TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 48

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 4️⃣8️⃣

_______


Tarr ta buɗe idanunta akan sa sae tsintarsa yana kallonta tayi, idanunsu ya daɗe a sarƙe da na juna kafin ya ɗauke idanunsa yace, "Ya jiki?" Bata so amsawa ba amma sun riga sun haɗa ido hakan yasa ta cewa, "Da sauƙi" dan dole. Ji yyi baze iya ƙara ko da minti ɗaya bane sae ya miƙe ya kalli Ya Jamilah yace, "Idan kun shirya ina waje.." cikin sarfa ya fice daga ɗakin baya son sake haɗa ido ta wani daga cikin su, yana fita ya wuce garden ɗin asibitin yyi zamansa a can yana tunanin abun duniya, yana cikin zaunen nan wayarsa ta fara ringing, ko daya duba sunan Abba ya gani a jikin screen ɗin wayar, picking yyi da sallama a bakinsa inda Abba ya amsa sannan suka gaisa, hira suka fara sosai kafin Abba yace, "Jamilah ɗazu ke gaya mun Safeerah bata ji daɗi ba.." wani ɗarrr yaji a jikinsa kar dae Ya Jamilah ta gayawa Abba ne yyi masa faɗa, da kyar yace, "Eh Abba, bata ji daɗi ba amma anjima kaɗan za'a sallame mu" Abba ne ya ɗora da, "Me suka ce yana damunta?" Ajiyar zuciya Abideen ya sauke jin bae san meya faru ba yace, "Ciwon su ne na mata haka!" Haka ya tsinci kansa da faɗi nan Abba yyi dariya yace, "Toh Allah Ya bata lafiya yasa ta sauka lafiya.." zaro ido Abideen yyi jin Abba ya ɗauki maganarsa ta wani shiga amma yyi shiru ya rufa wa Abba da, "Ameen.." a haka dae suka yi sallama Abba ya bar Abideen da zuciya a tsinke, wani ciki shi da ga abun da ya faru...😅


Sae can gurin ƙarfe biyar na yamma Ya Jamilah ta kira Abideen tace, "Ka taho mun shirya.." tana faɗin haka ta kashe wayar. Yana isa yaga Safeerah cikin Hijab ga Ya Jamilah dake riƙe da ita, Safna a gefe kuma tana riƙe da basket ɗin abincin da ta zo dashi da kuma wasu bags da Abideen ɗin ya kawo, fita suka yi a ɗakin shi kuwa Abideen yana bayansu, har sun sauka ƙasa gurin Reception Ya Jamilah ta saki Safeerah zata yiwa Receptionist ɗin magana, Safeerah dae ta tsaya tana ta ɗauriya da kyar can taji kamar zata faɗi ai kuwa ta kusa turguɗewa Abideen yyi sauri ya kamo hannunta, sae da ta gyara tsayuwarta tayi saurin kallon fuskarsa nan ta ɗauke kai ta fusge hannunta daga nasa, shiru yyi bae ce komai ba sae matsawa baya da yyi ganin Ya Jamilah na nufo su, murmushi Safna tayi da take bayansu tana ganin komai, wayarta da yyi ringing ta ɗauka tace, "Eh na fito.." 


A haka dae suka ƙarasa parking space, Safeerah na shiga backseat wani saurayi ya taho gurin tareda Safna, yana da kyaunsa sosai ga tsayi da haiba. Yana ƙarasowa ya gaishe da Ya Jamilah cikin martabawa sannan ya leƙa Safeerah a mota yace, "Madam ya jiki? Allah Ya ƙara sauƙi.." "Da sauƙi" Safeerah ta amsa daidai da ƙarasowar Abideen yaga wani yana yiwa matarsa magana har tana amsawa, hannu saurayin ya miƙawa Abideen su gaisa, bae yi niyyar amsa ba amma ganin Ya Jamilah da Safna suna kallonsa yasa ya amsa sannan saurayin yace, "Toh Allah Ya ƙara sauƙi.." yana faɗin haka ya juya ya wuce, murmushi Safna tayi wa Safeerah tace, "Allah Ya ƙara sauƙi, zan zo na sake duba ki InshaAllah.." kai Safeerah ta ɗaga tace, "Toh zan kira ki.." da haka Safna tace, "Aunty Jamilah Allah Ya huta gajiya.." murmushi Ya Jamilah tayi mata sannan ta shiga gidan gaba inda Abideen ya shiga motar ya kunna ta, Safna kuma ta bi bayan saurayin suka shiga motarsa zae ajiyeta a gida. 


Tafiya akeyi amma hankalin Safeerah yana can tana tunani yanzu gidan Abideen za'a mayar da ita, Ya Jamilah na kallon yanda Abideen ya riƙa kallon Safeerah ta rear view mirror, taɓe baki tayi tareda ɗauke kai har suka isa gida. Yana parking motar kafin kowa ya fita tace, "Ka ɗauko mata kayanta zuwa idan taji dauƙi sae ta dawo.." da sauri Abideen ya juyo ya kalli Ya Jamilah zuciyarsa na wani irin bugawa. Ya Jamilah na faɗin haka ta ɗauke kanta daga gareshi bare yyi mata idanun tausayi, jiki a sanyaye ya sauka daga motar ya shiga cikin gida, fitowa Ya Jamilah tayi ta taimaki Safeerah ta fito daga cikin motar Abideen ta mayar da ita cikin motarta da tazo dashi, sun ɗan jima cikin motar ya fito riƙe da jaka, yana sakawa a backseat Ya Jamilah ta yi reverse, tsayi yyi shi kam ya ma rasa mae zae yi har suka fita daga gidan, ya daɗe a tsaye sosai kafin ya fita ya wuce Masjid inda bae koma gidan ba sae bayan da aka yi sallar Ishaa. Dinner yyi order ya zauna a dinning table yana ci amma duk bbu daɗi, sae a yanzu yake sake tabbatar da kalan son da yake yi mata dan sosai yyi kewarta yana jin gidan bbu daɗi, a 3-settee ya ɗan kwanta amma a haka bacci ya kwashe shi. 


Ita kanta kwana biyun da tayi a gidan Ya Jamilah sae da taji ta gaji, ta saba ita zata yi aikin gidanta da girki amma anan duk ƴan aiki suke yin komai sae dae ta ɗan yi hira da Ya Jamilah, kaɗan da kaɗan taji kewar mijinta yana sake dasuwa a ranta, shi ma a can ɓangaren da kyar yake iya yin harkokin gabansa duk yyi kewarta ya ƙosa ta dawo, cikin kwana biyun nan sosai ya rame ya faɗa duk ya lalace. A kwana na uku dama haka Ya Jamilah tayi niyya tun farko, zaune Safeerah tayi TV ne gabanta amma kallonsa kawai take dan hankalinta baya kansa, a cikin kwana biyun ma dan Safna ta zo ta leƙa jikin nata ne yasa ta ɗan ji dama daman kaɗaicin dake damunta, ido Ya Jamilah ta zuba mata ganin duk hankalinta baya nan. Wayarta ta ɗauka tayi dialling numbern Abideen ɗin, yana ganin kiran Ya Jamilah around biyar na yamma yyi saurin ɗauka, yana picking Ya Jamilah tace, "Kazo ka ɗauki matarka."


 Tana faɗin haka ta kashe wayarta, wani farin ciki ne ya lulluɓe shi da sauri ya shige bathroom yyi yo wanka ya sake kaya yyi shiri cikin yaɗi baƙi da yaji zubin golden zare, sosai yyi kyau kuma cikin kwana biyun nan yyi shaving sae ramar tasa ta sake nunawa sosai. Ita dae Safeerah ido ta zubawa Ya Jamilah jin furucinta sae daga baya hankalinta ya dawo kan abunda yyi mata, rau rau tayi da ido ta tashi ta koma kusa da Ya Jamilah ta ɗaura kanta akan kafaɗar Ya Jamilah tace, "Ya Jamilah dan Allah kice ya fasa zuwa kinga ban gama warkewa ba fah.." kallonta Ya Jamilah tayi tace, "Kin gama shanye magungunan ai" yi da fuska tayi kamar zata yi kuka kafin ta sake cewa, "Ya Jamilah dan Allah kar ya tafi da ni.." banza da ita Ya Jamilah tayi har suka daɗe sosai a zaune, basu wani daɗe ba sosai aka yi knocking sae ga Abideen ya shigo cikin parlourn, gaishe da Ya Jamilah yyi yana sosa ƙeya yana ɗauke kai, sae a lokacin Safeerah ta buɗe idanunta da ta runtse ta sauke su akansa, wani haske da rama taga yyi ba ƙaramin tsorata ta yyi ba kamar wanda yyi watannin a asibiti..


Wani zabura tayi daga jikin Ya Jamilah ta ƙarasa gurin shi ta zauna a gefen shi, cikin muryar kuka ta kai hannunta kan fuskarsa tace, "Ya na.. ga kaa.. raame??" Shiru yyi mata yana kallon fuskarta da yanda ta ɗan sake yin haske, bae ɗauke idanunsa daga kanta ba yace, "Ya jiki?" Bata amsa shi ba tace, "Ba ka da lafiya ne?" Sheƙan kuka kuwa yanzu ta fara da gaske, Ya Jamilah dae tana daga zaune tana ganin ikon Allah kafin ta miƙe ta ɗauko mata kayanta tunda ita ƴar daɗi miji ce... 


Next chapter loading....✨️

Wattpad @_khanoum_

©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments