TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 41

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕

Page 4️⃣1️⃣

_______

Basu ƙarasa gida ba tayi masa murmushi tace, "Ya Abi-deen dan Allah muyi ordern abinci, I'm exhausted bazan iya girki ba!" Daurewa kawai tayi tareda yi masa maganar amma ji take kamar zuciyarta zata fashe, murmushi yyi mata tareda ɗaga mata kai, a nearby Eatery yyi masu ordern abinci sannan suka wuce gida, suna isa ta sauka duk ta kasa sakin jiki ta wuce bathroom tayi wanka, da towel ɗaure a jikinta ta fito nan ta tarar da Abideen zaune a gadonta yana jiranta, alamar tazo yyi mata da hannunsa, da kyar ta ƙarasa gurinsa jikinta a sanyaye ta zauna a gefensa. Jan ta yyi ta faɗa jikinsa nan ya fara shafa gashin kanta kafin yace, "Me yake damunki? You look stressed" Zaro ido tayi ta kalleshi amma daga ganin ido yasan tayi kuka da ta shiga bathroom, murmushi kawai tayi masa tace, "Ba abunda ke damuna kawai kaina ne yake ciwo!" Yasan kawai ta faɗi haka amma tabbas wani abu yana damunta, kuma daga gani yasan faking smile takeyi dan ya riga ya gama karantar ta har ta yanda bata tsammani.


 Shima murmushin yyi mata yace, "I'm always here for you, just tell me idan abu yana damunki.." saurin girgiza masa kai tayi tace, "Babu komai fah.." ita kanta bata ji daɗin ƙaryar da tayi masa ba amma ya zata yi, shafa kanta yyi ya miƙe ya fice daga ɗakin, tabbas yasan abu ya faru a school amma baza ta gaya masa ba dan yafi kowa sanin taurin kai irin nata, part ɗinsa ya koma ya watsa ruwa sannan ya shirya ya koma parlournsa ya zauna, wayarsa ya ɗauko daga table ya kira wani number, ba'a ɗauki lokaci ba aka ɗauka, murmushi Abideen yyi yace, "Class Rep!" Dariya kaɗan Class Rep yyi tareda cewa, "Ina wuni babban Yaya!" 😳🤭


Ranar da Abideen yyi masa duka yasa an kaishi asibiti aka yi masa treatment kuma aka kai shi gida, daga nan Daniel yake faɗawa Abideen cewa ai suna fama da halin rayuwa dan da kyar Class Rep yake iya biyawa kansa kuɗin makaranta ga mahaifiyarsa tsufa ya kamata, ciyar da kansu ma yana wahalar dasu, nan ne Abideen ya ɗauki Class Rep mae suna Waleed scholarship har sae ya gama karatun pharmacy a makarantar sannan ya bashi jari ya buɗe ƙaramin pharmacy duk akan zai riƙa bashi report akan Safeerah. 🙉💔


Bayan sun gama gaisawa ne Abideen yace, "Meya faru ne yau, naga mutumiyar ranta a ɓace!" Shiru yyi yana sauraran Abideen kafin yace, "Da yake an cire ni a Class Rep bayan abunda ya faru, the day before yesterday anyi submitting assignment, nace sabon Class Rep ya faɗa mata bansan ko ya faɗa mata ba and bata zo school ba ranar da akayi submitting. Sae yau taje office ɗinsa, possibly dan tayi submitting amma sae ta fito ranta a ɓace ta wuce Office ɗin President!" Zaro ido Abideen yyi yace, "Senate building?" "Eh, amma an chanza President yanzu wani ne aka ɗaura, nan ta fito dai ranta a ɓace kuma bata yiwa kowa magana ba" sallama suka yi inda Abideen yace idan ya samo wani labari akan Professor da President ɗin ya kira shi.." da haka ya kashe wayar, yana fita daga part ɗinsa ya ganta tana cin abinci akan dinning table cikin sanyi kamar ba ita ce lively matarsa dake sa shi farin ciki ba.


****


Zaune Abideen yyi yana jiran fitowar Safeerah amma yaji shiru kuma ya kira wayarta ba'a ɗauka, yana cikin jira a parking space ɗin makarantar ne Waleed ya kira shi cikin sauri yace, "Babban Yaya nayi tambaya naji wasu mata na cewa Professor ɗin nan yana neman mata and Madam tana Office ɗinsa a yanzu ta koma submitting assignment ɗinta.." bae ƙarasa ba Abideen ya kashe wayar, wani rawa jikinsa ya fara saboda tsabar ɓacin rai, wani kalar bugawa zuciyarsa take yi kamar zata fashe ta fito saboda ɓacin rai, wani dunƙula yyi wa hannunsa, ta ke jijiyoyin kansa da hannayensa suka fito raɗa raɗa, cike da fushi ya fice daga motar ya nufi office ɗin Professor Tasiu, kowa basa hanya yake yi ganin yanda ransa a ɓace ga idanu sunyi jajaye kamar ɗan kwaya. Tsaye Safeerah tayi jikin bango tana ƙanƙame jikinta, veil ɗin da tayi rolling ne a hannun Prof, matashin lecturer dake ji da jini a jika ga ilimi amma rashin mutunci da neman mata yyi masa yawa amma yau ya nemo wa kansa jaraba. 😝🔥


Abideen na locating Office ɗin Prof Tasiu ya wuce bakin ƙofar, kasancewar a ƙarshe office ɗin yake ga gurin shiru ba mutane sosai hakan yake bashi freedom ɗin lalata yaran jamaa, Abideen na zuwa ya doke ƙofar office ɗin da ƙafarsa nan ƙofar ta wangale, wani sarawa kan Abideen yyi ganin matarsa an maƙale a bango ana mata fin ƙarfi, wato akan matarsa Prof zaiyi lalata to zai kwame ba'a haife sa ba. Tsaye Abideen yyi yana ganin yanda Safeerah tayi kaca kaca kana gani kasan dole ake ƙoƙarin yi mata, ɗankwalin kanta ya zame ga mayafinta a hannun Prof, ga wuyar rigarta a farke har ana hango saman manyan boobs ɗinta, idan akwai abunda yafi ɓaci toh ran Abideen yyi gaba dashi, har waji jiri yake gani saboda tsabar kishi da bala'in ɓacin rai, Prof ne ya juyo ya kalli Abideen yace, "Uban waye yake damuna? Kai meya shigo da kai.." bae ƙarasa ba maganar ba hannun Abideen ya burma cikin bakin Prof, baka ganin komai sae jini da sauri Prof ya kai hannunsa kan bakinsa ya tare jini nan ya taro harda haƙora biyu, wani ihu yyi inda bae ƙarasa ba wani naushin ya koma masa akan hanci, zama daɓas Prof yyi kan table yana taɓa jinin dake fita daga fuskarsa. 


Safeerah kuwa ganin mijinta yazo sae ta gudu daga bangon ta koma bayan mijinta tana rirriƙeshi cikin tsoro da kaɗuwa, juyawa Abideen yyi ya fusge mayafinta daga hannun Prof ya rufe mata gashi da ƙirji da shi, juyawa yyi ya kalli Prof rai a ɓaci ya bugi table ɗin da ƙarfi yace, "Meya kai hannun ka jikinta?" Dariya Prof ya ɓare baki zaiyi aiko Abideen ya kai masa naushi, takaici ma yasa ya fara kai masa naushi ta ko ina, tun Prof na tarewa har ya gaji, tsayawa Abideen yyi yana huci yaji Safeerah tace cikin muryar kuka, "Ya taɓa ni da hannunsa.." taune haƙora Abideen yyi nan ya fara dube dube, katakon da ake rubuta sunan lecturers na kan table ya ɗauke ya kamo hannun Prof yyi smashing, wani ihu Prof yyi amma hakan bae sa Abideen yaji tausayin sa ba. Sae daya huce takaici har ya kai ga Safeerah ta fara kamo rigarsa kan ya bari kar ya kashe rai a school yasa shi kyale Prof amma Prof ko motsi baya iya yi, sae jini kaca kaca ya ɓata masa kaya, shima Abideen ɗin hannayensa duk jinin ne kamar yyi kisan kai, rai a ɓace yace, "Daga kanta baza ka sake taɓa wata mace da sunan lalata ba" gyara wa matarsa mayafinta yyi suka fice inda ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa tana matsar kwalla. Suna isa mota hawayen data danne suka fara zuba, jawota yyi ta faɗa kan ƙirjinsa nan ta fara kuka mae shiga zuciya, tausayinta yaji sosai sae a lokacin ya tuna cewa yaga message ɗin Class Rep kuma ya goge. 


Lallashinta yyi sannan suka wuce gida, a parlour tayi zaune a gefensa still bata dena kukan ba, shafa kanta Abideen yyi yace, "Kiyi shiru haka banason kanki yyi maki ciwo.." yana ƙarasawa ya fara ƙoƙarin janta jikinsa, fusge jikinta tayi tace, "I feel so dirty.." kallonta yyi yace, "Meya sa?" Matsar kwalla tayi tace, "Wani ba mijina ba ya taɓa ni.."  hannu tasa tana goge hawayenta nan Abideen yace, "Kiyi haƙuri, at least I came on time." tashi tayi ta wuce bathroom tayi wanka, ko da ta fito rarrashinta ya cigaba dayi, ahaka dae tayi ta maƙale masa har dare. Can around 11 suna kwance a gadon Abideen tace, "Thank you Ya Abideen" murmushi yyi mata yace, "Kiyi haƙuri laifi na ne har haka ta faru ranar naga text ɗin.." hannunta tasa kan lips ɗinsa tace, "Ko da na gani it won't make a difference, laifi nane da na kai kaina Office ɗinsa da baka je on time bah..." wani kukan ta sake fashewa dashi inda Abideen yyi ta faman rarrashinta, haka ta koma masa kamar wata ƙaramar yarinya inda yyi ta fama da ita, ya wahala ba laifi...😅


~~~~


Follow me on Wattpad @_khanoum_


©️Fateemah MG




Post a Comment

0 Comments