TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 40

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 4️⃣0️⃣

______


Abideen na gama cin breakfast ya matsa baya kaɗan yana shan ruwa daga goran ruwa, kwashe tray da sauran plates ɗin Safeerah tayi daga dinning table ɗin ta wuce kitchen, da azama ta fara wanke wanke dan ganin har 10 ta kusa kuma gashi lectures ɗin Mr Tasiu ne, tana cikin wanke wanken taji an rungumeta ta baya da ƙaƙƙarfar hannaye, tsorata tayi saboda bata yi expecting hakan ba, juyowa tayi zuciya a tsinke tayi, "Gosh, you scared the hell out of me!" Murmushi yyi mata tareda manna mata kiss a wuya yace, "Kin cika tsoro!" Turo masa baki yyi nan ya lura ashe ya sace daga kumburin shys zata je school yau. 😂💔


Lips ɗinta ya kamo da nasa ya shiga sarrafasu yadda ya kamata, bata so ya bari amma haka ta tureshi tayi tace, "Ya Abi-deen zan makara fah, kai zaka kaini school?" Kallonta yyi sosai kafin ya girgiza mata kai dan yana da Therapy yau sae yace, "Aah, Daniel zay kai ki, but maybe I'll pick you up!" Kai ta ɗaga masa sannan ta goge hannunta da towel dan har tagama, shigar dasu mazauninsu tayi kafin ta juya ta fice daga kitchen ɗin, mazaunanta ya bi da ido suna sake birgeshi, bayanta ya take zuwa parlourn. Veil ta fara rolling tayi shi yanda ya rufe mata ƙirji da baya gaba ɗaya, tote bag ɗinta ta rataya daya shiga da kayanta ta yi masa bye da hannu ta juya zata fita, har ta fara tafiya ya fisgota ta faɗa kan hard chest ɗinsa, gira ɗaya ya ɗaga mata ita kuma ta turo masa baki tana tunanin meyasa ya fusgeta bayan yasan zata makara.


 Murya can ƙasa yace, "Seems like kin manta da wani abu!" Shiru tayi masa tana tunani sae juya fararen idanunta take yi, rolling eyes ɗinsa yyi yana takaicin komai sae an gaya mata ne, bae gama tunanin nan ba tayi ɗagen ƙafa, gani tayi baza ta kai ba hakan yasa ta cire shoes ɗin ƙafarta ta hau kan kujeran parlourn ta manna masa soft lips ɗinta a goshinsa, murmushi yyi bayan ta sauka yace, "Do it properly, ba'a nan nake so ba.." tura masa baki tayi tana kallon handsome face ɗinsa daya sake ƙawatuwa da scruffs ɗin daya bari a fuskarsa, ɓata rai yyi yace, "Idan baki yi ba baza ki tafi ba!!" Lumshe idanunsa yyi yana kallon fararen idanunta dake kokwantan abun daya faɗa, agogon hannunta ta kalla nan yyi saurin rage mata tsayinsa ta hanyar sunkuyar da kansa harda rufe idanunsa, cikin sauri yaji ta manna masa lips ɗinta sannan ta juya ta fice da sauri, murmushi yyi bayan fitar ta daga parlourn. 


Cikin shiri ya wuce Therapy bayan ya gama by 12 ya wuce gidansu, part ɗin Umma ya fara shiga ya gaishe ta nan ta amsa tana wani basarwa kafin tace, "Shanyanye, mutumin banza. Yanzu maganar dana yi maka shine ka sa ƙafa kayi fatali da ita ko saboda an shanye ka?" Kicin kicin yyi da ido yana kallon yanda Umma tayi very serious akan kiransa shanyanye, daurewa yyi kawai yace, "Shanyanye kuma Umma? Ni banyi fatali da mgnr ki ba kawai nafi son sae na dawo daga Somalia sae a ɗaura tunda haka kike so" kallon banza ta watsa masa tace, "Idan ba shanyanye ba uban wa ke yawo da pant ɗin matarsa a mota ko kafi kowa son mata ne?" 


Shiru yyi dashi ya rasa bakin magana ga zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yana mamakin yanda ta sani, gyaran murya Umma tayi ta ɗaura da, "Kai dai ka sani, ai ba dama nayi maka magana sae ka nemo wani silly excuse! Idan kaso ma kayi fatali da mgnr mutumin banza ni tashi ka bani wuri kuma ka samu Zaytoonan kuyi magana. Aure bbu fashi indai ina numfashi na gaya maka dai.." tana kai nan ta miƙe ta wuce ɗakinta ta barshi da tunani kala kala, sam baya son ransa ya ɓaci a gida hakan yasa yyi ƙoƙarin kwantar da hankalinsa sannan ya wuce part ɗin Hajiya, ko daya je maraba tayi dashi sosai tana farin cikin ganinsa har take tambayarsa matarsa ko tana ƙalau, fura damamme ta kawo masa mae sanyi nan yyi masa aikin tas kafin ya gyara zama ya baje a One settee yana shan iskan AC dake tashi a ɗakin, Hajiya ce ta fito daga ɗakinta sanye da mayafi, gyara zamansa yyi da shirin tambayarta ina zuwa, dariya tayi tace, "Na san sae ka tambaya ai, nan maƙota zan shiga nayi barka, ince dae kana nan.." murmushi yyi sae ya koma ya baje tareda cewa, "Eh! A dawo lafiya.." ledar kan kujera ta ɗauka ta fice tareda jawo masa ƙofar, ya daɗe yana zaune sai ya tuna abunda Umma tace, ba shiri ta ciro wayarsa ya dannawa Zaytoona kira bae yi ringing ya kai sau biyu ba tayi picking kamar dama jira take dan taga motarsa a parking lot, tana ɗauka yace, "Ki zo ki same ni a part ɗin Hajiya.." yana gama faɗin haka yyi disconnecting kiran yana sake gyara zamansa. Bata ɗauki wani dogon lokaci ba ta shigo part ɗin sanye da doguwar riga straight gown, sae ɗaurin ɗankwalin da tayi ta feshe jikinta da turare ita a dole ga mai saurayi. (*Ni ko nace zaki ji jiki ne!😂🤭*)


A ƙasa ta zauna gefensa tana tsoron haɗa ido dashi saboda kwarjini daya ke yi mata, murya can ƙasa tace, "Yaya Ina wuni.." tasani sari bazai amsa ba hakan yasa taja baki tayi shiru, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Kika cewa Umma kina so na! Haka ne?" Shiru tayi kafin ta ɗaga masa kai, wato ma saboda tace tana sonsa shine take wani ɗaga masa kai kamar sa'an ta ne shi, cikin ɓacin rai yace, "You answer my damn questions! Ko bakya da baki NEY???" Ta tsorata sosai saboda this is the first time yyi mata ihu, kicin kicin tayi ta idanu tareda ɗagawa ta kalli fuskarsa da ta rasa duk wani fara'a da take gani a da, sannan tace, "Eh nice na faɗi mata!" Tsuka ya ja yace, "Saboda na zama sa'an aurenki?" Ba ƙaramin zafin maganar taji ba amma dole ta nuna masa soyayyar ta fili ko dan ta dena dakon sa a zuciyarta, cikin juriya da confidence ɗinta tace, "Aah Yaya amma wallahi Ina sonka tun ina ƙarama nake da burin zama mallakin ka.." saurin ɗauke idanunta tayi saboda hawaye da suka taru a ciki, mamaki yyi shknn ta faru ta ƙare, cize leɓensa yyi yace, "Zaki iya zama da ni a matsayin mijinki?" 


Saurin ɗago kanta tayi tace, "Eh Yaya! I'll try my best to make you happy!" Wai ƙaramar yarinyar nan ke cewa she'll make him happy, ya tabbatar da cewa bata wuce sa'ar Safeerah ba amma it doesn't matter tunda ita kallon ƙanwarsa yake yi mata, tana da ɗan jiki amma ko kaɗan bata da abunda Safeerah take dasu a jiki na burgewa duk da Safeerah na da sanyi akwai kaya dae, itako Zaytoona ba cas ba as. Murmushin mugunta yyi na lokaci kaɗan kafin ya ɗaure fuska tamau yace, "Zaki iya ko?" Kai ta ɗaga sannan tace, "Eh Yaya, zan iya!" Gira ya ɗage mata yace, "Mararki zata iya ɗauka na?" Jin tambayar yasa tayi saurin ɗaga kanta taga da gaske shi yake magana saboda bata taɓa jin yyi maganar banza ko abun banza ba sae dai abunda ta gani a motarsa kuma ta tabbatar na matarsa ce. Shiru tayi bata amsa ba sae idanu da ta kafesa dashi, rai a ɓace yace, "Bakya da baki ne?" Saurin girgiza kai tayi jiki na rawa tace, "I'll try my best!" Fusgota yyi ta faɗa kan jikinsa yace, "Ba trying zaki yi ba! You'll just do it!" Wani farin ciki taji yana karaɗe dukkan jikinta nan take ta fara sakin masa jiki wanda bae yi tsammanin hakan ba tunda tana tsoronsa bae kamata ace tayi saurin sake jiki ba a matsayin ta na budurwa, tureta yyi daga jikinsa yana maida numfashi, ƙofa ya nuna mata yana ɗauke kai yace, "Zaki iya tafiya.." simi simi ta miƙe ta fice daga ɗakin inda ya bita da idanu, bajewa ya sake yi yana tunanin yanda zaiyi tackling issue ɗin, yana cikin tunani kuwa sae yaji sallamar Hajiya, agogon hannunsa ya kalla yaga lokacin gama lectures ɗin Safeerah yyi kuma ya mata alƙwarin ɗaukarta hakan yasa yyi wa Hajiya sallama daga nan ya fice daga gidan sae makarantar su Safeerah...


Zaune yyi cikin motarsa yana jiranta, wayarsa ya ɗauka ya danna mata kira bbu ɓata lokaci ta ɗauka amma daga yanda tayi masa magana yaji muryarta yyi sanyi sosai, hango ta yyi tana takowa zuwa wurin da yyi parking ɗauke da fake smile a face ɗinta, tana shigowa tayi masa smiling amma da gani kasan fake ne shi dae bai wani damu ba saboda yyi farin ciki ganin kyakkyawar fuskar matarsa, yana driving yana yi yana satan kallonta ɗauke da smile a fuskarsa. At least ko da ya shiga damuwa idan ya ganta hankalinsa yana kwantawa sosai, hannunsa ya miƙa zai kamo nata kawai yaga ta wani tsorata ta buge hannunsa har tana ƙanƙame jikinta ga kakkarwa da take yi, fita hayyaci na kusan 2 minutes tayi kafin ta dawo hankalinta tayi saurin kamo hannunsa sannan tayi masa smiling, yyi mamakin reaction ɗinta sosai and daga nan yasan wani abu ya faru kuma zai yi bincike.....


Chapter 40 loading😘🥂💕...


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments