawa; ta tuna masa ‘first love affair din sa wato MADINAH ATTAHIRU (MADINAH SORON DINKI), yar ajinsu, wadda bai sha da dadi a hannun ta ba dama iyayen ta da sunan soyayya, shiyasa duk inda aka ambaci yana son mace, sai ran sa ya kai makura wajen baci.

    Ya so Madinah kamar rai, irin son da ake kira (love at first sight) tun bai gama sanin ciwon kan sa ba, amma Baban ta ya wulakanta shi, don a cewar sa nawa yake a shekaru da matsayi? Sune samarinnan masu hurewa yaran mutane kunne su hana su karatu, bai isa auren diyar sa ba. Sannan Uban sa ma bai isa ba, tunda ba wani bane banda malamin makaranta, ina shi ina auren diyar sa?

    A lokacin ko part three na karatun sa bai hada ba. Soyayya ta rufe musu ido, soyayya ce irin ta tashen balaga daga shi har Madinan, sun so juna shi da Madinah kamar daya bai iya rayuwa ba tareda dan uwansa ba, sun yi alkawarin aure da zarar sun kammala MBBS sabuda yadda suka zaku ga son mallakar juna, amma Baban ta sai ya canza mata makaranta ma, duk don ya raba su, ya nesanta Madinah daga gareshi kwatakwata, don yace ya fahimci zai hana yar sa karatun da ya kai ta ta yi a Jamiar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah ne kawai, shine dalilin da a karshe ma ya dauke yar sa ya maida ita  Jamiar Yamboa dake kusa da Madinatul Munawwara, inda acan ne Madinah ta samu ta kammala nata karatun, shikuma ya kammala a King Abdul Aziz University ya dawo kasar sa ta haihuwa, daga lokkacin basu kara haduwa ba shi da Madina ko a hanya ko a waya ko a mafarki.

Baya ko son tuna wata kalma wai ita soyayya saboda abinda Baban Madinah yayi masa, shi ya san tsakani da Allah ya so Madinah ya kuma yi niyyar auren ta da zarar sun kammala karatun matakin farko na koyon likitanci, itama kuma sai ta baiwa mahaifin ta goyon baya dari bisa dari, lokacin da ya maidata Yamboa sai bata kara nemansa ba koda kuwa a email, ko a telephone, ko ta wasika da ake aikawa ta post office a lokacin.

      ****        *****             *****

    

HAUWA-KULU 

Kusan shakuwar tafi yawa tsakanin Inna da Sarham maimakon Sarham da Hauwa, kasancewar Hauwa bata da magana kuma taki sabawa da Sarham har gobe, duk kuwa da yadda yake kyautata musu, kuma yake jan ta da wasa lokaci-lokaci, iyakaci in ta ji ya zo ta gaida shi, ta shige daki ta bar su, in ya mata tambaya akan karatu ta bashi amsa a gajarce, kuma in an bata sakamakon ta bata kasa a guiwa wajen nuna masa da zarar ya zo gidan. 

    Don ta yarda Dr. Sarham shine ginshikin karatun nata.  Kuma ta kwana da sanin taimakon da yake yi musu mai dimbin yawa ne, da yafi karfin a gode masa, don duk da Inna ta cigaba da sanaar ta ta sayar da wake da shinkafa duk wata hidima ta karatun Hauwa shi yake yin ta kamar biyan Salele albashin kaita makaranta da daukota, da basu kudin hawa hayis zuwa da dawowa, sayen littatafai da kananan abubuwan da makaranta ke bukata kasancewar special school makaranta ce ta gwamnati domin yara masu bukata ta musamman yasa babu bukatar biyan kudin makaranta. 

    Daga baya kuma Sarham baya zuwa gidan Inna sosai saboda ayyuka da suka tarar masa amma duk weekend baya fasa lekowa. Ya zama dan Inna, Inna ta zama uwar sa, ya zama dan gidan Bilyaminu kofar Naisa, don ganin sa take ya maye mata gurbin Zulkifilu.

A yanzu hatta a weekend dinma Dr. Sarham baya samun zuwa hira wajen Inna kamar da, domin yana shirye-shiryen komawar sa Jiddah, bayan kwashe shekaru biyu yana aikin gwamnati, tun akan abinda ya faru da Hauwa yasa a ran sa zai koma zurfafa karatun sa, domin ya ki yardarwa kansa har zuwa yanzu cewa ba rashin kwarewar sa bane ya janyo wa Hauwa’u cataract blindness, yasa a ran sa yana bukatar kara zurfafa ilmin sa zuwa mataki na gaba. Sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi daga ilmin likitancin ido, akan dai specialization din sa na ophthalmology a shirye yake har ya tsufa in dai da rai, bazai gushe ba kuma bazai gaji ba yana karawa kansa kwasa-kwasai na fadada ilmin sa da zurfafa shi, don zama kwararren ophthalmic surgeon din da zai zamowa kasar sa abin alfahari watarana da fiddawa kansa ‘inferiority complex’ din da yake fama da shi tun akan aikin da yayiwa Hauwa-Kulu. Duk da cdewa bayan nan yayi wasu ayyukan fidar da yawa kuma an yi nasara. Abba Prof. kuma ya lamunce masa ya koma din, don a cewar sa gara ya gama karatun duk da zai yi cikin kuruciyar sa, kamar yadda shima ya samu yayi nasa yake cin moriyar sat un da jimawa.

        ****             ****              ****

    Jikin kafatanin mutanen gidan yau a matukar sanyaye yake, wannan ya faru ne kasancewar gobe da asubah ake saka ran in sha Allah, Bhaiya (Dr. Sarham Shanono), zai tashi zuwa kasar da ya baro a can baya a karo na biyu wato kasar Saudi-Arabia don zurfafa karatun sa. 

Sabo, wani abu ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar iyali, musamman irin wannan wadanda suka gina tubalin rayuwar su akan tsari na (nuclear family) wanda akasari yan boko ke yi, wato rayuwa ta daga su sai yayan su, kamar yadda yake a gidan Prof. Abbas Shanono.

     Don haka ficewar daya daga cikin su rana daya zai haifar da wawakeken gibi ne a gidan, musamman shi Sarham da yake jigon gidansu, sannan ‘personality’ din shi ya banbanta dana kowa cikin gidan, shi mutum ne na kowa! 

    Likita mai farin jini da sakewa da mutane wanda kowa nasa ne, mai faram-faram da hidima da kowa nasa, shi kadai ne Da namiji a cikin su, in ka cire mahaifin nasu. 

    Don haka shi din, tamkar wani bango ne a gidan su abin jingina. Gabakidayan su jamaar gidan, in ka dubesu yau zaka fahimci tsantsar damuwar da suke ciki, kowa fuska ba annuri, banda Abba Prof. da ke shi babba ne, ya boye tasa damuwar, maimakon hakan, sai ya rajaa wajen lallashin su da karfafa musu gwiwa kan tafiyar Sarham din da cewa,

     menene abun damuwa don Sarhamu ya tafi? Tunda ga waya yanzu, ta fara zama abu mai sauki, kuma dukkan ku zaku so ganin ranar da Sarhamu zai zamowa kasar sa abin alfahari inace, wanda zai zo a dama da shi a harkar kiwon lafiya a Arewacin Najeriya”. 

    Amma fa shima Abban a ran sa ya fi kowa damuwa, ya fi su shiga kewar Sarhamu, tun ma kafin ya tafi, saboda yadda Sarham yake tsaye kullum kan hidimar sa data gidan sa, wani abun ko labari baya ji sai zance ya shigo da zance, Mama zata ce ai Sarham yayi kaza, kamar misali cefanen gidan sa, yana dadewa bai yi ba. Haka maganin da kowa yake sha idan rashin lafiya ta samu dayan su, Sarham da bai da iyali ya daukewa Abban su kananan abubuwa irin wadannan, su petrol din tada janerato, har ila yau, yana matukar taimakawa shi kansa Abban da nasa ayyukan ofis din kasancewar Allah yayiwa Sarham baiwar ilmi da sanin hikimar koyarwa, kuma da yake a fanni guda suke shi da Abban. Don haka shima yana cikin kewar Lelen Abba!

    Shima Sarham din karfin hali yake yi, musamman in ya dubi Sumayyah, da kukan da take yi. Sai Abba Prof. yace tayi hakuri yayi mata alkawarin bin bayan Sarham da zarar ta kammala sakandire itama zata je ta yi MBBS a can inda yake.

Kasancewar Abba Prof. yana da hanyar tagomashin karatu a kasar Saudiyyah (scholarship) na Jamiar KING ABDULAZEEZ UNIVERSITY domin akwai abokan karatun sa da yawa da suke aiki a jamiar, tun bayan bude tsangayar likitanci a jamiar. Da an samu rarar gurbin karatu su kan bashi.

Mama bayan Sarham ya shiga dakin sa yana hada kayan tafiyarsa, sai ta zare jiki ta bishi a baya, kujerar karatunsa dake dakin guda daya ta samu ta zauna, Mama ta ce,

     “Sarham haka muka yi da kai? Ya bar abinda yake yi ya bata hankalin sa ya ce akan me Mama? Tace maganar diyar Barr. Hannatu da na gaya maka muna so muyi muku yar gida don kara karfafa zumuncin dake tsakanin mu ni da mahaifiyar ta, mun yi da kai kafin ka tafi ko sau daya ne za kaje ku gaisa da ita Sadiya din, amma har yau ban ji ka kara tada zancen ba, gashi har zaka tafi. 

    Kasan dai yadda nake da Barr. Hannatu, babu wasa ko rainin hankali tsakanina da ita, bana so ka je ka shantake a Jeddah babu aure, so nake da ka samu good two or three years ka dawo gida kayi auren ka in ya so in ma komawar zaka yi ka koma da matar sai hankali na yafi kwanciya da zaman ka a koina ne, tunda na fahimci kafi son rayuwar Jeddah banda haka da ka zauna ka cigaba da aikin ka kawai. 

    Duk da nasan baka da matsala Sarham, tarbiyyah ta Allah bazan ce ni na baka ita ba, amma Allah ya yi maka tarbiyyar da kowacce uwa zata yi alfahari da ita, saidai kwanciyar hankalin iyaye a kullum shine ace yaran su sun yi aure a lokacin da ya dace.

    Sarham ya nisa, ya ajiye rigar da zai saka a cikin trolley a gefe, kafin yace cikin lallashi Mama bana so kisa ran ki a irin wannan hade-haden auren na favouritism domin ki dadadawa wasu, wanda a karshe maimakon ku gyara zumunci sai dai ku kai ga lalata shi, saboda ni gaskiya Mama bana raayin macen da iyayen ta ke nemo mata miji daga yayan kawaye.

    Yau da a ce ke da kan ki kika yi wannan raayin, zan iya bi, koda kuwa bana so, amma daga sanda kika gaya min Barr. Hannatu ce ta nemi alfarmar nace a raina yar ta ta rasa miji ne take nema mata, gashi ni ba rasa mata nayi ba, na tabbata lokaci ne.

    Mama kin san da labarin “Madinah” ba tun yau ba, to wallahi Mama har gobe tana raina, don nina gan ta naji ina so saboda wasu dalilai, amma na gwammace in hakura da ita tunda ubanta baya kaunata, kuma daga kanta bana jin zan kara son wata ya mace, daga kanta kuma na tsani soyayyar bakidayanta.

    Mama weve had a wonderful time together nida Madinah, for as long as four years muna tare cikin kauna da fahitar juna, mun yi wa juna alkawura masu yawa amma Madinah ta saka kafa ta take su tayi fatali dasu rana daya, don haka daga kanta na daina bata lokaci na a kan yammata wallahi. Duk marasa amana ne.

     Madinah ta dusar da hasken sauran mata daga idanuna Mama, ba wadda nake ganin farin ta. In fact, Mama bani da niyyar aure nan kusa. 

    Ban san me kaddara ta tanadar min gobe ba!.

     Mama ta ce in uban Madina baya son ka sabida ya raina ajin uban ka, su wadannan uwa da uban duka sun zo da kan su sun ce ka yi musu, suna son hada jini da ni, saboda sun san darajar mu da martabar mu, ni kuwa bana tulawa masoyi na kasa a ido. Amma ban isa in maka dole ba. 

    Duk abinda uban Madina ke takama da shi na tarin arziki da ilmi da har yake ganin baka isa auren diyar sa ba, uban Sadiya ya mallaki goman sa, 

    Da sauri Sarham yace ko ita Madinah ba dalilin da yasa na so ta ba kenan Mama, na rantse ban taba sanin waye ubanta ba har sai bayan ya yanke alaqar mu. 

    Na so Madinah ne akan wani dalili Mama. dalilin kuma shine. kokarin ta a karatu. zai fara bata labarin irin kokarin Madinah da yadda take ‘excelling with high grades a kowacce jarrabawa Mama ta katse shi da karfi, inda tace bana bukatar ji, na gaji da zancen Madinah Attahiru Sarham tunda ba itace autar mata ba.

     Ka karbi masu son ka, ka rabu da tsammanin warabbuka. 

    In dai labarin nan ne ka bani shi yafi sau shurin masaki, yafi cikin carbi, har na riga na haddace shi, kana son Madina saboda kokarin ta akan karatu, na gaji da jin wannan, abinda baka sani ba, Madina ba itace karshen masu kokari ba, Sadiya ma tana da irin nata domin kuwa Quantity Surveyor ce. Kuma uwarta ta tabbatar min tana son ka sosai, ba wai ita ta ga dacewar abin ba Sadiyar ce da kanta tace tana son ka.

    “Ahap! Anzo wurin. Mama ta bare ta gabadaya. Sarham ya fada kasa kasa su Mama an kara bare ta, to ai ni Mama bazan taba auren macen da ta ganni wai ta ce na yi mata ba, komai lalacewar zamani akwai mata masu aji, wadda ba ni na ce ina son ta ba in the first place hankalina bazai taba kwanciya da ita ba”.

     Duk ta inda Mama ta bullo don Sarham ya karbi tayin yar aminiyar ta Sadiya Sarham sai ya zuqe, amma fa cikin lallami da dabara yake bin Mama don su yi rabuwar salama. Ya san kan Maman sa sarai, yana yi yana dariya da hilatar ta yadda bazai bata mata rai ba.

    A karshe Mama ta gaji da jainjar, ta sakar masa inda ta ce Sarham! Na baka shekara daya ka kawo min matar da kake so ka aura, mai kokari irin Madinah wadda hankalin ka zai kwanta da ita din, tunda kai dai a kan Madina kowa dakiki ne, to ka nemo mai kokari irin nata, kafin shekara daya, amma ni wannan Madinar ko zancenta bana son ji.

     Sarham idan shekara ta zagayo baka kawomin mata ba na rantse Sadiya zan aura maka, kana so ko baka so, in kuma dauketa in bika da ita har inda kake.

     Sarham ya ce to Mama addua zaki yi min Allah ya kawo mai kama da Madinah, fara kamar balarabiya, doguwa siririya mai gashi yala-yala har gadon baya, sannan mai asalin kwanya a karatu irin ta Madinah Sorondinki. Tsaki Mama tayi ta tashi ta bar masa dakin don haushi. Ta sani daga Madina har iyayen ta babu wanda ya damu da shi shi, kadai yake kidan sa yake rawar sa a kan ta.

     Ita kuma bazata taba maraba da inda baa son nata ba.


    Washegarin ranar Sarham ya ga cewa ya kamata ya je wa su Inna sallama, kai zai yi kewar kawar sa Inna Safiyya… yadda baa zato, tsakanin itada Sumayyah bai san wa zai fi kewa ba. 

    Wata zuciyar a can kasan kirjinsa tayi whisphering a sace, inda tace masa MISKINIYA KULU!” Da sauri Sarham ya kalubalanci zaciyar sa da cewa capital NO! he will never HAUWA_KULU, zai yi kewar kowa tabbas, har Surayyah da basa jituwa, amma ko kadan ba zai yi kewar Maijidda ba, ba don komai ba ko don halin koin kulan ta da miskilancin da take nuna masa, da rashin maganar ta da sakewa da mutane wanda baya bari ayi sabo mai shiga jiki da ita irin wanda har zaayi kewar ta don an daina ganin ta a wuri. 

    Shin wai kodai shi kadai Maijidda take nunawa halin koin kula, da shariya, da miskilanci, da rashin walwala wani lokacin ma sai ya ga kamar sad face a tare da ita idan taji muryarsa a gidan su???

   

    Ya isa gidan ana kiran sallahr Isha, Inna na alwalah Hauwa na cin tuwo. Yayi sallama Inna ta amsa Kulu ko kamar yadda yayi tsammani a cikin cikinta ta amsa masa sannan bacin ran da yake zargin gani ya dan bayyana kansa a kan fuskar ta. Sai Sarham ya lallaba ya dauke kwanon tuwon daga gaban ta ba tare da yayi magana ba, ta shafa gabanta don kara kai loma sai taji wayam, babu kwanon, amma bai sani ba kamshin turaren sa da ya nashi hancinta (Oud Abyad) ya tabbatar mata shine a wurin ya dauke kwanon. 

    Baya jan ta da wasa amma yau da yake sallama ya zo, shiyasa ya ke son ko yaya ta kula shi. Dan murmushi tayi, wani basakkwacen murmushi ta share shi, ta janye hannu ta koma gefe, ai kuma ta mike don wanko hannu, tana tafe kanta tsaye zuwa famfo kamar ba mara ido ba, ba tare da ta nemi Inna tayi mata jagora ba. sai data kai bakin famfon ta kunna sannan tace ka hutar ni dauke kwanon, dama na koshi ai. Mamaki yasa Sarham rufe baki yana dariya yace.

     Inna ashe idon mu ya bude! Inna tace fata nagari lamiri, me yasa aka ce muyi fatan alkhairi akan komai? Ai don bamu san tasirin bakunan mu ba, mai yuwuwa Allah ya biye bakin ka watarana Likita”.

     Sarham ya ce haka yake Inna, amma shi ya san da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, sai dai duk wani mumini yayi amanna da cewa ba abinda ya gagari Allah, suma likitocin lalube suke yi a cikin duhu. Sanin gaibu sai Allah. Ya russuna har kasa ya gaida Inna, ta kawo masa darduma ta shimfida, sai ya ce,

     “tunda sallah za kuyi, muyi jami gaba daya kawai, ban taba jan ku sallah ba Inna. Maijidda dauro alwallah.

    Daga inda take tsaye a jikin famfo tayi dan sakale! Bata ce toh ko aah ba, don jiya ta fara ganin jinin alada a rayuwar ta, itama bata sani ba, Inna ce ta gani a jikin zanin ta ta gaya mata, ta kuma taimaka mata wajen kunzugu, ta koya mata yadda zata dinga killace kanta da tsaftataccen tsumma, dankwalin sabuwar atamfarta mai tsafta ta dauko ta tsaga shi gida biyar ta koya mata amfani da shi, ta kuma gaya mata baa sallah da komai na ibada sai an samu tsarki, koda yake duk ta sani a makaranta tun kafin ta fara din 

    Duk da cewa ta tsorata da Inna ta gaya mata ta fara alada, ta kuma tabbatar mata yanzu ta girma dole ta kula da kanta da tsare mutuncin ta daga wannan lokacin, da kuma koyon yadda zata ke muamala da maza daga yanzu.

     Inna ta zaunar da ita ta ja kunnen ta sosai, ta gaya mata yanzu da girman nan ya hau kan ta ko hannun ta namiji ya kama cikin shege ne zai shiga jikin ta kuma haramun ne. ta tsoratar da ita sosai akan maza ko yaya take dasu. Yinin jiya zungur laccar da Inna ta wuni tana yi mata kenan. Sarham ya gaji da jiran Kulu ta zo su tada sallah, don tunda ta shige daki ta ki fitowa ya dauka hijabi zata shiga ta dauko amma shiru kake ji. Sai Inna ce ta sadda kai ta ce,

     ja mu sallahr ka ji! Kuluwa girma ya zo!.

    Sarham cikin rashin fahimta ya tambayeta girma kamar yaya?.

     Duk surutun Inna da yadda ta ke sakewa da Sarham wannan karon kasa fada masa Hauwa ta fara alada tayi, ta hau inda-inda, har ya gaji ya tada sallah, amma daga karshe a matsayin sa na likita malamin kiwon lafiya sai ya dago su. 

    Abu daya zai hana mace sallah uwarta ta bi bayan ta shine idan tana fashin sallah. 

    Ikon Allah, har nawa Hauwa-Kulu take? Maiyuwuwa kuma irin jikin ta kenan. Irin su kuma sune masu haihuwar wurwuri. Koda yake kanwarsa Sumayyah ma haka ta fara da wuri, kuma shi ta fara gayawa tana kuka, don ta kasa gayawa Mama da Surayyah, tana ganin wani mugun abu ne ya faru da ita, ba zai manta ba shi ya fara saiwa Sumayya always pad ko Mama sai da Sumayya tayi wajen sau uku kafin ta sani.

    Bayan sun idar da sallah shi da Inna, kasa gaya mata tafiyar sa Saudi yayi, saboda sabo, da wata irin kewar su da tazo ta rufe shi, Inna kuwa tana ta hidimar hada masa tuwon masara miyar kuka da manshanu, ga yajin daddawa a gefe, ta kawo ta aje masa da ruwan randar ta mai sanyin dadi. Taga yayi shiru ya kasa cin abincin da doki kamar yadda ya saba, cikin kulawa Inna ta ce, likita ya dai? Jikin ko garin?” Ya nisa, kafin yayi kundumbala ya ce babu ko daya. Inna sallama na zo muku, zan bar kasar nan!.

    Ba Inna kadai ba hatta Kulu da ke daki fitowa tayi da sauri daga uwar dakin data je ta boye jin abinda Dr. Sarham yake cewa.

     Tafiya ta same ni zuwa kasa mai tsarki, zan tafi karo karatu na akalla shekaru uku, Inna ina fatan zaki cigaba da tayani kula da karatun Maijidda har ta kammala, alkawari ne na dauka tsakanina da Ubangiji sai na ga ta kammala sakandire hankali na zai kwanta, to amma ga yadda Allah ya tsara min.

    Ina fatan kafin in dawo Inna zaki tsaya akan karatun ta na sakandire har Allah ya cika min wannan burin nawa”.

     Inna gaba dayan jikin ta ya mutu. Bata san ta saba da Sarham ba sai yau da yake maganar barin kasar mu baki daya, bata san dimbin alkhairin sa mai yawa bane a gare su, sai yau da zai bar su. Kokari take ta mai da hawayen da suka kawo mata cafka, don kada ta kara karya masa guiwa da tata karayar, don hatta yadda yake maganar kadai zaka san ya fi ta shiga damuwa da kewa, ya karaya.

     Hauwa dai ba tace komai ba, amma a cikin ranta wani irin ‘dakace’ take yi, cewa take inamainama! Inama na ga fuskar sa yau, inama nayi masa kallon karshe yau kafin ya barmu, wanda zai sa kullum nake tuna fuskar sa, in yi ta masa addua!.

     Don duk tsayin lokacin nan da suka kasance da Sarham a cikin rayuwar su kusan koda yaushe cikin wannan fatan take, ba don komai Hauwa take son ganin fuskar Sarham a rayuwar ta ba, sai don ta yi quenching curiousity dinta a kan kamannin sa ta kuma yi matching din fuskar da kyawawan kalaman bakin sa na kullum a kan su, wadanda a kullu yaumin masu maana ne wadanda suke kara mata son ganin kamannin halittar sa, shi Sarham mutum ne mai fasahar zance na ilmi, da girmamawa ga mutane, ba tare da laakari da matsayi ko ajin rayuwar su ko nasa matsayin ba, kalaman Sarham har kullum masu tausasawa dan adam ne, a duk halin da yake ciki ya san kalaman da ya dace yayi masa, wato koyaushe kalaman sa na tafiya ne da irin yanayin da ya tarar da kai a ciki.

    Alal misali, in ya lura kana cikin farin ciki zai taya ka da zolaya da tsokana yakara maka farin ciki, haka in bakin ciki kake shima zai taya ka har a murya da zuciyarsa, daga yanayin kalaman sa kadai zaka tabbatar (he feels what you are feeling) kuma yana tayaka. Sarham ta kwana da sanin cewa shi din, wani kyautar Ubangiji ne koko tace (dauki) da Ubangiji ya kawo cikin rayuwar su, ya hada su da shi, a lokacin da suke tsananin bukatar tsayawar namiji a rayuwar su.

     Ubangiji ya nufe shida shigowa rayuwar su ne don ya zame musu fitila mai haske kuma sanyi daga kuncin da suka samu kan su rana daya na nakasar ta, wanda in ba hadin Allah ba, ba abinda zai sa ya shigo cikin rayuwar su ya tsaya kamar Yayanta na jini. Domin ta kowacce fuska babu ta inda rayuwar su ta zo daya.

Yau da yake cewa zai tafi, har tsayin shekaru uku sai taji cewa lallai zasu yi rashin da baa mayarwa, zasu yi kewar da bata karewa, don shekara uku ba kwana uku bace, abu ce ta mai yawan rai.

Inna ta cigaba da hana kanta kuka a gaban Sarham, tana gayawa kanta saboda su ba zai fasa gina rayuwar sa ba. Yo fisabilillah don su aka halicce shi? Daga taimako? Kuma dai duk wani abinda ya dace don kyautata rayuwar mutum Sarham ya gama yi musu shi, tunda yayi wa Hauwa sanadin cigaba da karatu bayan iftilain da ya same ta.

    Sun koyi abubuwa da dama daga gare shi, irin su magungunan da ya dace da taimakon farko na cikin gida (first aid), home hygiene, sanitation duk karshen wata, cin balance diet a gargajiyance da irin abincin da suke da shi, sun koyi abubuwa masu yawan gaske da suka shafi kiwon lafiya a bakin sa a dalilin zamansu tareda shi.

     Haka kuma ko yau bai yi shiru ba sai da ya ce da Inna ga kudi zai bar musu ta tabbata ta sayawa Hauwa auduga mai yawa a chemist, bai yarda da kunzugun tsumma ba, yace ita ba ido ba, don haka ba iya kula zata yi da kanta ba kada yaje ta dauki kwayoyin cuta.

Kunya duk ta kama Inna. Kulu kuwa da ace a da ne Dr. Sarham ya fadi haka da tuni ta hau shan kunu da fushi da bacin rai na cewa an yi mata gorin ido, watakila harda su kuka, amma da yake yau itama zuciyarta ta tabu da zancen tafiyar tasa ba tace ko uffan ba, saima kunya da taji sosai itama kamar Innar.

     Inna har sai da ta kasa rike hawayen nata a wannan karon, da ya ajiye mata kudi masu dama a gabanta, tace. Dan nan shekara uku ba kwana uku ba. Allah yasa ka same ni a raye, rayuwar nan da bata da tabbas. Allah yasa muna da rabon sake ganawa, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi. Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ilmin da zaka je nema, ya kuma baka dukkanin abinda kake nema a cikin samunsa, ya huwwace maka saukin sa, ya kuma baka albarkar sa. 

    Amin- amin Inna, nagode kwarai da gaske da wannan addua mai dadi daga bakinki, na ji dadin zama da ke Inna, zan kuma yi kewar ki ba dan kadan ba!. 

    Sai da ya tashi tafiya yaga Hauwa ba tace masa komai ba, koda kuwa adduar fatar baki ce, ta sunkuyar da kai kawai. Wannan karon kam ya kufula da wannan mugun hali nata, ya ce Kuluwa!!!”. (Sunan da ya san ta tsana, kuma yana kular da ita), ta dago manyan idanun nan tayi harrr! Dasu a saitin da ta jiyo tashin muryar sa, ga mamakinsa hawaye ya gani ya kwanta dankam a cikin su, ya basu wata irin kala kamar na mai jin barcin da ke hamma, ya sake cewa, ko ba da Hauwa-Kulu-AKA-Kuluwa nake magana ba?. 

    Hauwa ta tsuke baki, sannan ta sosa hanci cikin jin haushi, bata amsa ba, sai can data mula taga damar magana don kanta sannan tace,

     amma dai saboda Allah in mutum ya nuna baya son suna, bai kamata a dinga kiran sa da shi ba, har raina bana son suna KULUWA! an ce miki Kuluwar, Kulun Majadun, Hauwa-Kulu, Kululu, da wasu idanuwanki kamar na Kuliya (mage/mussa).

    Ke kam baki ji dadin halin ki ba, wallahi ba don Inna ta tabbatar min a gida ta haife ki ba, da na yi rantsuwa an canja mata ke a asibiti. 

    Don Inna ba sumumu-kasau bace, bakin ta baya shiru don ya cutar da ita, ki fada kar ta kashe ki, mai yuwuwa kafin shekara ukun na mutu! Ko ke kin mutu! Ko dukkan mu mun mutu! Don haka fadi abinda ke ran ki yau da nazo yi muku sallama, ba tare da mun san ranar sake haduwa da juna ba.

    Hauwa zan iya rantsuwa kan ban taba jin kin yi min magana da ta wuce sentence biyu ba, a tsayin shekaru biyun da nayi da sanin ki. Ga wani ‘sadness’ da nake gani akan fuskarki a duk lokacin da kika ji sallamata a gidan ku. Me nayi miki haka? Meye dalili? Na rantse gaisuwa ma akan dole kike yi min ita. Kulu baki dauke ni dan uwa kamar yadda na dauke ki ba.. 

    Hauwa-Kulu sai ta fara hawayen babu gaira babu dalili, ko da yake dama sun cika idon tuntuni suna so su zubo ne, tana fin karfin su. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ta ce dama kullace kake da ni haka duk tsayin lokacinnan ban sani ba?. Nake kullace da ke? Ko kike kullace da ni?.

    Inna bata san me yasa ta kasa sauraron takaddamar tasu ba, ko don cikin zafin rai kowanne yake furucinsa, sai ta tashi salin alin ta saka takalmanta ta dau buta da niyyar ta zagaya bayan gida, ba tare da tana jin fitsari ko kashi ba, kawai ta kasa jure ganin hawayen Hauwa shi kuma ta kasa jure ganin bacin ran sa karara yau, don bata taba ganin sa cikin bacin rai ba, shi Sarham ta fahimci kullum mai kirki ne, mai fara ne, mai walwala ne kuma mai farin-ciki da kowanne yanayi (jovial person).

     Kasancewar bai taba nuna bacin rai a kan share shin da halin koin kulan da Hauwa-Kulu ke nuna masa ba sai yau, wanda itama ta sha yi mata fada a kan bata kula shi, bata kyautata muamala da shi, bata masa fara kamar bata so yake zuwa gidan su, amma Hauwa sai ta ce,

     to Inna me kike so in dinga ce masa? Magana ba sai ta dauro ake yin ta ba? To ni ban da wata magana da shi banda gaisuwar da ta zame min dole, kuma ina gaida shi”.

     Rannan da Inna ta hau ta da fadan ya zo har ya fita ranar ko gaisuwar ma bata yi masa ba, Hauwa ta zaro manyan idanunta waje (ta manta da wa take magana) ta ce,

     Inna! Idan kin manta ni ban manta ba, daga gyaran ido ya karasa makanta ni, ni duk wannan kirkin nasa gare mu ta baya ta raggo, ido fa na rasa a hannun sa, Inna! Wani abu zai min ya biya ni?”

    A ranar Inna ta sha mamaki ta kuma tsorata, ta ce au, dama dalilin ki na kin girmama alamarin likita kenan?. Hauwa ta yi shiru, sai can ta kama hawaye. Tace Inna dalili na kenan, amma ba wai na rike shi a raina bane na san kaddara ta ce, amma kullum na tuna shi yasa idon ya karasa macewa saboda careless na aikin sa sai naji tsanar sa ta darsu min, tunda Inna ba abinda zai yi ya biya ni ido na, ba kuma abinda zai min da zan yi farin ciki da shi idan ba idanuna ne suka dawo min ba!”.

     Inna ta kai hannu zata mari Hauwa, ko me ta tuna? Malam Bilyaminu! Ya taba rokonta ko me Hauwa zata yi nasiha ta kasance tsakaninsu ba duka ko zagi ba, duka baya biyar da yaro yayi abinda kake so saidai ya kara kangarar da shi musamman mautum mai riko irin Hauwa-Kulu.

     Sai Inna ta rike hannun nata da daya hannun, ta hana shi isa ga fuskar Hauwa. Cikin tashin hankali tace mata na rasa me zan ce miki, Baban ki ya sha gaya min kina da kullata ban taba yarda ba sai yau, amma ina so ki sani Allah ne ya dora miki makanta ba Likita Sarhamu ba, su kawai masu taimakawa ne a samu lafiya amma suma basu hada sani da Allah ba, lalube suke cikin abinda suka karanta don su taimaki alumma kawai.

    Inaso ki sani Hauwa-Kulu, komai na rayuwar dan adam a rubuce yake a Lauhul Mahfuz, tun kafin halittar sa balle haihuwar sa.

Ban so kika saka wannan mummunan tunanin a ranki ba Hauwa-Kulu, domin ya zama rashin yarda da kaddara, ya nuna baki dauki kaddararki da kyakyawar zuciya ba kenan, wanda yana cikin sharuddan imanin mumini. 

    Yi maza ki ce “astagfirullah domin wani Likita duk kwarewarsa ko akasinta, bai isa yayi abinda Allah bai yi ba, kuma shi ba Allah bane da zai bayar da lafiya ko ya hana.

    Banda son zuciya irin naki, in ma tuhumar ne ni ya kamata ki tuhuma, ni da tun farko ban kai ki asibiti ba tun ciwon yana apolonsa, sai da idanun suka kusa tashi aiki.

    Haka Inna tayi ta mata waazi mai shiga jiki a lokacin, amma Hauwa-Kulu bata kara tankawa ba saboda miskilancin ta, don haka yanzun ma da Inna ta shige bayi ta bar su a nufin su gama fadan sannan ta dawo, Sarham ya ce wai ta fadi abinda ke ranta yau, kada ta bar shi a ranta ya kashe ta, sai taji kuka ya kwace mata ba kakkautawa a gaban sa. 

    Sarham sai gashi jabar! Ya koma ya zauna dabas a kasa, akan rairayin tsakar gidan su Hauwa. Taja gefen hijabinta ta rufe fuska cikin kakabi da fushi da muryar kuka ta ce, babu komai a raina, sai fatan alkhairi ga kowa”. Sarham ya ce karya kike yi, kuma ni bana shiri da mai karya. Ko amon muryarki ya karyata ki, ya karyata abinda kika fada. 

    Fatan Alkhairi ne a ranki game da kowa? Amma banda a kaina ni Sarham ko? Wa na kashe miki? Ko me nayi miki haka da zafi da kika kullace ni?. Hauwa ta rasa yadda zata yi da shi, don ba zata iya ce masa tana jin maqaqin sa a ranta ba, da cewa bai iya aiki bane ko kuma carelessness dinsa ga aikin sa ne yasa ta makance gabadaya. 

    Sai ta samu bakin ta ya bige da cewa cikin rawar murya da rishin kuka.

     Ina dakace ne na cewa, inama ina gani! Inama in ga fuskar ka a zahiri in san kamannunka! Rashin idona yana hanani farin ciki da kowa da komai”.

     Mamaki ya kashe Sarham daga zaunen da yake na yadda nan da nan ta kirkiri karya don kaucewa tunanin ta na hakika, ya dube ta sosai cikin manayan idanun ta kamar tana ganin sa, zai so ace a lokacin da zai fadi abinda zai fada yanzu sun hada ido, yace cikin wata irin murya mai rauni.

     Maijidda you are accusing me for being the cause of your blindness, (Maijidda kina tuhumata da zamowa sanadin makancewar ki), hakane ko ba haka ne ba?!”

    Hauwa ta cira ido a firgice, zuwa inda take jin tashin sautin sa, ya daga gira yace Yes, ba wani son ganina da kike yi, karewa ma ba kya son gani na, you are just accusing me.

    Ni kuma na san bani na makanta ki ba ALLAH ne ya tsara miki wannan jarrabawa domin ya jarrabi imanin ki Maijidda. Nakaa ba komai bace face jarrabawar Ubangiji ga wasu kebabbun bayinsa.

    Unfortunately, kina neman faduwa jarrabawar ki Maijiddah, domin a zuciyar ki babu TAUHIDI babu IKHLASI. So ya rage naki kiyi maza ki gyara, kiyi istgfari, ki yi kokarin cin jarrabawar ki, ko ki bari shaidan ya ci nasara da galaba akan jarrabawar ki ya barki da biyu babu; ba ido ba imani. Don ni, da ke duka mun san yarda da kaddara yana cikin cikar imani.

     Hauwa ta dan tsorata da bayanin nan da Sarham yayi mata, amma dai ko ta gamsu da bayanin Sarham bazaka taba gane hakan akan Bakanuwar fuskar ta ba, mai iya boye abubuwa iri-iri da ki-fadi, tace,

     ta yaya zaka fadi abinda baka shiga zuciya ta ka gani ba? Saidai in dama kana tuhumar kanka ne”. Sarham yayi dan murmushinsa mai ban shaawa domin yanzu ya gama gane manufar ta, da abinda ke cikin ranta a kansa tuntuni da yake saka shi ganin sad expression akan fuskarta, yace.

     Nayi laakari da maganar hausawa ne da suka ce labarin zuciya ai fuska ake tambaya, kuma dai ‘Im older than you, and Im good at reading minds. Da babbar murya zan iya kiran kaina ‘behavioural analyst’, amma mu barshi a abinda kika fada din, watau kina son ganin fuskata ne, me kike kissimawa akan fuskar tawa? 

    Idan kuma ni din mummuna ne fa Maijidda? Irin munin da in an gani sai an rufe ido don muninsa? 

    Hauwa bata san sanda tayi murmushi ba, alhalin ga hawaye face-face a fuskarta, ta ce mummunan mutum ba mutum bane? Ai mummuna da kyan hali irin naka, sai yafi kyakkyawan gaske nagarta da shiga ran mutum, bayan haka ma a hakikanin gaskiya ni ba wannan nake kissimawa ba, ina kissima yadda fuskar zata yi dai-dai da irin kyawawan kalaman ka ne, koyaushe kana magana wadda ta dace da muhallin ta, kana da tunani na ilmi (with abstract reasoning)”.

    Sarham wani irin kallon bakinta dake motsi a hankali yake yi, da murmushi yace ikon Allah. Ya akayi ni ban sani ba? Kamar wadanne iri ne kalamai na masu kunshe da abstract reasoning? Irin dai wadanda kake yawan yi cikin surutun ku kai da Inna, wani lokacin ina saurara, nafi zama mai sauraro a hirar mutane fiye da mai contributing, ta nan nake fahimtar yanayin zancen kowa, na fahimci maganganun naka duka a muhallin su kake yin su, kuma a takaice, amma cike da tarin maanoni da alfanu, sannan duk wani cukurkudadden alamari ka san ta yadda zaka bi ka warwareshi cikin hikima irin taka”. Sarham ya zura takalman sa, ya mike idonsa akan Hauwa, yana sakin dariyar da bai shirya zuwanta ba, ya lura yau in zasu kwana a haka, bazai gaji da sauraron dadadan furucin Maijidda gareshi ba, ya ce SAI WATARANA Maijidda sai watarana, ina rokon ki, duk runtsi kada ki bar zuwa makaranta, koda kin rasa dan jagora! Ina nufin against all odds, koda da rarrafe ne ki jure ki nemi ilmi, duk da nasan ba zai zamo abu mai sauki gareki ba, dama duk masu lalura irin taki, amma ki sani Allah ne gatan ki sai kuma shi (ilmin)”.

Idan na rasa dan jagora da wanne idon zani makarantar? Misali, idan Salele ya daina kaini ko ya mutu?”

    Hauwa bata san sanda ta jefe shi da wannan tambayar ba, a lokacin har ya saka kai zai bar tsakar gidan su. Amma jin yadda muryarta ke rawa da karkarwa kamar kuka zai kwace mata yayin fadar hakan, a lokacin da take fadin hakan ma tuni hawaye ya ciko idonta, sai Sarham ya juyo yana kallon Hauwa da wani irin expression a idanunsa, cikin wata irin karaya da kewa, hasken farin wata ya haske masa fararen idanun ta suna jujjuyawa a cikin lalurar rashin gani. Ya kamata ya bata amsar wannan tambayar ta yadda zata dade tana tuna ta, wato tayi ta shawagi a kwakwalwarta, har ta zame mata tsani a rayuwa.

Ta hanyar sakawa ran ki cewa zaki iya komai da mai lafiyar ido zai iya, hankali ke gani ido gululu ne, ki tuna kullum da karin maganar da Bahaushe ke cewa “ba nakasashshe sai kasashshe”. Bature kuma yace

   “theres ability in disability!”.

  Sannan kullum kisa a ranki “nakasa ba komai bace face wata kankanuwar jarrabawar imani ga wasu kebabbun bayin Allah na kwarai daga Azza wa Jallah”.


Wadannan kalaman nasa su suka zamewa Hauwa-Kulu a food for thought, har bayan tafiyar Dr. Sarham daga rayuwar su, bata bar mayar dasu madubin ta na rayuwa ba, fitilar dake haska mata duhun koina dake cikin nakasar ta, sannan jagoran ta a duk lokacin da ta rasa dan jagora, wato kalaman sa ta saka a gaba suke saita mata hanya a duk inda ta nufa, don cimma rayuwa mai amfani a cikin halin data ke ciki na nakasar idanu. 

    Watanni masu dama suka biyo baya suna cikin kewar sa mai yawa itada Inna. Cikin tuno ‘precious moments’ din su tare dashi. Ko na rana guda sun kasa mantawa da shi.

    Sun kasa mantawa da tarin gudunmuwarsa ga rayuwar su, da lokutan da suka kasance tare da shi cikin yanayi na zumunci da yan uwantaka. Zaman sa na dan lokaci cikin rayuwar su ya dauke musu kewar Baban ta watau Malam Bilyaminu kaso 50% data dan uwanta mai rasuwa wato Zulkifl, duk da a sanda yake zuwa wajen su din bata wani damu da shi ba, sai ma kullata data biyo baya, duk da repentance dinsa gare su akan laifin da ba lallai a kira shi nashi ba, amma bayan tafiyar sa, da irin emotional sallamar da suka yi mai zaunawa a rai, hakan yasa ta yin kewar sa bad an kadan ba. 

    Guzurin kudi da ya bar musu har naira dubu daya sun dade suna cin moriyar su, kafin bayan wasu watanni masu yawa su kare, duk da haka Inna bata bar sanaar ta ba ta sayar da wake da shinkafa da juyen dabbobi a kasuwa duk shekarar sallahr layya.

A lokacin Hauwa ta shiga babbar sakandire aji biyu, watarana ta dawo daga makaranta tare da Salele kafin su hawo motar bus da zata kawo su kofar Na’isa Salele ya hango ana hawan kilisa a kan dawakai a tsallaken titi. Saleleh mayen dokuna ne na gani kashe ni, yana matukar son wasan Polo da hawan angonci ko hawan sallah na sallah da sarki ke yi a Kano, tuni suka kwashe hankalin sa daga kan Hauwa, ya bata jakar makarantar ta ya ja sandar da suke kamawa shida ita a matsayin jagora tsakanin su, don ba hannun ta yake rikewa ba duk da ta girme shi, yace.

     Hauwa, zauna kan bencin can ki dan jira ni in ga wucewar masu kilisar can akan dokuna Hauwa tace toh, amma don Allah kayi sauri Salele, ka san yanzu Inna tana duban hanyar mu, kada ta ga mun dade ta damu. 

    Salele tunda ya nausa cikin yan kallo ya bace mata bat! Shiru shiru Hauwa na jiran Salele bai dawo ba, karambani irin nata yasa taga cewa bari dai kawai tarabu da shi yau tayi kokarin kai kanta gida kada hankalin Inna ya tashi. “Dr. Sarham” yace ba ido ke gani ba hankali ne ido gululu ne kawai. 

    Sai ta tashi da zummar ta tsallaka titi ta tari motar kofar Naisa, don daga yadda take jin karar motoci ta san a bakin titi suke, tana tafiya a hankali abunta kanta a kasa ba tare da ta san ina take saka kafa ba ai dai mutum ya gane da kansa bata gani shi ya kauce mata. 

    Ai kuwa bata jima tana tafiyar ba taji ‘horn’ din mota a tsakar kanta, wanda ya kidimata ta diririce ta kwasa da gudu, motar kuwa bata yi kasa a gwiwa ba wajen kwasheta, ta yi sama da ita sannan ta nana ta da kasa.

Salele dake tsallakowa titi akan idon sa mota ta kwashe Hauwa. Ya dora hannu a ka ya rafsa ihu yayi kanta a tsakiyar titin yana fadin na shiga uku, Hauwa ban ce ki jira ni ba? Hauwa!!!”

     Mai motar ya gangara gefen titi ya tsaya, ko kafin ya fito daga motar jamaa sun taru a kan Hauwa ana salati. Da yake na kirki ne sai bai gudu ba, ya taimaka aka saka Hauwa a motarsa, tareda wani dattijo da Salele da ya ce ai Yayar sa ce, suka nufi asibiti da ita jini nata disa a motar, amma mai motar nan bai damu ba ta ran Hauwa yake, yana rokon Allah yasa abun ya zo da sauki kada diyya ta hau kansa. 

    Hauwa bata san inda kanta yake ba har suka shiga babban asibiti.

    Asibitin Malam suka kai Hauwa, a ka karbe ta a imajensi likitoci uku suka rufu akan ta suna kokarin ceto ranta. Sai bayan an samu an yi treating raunukan da ta ji, an kuma daure karayar da ta samu a hannu sannan aka basu daki kwanciya. Wanda ya kade ta duk shi ya biya komai, kuma ya tsaya har aka kai su dakin kwanciya din na mata inda aka basu gado.

     A lokacin ne ma ya samu damar da ya kalli Hauwa tana barci, duk da ta kara girma sosai, ta zama budurwa sai yaga kamar ya santa. Ya tambayi Salele gidan su, don aje azo da iyayen ta, Salele ya ce zai je shi kadai ya zo da Innar ta.

    Don haka saurayin ya ja kujera gaban gadon Hauwa ya zauna bayan fitar Salele, ya dau wata jarida a kan lokar gadon ta asibitin yana dubawa yana satar kallon Hauwa yana fadi a ransa yau tsautsayi ne ya fito da shi daga wajen aikinsa ba tare da lokacin tashin sa yayi ba, tsautsayi da baya wuce ranar sa, banda haka shi baya wani fita cin abinci har cikin bankin a ke kai musu su biya, daga yaje ya ci abincin rana a restaurant ya koma office zuwa lokacin tashi tsautsayin nan ya ritsa da shi?

Ya sake kai duban sa ga Hauwa a karo na sau ba adadi, sosai take masa kama da wata fuska da ya jima da sani, amma ya kasa tuna inda ya san fuskar ba.

Har saida Inna tayi sallama a gigice ta fado dakin asibitin kamar an turo ta, Salele ya biyo ta a baya da buta da bokiti da tabarma da bargo, nan ne mutumin ya gane ta sarai. A tsorace ya mike tsaye, ita kuwa Inna bata ma lura da shi ba kan Hauwa tayi tana salati tana godewa Ubangiji. 

    Bayan ta dan nutsu ne Jamilu ya matsa gaban ta ya tsugunna, ya sadda kan sa kasa cikin kaduwa da mamaki da tsoron kada Inna tace da gayya ya kade Hauwa, yace Inna Safiya kiyi hakuri, ni na kade ta ban sani ba, ashe Hauwa-Kulu ce ma, kanwata. 

    Wallahi ina cikin tafiya kawai na ganta a gabana a tsakiyar titi, nayi kokari in kauce ta sake dawowa daya barin da ba yadda zan iya kauce mata.

     Inna ta kai duban ta ga saurayin, nan da nan ta gane shi duk da girma da cika idon da yayi, Jamilu ne dan wajen Zakari, Inna ta ce.

     Jamilu dan wajen Rumanatu? Yace ni ne Inna Inna tayi kwafa ta ce to babu komai, kana iya tafiya, mun gode.

     Jamilu ya ji babu dadi a ransa, yace Inna Safiya wallahi tsautsayi ne, ba inda zani sai taji sauki, zan kasance tare da ku har Allah ya bata lafiya.

     Inna bata sake komawa ta kansa ba, ta maida hankali kan gyarawa Hauwa kwanciya, har ya karaci durkuson sa ya tashi, ya tafi cikin damuwa. 

    Bayan fitarsa Inna ta tambayi Salele yadda aka yi ma ya rabu da Hauwa har ta hau titi bisa ita kadai, cikin kokarin boye bacin ran ta, Salele duk rashin gaskiya ya bayyana a fuskar sa ya ce Inna daga nace ta tsaya in je ni tsallake in dawo Inna tace ka dai fadi gaskiya, kai dai wallahi a kan kalle-kalle ko bakauye nan ya ganka ya barka. Allah ya kiyaye gaba”. Can kuma tace. “Oh ni Safiya, Hauwa-Kulu harda karaya? Idon ta ya kawo ruwa, tasa habar zaninta ta share tana sake gyarawa Hauwa kwanciya, an sakale hannun da aka gyara a jikin karfen gadon. 

    Ba jimawa da fitarsa Jamilu ya sake dawowa niki-niki da ledoji a hannayensa, yayi sallama akan su, dakin irin dogon dakin nan ne na kwantar da marasa lafiya mata zallah, suna daga gadon tsakiya da wasu a gefeda gefen su, Inna ta juya ta dube shi ta amsa sallamar sa, fuska kadaran-kadahan ta ce wani abu ka manta ne kuma? Ya ce aah Inna, ai na dinga zuwa kenan har sai an sallame ku, in sha Allah. Ya ajiye mata ledojin da ya shigo dasu a gaban ta cikin matsanancin ladabi, sai Inna ta rasa me zata ce, yaushe yayan Zakari suke da hankali balle su yi halin da yake yi a gabanta yanzu?

     Koda yake ko dama can shi daban yake a cikin su ta san wannan, saboda uwarsa ta masa tarbiyya daidai gwargwado, bayan Zakari ya saketa da shi ta tafi tayi aure a wani gidan, ba laifi yana gaida mutane duk inda ya gan su ba kamar kannen sa ba da sau dubu zasu wuce ta ko kallo bata ishe su ba. In zata iya tunawa rabon ta da Zakari da wani da ya shafe shi tun batan Malam Bilyaminu, shekaru hudu baya da ta je neman sa yayi mata korar kare. Wani cikin su shi ko yayan sa bai kara neman su ba, yau kuma sai ga Jamilu ya kade Hauwa. 

    Inna ta nisa, ta kasa ce masa ya kwashe tsiyar sa, don sosai taga damuwa a tare da shi na irin karbar da take masa. Haka suka zauna shi da ita zugum-zugum, ba mai iya ce da kowa uffan, daga baya yayi mata sallama ya tafi. Yace sai gobe in sha Allah kafin ya tafi wajen aiki zai leko ya ga jikin Kulun.

Inna tayi masa godiya, amma sai ta ce “don Allah ba sai ka dawo ba Jamilu, taimakon da kayi mata ma an gode sosai, madallah. Allah yayi albarka.

    Jamilu bai ce komai ba ya juya ya fita don ya san tabbas Inna ta kullace su duka ahalin gidansu daga su har mahaifin su, don ma dai tana da kai zuciya nesa.

To bayan fitar sa kuma ta samu kanta da bude ledojin da ya aje musu, ta farko kayan shayi ne a ciki, da katon biredi (Laziz) sabon gashi, sai kayan marmari shake a daya ledar harda Tuffa da Inabi, daya ledar kuma gasashshen naman rago ne mai zafi sosai a ciki. 

    A lokacin Hauwa ta farka tun bayan kawo ta asibitin da kyar ta iya ta dan motsa, sai ta ji ta kamar a daddaure, koina na jikin ta ciwo, bata san me ya faru da ita ba, ta kai hannun ta da baa daure ba kan goshin ta tace wash! Inna tace sannu Kulu kin ji, tsautsayi ne da baya wuce ranar sa, mota ta buge ki, Allah dai ya dada kiyaye gaba. 

    Nosis suka zo suka bata magungunan ta, suka ce a bata shayi mai zafi ta sha, kuma zata iya cin wani abu, Inna tace basu zo da ruwan zafi ba, sai suka bata aron karamar heater ta jona ta hada mata shayi mai kauri da kayan shayin da Jamilu ya kawo.

Ta taimaka mata ta zauna a jikin filo tana bata shayin a baki har ta koshi, ta debo naman da zafin sa a faranti irin gasashshen naman nan ne na babbar tukuba mai ruwa-ruwa wanda da kasa a bakin ka ka tauna zaka ji ya baje tsabar laushin sa, wanda yaji yajin citta, Hauwa duk da jikin ta na ciwo taji dadin cin naman nan, don baza ta iya tuna yaushe rabon ta da cin nama ba, tun zamanin Likita Sarham na zuwa gidan su! Balle mai dadi da laushi irin wannnan ai sai zamanin Dr. Sarham. 

    Daga nan ta koma barci har dare bata tashi ba, Inna ta sallami Salele ya tafi gida bayan ta masa sautun abubuwan bukata da zai zo musu da su washegari har da filas din ruwan zafin su da hita.

Washegari yan dubiya fululu daga kofar Naisa, Salele ya barabada musu mota ta kade Hauwar Inna. Hauwar Inna mai jamaa kowa na son ta, koda makanta ta same ta jamaar unguwar su kowa kokari yake ya kyautata musu, musamman da aka san mahaifin ta ya bata, kuma Innar ta bata da matallafi sai Allah.

    Makwabta na ta tururuwar zuwa duba Hauwa kullum, koda Inna ta aika Salele don ya fada a makarantar su Hauwa kada aga bata zuwa, sai ga Malaman su Hauwa sun yo kungiya a motar makarantar su a washegari daga ‘special school Kano’, suka zo suka duba ta da kayan dubiya niki-niki, kasan yaro mai kokari da shiga ran malamai. Don haka a wannan jinya su Hauwa sun samu alheri sosai, don Jamilu ma kullum yana tafe, abin arzikin da zai kawo na yau daban na gobe daban.

Tun Inna na daure masa fuska tana korar sa a wayance, har ta fara gane Jamilu neman shiri yake yi sosai dasu, rannan ya kawo dafaffen abinci yace mata inji Hajiyar sa, da yake bata gidan mahaifin sa ita kuma tare suka yi yanmatanci da Inna, kusan lokaci daya Bilyaminu da Zakari suka aure su.

    Ta manta rabon ta da Rumanatu don tun Jamilu na yaro Zakari ya aunata gaba.

    Daga baya ma ya dauko Innar tasa ya kawo dubiya, nan suka baje ita da Inna a kan tabarma ana labarin yaushe gamo da tuna baya. A bakin Hajiya Rumanatu Inna ta ji cewa Jamilu yayi karatun shi mai zurfi har digiri a hannun ita mahaifiyar shi a boye, ba tareda Baabnsa ya san yana yi ba, tace yanzu haka Jamilu aikin Banki yake da bankin Afrika (United Bank of Africa) da akafi sani da UBA. Kuma da wannan aikin har yana taimakawa kannensa sosai da suke garari da gararramba a gari, matan yawanci an sako su suna gidan uban suna zawarci, tace yayan Zakari mata basa jimawa a gidan miji zaki ji an sako su, uban duk kudin da ya tara baya iya saya musu ko gasarar koko, sai dai ya je tukubar mai shayi a lafta masa kwai da shayi mai kauri, ta ce ai ita kam Allah ya cece ta da ya raba ta da gidan su Jamilu. 

    Ta shiga lissafo wa Inna yawan matan da Zakari ya aura bayan ita yana shika musamman bayan yayi kudi abun babu ko dadin ji.

Tace bayan rabuwar ta da Zakari ta yi aure ta haifi wasu yayan mata guda biyu Hansatu da Lami, duk ta aurar dasu. Shekarar baya Allah ya yiwa mijin ta rasuwa wanda ya rike mata Jamilu kaamr shi ya haife shi.

Har yamma kafin Jamilu ya zo daukar Hajiyar sa, suna tafe a hanya Hajiyarsa na bashi labarin irin mutuncin Inna Safiya tun suna yammata. Jamilu ya sosa kai, da damuwa yace.

 Hajiyata ina da magana, tuntuni, amma ina shakka, kin ga ba don halin Baban mu ba da illar da ya yiwa mutuncin mu gun Inna Safiya ba, me zai hana na auri Hauwa? Da ba sai kawai a yi yar gida ba ni da Hauwau? Rai kwance hankali kwance?”

     Hajiya Rumana ta ce cikin mamaki wai kana nufin kana son Hauwa din ne? Jamilu ya koma sosa keya da hannun sa daya yace gaskiyar maganar kenan, Hajiyarmu tun ranar da na buge ta, nake fama da zuciyata a kanta, zuciyata bata kara zama lafiya ba a kan tunanin yadda zan yi na mallake ta, kullum tunani na shine yadda alamarin zai yiwu cikin sauki, amma na hanga na duba ta bangaren Babanmu na tabbatar zan samu matsala sosai da shi.

    Jiya na je gaishe shi, na same shi na gaya masa tsautsayin da ya gifta na kade Hauwa, cewa yayi tun da na kaita asibiti na biya magani kada ya kara jin na koma inda suke.

Haj. Rumanatu ta ce umh, ni na rasa irin wannnan yan ubanci da yake yi wa dan uwan sa, shikadai ya rage masa amma ya kasa kaunarsa, wallahi shi bai dauke shi haka ba Bilyaminun, baka ga irin cin kashin da yake masa ba, haka yake masa tun suna yara saboda bakin cikin ya fi shi samu a sanaar sa ta gwanjo.

     Kaima dai Yayan Hansatu banda kana son taro aradu da ka, ba zaka kaiwa mahaifin ka wannan maganar ba. 

    Jamilu ya ce (with boldness) idan har Hauwa ta amince min in sha Allahu zan yi nasara a kansa. Hakan ne kadai zai gyara wannangurbataccen zumuncin ya rage kiyayyar idan mun haihu nida Hauwa. Ta ce “to idon ta fa? Zaka iya zama da makauniya Jamilu?

     Ba wai ina kin Hauwa bane saboda lalurar ta, tunda kuwa yar uwar kace jininka ce, amma akwai abun dubawa.

    Tarbiyyar yaya, dawainiyar cikin gida, abubuwa ne da sai mai ido zai iya yin su. Da aikin banki zaka ji, ko da kula da nakasassar mata a cikin gida musamman in ta fara haihuwa? Kaida in ka fita tun sassafe wani zubin sai dare kake tasowa?

     Don kuwa Hauwa, kasa a ranka in ka aure ta duk kai zaka yi mata wadannan abubuwan dana fada a can baya tana daga zaune tana fama da kanta. 

    Jamilu ya nisa cikin jin karin kauna da soyayya da tausayin Hauwa, sannan ya ce Hajiyata, a irin son da na samu raina yana yi mata, sam ban hango wadannan kalubalen ba, amma ni Jamil Zakari naji na gani, na yarda in har zan samu auren Hauwa, zan hadasu duka ita da yayanta in raine su in kula dasu har aikin bankin duka bazan kasa ko daya ba. Hajiya Rumanatu tausayi ya cika ta, ta dade da sanin dan ta Jamilu mutum ne har mutum, mai kyakkyawar zuciya akasin ta mahaifinsa, ta dade tana dakacen dama ace Bilyaminu ne ya haife shi, saboda halinsa na yawan kirki da nagarta shiyasa ma mahaifin sa sam bai cika shiri da shi ba don komai nasu Allah daya ne gari banban.

    Sai ta ce Allah ya tabbatar da alkhari a tsakanin ku idan akwai, ya huwwace maka lamunin mahaifin ka cikin sauki. Auren Hauwa hakika Jihadi ne babba zaka yi, na gyaran zumunci da kuma na taimakon miskinin da baida maraba da maraya.

****              ****               ****


    An sallami su Inna daga gadon asibiti bayan an kwance karayar hannun Hauwa ranar wata lahadi, ta dauka shikenan sun rabu da jelen Jamilu. Amma ina! Ashe wasa farin girki, lokacin nema Jamilu ya maida gidan su wajen zuwansa. Aka ce in kaga kare na sunsunar takalmi.

Wani babban abinda yafi bata mata rai, duk shiru-shirun Hauwa da miskilancinta in da Jamilu suke hira kaji ta har tana kyakyatawa tun daga soro, tana hira rai-rai-rai kamar kanari ita da shi, ta sake da shi sosai abin ki da jini! Asabar da lahadi da baya zuwa aiki a gidan su yake wuni, makale da Hauwa, Inna ta rasa yadda zata yi da Jamilu. Daga baya ya fito fili ya gaya mata shi fa kamun kanwarsa yake yi, da zarar ta kare sakandire zai kawo sadakinsa.

Inna kam bata yi kasa a gwiwa ba ta ce Jamilu kana wasa! Kaima ka san wannna abu ne da ba zai taba yuwuwa ba, don haka na roke ka daga yau kada ka kara tada wannan maganar mara yuwuwa.

    Ni bazan raba ka zumunci da yar uwarka ba, amma bana bayan wannan maganar wai auren zumunci kai da ita.

Jikin sa a sanyaye ya koma gida ranar, kuma kai tsaye ya yanke shawarar tunkarar mahaifin sa a kan maganar, a yi ta ta kare. Komai ta fanjama-fanjam.

Malam Zakari sai da ya bari Jamilu ya gama bayani kaf cikin kankan da kai, da tsananin ladabi ga mahaifin nasa, sai ya ce masa, kai kai kai! Kai kuma ta nan ka bullo? 

    Auren makauniya? Diyar BILYAMINU jafai a cikin zuria ta? Toh ban shirya haifar jikan da zai zo ya zama dan jagora ba. Ko ya gado makanta ya saka min a cikin zurria, ko babu makanta haihata-haihata jinina ya gogi na Bilya jafai, jinin jaraba jinin masifa jinin tsiya da rashin arziki. 

    Idan ka kuskura ka sake zuwa inda suke, idan na ji labari, sai na tsine maka albarka.

A gigice Jamilu ya bar gaban Baban sa, o ganain gabansa baya yi, shi kuma Zakari Jamilu na tafiya ya saka takalman sa ya fito ya rufo shagon atamfofin sa dake cikin Singa. 

    Da ya fafuri mota bai tsaya a koina ba sai a Badalar Kofar Na’isa.

Gidan ai ba zai taba bace masa ba, tunda kuwa gidan gadon su ne, Bilyaminu yayi masa karfa-karfa ya raba shi da shi, don haka kai tsaye ya tuna hanya, bayan tsayin shekarun da ba zai iya tuna yawan su ba rabon sa da ko bin hanyar.

    Zakari ya yi sallama a zauren Inna, da katotuwar murya mai razana wanda ake yimawa.

    Ta na tsakiyar dabbobin ta tana zuba musu dussa, ta ji muryar sa yana kwada sallama kamar zai tada gidan Safiya, ina Safiyar ne? Diyar masu Danjangabo?.

    Nan da nan zuciyarta tace mata ZAKARI!. Don shikadai yake kirata diyar masu Danjangabo don sanaar mahaifiyarta kenan. Inna ta dago kai cikin mamaki ta tako ta iso soron ta yi tsaye a gaban sa, bazata iya tuna rana ta farko da ya tako kafar sa gidan su ba tun bayan rigimar mallakar gidan, da a karshe ya sayarwa Malam Bilyaminu.

Ai bai kamata kiyi mamakin gani na yau ba, tunda ke kika takalo ni, kuma kin sanni farin sani kamar kashi nake, sai an kula ni nake doyi”. Zakari ya fada cikin gyara murya da gyara tsayuwa. Inna tace,

     dole in yi mamaki mana tunda dai na san banza bata kai zomo kasuwa yo daman ina kuwa zata kai shi? Sai ya ji wuta! 

    Zuwa nayi in ja kunnen ki, in sake ja, da kwantareriyar murya, in kin ji kin dauka, ki zauna lafiya, in kin ki ji ba kya ki gani ba. 

Ki saki kurwar Da na Jamilu ta shakata, don shi ba nakasashshe bane, haka kawai kin ga yaro da maikon sa shine zaki bi dare ki bi rana ki lika masa makauniya ko? Yo Allah na tuba ko Kulu idon ta hudu kinga ta dace da Jamilu yaro son kowa dan gata dan asali, mai ilmi, mai nasaba, Uwar Bilya kuwa ki bincika tarihi kiji inda uban mu ya samo ta, can ne cikin zuriar su barbushe da tsimbirbira. 

    Inna Safiya ta yi tsaki ta ce kana tunanin ko Hauwa ta rasa miji saboda makanta, ko tana yawo tsirara saboda talauci, zan dauketa na baiwa dan ka ko shugaban kasa ya zama? 

    Ai ni martabar diyata da kake gani, duk da take marar ido, miskiniya, wallahi tafi karfin gidan ka, wulakantaccen gida na rashin tarbiyyah, gidan da daga yan daba sai yan shaye-shaye, sai sauta ga wawa rututu. Uba daya uwa kowa da tasa, kurwar ya ta kurr da shiga irin wannan laanannen gidan na Allah wadai, in sha Allahu.

Zakari ya kyabe baki duk da ya ji mugun ciwon maganganunta, ya ce ni dai na gaya miki, kuma aure-aure ai arziki ne, idan fitsari banza ne kaza tayi mana, shi bai iya ya kara ko daya ba saboda talaucin da yasa shi barin gida, ke da aka gudu aka bari bakin jini yasa ba wanda ya taba zuwa ya sunsuna ki da sunan aure, a haka zaki mutu gwauruwa, da makauniyar ya a gaban ki kina mata tsarkin kashi. 

    Daga yau zan zuba C.I.D a kofar gidan nan, aka kara gaya min an ga Jamilu ya shigo, duk abinda ya same ki ke da makauniyar yar taki ku kuka da kanku, ke kika saya muku da kudin ku, lakadan.

Ya juya ya tafi, ya bar Inna tana tsaki. Juyawar nan da zata yi sai taga Kulu a bayan ta curko-curko da ita, manyan idanun ta kamar sa fado kasa don tashin hankali, tayo waje dasu bakidaya. Inna tayi kwafa tace,

     gara da kika ji da kunnen ki, irin tijarar ubansa, marar lissafi, gobe ki kara tankwashe kafa kina hira da Jamilu da sautin murya kamar na gyare, a zo a ci mutuncina ban ji ba ban gani ba.

     Jamilun da kin riga kin san waye ubansa, ko wanene Zakari ba bakon ki bane ba.

Jamilun bai san an yi haka ba a washegari ya zo wa Hauwa sallama zai wuce wani workshop’ da banki ya tura su na sati daya a jihar Delta. 

    A take kuwa aka kira Alhaji Zakari a waya aka gaya masa, ga Jamilu nan ya sake zuwa.

A ranar, duk da Inna na cikin bacin rai, haka ta hadiye shi, ta zaunar da Jamilu a gabanta, cikin lalama ta roke shi Allah Annabi ya rabu da Hauwa-Kulu, kada ya kara zuwa gidan su.

    Ta warware musu shi da Hauwan irin tsohuwar gabar da ke tsakanin iyayen su maza tun kafin a haife su, a sanadin yan ubanci kawai, ba wani kwakkwaran dalili. Ta kuma gaya masa ita a yanzu girma ya cimmata, bata fama da ciwukan zamani ko guda daya, don haka bata son abinda zai tada hankalin ta.

    Ta ce masa Hauwa kuma ka gani nakasa ta same ta, wadda tasa bazan iya yi mata aure ba sam-sam, balle na kai ta cikin iyalin Zakari, zai iya hura wuta ya babbaka min ita, a karshe Inna tace.

     “Jamilu daga ni sai kuma Allah kadai muka ragewa Hauwa-Kulu, ni kadai ce karfin ta a yanzu, don haka ina tattalin rayuwar ta ne bazan iya kaita inda bazata taba samun kwanciyar hankali ba, koda zan mata auren, balle in kaita gidan ku. Balle kuma bazan taba yi mata aure ba in ba idanun ta ne suka dawo ba. Don haka na roke ka Allah da Manzonsa kan a bar zancen nan daga yau, anan inda zamu ajiye shi.

    Jamilu na yarda kai mutumin kirki ne, zuciyarka ba irin ta mahaifinka bace, kai daya ne cikin dubu a gidanku, kuma kai mai nufin Hauwa da alheri da soyayya ne, duk da lalurarta ka amince ta zamo maka uwar iyali a haka, babu wata kauna da taimako da soyayya da wani dan adam zai nuna ma Hauwa a duniya da ya wuce wannan a doron kasa. Hakika mun yaba maka, mun kuma gode maka, domin ka so kayi jihadi ne kuma Allah zai baka ladan niyya.

    Amma komai zamuyi sai da yardar iyaye zai yi albarka Jamilu ka sani, ina kuma tabbatar maka ba zaka taba samun albarkar mahaifin ka ba in kana tare da Hauwa-Kulu”.

Jamilu Zakari, yasa hankaci yana tsane tulin hawayen idon sa, ya fahimci Inna sosai, yau kam ya fahimci bata kinsa da Hauwa kamar yadda yake zato a baya, ya fahimci abinda ada ya kasa fahimta, wato su iyayen Hauwa da nasa mahaifin, bazasu taba zama a inuwa guda ba, a sanyaye Jamilu yace.

    “Inna na ji ki, na kuma fahimce ki, amma ku sani daga ke har Babana; Hauwa yar uwa ta ce ta jini, baa raba hanta da jini, ni kadai na rage mata matsayin Uba kuma dan uwa a yanzu.

     Maganar aure tsakanin mu na bar ta har abada! Amma ni Jamilu daga yau nine Yayan HAUWA-KULU na halali kuma Uban ta na jini, daga nan har karshen rayuwar ta, ko kuma ranar da mahaifin ta ya dawo na damka masa yar sa a hannunsa.

Kiyi min alfarmar cigaba da zumunci da ita, da kula da ita, tunda na hakura da maganar aurenta, ba don komai ba sai don samar muku kwanciyar hankali amma ba don na daina sonta ba, don ni da kaina na san Babana hatsabibi ne”.

Inna ta rasa kuma me zata ce. Ta rasa Jamilu kowanne irin mutum ne da baya gane abinda zaa shekara ana ganar da shi.

Da zai tafi ya kawo kudi masu yawa ya baiwa Inna, shi kan sa baisan adadin su ba, yace su yi amfani da su kafin Allah yayi masa dawowa daga tafiyar da ta same shi zuwa Delta.

Jamilu ya tafi Delta da kwana biyu aka yi sallama da Inna a zaure, maza ne magidanta su uku, nan suka gaya mata yaya har yanzu bata tashi daga gidan ba? 

    Inna ta ce wane gidan? Sai suka hau mata bayanin wannan data ke ciki yanzu, saboda mai gidan yana so zai rushe shi, zai mayar da wajen kamfanin buga ruwan leda, ko ba a gaya mata an bata notice din tashi na kwana uku ba? 

    Inna tayi musu kallon banza ta ce ban gane ba? Anya nan gidan kuke nema? Nan dai gidan Malam Bilyaminu Kofar Na’isa ne, wanda ya gada daga tsohon sa.

     Ya gada ko suka gada?.

     Mutumin ya gyara mata zance cikin gatse. Kafin ta bashi amsa yace to ai shi Zakari ya riga ya sayar mai da gidan a gaban wadannan shaidun”, ya nuna mutanen da suke tare, wadan da yan unguwar ne abokan Zakari, sannan ya fiddo ainahin takardun gidan ya nuna mata, wadanda Innar bata san ina aka je aka samo su ba.

Suka ce lallai suna son gidan su zuwa gobe, don zaa zo a rushe shi goben, da sauran gidajen da aka saya na makwabtan su.

Da fadin haka Inna ta rasa abinda zata yi, sai kawai ta saka kuka tana cewa su koma su gaya wa Zakari ta sallami dan sa Jamilu in dai a kan sa ne zai mata wannan tozarcin. Ko sauraron ta basu yi ba suka tafi.

Har washegari Inna ta kasa gayawa Hauwa maganar nan, tana ta fama da ita a kirjin ta dake faman zabalbala, zuwa yamma kuwa wasu tsagerun samari suka shigo suka soma fatali da kayan Inna suna jefo komai waje. Suka ce suma saka su aka yi. Ga masu rusau nan zuwa, in sun ki fita ta arziki zaa rushe har da su suna ciki.

     Yadda ake jifa da kayan Inna a unguwar ya janyo hankalin daukacin jamaar unguwa, suka taru don neman baasi, amma ba wani bayani sai na maigidan ya sayar da shi, ita kuma Inna an ce ta fita ta laluma taki fita. Inna na kuka, Hauwa kuwa don taurin da zuciyar ta tayi idon ta ko kyallin hawaye babu, amma ya kada ya yi jajir, jakar makarantar ta lalubo da gilashin ta da Sarham yayi mata ta sakaya idanunta, ta goya jakar ta mai dauke da komai nata na makaranta ta kama hannun Inna, kamar itace mai idon ba Inna ba, Hauwa tace.

     Kada ki damu Inna muje, Baba Zakari ya kara arziki da gidannan don Allah, in don ni ko a tashar mota da karkashin gada zan iya kwana, in dai idan gari ya waye zan je makaranta, ba kuma zaki bar ni in yi “bara” don bana gani ba.

Inna ta kasa magana sai kuka, a haka ta yafa mayafin ta ta kulle kayan ta da zata iya dauka a bakko, ta kama hannun Hauwa suka fice daga gidan. 

Gidan su mai tsohon tarihi! Gidan da tayi dukkan rayuwarta da yaya da mijinta, sama da shekaru talatin. Gidan da ba abinda take so a rayuwarta sama da shi.

    Ga Hauwa kuwa wannan gidan na bayan Badala shine farin cikin ta, da shi kadai take tuna ta rayu tare da mahaifinta.

    Ko minti goma basu yi da fita ba, masu rusau din suka iso, cikin dan lokaci suka hau rushe gidan Malam Bilyaminu. Kafin dare sai kasar gidan da duwarwatsu, Dabbobin Inna kam tuni sun yo waje da suka ji su a bude babu turke. Sai Malam Isa da ya dawo kasuwa ya ga dabbobin a kofar gidansa aka kuma gaya masa abinda ke faruwa wato Zakari ya kwace gidan ya sayar su kuma wadanda suka saya sun rusa, Hauwa da Inna suna tsaye a kofar gidan sa ake ta rushe gidansu akan idon su, sai ya tattara dabbobin ya kora su wani kango na gidan sa ya rufe su.

     Jamaar unguwa suka yi dafifi suka hana Inna barin unguwar suka ce tunda dare yayi ta shiga gidan Malam Isa zuwa gobe, dattijan unguwa sun ce ta zauna gobe a shigar da karar Zakari a kotu. Don mai unguwa ya dade da rasuwa.


Saidai cikin daren, a gidan Malam Isa, inda aka baiwa su Inna mafaka, Inna ta canza shawara, ba ita ba shiga kotu a rayuwarta saboda abun duniya, a wurin mutanen da shiga kotu na nufin karshen tozarci ga mutuncin su kenan, meye abun duniya wanda duka mutuwa zaayi a bar shi a inda yake?

  A gidan Malam Isa suka kwana dakin matar sa Mai kosai, da asubahi ta kama hannun Hauwa ta dora kayan su a kanta, suka faki idon kowa suka bar gidan Malam Isa. A lokacin shi yana masallaci sallahr asubahi, matar sa kuma tana daka tana jan rago (munshari). 

Kai tsaye Inna da Hauwa suka naushi hanyar fita daga BADALAR Kofar Naisa, ba don sun san inda suke nausa kafafun su ba, ko suna da wurin zuwa, burin Inna kawai su yi nisa da kusa da duk wata Badala ko Kofa da Zakari yake ciki ba kofar Naisa da Kofar Dan agundi kadai ba, kasancewar kofofin biyu suna makwabtaka da juna. In haka ne kuwa sai dai su bar duka kwaryar BADALOLIN KANO bakidayansu, kafin su iya yin nisa da Zakari, in ba haka bata tabbata zai sake biyo su ne ya batar da ita itama in ta tsaya shariah dahi a kotu, kamar yadda take da kyakkyawan zargin shi ya batar da dan uwan sa mijinta Malam Bilyaminu! 

    Hanyar da ya bi ya batar da shi dinne bata sani ba har gobe. Ta san dai ko don ya ganewa idon sa irin tagayyarar MISKINIYAR yar dan uwan sa a rayuwa da ya hana dan sa mai lafiya ya aura ta tabbata Zakari zai sake biyo su. Don haka dole ta dauke HAUWA-KULU suyi nisa da BADALOLIN KANO bakidaya, don dai ta nisance shi, ta kuma kare Hauwa daga kiyayyarsa da zalincinsa da hassadarsa. 

    Daga yau tayi kudurin zamewa Hauwa GARKUWA daga dukkan abinda zai cutar da ita musamman kanin Uban nan nata, Zakari, wanda yau ta kara tabbatarwa baya nufin su da alheri. Tayi kudurin cika burin masoyin su na hakika wato “Dr. Sarham” akan Hauwa, na ta tsayawa Hauwa komai runtsi ta samu rabauta daga ko ilmin sakandire ne, ba tare da ‘makanta’ ta zame mata shinge (barrier) ga neman ilmi da cigaban rayuwa ba.

    Tayi kudurin in har tana raye, da yardar Ubangiji sai Zakari ya ci arzikin dan uwansa Bilyaminu a rayuwa. Idan kuma malam Bilyaminu baya raye, ita SAFIYA UWAR HAUWA tana raye! Aka ce Uwa mafi Uba… koda uban Sarki ne.

    

    ****            ****      ****

                        

Tafiya suke ba tare da sun san inda suke jefa kafafun su ba, tsabar bacin rai yasa Inna bata ko gajiya da tafiyar da suke dirka, amma Hauwa tun baa yi nisa ba ta sare, tace “Inna na gaji”, Inna tace daure Hauwa, bana so makwabtan mu su biyo bayan mu su cimmana, bazan zame wa kowa nauyi ba, ba kuma zan zauna cin arzikin kowa ba sai na Ubangiji, don haka bazan zauna a gidan makwabta in hada su fada da iyalin su ba, musamman Malam Isa, kin dai san halin Mai kosai ba taso a rabe shi.

     Hauwa ta daure suka cigaba da tafiya har suka yi wa kofar Nasarawa fintinkau, ita kanta Inna bata san ina suke jefa kafa ba, kofofin cikin gari kawai take so su bari, sai da garin ya Allah ya waye rana ta fito, yunwa da gajiya suka sa Hauwa ta ce to Inna dan tsaya in huta ko na minti biyu ne.

    Suka tsaya a daidai sakateriyar gwamnati ta Audu Bako, suka zauna suna hutawa. Sai lokacin Inna ta tuna da kudin da Jamilu ya bata, cikin kunshin kayan ta, saboda yawan kudin ta san ba cikin hayyacin sa ya bata su ba, domin sun kai naira dubu biyu. Ta saka hannu cikin bakkon su, ta tabbatar suna nan, sai ta ce,

     “tashi Kulu mu hau abin hawa zuwa tasha, na tuna akwai kudi cikin kayanmu”.

     Kulu ta kwalalo manyan idanun ta waje, ta ce tasha Inna? Kano zamu bari? Kanon Dabon? Gari ba Kano ba dajin Allah Inna.

     Ai ni da kike gani na nan Inna, ban iya zuwa koina in bar mahaifata KANO saboda wani Kawu Zakari. In muka yi hakan ai ya ci galaba a kan mu kenan, ya raba mu da KANO farin cikin mu, tushenmu, tsatson mu, cibiyar mu, jihar mu ta gado. 

    Ni dai Inna ko a karkashin gada ne zan dinga kwana in dai ina cikin kwaryar Kano, ruhina yana Kano, zuciyata tana mahaifata, in muka bar Kano Baba ya dawo ina zai gan mu? Kuma makaranta ta fa Inna? 

    Sai ta fashe da kuka cike da tsoron, halin da karatunta zai shiga. A da kam, bata karaya ba, amma yanzu ta fara karairayewa, karfin halin ta ya kare, kuzarin jikin ta ya kau, data fara hango illar da Zakari ke son yiwa rayuwar su tunda muhalli shine rayuwa, ta san yanzu itada karatun sai wani babban ikon Allah, a lokacin da ya zo gangara tunda basu da matsuguni, bata san me Zakari ke nufi da su ba sai yanzu, me yake nufi kuwa banda su koma yin bara bisa titi da kwana a kasan gada? Matattarar duk wani abin cutarwa a matsayin su na mata ba maza ba. Inna ta rasa yadda zata yi da Kulu, don kukan nata har da gunji da majina ita atafau bata barin Kano saboda Zakari. Inna ta ce,

     “to Kuluwa sai ki gaya min ina zamu je in muka zauna a Kanon, gida dai kina gani akan idon ki aka rushe shi, takardun gidan na hannun su, don haka ni banida sauran buri a zaman kasar Kano da cikin BADALOLInta”.

    Hauwa-Kulu tace ko kan dutsen Dala da Gwauron dutse ne mu hau mu zauna, ai dai muna cikin Kano, kuma can babu mai rushewa, sannan idan gari yaw aye zan iya zuwa makaranta komai nisan dutsen in dawo in tadda ke anan. Inna ta ce cikin takaici, to “huda-huda, mungu Park uwar yan boko, ana ta makwanci da abinda zaaci ma babu, kina ta zancen wata makaranta? 

    Da idon uban wa zaki je makarantar daga kan dutsen Gwauron Dutsen?”

    Da ace cikin nutsuwarta ta ke, da kuwa ta tada ballin Inna ta mata gorin ido.

    Amma da yake babu nutsuwar ko ta kwabo a tare da ita bata tuna wannan ba, Hauwa tace da mahaifiyarta Inna.

    Inna kada ki manta kin yi ma DAN KI SARHAMU alkawarin duk runtsi ba zaki raba ni da makaranta ba, kin masa alkawarin cika masa burin sa in kammala sakandire, alkawari abu ne mai girma Inna, in ban je makaranta ba Inna ba abinda zai raba ni da BARA watarana. a matsayina na makauniya-miskiniya- musaka!.

    Ai jin furucin Hauwa haka wanda ya taso ya fito kai tsaye daka kasan zuciyarta da jijiyoyin wuyanta da suka mimmike. Inna taji kamar Hauwa ta bata vibe, ta zuba mata allurar karfi da kuzari daga sarewar data fara yi. Sai ta samu kanta da tare abin hawa (ba tare da tunani na biyu ba) ba kuma da ta san inda zasu nufa ba ta dai yarda bazasu bar Kano ba, zama daram! Domin ta yarda HAUWA-KULUnta ta fita gaskiya kuma ruhin HAUWA shine GIDANSU NA BADALA!!!

    

    ****        ****          ****

               MURFIN LITTAFI NA DAYA

    

    Abin tambayar anan shine; shin jarumar cikin BADALA (HAUWA-KULU) zata koma da rayuwar ta cikin BADALAR KOFAR NAISA inda ruhinta dana iyayenta yake, ko kuwa ta fito wajen gari kenan tana walagigi???


    Shin burin masoyin su na hakika (DR. SARHAM ABBAS SHANONO) zai cika akan HAUWA-KULU na ta samu koda ilmin sakandire ne ba tareda nakasar ido ta zame mata shinge (barrier) ba, ganin cewa tun baaje koina ba a bayan tafiyar sa, rayuwa ta juyawa Hauwa da Innarta upside-down??? 


    Wanene PACE-SETTER din Barr. H. Bilyaminu kuma sai yaushe zai bayyana a rayuwar yar cikin Badala Hauwa-Kulu???

     

    Shin Hauwa-Kulu zata yi rayuwar aure da tara iyali kamar kowacce mace, ko kuwa nakasar ido zata zame mata shinge (barrier) ga cikar farin ciki da dan adamtaka, kamar yadda take zamewa mafi yawan akasarin masu lalurar idanu irin nata???

     

Ina labarin mahifinta Malam Bilyaminu? A mace yake ko a raye???

Amsoshin duka wadannan tambayoyin in sha Allahu suna cikin littafin HAUWA-KULU kashi na biyu. 

    

          

    Daga taku har abada;

     Sumayyah Abdulkadir

     (Takori).

          2/09/2023 



         



Post a Comment

0 Comments