TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 51

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕

Page 5️⃣1️⃣

________

Hajiya na fitowa parlourn ta tarar da Aunty Luba da Umma suna dariya, kallon banza ta watsa musu kafin tace, "Ina matar ɗannan take?" Shiru Umma tayi abunta inda Aunty Luba tayi dariya tace, "Ta tafi tana kuka" kallon banza Hajiya ta sake watsa mata kafin tace, "Me kuka yi mata?" Taɓe baki Aunty Luba tayi tace, "Rashin kunya tayi mani daga nayi mata faɗa shine ta fice" Tsaki Hajiya tayi tace, "Da girman ku ku riƙa yin abu kamar yara, Allah Ya kyauta muku" rai a ɓace tasa ƙafa ta fice daga part ɗin ta wuce nata part ɗin. Abba na sallaman Abideen ya fito ya ruɗe ya ƙosa yaje ya samu matarsa yyi mata bayani, Umma na ganinsa tace, "Kai zo nan!" Kamar wani zararre haka ya nufi Umma amma hankalinsa baya gurin gaba ɗaya, a ƙasa yyi wa kansa gurin zama inda Umma tace, "Haka matarka take bata da kunya?" Kallon yanda yyi shiru tayi tana murmushi saboda kansa na ƙasa nan ta cigaba da, "Ace har ni zata yi wa rashin kunya saboda za'a yi mata kishiya?" Shiru ta sake ji yyi nan Aunty Luba tace, "Taya matarka zata yiwa uwarka rashin tarbiyya kuma ka barta? Wannan kawai ka sake ta bata da ɗa'a" still bae ɗago kansa ba bare yace wani abu nan Aunty Luba tace, "Kai Abideen bada kai nake magana ba, kayi mun shiru?" Sae a lokacin ya ɗago kansa a kiɗime yace, "Na'am Aunty me kika ce?" Kallon kallon Umma da Luba suka yi suna mamakin wannan yaro, miƙewa tsaye yyi yace, "Aunty zan dawo wani lokaci" yana faɗin haka ya sa kai ya fice daga parlourn, baki a sake Umma da Aunty Luba suka bishi da kallo suna mamakin yanda hankalinsa ya tashi sosai, rufe baki Aunty Luba tayi tace, "Ah lallai an shanye shi kuwa wallahi wannan idan baki tashi tsaye ba sae ta raba ku" 



Yana fita ya shige cikin motarsa ya cilla motar kan titi, wayarsa  ya zaro ya fara kiran line ɗinta  amma bata yi picking ba, yana jin wayar tana ringing daga baya kuma aka kashe wayar, a firgice yake taka accelerator har ya isa  gidansa, sojan dake kan duty a gate ya tambaya nan ya ce masa ai bata zo gida ba, reverse ya taka yyi hanyar gidan Aunty Jamilah. A parlour ya tarar da ita tana danna wayarta, tana ganin ya shigo kamar an koro shi tace, "Abideen lafiya?" Zama yyi kafin ya girgiza mata kai nan ya zayyane mata duk abunda ya faru, nan Ya Jamilah tace, "Tabbas tana gidansu Safna amma ka kira ta" ɗauke kai yyi yace, "Ina ta trying ta ƙi ɗauka daga ƙarshe kuma ta kashe wayar!" Tashi Ya Jamilah tayi ta koma gefensa tace, "Ka kwantar da hankalinka dae yanzu, ka barta ta huta zuwa Magrib sae kaje ka ɗauko ta, okayy?" Kai ya ɗaga mata kafin yyi mata sallama ya fice daga gidan, ai tun daya fita daga gidan Ya Jamilah ya wuce gidansu Safna yyi parking, a can yyi sallar Laasar da Magrib duka, zama yyi yana baza idanu ko zae ga ta fito amma shiru, can dar ana idarwa da sallar ya shiga motarsa ya ɗauki wayarsa ya danna mata kira, luckily yaji yana shiga. 


Zaune tayi gefen Safna da idanu duk a kumbure tace, "Safna wai aure zai sake!" Zaro ido Safna tayi tace, "Aure kuma? Dan baki da lafiya ne zae sake auren ko mae?" Taɓe baki Safeerah tayi tace, "Nima ban sani ba amma wai cousin ɗinsan nan dana baki labari zae aura" bata ƙarasa ba wayarta ta fara vibration, kallon Safna tayi tace, "Shi yake kira kuma wallahi bazan ɗauka ba" da kyar Safna ta roƙe ta ta kunna wayar amma baza ta iya yi mata dole akan ɗaukar wayar ba, suna a zaunen nan ya kira yafi sau goma, can daya ga haka sae ya turo mata message.


💬Abideen: Dan Allah ki fito muyi magana ina waje, please! 


Message ɗin ta kalla tayi tsaki, jin shiru bayan 10 minutes yasa ya sake kiran wayarta, still ta ƙi ɗauka zuwa lokacin kuwa  ransa ya fara ɓaci, wani message ya sake turo mata.


💬Abideen: Idan baki fito ba wallahi zan shigo gidan na fito dake! 


Tsaf tasan ba ƙaramin aikinsa bane ya shigowa mutane cikin gida ba saboda ba wata kunyar arziki ya cika ba tunda har ya shiga cikin ɗakinta na gidansu ya doke cousin ɗinta, veil ɗinta ta ɗauka ta miƙe nan Safna ta raka ta suka fita waje. A gaban motarsa suka tarar dashi yana tsaye, suna fitowa ya ƙarasa gurin Safeerah ya kamo hannunta, lokaci ɗaya ya koma abun tausayi, rage tsayinsa yyi ya koma daidai ita yace, "Meysa baki jira ni ba kika tafi ke kaɗai?" Fusge hannunta tayi daga nasa tana kallon cikin idanunsa, shima kumburarrun idanunta ya zubawa ido, sae ganin wasu sabbin hawayen yyi suna zuba daga idanunta. Cikin zafin nama ya fusgota ya rungume ta a jikinsa yana shafa bayanta, cikin burgewa Safna ke tsaye daga gefe tana kallonsu. Fusgewa Safeerah tayi kafin tace, "Na fito sae ka koma gurin wacce zaka aura ko me zan yi maka?" Sosai ya tsorata da jin furucinta nan ta juya tayi tafiyarta, bin bayanta yyi yana kiran sunanta amma tayi masa banza sae ma buga ƙofar gidan da tayi bayan ta shige wanda yasa yyi halting steps ɗinsa, Safna dake tsaye ya kalla ya ƙarasa gurin yace, "Dan Allah kiyi convincing ɗinta.." idanu Safna ta zuba masa dan tasan ya fi ta sanin taurin kan Safeerah zuwa yanzu, ajiyar zuciya ya sauke bayan yaji Safna tace, "Meysa baka gaya mata zaka sake aure ba? The poor girl was so shocked!" Sosa ƙeya yyi yace, "Umarnin Umma ne wallahi and she won't expect me to disobey right?" Cize leɓe Safna tayi tana tunanin maganar wa zata yarda da ita can tace, "She made it sound like kai kake son auren saboda bata da lafiya!" Zaro ido yyi kafin yace, "You of all people Safna ya kamata ace kinsan yanda nake sonta, I don't care ko bata lafiya, she's still the woman I love with all my heart!" Murmushi Safna tayi tana sake jin soyayyar su na burgeta, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Ba'a bani choice bane ko tafi so Umma ta tsine mun?" A tsorace Safna tace, "Subhanallah! I'll try my best na fito da ita..!" Kai ya ɗaga mata inda ta juya ta shiga gidan, a gaban motarsa ya koma ya tsaya yana jiran fitowarsu, sun daɗe sosai basu fito ba hakan yasa yyi tunanin ko taƙi yarda ne, wayarsa ya zaro daga aljihu ya kira Ya Jamilah, tana ḍauka yace, "Ya Jamilah taƙi fitowa dan Allah ki kirata ki gaya mata Umma tsine mun zata yi idan ban auri Zaytoona ba" kai ya ɗaga kafin ya kashe. Bae wani sake daɗewa ba Safeerah ta fito itada Safna da ke riƙe da handbag ɗinta, da kyar suka ƙarasa gurin motarsa tana ta faman turjewa kamar shanun daya san za'a yanka shi. Suna ƙarasawa ya buɗe mata motar ta shiga ta karɓa jakan ta ya rufe ya dawo yyi wa Safna godiya sosai kafin ya juya ya shiga motarsa suka bar anguwar, Safna ta daɗe a tsaye sosai kafin ta koma gida tana jin yanda suke burgeta tana roƙon Allah Ya sa wanda zata aura ya so ta kamr haka ko fiye da haka. Allah Yasa Ummanta ba da wuri zata dawo ba saboda Afternoon shift gareta a asibiti sae zuwa tara na dare zata dawo ta barwa ƴan night shift. 


Tunda suka shiga motar ko kallo ɗaya bata mishi ba shi kuwa duk bayan minti minti yake juyowa yana kallonta har suka ƙarasa gida, ɗakinta ta wuce ta barshi a parlour yana binta da idanu kamar maye...


*Next page is steamy, let's go!🥂🔥


©️Fateemah MG



Post a Comment

0 Comments