TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 83-84

 83-84



Ina jin tashin motar su na ja d’an k’aramin tsaki, takaicin Meema ne ya bi ya dame ni, nasan a yanzu za ta ji shakkar k’ara shiga gona ta tun da muka yi haka da ita.



Jiran Dr kawai nake yi ya zo ya k’ara min bayanin Meema kamar yadda ya ‘boye min alak’ar su a baya, sai a yanzu da nake ji a bakin Hanan da Meema cewa akwai alak'ar soyayya a tsakanin su a da wacce ban san da ita ba.



Shi kanshi haushin Dr d’in nake yi akan yadda ya ‘boye min alak’ar shi da Meema.



Da haka na k’arasa girkin na fito kitchen na wuce d’aki na.



Su Meema kuwa tun a hanyar su ta dawowa gida su da Meema da Hanan suke maganganun su akan abin da ya faru a gida na da suka zo, ita dai Farida kallon su take yi dan tasan in ta sa bakin ta fad’an kan ta zai dawo.



Har suka k’arasa gida ba su daina maganar da suke yi ba a kaina.



Momi suka samu a falo sanye da medicated glass a fuskar ta tana karanta jarida.



Suna shiga falon Meema ta fad’a jikin Momi ta fara kuka.



Hankalin Momi ne ya tashi ganin yadda Meema ke kuka.



Tambayar su tayi me ya sami Meema take kuka.



Hanan ce ta kwashe komai ta fad’a ma Momi abin da ya faru a tsakanin mu da Meema.



Ran Momi ne ya ‘baci jin cewa na mari Meema.



Wayarta ta d’akko ta kira Dr akan in ya tashi daga aiki yazo tana son ganin shi.



Dr yana tashi daga aiki ya wuto gidan su.



Samun su yayi a falo suna kallo, bayan sun gaisa ne ya tamaye su ina Momi.



Fad’a masa suka yi tana d’akin ta.



K’arasa wa d’akin ta yayi ya same ta resting chair, gaban ta kayan marmari ne a ajiye akan d’an k’aramin centre table tana ci.



Sallama yayi ya nemi kusa da ita ya zauna.



"Sannu da hutawa Momi" Dr ya fad’a.



"yawwa" ta amsa mishi a tak’aice.



Ci gaba tayi da cin fruit d’in ta ba tare da tayi magana ba.



Kau da shirun yayi da cewa "Momi gani, naji kin kira ni a waya ki na nema na".



Sai a lokacin ta maida hankalin shi gare ta tace " Magana nake so muyi akan matar ka".



Kallon ta yayi yana jiran jin mai za ta ce a kaina.



"Sadik!" Momi ta kira sunan shi.



"Na’am Momi" ya amsa mata.



Momi ce ta fara da cewa "Sadik tun farko na nuna maka sha’awar auran Meema amma ka ce kai sai Zarah kake so, ka fara kawo wasu hujjoji wanda ban gamsu dasu ba akan Meema da ka bayar, ban sani ba ko ita Zarah tafi saura mata ne da ka dage sai ita oho, let me go straight to the point in fad’a maka dalilin da yasa na kira ka, yau su Meema sun je gidan ka, matar ka ba ta ji kunyar kowa ba ta mari Meema, sannan daga Hanan ta yi mata magana ta fara mata fad’a, so ina so ka ja ma matar kunne akan ta fita harkar Meema, in ban da ka k’i ta da ita za ta zama matar ka, sannan kar ta k’ara kuskuren yi ma yara na fad’a dan ka san ko ni ba na matsa musu".



Tun da Momi ta fara magana yayi shiru yana sauraren ta, dalilin da yasa na mari Meema yake yi, gashi yanzu Momi sai fad’a take yi, shima kan shi bai ji dad’in abin da nayi ba duk da bai san abin da ya had'a ni da Meema ba.



"Amma Momi me ya had’a su da Meemam har ta mare ta" Dr ya tambayi Momi.



Momi ce ta bashi amsa da cewa "Just akan ita Zarah ta kunna Tv tana kallo, so shine Meema ta d’au remote ta canza da ta ga Zarah ta bar falon, shine ita Zarah da ta dawo wai ta fara fad’a musu magana akan canza channel d’in da Meema tayi, har ta nace mata kayan ta ne, in suna so su nuna iko ne su je can side d’in ka, duk wannan bai ishe ta ba har da sa parent d’in Meema a ciki".



Jin bayanin da Momi ta mishi ya k’ara ‘bata mishi rai, for what reason dan k’annen shi sun je gidan shi zan neme su da rigima, ba zai ti tolerating d’in abin da nayi ba.



"Ki yi hak’uri Momi, zan mata magana in na koma, I d’ont expect that a gurin Zarah, zan d’au mataki akai".



"That’s better" Momi ta fad’a.



Canza akalar hirar Dr yayi, dan yasan Momi abu kad’an take jira ta fad’i aibu na tun da Dr ya k’i auran Meema.



A nan Dr ya ci abincin dare, sai da yayi isha’i sannan ya bar gidan.


Ranar Dr bai dawo da wuri ba sai wajejen bayan sallar isha’i sannan ya shigo gidan.



Ina zaune a falo ina pressing d’in waya ta ya shigo da sallama, amsa mishi nayi kana na mishi sannu da zuwa, fuskar shi ba yabo ba fallasa, ya amsa min.



Nima yadda na ke jin haushin shi yasa na k’ara d’aure fuska ta ba tare da na k’ara mishi magana ba.



Side d’in shi ya wuce yayi wanka kana ya canza shigar shi cikin k’ananun kaya ya dawo side d’ina.



Kujerar da ke kallo na ya zo ya zauna yana kallo na ba tare da ya min magana ba.



"Dr ga abincin can a dinning, mu je in yi serving d’in ka, ko in kawo maka nan ne".



"Ki bar shi na ci a gurin Momi" cewar Dr.



Shiru nayi ban ce komai ba, sai ma ci gaba da pressing d’in waya ta da nake yi.



"Zarah! Dr ya kira suna na.



D’agowa nayi na kalle shi jin yanda ya kira suna na nace "Na’am Dr".



Cikin d’aurewar fuska ya ce "Akan wani dalili yasa ki ka mari Meema har ki ka sako parent d’in ta a ciki, sannan dan Hanan ta miki magana ita ma kika had’a da ita, ba ki san Meema ta girme ki ba, ko da a ce ba ta girme ki ba ya kamata a ce ta ci daraja ta ko me ta miki, duk abin da ta miki ba sai ki bari in na dawo ba sai ki fad’a min in d’au mataki amma sai ki zauna ki na fad’a mata bak’ak’en maganganu, Zarah ba na son rigima, ba na so tun yanzu ki fara samun matsala da family na".



Raina ne ya k’ara ‘baci da irin yadda ya je gidan su aka fad’a mishi gaskiya da k’arya kuma ya d’auka ba tare da ya ji ta baki na ba, ya tasa ni a gaba sai fad’a yake min ba tare da ya ji nawa bayanin ba.



Shiru na mishi duk da yadda raina yake a ‘bace na daure ban mishi magana ba har ya gama fad’an shi.



"Zahra kina ji ina miki magana shine kika min shiru, ko ke ba za ki yi laifi a miki fad’a ba" Dr ya fad’a cikin fushi.



Cikin ‘bacin rai na ce "Me kake so in ce Dr, ina ganin duk abin da zan fad’a an riga an fad’a maka shi kuma ka yarda, ka ga kenan bayani na bai da wani amfani a gurin ka, in da hukuncin gaskiya ka ke so ka yanke ai sai nima ka tambaye ni abin da ya had’a ni da Meeman har na mare ta, amma da yake abin son kai ne ka yarda da maganar da k’annen ka suka fad’a maka akan abin da ya had'a ni da Meema".



Wannan karan a hankali ya min magana ya ce "Me ya had’a ku da Meeman?".



Kallon shi nayi na ce "Abin da suka fad’a maka shi ya had’a ni da ita, duk abubuwan da Meema take min ban ta’ba kai k’arar ta gurin ka ba saboda rugudun rigima, yanzu ga shi su sun fad'a maka ka yarda da maganar su, ni da ban da Wanda zai tare min ai sai dai in yi hak'uri da abin da suka fad'a maka".



Ci gaba nayi da cewa " Ni ba ruwa na da girman ta tun da ita Meema ba ta ja girman ta ba..".



Dr ne ya katse ni da cewa "Ya isa haka Zarah, plss ki dinga hak’uri da abin da Meema za ta miki, ba na son hayaniya".



"A kan me zan yi hak’uri da ita ban da wanda nayi a farko, ko da yake ban ga laifin ka ba dan ka ce in yi hak’uri da ita tun da akwai alak’ar soyayya a tsakanin ku a da wanda ba ka fad’a min ba, sai a yau da nake ji a bakin su" Na k’arasa maganar ina jiran jin mai zai ce min.



Shiru yayi bai ce min komai ba, sai ma bi na da ido da yake yi.



Ci gaba nayi da cewa "Dr me yasa ka ‘boye min alak’ar ka da Meema bayan kasan duk daren dad’ewa zan ji mai ke tsakanin ku, shi yasa tun a farko nake tunanin wani irin laifi nayi ma Meema da take nema na da tashin hankali, ashe ni ce ban san abin da yake tafiya ba, soyayya ce a tsakanin ku a da wacce har ta so ta kai ku ga yin aure, Allah ne bai nufa ba, why Dr?".



A wannan lokacin cikin lallashi yayi min magana da cewa "Zarah don’t put that in your mind akan tsakani ni na da Meema, kamar yadda na fad’a miki a baya cewa Meema yarinyar abokin Dad d’in mu ce, akwai aminci tsakanin su, ni ban d’auki Meema a matsayin lover d’i ta ba, na d’auke ta ne a matsayin sister d’ita kamar yadda na d’auki su Hanan, though akwai shak’uwa a tsakanin mu, Meema ita take so na, bai kamata ki ga laifi na ba dan ban fad’a miki wannan maganar ba, dan ni ban d’auke ta mai mahimmanci a guri na ba shi yasa ban fad'a miki ita ba, I hope kin gamsu da bayanin da nayi miki" ya k’arasa maganar yana jefo min shu’umin kallo da yake sanyayar min da jiki.



Wani irin dad’i ne ya ziyarce ni a lokacin jin cewa shi Meema ita take son Dr, ba shi yake son ta ba, amma duk da haka ban gama samun natsuwa a zuciya ta ba in dai har Meema su na tare da Dr, nasan za ta iya yin duk wani dubarar ta taga ta jawo hankalin shi ya yarda ya aure ta, wannan shine babban fargaba ta.



Tunano kalamen ta nayi na d’azun da take ce min Dr na ta ne, sai ta aure shi, ban san me Meema take nufi da wa’innan kalamen ta ba, gashi dai Dr ya min bayanin cewa ita take son shi ba shi yake son ta ba, menene ribar ta in ta aure shi bayan ta san ba son ta yake yi ba?.



In har maganar da Meema ta fad’a akan sai ta auri Dr hakan yake a ranta ban san wani hali zan shiga ba nan gaba.



Ban san lokacin da Dr ya taso ya dawo kusa dani ya zauna ba.



Jin shi nayi ya tallabo fuska ta yana jefa min kallon da ke dawo dani cikin natsuwa ta.



Cikin cool voice d’in shi ya ce "Zarah stop bordering your self, ba na so ki ci gaba da sa tunanin Meema a ranki, daga yanzu in har ta miki wani abun in na dawo ki fad’a min kin ji, ba na so ki na biye mata kuna samun misunderstanding a tsakanin ku, ina fatan kin fahimta".



Murmushi na sakar mishi kana na ce "Na fahimce ka Dr, insha Allahu zan kiyaye".



Shima murmushin ya mayar min ya ce " That’s what i want to hear from you".



Cikin ‘yan mintuna sai gashi na daina jin haushin Dr, daman nasan har da kishi da yake damu na.



A ranar sai da Dr ya koyar dani wani darasi a babin soyayya irin ta ma’aurata da suka damu da junan su.




Tun bayar rigimar da muka yi da Meema, ban k’ara shiga harkar ta ba, duk yadda ta so in biye mata ba na kula ta, ita ma na lura a yanzu tana shakkar nema na da rigima, hakan yasa na k’udurta cewa zan danne duk abin da za ta min, dan ba na so in yi abin da zai ‘bata ma Dr rai.




******************************


A kwana a tashi ba wuya ga mai yawan rai.



 Sai gashi har na kammala HND d’ina nayi service.



Har a wannan lokacin ba ni da ciki, a yadda na lura shi Dr hankalin shi bai tashi ba da rashin cikin da ban samu ba.



Ni kuwa hankali na ne ya kasa kwanciya ganin ina neman shekara uku da aure amma har yanzu ban samu ciki ba.



Gashi har Anisa ta haifi yarinyar ta mace wacce ta ci suna Amatur-Rahman.



A ‘yan kwanakin sai na fara jin canje-canje a jiki na, zazza’bi da yawan kasala da ke damu na, ga wani fari da na k’ara yi.





Yau muna kwance ni da Dr a gado, gani nayi ya tashi ya kunna bulb ya dawo ya zauna kusa dani yana kallo na.



Hure mishi ido nayi na ce "Dr lafiya wannan kallon kuwa".



"Ba komai, na ga wasu changes ne a jikin ki, na ga kuma kin k’ara min kyau da fari" Dr ya fad’a yana kanne min ido.



K’ayataccen murmushi na sakar mishi kana na ce "Ni kaina Dr na rasa me yake damu na a ‘yan kwanakin nan, fever da kasala ke damu na, sannan ga haske da da na k’ara yi, ina jink o har da rashin lafiyar da nake yi ne yasa na k’ara haske oho".



Tun da na fara maganar nan Dr ke bi na ido bai ce min komai ba har sai da na gama magana sannan ya d’aura da cewa "Zarah me yasa ba ki fad’a min ba ki da lafiya ba?".



Marairaicewa nayi na kwanta a kafad’ar shi na ce " Yawanci sai ka tafi aiki nake jin zazza’bin da kasala, kan yamma sai ka ga na koma normal, shi yasa ban fad’a maka ba".



"Bayan nan ba in da yake miki ciwo?" Dr ya tambaye ni.



Shiru nayi kamar mai tunani kana na amsa mishi da cewa "Gaskiya babu, sai dai wani lokacin ina yin amai".



Hannu na ya rik’e ya kalla kana ya maida kallon shi gare ni.



"Yaushe rabon ki da ganin period d’in ki" Dr ya sake watso min tambaya.



Amsa mishi nayi da cewa "Ina ganin almost 2 month kenan".



"Ina zuwa" Dr ya fad’a a tak’aice.



Tashi yayi ya je ya d’akko kayan gwaje-gwajen shi ya dawo ya zauna ya fara auna ni.



Bayan ya gama gwajin shi ya ajiye kayan aiki a gefe.



Jin bai ce min komai ba game da gwajin da ya min yasa na ce "Dr na ga ka gwada ni ba ka min bayanin abin da yake damu na ba".



"A gwajin da na miki ban ga komai ba, amma zuwa gobe zan tafi da jinin ki da fitsarin ki sai a je dashi lab a ga me yake damun ki".



"Allah ya kaimu goben" na fad’a.



"Amin" ya amsa min a tak’aice.



Washegari kuwa Dr ya tafi da jini na da fitsari asibiti dan a min gwaji.



Tun a jiya da Dr da ya min gwaji ya gano ina da ciki, sai dai ba yaso zargin shi ya tabbata dan har yanzu bai shirya ma haihuwa ba, gani yake har yanzu suna da sauran lokaci kafin su haihu.



San da yaje asibiti yasa an mishi gwaji a lab, sakamakon ya fito da cewa ina da cikin sati goma.



Abin da yasa ya daina d’aura ni akan tsarin family planning saboda yadda nake mishi k’orafin rashin samun ciki na da kuma dad’ewar da nayi ban samu ciki ba sannan yana da tabbacin tsarin da ya d’aura ni akai zai yi wuya in samu ciki da wuri haka, sai gashi Allah yayi ikon shi ya bani ciki a lokacin da bai yi tsammani ba.



Shawarar da ya yanke shine ba zai fad’a min ba dan shi bai shirya ma haihuwa ba, yasan in na sani ba k’aramin farin ciki zan nuna da jin labarin ba dan yadda a yanzu nake buk’atar samun ciki.



Lokacin da zai tafi gida ne ya tawo da wasu pills da zai bani.



Ko da ya dawo na mishi tarba ta musaman kana na kawo mishi abinci ya ci.



Ganin bai ce min komai ba akan gwajin da yace in ya je asibiti za a min yasa na ce "Dr an yi gwajin kuwa, me yake damu na".



"Oh kin ga na sha’afa in fad’a miki result d’in gwajin, daman nayi zaton Typhoid ke damun ki san da jiya na miki gwaji, yau d’in ma da aka yi gwajin a lab haka ya nuna hakan, ga magani na zo miki dashi, ki je ki d’ebo ruwa ki sha a gaba na dan nasan za ki iya mantawa ba ki sha ba tun da ke ba son shan magani kike yi ba" cewar Dr.



Tashi nayi na je na d’ebo ruwa a cup na dawo na zauna a kusa dashi.



Bani maganin yayi na sha da ruwa ina zuba mishi shagwa’ba shi kuma yana biye min.



Ban fi mintuna 30 ba da shan maganin na ji marata ta fara min ciwo.



Yatsina fuska na fara yi saboda yadda maran take neman takura min.



Dr ne ya kalle ni ya ce "Ya akayi ne Zarah".



"Mara ta ce naji ta fara min ciwo" na amsa mishi.



Cikin kulawa ya fara min sannu.



Tashi nayi da niyyar tafiya dan in je in kwanta ko zan samu relief akan ciwon da mara ta take min.



"Ina zaki ne Zarah" Dr ya tambaye ni.



Amsa mishi nayi da cewa "Zan je in kwanta ne, na ji marar tana so ta matsa min".



Dr ne ya ce "Ayya, sannu Zaarah, jeki ki kwanta, za ki ji sauk’i in kika samu bacci".



D’akina na wuce naje na kwanta.



Abu kama wasa, tun ina jin ciwon marar a hankali har ciwon ya fara fin k’arfin tunani na.



Tunanin abin da yasa min ciwon marar na fara yi, gashi ba period d’ina ba ne zai zo ba re in ce shi ne ya haddasa min ciwon marar tunanin.



Tun ina iya daurewa har ta kai ga ba zan iya jure wa ba.



Yanda nake jin ciwon ne yasa hawaye ya fara zubo min a idanu na.



Rik’e mara ta nayi ina juye-juye a gado, a lokaci d’aya ina sai jero addu’o’i nake yi a raina ko zan samu sauk’in ciwon da nake ji.



Gani nayi jini ya fara gangarowa ta k’afa na, har wani guda-guda ne ke biyo bayan jinin.



Hankali na ne ya tashi ganin jini na gangaro wa.



A iya tunani na wannan ba jinin mensturation ba ne saboda yadda yake zuba.



Dr ne ya shigo d’akin ya same ni a halin da nake ciki.



Da sauri ya k’araso ya d’ago ni.



Jiki na ne ya saki saboda wahalar da na sha.



Cikin rud’u Dr ya ce "Zarah me ya same ki haka ba ki kira ni ba".



"Ciki na da Mara ta ciwo suke min Dr" na fad’a cikin galabaita.



"Sannu Zarah, insha Allah za ki samu sauk’i kin ji" Dr ya fad’a cikin tausayawa.



D’auka ta yayi ya shigar dani Ban d’aki.



Sai da ya gyara ni kana ya kai ni side d’in shi ya bani taimakon da ya dace a matsayin shi na likita.



Magunguna ya bani nasha kana ya min da allurar bacci.



Cikin d’an lokaci k’ank’ani bacci yayi awon gaba dani.



Sai da na kwashe sama da awa biyu sannan na farka daga baccin da nake yi.



Dr na gani zaune a kusa dani, alamu na nuna yana jiran farka wa ta ne.



Dr cikin tausayawa ya kalle ni ya ce "Sannu Zarah kin tashi, ina ne yake miki ciwo yanzu".



Cikin sanyin murya na ce "Mara ta ce har yanzu take min ciwo".



"Zai daina ne a hankali, bari in had’o miki tea ki sha" ya fad’a yana mik’ewa.



Bayan fitar Dr ne na fara tunanin jinin da ya zuba a jiki na, sai dai abin da yake bani mamaki shine tun da na sha maganin da Dr ya bani na fara ciwon marar na da ciwon ciki, tambayar da na yi ma kaina shine me ya had’a maganin typhoid da zubar jini wanda ya haddasa min tsananin ciwon mara da ciwon ciki.



Kau da wannan tunanin nayi a raina na barshi akan cewa may be maganin da Dr ya bani ya min k’arfi ne, shi ya haddasa min ciwon.



Dr ne ya dawo ya zauna rik’e da cup d’in da had’o shayi a ciki wanda ya sha madara a ciki.



A baki ya dinga bani, sai da yaga na sha ai yawa sannan ya k’yale ni.



Haka Dr ya wuni ya na bani kulawa ta musamman.



Waya yayi da Farida akan ta yi mi farfesun kayan ciki da girki ta kawo bani da lafiya.



Wajen magrib sai ga Farida ta kawo farfesun da tayi da fried rice da ji hanta a ciki.



Haka Dr ya matsa min na ci abinci duk da ban jin dad’in baki na.



A kwana biyu na samu sauk’i, sai k’arfin jiki na ne bai dawo dai-dai ba

Har a lokacin ban san ‘bari nayi ba.



""""""""""""""""""""""""""""""



Yau yaya Khalil ne yake zaune a falo d’auke da Amatur-Rahman a hannun shi.



Anisa ce tazo ta zauna kusa dashi tana sakar mishi tattausan murmushi.



Shima murmushin ya maida mata.

"yaya Khalil sannu da hutawa, na barka kai kad’ai".



"Kar ki damu k’anwa ta, nasan uzuri ne yasa kika barni ke kad’ai dan kin je ki mana delicious food d’in nan naki da yake sa ni santi".



 Fuskar tace ta yalwatu da annuri jin yadda yaya Khalil ke yaba mata.



Mik’a mata Amatur-Rahman yayi wacce ta fara kuka.



Amsar ta tayi ta fara jijjiga ta.



Kallon ta yayi cikin tsokana ya ce "babyn nan wai rigimar wa tayi ne, ni dai nasan ban da rigima".



Dariya tayi ta ce " Nima dai ban da rigima, ina jin rigimar Antyn ta tayi".



Shima dariyar yayi ya ce "Wace Antyn ta d’in".



Anisa ce ta ce "Kai wa kake tunanin nake nufi in ba Fatima ba".



Yaya Khalil ne ya ce "Sai yanzu nima nasan in da tayo rigimar, amma a ‘bangaren kuka ke tayo dan ki fi Fatima saurin kuka, tsiwa ce dai Fatima ta fi ki".



Murmushi Anisa tayi kana ta ce "Ina missing d’in Fatima, yaushe za ka kai ni gurin ta in wunin mata".



"Ki bari ran weekend sai in kai ki" yaya Khalil ya fad’a.



"Allah ya kaimu, amma yaya Khalil rashin haihuwar Fatima yana damu na, nasan haihuwa lokaci ne, sai in ga itama tana son haihuwa yanda take ma Amatur-Rahman in muka had’u, in na mata maganar sai ta nuna min ba ta damu ba, a yadda na fahimta ba taso a san ta damu ne, rashin haihuwar na damun ta" Anisa ta fad’a cikin nuna damuwar ta.



Yaya Khalil ne ya ce "Allah ne bai kawo mata haihuwar ba, in lokaci yayi sai ki ga ta haihu, ki ci gaba da taya ta da addu’a, Allah ya kawo mata masu albarka".



"Amin yaya Khalil, Allah ya amsa addu’ar mu" cewar Anisa.



"Amin Anisa" yaya Khalil ya amsa mata.



Da haka suka ci gaba da hirar su cikin so da kulawa.




 Bayan four month na sake jin canji a jiki na, wannan karan ban da zazza’bin da nake fama dashi da amai da nake yi, ga yawan bacci sannan ga kwad’ayi da yawan cin abinci da nake yi.



Ni da kaina na fara zargin ko ciki ne dani saboda na ga wasu alamomi na masu ciki a guri na.



Bayan Dr ya dawo ne na kai mishi ruwa yayi wanka kana ya fito ya shirya ya zo ya zauna akan dinning table naje nayi serving d’in shi dan ni na riga na ci nawa.



Lokacin da ya gama cin abincin ne muka dawo falo ya zauna a kujera yana kallon tauraron d’an adam.



Jikin shi nazo na kanta ya fara wasa da gashin kaina da na mishi gyara na musamman tare da turarurruka masu k’amshi na kai.



Ban wani jima a jikin shi ba bacci ya fara d’auka na.



Cikin kulawa Dr ya ce "Kwana biyu na ga alamar ba kya jin dad’i, ban san me yasa ki ke ‘boye min rashin lafiyar ki, ko kin manta mijin ki Dr ne".



"Ni kaina Dr ba zan ce ga in da yake min ciwo ba, ina dai jin jiki na so weak da fever, ni abin da yafi matsa min Dr shine yawan baccin da nake yi da kuma cin abinci da nake ci akai-akai ga kwad’ayi" na fad’a cikin shagwa’ba.



Tak’aitaccenn murmushi yayi kana ya ce "Kar ki damu, na zo miki da magani, bari in je in d’akko sai in baki ki sha".



Side d’in shi ya je ya d’akko maganin ya dawo d’auke da ruwa a hannun shi.



Maganin ya bani na sha, sai da ya bari maganin ya bi jiki na kana ya kwantar dani a jikin sa.



Bacci ne ya d’auke ni saboda daman baccin nake ji.



Cikin bacci naji ciwon mara ya ziyarce ni a lokaci guda.



Ba shiri na farka daga nannauyan baccin da ya d’auke ni a jikin Dr.



Tashi nayi na zauna ina rik’e mara ta tare da fad’in "Wash Allah! Mara ta".



Kallo na Dr yayi kana ya ce "Ya kike jin ciwon maran".



Kuka na fara yi saboda yadda nake ji na ce "Dr ba zan iya fasalta maka yadda nake jin ciwon marar ba, sai dai ina jin ciwon kamar na lokacin baya da nayi san da ka bani magani na sha, Dr ka taimake ni".



Rik’o ni yayi ya fara lallashi na ganin yadda na rik’e mara ta da nake ji kamar za ta fashe saboda ciwo.



D’auka ta Dr yayi da niyar kaini d’aki, jini ne ya fara gangarowa kamar wancan karan.



Da sauri Dr ya k’arasa dani band’aki ya gyara ni, ko da muka fito daga band’aki jinin bai daina zuba ba.



Duk wani taimako da Dr zai bani yayi iyakar k’okarin shi amma jinin bai tsaya ba, hakan yasa ya d’akko min hijab d’ina ya sa min.



D’auka ta yayi ya sani a motar shi muka nufi kangiwa hospital inda yake aiki.



Taimako na gaggawa aka bani tare da taimakon Dr, a k’arshe dai sai da aka min wankin ciki.



Nan na tabbatar da cewa ‘bari nayi.


Wajejen yamma Dr ya d’akko ni muka dawo gida.



Ni kad’ai nasan yadda naji san da na tabbatar da cewa ‘bari nayi, na sa rai da wannan cikin da na samu dan a yanzu baabin da nake fata da ya wuce in haihu, sai gashi Allah yayi ikon shi a kaina.



Tun da muka dawo gida nake faman kuka, duk lallashin da Dr ya min bai san a daina kukan ba, a yadda na fahimta shi Dr bai nuna damuwar shi akan ‘barin da nayi ba.



Kallo na yayi ya ce "Wai Zarah kukan me kike yi ne haka, duk lallashin da na miki bai ishe ki ba, ko akwai inda yake miki ciwo ne" ya k’arasa maganar da tambaya ta.



D’ago kaina nayi na kalle shi na ce "Dr yanzu laifi na kake gani dan nayi kuka, cikin da na dad’e ina burin in samu Allah ya bani a lokacin da ban yi tsammani ba, sai gashi Allah ya amshi kyautar da ya min amma ka ce ba zan yi kuka ba" na k’arasa maganar da k’ara sautin kuka na.



Jawo ni jikin shi yayi ya ce "for God sake miye amfanin kukan nan da kike yi, ni ban ga abin d’aga hankali ba dan kin yi ‘bari ba, at any time Allah zai iya baki wani, ba na so ki dinga d’aga hankalin ki akan k’aramun abu".



Janye jiki na nayi daga jikin shi na kalle shi cikin ‘bacin rai na ce "Dr miscarriage d’in ne k’aramin abu? In a gurin ka k’aramun abu ne, ni a babba na d’auke shi, daman na ga ba ka nuna damuwar ka akan ‘barin da nayi ba".



"ya kamata ki fahimce ni Zarah, you have to take patient tun da haka ya faru, har wani dad’ewa muka yi da aure da za ki sa kan ki a damuwa dan kin yi miscarriage, mu d’auki k’addara tun da Allah yayi babyn mu ba zai rayu a womb d’in ki ba" Dr ya fad’a.



Kasa ce mishi komai nayi saboda takiacin da maganar shi ta sa ni, nasan ci gaba da zama na a gurin ‘bacin rai da haushin abin da Dr yake fad’a min zai k’ara min matuk’ar Dr ba zai taya ni jimamin abin da ya same mu ba na miscarriage d’in da na samu ba.



Tashi nayi na bar mishi gurin na wuce d’aki na.



Ranar ma a d’akina nayi kwanciya ta dan har yanzu ban daina jin haushin rashin caring d’in da bai nuna min ba akan miscarriage d’in da nayi, ban san me yasa Dr bai son in haihu da wuri ba, ya d’auki halin turawa ya sa ma kanshi, dole ba zai nuna damuwar shi akan rashin haihuwa na ba.



Ganin ban zo d’akin shi ba yasa ya biyo ni muka kwanta a d’aki na.



Haka ya dinga fad’a min sweet words masu kwantar da hankali akan in cire damuwar da nayi akan miscarriage d’in da nayi.



Duk wannan maganganun da ya fad’a min jin shi kawai nake yi, da na gaji da sauraren maganar da yake fad’a min na lumshe ido na kamar mai bacci, hakan yasa yayi shiru shi ma.



Da haka bacci ya d’auke ni.



Washe gari Dr ne ya ya turo Farida akan ta taya ni aiki kasancewar jiki na ba k’arfi.



Momin Dr ce ta kira ni ta min ya jiki kasancewar Dr ya fad’a mata abin da ya same ni, ta ce in ta dawo daga aiki za ta zo ta gaishe ni, da haka muka yi sallama da ita.



Na kira Ummu na fad’a mata nayi ‘bari, ta nuna jajantawar ta gare ni saboda ita ma a yadda na lura ta damu da rashin haihuwa ta, ba tason yi min magana ne dan kar ta d’aga min hankali.



Da daddare Momi tazo da Hanan sun duba ni tare da jajanta min, ta kira Dadin Dr ta ba ni muka gaisa dashi shima ya min ya jiki kasancewar ba ya gari.


 

Anisa ma da Anty Jiddah sun kira ni a waya sun min ya jiki.



Cikin kwana biyu na samu sauk’in jiki na, hakan yasa na tashi na fara aikace-aikace na, na gyara d’aki na.



Bayan na gama ne na tafi side d’in Dr na je fara mishi gyara.



Ina cikin gyaran ne na tafi ‘bangaren wardrope d’in shi na fara jera mishi gogaggun kayan shi, a nan na ga wasu pills a cikin kwalin maganin ya ajiye su a cikin wardrope d’in.



D’aukar maganin nayi na karanta amma ban gane ko na menenen, sai dai maganin yayi kala d’aya da wanda Dr ya bani.



Maida wa nayi cikin wardrope d’in na ci gaba da aiki na.

Zuciya ta ce take ta sa min tunani akan maganin nan, zuciya ta sai bani shawara take yi akan in yi bincike akan maganin saboda yadda sau biyu ya saukar min da ciwo da ciwon mara had’e da zubar jini wanda har ya kai ni ga zuwa asibiti.



Iya tunani na, maganin da Dr ya bani ya min k’arfi a jiki na ne shi yasa na ke samu wannan matsalar.



Ina gama aikin nayi hanyar fita, maganin ne ya k’ara fad’o min a rai na, hakan yasa na koma na bud’e wardrope na d’akko maganin.



Zama nayi a bakin gado na bud’e data na sa sunan maganin a google.



Bayani ne akan maganin da yawa suka nuno min a site d’in, hakan yasa na bud’e d’aya daga ciki.



Bayanin da na gani akan maganin shi yayi barazanar d’auke numfashi na, sai da na d’auki tsawon mintuna biyar ban san a wani hali nake ciki ba.



Da k’yar na jawo jarumta na ara ma kaina na dawo cikin natsuwa ta.



Dan kar in gasgata zuciya ta yasa na k’ara shiga wani site d’in amma duk bayani d’aya yake zuwa min dashi.



Abin da bayanin ke sanar dani cewa wannan maganin zubar da ciki ne da na gani a wardrope d'in Dr wanda yake bani a matayin maganin typhoid.



Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo min daga idanu na.



Abu d’aya ne yazo min a raina shine maganin da Dr ya bani ba typhoid ba ne kamar yadda ya ce min, maganin abortion Dr ya d’auka ya bani da hannun shi na amsa na sha da kaina saboda yardar da nayi mishi da soyayyar da ke tsakanin mu.



"Me yasa Dr zai yaudare ni ta wannan hanyar, me yasa Dr zai raba ni da gudan jini na da nake son gani, me yasa Dr zai min sakayya ta irin wannan hanyar bayan yasan yadda nake so in samu ciki?" Na tambayi kaina.



Zuciya ta ce ta bani amsa da cewa yayi hakan ne dan bai shirya ma haihuwa ba kamar yadda yake fad’a.



Tunano lokutan da ya bani magani har sau biyu nayi, yanayin da na tsinci kaina a farkon maganin da Dr ya bani na zubar jini da ciwon mara kenan hakan na nufin miscarriage nayi kenan, hakan bai ishe shi ba sai da ya k’ara bani maganii a karo na biyu ya k’ara ‘barar min da ciki.



"Ashe daman so na iya zuwa da cutarwa?" Tambayar da nayi ma kaina kenan.



Tambayar da ya kamata a ce da kaina na gano amsar ta amma ban da halin yin haka saboda halin da nake ciki.



Kenan shi yasa bai nuna damuwar shi akan halin da na shiga ba lokacin da nayi ‘bari.



Wani irin ‘bacin rai ne na ji ya ziyarce ni a lokacin.



"Inna lillahi wa inna ilaihir raji’iun" na dinga ambata a raina daboda in samu sauk’in halin da na ke ciki.



Ba abin da a yanzu nake buk’ata da ya wuce dawowar Dr.



A yadda nake jin zuciya ta zan iya fito na fito dashi dan ba zan bari ya nakasa min rayuwa ta ina kallon shi ba saboda tunanin shi ina son shi.




Post a Comment

0 Comments