TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 43

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 4️⃣3️⃣


_______

Dawowarsa kenan daga gym wani ƙamshi ya daki hancinsa, tsintar kansa yyi da nufar kitchen a nan ya ganta tana ta stirring abun da ke ƙamshi a pot, ganin ta tashi da wuri sosai yasa shi mamaki kuma ga gidan tsab alamun ta daɗe da tashi kuma it's just 9, ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya wuce part ɗinsa, wanka yyi ya shirya cikin white long-sleeved shirt da baƙin wando, ko daya sauko downstairs ganinta yyi a parlour tana rungume da Juman kamar zata saka ta a ciki, kallonsa tayi a faƙaice tace, "Ina kwana.." bae amsa da wuri can kuma taji yace, "Lafiya.." dinning table ya wuce nan yaga ta zuba komai ta rufe da plate maybe tasan ya shigo ɗazun dama, abinci ya fara ci cikin natsuwa har ya gama ya haɗa kayan ya kai kitchen da kansa, ita dae tana daga zaune idanu ta raka sa dasu dan tayi mamaki, kafin ya fito ta haye upstairs tayi wanka ta shirya cikin wata fitted gown da tayi mata kyau sosai. 


Daga nan tayi zamanta a ɗaki, can taji motsinsa ya wuce part ɗinsa, bae wani daɗe ba ya fita ya shiga ɗakin Safeerahn, wani envelope ya bata da yasa zuciyarta tsinkewa, da kyar muryarta ya fita tace, "Na meye?" Kallonta yyi yana lumshe ido jin yadda take wani rikitaccen ƙamshi yace, "Ki ba wa friend ɗinki, what's her name again... Safna.." yana faɗin haka ya juya yyi ficewarsa inda ta bishi da ido, jin kamar fita zaeyi daga gidan yasa tayi saurin tashi ta bishi downstairs, bae kai ga fita ba tace, "Dan Allah ina son Shawarma da Ice-cream on your way back..." juyowa yyi ya kalleta sannan yyi tafiyarsa ya barta a tsaye, ita take fushi dashi saboda yyi mata faɗa jiya so meye nashi nayin banza da ita, turo baki tayi kamar yana ganinta tace, "kai dae ka sani" ɗakinta ta koma ta kirawo Safna inda Safna tace zata turo mae Napep yazo ya karɓa saƙon, haka aka yi kuwa ta aiko aka karɓar mata saƙon, ko daya isa gareta kuɗi ta gani a ciki kuma masu yawa sosai. Mamaki tayi toh saboda me Abideen zae bata kuɗi. (*Tukuicin wayarwa madam kai da book ɗinnan😂*)


Ba shi ya dawo gidan ba sae bayan sallar Azahar, tana idar da salla ta shige kitchen ta fara kiciniyar dafa lunch kafin ya dawo, kamar da wasa kuwa take ji kamar ƙaran motarsa, ina yaje ma oho tunda taga ya dena zuwa office tun bayan kwana biyu da suka wuce, shigowarsa parlourn ko a jikinta ta ko ƙi zuwa tayi masa sannu da zuwa da sunan tayi fushi dashi, zamanta tayi a kitchen har sae da ta tabbatar abincin nata ya gamu, lokacin da take kitchen taji kamar ƙaran doorbell da take kwashe abinci amma yanzu tabbas tasan taji motsin shigowar wani.


Tray ɗin abincin ta kwasa ta fita dasu daga kitchen, tana ajiyewa kan dinning tabla ta ɗaga kanta mae zata gani...

Cake ne a ajiye akan table ɗin parlour sae kuma Zaytoona dake tsaye ta wani ƙanƙame Abideen da sunan runguma, ƙoƙarin ɓanɓareta daga jikinsa yake amma sae ƙara manne masa take yi, ana cikin haka idanunsa ya faɗa cikin na Safeerah, ji yyi wani ƙarfi ya zo masa hakan yasa ya fusge jikinsa tareda ture Zaytoona gefe ita ko a jikinta dan ƙara yashe bakin daya sha lipstick tayi tana cewa, "Happy birthday Yaya nah.." wani kalan dumm Safeerah taji a zuciyarta, yau birthday ɗinsa shine ko ya faɗi mata wani kalulu ne ya taso mata a wuya hakan yasa ta nufi upstairs zata haye taji muryar Zaytoona tace, "Aunty amarya ina wuni.." banza da ita Safeerah tayi sae ma fara hayewa steps ɗin cikin karkaɗa da yanga, Abideen daya zuba mata ido ji yyi kamar zae zube a ƙasa ganin yanda kayansa ke rawa, lumshe ido yyi yana cize leɓensa na ƙasa bae kura da cewa Zaytoona na kallonsa ba, bata wani damu ba ta samu guri ta zauna tace, "Yaya mu yanka cake ɗin!"


Shiru yyi mata hakan yasa ta miƙe ta wuce kitchen, yanda taga gidan fess sosai tasan cewa matar gidan mae tsafta ce ajin farko, wuƙa madaidaiciya ta ɗauko da plate ta koma parlourn.  Yanka wa tayi ta ɗauko tace, "Yaya haaa.." shi kansa bae san lokacin daya buɗe baki ba, tana saka masa baki kuwa daidai lokacin Safeerah ta fito daga ɗakinta sanye da mayafi tana riƙe da jaka kuma akan idanunta Zaytoona ta bashi cake a baki, ita kanta ya ma ɗaure wai ƴan uwa ne ko masoya, duk da tasan Abideen is not interested in her kawai abun yana bata haushi ta ga wata na shishshigewa mijinta, wani yawu mae kauri ta haɗiye ta fara saukowa daga stairs ɗin cikin zarra. 


Shi dae Abideen cake ɗin daya kasa taunawa kenan, matarsa ya bi da ido yana ji kamar tana tafiya da numfashinsa, cake baze taunun masa ba hakan yasa ya haɗiye shi guda, cake yyi wa maƙogoransa girma ai kuwa ya maƙale ya ƙi ya wuce, ga numfashinsa dake neman ɗaukewa ganin kyau irin na matarsa, nan da nan idanunsa suka fito sukayi ja, jijiyoyin kansa suka miƙe sosai. Hannu ya kai wuyansa yana kakari ba shiri Zaytoona ta ruɗe amma Safeerah ko gezau bata nuna tayi ba a waje, amma a zuciyarta ji take kamar ita ta shaƙe ɗin, bae cire idanunsa daga kan Safeerah ba har ta tako ta ƙaraso ta zauna a kujerar can nesa dashi amma suna kallon juna, a firgice Zaytoona ta fito daga kitchen riƙe da goran ruwa ta ɓalle murfin ta bawa Abideen, tunda ya karɓa ya fara sha yana jin wani mugun ƙishi daya taso masa wanda Safeerah ce kaɗai zata iya shayar dashi, sae daya shanye ruwa tas ya ajiye goran ruwan. 


Tashi Safeerah tayi daga zaunen da tayi tareda kallon agogon hannunta tace, "Baby zamu fita ko ka manta ne?" Shiru yyi jin sunan data kirasa dan zuciyarsa zata iya bugawa at any time, ɗauke idanunta tayi ganin Zaytoona na kallonta, miƙewa yyi tsaye yana strengthening kayansa da suka fara motsewa, kallonsu Zaytoona tayi tace, "Zan jira ku dawo.." saurin kallonta Safeerah tayi tana watsa mata kallo tace, "Aah, ki tafi kawai ba da wuri zamu dawo ba.." shiru Zaytoona tayi ta kalli wannan ta kalli wannan, ganin kamar bata da niyyar tafiya yasa Safeerah ƙarasawa gurin Abideen ta rungumeshi ta gefe sannan ta riƙo waist ɗinsa ta tura baki cikin shagwaɓa tace, "Baby.. ka ce mata ta tafi mu ba da wuri zamu dawo bah" shiru yyi yana kallonta yana jin yanda ta riƙo sa ga yanda take maganar yana neman zautar dashi, rage tsayinsa yyi tareda kai bakinsa kusa da kunnenta yace, "Ki dena shagwaɓar, I'm horny wallahi.." taji mey yace sarai amma tayi kamar bata ji ba sae ma ƙara shige masa jiki da tayi tana cewa, ""Baby kaji... uhm uhm kace ta tafi..." harda wani buga ƙafa tayi cikin shagwaɓar, shi dae yasan da bbu Zaytoona a gurin bbu abunda zai hanashi ɗaukarta ta zube a gadonsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin yyi magana Zaytoona tace, "Okay, toh Yaya kuyi dropping ɗina.." bata ƙarasa ba Safeerah tayi charaf tace, "Mu ba ta hanyar za mu bi ba, it's the total opposite.." wata dariya ce ta tasowa Abideen amma haka ya danne ta, "Daniel zae kai ki gida.." yana faɗin haka Zaytoona ta ɗauki ledar cake ɗin ta rufe shi ta kai kitchen ta sa a fridge, tana fitowa ta ɗauki jakarta suka fita su uku duka, bayan Zaytoona ta shiga motar da Daniel zae kaita gida tace, "Yaya na sa a fridge, kar ka manta dashi fah.." kai ya ɗaga mata nan Safeerah ta taɓe baki ta buɗe ƙofar Audi R8 ɗin da zasu fita a ciki ta shige.


Shiru sukayi su biyun duka shi dae Abideen sae satar kallonta yake yi, tana sane dashi sarai amma tayi banza, can dae ya daure yace, "Ina zamu je?" Kallonsa tayi saurin yi tace, "Oops, na manta ban gaya maka ba. Saloon zaka yi dropping ɗina zanje gyaran kai.." tana faɗin haka ta ɗauke masa kai sae a lokacin ya lura da lipstick ɗin da ta goga a bakinta, tunda suke yau ne na biyu da ya ga ta shafa lipstick, saurin pointing wani building tayi masa tace, "Yawwa, you can park over there.." kallonta kawai yyi ya ƙarasa gurin tareda yin parking, zata sa hannu ta buɗe ƙofa taji ƙaran saka lock a ƙofar, ga windows ɗin da suke a buɗe suna rufewa suka koma tinted. Juyawa tayi a hankali ta kalleshi tana jin zuciyarta na bugawa, a sanyaye ta zuba masa fararen idanunta ga lips ɗin nan yasha red lipstick, shi da idanunsa suka fara chanza colour kallonta kawai yakeyi, murya can ƙasa yace, "Wa zaki nuna wa lipstick ɗin da kika shafa bayan gani a zaune?" Farr tayi da idanu tana kallonsa cikin rasa gane mae yake nufi, bata gama tunani ba yasa hannu ya fisgota aikuwa ta rikita ta faɗa jikinsa, cikin idanunsa ta kalla dake cike da wutar jaraba na fitan hankali ya ko zubawa lips ɗinta ido kuwa, ko ba'a faɗa mata ba tasan mae hakan ke nufi, kawai ji tayi ya manne lips ɗinsa da nata, a hankali harshensa ya fara zagaye lips ɗin nata kamar mae lashe jan bakin, da haka ya samu entrance sae jinsa tayi kawai yana tsotse lips ɗinta kamar an aikosa, suna cikin haka aka yi knocking windown motar an ga mota mae tinted glass yyi parking dole a duba waye kasancewar gurin babba sosai ko dan security purposes.


Duk da haka bae tsaya ba dan kamar bae ma san ana yi ba, jin tana son kwacewa yasa ya kamo kanta ya riƙe gam ta yanda zae yi controlling komai, ita dae ji tayi numfashinta na neman ɗaukewa da kyar ta samu ta tureshi tace, "Ba'a nan ba please.." da kyar ya daidaita numfashinsa yace, "sae a ina?" Kallonsa tayi cike da tausayi ganin yanda ya zauce tace, "Ko ina amma banda nan.." kai ya ɗaga mata tareda lumshe idanunsa da suka sauya kala, tana jin sa yana maida numfashi da kyar, sun daɗe a haka kafin ya kalle bakin yaga lipstick ɗin ya fita, hannu ya kai ya goge mata gefen bakinta inda ta bishi da idanu, gyara zama yyi yace, "Yaushe zaki gama?" 

Kallon agogonta tayi tace, "Around Magrib should be okay! Ina son yin gyaran jiki ne da na gashi so.. it'll take time.." murmushi yyi tareda zaro ATM card daga aljihunsa ya miƙa mata, ciro black card ɗin daya bata lokacin da zai tafi Somalia tayi ta nuna masa, still bae yarda ba sae da ya sake bata na hannunsa, sosai yake so a gyara ta saboda shi ake yiwa gyara dan yau ɗinnan me raba shi da ita sae Allah....😳😉🔥


*Let's go...!


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments