TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 34

𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥

*Written by Fateemah MG

🌸💕🌸💕🌸💕
#Zayn Abideen
#Safeerah♡
#Love
#Romance

               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)

🫶🏻💕 
Page 3️⃣4️⃣
_______
Part ɗin Hajiya Umma ta nufa fuskarta ɗaure tamau, ko sallama bata yi ba ta shiga ta tsaya akan Abideen, ganin Umma tsaye akansa yasa ya miƙe tsaye da sauri ya durƙusa ƙasa. "Shanyanye, har ta shanye ka ta hanaka zuwa gurina ne ko me?" Jin hayaniya a parlour yasa Hajiya fitowa daga ɗaki, riƙe da fura damamme ta fito ta ajiye akan table tace, "Hayaniyar me nake ji?" 

Ɗagowa Umma tayi tace, "Hajiya ki duba yaron nan kiga yanda aka shanye shi?" Cikin mamaki Hajiya ta juya ta kalli Abideen sannan tace, "Ni banga yanda ya zama shanyanye ba.." taɓe baki Umma tayi tace, "Toh koma meye dae, wannan yarinyar Zaytoona tace son Abideen takeyi kuma na gida bae ƙoshi ba har aka ɗauka aka kai waje toh baze yiwu ba, da sake wallahi" 

Cikin mamaki da kaɗuwa Abideen ya miƙe tsaye, gaba ɗaya hankalinsa ba ƙaramin tashi yyi ba, cikin ɓacin rai yace, "Ita Zaytoonan tace tana so na?" Umma a fusace ta kalleshi tace, "Ƙarya nake yi kaji? Kuma wallahi sae ka aureta.." kicin kicin yyi da idanu yace, "Umma ni a matsayin ƙanwa na ɗauki Zaytoona kuma bana son yiwa Safeerah kishiya.." a fusace Umma ta wanke shi da wani wawan mari tace, "Wato ta shanye ka ko? Toh wallahi ko ka auri Zaytoona ko na tsine maka sae dae ko..." bata ƙarasa ba Hajiya ta riƙota tace, "Ke lafiyarki kuwa?" 

Wani kallo Umma ta watsa wa Hajiya tace, "Da bana lafiya ai da baza ki ganni a haka ba.." tana faɗin haka ta juya ta fice daga part ɗin. Hannu Abideen yasa ya dafe kansa ya silale ya zauna akan kujera yace, "Hajiya ya zanyi da rai na!" Cikin tausayawa Hajiya ta ƙarasa ta zaune a gefensa tareda cire masa tagumi ta kwantar da kansa a cinyarta tana shafa gashin kansa tace, "Kayi haƙuri, ita mahaifiyar kace yanzu kaje ka bata haƙuri kuma kaga ta rantse.." zae yi magana tasa hannu abakinta alamar yyi mata shiru, shirun kuwa yyi yace, "Shknn Hajiya.." ajiyar zuciya ya sauke yana tunani. Miƙewa yyi ya nufi hanyar fita, ƙin zuwa part ɗin Hajiya kuwa yyi sae ma motarsa daya shige ya fice, bae zame ko ina ba sae gurin Sadique dan kansa ya kulle kuma yana neman mafita.

Zaune sukayi a Champagne Palace sun ji shiru dasu, ajiyar zuciya Sadique ya sauke yace, "Ka kawo ni guri kuma kayi shiru" lumshe idanu Abideen yyi yace, "Da matsala Sadique, Umma wai Zaytoona take so na aura ko ta tsine mun..." a tsorace Sadique ya katse shi yace, "Subhanallah, ta ya haka ta faru?" Cize leɓensa na ƙasa yyi yace, "Probably ita tace tana sona kuma kasan Umma bata son Safeerah" ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Sadique, kallonsa Sadique yyi cikin tausayi yace, "ka kira ita Zaytoona kuyi magana, idan ta ce ta haƙura qila Umma ta.." dariya daya ji Abideen nayi yasa yyi shiru yana kallonsa, gyaran murya Abideen yyi yace, "Kana tunani dan Zaytoona ta fasa Umma zata fasa ne? Lallai baka san Umma ba labarinta kawai kk ji.." ajiyar zuciya ya sauke tareda gyara zamansa a kujerar daya ke zaune, yana tunanin me zae sanar da Safeerah akan wannan zancen.

***
10:28 na dare...
Yana daga zaune a parlournsa cikin sweatpants ash colour bbu riga jikinsa ya ɗauki wayarsa ya duba time, 10:30pm ne so baya tunanin Zaytoona tayi bacci. Dialling numbernta yyi ba'a ɗauki lokaci ba tayi picking, daga jin muryarta kasan tasha kuka amma bae dameshi ba, gyaran murya yyi yace, "Zaytoona.." bae ƙarasa ba tace, "Na'am, Yaya ina wuni!" Tasan halinsa sarai ba cika amsa gaisuwa yyi ba hakan yasa bata yi expecting reply daga garesa ba, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Ke kika cewa Umma kina so na?" 

Shiru tayi na wasu ƴan mintuna tace, "Eh ni nace ina son ka.." takaici ma abun ya bashi wai yarinyar daya ɗauka a ƙanwarsa shine tana furta masa kalmar so saboda tsabar rainin wayo. Cikin baƙin ciki yace, "Za ki iya aure na kuma ki zauna da ni as your husband?" Wata ƴar dariya yaji tayi sannan tace, "Of course Yaya zan iya.." wata irin damƙa yyi wa wayar tasa dake kunnensa har saeda jijiyoyin hannayensa suka mimmiƙe, iska mae zafi ya furzar yyi disconnecting kiran yyi kwanciyarsa akan kujeran parlourn yana tunani. 

Ya jima a kwance a parlournsa kafin ya miƙe ya wuce bedroom ɗinsa, yau gaba ɗaya bae ga Safeerah ba kuma yana da tabbacin cewar tayi fushi dashi ne akan punishment ɗin daya yi mata.

Yana daga kwance yaga dae baze iya daurewa da kewar taba hakan yasa ya fice daga ɗakinsa ya nufi ɗakinta, knocking biyu yyi ya turo ƙofar ya shiga, cikin mamaki ya shiga ɗakin jin ta bar ƙofar a buɗe. A zaune ya tarar da ita tana karatu akan study table ɗinta, sosai ta maida hankali akan abunda takeyi, sarai taji ƙarar ƙofan kuma tasan shine ya shigo dan tun safe bata saka shi a ido ba amma ta ajiye masa breakfast kuma yaci. 

Ko kallon inda yake ba tayi ba bare ta tanka masa, a Sofa ya samu guri ya zauna kuma tana iya hangosa daga inda ta zauna, ganinsa tayi bbu riga kuma hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yyi ba ganin murɗaɗɗen surar san nan tana sake tuno punishment ɗinta. Ji tayi ƙirjinta ya fara bugu har ta rasa focus akan karatun da takeyi amma sam bata nuna masa alama ba, ganin bata da niyyar yi masa magana yasa yace, "Safeerah.." shiru tayi masa bata amsa ba kuma bata ɗaga kai ta kalleshi ba, miƙewa yyi ya ƙaraso har inda take zaune ya duƙa yana kallonta, ɗauke kai tayi tana gudun ganin fuskarsa saboda wani sabon tsoronsa take ji yana dawwama a zuciyarta. 

Bata ankara ba ya fusge ta daga jikin kujerar ya miƙar da ita tsaye ta yanda zasu fuskanci juna, ƙasa tayi da kanta cikin rashin son ganinsa ko kaɗan. Ga yanda fuskarta da idanunta suka kumbura saboda tsabar kuka kuma ko school bata je ba.

Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta amma idanunta kallon wani guri sukeyi, da zai sarara sai ya iya jiyo yanda zuciyarta ke bugawa da sauri tsabar tsoro. Ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata fararen idanunsa, taune haƙoransa yyi yace, "Look at me Safeerah.." matsalar kenan saboda duk inda ya kai ga bata umarni zuciyarta bata iya ƙin bi, bada son ranta ba ta tsinci idanunta sun kafe fuskarsa da kallo, gani tayi ya ƙara haske kuma ya ɗan rame. 

Shoulders ɗinta ya riƙe ya ja ta suka zauna akan gadonta yana kallon yanda idanunta suka kumbura sae yaji babu daɗi, akan cinyarsa ya zaunar da ita amma yasa ni sarai bata saki jiki ba. Numfashi ya sauke a hankali yace, "Safeerah.." a hankali ta kai dubanta gareshi nan ya sake kafe ta idanu cikin jin tausayinta yace, "Ki dena taurin kai kinji.." ba ƙaramin mamakin jin furucinsa tayi ba dan duk tunaninta zai bata haƙuri yace baze sake bane amma wai warning ma yake bata!!! Amma Ya Abideen ko ɗan raunin wayo.

Cikin takaici tace, "Taurin kan mene?" Lumshe idanunsa yyi yace, "Kar ki sake kula wani namiji idan kina son kwanciyar hankali.." bae ƙarasa ba tace, "Saboda me? How do you expect me to do that?" Sauka tayi daga cinyarsa tayi zamanta a gefensa tana ɓata rai, juyo da ita yyi yace, "Saboda ni kaɗai zaki kula kuma ke ɗin tawace.." girarta ta haɗe cikin rashin fahimta tace, "Yaya Abideen meysa kk haka?" Murmushin gefen baki yyi yace, "Because I love you!" Tsuka tayi tace, "wannan ba so bane, mugun so ne wannan.." bata ƙarasa ba ya kamo lips ɗinta ya fara kissing ɗinta cikin zallar mugunta, ya ɗan jima yana torturing lips ɗinta da kiss ɗin mugunta inda take ta faman tureshi amma ya riƙe ta gam. Kansa ya ɗago yana kallon yanda lips ɗin suka ɗan kumbura yace, "Kar ki ƙara yi mun tsuka ko na fasa miki baki.." wani quick kiss ya manna mata a baki yace, "Na san abunda ya dace da ke, just do as I say!" Lumshe mata idanu yyi yana yi mata daɗin baki inda tayi lamo a jikinsa jin ya kashe mata jiki gaba ɗaya. 

Janta yyi zuwa kan gadon ya kwantar da ita akan chest ɗinsa ya fara shafa gashin kanta, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin taya zai fara gaya mata cewar zai sake aure bayan ko shekara ɗaya basu yi ba. Wutan side lamp ɗin ɗakin ya kashe ya gyara masu duvet, tana tsorata da alamuransa amma idan yyi hugging ɗinta mantawa takeyi da komai, tayi kewar ɗumin jikinsa ga ƙamshin mae sanya natsuwar dake fita daga jikinsa. Amma hakan bae fasa kulle mata kai ba yanda yake da kala har biyu, yyi sanyi sae kuma yyi zafi. Ta kasa ganewa me hakan yake nufi amma wai shi yace So ne?? 

Don't forget to vote and comment, it's what keep me going...🥹❤️
Facebook #Fatee Mah
Wattpad #_khanoum_

©️ Fateemah MG



Post a Comment

0 Comments