TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 81-82

 *TUNATARWA*:



_Ka/ki zamo mai magana, amma idan za ka/ ki fad’i ka/ki fad’i alkhairi_.



_Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka/kin iya ma kowa_.



_Ka/ki so abin duniya, amma kar hakan yasa ka/ki mance da lahira_.







81-82



San da ta shiga ba ta ganshi a falon shi ba, hakan yasa ta nemi guri ta zauna.



Ya d’an jima a zaune a d’akin bai ji shigowar Nana ba, hakan yasa ya fito da niyyar ya fito falo ya jira ta.



Yana fitowa ya ganta zaune a falo.



"Khadihah ya kika zauna a falo, ki zo mu shiga daga ciki" cewar yaya Faruk.



Tashi tayi ta bi shi ba tare da ta ce komai ba.



Gefen gado ta nemi guri ta zauna tana wasa da hannun ta da ke sanye da azurfa.



Yanayin ta ya nuna a takure take da zaman.



"Khadija ki shiga cikin bayi ki yi alwala" yaya Faruk ya fad’a.



"Toh" ta amsa mishi.



Bayin ta shiga ta d’auro alwala kana ta fito ta zauna.



Tashi yayi suka yi sallar nafila raka’a biyu, bayan sun idar ne ya kama kanta ya dinga jero musu addu’o’i akan Allah ya basu zaman lafiya.



K’aramin frij d’in da ke d’akin ya tashi ya d’akko musu fresh milk.



Mik’a mata fresh milk d’in yayi ta amsa tare da cewa "Na gode".



Murmushi kawai yayi ya nemi guri ya zauna.



A hankali ta dinga sipping d’in fresh milk d’in, kad’an tasha ta ajiye sauran.



Kallon ta yaya Faruk yayi, a ranshi yana yabawa da natsuwar ta, komai za tayi tana yin shi ne a natse, hakan yasa take k’ara burge shi.



Tashi tayi ta d’auki ragowar fresh milk d’in ta maida cikin frij d’in.



Kallon yaya Faruk tayi ta ce "yaya Faruk sai da safe".



"Ina zaki tafi?" yaya Faruk ya tambaye ta a tak’aice.



"Zan je in kwanta ne" ta bashi amsa.



"Ba sai kin koma side d’in ki ba, ki yi kwanciyar ki a nan".



Jim tayi kamar mai tunani, a lokaci d’aya kuma mamakin yaya Faruk take yi da y ace ta kwanta a d’akin shi, bayan yau kusan watan su d’aya da aure bai ta’ba gayyatar ta kwana a d’akin shi ba sai yau.



Can k’arshen gado taje ta kwanta, yanayin kwanciyar ta kad'ai in ka kalla Kasan a takure take.



Laptop d’in shi ya d’akko ya fara danna wa, ya d’an jima a zaune yana danna laptop d’in.



Jefi-jefi yakan tsayar da danna laptop d’in da yake yi yana kallon Nana, ganin har yanzu ba tayi bacci ba, ga hijab da ta kwanta dashi yasa ya ce "Khadija ki cire hijab d’in nan, na ga kamar ya takura miki".



In ban da ba ta son yi ma yaya Faruk musu, da ba za ta cire hijab d’in ba, dan za ta fi takure fiye da yanzu.



Cire hijab d’in tayi ta linke shi ta ajiye a side bed.



Ba ta wani jima da kwanciya ba bacci ya d’auke ta.



Ganin tayi bacci ne yasa ya rage AC d’in da ke sanyaya d’akin, tashi yayi ya lullu’ba mata tattausan bargo.



Sai da ya gama aikin da yake yi a cikin laptop ya kashe kana ya kashe bulb d’in d’akin, ya kunna dim light.



Kwantawa yayi ya ci gaba da kallon Khadija da ke faman baccin ta, fuskar ta sai wani shek’i take yi kamar ba bacci take yi ba.



Lokaci d’aya yaji tausayin ta ya kama shi na tsawan wata d’aya da ya d’auka ba tare da tasan miye aure ba, gashi ba ta ta’ba nuna mishi alamun jin haushin shi a fuskar ta ba, yasan abin na damun ta.



Matsowa yayi kusa da ita, hannun shi ya kai kan fuskar ta, wani irin laushi yaji san da ya shafa fuskar ta, haka ya ci gaba da shafa fuskar ta har ya kai kan lips d’in ta, bai tsaya a nan ba ya fara shafa jikin ta.



Lokaci d’aya ya ji ba abin da yake buk’ata illah ya kasance da Khadija.



Kiss ya kai mata a goshin ta, a hankali ya gangaro zuwa le’ben ta ya manna mata kiss, a hankali yaya Faruk ya dinga sakar mata wani irin French kiss, haka yaya Faruk ya dinga aika mata kiss ko ta ina, lokaci d’aya yana shafa ta.



Daga nan labari ya fara canzawa a gurin yaya Faruk.



Ita kuwa Nana tun san da yaya Faruk ya fara shafata ta farka, sai dai ta k’i bud’e ido duk da tana tsoron abin da yaya Faruk yake mata, ga wani irin sak’o da yake aika marta da ya kashe mata jiki kasancewar wannan shine karo na farko da hakan ya kasance a tsakanin su.



Haka yaya Faruk ya ci gaba da sarrafa Nana yanda yake so, sam ya manta da cewa budurwa ce kuma wannan shine karon ta na farko da hakan ya ta’ba kasancewa da ita.



Ganin yadda yaya Faruk ya haukace mata yasa ta fara bashi hak’uri tana kuka, shi kuwa yaya Faruk duk wannan kukan da Nana take yi kamar k’ara ingiza shi take yi, tun tana kuka a hankali har kukan na ta ya fito fili, tsoron ta shine kar a ce allurer sojoji ce ta motsa zai sauke a kanta, da ko ta gama yawo, mutsu-mutsu ta fara yi ganin duk rok’on da tayi ma yaya Faruk bai san tana yi ba, tun tana ganin za ta iya jurewa har takai ga ko jikin ta ba ta iya motsawa, hawaye ne kawai yake zuba a idanun ta saboda gajiya da tayi da kuka.



Yaya Faruk sai da ya sami natsuwa da ita kana ya ga aika-aikar da ya aikata mata.



Kiran sunan ta yayi amma ba ta amsa mishi ba, sabod yadda bakin ta yayi nauyi ba ta jin za ta iya magana.



Ga dai idon ta a bud’e tana kallon shi, in ban da hawaye da yake ci gaba da zuba a idanuwanta saboda wahalar da ta sha a hannun yaya Faruk.



Tashi yayi ya shiga band’aki yayi wankan tsarki ya fito.



Yadda ya bar Nana haka ya zo ya tarar da ita, hakan yasa ya tsorata.



Da sauri ya hau gadon ya tallabo ta jikin shi.



"Sorry Khadija, I don’t mean to hurt you, nasan ban kyauta miki ba da na tafiyar dake a haka, bazan sake ba kin ji".



Ganin har yanzu ba ta ce mishi komai ba yasa ya ci gaba da cewa "Plsss Khadijah ki fad’a min in da yake miki ciwo, ko na ji miki ciwo ne?" ya k’arasa maganar da tambayar ta.



Har yanzu dai Nana ba ta bud’e baki tayi mishi magana ba, duk da tana jin abin da ya fad’a mata.



Tsoro ne ya k’ara kama yaya Faruk ganin re-action d’in Nana, kwantar da ita yayi ya sa mata pillow, tashi yayi ya d’ebo ruwa a bowl.



Shafa mata ya dinga yi a fuskar ta, wata ajiyar zuciya ta sauke, hakan da tayi ne yasa hankalin shi ya fara kwanciya.



Ajiye bowl d’in yayi ya dawo da kallon shi gare ta ya ce "Sannu Khadijah".



Sunkuyar da kanta tayi ba tare da amsa mishi ba.



"Za ki iya tashi ki yi wanka, ko in kai ki bayin" yaya Faruk ya tambaye ta.



"Zan iya" ta fad’a cikin sanyin murya.



A hankali ta sakko daga gadon, tafiya ta fara yi da niyar shiga band’akin, juwa ta fara d’ibar ta ganin ba wani k’arfi a jikin ta.



Sauran kad’an ta fad’i yaya Faruk ya tashi ya rungumeta ta fad’a jikin shi.



Kwantar da ita yayi akan gado yaje ya had’a mata ruwan d’umi kana ya dawo ya d’auke ta ya kai ta band’akin.



Duk yadda ya so ya taimaka mata Nana ta k’i, hakan ya sa ya k’yale ta dan bai son takura mata.



Dawowa yayi ya canza bedsheet d’in.



Tausayin Nana ne ya dabaibaye zuciyar shi da dukkan sassan jikin shi, yasan ba k’aramin wahala ya ba ta ba, yasan Nana tayi k’ok’ari wajen jure ma buk’atun shi, wani irin feeling ya fara ji a zuciyar shi game da Nana, sai dai ba zai iya fassara wwani irin feeling ba ne.



 Lumshe idanun shi yayi ya fara tunano halin da suka kasance a awowin da suka wuce, tsintar kanshi yayi cikin wani irin farin ciki da annashuwa.



Wani irin girma da matsayi ya k’ara ba ma Nana a zuciyar shi.



Nana kuwa tun da ta gama abin da take yi a band’aki ta kasa fitowa saboda kunyar yaya Faruk da take ji.



Ganin har yanzu ba ta fito daga band’aki ba yasa yaya Faruk ya tashi ya je yayi knocking d’in k’ofar.



Bud’e k’ofar tayi ba tare da ta fito daga band’akin ba.



Ganin ta yaya Faruk yayi ta jingina da tiles d’in da ke manne a jikin bangon bayin.



Su na had’a ido tayi saurin sunkuyar da kanta.



Murmushi kawai yayi ya shiga cikin band’akin ya rik’o hannun ta.



Zaunar da ita yayi a gefen gado ya fita daga d’akin.



Side d’in ta ya tafi ya d’akko mata wata night gown d’in kana ya dawo side d’in shi.



Mik’a mata rigar yayi ta amsa.



Kasa sa rigar tayi a gaban shi, hakan da ya fahimta ne yasa ya ce "Khadijah ki sa rigar".



"Zan sa" ta bashi amsa a tak’aice.



Tashi tayi ta koma band’akin tasa rigar, ta d’aura hijab d’inta a kai kana ta fito daga band’akin.



Zama tayi a bakin gado ta sunkuyar da kanta, sam ba ta son su had’a ido dashi saboda wani irin kunyar shi da take ji.



"Zo ki kwanta Khadijah" yaya Faruk ya fad’a cikin taushin murya.



Kamar wadda take jiran a ba ta umarni, tashi tayi ta zo ta kwanta dan dama jikin ta ba k’arfi.



Ba ta wni jima da kwantawa ba bacci ya d’auke ta.



Yaya Faruk jefi-jefi ya kan kalle ta ya lumshe ido kana ya saki murmushi.



Shi ma tashi yayi ya zo ya kwanta kusa da ita, nan bacci ya d’auke shi.



Kiran sallar asuba ne yasa ya tashi ya nufi band’aki ya d’auro alwala, san da ya fito ya ga har yanzu Nana bacci take yi ba ta tashi ba, tunani ya fara yi ya tashe ta ko ya bari sai ya dawo daga masallaci, zuciyar shi tafi karkata akan ya tashe ta tayi sallar, in yaso in tayi sallar sai ta koma ta kwanta.



Kunnen ta ya je yana hura wa, hakan da yaya Faruk ya ke mata ne yasa a hankali ta bud’e idanun ta.



Tana ganin yaya Faruk kusa da ita tayi saurin rufe idanun ta, hakan da yaya Faruk ya ga tayi ne yasa shi sakin murmushi ganin tsakanin jiya da yau Nana kunyar shi take ji, ba ta son su had’a ido.



A hankali ya ce "Ki tashi ki je ki yi sallah Khadijah an kira, zan je masallaci in dawo, in ki ka yi sallar sai ki kwanta".



Duk wannan maganar da yaya Faruk yayi bai sa ta bud’e idanun ta ba, hakan ya sa ya mik’e da niyyar tafiya masallaci dana san abin da ya fad’a taji, kunya ce ba za ta bari ta bashi amsa ba.



Bayan tafiyar shi masallacin ne ta tashi tayi sallar, bayan ta idar ne ta yi azkar d’in ta da addu’o’in ta kana ta tashi ta koma ta kwanta.



San da yaya Faruk ya dawo daga masallacin ya tarar da ita ta koma baccin.



Qur’ani ya d’auka ya koma falo ya zauna yana muraja’a, ya jima a zaune yana muraja’ar kana ya koma d’aki ya ajiye qur’anin.



Kitchen ya nufa ya d’aura musu breakfast ya jera shi akan dinning table kana ya koma d’akin.



Wanka ya shiga yayi kana ya fito ya shirya cikin wani tsadadden yadi.



Har yanzu Nana ba ta tashi daga barcin da take yi ba, kusa da ita yaje ya zauna ya shafa fuskar ta, zafin da yaji ne yasa yayi saurin d’aura hanun shi a dokin wuyan ta, nan ma wani zafin yaji da yafi na fuskar ta, hakan ya tabbatar mishi da zazza’bi ne ya rufe ta.



A hankali ya fara kiran sunan ta "Khadija".



Bud’e idon ta tayi ta kalle shi kana ta lumshe idanun ta saboda yadda baccim bai ishe ta ba, ga kuma zazza’bi da ya rufe ta.



"Kar ki koma baccin kin ji Khadijah, kwanciyar ta isa haka, na ji zafi a jikin ki ko ba ki da lafiya ne" ya k’arasa maganar yana kallon ta.



D’aga mishi kai tayi alamar Eh.



Tausayin ta ne ya k’ara kama shi dan yasan shi ya jawo mata wannan rashin lafiyar.



Tashi yayi ya je ya had’a mata ruwan wanka kana ya rik’o hannun ta ya kai ta bayin.



D’akin ta ya je ya d’akko mata wata doguwar riga na material da d’ankwali ya dawo ya ajiye mata akan gado.



Falo ya fito ya zauna yana jiran ta, dan yasa in ta fito wanka ba za ta iya shiryawa a gaban shi ba.



Nana na fito wa ta ta gogo jikin ta da d’an k’aramin tawul d’in da ke rataye a wata hanger ta musamman dan shanya tawul.



Mai ta shafa ta d’auki rigar ta sa kana ta d’aura d’ankwalin ta fesa turaren da ta gani a gaban mirrow d’in shi had’in saudiyya.



Fitowa daga d’akin tayi tana tafiya a hankali, daga gani har yanzu ba ta jin dad’in jikin ta.



Nesa dashi ta zauna kana ta ce "Ina kwana yaya Faruk".



Murmushi yayi kana ya amsa da cewa " lfy lau Khadija, ya jikin naki".



"Da sauk’i" ta amsa mishi.



"Yanzu ina ne yake miki ciwo?" yaya Faruk ya sake tambayar ta.



"Ba inda yake min ciwo" ta amsa mishi.



"Zo nan Khadijah" ya k’arasa maganar yana nuna kusa dashi.



A kunya ce ta taso ta zauna kusa dashi.



Hannun ta ya rik’o yana sakin wani tsadadden murmushi kana ya fara magana a hankali "Khadija na gode da kyautar da kika min mai mahimmancin, na gode da mallaka min kanki da kika yi, baki na ba zai iya fad’an farin cikin da nake ciki ba, duk yadda zan gode miki nasan yayi kad’an, ba abin da zan ce miki sai dai in ce na gode Khadijah, Allah ya saka miki da alkhairi ya miki albarka".



Sunkuyar da kai tayi kana a hankali ta ce "Amin".



Kwantar da kanta yayi akan kafad’ar shi, hannun shi ya kai kan dokin wuyan ta ya ji har yanzu da zafi a jikin ta.



Kallon ta yayi ya ce "Khadijah kika ce ba in da yake miki ciwo, gashi na ta’ba jikin ki na ji da zazza’bi, taso mu je muyi breakfast sai in kai ki asibiti a duba ki".



Hannun ta ya rik’e suka tafi dining suka zauna, da kanshi yayi serving d’in ta.



Bayan sun gama breakfast d’in ne ya ce ta d’akko hijab (himar) d’in ta su je asibiti.



Suna zuwa asibiti likita ya duba ta, magunguna da shawarwari likitan ya ba yaya akan nan gaba kar ya k’ara kwatanta ya da ya tafiyar da Nana kana suka ma Likitan sallama suka tafi.



Tun da suka dawo gida yake tarairayar ta, motsi kad’an za tayi zai tambaye ta ina yake mata ciwo, ita kanta mamakin yaya Faruk take yi ganin yanda ya damu da halin da take ciki.



Wayar shi ya d’auka ya kira yaya Mus’ab.



Bayan ya d’auka ne suka gaisa kana yaya Faruk ya d’aura da cewa "Mus’ab in ba damuwa kasa Madam ta dafa mana da abinci zan zo in amsa".



Yaya Mus’ab ne ya ce "Ina Nanan take da ba za ta dafa ba sai matata ta za a ce dafa abinci" ya fad’a da alamar tsokana.



"Ba ta jin dad’i ne" ya amsa mishi a tak’aice.



"Me yake damun ta" yaya Mus’ab ya sake tambayar shi.



Sai da ya kalle ta ganin yadda ta marairaice fuska tana kwance a jikin shi.



"Ina ruwan ka da sai ka ji abin da yake damun ta, tun da n ace maka ba ta da lafiya ba sai kayi mata addu’a ba, anya Mus’ab kai ba d’an jarida ba ne" shima yaya Faruk yay a amsa mishi cikin wasa.



Dariya yaya Mus’ab yayi ya ce "Lallai Bregadier ka shigo cikin sahun manya, dole ka ce haka, kar ka manta kai k’ani na ne dan ka na auran k’anwa ta, ka ga dole ka min biyayya".



Gaba d’ayan su suka sa dariya kana yaya Mus’ab ya ce "Bari in ma Maryam d’in magana, in ta gama girkin sai in kira ka a waya ka zo ka amsa, ka gaishe da Nanan".



"Ok za ta ji, a gaishe min da Asim" yaya Faruk ya fad’a.



Cikin wasa yaya Mus’ab ya ce "Au d’anka kad’ai za ka ce a gaisar, ba za ka ce in gaishe da Maryam ba ita da za ta muku girki, sai in fasa sa ta girkin".



Murmushi yaya Faruk yayi kana ya ce "A gaishe ta".



Dariya yaya Mus’ab yayi ya ce "Ko kai fa, har ka sa raina yayi sanyi".



Girgiza kanshi yaya Faruk yayi yana jinjina yanda yaya Mus’ab yake da son tsokana.



Sallama suka yi kana suka katse wayar.



"Mus’ab na gaishe ki" yaya Faruk ya fad’a yana kallon ta.



Tattausan murmushi tayi kana ta ce "Ina amsawa".



Haka yaci gaba da jan ta da hira.



Ranar haka yaya Faruk ya ba ma Nana lokacin shi tare da kulawar shi.



Tun daga wannan ranar yaya Faruk suka d’aura rayuwar auran su cikin kulawa da tarairaya, duk wanda ya ga yanda zaman su yake gudana sai yayi sha’awa, yanda suke gudanar da zaman su kamar wanda suka dad’e a cikin soyayyar junan su.



In ka yi duba da Nana da yaya Faruk kasan sun canza, har wani haske da fresh suka yi, saboda kwanciyar hankali da zaman lafiya da suke yi, ga kuma dad’in amarcin su da suke ci.



Kusan watan su biyar da aure aka tura su yaya Faruk wani course a can k’asar Morocco na tsawon wata uku, har da yaya Mus’ab za su yi tafiyar.



Lokacin da zasu yi tafiyar, haka Nana ta dinga ma yaya Faruk kuka, yaya Mus’ab sai tsokanar ta yake yi, shi kanshi yaya Faruk daurewa yake yi dan a yanzu yana jin Nana a duka sassan jikin shi, ga sabo da shak’uwa da suka k’ara yi, dad’in dad’awa ga jikin ta da zai yi missing, lallashin ta ya dinga yi tare da mata alk’awarin za su dinga waya, da k’yar yaya Faruk ya shawo kan Nana ta daina kukan.



Sai da taga sun shiga mota sun bar harabar gidan kan ta koma cikin gida cike da kewa, sai a yanzu ne ta tabbatar da feeling d’in da take ji tun kafin su yi aure ba komai bane illah son yaya Faruk, a yanzu ta tabbatar da cewa son yaya Faruk ya gama ratsa duk wani sassan jikin ta da jijiyoyin ta.



Duk da har yanzu ba ta san zuciyar yaya Faruk game da ita ba, tasan yadda yake kula da ita da ba ta kulawa ta musamman da kuma kyautata mata da yake yi tasan alamu ne na ya damu da ita, ita ko hakan da yake mata bak’aramin jin dad’i hakan yake sa ta ba, tasan nan gaba kad’an insha Allah tana sa ran cewa yaya Faruk zai so ta wanda a yanzu ba abin da take fata sama da hakan, tasan duk wani irin kyautata wa da zai mata zai biyo bayan soyayya ne, in har ta samu soyayyar yaya Faruk ba ta da sauran wata buk’ata a gurin shi, ko a yanzun da bai fito ya bayyana mata birnin zuciyar shi ba ta mishi uzuri akan halin da ya tsinci kan shi a dalilin soyayya wanda a k’arshe bai ci ribar soyayyar da yayi ba, dole ne yayi taka tsantsan dan guje ma faruwar hakan.



Ranar haka Nana ta wuni tana tunanin yaya Faruk.



Da daddare da tazo kwanciya wani irin kewar shi ce ta addabe ta saboda yadda ya saba mata da jikin shi, hakan yasa da k’yar bacci ya d’auke ta.



Haka Nana taci gaba da zuwa makaranta, wani lokacin in suka yi waya da yaya Faruk tana fad’a mishi za ta gidan Anty Maryam da gidan Hajiyan su, bai cika han ta zuwa ba dan yasan ka’aici na damun ta.



Yaya Aminu yazo da Anty Jiddah sun wuni kana suka juya Kaduna.



Yaya Khalil ya kawo Anisa da Ummu, kwanan su d'aya suka koma Kaduna.




Nana suna yawan waya da Momi suna gaisawa, Anisa ma na kiran ta koi ta ta kira ta, ko ta ina Nana ba ta da matsala, dan yaya Aminu ya kan zo Abujan yaji ko tana da wata damuwar ko dai wani abu da take buk’ata.



Sai da yaya Faruk suka kwashe wata uku har da k’arin sati biyu a kai kana suka dawo gida Nigeria.



Sai da suka fara zuwa office aka gabatar da liyafar da aka had’a musu na murnar dawowar su kana suka tafi gida.



Nana da take ta faman harkokin ta, sam ba tasan a ranar yaya Faruk zai dawo ba, ko da suka yi waya dashi a jiya bai fad’a mata za su dawo ba, shi yasa ba ta kawo dawowar shi a wannan lokacin ba, duk da a lissafin ta tasan sun wuce lokacin da ya ce mata za suyi a k’asar Morocco da suka je.



Tana zaune a falo tana kallon wani Nigerian series na Rahama Sadau mai suna *Shuga naija* da ake watsowa a tashar tauraron d’an adam.



Knocking taji ana yi, hakan yasa ta maida hankalin ta bakin k’ofa tana tunanin ko wa yake yin knocking.



Tashi tayi ta nufi k’ofar ta bud’e.



Idon ta ne ya sauka akan yaya Faruk dake tsaye sanye da kakin shi, wani irin kyau ta ga yaya Faruk ya mata.



"Ko dan sun jima ba su ga junan su ba ne?" ta tambayi kanta.



Wata zuciyar tace mata daman yaya Faruk tun ainihi mai kyau ne, sai dai canjin guri da ya samu yasa k’yan shi ya k’ara fitowa.



Yalwataccen murmushi ta sakar mai kana ta bashi hanya ya shigo cikin falon.



Tun da ya had’a ido da Nana ya ji wani farin ciki ya lullu’be shi ko ta ina, sai a yanzu ne ya k’ara tabbatar da yayi missing d’in ta da ya gan ta.



Wani irin tsadaddan kallo yake jifar ta dashi, a lokaci d’aya yana sakin wani lallausan murmushi.



"Sannu da zuwa yaya Faruk" ta fad’a cikin sweet voice.



"Yawwa Nana, amma haka ake wa miji sannu da zuwa in ya dawo daga tafiya" ya fad’a yana kallon ta.



Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ba tare da ta amsa mishi tambayar da yayi mata ba.



Yasan tayi farin cikin ganin shi lura da farin cikin da ya lullu’be fuskar ta, sai dai yasan kunya ba za ta barta ta nuna mishi hakan ba.



Hannun shi ya bud’e ya ce "Khadijah, come close to me".



A hankali ta dinga takowa har ta k’araso kusa dashi.



Hannayen shi yasa yayi hugging d’in ta.



"I miss you Khadijah" yaya Faruk ya fad'a a hankali.



Hannun ta ya rik'e har zuwa kan 2-sitter.



"Nana ki fad'a min kin yi missing d'ina" ya k'arasa maganar yana kallon ta.



Murmushi tayi ba tare da ta ce komai ba.



A ranta kuwa cewa take yi yaya Faruk ni kad'ai nasan halin da na shiga San da ba ka nan, baki na ba zai iya fad'a maka yadda nayi missing d'in ka ba.



"Ko ba ki yi missing d'ina ba" ya tambaye ta da alamar wasa.



"Nayi missing d'inka yaya Faruk".



Tashi yayi ya ce " Khadijah bari in je in kwanta, in an kira Sallah ki tashe ni".



"Toh yaya Faruk".



" yaya Faruk bari in sama maka abin da za ka ci, ban san yau za ka dawo ba".



"No ki barshi Khadijah, mun ci abinci a office lokacin da muka dawo, sai da daddare zan ci"   



Side d'in shi ya nufa yayin da Nana ta wuce kitchen dan tayi ma Yaya Faruk girki.



Ana gab da kiran sallah ta had'a mishi ruwan wanka kana ta je ta tashe shi daga barcin.


Bayan yayi wanka ne ya wuce massalaci kasancewar an fara kiran sallah.



Bai dawo ba sai da yayi sallar isha'i.



Bayan sun ci abinci ne suka dawo Falo, labarin tafiya course d'in da suka je ya ba ta kana daga k'arshe ya ce su tashi su je su kwanta.



Yau ma dai da suka kasance a tare sun nuna ma junan su sunyi missing d'in junan su.



Bayan sati d'aya da dawowar yaya Faruk ya ce ma Nana su shirya su je Kaduna kasancewar ranar weekend ne, sai su dawo a washegarin ranar.




Kwanan su d'aya a Kaduna suka dawo Abuja.




Haka rayuwar auran su ta ci gaba da gudana.






A ‘bangare na kuwa haka zaman mu ya ci gaba da gudana, yayin da na ci gaba da karatu na ba tare da wata matsala ba.



Tsakani na da Meema abin gaba yake yin a rashin jituwa, gashi Hanan na lura tana goya mata baya akan abin da take min.



Yanzu takai ba na jin zan juri abin da Meema ke min dan nasan in har na fad’a ma Dr ban san wani hukunci zai d’auka a kanta ba, ina ganin zan iya d’aukar mataki da kaina ba tare da na fad’a mishi ba.




Yau ranar ta kasance ranar Friday, na dawo school da wuri.



Kwanciya na je nayi saboda a gajiye na dawo.



Ban wani jima a baccin ba na tashi.



Wanka na shiga na yi na nemi simple dress na sa.



Fitowa nayi da niyyar in je in d’aura girkin dare naji ana Knocking d’in k’ofa.



Ina bud’ewa na ga su Meema ne da su Hanan.



Hanya na basu ina musu sannu da zuwa.



Farida ce kad’ai ta amsa min a cikin su.



Drinks na je na kawo musu da snacks dan ban a rabo da yin snacks saboda zuwan bak’i.



Hanan da Farida ne suka gaishe ni na amsa musu.



Sai bayan mun gaisa ne Meema ta gaishe ni a wulak’ance, yanayin yadda ta gaishe ni haka nima na amsa mata, dan a yanzu ina ganin ba zan jure ma abin da Meema ke min ba.



Zama nayi muka d’an ta’ba hira, gefe d’aya kuma hankali na yana kan wani shiri da ake gabatarwa a tashar Z Tv.



Tashi nayi na je na d’aura girki kana na dawo da niyyar ci gaba da kallon shirin da ake yi a tashar.



Samu nayi an canza channel d’in da nake kallo an sa wata channel d’in music, wak’ok’in da ake sa wa ba k’yan gani a channel d’in, Meema sai bin wak’ar take yi kamar ita ta rera wak’ar.



Ganin remote a hannun Meema ya tabbatar min da ita ta canza channel d’in da nake kallo.



Raina ne ya ‘baci da abin da Meema ta min amma sai na daure ban nuna hakan a fuska ta ba.



Cikin taushin murya na ce "Meema d’an dawo min da channel d’in da nake kallo, ina son shirin da ake yi ne, na ga ma sun kusa gama wa, in aka gama sai ki dawo da channel d’in da kike kallo".



Wani banzan kallo ta watsa min kana ta ce " Wannan nayi niyyar kallo, dan haka bazan canza ba".



Kallon mamaki na bi ta dashi, ganin yadda take son nuna min mulkin mallaka ni da gida na.



"Amma dai Meema kin san ni nake kallo kafin in bar gurin ko, dan na ce ki maida min channel d’in da nake kallo za ki ce ba za ki canza ba" na fad’a ina k’ok’arin controlling d’in fushi na.



"Ba zan canza ba Zarah" ta fad’a ba tare da wata shakka ba.



Ganin in na tsaya bin Meema a hankali za ta ci gaba da raina min hankali, dan haka na watsa mata harara na ce "Kin san dai gida na kika zo kika same ni, kin ga kenan baki da ikon nuna min isar ki a inda baki da ikon yin haka, dan haka dole ne a canza channel d’in nan dan ba ita nayi niyyar kalla ba".



Kallon mamaki ta bi ni dashi ganin yadda na fad’a mata maganar da ba tayi zaton zan maida mata martanin maganar da na fad’a mata.



Yatsina fuska tayi kana ta ce " Masu gida manya, amma ina jin shi gidan da kike tunk’ahon dashi, kema ba naki ba ne, na yaya Sadik ne, kin ga ina da ikon amfani da abin da yake nashi".

 


Dariyar tura haushi nayi kana na ce "Ina ganin bakin ki bai fad’a miki gaskiya ba, ki kalli falon nan da kyau, komai da kika gani a falon nan daga gidan iyaye na aka kawo ni dashi, kin ga kenan ba ki da power da kayan nan side d’in, in iko kike so ki nuna min, ki je can side d’in shi Sadik d’in sai ki yi ikon ki a can, in ma side d’in a kulle yake ki zo in baki key d’in side d’in, in nayi niyya ma ko can d’in side d’in Dr d’in, zan iya nuna matsayina na matar gidan ba ke  ‘yar d’osano ba".



Kwalliya ta biya kud’in sabulu dan maganar da na maida ma Meema sun k’ona mata rai, in ka kalli fuskar ta zaka ga canzawar da tayi zuwa ‘bacin rai.



"Ke Zarah har kin isa ki min gori dan na zo gidan yaya Sadik, kin san Dad d’ina yana da kud’in da zai iya siyan fiye da kayan da kike cika mana bakin an kawo ki dashi, in banda kin ci darajar yaya Sadik da sai kin yi danasanin maganar da kika fad’a min, da kike tunk’ahon ke matar gida ce, dan dai Allah bai nufa mun yi aure da yaya Sadik ba ne, da ba ki isa ki shigo cikin gidan nan ba" Meema ta fad'a cikin fushi.



Mamakin furucin Meema nayi wai dan Allah bai nufa sun yi aure da Dr ba ne, da ban isa in shigo gidan ba, sai yanzu ne na san alak’ar Meema da Dr ba kamar yadda Dr ya fad’a min cewa yarinyar abokin baban su ce, kenan bayan wannan har da alak’ar soyayya a tsananin su, no wonder shi yasa take min abinda ta gadama, ashe kishi ne ke damun ta da kuma takaicin Dr bai aure ta ba.



"Amma me yasa Dr bai fad’a min alak’ar su ba, dan me zai ‘boye min tsakanin su, me yasa bai aure ta ba?" duk wannan tambayoyin da nayi ma kaina nasan Dr ne ya kamata ya amsa min.



Duk da kishin da ya turnik’e ni, ban bari Meema ta gani a fuska ta ba.



Murmushin yak’e nayi na ce "wannan matsalar ki ce Meema, ko k’aruna ne Dad d’in ki k’arewar kud’i ba matsala ta ba ce dan ban ta’ba zuwa gidan ku maula ba bare ki goranta min, kuma me shi bay a fad’a sai dai a gani a jikin shi, kin san akwai masu kud’i, akwai muna masu kud’i, kin ga kenan za ki iya banbance a jerin da kuke, maganar alak’ar ki da Dr a da ba damuwa ta bace dan yanzu ni ce a matsayin matar shi, sai nayi niyyar bashi izini sannan zai k’ara, kin ga na zama zarah a cikin taurari, ba irin ki ba da ba ki kai matsayin da za a sa ki a jerin mata ba tun da har kika sa nuna kissar ki irin ta mata Dr ya aure ki".



Tun san da muka fara musayar yawu da Meema, ba wanda yayi magana a cikin su Hanan da Farida, sai wannan karan ne Hanan ta sa bakin ta da cewa "Anty Zarah,  bai kamata ki dinga fad’a ma Meema wa’innan maganganun ba, ita ma matsayin k’anwa take a gurin yaya Sadik, Allah ne bai nufa za su yi aure ba, da tana nan a matsayin matar shi".



"Ya ishe ki Hanan, kar ki k’ara sa min bakin a cikin maganar nan, ki bari wacce nake yi dominta ta bani amsa da bakin ta, dan daman nasan bayan ta za ki bi" na fad’a cikin ‘bacin rai.



Yatsina fuska Hanan tayi kanata ce "Dole in fad’i gaskiya in ya zama dole a fad’e ta".



A yanzu ban da lokacin kula Hanan, na fi so in fara maganin Meema dan ita ce take so ta shiga harka ta, so nake in nuna mata nima ba kanwar lasa ba ce.



Da alama na fara samun nasara akan Meema, dan tun da na bata amsar maganar da ta min take huci, a yanayin ta so take yi muyi wacce za muyi, nima kuma a shirye nake da duk wani abin da take ji dashi.



Juyowar da zan yi dan mu ci gaba daga inda muka tsaya da Meema, ba zato naji saukar mari a fuskata.



Meema ce ashe ta taso tazo in da nake lokacin da na juya ina ma Hanan magana.



Cikin huci ta ce "Ke har kin isa ki fad’a min magana in k’yale ki, nawa kike, wanda suka fi ki ma basu isa bare ke, ke ko kallon banza mutum ya min sai yasan ya ta’bo ne bare ke har da zaki bud’e rubbush mouth d’in ki kina fad’a min maganar da tazo bakin ki, ina so in yi warning d’in ki, daga rana mai kamar ta yau, in har kika k’ara bud’ar bakin ki kika fad’a min maganar da ba ta min ba sai kin gane kuren ki, ke ko kallon banza kika min ranar sai kin yi danasani, ki rubuta ki ajiye sai na nuna miki yaya Sadik nawa ne, sai na aure shi….".



Kan ta gama maganar da take yi ni tsinka mata kyawawan mari guda biyu wanda suka fi wanda ta min zafi.



A yadda re-action d’in ta da tayi ya nuna marin ya shige ta dan har dafe kuncin ta tayi.



Hannu ta d’aga da niyyar kai min wani marin, nayi saurin sa hannuna na rik’e hanun ta na watsar.



"Kin yi kuskure Meema da kike tunanin in kika mare ni kamar kin ci bulus, ko a yanzu hannun ki yakai kan fuskata sai na miki mafiyin shi, in kuma kina musu ki gwada ki gani yadda za mu kwashi ‘yan kallo dake, ni da kike gani ba na barin ta kwana, ina k’yale ki ne dan darajar Dr da kuma matsayin kin girme ni, tun da na lura shekarun naki basu da amfani ki da komai ba sai koma baya da ya haifar miki, to ni kuma zan taka girma" na fad'a.



Farida ce ta tashi tana bani hak’uri akan in yi shiru in k’yale Meema.



Ganin yadda Farida ke bani hak’uri ne yasa na yi hanyar kitchen dan ni sai yanzu na tuna da abin da na d’aura.



Ina cikin kitchen d’in ina jiyo maganganun da suke yi.



Wani dogon tsak’i Hanan tayi kana ta ce "Ke dai Farida banza ce, kina kallo ta mari Meema, ban da maganganun da ta fad’a ma ta, shine har da ba ta hak’uri, maimakon ki ba ma ita Meeman hak’uri akan zarafin ta da Anty Zarah taci mata, shine kike ba ma ita Anty Zarah hak’uri dan neman gindin zama".



Meema ce ta k’ar’bi zancen cikin masifa ta ce "Ki k’yale ta Hanan, na lura daman ita Farida tana bayan Zarah ne, sam Farida ba ta kishi na".



Maida kallonta tayi ga Hanan ta ce " Can you imagine Hanan, wai ni yarinyar nan ta d’aga hannu ta mara, sai tayi danasanin marin da ta min, zan koya mata hankali".



Hanan ce ta watsa mata harara ta ce "too late Meema, ai kin bani haushi da kika tsaya ta mare ki har two times ba tare da kin yi d’auki mataki ba, yanzu sai dai ki yi hak’uri kawai dan tayi winning akan ki".



Farida ce ta ce " Abin da kuke yi bai kamata ba, in maganar gaskiya tazo a fad’a, Anty Meema you a the one that start causing this fighting, abin da yasa kika ji haushi dan ta rama abin da kika mata ne, kuma ni ban ga laifin ta ba, dan ko ni aka yi ma haka matakin da zan d’auka kenan".



Gaba d’ayan su suka taso mata wai daman sun san baya na za ta bi.



Meema ce ta ce su taso su tafi gida.



Tashi suka yi suka fita daga falon ba tare da sun min sallama ba.



Farida ce ta shigo kitchen d’in ta min sallama.




Post a Comment

0 Comments