TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 32

𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕

Page 3️⃣2️⃣

 _____


Haka kawai ya ƙi komawa gida da wuri sae wurin 11 na dare, haka kawai ya fara jin nauyinta bayan amsar da ta bashi, har ƙasan zuciyarsa yana son ganinta amma baya son su haɗu kuma. Part ɗinsa ya wuce kai tsaye, a parlour yaga tray ɗin abinci da takarda a gefe, ko da wasa idan 10 na dare tayi ko da yunwa ce zata kashe shi baze ci abinci bh zae daure sae garin Allah Ya waye amma ganin trayn da yyi yaji kawai yana son ci, zama yyi akan kujera yana cize leɓensa na ƙasa. 


Wayarsa ya zaro daga aljihunsa yyi dialling numbernta, yyi ringing ya gama bata ɗauka bh, miƙewa yyi ya nufi ɗakinta bae dena kiran bh, yana isa ya tarar daita tayi bacci kan littafan karatun ta, ga wayar a gefenta amma sam bata ji ba bare ta sani. Kallo ya ƙare mata daga kai har ƙafa kafin ya juya ya fice daga ɗakin, cikin kasala yake tura abincin dukda yyi masa daɗi sosai, papern kan table ɗinne dae ya kasa karantawa nan ya barsa a inda ta ajiye ya shige bedroom ɗinsa. Ruwa ya watsa yyi shiri cikin wandon PJ ɗinsa ya haye gado, har ƙasan zuciyarsa yana son kasancewa tareda ita amma...


Washe gari...

Yana saukowa ya tarar da ita a dinning table tayi shiri cikin blue abaya, gidan ta gyara shi already sae ƙamshi yake tashi, kai tsaye ya wuce dinning table ya zauna, ajiye papern data ajiye masa yyi akan table ɗin yana gyara agogon hannunsa. "Ya Abideen Ina kwana" banza yyi mata dama kuma tayi expecting haka, serving ɗinsa tayi ta koma gefe ta zuba nata tana ci a hankali. 


Yana gamawa ya sha ruwa ya miƙe tareda tura mata papern gabanta, ɗagowa tayi tana kallonsa shima kallontan yyi yana lumshe idanu kafin ya buɗe su kanta yace, "Meye a ciki?" kallon papern tayi taga yadda ta ajiye wato be karanta bh knn, ajiyar zuciya tayi tace, "Lafiya na ƙalau, kawai gajiya nayi sae kuma haɓo... dama ina yawan yi.." kallonta yyi cikin rashin yarda ya juya ya bar mata papern akan table, yana ficewa tayi ajiyar zuciya ta ɗauke takardan hannunta na rawa, dama jiyan ta yanke shawarar sanar masa akan ciwonta amma ya riga ya dawo mata dashi.


Tsaye ta miƙe ta ɗauko handbag ɗinta ta fice, nan ta samu drivernta yana jiranta a waje, yau da ƙananun kaya ta ga Abideen hakan yasa tayi tunanin ko bazeje office bane yau amma yana shiga cikin motarsa yyi hanyar Garrison, gurin LTC ya je suka yi magana akan promotion ɗinsa da suke neman fixing date ayi. Ba shi ya bar Garrison bh sae gurin ƙarfe ɗaya da rabi, a hanya ya tsaya yyi sallah a Masjid kafin ya shiga gida gurin Umma.


 Kamar kullum dae bata sake masa fuska bh shi ko ya tashi yyi hanyar part ɗin Hajiya, a zaune ya ganta tana kallo a parlour tana dariya, guri ya samu ya zauna yace, "Hajiya ina wuni.." kallonsa tayi cike da mamaki dan bata ji shigowarsa bh, "Lafiya ɗannan, ya matar taka?" Murmushi yyi yace, "Tana nan lafiya, ke da kika guje mu" dariya tayi tace, "Oh so kk na zauna, ka zagaya kace na hanaka sakewa da matarka. Aah raba ni da shiga haƙƙin ma'aurata" dariya yyi jin amsar ta, ya taho mata da Yoghurt amma sam baze iya tashi ya koma parking space ya ɗauko bh hakan yasa kawai ya baje a kujera yana shan iska yana ƴan tunane tunane.


Suna cikin zama kuwa sae ga Zaytoona kamar an korota ta shigo ɗakin ganin motar Yaya Abideen a parking space tasan to yana part ɗin Hajiya, tana zuwa tayi murmushi ta durƙusa a gefensa. Hajiya dake zaune a gefe taɓe baki tayi tace, "Oh wata sabon gani, ashe da rabon naga Zaytoona a ɗaki na" kallon Hajiya Abideen yyi yana lumshe ido yace, "Bata zuwa gaishe ki ne?" Taɓe baki Hajiya ta sake yi tace, "Yo toh ni wa tazo gaishe ni?" Ransa ya ɓaci da jin haka yace, "Ke!" Turo baki tayi tace, "Naam, Yaya Ina wuni, Hajiya ina wuni" banza aka yi da gaisuwarta babu wanda ya amsa ta cikin su sae ma taɓe baki da Hajiya tayi, ƙananun idanunsa ya sauke kan nata yace, "From today, idan kika kuskura baki zo kin gaisar da Hajiya bh ni da ke ne" turo baki tayi tace, "Toh!"


 Murmushi tayi ta sake cewa, "Yaya dama kan maganar kuɗin nan ne.." kallonta yyi yana tuna lokacin data ce ya bata kuɗi, tana yarinya amma ta tambaye shi dubu ɗari duk da bae san mae zata yi dashi na gaskiya bh, sae dae ce masa da tayi wai na graduation ceremony ɗinsu da tayi, lumshe idanu yyi ya zuba mata ido. Wayarsa ya ciro cikin aljihu yace, "Account details.." karanto masa ta fara yi cike da annashuwa tana ƙara jin son Yayan nata har ranta, Hajiya dae ta bisu da kallo bata ce ƙala ba. Yana gama yi mata transfer ta ɗaga wayarta da tayi ƙara tace, "Ya shigo.. Yaya na gode!" Tsaye ta miƙe tana faman rungumeshi, ido Hajiya ta zaro tace, "Ke wai har yau baki san kin girma bane kinzo kine neman rungume mijin mata, Aah!"


 Turo baki Zaytoona tayi tana jin takaicin dakatar da ita da Hajiya tayi, makullin motarsa ya miƙawa Zaytoona yace, "Ki ɗauko mun leda a backseat" karɓa tayi tana ɗaga masa kai ta fice daga ɗakin. 


Jiki a sanyaye ta shigo ɗakin da ledar, Abideen ko kallonta bae sake yi bh bare ya lura da sanyin da tayi, ledar ta ajiye ta sake faɗin, "Yaya nagode.." sannan ta fice, Hajiya ta lura da yanda jikinta yyi sanyi amma bata ce ƙala bh, ledar ta buɗe ta ko washe baki tana yiwa Abideen ɗin godiya.


 Can bayan Laasar yyi wa Hajiya da Umma sallama ya fice daga gidan, Zaytoona dae ɗakinta ta shiga ta rufe tana rera kukan da ba wanda yasan sanadin kukan nata bare a lallasheta. 


Yana hanyar komawa gida yaronsa wanda yake kai Safeerah makaranta mae suna 'Daniel' ya kirashi a waya, tunanin very urgent yyi saboda basu taɓa kiransa sae idan abu ya faru, picking yyi muryar Daniel ya fito yana cewa, "Madam is done with her lectures and I got a flat tyre when.." bae ƙarasa bh Abideen yyi disconnecting kiran yyi U-turn ya nufi hanyar makarantar. 


Yana isa ya wuce department ɗinsu, zaune tayi tana danna wayarta akan wani kujera da aka yi su dan shan iska, kallonta Abideen ya tsaya yi yana murmushi ganin tana ta baza ido ko zata ga Daniel amma shiru. Wayarta ya kira yana kallonta, murmushi tayi tazo za tayi picking kuma wani namiji ya zo ya zauna kusa da ita, yana kallonta tasa hannu ta kashe sound ɗin ringing ɗin har ya katse. Bae san meya faɗa mata bh ta kama yin dariya yana mata magana tana amsashi, Abideen na daga cikin AC amma ji yyi kamar baze iya numfashi bh, saboda ɓacin rai jikinsa har kirma ya soma, idanunsa suka yi jaja zur dasu, steering wheel ya nausa kafin ya fice daga cikin motar ya nufi inda take zaune... 😳🙉


Tun daga nesa ta hango shi sae saurayin ya sake mata magana suka ko sake yin dariya, sae da Abideen ya ƙara matsowa kusa taga ransa a ɓace take zuciyarta ta fara bugu a ɗari, miƙewa tsaye tayi shima saurayin gefenta ya miƙe da murmushinsa yana farin cikin zae ga mijin matar auren ajinsu kuma matar soja tunda da uniform ake zuwa ɗaukanta ana buɗe mata mota. Da kwarjini Abideen ya iso gurin, yana zuwa bae yi wata wata ba ya danƙo wuyan Class Rep dake ɗokin ganinsa, kafin kace kobo Abideen ya kai masa naushi a baki, wani ya sake kai masa a hanci.


 Nan da nan sae fuskar Class Rep ta kicime da jini ga numfashinsa dake ƙoƙarin ɗaukewa, a zabure Safeerah tayi tsaye tana kallon bala'in dake afkuwa, hannun Abideen ta kama tana faɗin, "Dan Allah ka bari.." kallonta yyi da jajayen idanunsa sannan ya ɗauke kansa, wani naushi ya kaiwa Class Rep a ciki sannan ya sake shi ya faɗi ƙasa. Mutane ne suka fara taruwa a gurin suna kallon faɗa ya kaure da Class Rep da mijin matar auren ajinsu, duƙawa Abideen yyi yace, "Idan na sake ganin ka raɓi inda MATATA take, sae ka gwammace baka zo duniya bh!" 


Class Rep dae dake cikin azaba kallon Abideen kawai yake yi, jin bae amsa bh yasa Abideen cewa, "DO YOU GET THAT!!!" jin tsawan nan ba Class Rep kawai ya tsoratar bh har da Safeerah dake gefensa, kai Class Rep ya shiga ɗagawa da sauri sauri. Miƙewa tsaye yyi ya kalli Safeerah da jajayen idanunsa nan tayi mutuwar tsaye dan tasan yau na lahira sae ya fita jin daɗi, hannunta ya fusga ya shiga tafiya, kasa tafiyar tayi tana jinta kamar gawa sae jan ƙafa take yi har suka isa gurin motarsa, suna ƙarasawa yaga Daniel a tsaye da alamar ya jima da isowa, kai Abideen ya ɗaga masa nan Daniel ya sara ya nufi inda Class Rep yake. Cikin frontseat ya tura ta ya rufe ƙofar ya koma ya shige sannan suka fice daga makarantar. 


Banda hawaye bbu abunda yake zuba daga idanun Safeerah, kallonsa tayi taga har yanzu ransa a ɓace, jan hanci tayi tace, "Wallahi ba abunda kk tunani bane, wallahi kawai.." bata ƙarasa bh ya katse ta da, "Meya hanaki ɗaukan kirana? What did I tell you the last time?" Ji tayi zuciyarta ta dena bugawa da ta tuno da maganar dan shaf ta manta. "Kayi haƙuri dan Allah ba haka ban.." bata ƙarasa bh ya sake katse ta ba tareda ya kalleta bh yace, "Me na gaya miki akan kula maza?" Rau rau tayi da ido ta cigaba da kuka tace, "Shi kawai class..." bata ƙarasa bh ya daka mata tsawa tareda taka brake, "WILL YOU JUST SHUT UP!" sae da tayi gaba saboda birkin daya taka sannan ta koma baya, a lokacin ya juyo ya kalleta, fuskarta chaɓa chaɓa da hawaye da majina, ga yanda take kallonsa kamar ranta zai fita daga jikinta saboda tsabar tsoro.


 Lumshe jajayen idanunsa yyi ya ɗauke kansa, hawayenta ta share ta kamo hannunsa da ya cigaba da driving tace, "Dan Allah Ya Abideen, wallahi bazan sake.." runtse idanunsa yyi yana ji ransa na sake ɓaci, yace ta rufe masa baki amma sae tayi magana, wanne kalan taurin kai gareta ne. Wata tsawar ya daka mata yace, "Why the hell are you so stubborn? Didn't I just tell you to shut up!?" Kamar mara rai ta zauna tayi shiru tana tunanin yau tata kuma ta ƙare, sai yanda yyi daita idan suka je gida dama ga amsar da ta bashi ranar da dare. 


Kamar a mafarki taji yace, "I'll just have to punish you tunda shine yaren da kika fi ganewa!.." kuka ta shiga rerawa mae ƙuna tana salati a zuciyarta, tana tunanin wani kalan musiba Abideen zae gana mata, yana daga gefe amma ko kukanta baya ji, kansa yyi masa nauyi ji yake kamar an ɗaura masa drum ɗin ruwa akai yana sake jin takaici kula wani da tayi...


★Mae Zaytoona ta gani ne kam?🙉

★Wanni kalan punishment kenan? Muje zuwa...🙂‍↕️🔥


Vote, comment and share please!

Facebook #Fatee Mah

Wattpad #_khanoum_


©️ Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments