TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina book 2 page 8

 D. AUTA CE✍️


*ABOKIN AIKINA!*


 *TAKU NA BIYU.*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



      *LAMBA TA TAKWAS.*


         Kujerar baƙi Likitan ya nuna mini da hannunsa na zauna, fuskata a haɗe saboda ban san me zan faɗa ba, wanda zan tsayu da shi a matsayin shi ne ya kawo ni Asibitin. Sai da Likitan ya gama dube-duben wasu files sannan ya fiddo wani yana duba rubutun ciki. Mintuna a tsakani ya ɗago fuskarsa yana faɗin.

     "Me ke damunki?"

"Cikina ne yake ɗan riƙewa." Na faɗi maganar ina satar kallon MD.

        "Riƙewa kamar ya ya? Cikin yana zafi ne?"

     Na girgiza kai sannan na ce, "Ba sosai ba, amma wani lokaci ina jin ƙirjina yana zafi."


       Haka ya dinga mini tambayoyi ina amsawa, yana rubutu cikin file ɗin da na gano nawa ne. MD yana zaune gefe yana ta dannar wayarsa kamar ba ya nan. Bayan Likitan ya gama mini tambayoyin ya fisgo wata farar takarda ya yi rubutu a jiki. Wanda na gano magunguna ne ya rubuta mini, ya miƙo mini takardar yana faɗin,


     "Bawasa a nemo mata waɗannan magungunan, in Sha Allah za ta yi kwana biyu ulcer'r ba ta dame ta ba."

       Sunan da na ji ya faɗa 'Bawasa' shi na yi ta maimaitawa a bakina. Hannu ya miƙa masa suka yi sallama, na miƙe ina ƙoƙarin ficewa saƙo ya shigo wayata. Da sauri na ciro ta a jaka na duba.


    'Ku tafi kawai zan je ganin wata mara lafiya,  ga Aunty Salaha muna tare, da ita za mu koma gida.'

 

      Saƙon da Amina ta turo mini kenan, wanda ya sa na ji ƙirjina bugawa. Saboda ban so ta bar ni da MD ba, na so yadda ya ɗauko mu ya ajiye mu tare. Domin ba zan iya sakewa daga ni sai shi a cikin motar ba. 

      Yana gaba ina bin shi har muka fito harabar Asibitin. Ya buɗe motar ya shiga ni ma na buɗe baya na zauna, sannan na sha jinin jikina ta yadda numfashina ma da ƙyar nake fiddo shi a sarari.


      "Ina ƙawarki?"


Tambayar da ya yi kenan kamar ba da ni yake ba, fahimtar ni kaɗai ce a wurin ya sa na gano Amina yake nufi. 


    "Tana tare da Auntynta,  sun je wata dubiya."


    "Za mu jira su ne?"


"A'a ta ce mu je, da ita za su koma."


    Bai ce da ni komai ba ya tayar da motar, zuciyata cike da jin daɗin bai ce na dawo gaba na zauna ba. Har muka fita gate ɗin Asibitin muka kama titi bai sake cewa da ni komai ba. Sai da muka kai daidai Makarantar Gwiwa, saman titin da idan an sha kwana zai miƙe samɓal har cikin Bafarawa Estate. Sannan ya tsaya Chemist ɗin Doya, wurin Doctor Bello ya siye magungunan da aka rubuta sannan muka nufi gidan Kawu Sale. 

      Ƙofar gidan ya yi parking ina ƙoƙarin buɗe ƙofa ya miƙo mini ledar magungunan, na karɓa ina yi masa godiya cikin wata siririyar murya na fice.

      Har na shige gidan bai bar ƙofar gidan ba. Kuma jikina ya tabbatar mini da kallo na yake yi har na shige gidan. Duk da ni kaina na ji kamar na juya na ɗaga masa hannu alamun bye-bye. Sai kuma na dake cike da jatumta na basar.

     Laɓewa na yi ban shiga cikin gidan ba, har sai da na ji ƙarar juyawarsa alamun ya tafi. Sannan na leƙo da kaina kaɗan na hango bayan motarsa. Juyawar da zan yi muka yi kiciɓis da Umma, fuskarta a haɗe ta ce,


      "Wa kuma kike leƙe?" 


Ƙirjina ya hau bugawa cikin sauri na ce, "Ban da lafiya MD ya siyo mini magani. Shi ne da ya aiko yaro ya miƙo mini na leƙa na ga idan bai tafi ba na yi masa godiya!"


       "Godiyar da kika yi masa a cikin motarsa ba ta wadatar ba kenan?"


    Bakina na buɗe da nufin kare kaina, amma kallon da ta yi mini dole na yi saurin rufe shi, cikin sauri na shige gidan gabana yana ta bugawa. Saboda na san ba iya abin da za ta faɗa kenan ba. Kuma ba za ta bar zancen ya tsaya nan ba sai ta ƙara da dogon sharhi mai cike da kashedi. 

      Cikin sanyin jiki na tarbi su Umma Salma da ke ta murnar gani na, Inna Kulu ma tana ta yi mini sannu da zuwa. Gaishe ta na yi, sannan na miƙa wa Iman jakata da ledar maganin da ke  hannuna.

     Buta na ja na yi bayi da sauri saboda fitsarin da ya cika mini mara. Daga can bayin na ji sallamar wani yaro ya shigo yana faɗin, 


     "Wai wani ya ce ga kular da aka manta da ita a cikin mota!"


    Dirim-dim! Shi ne kalar bugun da na ji ƙirjina ya yi, saboda tuno kular gurasar da Amina ta ba ni ce, Wacce na manta shaf da ita a cikin motar MD. Muryar Inna Kulu na ji tana faɗin,


     "Kawo nan! Ka ce an gode!"


     A gurguje na fito bayin cikin borin kunya na ce, "Sai da na ce da Amina ta bar gurasar nan ta ƙi. Ga shi yau ulcer'r ta motsa mini za ta ƙara mini ciwo, idan na ci kayan maiƙo."


      Ɗaki kawai Umma ta shige ba ta ce da ni komai ba. Inna Kulu ce kawai ta nufo ni tana miƙo mini kular da nufin na karɓa. Fuska na yamutsa kamar gaske na ce,

     "Yau fa ba na jin daɗi Inna. Ba zan iya cin komai ba musamman mai maiƙon da zai ƙara tayar mini da ciwon. Ki bar gurasar a hannunki ku raba, idan an gama Ummu Salma ta wanke kular gobe na fitar mata da kayanta."


     "Da kin ci ko babu yawa. Na san ki da son gurasa."


     Tana maganar tana buɗe kular ƙamshin ƙulin ya daki hancina. Ina son gurasar amma dole na haƙura da ita saboda Umma ta gano da gaske ban da lafiyar. Ɗaki na shige na bar Inna Kulu tana kason gurasar daki-daki.

      A ɗarare na janyo hijabi na saka ina ƙoƙarin tayar da sallah, Inna Kulu ta shigo da gurasar a tiren da ta kasa tana faɗin, 

       "Habi zaɓi wanda kike so na kwashe miki."


     "Na ƙara muku auki!"


Zancen da ta faɗa kenan wanda ya sa na yi hanzarin tayar da sallar, Inna Kulu ta yi sororo da tire a hannu tana faɗin,

     "Da dai kin ɗauka, don ta yi daɗi sosai!"


     "Kulu don Allah ki fita da gurasar nan kina ƙara ɓata mini rai!"


     "Me ya kawo ɓacin rai daga magana?"


      Inna Kulu ta jefo mata tambayar ɗauke da mamaki a cikin muryarta. 

       "Yanzu ke har kin yarda da wata ta bayar da gurasar? Bayan da kunnuwanki kin ji wani ya aiko da ita da sunan an manta. To Zaituna ba za ta bari mu zauna lafiya a cikin gidan nan ba! Tun da ta ce za ta dinga bin wannan mutumin yana yawo da ita a cikin garin nan! Kuma wallahi ba zan zura mata ido ta janyo mana zagi ba! Daman ni na san har da wannan mutumin ya ƙara lalata zaman auren ta da Mukhtar! Ga shi ko'ina ba a je ba ya fara bibiyarta, ita kuma da yake wata shashasha ce ta saki jiki da shi yana ƙoƙarin tona mana asiri! To ki zamo shaida Kulu, wallahi muddin ta sake shiga motarsa da idda a kanta ban yafe mata ba! Idan kuma tana da wata uwar da ta kai ni ta je ta nemo gafarar ta! Amma ni ba da ni za a yi wannan rashin sanin darajar kai ba! In ban da zamani da ya juya, a baya mace mai idda ko fita ba a barin ta yi sai ta kammala. Saboda gudun gori da kauce wa abin da bai dace ba! Amma ita ta samu dama tana ƙoƙarin bankaɗe wa kanta labulen sirri ta tona mana asiri a cikin mutane!" 


    Addu'ar ma kasa yi na yi bayan na gama sallar, saboda faɗan Umma ya sa na daburce ban san me ya dace na yi ba. Hawaye ya dinga bin fuskata ina sharewa har ta dasa aya a zancenta. Inna Kulu tana ƙoƙarin yin magana na riga ta da cewa,

      "Wallahi Inna ban so shiga motarsa ba, amma ya kafe a kan dole sai ya kai ni Asibiti tun da ban da lafiya. Tare da Amina muka je Asibitin, ba daga ni sai shi muka je ba, lokacin da za mu dawo ma ban so ta bar ni da shi ba. Kuma gurasa ita ce ta kawo mini ita tun da safe, yanayin da nake ji a jikina ya sa ban ci ba na yi niyyar zo muku da ita. Shi ne na manta da ita a motarsa saboda ciwon da cikina yake yi."


     "To kin dai ji Habi! Don haka ki daina zargin abin da ba ki da tabbaci a kansa. In don laifi tabbas ta yi laifin shiga motarsa daga ita sai shi tana cikin idda, saboda son ta yake yi, kuma idan dama ta bayar zai iya fitowa neman auren ta. Hakan kuma zai iya janyo surutun mutane tun da abin magana ba wuya yake yi ba."


      "Wannan da kika gani har da ita wurin cusa wa Mukhtar zarginta a zuciya. Don babu namijin da yake jin daɗin ganin matarsa da wani ko da kuwa ɗan'uwanta ne, balle ABOKIN AIKIN da zai dinga zaƙewa. Don haka ko ta daina ta san Annabi ya faku, ko kuma ta ci gaba mu raba gari ni da ita a cikin gidan nan!"


     Umma ta ƙare maganar tana wurgo mini wata jar harara. Cikin sauri na goge hawayena na ce,

       "In dai wannan ce matsalar; in Sha Allah ba zan sake shiga motarsa ba!"

      "Da ya fi miki dai! Ko don kare sauran mutuncin da mutane suka hango mana! Tun da ke kin daɗe da ba da ƙofar da za a dinga yi miki wani ɗan kallo."


     "Yanzu dai tun da ta gano laifinta, don Allah ki bar maganar nan Habi! Don kina iya zazafenta daga nan har gobe kina mitar abu ɗaya!"


     "Tun da an san halina, ai sai a kauce wa abin da zai janyo hitina. Amma muddin ba ta bari ba ni ma ban gajiya!"


     "Allah ya kyauta, ni dai ɗauki gurasar idan kin gama masifar!"


     "Ai kuma Kulu tun da na ce ban ci; wallahi ban cin ta! Kuma gobe na sake ganin shi a ƙofar gidan nan; sai na fita na ci masa mutunci. Na ji lokacin da na haife ta da me ya taimaka mini a cikin naƙudarta! Wannan binbini har ina?"


     "Shi dai mai son abinka har abada ba ka da kamar shi Habi! Mutumin nan duk yadda yake tun da yake ƙaunarta ya dace ki ɗaga masa ƙafa! Balle kowa ya shaida mutumin gari ne kuma irin mijin da ya dace ta aura. Amma tun da ba ki so; ki nemo mata duk wanda kike so ki aura mata. Tun da har gani ga wane bai ishi wane tsoron Allah ba! Ummm! Kin ga inda na yi, tun da ke idan kika hau babu mai iya saukar da ke!"


     Inna Kulu ta fice tana ƙwala wa su Ummu Salma kira, daga nan ɗakin ina jin tana faɗin,

     "Ku kwashe kason Habi ku ƙara tun da ba ta ci!"

     "Ai ba gurasa ba! Ko mene ne zai fito a hannun mutumin nan; ban ce a kasa da ni ba! Ku ci kayanku ba na so!"


     Kallo kawai na bi ta da shi zuciyata tana bugawa, saboda tunanin yadda za ta yi ranar da na bijire mata a kan MD. Don na ci alwashin muddin ya fito neman aure na sai na amince masa, don ba zan taɓa  bari wankin hula ya kai ni dare ba. Na gani na yaba kuma ina so, don haka garin kallon ruwa ba zan bari kwaɗo ya mini ƙafa ba. 

        Wunin ranar har dare Umma ba ta sake mini fuska ba, duk da na san ina da laifi amma ƙiyayyar da take nuna wa MD ta yi yawa. A gani na bai dace ta dinga nuna rashin son shi a fili ba, ko babu komai ya yi mana taimakon da ya dace a jinjina masa.

      Amma tun da har ta hau dokin na ƙinta, ban ga wanda zai saukar da ita ba. Haka lokacin Mukhtar ta saka auduga ta toshe kunnuwanta a kan laifukansa. Sai da ta hango babu mafita sannan ta fara saduda, ko shi sai dai ta nuna bai kyauta ba, amma kullum zancenta ɗaya ne na yi haƙuri. 

      Da dare bayan na gama cin tuwon dawar Inna Kulu na sha magani. Na ɗan kishingiɗa a kan katifar su Ummu Salma, wacce aka shimfiɗa musu tsakar gida saboda kwanan zafi. Ina mayar da numfashi ɗaya bayan ɗaya Inna tana jera mini sannu, don yanayina ya sa ta zargi da gaske ban da lafiyar. Kira ya shigo wayata Iman ta je ɗakin Umma da gudu ta ɗauko mini.

       "Aunty ina wuni?"


"Lafiya lau Sajida, ya ƙarfin jikin?"


     "Da sauƙi sosai Aunty na warke. Ɗazu na ga wata kamar ke a Asibiti kina ƙoƙarin shiga mota, ko da na fito harabar har motar ta tafi. Shi ne nake tunanin kamar ke kamar ba ke ba!"

      "Ai kuwa dai ni ce Sajida, na je ganin Likita ni ma ba na jin daɗi."


     "Allah Sarki Aunty, Ashe shi ya sa ba ki biyo ganin Abban Taufiƙ ba. Har na fara jin haushin Aunty ba ta damu da ni ba!"

     Yanayin da ta ƙare maganar cikin muryar damuwa ya sa na yi saurin faɗin,

      "Wallahi na so zuwa ganin ki a raina Sajida, wanda ya kai nin ne kawai nake gudun ɓata wa lokaci daga taimako. Amma ki yi haƙuri jibi Asabar ina son zuwa ganin Hajiyar Amina, ita ma jikinta ya motsa in Sha Allah zan zo na duba shi."

      "To ya yi Aunty har na ji sanyi."

       "Ki gaishe shi, zan shigo jibin in Sha Allah!"

       "Na gode sosai Aunty sai kin zo."


     Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar, saving ɗin lambar na yi don kwana biyun da suka wuce ma da ita ta kira ni. Inna Kulu ta sauke ajiyar zuciya ta ce,


     "Ya jikin mijin nata da sauƙi dai ko?"


     "Da sauƙi gaskiya"


"Ya dace a ce kin daina shiga sabgar da ta shafi su Mukhtar! Idan kuma kika je aka yi miki wulaƙanci ke kika jiyo, muna gida ba mu san an yi ba!"


    Zancen Umma kenan tana juya kwanciya a kan shimfiɗarta, kafin na yi magana Inna Kulu ta riga ni da cewa,

      "Idan aka raba ta da wannan yarinyar kamar ba a yi mata adalci ba. Saboda tana ƙaunarta ko a baya, don haka bai dace a bari laifin kawunta ya shafe ta ba!"


     "Halin uwarta fa!"


Umma ta jefo wa Inna tambaya. Inna ta yi hanzarin faɗin, "Ko lahira, laifin wani ba ya shafar wani. Uwarta daban ita daban, kuma ke ma kin sani ra'ayinta da na uwarta ya sha bambam."


     "Allah dai ya kyauta!"


Cewar Umma kafin ta yi shiru kamar ta yi bacci, Inna Kulu ma daga "Amin" da ta ce, ba ta sake cewa komai ba. Sai tashin numfashinta da na fara ji alamun ta yi barci.

     Tsam na miƙe ina cewa da su Ummu Salma;  su ajiye karatun da na saka su, su kwanta. Ɗaki na shige saboda ni ba na kwana wajen, duk tsananin zafi na fi jin daɗin barci a ɗaki, saɓanin wajen da ake bajewa a lokacin bazara.

        Daren ranar ma sai da na yi nafilfili sannan na yi bacci, aka yi dace akwai nefa na baje kan gadon Umma ɗaɗɗaya na yi baccina, mai ɗauke da mafarkai iri-iri.






Asuba tagari😆




Post a Comment

0 Comments