TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 3

 👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT STORY AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____3💎



   Suna fitowa sukaci karo da Bassam aguje Batool ta biyo shi yana kwasar dariya, ganin yaya mahmud yasa suka shiga taitayinsu cike da fargabar kar yayi masu wani abun, wata uwar harara ya watsawa Batool had'e da cewa.


"Ke ko? Hmm! zaki zo hannuna ne, wato ana sallah ke kuma kintsaya yin shashanci da k'anenki don rashin sanin ciwon kai ko?, zaki wuce kiyi sallah ne ko saina makeki awurin nan?"


Cikin sigar shagwab'a Batool ta fara bubbuga K'afafuwan ta,


"Ni yaya Mahmud ba yanzu zanyi ba sai.... "


Kafin ta rufe baki Mahmud yayo kanta fuska a d'aure, tana ganin haka takwasa aguje ta shige wajen small mom tana qunquni had'e da tura baki shi kuma yaja hannun Bassam suka d'auro arwala a famfon dake cikin guading d'in sannan suka nufi masallaci. koda sukaje har an kusa sallame sallah saura raka'a d'aya, haka Mahmud yabi jam'in bayan an sallame ya tashi ya cika sauran taka'o'in da yarasa sannan ya baro masallacin hannuwansa rik'e da Bassam da Bilal yana koya masu addu'ar da ake yi idan anfito daga cikin masallaci...,


_"Bismil-lah wassalatu wassalamu ala rasoolil-lah, allahumma innee as-aluka min fadlik, allahumma iaasimnee minash-shayta nir-rajeem."_


Yana yi suna mai-maitawa  har suka isa wurin wani mai shago dake saida sweets dasu biscuit, d'ari biyar ya mik'awa  mai Shagon yace ya had'o masa biscuits da sweet amma yayi masa Leda leda kowanne na d'ari har guda biyar. Bacin angama had'a masa ya sake mik'a masa naira d'ari yace ya bashi chaculate  da lolipop, cike da jin dad'in cinikin Mai shagon ya had'o masa ya mik'a masa yana dariya wannan karon hadda gyara yasa masa yana fad'in,


"An gaida malam Mahmud shalelen alhaji kaga farin saurayi mai farar aniya, ranka ya dad'e yayi k'arko yayan Billy jepenese godiya nake yi"


Dariya Mahmud yayi don inda sabo ya saba da halin mai shagon duk lokacin da zaizo siyayya shagon mutumin sai yayi mashi wannan banbad'ancin kallonsa yayi kafin yace.


"Uh'umm..malam shehu kwalelanka akan sunan nan dan idan sister Billy taji wannan suna yana fitowa a bakin ka, ina tabbatar maka daga ranar ta dena son kayan shagon nan naka kuma zan dena siya saboda dama saboda ita nake saya" 


Yana gama fad'ar haka ya mik'awa Bassam da Bilal kowanen su leda d'aya tare da yiwa malam shehu mai shago sai anjima, Murmushi ya sake yi wanda ya k'ara fiddo masa da tsantsar kyawon da Allah yayi masa ganin yanda malam shehu yasa hannu biyu-biyu ya toshe bakinsa tare da turo idanuwansa waje saboda jin abinda ya fad'a, hannuwan su Bilal yaja suka nufi gida suna shiga yaci karo da Basmah k'anwarsa dake bimasa ta rako qawayenta earpiece lik'e a kunnenta ko d'an kwali batada shi balle mayafi kuma a haka take shirin fita har wajen gate, qawayenma nata kowanen su babu shigar kirki ajikinsu kaida ka gani su kasan k'awayen ban zane, tsuke fuska yayi tare da sakin hannuwan su Bilal..


"Oyah! Maza kushiga ciki gani nan shigowa" 


Suka bar wajen aguje hannuwansu rik'e da ledar sweet d'in daya siya masu,


Basmah na ganin haka gabanta ya fad'i don ta riga da tasan kwanan zancen, amma saboda kafuwa da k'arfin hali irin nata sai ta basar tare dayin kamar bata ganesa ba, cikin fad'uwar gaba tace da qawayenta.


"khady, shapsy bye-bye sai mun had'u gobe ko?"


 Tana k'ok'arin fita. Wata muguwar damk'a ya yiwa gashin kanta da ta sakawa ribon d'in acuci maza tare da jawota baya, 


"Ke wace irin wawuyace zaki fita a haka? Bakya ganin ko wud'annan dak'ik'an qawayen naki da basa iya sanya suturar k'warai ajikinsu sun d'an yafo abunda yarufe masu kansu, shine ke zaki fita haka" 


Sai alokacin khady da shapsy suka juyo suna kallonsa cike da son yi masa rashin mutunci saboda jin abunda ya fad'a akan su, tsantsar kwarjininsa yasa a maimakon suyi masa masifa sai gashi sun tsinci kansu da gaishe sa. 


Kallonsu yayi tun daga sama har k'asa tare da yatsine fuska yace


"Idan har zaku dinga irin wannan shigar banzar a matsayinku na 'ya'yan musulmi to kar in k'ara ganin k'afarku ta tako da sunan zuwa gidan nan, Infact idan ma ba zaku iya sauya irin muguwar shigannan ba kar nasake ganinku da qanwata if not i will make sure dt nasa kowacen ku tayi nadamar saninta."


k'arasa maganar yayi had'e da nuna Basmah da d'an yatsansa, har lokacin hannun sa rik'e yake da acucinta, cikin tsawa yace dasu.


"Get out now..."


Kallon Basmah suka yi da tuni idanuwanta sunyi jajir suna neman kawo k'walla saboda azabar da takeji, Kafin yace wani abun ya kaiga sake daka masu tsawar da tasa jikinsu na rawa suka bar gidan ba tare da sun yi mata maganar da suka tashi yi mata ba ita kuma yaja k'eyar kanta har cikin gida yana zuba mata masifar karya sake ganin kanta ba d'an kwali balle tayi tunanin fita haka!,


Basmah najin muryar small mom ta saki wani irin azababben kukan da yasa mom k'arasowa wajen aguje tana sallallami cikin sauri ta rik'o Basmah daya hankad'e can gefe yana cigaba da yi mata fad'a, kallonsa mom tayi a hasale tace.


"Amma Kai anyi mugun yaro anan, kai kenan kullum cikin cin zalin yaran nan ko tausayin su baka yi"


"Mom sune suke yin abubuwan da basu kamata ba wallahi duk da 'YAN UWANA NE SU banajin dad'in d'abi'un da suke yi, don Allah mom dubeta, a haka fa take shirin fita cikin gidan nan kanta babu d'an kwali sai kace ba d'iyar musulmai ba, ko Bilkisu da take k'anwar ta bata yin irin wud'annan mugayen d'abi'u sai su, to wlh kwanan nan idan basu dena ba jikinsu zai gaya masu"


Yana gama fad'ar haka yasa kai yabar part d'in ransa a b'ace,


"Eyyeeee...! lallai Mahmud wuyanka ya isa yanka, 'yan uwan naka kake cewa suna mugayen d'abi'u har kake cewa wata ta fisu? to ka canza wasu 'yan uwan mana tunda kanada wacce tafisu kyawawan d'abi'un, Jimun fitinannen yaro zaibi duk ya takurawa yarana, yi shiru ki k'yalesa zai dawo ya sameni idan ma turosa aka yi zanyi maganinsa, maza kishare hawayenki"


Mom ta fad'a tare da rad'awa Basmah wata magana akunne.


Hararar mom Basmah tayi had'e da langab'e kanta tace


"Da gaske?"


"Ha'a Basmah zan maki k'arya ne?"


"Yeee sai mom! Shi yasa nake masifar sonki"


Aguje Basmah ta wuce d'akinta kai tsaye ta nufi wardrobe d'in kayanta, tana bud'ewa taga wasu had'add'in kaya jins da t-shart har kala uku da mom tasiya mata, tsalle tayi had'e da yin ihu sannan taciro wayarta..


"Hello khady"


"Inaji basmah me kuma zaki fad'a mana bayan agabanki brother naki yaci mana mutunci amma kika kasa cewa komai"


"Haba khady Wlh yaya Mahmud matsalarshi ya wace da ita, ni bakiga wak'i'ar daya sani bane? wlh har yanzu kaina ciwo yakemun, abeg kimanta kawai kinji qawata"


"Hmm! Shikenan ammafa banji dad'in abinda yayi mana ba, don har nace keda ganina sai baba ya gani"


"Hhhhh matsoraciya"


"Naji d'in irin wannan red-face da yaya Mahmud yayi ai dole na tsorata, ammanfa ba k'arya basma yayan nan naki ya had'u ba kad'an basu don yafiki kyau sosae"


"mtsss manta kawai, naji yafini kinsan me?"


"A'a Basmah sai kin fad'a"


"Akwai chilling! Mom ta had'o min wasu had'addun kaya shine nace yaushe ne birthday din qawar nan taki sai mukece raini dasu"


"Haba bab da gaske? Wow kice akwai corrumboling"


"Yes woo....dama kala uku ne kinga sai na d'auki d'aya na baku sauran"


"Ok..shikenan Zanyi checking up naji ko yaushe ne I will call you back "


"Shikenan bye-bye sai najiki" daga haka tayi hanging wayar sannan tafad'a kan gado tana rera 'yan wak'ok'i cikin jin dad'in kyautar da mom tayi mata, 


Kai tsaye Mahmud ya wuce falon Ummi bakinsa d'auke da sallame yanemi wuri ya zauna, ganin babu kowa a falon sai k'amshin girlie dake tashi ya tabbatar masa da cewa suna kitchen, jin muryarsa tasa Ummi ta fito hannunta rik'e da cup d'in ruwa ta mik'a masa


"Babanah an dawo masallacin?"


"Eh Ummi me kike dafawa naji falon ya gauraye da k'amshi" Mahmud yafad'a tare da karb'ar cup d'in ruwan, dariya Ummi tayi sannan tace


"Kai babanah wane k'amshi kuma, Bilkisu ce ke dafuwar indomi" tana rufe baki sai ga Billy ta shigo falon d'auke da plate d'in indomien a hannu Bilal biye da ita yana kuka tana fad'in


"Yaro k'ara volume indai indomien nan ce bazaka cita ba"


Dariya Mahmud yayi had'e da girgiza kai


"Billy!.Billy!!..baki da dama wato ya k'ara volume  d'in kukan ba zaki basa ba ko?..Toh nima bari chaculate d'ina ya sha zamansa ba zan baki ba"


"Sorry yaya gashi na ajiye, Bilal zo muci" Har Bilal ya fara kokarin zaunawa ta jaye plate d'in tace "To kaje ka wanko hannunta ko malam"


Zaune shima mahmud yayi tare dasa hannunsa sukaci indomien yana yaba k'ok'arin Billy data iya girki haka.


"Lallai idan daddy ya dawo zance ya yiwa Billy aure tunda ta iya girki"


"Hmm Allah dai ya tsare wanda zae aureta a haka da shan jagwalgwalo, ai kaima daurewa kad'ai kayi don tana ta hannun damarka nasan da bazaka iya ciba" Bilal ne yake fad'i yana d'ago kai yana sud'ar hannu yace


"Hiynnmmm... su aunty Billy Japanese an iya dafa indomi" 


Dariya suka kwashe da ita har ummi na rik'e ciki


"Wato indomien tayi dad'i  Bilal?, ashe kaima karage iya fad'an Billy jepenese d'innan?" cike da k'warewa Billy ta d'aga hannu zata doke sa yaya mahmud yayi saurin rik'eta yana dariya


"Bafa shi ya fad'a haka ba malam..." 


Sai kuma yayi shiru tare da jawo ledar sweet da biscuit d'in da ya siyo mata ya mik'a mata har ya turo baki zatayi k'orafin chaculate d'inta taga ya mik'a mata had'e da lolipop, cikin jin dad'i tayi masa godiya tare da cewa


"yaya ina nasu aunty Basmah da batool? "


Nuna mata nasu yayi tare da mik'ewa yana cewa ummi.....




Post a Comment

0 Comments