TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Hauwa kulu book 4

      YAR CIKIN BADALA

    (HAUWA-KULU)

       

    4


                  PAID BOOK

       SUMAYYAH ABDULKADIR

    babbangoro2015@yahoo.com

                07030137870

                     (whtsp only)





           

      SADAUKARWA

SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTATAFAINA YAN CIKIN BADALAR KANON DABO.













          HAUWA-KULU 4

A

na i-gobe Sarham zai iso wato ana i-gobe daurin auren Surayyah, har zuwa lokacin Surayyah na gidan Haj. Kulu, sai dai ta zo gidan lokaci-lokaci ta gaida iyayenta ta koma. Ko dakin da Hauwa ta ke ba ta shiga, sai ko in sun hadu a babban falo su gaisa kadaran kadahan, shi ma sai in Hauwan ce ta fara kula ta. Yadda Mama ta yi wa Sumayyah uzuri a kan Madinah, haka ta yiwa Surayyah akan Hauwa-Kulu, wato jininsu ne bai hadu ba.

     Amma a hankali in sun zauna daga ita sai Surayyah tana yawan yima Surayya huduba akan Hauwa cewa amana ce ita a hannunsu bata da kowa sais u a Kano yanzu, kuma tunda tana auren dan uwanta dole tayi zumunci da ita, watarana har yayanta sai ta goya.

    Mama ba ta san a kasan ran Surayyah ba haka ba ne, kawai ta raina aji da asalin Hauwa ne. Haka kawai ta zo ta zame wa iyayenta 'liability' miji ba ya ta tata, amma an wani girke musu ita a gida sai faman habaka take kamar mai cin yeast.

    Mama ta shigo dakin Hauwa rike da wata gora ta ruwan swan ta ce, "Hauwa, kun yi sallahr la'asar ne ki ke faman barcin yamma haka? Barcin laasar baa bin arziki bane.

    Muryar Mama ce ta tashe ta daga nannauyan barcin. Ta yunkura ta mike zaune, ta ce, 'Mama lazimi nake, barcin ya dauke ni fa".

    Mama ta saka mata gorar da ke hannunta cikin nata hannun, ta ce, "Ga nan zuma ce ingantacciya maganin basir cikin wadanda aka hadawa Surayyah ne, kullum ki sha sosai sau uku a rana", sai kuma gorar tsimi jarka guda. Shi ma ta aje mata a gefen gado har da kofi a kai, ta ce, "Daga yau har kwana uku nan gaba su nake so su zama ruwan shanki, kin ji ko Hauwa'u?"

    Kai ta gyada tare da yin godiya wa Mama, duk da ba ta san ko na mene ne ba.

    Hauwa ta bi umarnin Mama tana shan komai ta kawo mata da zuciya daya, babu wani tunani na daban a ranta. Tasan dai Mama bazata bata abinda zai cuceta ba duk da tana ta cewa maganin basir ne. Ga tukudin Ghana shima tana ci lokaci lokaci don duk abinda kace ma Hauwa yana gyara fata bata wasa da shi. Fatar da ba ganinta take ba, amma tana kula da abarta sosai, tana kuma tattalin ‘dark complexion’ dinta. Yinin ranar zungur, ko abinci ba ta iya ta ci sosai ba, saboda kayan zakin da Mama ke dirka mata sun cika cikinta.

    Saukar yamma Dr. Sarham ya yi a gidan su, banda kalar fatarsa da bata da hasken tasu, tsammani za ka yi mutumin kasar Maghrib ne, 'yar kibar da ya yi ta kara fiddo asalin tsahon sa da kyawun surarsa, ilhamarsa da cikar zatinsa ya kara bayyana sarari a cikin shekarunsa na yanzu wato shekarun fita kuruciya talatin da biyar. 'yar kibar da ya kara ta kara fiddo kamalarsa ta cikakken magidanci mai wadatar jini ajika da rufin asirin rayuwa. 

    Dr. Sarham Abbas Shanono, ya yi sallama a dakin mahaifiyarsa, don bai samu kowa a babban falon ba. Kuma yayi sallama ba wanda ya amsa shiyasa ya nufo dakin Mama kansa tsaye. 

    Abin da ya gani ya matukar impressing dinsa, wato Hauwa ce duke a gaban Mama tana yi mata karin karatun Al’qur’ani. Mama Ta dade da fahimtar Hauwa ba ta samu yin zurfi a karatun addini ba, kuma ba ta yi saukar Alkur'ani ba don makarantar allo kawai ta yi a Badalar Kofar Naisa. 

    Ba tun yau ta soma yi mata karin ba. Sun dade tana kara mata daga sama (baqarah) musamman da ta fahimci kwakwalwar Hauwa daban ta ke a wajen rike abu. Hakan ta ke ga duk masu lalurar idanu (they are extra-brainlliants), suna da saurin hadda da saurin fahimta. Tun bayan tafiyar Sumayya ta ke yi mata karin lokaci-lokaci in tana gida ba yau suka fara ba. haka na bokon ma, da yake abu daya suka zaba (LAW) duk abinda ya shige mata duhu in ta dawo gida ko assignment aka bata Mama ce take facilitating dinta.

    Sarham ya tsurawa HAUWA ido daga bakin kofa yana dan murmushi, sai duk ya ji shi kamar mara gaskiya, musamman da bai ga wani ‘special’ abu da aka shirya domin taronsa ba kamar yadda Mama ta saba in zai zo, tun daga karkashin zuciyarsa yake jin guilt na yanyameshi. A yadda Hauewa ta duka a gabanta tana daukar hadda kai ka ce diya ce da uwar da ta haife ta.

    Hauwa ta yi wani irin kyau da girma a idanunsa, ta murje ta yi sumul da ita kamar dai 'yammatan gidan, wato Sumayyah da Surayyah. Ta kara girma na ban mamaki don a lokacin ta shiga shekaru 19, fatarta har da sirkin wankan tarwada da kai tsaye ba za ka kira ta baka ba, ba tare da kara da (black beauty) ba. Kirjin ta ya cika yayi full da madarar shanu irin dai 'teens' dinnan masu wanke goma su tsoma biyar a gidan 'yan boko.

    Mama ta amsa masa fuska a sake, amma Hauwa wani irin shiru ta yi, kamar ruwa ya cinyeta, sai dai ta amsa a zuciyarta don cika umarnin musulunci, wa take ji haka kamar muryar Yaya Doctor???

     Mama bata gaya mata zai zo ba koda wasa, duk da ta san gobe ne daurin auren Surayyah, tarewarta ce aka ce sai wani satin, inda zaa kai ta Ikko (Lagos inda Engnr. Aliyu ke aikinsa kenan). To ko daurin auren kanwar tasa ya zo? Don dai ta san ba don ita Yaya Doctor ya zo Kano ba, kuma bazai taba zuwa saboda ita ba.

    Sarham ya karasa har gaban Mama ya tankwashe kafafu yayi zaman rakuma a gabanta, kamar bafaden da yayiwa sarki karya, ita kuwa murmushi kawai take tana fadin, "Lale marhabin, maraba da baban Waheedah".

    Ya zauna a kujerar da ke fuskantar Hauwa yana ta murmushi yana kallonta, ya ce, "Karatu ku ke haka Maijidda? Masha Allah".

    Da farko Hauwa niyyar share shi ta yi, amma sai ta kasa ta gaishe shi a ladabce, sannan ta mike don ta ba su wuri, ta ce, "Mama zan je in yi sallah".

    Mama ta ce, "Babu laifi, kice da Mardiyya ta zo ta dauko miki shanyar da ta yi miki, magriba ta kawo kai".

    Sarham ya bi ta da kallo, tana ficewa tana dafa bango, yana ta mamakin girman jikin da ta kara da cikar idon da ta kara (idan cikar da ake kira kinfi karfin raini). Akwai wanda ya kai Mamansa iya kula da 'ya'ya mata?

     Sai da ta kai bakin kofa ya ce, "Maijidda, kin san hanyar dakin ne? Ko inzo in rakaki?"

    Mama ta ce, "Ai ita ba ta fiya son a yi mata jagora ba, ko Mardiyyah ta ce za ta raka ta wani wuri a cikin gidan nan cewa ta ke ta zauna, ta san kowanne ‘direction’ na cikin gidan nan. Mardiyyah ta ce min har a makaranta kanta tsaye ta ke shiga aji, ta manta da ita a baya".

    Hauwa ta wuce dakinta ba tare da ta tanka musu ba. Sai da ta bace masa ya iya dauke ido daga hanyar da ta bi, yayi wata sasanyar ajiyar zuciya ce,

     "Na ga alama Mama kina jin dadin zama da Maijiddah".

    Mama ta ce "ai ba sai kaga alama ba, ba zan boye maka ba ta dauke min kewar Sumayyah gabadaya. Hauwa mutum ce da ta san darajar mutane, ta ke kuma da son karatu, ga kula da addini da girmama babba wannan shaida ne na tarbiyyar uwa mai kyau data samu irin ta mutanen da. Kai dai barta da rashin daukar wargi, kuma ba ta so a ce ba ta gani, yanzu za ta hau fushi ba gaira babu dalili. 

    Akwai ranar da Barr. Hannatu ta zo, ta mike za ta ba mu wuri tana lalubar bango, sai Barr. Hannatu ta ce min "makauniya ce ne?" Ai kuwa shikenan, ranar mun ga boni, kada ka so ka ga fushi, duk gidan nan kasa gane kanta mukayi, don kuka ta hau yi, wai Ghana za ta tafi an mata gorin ido. 

    Saida fa Abba ya sa baki ya ba ta hakuri da kansa muka samu lafiya".

    Sarham nata dariya, sune bakin jin kalmar GORIN IDO daga bakin Hauwa, tuni ya manta da guilt din dake damunsa don Mama ko a fuska bata nuna yayi laifin komai ba, ta bar shi ya sake da welcome face, shi ya fi kowa sanin Hauwa ba ta son gorin ido, kuma ba ta so a ce mata mara gani, ko makauniya.

    Har gara ma ka ce mata kuluwan da ba ta so, a kan dai ka yi mata kalaman nan guda biyu.

    Mama ta tambayi lafiyar Waheedah da Madinah ya ce, “Mama suna lafiya bakidayan su har Sumayyah. Na barota tare dasu a gidan. Mama ta dube shi cikin ido. Tayi nazarin irin hutu da kwanciyar hankalin data gani a tare da shi. Sai ta girgiza kai. Tace.

     "Dama ina jiran ka ne kazo muyi magana ta gemu, wadda tafi karfin a yi ta a waya".

    Sarham yace "Amma Mama kya bari in huta in dan yi freshen up ko? Ko ruwa yau baki bani ba, ban ga komai na daga delicious dinky a kan dining yana jiran saukata ba".

     Wani zazzafan kallo da Mama ta sakar masa sai da ya sha jinin jikinsa a take, kuma nan da nan yanayin fuskarta ya sauya, ba shiri ya tattara hankalin sa wuri guda ya bata. Mama ta dauke ido daga kansa a hankali cikin dabara da hikima da fasahar zance irin nasu na kwararrun lauyoyi ta soma magana. 

    "Maganar tawa akan HAUWA KULU ne!".

    Ya kara shiga nutsuwar sa don kwatakwata babu wasa a tareda Mama yanzu.

    "Yarinyar nan masoya sun fara yawa, kuma ko ance musu da aurenta basa yarda, ciki harda Farfesa Alhassan abokin Abbanku na tsangayar su.

    To kaga dai itama mace ce, mutum mai cikkar lafiya kamar kowa, kuma yadda nakeson su Sumayyah da zaman gidan aure karkashin kulawar miji irin Abbansu haka itama nake son ta samu.

    Yanzu a misali ace mijin Sumayyah ya jingineta a gidan iyayensa tunda ya aureta, alhalin yana ikirarin zamansa take yi, yana aurenta har tsayin shekara guda da sunan ba sonta yake yi ba, in this regard, mu iyayen ta da kai Yayanta wane mataki ya kamata mu dauka???

    Kuma kaima ka fada ka sake har a gaban idona da gaban idonta cewa kai kanwar jini ka dauketa ba mata ba.

    Don haka nake ganin, abu mafi maslaha shine Sarham ka sahalewa Hauwa aurenka, yadda dana gama bikin Surayya itama in zo in fara shirin nata itada Sumayyah. Wannan karon aure zan yi mata na gata da soyayya da wanda yake sonta itama take son shi da zuciya daya. Don haka Sarham, ina jiran takardar sakin HAUWA-KULU daga nan zuwa gobe kafin ka fita daurin aure".

    Dr. Sarham tun daga yatsar kafarsa har zuwa tsakiyar gashin kansa gumi ya shiga karyo, ya rasa a yanayin da kalaman mahaifiyar sa suka jefa shi. SAKI! Saki fa. Kai tsaye Mama ke nema tsakaninsa da Hauwa-Kulu. 

    Shi ai babu saki tsakanin sa da Hauwa koda babu soyayyar aure. Da wane ido zai dubi Inna Safiya da Malam Bilyaminu yace dasu wai yau ya saki Hauwa???".

    Mama bata kara bi ta kansa ba, ta tashi ta bar masa dakin jin shigowar Abba Prof. Ko motsi ya kasa daga inda yake zaune balle ya fita don ya gaida Abba. 

    Abban ne da kansa ya karaso har kofar dakin Mama sai ya ganshi a zaune kamar sassakakken gunki. Ya ce "a'ah, mutanen Jiddah ne? Maraba lale da Lelen Abba, Jabbama-jabbama, yaya hanya da kuma amaryata-uwata Hajiya KULU?"

    Sai lokacin Abba ya lura da irin jibi (zufa) wato gumin da Dr. Sarham keyi daga zaune. Kamar wanda aka fiddo daga tanderu. Abba Prof. yace a hankali.

    "Ko lafiya?"

    Sarham bai san sanda ya zube gaban Abba Prof ba yana rokonsa, kan don Allah ya baiwa Mama hakuri.

    "Me ke faruwa? Me kayi mata?"

    Idanunsa sun kada sunyi jajir, yace "Abba koma wane irin laifi take tuhumata dashi na amsa laifina. 

    Amma don Allah ka roketa ta janye kalmar SAKI tsakanina da Maijidda. 

    Zan iya yi mata komai amma banda saki tsakanin mu. Auren mu na har abada nake burin ya zama. Me zance da su Malam Bilyaminu idan Mama ta takura min na saketa?"

    Mama ta dawo dakin tana cewa da babbar murya mai cike da bacin rai daya dade yana cinta a zucci; 

    "ai kawai cikakken bayani zaka yi musu na irin rikon auren da kake yi mata tunda suka baka ita, cewa kai kanwar jini ka dauketa ba mata ba, suyi hakuri kawai, zaifi musu alkhairi, su karbeta daga hannunmu su aurawa dan Malam Munkaila a kan ka. 

    Na tabbata zai kula da ita zai bata hakkin ta na aure kamar yadda addini ya ce yayi, ba zai bi son zuciyar sa a kanta ba wai don zumuncinsa da iyayenta.

    Ba zai zauna yana rusa mata rayuwa ta hanyar rashin bata gurbin matar aure, at the same time yana rusa lahirar sa ba da sunan wai yana taimaka mata". 

    Idanun Mama a warwaje take magana kamar zata kife Sarham da Marika, ko ta samu ya shiga hankalin sa ya gane meye a zuciyar sa game da Hauwa-Kulu.

    Budar bakin Abba Prof. Sai cewa yayi "Da kyau Mamansu, ina bayanki anan Mai Shari'ah uwar kowa. Ai mu saidai mu ce maka Allah yayi maka albarka ka kawo mana diya abar alfaharin kowadanne iyaye. 

    Don haka ka sahale mata shi yafi alkhairi in yaso ta cigaba da zama tare damu tana karatunta har Allah ya bata mijin dake sonta da gaskiya. Ko jiya an tambayeni ko tanada aure? Wannan al'amari daman ya isheni, don ko na ce tanada aure ba yarda ake yi ba".

    Iyakar tashin hankali Dr. Sarham ya shigeshi irin wanda bai taba shiga ba. Mama ta saka murya ta kwalawa Hauwa kira. Mardiyya ta fito da ita da hanzari ta zaunar a gaban Mama ita kuma ta koma daki jikinta na bari.

    Mama ta ce cikin zafin rai "ga ni, ga ka, ga Abba ga kuma Hauwa. Inaso ka sahalewa Hauwa aurenka".

    Ta dubi Hauwa wadda ke tsugunne kan kujera a dofane cikin firgita, don ta kasa gane me akeyi, ta san dai abinda zaisa Mama fushi irin haka ba karamin abu bane har dakinta take jiyo tahin fadanta. Mama ta daka mata tata tsawar "ke Hauwa! Nace wannan mutumin ya sake ki haka, ko kinason cigaba da zama da aurensa?"

    Hauwa ta hadiyi miyau da kyar, ji kake, mukut, da kyar ta daga manyan idanunta a daidai saitin da take jin sukar idanun Sarham a jikinta. A lokacin shima ya dago, goshi duk zufa, cikin kidima da tsoron abinda zata ce.

     Da kyarmar murya Hauwa tace "a'ah, bana son auren, Yaya Doctor ai Yayana ne babu son aure tsakanin mu".

     Kai kace Mama ta karanto mata abinda zata fada ne kafin ta kira ta, yadda take maganar tiryan-tiryan cikin kyarmar murya. Mama tace "to kaji, don haka daga yau zuwa gobe kafin fita daurin auren Surayyah ka rubuta takardar sakinta ka bani hannu da hannu, umarni ne ba zabi na baka ba".

    Daga haka Mai Shari'a ta bar wurin cikin tafasar zuciya kai kace Hauwa ce diyarta ta cikinta ba Sarham din ba. 

Abba Prof. Ma ya gyada kai kawai ya shige dakinsa don Mama ta gama yimasa jarumtar da shi ya kasa akan Sarham saboda yadda yake sonsa.

    Ya saura daga Sarham sai Hauwa a dakin Mama, ya ciro hankicinsa daga aljihunsa yana share zufar goshinsa.

    Ya dubi Hauwa cikin takaici tana kokarin tashi yace "koma ki zauna, nace ki tashi ne?" Hauwa ta koma ta zauna a kujerar dake fuskantarsa. Babu digon nadamar furucinta a tare da ita.

    "Da hadin bakinki Maijiddah aka shirya dagamin hankali haka? Daga zuwa na? Me nayi miki haka da zafi Maijiddah?"

     Hauwa tace cikin mamakinsa, "kamar yaya da hadin baki na? Wallahi Yaya Doctor kirana aka yi, bansan me ake yi ba, ta tambayeni ne kawai nikuma na bata amsa, nima Yayana na jini nake kallonka, banga amfanin cigaba da aurenmu ba". 

    Ta kara da cewa "Yaya ka baro su Anti Madinah da Takwara ta Waheedah?"

    Takaici ya hanashi amsa mata, ya tsura mata Ido kawai yana cewa a ransa ita ko dan irin kishin nan nasa irin na Madinah bata yi. Bai taba jin Madina ta ce ya take ba balle lafiyar ta. Daga bisani ya mike ya finciki hannunta zuwa dakinsa, suna shiga ya maida kofar ya rufe,

     yace "Hauwa open your blank eyes, look into my eyes kice kin yarda mu rabu ki auri wani!".

     Hauwa ta fiddo manyan gululun idanunta a kansa tace, "ni Hauwa Bilyaminu, na yarda in rabu da auren Yaya Doctor sabida hakan zai fi mana alkhairi".

     Sarham ya sake mata hannu cikin mutuwar jiki yace "wallahi bazaku hadu keda Mamanki ku haukata ni ba". Muryarsa bakidaya ta dushe a sanda yake fadin hakan ya dafe kirjinsa dake zafi. Ya rasa me zai cewa Hauwa ya huce kawai sai ya girgiza kai yayi mata wani sakaran kallo kamar tana ganinsa y ace fitar min daga daki!.

    Ta kuwa juya da lalube ta kama handle din kofar ta bude tayi ficewarta.

    Bakin gadon sa ya koma ya zauna, kafin ya tashi ya kulle kansa ya rasa abunda yake masa dadi, haka ya rasa inda zai saka ransa. Ya rasa ta inda zai bullo musu. Abu na karshe da yasan bazai iya ba koda za'a dora masa wuka a makoshi shine sakin Hauwa. 

    Ya samu kansa da daukar wayarsa yana kiran layin Hauwa karo na farko tun bayan tafiyar sa, shi kansa saida yaji kunyar kansa da kansa da yaga number dinta da sunanta na yawo akan screen din wayarsa.

    Mardiyya ta amsa wayar sannan ta miko mata kenan Mama ta shigo dakin, HAUWA na yin sallama batareda ta san wanda yayi kiranta ba. Da sauri Mama ta fauce wayar ta kashe sannnan ta rufe Hauwa da fada.

    "Yanzu don bakida hankali, kin rako mata, yau sai ya kiraki a waya ki dauka???

 Wata goma sha biyu yayi ba kwana sha biyu ba tareda ya kira ki ba. Zuciyar ki kare ya cinye ne halan, ko kuwa mata kika rako duniya don kawai bakida Ido???"

    Hauwa batasan sanda hawaye ya tsinke mata ba. Ta sa gefen mayafin ta ta rufe fuska tana kuka. Mama tace "to daga yau na kwace wayar, in da ita zai bi ya samu lagonki ta hanyar bata miki lokaci. Dole in san matsayinki cikin rayuwar sa ko kuma ya bani takardar sakin ki".

    Bayan fitar ta daga dakin itama Mama Mai Shari'ah sai taji hawaye ya balle mata, kuma ba na komai bane na tausayin Hauwa ne. Ta san ba don nakasarta ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba. Itama har ga Allah bata so auren ya mutu, tana kwadayin samun tsatso dasu Inna da dawwama da rayuwa tareda Hauwa matsayin surukarta. Amma fifita bukatarta bai yuwuwa, hakan bazai hana ta kwatowa Hauwa 'yancin ta ba wanda addini da al'ada suka bata, don ta lura bata san ciwon kanta ba Sarham ya gama raina mata hankali.

    Kasa barci yayi a daren, ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakinsa, daga karshe ya canza kayan jikinsa zuwa na barci, ya rufo dakinsa zuwa dakin Mama. Ya sameta tana karkade gadonta zata kwanta tana hawaye bata ko sharewa ba tareda ta san shigowarsa ba.

    Ba karamin tashin hankali Sarham ya kara shiga ba ganin Mama na kuka bata ko damuwa wani zai iya shigowa ya ganta. Ya zube gwiwoyinsa a kasa gabanta ya kasa cewa komai.

     Mama tayi karfin hali tace "Yaya dai? Takardar ka kawomin ince ko?" 

    "Kiyi hakuri! Kiyi hakuri! kiyi hakuri Mama. Na tuba na bi Allah na biki".

     "Ai ba maganar inyi hakuri bane Sarham, amma in tambayeka. Shin Hauwa gunki ce ko dutse ko kuwa sassakata akayi? Bata da feelings kamar na kowacce mace?"

     Ya girgiza kai da sauri cikin jin kunya ya kara dukar da kai kasa. "To kaje kayi tunani kamar yadda nace daga yau zuwa gobe da safe, in bata da gurbin soyayya ko yaya a zuciyarka ka sahale mata qaddararren aurennan, ka koma inda ka fito".

    Haka ya taso ya fito daga dakin Mama cikin gigita, baya ko ganin gabansa sosai.

    Surayyah na gidan Haj. Kulu, an saka ta a lalle, duk da tarewarta sai sati mai zuwa haka bikin ma, amma suna can suna lalle ita  da  kawayenta yan kwalisa.

    Sarham ya zarce dakin Hauwa kai tsaye, ya tsaya a gaban gadon Hauwa bayan fitowarsa dakin Mama, ya sameta tana tufke gashin kanta yadda za ta ji dadin barci, kasancewar ta kure radio cikin wata wakar yaran Larabawan Sudan ba ta ji shigowarsa ba. Sai da ta ji ya kashe radion, Mardiyyah na gaishe shi, yana amsawa a dake da yake yarinya ce mai hankali sai ta fita ta bar musu dakin. 

Ba ta san me ya sa ko ta yi fushi da Sarham a can kasan ranta tarin alkhairorinsa ta ke tunowa ba. Su shafe duk wasu kurakuransa da ke idanunta, musamman in ta tuna shi ne fa ya sake maido su cikin Badala, bayan an so har abada kada su dawo, shine Sarham din da ya gine gidansu na tarihi da Baba Zakari yasa zalunci ya rushe shi, shine Sarham din da ya sanya murmushi da farin ciki a fuskar Inna, a lokacin da bata da mataimaki a duniya sai Allah.

    Shine mutumin da ya kaita special school ta koyi karatun da yau ya taimaka mata wajen zama MUTUM! Shineshine. Shine komai na cigaban rayuwarta. Don haka ko baya sonta bai zama hujja a gareta ta ram aba, ko ta ki yi masa ladabi ko ta yi fito na fito dashi.

    Wannan tunanin kadai ya sa ta tattaro dukkan hankalinta da nutsuwarta ta bashi. Ta gaishe shi da murya mai sanyi, a lokacin da ya zauna a daidai kafafunta. Sambala-sambalan kafafun Hauwa ya tsura ma ido, tana sanye da irin wandon nan na mata na iya kwauri (three quarter) da farar T. Shirt mai hoton zanen katuwar jar zuciya data kama kirjinta sosai.

    Hannunsa ya kai bisa kan tafin kafarta ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba, taushin fatar a ido shiyasa shit aba kafar don jin irin laushinta a zahiri, ya ce, "Maijiddah".

     Hauwa ta ce, "Na'am, Yaya Sarham, yaya ka baro takwara ta?"

    Ya dan ji sanyi, don ya zaci itama ta dau zafi dashi kamar Mama, da gaske ta dauka da farko, abu daya ta tuna yayi cooling temper dinta. Wato ranar da ya dawo da ita inda ruhinta yake, wato ya gine musu gidan su na BADALA da kudin ginin nashi gidan, hakan ne yasa har gobe bai kammala nashi ginin na unguwar Rijiyar Zaki ba, amma dai yana yi kadan-kadan yanzu. Ya nisa a cikin samun relief. "Waheedah tana lafiya, ta rage kukan dare yanzu, amma da kullum kukanta ke hana mu runtsawa, kodayake nima na jima bana tare da ita, amma ranar da na dawo naga ta daina kukan dare".

    Ta ce, "ai daman haka yara suke, sai lokacin dainawarsu ya yi za su daina".

  "Ki ce haka Inna ta yi ta fama da ke.

Ta yi wani murmushi ta ce. "Fiye da haka ma. Ni ai Inna ta ce Kukana ina jaririya kamar na jiniyar mota yake, har makwabta ake jiyo shi, a shigo ana tayata rarrashina".

    Hauwa sai ji tayi Mama na kwala mata kira. Sarham ya hana mata tashi ta hanyar sarqe yatsun hannunsa cikin nata, sannan ya ja mata yatsun suka bada kara kas-kas! Hauwa ta rasa inda za ta saka kanta don kunya, shi kuwa tafin kafar da yatsun nata ne suka ba shi sha’awa. Sanda hannunsa ya kai ga sauka a kansu bai sani ba, ya dai samu kansa zaune a kan gadon Sumayyah gabadaya, wanda yanzu ya koma na Hauwa yana ja mata yatsun kafa cikin wani iri salo da wani irin feeling dake shigarsa. Gabadaya Hauwa ta susuce ta kidime ta kuma kasa amsa kiran Mama sannan ta kasa janye yatsunta daga alkintasun da Sarham yake yi domin wani abu ne da bata taba ji a kirjinta ba. Sarham ya samu yadda yake so cikin taushin murya da lallashi yace.

    "Maijidda kin amince za ki bi ni Jeddah? Ranar dana tashi komawa?"

    Hauwa ta zaro manyan idanunta waje, ta ce "Karatuna fa Yaya Dacta? Kuma ka manta na amsawa Mama cewa na yarda a raba aurenmu?"

Sarham ya samu kansa da kara matsawa jikin Hauwa, ya sunkuya daidai kunnenta yana mata magana kamar cikin rada, kamar ba ya son wani ya ji, kamar akwai wani a dakin bayan shi da ita.

    "Mamanki kawai tana so ta ce ne in disguise kin girma haka, kina bukatar mijinki a kusa da ke. Kin daina yi min zaman jiran daki. But she doesnt really mean it. I mean the divorce. 

    Don haka ki shirya gobe da sassafe za mu je immigration’ a yi miki fasfo, mu tafi mu bar mata gidanta. Sai ki shirya kawo wa Mama jikoki sharp-sharp daga Jeddah ta kara yarda na cika duty na, ke kuma kin amsa kira na da so da kauna".

    Wata irin kunyar Sarham da bata taba ji ba ta zo ta lullube ta, irin wadda ba ta taba ji a rayuwarta dashi ba. Kamar yau ne farko da wani namiji ya ce za ta haifi 'ya'ya tare da shi. In bata manta ba, Yaya Jamilu ma ya taba cewa har rainon 'ya'ya shi zai taya ta.

    Ta yi maza ta janye kunnenta daga radar da yake yi mata, domin wata irin kasala take saukar mata, garin kokarin janyewar kuma goshinta ya bugi nashi, ya ce, 

    "Ouch! Maijiddah kina buge ni da katon goshinki".

    Ta yi maza ta rufe fuska da tafukanta tana cewa, "Ka yi hakuri, ai ka san bana gani".

    "Da wani ne ya fada kuma da yanzu cibi ya zama kari, da yanzu kin ce ya miki gorin ido, ni matata Hauwa na gani, tunda hankali ke gani, ido gululu ne". Aka ce tsakanin mace da mijinta sai Allah sai ga Hauwa na dariya.

    Ta ce, "Kayya, wannan idon gululun gaske ne, ko dan yatsa na bana iya gani".

    Sarham ya yi maza ya ce, "Na yi alkawarin sai inda karfina ya kare da inda ilmi da bincike suka kare wannan karon wajen ganin idonki ya dawo daidai. Na gama gano matsalar idonki yanzu. Kada ki fidda rai da rahmar Ubangiji Maijiddah, shi da kansa ya ce, 

    "Lah taqnadou min rahmatullah”.

    Sabida ke har kwas na tafi Egypt na tsayin watanni uku ba haka kawai naki zuwa ba Meji. Scientifically and medically kuma, based on contemporary research, type of cataract dinki is 100% curable idan aka dace. Glaucoma shi ne idan ya tsananta yake zama ‘irreversable’. Amma kowacce lalura watarana mai wucewa ce idan Ubangiji yasaka hannu, kin ji ko Maijiddah?"

    Sai ga Mama ta shigo a fusace Sarham yayi maza ya saki hannun Hauwa. Cikin takaicin su su duka tace.

     "Hauwa'u baki ji Ina kiranki bane?" Hauwa jiki na rawa ta mike daga jikin Sarham tana cewa "dama.... dama... Gani nan Mama, wallahi yanzu za". Mama bata tsaya jin kame-kamenta ba ta kama hannunta suka fice daga dakin suka barshi a wurin.

    Dr. Sarham yayi ajiyar zuciya ya fidda wayarsa ya hau kiran Inna, bugu daya Inna ta daga da sallama, cikin tsokanar da suka saba kamar ba surukai ba Inna tace "Likitan larabawa, likitan idanun duk duniya!".

    Ya yi 'yar dariya mai ban tausayi cikin karfin hali ya gaida Inna, nadama tana kara mutstsike shi, inda kunya ai baya kai karar Mama gun Inna ba wanda dalilin kiran da yayi mata kenan, don haka sai buge da gaya mata ya zo Kano daukan Hauwa su wuce Saudiyyah tare, bisa umarnin Mama da Abba, tunda sun yi hutun jamia. 

    In ya so in hutun makaranta ya kare sai ta dawo Kano, ta tare a gidan sa na Rijiyar Zaki saboda zuwa makaranta”.

    Inna hawayen farin ciki ya zubo a saman kuncinta. Yau Hauwanta ce da aure a kasa mai tsarki, kasa mafi girman daraja a dukkan kasashen duniya. 

    Ta yi ta zubo wa Sarham addu'a da albarka irin yadda ta saba, wadda ta kara sa Sarham cikin jin guilt mai yawa na abinda ya aikata wa Hauwa, kafin suyi sallama. 

    A take ya fito daga dakin Hauwa ya nufi nasa dakin cikin damuwa, yana kissima Allah ya kaimu wayewar gari ya samu damar fita da Hauwa yin fasfo dinta, daga nan suje gidan sa na rijiyar zaki, duk yadda zaiyi zaiyi ya wanke dattinsa daga zuciyar matarsa, kuma zai hadiye duk wani ‘silent punishment’ din Mama, in dai a karshe zata yarda ya tafi tare da Hauwa Jeddah, sai yayi duk yadda zai yi ya gyara kurakuransa duk da ya san baa bari a kwashe daidai. 

    A ganin sa bai makara ba, zai iya gyara komai, wuyarta dai su kebe shi da Hauwa a wurin da babu interference na iyaye babu gilmawar kowa, wato a inda babu Mama mai yiwa Hauwa kwatar yanci, zai samu wannan damar kadai idan ya fita da Hauwa gobe da safe. Amma bai san meyasa duk wani azanci da confidence da yake dashi na zai iya gyarawa din ba tareda kowa yaji ba, yake jin yana gudu yana barinsa. Don bai san matsayin Hauwa a gun Mama ya kai har tayi kuka kan rashin kyautawarsa gareta ba. 

            

    A daren yau dai da Mama ta yanke masa wannan hukuncin, jinsa yake kamar mai nakuda, musamman data zo har gabansa ta dauke Hauwa zuwa dakinta mai nufin bata amince da kebewarsu ba, ya yarda da gaske Mama take ba barazana take masa kamar yadda ya dauka ba, don haka duk ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa kwanciya, ya rasa ta ina zai bi ya lallashi Mama. Shi kansa ya san abin da zai yi ya bata wa Mama rai har ta zubar da hawaye a kai, ba karamin abu bane. Ya fahimci Mama ta saka Hauwa a ranta fiye da yadda ta saka Madina a ranta ta kowane bangare, ta amshi Hauwa ne wholeheartedly sabanin Madina da dama tana kullace da abinda Babanta yayi musu, na rainin arziki, da auren da Madinah ta fara yi kafin shi ashe bata yafe ba, wannan abu kwarai ya ba shi mamaki don ya dauka tuni ta manta, ya kuma jinjina wa Mama don wani abu ne da a farko bai yi tsammani ba wato cewa zata so Hauwa ta karbeta.

  ****                    *****                         ****


       SELF-EVALUATION

    

A

bu daya Sarham yake so ya tantance a ransa da kwakwalwarsa daga yau zuwa gobe kadai, wato he has to evaluate himself in 24 hours kafin cikar awannin da Maisharia ta bashi, he has to find-out; shin YANA SON HAUWA-KULU???

    Wannan wata tambaya ce da Sarham bai san amsarta tuntuni ba, sai yau da yake cikin tsaka mai wuya, wato a sanda aka bashi zabi tsakanin cigaba da zama da Hauwa da kwace ta don ta koma ga wani wanda yafi shi sonta, wato ranar da ya samu kansa tsakanin samu da rashinta cikin rayuwarsa ne kadai ya gane Hauwa nada matukar muhimmanci a zuciyarsa da rayuwarsa kuma ya damu da ita fiyeda yadda zai iya bayyanawa. Sannan zamanta matsayin matarsa ta sunnan shi ya bashi kwanciyar hankalin da yake ciki a yanzu, wanda a baya ya rasa da ya nemeta a rayuwarsa da fadin garin Kano ya rasa.

    So yake ya tursasa wa ransa ya yarda cewa, har gobe Madinah kadai yake yi wa so na soyayyah, to amma me? Sai ya gane cewa yau Mama ta bankado sirrin dake kwance dankam shekara da shekaru a kasan zuciyarsa game da Hauwa. Bayan duk wasu self-examination ya yarda YES! Hauwa-Kulu tana da wani gurbi bayan na kanwar jini a tare dashi ko ya ki Allah, ko ya ki Annabi (she has a special place in his heart), wanda acan baya yake (underestimating) dinsa da gangan, in ba haka ba me ya kai shi saka wa first daughter dinshi WAHEEDAH sunanta? Shin soyayyarsa ga Inna ce kadai ta yi attaching dinsa gare su irin haka b tareda soyayyar mace ba? Shin Inna ce ta saka shi aiko da kudi duk wata daga Jeddah (for their survival) ko kuwa tunanin karatun Hauwa-Kulu? Shin Inna ta taba yi masa tayin auren Hauwa ko ta taba ce masa tana masa shaawar aurar da yarta? Shin an taba yi wa namiji (matured) kamarsa auren da baya so?

     Shin me ya sa yake kishin Jamilu, kishin nasa kuma ya tunzura shi ga auren Hauwa hajaran-majaran ganin cewa Jamilu da gaske yake? Shi dai ya san babu kishi ga maza a inda babu SO, kuma babu wanda ya yi masa dole ya auri Hauwa.

     Iyayensa suna zaman-zamansu  shi ya dauko Hauwa ya kawo musu har ta shiga ransu, bai kuma san dalilin da ya sayo mata soyayyah har haka a zuciyarsu ba, amma ya yarda sun amince da ita wanda babban abun farin ciki da alfahari ne a gareshi.

    Ya laluba, ya bincika, ko ta ina bai ga da abin da zai lallashi Mama ta janye takunkumin saki ba, ban da ya dauki Hauwa ya tafi da ita Jeddah.

    To amma ya zai yi da ita a Jeddah? A nan kam ba ta da matsalar komai, ya san Madinah ba za ta yi maraba da zuwanta ba kamar yadda kuma ba za ta hana shi yin abin da ya zame masa haqqi ba, sannan ba za ta yi wa Hauwa kowacce irin mugunta ba don keta da mugunta ba halinta bane, kai dai barta da kishinta wanda ya wuce kima, amma tabbas daga shi har Hauwa suka sake suka shiga gonarta sai ta dafa su ta ruwan sanyi babu duka babu zagi. Hakan kuma ba zai hana shi faranta wa Mama rai ba, da ceton igiyoyin aurensa dake reto, da mutuncinsa a idon su Inna ba.

    Don haka barcin Dr. Sarham a wannan daren bakidaya bai fi na awanni biyu ba, shi ma sai goshin asubahi ya same shi. Abin da ya kwana mafarki kuma bakidaya a daren bai wuce Hauwan da ya kwana da ita a ransa ba.

    Kusan sai da ya makara tashi sallar asubahi, abin da ba halinsa ba, Abba na hanyar dawowa daga masallaci suka hade a kofa, ya ce, Lelen Abba, ya da makara?

    Ya sunkuyar da kai.

    Abba ya ga har wani ramewa ya yi cikin kwana daya, yayi murmushi a ransa shikadai yace yaro wa ya gaya maka ana raina mace? Ya wuce shi yana cewa, A dinga kula da lokacin sallah, damuwoyin duniya ba masu karewa ba ne, balle su hana dan Adam barci a kan lokaci. Wani lokacin ma mu muke sayo wa kanmu damuwar da kudin mu. Ni ban ga laifin Mai Sharia ba, shes in judiciary, dole ta kasance mai adalci ga dan kowa.

    Maganar nan mai sauki ce in baka son ta ka saki ka baiwa maso sonta dama, short and simple, ban ga name zaka sa damuwa a cikinta ba. Ka tabbatar kafin ta tashi daga barci ka aiwatar da umarninta don wallahi ba barazana take maka ba, iyakar gaskiyarta kenan da hukuncin da zata iya dauka a matsayinta na uwa ga kowannenku. Annan mai tabbatar da adalci a cikin alumma.

    Ya sa kai ya yi wucewarsa cikin gida.

    

    Kai! Yau hatta karatun sallah ba daidai Sarham ya karanta shi ba, astagfirullah. Ko da ya idar kuma ya kasa dawowa gida gudun haduwa da Mama. Ya ci gaba da zama a masallaci har sai da gari ya yi haske, sai a lokacin ya tuna yau ne daurin auren Surayyah, kuma karfe tara za a hallara a gadon kaya. Dole ya koma dakinsa wajen karfe bakwai na safe, yana shiga wanka ya fara yi, ya fito yana tsane kansa da tawul da wani daure a kugunsa ya hau kiran lambar Hauwa. Shi kansa bai san me zai ce mata ba. Kawai ya samu kansa da son jin muryarta.

    Anyi saa Mama ta bar wayar gun Mardiyyah ita kuma tana sassan Abba, baccin safe dole ne ga Mama in dai ta san bata kwanta da wuri ba, to muddin tayi sallahr asubah zata koma barci, sai inda ‘alarm’ din data saita ya tashe ta, duk da kuwa ta san yau tana da hidimar jamaa amma jiya bata samu barci da wuri ba, bayan ta tabbatar Sarham ya tafi ta maida Hauwa dakinta kwana tayi tana rokon Allah da nafilfili akan Allah ya daidaita tsakanin su.

    Mardiyya na zaune tana karanta morning azkar a cikin hisnul muslim kiran Yaya Sarham ya shigo. Tana dagawa ta gaida shi a ladabce, ya amsa, sannan yace, Me ku ke yi yanzu Mardiyya?

    Ta ce, Anti tana shafa mai ne ta fito wanka, ni kuma ina azkar.

    Ya ce, Mardiyyah maza ba ta wayar kafin Mama ta shigo kinji kanwata?.

    Mardiyyah ta tashi ta kai wa Hauwa waya, wadda fitowarta kenan daga wanka tana shafa. Ta yi sallama a nutse, ya yi ajiyar zuciya ya ce, Maijiddah kanwar Sarham, autar Inna da Baba, yar gatan Mamanta, ki shirya maza yanzu ina jiranki kafin daurin aure zamu dan fita, don Allah bana so Mama ta sani, kiyi sauri.

    Hauwa ta zaro manyan idon kamar yana kallonta cikin tsoro, Yaya Sarham! Ta yaya za mu fita  Mama ba ta sani ba bata yi izni ba?

    Ya ce, In ci darajar Inna, in ci albarkacin Malam, yau tana cikin hidima, ba ganewa za ta yi ba.

     Musamman in muka bar Mardiyyah a dakin. Zan roke ta in ta shigo ta ce, kina toilet.

    Hauwa duk ta tsure, ita ba ta saba abun rashin gaskiya ba, besides mutumin nan ina zai kai ta???

     In kuma ya je ya sayar da ita fa duk a cikin rashin SO? Ta tabbata Maman ta fi shi sonta, ita ba ta da wani ‘hope’ a kansa yanzu. Dadin bakinsa na jiya bai wani dadata da kasa ba. Wallahi yanzu za ta iya zabar Mama sau dubu ta bar likitan Inna.

    Hauwa ta nisa, jin wata kwalla ta taru a idonta da ta tuna yau shekara guda fa mutumin nan bai kara bi ta kanta ba, bai neme ta ba, bai damu da ita ba sai yanzu da aka ba shi yancin da yake nema ne zai bi ya kalallame ta? Hauwa ta bude manyan idanun nan ta kada su harr! Kaman Sarham yana gabanta, ta ce,

     Ni kam babu inda zani Yaya Doctor ba izinin Mama.

Za ta kashe wayar kamar ya sani ya ce, Kada ki sake ki kashe min waya!.

    Hauwa ta yi shiru, cikin fushin ban mamaki ya ce, Kuluwa! Na ce ko ba da Kuluwa nake magana ba?

     Umarni na za ki bi ko na Mama? Shin ni da Mama wa ya biya sadakin aurenki? Kuma wa ya kawo ki cikin rayuwarsa?”

    Hauwa ta sake yin shiru, kamar ta saki kuka.

    Ya ce, To idan ni nake auren ki ba Mama ba, na yi miki umarnin Mardiyyah ta kawo ki mota ta yanzu-yanzu kafin Mama ta fito daga turakar Abba, ko two hours ba za mu yi ba, za mu dawo, I promised!.

    Za ta yi magana ya ce, 

    Umarni ne ba jin raayi ba. Ya kashe wayarsa.

    Hauwa har da wani gumi dake tsatstsaafo mata a goshinta ta yarfe shi da hannu, ta ce cikin yanayi na shiga rudu.

    

     Mardiyyah na shiga uku!!!”

    

    Ba ki shiga uku ba Anti, ina jin komai kin manta wayar a handsfree ta ke. Anti Hauwa Yaya Doctor ya fi ki gaskiya shine mijinki wanda aljannar ki ke tare dashi ba Mama ba, ki bi umarninshi bazaki tabe ba, na rantse zan rufa miki asiri, ni ma bana son abin da Mama ta ke masa tun jiya wallahi ko abinci bata bashi ba.

    Ta zaro abaya mai kyau ruwan toka-toka kirar Dubai ta kawo mata, Hauwa ta karba cikin mutuwar jiki jin an ce tunda yazo Mama bata bashi abinci ba, ta saka da sabuwar ‘brazier’ da sabon pant da vest, duk farare kal sababbi, cikin akwatinta na lefe Mardiyyah ta debo mata su, ta kawo mata khumrah oil perfume da Mama ta bata cikin wadanda aka hadawa Surayyah ta bata ta shafa a koina, sannan ta nannada mayafin abayar a kanta, ta miko mata ‘photocromic glass’ dinta shi ma ta saka, takalmi ma sabo dal ta dauko mata samfurin vincci maras tudun dunduniya da jakarsa yar karama. Hauwa ta yi kyau sosai kamar balarabiyyar kasar Kuwait mai duhun fata amma. Mardiyyah tayi ta cewa Anti kamar ba ke ba yau. Sai da ta leka ta tabbatar Mama ba ta nan a falo kuma bata dakinta sannan ta zo ta kamata zuwa parking lot na gidan.

     Tuni Sarham yana cikin motarsa a zaune ya yi kyau shima sosai cikin farar shadda sol sabuwa daga ledarta, kai ka ce shi ne angon da za a daurawa aure yau.

    

    Tun daga nesa yake hango Hauwa da Mardiyya suna takowa, sai da gabansa ya fadi ganin yadda Hauwa ta koma a zahiri. Tun zuwansa bai mata wannan kallon na tsanaki ba sai yau. Yadda gabbanta suka bubbude ya bashi mamaki  musamman kirjinta. Tun kafin su karaso ya bude mata kofar gidan gaba, Mardiyyah ta taimaka mata ta zauna ya dube ta da murmushi, ya ce, 

    Na gode kanwata ta kaina, nagode Mardhiyyah kinji. Allah ya yi miki albarka, Allah ya kawo miji nagari. Mai albarka kin ji?.

    Mardiyyah ta daga masa hannu tana dariya, Amma don Allah Yaya Doctor kada ku dade, in Mama ta fito wajenmu ta ke fara zuwa.

    Ya kunna motar yana cewa, Haan, ni yau ina ganin abu, ni da matata ake min duk wadannan iyakokin? To je ki na gode, me Antin za ta sayo miki?

    Bakin Mardiyyah har kunne ta ce, Ice cream.

    Ya ce, To ke Maijidda kada ki manta da tsarabar Mardiyya.

    Fuskarta ba annuri ko kadan, sai cika take tana juya manyan idanun nan ko amsawa ba ta yi ba, ya yi reverse ya fita daga flat dinsu yana ta mamakin duk yaushe Hauwa tayi wannan wayewar da class din bashi da labari?.

    Tunda suka hau titi, Hauwa ba ta ce masa uffan ba, bayan gaisuwa a rowace, wata irin gajeruwar gaisuwa wai ina kwana ya gajiyar hanya? kada ki kara kada ki rage bayan wannnan. Shima ganin take-takenta sai ya share ta, yaki amsa gaisuwar, ya saki radion motar ana labaran safe a tashar BBC Hausa. Sun yi nisa sosai da tafiya, cikin muryar jan raayi ya ce, Maijiddah.

    Ta juya inda yake, idanunta fal kwallah da kiris take jira ta zubo, don ba ta taba bata wa Mama rai ba, even by mistake a tsayin zaman su na shekara guda. Amma yau shi da ya wulakantata ya zo ya ssaka ta yin laifin da bata san yaya zata yi da shi ba.

    Ya ce, Maijiddah ni ne fa, ni kika fara sani kafin Mama. Ki sa a ranki ni na kawo wa Maman ke, kuma ni nake aurenki ba ita ba. In kin yarda da hakan, kin huta, in ba ki yarda ba kece ke da wahala, don ni ba ma yanzu za mu koma gida ba gakiya sai na huta.

    Tunda na sauka kasar nan hatsi bai ga baki na ba, ruwa bai shiga hanjina ba duk an daga min hankali ko neman jin uzurina baayi. Saboda Allah in Mama ta daina so na ai ke ba zaki ki ni ba Maijiddah ko don albarkacin Inna, na san da tana garin nan da ban kwana da yunwa ba.

    Ta cikin gilashinta take bubbude ido tana kara musu girma. Sai ta ji hannunsa na hagu a kan nata ya damke shi sosai yana cakuda tafin hannunta, yana ci gaba da tuki da hannu guda. Ya ce, Kafin ta kashe min aure, zan dauki nawa matakin, tunda Mama ba ta jin lallashi.

    Hauwa dai ba ta san ina suka je ba, amma daga wayar da yake yi da wani abokinsa ta fahimci wajen yin fasfo immigration office’ ne. Kafin su zo kuma har an saka file dinsu a layi na neman fasfo. 

    Don haka suna shiga ba su bata lokaci ba ta yi ‘thumb-print’ da taimakon Sarham da na abokinsa Rislan maaikacin immigration. Sai da suka kammala Rislan din ya ce nan da kwanaki uku zai kawo masa fasfon Hauwa har gida, hannunsa cikin na Hauwa suka dawo mota, kada ka so ka ga yadda suke jan attention sabida glass din ya boye ainahin rashin ganin kuma ga miji ya kama hannun matarsa a bainar nasi suna shiga duk inda suka zo a immmigration, har suka gama suka fito zuwa motarsu ya bude mata ta shiga ya rufe, sannan ya zagaya ya shiga barinsa, ya tada motar.

    Maimakon su nufi gida New Site sai ya wuce zuwa wani wajen daban. A rashin saninta gidansa ne da ya kammala ginawa a rijiyar zaki. 

    Sai da ya tsaya ya karba musu abincin ‘breakfast a AlAmir Restaurant sannan ya ce ta fito su shiga ba jimawa za su yi ba, wai abinci zai ci. Kamar ba za ta fito daga motar ba, ta ji hannun Sarham cikin nata ya dagota tsaye, ya ce, 

    Yau ni ne dan jagora tunda na kori Mardiyyah.

    Yaya Doctor nan din ina ne? Na dauka mun gama abinda ya fiddomu gida za mu koma?

    Ya ce, Ba wani abu, Inna zan daukarwa sako kuma inci abinci, nan din ba wani waje bane gidanki ne dana gina miki keda yayanki.

    Ai jin ya ce Inna babu tambaya ta fito don da ma ya san ‘weakness’ dinta a komai Inna ne.

    Ya bude gate din da kansa ya shigar da motar ya fito ya rufe, sannan ya kama hannunta suka hau har zuwa dakinsa da ke saman bene kasancewar duk muhimman abubuwansa a dakin suke ajiye. Akwai dindimemiyar katifa a kasa shimfide da bedsheet da filallika. An gama komai na ginin gidan sai fenti ne baa yi ba. Gida ne mai bangare biyu kowanne da dakuna uku da babban falo sai nasa dakin masterbedroom falle daya a saman bene. Suna shiga ya ajiye ledar breakfast din da ya yi order din. Ya maida kofar ya rufe bayan ya zaunar da ita cikin kujerar sofa bed guda daya dake dakin, ya ce,

     For Allahs sake, tunda aka daura mana aure, ko ince tun kafin nan, mun taba zama mun yi magana kuwa irin ta saurayi da budurwa?

    Hauwa saura kadan dariya ta kwace mata, amma ta fuske, ita yanzu kome zai yi ta baya ta raggo, ta san pressure ne ya saka shi ba wani abu ba, ya zauna kusa da ita, har kafadunsu na gugar na juna. Da sanyin murya ya ce,

     Hauwau-Maijiddah. Ya sake cewa, Kuluwa-Hauwa-Kulu, yau zance na zo, da neman iri.

    Hauwa ta zumburo baki gaba don ko kadan kashe muryan bai huda ta ba don jin abun take banbarakwai wai namiji da suna Hajara don ba haka ya sabar mata ba, kamar ta ce masa, fisabilillah Yaya Doctor kai ba ka ji kunya ba da ka ke kiran ma kanka samartaka? Ashe bata sani ba tsabar haushin da ya bata a fili ta fadi hakan ba tare da ta sani ba.

    Sarham yace ya ce, Naam, wai da ni kike? To bari in gaya miki wallahi na fi saurayi yau jin samartaka, zance kuma na fara zuwa daga yau har mu koma Jeddah”, ya dora hannayen shi kan kafadunta idonsa narai-narai kamar tana kallonsa, ya zare mata glass din ya ajiye a gefe, ya dora wuyansa kan kafadunta cikin dabarar da bata san yaushe hakan ta faru ba ya soma magana cikin wata irin murya mai tsuma zuciya da gangar jikin diya mace.

    Na yi kuskure mai yawa Maijiddah da na ke so ki ba ni dama in gyara.

    Na san ba a bari a kwashe daidai, amma aka ce matar na-tuba ba ta rasa mijin aure.

    Hauwau na san ba ni da wani matsayi a zuciyarki yanzu na rasa, har nawa na da kuwa, duk a dalilin ajizancina.

    Ya kai hannunsa na dama bisa habar Hauwa, ya wani irin rungumo ta jikinsa cikin zafin nama yana rirrigawa irin lallashin da ake yi wa baby.

    Forgive your husband, forgive him!.

    Hawaye masu dumi suka biyo kuncin Hauwa, ta rasa inda zuciyarta ke tsalle-tsalle a cikin kirjinta. Sarham ya sa hannunshi daya ya dago fuskar Hauwa yana kallon yadda hawayen ke gudu a kan kuncinta luwai-luwai da shi jikinta yana rawa. Don wannan kusancin da ya samar a tsakanin su baaia taba faruwa ba. gabadaya ta firgice ta tsorace don tana ganin babu kyau kuma bai kamata ba ace ta yi hakan da Likita Sarham din Inna. Ya ci gaba da fadi cikin muryar da tafi ta dazu ragaita, 

    Hauwa-Jiddah na tuba na bi Allah na maida kalamaina, na hadiyesu kamar yadda nayi amonsu a cikin wauta da ajizanci irinna dan adam.

    Daga yau ke matata ce ta sunnah da na aura don ina so, wallahi tun ranar da nayi miki aikin ido na ga irin kallon dakacen da kike yi min, raina yake matukar son ki. Na rasa irin ajizancin da ya debe ni wallahi Im selfish. 

    Ya kara matse Hauwa sosai a jikin sa, tana jin yadda kirjinsa de bugawa numfashin sa ke sauka heavily. Hauwa ta kasa ko kwakkwaran motsi. Sai zuciyarta dake wani irin racing helter-skelter a tsakiyar kirjinta. 

    “Amma ki yarda da ni duka lokacin nan daidai da rana guda ban taba manta ki ba Maijiddah, ban taba fasa tuna ki ba. burina da tunanina duka ya koma kan yaddaa ganin ki zai dawo daidai. Im deep in research watana uku yanzu haka bana Jeddah ma saboda ke ina Al-Qahirah ina bincike da neman karin ilimi a kan lalurarki.

     Maijidda ke fa amanar Innata ce, ko ban rike amanar kowa ba zan rike ta yar Innata, ta yaya zan ce bana sonki? Inada uzurori masu yawa a gaba na. Ba nufina kenan ba. duk da haka na yarda nayi wannnan kuskuren, nayi wauta nayi sakaci da amanar da Allah da iyayenki suka damka mini, a yanzu inaso ki yi hakuri ki bani dama in gyara tunda babu wanda yake sama da aikata kuskure sai Mazon mu SAW”.

    Hauwa ta mike a hankali daga jikinsa, jikinta yana tsuma saboda muryar da yake mata maganar da ita, sannan kuma a cikin kunnenta har da hura mata sassanyar iskar bakinsa, wanda hakan janta yakeyi deep down inside her yana arousing something different, tamkar yadda lantarki ke jan zuciyar mutum. Ba ta san inane ‘direction’ din kofa ba, amma a haka ta juya tana tafiya abunta. Fatanta kawai ta bar masa dakin sa.

    Yaya Doctor, don Allah tashi ka kai ni gida, babu irin wannan abun ko irin wannan maganar tsakanina da kai, kunya suke bani, you are my brother and you will always be, ban ga dalilin kawo ni nan kana gaya min wadannan maganganun ba, wadanda ban nemi jinsu ba, kuma I have no room for them.

    Sai ji ta yi ta yi tuntube da katifa saura kadan ta fadi. Maganarta ta batawa Sarham rai kwarai, ya ce, Haka ki ka ce ko? Yau kuwa za ki san ni ba Yayanki ba ne, ba mu hada kowanne irin jini ba. Kuma zan tabbatar miki sadaki na biya na aure ki ba Inna ce ta haife ni ba.

    Ya karaso dora hannayensa bisa kafadunta ya juyo ta suka fuskanci juna. How he wish Maijidda could see his eyes today! A wannan yanayin da yake ciki, tabbas da ta yarda shi din ba Yayanta ba ne mijinta ne wanda Allah ya halatta aure a tsakanin su.

    Kirjinta na bugawa da sauri-da-sauri, shi kuma numfashinsa kamar zai bar kirjinsa ya soma sumbatar kasan wuyan Hauwa wuri-wuri, da wani irin gentle soft kiss! Sannan ya dora ‘lips dinshi a kan nata ya manne bakinshi da na Hauwa in a gentle manner yana kissing aggressively da wani irin urge dake taso masa da bai taba jin kamarsa ko makamancinsa a rayuwarsa ba. Kai yau ji yake bai taba kusantar kowacce mace ba a rayuwarsa sai Hauwa, this will be his first time of marital life.

     Duk kiss daya in ya yi sai ta ji shi har cikin kwakwalwarta, sai ya tsirga har cikin zuciya da ruhinta. Kafafunta ta ji suna neman kayar da ita, Sarham ya yi maza ya dauke ta a hannayensa ya kwantar a kan sofa-bed din da suka taso, hakan ya sa Hauwa sakin kukan da ta ke rikewa gabadaya jin Sarham ya rabata da doguwar abayarta, ta tabbatar yau mai kwatarta a hannun Yaya Doctor sai Allah daya haliccesu ya kuma halatta masa ita.

    Ta yarda yau ta fado wata rayuwa da ba ta taba sanin akwai irinta a duniya ba.

     Tun daga babban yatsanta Sarham yake bi yana kissing yana yowa sama a hankali, ya yi birki a kan cibinta. Hauwa ta rasa inda za ta sa kanta ban da rishin kuka da ta ke yi mai cakude da wani irin pleasure dake ziyartarta. In wannan shi ne auren da Mama ke kokarin kwato mata ashe Mama ba ta san ya yake ba.

     Kokarin Sarham a lokacin na son raba ta da innerwears din jikinta ne gabadaya, amma ta rike gam! Cikin wani irin sauti ya ce, Kada ki sa in tsaga ta, ki bar ni in fidda ta a hankali, wata na uku banida mata saboda ke!.

    Sai ta sakar masa.

    

    Sarham bai san sanda ya kankame Hauwa yana groaning kamar ransa zai fita ba. Yayi rantsuwa bai taba jin abinda yake ji a halin yanzu akan kowacce mace kafin yau ba. don ya san in soyayya tana kisa a yau zata kasheshi ne kowa ya huta Mama ta huta Hauwanma ta huta Madinar ma ta rasa

    

    Alamarin da ya tsoratar da Hauwa don ta dauka Sarham suma yayi, amma jin yana gab da samun abinda yake hari da zafin da taji ya ankarar da ita abin da ke shirin faruwa a lokacin.

    Janyewa ta soma yi cikin kokarin dawowa hayyacinta, Sarham kuwa a wannan lokacin ba ka jin komai a bakinsa sai “janye kalamansa na baya”, wani ma in ka ji sai ya ba ka dariya ya ce, Na ce miki I am not your brother, Im your loving husband, ki barni in nuna miki hakan yanzunnan, na rantse na fi ki shiga wahala a shekara dayan nan, ba mantawa na yi da ke ba, tunanin hanyar da zan nema miki lafiya nake yi.

    Hauwa ta rikice da kuka da razanar alamarin da ke shirin faruwa da ita. Ta ce,

     Don Allah Yaya Doctor ka bar ni in koma wa Mama lafiya wallahi wani abu ya same ni za ta gane. Ni ban taba yin wannan rashin kunyar ba. Ka rufa min asiri yadda Allah ya rufa maka.

    Jikinsa ya yi mugun sanyi ganin tana neman shidewa don kuka da razana. Ya kifa kai a kan kirjinta ya yi shiru, kuzarin jikinsa ya ragu, ya daina duk abin da yake yi. Ya soma maida mata sitturun jikinta.

    Ya kama hannunta ya dago ta ya dora ta bisa cinyoyinsa, fuskarsa a saman kafadunta ya sumbaci dogon wuyanta a hankali ya ce, 

    Does this make a difference? Daga yau za ki daina ce min Yaya Doctor?

    Hauwa kamar ta ce kasar wajen ta tsage ta shige haka ta sa tafuka tana rufe fuska, shi kuwa ya kara rungume ta tsaf a jikinsa.

    Sun dauki lokaci a haka, ba ka jin komai sai bugun zuciyoyinsu a kirjin junansu.

    

    Karar wayarsa ce ta dawo dasu daga wata duniya mai ban mamaki da suka samu kawunansu cikin abinda bai gaza mintuna talatin ba. Yana dubawa ya ga Abba ke kira.

     Kasa dagawa yayi, sai ga kiran Mama ita ma. Itama bai daga ba ya sauke Hauwa daga jikinsa bayan ya sumbaci kirjinta son ransa, ya kuma sake fidda su a hayyacinsu. Karar kiran wayar akai-akai duk ya dagawa Hauwa hankali, amma shi ko a jikinsa.  Da kyar da lallashi da kalaman yarda da daukar alkawarin cewa,

     Ni Hauwa na yarda Yaya Doctor ba Yayana ba ne, mijina ne na sunnah, kuma na janye kalmar a SAKE NI!.

    Sarham ya kyale Hauwa yana murmushi da godiyar Ubangiji a fili, ya ce,

     Saura mu je gaban Mama ki canza magana, wallahi sai kin san sauran, don a gidanta zaa yi komai kuma a dakin yar ta, don wallahi na gaji da bata hakuri, inyaso in ta ganki da ciki a gabanta ta janye kalmar saki, ta yarda auren Sarham da Hauwa;

     Mutu ka raba ne..

    Hauwa ta ce cikin dimuwa da tsoron wai zai iya irin wannan a dakin Sumayyah a gidan Mama, da sauri tace Na yarda, wallahi in ta ce ko inaso a yi saki? Zan ce aah.

    Shi har dariya Hauwa ta ba shi, ya dara sosai yana bubbuga bayanta, domin ba karamin tsorata da alamarinsa ta yi ba.

    Ko break fast din da ya sayo musu ba ta yarda ta ci ko loma daya ba, shi kuwa sai da ya ci abinsa cikin kwanciyar hankali kamar bashi ake ta kira a waya ba, sannan ya yarda suka fito.

    Suna shiga mota ya yi reverse ya hau kan titi, sai a lokacin Hauwa ta ji wani irin kukan kunyar Mama ya zo mata. 

    Ta rasa da wace fuska za ta je wa Mama yau? Gani ta ke duk abin da suka yi din nan da Yaya Doctor is written on her forehead (a rubuce yake a kan goshinta). Sarham tuki yake yau wani irin tuki cikin nishadi. Kamar tayar motarsa ta samu matsala, ya dora hannunsa bisa nata, ya ce,

     Cry more! Its all in LOVE! Wani kukan ma yarinya sai an je Jeddah.

    

    Hauwa ta ce, cikin kuka Ni kam na shiga uku yau, Yaya Doctor ka jawo min nayi rashin kunya nayi rashin gaskiya na yi butulci, za ka jawo Mama ta daina tattalina, ka shiga tsakanin Uwa da yar ta. 

    

    My dear Jeddah, in ta daina tattalinki, ni zan yi kin ji?

    

    Da sauri tace wallahi ba irin nata ba, dame zaka yi tattalin nawa? In dai irin wannan tattalin na rashin kunya ne wallahi ni na yafe. Dariya kamar ta kashe Sarham ya kara manne hannunsa cikin taushin fatar hannunta.

    Suna isowa gidan dankam da yan daurin aure don nan ne meeting point inda daga nan zaa wuce Kofar Gadon kaya, sabida an cika kofar gidan su ba hanya sai ta kofar kitchen suka zaga ya bi da Hauwa zuwa cikin gidan, nan ya hadu da Nancy a hanya ya damka mata ita, ya ce ta kai ta dakinta. Sannan ya ce, 

    To Maijidda sai na zo zancen dare.

    Ta yi saurin daga kafa tana gode Allah da Nancy ba ta jin Hausa. Kuma da ita suka fara haduwa

    Jamaa kam sun dauke hankalin Mama, don haka har suka kai dakin Hauwa Mama tana falonta da kawayenta yan chamber dinsu, sau biyu tana shiga neman Hauwa, Mardiyyah na cewa tana wanka. Har a shigowa ta biyu Mama tace to wannan wankan na sake fata ne kenan? 

    Aka yi daurin auren Surayyah aka zarce da reception a ‘Niima Guest Palace, so sai ya zamanto har dare gidan ana kai kawo Mama uwar amarya kanta ya dinke da hidimar bakin da suka gayyato daga bangarenta dana Abba Prof. da suka zo daga Shanono.

    Mardiyyah ce ta je ta karbo musu abinci, sai Mama ta ce mata ta je ta zo da Antinta ta gaida su Barr. Hannatu. 

    Hauwa ta sauke wata wahalalliyar ajiyar zuciyar hayewa tudun muntsira, bayan ta ji ta kwance a kan gadon dakinta ba tareda Mama ta san dawowarta ba, sannan ta biyo Mardiyyah suka fito.

    Falon cike yake kuma duk manyan lauyoyi mata ne kawayen Mama.

    Mama ta ce, Hauwa, yau wane irin wanka ki ke tun dazu kamar mai wankan jego? Shigata biyu ana cewa baki fito ba”.

    Cikin in-ina ta ce, 

    Yiyi hakuri Mama.

     Mama ta kada kai, ta ce, Kawayena ne na ce ki zo ku gaisa.

    Suna ta kallon Hauwa da mamaki ban da Barr. Hannatu, tunda ita ba yau ta san Hauwa ba. Hauwa ta tsugunna tana gaishe su cikin ladabi ba tare da ta kalli sashen da kowacce ta ke ba. wannan ya tabbatar musu da cewa surukar Maishariah din bata gani.

    

    Barr. Shafaatu ta kasa shiru, ta ce,

     Ita ce second wife din Sarham da aka ce ba ta gani ko?

    Barr. Habiba ta ce, So beautiful masha Allah, and so pathetic!.

    Mama ta san halin yan kayanta, tuni Hauwa har ta fara kumburowa, ta ce da Mardhiyyah, Mardiyyah maza ku je falo cikin yan Shanono, ku daina kulewa a daki ku kadai bayan ga yan uwa duk sun zo, ki kai ta ta gaida kowa ki gabatar da ita kinji kafin nazo?.

    Suna fita ta kama hanyar komawa daki wato bazata gun yan Shanonon ba. Mardiyyah ta ga Antinta na share hawaye. Yau an tabo ta, tunda an mata gorin ido. Cikin ikon Allah suna shiga dakin Sarham na shigowa. Ta kifa kai a jikin gado tana rusa kuka.

    Ba karamin kaduwa yayi ba ya iso gareta da sauri, ya manta da Mardhiyyah a wajen yayi maza ya rungumota barin jikinsa na dama.

     Mardiyya lafiya? Me aka yi mata? Ko kin fadawa Mama mun fita ne? Ya tambaya a dan rikice da damuwa.

    Mardiyyah ta ce, Yaya Likita ba abinda aka yi mata, Mama kawai ta ce in raka ta ta gaida yan Shanono, kada ka dada kada ka rage shikenan fa!.

    Hauwa ta dago ido tana hararar inda Mardiyya ta ke tsaye, ta ce, yi min shiru. Ba a kunnenki aka yi min GORIN IDO ba? Har tana ce mun abun tausayi, wani so pathetic?

    Sarham ya zauna a gefen gadon yana hadiye dariya ce, nagode, je ki abinki Mardiyyah.

    Ita dai bata ga abin kuka ba tunda ba da tozarci suka fada ba. Dukkansu manya ne. haka Mardhiyyah ta sa kai ta fita tana yar dariyar shagwabar Antin nata.

    Ya sake kankameta yace, Kin ga Mardiyya ma dariya ta ke miki.

    Eh, da yake ba ita aka cewa MAKAUNIYA ba.

    To karya suke? Ina idon yake?

    

    Ai kuwa Hauwa ta balle da sabon kuka riri-ririiiiii.

    Sarham ya sa hannu a kwibinta yana mata cakulkuli, ta zame da mugun zafin nama.

    Tashi ka fita, kafin a ce maka mijin makauniya kaima.

    Sarham ya lumshe ido ya nuna kansa da dan alinsa kamar Hauwa na ganinsa, ya ce, Sai in ba su amsa da ni na makantar da matar tawa saboda rashin iya aiki na, daga cire hakiya. Ya kara rungumo ta ya manne bakinsu wuri guda yana sumbata hungrily, ta haka ya hana sautin kukan fitowa.

    

    Ya salamu sallim, Ya jamilal Munzar (Ya mafi kyawun masu gani). 

    

    In ji Mama Maishariah da ta sawo kai dakin da zummar bai wa Hauwa hakuri, donta san an mata abinda ba ta so. An mata GORIN IDO (ta bakinta).

    Da sauri Mama ta koma da baya har tana tuntube da dokin kofa. Dukkansu kuma ba wanda ya san da shigowarta, Hauwa ce ta yi maza ta janye tana fadin,

     Hasbunallah!” Motsi nake ji. Tare da dafe goshinta don tabbas taji motsin mutum a kofa.

    Sarham ya yi murmushi idanunsa a lumshe, ya ce, Yarinya tun ba a je ko ina ba ta fara sanin dadin kiss din miji.

    Hauwa sai ta dau filo ta rufe ido da shi tana fadin, Ni wallahi ba ruwana, ni ban san wannan abin ba, duk kai ka koya min yau kuma sai Allah ya saka mini in wani ne yazo ya gani, ai kasan gidan cike yake mutane, ni bana so ma ka daina dakin nan don Allah, kuma ba zan kara binka koina ba.

    Har ya kai bakin kofa ya juyo. Ya kanne mata ido kamar tana kallonsa. Cikin kankanuwar murya yace.

    This is light kiss, ki shirya ‘hot kiss’ later tonight!.

    Hauwa ta danna kai cikin cinyoyinta tana rokon Allah ya sa kasar ta tsage ta shige yau ta huta.

    Mama tana kallon wucewarsa zuwa dakinsa ta baro jamaa ta dawo  dakin Hauwa. Gaba daya dakin Hauwan yanzu kamshin Sandalia ko Oud-Abyad din Sarham yake yi, wato turarukansa na dindindin (Non-alcoholic Arab  perfumes).

    

    Hauwau!

     In ji Mama tun daga bakin kofa.

    Ashe ni tufka nake kina min warwara?

    Hauwa ta kidime iyaka, ta fara mazari na rashin gaskiya murararn. Kada dai motsin data ji Mama ce? Yau da ta kade har ganyenta.

    Mama ta ce cikin takaici, 

    Ban taba ganin sakarar mace irinki ba, kai jamaa, Allah wadaran rashin wayo.

    Sai Hauwa ta soma hawaye nan take kamar an balle famfo. Fadi ta ke,

    Wallahi Mama babu ruwana, sai da na ce masa ba zani ba. Ta kifa kai a cinyoyinta tana rizgar kuka.

    Mama ba ta san da zancen fita ba, rikicewa da rashin sabo da karya tasa Hauwa ta fallasa komai.

    Wallahi Mama ban yarda ba, bai yi komai ba nan nan (ta nuna bakinta), kawai na bari, kuma shi ma din fin karfina ya yi.

    Mama takaici kamar ya kashe ta, ta mike tsaye tana cewa, Na kuwa daina tada hakarkarina a kan a sake ki, don ki auri mai sonki da gaskiya, tunda naga kina son abinki duk rashin kirkinsa, hada kayanki kafarki kafarsa, kafin a kara yi min abin da yafi karfin idona.

    Haba! Hauwa ta rushe da kuka tana, Na tuba Mama, na tuba na bi Allah na bi ki, wallahi ba inda zan iya zuwa in barki.

    Mama ta yi kwafa ta ce, ji min munafurcin Hauwa-Kulu, yau da kika sa kafa kika bishi kika barni ma na sani? Ni a wa? Bi mijinki a sha soyayya lafiya, da ma tare na ganku. 

    Na so ki bari mu wujijjiga shi yadda zai kara sanin darajarki, to kin kwashi jiki kin bi shi kun sha soyayya ko? Bayan ya kwashe shekara bai neme ki ba, da yake ke sakarya ce wadda ta rako mata, kiss din abun banza ne da ki ka barshi ya samu a arha?.

    Hauwa kuka kawai ta ke na nadama da kaka-nikayi ta kasa magana, duk sai ta bai wa Mama tausayi.

    Ta sassauta ta kama hannun Hauwa, ta ce, Ba ki yi min laifi ba Hauwa kin ji, kuma ba ki yi wa Ubangijinki ba. 

    Karewa ma lada ki ka samu kinji.

    Ni na san Sarham yana sonki duk abin da nake yi kuma ina sane. So nake in sa shi ya gane da kansa yana sonki ba auren jihadi da taimako ya yi da ke ba. So nake ya furta min da bakinsa ya janye kalaman kanwar nan da yake jifanki da ita, It does hurts me a lot!

     Karshen kaskancin da namiji zai miki kenan, ya tari gaban idon ki yace, ba ya miki so na soyayya. Sarham ba shi da saiti, ki bar ni in saita shi yadda ko wani ya ji ya ce ke kanwarsa ce zai musa da bakinsa yace aah matata ce abar so na.

    Hauwa na kuka da sharbe ta ce,

    Insha Allah Mama ba zan sake yarda ba.

    Tausayi ya kama Mama don kuru-kuru ga soyayyar lelen Abba nan ta fito yau a idonta, da ko gani ba sa yi, ina ga suna ganin cool kamanninsa da kyakkywan sajen sa da murmushinsa mai daukar hankalin mata? 

    Mama ta tashi ta fita kwallar tausayi fal idonta.

    Mardiyya ta dawo dakin tana cewa,

     Anti ba ki ci abinci ba, Anti don Allah ki daina kuka yana daga min hankali.

      

    Ta hau share hawayen da gefen mayafi ta ce,  Na daina Mardi!.

    Ta ce, To abincin fa?

    Sai an jima, ki kulle mu ta ciki, ko Yaya Doctor ne ya buga kada ki bude kin ji? Murajiar karatuna zan yi.

    Taje ta dauro alwalla, sai ta ga cewa ba za ta iya alwala a haka ba, dole sai ta yi wanka don abin da ba ta taba gani ba ne ta gani a tare da ita yau. 

    An gaya mata kuma da jimawa wankan iri daya ne da na sallah.

    Ta yi sallah ta dora da nafila ta zauna tana murajiar karatun da Mama ta kara mata jiya.

    Cikowar yan uwansu da abokan arziki a gidan ma bai barshi ya iya sake shigowa da daddaren ba balle ya tadda kofar tasu a kulle da mukulli bisa umarnin ko ya buga kada Mardiya ta bude.

    Dangin mijin Surayyah suka ce su a wannan ssatin zasu dauki amarya zuwa Ikko don haka dole aka zarce da bikin maimakon sai sati mai zuwa da mama ta saka. Don haka a washegari aka yi wunin Surayya a Gadon Kaya, da daddare dinner sai shirin kai amarya gidan su Engnr. Aliyu a Dorayi washegarin ranar.

    Hauwa ba ta je dinner ba ta kulle kanta a daki, amma Mardiyya ta je. Mama ta sameshi har dakinsa ta kora masa ‘warning’ din kada ya kara shiga dakin Hauwa sai ya zo mata da hukuncin da ya yanke wa zamansu.

    Shi ma kuma yana ta nasa shirin duk don ya wanke ran Mama, ya kuma yi ‘repenting’ kuskurensa, tuni ya karbo passport din Hauwa ya kai gun visa.

    Yan biki duk sun watse bayan an kai Surayya family house din su mijinta. Yau kwana uku kenan Mama na gadin Hauwa, ta hana shi kebewa da ita. Ta hanashi rawar gaban hantsi. Iyakar tsaka mai wuya Sarham ya shige ta don sosai yake cikin bukatuwa da Hauwa, don haka ya maida hankali wajen sakin kudi a yi a gama visarta. Ga Abba ya ki shiga maganar, ya ce shi a bayan mai sharia yake.

    

    ***                 ***                  ***

      

     MUTANEN JEDDAH

    

    Sumayyah ce kadai  zaune a falon gidan Yayanta tana karatu da gilashi a idanunta, aka danna kararrawar son shigowa, Sumayyah ta mike ta aje littafin da ke hannunta tana fadin, Naam, ina zuwa. A zatonta Madinah ce ta dawo daga unguwar data tafi.

    Tana budewa suka yi tozali da wani sardidin saurayi son kowa. Amma kuma fuskarsa looks so familiar to her.

    Ya yi mata murmushi, ya ce, Salam, how are you? Tana ciki ne matar gidan? Na kasa kama ta a waya”.

    Sumayyah ta kasa magana, don gayen ya kai makura wajen kyau, ga tsafta ga sanyin murya.

    Da kyar ta iya cewa, Ba ta nan!.

    Sai ya mika mata wata leda ya ce, ok. Please ga shi ki bata, kice in ji Hajja Ramlah.

    Hannun Sumy na rawa ta karba sai ya ce, Ke bakuwa ce suka yi halan daga Nigeria?

    Eh. Kawai ta  ce.

    Ya  ce, Ok, toh. Ki gaya mata zan dawo bayan magriba. Sunana Usman Attahiru, yaya sunan malamar?

    Oh! Are you? Usman?

    Ya ce, Yeah.

    Anti na yawan zancenka, ina ji kullum. Nice meeting you.

    Ya ce, Na gode, kin san sakuwata ce. Kullum fada muke a baya, ina cin zalinta in more, shiyasa yanzu nake kyautata mata, na maida kaina ma direbanta at times, don in wanke kuruciya mara dadi da muka yi nida ita.

    Duk suka yi dariya mai sanyi.

    

    Ya ce, Ya sunanki?

    

    Sumayyah Abbas.

    

    Oh-oh! Ko ke ce Sumayyah kanwar Baban Waheedah?

    Eh ni ce.

    By the way, nice to meet you too Sumayya, I love the name.

    Cikin murmushi Sumayya ta ce, Na gode Uncle Usman. A gaida gida.

    Bayan tafiyarsa Sumayyah ta adana sakon, amma sai ta kasa zaune ta kasa tsaye, Usman Sorondinki da muryarsa ya tsaya mata a rai farat daya, irin yadda wani namiji bai taba shiga ranta ba.

    Madinah na dawowa Sumayyah ta bata lokaci ta  kintsa, kafin ta kai mata sakon har dakinta, karonta na afarako da sanya kafarta a dakin Madinah tun zuwanta gidan. Ita kanta Madinah ta sha mamaki. 

    Ya zo nan kadan kafin dawowarki, yace shi Yayanki ne, wai Osman sunansa.

    Oh! Zai dawo an jima, mun yi waya na manta da zuwansa ne na fita.

    Sumayyah ta ci gaba da shiru a tsaye, ta kasa tafiya, Madinah ta ci gaba da sabgoginta ta manta da ita. Ganin haka ta ja matattun kafafunta ta fito daga dakin.

    Ko da ya dawo kamar yadda ya ce zai dawo, Sumayyah ya cimma a falo Madiah tana daka tana sallah don haka suka balle da hira shi da Sumayyah, kan kace meye wanan sabo ya fara shiga tsakanin Usman da Sumayyah, bini bini ya zo gidan bayan ada sai in Madinah ce ta kira shi ko Hajjah Ramlah ta aiko shi, ya zama suna dasawa sosai har ta kai su ga karbar lambar wayar juna. 

    Kafin ka ce me? Madinah ba ta ankara ba aka soma yi mata midnight call’ a gida. Sumayyah har mantawa ta ke Usman Attahiru Yayan Anti Madinah ne, gabadaya ta rufta nan take, kafin dawowar Sarham.

    

    Ranar da Madinah ta fahimci wai soyayya ake tsakanin Sumayya da Usman ta sha mamaki, at the same time a take anan ta nuna wa Usman rashin goyon bayanta, da hujjarta na cewa Sumayyah tun fil azal ba ta kaunarta, kuma an gaya mata ita ce ta hannun daman matar wulakancin da sarham ya auro mata.

    Usman kuma ya ce mata, a gaskiya shi bai son gutsiri tsoma irin na mata ba, ya ga Sumayyah ta yi masa, komai nata ya yi masa ba ruwanshi da shirmensu, Sarham kawai yake jira ya dawo ya gabatar da kansa.

    Madinah ta lashi takobin ita kuma sai bayan ranta Usman zai auri makiyarta. Ko mata sun kare a duniya bazata bada goyon baya ba, dama dai Surayyah ce kuma tayi aure ita.

****                   ****                ****

    

       KANON-DABO

A

ka kawo masa visa din Hauwa a wayewar garin litinin, bayan an gama bugawa. Mama na shirin fita office sallamar Sarham ta dakatar da ita. Ya shigo dakin da karfin gwiwarsa yau dai, da kallon marairaita da karbar laifi, suka gaisa shi da Mama ba yabo ba fallasa.

    Cikin brown envelope ya mika mata abu, 

    Ga shi Mama na karbo!.

    

    Mama ta amsa ba tare da ta san meye a ciki ba, tana kokarin budewa ta gane passport ne.

    Za ta fara fadan har yaushe aka je aka yi passport din ita bata sani ba, ta tuna subutar bakin Hauwa na cewa, sun fita da Sarham kwanaki. Ta yi kwafa kawai ta aje a gefe ko bude visar ba ta yi ba balle ta ga wace iri ce ko ta wata nawa ce. Murya fal ladabi Sarham ya dukar da kai yace,

     Mama kin yi izni za mu iya tafiya tare? Already na yi mana booking jibi ne tashin namu insha Allah.

    Mama ta yi shiru, ya ci gaba da roko, da ban hakuri da ban baki da alkawarin bazai kara maimaita kuskurensa ba kuma zai kula da Hauwa tsakaninsa da Allah. Da kyar Mama ta ce, 

    To karatunta fa?

    Ma yi wannan shawarar daga baya in mun je naga yadda abubuwa zasu kasance.

    Mama sai ta kasa musantawa, tunda  abin da ta ke rokon Allah dare da rana ne yau Ya amsa musu. Sarham ya dawo kan hanya kuma ya fahimci kansa. Ko bai fada ba ta ga ‘seriousness’ a kan Hauwa wannan karon a tare da shi sosai.

    Duk da haka ta kawo nata kalubalen na cewa, ya zai tafi da Hauwa babu Mardiyyah?

     Wa zai dinga taimaka mata?

    Sarham ba tare da tunanin komai ba, ya ce, I will take care of her, my self Mama, for the mean time, kafin in yi deciding akan ko zan iya daukar Mardiyyar a gaba. I will do everthing to undo the hurt I caused you Sweet Mum.

    Mama tayi ajiyar zuciya a karshe, ko bata ce ba hakan na nufin amincewarta.

    

    Hankalin Mardiyyah ba karamin tashi ya yi ba jin Mama ta ce ta hada wa Antinta kaya za su tafi Jeddah. 

    Mardiyyah tana kayan Hauwa a jakar matafiya tana kuka wiwi, amma ta danne bakin da dankwalin ta kada Hauwa taji kukanta, amma saida taji sheshsheka. A kwance take amma saida ta tashi zaune tace Mardhiyya lafiya? Ta gaya mata abinda aka ce da ita. Hauwa kanta jikinta yayi wani irin sanyi. Mama ta alkawarta ma Mardhiyyah tafiya Saudiyyah tare da ita duk lokacin da za ta je umrah, kuma ba za ta mayar da ita Shanono ba ko ba Hauwa a gidan, za ta ci gaba da zama tare da ita ne har aurenta.

    Hauwa kanta na kasa, ko dagowa ta kasa yi sabida nauyin Mama da damuwar data cika ranta. Mama lakca guda ta hau yi mata a kan ta zauna lafiya da kowa da zama ya hada ta da shi, kuma ta girmama Madinah tunda ko a girme ta girme ta, ba a aure kawai ba.

    Ta ce, Na san ba ki da matsala ko kadan a kan girmama na gaba da ke Hauwau, amma zaman mata biyu karkashin inuwar miji daya sai an daure an kai zuciya nesa ba kusa ba. in ba haka ba duk zaku taru ne ku kai junanku wuta. Ki sa a ranki ibadah ki ka je yi domin zaman aure ibada ne Hauwa, balle wanda ya zamo ku biyu ne a wurin mijin.

    Jikin Hauwa bakidaya ya yi laasar ta soma hango babban kalubalen dake gabanta, nan take ta ji kamar ta ce da Mama babu inda za ta je, amma ganin yadda Mama ke ta kai da komowa wajen yi mata shirin tafiyar, da bata magungunan da bata san ma kona menene ba da yadda Sarham din kansa ya dauki komen nata Jeddah da matukar muhimmanci sai ta kasa magana, duk da Mama ba ta kara bari sun kebe ba, ta maida Hauwa dakintama kwata-kwata ana saura kwana biyun su tafi, tana ta yi mata kyakkyawan shiri da tsumi kala-kala da tukudi.

    Ita kanta Hajiyar Abba, wato Hajiyar Gadon Kaya cewa tayi ba ta ga dalilin zaman Hauwa tare da su ba, in makaranta ce ai babu inda babu ita. Kada su sake su bata mata rai su tattara mishi Hauwa ya dau kayarsa. In don rashin ido ne ya sa Mama ajiye ta shekara guda a daki  ai ya fi kowa sanin ba ta da idon ya je ya auro ta.

    Ranar sun sha fadan Hajiya Kulu wadda ta yi tattaki har gida ta sille Mama da Abba don Sarham ya gaya mata takunkumin da Mama ta saka masa na saki, da yaki kuma ta kuma hana shi ko magana da Hauwa. 

    Shi ya sa ma ranar da ya kawo visa mama ba ta yi dogon jainja ba, don Abba ya ce a daina yin duk abin da zai saka Hajiya Kulu yin fada, saboda BP dinta.

    ****                  ****                     ****

    

    Duk wani shiri na tafiyar hauwa Mama ta gama sbhi cikin lokaci, komai da tasan zata bukata ta tanadar mata. Kuma ita da kanta ta kai su filin jirgin Malam Aminu a ranar tashin nasu. Bata dawo gida ba sai da aka kira fasinjoji domin shiga jirgi.

    A daren ranar duk kokarin Sarham na samun Madinah a waya bai yiwu ba, ko network ne ko wayar tata a kashe take? Ya so tun a daren ya gaya mata cewa tareda Hauwa zai dawo. Ta shirya mata daki daya cikin dakuna biyun da bata amfani dasu. A zuciyarsa baabu fargabar komai, don yarda zuwa yanzu dole ya kara zama namijin duniya a tsakanin matan nasa kuma ya zauna da Hauwa cikin iyalinsa cikin adalci, bai yarda da raba gida ba shi raayin sa shine samar da kyakkyawar muamala  ta fahimta da taimakekeniya tsakanin Jiddah da Madinah kasancewar Hauwa nada lalura. Ba zai kaita wani gida ta rayu ita kadai ba.

    Yana fatan wannan din ya hada kan iyalin sa da samar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin su. Don shi wai bai yarda da hargagin Madinah na cewa ita Madinah tafi Hauwa komai ba, wai don tana takama da tanada zurfin ilmi da iyaye masu kudi yen-yen-yen to shi ina ruwansa da wadannan din, tunda dai shi ko wani nasa bai taba aikawa gun Daddy neman taimako daga ISDB ba, itama ba su ne dalilan da suka yi mujazar auren shi da ita ba.

    Dr. Sarham Abbas ne rike da hannun matarsa Hauwa Bilyaminu, suna taka matattakalar jirgin ‘emirate’ wanda zai tashi da su zuwa kasa mai tsarki a daren yau.

    Hauwa kankame ta ke da hannun Sarham cikin tsoro na rashin sabo take taka matattakalar, shi kuma ba tare da damuwa da kallon da ake musu ba ya rike hannun nata sosai yana gaya mata cewa,

     Mind the stairs (ki kula da matattakalar).

    Lokacin da jirgin ya karci kasa zai tashi, Hauwa ba ta san sanda ta saki salati ta kara damqo Sarham ba. Wasu Larabawa mata da miji a kusa da su, sai da suka yi mata dariya, don sosai ta ke cikin gigita da karar tashin jirgin. Wani hargagi ne da bata taba ji ba mai barazanar buga dodon kunnenta. 

    

    A cikin jirgin, shi ya sanya hannu a kwibin Hauwa ya daura mata belt, lokacin da larabawan na kusa da su suka fahimci cewa matarsa ce kuma bata gani ba karamin burgesu Sarham yayi ba sabida yadda yake kula da duk wani motsinta. Ga idanun nata a bude tar masha Allah dasu. Sai da matar ta karbi adireshin su na can Jeddah suka ce su kuma a Taif suke zaune In sha Allah suka shigo Jeddah Sayayya watarana zasu kawowa Hauwa ziyara har gida. 

    Ba su tsaya a koina ba wato babu transit sai a airport din Sarki Abdulaziz.

    Hannun Sarham still cikin na Hauwa, a lokacin da suke (passing immigration checks) na shiga kasar Saudiyyah har suka kammala. Taxi (Ajrah) suka hau, mai Ajrah ya ja mota zuwa hanyar gidanshi da ke cikin gidajen likitoci na Saudi-German.

    

    Tunda suka hautiti Hauwa ta cire yatsunta daga cikin na Sarham. A lokacin shi yanata kokarin saka layin shi na Saudiyyah a wayarsa. Ta mika cikin tunani. Ba kuma tunanin komai take ba face tunanin irin tarbar da matar likitan nata zata yi mata. Da kuma irin zaman da zasu yi tare, duk da cewa na dan takaitaccen lokaci ne wato hutun ta na semester inji Mama. 

    Shikuma ya sa a ransa Hauwa ta zo Jeddah kenan, wato bazata koma Najeriya ba. tun a cikin motar ya soma browsing din makarantu a cikin birnin Jeddah don nema wadanda ke hada karatun su da speciality na masu bukata ta musamman wato makarantun da ke yin (Inclusive Education). 

    ****                     ****                 ****

    

    

    

      KAFIN SAUKAR SU DA AWANNI BIYU

    

S

umayyah na goye da Waheedah tana goge dining, Madina na daki tana waya da Usman cikin zafin rai, sai Allah ya baiwa kunnuwan Sumayyah damar zuqowa. 


    Wallahi sai dai ka daina alaka da ni din Ussy, da dai in bari ka auri Sumayya, kai ne ba ka san irin halinta ba, wallahi annamimiya ce zuciyarta bata da kyau bata kauna ta.

    Sai kin gaya min me ta yi miki na rashin kauna, sai kin gaya min me tayi na annamimancin, alhalin ita din ba kishiyarki ba ce, kanwar mijinki ce, uwa daya uba daya.

    Madinah ta kara hassala ta ce, Yaya Usman ban yi niyyar gaya muku ba sam, nikadai na binne abun ina fama dashi a raina don kada Daddy ya kashe min aure, amma yau tunda ka dage a kan Sumayyah zan gaya maka, Hajjah Ramlah ma zan gaya mata. Sarham ya kara aure a Kano, itada uwarsu sun baiwa yarinyar masauki, tun filazal Sumayyah bata taba sona ba, na rasa laifin da na yi mata. 

    Ko don in rama abin da Sumayyah tayi min na kiyayyar babu gaira babu dalili na rantse ba zaa yi auren nan ba, don na lura ita ma munafukar tana raayinka, har da yi min wani sabon ladabi yanzu, ba ta san kar nake kallonta kamar takarda ba..

    Sumayyah ta yi mata gyaran murya daga bakin kofa, Madinah ta kashe wayar ta tsuke fuska, sai ta karasa shigowa dakin ta kwantar da Waheedah a gadonta hannunta rataye da jakar kayanta, kamar ba ta ji me Madinah ke fada a kanta ba, ta ce,

     To Anty Madinah da alkhairi, zan koma hostel, tunda Yaya Sarham ya ce yau zai dawo, nagode da zumuncin ki.

Madinah ta harareta kasa-kasa, ta ce, 


A gaishe su!.


    Sumayyah ta juya cikin bacin rai za ta bar dakin tana fadi a ranta, ko son Usman zai kashe ta itama ta hakura ba za ta aure shi ba, ko da gold aka kera shi.

    Har ta kai kofa zata fita Madinah ta ce, Umh! Ji mana Summy???”

    Sumayyah ta dakata ba tare da ta juyo ba, idonta fal kwallah don har ga Allah tana son Usman Sorondinki. Ba ta san me ya sa zuciyarta ta yi mata wannan rashin adalcin ba, tunda Yayan Madinah ne da baasa ga maciji.

    Madinah ta ce, Makauniya ba ta da Yaya ne? I mean ita kadai ce a wurin iyayenta babu dan uwa babba namiji haka?”

    Cikin rashin fahimta Sumayyah ta juyo tana kallonta.

    Madinah ta ware mata fararen idanunta sosai, ta kwance ribbons din data daure gashinta dashi ya zubu a wuyanta ta girgizashi sannan ta kara daure shi cikin ‘hairbound’ din, ta ce,

     Eh, ai ba za ta rasa dan uwa ba, I mean makauniyar gidanku, ina ga shi zai fi dacewa da ke, dangin yar Badala yan cikin gari ba nawa dan uwan ba haifaffen Saudiyyah.

    Sumayyah ta saki kwallar idonta, ta fice ba tare da ta ce da Madina komai ba, tana tsoron tayi abinda zaa ce tayi fitina a gidan Yayanta amma data baiwa Madinah amsa, ta so ta ce da ita “dadin abun ma mun san asalin balbela, kowa ya san SORONDINKI a Kano, nan ma cikin Badalar ne yar rainin wayo kawai hankaka maida gidan wani naka.

     Wannan da yar sarkin Kano ce watakila ko daga ido ba za ta rika yi tana kallon mutane da kima ba. 

    Shin me ta maida yaran cikin badala ne? Yan kauye ko? Za kuwa ta ga kauyanci ganin idonta, sai ta kilar da HAUWA, duk da haka ma Mama tana yawan gaya mata irin ci gaban da Hauwa ke samu a jamiah tun dawowarsu.

     Daga karshe kuma tana tafe a hanya don komawa hostel ta canza shawara, ta sa a ranta rashin mutuncin Madina a kan alakarta da Usman ba zai sa ta fasa son Usman ba, kuma ba zai sa ta barshi ba, don kam tana matukar sonshi. Gara ma ta rike abinta tayi ta gumawa Madina haushi. Ai Usman gaba yake da ita ba shine kanin ta ba da zata saka shi ko ta hana shi ba, bakin cikin ta daya yadda ta gama bata ta gun mahaifiyarsu Hajjah Ramlah.

    Ko awanni biyu Sumayya ba ta yi da komawa hostel ba, Ajrah ta sauke Dr. Sarham da maidakinsa, wato amaryarsa Hauwau a kofar flat dinsu. Watakila Sumayyah da ta san cewa da Hauwa ya taho da ba ta tafi ba. 

    Shi kuma bai gaya wa kowaccensu cewa tare zai zo da Hauwa ba. Ita Madinah bai samu wayarta ba ita kuma Sumayyah surprising dinta yaso yi.

    Usman ne ya yi mata waya cewa su hadu a jamiarsu don Madina ta masa iyaka da zuwa gidanta, shi ya sa ta bar gidan, da kuma maganganun data ji Madinah nayi da Hajjarsu a kanta sun tsoratata.

    Dr. Sarham ke danna kararrawar shiga kofar falon gidanshi, Hauwa na daga dan bayansa ta sha glass da shudiyar abaya, harde da hannuwanta biyu a kirji. 

    

    Dr. Madinah wadda a lokacin take shilla Waheedah cikin lilonta cikin murnar ta kori Sumayyah at the same time tana waya da Hajja Ramlah, korafin dai taci gaba da kai mata iri-iri kan kanwar mijinnata wadda ta tabbatar ba tun yau ba ba ta kaunar ta bude ido ta ganta tare da dan uwanta.

    Ta ce ma Hajja Ramlah,

    Ban taba gaya muku ba don bana son ki ce in dawo gida Hajjah, Sarham ya dade da kara aure, kuma sun baiwa yarinyar masauki a gidansu. 

    Hajjah ke shaida ce kan cewa raina ne kawai ban cire na bai wa Sarham da uwarsa da kannensa ba don so da kauna, duk wata kulawa da mace ke yi wa dangin mijinta babu irin wacce ban yi musu ba. Ta karasa cikin karyewar murya.

    Hajja Ramlah bata san sanda ta yi wani ashar mara dadin ji ba, lokacin da Madinah ta idasa gaya mata irin macen da Sarham ya aura da irin nakasarta.

    Idan dai ni na haife ki Madinah, to tattaro kayanki ki ajiye masa yarsa ki dawo gida, martabarki da ajinki bai yi wannan lalacewar ba. 

    Bari Daddy ya shigo in ma kin ki tahowa ni da kaina zan zo in fito da ke tunda Sarham ba shi ne autan maza ba.

    Madinah ta ce, Abin da na guda kenan da yasa tun farko na ki gaya muku Hajjah, Sarham ba zai taba sakina ba, don haka ina amfanin in tafi gida da dakon aurensa watarana in dawo?

     Besides na lura yanzu baya ta yarinyar, for as long as a year bai je inda ta ke ba, sai yanzu da ya tafi daurin auren kanwarsa ta farko. 

    Ta ci gaba da dannar mahaifiyarta ta roke ta kada ta daga wa Daddy hankali a kai saboda Sugar (diabet) dinsa yayi tsanani, taroketa tayi shiru kawai, za ta iya da rayuwa da Sarham a duk yadda ta same ta.

    

    Hajja Ramlah ta san cikin yaranta, Madina ce kadai mace amma Allah ya azurtata da hankali. Sau tari ita ce mai yi mata fadan tayi ba daidai ba in ta kuskure wa mahaifinta. Hajja Ramlah ta samu kanta da cewa,

     Ke dai ki ka kawo yaron nan ki ka ce kina so Madinah, kada ki tilasta kanki zama da shi in akwai wulakantarwa da tozarci, abu ne da daga ni har mahaifinki ba za mu lamunta ba, wato ya wulakanta ki ko ya kaskantaki ko ya hada matayinki da makauniya.

    Hajja kada ki damu, I can handle everything, I can take care myself, amma babu batun ‘yaji’ a policy dina. Yau in Sarham ya sake ni zan bar masa gidansa, amma ba zan taba yin yaji da aure a kaina ba.

    Karar kararrawar shigowa ta sa ta yi wa Hajja Ramlah sallama, ta dauki Waheedah da ta fara kuka a kan kafadarta, ta isa ga kofar bayan ta amsa da cewa, 

    Ina zuwa.

    

    Ko da ta bude ita ta san ko kowa bai gaya mata ba, wannan din da ya rike hannunta cikin nasa, na nufin HAUWA-KULU.

    To amma a yadda Surayyah ta fasalta mata ita ba a hakan ta ganta ba, wato irin yan tallan abincin Tashar cikin gari, talauci sama da kasa, yan babu cin yau babu na gobe, almajira, musaka.

     Wannan din da ke tsaye a gabanta wata ‘classy’ yarinya ce da idanu ne kawai ba ta da su, amma za ta goga da kowacce irin macen kasar Najeriya.

     Sakamakon cewa fuskarta fes, babu ko digon pimples, idanunta cikin gilashi mai duhu ainun don haka ba ta samu ganin kalar kwayar idanunta ba.

    

    Da farko Madinah gabanta faduwa ya yi, amma haka ta daure ta basu hanya. Wani irin makoko na yunkuro mata, ji ta yi kamar suna shigewa din, ta fita a guje kawai ta bar gidan. Muryar Baban Waheedah ta dawo da ita tunaninta, yana fadin, 

    Come on Waheedah.

    Ya mika hannu ya karbi yarinyar da ke ta mika masa hannu tana zillo daga jikin Madinah.

    Madinah ta ba shi hanya, cikin kauda ido, hannunsa daya rike da Waheedah, daya rike da hannun Hauwa suka shiga cikin falon.

    Sai da ya tabbatar Hauwa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, ya mike ya bi bayan Madinah wadda ta yi wucewarta daki ba tare da ta ce musu ko ci kan ku ba. ko ta nuna ta san tare yake da wata halitta, mutum din ma dan adam mai daraja. Wannan abu ya bakantawa Sarham ba da kadan ba.

    Tana shiga yana shiga, ya tura kofar. Da ta daga ido ta dube shi bai iya gasgata cewa kwayar idon Madinah ba ce, sabida yadda ta rine da bacin rai da wani zazzafan kishi mai barazanar fasa mata ido. 

    Kin kyauta kenan Madina? Ai ko ni ba ki yi min sannu da zuwa ba, kya yi wa Maijidda wadda ta zo bakon wuri, ta tadda ke a gidanki.

    Dakata don Allah Baban Waheedah!

     Ka gaya min za ka zo min da wannan yarinyar? 

    Kana tsammanin ni Madina zan iya zama gida daya da kishiya ne? Kishiyar ma irin wannan musakar?

    Sarham ya yi kokarin kama hannun Madina, ta yi maza ta ja da baya, 

    Dont dare touch me again, bayan ka gama tattaba makauniya.

    Maganar sai da ta yi amsa kuwwa a kunnen Hauwa sabida yadda ta ware makogaro ta fadeta.

    Sarham kuma ya kai wa Madinah wani wawan mari, sai dai kafin hannun nasa ya sauka a lafiyayyar fuskar Madinah tayi maza ta kare da hannunta, ta kuma yi saurin ja da baya kada ya illata mata fuska.

    Nashi idon har ya fi nata rinewa da bacin rai, ya ce, Munawwarah, ke ce kuwa? Yau ina hankalinki da tunaninki ya je ki ke ma wani dan Adam gorin halitta? 

    Are you not a medical personnel? 

    Ni kike dagawa murya kamar wani dan ki? Anya ke ce ko sauya ki aka yi kafin naje na dawo?

    Tsaki Madinah ta yi, ta juya ta bar masa dakin tana cewa,

     Aah, ba ni ba ce, ko kuma kawai kace daga turu na fito. Ka sa a ranka ba zan taba zama gida daya da wannan musakar ba, balle in hada shimfidar miji da ita. Ko ta fita yanzunnan ka kama mata wani gidan ko ni in fita in bar muku gidanku, amma tareda takardata don bazan yi yaji a dawo dani ba.

    Ta yi maza ta shige toilet ta saka key, ganin yadda maganganunta ke kaskanta shi, baa fuskarsa kadai ba har a jikinsa dake mazari kamar ana kada masa gangi.

    Ka fita a dakina Sarham, don Allah, saboda wallahi bakidaya ka koma min wani musaki….

    Kwafa Sarham ya yi ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya dauki Waheedah da ya ajiye a gado tana tsala kuka ba.

    Dakin Sumayyah ya nufa, sai ya tarar da dakin a kulle. Wato ita kuma ta tafi ba izninsa. Ya fiddo waya ya kira ta,

     kina ina ne dakinki a kulle?

    Wa? Ni? Bhaiya ai na tsufa a hostel, ba ni ba kara kwanan gidanka.

    Sarham ya kara hassala fiye da farko, ya ma fasa gaya mata cewa ya zo da Hauwa don bai ga amfani ba, ya ce, 

    In na kara cewa ki zo gidana Summy ki ce shege ne ni ba haihuwar Maisharia da Prof. ba. Na yafe miki zuwa gidana daga yau har gaban abada.

    Jikin Sumayyah ya yi sanyi, ta ce, Bhaiya

    Ya yi maza ya kashe wayar, jikinsa yana tsuma da bacin rai, ba tare da ya saurare ta ba, ya koma falo ya tadda Hauwa.

    A yadda ya bar Hauwa a haka ya same ta a zaune a kan kujera ita ma ta kumbura tayi fam, kiris ta ke jira ta fashe. Don bata taba jin cin mutunci akan lalurarta rabin wanda ta ji a bakin Madinah yau ba. Hakika makanta abu ce mai saka karfin ji!

    Ya yi kamar bai ga kumburin da ta ke yi din ba, ya dauki jakar kayanta ya kama hannunta ya ce, 

    Taso ki biyo ni mu je ki huta.

    Ta ja tunga a inda ta ke zaune ko motsawa ba ta yi ba. Ta kuma warce hannunta.

    Yaya Doctor ni gida zan koma!.

    Idanuwanta suka yi narai-narai cikin kwalla,  wadda ba ta idasa zubowa ba.

    Ya dube ta a matukar hassale itama, ya ce, 

    Ga hanya nan ki koma din, idan ba ku hadu ku ukun kun haukata ni ba, ba ku ci sunanku na mata tumakai ba!.

    Ya dauki jakarta ya nufi wani daki da ke rufe wanda ke kallon dakin Madinah, ta shirya dakin ne don bakinta yan gidansu na Sorondinki in sun zo aikin Hajji su kan shigo su kwana, shi kuma nan ya ga nan ya dace Hauwa ta zauna don girmansa daya da dakin Madina.

    Dakin a gyare yake tsaf babu abinda babu na bukata, ga sabon bayi (toilet) makale a cikinsa. Ya ajiye jakar Hauwa ya fito.

     Daidai fitowarsa ya ga Madinah tana kwashe warmers din abincin da ta girka daga kan dining table. Ta kwashe komai ta juye a leda ta saka a freezer.

    Tana kallon Hauwa a zaune tana tsane ido da gefen mayafin abayarta, ta wutsiyar ido ta harare ta, bayan ta gama kwashe komai ta shige dakinta ta kulle ta ciki.

    Sarham ya dawo ya zauna daf da Hauwa, ya rasa ta ina ma zai bullo musu su duka. Hauwa jin zamansa a kusa da ita sai ta kara sautin shesshekar kukanta, wai ita kawai ya maida ita wurin Mama bazata kwana a gidan ba.

    Ga gajiya, ga yunwa, ga bacin rai da suka tarun masa don haka bai kula ta ba. Ya fiddo waya ya kira Abbansa yana maida fushinsa, ya gaya masa sun sauka lafiya, haka Mama ma. Bai ja hirar da tsayi ba kuma ya kama hannun Hauwa ya soma janta ta karfi zuwa dakin da ya zabar mata.

    

    A gefen gadon dakin ya zaunar da ita, This is your room, in kin ga dama kuma ki kama hanyar Kano a kafa daidai ne. zan je in yi sallah, muje ga toilet in nuna miki yanda yake ki gane komai, ko kina son shiga.

    Wannan karon ta bashi amsa cikin share ido jin yace su je kuma bai kama hannunta ba.

    Idan na fadi fa, tunda ban san hanyar koina a gidan ba?

    Tausayi ne mai tsanani ya kama shi, kawai sai Hauwa taji Sarham ya dauketa yana tafiya da ita zuwa toilet din a hannayensa.

    Kunya taji soai ta hau sunne kanta a kirjinsa. Daka barni na tafi da kafata don in gane hanyar koina.

    

    Dr. Sarham bai yarda ya direta ba sai a toilet din, ya nuna mata yadda za ta yi amfani da komai na bandakin, ta hanyar dora hannunta akan komai yana bayani. A karshe ya nuna mata (shower) ta wanka da yadda zata dinga kunnawa da rage zafin ruwan daga famfon kada ya kona ta, ya nuna mata kunna (water heater) wadda yace in ta kunna ba sai ta kashe ba don tana kashe kanta automatically. 

    Ita ba ta san dalilin yawan taba hannayenta da yake yi ba wai yana nuna mata abubuwa, nan kuwa ba ya gajiya da touching dinsu ne sabida taushin fatar hannunta.

    Na gane, ka je zan yi wanka!.

    Kin fasa komawa gun Maman? Ya tambaya cikin gatse, yana janyota yana makalewa.

    Hauwa ta tsuke fuska da baki, ta ce, Ya danganta da sunan da aka kara kirana da shi a gidan nan. Ni duk duniya ba wanda ya taba ce min musaka. In ma musakar ce shin miskini ba mutum bane? Ni dai na san;

    

     Inna Akramakum Indallahi Atqakum.

    

    Ta hakan ne ya gane cewa ta ji me Madina ta fada a kanta. Ita makanta da ma sanya karfin ji ne da ita. Ya kuma san ba abinda ta tsana a duniya irin sunan da Madinah ta kira ta da shi, yau mafi muni, don haka ya sassauta murya ya sake makalkaleta a jikinsa yana shafa gadon bayanta, yace.

    Ki yi hakuri, ki kara yin hakuri, ki kuma koyi karbar ‘labelling’ na sunan lalurarki, hakan ne zai sa ki zauna lafiya ko da wani ya fada ki daina damuwa irin haka da shiga bacin rai, ba lallai ne kowa da niyyar gorin ido yake ce miki makauniya ba, wani kuma bada isgilanci bane, aah suna ne da Malam Bahaushe ke kiran duk wani mai lalurar gani dashi don banbance lalurarsa.

     Ki koyi kauda kai a kan hakan muddin kina so ki rabu da bacin rai.

    Ya kara sassauta murya, ya ce,

    Ki gama wankan kiyi sallah mu je tare mu sayo abinci.

    Saboda ya ga sanda matar gidan ta fito ta kwashe nata bakidaya, (amma bai fadi hakan ga Hauwa ba ya barwa ransa).

    

    Wannan ya sa Hauwa ta dan saki ranta, jin cewa  za su fita su mike kafafunsu. Don  dama sai mutsuka suke mata na zaman jirgi.

    To ka fita zan yi wanka

    Allah ya yarje min inga komai na jikin matata Hauwa

    Ya fada yana sirka mata ruwan wanka.

    Saida ta hada da rokon shi Allah Annabi ya bata waje sannan ya fita ya rufo mata kofar.

    Ta yi wankanta da kyau da ruwa mai zafi domin warware gajiyar da zaman jirgi ya haddasa mata, tana wanka tana tunanin yadda zamanta da Maman Waheedah dinnan mara kirki zai kasance a gidan, wadda a zahiri ba ta marabci zuwanta ba, kuma ba ta shirya zama tare da ita ba, kafin maigidan ya kawo ta meyasa bai gaya mata matarsa bata da kirki ba, kuma bai nemi yardarta ba ya daukota ya kawo mata gida?

    Wannan ya nuna shi Sarham mutum ne mai yin abin da ya sa kansa a gidansa ba tare da shawara da mata ba. Ita dai ta san za ta yi ‘tolerating’ komai, za ta yi wa Madinah biyayya kamar yadda Mama da Inna suka nusarsheta, abu daya ne ba za ta lamunta ba, Madinah ta keta rigar mutuncinta ko ta ci gaba da kiranta da duk sunayen wulakancin da ta ga dama

    Wata doguwar rigar atamfa Hauwa ta sanya Chiganvy da aka yi wa wani ubansun dinki wanda ya fiddo kyakkyawar surarta sosai ba tare da ta san yadda kayan suka karbi jikinta ba, ta dauki mayafin da Mardiyyah ta manna a cikinsu ta yafa.

     Tana cikin fesa turare Dr. Sarham ya shigo sanye da farar sabuwar jallabiya mai matukar tsada, sai tashin nasa kamshin na musamman yake yi.

    Oya lets go, kin gama ai ko?

    Idonsa ya kai ga dressing dinta ya kankance ido, Me-ji! Cire wadannan kayan maza-maza, kin manta a Saudi-Arabia ki ke? Ko ba a can ba ne in aka ce ki fita da wannan dinkin jikinki na juyawa  a cikinsa sai ki fita don hankali ya wadace ki ko?

    Hauwa ta hau shafa dinkin jikin nata wai ta ji me ye  laifinsa.

    Ka yi hakuri, ka san dai ba na gani.

    Umh! Da wani ne ya fada da yanzu cibi ya zama kari, canza su maza-maza ina jiranki.

    Ya ci gaba da tsayuwa kuma bai fita ba.

    Hauwa ta rausayar da kai gefe, To a gabanka zan canza ne Yaya Sarham?

    Ya yi  wani dan murmushi cikin rashin jin dadi ya juya ya fita yana cewa, 

    Na ba ki wuri,  Mrs., matsayina na Yaya har yanzu yana nan bai canza ba kenan ko?

    Bai kuma tsaya sauraron amsarta ba ya juya zai fita tayi maza ta riko shi.

    Za ta so kwarai ta ga fuskar likita Sarham a yau, ta tabbata wanka ya dauka ko daga niimtaccen kamshin da yake zubawa a dakin. 

    Hauwa ta yi ajiyar zuciya tana ji a jikinta lalurar makantarta ta har abada ce ba ta da magani, don ba ta taba ji ko ganin makahon da idonsa ya bude ba. 

    Don haka fatanta na ganin fuskar likita Sarham zai ci gaba da kasancewa fata (hope) irin wanda har dan Adam ya koma ga Ubangijinsa bai samu cikarsa ba (actualizing of dream) dinsa.

    Ta hau lalubar fuskar Dr. Sarham ta saka fuskar shi a tsakanin tafukanta biyu, tana shafa tattausan sajen gefe da gefen fuskar tasa, ta ce You are my HUSBAND, not a brother, and my everlasting dream is to see you with my naked eyes.

    Sarham yayi maza ya hade bakin su wuri guda, yana sakar mata mata wata irin zazzafar sumba mai tsayi da zurfi kusufa-kusufa lungu lungu sako sako a cikin bakinta.

    Hauwa sai ajiyar zuciya take yi, kwalla ta taru a idonta, ta yi maza ta rike shi gamgam itama, nan ya idasa rikitata ta hanyar kai bakin shi saman kirjinta, daga wannan lokacin suka lula a wata duniyar maaurata mai ban mamaki da shiga rai. Hauwa na neman shidewa Sarham ya dauketa a hannunsa zuwa gadon dakin, har da wata irin sheshshekar fita hayyaci yake yi a jikin Hauwa kai kace bai taba rike mace ba, yana kiranta da sunayenta kala-kala. Wadanda take so (Hauwau-Jiddah-Maijiddah) da wadanda bata so (Kuluwa ta, Kulun-Majadun dina, ni ina ganin ki kuma ina son ki a hakan, ko baki ganni ba)”.

    

    Tunda Madinah ta kulle kanta a daki ba ta kara ko lekowa falo ba, sai kukan Waheedah ka ke ji yana tashi a gidan, wadda da alama ba ta samu lallashin uwa ba. Wannan kukan na Waheeda har cikin kwakwalwarsa yake tabawa, kukan Waheedah shi ya ceci Hauwa a hannun Dr. Sarham yau kuma, ba don haka ba da tuni ta amsa sunan sauran mata yan uwanta.

    Taimaka mata yayi ta canza kayan zuwa bakar abaya da mayafinta. Ya san da gayya ta kyale Waheeda take jiniya don haka ya kama hannun Hauwa suka fito ya rufe dakin suka bar gidan.

    Madinah na jin rufe kofarsa ta leka waje ta tagar dakinta. Nan ta hange su suna takawa a kasa gwanin ban shaawa, ya rike hannun Hauwa cikin nasa. Ba ta san dai ina za su je ba, amma jikinta ya ba ta ‘mudam (restaurant) da ke cikin estate din nasu za su je, wato wajen cin abincin likitocin Saudi-German.

    Wani abu ne da za ta iya cewa tunda suka yi aure rabon Sarham da shi wato cin abinci a Mudam, don ko ba ta dafa abinci ba zai wa cikinsa yan dabaru ne ya zauna lafiya. Sai ta shiga tambayar kanta shin abincin da ta dafa ta kwashe don kar su ci ta kyauta? Lallai kishi mai maida babba yarinya mai juya hankalin mai hankali. Kyabe baki ta yi, ta ce, 

    Ba hakkina ne ciyar da su ba daga shi har matar tasa.

     Shi da ya ga zai iya wahala da makauniya sai ya fara tunda wuri, kafin wankin hula ya kai shi dare don in yana zaton ni zan kula masa da mata ya yaudari kansa.

    

    Suna tafe cikin tsanaki a gefen titi, Sarham na tausar zuciyarta a kan kalaman Madinah.

    Ya ce, Ki daina damuwa don wani ya ce miki makauniya, ko mara gani. Makaho bai isa ya hana alumma kiransa makaho ba, haka kurma bai isa ya hana alumma kiransa kurma ba. Thats the same with gurgun mutum (physically challanged) bai isa ya hana a kira shi gurgu ba, but accept it, like it, appreciate it. Accept your disability, enjoy it sai ta zame miki unique identification ba tare da ranki ya baci a banza ba. 

    Ni idon nan da ana musanye da mun yi na huta da wannan bacin ran na GORIN IDO tunda ban isa hana mutane kiran Hauwa-Jeddah makauniya ba.

    Hauwa, ta daga manyan idanunnan farare kal, tayi harr! Dasu a kan Sarham da wani irin murmushin jin dadi a fuskarta. Sarham ya shafa kansa zuwa keyarsa jin wani ignition na fizgarsa, yace kada ki kashe ni da idanunnan Hauwa, I loved them, ina son daren yau in samu Safiyyah ko Maimunatu mai irin su, daga daren farko mai albarka.

    Hauwa ta kai tafukanta ta rufe fuska cikin jin kunya da karuwar Son Sarham mai tsanani a zuciyarta.

     Daidai lokacin da suka isa mudam din suka shiga. Akwai tsirarun mutane, amma ba su da yawa, ya samar musu waje can nesa da kowa ya zaunar da ita, sannan ya je ya yo musu order din zazzafar kazar nan ta (Kentucky Fried Chicken) da aka fi sani da KFC da Chips, aka hado da zazzafan coffee mara sugar aka kawo musu.

    Yau Hauwa sai ta samu kanta da jin kunyar cin abinci a gaban likita Sarham, ba su taba cin abinci tare ba sai yau. Shi kuwa bai lura wai kunya ta ke ji ba ya dinga dauko tsokar kazar da chicken nugget yana saka mata a baki ko ya tula mata tsokar a gabanta.

    Ki ci ki koshi fa, kada ki ji yunwa cikin dare.

    Ta soma ci a yangance ya ce, Maijiddah ni saurayinki ne ne da ki ke min wannan yangar taunar yen-yen- alhalin na san yunwa ki ke ji?

    Hauwa ta rufe ido tana yar dariya a haka ya saka mata nugget guda a baki ya cika mata bakin taf, ta hau dariya tana tauna tana rufe ido.

    Da suka gama suka tako zuwa gida kasancewar ba tazara sosai tsakanin flat dinsu da mudam din.

    Tunda suka dawo a falo ya zaunar da Hauwa ya fita ya rufe koina na gidan. Madinah dama ta garkame dakinta tuni amma tana jin dawowarsu kuma lokacin ta gaji da kukan Waheedah itama ta bata nono wanda hakan yasa Waheedah barci.

    Suna falo tare har karfe tara na dare  yana kallon labaran Aljazeerah kafin yunwa ta koro Madinah daga daki zuwa kitchen. 

    Ta wuce su, ko kallo ba su ishe ta ba, shi ma ya kalle ta da wutsiyar ido ya kauda kai, yana kokarin kashe talabijin ya ce da Hauwa, Mu je mu kwanta haka, don gobe insha Allah zan fita da wuri na shiga asibiti.

    

    Ya kama hannunta zuwa dakinta duk a kan idon Madinah. Wani zazzafan hawaye ya feso wa Madinah. Suka shige ya rufo kofar harda key. A can baya idan wani ya gaya mata cewa Sarham zai iya kama hannun wata mace a duniya bayan ita, za ta karya ta ne da babbar murya. Yau dai ga shi tana ganin halin maza, ganin idanunta. Shin me ta yiswa Sarham data cancanci haka? Tabbas duk wadda ta ce namiji uba ne ko abin yarda da baiwa amana akan SOYAYYAH ita Madinah za ta kwana tana gaya mata itace marainiyar da ta fi kowa maraici. 

    Sanin cewa hankalin Madina yana kansu sai bai jima sosai a dakin Hauwa ba ya fito ya jawo mata kofar ya ce ina zuwa.

    Ya tadda Madina a kitchen ta hada custard da madara a kofi mug ta dauka za ta wuce daki, sai ya dakata a bakin kofar kitchen din, wato ya tare mata hanyar ficewa.

     Ya ce da ita (authoritatively), Munauwarah, abincin da ki ka kwashe daga dining wa zai ci? Ina ki ka kai shi, ko zubarwa ki ka yi?

    Madinah ta yi banza da shi.

    Ya ce, Ina soki sani ni ba mai kudi ba ne da zan zubar da abinci a shara wai don kada wani ya ci, sannan bana son almubazzaranci, kin dafa abinci amma sai fita na yi na sa kudi na saya, mene ne hujjarki ta yin hakan?

     A da dai ban sanki da wadannan baudaddun halayen ba, ko kusa wannan ba Munawwarar da na sani ba ce ba Giwar Sarham..bace.

    Kamar jira ta ke ya fadi hakan, hawayen da ta ke ta tattali tun dazu da ta fito ta ganshi yana kula da makauniyar matarsa, suka samu yancin kansu yanzu.

    Ta ce, Kada ka kara ce min wata giwarka daga yau. Ita giwar miji ita ce matar da ta ishe shi ta kowanne bangare, ta kuma ke satisfying dukkan bukatunsa, har ta hana shi hango kyalkyalin wasu matan.

     Wato wadda ta dusar da hasken sauran mata a idanunsa, amma ni fa? 

    Nawa mijin ban ishe shi ba, karewar ban ishe shi ba musaka ya dauko min ya zama bawanta, ya daidaita matsayina da nata. 

    Na tsane ka Sarham. Wallahi na tsane ka, ka tafi daga idona kada in yi furucin da Allah zai yi fushi da ni, wato in ce ka sake ni in koma gidanmu ya fi min alkhairi a kan ganin fuskarka yanzu.

    Murmushi ya yi ciki-ciki, ya dauki kofin glass ya zuba ruwan gora ya sha ya juya ya bar mata kitchen din. Wannan shirun da ya yi mata ya fi komai kara fusatata.

    Tun yana tsammanin abin na Madina mai karewa ne amma har zuwa wayewar garin ranar da shi ya tashi cikin farin ciki mara misaltuwa, na karbar ragamar rayuwar HAUWA-KULU. Hauwa kuma aka bi sahun sauran mata ya soma jinyar barnar da yayi a matsayin sa na likita bai wahalar da ita fiyeda kima ba, bai kara ganin kyallin Madinah ba.

     Ta kulle kanta da yarta a dakinta, ta daina fitowa kwata-kwata, shi kuma tunanin cewa yau din girkin Hauwa ne a bisa tsari na musulunci daga nan har kwanaki bakwai masu zuwa ya sa bai kara shiga dakin Madinah ba har washegari duk da ya san ta kulle kanta amma yayi niyyar duba lafiyarsu.

    Da safe yana so ya tafi asibiti, amma yana tunanin yadda Hauwa za ta yi coping cikin gidan, sababbin halayen da Madinah ta tsuro da su na yin biris da alamarinsa  balle yayi tunanin za ta taimaki Hauwa ya daga masa hankali, da ma ya yi niyyar fita tare da ita yau ya kai ta top ten ta yi sayayyar abubuwan da ta ke da bukata, duk da yasan Mama ba abinda ba ta hado ta da shi na amfanin ta ba. 

    Gyaran muryarsa a kofar dakinta ya sa Hauwa da ke idar da sallar walha juyowa da hanzari don dama a kage ta ke da ganin nasa, tunda ya tafi dakinsa don ya shiryo take jin yunwa. 

    Ya karaso har inda take ya dagata daga kan dardumar suka karasa gefen gadon, ya zaunar da ita bisa cinyoyinsa yana wani irin sunsuna ta, yace cikin taushin murya,

     Maijidda ya ki ka tashi, ya kwanan bakunta? Hope babu pain din sosai yanzu?

    Dan murmushi ta yi. Tana sunne kanta a kirjinsa.

    Ya ce, naga kamar ba ki yi sallah daidai ba, nan din ba nan ne gabas ba, let me adjust.

    Ya gyara mata inda za ta fuskanta a dakin yayin sallah, ya zauna nan makale da ita ya kasa tafiya asibiti, ya ce, Ba ni labarin yadda ki ka kwana a gidanki? How do you feel the night? I know its hurting a little, amma da kinsan rahma da gafarar dana roka miki daren jiya bakidayansa da kin san cewa kin rabauta da albarkar aure.

     Aljannarki in dai har tana kasan dugadugaina, ni Sarham na daga miki ki shiga cikin amincewa ta udkhuluha bissalam.

    Hauwa dai murmushi take tayi ba ta amsa ba.

    To zan tafi asibiti, ko za ki bi ni mu je in fara kai ki ki sayi abin da ki ke so kafin na wuce?

    A nan ne ta yi magana, ta ce, 

    Ba ni da bukatar komai, Mama ta hado ni da komai na bukatata, ka je lafiya ka dawo lafiya Yaya Doctorau! Baban Waheedah.

    Yana jiyo bude kofar Madinah ta fito cikin shiri dauke da Waheedah, sai ya ajiye Hauwa a gefensa ya tashi ya fita, yana cewa cikin ransa, zai yi maganin Madinah.

    Yana fitowa daga dakin hauwa suka hada ido shida ita, Madinah ta hadiye wani bakin ciki da ya taso mata, ta juyar da kai gefe tace.

     Zan fita neman aiki.

    Har ya kai bakin kofar nasa dakin sai ya dakata, kafin ya juyo ya yi mata wani irin kallo na gargadi. Madinah ta kauda kai ta ce,

     Ah toh, dole in fara aiki yanzu, don ba zan zauna jire maka musakar da ka ajiye a gida ba, ko in zama yar jagora. 

    Allah ya tsare ni aikin wahalar da babu lada wai aikin kishiya. 

    Wallahi da ma don kai da yarka ne  bana aiki, don in samu lokacin kula da gidana da iyalina, a yanzu na gane ba abin da mace za ta yi ta mallaki namiji da sunan kyautatawa da kiyaye hakkokinsa don hana shi hango wata, sai dai kawai ta bata wa kanta lokaci.

    Ya gyada kai yana kallonta da budadden ido, Shi ya sa yanzu ki ka zabi fita gantali, tunda ba ki mallake ni din ba kuma don na yi aure cika sunnar Manzo SAW? Don dai na san ba za ki ce neman na kai ne ya saka ki yin aikin ba.

    Ai kamar ba ka ji ba Dr. Sarham, in zauna yi maka gadin mata ne ba zan yi ba, sabida ni dai duk danginmu babu makaho, ban iya yar jagorar zuwa bandaki da kitchen ba.

    Sarham ya shige dakinsa da sauri gudun kada ya yi loosing temper ya kai mata mari again irin jiya, yana cewa, 

    I can relate. Lalura dai ba ta wuce kan kowa ba. Kuma Hauwa ba ta dora wa kanta ba, ni din dai ni na jawo mata.

    Haka ko da ya je office din kasa zama yayi ya jima yadda ya saba saboda tunanin halin da Hauwa ke ciki. Don haka karfe biyun rana na bugawa wato lokacin cin lunch dinsa ya baro Saudi-German zuwa Estate dinsu.

     Yana hanya Sumayya ta kira shi, yana ganin kiran nata ya ki dagawa, ya shiga gida kenan ya yi parking. Sumayya ta sake kira, tsaki ya yi ya daga kiran nata, bai ce komai ba, Sumayya sai ta sa kuka.

    

    Da kyar ta soma  magana jin Yayan bai katse ta ba, bai kuma tambayi dalilin kukan nata ba, saida ta gaji don kanta tace.

     Ni dama na san Aunty Madinah ce ajalin zumuncinmu, Bhaiya, na san dama sai ta raba mu, tunda har yau ka ki daga kirana da gangan, kuma ka ce kada in kara zuwa gidanka har abada.

    Sarham takaici goma da ashirin ya ishe shi.

    Sumayya, wace irin yarinya ce ne ke fitinanniya mai kishi da matar Yayanta?

    Sumayya ta zaro ido, kamar Sarham yana kallonta, ya ce, Yes, na gaji da korafinki a kan Madinah, na gaji da gaya miki ba ta isa ta sa ni ba, ba ta isa ta hana zumuncina da kowa nawa ba.

     Kada ki koma daukan alhakinta, na yi karin auren ma don dai ku yarda Madinah ba ta fi karfina ba bata mallakeni irin yadda kuke zato ba shima ban tsira ba. 

    To yau na dauko Hauwa na hada da Madinah, za ku daina yi min kallon sakarai a son matarsa ko?

     Ba tun yau ba na gane ke irin kannen mijin nan ne fitinannu marasa adalci, yadda ki ka dauki Madinah ita ko kusa ba haka ta dauke ki ba.

     Ki bi rayuwa a sannu Sumayyah, ki daina saka wa kowanne dan Adam kahon zuka, babu mai bai wa wani numfashi ke da ita, kuma ba ki san ranar da Madinah za ta iya yi miki a rayuwa ba.

     Ina yi  miki nasihar nan ne a matsayina na dan uwanki ba a matsayin mijin Madina ba. 

    Change your behaviour Sumayyah da duk kannen miji masu irin halinki, don kuma mata ne, gidan aure za ku je, kada kaddara ta kai ku gidan masu irin halinku abubuwa su cabalbale muku. Ki sa a ranki the more ki ka bar matar Yayanki ta zauna lafiya da shi, the more kema za ki samu zaman lafiya da naki yan uwan mijin, tarihi maimaita kansa yake Sumayyah.

    Sumayyah na kuka ta ce, Na daina, wallahi Bhaiya na daina kinta babu dalili, ni na ga ishara Bhaiya don yanzu ga shi tana ramawa, farin cikina duka yana hannunta tunda ta yi rantsuwa ko ni na saura ya mace a duniya Usman ba zai aure ni ba. 

    Bhaiya mu kuma, nida Usman, muna matukar son juna.

    

    Sarham ya daskare da mamaki, kafin ya ce, Are you sure kin daina negative behaviour toward her?

    Sumayyah ta yi rantsuwa kan cewa ta daina, ya roki Madina ta yi hakuri ta barta da dan uwanta, she promised to become a changed person. Daga yau ba ruwanta da sabgar matansa. And she will treat both his wives  equally (tana nufin Madinah da Hauwa) duk zata daukesu abu guda.

    Murmushin samun kwanciyar hankali ta fannin Sumayyah Sarham ya yi, ya ce,

     Thats my sister, kada ki damu da Madinah idan Usman mijinki ne Allah zai baki, idan kuma ba mijinki bane Allah bai rubuta ba, amma ki bar mata dan uwanta in ta dage bata so Sumayyah babu abinda yake dole a rayuwa, kuma bazaki rasa miji ba in sha Allahu har wanda yafi Usman komai. Ni banason aikin zubar da kima kinji?

    Ki hado kayanki ki dawo ki zauna tare da mu cikin aminci in fara ganin canji daga yanzu, ga Maijidda na kawo.

    Wani dan ihu Summy ta saki na murna da farin cikin isowar Hauwa birnin Jeddah.

    Da ya dawo gidan yayi saar ganin Madinah na gida ba ta je ko ina ba, don ga shi nan yana jiyo sautin talabijin daga dakinta, kuma ba ta rufe dakin ba, don haka tunda ya shiga dakin Hauwa ba ta kara jin duriyarshi ba, watakila ya manta cewa ko abinci ba su bata ba a gidan.

    Ya shiga dakin Madinah da sallama, Waheedah ta taho da saurinta zuwa gare shi ya sure ta ya dauka.. ya samu Madinah  na cin abinci ta yi girkinta na gani na fada iya cikinta. 

    Ransa ya kara baci sosai, amma ya hadiye fushinsa ya bi ta da lalama.

    Ina fatan kin bai wa Maijidda nata?

    Ta ciko cokali mai yatsu (fork)da soyayyen dankali ta kai bakinta ta cika bakin taf, ta tauna a yangace ta hadiye sannan ta ce da shi,

     Da ma hakkina ne ciyar da matarka? Gaya min inda addini ya ce ciyar da Hauwa hakkin Madinah ne, daga kai har matarka ba kwa gabana wallahi, don ni in na raina kasuwa ko sautu bana bayarwa.

    Ba abinda ya hada ni da matarka Hauwa ta ke ko Kuluwa? Face addinin musulunci, kowa ya iya allonsa a gidan nan ya wanke, tunda dukkanninmu muna kwana da miji daya ban ga dalilin da zan zama kukunta ko yar jagorarta ba.

    Kai wallahi Baban Waheedah idan ka nemi takura min a kan matarka, ko ka ce lallai sai ka hada sabgata da tata, to kuwa zan nemi wani apartment din in yi parking acan ni da Waheedah, in ya so in barka da yar makauniyarka ku shana.

    Ta soma kuka tana ci gaba da fadin, Sarham! Ka gama wulakanta ni a duniya. Ka ci amanar yarda da soyayyar gaskiya da na baka.

    Jiki babu kwari Sarham ya zauna a gefen Madinah, da muryar da ya san yana sace zuciyarta a lokacin samartaka yau ma yake yi wa Madina magana cikin salo na mijin da yasan kan matarsa.

    Ki yi hakuri kin ji ko Munauwarahta. Abin bai kai da ki yi parking ki bar mana gida ba. Tunda har ki ka yarda za ki ci gaba da zama da iyalinki baki barni ba, duk da irin sabawar da na yi miki, wannan kadai ya sa na jinjina miki. 

    Sannan na kara martaba ki da na dawo na tarar ba ki yi yaji ba a wancan karon. 

    Sai yanzu don Hauwa ta zo? Kada ki manta ita ma aurenta nake kamar yadda nake aurenki, in kika bar mana gidan ai ba za mu ji dadin gidan ba balle mu shana. 

    Za mu kasance cikin damuwa ne da kewarki, kuma duniya da makwabta su zage ni cewa, don na auri Hauwa na raba gida da Madinah ta.

    Amma ina so ki sani, ni ne uwar Hauwa, ni ne kuma ubanta a kasar nan da ba ta da kowa. Haka ni ne guardian dinta, ko da ace tare take gari daya kuma kasa daya da iyayenta ni ne majibincin lamarinta. Don haka duk wani abu da zai cuta mata ko ya taba mutuncinta agidan nan wai don wannan lalura da Allah Subhana ya dora mata dalilina, kamar yadda kike yawan gorantawa kamar ba mai ilmin addini ba Madinah ba zan lamunce shi ba. 

    Son ki da kowa yake fadin ya yi min yawa, bai yi yawan da zai sa in kasa yin abinda ya kamata ba. Amma Madinah ko ba soyayyah yar usuli tsakanina da ke a matsayinki na matata uwargidana, sannan my first love, wallahi a kan wata mace daban da na kara aure ba zan taba wulakanta ki ba.

     Balle kuma ga aure, ga Waheedah a tsakani, uwa-uba soyayyar nan da nake miki tun tali-tali ba ta canza komai ba, kullum karuwa ta ke, sabuwa take kara komawa Madinah.

    Ni kam kin fi gaban wulakanci da tozarci da ki ke kira min a idona, haka Hauwa, she have a special place in my heart, ina son gaya miki yau ina son Hauwa ne yadda nake son ki, ba kuma saboda mahaifiyarta da wasu dalilan da nake ta fada a baya ba aboda wauta da ajizanci, na dade da janye dalilaina. 

    A yau ina fada ne da babbar murya ina son tane kasancewarta matata kamar ke. Sauran alamarin na kuma bar wa raina. 

    Don haka it is up to you now, duk hukuncin da ki ka yankewa aurenmu zan karbe shi Madinah, wanda ki ka ga shine daidai, ni dai na gaya miki iyakar gaskiyata ina sonki, ina kuma son zama da Hauwa har karshen rayuwata, ba zan taba ce miki bana son Hauwa ba, wai don ki daina sababbin halayen da kika tsuro dasu, ko ki daina cewa kin daina hada jiki dani wai saboda na auri Hauwa bata gani waye-waye, umh, Madinah akwai bukatar komawa islamiyya anan, bokon naki ya rinjayi addini.

    Kisa a ranki daga yau kowacce cikinku da matsayinta a gurina wanda babu na wacce zai rinjaye ni in yiwa daya abin da bai kamata ba, ko in rabu da daya saboda daya. Muddin ina cikin hankali na.

    Don haka in kin ga barin gidan shi ne mafitarki babu damuwa, ni bana son ganinki cikin wannan halin da wadannan sababbin halayen da ki ka aro ki ka yafa saboda Hauwau. 

    Don haka  duk abin da kika ga shine daidai har hana ta abinci din da rashin samar da muamalar musulunci a tsakaninku ki ci gaba Madinah ba kabarinmu daya ba.

    Yarinyar nan ko da ta ke makauniyar da ki ke ta goranta mata, tofa ba ta taba ganina ba, sannan ba ita ta ganni ta ce tana sona ba, haka ba iyayenta ne suka ba ni sadakarta wai don ta makance ba. 

    Ni na ce na gani ina so a bani, na aureta cikin mutunci kamar yadda na aure ki. Dalilin da nake ta fada cewa, shi ya sa na aure ta ni ban sani ba, ashe zai iya zama SO. Tunda baka taba auren macen da ba ka so”.

     Yayi shiru yana observing tasirin maganganunsa a tare da ita, da gaske maganganunsa na dukanta yadda baya zato. Bai damu da yadda fuskarta ta canza tayi jazir ba ya cigaba da maganarsa.

    Na gaji da cewa da ki ke kina kyamar hada jiki da ni wai saboda na auri Hauwau, shin makaho ba mutum bane, ko shi ba shi da tsarkin addinin musulunci a tare dashi? Madinah ina addininki ne? Ina imaninki? Ina compassion dinki na likitancin ido? Anya Madinah ke ce? Anya GIWAta ce wannan ta koma MONSTER haka?

    Yanzu dai zabin yana hannunki, na ci gaba da zama da mu ko aah, tunda dai na gaya miki iyakar gaskiyar da ke zuciyata Madinah, da kuma abin da zan iya dauka da wanda ba zan iya dauka daga gare ki ba. Hauwa zama daram, daga nan har ranar da muka daina numfashi.

    Sarham ya mike ya bar dakin ya bar Madinah ta hada tagumi. Sai tsiyayar gumi take yi. Dakinsa ya koma ya yi wanka ya sanya riga da wando marassa nauyi ya shiga dakin Hauwa sai ya samu barci yayi awon gaba da ita ya kuma san yunwa ce. Wuyanta ya lankwashe a kan filo, gyara mata kwanciyar yayi ya fito zuwa kitchen.

     Tunanin me zai dafa ma Hauwa mai sauki yake yi, don dole ya sanya shiga kitchen da kansa cikin schedules dinsa na yanzu. Ba zai dogara da taimakon kowa akan kula da Hauwa ba, tunda shi ya ce da iyayenta da nasa zai iya. 

    Ko da kuwa Sumayya ce ba zai kawo ta gidan ta zauna wai don ta kula masa da mata ba, sai dai ta zauna don radin kanta. Yayiwa Mama alkawarin shi da kansa zai kula da ita, kuma zai fara daga yanzu.

    

    Madinah dai na jin motsi a kitchen ba ta san waye ba, don haka ta fito don ganin waye a kitchen dinta kada ayi mata barna tunda ta san dai amaryar ba gani take ba.

    Sarham ta gani ya yi kace-kace yana aikin girki. Yana hada zufa na rashin sabo. Ko iblis ce ita, dole ta ji ba dadi a ranta, zuciyarta kuma ta kara gasgata abubuwan da ya fada mata na matsayin da shi Sarham ya baiwa Hauwa-Kulu a rayuwarsa.

    Yana kallonta ta zo kofar kitchen din ta koma cikin sauri, ga jin kishin mijinta na dafawa kishiyarta abinci ga guilty conscience daya hanata sakat, na cewa bata kyautawa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, a tsakar dakinta, ta yaya ita za ta dinga dafawa miji abinci? Shi kuma ya zage kwanji yasa ‘apron’ ya dafawa kishiyarta? 

    Kuka wiwi Madina ta soma, abu goma da ashirin ya damu Dr. Madinah Sorondinki, a karshe ta yanke wa ranta fita sabgar Sarham da matarshi Hauwa-Kulu take ko Kululu! Gara ta saka su a gefe kafin su manna mata ciwon hauka. 

    Don cikin abubuwan da ya lissafa bakidaya wato abubuwanda ya bata zabi ciki har dana zama da shi ko aah? Ko yin muamala mai kyau da matarsa Hauwau, ko ta dinga dafa abinci tana bata ita tana kwana da miji, ko ta zauna da matarsa cikin aminci, babu wanda za ta iya aikatawa a cikinsu gabadaya.

     Don haka ta yanke shawarar yin abinda take ganin ya fiye mata aala, wato komawa aikin asibiti, in yaso ta dauke ido daga kansu ta bar musu filin gidan ya cinye matarsa Hauwa-Kulu makauniya Kulu don soyayya.

     Amma ita kam ta gama hada jiki da Sarham! Don zuciyarta ba za ta jure sharing miji da makauniya ba. Sannan ba za ta zabi zuwa gida ta yi rayuwar zawarci da yi masa rainon Waheedah a gidan iyayenta saboda kishiya ba.

    A take ta dauki waya ta buga zuwa Dr. Siddiqah Hospital Jeddah. Zuciyarta a matukar kuntace. Hakika kishin mijin da kake matukar so abu ne mai matukar ciwo da sai wanda aka yiwa ne kawai zai iya bada labari. Amma abu daya zamu tuna mu kwantar da hankulanmu cewa auren mazajenmu sunnar Annabi ne, umarnin Ubangiji ne, na su aura daga abinda yayi musu dadi daga daya-daya ko biyu-biyu ko uku-uku har hur-hudu, don kare kansu daga dattin zina. 

    Abinda ya kamata Madinah da sauran mata irinta mu duba kenan, mu sassautawa zukatanmu.

     Ta tabbatar musu da amsar aikinta da ta ce a dakatar sai ta yi yayen Waheedah, Dr. Madinah dai ta yi kyakkyawan kudiri na fita harkar mijinta a dalilin kishiyar da ta ke ganin ba ta isa zama kishiyarta ba, saboda makasar ido da Allah ya dora mata da kuma da asalinta. 

    Har gobe tana son Sarham dinta, kuma matsayinsa bai canza a zuciyarta ba, amma ta yanke shawarar jingine shi a kan dai ta yi sharing dinsa da Hauwa.

    Maganar da ya yi na bata zabi na zama da shi ko aah ya girgiza ta, tabbas namiji ya baka option na zama da shi ko barinsa to hakika ya kasa jure drama dinka ne. Yanaso ya kawo karshen ta ya huta.

    A rayuwarsu bata taba yi wa mijinta horon yunwa ba amma yau kishi ya koya mata, bata taba kwararsa a shimfidar auren su ba, amma yau duk kishi ya koya mata har ta kware da hakan, ta jingine komai na hidimar mijin, wato shi kansa Sarham din ta yafe, da ita kanta soyayyarsa da ke ranta duk ta basu baya, da bukatuwarta da shi a matsayinsa na mijin da ta ke matukar so wanda suka gama gina rayuwarsu tare duk ta yafe, tunda har ya iya rufe ido ya yi mata kishiyar da bata kai ta komai ba, a lokacin da bata taba tsammani ba, don haka duk ta hakura da su ta barwa yar cikin Badala, watakila ta hakan ne zai gano muhimmancinta da bambancin da ke tsakaninta da Hauwa.

    Asibitin sun tabbatar mata ko a gobe ne ta zo ta yi reporting don suna matukar bukatarta dama. Don haka tun a daren ta ce ma Hajjah Ramlah gobe za ta kawo mata Waheedah zata fara zuwa aiki a Dr. Siddiqah.

     Hajjah Ramlah da tausayi Madinah ke bata yanzu, don ta fahimci son da take ma Sarham ya zama jarabta ga rayuwarta, tunda har ya iya yi mata wannan tozarcin, amma ta kasa barinsa.

    Ta ce, Ki kawo ta, bayan aiki ma ki kara da ayyukan sa-kai a asibitin gwamnati da philanthropic ayyuka duka, kuma ki ci gaba da tafiya programs da ki ke zuwa na marriage coaches rana daya kika daina yanzu, ki bar musu gidan tun safe har dare, in yaso ki barshi da makauniyar ya ci uwar da zai ci da ita, fitinannen yaro kawai marar godiyar Allah, ina ganinsa mai kirki ashe macijin sari ka noke ne, in ki ka daina wuni a gidan na ga wanda zai kula masa da makauniya.

     Tunda aurensa ya zame miki jaraba kema dai kamar aka ce shi ne autan maza.

    Murmushi Madinah ta yi, Hajjah ba za ta gane ba. Tabbas Sarham shi ne autan maza, amma a wurinta da duniyarta kadai, don ita kadai ta san ko waye shi, da darajojin da Allah ya yi masa, wadanda ba duka maza ya yi wa alfarmarsu ba. 

    Za ta ci gaba da zama karkashin aurensa har karshen rayuwarta, ko da ya sake ta ne a kan karan kansa to kuwa za ta ci gaba da zaman rainon Waheedah don ba za ta iya auren kowa in ba shi ba, Sarham is her life, her happiness, amma dole ta jingine shi yanzu, tunda ya ki zame mata namiji dan goyo. 

    Sannan maganganunsa na yau sun kara kashe jikinta daga tunanin rabuwa da shi haihata-haihata, amma dole ta janye masa.

    Tayi zurfi a wannan tunanin lokaci mai tsaho, tana jin sanda ya gama girkinsa ya rufo kitchen din, gidan duk ya bade da kamshin farfesun kayan ciki da jallop din cous-cous da Sarham yayi, don su suka fi masa saukin hadawa. Ya dauka da kansa akan ‘tray’ ya jera duk abinda zasu bukata ya dauka zuwa dakin Hauwa.

    Sai Madinah ta yi mishi ‘text messege wanda bata da tabbacin ya gani ko ya karanta, cewa gobe in Allah ya kaimu za ta yi reporting fara aiki da Dr. Siddiqah hospital. 

    A karshe ta ce masa “tana neman yardarsa”.

    

    Yana dakin Hauwa sakon nata ya shigo wayarsa don haka bai duba da wuri ba.

    Maijidda barcin bayan isha ba shi da kyau, tashi ga abinci na hada mana.

    Jin muryarsa ya sa Hauwa tashi zaune daga kwanciyarta, yace ba kya ko cigiyar mijinki cikin gidannan. Hauwa ta ji kunya na mijinta da ya ce din don dai ita har yau ta kasa sabawa. Wai Likitan Innane miji agareta.

    Ya ajiye abincin akan ‘center table’. Ya zauna daidai kafafunta, idanunsa na bin yatsunta da suka sha adon baki da jan lalle a hade da Mardiyyah ta yi mata da wani nisantaccen kallo na yabawa. Sai ya ji motsin shigowar sakon Madinah a wayarsa.

    Fiddo wayar ya yi, ya karanta sakon nata. Girgiza kai ya yi, ya kuma mayar mata da gajeruwar amsar cewa, 

    

    Allah ya yi jagora.

    

    Daga haka ya kishingide abinsa a gadon Hauwa, ya dora kansa bisa cinyoyinta, ita kuma tana zaune tsakiyar gadon ta mike sambala-sambalan kafafunta, ta bar masa cinyar yana shan raba, ya ce kasa-kasa kamar cikin rada.

     Ba ni labarin rayuwar makarantarku BUK, da yadda ki ke coping a aji kullum, I know it will not be easy for you at all.

    Sannan kuma dai an gayamin wai har da samari da Farfesoshin jamia ke bin layi gun Abba, duk da aure na? Ya fada (with a little bitterness) a muryarsa. Hauwa dai bata tanka ba sabida a lokacin hannunsa ya kai bisa lallausar tafin kafar ta, ya ja babban yatsanta da wani irin salo, mai bayyana manufa ingantacciya. 

    Kafin ya mirgina ya kai bakinsa tsakiyar tafin kafar tata ya sumbata. Tsigar jikin Hauwa ta tashi yarrr! Gabadaya, ta kasa ce masa komai, tana jin sanda Dr. Sarham ya janyo ta bakidaya jikinsa ya ce,

     Maijiddah, zo ki samu lada kinji, wannan yunwar da ke ji tafi wadda nake ji ta abincin dana dafa mana. 

    Nan ma shiru ta yi, jikinta ya soma bari, don ba duka ta gama healing ba, kamshin jikinsa da niimar numfashinsa su suka agaza mata tsoron yake raguwa, lokacin da ya fara sarrafata son ransa, bakidaya ya hautsina Hauwa-Kulu. Yayi sama da bakinshi a hankali ya bata kyakkyawar sumba a kuncinta da lips dinta hannunsa sarke cikin yatsunta.

    Daga nan yace. “wannan barin jiki haka? Ki yi hakuri zan yi a sannu, I promised I will not hurt you kamar jiya.

    Hauwa ta rasa inda za ta saka kanta don kunya, gabadaya Sarham ya shige cikin jikinta, ga numfashinsu ya sarke wuri guda, wato ya zamanto numfashi guda suke shaka nasa kadai sabida kusancin da ya assassawa fuskokinsu, da lips dinsu daya sarke wuri guda yana caressing dinsu softly. Hannunsa ya kai ga zip  din rigarta kuma ba tare da ta samu sukunin rikewa ko gardamawa ba, ya kai zip din kasa. Cewa yake cikin gigicewa.

    

     Na kara janye kalamaina, na kara janye su daga gareki Maijidda, YOU ARE MY LOVE! My true love and eternal happiness. Not a sister!.

    

    Hauwa ji ta yi hawayen farin ciki na sauko mata ta koina saboda yadda Dr. Sarham ya himmatu wajen fassara son nan a aikace, by caressing her tears da tsinin halshensa. Ya hanata kowanne irin katabus, nauikan sumbar yau daban suke, sumbace yake mata kala-kala naui-nauI data kassara dukkan gabbanta, ta kuma fahimtar da ita irin yadda Dr. Sarham yake da matukar son sumbatar matarsa har fiyeda ya tara da ita.

     Wayyo Inna! Hauwa ta furta cikin son kasar ta tsage ta hadiye ta kawai ta huta da kunyar da Sarham yake jefa ta a yau.

    

    Wato wannan din ita ce rayuwar da Mama ke mata fighting mata don ta samu, shima kuma akan karan-kansa ita ce irin soyayyar da yake ikirarin ita baya yi mata a can baya? 

    Tana iya jin amon sautin muryarsa har zuwa lokacin cikin kwanyarta, a sanda yake cewa, ya janye kalamansa na baya.

    

     Yau kam ta gasgata cewa Mama Uwa ce ta gari kuma mai sonta da alkhairin da kowacce mace ke samu a gidan aure, ta yarda Mama Uwar kowa ce ba ta Sarham kadai ba, domin yau ne ita ma ta san tana da wani boyayyen feeling mara fassaruwa a kan Sarham da ba ta san da shi ba sai yau. Kuma yau ne ta san mecece soyayyar kanta.

    Da kyar ta roke shi kan yayi hakuri tana jin yunwa kuma bata yi sallah ba. Abincin da sai da ya sandare Sarham da Hauwa suka samu cin sa. Kasancewar dama a bowl na tangaran ya zuba musu baa warmers ba.

    Da ya dawo sallah ya samu itama tana sallah, sai ya dauki abincin ya ajiye a kan ‘center-table’ ya jira har ta idar, shi ya zuba musu abincin suka ci a bowl guda.

     Tun kafin ma ta gama cin abincin ya karkade gadon ya sake shimfida da sabon zanin gado hade da duvet dinsa, ya dauke wancan ya saka a kayan wanki, ya gyara dakin ya kimtsa komai da ta bata a dakin ya fesa room fresh, ya kuma hada mata ruwan wanka.

    Hauwa na kammala cin abinci ta ji ta dauke a hannun Sarham. Bai direta ko a ina ba sai cikin ruwan wankan da ya hada ya saka ta da kayan jikinta da komai gaba daya, yace I wish you could see.. cewa yau tare Sarham da Hauwa zasuyi wanka abinsu. Gadaya ya sukurkuta Hauwa, ya kidimata da abinda yake fada. Daga bisani ta dauka marfi take yi saboda alamuran da yake gudanawar a gare ta masu ruda kwakwalwa ne da kidima masoyi, Hauwa-Kulu za ta iya cewa a cikin kwamin wankannan ta kara amsa sunan matar Sarham ba tare da ta ankara da yadda hakan ta faru ba. Amma hakika ta yi dauriyar da shikansa ya yaba mata. Don ba ta yi wani hobbasa don hana shi samun nutsuwar da ya nemi samu daga gare ta ba don ganin cewa a toilet ne, ta jure duk ta faranta masa rai a yadda ya bukata. 

    Shi ma kuma ya biyar da ita ne ta hanyar da ya kara mamaye zuciyarta da so da matsanancin so da kaunarsa.

    Tun daga ranar Sarham da Hauwa suka dinke suka zama abu guda, musamman da Madinah ta ba su fili ta hanyar fita sabgar mijin kwatakwata, sai hakan ya bashi damar samun wani irin kusanci da Hauwa-Kulu, Madinah ta fara zuwa aikin dole datasa kanta, su kuma sun zama tantabaru don soyayya a gida. Wani lokacin yana office da ya samu sararin aiki kawai zai tuko motarshi ya dawo gida, ya kuma samu Hauwa matan da ake shuara bata nuna gazawa bata korafi akan dukkan bukatunsa, Hauwa sai yadda yake so ta ke yi, wato sai abin da ya koyar da ita.

    Madinah na tunanin bar musu filin gidan da ta yi shi zai sa Sarham ya yi marmarinta, ya gane banbancinta da Hauwa, wato ya gane bambancin da ke tsakanin musaka da mai aji, bata san cewa a fannin matantaka duk mace sunanta mace ba, in dai tanada koshin lafiya kuma tana kula da jikinta, bata san hakan ya bai wa Sarham da Hauwa damar dinkewa ba suka manne wa juna suka like kamar tip da taya cikin morar niimar da Allah ya halatta a tsakaninsu, da wata irin soyayyar auratayya mai wuyar fassaruwa. 

    Kusan kullum ne Sarham sai ya sato jiki daga office ya dawo gida, don dai ya tabbatar da lafiyar Hauwa dama kuma Mama ta gama shirya yar ta tsaf, fiye da tsammanin dan Adam, don haka Hauwa ta gama tashin kan Sarham gaba daya, tunda Madinah ta shata layi a tsakaninshi da ita tun zuwan Hauwa gidan, a cewarta ta barwa Hauwa, tana kyamar hada miji da mijin musaka. 

    Madinah kam sai dai ya gode mata da wannan filin da ta bashi yake wani irin amarci kamar bai taba samun lafiyayyar mace a hannunsa ba sai a kan Hauwa. Shi da kansa ya hana Sumayya dawowa gidan, ya gaya mata ba yanzu ba, sai sun gama honeymoon, kada tazo ta bata masa mata da kilbibi. 

    Ko daga nan Sumayya ta gane Hauwa komai zamzam, don ko waya bata samun amsawa yanzu, kullum likita na makale da ita, ta nan Sumayyah ta gane komai ya fara saisaita. Farin cikin Sumayyah ya kasa boyuwa. Ga Usman ya like yana bin Sarham da gaske yana so ya turo ayi tambayar aurensa da Sumayya. Sarham kuma yana basarwa yana cewa ya nemi amincewar Madinah. 

    Madinah wadda a lokacin fama take da kanta, cikinta ya fara girma da ga matsaloli irin na mace mai juna biyun da ya fara tasawa, ga rashin kwanciyar hankalin data sawa ranta na barranta kanta da rayuwa da mijinta, wanda ta debi shekara da shekaru cikin fafutukar samunsa. Wannan yasa ba tareda sanin ta ba, a tsaitsaye BP dinta ya hau, yau tana asibitinsu tana duba patient mai hakiyar ido, Hauwan Sarham ta fado mata a rai. Tsaki tayi kanta yayi mugun sarawa, kawai sai ta saki komai ta dafe kanta, ta sulale a kujerarta cikin wani hali na unconsciousness. With high blood pressure.

    Nurse din da suke tare suna duba patient din ce ta ankara da gushewar hayyacin Dr. madinah, tayi maza ta yi kanta ta, kuma dinga danna ‘alarm’ na kiran likitoci da gaggawa.

    A karshe gado aka baiwa Dr. Madinah a asibitinsu. Nan da nan aka shiga bata taimakon gaggawa don tana bleeding, kokarin su shine su tsayar da cikin jikin ta amma a karshe suka ga tsayar da shawarar gara su cire shi don ceton nata rayuwar.

    Sarham na asibiti yana aiki Usman ya kira shi wai yazo yasa hannu zaa yiwa Madina tiyata a Dr. Siddiqah.

    Tsananin kidima data same shi a lokacin manta hanyar asibitin nasu yayi sai Usman ne suka hadu a hanya yayi masa jagora.

    Ya samu duk yan gidansu Madina sun riga shi hallara a asibitin shikadai ake jira amma kafin ya zo ma Daddy ya kulu ya saka hannu yace a shiga ayi mata, ciki kuma a cire shi in shi ke bata matsala. Babban Yayansu Madinah wato Abubakar Attahiru yace Daddy baka da wannan hurumin fa, ka bari mijinta ya karaso. Sai gashi ya shigo kamar an jefo shi shida Usman.

    Daga kallon da Hajjah Ramlah take masa duk ya sha jinin jikinsa.  Amma ya maida hankali ga yin needful, wato ya saka hannu aka shiga da Madina dakin tiyata.

    Dukkansu jigum-jigum sukayi a reception shida iyayen Madina da yayyenta, Hajjah Ramlah ta kasa shiru tana tsane ido tace wallahi in Madinah ta rasa ranta saboda kai Sarhamu, bazan taba yafe maka ba, tun farko ai nace ta hakura da aurennan babu dole tunda har zaka iya rufe ido kayi mata kishiya da makauniya nace ta hakura, amma da yake kunnenta na kashi ne ta zauna a gidan kuna guma mata takaicin da yau yake neman ranta.

    Alhaji Attahiru Habibu Sorondinki, ya kankance ido akan matarsa yana neman karin bayani yace me ke faruwa wai? Ki yi min bayani. Hajjah Ramlah na kuka ta zayyane masa komai cewa Sarham kara aure yayi da makauniya yar talakawa shine fa tun lokacin Madina take boye musu itama daliline yasa taji data yi tsami tsakanin ta da kanwar mijin nata.

    Alhaji Attahiru jikinsa har tsuma yake ya nuna Sarham da dan alinsa yace wallahi in ya ta ta mutu sai nayi karar ka, azzalumi wanda bai san mutunci ba. ai shiyasa tun farko naki yarda ta aureka don yayan talakawannan ko a tandun mai aka saka ku sai kun fito kandas wajen nuna halinku na rashin halacci. Banda mutuwa mai tonon asiri ai Madinah matar manya ce ba irinka ba.

    Kan Sarham a kasa yana jin cin mutuncin da Daddyn Madinah ke masa bai dago ba saida Daddyn yazo nan. Ya dago a hankali ya dubeshi idanunsa sun kada kamar gauta amma uffan ya kasa cewa. A lokacin aka fito da Madina daga dakin tiyata zuwa dakin jinya aka kuma hana su shiga sai bayan awa daya.

    Saida Madinah ta dawo hayyacinta aka bar su suka shiga, family dinta suka rufu a kanta Waheedah na hannunHajjah Ramlah shi suka manta da shi a gefe. Abin yayi masa ciwo kwarai sai Usman ne ya zo ya kama hannunsa zuwa kan Madinah. Ta dube shi, ya dubeta suka kuma hada ido, ta lumshe idanunta bata kara budewa don bata son ma ganinsa a kanta.

    Da aka bata sallama ma bayan kwana uku gidansa Daddy ya tafi da ita ba tareda nemsn iznin Sarham ba. ciki kuma an cireshi bayan ya fara girma.

    Ko kusa Hauwa bata san me yake faruwa ba amma ta lura Sarhamya rage magana kuma baya cikin walwala kamar da. Shiyasa yau da Sumayyah ta nemi zuwa gidan don tayi weekend tare dasu bai hanata ba yace tana iya zuwa dakinta yana nan. Hauwa kuma yace su koma nasa dakin don nata yayi kusa dana Sumayyah, ta tambayeshi ko hakan bazai zama matsala ga Anti Madinah ba? sai yace bata nan tayi tafiya. Da haka sukayi parking dakinsa soyayya a tsakaninsu sai abinda ya karu.

    Jumaah da yamma Sumayyah ta iso gidan daga makaranta.    

    Har ila yau, shi da team dinsa na Saudi-German suna ci gaba da shirye-shiryen aikin idon da za su yi wa Hauwa.

    Tun ba a je ko ina ba Sarham ya gane shigar ciki a tare da Hauwa, tunda yanzu tare suke a daki guda duk wani motsinta ya sani. Wanda ita koda wasa bata san da cikin ba.

     Kasa shiru ya yi don farin cikin da ya cika shi, wani na tafiya rariya wani na zuwa, har sai da yayi mata shagube cikin tsokana.

     Ya daga PT strip din da ya auna fitsarin ta, yace wai yanzu Hauwa-Jiddah daga zuwa sai ciki? Bazaki barni ma in gama yada samartakata a jikin ki ba mu tsufa tare? Kamar wadda ta yi tuntube da shi a dokin kofa?

    Hauwa saita saka kuka don tsakani da Allah ta tsorata da wannan maganar, ciki fa na haihuwa yake nufi? Ta yaya ta sameshi ma bata sani ba.

Yace Cry more Sweetheart, wani kukan ma sai an je labour room!.


    Sabuwar kulawa, sabon amarci ya balle wa Sarham da Hauwa a dalilin wannan niimar da ke tattare da mace mai yaron ciki. Sarham da Hauwa sai sam-barka, a yayin da Dr. Madina ta yi nisa kan ayyukanta na Dr. Siddiqah, da ayyukan tiyatar ido na sa-kai (philanthropic eye surgery) da takeyi don taimakon marasa karfi bayan ta warke daga tiyatar da aka yi mata. 

    Daddy ya tabbatar mata tunda Sarham yaki sakinta ta ruwan sanyi kamar yadda ya bukata, wallahi kotu zaiyi kararsa sai ya saketa. Bazai zuba ido ya kashe masa ya ba.

    Hankalin Madinah yayi matukar tashi gashi an hanata sauraron Sarham. Aka ce tsakanin mace da miji sai Allah, lokacin da ta sauko tana son ta karbi mijinta ya dade da sabawa da Hauwa, irin sabon da ko ita Madinah da ya kwashi ‘decade’ yana soyayya da ita bai yi shi da ita ba. 

    Kasancewar shi ne komai din Hauwa a gidan, dakinsu daya makwancinsu daya kullum, kullum kafin ya fita sai sun karya kumallo tare wanda shi yake sarrafawa da kansa, da rana kuma zai sa ‘mudam’ din cikin estate dinsu su yi mata home delivery’ na abincin rana, idan kuma ya dawo da daddare ya girka musu. Yayi musu wanki a injin wanki ya zauna zaman goge mata abayoyinta da hoover.

    Ita da kanta Madina ta koma tunanin anya wannan sabuwar rayuwar ta zaman gida da iyayenta suka zabar mata mai billewa ce? Gashi mijin ba sakinta yayi ba yanata bin Daddy har office da ban hakuri itama Madina yana bata. Ta soma tuno yadda yake saka apron ya shiga kitchen yana girki tukuru domin hidimtawa miskiniyar matarsa. Duk a kokarinsa na sauke nauyinsu su duka da Allah ya dora masa da kuma cewa da tayi baza basu abinci duk ranar girkinHauwa ba.

    Ta yarda Sarham ba mijin yadawa bane domin nagartarsa ta wuce ta sauran mazan da ubanta ke mata hange. Don haka ta soma tunanin mafita, wato yadda zata koma dakinta ba tareda daddy yayi fushi da ita ba don ita kanta ta san Sarham bai yi mata laifin komai ba laifinsa daya ne kara aure na tawaliu. Don haka ta koma lallashin Daddynta, ta tuna sanda Sarham ya ce in har ba za ta dinga dafawa tare da Hauwa ba kuma ba za ta yi muamalar makwabtakar musulunci da ita ba, to ya yafe cin abincin nata shima da take ajiyewa a dining ta fita.

    Ta tuno irin kalaman batancin data ke masa amma duk Sarham ya shanye bai taba korarta daga gidansa ba. Irinsu;

    A wane dalili za ka ce wai lallai sai na zama kukun matarka? Ka gaya min inda shariah ta dora min wannan nauyin.

    A wane dalili za ka dage lallai sai na yi muamala da matarka? Na gaya maka in na raina kasuwa ko sauti bana bayarwa a cikinta.

    Shin ajin rayuwata da na matarka daya ne da za ka ce sai na muamalanci wadda ko matsayin zama yar aikin gidanmu ba ta kai ba?

    Ire-iren kalamanta kenan gareshi tun zuwan Hauwa, da saidai Sarham ya daga ido a hankali ya dubeta da wani irin kallo na mamaki da disappointment.

     Ya ce,, In wani ne ya gaya min cewa Madinah za ta rasa hankalinta, kyakkyawan tunaninta da iliminta na jin kan alumma kai har ma da imaninta, a dalilin KISHI wallahi zan musa. Sai dai kash! Im witnessing it myself to the mere of my disappoitnment.

    Ina fatan wannan halin da ki ka ara ki ka yafa babu gaira babu dalili ba zai shafi rayuwar yayana ba, wato ba zai sa ki raba min kansu ba. Da sunan Mamar wadancan ba ajinki ba ce. Ya Allah ka cire rabon shaidan daga zuciyar matata Madinah. 

    Ya Allah Ka raba ta da GIRMAN KAI da superiority complex wanda shi ya hallaka Kakanmu Annabi Adamu A.S.

    Daga fadin hakan sai ya sa kai ya bar mata dakin. Jikin Madinah ya yi matukar sanyi yau, da tunaninta yazo nan, irin sanyin jikin da rabonta da shi har ta manta, tunda Hauwa tazo zuciyarta ta zama gardamammiya ta tsaya cur a kirjinta sai yau ta russuna.

    Dr. Madinah Attahiru. Ta soma kokarin tattaro ragowar mutuncinta wanda ta san, har abada ba mai gushewa ba ne daga idanun Dr. Sarhamu.

    Itada Usman sukayi shawarar Sarham ya gayawa Haj. Lailah hukuncin da Daddy yayankewa auren ta. tace ita kuma tanason komawa dakinta bazata kara tada hankalinta ba.

    Haj. Lailah suka shiryawa zuwa Saudiyyah itada Usman musannan don ta lallashi Daddy tayi sasanci, har bukatar Usman na auren Sumayyah sun gayawa Haj. Lailah ita kuma ta kama Attahiru da fada tace wannna ba gata yakewa yaransa ba yaranma sun fi shi hankali, ita Madina wacwcw data fi karfin ayi mata kishiya? Taga Nana Aisha da Nana Khadija ma duk da kishiyoyi suka zauna. Tayiwa Daddy kaca-kaca ta kuma saka shi ya kira Sarham a waya yace ya zo ya dau matarsa.

    Sarham a take ya baro office yaje ya taho da Madina daga gidan mahaigfinta. A hanya kuma kafin su iso gida suka kara dinkewa, suka fabhimci juna, ya kara yi mata kyakkyawan bayanin da yafi na baya akan Hauwa da muhimmancinta ga rayuwarsa kuma ba wadda za iya bari saboda yar uuwarta. 

    Abu na farko da Madinah ta fara yi bayan dawowarta gidan shi ne, in za ta fita office ta kan leka ta ce wa Hauwa za ta fita, Hauwa da yake bata kullace ta kamar yadda ita ta kullace ta ba sai ta amsa har da adduar.

     Allah yasa a dawo lafiya”.

    

    Ya dawo gida yau da wuri than usual ya samu Sumayyah ta zo gidan, suna falo itada Hauwa. Lokacin an kai kudin auren su itada Usman Kano. Duk basu ji shigowarsa ba daga ita har Sumayyah sun baiwa kofa kofa baya. Sumayya na mata famfo irin na yaran likitoci.

    Wallahi Aunty Hauwa kin bari kinyi saurin samun ciki, maimakon ki bari sai nan da yan shekaru biyu haka kina sa shi kuna yan dabaru da bazasu cutar da lafiyarki ba, not necessarily family planning na asibiti ai kin gane, amma kawai kika bari kika dau ciki as early as six month da zuwanki ko amarcin baku ci yadda ya kamata ba. Ga zancen aikin idon ki ya shantakar dashi tunda ya lura kinada ciki, kuma ke kullum yazo shikenan sai ki amsa kira ba dan jan ajin nan namu na mata koyaushe yake so zai samu, ai ni wallahi sai mun shekara uku nida Usman kafin mu fara tunanin tara yara, kuma sau biyu ko sau uku a sati zan ke yarda, ba kya ko tunanin yaya ake haihuwa, bafa sauki ne da ita ba, ke kinga yadda mata ke gumurzu a dakin haihuwar? Alhalin in kin haife shi ke ba ganin dan zaki yi ba, maimakon ki bari sai bayan aikin idonki muga abinda Allah zai yi. 

    I am imagining yadda zaki raini yaro a hannunki without seeing him, it will not be easy for you a halin yanzu, ga Bhaiya ba hakuri kullum yana like dake ko zama a office baya yi sosai yanzu, baya barinki ki huta ko kadan ki maida jikinki, bayan ana son gap don a maida ruwan jiki, shiyasa sanda Madinah ta tafi bai damu da tafiyar ta ba, ya san yana hutawa sosai, har fiyeda in tana gidan. Na tabbata ita ba haka take barinsa yana caskalar ta kullum ba, duk kin wani rame kamar ba luscious Hauwar Mama ba.

    Yanzu da kin haihu baby yana tsotseki, shima ba hakura zai yi ba, duk su taru su tsofar dake (at twetieth) dinki. Maganar karatunki ma naga alama ta bi ruwa, Mama tayi tayi ya dawo dake in bazai saki a makaranta ba har ta gaji ta zuba masa ido.

    Sarham ya yi maza ya koma da baya ya bar gidan, yana lissafa irin yadda zai ci uban Sumayyah laada waje.

    Asibiti ya koma ransa a mugun bace da Sumayyah. Ya kirata a waya lokacin tana dakinta ita kadai ta bar Hauwa cikin zurfin tunanin, kome Summy ta fada haka ne Sarham baya tausayinta ta wannan fannin kuma ta tabbata ba haka yakewa Madina wannan rashin tausayin ba, kullum ba hutu kamar ya samu engine har gashi mutane sun soma noticing tana ramewa. Dole ta sake lale itama ta koyi jan aji kamar yadda Sumayya tace. 

    Sumayyah na dagawa da sallama yace Summy! Tace naam Bhaiyana 

    Ba wani nan. I am no more your Bhaiya daga yau. Fito ki bar min gidana kada ki lalata min tarbiyyar matata.

     Na rantse da Allah in sha Allah wata mai kamawa zaa tattaraki ki tafi naki gidan mijin, shi ki je ki ja masa ajin ki gane in zai yi tolerating iskancin ki, kada in kara ganin kafarki a gidana sai kin haihu kinsan ciwon haihuwa da darajar mijin aure. 

    Sumayyah ta bude ido da baki a tare, nan ta gane ya ji gulmarta. Ta soma afi tana hurwar kayimin rai na tuba Bhaiya, kayimin aikin gafara Bhaiya, subutar baki ne, I dont really mean it. Yace subutar baki ko raayin banza na mata yan duniya kike son cusa mata, naki nayi mata aikin idon, da can ke kika sani? Ko kuwa mace na fama da kanta sai in kwantar da ita in fede mata ido wani abu ya samu Baby na? Wallahi Sumayyah kilbibinki ya isheni dama nasan kina kaita Saloon a cikin estate kuma na gaya miki tun na farko bana so, tunda ina sayo mata shampoo na wanke kai dana zaba mata, wanda bazai canza mata launin gashin kanta daga asalin na hausawa ba.

     Sannan ina sane da cewa kin kawo mata wasu mayuka da sabulai na banza da hofinki, wai irin wadanda kike shafawa, kina so ki koya mata bleaching ne? Na taba ce miki kina da kyau ko shafe-shafen yammata yana burgeni? Itada ko ido babu!

     I am observing you Summy, ke shaidaniya ce wasa-wasa, duk abinda kike yi wai ke a dole sai kin mayar min da mata yar duniya ko, na ce bansan kalarta bane sanda na aureta?

     Ko bansan yadda gashinta yake ba? Ko nace miki in farin fata nake so na Madinah bai ishe ni ba? Ke dai wallahi Usman ya shiga uku, Maijiddah ki bar min kayata yadda nake sonta, muna zaman mu lafiya cikin fahimtar juna da kula da bukatun juna zaki hargitsa mu ko, kema kuma zuwanki kasar nan ne duk kika fara wadannan duniyancin. A da ba haka kike ba wallahi Sumayyah. 

    I love my wife and her natural beauty, dont dare try to change her for me. 

    Haka ya cashewa Sumayyah son ransa, har saida ta fidda kwallah. Cewa take In sha Allahu Bhaiya bazan sake ba. na tuba nabi Allah na bi ka.

     Kafin in dawo ki tabbbatar kin bar min gida na, tunda ba nida ke muka hada kudi muka auri Hauwa ba.

    Jikin Sumayyah na rawa ta shiga dakin Hauwa ta dau jakarta tace Anti Hauwa wannan mijin naki hummm! Sai Allah ya baki hakuri, kinsan Allah mijin ki aljani ne wajen jin magana, Mama tace haka yake da zuqo zance a kunnuwansa tun yana yaro, na tafi, sai an kwana biyu. 

    Bata kuma gaya mata yaji komai data fada ba. Ta bar Hauwa cikin sake-sake tayi tafiyarta tana cewa Summy kiyi min bayani mana? Daga can bakin kofa ta ce in yazo yayi miki fashin bakin da kansa kuma bazan kara baki shawarar komai ba, daga yau ba ruwana da sabgarku, mijin ki ya maida ke duk yadda yake son ganinki, ni dama nawa shawara.

     Murmushi Hauwa tayi tana fadi cikin ranta Sumayyah da Bhaiyanta ba dama ne, ayi fada ayi dadi. Inama itama Zulkifl yana raye da haka zasu zama kamar Sumayyah da Bhaiya, yau fada gobe shiri. In suna shiri kuma sun fi kowa ji da juna.

    Sarham bai dawo gidan ba sai dare, yana hanya ma Madina ta kira shi tace motarta ta baci yazo ya dauketa a asibiti sai ya biya ya dauketa sannan suka wuce gida, suka tsaya suka yi take away na pizza da KFC don yau girkin Hauwa ne bana Madina ba ko ya saya ne ko ya girka musu, don har bayan Madina ta dawo bata karbi yiwa Hauwa girkin abinci ba saidai in ta dafa yanzu tana zuba musu ranar nata girkin. 

    Suna shiga gida ya nufi dakin Hauwa, ta sha wankanta tana shafa mai ga hoda a gefe. Yayi salama ta amsa, ya bata peck a kumatu, ya shafa cikin ta wanda zuwa yanzu ya soma turowa cikin zani, yace hope hes kikcking well? cikin rashin fahimta tace waye? yace baby! Mai sunan Innata. Ta kare fuska da tafin hannunta ta ce aa gaskiya mai sunan Mama ce Yaya doctor. Nan suka hau gardama yace sai an fara saka Inna ita kuma tace sai an fara da Mama.

    Daman jiranka nake ka dawo, in shafa hoda ka gayamin ko tayi daidai? Shiyasa tun dazu ban shafa ba yana fesa turare ya juyo ya ce ba na ce ki dinga shafa abarki ko yaya ba? in tayi yawa inna dawo na gani zan gyara miki? ta soma shafawa ya koma daga bayan ta ya dora kai a masangalin wuyanta fuskar shi da tata cikin mudubin hannun ta sun yi kyau har sun gaji, sun yi matching dukkan su choculate incomplexion da wani irin annuri da hasken imani a fuskokinsu. Daga nan Sarha ya kama hannun ta ya cirata tsaye ya soma kokarin kai mata sumba, nan da na ta noke ta ja baya, ya sake rikota yace lafiya? idonta narai narai tace wai mu bazamu dinga hutawa bane? Ina laifin sau biyu a sati ni gaskiya.. Nan da nan ya gane hudubar Sumayyah tayi aiki ta wanke mata kwakwalwa, yace ok. Ok to bari kiji in gaya miki daga yau Sumayyah na koreta kada ta kara zuwar min gida. Ya suri mukullin dakin shi ya bar dakin, yayi fushi sosai, kuma gashi girkinta ne bana Madinah ba don haka ya koma dakinsa ya kunna laptop ya hau aikin da bai yi a asibiti ba.

    Hauwa duk taji guilt ya dameta data tuna tafiyar Summy ba shiri da abinda ta fada mata sai ta gane yaji hirar su ne. ai kuwa kunya tayi balain kama Hauwa da sauri ta saka doguwar rigar barci mai kyau ta bi bayan sa zuwa dakinsa don ta san hanyar dakin. Ta kwankwasa ya amsa da yes daga ciki sai ta shiga.

    Ya kalleta ya dauke kai zuwa aikin sa, tace Baban Waheedah please kayi hakuri wallahi ba zan sake ba yayi shiru yana cigaba da operating system dinsa, ta taho kamar zata bi ta kansa yace in kika fasa min laptop sai kin biya ni ta muryarsa ta san inda yake zaune  ta laluba ta zauna akan cinyarsa shikuma ya hau kokarin zillewa amma Hauwa bata bashi wannan damar ba.

    Sosai ta inganta mishi daren yau kamar babu ciki a jikin ta, kamar babu lalurar ido a tare da ita, yau Sarham shi ya koma dan gata sai yadda Hauwa tayi da shi. Sun farantawa juna rai kamar bazasu ragewa gobe ba kafin su koma maida numfashi manne da juna. Saida ya koma Sarham din sa ya ce mata Maijidda, naji hudubar da kawar ki tayi miki, amma ki sani ni ba daya nake da sauran maza ba.

    Ba wani canjin halitta ko tsofewa da zai sa in daina son matata.

    Sannan barin ain samu abinda nake so a lokacinda nake so shi yake kara ninka wannan son yake kuma kara kusantoki da zuciyata.

    Hauhuwa da wuri kuwa kuwa in duk sati ake yin ta ni kulllum nake so kiyi min.

    Makaranta kuma ina sane na barki sai wata shekarar don bana son kiyi jigilar karatu da yaron ciki.

    Maganar aikin ido kuma ban gama abinda nake tattarawa ba sannanba zan miki aiki alhalin kinada ciki ba sai Allah ya saukeki lafiya kinji?

    The more you give me access to it, the more I addittionally love you.

    Don haka ba Sumayyah kadai ba, duk wani wanda zai baki shawara akaina ko akan abinda zai amafni jikinki yabi bayan ni. Ban ce kada kiyi kawance da kowa ba amma ina so ya zama nine amininki sama da kowa, feel free to discuss everything about our marital life with me kin ji? Not the third party wadanda ba lallai bane su san meye sexual likes and likes dina ba.

    Kunya sosai ta kama Hauwa, ta roki gafara, ta dauki alkawarin bazata sake yi masa rowar wannan ba, sannan bazata zancen mijin ta da kowa ba sai da shi kansa. Kuma daga wannan ranar ne, HAUWA BILYAMINU, ta fara kiransa da suna MY PACESETTER!!!.

    

     Sati mai zuwa insha Allah za mu shiga umrah cikin makkah ni da ke, daga nan muje Madinah ziyara mu yi addua solely a kan Allah ya saukeki lafiya HAUWA, ya bamu Inna mai albarka, mai irin dukkan halin INNATA, mai tsafta mai kyautar abinci mai kula da yayan ta kamar yadda take kula da ranta. 

    A karshe ya shafa kanta tana durkushe gabansa yace Allah ya saukeki lafiya Hauwa-Jiddah, Allah yayi miki albarka Hauwau-Maijiddah, yadda kika faranta min yau, Allah ya faranta dukkan rayuwarki.

    

    Hauwa ta ji wani irin dadi ya mamaye ruhinta, ya daura hannunsa a kan nata hannun, ya matse su sosai cikin na juna, alkawari ne ya dauka tsakanin sa da Ubangijinsa; zai yi duk iya kokarinsa ya gyara idanun nan na Hauwa-Kulu, koda remnant cikin yarda da amincewar Ubangijii wato koda ba duka aka samu dawowar su ba.

    

    ***            ***           ****

    

    Can daga nesa na hango Dr. Sarham Abbas da matarsa Hauwa-Kulu suna dawafi a Kaabah, hannunsa makale cikin nata. A zagayen karshe na kowanne dawafi addua daya suke yi, Allah ya sauki Kulu lafiya, ya bata ikon sharwa da kula da yayanta koda idanun ta basu bude har abada ba, aikinda zaayi mata kuma, wanda zaayi ne immediately bayan ta haihu, Allah yasa ayi shi cikin nasara.

    Suka gabatar da cikakkiyar Umrah suka dawo gida Jeddah.

    Mama tasa rigimar ya dawo mata da Hauwa ta haihu a gida, tunda haihuwar fari ce. Sarham yace Ina! Ya gama wannan daga haihuwar Waheedah. Saidai a kawo wata ta zauna masa da ita har tayi arbain din. 

    

    “Na kwana guda bai iya jure zaman gidan da babu HAUWA!.

    A lokuta da yawa har wani kirarin baitocin waka Sarhamu ke rero mata, daga baitocin wakar mawaki (Ali Jita), a irin lokutan da soyayya ta cicciko a kirjinsa, wato tayi tantsan a zuciyarsa; 

    Zana gaida HAUWA-KULU.Sannu HAUWA-..HAUWA..

    Baa raina suna da lokacinki HAUWA.

    Baa finki haske a zuciyata HAUWA..

    

    Babu wanda zai bata zamaninki a zuciyata HAUWA. 

    In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.

    Babu wanda zaya ruda zuciyata a kanki HAUWA. 

    Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA.

    Da zaa bani biro na baki maki HAUWA

    To zaki haura lambar da zaa baki HAUWA.

    In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.

    To addua nake... Allah ya taimakeki HAUWA.

    A irin wadannan lokutan da yake rero mata wadannan baitocin, zaka samu Hauwa-Kulu manne dashi cikin shauki, tana sauraronsa tana murmushi from ear to ear, kanta ya kumbura.. irin na macen da tayi dacen saar mijin da ta san har zuciyarsa yana matukar son ta.

    ****                  ****                  ****     

    Ranar da suka dawo Jiddah Madinah ta karbi girki. Ta dade bata ga Hauwa ba, duk da suna rayuwa a gida daya, to wata irin rayuwa suke yi ta  kowa tasa ta fishsheshi, wato ba mai shiga shaanin kowa saidai sallama da gaisuwa irin wadda addinin musulunci ya shardanta a tsakanin musulmi. Madinah ta daga ido taga Hauwa da ciki tororo, alhalin bata gani. Wannan kadai ya kara ma Madinah tsoron Allah, ganin cewa mijin da matar ko a jikin su akan lalurarta, suna cikin farin ciki mara misaltuwa na ibadar da suka yo guzurinta suka dawo.

    Silar kasancewarsu kullum cikin farin ciki shine wani boyayyen sirri ne na IKHLASI (sincerity); Sun dade da tsarkake zuciyarsu da karbar kaddarar rayuwar Hauwa da hannu bibbiyu, wato sun yarda cewa nakasar ba kasawa bace at all cost, kuma ba itace karshen komai na rayuwar bawa ba. 

    Sun yarda mara lafiyan da ya samu kulawar iyaye da ilmi mai amfani hakika zai iya hada kafadar rayuwa da kowane mai lafiya, in such a way that, an bashi spacial consideration na abinda yake bukata don gudanar da rayuwarsa ta hanya mai sauki. Ko yau Allah zai bata Da mai lalurar gani, dama kowacce irin lalura ta halittar jiki, Madinah sai taji bata fargaba kamar da, zata maida rayuwar kishiyarta mudubin dubawa ne ta tsaya ta kula da shi tun yana karamin sa, ta bashi kulawa ta musamman a cikin yayanta kamar yadda Innar Hauwa da Mama suka kula da Hauwa cikin yayansu basu bar rayuwarta ta wulakanta saboda nakasa ba, zata tsaya ta gina rayuwarsa yadda in ya girma bazai sha wahala sosai ba, zai rayu ne adequately and independently kamar kowa da taimakon na jikin sa. 

    Kenan matar Sarham ta zamo role-model, haka ga duk wani mai nakasar ido ya gane cewa makanta ba karshen rayuwa bace.

    Ya shiga toilet ya bar Madinah nata sake-sake cikin mutuwar jiki da karin imani, Hauwa ta gaishe da Madina sannan ta wuce dakinta. 

    Dr. Sarham kenan mai Jidda mai Madinah bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi.

    Kullum kokarinsa shi ne ya samar da cordial relationship a tsakaninsu, amma hakan ya faskara. Don kowacce gwanace ta gwanaye a kishin SARHAM! Shikadai ransa, sun fi ganewa rayuwa ta gaisuwar musulunci da gasar kyautatawa maigida.

    Lokacin da cikin hauwa ya shiga watan haihuwa kuma Sarham ya hana ta dawowa gida bata nuna bacin rai ba, duk dokin ta da ganin iyayenta kuwa, sai yayi kudurin shi kuma zai yi mata abinda zai faranta ranta matuka.

    EDD dinta saura kwana uku, tana zaune akan kilishin dakin ta, tana cin mutumin nata gugguru, ta saka tirtstsen cikin ta a gabanta, ta ji kamar sallamar Inna a dakinta. 

    Haan, yau kuma kunnena ya koma yi min gizo da muryar Innata? 

    To tunda gizo ne bari kawai in koma ya cigaba da gizago. Irin mikewar da Hauwa tayi ta manta da tshohon ciki a jikinta saida Inna tayi maza ta kamata ta zaunar. Tana fadin Yi a hankali, likita ya gayamin yan biyu ne a tare dake.

    Zaro idon da Hauwa tayi shi ya tabbatarwa Inna bata taba jin wannan zancen ko makamancinsa ba, haba! Biri yayi kama da mutum. Shagalin da take ji a cikin ta da nauyin sa da girmansa ya wuce na jariri daya. Pacesetter kuma bai taba gigin gayamata ba kada ya tsoratata amma komai biyu yake saye iri daya unisex. Tuni Hauwa ta soma hango kanta rungume yaya guda biyu alhalin babu ido. Wata qudururar sai Ubangiji Subhana. Tun tali-tali Hauwa na kwadayin haifar Da, ko don iyayenta da basu dasu da yawa. Da Ubangiji ya tashi yi mata kyautar Da sai ya bata da gaggawa kuma guda biyu a lokaci guda ciki lalurar makanta.

    Akace sau tari wani farincikin yafi gaban ayi masa kuka ko ayi masa dariya. Don haka Hauwa a wannan daren kwana tayi sallah a zaunde, ga farin ciki zuwan Inna ga na albishir dinda tayi mata.

    Tun daga ranar Inna ta soma aikin ta na kula da Hauwa dama ta zo da duk wani tanadinta na jego.

    Kwanan Inna biyu da sauka nakuda ta fara, Pacesetter ya kwashe su sai asibitin Doctoor Sulayman Faqeeh. Ko awanni biyu baayi da karbar Hauwa a dakin Haihuwa ba a hannun Sarham ta sambalo yammatanta guda biyu, Hassana da Hussaina identical twins masu irin idanun Hauwa da Sarham yayi fata, yatsun da dogon hancin da sumar fulanin Shanonon kuwa duk nashi ne.

    Madina har asibitin ta zo ta duba su, dama kuma taje har dakin Hauwa ta gaida Inna shekaranjiya, karonta na farko da shiga dakin Hauwa albarkacin mahaifiyarta. Tayi tayi hajjah Ramlah ta zo barka ta ki, ta dai yiwa Sarham din barka shikadai don su Hauwa basu isa ba, itada Usman sukaje MAX’ sukayowa jariran sayayya ta burgewa suka kawowa Hauwa. Dama wajen kyauta da mikakken hannun alkhairi  Madinah ba daga nan ba. Circumstances ne ya canza Madinah, amma a hankali tana farfadowa tana dawowa Dr. Madinah Sorondinkinta da kowa ya sani.

    Tun sanda suka fado duniya yayi musu  khutbah da sunayen da suka dade da zabar musu wato Hassana (Maimunatu) da Hussaina (Safiyyatu). Mama da Abba dai basu amince ba suka saka shi agaba kan lallai ya maido su gida sai ya ce ai ga Inna ya dauko tazo daga Ghana. Sannan ne hankalin Mama ya kwanta. 

    Inna ta shiga Makkah tayo Umarah cikakkiya, ta je Madinah tayi ziyarar fiyayyen halitta SAW. Tana rokawa Hauwa da Sarham ‘long life and prosperity’ da zasu raini yayansu, su kuma tarbiyyantar dasu tare a duk inda ta tsaya a indararon Rahma na ubangiji adduarta kenan, ta kuma roki ubangiji idan Hauwa nada rabon gani a rayuwarta, Allah ya hada idonta dana Sarham a gidan duniya ba sai sunje aljannah kadai ba. satin Inna daya a cikin Makkah tadawo Jeddah suka soma shirin tahowa gida Najeriya. 

    Suna yin arbain suka tattaro har Sarham zuwa gida Kanon Dabo tareda Inna, dona kaima Abba da Mama yan biyu su gansu. Basu san Malam Bilyaminu yana can yana shirya musu surprised ba. Wato abun mamakin shine da Sarham ya kira Malam Isa yace masa ya shigo kasar Kano zai zo ya gaidashi sai Malam Isa yace ai ga BILYAMINU muna tare a soro na, tuni Malam Bilyainu ya dawo gidansa na BADALA tun kafin Innar Hauwa ta dawo. Ya kwaso komai da ya mallaka daga Ghana ya dawo dashi Kano, har ya cigaba da raba sanaarsa a Kofar Wambai ya zama babban dealer dake shigo da gwanjo ya rabasu da kansa ga kananun masu kwance dealer su sayar da dai-daya”. 

    

    Ya kara kawata gidansa tun kafin Inna ta dawo ya zuba musu komai na bukatar rayuwa yadda suke rayuwarsu a gidan su na Ghana.

    Ina rijiyar farin ciki take Hauwa ta fada da jin wannan labari da Sarham ya bata. Hauwa tafi kowa murnar dawowar iyayenta cikin Badala ba don komai ba sai don cewa har gobe ruhin HAUWA-KULU yana nan cikin gidajen Badala. Don haka walima sosai Sarham ya shiryawa su Inna don kowa dake Kofar Naisa ya san sun dawo, inda aka gayyato dukkan makwabtansu na kusa dana nesa. Baka jin komai a Badalar Kofar Naisa ranar walimar nan sai labarin Malam Bilyaminu, batansa da abinda Zakari yayi masa, da labarin Innar Hauwa da Hauwa data makance Allah yayi mata ludufin rayuwa tayi a aure a Saudiyyah da makanta da komai ta haifi yan biyu son kowa. Ai an ance ma gawurtaccen likitan ido take aure acan din.

     Wai wacce Hauwar kuke nufi? Ba dai yarinyar nan mai ciwon ido na apolo Hauwar Inna ta lokonsu Malam Isa ba? Ita fa, wadda Salele yake yiwa jagora”.

    Ai kuwa wqadanda aka gayyata dama wadanda baa gayyata ba a kofar Naisa duk sun taho walima da gulmar gani da ido gidan Malam Bilyaminu dan kofar Naisa. Mama da wasu daga cikin yan uwanta dana Abba da ke Shanono da Mardiyya sun samu halarta. Mardiyya da Salele sune masu rabon abinci da abin sha natake away  ga mahalarta taron. An ci an sha anyi hanian an yi hotuna da vedio na tarihi yan biyu kowa ya gansu ya daukesu ya musu addua.

    Sunje wa Mama zasuyi sati a wurinta nan Mama ta koma gyaran haihuwa, wanan karon wane gyaran amarci don Maman Farida  guda ta yiwa waya tace tayiwa Hauwa gyaran haihuwa ko nawa ne zata biya.

    yan biyu kuwa kusan tsakiyarMama da Abba Prof.suke kwana suna lelensu da shafesu da addua. Ana I gobe zasu koma Jiddah Abbah ya sa Sarham a gaba yace sai ya gaya masa ina zancen karatun Hauwa ya kwana, da yanzu ta gama year two dinta a wanda ta jingine. Sarham yace ya samar mata makarantar da suke Inclusive Education wato jamiar DAAR EL-HIKMAH UNIVERSITY da sun koma zata fara don haka wanna karon Sarham da kansa ya bukaci tafiya tareda Mardhiyyah don ta taimakawa Hauwa da rainon yan biyu da sauransu.

    Dakin Sumayyah aka baiwa Mardiyyah take hidimar ta da yan biyun ta, tana taimakawa Hauwa su in zata shayar dasu ta rike mata daya. In kaga yadda Hauwa ke hidimar yayanta wajen saka musu diaper da yi musu tsarkin kashi da goge tumbidi da bada madarar jarirai abun zai matukar baka mamaki, haka duk kuka idan dayansu tayi ta san me take bukata. Sarham in yana gida tareda shi ake komai duka da yanata shirye-shiryen makarantar Hauwa a lokacin amma kuma tunda ya kyalla yaga ta fara sallah a wani dare abubuwa suka canza. Baiwar Allah tayi kokarin nuna masa cewa yan biyunta basu yi kwari ba Sarham yace Allah yasa jiya aka haife su, nima tun haihuwarsu banida kwari, Allah shine mai rayawa kuma shine mai kashewa kin ji ko? In kuma wannan yarinyar ce ta kara yi miki huduba sai in bar ki da ita in karo ta uku. Ya fada yana saita alamuran yadda yake son su Hauwa na kwallah har da tsane hawaye tana fushin da Sarham bai san tana yi ba a lokacin sabida ya tafi da yawa, bai nutsu ba sai da ya kwashe gyaran Mama tsaf a daren yau. Da aikin tukudin Inna. Ya bar Mardhiyya da yan biyu tana ta fama, duk sun rikice mata da kuka sun ki kama madarar da take basu a feeder.   

    Shiyasa ake cewa Uwa tafi tausayi yayan ta, sai da ya koma Sarhamun sa sannan ya koma lallashi. Yace Maijidda abun alfaharinki ne ace mijin ki cannot do without you. Ni kadai nasan manejin danayi har kwanakinnan arbain, kiyi hakuri ni bana gudun kaddarar yaya karewa ma son su nake yi, so nake ki cika min gida dasu son samu duk shekara ki juye min yan biyu. Bari in gaya miki abinda bai kamata in gaya miki ba nafi samun duk wani contentment da duk nutsuwar aure idan ina tare da ke. Soyayya daban, sexual satisfaction shima daban. Madinah ina mata soyayya ke ina miki so da kauna wanda yafi gaban ina ganin ki in iya kauda kwadayina sai dai in bakida lafiya to wannan kuwa zanjure har ki samu lafiya. Ni likita ne na san yadda zan kula da lafiyar yaya na kin ji ko?

    Ta gyada kai cikin sanyin jiki, yana daura mata tawul a jikin ta yace karbo su ki basu nono kukan su ya dame ni.

    Anan ne tayi magan cikin hararar sa.

    wallahi bai dameka ba, da ya dameka da ka hakura sai sun yi shiru. Yace to sai me? Ba da hakan ba da an same su? Yanzunma kannen su nake hari shiyasa ban sauraresu ba ta zuba jallabiyya a jikin ta zata fita bata saurare shi ba yace dakata, tsofaffi sun ce sai kin yi wanka zaki taba su kada ki shafa masu datti, kodayake ni na san jiki na ba datti sai albarka ta dan dakata jimmm a bakin kofa, ai kuwa Innama ta gaya mata haka wai in taje dakin miji kada gta yarda ta taba su sai tayi tsarki, sai kawai ta juya ta nufi toilet. Ya ce ai kya tsaya in gama hada miki ruwan mai zafi sosai ance baki gama jegon ba har gobe. Tace don Allah don annabi kaje ka basu madara zan kula da kaina ka cika ni da magana ga kukan su yana ruda ni. Tausayi ta bashi sosai yace to ai nima ban yi wankan ba ko inzo muyi tare? Kin ga daga nan in cuda miki baya da dogon wuyanki. Hauwa takaicinsa ya isheta ta shige toilet dinta harda saka key. Sarham yayi jifa da filo ya mike yana saka jallabiyyarsa yana rero baitukan sa na ;

    

    -Addua nake Allah ya taimakeki HAUWA-HAUWA!.

    

    Daga cikin toilet Hauwa tana zuba ruwa mai zafi cikin gashin kanta, take jin sa tana sakin murmushi daga zuciya zuwa ruhi. Ta ce a hankali;

    

    Nima Adduaa nake Allah ya ja da ran maigidana Lelen Abba a dade ana aikin lada.. shi da HAUWA!.

    

    Ya gama dukkan shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aiki ranar Litinin amma sai me? 

    Ya dawo gida yau a bit late kuma ranar girkin Hauwa ne, suna girki a kitchen ita da Mardiyya shinkafar Basmati ta tafaso Mardiyya ta bude tukunyar, Hauwa ta shaka sosai kawai sai taji wani mugun amai ya yunkuro mata.

    Ta tsugunne a wurin tana kakari amma aman yaki fita kamar zuciyarta zata fito ta bakinta ga goyon Safiyya a bayanta. Da sauri Sarham ya bar maganar da suke yi da Madinah a falo ya karso kitchen din, kai kakarin me nake ji haka? Dai dai lokacin ta samu aman kore fatau dashi ya biyo makogaronta don azumi take na alhamis bata ci komai ba shirin buda baki suke yi. Da sauri ya sauri ya ida gareta ya daga bayan ta yana shafawa har ta samu ta amayar da komai dake cikin hanjinta. Madina ta gifta zata wuce dakin ta kallo daya ta yi mata tasan ciki ne da ita ana mata amai a kitchen ta wuce daki cikin gigicewa.

    Ita kuma Hauwa haka take da Haihuwa cikin lalura Allah mai girma!

    Ya kamo Hauwa zuwa dakinta yace Mardhiyya ta gyara wurin.  Suna shiga ya soma checking dinta har fitsari tayi ya saka masa PT strip. Wata wawuyar runguma da Sarham yayiwa Hauwa saida ya kayar da ita a saman gadon aurensu. Tana tambayarsa cikin tsoro da fargaba ko meye yakewa murna haka? Kuma me sakamako PT strip ya nuna? Amma bai saurareta ba sai sukuwa yake cikin rawa da waka yana narkewa cikin jikin Hauwa; 

    “Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA.

    Da zaa bani biro na baki maki HAUWA

    To zaki haura lambar da zaa baki HAUWA.

    In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.

    To addua nake... Allah ya taimakeki HAUWA.

    ****              *****                   *****

    Aikin da baa yiwa Hauwa ba enan a wannan shekarar amma dai tayi borin zuwa makaranta duk da haka. Bayan ta ci kukanta ta gode Allah na gwarne da take ganin wahala ne. Shima kuma da yake lallabata yake ya yarda ta fara zuwa DAAR AL HEKMAH UNIVERSITY a wannan shekarar duk da yaron cikin, ya kuma dauki alhakin kaita lacca da daukota da kansa kullum.

    Haka Hauwa-Kulu ta soma karatunta karkashin BLaw (Bachelor of Law) wanda zai dauketa tsayin shekaru hudu a jamiar Daar Al Hekmah, Jeddah, KSA.

    Cikin Hauwa wata takwas ta haifi yarta ta uku a duniya wadda ta rokiSarham Allah da Annabi ya saka mata sunan aminiyarta Sumayyah.

    Sumayyah wadda har lokacin ake ake kai ruwa rana akan maganar aurenta, don Hajja Ramlah ma tabi bayan su Madinah tace ya nemo wata, bata ga dalilin sai wadda ke kin yar uwarsa zaice zai aura ba. Baban su kuwa wato Ahaji Attahiru tun karin auren Sarham dama basa ga maciji shi da Sarham don yaji ciwon abinda yace masa a asibiti lokacin da zaa yiwa Madina tiyata. Don haka ma da yaji wai kanwar Sarham ce Usman yake so bai saka baki ba kuma bai yi adawa ba ya dai ce sai abinda suka shawarta shi da yar uwarsa.

    Shikuma Usman ya dage baiga dalilin da zaa ce  Madinah ce zata yi masa deciding matar da zai aura ba tunda gaba yake da ita. Don haka ya kai karar Madinah gun Kakar su Haj Laila kan tana bata masa zancen aure ta karkashin kasa a gurin iyayensu. Haj Laila sai kawai ta tada waliyyai suka tafi gun Abba suka kai kudin aure, Abba bai karba ba yace sai yayi magana da Sarham tukunnah tunda shi yasan Usman fiyeda kowa.

    A karshe dai Kakar saida ta tafi har Jeddah ta samu Alh. Attahiru ta gyara komai tsakaninsa da Sarham, tace ita bata ga dalili ba da don suna son autar su Madinah zasu ce bazaa yiwa Madina kishiya ba tunda ba alkawari sukayi a rubuce ba na cewa daga kanta Sarham ba zai kara aure ba, kuma wulakantata yake yi ba sannan polygamy aladar mutanen Kano ce. Itama da suk ganin baayi mata ba harsuke reference da ita to bari ta gaya musu gaskiya Alkalin Alkalai ya so yi ita ke lalata zancen duk inda yaje neman aure har ya gaji bari, tace tayi nadama lokacin da yayanta mata biyu suka ki auruwa har bayan digiri na uku suna gabanta. Don haka su bar Usman ya auri wadda yake so yar gidan mutunci wato gidansu Sarham su bi su da addua. su daina biyewa kishin Madinah sauda dama tana gyara gidanta ne shi Usman ta saka shi a matsala don ta san suna matukar sonta.

    Da waannan Haj Laila ta gyara zancen auren Sumayya da Usman. A wata asabar, a masallacin jumaa na tsohuwar jamiar Bayero aka daura auren SUMAYYAH SHANONO da USMAN SORONDINKI. Kasancewar duk suna birnin Jeddah daga angon har amaryar  kuma Sumayyah na tsakiyar karatu dole iyayen da kakannin ne sukayi yinin bikinsu sukadai. Sumayyah ta koma gidan Bhaiya dakin Hauwa acan aka shafa mata lalle dole Madinah ma ta saki ranta albarkarkacin Sarham da Usman da yae ta mata hidima don ta sa hannu a aurensa. Ita taje ta shirya musu kasaitaccen gidansu a Jeddah ta tsara komai dama dai Madinah ba daga nan ba. yayinda Hauwa ke kula da yaranta da danyen jegonta da kawayen Sumayyah da ke cike a gidan kowa nata shaawar yaran Hauwa da yadda take sabgar kula dasu musamman wajen breast- feeding. Sarham dole ya daga kafa a gidansa sabida hidimar da akeyi kuma shi Abba Prof. ya turowa kudi ya hada da abinda ya tara musamman don auren Sumayyah ya baiwa Madinah ta zabar mata kayan daki daidai karfinsu. Duk da cewa Usman yace baya bukatar komai amma saida suka yi wanda zasu iya kasancewar Usman yana ISDB ne tareda Babansu.

    Watan Hauwa uku kenan da haihuwar Sumayyah yarinyar tayi bul-bul gwanin shaawa haka kamanninta da Sumayyah yayi yawa, a lokacin Hauwa na shekararta ta biyu a (BLaw) Sarham ya gama duk wasu shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aikin ido. Ya saka ranar Litinin 5/5 a matayin ranar da zai shiga da Hauwa tiyata, ya kuma kira waya ya gayawa gida, nasa iyayen dana Hauwa, sannan ya gaya musu itada Madinah.

     Ya roki Madinah wata alfarma data sanyaya mata jiki.

    Na san a policy dinki Munawwarah, babu taimakawa kishiya, amma ina rokon ki ki taya Mardhiyyah kularmin da yaya na, har Allah yasa ayi aikinnan na mahaifiyarsu lafiya a gama, kuma idan Waheedah ta shiga wajen su ki daina cewa Mardiyyah ta daina goya mata su bazata iya daukar su ba sabida girman jikinsu, in ma ta tika su da kasa babu ruwanki yan uwanta ne, kinji ni ko?.

    Mama dama tayi shirin zuwa Umrah a wannan shekarar kasancewar watan Ramadhan ya kama. Don haka ta hau shiri don tuni ta samu visar Umrah. So take ta isa Jeddah kafin ranar da zaa yiwa Hauwa aikin.

    Dr. Madinah ta kai gwauro ta kai mari ana I gobe zaa yiwa Hauwa aikin idanunta, tana fafatawa da zuciyarta da kuma shaidan, a karshe ta rinjayi shaidan din, da taimakon Ubangiji. 

    Ta fuskanci maigidanta Dr. Sarham da ke fitowa daga toilet cikin fararen kayan barci, ya yi wanka ruwa na yarari daga kansa yana yarfewa da santala-satalan hannayensa.

    “Babansu Waheedah, please ina so ka bani dama in shiga cikin ‘team’ din ku, wato likitocin da za su yi wa Hauwa aiki gobe. Albarkacin musulunci. Ina so a yi wannan aikin ladan da ni. I mean it.

    Hawaye ya digo daga kwayar idonta. Ta tuno tarin rashin kyautawarta garesu shida Hauwa, da tarin gorinta ga nakasar Hauwa, yau ga HAUWA-KULU-MISKINIYA-MUSAKA ta cikawa SARHAMU da gayu gida da yaya, don ita ta fahimci abinda su duka hankalinsu ma bai kai ba, a matsayin ta na mace kuma cikakkar likita cewa Hauwa-Kulu wani cikin ne da ita, tana boyewa Sarham wannan karon kada ya kara fasa yi mata aiki. Duk abin da zai dawo mata da Sarham dinta na baya (very jovial) domin ya dan canza mata tun dawowarta gidan, saboda yadda take ja baya da duk wata harka ta iyalinsa, tana so ta dawo dashi yadda yake a baya kuma mai yarda da ita, don haka duk abinda tasan zai faranta masa shi ta ke son yi yanzu. Duk da ta san baa bari a kwashe daidai.

    Ya kama hannunta suka zauna tare a bakin gadonta, ya ce, 

    Ni na dade da sanin Madinah-Munawwarahta mai kirki ce, mai imani ce kuma mai tsoron Allah ce. KISHI ne mara amfani yake sarrafa min ita a baya.

    Ina rokon Allah ya albarkace mu bakidaya ni da ku iyalina, ya hadamin kan yayana ko bayan raina.

    Ni na san ba za ki iya alaka ta jiki da Hauwau ba, sabida kina mata kallon tasgaro ga soyayyarmu, kuma ‘barrier’ ga cikar farin cikinki, wanda ko daya in kin duba ba haka ba ne.

    Ki sa a ranki aurena da Maijiddah rubutaccen alamari ne daga Allah (S.W.T) wanda ni ma ban taba hasashensa ba, sannan ba gazawarki ce ta wani bangare tasa na yi shi ba. 

    Haka nake so duk mata irinki su saka a ransu, sai a samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu da mazajensu.

    Komai Ubangiji ya nufeka da yi, ko Ya rubuta yana cikin kaddararka, hakika sai ya same ka. Addua ba ta canza kaddara amma tana rage tasirinta. 

    Don haka ban auri Hauwa ba sai da na yi addua da istikhara cewa, idan ba alkhairi bace a gare mu, ni da ke kada Allah ya ba ni ikon aurenta.

     Madinah ki yarda ba ki gaza da ni ta kowanne bangare ba, sannan rashin gazawar taki baya nufin shikenan bani da hurumin auren kowa kuma. Hudu Allah ya halattamin. Bayan Hauwa ma Allah Ubangiji ya halatta min wasu biyun sai in ban yi raayi ba, ko ba sa cikin kaddara ta.

    Allah Ubangiji ya yi umarnin a kyautata wa MISKINI da MARAYA a cikinAlqurani, wannan rubutacciyar ayar Ubangiji ce.

    Don haka kyautatawarki ga Hauwa ko akasinta yana cikin mizanin ayyukanki na alkhairi da na sharri. Na gode da kika fara karkata mizanin don ya koma na alkhairi”.

    Madina ta yi maza ta rungume shi tana kuka, ta ce, Wallahi daga yau na tuba da duk abin da nake yi a kanta. Ka bani dama in shiga cikin likitocinta in yi ‘repenting’ kuskurena ko Allah Ya dube ni ya yafe mini.

     Amma ka sani KISHI da kishinka Sarham wani abu ne da har abada ba zan daina ba, saboda ba ni nake sawa raina ba, halitta ne. Alkawari daya iya yi maka shine; zan koyi rike linzaminsa… in dinga controlling dinsa ta hanya mai kyau.

    In ki ka yi hakan, ni kuma na daga miki kafa, ki shige aljanna ba jainja Madinah.

    Ya subhanallahi. In ji Madina tana kara kanainayewa a jikinsa.

    Amma wani hanzari ba gudu ba, bana bukatar taimakon kowanne likita a aikin da zan yi wa Hauwa, ni kadai nayi nazarina kuma nikadai na gano kan matsalar, don haka nikadai zan yi in kika cire (perioperatives) dina da masu allurar tafi da ranka (anaesthethians). Its a ONE MAN JOB!!!

    ****               ****               ****

      

    ASIBITIN SAUDI-GERMAN

RANAR AIKIN IDON HAUWA-KULU 

                  (KARO NA BIYU)

    Dr. Sarham, da sauran masu taimaka maa a yayin tiyata sun zama ready a dakin tiyatar da zaa yiwa Hauwa aikin ido, haka masu allurar anaesthesia. Dr. Madinah Attahiru, ta turo yar uwarta Hauwa Bilyaminu a kan gadon marassa lafiya tana sanye da korayen kayan aiki na wanda zaa yiwa tiyata, haka shima likitan korayen kayanne a jikinsa da hularsu. Bisa umarnin likita Sarham, masu allurar tafi da ranka suka fara, daga nan suka shiga aikinsu ba ka jin tashin komai sai tashin yaren likitanci a yayin surgery na idanu. Kalmomin da su kadai suka san me suke nufi da fadarsu. Da yake sun dade da gano matsalar Hauwa-Kulu tuntuni sun kuma dade da tsara komai daga binciken da suka dade suna gudanarwa akan idon Hauwa nada nan aka gama phacoemulsification surgery din, cikin abinda baifi mintuna 45 ba.

     Ana fatan kwancewa nan da awanni biyu masu zuwa. Zukatan su Mama, Madinah, Sumayyah, Usman, da Mardhiyyah dake gefe goye da baby Sumayyah, ga ‘yan biyu suma a hannunta na hagu da dama tana lallashinsu kamar su fita daga cikin kirazansu with so much high anticipation.

    ****                    ****                     ****

    

        KOFAR DANAGUNDI (KANO)

C

ikin rikicewa da tsananin tashin hankali yake ta trying kiran wayar Dalha ana cewa bata shiga, sai ya koma kiran dansa Jamilu cikin hada uban gumi. Baba zakari kenan cikin gigicewar rasa Dalha babban yaronsa daya tattarawa dukkan jarinsa ya tafi Cotonou domin shigo da atamfofi. Ba wannan ne karo na farko da suka fara wannan sanaar shida Dalha ba sun fara da yi kadan kadan ne har Dalha ya tabbatar Zakari ya gama amincewa da shi kafin yace suyi babban sari na atamfofi da shaddoji kasancewar karamar sallah ta matso.

    Amma yau kwana goma sha biyar ya kasa samun layin Dalha wato tun tafiyarsa. Da ya kasa samun Dalha sai ya koma kiran Jamilu, Jamilu ya daga ya tabbatar masa motarsu Dalha ta kife a bisa binciken da yasa aka yi masa kuma ba abinda ya tsira a motar, kamar yadda babu wata rai data tsira.

     Tsananin gigicewa (bata mutuwar dalha daya shekara kusan 10 yana wahalta masa ba, aah ta kafatanin dukiyarsa da ya tattatara ya damka masa ya tafi da ita ne) tasa ya kama hanyar Singa a kafa, yana tafe yana sambatu, duk nisan kofar Danagundi zuwa kasuwar Singa bai ganshi ba, saboda tashin hankali. 

    Bai yarda da abin da Jamilu ya fada ba shi ya sa ya taka sayyadarsa har Singa, don ya san yana zuwa zai ga Dalha a shago yana fama da kwastomomi yadda suka saba kullum.

    Tun daga nesa yake hango hayakin dake tashi kamar bakin hadari a kasuwar SINGA. Ya kara daga kafa yana fadi a ransa lallai damuna ta zo ba shiri a watan da ba nata ba. irin wannan hadari haka?

    Yana kara matsowa yaga dafifin mutane suna darawa yan kwana-kwana suna wucewa da motar su bayan already wutar tagama cinye rabon sa, ciki har da sashen yan atamfa. A kusa da shi yaji daya daga cikin yaransa yaa gaya masa.

    “Baba Zakari sai hakuri. Haruna ne jiya da yamma ya jona heater a shagonmu, sai ya manta ya tafi gida, kuma a kofin roba ya jona, shi ne heater ta cinye kofin ta kama shagon da wuta”.

     Abinka da wutar dare, ko kafin masu gadin kasuwar su ankara wutar ta lashe shagon Alh. Zakari mai atamfa har ta soma laso makwabtansa.

    Baba Zakari sai kwasar shi akayi a wheel-barrow zuwa gida saboda sumewa yayi a wurin aka tattakeshi a wurin baa sani ba sabida dafifin alumma da kokarinsu na kashe wutar shikuma sai kara kutsawa yake yi har karfin sa ya kare jininsa ya hau, ya fadi a wurin baa kula ba aka yi ta bi ta kansa ana tuntube ana wucewa saida wasu suka daga shi da kyar suka saka a wheel-barror yaran da suka san shi a kasuwar suka tura shi zuwa gidan sa a dan agundi. 

    ****                  ****                    ****

    

    Tundai da suka fahimci ya tsiyace yau kafin sati ya zagayo nbiyu daga cikinmatan da ya auro zawarawa masu kuruciya suka kama gabansu don tunda ya fadi yake jinya har inda nan ke motsi. Biyu sun zauna sabida yaran su da rashin muhalli wato Zainaba da Alto, don ko da yake cikin daularsa aai su baya tsinana musu komai su suke ci da kansu da yaran nasu ta hanyar yan sanaoin cikin gida.

    Jamilu ne kadai yake jigilar kai Baabn nashi asibiti amma duk sauran yaran sun fantsama cikin ganuwa suna sanaar daba, wasu sane wasu kwace, matan kuwa sai addua don sun ki zaman aure sun dabbi maza a unguwar dan agundi.

    Abinci wannan babu a gidan Zakari don matan in sun dafa basa bashi, sunce sanda yana da shi su ya basu? yayana kuwa babu mai lokacinsa. Kashi da fitsari duk akan gadon sa yake yin abinsa don faduwar da yayi ta sabbaba masa lalurar ‘stroke’.

    Jamilu dake tsaye a kansa maaikacin banki ne da in ya tafi aiki kullum sai kusan dare yake dawowa, nan zai shiga hidimar gyarawa uban jiki da wani yaron makwabtansu da yake biya yana kula dashi in baya nan.

    Da Jamilu yaga abin ya kazanta sai ya dauke shi ya mayar asibitin murtala ake kula da shi a bangaren physiotheraphy. 

    Da jimawa can Salele ya gaya masa Hauwa tayi aure da Likita Sarham suna kasar Saudi Arabia.

    Sannan bada jimawa ba sun kara haduwa yake gaya masa Malam Bilyaminu da Inna sundawo gidan su na Badala.

    Haka kawai jikin sa ke gaya masa ciwon mahaifinsa bana tashi bane don haka akwai bukatar ya hada shi da dan uwansa ya nema masa gafara a wurin sa don da karkataccen bakin sa ya gaya masa shi ya kori Bilyaminu daga Kano don ya cinye gonar gadonsu shikadai.

    Haka ya gaya masa shi ya rushe gidan su bayan ya saya biya shi kudin a gaban shaidu da mai unguwa.

    Ba don kuma komai ya rushe gidan ba sai don kada shi Jamilu ya auri Hauwa itama kuma Innar da Hauwan su rasa matsuguni.

    Da Jamilu ya tambayeshi cikin takaici ko meye dalinlinsa na yin duk wannan taasar a ma tsayinsa na musulmi gad an uwansa na jini? Cewa yayi saboda tun suna yara ya lura Bilyaminu ya fishi tauraruwa mai haske ya kuma fishi kashin arziki, duk abinda ya sakawa hannu sai yayi albarka, sannan ana yawan cewa ya fishi kyau a duk inda suka shiga tare.

     Jamilu kuka riris ya rika yi saida ya kwana uku bai dawi inda babansa yake ba.

    A karshe ya tuna shi din dai shi ya haife shi, kuma cikin yaya ashirin da ya Haifa kaf babu mai tsaya masa in bashi din ba.

    Haka ya cigabada kula da shi a asibiti har suka yi wata uku yaron da ke taimakawa Jamilukula da shi din ma ya gaji ya kama gabansa don bai ga alamarBaab Zakari zai tashi ko zaune ba.

    Abubuwa suka damu bawan Allah Jamilu gashi ya kai kudin aure an dawo masa da shi sabida gidan su yarinyar sunyi bincike akan gidan mahaifinsa sun samu labarin da baiyi kama da rayuwar Jamil Zakari ba.

    Don haka sanda Salele ya gaya masa dawowar su Baabn Hauwa gidansu Jamilu ya je har gida ya gaida Baban Hauwa da Inna. Da farko Inna ta tada hankalinta da zuwan Jamilu Malam yace da ita Jamilu duk sanda ya ga dama yazo gidansa, bashida inda yafi wurinsa. Ya kuma ce da bakinsa inama yanada wata yar da ya baiwa Jamilu!

    Wannan kalamai sun saka Jamilu kuka. Gashi dai Allah yayi masa duk wani ludufi da matashi kamarsa yake nema a rayuwa amma baiyi saar mahaifi ba, shiyasa komai na rayuwarsa yaki komawa daidai, musamman ta fuskar aure, ya nema sau biyu ana hana shi. Har hotunan ya;yan Hauwa Jamilu ya gani a wayar Inna nan ma kuka yayi ta yi. Da tuni wadannan zukakan yaya nasa ne ba don halin Babansa ba.

    Duk yaji ya tsani uban nasa, ya rika dakacen INAMA BILYAMINU NE YA HAIFESHI BA ZAKARI BA!

    Tun daga ranar da ya gayawa Malam Bilyaminu halin da mahaifinsa ke ciki, Malam Bilyaminuya salladawa Inna dafa abinci kullum tareda Zakari. In yaso Jamilu ya zo ya dauka ya kai in ya taso banki.

    Inna Safiya uwar Hauwa, bata gardama da umarnin mijinta ko kadan haka take dafa abincin da Baba Zakari yake ci kullum mai dan ruwa-ruwa Jamilu ya kai masa.

     Malam Biyaminu yake baiwa Dr. sarham labarin halin da dan uwansa Zakari yake ciki cikin tarin damuwa, ya kuma nemi shawararsa ko akwai maganin shanyewar barin jiki?

    Dr. sarham yanata jinjina zuciya irin ta wannan bawan Allah yace zan turo abokina Dr. Sammani (Physiotherapist) ne in sha Allahu duk taimakon da ya dace ya bahi zai dinga bashi a gida su baro gadon asibitin Murtala.

    Da farko Jamilu yayi gardama da yaji mijin Hauwa ne zai taimaki Babansa sai ya tuna da Malam Bilyaminu yake Magana bazai yuwu yayi hukunci y ace masa bai masa ba, amma a duniya babu wanda yake kishi irin LIKITA SARHAM!!! 

    Dr. sammani ya cigaba da kula da lafiyar Zakari a gidan sa, kullum yana zuwa yana masa gashin kashi mai kyau. Duk abinda ake bukata Sarham na tura masa daga account dinsa. Inna kuma bata fasa dafa abincin da ya dace da masu lalurarsa kullum a kai masa ba bisa umarnin irin abincin da Dr. Sammani yayi umarnin ya dinga ci.

Cikin watanni uku hannun Zakari ya fara moruwa, ya soma iya atashi zaune har yana sallah daga zaune. Sai Jamilu ya saya masa wheel-chair yake dora shi ya fiddo shi tsakar gida ya sha iska duk sanda ya zo gidan.

Da haka ya lallashi uwargidansa Alto kan ta tuna aljannahrta ta dinga duba lafiyarsa in baya nan bai ce ta dinga bashi komai ba. 

Albarkacin Jamilu malam Bilyaminu yace ya yafewa Zakari amma don Allh Jamilu kada ya kawo masa shi gidansa ko sau daya, kowa yayi rayuwarsa har ta Allah ta cimmasu su duka.

Ranar da anka yiwa Hauwa aikin ido ranar ne Jamilu ya shigo ya tadda gawar mahaifinsa har ta fara kumbura a daki Alto bata sani ba, don yaje seminar ta kwana biyu daga bankinsu.

Dama sai ta ga idon Jamilu ne take dan zagawa dakin da ya tafi kuwa ko kofar dakin bata kallo.

Ya taho gidan Babansa Malam Bilyaminu yana kuka ya gaya masa rasuwar dan uwansa ya kuma roke shi suje ya taya shi suturta shi.

Malam Bilyaminu har cikin kwakwawarsa sai da yaaji mutuwar Zakari, ya soma ambaton innalillahi wa inna ilaihi rajioun. Suna kokarin fita wayarsa tayi kara.

Sarham ne.

An kwance idon KULULU Malam!

Mama ta amshe wayar tace Malam Bilyaminu sada Hauwa da Innnarta..

Duk sun kidima shi, ya rasa ta ina zai fara, janaizar dan uwansa zai tafi ? ko sauraron inda aka kwana a Jeddah da masu tiyatar ido?

Inna ta amshe wayar da sauri jin kukan Hauwa cikin wayar, tace HAUWA-KULU, KULUN MAJADUN, KULUWAR INNNARTA yaya akayi ne?

Cikin kuka Hauwa tace tana rufe ido daga kallon dariyar da Mama take mata, tace cikin rada kada Mama taji, wadda ke manna mata Sumayya cinyarta tana ta canyara kuka tana neman nonon uwarta.

Inna dama ashe! Ashe-Ashe haka LIKITAN KI YAKE DA KYAU?? Ashe haka yake murmushinsa? Ashe haka yake komawa in yana dariya? 

Wayar ta subuce daga hannun Inna domin faduwa tayi a wurin cikin sujjadah. Tun bat agama jin arshen bayanin Hauwa ba, na cewa in ta cire gilashin da aka kara yi mata yanzu bata gane fuskar kowa, tana gani ne da taimakon gilashin.

****                      ****                      ****

          SHEKARU MASU YAWA A GABA

(HAUWA BILYAMINU DISABILITY SUPPORT CENTER).

    Shine sunan NGO din da Hauwa ta bude a shekarun girmanta. Bayan kammala LLB, BL, da LLM. Da yaransu maza da mata har guda bakwai tareda PACESETTER dinta. Barrister Hauwa Bilyaminu, ta bude (DISABILITY SUPPORT CENTER) da sunanta, domin tallafawa mata da yara masu nakasar idanu, inda ta zama jagora ga mutane masu nakasa kowacce iri ce musamman ta ido, tana coaching, tana mentoring dinsu akan harkar ilmi da cigabansu. Sannan tana ‘advocating ga gwamnati da alumma kan dabbaqa ‘disability right, inclusion and justice for people with disabilities’.

Sannan kuma cibiyar nayi wa masu bukata ta musamman training na skills acquisition daban-daban musamman akan sanaa, ilmin naura mai kwakwalwa ga masu matsalar gani, da koyar dasu rubutu da karatun Braille da amfani da assistive technology da sauran ‘soft skills’ da zasu taimaka musu. Har a hankali cibiyar ta soma samun tallafi daga International Organizations irin su Sight-savers, AGILE, PERL da Commonwealth. 

    Shekarun HAUWA-KULU (50) a duniya suka bar Jeddah, wato da tafiya tayi tafiya Dr. Sarham da iyalinsa bakidaya suka dungumo suka dawo gida Najeriya bayan yayi retire da asibitin Saudi-German, inda suka sauka a gidan su na tarihi dake unguwar Rijiyar Zaki suka cigaba da rayuwar kauna da soyayya da kula da yayan su, a lokacin Dr. Sarham ya mallaki asibitin ido nasa na kashin kansa, hakan kuma bai sa ya bar aiki da gwamnati ba. Da yaransu goma cur; na Hauwa 7 na Dr. Madinah 3.

     A lokacin Hauwa Bilyaminu ta zama UN Volunteer akan Disability Support and Inclusion, sannan ta zama wakiliyar dabbaqa ‘Sustainable Development Goals’ a kasar Najeriya.

    -TAKORI

    Na bibiyi labarin Barr. Hauwa-Kulu ne har zuwa ranar yau ta taron Meet&Greet, wadda hadakar kungiyoyi masu zama kansu suka shirya domin karramata da fito da ita duniya ta ganta, bayan buya da take a bayan fage tana ayyukan tallafawa nakasassu, da taya ta murnar cika shekarun haihuwarta 50 da shekarun aurenta 31, sannan da karbar ragamar jagorancin kungiyar lauyoyi ta kasa da aka fi sani da Nigerian Bar Association

    -SUMAYYAH ABDULKADIR

        22/10/2023

    07030137870

    (WHTSP 




Post a Comment

0 Comments