TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 89-90

 _Naji dadin ganin comment din ku, hakan ya fahimtar dani kuna bibibiiyar wannan labarin, ina muku fatan alkhairi a duk in da ku ke_.







89-90



Momi ta k'ara kiran Dr karo na biyu akan maganar shi da Meema.



San da yaje gidan ne ya ba ta hak'uri akan ta k'ara mishi lokaci.



Momi ta amince da rok'on shi akan k'arin lokacin da ya nema amma akan sharad'in Dadin su Dr zai je gurin Dadin Meema suyi magana akan bikin.



Dr ya amince da hakan.



Bayan Dadi ya dawo ne Momi ta sanar dashi halin da ake ciki.



Da farko Dadi bai amince da maganar ba saboda yasan Dr ba ya son Meema da aure, jin cewa Dr ya amince yasa ya kira shi akan maganar ya kuma tabbatar mishi da amincewar shi.



Ba a d'au lokaci ba Dadin su Dr ya nemi Dadin Meema akan maganar, sun yake nan ba da dad'ewa ba sai ayi fixing d'in bikin.




Lokacin da Momi ta fad'a ma su Hanan maganar auren Meema da Dr Hanan ce kad'ai ta nuna jin dad'in ta amma ita Farida ba ta son Dr ya auri Meema saboda wayewar ta tayi yawa.



Yanzu fitar Dr ya canza salo saboda yanzu in ya fita wani lokacin sai nayi bacci yake dawo wa, tun ina nuna b'acin raina har na dawo na zuba mishi ido ba dan raina ba ya b'aci ba, sai dan ba ni da yadda zan yi akan Dr.



 Hakan yasa damuwa ta fara min yawa, gashi har yanzu ban samu cikin da nake fatan samu ba.



Tambayar Dr nayi akan zan je gidan Anisa, cikin sa'a ya bar ni.



Shiryawa nayi na shiga mota ta na nufi gidan Yaya Khalil.



San da naje gidan yaya Khalil  ba ya nan.



Zama nayi muka sha hira da Anisa yayin da Amatur-Rahman ke hannu na ina mata wasa.



A cikin hirar ne Anisa ta kalle ni kana ta kira suna na da cewa "Fatima".



D'agowa nayi na kalle ta ba tare da na amsa mata ba.



" Me yake damun ki Fatima" Anisa ta tambaye ni.



Kallon mamaki na mata kana na ce "Me kika gani Anisa?".



" Naga abubuwa da dama a fuskar ki da nake so ki fad'a min" cewar Anisa.



Cikin wasa na ce "Idon ki bai nuna miki gaskiya ba dan ba abin da yake damu na".



Anisa ce ta ce "Fatima a ture maganar wasa, kin san na san ki ciki da waje, kar ki manta tun muna yara muke tare har zuwa yanzu, ina iya fahimta yanayin ki a kowane lokaci, yanayin ki ya nuna something is bordering you wanda ba kya so a sani, ba ma ni ba Fatima, duk wanda ya ganki yasan kina cikin damuwa, bazan matsa miki ki fad'a min damuwar ki ba, sai dai ina so ki rage ma kan ki tunani, sannan Fatima ki k'ara hak'uri a dukkan jarabawar da Allah zai miki, sai ki ga a dalilin wannan hak'urin da kika yi Allah ya biya miki buk'atun ki".



A yanda na fahimci maganar Anisa tana min magana ne akan rashin samun cikin da ban yi ba, ba ta san bayan wannan ba akwai wata damuwar halin da Dr yasa ni a ciki da na rasa yadda zan b'ullo mishi akan fitar da yake yi, ina da tabbacin in har na fad'a ma Anisa za ta bani shawara wacce ta dace, sai dai nasan in Anisa taji wannan maganar za ta tuno min baya ne akan yadda a kullum nake yabon Dr da cewa ina da tabbaci a kanshi, gwara in danne matsala ta har lokacin da komai zai zama normal tsakani na da Dr.



Murmushi nayi kana na ce "Na gode Anisa da shawarar ki gare ni".



Ita ma Murmushin ta mayar min.



Haka muka ci gaba da Hira har Yaya Khalil ya dawo muka gaisa dashi kana na musu sallama na tafi.



Haka san da naje gidan Anty Jidderh ita ma haka ta tambaye ni me yake damu na, sai da na ce mata ba komai, girgiza kai kawai tayi alamar ba ta yarda da abin da na fad'a ba sannan ta canza wata hirar.




A can b'angaren su Yaya Faruk kuwa Khadijah ce ke fama da rashin lafiya, hakan yasa yaya Faruk ya kaita asibiti, gwajin farko aka tabbatar mishi tana d'auke da ciki.



Farin ciki kasa b'oyuwa yayi akan fuskar Dr jin wannan labarin.



Tun a asibiti Yaya Faruk ya rungume ta yana murnar samun baby da za su yi.



Ita kuwa Khadijah sai faman sunkuyar da kai take yi saboda kunya.



Da suka dawo gida haka ya dinga tambayar ta ko akwai abin da take so ya mata.



Motsi kad'an za tayi zai tambaye ta ko akwai inda yake mata ciwo ne.



Ita abin har dariya yake ba ta ganin yadda Yaya Faruk yake mata.



Kusa da ita Yaya Faruk ya zo ya zauna ya kwantar da ita akan cinyar shi.



Cikin cool voice d'in shi ya ce "Khadijah kin sa ni a farin ciki, ban san da me zan saka miki ba, na da 'yan month za ki bani baby, ki fad'a min abin da kike so in miki ko miye shi in har bai fi k'arfi na ba zan miki shi".



Wannan maganar da Yaya Faruk yayi yasa taji kamar ta ce mishi ya ce yana son ta, ita ta na ganin in ya fad'a mata wannan Kalmar ta ishe ta ba sai ya ba ta komai ba, saboda yadda take jin son Yaya Faruk a ranta ba tasan yadda za ta fasalta shi ba, tasan son Yaya Faruk ya gama dabaibayi a ranta da dukkan sassan jikin ta gaba d'aya.



Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah ba ki ce komai ba, ko ba kya so in miki kyauta ne kamar yadda za ki min babbar kyauta da baby da Allah ya bamu a cikin ki".



"Duk abin da ka ga ya dace da ni Yaya Faruk " cewar Khadijah.



Tsadadden Murmushi Yaya Faruk yayi kana a hankali ya ce "I Love you Khadijah......".



Kallon mamaki Khadijah ta bi shi dashi saboda jin Kalmar da ba yayi tsammanin ta a yanzu ba a gurin Yaya Faruk.



Lallai ta zama tauraruwa tun da har ta samu Kalmar da ta ke jira daga gurin gwarzon mijin ta.



Ba tasan yadda za ta bayyana farin cikin da take ciki ba.



Ba abin da za tayi da ya wuce tayi ma Allah godiya da ya ba ta miji d'aya tamkar da goma.



D'aga mata gira yayi kana ya kanne mata ido ya ce " Are you surprise?".



Murmushi kawai tayi kana ta girgiza mishi kai alamar a'ah.



Hannun ta ya rik'e kana Yaya Faruk ya ce " I mean my word Khadijah, Ina son ki Khadijah kamar yadda kika ji na fad'a, ki daina mamakin jin wannan Kalmar daga guri na, kin cancanci haka a guri na, kina min duk abin da nake so, kina son ganin farin ciki na da nuna kulawar ki akan 'yan uwa na da duk abin da ya shafe ni, Khadijah zan iya miki komai dan na faranta miki saboda a kullum kike son faranta min".



"Yaya Faruk na gode da yabawar ka gare ni, ba abin da zan ce maka sai dai Allah ya ci gaba da taimakon ka da yi maka jagora a dukkan lamarin ka".



Murmushi yayi ya ce " Amin Khadijah"



Cikin tsokana ya ce "Ni ba ki fad'a min kina so na ba Khadijah".



Jikin shi ta k'ara shigewa a hankali ta ce " I love you Yaya Faruk very much".



D'ago fuskar ta yayi ya ce "Really?".



D'aga mishi kai tayi alamar Eh.



Rungume ta yayi yana jin wani farin ciki na yawo a dukkan sassan jikin shi, a wani b'angaren yana gode ma Allah da ya kawo mishi Khadijah a rayuwar shi.



San da su Yaya Mus'ab suka zo duba Nana haka Maryam ta dinga tsokanar shi yana biye mata.



Dr ya sami Hutu a gurin aikin shi Wanda yayi daidai da shigar Khadijah next class, saboda haka ne aka basu hutu dan new student su fara registration d'in su.



Ganin ita ma Khadijah na hutu ne yasa Yaya Faruk suka shirya suka tawo Kaduna dan su k'arasa hutun su a can.





Yau da daddare in zaune a falo na kasa bacci saboda har yanzu ban ji motsin dawowar Dr ba, ga shiru da gidan yayi, in ban da mai gadi da yake can gefen shi, ba motsin kowa da nake ji.



Jefi-Jefi na kan kalli agogo na goge hawayen da yake zubo min.



Tagumi nayi ina tunanin rayuwa mai juya wa a ko wane lokaci, in ba haka ba mai nayi ma Dr da yake min sakayya irin wannan.



Guraren k'arfe 10 na ji bud'e gate d'in da naji ne ya tabbatar min Dr ne ya dawo.



Slice window na je na bud'e na hango Dr yayi parking d'in motar shi a parking space.



Dawowa nayi na zauna ina jiran shigowar Dr.



Bud'e k'ofar da yayi ne yasa na maida hankali na bakin k'ofar.



Sallama yayi kana ya k'araso in da nake zaune ya zauna.



Amsa mishi sallamar nayi ina bin shi da kallon tuhuma.



" Ashe ba ki yi bacci ba Zarah" Dr ya fad'a.



"Kana tunanin nayi bacci ne shi yasa ka dawo at this time Dr" na fad'a cikin b'acin rai.



Dr ne ya ce "Sorry Zarah, a asibiti ne wani emergency work ya tashi, shi yasa ki ka ga ban dawo da wuri ba, da na so na kwana a can ne dan ban za ci za mu gama aikin da wuri haka ba".



Murmushin takaici nayi ganin yadda Dr yake so ya raina min hankali wai daga gurin aiki yake.



"Dr jiki na bai bani daga gurin aiki kake ba, na fi gamsuwa da ka je b'oyayyar unguwar da kake zuwa amma ba gurin aiki ba, a duk lokacin da wani important work ya taso maka ko aka kawo emergency patient ka na kira na a waya ka fad'a min ba za ka dawo da wuri ba, amma me yasa wannan karan ba ka kira ni ka fad'a min ba".



Cikin kwantar da murya Dr ya ce "Believe me Zarah, daga asibiti nake, kin san aikin likita bai da specific time na kan shi".



Kuka na fara yi mai tsuma rai na ce "Dr you have change, na fara gajiya da sababbin halayen da kake zuwa min dasu".



Hawayen da yake zuba a idanu na ya fara goge min yasa lallashi na.



Sweet words d'in da Dr ke fad'a min ne yasa na hak'ura na da ina kukan da nake yi.



Ko da na tashi zan zubo mishi abinci cewa yayi in bar shi ya k'oshi, hakan ya tabbatar min da ba daga asibiti yake ba.



Hannu na ya kama muka tafi side d'in shi muka kwanta.



Washegari da daddare ina kwance a jikin Dr muna hira wayar shi ta fara ruri alamar kira ya shigo.



Wayar tafi kusa dani, hakan yasa na sa hannu na d'auki wayar dan na mik'a mishi.



Sunan Meema na gani a jikin screen d'in yana yawo.



Mik'a mishi wayar nayi ba tare da na ce mishi komai ba.



Amsar wayar yayi yaga sunan Meema ya ajiye wayar ba tare da ya d'auka ba.



Tambayar da tazo min shine "Me yasa Dr ya k'i d'aukan wayar a gaba na".



Jiki na yana bani akwai wata a k'asa da Dr ba ya  so in sani.



Na gaji da wannan rainin hankalin da Meema take min na kiran Dr a ko wane lokaci ta gadama, kiran da take mishi ko su Hanan ba za mishi irin shi.



"Dr me yasa kak'i d'auka" Na watso mishi tambaya.



"Meema ce, ta cika matsawa mutum" Dr ya amsa min.



In a serious speaking na ce "Dr hak'uri na ya k'are akan kiran da Meema take maka, ban ga dalilin da za tayi ta kiran ka ba day and night, in wani abu take so ta fad'a maka me yasa ba za ta bari ku had'u ba, ka dakatar da ita ko kuma ka bari in ka fita sai kuyi ta wayar Ku a waje, I can't tolerate it anymore".



Kallo Dr ya bi ni dashi kana ya ce " Zan mata magana".



"That will be better" na fad'a.



Ina gama fad'ar haka na tashi na bar gurin.





Yau muna zaune da daddare aka kira Dr a waya ana neman shi a asibiti, an kawo wani patient emergency, hakan yasa ya tashi ya tafi.




Sai bayan tafiyar shi ne na ga wayar shi a inda ya tashi.



Hasken da naga wayar shi nayi ne yasa na tashi na d'akko wayar.



Sunan Meema na gani a jikin screen d'in.



Wani dogon tsaki nayi kana na ajiye wayar.



Ba a jima ba sai ga text ya shigo na Meema.



Kamar ka bud'e text d'in amma zuciya ta sai ingiza ni take yi akan in bud'e in ga mai ta turo mishi.



Shiga inbox din nayi na fara cin karo da messages din Meema take turo ma Dr.



Yawanci love messages ne da na greetings take turo mishi.



Shiga sent message nayi ban ga wasu reply da Dr yayi ma Meema ba, sai dan kadan na greetings da ya mata reply da ta turo mishi.



Ba wanda ya fi daga min hankali a cikin messages din sai wanda Meema ta turo ma Dr tana pleading din shi akan ya su ma Dad magana a yi fixing din bikin su tun da ya amince zai aure ta. 



Hannu na ne ya kama rawa da wasu hawaye masu zafi da suka fara zubo min a dalilin message d'in da na ga Meema ta turo mishi.



Tambayar da na fara yi ma kaina shine Yaushe Dr ya amince da maganar auren Meema ni ban sani ba? Me yasa a kullum na tuhume shi akan Meema yake nuna min cewa babu wata alaka ta soyayya a tsakanin su da ta wuce brother and sister?



Kenan Meema na da tabbacin cewa Dr zai aure ta shi yasa take kara jaddada min cewa sai ta auri Dr nake daukan hakan a matsayin wasa.



Kenan duk wannan fitar da Dr yake yi gurin Meema yake zuwa ni ina nan a zaune ban sani ba, shi yasa in zai fita yake cin kwalliya sannan in na tambayeshi yace min wata unguwa zai je da na rasa sanin wace unguwa ce wannan.




"Ashe ni ce suka maida mara wayau da suka b'ullo min ta haka".



Kuka na fara yi mai cin rai da kona zuciya akan auran da Dr yake shirin yi da Meema.



"Why Dr?" na fada a fili kamar Dr yana gurin.



"Me yasa Dr zai min irin wannan mummunar sakayyar duk kuwa da irin son da nake mishi?".



"Ashe laifi ne dan ka nuna ma namiji so da zai yi amfani da wannan damar yana maka abin da yake so?".




Kalamen su Anty Jiddarh da Anisa da Aisha ne suka fara min yawo a kaina akan cewa in rage makauniyar soyayyar da nake nuna ma Dr dan wataran da ita zai yi amfani yam n abin da zai dade yana min ciwo.



A lokacin ban dauki maganar su da mahimmanci ba saboda ina ganin suna adawa da auren na daDr ne, sai gashi Dr ya min abubuwa da dama da suke sa ni a cikin damuwa. 



Ciki kuwa har da pills din da ya bani wanda nake da tabbacin a dalilin shi ne har yanzu ban samu ciki ba duk da nasan haihuwa lokaci ce, amma saboda son Dr ya rufe min ido yasa na yi saurin manta abin da ya min da yafe mishi saboda nasan yana da dalilin yin hakan a kaina, sai gashi yana shirin sa zuciya ta da buga a dalilin auren da yake niyyar yi da Meema.



Ni kaina ban san wani irin kishi nake ma Dr ba saboda nasan duk son shin e ya jawo min haka, ba na jin zan iya jure wa in ga Dr da wata a matsayin kishiya ta, ba zan iya jurar sharing din Dr da wata ya mace ba,

 kishin ma wai a ce da Meema da muke takun saka da ita.



A wannan karan ina jin zamu iya fito na fito Dr akan auren da yake shirin yi ba tare da sani na ba, ni ya dauki pills ya bani, ga family planning da yasa nayi, gashi har yanzu ban sami ciki ba, sannan yana kokarin shigo da wata, nasan duk yadda Dr yake da tsarin turawa wataran zai ajiye wannan raayin ya bukaci haihuwa, idan ni kuma har lokacin ban samu haihuwa ba na san zai bukaci haihuwa daga gurin Meema, a lokacin ni kuma zan zama y'ar kallo.



Da kyar na iya samu na tashi daga gurin na koma cikin daki na.



Washe gari ko da na hada breakfast da kyar na iya daurewa na kai ruwan shayi baki na saboda yadda na ji baki na yana min daci, bacin rai ne kawai a tattare dani da haushin Dr da nake ji.



A gefe guda kuma tsanar Meema ce ta ke yawo a raina saboda yadda take so ta yi ma rayuwa ta karan tsaye ta hanyar auren Dr.



Da yamma sai ga Dr ya dawo daga aiki da faraar shi ya tare ni.



Daurewa nayi na ari murmushi na tarbe shi duk da yadda nake jin zuciya ta na min zafi.



Ba na son in yi saurin yanke hukunci sai na samu hujjar da zan gabatar mishi da ita, nasan yanzu in na mishi maganar zai iya musa min akan cewa ni ce nake zargin haka.



Haka na daure na mishi duk abin da ya kamata, amma shi kanshi ya fahimci akwai abin da yake damuna da har sai da ya tambaye ni.



Nunar mishi nayi da ba abin da yake damu na, kawai dai ina ji na so weak ne.



Ranar na taki sa'a Dr bai fita ba, sai da ya d'auki kusan two weeks bai fita da daddare ba.




Wata Ranar Talata Dr ya dawo aiki da wuri, ranar na ji  sun yi waya da Momi, ban san dai maganar da suke yi ba, na ji dai yana ce mata bai samun lokaci ne amma in ya samu lokaci zai je.



Da daddare wani irin bak'in ciki ne ya kama ni da wani irin kishin Dr da hakan ya nuna a fuska ta, tuni fuskata ta canza zuwa b'acin rai.



Yau na shirya ma tunkarar Dr mu yi wacce za muyi dashi, ba zan juri d'aukar rainin hankalin da yake min.



Kusa dani ya zo ya zauna, in ban da k'amshi ba abin da ke tashi.



Jin zuciya ta nake tana tafarfasa, yanzu duk wannan kwalliya da wannan k'amshin duk Meema yayi ms wa.



"Zarah ba ri in je gidan su Mema mu gaisa da su Dad, kwana biyu ban samu time na je ba" cewar Dr.



Lallai yau na tabbatar da Dr ya maida ni k'aramar Yarinya mara wayau wacce ba tasan me duniya ke ciki, amma zan nuna mishi na wuce a raina min hankali, nasan me Duniya ke ciki.



Cikin d'aura fuska na ce " Za ka gaida su Dadi ko za ka ga Meema".



Murmushi yayi kana ya ce "In ban da abin ki Zarah, tun da gidan su zani kin san dole mu had'u da Meema".



Mik'e wa yayi had'e da fad'in " Sai na dawo, i will not take long time".



Ya kusa kai wa bakin k'ofa nayi saurin mik'ewa na sha gaban shi, fuskar nan tawa ba fara'a a cikin ta.



Mamaki ne ya kama Dr ganin yanda na zo na tsaya a gaban shi ya ce "ya aka yi ne Zarah, zan fita kin zo kin tare min hanya".



" Dr ban yarda da fitar nan da za ka yi ba, saboda haka ka fasa fitar nan da za kayi" na fad'a cikin d'aure fuska.



"What do you mean Zarah da za ki ce in fasa fita?" Dr ya tambaye ni.



"Yanda ka ji na fad'a haka nake nufi Dr" na fad'a.



"Saboda me ba zan fita ba?" Dr ya sake tambaya ta.



Kai na tsaye na ce "Saboda na gaji da yawo da hankalin da kake min da kuma mayar dani yarinya da kake yi wacce ba tasan abin da duniyar ke ciki ba".



Ran Dr ne ya fara b'aci da yanda na ke mishi magana, dan haka shima cikin fad'a ya ce " Look Zarah, i don't want any trouble, bani hanya in wuce".



Ni ce na ce na ce "Dr I mean what i  said, yau ina son gane matsayina a gurin ka".



Dr ne ya ce " Zarah wai me ya faru ne kike irin wannan maganar, pls ki ajiye wannan maganar da kike yi, ki bari in na je na dawo sai ki fad'a min me yake faruwa". 



"Ka na d'auka maganar da nake yi da wasa nake yi, wlh Dr fitar ka gidan nan na nufin neman rashin zaman lafiya a gidan nan, ko kana sha ban san abin da yake faruwa tsakanin ka da Meema kamar yadda a kullum kake son b'oye min me ke tsakanin ku, a duk lokacin da na maka tambaya akan Meema amsa d'aya ka ke bani cewa ba soyayya a tsakanin ku, ka d'auke ta ne a matsayin k'anwa, duk abin da aka yi shi a rashin gaskiya duk daren dad'ewa sai ya bayyana, na gano cewa fitar daren da kake yi gurin Meema kake zuwa a matsayin unguwa da ka ce min kana zuwa, ni kuma ka bar ni in maka jiran gida, to Dr in ba son Meema  ka ke yi ba amma ai kana shirin auren ta ko?" Na k'arasa maganar da tambayar Dr.



Mamaki ne ya kama Dr da har hakan ya nuna a fuskar shi.



Bi na kawai yake da kallo saboda mamakin jin maganganun da na fad'a mishi.



Jin bai bani amsa ta Ba yasa nayi murmushin takaici na ce "Me yasa kayi shiru Dr? kasan duk abin da na fad'a gaskiya ne, shi yasa ka kasa bud'e bakinka ka kare kan ka, Dr zan iya maka uzuri ko yafiya a duk abin da za ka min amma ba zan maka wannan alfarmar ba gurin yi min kishiya ba, kishiyar ma Meema wacce kasan ba ma shiri da ita".



Nasan yau Dr yayi mamakin maganganun da na fad'a mishi, saboda a ko yaushe yana ganin zan iya hak'uri a duk abin da ya min.



Cikin lallashi Dr ya ce " Zarah dole ki d'auki k'addara a yanda tazo domin auren Meema zan yi, abin da yasa ban fad'a mi ki ba saboda ba na so in d'aga miki hankali, amma tun da kin gano auren ta zan yi kin ga no need in k'ara b'oye mi ki".



Meema nasan kina so na, dole ne kuma ki yi kishi na, wannan auren zan yi shi ne dan tausayin Meema da kuma umarnin da Momi ta bani akan in auri Meema, pls Zarah am sorry".



Duk wannan maganganun da Dr yake yi  kamar yana sa mashi yana caccaka min a cikin zuciya ta haka nake ji, wani irin b'acin rai na ke ji yana ziyarta ta a lokacin, wai ni Dr zai kalli ido na  ya ce min zai auri Meema ne dan tausaya mata da yake yi da kuma umarni da Momin shi ta bashi akan ya auri Meema.



Wasu hawaye ne suka fara zubo min ba tsayawa.



Baki na ne ya kama rawa saboda kukan da yake son tawo min.



Kallon takaici nayi ma Dr kana na ce "Me...kake...nufi...da...wannan maganar...da...ka...fad'a...min..cewa...za...ka...auri Meema...saboda...tausayin...ta...da...umarnin...Mom...".



" Wannan Dalilin da na fad'a miki haka yake Zarah, apart from that ban da wani dalili da zai sa in auri Meema" Cewar Dr.



"Kenan yanzu Dr auran Meema za kayi kenan..." Na k'arasa maganar da fashewa da kuka.



"Ya zaman min dole in aure ta Zarah saboda umarni Mom ta bani" Dr ya fad'a.



"Dr dama can kayi niyar auren ta, da kake cewa saboda Mom za ka aure ta, idan ba ka yi niyya ba Momi za ta maka dole ne" na fad'a cikin shashshek'ar kuka.



Dr ne ya ce "Zarah ba zan iya musa wa Mom duk abin da ta buk'ace ni da nayi ba, shi yasa zan auri Meema".



Dr ba ka isa ka auri Meemba, in kuma ka ce sai ka aure ta sai dai ka zab'a ko ni ko Meema".



Tak'aitaccen murmushi Dr yayi ya ce " Zarah ke zab'i na ce, Meema kuma zabdamuwam ce, kin ga kenan dukkan ku zan zab'a".



Dr daman akwai ranar da za ta zo ka min irin wannan sakayyar, duk irin soyayyar da na nuna maka da halaccin da na maka amma sakayyar da za ka min kenan, a dalilin kishin ka da son da na ke maka yasa zan Shiga wani hali idan ka auri Meema amma shine Dr kake fad'a min dukkan mu za ka za'ba, Dr kana kallon yadda tun kafin auren ka na samu matsala da iyaye na da y'an uwa na akan auran ka da nake son yi duk da d'an uwa na da yake matuk'ar so na amma na zab'e ka na k'i auren shi, a dalilin auren ka na shiga damuwa duk na jure saboda ina tunanin in na aure ka za ka maye min gurbi da farin cikin da na rasa a lokacin za ka kuma rik'e ni amana da yarda, ashe ni ce nake nawa wautar ban sani ba, sai gashi ka nuna min duk ba zan sami hakan a wajen ka ba" na k'arasa maganar da k'ara sautin kuka na.



Zarah ba zan biye miki ba saboda ina son ki sai in k'i yi ma Momi biyayya?, da kike cewa kin zab'e ni akan d'an uwan ki ina ce saboda son da kike min ne, Zarah ni ban ce kar ki yi ma iyayen ki biyayya a kaina ba, nasan dai na ce ki nemar mana mafita akan yadda za mu mallaki junan mu, nasan tabbas Zarah kin nuna min so da ba kowace mace ba ce za ta iya nuna min ba tun da har kika zab'i farin ciki na akan ki bi umarnin iyayen ki, tabbas duk wacce tayi haka ta zama jaruma a soyayya, shi yasa nima ba zan yi irin kuskuren ki ba Zarah, dan haka ne ma yasa zan ma Momi biyayya in auri Meema domin yi wa iyaye biyayya nasa mutum ya samu farin ciki a rayuwar sa da ci gaban sa".



Ji nayi kukan da na ke yi ya tsaya cak sakamakon maganganun da Dr ya fad'a min.



jijiyoyin jiki na ke na ji sun daina aiki, jiki na yayi wani irin sanyi wanda ba na jin zan iya wani k'wak'k'waran motsi a gurin, ko idona na kasa motsa shi.



Wani abu ne na ji ya tokare min makoshi.



Yau ni Dr yake wa jirwaye mai kamar wanka akan k'in bin umarnin su Abbu da ban da ban yi ba duk da a dalilin shi yasa na k'i auran Yaya Faruk d'in da kuma shawarar shi da na bi dan in ga na mallake shi a matsayin miji, sai gashi wai yau ni Dr yake goranta mawa akan ban yi ma su Abbu biyayya ba, ban tab'a zaton Dr zai min wannan maganar ba, sai gashi yau a dalilin auren Meema Dr ya goranta min, ta yaya zanyi farin ciki da wannan auren da zai yi? 



Ko ina a jiki na rawa yake yi, durk'ushewa nayi a gurin na fashe da wani matsanancin kuka.



Cikin kuka na ce "Dr na gode da tunasar dani abin da na manta a baya, wannan maganar da ka min ta sa na d'auki wani darasi na rayuwa, hakan da ka fad'a min yasa na gane kuskuren da nayi a baya, nasan ba komai ya ja min haka ba illah Makauniyar Soyayya da na nuna maka wanda daman irin ta take jawo wa mutum danasani, yau ni Dr kake goranta ma wa akan son da na nuna maka,  na gode Dr..." Na k'arasa maganar cikin shak'ewar murya sakamakon kukan da ya tokare min a mak'oshi".



Da k'yar na iya tashi na ja k'afa ta saboda nauyin da k'afa ta tayi min.



Ina shiga d'aki na zauna a k'asan rug na saki wani kuka mai ban tausayi.



Jin kaina nake yi kamar zai tsage saboda ciwon da yake min.



Ban San tsawon lokacin da na d'auka ba a zaune ina kuka.



Maganganun da Dr ya fad'a min su suke min yawo a k'wak'walwata.



Sai a yanzu na gano kuskuren da nayi a baya wanda a da ban tab'a hango zai zaman min k'alubale ba, sai a yanzu na gano kuskuren da na tafka a baya da ban bi abin da su Ummu da Abbu da sauran mutane suke hango min ba.



"Me ya hana ni yi musu biyayya in auri yaya Faruk ko sa da k'in shi zai iya ajalina?".



"Me yasa ban faranta musu ransu ba a lokacin da suka buk'aci in musu abin da suke so duk da nasan ba za su tab'a zab'a min abin da zai cutar dani".



"Me yasa duk son da iyaye na suka nuna min nima ban yi k'ok'ari na faranta musu da abin da suke so ba?".



Duk wannan tambayoyin da nayi ma kaina nasan ba ni da buk'atar amsan su dan nayi wannan tunanin ne a lokacin da yake neman k'ure min.



Nasan duk wannan misunderstanding din da muke samu da Dr har da rashin d'aukar magar su Abbu ya jawo min da hakk'in Yaya Faruk da ya nuna min soyayya ta gaskiya amma na k'i auren shi.



Gashi yanzu ina fuskantar k'alubale a zamantakewar mu da Dr, ya kuma zaman min dole in yi hak'uri da duk abin da zai min ko zai fad'a min tun da ni na ce na ji na gani.



Wannan abin da Dr ya min ya dasa jin haushin shi, na kuma sa ma raina a shirye nake da fuskantar duk wani hukunci sa da zai yanke min in dai akan maganar auren Meema ne, ba zan bari ya auri Meema ba, in kuwa har ya ce sai ya aure ta to hakan na nufin zaman lafiya a tsakanin mu ya k'are.



Dole gobe Dr ya tsaya mu tsayar da mafita a tsakanin mu.



Ranar nayi kukan da na dad'e ban yi irin shi ba.



Ko sa da na kwanta ban yi baccin dad'i ba.



Washegari da ciwon kai na tashi, gashi ba ni da magani a side d'ina, first aid box yana side d'in Dr.



A yadda nake jin zuciya ta game da Dr ba na jin zan iya zuwa side d'in shi in d'auki magani in sha.



Haka na ci gaba da kwanciya duk da ba bacci nake yi ba.



Sai da na d'auki lokaci a kwance kana na tashi naje na dama kunun gyad'a na sha.



Wanka na shiga nayi na nemi simple dress na sa, ko mai ban tsaya shafawa ba na koma na kwanta.



Sallah kawai nake tashi na ke yi kana in koma in kwanta.



Sai wajen yamma na ji kaina ya min sauk'i,  tashi na yi na gyara gidan sannan na je na d'aura simple food.



Ko da na gama girkin na ci, d'aki na koma na ci gaba tunani.



Gaba d'aya na rasa abin da yake min dad'i a raina.



Har zuwa dare ban k'ara fita falo ba.



Dr ne yayi sallama ya shigo d'akin.



Tun da ya shigo na zuba mishi ido ina kallon shi, ji nake yi kamar a yanzu ne yake fad'a min zafafan kalamen da ya fad'a min a jiya.



Wasu hawaye ne naji suna k'ok'arin zubo min, saurin maida su nayi.



Kusa dani ya zo ya zauna yana kallo na.



Kau da kaina nayi na juya wani b'angaren saboda yadda naji raina na k'ara min zafi.



Shiru ne ya ratsa d'akin  kafin Dr yayi k'ok'arin kau da shirun da cewa "Zarah am sorry".



Murmushin yak'e nayi na ce " Sorry for what Dr".



Cikin sanyin murya Dr ya ce "Zarah I know i  have hurt you, is a mistake".



" Dr ni ba ka min komai ba, abin da ka fad'a min kamata yayi in gode maka saboda ka tunasar dani abin da na manta ne, saboda haka kar ka da mu" na fad'a.



Duk yadda Dr yaso in tsaya mu fahimci juna ban saurare shi ba, haka ya gaji da zama ya tashi ya tafi side d'in shi.



Tun daga wannan ranar muka fara samin sab'ani da Dr.



Sai da muka kai kwana goma a haka kullum sab'anin mu gaba yake yi, duk yadda na nuna b'acin raina akan Dr ya janye maganar auran Meema amma Dr ban ga alamar janyewar shi ba, hakan yasa zaman mu yak'i dad'i.



Duk na bi na canza kamar ba ni ba, ga rama da nayi a y'an kwanakin saboda rashin kwanciyar hankali.




Yau ranar ta kasance ranar weekend, Dr na gida bai je aiki ba, a yau na shirya ma fuskantar Dr dan nima na gaji da irin zaman da muke yi.



A side d'in shi na same shi yana danna waya.



Can nesa dashi na zauna ina fuskantar shi.



"Dr ina so in yi  magana da kai ne" na fad'a kai tsaye.



"Ina jin ki" ya ba ni amsa a tak'aice.



Ni ce na ce "Ina so ka fad'a min me ka yayanke akan maganar da muka yi da kai akan Meema".



Tsayar da danna wayar yayi kana ya d'ago ya kalle ni.



"Amsar ba ta canza ba Zarah, zan auri Meema" cewar Dr.



 Cikin b'acin rai na ce "Dr wai dole ne sai ka auri Meema? to sai dai ka zab'i zama da Meema ko ni dan ni ba zan tab'a zama da ita ba, ba ma Meema ba, ba na jin zan yarda ka auri wata ka kawo min ita a matsayin kishiya bayan ni ka gama cuta ta, tun da ka bani pills d'in abortion da family planning da kasa nayi, gashi nan har yanzu ban sake samun ciki ba, ka na sha ban da hankali ne zan k'yale ka kayi aure alhalin ni ka nakasta min rayuwa dan a yanzu ban da tabbacin zan haihu ko ba zan haihu ba, nufin ka kayi aure nan gaba ka bukaci haihuwa amaryar ka ta haifa maka yara ni ina nan a zaune, impossible! dole mu ci gaba da zama ni da kai a haka, maganar wai za kayi wa Momi biyayya ka ajiye ta a gefe dan nima kai ka ja min na k'i yi wa iyaye na abin da suke so akan in auri Yaya Faruk na k'i bin maganar su, saboda son da nake maka yasa nayi haka".



 Shi ma cikin fad'a Dr ya ce " Zarah ni kike fad'a ma wannan maganar".



A lokacin ina jin zan iya fad'a ma Dr duk maganar da ta fito daga baki na saboda yadda nake cikin b'acin rai.



Ba tare da tsoro ko shakka ba na ce "Kai na ke fad'a ma wa Dr, a abin da na fad'a maka ka fad'a min wanda ba gaskiya ba".



Wani banzan Kallo Dr ya jefo min kana ya ce " Tun da kin ce ni na jawo kika k'i yi ma iyayen ki biyayya ko in kawo miki hanya mafi sauk'i ne da za ki je ki auri d'an uwanki dan ki yi musu biyayya".



Kai tsaye na ce "Za ka iya yin hakan Dr dan nima a yanzu zan so in share ma iyaye na hawayen da ban share musu a baya ba, nima  zan so in gyara kuskuren da nayi a baya dan sa iyaye na farin ciki da ban sa su a baya ba da kuma guje ma gorin da ka min".



Wani murmushi ya yi iya leb'e da na rasa ma'anar murmushi sannan ya ce " Zarah kar ki yi saurin cewa haka, nasan duk hukuncin da zan yanke ke za ki fi shiga wani hali dan son da kike min ba na wasa ba ne, kar ki zo daga baya kina danasani akan haka ".



Murmushi mai cin rai nayi kana na ce " Dr duk hukuncin da za ka yanke min zan jura tun da dai nasan ba zan rasa raina ba" na fad'a.



"Haka ki ka fad'a ko?" Dr ya watso min tambaya.



Ba tare da nazari ko tunanin wani hukunci Dr zai yanke min ba na ce "of course haka na ce".



"Ki je Zarah na sake ki saki d'aya..." Dr ya fad'a.



Wani irin fad'uwar gaba ne na ji ya ziyarce ni a lokacin, k'irji na ne ke faman harba wa kamar zai fito, tun da Dr ya fad'a min kalmar saki na rasa a wace duniyar yake, ban tab'a tunanin wannan hukuncin Dr zai yanke min ba, a yanzu ina ganin lokaci yayi da zan hak'ura da Dr ko da shine autan maza, a yanzu na sa ma kaina juriya da hak'uri da Dr tun da zaman mu ya k'are dashi, yanzu babu wani sauran wata alak'a a tsakanin mu.



Da k'yar na had'o kalmomi na fad'a ma Dr saboda juwar da ke naman d'auka ta.



"Na gode da hallacin ka Dr, sakamakon *Makauniyar soyayyar* da na nuna maka ne ya jawo min haka da rashin d'aukar magana iyaye na ya jawo min, nasan na cancanci fiye da haka, mutane sun sha fad'a min illar makauniyar soyayyar da nake maka amma ban ji shawarar du ba saboda a lokacin ido na ya rufe da soyayyar ka sai a yanzu na gano illar son da na nuna maka dan shi ya sa ni a halin da nake ciki a yau, a yau na d'auki babban darasi a gurin ka na rayuwa, kuskuren da na aikata ba zan sake maimaita irin shi ba, sai dai kafin in tafi zan fad'a maka wata magana, duk wanda ya zalunci wani a zamantakewar mu Allah ya saka mishi".



Ina gama fad'ar haka naje na fara had'a kaya na a trolik, sai a lokacin kuka yazo min mai k'arfi.



dressing Mirrow na zauna na ci kuka na ba mai rarrashi na.



Da k'yar na samu nayi controlling d'in kuka na ya tsaya saboda ba na fatan ci gaba da zama a gidan Dr, yanzu ganin gidan nake yi yamin bak'i, ji nake kamar a kan k'aya nake.

 



Jiki a sanyaye na tashi na d'auki hijab na saka kana na jawo trolik d'in na fito.



Ina fitowa wasu hawaye suka zubo min, saurin goge hawaye na nayi na nufi hanyar fita.



Sai a lokacin na lura da Dr da yake zaune a falon.



Saurin fita nayi daga falon na fita daga gidan.



Ko motar da Dr ya siya min ban tsaya d'auka ba dan ba ta da amfani a gurin na.



Kasancewar unguwar ta masu kud'i ce yasa ba wasu mutane a layin sai d'aid'aiku dake wuce a motar su, ga kuma yamma da tayi.



K'arasowa bakin titi nayi na tsaya ko zan yi sa'a na samu abin hawa.



Sai a lokacin sharad'in Abbu ya fad'a min a rai akan duk matsalar da za ta fad'a ni da Dr kar in tunkaro shi da maganar.



Yanzu ina zani? Na tambayi kaina.



Sai a yanzu na k'ara jin danasani ya k'ara shiga ta.



"Wayyo Allah! Na ga ta kaina".



Na d'an jima a tsaye kafin wata bak'ar mota ta tsaya a gaba na.



Bud'e motar a kayi kana ya sakko da k'afafuwan shi waje sannan ya fito daga motar.



Wanda na gani ya fito a motar ne yasa na ji kamar in ruga da gudu.







_To ni kaina 'yar mutan paki zan so sanin waye a cikin motar dan ban da wannan amsar_.




Post a Comment

0 Comments