TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 97-98

 97 & 98



Tun daga wannan lokacin zama na yaci gaba da kasancewa a gidan yaya Faruka a Abuja.



Sai dai zama na a Abuja ba wani ci gaba da na samu na raguwar damuwa ta sai ma k’arin damuwa da na samu saboda yanda zaman kad’aici yake damu na in Nana ta tafi makaranta, ga rashin sakewar fuskar yaya Faruk da ba na gani, in an ga walwala ta wani lokacin bai wuce gurin Nana ba, sai wani lokacin in Nana za ta je block d’in Anty Maryam ta kan nemi rakiyata.



Ba laifi muna waya da yaya Khalil da Anty Jidderh da Ummu, yaya Aminu ma yak an kira ni, Anisa ma da Halima da Aisha muna waya dasu, Dadi da Momi sun kira ni sun jajanta min abin da ya faru, san da Dadii ya kira ni haka ya dinga kwantar min da hankali da min nasihohi masu ratsa zuk’ata, tabbas na ji dad’in maganganun Dadi da ya fad’a min.



Zaman Abuja ya ishe ni, ji nake yi kamar in yi tsuntsuwa in ganni a gaban iyaye na, sai dai abin da yake k’ara sanyayar min da jiki shine duk wayar da muke yi da Ummu ban ji wani labari mai dad’i a gurin ta na cewa Abbu ya hak’ura da fushin da yake yi, nasan in har Abbu ya sauka daga fushin da yake yi zai nemi da in dawo gida.



Duk wanda ya ganni a lokacin sai ya tausaya min, na yi bak’i na rame, da ka kalle ni kasan ina cikin damuwa, Na dawo so silent & cool.



Tun ina mamakin rashin kiran wayar Dr da bai min ba har na daina dan nasa ma raina cewa a yanzu na daina d’aura ma kaina wani tunani a game da soyayyar Dr, nasan a yanzu ba ta ni yake yi ba, ta amaryar da yake shirin yi yake yi, na san cewa dole wataran sai Dr yayi nadamar abin da ya min dan ya ci amanar soyayyar da na mishi ta gaskiya.



Haka na ci gaba da zama a gidan yaya Faruk, gashi a yanzu ina neman wata d’aya a gidan, kullum buri na shine in ji Ummu ta ce Abbu ya ce in dawo gida.



Ganin har yanzu Yaya Faruk bai ce min komai ba ga me da komawa ta Kaduna amma har yanzu shiru, hakan yasa nayi shahadar tunkarar Yaya Faruk.



Samun shi nayi a falo yana kallon wani American film.



Tun da na gaishe shi ya amsa min ba Wanda ya sake magana a tsakanin mu.



Ganin zaman ya ishe ni gashi ni American film d'in ba wani damu na yayi ba yasa na kau da shirun da cewa " Yaya Faruk in ban takura maka ba ina so muyi magana ne".



"Ina jin ki" ya amsa min ba tare da ya daina kallon da yake yi ba.



Nisawa nayi kana na ce "Yaya Faruk daman na ji shiru ne har yanzu ba ka min maganar komawa ta Kaduna ba kuma Yaya Faruk Sai na ga kamar zama na kamar ina takura mu ku ".



Sai a lokacin ya d'ago ya kalle ni.



Cikin d'aurewar fuska yace " Yanzu me kike so a miki da kika zauna kina min explanation, k'ofa a bud'e take in za ki koma Kadunan ne, in ban da ke stupid ce za ki zo kina ce min wai ko kin takura mana, dan uban ki ni ko Khadija ce muka ce kin takura mana ko kin ga wata alama ta an gaji dake ne?" ya k'arasa maganar yana kallo na.



Hawaye ne ya tarun ma a ido, danasanin tunkarar Yaya Faruk nayi da wannan maganar, ga zagin da ya min ya min ciwo amma ba halin in nuna.



Tsawa ya daka min ya ce "Ba da ke nake magana ba Fatima, ko Sai kin ji a jikin ki".



Girgiza mi shi kai nayi alamar a'ah, dan nasan in na yi magana kula ne zai biyo baya.



Yaya Faruk ya d'aura da cewa " Ke in ban da ba ki da kunya ba, ban yi tunanin za ki iya tunkara ta da maganar cewa wai kin ji shiru akan maganar komawar ki Kaduna, ko da yake tuntuni na fahimci kin canza dabi'un ki, saboda haka ba abin mamaki bane, in kinga  kin koma Kaduna to Abbu ne ya ce in dawo da ke, ke in ban da baki da hankali ma Fatima, ni ina sha kin zo ne ki min magana akan in kira Abbu da Ummu in basu hak'uri amma shine za ki zo min da rubbish words d'in ki, in kin San zaman wani guri zai takura ki me yasa tun farko kika yarda da sharad'in Abbu, sai yanzu za ki zo kina min complain, in kika k'ara tunkara ta da wannan maganar sai jikin ki ya fad'a miki, kar kiyi zaton ko yanzu kin girma, a guri na har yanzu ke yarinya ce a guri na, dan haka ki tashi ki ba ni guri".



Wani irin abu ne ya tsaya min a mak'oshi na d'acin maganganun da Yaya Faruk ya fad'a min, nasan duk maganar da Yaya Faruk ya fad'a min ni na jawo ma kaina.



Gaba d'aya jiki na ba laka haka na tashi na koma d'aki na dasa kukan b'acin ran maganganun da Yaya Faruk ya fad'a min.



Da na gaji da kukan ne na goge hawaye na.



Ni kaina yanzu nasan kuka ya zama abin ci na dan yanzu abin kuka ba ya min yawa.

 




Yau Dadi ne ya sami Abbu a office d’in su na Wagini motors.



Bayan sun gaisa ne su ka tattauna akan b’angaren business d’in su, daga nan Dadi ne ya canza hirar da zuwa magana ta.



Dadi ne ya ce "Ibrahim akwai maganar da na ke so mu yi".



Abbu ne ya amsa masa da cewa "To yaya ina jin ka".



"Ibrahim tun san da ka fad’a min an saki Fatima ban k’ara jin kayi maganar ta ba, na ji duk abin da ya faru da ka cewa Faruk wai Fatima ta bar gidan shi sannan kai kuma ba ka ce ta dawo gidan ka ba, abin da yasa ban ce ma Faruk ya kawo ta gida na ba saboda nasan in ta je Abujan za ta samu sauk’in damuwar da take ciki, da ka ce ta tafi to ina kake so ta je? San da ka sa ma Fatima sharad’in na d’auka saboda a lokacin ran ka a b’ace yake shi yasa, ashe kai da gaske ka ke yi, wannan hukuncin da ka yanke sam ba mafita ba ne, nasan Fatima tayi laifi a baya amma kuma ba wanda ya wuce kuskure, duk abin da ka ga ya samu mutum to Allah ya k’addara hakan zai same shi ko yaso ko yak’i, in dai Allah yace (kun) kasance to sai ya kasance, in ita Fatima yarinya ce da k’uruciya kai ai mahaifin ta ne, dole ka mata uzuri a matsayin ta na y’ar da ka haifa, nasan ita kan ta Fatiman sai tayi nadamar abin da ta aikata a baya sannan ba inda za ta ji dad’in zama fiye da gidan iyayen ta, nasan ita ma mahaifiyar ta d’in hankalin  ta ba a kwance yake ba akan abin da ya sami Fatiman sannan gashi ba a gaban ta take ba, na zuba maka ido ne dan in ga iya gudun ruwan ka amma na ga kai ba ka da ranar sauka daga fushin da ka yi, hakan da ka yi ya nuna kamar ba ka yarda da k’addarar da za ta iya samun bawa a ko wani lokaci ba, saboda haka ina so Ibrahim ka amince da dawowar Fatima gidan ka sannan ka mata addu’ar Allah ya zab’a mata abin da yafi alkhairi sannan ka yafe mata kuskuren da tayi maka a baya".



Nisawa Abbu yayi kana ya ce "yaya na yafe ma Fatima abin da ta min, na kuma gano kuskuren da nayi na cewa kar ta tunkare ni da matsalar ta in ta sami matsala da mijin ta, zan ma Faruk d’in magana ya dawo da ita".



"yawwa Ibrahim hakan ya kamata ka yi, hak’uri ake yi da yara, Allah ya shirya mana zuri’ar mu baki d’aya" cewar Dadi.



"Amin ya Allah" Abbu ya amsa.



Da haka Dadi ya koma office d’in shi dan ci gaba da aikin shi.



Ganin har yanzu Yaya Faruk bai ce min komai ba ga me da komawa ta Kaduna amma har yanzu shiru, hakan yasa nayi shahadar tunkarar Yaya Faruk.



Samun shi nayi a falo yana Da





A b’angaren Dr kuwa ya ci gaba da mu’amalar shi da zuwa ayyukan shi cikin kwanciyar hankali.



Wani lokacin in ya ga tunani na zai kama shi sai yayi saurin kau da tunanin.



Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka sa bikin Dr da Meema.



Wata d'aya kawai aka sa kasancewar ko wani b'angare a shirye su ke.



Meema tun da taji an yi fixing d'in bikin su ta rasa in da za tasa kan ta saboda murna.



Shirye-shirye da event suka dinga shirya ita da Hanan.



A gurin Dr kuwa ba yabo ba fallasa haka game da shirye-shiryen bikin.



Komai aka sa ma rana sai yazo dan a yau ne aka d'aura auren Meema da Dr.



Wani b'angare a gidan Dr ya gyara ma Meema saboda gidan babba ne.



Ko san da aka d'aura auren Dr bai yi wani farin ciki ba, yasan ya amince da auren ne saboda yayi ma Momin shi biyayya da kuma tausaya ma Meema da yake yi.



Ran first night d'in su da ya kasance da Meema yayi mamakin samun ta a virgin da yayi saboda ganin yanda ta ke a waye, sai dai da difference is clear.




Yafi jin dad'in kasancewa da ni akan Meema, yasan ni ta daban ce da baiwar da Allah ya min, yasan zai yi wuya ya samu iri na wajen faranta mi shi yanda yake so.



Tun a nan ya fara missing d'ina, saurin kau da tunani na yayi a ran shi, a yanxu yana ganin bai da buk'atar yin tunani na tun da nuna ban damu dashi ba tun da ban ne me shi ba tun da muka rabu.

 


A haka zaman su ya ci gaba da kasancewa, ba laifi Dr yana ba ma Meema Kula ita ma Meema tana k'ok'arin yin abin da Dr ya ke so da kauce ma abin da bai so.




Da zama yaci gaba da gudana a tsakanin su ne zaman nasu ya fara canza salo.



Matsalar da suka fara samu shine rashin son yin girki da Meema ba ta son yi saboda ba wani iya different foods tayi ba kasancewar tun tasowar ta ba ta shiga kitchen da niyyar yin girki har tafiyar ta turai karatu, ko a can tafi gane ma yin take away, sai in taso ne za ta yi simple food, ko da ta dawo gida Nigeria bai sa ta maida hankalin ta wajen koyan girki ba, abin da ta fi maida hankali shine dafa indomie da kuskus da dai irin simple food , sai dai ta ce ma Dr yaje restaurant ya musu take away, hakan ba k'aramin b'ata ma Dr rai yake yi ba kasancewar shi mai k'yank'yami ne, ba ya son cin abinci waje, hakan yasa wani lokacin yake zuwa gidan Momi yana cin abincin, ga fita da take yi without his permission, idan yayi mata magana sai tace mi shi tana da damar zuwa in da ta gadama dan ita ba matar kulle ba ce, ga yin shigar da ta gadama ko za ta fita ne ba tare da tayi la'akari da cewa a yanzu ita matar aure ce, gashi sometimes ba ta yarda dashi in zai yi love making da ita, sai dai in ita ta gadama, a tak'aice dai Meema nayi duk abin da ranta yake so.



Kasancewar shima Dr d'an Human right ne da koyi da rayuwar turawa yasa bai cika damuwa da sa mata ido akan al'amuran ta ba, daga baya ne da yaga abin na ta ba na k'are ba ne yasa suka fara kai ruwa a tsakanin su.



Wani lokacin in ya mata fad'a takan d'auka saboda son da take mi shi amma da an kwana biyu za ta dawo yin abin da ta gadama.



Tun Dr na mata fad'a akan abin da take yi har ta kai ga yanzu tana maida mi shi magana dan ita a ganin ta ba za ta iya rayuwar takura ba.



Wani lokacin in ya  ma Momi complain akan halin Meema sai dai ta ba shi hak'uri dan tana ganin kamar yanakawo k'arar Meema ne dan ba choice d'in shi ba ce, daga baya da ta gano gaskiyar maganar da Dr yake fad'a mata akan Meema yasa ta ci gaba da bashi hak'uri had'e da kwantar mi shi da hankali.



Dr ya fara shiga damuwa akan irin wannan zaman da suke yi da Meema.



A lokacin ne ya fara danasanin rabuwa da yayi da ni, ga kewa ta dake addabar shi, hakan yasa damuwar ta mi shi yawa.



Shi kan shi in ka ga Dr kasan ya canza in kayi duba da ramewar da yayi.





Yau ranar ta kasance ranar lahadi, Dr yana gida yana hutawa yayin da Meema ke cikin d'aki.



Meema ce ta fito cikin wani irin material mai tsada transparent kalar pink yayin da yafa d'an k'aramin veil a kan ta.



Cikin takun k'asaita take tawowa, ba abin da kake ji sai k'arar takalmin ta, hakan yasa Dr ya d'ago ya kalle ta.



Cikin murmushi ta zo ta zauna kusa dashi.



D'aure fuska yayi yana ci gaba da kallon ta.



"Ina za ki ne Meema na ga kin yi shirin fita?".



Meema ta amsa mishi da cewa " Yau birthday d'in Leema, shine nake so in je".



Da mamaki Dr  ya kalle ta ya ce "At this tym za ki birthday, yanzu fa aka yi sallar magrib, shine kike shirin fita, wai da izinin wa za ki fita".



"Haka aka yi fixing din tym d'in sannan kasan dai yanda mu ke da Leema, kasan ya kamata in halarci birthday d'in ta" Meema ta fad'a kai tsaye.



" Ba za ki ba" Dr ya fad'a.



Da sauri ta kalle shi ta ce "Because of what yaya Sadik za ka ce ba za ni ba".



Dr ne ya ce " Saboda ni ke da iko da ke tun da ina matsayin mijin ki".



"Amma Yaya Sadik kasan dai Leema ba za taji dad'i ba in ban yi attending ba saboda kasan she is my close friend" Meema ta fad'a cikin marairaicewa.



"That's your business not mine" Dr ya fad'a cikin ko in kula.



Wayar shi ya fara pressing ba tare da ya k'ara kula ta ba.



Mik'ewa tsaye tayi cikin b'acin rai ta ce " Am sorry Dr, but i must attend that birthday, akan nayi aure sai ka ce ba zan dinga fita ba, am social yaya Sadik, so gaskiya ba zan juri takura ba, sai na dawo Yaya Sadik".



Tana gama fad'ar haka ta nufi bakin k'ofa. 



Bin ta yayi da kallo har ta fita daga d'akin.



Dafe kan shi yayi saboda a yanzu ba ya jin zai iya jurar abin da Meema ke mi shi.



Nadamar rabuwa da ni ne ya fara d'awainiya dashi.



A yanzu ya rasa mafitar da zai Samar wa kan shi.



Tashi yayi ya d'auki key d'in motar shi ya bar gidan.



A can b'angare na kuwa gashi ina Neman fin wata a Abuja amma har yanzu babu alamar komawa ta Kaduna.



Tun san da Yaya Faruk ya fad'a min magana san da na mi shi magana ya fad'a min magana na k'ara shayin in k'ara tunkarar shi da maganar.



Abbu ya kira yaya Faruk ya mi shi magana akan ya dawo dani Kaduna.



Yau ina zaune a d'aki Nana ta shigo ta sanar da ni yaya Faruk na kira na.



Bayan ta fita ne na biyo ta a baya.



D'aya daga cikin kujerun na nemi guri na zauna.



"Yaya Faruk sannu da hutawa" na fad'a.



"Yawwa" ya fad'a a tak'aice.



Ni ce na ce "Gani yaya Faruk".



"A satin nan in na samu free time zan maida ke Kaduna, Abbu mun yi waya dashi ya ce in dawo da ke".



" To yaya Faruk " na fad'a cikin sanyin murya.



Shiru ne ya ratsa kafin yaya Faruk ya d'aura da cewa "Za ki iya tafiya".



Tashi nayi na koma d'akin.



Abubuwa biyu ne suka had'un min a lokacin, farin cikin komawa ta Kaduna da kuma fargabar had'uwa ta da Abbu.



A satin yaya Faruk ya nemi excuse a gurin aiki.



Ran da za mu tafi sai da na ji wani iri a raina saboda yanda muka saba da Nana.



Naji dad'in  zama da ita saboda yanda ta ke sakar min fuska duk da tasan alak'ar soyayya ta tab'a had'a ni da mijin ta, halayen Nana sun burge ni saboda yanda ba ruwan ta da shiga harkar abin da ba ruwan ta, gashi magana ba ta dame ta ba.



Da za mu tafi haka ta had'o ni da tsaraba.



Har gurin mota ta raka mu, sai da ta ga fitar mu sannan ta koma cikin gida.



Tun da muka d'auki hanya ba Wanda ya kula d'an uwan shi har muka kawo Kaduna.



K'ira'ar Sheikh Shureim kad'ai ke tashi a motar.



Wannan tafiyar ba ta min dad'i ba saboda yanda shirun ya min yawa, shi yaya Faruk nasan daman magana ba damun shi tayi ba.



Tun da muka doshi gidan mu gaba na ke fad'uwa har mu ka k'arasa cikin gida.



Ko da muka isa parking space yaya Faruk ya riga ni fitowa.



Jiki a sanyaye na fito na bi shi.



San da na shiga samun yaya Faruk nayi suna gaisawa da Ummu.



Sallama nayi Ummu ta amsa min.



Tun da na shigo Ummu ta ke bi na da kallo.



A lokacin ba abin da nake buk'ata da ya wuce in ji ni jikin Ummu.



Jikin Ummu na fad'a na fashe da kuka.



Ummu cikin lallashi ta fara shafa baya na tana cewa "Miye abin kuka".



" Ummu am sorry, ki yafe min" na fad'a cikin kuka.



"Ya isa haka Auta, ai na ce na yafe miki, ki je d'aki anjima za muyi maganar".



Had'a ido muka yi dashi yayi saurin kau da fuskar shi.



Tashi nayi na tafi d'aki na, d'akin da na d'auki shekaru ba na kwana a cikin shi sai gashi a yanzu na dawo da niyyar zama a cikin shi.



Haka naci gaba da kuka na har bacci yayi awon gaba dani.



Bayan tafiya ta d'aki ne Ummu ta dinga yi ma yaya Faruk godiya a bisa rik'e ni da yayi.



Sun jima suna hira kafin ya mata sallama akan da daddare zai zo su gaisa da Abbu.



Da daddare tun da naji dawowar Abbu na rasa sukuni.



Ummu ce ta shigo ta min magana akan in fito in gaida Abbu.



Jiki a sanyaye na fito daga d'akin na tsugunna nesa da Abbu.



San da na gaishe da Abbu ba laifi ya amsa min ba yabo ba fallasa.



Abbu ne ya d'aura da cewa "Fatima, a yanzu nasan kin fahimci mecece rayuwa da yanda rayuwa ka iya canzawa a kowane lokaci, nasan a yanzu ki d'auki darasi ko akan abin da shi Sadik d'in ya miki, Ni da Ummun ki wani irin so da kulawa da so ne ba mu nuna miki ba amma saboda soyayya kika zab'i faranta ran ki akan namu farin cikin, a gaban mutane Fatima nasa miki sharad'i dan ki janye k'udurin ki amma ba ki duba hakan ba kika ce kin amince da sharad'in da na sa miki, ko a lokacin raina ya b'aci da abin da kika yi amma saboda fushi na illah ne a gare ki yasa nayi saurin yafe miki a lokacin, yanzu kin ga sakayayyar da Makauniyar soyayya ta jawo miki, shi yasa San da Faruk ya zo min da maganar ki na ce mi shi kar ya kawo min ke tun da ke da kan ki kika yarda da sharad'in da na sa miki, ko a yanzu na ji ciwon rabuwar da kika yi da shi Sadik d'in".



Maganganun Abbu ba k'aramin tab'a min zuciya yayi ba, nasan ban kyauta ma su Abbu ba.



Kusa da Abbu na zo na tsugunna ina cewa " Abbu ka yafe min, na gano kuskure na, insha Allah ba zan k'ara kwatanta irin laifin da nayi ba..."  Na k'arasa maganar da fashewa da kuka.



Sunkuyar da kan shi Abbu yayi kana ya d'ago ya kalle ni ya ce " Na yafe miki Fatima".



"Na gode Abbu" na fad'a cikin kuka.



Ummu ce ta d'aura da cewa " Fatima ita Makauniyar soyayya da kike gani ba ta da amfani, ba abin da take jawowa fa ce danasani, duk soyayyar da idon ka zai rufe ba ka ji ba ka gani sannan ba ka duba me nan gaba za ta haifar maka sannan ba za ka ji shawarar da mutane suke ba ka akan ta ba, to wannan soyayya ba alkhairi ba ce, ina fatan kamar yanda kika fad'a cewa kin gano kuskuren ki hakan yake har cikin zuciyar ki, ina fatan kin d'auki maganar da ni da Abbun ki muka mi ki".



"Na d'auka Ummu, insha Allah ba zan k'ara kwatanta irin laifin da na yi a baya ba" na fad'a.



Haka Abbu da Ummu suka ci gaba da min fad'a da nasiha kafin daga bisani Abbu yace in tafi in kwanta.



Tun daga wannan lokacin na samu sukuni a raina had'e da walwala saboda yanda na samu yafiyar iyaye na.



Cikin ikon Allah sai gashi Allah ya cire min k'ulafuncin Dr a raina.



Na cire ma raina tunanin shi dan guje ma kaina wata matsalar.



A haka na ci gaba da zama a gidan mu.



Lokacin da muka yi waya da Aisha take cewa za tazo gida na nake fad'a mata rabuwar da muka yi da Dr.



Ta jajanta min kana ta ce min za tazo.



Ba a d'au wasu lokaci ba sai gashi tazo.



A hirar da muka yi da ita ne take fad'a min taji labarin Dr ya yi aure.



San da ta fad'a min ban nuna damuwa ta ba duk da a lokacin sai da na ji b'acin rai a zuciya ta.



Mun dad'e da ita muna hira kafin ta min sallama ta tafi.



A haka lokaci ya dinga tafiya, sai gashi har na gama iddah ta, har lokacin Dr bai maida ni d'aki na ba.



Hakan yasa Abbu yasa aka je gidan Dr aka d'ibo min kaya na. 



Tun bayan tawowa ta daga Abuja muna waya da Nana muna gaisawa da ita, San da ta kira ni ne take fad'a min sun rubuta final exam d'in su, ta had'a Degree d'in ta, na taya ta murna kana muka yi sallama.



Yanzu ma Anisa tana final class d'in ta na Degree.




Yau muna zaune da Abbu da Ummu muna hira da daddare bayan tafiyar su Yaya Aminu da Yaya Khalil.



Bayan mun gama hirar ne Abbu ya kalle ni ya ce "Fatima tun da kin gama iddar ki, ina ganin ya kamata ki shirya ki je can Wagini gurin Hajiya, ina so in Neman miki aiki saboda ki rage zaman kad'aici, in an sami aikin zan sa Khalil ko Aminu su je so d'akko ki".



Jin tafiya ta Wagini yasa jiki na ya k'ara sanyi, a yanda na fahimta in na tafi Wagini ban San ranar dawowa ta ba tun da Abbu yace sai ya Samar min aiki, babban fargabata shine yanda in naje Hajiya za ta tasa ni gaba akan rabuwa ta da Dr dan tun lokacin da ban auri yaya Faruk ba tasa ni a gaba, nasan in dai naje Wagini sai nayi hak'uri da Hajiya, a yanzu ban da kuma damar cewa Abbu ba na son zuwa Waginin ko dan kar in b'ata ma Abbu rai.



" Allah ya kaimu Abbu" abin da na iya fad'a kenan.



"Amin Fatima" cewar Abbu.



Jiki a sanyaye na tashi na tafi d'aki.




Post a Comment

0 Comments